Back to novel

Chapter 5 of 41

BAƘIN HAURE Jini da Dukiya by zahra'u yahaya

kwadaitu da son sanin wacece Ni?"

&&

Tarkon makiya

"Bayan an yi sallar Isha, da ya jagorance su, yayi musu addu'a. Sannan ya mike tare da kallon sauran abokan shi da suke su bakwai ne, sauran kaso masu girman suna tare da Commodore Magaji Abba Chindo, murmushi yayi sannan ya dauko kayan aiki, yana kuma da kayan da zasu saka idan zasu faWa cikin ruwa. ""John ko zaka zauna anan ne naji kace matarka ta kusan haihuwa."""

"Daukar kayanshi yayi yana sakawa, ""Cab ai nayi Imani da Allah, amma gara na mutu a filin yaki da ace ina nan, ina jiran dawowarku."" Ya fada yana saka rigar ruwanshi domin ana iska don har tana kad'a jirgin ruwansu."

"""Ammar kai ma ko zaka zauna ne, kace rabonka da Misau tun haihuwar Anam, saboda inda zamu mutanen suna dauke da miyagun makamai."""

"""Hmm! Fatana kada Kasata ta mance da 'ya ta."""

"""Kana nufin zaka bi ni kenan!"" Haka yayi ta rokonsu da su hakura da bin shi, amma ina baki daya suka nace, sai sun bishi anan ne suke ta hira da zasu tafi wurin karfe tara na dare, ya dauke su zuwa wurin Commodore. ""Zamu tafi Sir! Dayawa sun daura hakkin kula da rayuwarsu akanka da kuma ni, Sir sun yarda da kai ne suka gwammaci su zauna da kai, Sir hakkin mu ne mu kare kasarmu da mutanen da suke karkashin kulawarmu. Please Sir gasu nan"""

"Har ya gama maganar Magaji Abba Chindo,bai ce mishi cikanka ba domin kuwa baya fatan ya bude baki yayi magana, Babban burin shi Captain yana barin jirginsu yan tada kayar baya su yi musu daga-daga da namar su, shi yasa da ya ce ya tafi,ya fara bin sauran yana gaya musu ai fa Captain da suke ganin zasu bi, bai da lafiya da zaran an fara harbe-harbe cutarshi zata motsa. Muna cikin zamani ne da son kai yayi mana katutu, kowa son ranshi yake haka yasa baki daya suka janye bin bayan Captain."

"Kuma an gayawa Captain amma kuma bai ce kome ba, domin bai dauki haka a matsayin wani abu me"

"muhimmanci ba. Yasan Commodore Magaji Abba Chindo yana jin haushinsa, amma kuma bai kawo a ranshi kiyayyar zata girmama haka ba, sai dai ya ce Allah ya kyauta."

"Haka suka bar wurin da jirgin yake da wasu kananun jiragen ruwan, masu colour din navy blue. Haka suka shiga tafiya daidai an fara ruwan sama me karfin gaske."

"Haka suka yi ta tsala gudu, a nan Jirgin aikinsu, suna barin wurin aka shiga shagali da hidima, dama kafin dare sai da Commodore ya tura wasu matasan sojoji biyu suka kwasu musu yan mata, aka shiga shagali."

"Haka yasa yaki barin Captain zama domin, yasan matu™ar yana nan ba zai bari ayi shagalin ba, asalin sun manta da aiki suka zo yi, haka yasa suka yi ta shagali ga shi ana ta ruwa kamar da bakin kwarya."

"---- A bangaren Captain da mutanen shi, ba karamin gudu suke ba, kasancewar takun yana jan jirginsu, karshe shi"

"ya amshi tukin, ya kalli John ya ce mishi. ""Da matukar hatsari fadawarku ruwan nan, a daidai wannan lokacin don haka tunda ana ruwa ku kashe fitilar goshinku, zamu isa har jikin jirgin."""

"""Ok Sir"" shi ya fara kashe wutar nashi sauran mutane bakwan suka kashe nasu."

"A hankali suka yi ta tafiya, har suka isa wurin babban jirgin da yake dauke manya cantainers, zuwa kasashen"

"waje. Tsayawa suka yi kusa da jirgin, sannan suka harba abin da zai rike su idan suka sauka daga cikin jirginsu. Hakance kuwa ta faru duk su bakwai suka shiga cikin ruwan bayan sun daure kugunsu da wata igiya, sannan suka fara hawa jikin jirgin har suka shiga saman jirgin."

