Chapter 14 of 45
ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA
ZUCIYAR ALIYU CE.
♪♦Fatima Zarah Shamsuddeen
♪♦Ramlat Ikram Ibrahim Lele
@YMA DUTSE
PAGE 25
Nihal tana tsaye a jikin motar su driver yana ciki a zaune hangen ta inda zata ga Zarah ta 6ullo take yi amma babu alamarta gashi ta barsu suna jiranta kamar wanda tayi shanya d'an tsaki taja tana sake kallon kofar shiga school amma dai labarin d'aya ne ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa ta bud'e mota ta aje takardun hannunta da handbag d'inta sannan tacewa driver.
"Dan jira na shiga na duba inda tayi kamar fa ciki naga ta koma" kai ya d'aga yana cewa "ok madam ba damuwa" wucewa tayi tana shiga cikin school d'in ita kad'ai sai magana take "wanne irin iskanci ne a gurin Zarah yarinya rashin ji yayi mata yawa kullum sai ana jiranta kamar wata uwar mutane"? Ganin datai har 6anfmgaren da take karatun taje bata nan yasa ta dawo tana cewa.
"Wai bata dawo ba"? Kai driver ya d'aga yana cewa "ban ganta ba bari na fito mu gani" d'an tsaki Nihal tayi tana kallon lokacin da driver shima ya tafi yana d'an hahhangawa ko zai ganta ita ma wani gurin ta sake shiga ta duba ta nan ma babu ita fitowa tayi a lokacin Shareef yayi parking da motarsa zai shiga gurin ya ganta farko yayi tunanin tare da yayanta Ammar take sai kuma yaga ita kad'ai ce yana so zaiyi magana mai muhimmanci da yarinyar nan amma sai ya fara samun Ammar d'in tukuna yana daga cikin mota yana kallonta kuma yaga yadda take waige-waige alamar akwai abinda take nema kamar zai fita yaje inda take sai kuma ya fasa yaci gaba da zama a cikin motar.
Baby da Badiyah su na tsaye a gurin da Nihal ta shiga su kuma za su fito da alamar abu suka siyo hannun su ri'ke da ledoji ta'be baki Badiyah tayi tana kallon inda Nihal take tace "kinga irin 'yan 'karyan nan haushi suke bani kiga dai wancan budurwar yadda ta saka glass saboda iyayi sai wani sham 'kamshi take sai kace 'yar gwamna kuma maybe idan kika bibiya 'yar talakawa ce aron kayan take yi dan tazo ta burge samari" juyawa Baby tai tana cewa "a Ina kika ganta"? Da hannu ta nuna inda Nihal ke tsaye zaro ido waje Baby tai tana cewa "wancan ai yarinyar da Shareef yayi fushi dani a kanta ne".
"Waye Shareef kuma"?.
"Wani guy ne a hospital d'in mu yake masifar jin kansa tayi yawa a kanta nake ta faman binsa Ina bashi a ha'kuri amma ya'ki ya saurare ni bari naje naci uwarta kona huce takaici na" ta fad'a tana shirin fara tafiya da sauri Badiyah ta ri'ke ta tana girgiza mata kai tace "a'a kada kiyi haka bana son abun jawo rigima wannan ba girman ki bane" fisgewa tayi tana cewa "ke wallahi sai naje naci ubanta maybe idan nayi haka ta kiyaye ni a gaba".
Nihal kam bata lura da su Baby ba hankalinta yana kan Zarah data fito tare da wata 'kawarta taga ice-cream suke je siya ba komai ba suna karasowa ta soma mata fad'a "haba Zarah me kike yi haka kinsa hankali na ya tashi dama nan kika taho siyan ice-cream kuma maimakon ki fad'a min kika barni nayi ta neman ki"? Ta'be baki Zarah tai tana cewa.
"Akan me zan fad'a miki sai kace wata uwata dole sai nace miki na tafi siyan ice-cream yanzu da kika ganni dashi ai ya baki amsar tambayar ki ko"? Kai Nihal ta jinjina tana kallon ta tace "bansan yaushe kika koyi raini ba amma bari muje gidan wallahi saina had'a ki da Yaya Ammar yayi min maganin ki" tana rufe baki Zarah ta murgud'a mata baki tana gatsinin ta ran Nihal a 6ace ta d'aga hannu zata mareta a fuska hannu Zarah ta saka za ta tare marin kawai bata sani ba ta buge glass d'in dake fuskar Nihal ya fad'o kasa da sauri Nihal ta sunkuya tana laluben ta inda zata ji glass d'in ta d'auko jin bata ta'bo shi ba yasa tace.
