Showing 12001 words to 15000 words out of 59199 words

Chapter 5 - FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf

fara WAEC kullum tana dakinta tana bitar littattafanta.
Zuwa yanzu Fahimah ta san zuciyarta ta samu sukuni daga duk wani kalubale dake addabar ta
a baya, sabida karatu ya dauke mata hankali, amma na awa daya ba ta taba manta Uwais ba.
Kullum yana nan like a zuciyarta sai dai tunanin nasa ba ya hana ta sukuni kamar da, kuma ba
ya hana ta fahimtar karatu, sannan ba ta da masaniya a kan batun aurensu, wanda ko a
mafarkinta ba ta kawowa.

A haka ta fara zana WAEC cikin dimbin nasara, ta gama ta yi NECO sannan suka zauna suna
hutawa kafin su zana jamb.

A can gidan Alhaji Umar Dikko gagarumin shiri suke na bikin Amrah, don ana ji da Amrah a
familyn. Tuni Aunty Murjanatu da Yayarta Aunty Wasila suka karbi kudi wajen Daddyn suka tafi
Dubai don hado mata kayan daki.
Shi ma Uwais a nasa bangaren yana ta nasa shirin, ya kammala ginin gidansa da ke unguwar
Sultan Road a Kano, gida madaidaici daidai babban maaikacin banki. Amma fa komai na mace
daya ne a gidan, kuma na mace daya ake ci gaba da yi. Ba ya son tuna zancen wata Fahimah
domin amai ne yake taso masa a duk lokacin da ya tuna wai tare zai aure su ita da Amrah....
Ban da uwa-uwa ce wa ya isa ya yi masa wannan kutsen cikin rayuwarsa?
A nasu bangaren, Ammi da yarta Fahimah babu wani shiri da suke yi, sun ci gaba da rayuwarsu
as normal as before. Ita Fahimah da ma ba ta san me ake yi ba, ko da wasa Ammi ba ta gaya
mata ba. Ta san in ta yi mata umarni ba za ta tsallake ba, amma ta zabi kawai ta yi shiru akwai
lokaci mafi dacewa da ya kamata ta fada matan ba yanzu da ta ke fama da jarrabawa ba. Haka ta je centre din da aka tura ta ta zana jamb dinta lami lafiya.

Fahimah ta yi sallama da Yan Dutse da kawayenta da suka yi zaman aminci musamman Majida
Salisu. Ya zama kullum tana gida, amma sam ba sa haduwa da Uwais. Yanzu ta daina lekensa
in ta san zai shigo gaida Ammi, daga ta ga karfe shidda na yamma ta yi, ta yi sallama da falo
kenan. Don ta san duk inda bakwai na magriba ta yi yana cikin gidan. Da ma sun fi haduwa da

safe, in ta fito za ta tafi makaranta, shi ma ya fito zai tafi aiki, to ita yanzu ta yi sallama da
makaranta.
A hankali ta ji zuciyarta na samun sauki daga azalzalarta da ta ke yi a kan Uwais infatuation din
yana raguwa musamman da ta daina ganinsa.

Yau saura sati biyu kenan daurin aure. Ammi ta gaya masa yadda ya yi wa Amrah kayan aure,
haka zai yi wa Fahimah, adadin sadakin da ya biya na Amrah haka zai biya na Fahimah. Bai
tanka ta ba a lokacin da ta ke maganar, amma zuciyarsa ta yi bakikkirin, sai babbakewa ta ke
kamar ta kama da wuta. Musamman ya kira Jabeer ya ce, yana son ganin Murjanatu, Jabeer ya yi masa iznin zuwa,
suka zauna yana tambayarta dukkan favourite abubuwa na Amrah, colour da design da size. Ita
Murjanatu ya bai wa kwangilar hada komai don ta fi kowa kusanci da Amrah. Amma ya roke ta
kome ta saya ta sayi guda biyu kala ba daya ba kuma girma daya. Murjanatu ta so ta yi mishi
tambaya kan hakan ta fasa. Don a yadda suka tabbatar Uwais na son Amrah, tunanin aurenta
tare da wata ko yi mata kishiya ba zai taba zuwa kansu ba.
Cikin sati daya Murjanatu da kawarta suka hada komai na gani na fada irin nasu na 'yan gayu
ya zo a kwashe saitin akwatunan a booth din motarsa ya kai wa Ammi, sai da ya yi sawu biyu
sabida dozen biyu ne akwatunan, kowacce sha biyu, samfurin LV (Louis Vuitton).

