Chapter 7 of 23
Nanny (mai Reno..) Complete Hausa Novel by Aishat Alto
Ran goggo Abu ya baci Ta Dinga Sauke Numfashi Takaichi Attahiru na Damunta Ashe ce Tace"goggo Kada ki yanke Hukunci Cikin Fushi yakamata Shima yayan Ki kirashi ki Fara jin Ta Bakinshi Tukunah.."Tafada Da Sigar Lallashi,Cikin Kuluwa Farida Ta Dago Tana Hararan Ashe kafin tace"Eh mana Akirashi mana ai ba karya namai ba Jiya agaban ya'yana Da yan Aiki ya Tozartani nidai kam goggo Ki kirashi na Gama zama da Tahir kamar yadda yace banda Wani Amfani Acikin Rayuwarshi Nima Tahir baida Amfani Awajena ya"yana yaje ya Rike na barmai Dama badasu nazo ba..."Tafada Tana Shesshekan Kuka Lokaci Daya Tana Hararan Ashe din Domin Dama Jininsu baizo Daya Saboda yadda Tahir yake matukar ji da Ashe Ita Kuma Duk Abunda ya Shafi Dan"uwanta bata Wasa Dashi.
Ashe bata mata mgana ba illah kallon Goggo Abu Datakeyi kafin Tace"Kinji goggo Don Allah Kifara Kiranshi Tukunnah.."Jin Haka yasa goggo Ta Mike Ta Shiga Ciki Ta bar Ashe da Farida Anan Cikin Falonta Kowa na kallon Kowa Cike da Takaichi Mikewa Ashe tayi ta Fice Zuwa Shashen Innaro Tana Fadin"Allah ya kawo maka mafita Dan"uwana..."Tafada Cike da Habaici da Kuluwa,Da Ido Farida Ta Bita kafin Ta Rakata da Tsaki Tana Share Kwallah.
Fitowarsu kenan Daga Meeting yana Hanyar Komawa Office ya Fito da Wayarshi Wacce Tun Shigansu meeting din ya sakata A Silent Hankalinsa ne ya Tashi Ganin Misseds Rututu Na goggo Abu gabansa sai dai ya Fadi yana Bude Kofar Office din ya Na Kokarin Kiranta gabda zata Katse Ta Dauka yana Kokarin gaisheta ta katseshi A Fusace Tana Fadin"Dagata min Attahiru Nagode da Abunda Kamin in Har na Isa dakai kazo gida yanzu ka sameni mutumin banza kawai..."Tafada Cikin Fushi kafin ta yanke Kiran,Dafe kai yayi yana salallami,Domin yasan Cewa Farida Tagama Hadama goggo Abu Famfo shi bama Wannan ya Dameshi ba Irin yadda Ta Dau Zafi Dashi Allah ne kadai Zai Kwaceshi.
Office din Ishaq ya Tafi Agurguje Sukayi mgana Sama sama Kafin Suyi sallama ya Fito bai Tsaya bata Lokaci ba yace ma garzali Su kama Hanyar Danbatta sai da Sukayi Nisa ne Garzali ke Tunamai dasu basma Ba Wanda Zai Daukosu Daga Sch,Dafe kai yayi yana Salati kafin ya Dauki Wayanshi Shugaban mkrantan Su Basma ya Fara Kira inda yabada Umarnin Indan Antashi Daga Mkranta Basma da Bassam Su bi Sch Bus Su Dawo gida Saboda Dukkansu basunan bamai Zuwa ya Daukesu,Daganan sai Shugaban Mkrantar su Mufeeda Itama Abunda yace Kenan Kafin ya Katse Kiran,yana Sakin Numfashi kadan yasan yau sai sunyi Rashin Islamiya Saboda baita yarda Sun Fita Waje Su kadai ba Duk inda Zasu sai dai garzali ya kaisu Kuma yana Da Tabbatacin Tunda Sukaga babu mai Kaisu bazasuyi gangancin Fita ba.
