Chapter 4 of 14
MATAR HARIJI Haramtacciyar Soyayya By Maman Teddy
________📝Cikin tausayawa Inna Jumme tayi masa gdy ta nufi hanyar da zata isar da ita gda tana zuwa ta tarar da Jiddoh tsaye tana leqensu ta cafketa ta.
Juyowa tayi cikin muguwar kidima tana ganin Inna Jumme ta sauke ajiyar zuciya tace “inna Kado tausayi yake bani wlh kamar nayi masa kuka yau har qwallah naga yanayi dazun fah"
Kamata tayi tare da daukar ledar kayan suka shiga suka bajeshi a tsakar daki Jiddoh ta rinqa bin kayan da kallo kayane bana wasa ba ya hado Mata harda dogayen ruguna turaruka hijjabai da takalma sannan kayan kwalliya hatda relacxer ta manya guda biyu.
Wani tsalle tayi tace “Aradun Allah wannan shi zan rinqa shafawa nima jikina ya koma irin nasa ya daina kaushi da kirci Inna Jumme jikinsa fa shi har wani danshi yakeyi kuma duk jikinsa gashine irin na yan majigi"
Daquwa Jumme tayi mata tace “ke ar wannan ai saidai abawa Gwaggonki amma yayi miki yawa a man shafawa irin nasa farin nan nefa ke kuwa ai farace"
Turo baki gaba tayi tace “aa ne yaseen shi meye yasa baiyi farin ba nidai kibani abuna na bude na gani" mangari takai mata tace “uwariyonki ko sille baki tabawa cikin kayan nan nasan baffanki bazai bari ki karba ba ki bari mu boye sai mu nunawa Gwaggnki kudin kinsan su bakinsu daya da Ardo fah"
Shiru tayi kamar me nazari kafin ta kunto kudin daya bata kel kel dasu yan dari bibbiyu har na dubu ashirin ta zaro ido tace “Inna jaka dari ce mun shiga uku siyemu zaiyi fah"
Karba Inna tayi ta qirga jikinta na rawa tace “mun boni Jiddoh jaka dari uku da hamsin ya bamu Ina zamu kaisu?...."
“Ku kawo nan sukaji an ambata tare da bude labulen Ardo ya shigo a fusace yace “wato na lura kema kina daya daga cikin masu budewa yarinyar nan ido da kudi ko to bari kiji Jumme aradun Allah ko Moddibo ubana daya kawoni dunniya zan iya dagawa sanda akan wannan shegen yaron me idon agwagwa"
Wartar kudin yayi da qarfi a hannun Inna ya fita da sauri duka suka miqe suka bisa ya nufi madafi da aka balbala wutar kashin shanu ana girki ya cusa kudin.
Inna Jumme tace “Ardo sheden ka qona da wuta oye Ardo kanada hankali kuwa jaka dari uku da hamsin fah Ardo"
Itakuwa Jiddoh durqushewa tayi a gurin ta rusa ihu tace “na shiga ukuna Baffa ka qona masa kudinsa wayyohh Kado dama ban karbar maka kudinka ba Baffa me zance masa...."
Sanda ya daga zai maka mata Gwaggo ta tareshi tace “oye Ardo diyagga da gaskiyarta wannan qiyayya taka da yaron nan Lameeru tayi yawa koma meye ai bai kamata ka huce akan kudi ba yanzu idan yazo yace a biyashi me zaka bashi"
Hayayyaqo Mata yayi yace “ya kada galkena ya tafi dasu ai dama ba yau suka saba kashe mana shanu da hada baki da barayin burtali su kada mana shanu ba aradun Allah Hari da Jumme kowacce ta sake sakan baki akan mgnr makirin yaron nan jikan sarkin noma qur'anin Allah saita tafi gdan tsohonta"
Yana fadin haka ya juya ya shiga dakin ya dauko kayan kwalliyar ya fita dasu Jiddoh ta bishi da sauri cikin tashin hankali tana kuka tana fadin “ayyah Baffa kada ka rabani da kayan kwalliya na nima so yake nayi kyau na zama yar gayu...."
Bai tsaya sauraronta ba ya zubasu a wata tsohuwar rijiya ta qarasa da gudu ta leqa rijiyar ko hango batayi saijin zubarsu ciki tayi ta zube a gurin ta dora hannunta akanta ta runtuma wani ihu tare da fizgar ledar ta rungume a qirjinta shi kuwa Ardo ya angijeta ya wucce abinsa ya barta rungume da leda tana kuka tana kirar “shikenan kayan kwalliya na sun tafi rijiya Kado yaushe zaka dawo ka kawomin wasu..................