"Babu kowa, Captain shi ya musu jagora, har cikin jirgin inda ya fahimci za a fara kwasar man saura wani lokaci"

"kadan, don haka suka samu maboya suka boye, tare da samun bayanai akan kari. Sun kai wurin karfe sha biyu kafin aka fara aikin kawo danyen man fetur din, don haka sai da suka samu damar musu kawanya, kafin suka bude wuta a sama, dole yan daban suka yarda makamansu, domin abin ya basu mamaki, ""dama sojojin da aka kaiwa hari daban ne da waWannan sojojin?"" Inji Shugaban yan daban. ""Captain ka ji sun kai hari jirginmu........."

Waye zai mutu? Waye zai rayu follow my golden Pen. #Thedambuje

"[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*ZINARIYAR MACE *

"*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*"

Na gyaran nono. Na sanyi.

Dilka tare da hadin sabulu.

Duk Wani nau'in maganin mata.

"Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani."

*08089965176*

*07084653262*

*005*

"""Captain mai zamu yi?"" Shiru yayi yana kallon yan tadda daya bayan daya. ""Sir me zamu yi?"" A hankali ya saka hannunshi ya ballo tear gas, tare cilla musu, sannan suka ™are fuskokin su, ai kuwa sai ga hayaki fuuuuu, haka yasa shi shiga cikin hayakin tare da kama su sannan suka daure su baki daya, kafin ya mike yana faWin. ""John zaka tsaya anan, kai dasu Ammar, duk wanda ya motsa ku sakar miishi wuta ko waye shi?"" ""Ok Sir!"" Sai da ya karkasa su sannan ya sauko ruwa ya nufi inda jirginsu ya™e na aiki. Sosai yayi shirin tunkarar asalin jirginsu da aka kaiwa hari."

"Koda ya isa ya samu babu kowa a cikin jirgin sai wasu mutane biyu, da suka jikata sosai. Durkusawa yayi a"

"gabansu. ""Me ya faru?"" Cikin azaba da Harbin da aka mishi ya fara bashi labarin. ""Muna cikin shagali bayan tafiyarku"

"sai kawai muka kaji ™aran harbi, ashe yan fashin tekun ne suka mana tarko."" A hankali ya mike tsaye duk da ruwan"

"da ake yi, dafe kanshi yayi ya koma cikin jirgin mutum daya ne a cikin matu™an ya tsira shima yadda ya fada don ya shiga ban dakin kasa Allah ya kubutar dashi. ""Yanzu ka juya da jirgin zuwa headquarter zan tawo da sauran mutanen."" Ya fadi haka yana fita daga jirgin, a hannun dayan mutumin ya samu takarda. Amsa yayi yana dubawa,"

"*Mun ji labarin baka tab'a fita operation ka fadi ba, so wannan karon ka zo ka amshi yan uwanka sannan ka sakar min mutane na, ko na kashe Commodore.*"

"""Zaku wuce headquarter zan tawo da wancan jirgin."" Ya fita da sauri ya koma asalin jirgin yan fashin tekun, tsoron shi daya kada suma tarko aka musu. Koda ya isa ya same su, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya saka aka karkato kan jirgin, baki daya suka nufi headquarter Winsu,. Suna isa dama labarin ya isa an kaiwa jirginsu hari har an sace wasu sojojin. Yana isa da wadanda aka harba, asibiti aka wuce da su. Admiral da kanshi ya zo inda aka ajiye jirgin. A lokacin karfe biyu na dare, ""Sir!"" Ya sarawa Admiral. ""Aiki yayi kyau, yanzu wani hali Magaji yake ciki tare da sauran abokan aikinku."""

"""Umarni nake jira mu sake sabon shiri."" Captain ya faWa yana sarawa. ""Zan duba lamarin yau, amma tabbas dole a kai musu Wauki."" Mika mishi takardar da aka ajiye musu yayi. Shiru Admiral yayi yana kallon takardar. ""zan tura yau kafin gobe zan nema maka _permission_ """

"""Ok Sir!"" Ya sara mishi, sannan suka bar wurin aka wuce da mutanen da suka kamo, lokacin da ya shiga barrack din baki daya labarin ya karad'e cikin barrack din, waWanda mazajensu suke hannun hankalinsu ya tashi, waWanda mazajensu suke asibiti, a daren wasu suka yi ta wucewa, su kuma suna tafiya a mota. ""Yallabai wannan abin da ya faru, da damu zai faru Allah ya tsare mu."" Gyada kai yayi yana kallon hanya, kofar gidanshi aka sauke shi, kasancewar shi ne babba a cikinsu. Sai da ya fito ya ce musu. ""Kada ku manta ku kula da kanku. Idan sun gama zamu tafi gobe ko jibi."""

