Chapter 11 of 13
RIBAR BiYAYYA Daure da Iyali By Sawwama A
Bai rufe baki ba ta bude idonta tangararau sai kuma hawaye ya fara zarya a kumatunta matsowa jikin gadon fatima tayi ta rike hannunta tace sannu adda me kike so?
Matse hannun fatima tayi tana rintse idonta gaba daya suka karaso jikin gadon.
Cikin kuka tace baba don Allah ka yafe min ko zan dinga ganin da kyau mamah,hajiya, baba karami ku yafe min halin kuncin da na saka ku ko hakkinku zai sakeni in dinga ganin da kyau a rayuwata wallahi na tuba na tsani zama da Hameed.
Shafa kanta hajiya tayi tace ya isa haka kiyi shiru ba wanda yake rike dake ba hakkin dakw bibiyanki jarabawa ce kuma kowa da irin nashi ki roki Allah ya baki ikon cin jarabawarki aure kuma dole za a raba in akwai cutarwa.
Kiji tsoron Allah ki fada mana gaskiyan abinda ya hadaki da mijinki cewar mamah.
Lumshe ido tayi hawaye ya kara gangaro mata tace kawai ina zaune ya shigo dakina yana masifan in fito masa da kudin da na dauka a dakinsa tunda kab ni kadai na shiga dakin
Shiru tayi hade jan hanci tace nace mishi n ban dauka ba ai nima ana daukan min kudi kuma ban san waye ba.
Shikenan fah ya dinga jaraba ni dai ban kulashi ba sai da yace duk inda kudinsa yake in fito mishi dashi shine nace ni ban dau kudi ba dan haka ba abinda zan fio dashi shine ta fqrq mari na ni kuma nace Allah sai ya saka min shine yq rufenj da duka.
Sallati duk suka sa hajiya tace bai san kina da ciki bane cikin kuka tace ya sani mana ai daman ba kaunar ccikin yake ba ya faje da kudinsa ne kawai yayi sanadin cikin dan Allah na rokeku na san ni na zabi aurenshi amma ku taimakeni ku raba auran nan ta karasa magana tana wani irin kuka mai taba zuciya.....
SAWWAMA QAWWAMAπ
πRIBAR BIYAYYAπ
By Sawwama A.
Page 34.
*Aunty Haleema ban fa manta ba ta yaya ma za ayi in manta duk irin comments dinki* *wannan shafin naki ne kiyi yanda kika so dashi*
Kuka take yi mai tsuma rai hajiya na lallashinta har sai da ta samu nutsuwa.
Baba ne yace toh a tafi a bar fatima a wajenta tunda a farfado da sauri fatima tace ah ah baba na gaji kaina na ciwo dan tunda ta shigo asibitin daurewa kawai take amma warin asibitin ba karamin daga mata hankali yake ba.
Subhanallahi baby shine ba kiyi magana ba tun dazu da doctor ya dubaki ai cewar sageer.
Dan yamutsa fuska tayi tace ba fa komi bane na sam stress ne kawai.
Baba yace gaskiya ne yanzu su kuma ka kaisu gidq ita da hajiya su huta in yaso mamansu ta zauna da ita.
Hajiya tace wah ai ni in kaga na huta toh na gana da wannan na kusun uwar ku muje maza
Mama tace nima binku zanyi inje inyi girki in ya so charity ko susan wani ya zo ya zauna da ita.
Da wannan shawaran suka tafi.
Hajiya na ido hudu da Hameed duk da lillisa shi da police suka yi sai da ta kwakwade shi da jakan hannunta tana debe mishi albarka kuma ta nemi ya sakar mata diya.
Kuka yake sosai yana magiyan tayi hakuri amma laifi adeejata mishi kudinsa ta dauka
A zahirin gaskiya hameed nace adeeja ta daukan mishi kudine wanda ita kwata kwata bata san dashi ba zaliha ce duk ta hada tuggun nan.
