Chapter 19 of 60
RUWA CIKIN COKALI Sirrin Baƙo By MAMAN AFRAH
"Ashe wannan rogon shi ne ajalin iyayena, ni kuma kwanana ne a gaba shi ya sa ban ci ba, bayan mahaifiyata ta wanke ta dafa ta zuba min nawa ni da Aliya ta ajiye mana suka ci nasu daga cin wannan rogo sai ciwon ciki babu wanda ya san ciwon cikin har ya yi ajalinsu gabaɗayansu sai da muka je ni da Aliya mu ci rogo a nan na yi tozali da gawar mahaifana kwance kowa da dafara a bakinsa" Kukan da take yi ne ya hana ta ci gaba, sai da ta tsagaita ta ce
"Ashe dai wannan rogon taki ne aka zuba mai ƙarfi a gonar wanda gubar da jikin takin da yake jikin rogon bai fita ba shi ne ya yi ajalinsu duk da cewa an dafa shi amma dai takin bai bar jiki ba" Daga shi har ita kuka suke ta ci gaba da faɗin
Tun daga wannan rana na yi bankwana da iyayena, sannan Abba ya je har Doso amma neman duniyar nan ba a samu wanda ya san mahaifana ko wani wanda yake da alaƙa da su, riƙona ya koma hannun Abba har kawo yanzu" Ta faɗa tana share hawaye, ko a fuska bata faɗa masa irin ƙalubalen da ta shiga bayan mutuwar iyayen ba da irin canjin da ta samu daga Umma da Aliya ba wanda shi ne har yau bata sauya zani ba, a ganin Umma babu yadda za a yi Abba yake riƙe da ƴar da bai san wani dangi nata ba, sai kuma ƙoƙari da farin jininta wanda shi ne ummul aba,isin faruwar komai.
Ya daɗe yana jimanta abin sai ya ji wani mugun tausayinta ya shige shi, tabbas tsautsayi ba ya wuce ranarsa sannan rashin sani ya fi dare duhu da sun san rogon zai yi ajalinsu da basu ci ba, amma dama rai ba bakin komai yake ba. Haƙuri ya ringa bata har dai ta huce da za ta shiga gida ya ɗakko waya iphone 16 ya bata a kwalinta, dakyar ta karɓa sai da ya ɓata ransa, don dama kayan fitar biki da ya ɗinka mata cewa ta yi kar ya kawo saboda ita ko kaɗan bata son ran Aliya ya sosu.
Da sallama ta shiga gidan, Umma ta amsa tana washe baki, suna zaune da Abba suna magana ita kuma Aliya tana ɗaki ko da ta shigo a kan tabarmar ta durƙusa ta miƙawa Umma kwalin wayar tana mata bayanin wanda ya bata, Umma sosai ta nuna murna tana nunawa Abba ya karɓa ya saka albarka, Umma ta miƙo mata ta karɓa ta nufi ɗaki, abin mamaki tana shiga Aliya ta ce
"Ƙawata ƴar uwata" Lafazin ya zo mata a bazata har ta kasa riƙe farincikinta ta ajiye kwalin wayar a kan katifa ta je ta rungume Aliya tana faɗin
"Aliyata ta dawo gareni haƙiƙa na yi farin ciki" Ta faɗa har lokacin tana rungume da Aliya, tabbas tana son Aliya, Aliya kuwa ji take tamkar ta shaƙe Jidda amma haka ta daure ta danne zuciyarta ta nuna mata farincikin ta.
Bayan sun saki juna ta ɗakko wayar cike da murna ta nuna mata wani abu ya caki zuciyar Aliya wai Jidda ce za ta riƙe Iphone bayan ita tana fama da waya mai screen a ragargaje, haka ta danne zuciyarta ta nuna mata farincikin ƙarya, don yanzu dai ta ga Jidda ta kere ta a komai.
An shiga hidimae biki a inda Umam ta ɗauko duka kayan kicin ɗin da ta saya domin Aliya ta raba a biyu ta ce kowa ya ɗauki ɗaya a fili tana nufin saboda soyayya amma a baɗini ta bayar ne don su ƙara saka yarda a zuciyar Jidda, ita kuma Jidda sai take ji tamkar bata yi rashin mahaifiyata ba irin yadda Umma take nuna mata soyayya da kukawa. Ana saura kwana huɗu biki aka je aka yi jere mutane anguwa da kuma ƴan uwa, gidan Aliya suka fara zuwa ciki da falo da banɗaki sai ɗaki ɗaya da kuma kicin shi ma ba mallakin Nasir ba ne mahaifinsa ne ya bashi a kan cewar kafin ya mallaki nasa. Ranar da ya kasance saura kwana uku aka je aka yi wa Jidda sam barka jama,a suna ta yabon gida da kuma yadda kaya ya amshi gida faɗa ma ɓata baki ne.
