Chapter 4 of 44

Mazan Ko Matan Complete Hausa Complete Hausa Novel by M Shakur

kullen gam tana ihu sosai jikinta nawani kalan rawa kaman wace ta zare tsabagen azaban
zafin datakeji na miyan dakuma yajin miyan a idanunta yasa suka taho wajen da gudu Aman
yace “Anty Ummi” cikeda masifa Hadiza tanunata da hannu tace “kina gidana, kinacin abinci na,
nabaki makwanci, nabaki kayan sawa, nabaki sabulun wanka dana wanki, sannan ina biyanki
kizo bazakimin biyayya ba, sau nawa ina gayamiki ni bancin tuwo sau nawa nake gayamiki? So
kike nayi kiba nai katon ciki? Zanje sama nai wanka ki tabbata kin dafamin wani abun kin
kawomin dakina kafin nagama wanka inba hakaba wlh saina koraki daga gidan nan this night”
ta dauki jakanta tawuce sama fuuuuu, tsugunnawa daga Aman har Amal sukayi agaban Ummi
da jikinta har bari yake sabida zafin miyan dan bata dade da gama miyanba ta juye a kulan
gidan ga kulan su irin na millions din nan ne masu rike zafi kaman me, dudda Aman yaro ne
amman saida yakai hannunshi yacire tuwon daga jikinta yana kuka sosai ya yar akasa yace
“Anty Ummi sorry stop crying” Amal tace “Mommy is badddd mommy” sosai Ummi ke kokarin
tabude idanunta takasa sai kuka take dudda kukan take na tausayin kanta tariga tai alkawari
komenene zatai hakuri tana bukatan albashinta dashi Gwaggo ke zuwa asibiti dakuma shi ake
tara kudin auren kanninta, dole ta jure komi itane hanyan cin abincin gidansu, so take ta mike
but tama kasa hannunta Aman yakama Amal ma takama dayan yace “let’s go Anty Ummi ki
wanke fuskanki” gydamusu kai tayi tana tsayar da kukan datake ta yunkura zata tashi tama
kasa saita kara fashewa da kuka daidai lokacin an bude kofa da sauri su Aman suka juyo ganin
Baban su shima ya shigo ya tsaya chak yana kallon daga yaranshi har Ummi dake kuka sosai
kaman anyi mutuwa agidan ga jikin Ummi duk miya, fuskanta ma haka takasa bude idanu yasa
yayi wajensu dasauri baima cire takalmi ba yace “Subhanallahi meya faru faduwa kikayi Ummi”
Tsayar da kukan tayi dasauri muryanta na rawan sheshekan kuka tace “eh” tana yunkurawa
zata tashi dasauri Aman yace “is Mommy Dady, ita ta kwara mata the whole tray na abinci akai
Anty Ummi has been crying” warware handky daya ciro Nura yayi daga aljihunshi baiyi wata
wata ba yakai kan fuskanta cikeda damuwa ahankali yace “tsaya” batai musu ba tsayawa tayi
kwashe miyan kan idanunwanta yayi tass, miyan yayi fasha fasha awajen harda gashin
idanunta, sannan ya kwashe na goshinta dana kumata batare daya taba na wuyanta ba dudda

baka ce but he could see yanda fatan fuskan yayi ja, ijiye handky yayi dasauri kafin ahankali
yakai hannuwanshi duka biyun yakama kafadanta dagashi har ita atare duka sukaji wani iri
dasauri tayi kokari fizge kanta strictly yace “stop banson gardama, tashi muje” yanda yayi
maganan ba wasa hakan yasa bata kara gardama ba, yana rikeda ita haka yayi kitchen da ita
su Aman suka bisu bude kofan kitchen din yayi zuwa nan backyard gaban wani tap dasuke
dashi awajen, yabude tap din yajuyo yakalli Aman yace “je bayin Anty Ummi kadauko mini
sabulun wankanta” “okay Dady” Aman ya amsa yajuya da gudu shikuma yabude tap din yace
“tsugunna” ahankali Ummi ta tsugunna, gently yadinga tara ruwan da hannunshi yana watsa
mata a fuska har saida miyan ya fiffita duka da wayanda sukenan asaman gashin idanunta
daidai Aman yakawo sabulan, ga mamakinshi sabulun vivo yagani ahankali ya karbe yakama
hannunta yasa sabulun aciki yace “wanke fuskan mugani da sabulu” shafa sabulun tayi ta
dirdirje da kanshi yake zuba mata ruwa tana wankewa tass ta wanke fuskan, igiyan wajen ya
kalla ganin wata singlet dinshi wanda yasan itane ta wanke yajawo yabata yace “share fuskanki
saiki bude idanun nagani”



