Showing 9001 words to 12000 words out of 59199 words
Chapter 4 - FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf
bi ta da ragaitattun idanunsa.
Tunda yake a rayuwarsa bai taba jin yana son mace da dukkan zuciyarsa da ruhi irin yau ba.
Yes, ya yi dating iri-iri a makaranta amma bai taba jin abin har zuciyarsa ba. Yawanci ma matan
ke fara kawo kansu. Yau kuwa ji ya ke ba shi da sauran buri a rayuwa irin na mallakar
kyakkyawan abin da ya gani yanzun nan.
Jabir na ta yi masa hira, sai ya lura Uwais absent - mindedly yake sauraronsa. Ya dan doki
kafadarsa,
Kai tunanin me ka ke haka ina ta magana ba ka jina?
Suka ci gaba da cin abincin su, amma Uwais bai kara nutsuwa ba. Sannan dandanon abincin
bai kara hawa kansa ba duk da kwarewar da Murjanatu ta nuna wajen sarrafa shi.
Sai da Jabir ya rako shi zai tafi ne ya tambaye shi game da yarinyar da ya gani dazu, Jabir ya
ce,
Wai Amrah? Kanwata ce uwa daya uba daya, ta zo mana hutu ne, a Malaysia ta ke karatu.
Duk miskilancin Uwais yau ya kasa sarrafa kansa.
Ya ce, To Jabir, ko in shigo daga ciki ne?
Dariya Jabir ya yi sosai ya ce, Ta yi kankanta da aure a gidan mu. Yanzu ne ta ke shekarar
farko a karatunta na medicine, Daddy ya fi so ta kammala MBBS ma kafin ya yi mata aure.
Uwais ya marairaice wa Jabir, Ni dai don Allah ka shige min gaba, ka gabatar da ni ga Daddy,
sai da izininsa zan fara nemanta. Wallahi na yi alkawarin barinta ta yi karatu har sai ta ce ya
ishe ta. Ka ji tausayi na Jabir na kai 30 fa, kullum da jikakkiyar kanwa ta a kofi a gefen gado
nake kwana. Dariya sosai Jabir ke yi, dama gwanin dariya ne, ya ce, Ina su Salma? Firdaus? Jennifer and
co? Ka fi karfin autar mu Uwais, you never take any dating serious, ina tsoron in shigar maka ka
gano wata ka bar min kanwa emotionally touched.
Uwais ya shafi lallausar sumar kansa, ya ce, Joke apart Jabir, ni fa na ga mata a gidanka. So ko
ka ki supporting dina zan kai kaina ga Daddy, amanar kanwarka idan na ci ta Allah ya ci tawa.
Ko daga cikin amon muryarsa Jabir ya san he is now talking serious, amma gani yake Uwais ya
fi karfin Amrah domin shekarunsa sun kusa ninka nata. Ga shi da matukar wayewa tun suna
jamia da farin jinin mata fiye da dukkan abokansu. Sai dai ta fannin tarbiyya ya yarda Uwais ya
same ta cikakkiya. Maman shi is over-protective.
Don haka ya yi masa alkawarin zai kai shi wajen mahaifinsu in ya zo gari kasancewar a Abuja
iyayensu ke zaune. Yana da wata matar a nan Kano bayan mahaifiyarsu duk karshen wata yake
zuwa Kano ya yi kwana uku kacal. Ko shi zai so Amrah ta samu gwarzon miji irin Uwais
Shagari.
Tun daga ranar Uwais ya maida gidan Jabir wajen cin abincin darensa, don kawai ya ga Amrah.
Ya yi alkawarin ba zai tunkare ta ba sai da yardar mahaifinta kamar yadda shariah ta umarta. Ya
kuma roki Jabir ko Murja kada ya bari ta ji don Amrah yake zuwa, shi kuma Jabir da gayya yake
kiranta ya sa ta aiki in Uwais ya zo don ya samu ya ganta hankalinsa ya kwanta. Girkin ma
cewa yake Murjanatu ta sakar mata don Uwais ya ce ba abin da yake so irin ya ci abin da ta
sarrafa da hannunta.
