Chapter 16 of 45
ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA
"Yaya Sameer ne ya kawo min".
"Sameer kuma ina taki wayar"? Numfashi Zainab ta sauke tana cewa "d'azu bayan fitar ku anguwa ta fad'a ruwa shine na bashi ya gyaro min kuma daya dawo maimakon na ganshi da tawa sai yace wai baza ta gyaru a yau ba amma ga wata" da mamaki Umma tace "ga wata kamar ya siya miki yayi"?.
"A'a wai wanda ya siya min makaranta ne ya bashi kud'in ya siya min" zaro ido Umma tai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un wai dan waye wannan me miki wadannan abubuwan meyasa Sameer bazai fito fili ya fad'a miki ba wannan abun ya zarta hankali bari naje na kaina gurin nasa naji abinda yake faruwa" ta fad'a tana d'aukar hijab ta kar'bi wayar a sanyaye Zainab ta kalle ta tana cewa.
"Yana chemist fa" Umma data gama saka hijab tace "eh ai can chemist d'in zanje" fita tayi ta bar Zainab shiru a d'aki ta rasa me yake mata dad'i.
Umma kam da saurinta ta fita daga gidan kana ganinta kasan hankalinta ba'a kwance yake ba a lokacin da taje tayi sa'a kuwa shi kad'ai ne ba kowa da sallama ta shiga tana aje masa wayar tace "Sameer waye ya siyawa Zainab wannan wayar? Kace wanda ya siya mata makaranta ne haka ne"? D'an murmushi yayi yana d'aga kai yace "eh Umma haka ne d'azu wayar tace ta fad'a a ruwa na shiga gidan ta bani na kai a gyara mata acan yayi kirana a waya nace na kawo mata gyaran waya ne shine yayi transfer na siya mata wata na kawo mata nima da nasan idan nace wayarta ce ta 6aci zai zaice zai siya mata wata wallahi Umma bazan fad'a masa ba".
Da alamar tambaya Umma tace "to wai Sameer waye shi"? Shiru yayi ya rasa me zaice mata domin bai da amsa ita ma Umman ta fahimci hakan sosai shirun ya ratsa gurin can ya d'ago yaga yadda ta 'kure shi da kallon jiran amsa numfashi ya fitar a hankali yace.
"Umma aboki na ne kuma yana son Zainab ne amma yace baya so a sani yanzu sai ya tashi zaiyi auren zai zo ya bayyana mata kansa alkawari na d'auka masa cewa bazan ta'ba fad'a mata shi ba sai lokacin daya d'iba da kansa ya cika zuwa da kai yafi sa'ko sannan duk abinda da kika ga yana yi mata yace min bai saka hannu a cikin yi mata hidima ba shiyasa nake rasa abun cewa a duk lokacin da Zainab ta tare ni da tambayar waye shi dan Allah Umma kiyi hakuri bazan iya fad'a miki shi ba saboda alkawarin dana d'auka masa insha Allah yana nan zai zo gare ku" tunda ya fara magana jikin Umma ke rawa har ya kai karshe waye wannan yake son Zainab a ina yake dama sonta yake?..............
Kai ta girgiza tana sau'ke ajiyar zuciya mai 'karfi tace "kuma Sameer idan lokaci yayi ya bayyana tace ba ta son sa fa shine abun damuwar"?.
"In sha Allahu Umma Zainab ba za ta 'ki ba saboda ina da tabbacin hakan ba za ta ta'ba juya baya ba za ta amince masa shine ya dace da rayuwar ta" kad'a kai Umma tayi ba tare da sanin abun dafawa ba tace "shikenan Allah ya rufa asiri ubangiji ya za6a mana abinda ya fi alkhairi a rayuwar mu bari na koma kawai" tana fad'in haka ta juya ta bar chemist d'in sansanyan numfashi Sameer ya fitar bayan ta tafi ya kira Aliyu.