"Zarah ki d'auko ki bani baza kizo ki mi'ko min ba" tsaye Zarah tai tana gefe tana kallonta ta'ki magana Shareef dake cikin mota tsananin mamaki ne ya kusan sumar dashi ganin da glass d'in ya fad'i tana laluben sa alamar bata gani kenan sai dashi dama ciwon ido take shiyasa yake yawan ganinta a hospital, baki Badiyah dake tsaye ta bud'e tana kallon su ganin yadda Nihal ta gigice yasa tace.
"Ayya Allah sarki ashe bata gani saida glass d'in ni kuma har nayi mata muguwar fassara astagfirllah Allah na tuba bari naje na d'auka na bata wannan 'kanwar tata anyi mara kunyar yarinya" ganin da Baby tayi zata tafi inda Nihal take yasa ta ri'ke ta tana cewa "wallahi baza ki taimake ta ba na tsane ta bana son ganinta da nasan zan had'u da ita bazan zo gurin nan ba" da mamaki tace.
"Haba Baby ke fa musulma ce sannan taimako take nema".
"Ai ba a wajen ki take neman taimakon ba ko ke kad'ai ce mai rai a gurin".
"Ni banyi la'akari da kowa da yake nan ba zanje na taimake ta Allah yana taimakon bawa ne matu'kar bawan yana taimakon d'an uwansa musulmi kin gane"? Kai Baby ta girgiza tana cewa "ban gane ba" zaro ido 'kawar tayi da mamaki zatai magana suka ga Shareef wanda basu san da zuwansa gurin ba sakamakon bada motar sa ya fito ba ta Mami ya d'auko da sauri suka ga ya fito daga cikin motar ya karasa ya d'auka ya saka towel ya goge yace.
"Kar'bi" ya fad'a yana kara Mata a hannunta kar'ba tayi ta mayar dashi idonta tana sauke ajiyar zuciya tace "na gode" kai ya d'aga mata zai juya tace "amma kamar kaine wanda nayi wa laifi a hospital kwanan baya ko"? Jin abinda tace yasa ya kalleta yana girgiza yace.
"No baki min laifi ba ki saka a ranki kece da gaskiya bayan wayarki data 6aci wanne rashin gaskiyar za'a baki".
"Shikenan na gode".
"Karki damu" yana fad'in haka ya koma ya kulle motarsa ya shiga gurin ko lura da baby baiyi ba wacce tsananin rud'ewa ta kama ta ita kam Nihal tana ganin ya bar gurin itama ta juya ta fita domin Zarah tun ganin datai yazo ya d'auki glass d'in da gudu ta bar gurin saboda kar Nihal ta saka glass d'in taga tana nan ta'ki mi'ko mata.
A mota ta samu Zarah sai kallonta take bayan ta shiga bata kula ta ba har driver ya tu'ka motar suka bar gurin suna zuwa kuwa sukai sa'a Daddyn su yana nan a parlor Nihal ta tsaya bayan ta gaisar dashi tace "Daddy daga yau warewa Zarah nata driver da zai ri'ka zuwa d'auko ta domin na gaji da halinta tun ina dannewa yau ta kaini bango".
"Me ya faru"?.
"Wai Daddy yarinyar nan ta buge min glass ya fad'i tana ji ina ta 'kwalla mata kiran tazo ta mi'ko min ta'ki sai wani saurayi ne ya taimaka min".
"Subanallahi ita Zarah d'in"?.
"Eh Daddy wallahi na gaji da halinta na rashin ji bazan iya ba kawai a samar mata wanda zai ri'ka d'aukar tsiyar ta amma bani ba".
"Ok na fahimta ina ita Zaran take"?.
"Ana yin parking da motar ko bari ya kashe batai ba ta bud'e murfi ta fito ta kofar baya ta shigo part d'in mu".
