Chapter 3 of 7
ƳAN ASHAWO Ciniki a Ɓoye by Oum Aphnan
Tana ankare da tana take mata baya ,saida ta taka step ta riƙe ƙarfen ta jiyo cikeda masifa "meye kike bina ? Ko an aiko ki ki taken inuwa ne ,eye jikan Alya mayya?!" A sanyaye ta kalleta da jajayen Idanuwarta "Makullin motarki zan baki " tayi magana tana miƙa mata makullin ,warcewa tayi ta haye sama tana sababin kar ta fito taga kowa a falon nan ,murɗa ƙofar tayi ta shiga ɗakin Nazeefa tana zaune akan darduma ta idar da sallah hannunta a sama tana addu'a tana kuka
Gaban Tahreem ne kawai taji ya faɗi dukda batasan dalilin hakan ba
"Nazee kin dawo ?" Shafa addu'ar tayi a hankali ta waigo ta kalleta "Na dawo uwarɗakina "
Haɗe fuska tayi "Wai sai yaushe zaki daina isana da kukan nan na banza da wofi ,wai wanine ya aikeki shigowa bariki?" A sanyaye tace "kiyi haƙuri wannan kukan na dolene ,Anty ko ke kika ga abunda na gani a yanda na sanki sai kinyi kukan da yafi nawa"
Katseta tayi cikin gwasalewa da nuna halin ko In kula "Ina en matan da kikaje samowa ?"
"Anty ban samo ba ,wallahi ance duk an turasu aikatau...!"
Tsawa ta daka mata sannan ta fara magana kamar za tayi kuka "shikenan kinaso kiyi mun ta leƙo ta koma,yanzu lokacin zaɓe yayi gari zai fara jiƙewa da kuɗi mai guntun sha'awa ma yinajin aljihunsa ya cika da kudi neman matan harka zaiyi ,shine kike so kimun baƙin ciki?...Haba nazee tunda na saki a matsayin PA ɗita business ɗina ya soma rawa , Innalillahi wainnailaihir rajiun ,to yanzu da kikaje kika dawo guzurin uwar me kika dawo mun dashi ko sai kukan iska?"
"Aunty wallahi kukana bashida alaka da zamana dake,a hanyane na haɗu da wata miskiniyar bafullatana ,ta rasa uwanta da ubanta da kowa nata,shine na taimaketa na fiddota daga daji yanzu haka tana asibiti '"
Tsaki taja ta juya tai ficewarta tana mata magana cikin gatsali da izgilanci "Allah ya baki lada ya sayyada,amma tabbas na soma gajiya da ciyar daku matuƙar kwalliya bata biyan kudin sabulu shara zanyi in rage en iskan can da basu da farinjinin anini sai shaye²n tsiya........................
Littafin ƳAN ASHAWO Isn't for free Drop your payment via this Account details 7782217014, Mohammad Hassana,Fcmb . Evidence of payment thru 09065990265
Regular group ₦300
VIP 500₦
Special ₦1000
*Garin Naji daɗi Yafi garin Na saba ,Kazalika tafiya da gwaninka Akwai matuƙar daɗi*
Thanks for voting and patronizing,Hrt u all❤️
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951
[7/30, 10:09] أم افنان✍️💞: *ƳAN ASHAWO💅*
_(Romantic story)_
Free page
9️⃣
Oum Aphnan✍️
Ayyah nayi kuskuren Numbering pages en 9_10 ,so consider this one as page 9 plz
*___________________________________*
Tahreem tana shiga ɗakinta jifa tayi da keys ɗin ta da jakanta tayi mika ta tuɓe kayan jikinta ta ɗaura towel da nufin ta shiga wanka,sai kuma ta zauna tayi shiru tana ɗan tunani "Anya Tahreem kinayiwa kanki daidai kuwa? Kinsani kin take sani ,kwana nawa yau baki dauki Kur'ani kin karanta ba " janye taguminta tayi ta maida a ɗayan haɓar ,saiga hawaye yina kwanciya mata a kunci,daidai nan ƙaramar wayarta ya ɗauki kiɗan neman agaji da sauri tayi jifa da pillow ɗin da ta rungume ta ɗauki wayar da sauri ta kanga a kunne "Hello mamana my love" a ɗan ruɗe tace "babyna kina lapy?"