"Marshall akwai matsala fa dama na fad'a maka in dai na siya mata wayar ne dole zata nemi sanin waye kai kuma gashi hasashe na ya tabbata yanzun nan Umma ta bar chemist d'in nan tazo jin waye ya siya mata".
"Kuma ka fad'a mata"?.
"A'a taya zan fad'a mata bayan alkawari mu kai dakai cewa kaine da kanka zaka fad'a mata kuma saina karya maka alkawari".
"Yanzu ka fad'a mata wani abu ta yadda zata fahimta ne"?.
"Eh nayi mata kyakkyawan bayani nasan ta yarda kuma idan ta koma gida zatai wa Zainab bayani ita ma zata fahimta".
"Ok yayi ina so ne saita gama school d'in idan ta samu offer ta fara aiki saina fito mata da maganar son ta sannan koma menene sai ayi kawai".
"Allah ya yarda Aliyu muna godiya"..
"Karka damu kaina nake wa domin ko me Zainab zata zama dai muna tare idan na aure ta sai ranar da kuka ganta idan na 6oye ta duk ranar da tazo gida baza ku gane ta ba saboda yadda kamannin ta zasu canza tayi kyau akan wanda take dashi ta 'kara haske tayi 'kiba sosai" dariya Sameer yayi yana cewa "Allah yasa Marshall zan fi kowa jin dad'in hakan wallahi har na matsu lokacin nan yayi Zainab ta zama matarka".
"Na fika damuwa da hakan Sameer yanzu maganar nan da muke da kai ji nake kamar nayi tsuntsuwa nazo na ganta kawai ko zuciya ta zata samu salama daga tafasa da 'kaunarta take yi".
"Lokaci ne yana nan zuwa".
"Haka ne dalilin da yasa bazan sake zuwa gida pass ba sai ta gama school d'inta".
"Ok tom Allah ya dawo da kai lafiya".
"Amin na gode Sameer" yana fad'in haka ya katse kiran murmushi Sameer yayi yana aje wayar a gefe daidai wasu mutum biyu sun shigo ya tashi yana kallon a yadda aka ri'ko d'ayan da gani baida lafiya sosai..................
JGW STATE.
ZUCIYAR ALIYU CE.
@YUSRAH MUSA
PAGE 29
Umma tana komawa a yadda ta bar Zainab a d'akinta anan ta dawo ta same ta tayi tagumi ta zubawa guri d'aya ido ko sanin tayi sallama ba tai ba saida ta kira sunanta sannan ta d'ago tana sau'ke ajiyar zuciya mi'ka mata wayar Umma tai tana cire hijab ta aje tare da zama ta kalle ta tana cewa "Zainab naje gurin Sameer yayi min bayani abokinsa ne yake miki wadannan abubuwan sannan yace min sonki yake amma ba yanzu zai bayyana miki kansa ki ganshi ba ni dai da ace akwai abinda zan iya yi gara koma waye ya fito mu ganshi tsoro na nan gaba Zainab kice bakya son shi bayan duk wannan d'awainiyar da yayi miki"? Shiru Zainab tayi ta kasa magana gaba d'aya bata san me zata ce ba waye abokin Sameer a ina yake duk iya zurfafa tunanin ta bata gano ko waye ba.............
"Zainab"
Numfashi ta fitar tana kallon Umma a sanyaye jikinta ba wani sauran 'karfi tace "na'am" ita ma Umman zuba mata ido tayi tasan tana cikin halin rud'ani ta yadda duk abinda zata fad'a mata ba lallai ta fahimce ta ba shiyasa kawai tace mata "tashi kije koma waye Allah yasa shine mafi alkhairi a rayuwarki idan babu alkhairi Allah kar ya shigo dashi cikin rayuwarki balle har a samu matsala nasan dama bazai wuce hakan ba domin ruwa baya tsami banza duba irin abubuwan da yake miki dole saidai so d'in ni kam Allah yasa kar Hajiya taji labarin siyo miki wayar nan tazo ta d'aga mana hankali" ita dai Zainab tari da bai kama ta ba bata yi ba 'karshe ta mi'ke ta fita daga d'akin tana jin yadda wani zazza'bin fargaba da damuwa ya lullu'be ta lokaci guda.