Download : Walijam Complete Novel
________📝Tajima kafin taga zaman bazai kaitaba ta tashi ta nufi gidan tana haɗa hanya ta shiga ɗakin gwaggonta ta kwanta tanata sauke ajiyar zuciya zazzabi me zafi ya rufeta zuciyarta cike da tunanin Lameer da maganganunsa da suketa yimata yawo a ƙwanya.
___________Kada ya shiga gari kai tsaye gdansu yanufa yayi saa kuw ya tarar da Alh a falon ƙasa yana hutawa ya zauna suka gaisa dashi sannan suka gaisa da hajiya yayi shiru gabansa na faduwa yana tunanin ta inda zai fara.
Alh ne ya katseshi da cewa "Magaji meye yake faruwa ne kamar bakinka akwai magana ince dai ba matsala bace a gdan naka?"
Girgiza kai yayi yace "ba wannan matsalar bace Alh don allah alfarma nake nema a gurinka"
Da mamaki Alh ya dubesa yace "tame babana?" shafa sumarsa yayi yanason faɗar sirrin ransa yanajin tsoron tujarar hajiya.
Yanda yake kallonta ne yasa alh cewa hajiya abamu guri yaron nan tsoron masifarki yakeji" taɓe baki tayi tace "bashida gsky ne shiyasa yake tsoron faɗa a gabana" tana faɗin haka ta miƙe tayi shigewarta ɗakinta shikuma alh ya zubawa Lameer ido yana nazarin damuwa kwance saman fuskarsa yace "kai nake sauraro magaji Allahu yasa dai lfy"
Sumarsa ya shafa yace "lfy lau Alh dama inason na sanar dakai ne...." sai kuma yayi shiru bakinsa ya sarƙe murmushi Alh yayi yace "kamar ba namiji ba kana mgn kana fargaba ita faɗuwar gaba asarar namiji ce ai Lameer ka fito kayi mgn darect mana"
Cikin in...ina yace "in...inason zanyi au...r...e ne dama..." zuba masa ido uban yayi cikin naƙaltar yanayi da mamaki yace "aure wanne irin aure Lameer kana zaune ƙalau zaka tashi hankalinka ƙanƙaninka dakai zaka tarawa kanka iyali meye damuwarka da matarka ta gda?"
"Bashida wata damuwa da ita saima ita da yake tatawa rashin mutumci kullum cikin ƙorafi take alh kai shaida ne basa wata guda baayi musu sulhu ba wani sabon tashin hankali ma watnnin nan daya sawo kai kaga yaron nan sai suyi watada watanni bai sauke mata haƙƙin aureba kuma wlh ba yau aka fara ba dama duk gdan da kaji an fiya samun saɓani to ɗaya yayi watsi da haƙƙin ɗaya, yo bandama iskancinsa Alh da tsabar ya raina mutane Lameer har nawa yake da zaice zai auri mace sama da ɗaya kuma bayqn ɗayar bata ƙoshi ba, eh mana bata ƙoshi ba mana Alh ci da sha ai duk mace tana samu a gdan iyayenta kwanciyar aure itace aure ai"
Tuda ta fara faɗan jikin Lameer yayi matuƙar sanyi baisan sanda hawaye ya fara fita a idanunsa ba tsoronsa Allah tsoronsa suce zasu hanashi auren Hauwah ya tabbatar rayuwarsa ta shiga kwale-kwalen masifa da tashin hankali saboda yanzu hakan jinsa yake kamar ransa hade yake dana Hauwah.
