Follow us on social media
Showing 30001 words to 31587 words out of 31587 words
Chapter 11 - Dubai Part 2 Complete Hausa Novel by Oum Hairan
sauqi tana zaune ita da me kula da ita sai Abba da Addah sunata yimata sannu
Adda na shafa mata magani.
Sannu tayi mata ta zauna sukaci gaba da kula da ita har bayan magrib da Taheer yasa aka
kirata yace tazo su tafi, kallonsa tayi a mamakance tace “na dauka anan zamu kwana?"
Girgiza mata kai yayi yace “ba haka na tsara ba kizo kawai mu tafi" bazata iya yi masa musu ba
amma qwarai bataji dadi ba Addah ce tace “to dama zaman me zakiyi kema da ba cikakkiyar lfy
ba shi mamaci ai addu'a kawai yake buqata" da wadannan kalaman suka tafi har sukaje gda
bata kulashi ba, suna isa ta bude motar ta fita shima ya shigo. A sama ya tarar da ita ta cire kayanta zata shiga wanka zama yayi a gefen gadon yana kallonta
har ta wucceshi taje tayi wanka ta fito ta fara shafa mai ya miqe ya zagaya ta bayanta tare da
tallafo qugunta ya kwantar da kansa a kafadarta hawaye nabin kuncinsa,
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta shafo kansa ya qara shigewa jikinta yace “kiyi hqr don Allah
ki yafewa Mom ko ta samu salama cikin kabarinta Habeey duk wani hali da rayuwarki ta shiga
Mom tanada hanu a ciki ta roqi Bushirah ta roqeki ki yafe mata ita Kuma tace kunyarki takeji...."
Hannunta ta dora saman bakinsa tana hawaye tana girgiza masa kai tace “ka...kadaina roqona
don Allah wlh ni na yafe mata tun kafin wannan lkcn Mom uwatace kamar Addah bazan taba
barinta da nauyin haqqina akanta ba Taheer ba itaba kowa ma daya cutar da rayuwata ta baya
na yafe masa banda mutum daya..."
Dago kanta yayi da sauri yace “waye?" Jan zuciya tayi tace “pappa Taheer shine mutumin da
bazan taba yafe masa ba ya cutar dani fiye da kowa ya rabani da gatana ya zama silar
lalacewar rayuwata ya cutar da mahaifiyata ya nakasta mata farin cikinta, ta Yaya zan yafe
masa?"
Numfashi ya sauke yajata suka zauna yace “watanmu biyu a U.S.A Abba yace ya makashi qara
kotu akan abubuwan da suka faru lkcn da aka kai masa sammacin kotu sai ya gudu yaje wani
guri ya kama haya dama ya rabu da matarsa sabida babu kudi kece me turo masa da kudi ke
kuma kin dawo shiyasa Deborah ta gudu ta yasheshi tsaf, ranar da sukaji lbrn inda yake akaje
domin a kamashi sai ya haura katanga domin ya gudu bai sani ba ashe bayan gdan tsohuwar
rijiyar kankare ce kawai saiya zunduma ciki aikuwa filla fillah aka fito dashi daga rijiyar rai yayi
halinsa"
Numfashi ta sauke tace “to Ina su Ibrahim da akace ya debe ya gudu dasu?" Murmushi yayi
yace “Ibrahim yana A.B.U Zaria Idris Kuma yace Solder yakeson zama yanacan makaranta
sojoji Fatima kuwa ta dawo harma ansa bikinta da Dr Shattima, ita kuwa Aisha tayi aure a
Saudia"
Daga hannu tayi tace “Alhmdllh naji dadin wannan lbr my life saura Hajiyan data kaini Saudia "
dariya yayi Mata yace “wato fansa kikeso akan kowa to hukumar yaqi da safarar mutane ta
kamata ita kuwa qawarki Aysher Jabir ne ya aureta suna Dubai amma gobe zasuzo
magajiyarku kuwa tananan qanjamau ta nakasata tana faman bara tsakanin wannan rumfa da
wannan, saiwa Kuma?"
Murmushi tayi tace “saura kai daka rabani da Abu mafi daraja a gurin kowacce ya mac...."
Rungumota yayi yana shafa cikinta yace “nima na haifi ya daya babu aure wacce kullum
tunanin makomar rayuwarta yake damun zuciyata" daga haka bai qara bata damar mgn ba yaci
gaba da romance dinta saida suka samu nutsuwa sannan sukayi wanka sukayi Isha suka
kwanta.
Washe gari da wuri suka tafi gdan karbar gaisuwar hakadai Taheer ya sanya Habeey yawo a
hanya kowa kowa yakeyi har akayi bakwai amma shi jarabarsa ta hana yabarta ta huta ga
girman ciki daqyar take takawa,
Shima Mahfuz ya dawo da amaryarsa yar izza da dagawar tsiya kowa kallon banza takeyi masa
a gdan harshi bai tsira daga rashin mutuncinta ba, cikin lkcn nan Saudat sauqi yanata samuwa
abinka da aikin sihiri ana dacewa da magani shikenan qurajen suka rinqa salubewa asalin
fatarta tana fitowa abin mamaki cikin sati dayan nan kwata² babu alamar qurajen sai saba da
fatarta taketayi ko tabo babu, nanfah hankalin Mahfuz ya koma kanta babu kunya yaje yana
bata hqr waishi wlh bayin kansa bane baisan sanda ya auri Raliya ba baisan sanda ya tsallake
yabar Saudat ba.