*** ** ***
Kwanaki sun sake ja lokaci yana ta tafiya abubuwa suna ta faruwa tun Hajiya tana fad'a da zage zage har tazo ta zuba musu ido taga iya gudun ruwan su so take su kaita bango rana d'aya ta fito tayi musu uwar watsi ta gigita musu lissafi daga iyayen har 'ya'yan nasu zata nuna musu duk abinda suke ji dashi nata yafi nasu idan rashin mutunci ne tun kafin a haife su ta iya idan wula'kanci da fitina ne ma duk saidai su biyo bayan ta.
Tana zaune ita kad'ai babu kowa Zain ya shiga gaida ita yana zama ko ina kwana bata bari yace ba tace "Zaidu d'aga idon ka ka kalle ni nan" da yake d'an zamani ne tar ya d'aga idonsa ya zuba mata taci "Zaidu kuna son gani kalata a gidan nan kuna son ganin rashin mutunci na zan gwada muku ni ba tsohuwar kwantu kwan bace" da mamaki Zain yace .
"Me kuma ya faru Hajiya"?.
"Au meya faru kake tambaya ta"?.
"To ya kike so nace Hajiya ke fa kina da d'orawa mutum laifi daga shigowa ta ko bari na gaida ke baki yi ba kin kama balbala min bala'i".
"Dan ubanka ni nake balbala maka bala'in"? Shiru yayi bai amsa mata ba taci gaba "batu nake akan maganar aure dana had'a ku kai da Zainab har yanzu tsabar raini banji tsinannan da yazo yace min ya amince a cikin ku ba"? Wani irin kallo yayi mata jin abinda tace lallai ma Hajiyan nan da neman rashin zama lafiya take ta'be baki yayi yana cewa.
"Ni dai banda ni a cikin su kiwa sauran dai amma ban da Zaid".
"Uban wa ka fi"?.
"Me kike nufi ni dai karki saka ni a cikin wannan shirmen banga mai yi min auren had'i ba wallahi".
"Sai ni dan ubanka".
"Kinsan Allah Hajiya bazan auri kowacce yarinya a gidan nan ba gara ma ki sani".
"Ni kuma saina aura maka in yaso ana shafa fatiha ka furta mata kalmar saki".
"Ai kuwa zan furta".
"Da naci 'kwal ubanka wallahi" kallon mamaki Zaid ya bita dashi ganin tunda ya zauna take masa zagi na tsamar nama yace "wai ke Hajiya dan Allah haka ake rayuwa ne ke haka akai miki auren dole ne ko me da kika matsa sai munyi gadon ki kike so muyi ko me"?.
"uban wa ya fad'a maka auren dole a kai min ni auren so nayi da kakan ku".
"Kuma mu kike neman 'ka'kaba mana abinda ba mune mukai ra'ayi ba"?.
"K'warai kuwa sakawa tace umarni na ne dole ka auri Zainab saina aura maka ita" kaiya jinjina yana she'kewa da dariya yace "waye zaki aurawa Zainab d'in amma dai bani ba"?.
"To da ubanka zan d'aura idan ba da kai ba"?.
"Caf lallai Hajiya wacce irin magana kike yi wannan mara dad'in ji kema kinsan abunda bazai yuwa bane wallahi. .
"Kuma dan ubanka ni kake cewa caf fad'a min dalilin da yasa baza ka auri Zainab d'in ba"?.
"Saboda babu soyayya tsakani na da ita kuma bayan haka ni ina da wacce nake so".
"Yar gidan uban waye a ina take"?.
"Yar gidan baban ta ce a sabuwar 'kofa suke da zama" yana rufe baki Hajiya tace "to wallahi bari kiji ko a gidan uwar wa take ba sabuwar 'kofa ba dole ka barta ka auri Zainab ko kuma ka had'a ka aure su duk su biyun ranar d'aya a cikin biyu ka za'bi d'aya ko rabuwa da wancan ko auren su biyun lokaci guda ina jin ka"? Ta'be baki yayi yana cewa.