Amare sun sha gyara don sai Aliya da ƙawayenta suka bi ayarin gyaran jikin su Jidda komai dai a na Jidda aka musu suka fito gwanin sha,awa an sha lalle ja da baƙi.
Umma aka samo mata number maman afrah marubuciya a jikin littfinta ta ruɓaɓɓiyar igiya, jin ana ta yabon kayan matan maman afrar mai suna DARAJAR MATA haka ta saya musu tsumin ƙorama, maganin sanyi mai suna a fatattaki sanyi kasancewar duk wani maganin mata ba ya aiki in dai akwai sanyi a jikin mace. Daka mai suna sirrin ma,aurata wanda yake saukar da ni,ima ga mace sai ɓulɓul na gyaran breast sosai maman afrah ta musu haɗi na kece raini wanda zai kankaro musu mutunci wajen mazajensu Umma ta yi hakan ne don Jidda ta yarda ɗaya suke da Aliya. Mai buƙatar maganin sanyi ko magungunan mata ya yi wa maman afrah magana a 09925576222
Duk haɗe haɗen da aka musu amma Aliya don ta fi Jidda sai da ta samo wami group na wata mai siyar da supplement mai suna mom farhan ta saya wani haɗi na combo wanda ta ga an rubuta a jikin set ɗin kamar haka Hajia indai mgnr emergency ne toh wanan shine kankat
Indai matsalar ki rashin niima da matsi ne toh ki siya wnn combo din zaki gode min, ina masu cewa sun sha magani har sun gaji basu taba sanin ya dadin se yake ba toh dan ALLAH ki gwada wannan combo din, ai Aliya tana ganin haka ta kwafi no admin ɗin kamar haka 0814 153 5308 ta mata magana ta turawa mom farhan hoton combo ɗin ta faɗa mata kuɗin ta tura mata aika aika mata ta ɓoye don ma kar Jidda ta gani.
An yi biki an sha kyau amma Aliya saboda baƙin hali duk wanda suka zo ƴan makarantar su sai ta faɗa musu cewa ai Jidda riƙw ta ake yi a gidansu ita ba uwarsu ɗaya ba ba ubansu ɗaya ba, amma a bayan idanun Jiddar take faɗa.
A masallacin unguwar aka yi walima ranar yini da yamma inda aka cika aka ɗakko malama juwairiyya ta yi wa,azi a kan biyayyar gidan aure, sai magriba aka tashi, duk da Aliya ta so Abba ya bari an yi bidi,a a bikin amma ina, don kafin ma a tafi walimar an sha hotunan amare da angwaye da kuma abokai da ƙawaye. Aliya tana ganin ta fi Jidda yin kyau amma dai kowa da irin nasa kyan.
Amare sun shirya tsaf sai ƙamshi suke, sun shirya cikin fararen laffaya mai goldin ɗin flowers sun yi kyau har sun gaji, Abba ya musu nasiha a kan biyayya da kauda kai a kan komai mutum ya ji kamar bai ji ba ya gani kamar bai gani ba. Umma sai hawaye take sharewa na rabuwa da yaran a fili amma a baɗini kukan rabuwa da Aliya take yi, sanna kuma tana kukan takaicin Jidda za ta tafi gidan jin daɗi da hutu.
Kasim ya kawo mutoci guda huɗu a inda motocin ɗaukan Jidda sun fi ashirin motoci ne na alfarma, sannan Abba ya ce a tare za a tafi idan aka kai ɗaya sai a wuce a kai ɗaya. Jama,a sun shiga motoci inda mota ɗaya aka saka amare a ciki sai iyaye guda biyu don amaren ne a tsakiya, Jidda tana kukan rabuwa da gidan a gefe ɗaya tana kukan tunano iyayenta musamman da ta kalli gidan da suka rayu da mahaifanta amma kuma yanzu gashi za ta tafi ɗakin miji ba tare da suna duniyar ba rayuwa kenan.