Ammi ta yaba da kayan ta ce masa kowace ce ta hada kayan ta san abu mai kyau da quality, ya
ce,
"Murjanatu ce matar Jabir".
"To Allah ya shi albarka". In ji Ammi.
Talatu Ammi ta sa ta kwashe kayan ta kai dakin Fahimah, ta ce ajiya ce ta ajiye mata. Talatu ta
san komai, kusan ta fi kowa farin ciki da wannan hukunci na Ammi, don kullum tana zama ta yi
tunani mai zurfi a kan auren Fahimah zai zamo kalubale mai girma ga rayuwarta. Don haka
hukuncin Ammi shi ne daidai ko da mata goma Uwais zai aura in dai zai hada da Fahimah
hankalinsu ya kwanta.
Talatu ta zarce matsayin 'yar aiki a gare su don ko kudin aiki ba ta karba, shekara da shekaru
sai ihsanin da Ammi ta ga damar yi mata. Ta zame musu kamar 'yar uwa ta jini.

******
Aka ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya. Kwanakin daurin aure na matsowa,
soyayya gangariya na karuwa tsakanin Uwais da amaryarsa Amrah talkless of Fahima da ba ta
cikin lissafin sa.
Ya kama gobe daurin aure, wanda za a yi a gidan Alh. Umar Dikko na Kano, tun jiya kawu
Shureim da manyan 'ya'yan sa biyu Mahdi da Mohamed da kannen Ammi biyu su biyar kenan
suka iso daga Khartoum, sai mutanen Shagari kwansu da kwarkwatarsu. Duk Uwais ya yi musu
masauki a gidan saukar baki na Tahir Guest Palace. Yana zaune a kujera gefen Ammi, sanye
cikin wani lallausar voyel milk colour kansa babu hula, sumar nan ta kara kwanciya sosai, ta
kuma kara cika da yawa domin ya dade bai rage ta ba. Ammi na daga gefensa tana shan
shayin da Fahimah ta dafa mata ta kule a daki musamman da ta san Uwais zama zai yi a falon.
Wayoyin jama'a yake ta amsawa kala-kala, duk a kan shirin daurin auren gobe. Sai da Ammi ta

fahimci ya tsagaita da amsa wayoyin ta kira sunansa.

"Uwais!".
Ya dago lumsassun idanunsa ya dube ta.
"Gobe nan ne wurin haduwa (meeting point) na daurin aure kafin ku tafi gidan su yarinyar?"
Ya amsa mata da "Eh, Ammi".
Ammi ta ce, "tam... To aurenka da Fahimah za a fara daurawa, ina nufin Fahimah ita ce za ta
zama uwargida, sannan a yi na ita MATAR SO".
A yadda ta fadi maganar cikin shagube ya yi bala'in touching dinsa. Sai dai ya yarda da abin da
ta ce din, "Eh, Amrah matar so ce, ta ki 'yar kuwa matar shige wadda anka ce ba ta daraja
sam".
Bai ba ta amsa ba sai ma tashi da ya yi ya bar wurin. Ta san za a rina, da ma ba ta tsammaci ya
tankata ba, umarni ta bayar kuma dole a bi in ana son zaman lafiya.
Ta kira Kawu Shuraim da madaurin aurensa su Baffa Haruna duk ta gaya musu hakan, su Baffa
Haruna sun yi mamaki matuka, amma da Kawu Shuraim ya yi musu bayanin komai sai suka
fahimta.