Wajen 2pm suka iso Kofar gidan Hakimi,Shikanshi Hakimi da Jama"arsa Sunyi mamakin ganinshi don Akasari bai Cika Zuwa Cikin Sati ba Sai karshen Sati,Hakimi bai yi mamaki Sosai ba Saboda yaga Zuwan Farida Hartazo ta gaisheshi Yaga Fuskarta ta Chanza kamar tayi Kuka Daya Tambayeta sai tace bakomai tatashi Ta Shiga To Tunda yaga Zuwan Tahir sai yasha Jinin Jikinsa Ammh Dayake yana da Miskilanci sai bai Nunama Tahir din Komai ba Wanda Sai da yagama gaisawa da Jama"ar Wajen kafin ya Karisa garesa yana Kwasan gaisuwa,bayan Tambayi Aiki da yara,bai Zauna ba ya Mike yacemai Zai Shiga Cikin gida,Hakimi yayi Mirmishin su na manya kafin ya kalli Tahir din yana Fadin"Attahiru yau kazama Mara Hakuri ko...? Akullum ina maka Nasihan ka Rika kai Zuciyarka Nesa Domin Akasari mata akarkarce suke Kana Kokarin Daidatasu Suna kara famdarewa ne,Toh Dole sai munyi Hakuri Dasu kaji...?"Yafada kasa kasa Wanda Inba Tahir din ba Wanda yakejin meyake Fada,Sadda kanshi yayi kasa yana Fadin"Naji Hakimi Insha Allahu Zan Kiyaye.."Kai ya gyada kafin yace"Tashi ka Shiga Ciki Allah yayi maka albarka.."Da Ameen ya amsa kafin ya Wuce Zuwa Cikin Gidan...
Sheshen Innaro ya Wuce Direct nan Suka Ci karo da Inna Fulera ta Zube Tana gaisheshi ya amsa Cikin sakin Fuska Kafin ya Wuce Zuwa Babban Falon Innaro Dake Shashenta,Nan ya iske Innaro da Ashe Suna Hira,Ashe Dataji Dadin ganin Dan"uwanta sai da tatashi ta Fada Jikinsa Tanamai Oyoyo Riketa yayi yana Dariya Lokaci Daya yana Shafa Kanta,Tare Suka Zauna gaban Innaro,Tahir yafara gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska da Fara"a Tana Tambayanshi su Basma ya amsa da Suna Mkranta,Yadade Awajenta Suna gaiswa da Hira kafin ya barota Zuwa Shashen Goggo Abu Ashe bata biyoshi ba Saboda tasan Goggo Abu Korarta Zatayi.
Lokacin Daya Sawo kanshi Falon goggo Abu Da sallama Abakinshi da Farida yaci karo Tayi Rashe Rashe Atsakiyar Falon Tana Shan Fura,Suka Hada Ido,Daure Fuska yayi kamar bai Taba Dariya ba yana karisowa Cikin Falon Goggo Abu Tana Fitowa Daga Uwar Dakinta Suka Ci karo,Takalmin kafarsa yacire kafin ya Zauna yana gaishe da goggo Abu Wacce Ke Dankaramai Harara kafin Tace"Tashi Tsaye bana Bukatar gaisuwaarka Attahiru,domin ka gama Nunamin Iyakata..."Tafada Cikin Kakkausan Murya.
Kasa yayi Dakai yana Jin Wani Daci Acikin Ransa,Dagowa yayi yana Kallon Farida Wacce Ke kallonshi gabanta ne yafadi ganin Irin Kallon Dayake Jifanta Dashi bai iya mgana baa,sai ma Sauraran Goggo Abu Dayayi Tayi Ta Inda Take Shiga batanan Take Fita ba Sai da Tagama Wanke shi Tas Kamar Zata Dakeshi Ta Koma Gefe Tana Haki,sai da yaga Ta gama kana ya Dago yana kallon Goggo Abu kamar yayi kuka yana Fadin"Goggo Ta Fada miki Fita Take bada Izinina ba,Ta sanar dake batamin Kallon Mijinta Dauka na Take tamkar Wani yaronta ko Ma"aikacinta Ta gayamiki Wannan Ko bata gayamiki ba.."?Yafada kamar Zai Fashe da Kuka.