A fannin ita Amrah ba ta san manufarsu ba, don haka da zuciyarta daya ta ke yin komai da
Jabir ya sa ta yi musu. Murja dai duk da Jabir bai gaya mata don Amrah abokin nasa yake zuwa
ba ta fara ramfo su, ko tsakiyar idanun Uwais ka kalla sai ka ga kwantacciyar soyayyah. Cikin
kallon da yake yi wa Amrah. A ranta dari bisa dari tana supporting abun don har zuciyarta ta
san in Amrah ta yi nasarar samun Uwais a matsayin miji ta yi matukar dacen miji daya da daya
a cikin maza.
Yawan fitar da ya tsira kullum bayan ya dawo ofis wanda a baya ba ya yi kuma ba halin sa bane
ya soma damun Ammi. Ta tsare shi da tambayar ina yake zuwa ko abincin dare ba ya ci a gida?
Ya ce mata babu inda yake zuwa sai gidan Jabir dole ta kyale shi.
Ranar jumaa Alhaji Umar Dikko ya sauka garin Kano daga birnin tarayya. Gidansa na Kano
yana unguwar Bompai. Tsohon dan boko ne da aka dade ana damawa da shi a gwamnatin
tarayyah, a halin yanzu shine shugaban hukumar Haraji ta kasa. Yayansa takwas biyar ciki
daya, uku ciki daya, Jabir ne babba, sai Hassan da Hussaini, Wasila sannan autarsu Amrah.
Amaryarsa da ke Kano tana da yaya uku kanana.
Sun yi shi da Jabir cewa in daddy ya sauka jumaa, washegari asabar za su je su same shi da
kokon barar su. Duk da Jabir ya san mawuyaci ne Baban nasu ya amince ya aurar da Amrah a
wannan lokacin. Sai dai an ce a rashin tayi akan bar arha kuma a rashin kira karen bebe ya
bata. Tun karfe bakwai yake shiri, kayan da ya tanada musamman don ranar babban riga da yar ciki
da wando na wani rantsattsen yadin filtex milk colour ya sanya ya feshe su da 'Maison Francis'
dinsa. Agogon rolex mai fata ruwan kasa-kasa ya daura a damtsen hannunsa, haka hular kansa
da budadden takalminsa ALDO duk ruwan kasa-kasa ne. kowa ya kalle shi sai ya kara, ya hadu
iyakar haduwar da kowacce rantsatstsiyar mace ke buri a mijin aurenta. Uwais Abdulkarim
Shagari kenan.
A falo ya tadda Ammi da Fahimah suna shan shayin da ba ya rabo da gaban Ammi. Fahima
sanye cikin wani lallausan cotton lace ruwan makuba mai ratsin orange, ta kalmasa daurin kai
mai tsari a kanta kamar mai shirin zuwa dinner. Nan kuwa daga ita sai Allah Ubangijinta suka
san don wa ta yi kwalliyar nan, a daidai lokacin da ta tabbatar zai fito ya tafi yawon magribarsa
da ya tsira kwanan nan. Bayan ya yi mugun daukar wanka.
Ita a kan karan-kanta ba maabociyar kwalliya ba ce, kuma ba ta yinta sam a fuskarta, amma
tana zama ta bata lokaci wajen kalmasa daurin kai mai tsari wanda zai fiddo cute fuskarta, da
lace ko atamfa (her fovourite attire). Ta shafa wet-lips mai kamshi da tausasa lebe. Burin
zuciyarta in zai shige ta ganshi, ko da ba zai kalle ta ba, ita za ta saci kallonsa zuciyarta ta rage
zugi da radadin da ta ke mata a kansa.
Sai ina kuma? Wannan babbar riga haka?
Ammi ta fada trying hard ta tuna lokaci na karshe da ta ganshi cikin babbar riga. Baki sake ta ke
kallonsa don alamuransa a dan tsukin nan ta kasa gane musu. Kamar wanda yayi gamo sai
aukin wanka kamar kwado. Wani sassanyan murmushi ya yi, a miskile ya ce,
Ammi, neman aure za ni, ki yi min addua. sai na dawo.