Tattare gira tayi kamar tana kallonta "oh mom I'm cool me kika gani"
"Muryarki ya nuna kina da damuwa ,what's wrong?"
"Oh bakomai wlh kawai gajiyar school ne tun safe naje lectures har yamma shine" ɗan jim tayi kamar bata gamsu da bayaninta ba kana tace "Muyi video call plz" turo baki tayi ,kana tace a hankali "Ohshh she come to disturb my life" washe baki tayi "Yes mom" ta ƙare tana jawo system ɗin ta
"Hi mamana my love Ina za'a haka akasha gayu"
Tahreem me kikeyi "
Ɗan ɗage kafaɗa tayi "Just chilling momy "
"Chilling Ina karatun? In kin gaji da boko karatun Alkur'ani fa?" Yamutse fuska tayi kamar za tayi kuka "Haba mama karatu da safe da rana da dare ba lokacin hutawa ? Gaskiya yanzu dai ina bukatar in wanka ina barci in Kallon film"
"Ok shikenan damuwarki ,bansan me yasa ba Tahreem bakison aiki ,Ni da babanki muna nan muna shan wahala muna neman kuɗi muna saki a makaranta masu tsada da yafi ƙarfin Aljihun mu duk saboda gaba ki alfahari da hakan amma ke na lura baki tausaya mana "
"Haba mama ba haka bane ,akwai wani American philosopher da yike cewa ka samu lokacin wasa barci da nishadi shi zaisa ƙwalwarka ta buɗe "
Ware baki tayi "aihooo shiyasa naga shekara goma da kaiki jami'a har yanzu ba result ,kin maƙale a jikina Ni da babanki ,mu ɗin da kinsan ba ƙarfi gare mu ba"
"Ohhh mama haba don Allah is unfair ki ta mun gori ilimi fa na Allah ne,beside wannan gorin da kullum kuke mun shiyasa na zama horzila don in nema kuɗi In kawo maku nawa gudunmawar ..."
"Kinga Tahreem dakata ,idan bakison karatun shikenan amma kawai ki fito da miji kiyi aure Ni gori ya isheni a cikin dangi"
"Haba momy aure fa da mutuwa lokacine ,ni yanzu haka ma I'm researching for my new project raina a ɓace yike an betraying ɗina "
"Ke kika sani wannan ,nidai kinji na gaya maki kuma ki shirya zan zo a satin nan makarantan naku I need to know more about your academic performance....Amma yanzu I'm off to gidan barka sai na dawo"
Ɗaga mata hannu tayi alamun waving bye ,sannan ta miƙe ta kashe system ɗin tana ƙorafi "I'm tired with this constant insult dole in doubling effort ɗina don in Tara kudi masu yawa kafin a taso mun da mganar aure na tara kudin siyan manyan kayan ɗaki na kece raini kar ,inzo aure ba kayan ɗaki masu tsada ƙawayena suna mun dariya...." Fita ɗakin tayi ta koma ɗakin nazeefa a bakin ƙofa ta ganta da doguwar jilbab milk colour da wayarta a hannu .waro ido tayi "ina zaki in this late evening ? Da wani dogon hijabinki kamar matar liman nifa gaskiya na gaji da biyan kudin haya duk shekara ina ciyar daku all in vain baku kawo mun manyan attajirai yanzu tsakani da Allah wani ɗan duniya zai ganki yayi sha'awar toaster ki a haka?"
Dafe kai Nazeefa tayi sam masifan Tahreem ya fara yi mata yawa"Anty inada mara lafiya ,ya kamata inje in dubata ba gantali zani ba ,infact I'm moody now"
Sakin baki tayi tana kallonta sannan ta kwaikwayi maganar ta "yen yen yen I'm moody now ,nima Ina cikin ɓacin ran ne shiyasa nazo in sameki muyi resolving wasu issues ɗin"
Ɗauke fuska tayi "ki bari in dawo to" mamaki Nazzefa taba Tahreem ,mai ke damunta take mata magana kai tsaye ba ɗan girmamawa ɗin nan ko shayi ² ?