Share fuskan tayi ahankali sannan tashiga bude idanun yajin dataji yasa tamaida idanun
ahaukace tarufe tafashe da kuka kunsan yanda yaji ke birkita mutum tace “wlh da kwai yaji
sosai Alhaji, wayyoo Gwaggo na nashiga uku” shi arayuwanshi yanada tausayi, ya tsani aga
ana hurting mutane in general balle kuma yaga mace in pains, da sauri yasa hannunshi ya karbi
hanky yamikama Aman yace “hold it nagani“ sabulun yadauka daga kasa yasa a hannunshi ya
fara wankewa sannan ya murza sabulun a hannunshi ahankali yadan kalli fuskanta yanda ta
kankame idanunta gam jikinta har lokacin rawa yake tana dan kuka, dan ijiyan zuciya yasauke
sannan yakai hannunshi gently yashafa sabulun a fuskanta kaman yanda ake wankema yaro
karami fuska, fuskanta is sooo soft kaman na dan yaro, almost 30sec yayi yana chuda fuskan
sannan ya kunna pampoo yashiga wanke mata fuskan tass kafin yakarbi singlet din ya share
fuskan da kyau ya tsane dogayen eyelash nata kafin ahankali yana tsugunne agabanta yaciro
wayanshi dudda akwai haske wajen bauuu flash na wayanshi ya kunna yabama Amal yace
“princess haskamin fuskanta” dasauri Amal ta karba ta haska fuskan Ummi, shima yana kallon
fuskanta dake sheki yaji wanki da sabulu yace “bude idon nagani” gently tashiga bude idanun
dake rawa sosai na haggu tabude tass na dama ne tabude kadan dan tanajin yaji sai yarfe
hannu take ta rude sosai ganin yanda takeyi yasa ahankali yace “tsaya” tsayawa tayi ijiye
singlet din yayi kan jikinshi yakai duka hannunshi ahankali yayi cupping fuskanta dasauri Ummi
takalleshi tadade rabon dataji namiji dab da ita haka, ahankali babu komi aranshi yakai
hannanyenshi ya ware kwayar idannun nata dake mata yaji kafin gently Ya hura iskan bakinshi
ciki wani kamshi Ummi taji da sanyi daya ratsa jikinta feeling inama ace zata sami miji dazai
dinga kula da ita haka kaman yanda Alhaji keyi yanz, Alhaji nada kirki gashi kyakkyawa fari
dashi kaman wani balarabe ga bakin saje, tsayar da hura idanun yayi ganin tabude su rass tana
kallonshi kaman yaune rana na farko datake ganinshi shima zuba mata idanu yayi yana kallon
kwayar idanunta yanda suke walkiya sabida hasken flash da Amal ke hasko musu, idanun sunyi
ja na kukan dataci da yanda tai looking so helpless dakuma yanda take kallonshi hakanan
saiyaji kaman yasata ajikinshi ya lallasheta, there’s something about her da kawai he finds

interesting baisan menene ba. “Anty Ummi yadena yajin”? Maganan Aman yadawo da dukansu
daga duniyan tunani atare dukansu kowa ya janye idanunshi, Nura ya mike tsaye da sauri
yawuce ciki batare daya kara kallonta ba itakuma ahankali tamike tsaye tana goge wuyanta,
gyadama Aman kai tayi tace “yadena” dasauri sukazo kusa da ita suna kallon fuskan hakan
yasa ta tsugunna dukansu taba fuskan nata sukayi cikeda so sukace “sorry Anty Ummi”
murmushi tayi sosai cikeda kokarin cheering nasu up tawani daga hannunta sama tace “Anty
Ummi jaruma ce kaman Amalili, ko Mudi da Kumurci tsorona suke menene yajin miya dashima
bazai tsorata dani ba” haba zokaga yanda sukahau dariya, Aman yace “Anty Ummi yaushe zaki
kaimu kauyenku muma muga Mudin nan da Kumurci” hannunta takai kan kumatunta kaman mai
tunani kafin tace “wata rana zamuje” ihu sukahau yi suna tsalle Nura daya dade yana kallonsu
ta window kitchen murmushi yayi yawuce yadauki mop yafice gyara dunning din yayi da kanshi.
Shigowa sukayi a kitchen din fita tayi taje dakinta ta chanzo kaya zuwa wani atampa dogon red
yamata kyau sosai.



