Chapter 6 of 10
AISHATUL MUBEENA Dama Ta Biyu by Miss Hafcy
bakiyi mana komai ba Iya wannan maganar ta
huce saboda ni tun d'ad'ewa da kika nemi
gafarata na yafe miki, dama ko baki nemi na yafe
miki zan yafe miki dan wallahi ni tamkar Uwa na
d'auke ki!" Ga wannnan ta aje mata bandir din
yan dubu d'aya(1) sannan tace "gobe insha Allah
zan aiko miki da sauran abinda kike buk'ata,
kuma insha Allahu za mu dinga ziyartar ki akai-
akai. Iya ta rik'e hannunta " Ma'u tsaya na fad'a
miki wani abu,, yau tsawon shekaru goma(10)
kenan ban sa Sule a idona ba, tunda yazo yace
min ya tafi birni cirani na nuna ban amince ba
amma sam ya k' jin maganata ya tafi ya barni, be
kuma waiwayata ba, ko yana da rai? Ko ya rasu?
Allahu a'alam,, amma dan Allah in Allah ya had'a
ku dan Allah ma'u ku yafe masa ke da Aiha
(Aisha), ki kuma ce nima na yafe masa, dan ina ji
ajikina kwanan ya kusa k'are da k'yar na k'ara
kwana a duniya ,nima ku yafe min Allah ya had'a
fuskokin mu a aljana..." ta fashe da kuka,,,,jikin
Umma da Mubeena yayi sanyi sosaii Mubeena tayi
dauriyar cewa "ni na yafe miki Iya, kuma ki dena
ambaton mutuwa insha Allahu zaki tashi, cuta ba
mutuwa bace! " Iya ta girgiza kai "kayya! Suka
mata sallama suna kuka tana kuka suka rabu. A
gidan Mama ne, Mama ta kwantar da murya
tayiwa Mubeena bayanin komai, Mubeena wani
sabon kukan ta sake Mama na rarashinta, taji
tausayin Ummanta sosaii sosaii ga wani sonta
dake k'aruwa a zuciyarta,, sannan kuma taji
tsanar Mal Sule a zuciyarta, ji take ba wanda ta
tsana sama dashi..godewa Allah tayi daya bata
uwa ta gari kamar Umma dan ita gani take tafi
kowa dacen uwa a duniya! Haka suka koma gida
dukkansu ba farin ciki da walwala.. ◆◆◆◆◆◆◆
Washe garin rana Allah yayi wa Iya cikawa,, su
Umma sunji mutuwarta sosaii a wannan dak'in
Allah yayi mata cikawa cikin dare. Da sassafe su
Umma suka tafi suna ta kuka abun tausayi
mussaman ma Mubeena, da 'yan gidan suka tafi
gabad'aya har da Abba, dan shima yaji mutuwar
dan ya santa, lokacin da 'aka kwantar da
Mubeena a asibiti da cutar polio ta sameta,,sai
da suka fara sauka a gidan Mama sannan sukaje
gidan marigayiya Iya,, a lokacin ma ko wanka
ba'a yiwa gawar ba, Umma da taimakon Mubeena
su suka wanke gawar tas aka samata likafani aka
fita da ita ,maza suka sallaci gawar aka kaita
kuhewarta , Allahu akbar Allah kasa mu cika da
imani, ka bamu kyakyawan K'arshe Ameen ya
Allah.. Ba wani zaman makoki akayi ba tunda wa
za'ayiwa gaisuwar? Dama Mal Sule ne kawai d'an
data haifa kuma baya nan bai san ta rasu bama,
'yayan mijnata kuwa Bashir da Hauwa sun dad'e
da dena kulata bama sa k'asar gabadaya. A 'yan-
uwanta kuwa ita kad'ai tayi ragowa duk sun
rasu,, sai dai sauran dangi da ba'a rasa
ba..Masa'udu dama shi ake yiwa gaisuwar dan
shine ya kula da ita tun data sami rashin lafiyar
har ta warke, shima kuwa a rannar data rasu
admission dinsa ya fito yaci Ahmadu Bello
unibasiti zaria(ABU zaria) dan haka ya had'a
kayansa ya tafi Umma kuwa kud'i me yawa ta
bashi tace yayi harkar makaranta dashi ya yafi
yana ta godiya.