"Ni bani da 'karfin da zan auri mata biyu rana d'aya dame zan ji da yi musu lefe ko da kud'in sadaki ko kuma gini na da ban 'karasa ba? Gaskiya bazan iya ba".
"To tunda haka ne sai ka bar waccan yarinyar ka auri iya Zainab domin gida bai koshi ba kaga ai baka isa ka d'auko mana yar wani gidan ka kawo ta ba so nake suma sauran su shigo nayi musu magana ku taru ku rufawa junan ku asiri idan ku 'ki humm abun bazai muku kyau ba".
"To wai Hajiya ni ban gane inda kika dosa ba meye hakan ne wai"?.
"Taya kuwa zaka gane abinda nake nufi ka tsaya kana min fitsara mara kunya kawai tashi ka bani guri kafin na buga maka wannan sandan" ta fad'a tana d'ago masa shi yasan ba 'karamin aikin ta bane ta buga masa d'in shiyasa bai sake magana ba ya mi'ke ya fita daga gurin Hajiya kofar su ya shiga a lokacin mamarsa tana d'aki yaje ya same ta.
"Lafiya naga ka shigo ranka a 6ace"? Yana daga tsaye ba tare daya zauna ba yace "gaskiya Mama bazai yuwu ba bazan iya wannan masifar ba zan nemi transfer aikina na koma kaduna kawai" jin abinda yace yasa ta kallon sa da mamaki tace.
"Saboda me zaka nemi transfer ana zaune 'kalau"? Bud'e hannu yayi cikin fad'a ya fara magana "ba kowa ba saboda Hajiya haka kawai daga na shiga gurin ta na gaisar da ita wai ta tsare ni da maganar aure dole saina had'a lefe na auri Zainab bayan ni ba sonta nake ba sannan tayi min girma sa'ata ce fa shekara ta ashirin da biyar ita da had'u dame na fita haka kawai za'a d'ora min aiki" zaro ido Asiya tai tana cewa.
"Meee Hajiyan ce tace kayo lefe ka auri Zainab"?.
"Eh man yanzu fa daga gurin ta nake fita zanyi amma wannan maganar data fad'a min yasa bana jin zan iya karyawa idan na fita shiyasa ma na dawo" a masife Asiya tace "kuturun ubancan akan wata shegiya zaka hana kanka sukuni wallahi bazai yuwu ba tashi kayi fitar ka babu wani transfer aiki da zaka yi sannan Zainab tunda baka sonta kar ka yarda su aura maka ita ko tsine maka zatai bazai bika ba dan naga Hajiya niyyar ta kenan idan kaci gaba da jayayya da ita".
"Wai taya ma zatai min haka nifa ina da budurwa 'yar sabuwar 'kofa ce kuma ita nake so ba wai Zainab ce bana so ba ni auren had'i ne bana ra'ayi".
"Ka daina wani 6ata bakin ka kana maimaita magana tunda baka so ba wani shege da zaiyi maka abi da baka ga dama ba ka manta da wata Hajiya ka daina tada zancen dan Allah yanzu nafi tunanin gigin tsufa ne yasa take yin duk wadannan abubuwan abinda za'ai kawai kayi wa babanku magana akai maka kud'in gaisuwa can sabuwar 'kofan kayi auren ka kawai shine magana ina ruwanka da wata Zainab yadda take ganin tana da ilmi gashi tana da hanyar samun kud'i ai raina naka arzikim zatai ko ka aure ta ba za ta baka daraja ba kayi tafiyar ka kaje ka karya ka manta da batun".
