Follow us on social media
Showing 48001 words to 51000 words out of 79746 words
Chapter 17 - A Bari Ya Huce Book Complete Complete Hausa Novel by Sumayya Abdulkadir
har kasa ta gaida shi. Ya dora hannun damanshi a kanta ya ce
"Barka da zuwa Maryamu. Godiya ga Allah da Ya sauke ku lafiya".
Yaya Habibun kuwa ko arzikin kallo bai samu ba, sai matarshi ke binshi da kallon mamakin
muguwar zabgewar da ya yi cikin kwanaki biyar kacal.
Mairo ta sha mamakin ganin 'chebrolit' yau a gida Najeriya. Motar da ko a America, sai wanda
ya ci ya tada kai. Ba wannan ne kadai ya razanata ba, sai tangamemen 'gate' irin wanda ake
kira 'Mahdi ka-ture' da aka wangame musu a lokacin da motarsu ta sawo kai cikin unguwar
Asokoro. Ta hango wani irin ‘American billa’ mai kama da jirgin ruwa. Ita dai Mairo ido ne nata, sai kuma ta cilla kafa duk inda ta ga an cilla. Tana cewa a ranta,
watakila Yaya Habibu siyar da mu zai yi. Dama ni kudin nan nasa ai ban yarda da su ba. Sai dai
kuma babu dar ko tsoro ko yaya cikin kalbinta, wadda ke cike taf da takaicin rabota da karatunta
da aka yi babu gaira babu dalili.
A kofar wani kayataccen falo mai kofar gilashi Yaya Habibu, dattijon da sauran mutanen da ke
take mishi baya suka tsaya. Su kuma aka sa wata mace wadda ga dukkan alamu mai aiki ce, ta
yi musu jagora cikin gidan. Ta nuna musu dakin da za su sauka, sannan ta sanar da su cewa,
matar gidan tana asibiti, idan sun kimtsa su danna 'bell' za a shigo musu da abinci. Dina ce ta
amsa, amma Mairo ta zama hoto.
Dina ce ta fara yin wanka, sannan Mairo. Suka dauro alwala suka bada faralin sallar subhi da ta
riske su a jirgi. Suka shirya tsaf, Mairo cikin 'swiss lace' ruwan madara da yarfin kananan
duwatsu, riga da 'wrapper zani', ta yi 'simple' nadin kallabi a kanta. Dina cikin atamfar 'super'
shudiya ita ma riga da zani da yalwataccen mayafi. A tsaitsaye suka ci abincin sabida kiran
Yaya Habibu cikin wayar Dina cewa, su fito za su wuce asibiti.
A babban asibitin koyarwa na Abuja, ita Mairo ta sha wajen matar gidan suka zo da ta ji an ce
tana asibiti, sai raba ido ta ke cike da son ganin wace ce mamallakiyar wannan 'bungalow' din.
Wanda aka yi amfani da hikima, ilmi da tunani wajen sarrafa shi. Kai ita a iya yawonta cikin U.S
ba ta taba ganin irin wannan ginin ba, wanda ta fahimci cewa gidan wannan farin dattijon ne, da
ya je tarbo su filin jirgi.
Dattijon ne a gaba, sai 'escort' dinshi, sannan Habibu da Dina biye da shi, Mairo ce karshen
shiga dakin, wanda ya kasance 'amenity'. Sabida cikowar da dakin ya yi da kyawawan mata
masu kama daya, kuma masu kananan shekaru akalla daga mai talatin sai mai kasa da haka,
sai kuma 'yammata tsararrakinta, wadanda ga dukkan alamu ko auren fari ba su yi ba, ta rasa
inda tasan fuskarsu kamar ta sansu a wani wuri. Daga can gefe wata dattijuwa ce kyakkyawa
cikin kyakkyawar suttura zaune bisa darduma, ta yi nisa cikin sujjadarta ba ta san me ake a
dakin ba.
Cikowar da dakin ya yi, shi yasa Mairo ba ta yi nasarar hango 'patient' din ba, wanda ke ta
kelayo aman jini, har da guda-guda. Daya daga cikin matan ta rike shi tana kuka, sauran ma
duk sharar hawaye suke yi da gefen mayafansu, wanda ke nuni da cewa kauna ce mai tsanani
tsakaninsu da dan uwansu. Da sauri dattijon ya karasa gaban gadon ya tallafe shi cikin kirjinsa. Ya danna wani abu, da
gudu likitoci biyar suka shigo. Nan suka yi umarnin kowa ya fita.