Daga Farida Har Goggo Abu Jikinsu yayi Sanyi Saboda yadda Tahir din yayi mganar,Sai goggo Abu Ta Koma Da Kallonta kan Farida tana Fadin"Kinji Abunda Mijinki yace In Hakane To Tabbas baki kyauta ba,Taya zaki Dinga Fita bada Izininsa ba Ai ba Zaman kanki kikeyi ba Ko Farida,Gaskiya ki gyara Kina Cikin Fushin Allah da Tsinuwar mala"iku matukar baki Roke Mijinki Gafara ba.."
Farida ta kanta ke kasa ta Fashe da Kuka,Jawota Jikinta goggo Abu Tayi Tana lallashinta Lokaci Daya Tana Fadin"Yi Shuru kibar Kuka,Ki bama Mijinki Hakuri Kune mi gafaran Juna Don Allah bana Jin Dadin Wannam Rashin Jituwar naku,kufa ba yara bane Kune fa Kuke da yara kamar basma da bassam Haba Don Allah Farida Don Allah Ku Sansanta kanku.."Tafada Cikin Sanyi Dagowa Farida Tayi Tana Share Kwallah kafin tace"Toh Goggo.. "Muryanta ta Dishe Sosai...
Mirmishi goggo Abu Tayi kafin Ta Mike tana Fadin"Yauwa Naji Dadi bari naje na Karboma Atrahiru Fura Wajen Innaro yanzu zan Komo ."Tafada Tana Ficewa Don ta basu Waje bayan Fitanta Falo ya Dade Shuru kafin Farida ta yanke Shurun bayan Ta Dago Tana kallon Tahir Daya Tsurama Cafet din Goggo Abu Ido Fuskarsa ba Annuri ko Kadan Duk da gabanta na Fadi hakanan ta Daure Ta Furta.."Srry...'Tafada Muryanta na Rawa Ko kallonta baiyi ba,ganin Haka yasa sai Jikinta yayi sanyi Tatashi Ta Koma Side din daya ke kallo Ta Sake Furta"Am Srry..."Kauda kai yayi Yana Neman Tashi sai Ta Riko Hanmunshi Da Sauri ta Fashemai da Kuka bayan ta Dora kanta bisa Cinyarsa,tsayawa yayi yana Kallonta Kukanta na Dakarmai Zuciya,Runtse ido yayi kafin ya Dora Hannunshi bisa kanta yana Tapping cikin Ajiyar Zuciya yake Fadin"Shiii...is ok.."..
Jin Abunda yace ne yasa Ta Dago Da Sauri Fuskarta Jage jage da Hawaye,tana kallonshi Mirmishi ya sakarmata kafin ya Zaro Wani Farin Hankey Daga Aljihunsa,yana Share mata Hawaye yana Fadin"Nace komai ya Wuce ko..? Kece fa kike ja muna Fada Farida,in da bakiyi Saurin Zuwa Wajen goggo Abu banayii Regreating din marin da nayi miki zan baki Hakuri,plz Farida..."Bai karisa ba goggo Abu Ta Shigo Dole yayi Shuru ganinsu haka sai ya sanyayamata Rai,Furar ta mikamai ta sake Ficewa,yana kallon Farida kasa kasa yafara Shan Furarsa,yana gamawa ana Kiran sallar La"asar nan yafice Zuwa Msallaci Ita Kuma goggo Abu Ta Dingama Faridar Nasihan bayan Suma Sun Idar da Sallar.
Bai komo dakin Goggo Abu ba sai da ya sallami kanwarsa Ashe,Har gida ya karata akafa suna Tafe Suna Hiransu gwanin ban Sha"awa,sai da ya Dawo ya Shigo bangaren Goggo Abu yace Farida tataso Su Tafi,nan ma goggo Abu Hadasu Tayi tana musu nasiha Sosai kafin Su mata sallama Shashen Innaro Suka Koma Suka mata sallama nan Tabada Sakon Fura mai Dadi Tace akaima basma da Bassam,Awajema Sallama Suka ma Hakimi ya bisu Shima da Sanya albarka.
