Chapter 6 of 44
Mazan Ko Matan Complete Hausa Complete Hausa Novel by M Shakur
yakalli Amina hannu yabude mata dasauri ta rungumeshi tace “Yaya ina yini” kanta yashafa
yace “lafiya lau Autan Hajiya” wheelchair ya karbe yashiga tura Hajiya da kanshi har mota saida
ya zaunar da Hajiya tazama comfortable sannan ya sallami mai cart suka shiga mota suka tafi,
Hajiya sai kallonshi take ta madubi tanamai hira tace “amman kai rashin lafiya ne ko Nura?
Naga kafada sosai”? Dan murmushi yayi yace “aiki ne wlh Hajiya” ijiyan zuciya tasauke tace “to
Allah yabaku sa’a kadinga hutawa kanacin abinci akai akai kaji ko” “to Mamana” ya amsa yana
murmushi, tace “nataho maka da danderu” baki yabude yadan juyo zai kalleta dasauri tace “kul
maida hankali tuki kake” dan dariya yayi yace “Meenah ya akayi akabar Hajiya tawuce da
danderu”? Dan dariya tayi tace “ba anga batada lafiya ba babu wanda yayi musu da ita”
murmushi kawai yayi yace “inason Mamana Ameena sosai” Hajiya data washe baki tace “nima
inason d’ana sosai” Ameena ta turo baki tace “Hajiya nifa” dan dariya Hajiya tayi tace “Inason
ku duka akwai wanda ma yasamu soyayyata irinki Auta na” ahaka suna family hira sukakai gida
Nura yace “specialist danai consulting yace zai ganmu by 12 yanzu zakici abinci kihuta anjima
saimuje asibitin ko” yayi maganan tareda yin Parking yafito da ita sabida dakali da kafanta tayi
tafiya tana rikeda shi suna tafiya ahankali Ameena biye dasu tana kallon hadadden gidan, bude
kofa sukayi suka shiga ciki wani lafiyayyen kamshi yamusu sallama dasauri Ummi tafito daga
kitchen tazo har tsakiyan falon ta duka tace “sannu da zuwa Mama, ya hanya ya jiki, Allah
yabaki lafiya Mama, Allah yasa kaffara ne” washe baki Hajiya tayi tana kallon Ummi tace “waye
wannan yarinyar mai ladabi ba irin su Auta ba da basu gaida mutane da kyau, ga iya addu’a,
waye ita”? Dan murmushi kadan Nura yayi yace “Ummi sunanta” daidai Hajiya na zama, Hajiya
tasauke ijiyan zuciya tace “jiki Alhamdulillah Ummi, sannu kinji Allah miki albarka tashi tashi ki
zauna, ina Hadiza? Nasan jikoki na ana makaranta ina Hadiza?” Hajiya takara tambayan da
zuciya daya tana waige waige neman Hadiza, cikeda hikima Ummi tace “tadanje tadawo wani
uzuri yakamata amman tace na kula dake da kyau kome kikeso namiki” sosai Nura ke kallon
Ummi yanda yarinyar keda hikima baitaba sanin zata iya fadan magana hakaba, dariya Hajiya
tayi tace “ayyooo” kallon Amina data shigo da jaka Ummi tayi gateman biye da ita da kayansu
da sauri ta tashi tace “kawo nakai miki daki jeki zauna kihuta kinsha hanya” murmushi Meena
tayi tace “thanks” kai kayan sukayi sama sannan Ummi tadawo tashiga kitchen a tray tajera
abincin Hajiya da ruwa a bowl mai kyau na wanke hannu tafito takawo har gaban Hajiya, Hajiya
tace “Ayyah sannu da aiki Ummi, Allah dai yasa cimata ne dan yanzu bakomi nakeci ba, cuta
batayi ba” tai maganan tana bude kulan ganin tuwon Alkama da miyan zogale dayaji ganye
yasa Hajiya tace “laaaaaaa Hadiza tamin girkin nan kafin tafice” dasauri Ummi tabude baki
zatace eh Nura yace “Ummi ta dafa miki Hajiya” kara kallon Ummi Hajiya tayi saikuma ta
nunawa Meena Ummi tace “kinga girkin sa’onninki ko ke sai shegen kiwuya, wai wannan
kamshi haka bari naci abincin nan akasa zan zauna ma” da taimakon Nura tazauna akasa ta
wanke hannu takai abincin baki saita kalli Nura takuma kalli Ummi takara kallon Nura again tace
“Ummin nan dai danake gani tai girkin nan”? Gyadamata kai Nura yayi sai kawai Hajiya tace
“Allahu Akbar wlh tayi girkin yanda nakeso, kaga ba gishiri ba magi, sannan bata sakamin jan
nama ba hanta da Koda kadai ne amiyan, cimata tamin kuma yanda nakeso, bani jakana
Meena kigani” bata jakanta Meena tayi Nura ya karba, dasauri Hajiya tace “ciro duka kudin