"""Ok Sir!"" Sannan ya ce musu. ""Ku kula da iyalinku."" Ya wuce ciki da sauri, yana shiga ya sauke ajiyar zuciya bayan ya shiga da sallama, a ka'idar wannan operation din ba a fita da waya, daga nesa ya hango wayarshi yana haske, a matu™ar gajiye ya isa wurin. *Brother* ya gani baro-baro a saman screen din wayar, a hankali yayi picking yana sakawa wayar a kunnen shi. ""Baka yi barci ba?"""

"""Taya zan yi barci bayan wurinka na zo."""

"""Ka koma, ina da abinda zan yi nan da kwana biyar."""

"""Ai na gama nawa kawai, ka shirya."" Brother ya gaya mishi. Dafe goshi yayi yana sosawa ya ce mishi. ""Ka koma inda ka fito, don Allah."" ""Babu inda zan tafi."" Yana fadar haka ya kashe wayar. Zama yayi jikinshi da matukar damuwa."

*Zahrah*

"Muna kwance muka ji kar'ar motar daukar marasa lafiya. Kafin wani lokaci asibitin ya cika da hayaniyar mutane. Har kusan karfe hudu na asuba, can sai ga Dr Umaima ita da wasu Nurses su uku. ""Baku yi barci ba?"" Girgza kai nayi nace mata. ""Eh Aunty, amma lafiya?"" ""Sojojin mu ne suka hadu da tsautsayi, Sisi kira mana Captain aikin nan ba zan yi ni daya, sannan ki haWa da Mrs Kayode hutun ya ™are."" A hankali ta tawo kaina. ""Nasan kuna da hankali, please ku kula da kanku sannan kada ku ce wani abu."""

"Gyad'a kai nayi nace mata. ""tow Aunty Umaimah."" Fita suka yi, can kuwa muka kara jin hayaniyarsu ya karu, Zuzu kan duk abin da ake tana ta barci, sai da na gaji na tashi zaune ina yatsina fuska."

"Suna fita basu wani Wauki wani lokaci ba, suka yi ta kiran wayar likitocinsu."

"Haka suka halarta kafin wani lokaci sun fara aiki, kafin karfe shida na safe, sun fito daga aikin. ""Captain ko zaka kwanta ne?"" Ta tambaye shi cikin kulawa, domin Allah ya jarabceta da kaunarshi, amma shi babu haka a ranshi. Gyada mata kai yayi, ko bude idanunshi baya iyawa balle yasan inda yake jefa kafarshi, haka ta juya itama ta bar sauran aikin a hannun Mrs Kayode ta tafi gida."

"Dama mun yi da Zuzu karfe shida zata wuce ko shida saura domin tun fitar Dr Umaima, itama ta farka ta leko mana abinda yake faruwa. Har tayo saurayi a cikin sojojin. Shi yace zai kai ta gida, muna idar da sallar asuba, ya zo suka tafi ni wani barci me karfi ya dauke ni. Ko don mun raba dare bamu yi barci ba ne. Haka nayi ta barci kamar me, yana shigowa ko don ya gaji ne, kawai yana shigowa ya kwanta. Tuni barci yayi gaba da shi, duk da yana son yin sallar asuba, amma ina barci me nauyi yayi gaba da shi."

"Wani ikon Allah dukkan mu biyu babu wanda ya fahimci halin da dayan mu yake ciki. Har wurin sha biyu lokacin Nurse tazo duba ni, anan ta same mu kwance ya tattara ni ya cusa cikin jikinshi ni kuma kamar mage na kwanta kwayam kamar mage, ko yanayin ba mamaki ko dumin da muka ji daga junanmu ya haifar mana da barci me nauyi, ganin haka ta juya tana me barin dakin, Dr Umaima ta kira ta gaya mata. Ai babu shiri sai gata a asibitin, tana isowa Zuzu tana isowa itama. Kallon juna suka yi, kafin Dr Umaima ta Wan bata rai tana faWin. ""Ki jira ina zuwa.""tana faWin haka ta shigo, a hankali ta tashe shi, kaina yana kirjinshi, hannunshi dukkan biyu ya zagaye ni dasu. Sake tab'a shi"

"tayi ya buWe ido dakyar yana kallon ta. ""Kafin ka dawo hankalinka ya kamata ka san inda kake."" Kallonta yayi, sannan"