Tahir shi ya Tukasu Shida Farida Acikin Motarta Shi Kuma garzali ya Tuko ta Tahir,acikin Motan Ma Hannunshi Farida Ta Damke tana Fadin"Shine ni baka bani Hakuri ba.."Tafada Cike da Shagwaba,Hankalinsa na Wajen Tuki ya Waigo yana Fadin"Ah...Waht Are u Eating na baka is Fooling Down,Zan baki mana ammh ai kinsa nawa Is so Special ko.."Yafada yana kallonta Lokaci Daya yana Kashe mata ido,Dariya tayi tana Kwantar da kanta Cikin kujeran Mota batace komau ba Ammh Hannayesu Sarke da Juna Jefi Jefi suna Hira Har Suka Kariso gida.
Abun mamaki Haka yaran Suka ga Iyayen nasu Sun Shigo Hannuwansu Sarke da Juna,Saboda Jin Dadi basma da bassam Suka Ruga suka Rumgumesu suna Ihun Oyoyo momy da Daddy,Hatta Iya da Mufeeda Sunji Dadin ganin Farida da Tahir Da Alamun Komai ya Wuce,Ranar dai gidan Gabadaya yayi Dadi Dukkansu tare Sukayi Dinner Suna Yi Suna Hira Fuskar ya"yansu cike da Farinciki,Da Suka gama Cin Abunci Suka koma Falo Suna Hira da ya"yansu Hatta Naila Taji Dadi Sosai ganin yadda Take Tsallake Tsakanin Cinyar Tahir dana Farida,sai Wajen Goma Kana Suka Umarcin yaran da Su Tafi Dakinsu su kwanta Naila Kuma Farida Ta Mikama Mufeeda.
Awannan Daren dai Farida ta Hakura ta bama Tahir Ahakkinshi nan Suka Fahimci Duka Sunyi Kewar Juna,Farida tagayama aya Zagi,domin Tahir dai sai da ya Fanshe,koda Asuba ma Daya Dawo masallaci sai da Ya Dora Farida Tafara gajiya Sosai Sai Tura baki Takeyi Domin Abunda Ke Hadata Tahir kenan Jarabarsa.
*Aisha Alto..*
*Anitha..*
*NANNY...!*
(Mai Reno..)
*Alƙaluman:*✍🏻
*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*
_Don't Forget to Follow us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_
*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*BABI NA TAKWAS*
*BAYAN SATI BIYU*
Zuwa wannan lokacin komai ya gama daidaita a tsakanin Tahir da Fareeda basu da matsalar komai yanzu, Fareeda ta natsu ta bar duk abun da take yi ta daina fita ko'ina kullum tana gida tana baiwa mijinta da 'ya'yanta kulawar data dace, wanda sauyin wannan hali nata ya yiwa kowa daɗi a cikinsu gidan ya zama cikakken gidan ma'aurata masu tsananin so da ƙaunar juna haɗe da tarairaya. Kullum cikin farin ciki da ɗoki 'ya'yanta suke, yanzu babu abunda ke damunsu saboda suna samun kulawar mahaifiyarsu kuma tana jansu a jikinta bata kyararsu komai suke so tana yi musu, Mufeeda da Iya suma abun yayi matuƙar yi musu daɗi gidan ya zama happy family babu damuwa ko matsalar komai a gabansu sai farin ciki.
Suna zaune dukansu a falo gidan suna kallo a makeken talabijin ɗin dake manne a bangon falon Naila na kan cinyar Mufeeda tana bata madararta yayinda Basma da Bassam ke gefe zaune a kan kafet suna yin Homework ɗinsu kasancewar gobe Monday akwai makaranta Iya ta fito daga ɗakinta da sauri tana share hawayen dake zubo mata ta nufo Tahir ɗa Fareeda dake zaune a saman kujera suna magana ƙasa ƙasa wanda su kaɗai suka san abinda suke faɗawa junansu dan babu mai jinsu ta ɗan rusuna a gaban Tahir tana goge ƙwallah tace "Sannunku da hutawa Alhaji." A hankali Tahir ya ɗago da kansa yana kallonta kafin ya gyara zama sosai yace "Yauwa Iya sannu da fitowa... amma lafiya kuwa na ganki haka?"