dake purse dina” murmushi yayi ba musu yaciro dubu goma da dari biyar ne ta karba tamikama
Ummi tace “ga tukuicin ki dan kin dadada mini rai kinsa natuna na diyata Aisha mai bin Nura
tana aure a eygpt ita kadai kemini abinci irin wannan taste din wannan tarban da akamin bazan
taba mancewa da ita ba, nagode ko Ummi amshi kudinki” akunyace tace “Mama kibar shi ni
nadafa miki ne kawai wlh” Hajiya tace “laaaa ungo amshi nace” dan satan kallon Nura tayi
shima kallonta yake ahankali yace “bazaki amsa kudin Hajiya ba kinsan kalan makon Hajiya
kuwa? Ba kasafai akecin kudinta ba, ke kinyi sa’a tabaki” dariya duka sukayi harda Ameena,
Hajiya tace “atoh dan haka karbi abinki” gently Ummi tasa hannu ta amsa ahankali tace
“nagode Mama Allah ya ninka miki dubun su” Hajiya tace “Ameeen Ameeen” Ummi na
murmushi takalli Ameena tace “nadafa miki shinkafa dafa duka dakuma taliya na manja wanne
zan kawo miki” dasauri Ameena tace “taliyan manja” harzata tashi saikuma tadan kalli Nura
dake kallonta kasa kasa tace “Alhaji mezan kawo maka bakayi breakfast ba kaima” abincin
Hajiya yakalla yace “zanci abincin Hajiya” gyadamai kai tayi tawuce kitchen karaf akan idanun
Hajiya yanda Nura ke kallon yarinyar amman batace komi ba, saida sukaci sukai kat Ummi
takawo mata juice na cucumber kadai data mata Hajiya tasha sosai sannan Nura yakaita sama
dakinsu dakin dake kusada na Hadiza inda Hadiza ta kwana ranan ta gyara Hajiya ma sai
complain take ita batason sama Nura yace yafiso ta kwana inda zai dinga jin motsinta hakanan
ta hakura.
Wuraren 12 suka fice asibiti Ummi tasake gyara gidan.
Sai wajajen shidda saura suka suka shigo gidan da gudu daga Aman har Amal sukazo suka
rungume kakansu abinci Ummi takawo, tama Hajiya unripe plantain porridge datasa shuwaka
da bushashen kifi da daddawa aciki shima ba maggi ba gishiri sai kamshi daddawa da kifi sun
bama abincin taste, tayi jellof rice da naman rago ma sauran mutane, duk suka baje harda Nura
za’aci abinci anan falo, Ummi takoma gefe ta duka Hajiya tace “kema taho nan kici, an taba
haka ki mana girki saiki koma gefe, tahonan” dan satan kallon Nura tayi shi harya faracin faten
Hajiya ma, da idanu yamata tazo nan, hakanan taje tashiga cikinsu suka faracin abinci, ita da
Ameena da su Aman shinkafa sukeci, tunda tafara aiki yaune rana na farko data ji kaman tana
gidansu Hajiya ne Gwaggon ta Amina kuma yan uwanta, sai hayaniya su Amal keyi anacin
abinci, no wonder Alhaji keda kirki mahaifiyar shi batada matsala at all. Nura yace “Hajiya dan
ban juice din cucumber dinki nasha” jug din Hajiya ta kalla tace “kai Nura na tsammaka na
tsammaka harna gaji da sammaka wai kaine mara lafiyan nan ne”? Dariya akayi Ummi itama
dan boye dariya ta tayi ganin yanda Hajiya keda barkwanci, takalli Nura tace “inje inmaka kaima
Alhaji”? Batare daya kalleta ba yace “a’a kihuta zansha na Hajiya” kofi Hajiya ta dauka ta
tsiyaya mai rabi ya karbe ita ta shanye rabin tace “Allah miki albarka Ummi zaki koyama
wannan shashashan Autan nawa kafin mu koma” gyadama Hajiya kai tayi, Hajiya tace “Auta
dukta cinye ke bakici komiba” dasauri Ummi tace “naci sosai wlh” kashigo falon ji zakayi inama
haka farin ciki zai dawwama agidan, Nura yana lura da yanda bini bini Ummi kecin abincin tana
duba Amal da Aman, chan kuma saita debo tai feeding Amal da mostly wasa take da abincin at
this point bazaiyi karyaba yarinyar ta shiga ranshi sosai barinma dayaji labarinta dazu, yaji ta
taba aure har ta haihu dudda pre matured birth tayi amma saiyaji yakara natsuwa da ita, wato
saisa takeson yaranshi kuma saisa takeda hankali koba komi tanada experience, baison yayi
mu’amala da yara masu danyan kai that knows nothing akan aure koba komi tasan menene
aure kuma tayi zaman aure, tayi rainon ciki, sannan tayi nakuda, hakan is perfect for him.