Mairo dama tana bakin kofa, don haka ita ce ta farkon fita. Dattijiyar ma tana sallarta ko dagowa
ba ta yi ba, su ma likitocin ba su ce ta fita ba. Daga likitocin sai dattijon sai Habibu, wanda
idanunshi suka kada suka yi jajur, zaka iya hango tsabar tashin hankalin da ke kwance cikinsu.
Don ma yana dauriya ne, amma da fashewa zai yi da kuka.
Cikin gaggawa kowannensu ke ba shi taimakon da zai iya. Masu jona abin janyo numfashi na
yi, masu auna bugun zuciya na yi, da ya ja wata doguwar ajiyar zuciya su dukka suka kalli juna
suka girgiza kai, sannan suka ci gaba da aikinsu cikin kwarewa da sanin makamar aiki.
Kafin su cire 'odygen' din su yi wa Habibu da dattijon alamar su biyo su ofishinsu. Fitarsu ke da
wuya leburori suka shiga dakin suka soma tsaftace wajen. Har zuwa wannan lokacin dattijuwar
nan ba ta daina sallah ba. Ba ta daina kai goshinta gaban mahaliccinta ba, domin ta yi imanin
Shi kadai ne zai tashi kafadar danta, amma ba wadannan tarkacen nasaran ba.
A can ofishin Dr. Fredrick Engles (consultant) na bangaren zuciya, bayani yake musu dalla-dalla
na bugun zuciyar ba-zata da 'patient' dinsu ya samu, wanda ya yi mugun yi wa zuciyarshi illa
farat daya.
Ciwon zuciya na lokaci daya ya yi mishi mugun kaye, wanda idan ba a yi gaggawar magance
mishi damuwarshi ba, daga yanzu zuwa kowanne lokaci komai zai iya faruwa. Ya kare da
tambayarsu, shin ko sun san hakikanin abin da ke damun mara lafiyan? Domin su sunyi-sunyi
ya fada musu, amma ya ki cewa komai. A nan ne dattijon ya soma yi wa babban likitan bayanin duk abin da Amirun ya fada mishi ranar
da ya dawo, kafin ciwon ya ci karfinshi. Wato kanwar Habibu yake so, ita kuma ta ce ba zata
aure shi ba.
Habibu kuma ya dubi likitan ya ce
"Ni kuma na yi alkawarin zan aurawa Amiru Mairo, ko da a gobe ne, idan hakan shi ne zai
zamo FANSA ga lafiyarshi. Ko da kuwa ace wannan shi ne abu na KARSHE da zan gabatar a
rayuwata".
Dattijon ya ce, "A'a Habibu, ba za a yi haka ba, a bi-ta a hankali, domin dai da na kowa ne, ban
yarda a tursasata bisa abin da ba ta so ba".
Dr. Fredrick ya ce
"Yanzu ina yarinyar?"
Habibu ya ce "Tana waje, sun zo tun dazu. Sai dai ba tasan abin da ke faruwa ba. Da kyar ma
idan tasan Amirun ne kwance a gadon asibiti".
Likitan ya ce "A kirawo ta".
Habibu ya fita, jim kadan suka shigo tare da Mairo, duk da ranta a bace yake, amma ba zaka
karanci hakan a fuskarta ba. Ta nemi kujera gefen Habibu ta zauna, kanta a sunkuye, Dr.
Fredrick ya yiwa su Habibu alamar su fita, yana mai ci gaba da rubuce-rubucensa cikin 'file'.
Ofishin ya rage daga shi sai Mairo, har zuwa lokacin bai gama rubutun da yake yi ba. Daga
bisani ya dago, ta karkashin farin gilashinsa yake kare mata kallo. Cikin ranshi ya ce, Dole
maza su kwanta ciwo.
Ya yi gyaran murya, sannan ya yi murmushi, ya ce "Maryam".
Ta dago a hankali ta dube shi cikin fararen idanunta ba tare da ta ce dashi komai ba.