Muryar Alh ce ta katseshi da cewa "wai hakane Magaji?" ɗagowa yayi da manyan idanunsa da suka kaɗa sukayi jah cikin sanyin jiki yace "eh hakane Alh amma don Allah kada ka yankemin ƙauna da samun dawwamammen farin ciki Alh Hauwah yarinya ce ƙarama batasan komai ba kafin lkcn da zata fara buƙatata insha Allahu nasamu lfy tunda ina neman magani"
_Kuji fa wata gwari_
Ajiyar numfashi Alh yayi yace "Wannan falsafar taka akan qarya kayita ka nemi maganin kafin ka buƙaci ƙara aure shi aure meye yakesa ayisa ne Lameer anya ma kuwa kasan sharruɗan aurevoir? To bari kaji wani abu Magaji ko matarka ta gida wato Mubaraka indai kayi wata shidda baka kusanceta ba warware aurenku ya kamata ayi saboda hasashen masana halayyar ƴa mace na duniya ya tabbatar mace lafiyayiya watanni uku take iya jure rashin namiji a tare da ita wannan dalilin yasa kaga addini ma ya sassauta musu yace suyi iddah watanni uku idan rabuwar aure ta gifta"
Ɗagowa yayi yace "amma Alh..." katseshi yayi da cewa kaje ka Lameer banson shirme fah" hawayene ya zubo a idanunsa sharrrr ya miƙe a matuƙar sanyaye ya nufi ƙofar ya buɗeya fita ya shiga motarsa ya zauna tare da buga kansa da sitiyari yace "innanillahi wa innah ilaihir raji'un"
Daƙyar ya iya yima motar key ya nufi gdansa cikin wani yanayi dashi kaɗai yasan ya yakeji a zuciyarsa yana shiga ya buɗe motar ya fita ya buɗe ƙofar falon ya shiga daƙyar ya iya sallama ya hangi Mubaraka zaune da apple a hannunta Fadwah nata wasanta ta nufoshi da tafiyarta da batayi ƙwari ba ta riƙe masa ƙafafu ya ɗagota a hankali yana amsa sannu da zuwan da Mubaraka takeyi masa ya nufi sama da ƴartasu a hannunsa ya sauketa a saman gado ya dauko choculate ya bata ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa sannan ya dawo ya zauna a ƙasa dirshen yana kallon yarinyar jikinsa yana rawa saboda a rayuwarsa bai iyasa abu a ransa ba.
Tunda yake bai taɓajin ciwo da takaicin rashin mazantaka ba sai yau wannan wacce irin masifa ce, shidai yasan yace zai hƙr da Hauwah ma zance ne bazai iyaba yanzu meye abinda ya dace yayi?.................
________📝Daqyar ya tashi ya haura gadon ya kwanta yana tufka da warwara zuciyarsa cunkushe da abubuwa kala².
Wannan dare shidai bai rintsa ba asubar fari yayiwa gdansu tsinke mahaifinsa yana dawowa daga masallaci ya tarar dashi zaune tare da maigadi ya tashi da sauri ta tareshi.
Shikam Alh saida gabansa ya fadi ya zubawa dan nasa ido yana ayyana wanne irin abune wannan me yake damunsa haka da zai baro gdansa cikin duhun asubar nan.
Shiga gdan sukayi yajashi har dakinsa yace “babana meye ya fito dakai da sanyin safiyar nan" shafa kansa yayi ya durqushe yace “Alh na kasa jurewa jiya ban iya rintsawa ba don Allah ka taimakeni ka amince da aurena da Hauwah wlh zuciyata ta kamu da qaunar yarinyar fiye da inda kake tunani Alh komai zai iya faruwa dani idan ka hanani auren Hauwa"
Mamaki ne ya cika zuciyar Alh Lameer dinsa me kunya wai shine yake roqonsa ya amince yayi aure to yanzu idan ya amince da wannan aure me yayi kenan? Da ace baisan matsalar Dan nasa ba dasai ya shige masa gaba yayi aure amma yasan matsalarsa.
Towai meyema ya dauki hankalinsa haka har ya damu da auren? Katseshi yayi da cewa “kace wani abu don Allah Alh wlh aure suke shirin yimata kuma itama ni takeso zata zauna dani a duk yanda nake nasan bazan samu matsala da itaba tunda yarinya ce wlh nayi maka alqawarin daganan hsr bangon duniya zanci gaba da neman magani kuma duk yanda zanyi naga na sauke haqqinsu duka zanyi insha Allah"
Kada kai yayi yace “naji magaji kaje zanyi tunani akai yauwa ya maganar tafiyarka Lagos?" Numfashi ya sauke yace “sunyi posting dina tun sati daya daya wucce wannan mgnr ta hanani tafiya nafiso a gama komai kafin na tafi inyaso tunda Mubaraka tana aiki idan aka daura sai kawai na wucce da Hauwah can"
Shiru Alh yayi kuma fa a mgnr dannasa akwai abin dubawa duk lalacewar namiji mace kusa dashi garkuwa ce ko banza sayi hira yace bani kaza ta bashi" ajiyar numfashi Alh yayi yace “kaje idan nayi nazari zan nemeka"
Gdy yayi tare da miqewa ya fito sukayi kicibis ds Hajiya itama ta fito saida gabansa yayi wata muguwar faduwa ya tsugunna yace “ina kwana Hajiya" tabe baki tayi tace “lfy meye ya kawoka gidannan da asubar nan?"