Sake lura da yanda yake satan kallonta Hajiya tayi daidai nan aka bude kofa aka shigo dukansu
suka dago kai cikeda fara’a Hajiya tace “oyoyo oyoyoo, sannu da dawowa Hadiza” tundaga inda
Hadiza ke tsaye tabi kowa na falon da kallo da yanda falon yayi kacha kacha dudda bawai
kacha kachan yayi ba kayansu ne jaka da gyaluluwa dasuka zuba akan kujera dan dawowansu
kenan Ummi ta taresu da abinci sai abincin da Amal da zuzzubar a falon rice din, daidai nan
idanunta yasauka akan Ummi dake cin abinci tareda Amina dakuma yaranta akasa tana kokarin
bama Amal abinci abaki hankalinta kwance dan akasa take zaune technically batayi laifi ba yau.
“Ke menene aikinki? Jibi yanda gidana yayi kacha kacha zama kikayi kinacin abinci? Kina yar
aiki waya gayamiki kinada darajan zama inda mijina yake kici abinci eh”? Yunkurawa Ummi tayi
jikinta yayi sanyi zata tashi dasauri Hajiya tace “dakata Ummi” takalli Hadiza dake tsaye awajen
da taje tace “ninace taci abinc……” “Hajiya dan Allah kidakata badake nake magana ba” Hadiza
tayi maganan rai abace dasauri daga Nura har Ameena suka juyo suka kalleta da mugun
mamaki itama Hajiya tayi tsuri tana kallonta dan batasan haka Hadiza tazama tasan ta dai da
rashin son aiki ko sunzo babban salla Kano dama ba zama take agidanta ba saidai ta gudu
gidansu so bata wani zauna da Hadiza one on one na dogon lokaci ba, ganin abun zai zama
wani kala yasa dasauri Ummi ta tashi zata juya strictly Nura yace “dawo ki zauna kicigaba da
cin abincin ki” cikeda tsoro Ummi takalli Nura gabanta na faduwa tadan kalli Hadiza dake
kallonta rai abace ahankali takoma ta zauna abun ya mugun mugun yima Hadiza ciwo dan
yaune rana na farko daya nuna bata isaba agaban yar aikin yawanci ba agaban idanunta suke
tsiyansu ba, zuciyanta wani kalan baki yayi takalli Nura tace “muzuba nidakai badai anzo har
cikin gidana ana nema ajuyamaka kai ba tun yanzu an fara kulla kisisina da shairi ko da sunan
rashin lafiya amman bakin mutum rass yazauna yana zakalkalan abinci to wlh muzuba dani
dakai” Ameena jitayi kirjinta na tafarfasa badan Ya Nura na zaune wajen ba da wlh saita durama
Hadiza ashar wucewa tayi fuuuu tayi sama kunyan duniya rufe Nura yayi abinda matarshi tama
Hajiya jiyayi ma abincin ya isheshi kowama hatta yaran jisukayi abincin ya ishesu Hajiya ta kalli
Ameena tace “tashi keda Ummi ku gyara wurin” kunya yasa Nura yamike yama kasa kallon
kwayan idanun Hajiya yajuya yace “bari nazo Hajiya” baima jira amsanta ba yafice dasauri
Hajiya tabishi da kallo saitaji dan nata yabata tausayi.
Kayan daya sayo dazu yasa mai gadi ya kwashe yakaima Ummi sannan yaja mota yabar gidan.