Ya mike zuwa dan karamin firij da ke gefenshi ya fiddo gorar ruwan (Faro) ya bincire murfin ya
sha, ya maida robar. Maimakon ya koma mazauninshi, sai ya ja kujerar da ke fuskantarta ya
zauna. Ya sake yin murmushi kafin ya sake kiran sunanta. Wannan karon kam ta amsa, ta ce
"Na'am".
Ya ce "Sunana Dr. Fredrick, ni ne likitan da ke kula da lafiyar iyalin ABDURRAHMAN GAYA. Ina
so ki ba mu hadin kai mu ceto rai, wanda ke cikin halin ha'u'la'i akan soyayyarki. Shin za mu
samu wannan taimakon Mairo?"
Cikin murya mai sanyi ta ce
"Ni Doctor?"
Ya ce "Ke fa Maryam".
"Ta ya ya zan taimaka?"
"Ta hanyar tayamu jinya, har sai ya samu lafiyarshi, domin a halin yanzu ba ya bukatar komai
Maryam, sai soyayyarki, sannan ne mu ma za mu samu namu aikin ya yi kyau. Mai zai hana ki
yarda ki auri mai sonki Maryam? Har ya ke neman rasa kyakkyawar rayuwarshi a dalilinki?"
Cike da matsanancin mamaki ta ce "wai wanene?"
Yayi murmushi ya ce
"Taso mu je".
Dr. Fredrick ne a gaba, Mairo na biye da shi. Ya tura kofar dakin dazu ya shiga, ita ma ta sa kai.
Dakin babu kowa, sai mara lafiyan, wanda ke barci sadidan. Sai dai fa da ganin irin barcin da
yake yi kasan ba na Allah da Annabi ba ne, na karfin allurai ne.
Ba karamin bugawa zuciyarta ta yi ba (kamar wancan lokacin da ta fara ganinsa) a lokacin da ta
sake yin arba, da dan Abdurrahman Gaya. Sai dai fa wannan Amirun ya sha ban-ban da wanda
ta gani satittikan da suka gabata, ma'abocin kuzari da koshin lafiya, hadi da wasu nasibobi da
ba duk maza Allah Ya mallakawa ba. Wannan Amirun ya rame fiye da tunaninta, sannan ga
dukkan alamu ba karamin jin jiki yake yi ba.
Ta tsaya jikin gadon kawai ba ta ce komai ba, sai dai zaka iya karantar karyewar da zuciyarta ta
yi, hadi da tausayi tsantsa, da shi ma ya bayyana bisa kyakkyawar fuskarta. Tambaya ta ke
cikin ranta, ita kuwa wace ce da Amiru zai kwanta ciwo a dalilinta?
Kamar an ce da shi bude idonka, a hankali ya ke bude idonshi a kanta. To ita ma din kallonshi
ta ke, sai ya dauka ko mafarki ne da gizon da ta ke mishi dare da rana, don haka ya dauke
kanshi daga kanta, don bai gasgata idanunshi ba. Ya mayar da su kan Dr. Fredrick, wanda ke ta
murmushi. Shi kam al'ummar Hausa suna ba shi mamaki akan soyayya, shi wallahi har duniya ta nade, bai
ga macen da zata kwantar da shi a gadon asibiti ba. Balle mutun irin Amiru, dan gata gaba da
baya, wanda duk irin macen da yake so a duniya zai iya aura. Ganin abinnasu yake kamar irin a
fina-finan India. Ya kama hannun Amirun yana murmushi, ya ce "Kana da bakuwa fa? Wadda tayo tattaki tun daga U.S domin ta duba jikin ka!"
Bai juya ya kara kallon Mairon ba, wadda ganinta ya kara haifar mishi da faduwar gaba. Kirjinshi
in banda bugawa ba abin da yakeyi. Zuwa yanzu ya yarda ita din ce, ba gizo idanun shi ke
mishi ba. Likita ya kama hannun Mairo ya dora mishi kan kirjinshi, dai-dai santar zuciyarshi.
Tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa fat-fat-fat! Amma don karfin hali bai fasa magana ba cikin
nishi.
"Ba wajena ta zo ba, ta biyo bayan Yayanta ne".
Mace mai rauni da saurin karaya, sai ta soma kuka.