Shafa kansa yayi yace “nazo naga Alh ne" tsaki tayi tace “au dama mgnr nan tun jiya baa barta ba to wlh tallahi kaji na rantse wannan auren bazaayishi ba indai nice na haifeka bazan yarda da wannan kwadon hatsin barar ba ta gdanma baka iya da itaba balle ka kawo wata"
A hassale ya kalleta yace “wai waye yace miki bana iyawada da iyalina ne meye na ragesu dashi ci ko sha ko sutura? Me takeyiwa kanta a rayuwarta to nidai don Allah ki cire bakinki a mgnr aurena Hajiya ni namiji ne kuma tsayayye a gdansa sannan nakai lkcn da yakamata ace nasan daidai nasan akasin daidai"
Tafa hannu tayi cikin salati tace “ehhh lallai Lameer kakai harma ka isa wato ni kake fadawa cewa kai namiji ne ko tabdi lallai da aiki a gabana dannan tunda nake dakai baka taba tsallake mgnta ba sai yau saboda kaso qara aure har kake yimin tsawa"
Kallonta yayi yana mamaki wai yayi mata tsawa shikam ya rasa wacce irin uwa Allah hadashi da ita da kullum burinta taga kasawarsa tayi masa gori akai.
Miqewa yayi ya fice tanata sababin bala'inta ya nufi gdan wan babansa don yasan tunda Hajiya taqi mgnr idan bata sama ya biyowa Alh ba to baza ayiba.
Bai boye masa komai ba ya zayyane masa harda takun saqar da suke fuskanta da dangin Hauwah Mal Yahaya yayi qwafa yace “aikuwa ka taro March bakada fili Lameer shi aure nufin Allah ne amma fa zaakai ruwa rana saboda Rugar Sambajo munsansu sanin gaske tun duniya na kwance basa bawa Kado aure ni kaina na nemi aure a rugar amma daga qarshe cin mutunci ya biyo baya da qage hadi da qazafi sufa sun tsani Bahaushe musamman wanda ya hada alaqa da garin Alqalawa Lameer abubuwa da yawa sukaja wannan gabar fah saboda haka indai zakaji shawara ka janyewa auren yar gdan Ardo Jibbo saboda tujararren bafulatani ne fiye da kwatance shi duk cikin yayan Moddibo Durange shine baudadde har ya baudar da yan uwansa wlh ni kaina tsoronsu nakeji sau uku suna fasamin glass din motata saboda wani dalili nasu mara kan gado...............
__________
Ajiyar zuciya yaja ya miqe ya matsa gabanta yace “ki nutsu kizo kiyi sallama dasu abokai nane tafiya zasuyi"
Noqe kafada tayi tare da qarayin baya yayi murmushin takaici yace “kedai bazaki daina shirme ba" juyawa yayi ya fita ta sake zama tana kukanta tana Kiran “wayyohhhh Gwaggota ya saceni barawon mutane ne Kado aradu bazan qara yarda na shiga motarka ba tunda kai azzalumi ne....."😂
Turo qofar da yayi ya shigo da kayan abinci a hannunsa shine yasata qara miqewa ta tattare zaninta ta tura tsakanin cinyoyinta zuciyarta tana bugawa da qarfi saboda mugun tsoronsa da takeji.
Ajiye kayan yayi ya nufeta ta janye ya qara nufarta ta janye ya tsaya yana kallonta yace.
“Dagani saike zamu kwana a gidannan idan kika wahalar dani nima zan wahalar dake" yana fadin haka ya janyota ya mannata da jikinsa.
Ta cure tare da dungulewa guri daya tana tureshi tana kuka na fitar rai mai gunji tana yaqushinsa tana cizonsa, sakinta yayi da sauri yana fuzgo numfashi daqyar saboda gashinta daya nadi manshanu babu abinda yakeyi sai qarni da tsamin dauda.