Tana fitowa hada ido sukayi da Nura dake zaune a dinning yanacin tuwo adan kunyace ta
sauke kanta kasa tazo wajen ta duka har kasa tace “Nagode Alhaji, kana bukatan wani abune
dazan kawo maka”? Sosai yake kallonta red yamata kyau dudda babu wani special abu game
da atampan but yamata kyau, jin shiru baice komiba yasa tadago kanta ahankali hada idanu
sukayi da sauri yadauke kai itama maida nata kasa tayi dasauri, ahankali yace “bana bukatan
komi, thank u” mikewa tayi harta juya tafara tafiya kaman daga sama taji yace “abincin yayi dadi
sosai, thank u Ummi” dadan sauri tajuyo ga mamakinta kallonta yake suka sake hada idanu
sukayi, faduwa gabanta yayi dasauri tasauke kanta kasa tasake juyawa zata shiga kitchen
batare datace komi ba yace “mezakiyi a kitchen”? Ahankali tace “Anty zan daurama wani abinci
batacin tuwo” strictly yace “wuce kije ki kwanta kihuta” dudda bataso ba dan batasan mezai biyo
bayaba kasa musu tayi tawuce takoma dakinta ta kwanta.

Fess yagama cin abinci yakai komi kitchen dakanshi yafito yaje sama fitowa yayi da
paracetamol, bottle water yadauka mara sanyi yaba Aman yace “kaima Anty Ummi kace nace
tasha” gyadamai kai tayi yawuce da gudu yatafi dakinta Amal na binshi yakoma falo yazauna
yana saka news duk yanda yaso yama gane meke faruwa a news din kasawa yayi yawuce
sama fuuu, bude kofan dakin Hadizan yayi ranshi abace tana zaune gaban dressing mirror
daure da towel tana shafe shafen ta na night routine batare da tajuyo ba tace “ki ijiye abincin
kiwuce kifita dakikiya kawai next time try this nonsense kinbar gidana kenan jaka kawai yar
kauy…..” “Hadiza!” Nura yakirata da kakkausan murya saida gabanta yafadi dan baitaba kiranta
da zafi haka ba juyowa tayi da sauri ta kalleshi ganinshi tsaye a tsakiyar dakin yana kallonta
ranshi abace, haderai itama tayi tace “badai kahana yarinyar nan dafamin abinci ba dan idan
kayi haka u will see the other side of me Nura” wani kallo yamata yace “inason naga other side
of you din today are you crazy? Ke wace kalan senseless mata ce? Kissan kai kike kokarin yi
agidana? Are you trying to kill that girl?” Hannu ta dagamai tace “please lower your tone ni
matarka ne ba some yan aiki dazaka dinga dagama murya ba Nuri, I’m your wife not slave so
keeep muryanka down by now kasan I don’t take that shit, namiji yazo yana wani mini ihu akai