Tun fil'azal Mairo mace ce mai tausayi, abin kuka bai da wuya a gurinta, bare an ce a dalilinta
ne Amir ya kamu da ciwon zuciya. Wato wannan ne dalilin Habibu na yanke mata karatunta,
Allah sarki Yaya Habibu, a da har ta kullace shi tayi fushi dashi mai tsanani. Ban da abinsu ita
wace ce? Da kasancewarta tare da shi zai sa ya samu sauki? Likita ya daga mata gira, ya rausayar da kai, ta gane yana lallaminta ne ta rarrashi Amiru. Ta
janye hannunta daga kirjinshi, cikin sassanyar murya ta ce
"Ni na fada maka cewa ba wajenka na zo ba?"
Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude ba. Dr. Fredrick ya zame ya fita, don ya
lura Amirun ba zai iya yi mata magana ba idan yana kallonsu.
Ya sake bude ido a hankali ya dubeta, da wani irin sassanyan kallo. Ta yi hanzarin sunkuyar da
kanta, sabida wasu irin allurai da ta ji suna bin jinin jikinta. Hawayenta na diga a kasa dis-dis.
Ya tara hannu ya taro hawayen, ya ce "Wannan hawayen kuma na mene ne? Ni da kika ce ba
kya so na? Ban yi kuka ba, sai ke?"
Muryarshi bata fita sosai, ba don tana kusa da shi sosai ba, da ba zata ji shi ba.
"How dare you want to me to believe you (ta yaya kike so in yarda da ke cewa) kin zo sabida ni
ne? Bayan kin fada min ga wanda kike so, ni ba kya so na? Na hakura na tafi, don me Habibu
zai takuraki ki biyo ni?
To me kika zo ki yi min? Kin zo ne ki kara min ciwon, ko kin zo karasar da ni zuwa kushewata
ne?"
Ta dago sosai ta dube shi, ya yi saurin kauda kai, don ba zai iya jurar kallon tsakiyar idanunta a
wannan lokacin ba, wadanda suke kamar 'magnet' cikin nashi idanun, suke kuma sanyaya mishi
zuciya, tare da karya karfin zuciyar duk da yake rikewa da jarumtar zucin duk da yake takama
da ita. Har yake ganin zai iya jayayya da ita, ga shi tun ba a je ko'ina ba, ta fara karya lagon
zuciyarshi.
Ta ce a sanyaye
"Har airport na bika, dai-dai lokacin da jirginku ya tashi. Ban ce lallai ka yarda da ni ba, amma
Allah shaidata ne!"
Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa, ya tattara iya sautin da ya rage mishi a makoshi ya ce
"Mairo!"
Ta dakata, hannunta jikin marikin kofar, amma ba ta juyo ba. Ya yi tari kuful-kuful! sau uku,
kamin ya ce "Fushi kika yi? Za ki sake tafiya ki barni? Ciwon sonki ya karasa ni?
Ki yi hakuri idan na fadi wani abu wanda ya bata miki rai, zafin sonki ne ya kawo hakan. Dawo
ki zauna tare da ni, ina jin wani sanyi cikin zuciyata, a dalilin tsayawarki tare da ni.
Ki yi wa Allah, kada ki sake barina, har zuwa karshen rayuwarmu. My life has no meaning…...
Idan na rasa soyayyarki. I’m impotent….idan ba tare dake ba!
Bana son Habibu ya takuraki ki aure ni, soyayyarki na ke nema, ba da tursasawar wani ba".
Wannan lokacin ba ta ce komi ba. Ta rasa abin da zata ce, ta kasa tantance shin abin da ta ke ji
game da Amirun cikin zuciyarta da illahirin gangar jikinta a halin yanzu, soyayya ce ko kauna
ce? Idan kauna da soyayyar ne baki daya, to shi kuma Uncle Junaidu fa? Shi kuma me ta ke
masa idan ba so da kauna ba?
Idan haka ne ke nan MAZA BIYU ta ke so ko yaya ne? Soyayya guda daya ce, wadda a halin
yanzu ba ta san ko ta waye ba, don haka ba zata ce ba. Amma data tuna halin da Amirun ke
ciki, yana bukatar lallashi da kauna daga gareta a daidai wannan lokacin kamar yadda likitanshi
yace, sai ta dawo kujerar da ke fuskartarshi ta zauna kanta a kasa. Kamun kai da kunyar
Mairon, su ne manyan al'amuran yarinyar da suke kara masa kaunarta.