Sake fuzgota yayi ya daga hannunta da qarfi zai zare Mata riga ta qamqame tana kuka tana girgiza masa kai amma baiko kulata ba ya hade qarfinsa ya cire rigar ya koma zai kunce zanin tayi saurin durqushewa ta qara qanqame qirjinta tana kuka tana fadin “Allah ya isana mugu azzalumi bazan taba yafewa ba indai ka qara kallonmin Inninina"
Dafe kansa yayi yace “oh God Hauwah damuwa ce ke gabadayanki nace kiyi wanka bakiyi ba kinmaji yanda kanki yake qarnin manshanu kuwa nace miki banasonsa shiyasa na siyo miki shampoo da mayukan gashi Amma baki daina shafawa ba to wlh yau ko ki bari na tayaki ki wanke kanki ta dadi ko kuma na gwada miki qwanji kinsan dai zan iya"
Murguda masa baki tayi tace “tarnatsa muliyan bazaka wankemin kayina ba saidai kasani a turmi ka kwakwatsa ka niqa ka soya kayi dambun nama Dani...."
Wata uwar wawura da yayi Mata yasata wani juyi a tsakar dakin ta shige qarqashin resting chair abinta da yake dakin babu gado katifa ce number one maigida sauko mu gaisa sai wardrobe ta jikin bango sai tv da lamp kawai.
Takaici ne yasashi zama kawai dirshan yana kallonta shi yama rasa ya zaiyi da gidadancin yarinyar, miqewa ya sakeyi ya bude qofar ya fita ya koma wani dakin ya dauko belt ya dawo har yanzu tana qarqashin resting chair din sai uban gumi take hadawa.
Matsar da kujerar yayi sai gata shanye gaho a qarqashi tanata faman muzurai rungume da qirjinta yayi saurin kashe fitilar ta miqe da sauri tana shassheqar kuka tana wawuren inda zata kama kawai sai jinta tayi a jikinsa.
Dama hakan yakeso aikuwa ya dagata cak ya nufi bathroom din da ita ya bude ya shiga nan din haskene sosai ya sauke idonsa akan lallausar fatarta me santsi da sheqi yaja numfashi ya direta yace “cire zanin nan kafin na zaneki"
Bude idonta tayi zatayi rashin kunya taga zabgegiyar bulalar dake hannunsa aisai ta nutsu tana kuka jikinta na rawa ta kunce zanin ya rage daga ita sai dan kamfe kawai saita durqushe tace.
“Wayyoh ni Allah ka ceceni Allah ka ceceni hannun wannan mugun bawan ko Gwaggo na bata taba ganina a hak......"
Download>>> Cousin Ne Complete Romantic Novel Document
Tsawa ya daka Mata data sata sakin fitsari a zaune ta sakeyin zaman yan bori ya matso ya tsugunna gabanta yace “tashi ki cire wannan munafukin wandon na jikinki"
Saurin kada masa Kai tayi tace “aa nidai Kado bazan iya ba kaje kawai ni ka fitama zanyi wankana" murmushi yayi yace “kin makara yari ya tun sanda nace ki tashi kiyi da kinyi da ba wannan zancen akeyi ba nifa yanzu zabi zan baki dama na gama cinikin kanki har nabawa Gwaggo da Baffa kudin kina cika yimin musu zan Kira mutanen nanna dazu du fedemin ke..."🤣
Ai bai ida rufe bakinsa ba ta miqe ta zare wandon tayi qasa zata zauna yayi saurin tarota yanajin faduwar gabansa na qaruwa, by mistake hannunsa ya dunguri nononta ai sai ta qwallah qara tace.
“Wayyohhh zaiyimin adumbuli nashiga ukuna shima ashe irinsu Rubado ne wayyohhhh mutuwa shikenan ni nasan tunda ma bakabadani an yankani ba mutuwar ma dolene garama a yankani a gasani a cinye amma nidai wasiyyah ta idan an yankani akaiwa su Gwaggo kai da qafa.........🤣🤣🤣🤣
__________📝Wani irin haushi ne ya cikansa zuciya ya kamota ya dagata cak tana zillewa tana koke kokenta shikuma yaqi sakinta saida ya kaita cikin bowl din yana shirin sanyata ta qanqameshi tana cewa “wayyoh Kado ruwan gudu yakeyi kada ya tafi dani ya cinyeni"
Hannunsa yasa saman bakinsa yace “kada ki qara yimin mgn idan ba hakaba da kaina zan hukuntaki" aikuwa kamar ya dinke bakinta haka tayi masa