Tana ƙara duƙar da kai tace "Yanzu ne aka yo min waya daga can gida Allah ya yiwa Yayana Malam Danladi rasuwa..." Ta ƙarashe maganar ƙwallah na ziraro mata ta kwanto haɓar zaninta ta share wasu na ƙara zubo mata, salati Tahir da Fareeda suka yi yayinda Fareeda ta miƙe ta kamo Iya ta miƙar da ita tsaye tana kallonta tace "Sannu Iya, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Allah yasa ya huta." Da Ameen ita da Tahir suka amsa kafin ya tashi tsaye shima yayi mata gaisuwa cike da alhini kana ya fice waje ya kira Garzali yace ya shirya ya fito da mota zai kai Iya Kano ba ɓata lokaci ya dawo ciki yace da Iya taje ta shirya su wuce Garzali ya kaita, sannan ya haura sama zuwa ɗakinsa ya ɗebo kuɗi masu yawa yazo ya bata ta duƙa tasa hannu biyu ta amsa tana masa godiya ta koma ɗakinta ta ɗauko 'yar jakar gana most go ɗinta ta fito Mufeeda dasu Basma da Bassam harma da Fareeda suka rakata har bakin mota ta shiga Garzali yaja suka fice daga gidan, su kuma suka koma cikin gida cike da kewarta da tayata alhinin rasa ɗan'uwanta da tayi.
Washegari da sassafe wayar Umman Fareeda ta tashesu daga barcinsu mai daɗi da sukeyi rungume da juna, da magagi ta lalubo wayar ta ɗauka ta kara a kunnenta nan take faɗa mata Abbanta ba lafiya ciwon sugansa ya tashi an kwantar dashi a asibiti. A gigice ta tashi ta sauka daga gadon tana tashin Tahir shima ya tashi ta faɗa masa abunda Ummanta tace cikin tashin hankali tashi zaune ya ziro ƙafafuwansa ƙasa ya sauka daga gadon ya riƙe hannunta suka shiga toilet agurguje sukayo wanka suka fito suka shirya Fareeda ta ɗebi kayanta kala biyu ta zuba a ƙaramar jakarta suka fice zuwa falo.
Ɗakin Mufeeda ta nufa ta samu har tayi wanka ta yiwa Naila itama tana shiryata ta shiga ta ɗauki Naila tace Mufeeda ta ɗauko hijabinta ta fito, da mamaki Mufeeda ta ɗauki hijabinta ta saka ta biyo bayanta suna fitowa falo taga Basma da Bassam a shirye cikin kayan gida saɓanin na makaranta da tayi tsammanin zata gansu dashi, duƙawa tayi zata gaida Tahir dake tsaye yana kallonta, ɗaga mata hannu yayi yana faɗin "Lafiya Alhamdulillahi Mufeeda... Ku muje lokaci na ƙurewa." Ya ƙarasa faɗa yana karɓar Naila dake hannun Fareeda ya saɓata a kafaɗarsa ya fice suna biye dashi a baya. Garzali na ganinsu ya taso da sauri ya nufosu ya buɗe masa mota ya shiga gaba ya zauna sannan ya buɗewa Fareeda ta shiga baya Mufeeda ta shiga kusa da ita ta zauna sannan Basma da Bassam suma suka shiga ya rufe ya zagaya da sauri ya shiga ya tada motar maigadi ya buɗe musu gate suka fice sai daya hau titi sannan Tahir ya faɗa masa inda suka nufa, nan ya taka mota suka ɗauki hanyar Kano.
Ƙarfe 12pm. Dai-dai suka shiga garin Kano direct asibitin da aka kwantar dashi suka nufa international Hospital kasancewar Fareeda tasan asibitin saboda anan ake dubasa duk lokacin da jikinsa ya motsa irin haka.