Ya tabbatar ba zata taba bude baki ta ce, tana sonshi ba, sai dai idan su kwana a hakan,
wannan din ma ba karamin burge shi ya yi ba. Domin duk yarinyar da zata budi baki gatsar ta
ce da namijin da bai zamo mijinta ba, ina sonka. To wallahi ba matar aure ba ce.
Inda Allah Ya ceceta daga kaifafan idanun Amirun, shi ne shigowar Yaya Habibu, Dr. Fredrick
da dattijon da a yanzu ta gane shi ne Alh. Abdurrahman Gaya. Mahaifin Amiru.
Cikin murmushin jin dadin ganin dan nashi cikin yanayin da ya bashi mamaki, zaune sosai bisa
gadon ya zuro kafafunshi kasa. Fuskarshi cike da walwala da yalwataccen murmushi ya karaso
gare su, shima Amirun murmushin yake yi.
"A'ah sauki ya samu, lallai, kai Mairo ta iya jinya!".
Amiru ya harare ta, ya ce
"Ni ba wani jinyata da ta yi, sai kuka ta ke yi mini. Kai Yaya Habibu mai yasa ka takurata ta zo?
Me ya hada ciwona da zuwan Mairo Nigeria? Alhalin karatu take yi? Da ka kyale ta ai zan samu
sauki ne a hankali cikin yardar Allah".
Habibu ya harare shi ya ce
"Kwarai fa, shi yasa na ga kamin ta zo ana ta janyo maka numfashi".
Duk suka yi dariya ban da shi Amirun. Da kalaman Habibu suka jefa shi a tunanin anya ya cika
namiji? Anya shigowar Mairo rayuwarsa bata maida shi mace ba?
Dr. Fredrick ya ce
"Ya ci abinci Mairo?"
Ta girgiza kai, sannan ta dubi kular abincin da ke kan lokar jikin gadon, ta dauko ta bude,
farfesun kaza ne da ya ji kayan kamshi, a daya kular 'chips' ne da soyayyen kwai. Tana son ta
tambaye shi wanne zai ci a ciki, amma kunya ta hana ta, don haka ta zuba kowanne kadan cikin
faranti daban-daban ta mika mishi.
Dai-dai sanda ya debo shanyayyun idanunshi ya dora a kanta, sannan ya mika hannu ya karba.
A hankali ta ce
"Ba zaka wanke baki ba?"
Cikin kankanuwar murya shima ya ce
"Kin bani abin wanke bakin na ce ba zan wanke ba?"
Ta ce
"Ai ban san inda ya ke ba".
Alh. Abdurrahman da kansa ya bude lokar ya fiddo sabbin burushi da makilin ya mika mata, ta
bude ta shafa jikin burushin, Yaya Habibu ya mika mata roba. Tana zuba mishi ruwan robar
'swan' yana wankewa har ya gama, sannan ya soma cin abincin. Shi kanshi likitan ya yi
mamakin yawan abincin da Amiru ya ci, wanda tunda aka kawo shi sai yau ya ci, “lallai so ba
dama”. (Ya ce a zuciyarshi) sai ruwa ake kara masa mai dauke da sinadaran abincin maras
lafiya.
Hajiyar Amiru ta shigo, bakinta ya kasa rufo, ganin Amirunta na cin abinci, alamun sauki sun
bayyana sosai a gare shi.
Ta ce
"Kai masha'Allah, har abinci ake ci? Lallai sauki ya samu (don ita ba ta san musabbabin ciwon
Amirun ba)".
Ta kalli Mairo da fuska ma'abociyar walwala, ta ce
"Ina muka samo 'yar kyakkyawar budurwa?"
Mairo ta dukar da kai, Alhajin ya ce,
"Kanwar Habibu ce, kuma surukarki insha Allahu".
Murmushinta ya fadada sosai zuwa dariya, ta ce
"Da gaske?"
Ta juya ta kalli Habibu
"Na ce da gaske ne Habibu?"
Ya yi murmushi ya ce
"Idan Allah Ya yarda".
Kunya a wajen Mairo, kamar ta nutse cikin kasa. Hajiya A’isha ta kamo hannunta ta rike cikin
nata cike da matsananciyar kauna da kulawa.
Ana