Daga farko yaso ya bijire batun sakinta dan shi har ga Allah yana son matarsa da ta hakura da maganan haihuwa kuma bata sace mishi kudi da tafi ko wace morewaπ
Hajiya tace toh ai shikenan kar ka bamu takarda in munje can kotun musulunci ka bamu a can inda zasu cire mata sauran hakkokinta da jin haka ba shirri ya nemi biro da takarda ya rubuta mata saki daya shi da kanshi yake tausan kanshi na gwara ya rabu da ita zai ma fi samun nusuwa ya huta da wadannan jarabbabun yan uwan nata dan da alama wannan hajiyar da namiji ne da ya gane kurensa dan duk magana daya sai ta kai mishi duka.
ππππππ
Adeeja ta. Samu lafiyan jiki da na zuciya dan tunda akayi sakin nan taji kaman an sauke mata wani kaya mai nauyi.
Tabbasa saki bashi da dadi ko kadan haka yake a wajen iyayenta dauriya kawai suke amma suna tausayawa yarsu da kananan shekarunta an mayar da ita bazawara dadin abin ma ta taho da danta dan tace tana tsoron gurbacewan tarbiyarsa toj musulunci ma ta yarda ta taho dashi har sai ya balaga.
Hajiya cewa tayi da ita zata tafi ta huta kafin a san abinda hali zai yi nan aka bar muhd sani wajen mamah su kuma suka koma Bauchi.
Fatima kam sageer ya kasa gane kanta yanzu kam kinshi take gashi taki lafiya kullum cikin zazzabi take yayi yayi suje asibiti taki wai bata son warin asibiti.
Shi duk ya rasa ma dabarar da zai yi me gadine ke fada mishi akwai wata likita a nan kasan layinsu kadan lakuta da yawa itake karban haihuwan matan anguwan duk da basu fi shekara a nan ba.
Da sauri sageer yace baba dan Allah ka taimakeni ka kaini gidan. Baba mai gadi yace kar ka damh yallabai nan mijinta ke sallah ga la'asar ta iso yanzu zaka ganshi soja ne ba a dade da turo shi nan ba.
Suna zaune mutumin yazo wucewa masallaci baba me gadi ya nunawa sageer shi sosai mutumin ya mishi kwarjini
Bayan sun fito ne sageer ya mishi sallama ya ansa yace sunana sageer nike zaune a can gidan wallahi iyalina ne ba lafiya nayi nayi tazi muje hospital taki sai na samu labarin matarka likita ce dan Allah ko zaka min alfarma tazo ta duba min ita.
Murmushi mutumin yayi yace ba damuwa dan kanina barin karasa gidan in kawo muku ita Allah ya kara sauki ameen.
Da haka suka rabu mutumin na shiga gida ya fara kwala kiran precious ina kike your help is needed wata kyakyawar yarinya ce yar kimanin shekara biyar ta sha kwalliya cikin farar riga da pinki short skirt sai dogon gashin kanta da aka mata kalba manya manyan sunsha adon ribbon dan uwarta bata son sa mata beads wai yana da takura.
Dan tabe baki tayi tace daddy mimi tana sallah kayi hakuri kace ta bani ice cream din ko chocolate ba zan kara wasan ruwa ba.
Uwar ce ta fito sanye da hijabi tace ba za a hakuran ba wa ya koya miki wasan ruwan banda shi da rigimammun yayunki.
Karyar da wuya yayi yace yi hakuri precious miemie ya hada yanda yake kiranta da yanda yaran ke kiranta.
Hararan wasa ta galla mishi tace wa ke buqatan taimakone ? Oops i almost forget wasu amarene nake tunani kusa damu wai matarsa ba lafiya kuma taki zuwa hospital.
Gyada kai tayi tace ok bari in dauko box dina ke abeer dauko dress dinki ki saka ki zo muje tuni ta manta da batun ice cream anji yawo.
Nikab dinta ya dauko mata tare da box din ya daura mata nikab din yace kim san ina kishin wannan kyakyawan fuska
Matar da yarta ne suka shiga yyin da mijin ya tsaya a bakin gate fatima na kwance kanta bisa cinyan sageee suka ji sallama amsawa suka yi ba tare da sun canza position ba ganinta rike da box sageer ya gane wacece.