"Ok tom shikenan Mama hakan zanyi kawai a wuce gurin nayi maganin ta" yana fad'in haka ya fita Asiya da tabi kofar daya fitan da kallo tsaki taja tana cewa "wallahi indai ina raye babu wanda ya isa ka auri Zainab a gidan nan idan guguwa suke bu'kata ni masifa ce zanyi maganin duk d'an iskan da yake neman saka ka Zainab cikin rayuwar Zaid haba dan jaraba mutum da ransa da lafiyar sa a nemi hana shi ya sha'ki iska me kyau" ta karasa maganar tana jan tsaki ji take kamar ta tashi taje ta yiwa Hajiya magana akam takura Zaid da take sai kuma ta fasa domin tasan sharrin ta yanzu Habibu yana dawowa zata had'a mata bom abinda batai bama saita fad'a.
Ko da dare bayan sallar isha da Hajiya taga Habibu bai shigo ya gaida ita ba yasa ta saka akai mata kiran sa lokacin bai jima da dawowa ba ko wanka baiyi ba saboda gudun laifi yasa ya amsa kiran nata yana shiga da'kyar ta bari suka gaisa kamar wani zai riga ta tace "Habibu ashe har yanzu baku fi 'karfin 'ya'yan ku ba ace kamar ni Zaidu d'azu zai ciwa mutunci akan nace ya auri Zainab yana fad'a min wata banzar magana wai akwai wacce yake so 'yar sabuwar 'kofa ce"? Jin abinda tace yasa ran Habibu ya soma 6ata ya gaji da maimaita wannan maganar shiyasa yace.
"Hajiya dan Allah tunda duk yaran nan basa son za6in da kikai musu ki barsu kowa ya za6o da kansa a gani na hakan zai fi zaman lafiya dan wallahi idan kika matsa akai auren ba bazai yi 'karko ba babu jin dad'i kullum ana cikin sasanto da rabiyar fad'a ne" kai Hajiya ta jinjina tana kallon sa ya d'auka ta gamsu da maganar da yayi mata ne sai kuma yaji tace.
"Habibu kasan abinda kake fad'a kuwa na riga na yanke maganar auren nasu yanzu kuma ka zo min da batun wai wani Zaidu yana da budurwa kai ma abinda zaka ce min kenan baza kuyi abinda nace ba"?.
"Ba haka bane Hajiya su fa yaran zamani ne dan Allah ki barsu kowa ya samo matar aure kar ki matsa ayi had'in nan za'a samu matsala ba karama ba gaba ce abun ji muddin hakan da faru sai anyi dana sani akan gagarumar matsalar da zata faru a gaba".
"Matsala daga wajen ka kenan tunda naga alamar kaine baka so da ace ka tilasta masa ka nuna 6acin ranka ya isa ya tsalle maganar kane shi d'in banza amma kaima ka nuna baka bu'katar abinda nace shiyasa duk sauran ma suka juya min baya".
"Ba haka bane Hajiya anan ina iya bakin kokari na duk dan a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin mu dake da kuma 'ya'yan mu kamar yadda muke a baya amma indai kika matsa sai anyi auren nan wallahi ba karamin ya'ki da tashin hankali za'ai ba bama ga yaran ba harma da iyayen su mata tunda ba so suke ba kina kallo ranar da kikai maganar ba wacce ta yarda" yana rufe baki Hajiya tace.
"Duk tsinanniyar da bata so ku saketa ta bar gidan saita koma gidan su taje can tayi isar ta amma ba'a nan ba indai ina raye a wannan gidan ba shegiyar da zatai mulki" murmushin fitinar Hajiya Habibu ya saki ganin bata rasa abun fad'a ko za'a kwana ana zance yace "yanzu dai Hajiya me za'ai"?.
"Me za'ai kake tambaya ta Habibu me nake so ayi kuwa bayan wanda na fad'a ko Zaidu baya so sai ya auri Zainab kana kallo yadda suka bar yarinya ta lalace wai itace harda koyarwa ga wani sabon salon 'karya da suka d'auko har wata makarantar boko take zuwa labari yazo min wayar hannunta ma ta dubu d'ari biyu da hamsin ce uban waya siya