Motoci sun miƙa a kan titi suna tafiya a laye inda amare suke ta kuka abinsu. Gidan Jidda aka nufa inda yake unguwar GRA a ƙofar wani tanfatsetsan gida motocin suka fara tsayawa horn ɗin da aka saki a kusan tare-tare shi ne ya ankarar da Aliya da take zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka wanda ya zama kuka biyu na rabuwa da Umma da na baƙincikin Jidda. Matan cikin motar ƴar uwar Umma da Abba ne suka haɗa baki wajen faɗin
"Kai jama'a wannan gida tamfatsi, tamkar ba a nigeri,a ba wannan ai shi ne aljannar duniya!". Aliya wacce maganar ta su ta saka ta faɗuwar gaba mai ƙarfi bata san lokacin da ta ɗago da kanta ba, don wannan furucin ya tabbatar mata gidan Jidda aka fara zuwa, domin ta san da gidanta ne ba za a faɗi haka ba, ɗago kan da za ta yi ya yi daidai da wangale get da mai gadin ya yi, motocin suka fara shigewa ciki a jere, a inda Aliya da ta ɗago ta sauke a kan wani haɗaɗɗan gida na masu aji kuma masu hannu da shuni, wanda ko ita bata taɓa tunin za ta shiga ba bare wata Jidda baƙa mummmuna!.
Ganin gidan ya sa hankalinta ya tashi irin tsaruwarsa da yadda wasu kyawawa fitilu suka masa ƙawanya, tana ganin hakan ta cikin laffyar da ta lulluɓa ita kanta bata san lokacin da ta cire lulluɓin ba, babu zato da tsammani ƴan cikin motar suka ji ta ce
"Wayyo Allah na shiga uku!!!".
MAMAN AFRAH
09025576222
https://chat.whatsapp.com/DNhoKsIb9qP8PlVQdpQ4BW?mode=ems_copy_c
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1️2️⃣
*SADIYA*
Tun da ta zauna take ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tashin hankalinta ruɓanya yake idan tana tuna cewa Nasir ba ya son haihuwa kuma ko ɗazu yana nannagon ta , sannan tun yanzu tana ita kaɗai da ɗa guda ɗaya yana nuna gajiyawa da ɗaukan ɗawainiyarta bare kuma aka ce ta sake haihuwa, mutumin da yake batun ta kama sana,a don take tallafawa a cikin gidan bayan kuma ko ciyarwa ƙauro yake sai abin sa ya ga dama zai bayar.
Hannu ta ɗaga idanunta yana zubar da hawaye ta ce
"Ya Allah kai kake bayarwa, kuma kai ne kake hanawa, wasu bayinka suna neman haihuwa baka basu ba, ina godiya da ka bani kuma ka ƙara min, ya Allah bam gajiya da kyauta da ƙarin da ka min ba,ya rabbi ka sassauto da zuciyar Naasir kar ya wulaƙantani a kan cikin nan" Tana gama faɗar hakan ta koma ta jingina da jikin kujera tana ta saƙa da warwara kan cewar ta sanar da shi ko kuma ta ƙyale shi, idan ra sanar da shi ba tira za ta yi daga matsalarsa ba sannan idan ta ƙyale ɗin ma akwai ranar ƙin dillanci tun da shi ciki ɗan duba ne duk daren daɗewa, zai bayyana kansa!.
Bayan kwana biyu bata faɗa masa ba, tana nan tana ta nuƙu-nuƙun sanar da shi tana tsoron abin da zai biyo baya, saboda haka ko yana gidan idan ta ji amai yana yunƙuro mata sai ta yi ta dannewa tana addu'ar Allah rufa mata asiri kar ya gane, saboda idan ya sani a ɗaya za a yi biyu ko dai ya sake ta ko kuma ya ringa ƙuntata mata a cikin gidan. Bayan sati guda da sanin tana ɗauke da ciki har lokacin Nasir bai san wainar da take toyawa ba, ita kaɗai ta san tana da ciki sai kuma ƙawarta, amma duk wani laulayi da take fama da shi dannewa take duk ta yi baƙi ta rame. A wata ranar alhamis ne bayan ya fita dama yau bata ga ya yi shirin fita kasuwa ba, zuwa can sai ta ji daga windown ta da yake ta waje ana cewa daga nan za a ajiye bulo, da siminti ta yi mamakin masu ajiyewar don bata ji muryar Nasir ba hakan ya bata tabbacin ko dai wasu ne suka kawo ajiya.
