Chapter 11 of 60
RUWA CIKIN COKALI Sirrin Baƙo By MAMAN AFRAH
"Kawo in taimaka miki" Kawai da ta juyo sai ta kasa hana shi kwarjini ya mata ta ga yana da kima da kuma kamala. Ɗakko mata ruwan ya yi har ya kawo ƙofar gidan, kasancewar ya saba ruwa a banɗaki sai dai ya tara ya yi wanka tunaninsa zai ji nauyin bokiti amma da yake soyayya yake yi wa bauta sai ya ji ko alamar nauyi babu kamar dai ya ɗauki bokiti mai auduga ne. Yana zuwa ya ajiye ya ɗago yana kallon ta cike da jin daɗin abin da ya mata ta ce
"Sannu da ƙoƙari na gode ƙwarai"
Wani daɗi ne ya cika shi kamar ya taka rawa jin muryarta tana masa godiya da jinjina masa.
Har za ta ɗauki bokitin ta juyo ta ce
"Don Allah ka yi haƙuri abin da Aliya ta farfaɗa maka" Yana jinjina dattakon ta ya ce
"Ni dama ...am dama ke zan ce ta yi min magana da ke shi ne ... Ya faɗa yana inda -inda
Cike da mamaki ta kalle shi tsantsar mamaki yana bayyana a kan fuskarta ta ce
"Ni kuma?" Ta faɗa zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, ta san dai jiya ta yi ta addu'ar ita ma Allah ya fito mata da mai son ta wanda zai aure ta ya riƙe ta da daraja idanu ta ɗan runtse ta buɗe ta ce
"Lafiya dai ko?"
Yana kallon yanayin ta ya ce
"Na zo don in bayyana miki soyayyata wallahi ina ƙaunarki da gaskiya tun daga ranar da na fara tozali da ke" Ya faɗa zuciyarsa tana zillo kawai gani yake ba za ta amince da shi ba saboda kyaun da yake da shi tun da da kunnensa ya ji ta ce bata son mai kuɗi kyakkyawa.
Jidda kuwa jikin ta ne ya fara rawa kasantuwar abin ya zo mata a bazata, kuma dai mutumin ya birge ta musamman da ta ga cin mutuncin da Aliya ta masa bai biye mata ba duk da bata san abin da ya haɗa su ba sannan da taimakon ta da ya yi ya ɗaukar mata ruwa.
Rasa amsar da za ta bashi ya sa ta ce
"Sai na yi tunani tukunna"
Wannan furucin nata ya saka shi a wasi-wasi amma ya danne ya ce
"Babu damuwa Allah sa ki yanke abin da ya fi zama alkairi " Yanayin yadda ya yi maganar ya sa ta ji wani iri kamar dai bata kyauta masa ba kamar dai bai ji daɗin furucin ba.
Bata ce masa komai ba ta sunkuya ta ɗauki bokiti har ta fara tafiya ya ce
"Jidda" Har tsakiyar kanta ta ji kiran sai ta ji tamkar shi kaɗai ne ya iya kiran sunanta daidai, sai dai bata san dalilin hakan ba, juyawa ta yi bayan ta ajiye bokitin ta ce
"Na'am" Ta faɗa idanunsu suna sarƙewa da juna da sauri ta yi saurin kawar da nata, kasancewar sai ta ji kallon da idanunsa suka jefe ta da shi ya sha bamban da kallon kowane mutum.
Iska ya ɗan hurar daga bakinsa ya ce
"Ki daure ki bani phone no ki" Kamar ba za ta ce komai ba har ya cire rai za ta bashi sai ya ji ta fara karanto masa, nan ya shiga rubutawa a ƙaramar wayar da ya taho da ita. Tana gama faɗa masa va tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta ɗauki ruwan ta shige gidan.
Tsabar murna bai san ya isa bakin titi ba don ko wahalar tafiyar ba ya ji, wani irin farinciki da yanayi marar misaltuwa da yake ziyartarsa, haka ya yi kwanan farinciki amma dai ya kasa kiran wayarta don sai ya rasa mai zai ce idan ya kira.
Bayan kwana biyu, har lokacin bai koma gidansu ba kuma bai kira ta ba, sai dai yana ta dakon soyayyarta. A ɓangaren Jidda tun daga wannan ranar ta ji ta damu da Ibrahim sai dai rashin kiranta a waya sai ta ji duk babu daɗi, tun tana jiran kiransa har ta cire rai, da ko baƙuwar no ta gani sai ta yi tunanin shi ne har dai ta cire rai daga kiran nasa. Sai da aka yi sati sannan watarana da yammaci yana zaune a ƙasan wata bishiya a wata unguwa yammaci ne mai cike da ni'ima sassanyar iska tana kaɗawa, yana zaune saman motarsa ya kamo sunan ya shiga kiranta, Jidda tana hura wutar da take tuwon dare ta fara jiyo ƙaran wayarta, amma bata je ta ɗakko wayar daga ɗaki ba. Har kiran ya tsinke bata je ba, Ibrahim kuma sai ya fara wata zufa hankalinsa ya tashi ya fara tunanin ko dai ta yanke shawara marar kyau a kansa, kuma da ya yi tunanin ai bata san numbersa ba sai ya ji hankalinsa ya ɗan kwanata a ƙara gwada kiran.