Bai jira cewarta ba ya sa kai ya fice. Ammi ta bi shi da sakakken baki kafin ta ce da Fahima,
wadda ta daskare a wurin,
Anya Uwais lafiyarsa? Aure? A ina?
Ba don bai kai munzalin ya yi auren ba ne ya sa Ammi ta yi wa kanta wannan tambayar ba, sai
don kallon da ta ke masa na miskilancinsa ba zai taba bari ya taba cewa yana son mace ba. Sai
fargawa ta yi babu Fahimah a wajen, ta shige dakinta ta bame kofa.
Tana rufe kofar ta jingina jikinta ta lumshe idanunta tana amsar sababbin feelings din da
maganar Uwais ta haifar. Masu kama da fitar bullet zuwa tsakiyar kirjinta.
AMMI NEMAN AURE ZA NI!
She dont actually know the meaning of the feelings, amma ta san it deeply hurts, some hidden
parts da ke karkashin zuciyarta.
Neman aure za ni, Ammi ki yi min addua.
Maganar Uwais ta yi amsa-kuwwa a cikin kanta a karo na biyu, ta kuma rasa dalilin da ya sa ta
haifar mata da wannan bitterness din a kasan ranta. Me hakan ke nufi? Zuciyarta na nufin
Uwais ba zai yi aure ba? Ko kuwa bai kai munzalin yin aure ba? Amma da ta yi tsam da ranta
da hankalinta waje guda a yau, sai ta fahimci cewa Uwais zuciyarta da gangar jikinta ke son
aure, wanda hakan na nufin zuciyarta LOVES UWAIS DEARLY..... shine dalilin da yasa taji
wannan bitterness din a karkashin ranta don ya ce ya tafi neman aure.
Da ta ki da ta so gaskiyar magana kenan, shi ne kuma fassarar duka unexpressable feelings
din da ke dankare cike da zuciyarta shekara da shekaru akan Yaya Uwais, shi ne kuma silar jin
abin da ta ke ji yanzu da ya ce ya tafi neman aure, something unbelievably like KISHI.
A hankali Fahima ta sauke ajiyar zuciya tana jin tamkar zuciyarta na gutsittsirewa into pieces
tana narkewa kamar dalma, kawai saboda Uwais ya ce ya tafi neman aure! To ina ga ranar da
aka daura auren sa da wata akan idon ta!?
Da kyar ta ja kafa zuwa gadonta ta kwanta rigingine, abubuwa da yawa na gilmawa a
idanunta.... zuciyarta na hasko mata ranar da za ta ga matar Uwais a gabanta, ko how does she
look? Ta tabbata She must be beautiful like him in one way or the other.....ba kamar ita ba, and
the LUCKIEST woman on earth...... watakila ranar ce ranar karewar numfashinta a duniyar
Subhana......(ranar da zata ga matar Uwais).
******
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Kwana uku bayan nan suka wayi gari da bako na ba-zata, kawu
Shuraim daga Khartoum. Ko kusa Ammi ba ta kawo a ranta abin da ya kawo Shuraim har
Nigeria a kan maganar auren Uwais ne ba. Rabon shi da kasar Nigeria an fi shekaru ashirin, tun
rasuwar Baban Uwais, bayan nan kuma sau daya ya taba zuwa tun Uwais na yaro don kawai
ya gan shi, sai kuma yau da ta ganshi a falonta bisa jagorancin Uwais ba zato ba tsammani.
Ammi ta rasa ina taka saka ina taka aje da Yayanta. Ta cika shi da cima ta alfarma. Ta sa Talatu
ta gyare masa dakin baki, amma tun a wajen cin abinci ya gaya wa Ammi kwana uku kawai zai
yi ya koma Sudan.
Sai dare suka samu zama officially ita da Kawu Shuraim. Ta tambayi duka yan uwanta da
yayansu, ya tabbatar mata kowa lafiya, sannan ya ba ta jakar himilin tsaraba da yan uwanta
suka aiko ya kawo mata, wadda duk ta danganci cimar kasar Sudan da kayayyakin amfaninsu
na yau da kullum.