[12:35AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:46AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [135]-[140] Bayan an
dawo hutun tak'aitacen lokaci. Aysha Amatulah:
to barkan mu da dawowa. Hajiya Mubeena shin
wai ta yaya kika tsunduma cikin harkar zane-
zane? Mubeena: To agaskiya nidai na taso ne
kawai na gani inayi, a lokacin inga abu ya min
kyau sai na zana shi, cikin ikon Allah kuma sai
kiga zanen ya fita sosaii...lokacin da ina primary
kuma in kika duba littafai na na arts zaki ga inaci
sosaii, koda merit za'a bada ma a Art ni ake
bawa. Kuma akwai Yayana Ya Ameen shine ya
cigaba da ban kwarin gwiwa har nazo matakin
danake yanzu. Aysha Amatullah: madalah, to
kafin ki fara wanan zane-zanen mene burinki a
rayuwa? Mubeena: Burin na da shine na zama
likita dan nima na bada gudunmawa ta wajen
yak'i da wannan cutar sai kuma Allah beyi ba.
Aysha Amatullah: to Allah zaba mafi alheri, meye
ya fi b'ata miki rai da kuma abinda yafi faranta
miki rai? Mubeena: Abinda ya fi b'ata min rai
guda biyu ne na d'aya ya shafi personal life dina,
na biyun kuwa shine, idan naga yan'uwana masu
wannan cuta ta polio suna bara ko kuma suna
cikin wani hali na rashin gata a gaskiya raina na
sosuwa kuma ina iya k'ok'ari na dan ganin na
taimake su. Sannan abinda yafi faranta min rai
shine, ina tuno irin nasororin dana samu a
rayuwa, sannan kuma ina ga masu irin cuta ta
wato polio basa fuskantar wani k'alubale a
rayuwa ,suna jin dadin rayuwarsu sannan suna
samin gata daga wajen iyayensu dama al'uma
baki d'aya, to nakan ji raina yayi fari . Aysha
Amatullah: Allah sarki, yanzu zamu d'auki waya
guda biyu(2) duba da yanayin lokaci, zaku turo
sak'o ne ta wannan lambar 064**** sannan zaku
kira mu ta 064****. Mutane an kira an mata
fatan alheri, an kuma turo sak'oni ba adadi.
Aysha Amatulah:wani kira zaki yi ga iyaye da
kuma masu cutar polio? Mubeena: kiran da zanyi
shine dan Allah iyaye su dinga bada yayansu a
dinga musu d'igon rigakafi, sannan iyaye su dage
su dinga gano talent din da suke dashi su
k'arfafa musu gwiwa, bawai su dinga barinsu
suna bara ba, da sauransu. Sannan irina masu
wannan cuta ta polio, ganin suna da nakasa kar
hakan yasa su fidda rai da rayuwa , su d'age suyi
karatu suma su zama wasu a dinga damawa
dasu, in hakan ya faru zan fi kowa farin ciki.
Aysha Amatullah: to duba da yanayin lokaci mene
sak'on ki na k'arshe? Mubeena: to Alhamdulilah
ba abinda zance sai in godewa Allah da kuma
iyayena nakan ji farin ciki sosaii in na tuno da
iyayena,yayena da k'anina, da sauran dangi.
Aysha Amatulah: to masu sauraron mu lokaci
yayi halinsa , anan zamu k'ark'are wannan shirin,
Hajiya Mubeena muna godiya da kika amsa
gayyatar mu, da fatan duk sanda muka sake
neman ki zaki amsa kiranmu. Mubeena: to nima
nagode masu saurarona da kallona ina muku
fatan Alheri,(tayi murmushi) sai anjima. Ahaka aka
gama shirin, ta fito driver yaja suka tafi.