Tunanin ta ma ko Salama ce ita ce idan ta fara kira bata san ta daina ba, hakan ya sa ta iza wutar ta nufi ɗakin, tana ɗaukan wayar ta ga baƙuwar no dama gidan babu kowa sai ita kaɗai duk sun fita gidan biki. Bata san mai ya sa ba amma sai da gabanta ya faɗi tana dannawa ta ƙara wayar a kunne.
Sassanyar muryarsa mai amo mai daɗi da ita ya fara mata sallama, idanu ta lumshe kaɗan ta buɗe su bata san dalili ba amma sai ta ji ta yi farin ciki da kiran, bata san ko don ta daɗe tana jiran ya kira ta ba ko kuwa mene ne oho.
Amsa sallamar ta yi sai ya ce
"Sunana Ibrahim ni ne kika ba numberki ranar da kika ɗauki ruwa" Wani murmushi ya kuɓuce mata marar sauti a zuciyarta tana raya da a ce ya san cewa bata da wani saurayi da bai wahalar da kansa wajen tuna mata ranar da suka haɗu ba.
Cike da murnar da bata bari ta bayyana ta a fili ba ta ce
"Na gane ka"
Ya ce
"Ya batun tunanin kin yanke hukuncin"
Ta ce
"Hukuncin me?"
Ya ce
"Hukuncin na cancanta ki kula ni ko ban kai ki kula ni ba" Maganarsa ta bata dariya hakan ya sa ta dara har yana iya jiyo sautin dariyar ta cikin wayar.
Jingina ta yi da bango ta don dama a tsaye take ta ce
"Ban amince ba" Gabansa ne ya buga da ƙarfi a take ya ji gabaɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi, ɗan walwalar da ya tsinci kanaa sanadin magana da ita duk sun gaushe.
Bata tantance ba ta ji saurin maganarsa cikin tashin hankali yana cewa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Bata san dalili ba sai ta ji zuciyarta babu daɗi ta ji duk ta damu da yanayin sa ya shiga bata san lokacin da ta ce
"Da wasa fa nake maka na amince" Daga ita har shi dariya ce ta ƙwace musu.
Sun daɗe suna hira kamar sun saba daga bisani ta ce masa aiki take saboda ta ga abin nasa ba na ƙare ba ne, wayar ta ajiye ta fita ta ƙarasa tuƙa tuwon, sai bayan ta kallama aikin ta yi wanka ta zo ta ɗauki wayar ta yi saving no da IB tana ta maimaita hirarsu a zuciyarta.
Washe gari tun da asubar fari Aliya ta ishe ta da cewa saura sati guda a kawo mata kayan saka rana, amma Jidda ta yi kamar vata ji ba daga ƙarshe ta ce Allah sanya alkairi amma sai Aliya ta ce baƙin ciki take. Ita kuwa ko da Abba ya sake tambayarta sai ta ce za ta turo wanda zai gaishe shi ya ce za a aiko suna shiri ne daga haka Abban bai sake tambayarta ba.
Bini-bini waya da Ibrahim da Jidda har dai ta kai ta kawo yana zuwa hirar tsakanin magriba da isha, a hakan Aliya ta sha yanka masa magana wai laila ta ƙiya an koma caca. Ranar da ya zo ma kayan gwanjon ya sako abinsa, bayan Jidda ta koma gida Aliya take cewa wai wannan mai zuwa wajen nata matsiyaci ne.
*BAYAN SATI GUDA*
Ana ƙoƙarin kawo kayan saka ranar Aliya sai gobe, sai Ibrahim ya sanar da Jidda cewa zai aiko in ta amince duk da basu daɗe da haɗuwa ba, ita kuma ta yarda da shi ta yaba da halayyarsa don haka ta amince cewa ya aika a samu Abban nasu, lokacin da ya sanar da su Mummy cewa ya samu wacce yake so sun yi matuƙar mamaki sun yi murna ƙwarai . Daga haka ne ma ya samu damar saka kayan gwanjonnsa babu ɓoye-ɓoye ya ce saboda yana son ya auri mai sonsa da gaskiya ne ba wai don dukiya ba, basu san cewa yana amfani da kayan va ne saboda ita wacce yake so ɗin kuɗin basa gabanta.