saikace ubana kuma ma idan na kasheta sai me? Eh? Ba yar aiki bace, yarinya mara galihu
duk irinsu ne irin yaran da akauyen su akekai yara maza almajiranci mata kuma akaisu aikatau
kota mutu sai me mezai faru? Almajirai nawa suka mutu wani abu yataba faruwa? Ai yara da
iyayensu suka nuna basu da gata mutane ma basa gatanta su so bakaina farau ba dan yar aiki
ta mutu agidana ehe” Sosai Nura ke kallon Hadiza shi baimasan tayi nisa haka ba sai yau wato
tanada answer for anything, at this point baimaso maganan nasu yayi nisa dan kar zuciya ya
debe shi yadauketa da mari hakan yasa cikin kakkausan murya yace “duk randa kika sake
trying nonsense din nan wlh saikin bar gidane duk wani abu dake gidan nan fara tundaga kan
gateman suna karkashina ne, hakki na ne nakare kowa na tsaresu dan haka don’t ever try
hurting mutanen dakemin aiki inba hakaba u will leave this house!” dudda maganan ya mugun
mugun sosama Hadiza rai amman daurewa tayi dan bataso yagane tai wani kalan shewa.
“Ahayyeeee nanaye ance dama idan baka mutu ba bakagama sanin halin maza ba, Nuri ni
kakema gorin zaka kora daga this rat hole dakake kira gida”? Ta nuna dakinta da ko’ina da
hannu, tsaki kawai Nura yayi yajuya yafita tabishi da sauri dan idan bata bashi amsan maganan
nan ba hankalinta bazai kwanta ba kai zazzabi ma zai iya kamata, tana biye dashi yana tafiya
tace “zan iya gina gidan dayafi nakan nan sau dubu a kyau dakuma girma Nura kada kayi
kuskuren yimini gorin gida, duka duka yaushe kayi kudin lokacin dana aureka kagama masters
akan architecture kanama wani building agency aiki har kazo kabude naka kampanin na harkan
filaye da gine ginen estate anan Abuja, who do you think you are dazaka min gorin gida nixaka
kora Nuri, au ina maka magana ka maidani mahaukaciya kayi tafiyan ka wlh wlh yanda ka
batamin rai dinnan saina huce akan mahaifiyark…….” Chak Nura ya tsayar da tafiyan dayakeyi
akan staircase yajuyo ahankali yakalleta itama daidai tana tsayawa dab da shi tana kara rike
gaban towel nata da kyau tana kallonshi tace “da ilimina da sana’ata da darajata har ka isa kazo
kana gayamin na kara dukan wata yar aiki sainabar maka gidan ka, sabida yar aiki Nuri zakace
zaka koreni, what on earth do you take yourself for? Are you God? Sabida kaganni mace
kadauka I am weak ne I can’t defend myself? Zakace zaka korini daga gidanka u think bazanyi
speaking up ba, Listen Nuri, me and you are two equal people! Baka fini da komi ba, duk inda
kasa kafa nima zan iya saka kafan, nasan kimata nasan daraja ta and my worth u cannot
downgrade me or downgrade my status and for batamin rai din nan dakayi this night wlh saina
batama mamank…….” Azuciye Nura yadaga hannu zaikai mata mari kaman daga sama sukaji
Aman yace “Daddy!” Chak Nura ya tsaya da hannunshi batare dayakai marin ba, he don’t ever
wants yaranshi to have a memory of him yana dukan mahaifiyar su, dunkule hannunshi yayi
tareda saukewa kasa ahankali yajuyo yakalli Aman din, dasauri Aman yazo ya rungumeshi
tsamtsam yana kuka sosai yace “Daddy sorry kayakuri Mommy is sooo baddd but don’t slap her
okay Dady, beating girls is not good katuna ranan dana daki Amal haka kagayamin” daukan
yaron Nura yayi ya rungume ahankali tareda mannamai kiss akai yama kasa magana yashiga
tafiya dashi yana sauka, Hadiza dake kallonsu tace “ai naso ka maren wlh danai suining naka
for domestic violence, try that next time kagani I will mess you up Nura” sauka yashiga yi kasa
yana dauke da Aman a hannunshi gaban dakin Ummi yakaishi yace “shiga” shiga yayi sannan
yajuya yawuce yafita daga gidan yashiga motanshi yamabar estate din gabaki daya zuciyanshi
daci takemai da gaske idan Allah yabaka mata nagari wlh ka gode kama kara godemai dan
shaidanun mata azaba ne, they will so push you to the wall kaji kaman zaka kashesu, yayi tafiya
mai nisa sannan yayi parking yakalli wayanshi yadade yana kallo kafin yasauke ijiyan zuciya