*********** A yau ne aka d'aura auren Ameen
Muhammad Ameen da Fatima Adam, Aisha
Muhammad Ameen(Nana) da kuma Saifulahi
Abdalah. Ansha biki sosaii an kuma kashe kudi
dai-dai misali, Mubeena kuwa lemukan nan da'aka
bata kyauta su ta bada akayi hidimar biki da su,
sannan katuwar jaka da calanda me sunayen Allah
ta musu a matsayin gudunmawa sun sha murna
tare da yi mata addu'ar Allah ya saka mata da
alheri. Bayan biki aka kai amarya Nana gidanta
dake Hotoro, Sannan amaryar Ya Ameen Faty aka
kaita gidan ta dake Janbulo. A yau su Mubeena
sukayi final exam dinsu, sunsha kukan rabuwa da
dalibai, Mubeena da Asiya ma ansha kuka,
malamai sunyi bak'in cikin rabuwa da Mubeena
sosai , hadda masu kwala, bayan sunyi sharing
contacts driver yazo ya d'auki Mubeena suka
koma gida, Mubeena cike da kewayar dalibai,
malamai dama makarantar baki d'aya. Yau ta
kama rannar lahadi kuma dama duk Lahadin
k'arshen wata sukan je shopping... Suna cikin
mota dan zuwa shopping d'in Abba ne ke driving
dan yau yace sha'awar driving yake saboda ya
d'ad'e beyi ba, Umma na gaba, yayin da Husna,
Amir da Mubeena ke bayan mota Ummi kuwa taje
bikin 'yar aminiyata. Suna tafe cikin raha da
anashuwa. Can wata mota ta taho da gudun
gaske, dai-dai lokacin da wani datijjon mutum
yazo tsalaka titi, ai kuwa fuu motar ta bige shi,
bata ko tsaya ba drivern mota ya k'ara falawa da
gudu, cikin 'yan sakani aka dena hango motar sai
k'ura da motar ta tayar... shikuwa dattijon
mutumin nan yana baje a titi jini sai zuba yake.
Abba da sauri ya fito daga motar yana salati
suma su Umma suka fito dan ganewa idonsu, a
firgice suka k'araso wajen da mutumin ke kwance
cikin jini, Umma da ta k'araso wajen da sauri,
dora idonta akan mutumin keda wuya ta kwala
wani k'ara anan ta fad'i k'asa sumamiya!
Lik
[11:47AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [130]-[135] Nan take
wajen ya d'auka sai ihu akeyi su Husna dake gefe
sai dariya suke yi dan sunsan Mubeena yau ta
shak'i haushi itada ko hannunta bata san wani
namiji ya tab'a, sai gashi yau k'aton arne ya
d'aga ta, shikuwa Ya Abdul ji yake kamar yaje ya
wankawa Mr Mike mari dan haushi. Da kyar ta
samu ya sauke ta k'asa, ai kuwa sai tabar
wajenshi ta koma d'ayan banganren, sai
d'aukanta hoto ake. Certificate aka bata ta,
sannan aka buk'aci ta sa hannu taje ta saka kuwa,
sannan aka mik'a mata shi, bayan nan aka shiga
raba kyautuka ga wanda suka yi participating
kyauta kuwa ta samu kala-kala, kamfaanin wani
shahararen lemu ya bata da kuma sauran
participant's d'in kud'i da kuma lemuka, kyauta
dai iri-iri ta sha su wai kuma aka samun tab'i ne
dan ba'a bata babbar kyautar tata ba. Check na
miliyan d'aya(1) aka bata daga hukumar da suka
shirya gasar sannan kuma k'ungiya masu zane
dake kano suka bata kudi naira dubu d'ari(100).