Washegari kofar gidan Late Grand Khadi Abdulkarim Shagari ya dinke da jama'a ko ta ina,
musamman ma'aikata GT na Kano. Aka daura auren Fahimah Abdulkarim Shagari da Uwais
Abdulkarim Shagari a kan sadaki mafi kankanta amma mafi albarka. Daga nan suka zarce
gidan Alh. Umar Dikko aka daura na Amrah Umar Dikko da Uwais Abdulkarim Shagari. Daga nan shi da ma'aikatansa da abokansa suka wuce liyafar cin abinci ta bayan daurin aure
wadda abokai suka shirya karkashin jagorancin Jabeer, a gidan saukar baki na Ni'ima.

Uwais farin cikin da yake ciki a yau ba zai misaltu ba, biro ya yi kadan ya bayyana shi. At last ya
mallaki AMRAH so duk wani kalubale, duk wani bacin rai zai zamanto nafilah.
Suna fitowa daga wajen liyafar ya kebe kansa a gefe, Amrah ya kira.
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Cikin wani yanayi ta ganta tare da Yaya Uwais, yanayin da ya fi
kama da muamalar auratayya.... it is something which goes far beyond mere explanation..da
fatar baki but extent reality cikin idanunta, kamar ido biyu ba mafarki ba; mafarki ta yi ma ga ta a
matsayin matar Uwais, sabida abinda ta gani yana faruwa cikin mafarkin ta sani baya yiwuwa
sai da aure. A karshen mafarkinta kuma ta ga yaya rututu zagaye da su, wadanda har ba ta iya
kirga su ba sabida yawansu ya cika dakin da suke ciki.

A matukar firgice fahimah ta farka, jikinta ba inda ba ya rawa, a karshe ta mike zuwa toilet ta
sakarwa kanta shower ta ruwa mai dumi ko ta samu karkarwar da jikinta ke yi ya tsaya, ko ta
samu ta yi regaining consciousness dinta. Barcin da ba ta koma ba kenan har rana ta fito.
Tana kwance lamo a cikin bargo, ta kasa fita taya Talatu aiki yadda ta saba, kasancewar yau
lahadi ba ta da makaranta, kuma ta yi sallar asuba da azkar dinta na safiya, sai kawai ta ci gaba
da kwanciyarta.

Karfe goma na safe Uwais ya fito daga bangarensa zuwa sassan Ammi, ya same ta tana sallar
walha, sai ya samu gefen gadonta ya zauna yana tsumayinta har ta idar, ta yi addua suka shafa

tare.
A yadda Hajiya Safiyya ta ga fuskar Uwais yau, tana wani irin annuri ta tabbata yana dauke da
labarin da ya faranta ransa. Ya sauko daga gefen gadon ya dawo daidai kafafun Ammi ya
zauna. Ko daga irin zaman da ya yi Ammi ta fahimci muhimmiyar magana ta kawo shi.
Ya ya aka yi ne ka zo ka sa ni a gaba yau Lahadi ma me ya fiddo ka da wuri haka? Na dauka
duk lahadin karshen mako sai sha biyun rana ka ke fitowa?
Uwais ya gyara zamansa sosai ya ce, Ammi na kasa barcin ne, sabida ina cikin farin ciki, Amrah
ta amince min in tura magabatana a yi maganar aurenmu. Ba sai ta kare karatu ba.
Ammi ta dube shi da sakakken baki, idonta na wani irin budewa ta ce,
Wace ce haka?
Kansa a kasa ya ce, Yarinyar da na ke nema, kanwar Jabir, na dade da gaya miki ina neman
aure.
Hajiya Safiyyah ta yi masa wani irin sakaran kallo, ta ce, Uwais! Da kakkausar murya.
Da sauri ya dago ya dube ta cikin tsananin fargaba.
Ta ce, Ba kanwar abokinka ba, ko kanwar shugaban kasa ce ban yarje maka aurenta ba. Mace
ko da zubarjadu da yakutu aka kera ta haka za ta ganka ta barka, don tuntuni kana da matarka.
Kalaman karshe tamkar saukar alburushi ya ji su a kirjinsa. Hajiya Safiyyah ta ci gaba da cewa,
Da ma na zuba maka ido ne in ga iya gudun ruwanka, wannan rawar kan da ka ke a kan
yarinyar nan kadai zai hana ni yarda da batunta, don na san muddin ka aure ta ba za ka taba yi
wa FAHIMAH adalci ba! A matukar razane kuma a firgice Uwais ya dago ya dubi mahaifiyarsa.
Fahima? Fahimah! Fahima!! A ina ya taba jin wannan sunan???
Kamar kullum yana jinsa cikin gidan nan. Daga bakin Talatu da Ammi. Cikin wani irin rashin
kuzari yake kallon mahaifiyarsa.
Ammi, I didnt get you right, wallahi ban gane maganar da ki ke yi ba.
Hajiya Safiyyah ta mike tsaye tana nade sallayarta, In ma ka gane ai cewa za ka yi ba ka gane
ba, sabida rainin hankali irin naka Uwais, tunda dai ni da Hausa na yi maganata. In hausar ce
ba ka ji sai ka je ka nemi wanda zai fassara maka.