Da sauri ya mike ya sawa fatima pillow yana yiwa matar da yarta sannu da zuwa ya tambayeta me gidan tace yana waje yace toh ga madam din please kiyi kokarin gano min matsalarta barin je wajen oga a waje murmushi tayi tace kar ka damu aikina kenan
Bayan ya fitane fatima ta tashi ta gaisheta cike da faraa ta amsa mikewa tayi ta kawo musu abinsha ta hadowa yarinyan da ice cream ai tuni abeer ta fara murna girgiza kai kawai uwar tayi tace Allah yq shiryeki abeer.
Fatima tayi murmushi tace aunty me tayi she ia cute ba ruwanta da bakonta gata kyakyawa abinta aunty dake take kama? Dna Alah in gani cire nikan din matar tayi tana murmushi subhanllahi tinda fatima taje bata taba ganin mace mai kyaun nan ba.
Matar tayi mmurmushi tace sunana *zakiyyan yah rid* murmushi ta kuma yi ganin fatima ta kasa magana shi yasa yah rid ya nace ta dinga sa nikab
Tambayoyi tayiwa fatima nan take ta fahimci me ke damunta amma kqsancewan bata aiki da ka yasa ta bata dan bottle tace gobe in zan wuce hospital zan biyo in ansa fitsarinki kai ta gyada mata.
Muryoyin mazansu suka ji da sauri zakiyya ta sauke nikab dinta tacewa fatima maza jeki ki sanyo hijab.
Tashi tayi taje ta sanyo hijab tare da kawowa yah rid abinsha a nan suka zauna aka yi ta hira sai da aka yi mangrib suka tafi.
Washegari test din da akayi ya tabbatar da fatima na da cikin sati goma sha biyar murna a wajensu ba a magana a take suka nufi gidan hajiya dan gaya mata daddadan labari ai kuwa hajiya tayi murna dan rasa inda zata sa kanta tayi adeeja ma tayi tsananin farin ciki gashi tayi kyau ta murmure baza kace ta taba aure ba yanzu take da shekara 22 yayin da fatima ke da shekaru 19 so yarintan adeeja ya kara fitowa dama ku can kyakyawa ce abinta.
πRIBIR BIYAYYAπ
By Sawwama A.
Page 35.
πππππππππ?π?π
RUBUTACCEN AL'AMARI
*Na*
*Aysha Aliyu Garkuwa*
πππππππππ?ππ
Hakika ke din zakaran gwajin dafi ce ke zara ce a cikin taurari
Adda amm kasancewarki cikin duniyar marubuta babban alfarma ce ga makaranta ubangiji Allah ya kara daukaki ya dafa miki ya kuma baki ladan abinda kika isar inda kika kuskure kuma Allah ya gafarceki damu gaba daya.
ππππππππππ
Ummul
Hakika mutuwa na da ciwo amma babu abinda mamaci ke buqata da ya wuce adu'armu, damuwa, da saka shi a rai, ko yawan daga hankalinki da makusantanki bashi zai dawo miki da Hamma ba. Ki sani yarda da kaddara me kyau ko mara kyau yana daga cikin imani ki rungumi kaddararki hannu bibbiyu Hamma umar kam ya tafi kuma inshaa Allah tafiyar hutu ce a gareshi tunda kowa ya shaida yayi mutuwar shahada.