Mr Mike ne ya d'auko wasu sarkok'in medal's
guda uku(3) 'yan k'anana d'aya na gold d'aya na
silver na ukun kuma na bronze. Ta uku ya rataya
wa bronze medal aka fara tafi ana d'aukan
hotuna, sannan ya kira Ahmad Huzaifa ya rataya
masa na silver, shima aka d'au tafi. Bayan nan
kuma wakilin gwamnati ya tabbatar mata da
cewa bayan ta kammala karatun sakandire
gwamntani zata d'auki nauyin ta taje tayi course
din zane a wata makatantar zane-zane(art school)
dake amurka(America) Na gold din kuwa
Mubeena ya ratayawa nan waje ya k'ara d'aukan
ihu 'yan jarida nata d'aukan hoto da kuma hoto
mai motsi(video) domin a yawancin kafafen yad'a
labarai ta talabijin abin live ake nunawa. Su Abba
dake zaune suna kallo LIVE murna a wajensu
kamar me, sun ma rasa me zasuyi saboda murna,
hak'k'ika wannan rana tana cikin rana mafi farin
ciki a rayuwarsu, mussaman ma Umma da
alk'warin da tayiwa Mal Sule ya cika yau, a
zuciyarta cewa take dama Mal Sule ya ji ko ya ga
wannan abin alherin. Bayan an kammala taro aka
rufe taro da add'ua, nan aka fara d'aukan hotuna
dasu Uncle Hashim da bakinsa ya kasa rufuwa
saboda farin ciki, su Ya Abdul ma haka, kana
ganinsu zaka gane irin halin da suke ciki. Zanen
kuwa tafiya Mr Mike zeyi dashi, inda za'a kai shi
wannan babban ART GALLERY dake Abuja. Su
Alhaji Bawa basu so hakan ba dan su sunfi san a
barshi a Art gallery din dake kano amma ba
yadda suka iya. Fitowar su Mubeena ke da wuya
wakilan 'yan jarida da gidajen radio sukawo mata
caa akanta, sai tambayoyi suke mata tama rasa
wadda zata amsa, can dai tace "Alhamdulilah ba
abinda zance sai godiya ga Allah da ya bani
nasara a wannan gasar, sannan ina godewa
iyayena da suka bani k'warin gwiwa har nazo
matakin dana ke yanzu! Nagode.". Tana gama
fad'an hakan tayi hanyar motarsu. Zwan ta keda
wuya ta tadda wakilan wani shahararen gidan TV
suna jiranta, numfasawa tayi tace "wannan shine
anyi gudun gara an tadda zago". Nan suka shiga
yi mata magiya akan suna so su tautana da ita
gobe, saboda gobe ne ta kama rannar masu
cutar polio da duniya wato (WORLD POLIO DAY)
wato ashirin da hud'u ga watan oktoba(24th
october) bata musu musu ba kuwa ta amsa sunyi
farin cika sosaii inda suka bata wani kati na
gayyata. Farin ciki ya dawo sabo sanda suka
koma gida su Umma hadda kukan murna, Ya
Ameen dake can k'asar holland ya sami labari
daya duba news ya kira su aka sha murna,
makarantarsu kuwa dayake tana final year suka ce
sun d'auki nauyin ta har ta gama su waec da
neco duk zasu biya mata, saboda ta fito da
sunan makarantarsu, bayan k'ananun kyaututuka
da suka bata. Yau ta kama 24th october(World
polio day), tun da safe ta ta shirya driver ya
kaita dan Ya Abdul ya tafi wajen aiki. Tana zuwa
dama ita suka jira, aka shirya komai tazo ta zauna
akan kujerar da za'a tautauna da ita.(wasu
gidajen radio suma sun juno dan masu saurarun
radiyo suma suji) Me gabatarwa ta fara:
Assalamu alaikum warahamatul lahi ta'ala wa
barkatuhu masu kallo da sauraranmu. Barkan mu
da sake saduwa a wannan shiri na mussaman da
muke gabatarwa duk a rannar polio ta duniya
duk shekara. A yau shirin namu yayi babban
kamu, domin yau zamu tautauna da AISHATUL
MUBEENA Muhammad Ameen, wadda itama ta
zamo polio victim ta farko tada fara lashe gasar
zane-zane dake gabatarwa duk bayan shekara
hud'u a jihohi dama k'asa baki d'aya... Sunana
Aysha Amatullah wadda zan gabatar da shirin,
Hajiya Mubeena ko nace Artist Mubeena barka da
zuwa. Mubeena: Barka kadai. Aysha Amatullah:
shin zamu iya jin tak'aitacen tarihin ki? Mubeena:
To Alhamdulilah, nidai sunana Aishatul Mubeena
Muhammad Ameen an haifeni a garin Kano na
taso a Kano, kuma a yanzu haka inada shekara
sha bakwai next year zan shiga sha takwas(18),
saboda ban fara makaranta da wuri ba yanzu dai
ina ss3 a sakandire. Aysha Amatullah: Masha
Allahu, shin kina shekara nawa wannan cuta ta
sameki? Kuma mene ne dalili? Mubeena: A
gaskiya wannan cuta ta same ni ina 3-4 years,
dan dama kinsan a yara masu shekara d'aya zuwa
biyar(1-5) tafi kamawa..kuma a gaskiya zan iya
cewa wannan cuta kaddara ce daga Allah, dama
can Allah ya riga ya rubuta cewa a haka zan
tashi, cutar zata same ni. Aysha
Miss Hafcy
Newer Post Older Post Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)
Saturday, 15 October 2016
Posted by MissHafcy at 08:01
AISHATUL MUBEENA 110-140
[12:33AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:51AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS A tak'aice dai ansa
rannar Ya Ameen da Faty, da kuma Aisha( Ya
Nana) da Saifulah nan da wata biyu(2) ,, Su
Umma kuwa sai shirye shiryen biki sukeyi.. Ya
Abdul kuwa har ya gama karatunshi Abba ya
samar masa aiki har ya fara yi dan haka ma ba
kullum yake zama a gida ba. Baiwar Allah
Mubeena kuwa tacan duk ta damu dan ta dad'e
da gane cewa tana son ya Abdul ! amma sai take
ganin abun da kamar wuya, na farko dai Umma
tace mata Abba ne babanta to indai har kuwa
Abba ne babanta to ba aure a tsakaninsu saboda
wanta ne uba d'aya kuma ba aure a tsakaninsu
k'anwa da wa.!.na biyu kuwa, tasan halin ya
Abdul shida ko magana bata shiga tsakaninsu sai
ta k'ure,, in ba kwanan nan dayake d'an sakar
mata fuska,,kuma tasan ma baze rasa budurwa
wadda yake so ba,,,,yadda yake d'in nan
tubarkalah gashi kuma d'an gayu,, doleh 'yan
mata suyi rububinsa... dan haka sai ta dinga
addu'ar Allah ya cire mata sanshi a zuciyarta,, a
kullum kuma tana k'ok'arin cire sanshi daga
zuciyarta,, dan a iya tunaninta ko da da aure a
tsakanin su, in ba wani ikon Allan ba,to ko a
mafarki baza ta tab'a zama matarsa ba,, Ita dai
kullum addu'arta shine Allah ya bata miji na gari
ya kuma zab'a mata mafi alheri Yau saura befi
kwana biyar (5) suyi gasar ba,kuma dama sun
gama exams an basu hutu, dan haka lokacin hutu
za'ayi gasar.. Mubeena na zaune a falo tana kallan
musab'akar alkur'ani da akasa a sunnah Tv,,
Umma ta fito daga d'aki cikin shirin fita unguwa,
Mubeena ta d'ago ta kalleta "Umma fita zaki yi
ne?" Umma tace "eh k'auye zani wajen Mama"
Mubeena da sauri ta tashi "Umma dan Allah nazo
muje? Na dad'e banga Mama ba" Umma tace to
maza shirya muje,kafin rigimaman nan yazo(Amir)
dama neman dalilin k'in zuwa islamiya yake yi"
Mubeena tayi dariya sannan ta shiga dakinsu ta
dauko hijab dinta ta bi bayan umma ,, suka yiwa
su Ummi sallama sannan suka nufi k'auye. Bayan
sun isa Mama tayi murna sosaii da ganin su,
bayan sun gaisa sun sha ruwa , Mubeena nakan
cinyar Mama suna wasan su na jika da kaka,
Mama ta kalli Umma," Ma'u kinsan IYA ta samu
mutuwar b'arin jiki kuwa? Gaban Umma ya fad'i ,
"subhanalahi,wacca iyan??" ta fad'a had'e da
dafe k'irji, Mama tace " Iya dai surikarki, wallahi
abun tausayi kuje ki duba ta dan Allah kullum
fad'i take a kirawo mata ke da yarki ta nemi
gafarar ku . Umma tace "Allah sarki Iya, a ina
take zaune? Mama tace "inda dai kika santa tana
nan' Mubeena dake kwance akan cinyar Mama da
sauri ta taso ta tsutsura musu ido ,, ta kalli