Ta fice daga dakin ta barshi nan a zaune.
Uwais ya ci gaba da zama a inda ya ke tamkar an kafe shi. Kokari yake ya yi digesting
maganganun Ammi cikin kwakwalwarsa abu ya gagara. Allah ne ya kawo Talatu wadda yake
kira "Baba Talatu" da tsintsiyar kwakwa a hannunta za ta yi wa Ammi shara. Ta ganshi a zaune
kamar statue, ta ce, Uban masu gida tunanin me ake haka? Can tsakiyar kansa ya jiyo muryar Baba Talatu, ji ya yi tamkar mai fassarar da Ammi ta ambata
ce Allah ya kawo masa.
Talatu couldnt believe cewa muryar Uwais ce ke yi mata magana, sabida yadda ta sirance ta
zaftare, duk wani thickeness da huskness da ke cikinta ya tafi.

Baba Talatu idan aka ce mutum tuntuni yana da mata me ake nufi?
Tambayar ta bai wa Talatu dariya, ta ce, Ubangidana ana nufin yana da matar aure ko? Abin da
ban fahimta ba shi ne, an yi auren ko za a yi ne nan gaba?
Uwais ya hadiyi miyau kamar ya hadiyi kunama, ya ce, Baba Talatu wace ce FAHIMAH?

Talatu ta kai idonta da sauri ga hoton Fahimah da ke gefen gadon Ammi daidai inda ta ke saka
kanta. Ta ce, Uban masu gida, Fahimah ai daya muke da ita, kuma daya muka sani wata ce
ban da abokiyar haihuwarka? Ina nufin Fahimah ta gidan nan, autar Ammi.
A lokacin ne kwakwalwar Uwais ta soma daukan caji, ya ji wani irin bacin rai da bakin ciki sun
zo sun tokare shi a kahon zuci. Bai yi aune ba ya ji cikinsa na hautsinawa Talatu ba ta ankara
ba sai ganin Uwais ta yi yana kelayo amai a tsakar dakin Ammi. Amai sosai ya yi kamar zai
amayar da yan hajinsa. Talatu sai faman sannu ta ke masa ya tashi yana rangaji ya bar dakin
ba tare da ya karbi ruwan da ta kawo masa daga firji tana fadin ya wanke fuskarsa ya kurkure
baki ba, zai ji dan dama-dama.
Ta gaban Ammi ya wuce fuuu tana zaune a falo, ko kallon fuskarta bai yi ba ya wuce, abinda bai
taba yi ba. Ammi ta kyabe baki ta dauke kanta daga bayan sa. Ba don aikinsa ba yau zai bar
garin. Tafiyar da sai Ammi ta janye mummunan furucinta sannan ya dawo. To Banki ba su san
excuse ba. Yau yayi nadamar zabar aikin banki matsayin career din sa. Amma ya kudire a
ransa cewa Ammi ta samu matsala irin ta cutar dimentia wadda tsofaffi ke fama da ita. Zai yi
kokari ya nema mata magani.