Ya fahimci Jidda tana son ss duk sa ya san nasa son ya linka nata. Bai san dalilin da ya kore mata ƙuduri da burin auren kyakkyawa ba.
Tun da yake zuwa ko biyar bai taɓa bata ba, ko da Ibrahim ya sanar da ita za a je gaisuwar iyaye ta faɗawa Umma a kan ta sanar da Abba saboda tana jin kunya Umma ta ce
"Shi ma dai wannan zai kwasawa kansa jangwam, ko don talaka ne ai dama talaka ya saba da wahala" Jidda bata ji daɗin maganar ba amma babu yadda za ta yi.
MAMAN AFRAH
09025576222
[10/18, 9:27 AM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/C12RFYqXnWf36AhjVZWDw4?mode=ems_copy_t
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 8️⃣
*SADIYA*
Tana yin sallar asuba ta fita ta hura gawayi ya kama ta ɗora ruwan zafi, tuwon masara ta tuƙa wanda Nasir ya bata garin ta yi miya ta gama ta ɗora ruwan ɗumi ta dawo ta fara gyaran falon, lokacin ƙarfe bakwai da arba'in. Bayan ta kammala lokacin Nasir ya taso ya shiga wanka ya shiga bedroom ɗin zai shirya lokacin tana gyaran gado yana kawo kai ya ce
"Sadiya warin mene ne a ɗakin nan? Yanzu da girmanki kike sakarwa mutane tusa a ɗaki gabaɗaya ɗaki ya ɗumi da wari?" Ya faɗa yana saka hannu ya toshe hanci yana mata wani kallo. Ɗagowa ta yi daga sunkuyen da ta yi tana totsa zanin gadon sai lokacin ita ma ta ji ɗakin ya haɗe da wari cike da ladabi ta ce
"Haba Abban Kalifa tun da nake a gidan nan ka taɓa jin warin tusata?" Bata bashi damar magana ba ta ɗora da faɗin
"Wannan ba halayyata ba ce gaskiya sai dai ko Kalifa ne ya yi" Bai amsa mata ba ya ɗauki kayansa a drower ya ɗauki man shafawa ya fita falo a daidai nan Kalifa da ya yi juyi ya tashi zaune sai ta ji warin ya tsananta hakan ya sa ta fara tunanin ko kashi ya yi, net ɗin ta cire tana dubawa kuwa sai ta ga kashi ya yi gabaɗaya kashin har ya ɓata shimfiɗar, Kalifa ya ce
"Momma ruwa" Ta ce
"To Kalifa kalli kashin da ka yi duk ka mata shimfiɗa wannan kashin haƙorin naka da yake baka wahala ne ya dawo maka" Ta faɗa tana ɗago shi ta fito da shi, suna zuwa falo tana dab da fita a zuciye Nasir ya ce
"Sadiya mene ne wanann wai? Mai ya sa kike son shiga rayuwata kike hanani sukuni, kin cika ɗaki da wari na fito falo sannan kin kawo min wari falo" Ranta ne ya sosu da furucin sa tana riƙe da yaron ta ce
"Shin ni na yi kashin?" Tambayar da ta masa sai ya ga ta raina masa hankali hakan ya sa ya ƙara ƙufula, ganin bai ce komai ba sai ta juya ta saka silifas ɗinta ta kai Kalifan waje ta tsayar da shi, dawowa ta yi ta kwashe shimfiɗar ganin kashin bai taɓa katifar ba sai ta fito da kayan waje, wankewa Kalifan ta yi ta juye ruwan zafin da ta ɗora ta masa wanka tas. Kayan ta wanke ta shanya kafin ta ɗakko Kalifan suka dawo ɗaki turaren tsinke ta kunna duk da zuwa lokacin ma warin ya fita dama saboda kashin haƙori yana da wari ne, kaya ta sakawa Kalifan sai kuwa ya fito falon wajen uban yana ƴar dariyarsu ta yara ya je gaban Nasir da yake danna waya ya ce
"Abba" Nasir bai amsa ba fitowar Sadiya sai ta ga Kalifan yana tsaye a gaban Nasir ɗin ne ya ɗora hannunsa a kan gwiwar Nasir ɗin.
Kalifa ya sake cewa
"Abba" Maimakon ya amsa sai ya ɗago daga dannar wayar da yake ya ce
"Sadiya ni kika cewa wai ke kika yi kashin?" Sadiya da take tsaye ta zauna a kujera ta ce
"Wannan maganar da ta wuce mene ne na dawo da ita?"