"ya kalli inda nake kwance. Bai ga fuskata ba, amma baki daya yaji lissafinshi ya fara aiki kamar wanda ya aikata wani mugun aiki, ya ware manyan idanunshi ya kafeta da shi. ""Su waye a waje?"" Sanin ko ta fusata ba zai dame shi ba. Ta ce ""babu sosai."" A hankali ya zare jikinshi a nawa, kafin ya saka kafarshi cikin takalminshi, yana kallonta. ""Baka duba ciwon ba, sau biyu aka yi aikin fa."" Cikin kamewa da nuna kamar bai aikata kome ba, ""Good!"" Ya saka kai ya fita. ""Karfe nawa?"" Agogon hannunta ta kalla ta ce. ""12:30"" ""innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Ban yi sallah asuba ba."" ""Sai dai sallah safe."" Inji Dr Umaima. Da dan sauri ya bar ward din, dama dabi'arshi ce matukar yayi aikin dare tow ba makawa sai ya shiga daki daya yayi barci, a gidanshi baya iya barci kwana yake yana mafarki."

"Koda ya fita motarshi ya faWa, da gudu yana shiga ya bata wuta, kan lokaci ya isa gidan, a kofar gidan ya taradda motar bmw, sai da ya tura motar gefen gidan,a kasar bishiyar lim, yayi parking da sauri ya fito tare da kallon inda motar take. Bai ga alamar da wani ba, haka ya wuce motar ba tare da ya kalli inda motar take ba, ya shiga kokarin buWe kofar gidanshi, a hankali yaga kofar a buWe ya™e. ""Emmanuel yazo aiki kenan?"" Ya tambayi kanshi,cikin gidan ya shiga tare zubawa wanda yake zaune idanuwa. Dauke wuta yayi tabbas a duniya an rena shi. Wucewa yayi a gaggauce ya nufi dakinshi. ""Na ga kayan jini, na san baka fara kisan kai ba, balle na ce ka fara amma na wanke Yaronka bai sani ba, domin ya same ni a kofar inajiranka."""

"Bai ce mishi cikanka ba, ya wuce dakin yayi wanka da alola yazo ya gabatar da sallar asuba, sannan ya hada da zuhur. Shima bakon zuhur din yayi sannan ya wuce kitchen. Abinci ya dafa musu mai kyau sai kamshi yake, a hankali ya nufi falo da abincin, ya ajiye nashi sannan ya wuce da na Captain Win ya ajiye mishi a gabanshi. ""Kaci nasan kana nan kana wasa da cikinka, ga aikinka aikin hatsari ne."" ""Me yasa baka jin magana?"" Ya tambaye shi yana kallonshi. ""Ni kuma? Ai idan akwai mara yafiya da rashin jin magana kai ne dai baka jin shi, kai a dadin ranka ne ka bar mahaifiyarmu tana kuka tana gayawa Allah yaushe zaka dawo gare ta? Ya Majeed duk abinda ya wuce ya wuce, a barshi ya wuce ban ga amfanin datse ala™ar da kayi ba."""

"""Aryan ka koma kace baka ganni ba."""

"""Zan koma amma ka sani na gama abin da ya kawo ni, gashi ka duba."""

"Ya ajiye mishi takardar izinin tafiya da Captain Majeed Mamman Ba'are, kuma Doctor a wani bangaren."

"""Akan me zaka min haka?"" ""Muna da Kyakyawar ala™ar kasuwanci da kamfanonin mu da mahukuntan Nigeria, don haka kai tsaye daga sama na liko da kai kasa, don haka sun baka hutun wata guda."""

"""Kasan hatsarin da abokan aikina suke ciki?"" Ya fada a fusace, ""bai kai hatsarin da BA'ARE GOLDEN EMPIRES yake ciki ba, sai ka zab'a saura kwana uku zaben, su kuma abokanka, zai dauki sati kafin su fito domin sun bada zabin a sake musu kayansu ko su kashe su. Na gama hada maka kayanka."" Ya fada yana ™o™arin barin dakin yana faWin. ""Akan shegen aikin da albashinsa bai wuce a sayawa karen gidan mu abinci ba, kazo zaka kare rayuwarka akanshi."""

"Shiru yayi yana kallon abincin, tabbas abubuwa dayawa sun faru. Amma kuma ba zai tab'a yarda ya rike musu kome ba, zai dawo bakin aikinshi. Kamshin abincin yasa shi jin wani irin yunwa, da sauri ya fara ci, shigowar Aryan Ba'are yasa shi d'ago kai yana kallon shi, zama yayi a gaban Aryan Mamman Ba'are, murmushi suka yiwa juna, zama yayi ya juye abincin kan na Captain Majeed, suka fara ci hawaye na zuba daga idanun Aryan Mamman Ba'are, diban abincin yayi a cokali ya mikawa Majeed din, amsa yayi yana kallon shi, ""kayi hakuri saura kwana huWu ne ba uku ba,