yakai hannunshi yadauka yabude yaciro wani lomba yakira wayan na gab da katsewa aka
dauka daga dayan bangaren wata yar dattijuwan manyantaccen murya ne tai magana. “Nura
barka da dare ya wurinku yasu Amalily?” Ahankali yace “lafiya lau” saikuma yayi shiru all this
years baitaba daga waya yakai karan matanshi ba sai yau jin yanda baiyi magana ba yasa tace
“lafiya Nura Maiya faru? Ina ganin wayan nasan da wani abu duba da lokacin dakama kirani,
what happened?” Ahankali yace “Hadiza bansan menene damuwanta ba, tunda na auri Hadiza
Anty Jamila for once bantaba kokarin takata ba ko shut her up, ni mutum ne dana tsani
takurama mata ko basu damuwa I have 4 sisters dukansu mata nataso da sanin yanda ake
girmama mace kare mace dakuma daraja mace” Anty Jamila tace “kwarai Nura wannan haka
yake zan shaideka ako’ina” ahankali yace “the whole idea da concept na feminism ya shiga
kanta, I’m not saying feminism is wrong no, ko Allah yasani inaso naga matata tacigaba, banki
duk matakin dazan taka aduniyan nan matata ta takashi ba, I empower her nabata jari tafara
business nakaita su dubai oman Egypt dasauran kasashe alokacin sabida ta saro abayoyi
tafara, bansan gobeba I believe empowering matata will go a long way for yaranmu incase of
gobe dabata da tabbas, bantaba ma Hadiza kallon wata baiwa ko yar aiki ba rather I see her as
life partner dina wacce nakeson to go through every phase na Rayuwa together mu tsufa
together but ita bahaka take ganin komi ba, gani take anything daya kamata tayi agida nima
yakamata nayi nida ita we are equal, yimin girki gaidani bani abinci is not her duty duka
abubuwan nima nayi we are equal afterall, gaidani akan me zata gaidani nima na gaidata…”
dasauri Anty Jamila tace “subhanallahi” dan ijiyan zuciya yasauke yace “Anty Jamila the whole
feminism din nata haukane kawai, rashin kunya menene menene babu wanda bata mini nakasa
gane kanta balle kafanta, i can’t even talk to her kafin nayi magana daya tayi dari, Anty Jamila I
am tireddddd nagaji, I want peace of mind at this my age” yanda yayi maganan saida yabama
Anty Jamila tausayi tasan yanda Nura keda hakuri tasan for Nura yadauki waya yakirata
takaishi bango anatse tace “Nura kayakuri kayakuri shikenan abinda zan iya fadi kaga wannan
halin shine dalilin dayasa maza da yawa basason bama matayensu freedom har subarsu suyi
sana’a dan wasu matan dazaran sun soma taba kudi shikenan sai sudinga jin kansu kaman
giwaye suma yanzu sun faso, amman kabarni da ita zan kirata zan kira Mama kuma” ahankali
yace “please kada ki sanarda Mama tana fama da hawan jini saisa nakiraki ban kirata ba”
murmushi tayi tace “to shikenan amman dan Allah kayakuri” ahankali yace “to saida safe agaida
yara” yakatse wayan yadade ahaka yau bacin ran yasa he wanna be alone ma inda bahaka ba
zai iya kiran abokan shi yaji inda suke yaje yasamesu, yayi kusan 3hrs awajen sannan yatada
mota yabar wajen.
Domin magana dani M shakur koso nasaki a group dina chat me up tanan
wa.me/+2347012181461

Yana katse wayan Jamila ta danna mata kira wayan harya katse bata dauka ba akaro nabiyu ne
tadauka tace “Hellooo Anty Jamila” cikin fushi Jamila tace “ke wace irin mahaukaciya ce
Hadiza? Ni wlh I don’t even need to ask you nasan kene da laifi dan nasan kalan hakurin Nura
tunda yau dakanshi yadaga waya yakirani nasan kin mai babban laifi” tsaki Hadiza taja dayasa
Anty Jamila tasake baki, cikin fushi Hadiza tace “ohhh kiranki yayi yahada mini munafinci? To
wlh zaizo gidan nan yasameni ina jiranshi” jin yanda yake magana kaman tana jiran wani saran
wasanta yasa Anty Jamila tace “Hadiza are you okay kuwa? What has gotten into your head?

Nuran kike magana haka akanshi?” Cikin fushi sosai Hadiza tace “Anty Jams bazaki gane bane,
Nuri finds every little way to belittle me, nan Abuja ne fa ba kano ba but kullum so yake ina
shiga kitchen namai abinci, a Abuja yan aiki ke girki matan gida relaxing take bayinta namata
aiki, inada yar aiki ai nama baki labari wacce nace miki su Aman na sonta, ita ke kula dasu I am
busy da shigo gida nawa yake so naraba kaina? Sai nasa yar aiki tamin wani abu yahanata
yimin sabida shike biyan kudin shine nacemai