Nasir ya ce
"Ban da shashanci da rashin sanin ciwon kai a ce yaro yake kashi a kwance wannan ai sangarta ce, ke ce baki koya masa ba amma sauran mata da suke da tarbiya ai suna koyawa ƴaƴansu abubuwa" Baki sake take kallonsa kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta ce
"Yanzu yaro ɗan shekara biyu ne za a ce wai ba a koya masa tarbiyar kashi a kwance ba, shin kana ganin yana kashi a kwance idan ba na jinya ba, wanna fa kashin haƙori ne, kuma ko da a ce akwai famfas a jikinsa kashin zai iya fitowa saboda wani lokacin ko famfas ba ya riƙe shi, wai don Allah Nasir mai na maka a rayuwa? Mai ya sa koyaushe cikin neman laifukana kake don ka hukuntani, komai na yi ban iya ba, mai ya sa ban taɓa birgeka a rayuwa ba duk abin da zan yi kuwa... Wani dogon tsaki da ya ja ne ya sa ta maƙale sauran kalamanta, ga haushin bai yi wa Kalifa magana ba sai ta ce
"Kalifa zo nan" Juyowa Kalifan ya yi ya kalle ta amma bai je ba ya sake buga gwiwar uban ya ce
"Abba" Ajiye wayar Nasir ya yi ya kama hannun Kalifan duka biyu ya ce
"Na'am Kalifa" Wani irin washe baki Kalifan ya yi da alama ya ji daɗin hakan. Sadiya kuwa sai ta ji sanyi a ranta ganin walwala a fuskar yaron ta.
Nasir ya ce
"Kalifa kai da jiya ka tafi ka barni, ka tafi gidan kakanka wuni kuma ya koro ku" Ya faɗa yana dariya, sosai Kalifan yake dariya da alama ya ɗauka wata kalma mau daɗi ce abinka da yaro, Sadiya kuma sai yanzu ta gane cewa ya yi haka ne don ya baƙanta mata zuciya, kuma cin fuska ne yake mata kai ta sunkuyar sai Nasir ɗin ya ce
"Maza je a zuba maka tuwo" Yana ta dariya ya juya zuwa wajen Sadiya, ɗago kai ta yi ta kalli Nasir ya sakar mata wani murmushin gefen baki tare da ɗaukan wayarsa ya cigaba da dannawa, ta rasa mai ya sa Nasir in dai zai ga walwala a fuskarta sai ya san yadda ya yi ya daƙusar da ita, ya fi so ko yaushe ta kasance cikin ƙunci.
Fita ta yi ta zubo musu tuwo ta ajiyewa Nasir, shi ma Kalifan ta ajiye masa har zai zauna ta ce
"Baka cewa Abbanka ina kwana ba"
Da sauri ya masa yana washe baki ya ce
"Abba nawana(Ina kwana)" Amsa masa ya yi ya koma ya fara cin tuwon bayan ta sa ya yi bismilla da bata fita a bakin ba.Bayan ya gama ci ta wanke masa hannu suna shirin juyowa zuwa ɗaki sai kawai ta ji ƙaran kashi sai ganinsa ta yi kamar ruwa yana biyowa ta ƙasan wandon sai Kalifa ya ce
"Momma foo" Haka ta cire masa ta wanke masa ta ɗora shi, wandon ta wanke ta wanke masa ta ɗauke foo ɗin tana taɓa jikinsa ta ji zafi sosai zazzaɓi ya rufe shi, haka ta ɗakko shi ta dawo da shi ta saka masa wandon ta kwantar da shi.
Nasir da ya gama zai fita kasuwa ta kalle shi ta ce
"Ina son zan kai Kalifa asibi... Tun bata ƙarasa ba ya ce
"Sadiya baki san wahalar da maza suke sha ba a wajen neman kuɗi ko? Wato daga yaro ya yi kashi sai ki ce wai za ki kai shi asibiti to ni bani da kuɗi idan kuma har kinnga sai kun kai shi ga hanya nan ba zan hana ki ba, amma naira biyar tawa ba za ta yi kuka ba"
Kamar za ta yi kuka ta ce
"Wallahi yanzu ma jikinsa zafi kuma kashin fa ya sake yi kar ya ci ƙarfinsa don All... Bata ƙarasa ba ta ji ƙaran aman Kalifan dama haka yake jinyar haƙori kashi da amai ga zazzaɓi kansa zafi.
Bedroom ɗin ta nufa, tana zuwa duk ya kelaya amai haka ta ɗane kayan shimfiɗar ta goge masa bakin gabaɗaya har jikinsa ya yi sanyi alamar abin ya fara ci ƙarfinsa.
Tana fitowa falon ta ga Nasir ya kara waya a kunne, Nasir kuwa mahaifiyarsa yake kira. A can gidan su Nasir mahaifiyarsa ce Hajiya Mariya wacce suke kira da Hajiya suna zaune ita da yaranta ƙannen Nasir