"Shikenan yanzu tashi kuje kuyi wanka da sallah kuzo kuci abinci ita kuma nida ita ne ki rabu da ita zanyi maganinta sannan daga yau driver na shine zai ri'ka kaita" murmushi Nihal tai cikin jin dad'i tasan ko ba komai an wuce gurin tunda har Daddyn yace haka tasan idan zai tafi gurin aiki tare zasu tafi ya sau'ke ta haka idan an tashi zai tura driver ya d'auko ta ya dawo da ita gaskiya bazata taji dad'i ita kad'ai ba amma tunda haka ta za6a shikenan.......................
ZUCIYAR ALIYU CE...............
YMA DUTSE JIGAWA VNTRS.
.................PAGE 26
Su Afifah suna zaune a parlor gaba d'ayan su harda Afif daya dawo daga gurin aiki ko part d'insa bai shiga ba saboda ya d'ebo yunwa yana zaune tare da su Momy ana zance suka ji sallamar Amirah kowa zuba mata ido yayi harta karaso ta zauna Momy ta fara gaisarwa sannan suka gaisa da Afifah sauran ma suka gaishe ta.
"Fati tashi ki d'aukowa Amirah lemo da cup man" to Fati tace tana mi'kewa shiru Amirah tai so take ta tambaye su ina Aliyu kuma tana tunanin ta yadda zata tambaya d'in da kamar a bedroom suke su kad'ai zata iya tambayar Afifah.
Har Fati ta d'auko juice da kofi ta kawo mata bata sani ba saida Momy tayi mata magana sannan ta dawo daidai cikin hayyacinta amma data zuba ma kur6a d'aya tayi ta aje tai shiru kallonta Momy tayi cikin kulawa ganin ta d'an rame kad'an tace.
"Amirah ko baki da lafiya ne"? Kaita d'aga a sanyaye muryarta a hankali tace "wallahi nayi zazza'bi kwanan nan shiyasa yau ma a kwancen nake kawai dai cewa nayi bari nazo na gaishe ki saboda na d'an yi yawo jini na ya tsinke".
"Kin kyauta kuwa ni da naga shiru-shiru ma baki dawo ba nasa Afifah ta kira ki kika ce lafiya kalau kina dawowa shiyasa daga haka na bar batun".
"Eh a lokacin nayi tafiya ne naje Abuja gidan Aunty Fadeelah ban dad'e da dawowar ba na fara zazza'bin kuma asma ta ta tashi".
"Ayya babu wanda ya sani ai da za'a je a dubo ki kuma baki kira Afifah kin fad'a mata ba Allah ya 'kara sau'ki".
"Amin" Amirah tace tana kallon Afifah tayi mata magana da ido kaita d'aga tana mi'kewa suka hau stairs tare bedroom d'insu suka shiga akwatin Amirah dake aje Afifah ta d'auko tana kawo mata zama a gefen gadon Amirah tayi tana zuge zif d'in ta soma fito da kayan tana cewa "dole idan na koma na baiwa mai yi mana wanke ya d'auraye min su saiya goge min sun d'an yi 'kura".
"Wai nikam Afifah ina Aliyu ne naga motarsa a parking space amma kuma naga an rufeta da rigar rufe mota ko ya koma ne"?.
"Eh ya koma bai kira ki ya fad'a miki ba"? Shiru Amirah tai tana kallon waje daya daga baya tace "taya zai fad'a min ban sani ba sai yanzu dana kasa ha'kura na tambaya amma ko ba komai ya kirani kota waya ne ya fad'a min nayi masa fatan alkhairi".
"Maybe zai kira ki daga baya" Afifah ta fad'a tana dariya numfashi Amirah ta sauke tana cewa "wanne irin zai kira ni tun da bai kirani ba sanda ya tafi sai yanzu ya dad'e fa da tafiya ko"?.
"Ya dad'e man dama ai ba wani dogon hutu ya d'auka ba sai ranar daya sake dawowa kuma" kai Amirah ta kad'a tana cewa "Allah ya dawo dashi lafiya" daga haka bata sake cewa komai ba ta fara kad'e kayanta tana linkesu tana mayarwa cikin trolley Afifah kuma ta shiga wanka sakamakon lokacin tafiya islamiyya ya kusa sanda ta fito Amirah harta gama ta rufe akwatin da wayarta a hannunta tana dubawa jiran Afifah tai ta shirya ta saka hijab d'in islamiyyar da nikaf ta d'auki jakarta sannan suka fito tare ganinta da akwati yasa Momy cewa.