Bayan kamar awa guda ta ji ƙaran babbar mota, motar bata tsaya a ko ina ba sai ta ji ƙaran tsayawarta a ƙofar gidan, motar yashi ce don haka tana ji aka juye yashin motar ta tafi. Muryoyin mutane ta ji sai kuma ta ji muryar Nasir yana cewa su kwaɓa yashin da siminti sai kuma ta ji an turo ƙofa wasu matasa suka yi sallama sai ta ji Nasir tana cewa su shigo da shi, tana ɗaga labule ta ga bulo ne suke ta shigowa da shi, hakan ya bata tabbacin ginin ɗaya part ɗin ne za a tada da alama auren nasa ne ya kusa.
Bai sanar da ita cewa za a yi aiki ba, don haka sai take saka hijabi idan za ta fito tsakar gidan, haka ma,aikata suka fara aikin ƙarasa ginin nan tuƙuru ita dai babu wanda ya ce mata ita ma kuma bata ce ba.
Cikin sati ɗaya aka gama komai na ɓangaren, an saka ƙofofi an yi fenty hatta wuta an ja ɓangaren, da yake har da ɗakin Nasir ɗin mai bayi a ciki, ɗayan kuma ciki da falo ne da banɗaki a ciki. Ita dai bata ce komai ba tana ganin ikon Allah.
Ranar wata juma'a da safe tana zaune haka kawai ta ji tana jin amai ta yi iya ƙoƙarinta na ta dakatar amma abin ya ci tura, haka ya sa ta fita da sauri ta shiga sheƙa aman, kamar an jefo Naair sai ganinsa ta yi ko riga babu ya zo ya tsaya yana wani zazzare idanu ko aman bai tsaya mata ba ya buɗe baki cikin hargowa ya ce
"Wai aman mene ne kike yi bayan lafiyar ki ƙalau?" Tambayar ta kiɗima ta haɗe da ruɗa mata ciki don ta ji tsoro sosai don da alama ko ya fahimci wani abu dangane da ita. Sai da aman ya tsagaita mata ta wanke bakinta da fuskarta a famfon wajen duk ta galabaita a daidai lokacin ne ya sake jefo mata wata tambayar tamkar zai hau ta da duka.
"Sadiya na ce aman uban mene ne kike yi?" Idanu ta ɗaga tana kallonsa ƙirjinta yana dokawa da ƙarfi, ta san dai ko da a ce cikin ne ai ya san ba a waje ta samo ba, tun da sh ne maijinta kuma shi ne mai yawan buƙata kullum abu ɗaya, sannan ai ita ba za ta hana ubangiji ikonsa ba.
Bakinta ne ya yi nauyi tana tunanin ta ina za ta fara, kafin ta samu ƙarfin gwiwar amsa masa, don a ganinta baƙin alƙalami ya bushe, kawai ya kamata ta sanar da shi in ma yankata zai yi to gwara ta faɗa ta fita daga zulumin da take kwana take tashi da shi tamkar wacce ta yi cikin shege!.
A hargitse ya ce
"Idan baki faɗa min ba wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi in har ya yi aiki mai kyau!" Cike da karkarwar baki ta ce
"Lafiyata ƙala...Tun kafin ta ƙarasa faɗa ya katse mata hanzari da faɗin
"Yanzu ba lafiyarki nake tambaya ba aman mene ne?" Kamar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito haka ta ji ganin yadda yake zare ido, a take ta fara tunanin cewa dama haka wasu matan suke fuskanta idan mazajensu basa son haihuwa? Kuma ya kasance macen ta samu ciki haka suke shiga fargaba da tashin hankali?.
Maganarsa ta katse mata tunanin inda ya ce
"Wai ba magana nake miki ba Sadiya? Wato kin mayar da ni kare in yi ta haushi?" Cikin inda -inda ta ce
"Ci...ci...ciki ne da..." Wata wawiyar tsawa da ya doka ita ce silar tashin Kalifa da ya koma baccin safe sai kukansa ta ji,
Nasir ya ce
"Wato kin samu ciki shi ne kike ƙunbiya-ƙunbiya baki faɗa mini ba, wato ga Nasir ɗangote ko Nasir A A Rano shi ya sa za a ke mini haihuwa a kai-akai tun da ni me dukiya ne ko? Ɗan rufin asirin da Allah ya mini kike so sai kin kwantar da ni Sadiya ki tara min ƴaƴa tsufa ya hau ni, a zamana bani da kataɓus sai ƴaƴa to wallahi baki isa ba!" Ya faɗa yana nunata da yatsa, fitowar Kalifa ya sa ya kalli Kalifan yana sakin wani wawan tsaki, shi kuma Kalifan da sauri ya kauce daga hanyar da Nasir ɗin yake tsaye ya yi wajen Sadiya yana ɗan kuka tare da murza idanu.
Fuuuu ya juya