Kawu Shuraim ya yi amfani da hikima irin ta manya bai nuna Uwais kararta ya kai ba, ya ce,
Safeeyyah abin da ya kawo ni takanas kasarku ba komai ba ne face maganar auren Uwais. Sai
yaushe ki ka shirya yi masa aure, ko ko shi ke nan don ba mahaifinsa sai ki yi ta zama da shi a
cikin gida har sai ya zama tuzuru? In matar ce bai samu ba a duba masa a can Sudan cikin
yayan dangi.
Da sauri Ammi ta ce, Ko kusa, ba mace ce bai samu ba, hasalima ni na dade da tanadar masa
mata, ina jira ne ta kare karatun sakandire a daura musu aure.
Sai kuma ya kawo min wani zancen banza wai kanwar abokinsa yake so zai aura, ni kuma na
soke zancen tuntuni. Ba zan gaji da cewa mace ko da zubarjadu da yaqutu aka kerata ba za ta
auri Uwais ba face Fahima ta.
Kawu Shuraim ya yi murmushi, ya ce, Wace ce ita Fahimar?
Ta ce, Fahima tawa dai da ka sani, wadda na dauka tun tana yarinya.
Ta gidan marayu?
In ji kawu Shuraim cikin shagube.
Ammi ta yi shiru, ya ce, To su waye madaura aurenta, kuma su waye suka kawo ta duniya?
Idan yar zina ce fa? Sai ki hada da tsarkakakken Dan ki? Wannan halaka kai don farantawa
wani da me ya yi kama? To ba da mu za a yi wannan danyen kazamin aikin ba. Idan mafarki ki
ke ki farka. Gobe insha Allahu zan sa shi a gaba ya kai ni har Shagari wajen dangin mahaifinsa. Mu hadu
mu je mu nemo masa aure na mutunci da martaba. Tun wuri ki san yadda za ki yi da bakar yar
ki, Uwais ba zai karba bayafi karfin ta
Kawu Shuraim bai ankara ba sai jin shesshekar kukan Ammi ya yi a hankali ta ke kuka mai
motsa zuciya. Kafin ta share hawaye ta dago ido ta dubi Yayanta.
Alummar Annabi ina za ku kai rashin adalci? Su wadannan yaran me ye laifinsu? Zabin su ne
zuwan su duniya a haka? Ko kuwa laifin iyayen su? Har ce mata ka ke BAKA don kawai kuna
farare larabawa, shin zabinku ne fitowa da farar fata? Ko kuwa tsarinku ne irin halittar da ku ke
so Ubangiji ya baku? Ni a wajena HALIN MUTUM shi ne yake sa wa a so shi, amma ba nasaba
ko zubin halitta ba.
Don haka in har ni na haifi Uwais na kuma raine shi ba tare da taimakon kowa ba, Fahimah na
yarje masa ya aura.
Duk da jikin Kawu Shuraim ya yi sanyi, amma bai ji dadin kalamanta na karshe ba, Safeeyyah
ni ki ke gaya wa ke kadai ki ka raini dan ki ba tare da taimakonmu ba?
Ta girgiza kai da sauri, Ka yi hakuri dan uwana, ban fada da wannan manufar ba, amma idan
har kun amince, Uwais zai auri Fahimah, ni ma na yi masa adalci ya hada su ita da zabin ran
nasa ya aura. Amma ita Fahima zan ci gaba da rikonta a wurina sai ranar da ya zo min da bakin
sa ya ce ya karbi auren ta, burina kawai ya kasance da auren Uwais a kan ta, kuma da aurenta
za ta yi karatun jamia. Duk ranar da ya ankara cewa zabi na gari na yi masa, kuma ya shirya
karbar matarsa sai ya yi min magana in kai ta dakinta.
Kawu ya ji dadin adalcin da Ammi ta yi wa Uwais a dalilin sa. Ya sa mata albarka, ya ce kuma
insha Allahu zai yi convincing Uwais ya amince da tsarinta.