Allah ya kara baki hakuri ya jibanci lamuranki ko er kanwataπ
ππππππππππ
Usman
Hakika kai din jarumine a zahiri da kuma cikin littafin addana βΊ Allah ya kara mala jarumta da hakurin zama da ummul tamu ka sani rarrashi da kwantar mata da hankali shine naka da sannu komi zai wuce inshaa Allah. Allah ya kara muku son juna ameen yayana kuma dan tsoho kakana jauroπ
ππππππππππ
*Iyalan shuwa*
Ina kara mika muku ta'aziyata rabbi ya jiqan hamma ya kara baki hakurin rashinshi kyawawan halayensa su bisa amin Allah ya bawa mara lafiyan cikinku lafiya ameenπ
Fatima zaune gaban hajiya sai riritata ake yi hajiyar ce ta gyara zama tace fatima ki saurareni da kyau ban taba kin daya daga cikinku ba ta nunasu su biyun ita da adeeja
Ta cigaba da fadin ku din ya'yana ne ta yaya zan ki ku? Mu biyu Allah ya bawa iyayenmu bamu da yawa muma din sai kuma Allah bai bamu haihuwa da yawa ba har gwara ni nayi hudu shi yasa kika ga na matsu in ganki da ciki shi yasa kika ga na sa an raba auren Khadija saboda ganin mijin na neman kashe mana zuriya eh mana in ya kashe mata mahaifa ai har muma aabin ya shafe mu tunda ya hana zuriyar mu yaduwa ubangiji Allah ya rabaki da cikin nan lafiya kema kuma Allah ya fito miki da miji na gari kije kema ta hayayyfo mana jikoki dariya duk suka yi tace Allah ya muki albarka.
Sai dai me cikin nan ba karamin wahalar da fatima yake ba kaman jira yake yi a san dashi ciwi take yi sosai bata iya yin komi bata iya cin komi duk ta dawo abin tausayi hajiya taso a dawo da ita wajenta amma dake sun hadu da makwabta ma gari dr zakiyya tace kullum zata dinga zuwa dubata sai adeeja ce ta koma gidan dukda bat so ba amma ba yanda za tayi dan woosai take jin kunyan sageer kuma a duk lokacin da ta ganshi sai taji gabanta ya fadi.
Shi yasa bata tana fitowa sai ya tafi aiki fatima na lura da hakan sosai tausayin 'yar uwarta ke ratsata kullum cikin yi mata addua take yi
Sai da cikin ya kai wata bakwai ta dan sami lafiya shima ba sosai ba.
Sageer duk ya birkice inda kuka san shi ke dauke da cikin ko ciwon dole yasa ya ajiye koyarwan da yake yi a ATBU ya zauna zaman jinyarsa dan ba zuwa office dinsa na company dinshi yake yi ba ji yake kan ya dauko ciwon ya maida jikinsa.
Bangaren adeeja ma ba karamin tausayawa er uwarta take yi ba gaba daya ta fice hayyacinta bacci adeeja bata yi kullum tana cikin sallan dare tana rokanwa kanwarta afuwan wannan ciwon da abinda ita adeejan ke ji a zuciyanta.
Hajiya ma bata kwana biyu bata zo dubasu ba gashi dai lafiyan baby kalau amma uwar kullum cikin ciwo take in kaga fatima sai kun tausaya mata amma duk da hkaa ita ke kwantar musu da hankali kullum murmushi ne kwamcw a fuskanta tana nuna musu ba komi su kwantar da hankalinsu zata haihu lafiya.
Kamar ko yaushe hajiya tazo dubata dr zakiyya ma tana gidan dukkansu har sageer din suna palo sun sa fatiman a gaba ta samu taci abinci fir taki dauriya kawai take ti amma wani irin murdawa cikinta ke yi ga kafanta da ya rike shiru tayi dan bata son tayar musu da hankali.
Dr zakiyya ce ta lura da halin da take ciki tace anya fatima ba labour kike yi ba kuwa murmushi tayi wanda kina ganinshi kin san a fatar fuska ne kawai da sauri dr zakiyya tace da sageer dauko mota ka kawo bakin palon nan mu tafi hospital.
Cikin minti biyu ya dawo ya kinkimeta duk da girman cikin dukkansu suka dunguma suka tafi asibitin.
Tun bayan la'asar ake abu daya har asuba fatima ta kasa haihuwa duk tabi ta galabaita dole tasa aka yanke shawaran yi mata aiki.