Abin yama Hajiya ciwo sosai, ya sosa mata rai, ta haifi yaran dasuka girmi Hadiza, yaranta mata
uku biyu sunyi aure saura daya, ita Hadiza zatama rashin kunya haka. Dawowa daga kitchen
Meena tayi ganin ba Yayanta awajen tazauna kusada Hajiya tace “Hajiya Hadizan nan yar iska
ce kuma wlh wlh ta ijiye iskancin ta a inda tasabayi let her not try that nonsense da ke inba
hakaba ni kadai na isheta wlh dan idan nakira su Ya Aisha har gida zasuzo sumata shegen
duka ba Egypt ba Ya Aisha zata iya barin ko’ina take aduniya tazo muma duk wacce ta zageki
shegen duka……” hannu Hajiya tadaga mata tace “banson maganan nan Auta, Matar yayanki
ne” cikin fushi Meena tace “koma waye dama nasha gayamiki halinta tunda kika fara rashin
lafiya sau daya bata taba kiranki taji yajikinki ba, yar iska kawai mahaukaciya wacce batasan
darajan iyaye ba idanma kinci abinci na kanin ubanta kikaci kona danki, okay saitaga kina
shurin mutuwa ne zatasan baki da lafiya dakikiya kawai” Hadiza dataji duka maganganun
Meena dan saukowa tayi zataci abinci takoma sama saikuma gobe, takarasa saukowa takalli
Ameena dabama ta lurada itaba tace “did u just call me dakikiya Ameena”? Dasauri daga Hajiya
har Meena suka juyo suka kalleta Meeena zatai magana Hajiya taja hannunta cikeda hikima irin
na manya tace “a’a badake takeba Hadiza wani labari take bani daya faru a kano” kwafa Hadiza
tayi tace “gwara dan wlh dasaita bar gidan nan yanzun nan kema kibita” fizge hannunta Meena
tayi daga hannun Hajiya tamike tsaye tai wajen Hadizan dan rainin wayon ta yayi yawa ta
nunata da hannu tace “an kiraki dakikiya dake nake Hadiza idan baki koreni daga gidan nan ba
baki cika yar halas ba” Hajiya datake daga zaune tahau yunkurin tashi tana kwalama Meena
kira itama Ummi tafito daga kitchen da gudu tazo wajen yaran ma haka daidai Hadiza na nuna
Hajiya tace “kinga dakikiya chan not me” Meena batai wata wata ba ta daurama Hadiza mari
abaki jikake tasss!!!! Haba sai jini Hadiza ta kurma ihu tadaura hannunta kan bakinta dataji lema
lema tacire hannu taga jini ahaukace tace “ni kika mara”? Ta chakume gaban rigan Meena da
karfi, dambe sukahauyi ba kama hannun yaro Hajiya tafashe da kuka sosai Ummi tashiga
rabasu amman ina basa rabuwa, dukan juna suke sosai bana wasa ba, Meena ta fizge ribbon
din gashin nan taja gashin kaman zata cire mata su daga tushen kwakwalwa, da gudu Ummi
tayi waje Mai gadin su takira yazo da kyar aka iya rabasu aiko Meena ta bala’in lallasa Hadiza
bakinta sai jini yake ta yayyakusheta a wuya da hannu, dudda itama Meena ta daku a hannun
Hadizan amman bata sami any ciwo ba kaman yanda tama Hadiza kowa sai nishi yake, shiga
tsakaninsu gateman yayi Ummi tarike Meena tace “dan Allah kuyakuri” cikide zuciya Meena
tace “kada kice na yakuri Ummi ba’a haifi wacce zata zagan mini uwa agabana banyi wani abu
ba, am I even my mother’s daughter idan agabana za’ahau zagin Mamana nai yi shiru eh? Is
she mad? Ba’a bata tarbiya agidan su bane? Idan ba’a bataba ni I will give u, dagayau kowace
uwa kika tashi zagi zaki tuna diyar wata ta taba miki duka dakika zagan mata uwa, you are very
very very stupid to insult Hajiya kinji, shegiya mai halin matan da iyayensu sukama baki” cikin
ihu da kururuwa Hadiza tace “wlh, wlh, wlh yau saina kulleki a police station na rantse da Allah,
ni kika daka kin san wacece ni anan Abuja? Number one, the most successful business owner
anan Abuja, kinsan award guda nawa ke cikin office dina? BBC waye waye duk anyi hira dani,
nizaki zo har gidana ki daka? Wlh wlh u are a small girl yau zan nuna miki your place” tana
maganan tayi kofa bayan ta fincike key nata awajen tray na car key ta shiga motanta tafice
dasauri Ummi tasaki Meena tayi wajen Hajiya dake kuka shikuma gateman yace “ayi hakuri ayi
hakuri” yawuce yafita.