Tun daga ranar gidan ya koma wani iri ba dadi, kowa ba ya cikin walwala. Ammi ranta a mugun
bace yake da maganar auren da Uwais ya rakito, Fahimah ciwon so ya gama kassara ta, ya
karar da kuzarinta, ya tafi da duk wani karsashi da ta ke da shi a cikin gidan ko falo ta daina
fitowa. Yayin da Uwais yana can yana neman mafita, ga balain da ke shirin tunkaro shi yo bala'i mana!
Rashin Amrah ai catastroph ne, haka zancen da Ammi ta yi (abin amai), shi ma babban balaI ne
a gare shi. Don in ya tabbata Ammi ba ta da dimentia kuma tana nufin abin da ta ke fadi ne har
zuciyarta wace irin mafita zai nema wa kansa ba tare da ya fada fushin Ubangiji ba? Ammi ba uwa ba ce kadai, Uba ce, dangi ce, abokiya ce komai ce a gare shi, amma ba zai iya
yi mata wannan uzurin ba, ko da duk duniya za ta taru a kanshi. Zai iya hakura da Amrah in
abinda auren ta zai janyo masa kenan, amma auren Fahimah sai dai ayi da gawar sa.

******
Walwalar gidan duk sai ta ragu, kowa yana dakinsa kullum, Talatu ce kadai ke shige da fice don
tsaftace muhalli, abinci sun daina ci tare a dining yadda suka saba, sai dai ta kai wa kowa
dakinsa, ta kuma lura ko ta kai din ba wani cin kirki suke masa ba kamar da, musamman Uwais
ko tabawa ba ya yi, in ya fice tun bakwai na safe sai bakwai na magriba ko a ofis coffee kawai
yake sha wanda yake hadawa da kansa.
Amrah ta koma Malaysia tuntuni, kullum suka yi waya tana jin muryar Uwais ba yadda ta saba
jinta ba, ko da ta tambayi dalili sai ya ce mata,
Aiki ne yake masa yawa.
Yanzu ya rage zuwa gidan Jabir tun bayan komawar Amrah, tsiya iri-iri Jabir ya masa amma sai
dai kawai ya yi murmushi ya ce, To me zan zo in yi maka, kai ma ka san ba don kai nake zuwa
ba.
Ko kusa bai gaya masa yana da matsala da Amminsa a kan maganar Amrah ba.
Yau yana ofis kawai wani tunani ya fado masa, Kawu Shuraim. A kasar Sudan, shi ya fado
masa a rai, Yayan Ammi da suke uwa daya uba daya, kuma wanda Ammi ba ta iya tsallake

maganarsa.
Wata ajiyar zuciya Uwais ya saki, ya mika hannu ya dauko wayarsa a kan tebir din gabansa ya
lalubo lambar Kawun nasa.
Uwais na nan da larabci zam a bakinsa, don Ammi tana yi masa sosai tun yana yaro. Sannan
akwai aminci sosai tsakaninsa da Kawun nasa don yana yawan yi masa alkhairi ba tare da
sanin Ammi bama. Shi kadai ya rage babba a family din su Ammi, ya manyanta, ragowar duk
kannenta ne maza da mata. Suka gaisa sosai da Kawun, shi da kansa ya tsinkayi damuwa a muryar Uwais, ya ce,
Uwais gaya min ko me ke damunka, insha Allahu za'a samu mafita.
Uwais ya runtse idonsa ya ce, Kawu, matar aure na samu wadda nake so, daidai da ra'ayi na,
mai duk qualities din da nake bukata a matar aurena, ina sonta sosai, kuma ta amince min in
turo magabatana yanzu haka.
Da na zo na gaya wa Ammi, sai ta kawo wani batu wanda har yau na kasa daidaita maanarsa a
kwakwalwata. Kawu, na dai fahimci wai ta yi min mata ne already, imagine Kawu da wannan
tsintacciyar magen da ta dauko a gidan marayu.

Yaa Subhanallah!

In ji kawu Shuraim cikin kakabi. Ya ce, Ita Safiyyar da hankalinta za ta aura maka wannan bakar
yar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login