Amma ko da Kawun ya yi wa Uwais bayanin da Ammi ta yi a washegari da safe, Kawu Shuraim
na ganin yadda gumi/zufa ke barkowa daga kowacce kafa ta jikin Uwais kamar bai taba jin abin
da ya girgiza shi irin wannan ba.
Don haka Uwais ka amince kawai, ban ga laifi cikin hukuncinta ba. Mahaifiyarka ce da ta fi
kowa hakki a kanka. Hakkinka ne ka faranta mata don samun aljannah. Na yarda va karamin so
take yiwa yarinyar nan ba, domin kuwa har hawaye ta zubar a gabana.
Ta ce ba za ka dau yarinyar zuwa gidanka ba sai sanda ka shirya karbar auren ta, zuwa lokacin
Uwais kana tare da matar da ka ke so kun hayayyafa, wannan auren garkuwa ne kawai ga
yarinyar kamar yadda na fahimci yar uwata.
Uwais kowa ya rufa wa wani asiri, Allah zai rufa nasa. Uwais Da na kowa ne, kuma samun uwa
irin taka sai an tona. A kan wannan marainiyar sai ka ga ta shiga aljanna kamar kiftawar ido mu
muna gefe muna jan gindi a kan siradi, saboda girman kan mu da rashin tausayi.
Haka Kawu Shuraim ya ci gaba da yi masa nasiha da nusar da shi muhimmancin biyayya ga
iyaye, musamman UWA, musamman ga su maza.
A fatar bakinsa bai ce ya amince zai auri Fahimah ba, amma shirun da ya yi da sunkuyar da
kansa da ya yi na lokaci mai tsawo ba tare da ya ce komai ba, ya tabbatar wa Kawu Shuraim ba
shi da ta cewa wai barawo a hannun mata.
Don haka Kawu ya yi ta sa masa albarka ya ce ya yi musu shirin tafiya Shagari washegari, ba
zai bar kasar ba sai an karba masa auren Amrah tare da shi, sannan shi zai zama waliyyin
Fahimah idan lokaci ya yi ba don komai ba sai don shima yana kwadayin irin ladan da yar
uwarsa ke kwadayi. Washegari ta jirgi suka tafi Sokoto shi da Kawu Shuraim, inda suka hadu da Baffaninsa na can
Malam Haruna da Malam Sufyan wadanda kanne suke ga marigayi mahaifinsa Grand Khadi
Shagari suka wuce Abuja gidan su Amrah.
Alhaji Omar Dikko ya yi musu tarba ta mutunci, aka tattauna a kan siyasa kafin su gangaro ga
abin da ya kawo su, wato nema wa dan su Uwais auren diyarsa Amrah, Kawu Shuraimn bai fadi
zancen Fahimah ba kada su rusa neman auren ta hanyar bata rawar su da tsalle.
Alhaji Omar Dikko ya ce, A da ban yi niyyar aurar da Amrah nan kusa ba, amma sabida yadda
na ga Uwais da gaske yake sonta, sannan ya amince ta ci gaba da karatunta a Malaysia in ta yi
hutu sannan ta zo masa, ko shi ya je, to ni ma na amince.
Amma in za a saba wannan yarjejeniyar tun wuri a yi hakuri kawai sai ta kammala".
Kawu Shuraim ya ce, an riga da an wuce wurin, domin Uwais ya amince, kuma su da komai
nasu suke tafe, lokaci kawai suke so a sanya musu.
A takaice ba su bar Abuja ba sai da aka tsayar da ranar daurin aure watanni uku masu zuwa,
lokacin ita Amrah ta samu hutu tana gida. Hatta sadaki da kudin aure sun biya. Farin cikin da
Uwais ya samu kansa a ciki ya mantar da shi zancen wata Fahimah. Bai kara tunawa da
zancenta ba musamman da ya daina ganinta ma kwata-kwata. Ta daina zaman falo don karatu
ya yi mata zafi. Nan da sati biyu za su