Turota akayi za a shiga dakin tiyata da ita hannunta ta daga alaman a tsaya adeeja ta yafito ta rike mata hannu murmushi tayi tace ki daina kuka adda ki min addua tunda nake nakudan nan aduan miji na gari nake ta miki sai kuma tayi mirmushi tace kin san me Allah ya karbi adduata dan na san da kyar in fito adda ki daure ki cikawa iyayenmu burinsu ki aure yah sageer ki kulan min da baby na ke kadaice zaki iya rike min babyna a gidan ubanshi kiyi biyayyan da baki yi shi ba a shekarun baya na sani rabon yaranmu yasa kika kasa yin biyayya adda adeeja kiyi shi a wannan karon hawayene ya gangaro mata adeeja ta sa hannu ta goge mata tana wani irin kuka tace ba ki da hankaline inshaa Allahu zaki fito lafiya zafin ciwo ke saki maganganun banza komawa gefe tayi dan bata son jin irin maganganun da take yi hajiya ta yafito tace hajiya ki yafe min duk rashin kunyan da nayi ta mike hajiya na share kwala tace na yafe miki fatima na san yarinta ce lumshe ido tayi ta bude tace hajiya ki min alfarma bayan ba ni ki hada auren yah sageer da adda adeeja hajiya tace fatima zaki fito da yardan Allah ki raini abinda kika haifa murmushi tayi cikin jin ciwo tace hajiya in ban fito ba zaki cika min alkawari? Gyada kai hajiya tayi saboda kukan da yazo mata sageer ne ya karaso hannunta ya rike yace do this for me baby please yanda kika shiga ki fito min lafiya murmushi tayi tace yah hakan ba a hannuna yake ba yana hannun rabbi gyada kai yayo sosai yayi dauriya bai zubar da hawaye ba tace yah sageer ka yafe min duk wani laifi da nayi maka tsawon zaman da muka yi a tare...
Kafin ta dire yace na yafe miki habibty ki daina iein maganganun nan zafa ki fito lafiya murmushi tayi hade da lumshe ido ta bude tace na gode yah sageer in ban fito ba ka min alkawarin zaka auri adda adeeja?
Kafin ya bata ansa nurse ta turata akayi dakin tiyata da ita
Tsawon awanni aka dauka a ciki yayinda yan uwanta ke ta zarya a bakin kofan suna adduan Allah ya fito da ita lafiya.
Dr zakiyya ce ta fito ta jingina da kofan hawaye na zarya a kumatunta da sauri suka karaso wajenta suna tambayanta anyi nasara?
Idonta a lumshi hawaye na gangarowa tace she went into an arrest and her heart beat stopped ta karasa tare da sulalewa ta zauna kara adeeja ta saki lokaci daya suka fadi sumammu ita da sageer...........πππ
πRIBAR BIYAYYAπ
By Sawwama A.
Page 36.
Cikin gaggawa nurses suka kai musu dauki aka shiga dasu wani ward.
Hajiya kam zaman dirshan tayi a wajen ta kasa kwakwaran motsi sai lebenta dake furta innalillah wa'inna ilaihirraju'un Allahuma ajirni fi musibati wa akfilni khairan min ha.
Yayinda zakiyya ma take zaune a jikin kofa tana rera kuka sosai take jin fatima a cikin ranta tana jinta kamar kanwarta salma da suka fito ciki daya cikin 'yan watanin da suka san juna shakuwa mai karfine ya shiga tsakaninsu gashi yanzu mutuwa ta raba su.
Nurse ta fito daga dakin da fatima take ta tsuguna dai dai kunnanta ta rada mata wata magana zumbur ta mike ta shiga dakin jim kadan wata nurse ta fito da yara biyu a nannade kasancewan dama am cire yaran mikawa hajiya hajiya yaranta tayi duk su biyun hajiya ta rungume tana kuka me tsuma zuciya.
Har nurse din ta juyq zata tafi sai ta dawo ta,dafa kafada hajia tace mama kiyi hakuri ki daina kuka tayi jimmm sai tayi kasa da muryanta sosai tace *bugun zuciyan* ta ya dawo