Ana bincikawa akaga ashe kuwa asirin da akayine idan Habeey ta kamu da ciwon Taheer ya
gudu ya barta yayi aure ya fada kan Mahfuz, sannan itama Raliya da asirin ta aureshi aikuwa
ranar bakwai din da daddare bayan kowa ya watse zatayi masa hauka ya nada Mata dukan da
yaja mata barin cikinta dan watanni uku sannan ya rattaba mata saki uku. Sosai su Dad sukayi masa fada shikuwa yace aikin gama ya gama saboda haka taje da abinda
ta satar masa.
Satinsu biyar da dawowa Saudat ta murmure sosai tace “itafa bazata koma gdan Mahfuz ba
qarshe ma ta gudo gdan Habeey ta buya shikuwa Taheer da taya bera bari shine me qara
boyeta wai bazata koma gurin butulu irin Mahfuz ba.
Shikuwa kullum yana hanyar gdan nasu har kuka yasha yiwa Habeey yana Mata magiyar ta
bawa qanwarta hqr ta dawo rayuwarsa wlh baisan yana sonta ba saida ya auri Raliya, sosai
Habeey ta rinqa yi mata fada itakuma sai tasa Mata kuka tace “Aunty a tarihin soyayya bantaba
ganin halaccin qauna irin taking da Yaya Taheer ba a halin Suma ma da bazaki masa amfanin
komai ba ya zauna dake ya yarda zai rayu dake amma mutumin nan irin cin mutuncin da
yayimin akan abinda bani na dorawa kaina ba idan kikaji sai kin zubar da hawaye Kuma yanzu
saboda lfyta yakeso ya wani dawo yace na koma gdansa, hmmm wlh aunty ko su Abba basu
raba aurena dashi ba saina kaishi qara ya sakeni"
Ana haka Bushirah ta haihu a wannan jigilar haihuwar ne Allah yabawa Mahfuz saa ya sace
Saudat ya gudu da ita ya boyeta a gdansa neman duniya yace shima bai sani ba sai daga baya
yace shine ya dauke matarsa.
Bayan haihuwar Bushirah da sati hudu Habeey suna kwance a daki da dare ciwon baya ya
tasheta aikuwa ta tashi Taheer da sauri yana ganin halin da take ciki ya dauketa sai asibiti.
Wasa farin girki tun yana boyewa har ya fito ya fadawa su Addah aikuwa tun daren saigasu,
Habeey dai bata haihu ba sai safiya ta haifo yaranta uku kyawawa maza biyu mace daya.
Wayyoh murna gurin Taheer kamar anyi masa busharar aljannah har kusan susucewa yayi da
anzo barka zai tareka yace “uku...uku Habbatullah ta haifamin"
Aikuwa yan uwa da abokan wasa suka samu abin tsokana da sun ganshi zasuce “uku
Habbatullah ta haifamin" saidai yayi dariya kawai.
Ranar suna yara sukaci sunan kakanninsu Aliyu da Salahuddeen macen taci sunan Granny
wato Khadijatul Kubrah, akasha shagalin suna hatta gdajen TV da jaridu ranar zancen da akeyi
kenan Matar dan governor Aliyu Waziri sannan matar shugaban rukunin kamfanonin T.H
Fabrics and Counseling Kuma ya a gurin shugaban likitocin qasar 9ja ta haifi yara uku.
Yaran da iyayensu sunsha addu'a sosai, itama Aunty Zahrah taga rayuwa tayi ladab saboda
babu jigogin nata Mom da Hajiya Ummah ga Kuma shagidewa da tayi saboda karairayewar da
tayi.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya duk jarabar Taheer saida ya qyale Habeey ta koma gda na
kwanaki arba'in aikuwa Abba yanashan zarya don a rana sai yaje gurin yaransa da matarsa sau
uku sau hudu hakadai daqyar aka rurruma tayi arba'in din, a nufin Addah sai yaran sun qara
qwari wata biyu ta mayar da Habeey. Ai yanajin haka ya saka musu daru dan iskanci harda cewa shi tsoron gdan yakeji shi kadai,
babu arziki suka bashi matarsa da yayansa tare da Mai rainonsu suka tafi Safnah ce kawai ta
zauna a gdan saboda tafi sabawa da kakanninta.
Wannan dare an kashe arna iyakar arna duk wata tsumammiyar sha'awarsa ta kwanaki arba'in
dinnan saida ya sauketa saboda Tasha qyara baga iyayen ba baga kakarsu ba baga qannen
mijin nata ba hattada Yadikko Laure Amaryar Dad Kuma Yaya a gurin Addah uwa daya uba
daya da mijinta ya rasu kasancewar bata taba haihuwaba Dad ya aurota itama gyara matar
dan nata take Kuma yarta, aikuwa watan yan uku hudu saiga wani cikin itadai Habeey bataso
ba amma Taheer murna kamar baa tabayi masa haihuwa ba wata tara ta haifi danta namiji
ranar sunan Muhammad ranar Saudat itakuma ta haihu yarta mace kwana uku tsakani Kubrah
ta haifi Namiji habawa aikuwa anyi shagali sosai a wannan Fam din zumunci ya qullu zaman lfy
ya dore kamar baa taba samun sabani ba,
Alh Taheer da manyan Mata Habeey an zama manyan mutane rayuwa sai yanda sukaso
sukeyinta Habeey anata karatu haihuwa ta tsaya ko nace sun tsayar yau gata harda Masters a
bangaren Business administration lkcn data gama ta fantsama kasuwanci da manyan nairori
aikuwa ana ganin albarka.
_Tammat bi hamdullah_
_Nan wannan lbr yazo qarshe me taken *DUBAI* kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana baki
daya, sai mun sake haduwa a sabon lbrnmu me taken *NAJMAH* Wanda zai fara zuwar muku
*20/8/2020*_
# *UMMUH HAIRAN*