"Wai tafiya dashi zakiyi shikenan kuma na d'auka kinzo ki d'an yi mana sati d'aya ne"?.
"A'a wallahi Momy zan dawo nayi muku satin amma ba yanzu ba".
"Ok to mun gode ki gaida maman naki".
"To Momy insha Allahu zata ji" kallon Afifah Momy tayi tana cewa "Afifah kiwa driver magana ya kaita" kai Amirah ta girgiza tana cewa "a'a da mota nazo tana harabar gidan".
"Ok to ba damuwa ki gaida gida" to tace suna fita tare da Afifah ita ta shiga motarta Afifah kuma ta fita daga gidan har tayi tunanin zuwa gidan su Zainab ta gani ko bata taho islamiyyar ba sai kuma ta fasa ta wuce kawai saidai tana shiga ta hangota suna tsaye tare da wata suna zance murmushi tai bayan ta karasa tayi musu sallama d'age nikaf d'in tayi tana kallon Zainab tace.
"Hajiya zee zee ikon Allah kin shigo islamiyyar ma bazaki cire nikaf d'in nan ki d'an huta ba"? Kaita girgiza tana cewa "Afifah bazan iya cire nikaf a ko'ina ba saidai a gidan mu balle nan islamiyyar ba maza ne"? Dariya tai tana cewa "da maza man amma ai ba ruwan su da hakan".
"Waya fad'a miki babu inda shed'an baya zuwa ya haddasa fitina shiyasa nake kokarin kare kaina daga shiga fitinar tasa" kai Afifah ta jinjina daidai ya sayyadi ya shigo da littafai a hannunsa fuskarsa fal da gashi irin na ustazai yasha jallabiyya da rawani a kansa yana karasowa suka dur'kusa suna gaida shi amsa yai yana cewa.
"Malama Zainab Abdullahi ki shiga ajin da kike koyarwa ki kar6i hadda" kaita d'aga cikin ladabi tace "to sayyadi insha Allah" saida ya wuce sannan suka mi'ke da yake ajin su Afifan take koyarwa nan suka shiga duk su ukun saida ta fara kar'bar haddan kowa ya biya tukuna sannan tayi musu sabon d'ori suna biyawa har akai kiran sallar la'asar kowa ya fita zasu yi alwala Afifah dake tsaye bayan ta gama alwalar ta baiwa Zainab butar taje ta d'ebo ruwa a famfo ta dawo ido ta zuba mata taga yadda zatai domin kullum haka ake fama bata son aga fuskarta ko kad'an tsayawa tayi ta duba gabas yamma kudu arewa ganin ba namaji a cikin malaman islamiyyar sai zallar mata yasa ta cire nikaf d'in ta mi'kawa Afifah wacce tayi dariya tana kallon yadda fuskarta tata take dad'a wani irin yellow tsabar sabon saka nikaf kaita jinjina tana cewa.
"Allah mai iko kenan kowa da kiwon daya kar'be shi wai makwafcin mai akuya ya sayi kura" mi'kewa Zainab tai bayan ta shafa addu'a tace "ke kuma dawa kike wannan karin maganar"? Ta fad'a tana kar'bar nikaf d'in ta mayar kai Afifah ta girgiza tana cewa "dawa nake kuwa banda ke"?.
"Ni kuma da nayi me"?.
"Da naga kina wasu abubuwan da suke bani mamaki".
"Haka ne"? Da kyau muje kar a shiga sallar muna nan" Zainab ta fad'a tana d'aukar carbinta data aje a gefe ta mayar shi yadda yake a yatsarta ta zura shi sannan suka wuce bayan an idar da sallar kowa ya koma cikin aji aka ci gaba da karatu sai da rana tayi sanyi sosai jikin magriba daidai lokacin tashi ya sayyadi ya le'ko yace tayi musu addu'a sai gobe kuma.
Addu'ar tayi suka shafa sannan d'aya bayan d'aya suka fara fitowa suna fita daga islamiyyar saida kowa ya tafi ya sayyadi ya tura gate d'in ya rufe shima ya nufi hanyar anguwar su.
AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE.
J.W.A
Yusrah Musa Abubakar
@♠Y♠M♠A♠ DUTSE
PAGE 27
Zainab tana shiga ta tarar da Umman ta a kofar kitchen tana zaune akan kujera tana mulmula tuwon shinkafa shiga d'aki tayi ta aje jakarta ta cire nikaf da hijab d'in sannan ta fito tayi mata sannu da gida ta kama mata aikin ita kuma Umma ta mayar da hankalinta kan miya saboda kar Abba ya dawo daga gurin sana'a bata gama ba lokacin anyi kiran sallar magriba Zainab ta saka dukkan tuwon a cooler ta saka murfin ta rufe ta tashi taje tayi alwala ta shiga d'aki bata sake fitowa ba saida taji sallamar babansu ya dawo ta fito tayi masa sannu da dawowa ta koma bayan isha tana zaune a d'aki Umma ta le'ko tana cewa.
"Zainab kizo ki d'auki abinci man" kaita d'aga mata tana cewa "ina zuwa Umma wannan atamfar nake so na karasa yankawa gobe idan Allah ya tashe mu lafiya dana dawo daga makaranta saina fara d'inkin ta" sakin labulen Umma tai tana cewa "to shikenan gashi nan dai a d'aki ni gurin Hajiya zanje" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa cike da fargaba ta fito tana cewa.
"Me zaki yo acan"? Umma dake kokarin saka hijabi tace "bani kad'ai bace taron matan gidan ne gaba d'aya bansan me ya faru ba" numfashi Zainab ta sauke tana cewa "Allah yasa alkhairi ne" daga haka bata sake cewa komai ba har Umma ta fita ita kuma ta koma d'aki samun kanta tayi da kasa ci gaba da yanka atamfar duk jikinta yayi sanyi tasan kiran nan ba kiran alkhairi bane Allah yasa ba akan Umma ko baban su abun zai 'kare ba shiru ta zauna har Sameer ya shigo ganin kofar ba kowa yasa yace.
"Zainab".
"Na'am Yaya Sameer" ta fad'a tana fitowa kallonta yai ganin yadda fuskarta ta nuna alamun da akwai damuwa yace "ina yan kofar suke"?.
"Suna gurin Hajiya".
"Gurin Hajiya kuma me take musu"?.
"Wallahi Yaya Sameer ban sani ba amma dai naji Umma tace taron na duka gidan ne".
"Na duka gidan har yaran gidan kenan"?.
"A'a nufi iya su matan gidan dasu Abba".
"Ok na fahimta yau me aka dafa"?.
"Tuwon shinkafa ne"?.
"Da wacce kalar miya"?.
"Miyar ganye" "ok" kawai yace yana wucewa ya shiga d'akin sa ita ma nata d'akin ta koma kafin Umman ta dawo.
Batun su Umma suna can sun hallara maza su uku mata su shida Hajiya tana zaune daga kan kujera su kuma suna 'kasa a zaune kowa yayi shiru suna sauraron su ji dalilin da yasa ta tara su kallon su Hajiya ke yi d'aya bayan d'aya kafin tayi gyaran murya tana cewa.
"To jama'a salamu alaikum" amsa mata sukai "wa alaikum salaam" kafin taci gaba "nasan wasu daga cikin zasu yi mamakin me yasa na tara ku anan wasu ransu bai so ba amma ni na zama ciwon ido zama dani sai mai ha'kuri ba wani abu ne yasa na tara ku magana ce akan 'ya'yan ku dama ku kanku wanda yaji hukuncin da zan yanke baiyi masa ba sai yakai ni hukumar kare hakkin d'an adam tunda naga so kuke kuna kallo 'ya'yan ku su maida mana gida gidan karuwai to wallahi baku isa ba 'ya'ya sun kawo mizanin aure sun zama gird'a gird'a kamar shanu kuna kallon su kun 'ki ku tsaresu su fad'a muku gaskiyar samarin su na kwarai yau zan kawo karshen komai ta kanka zan fara kai Habibu kaine babba a gidan nan kuma kana samun kud'in da zakaiwa 'ya'yanka kayan d'aki meyasa ka barsu kara zube ka'ki musu aure"?.
Ajiyar zuciya Habibu ya sauke yana