Dukawa Ummi tayi takai hannunta tana sharema Hajiya fuska tace “Hajiya kiyakuri” da kyar
Hajiya ke iya magana tace “Ummi kiramini Nura gobe goben nan zan koma gida Meena batajin
magana nasha gayamata zuciya batakai mutum ko’ina, kowani zagi Hadiza tamini sai mene ita
ta zaga basaita bartaba akanme zatai dambe da Matar yayanta eh akan mene daga zuwa na
garin nan yau yau din nan? To ko warakata na nan nahakura kiramin Nura idan akwai jirgi
yanzun yanzun nan ma komawata zanyi kano” yanda Hajiya ke kuka tana bama Ummi wayanta
yasa takira Nura, yana dauka yace “Hajiya” ahankali tace “nice kazo gida Hajiya na nemanka”
hakanan jikinshi yabashi wani abu daman baiyi nisa ba duka duka yana ta gaban estate nasu
fruits yaje saya yasan yanda Hadiza tadawo saitai rashin mutunci saisa baiyi nisa ba at all
dasauri ya katse wayan, ijiye wayan Ummi tayi tadauki Amal dake kuka sosai ta goya Aman ma
ta lallasheshi dan duk kuka suke sunga anci uwar Maman su, taje wajen Meena dake wajen
dinning zaune akasa yanda Hajiya ke kuka yasa she’s feeling so guilty dan yanzun nan hawan
jininta zakaga yatashi, yana isowa gidan ko parking baiyi da kyau ba yafito yashigo gidan Hajiya
yagani tana kuka sosai yaranshi suma kuka Ummi sai jijjiga Amal take ga Meena akasan
dinning idanunta sunyi jazur kayanta ya chukurkude kaman wani abu yafaru dasauri yayi wajen
Hajiya ya duka yace “subhanallahi hajiya menene haka?” Cikin kuka tace “kaga Ameenatu
yarinyar chan bazata taba daina jamini bala’i aduniya ba, duba jirgi yanzun nan idan an samu
mukoma kano nahakura da asibitin Nura bazan iyaba bazan iya da tashin hankali ba” rungume
Hajiya yayi yace “ya isa Hajiya ya isa daina kuka muje ki kwanta gobe da sassafe saiki koma”
yay maganan trying to just calm her down, yace “ya isa ko I’m here now, everything is gonna be
fine”.
Sama yakaita yana zuwa wani allura yamata a hannu da Dr yace adinga mata idan anga
hankalinta yatashi nan da nan bacci yadauketa yasauko kasa yazo inda Meena take zaune
yace “Meya faru?” Baki tabude zatayi magana saikuma tafashe da kuka cikin kuka tafada mai
duka abinda yafaru batai karyaba zaiyi magana daidai an bugo kofa an shigo Ummi ce dawasu
yan sanda guda biyu ta nuna Meena tace “officer ga tachan” tashi da sauri Nura yayi yana
kallon Hadiza da yan sandan guda biyu wanda ganin Nura yasa basu karasa shigowa falon ba
duk suka tsaya anan mini parlor dasauri yakaraso inda suke ya mike musu hannu yace “officer
lafiya”? Mutumin yace “Madam dinka ne tashigar da kara kan mother Inlaw ta da sister Inlaw
sunzo har gidanta sun mata taron dangi anmata duka, kuma munga shaida bakinta da wuyanta
saisa muka biyota muyi arresting sai amusu sulhu a police station” ijiyan zuciya yasauke yajuyo
yakalli Ummi dake faman jijjiga Amal tana kuka tarike hannun Aman yace “ku tafi sama keda
Meena dakin Hajiya ku rufo kofa” dan yasan Hadiza zata iya kamasu da duka kuma, gyadamai
kai tayi tawuce takama Meena duk sukai sama, Hadiza tace “ba sama ba ko lahira kukaje sai
anyi arresting naku yau wlh” officers din duk suka kalli Hadiza Nura yace “bismillah ku muje
waje” binshi sukai waje Hadiza tabiyosu officer da kanshi yace “ki barmu maza muyi magana
mana Madam” tsayawa tayi saikuma ta buga tsaki takoma daki, explaining komi Nura yamusu
yama nuna musu some magungunan Hajiya dake motanshi yabasu hakuri kan kada suyi
arresting kanwarshi, ganin kamalan shi da natsuwan shi duba kuma da babban mutum ne, a
well known businessman anan Abuja