Lokacin da suka shiga room ɗin da aka kwantar dashi yana barci sai Umman Fareeda ce kaɗai suka samu wacce ke zaune a kujerar dake gaban gadon ta zuba masa idanu tana kallonsa, da gudu Basma da Bassam suka nufeta haɗe da faɗawa jikinta suka rungumeta tsam suna tambayarta meya samu Baban Mummynsu cike da so da ƙaunar jikokin nata ta rungumesu tana basu amsa da baida lafiya ne, a hankali Tahir ya ƙarasa gabanta ya durƙusa cike da ladabi ya gaisheta tare da tambayarta mai jiki? Da sakin fuska ta amsa masa da "Alhamdulillahi jiki da sauƙi, barci yake tayi tun ɗazu da akayi masa allura bai tashi ba har yanzu." Yana jinjina kai ya miƙe ya dafa ƙarfen gadon yana faɗin "Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffarane.." da "Ameen." Duk suka amsa kafin Fareeda ta zauna bakin gadon da Abban nata yake a kwance tana kallon fuskarsa cike da damuwa kafin ta ɗauke kanta tana kallon Ummanta cikin sanyin murya ta gaisheta haɗe da tambayarta mai jikin itama, cike da kulawa ta amsa mata da faɗin "Ai da alamun yaji sauƙin jikin sosai, dan kwana biyu ko barcin kwata-kwata baya iya samu, yanzu kuwa kinga tunda likita yay masa allura bai tashi ba sai barcinsa yake yi." Gyaɗa kanta Fareeda tayi fuskarta cike da tausayin mahaifinta tace "Allah ya ƙaro sauƙi ya bashi lafiya." Bayan sun amsa Mufeeda itama ta matso tana ɗauke da Naila ta duƙa a gaban Umman Fareeda ta gaisheta haɗe da tambayarta mai jiki, tana murmushi ta amsa mata tare da miƙa hannu ta ɗauki Naila dake riƙe a hannunta tana kallonta ta fara mata wasa tana ɓangala mata dariya, juyawa Tahir yayi zai fita daga room ɗin da sauri Fareeda ta kallesa "Abban Basma ina kuma zaka je?" Ɗan juyowa yayi ya kalleta yace "Zanje inga likitan ne, yanzu zan dawo." Gyaɗa masa kai tayi ba tare da tace komai ba ya juya ya fice.
Koda Tahir yaje yaga Likita Hankalinsa ya Kwanta Tunda Likitan ya Nunamai ba Mtsala ba kamar yadda Suke Tunani bane,wajen 2pm na Rana Abba ya Farka ba laifin Jikin Nashi da Sauki nan yaji Dadi ganin Farida da Tahir din Hade da Jikokinsa,ganin Hakane yasa Karfe 5 na yamma yayi Shirin Komawa Kaduna Shida Su bassam saboda Mkranta ammh Farida Zata Zauna anan Tataya Umma Zama,Da Zasu Tafi Naila Ta makalema Mufeeda sai Farida tace su Tafi da Ita,Umma ce ta Hana Tace Maza Farida Ta karbi Naila Ta Zauna A Wajenta ai ba yayeta Tayi ba,Bude bakin Farida Sai Tace Ai Ta yayeta,Wata Uwar Harara Umma ta sakarmata kafin ta Karbi Nailan Dake Hannun Mufeedan Tana basu Umurnin Suyi Tafiyarsu Tahir yaji Dadin Haka Har saida Fuskarsa Ta Nuna Farida ko Ta Bata Rai ita Dole An Takura mata,nan dai Suka musu sallama Suka Juyo Zuwa kaduna.
Washehari Duka yaran Suka Tafi Mkranta Shima Tahir yatafi Office Gidan ba Kowa,shiyasa bayan garzali ya Daukosu Daga Mkranta ya biya Dasu Restaurant ya Siya musu Takeaway din Abinci kamar yadda Tahir ya Umarceshi Shi sukaci bayan Sun Dawo kafin Suyi Shirin zuwa Islamiya,Sai yammah Suka Dawo Karfe 7 Tahir ya Dawo Gidan,Shi ya Shigo musu Takeaway din Abinci Wanda ya biya Siyomusu kafin ya dawo Gidan Tunda Iya bata nan,kuma bayason Su basma na Shiga Kichen sai Sun kara girma Mufeeda kuma