Mama tace"Mama wacce ce Iya?" Mama na
k'ok'arin magana Umma ta dakawa Mubeena
tsawa "bansani ba,dake muke magana,ban hanaki
sa min baki in ina magana ba?" Mubeena ta
sunkuyar da kanta , yayin da Mama tace "ke Ma'u
wai meyasa kike haka ne? Daga tambaya saiki
hayayak'o mata?" Umma tace "Mama haushi
taban ai manya na magana ta dinga sako baki,
bari na tashi naje na dubo ta"" ta tashi ta dauki
jakarta tana k'ok'arin saka takalminta, Mama ta
kalleta," Ma'u indai nina haifeki to ki tafi da
Mubeena" Umma ta juyo jiki ba kwari tace "to se
ki taso muje" bata jira amsar Mubeena ba ta sakai
ta fita, Mubeena da sauri tasa hijab dinta tabi
bayanta. Har suka iso gidan Umma bata yiwa
Mubeena magana ba, da sallama suka shiga gidan
amma suka ji shiru,, sai da sukayi sallama yakai
guda hudu(4) sannan suka jiyo wata dashashiyar
murya nacewa "Wa..alai..kum..us..salam...,k
u..shigo..mana,, Umma ta kad'a kai sannan ta
shiga dakin data juyo murya, Mubeena tabi
bayanta. Umma ta zaro ido saboda abinda ta
gani ya masifar tsorata ta, duniya kenan! ... IYA
ce kwance akan wata yagalaliyar tabarma duk tayi
fitsari akai, dakin in banda zarni ba abinda yake
yi. Umma a firgice ta k'arasa wajen Mubeena ta
bi bayanta, Iya ta k'are musu kallo sannan tace
"Wannan kamar Ma'u nake gani kodai mafarki
nakeyi? Umma ta runtse idonta sai hawaye 'Nice
Iya!" Iya ta fashe da kuka "kece Ma'u ! ashe rai
kanga rai? Ina jikar tawa take?" Umma ta nuna
Mubeena "gata nan, tare muke ma" Iya ta k'ara
fashewa da kuka "zo nan 'yar jikalle ta, ni bansan
ma da wani ido zan kalle ki ba, randa aka haife ki
nida mahai....." Umma ta da sauri ta katse ta "Iya
komai ya wuce dan Allah a bar zancen nan baki
yimin komai ba ni kuma koda kin min ma na yafe
miki, garin yaya kika sami wannan ciwon?". Iya
tana kuka tace "rannar ina zaune ni kad'ai a daki
naji mage a gefena, kinsan dama ina tsoron mage
,to tun daga nan na tsorata sosai bakina ya juye
magana ma na kasa yi, hannuna ma na kasa
d'agawa balle na d'aga kafata,, Haka na kwana
ina kuka bame ceto na,, washe gari makota da
suka ji shiru suka zo suka bud'e kofar aka fito
dani aka kaini asibiti anan akace mutuwar b'arin
jiki nasamu,,shine nake kwance anan masa'udu
(dan k'anwar iya) shine kawai yake kula dani,,, ta
sake fashewa da kuka,, Umma ta fashe da kuka
hakama Mubeena dama ga Mubeena da tausayi.
Iya ce ta katse musu kukan da cewa "Ma'u baki
fad'a wa jikartawa ni kakar ta bace ba? Dan daga
ganin alama bata san nice na....Umma ta katse ta
" Iya dan Allah ya isa haka, zancen nan ya wuce
banse tasan komai ba ai" Mubeena duk ta rikice
ta kasa gane maganar tasu, sun caja mata
kwakwalwa....Iya cikin dashashiyar murya tace
"Ma'u RANNAR WANKA BA'A BOYEN CIBI!
Like · 2 · Reply · Edit · 3 February
Khadija Muhamed
[11:52AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [105]-[110] Mubeena
ta shafa fuskarta" bakomai yusra Allah ya baki
lafiya" yusra ta rik'e hannunta "Amin",, sukai
musu sallama suka juya suka bar Maman nata
kukan murna k'aninta mu'az yazo shima murna
kamar me, ya dinga shiwa su Mubeena
albarka,,dama kudin reg din makaranta yake
nema ya cika dubu biyar(5000)amma ta gagara
sai gashi Allah ya share musu kukunsu. A mota ne
Umma ke ba ya Abdul labarin yarinya jaji
tausayinta sosaii shima ya kuma ji dad'i da'aka
musu wannnan taimakon..Suka aje Asiya a gida
suka mata godiya sannan suka koma gida. Kwanci
tashi ,gobe ne Mubeena da Nafisa zasuyi gasar
su, Mubeena tayi