"Wai wannan wata kalar yarinya ce kika gani da ta juyar maki da lissafin ƙwalwarki kina mun magana caka caka....(sai kuma tayi shiru cikin tunani) ohkkk karkice mun kin soma les ne kinga jar fata kin fara mata rawar ƙafa ki siyeta da kyautatawa "
"Anty don Allah ki ƙyaleni da maganar nan duk abunda kike tunani ba haka bane ba ,kawai tausayinta nike don Allah saboda duk duniya yanzu bata da kowa ,in ban kula da maganin ta ba zata iya shiga wani halin ko asibitin in sunga babu mai kula da ita su sallameta a haka"
Shiru Tahreem tayi kana tace "jirani inje inga patient din "
*****
Gidan Manjo Tanimu siwiɗi .
Matsakaicin falone mai ɗauke da madaidaitan kujeru set ɗaya ,ba wasu tarkace a falon sai manyan hotuna window size ɗaya an zana Manjo Tanimu siwiɗi ne cikin kakinsa na sojoji sai kuma ilahirin hotunan en gidan rayuka huɗu zuwa biyar wato Hajiya Zuwaira matar me gidan kenan sai kuma Mohammadul kabeer ,Sarah da Salima
Nagane iyakan yawan en Gidan ne yanda na gansu Zazzaune a falon
Sarah da Salima suna zaune a ƙasa karfet ɗin tsakiyar falon saye da hijabansu kalan dark blue da Alƙur'aninsu a hannu zasu tafi makarantar Addini , sai Mohammadul kabeer tsaye daga bakin ƙofa cikin shigan nigga da Chain a wuyarsa gashin kansa yasha Askin en Allah ya shirya ,riƙe da mukullin mota
Cigaba da nasiha Hajiya Zuwaira take masu amma Mohammadul kabeer yanda kasan yina kan ƙaya,ga kiransa da ake tayi a wayarsa dake aljuhu ,cikin tsawa yace "Hajiya a sallamesu hakanan Alfatiha ,Ni na gaji da tsayuwa ko kuma wallahi gaba naci ,bazakuyi ta ɓata mun lokaci ba,haba wa'azi tun dazu sai kace ba gida ɗaya kuke ba mtseww"
Ba wanda ya tankasa ita dai ta gama yiwa yaranta nasiha suka tashi suka nufi motar da zai kaisu makarantar a ciki
"Shegu kuna jin ku gijif ² kamar tukwane munana daku ga baƙi ga gajarta ,wani ɗan iskan namiji ma zai soku har ya lalataku amma kullum aita ɓata ma mutane lokaci a kanku ku shiga ko in ɓarar daku" da gudu suka faɗa motar suna kakkare hannu kowacce ta ɗauka zai kifa mata marine ,Yina shiga motar ya danna wata doguwar horn wanda yasa me gadi tala gate da sauri ya kuwa fita da gudu ,daidai kazan maƙoftansu tazo giftawa da en yarorinta ya kuwa bi ta kanta ya murje mata kai ,aikuwa take anan tayi mushe ,shikan bema san yayi ba ya cigaba da sharara gudunsa kamar ya sama babbar kwalta.
A bakin ƙofar islamiyyar ya ajiye su Salima ,Saidai jikinsu ba inda baya rawa saboda hango malam Lawal da bulalan dukan makara da sukayi ,haka suka wuce sunma manta da kur'anan su.
KB kam dafa bayan kujeransa yayi yinaso yayi reverse ya bar wajen kawai ya hangi ƙur'aninsu a back seat ,tsaki yaja ya kashe motar ya kwaso ƙur'anan yina tafiya yina bubbuɗawa yina tsallake kwatocin yina ƙorafi ,yina shiga gate ɗin makarantar daidai sanda malam Lawal ya ɗaga bulala ya shimfidawa Salima a gadon baya shikuma ya sawo kai
Wani shock yayi a hankali ya fara sanɗa ya sama kan ɗaya daga cikin mashinan daliban ya ajiye ƙur'anan ,ta bayan malam Lawal yazo daidai ya ƙara ɗaga bulalar zai caula mata kawai ya saita ƙeyarsa ya fyalla masa mari Ji kake yauuuuun!!!! Ɗif malam Lawal ya daina gani atake ya fara lingering ,kafin ya dawo hayyacinsa ya haɗa hannuwansa biyu ya makama gefen kunnuwansa mari ɗif ya daina ji sai wani dimmm dayaji kunnuwansa sun ɗauka kamar an cikasu da ruwa ,ji yayi duniyar da ta gurɓata kawai baisan sanda ya yanka ihu ba .
Ɗalibai koda suka ga haka ratatawa da gudu sukayi kowa yayi ajinsu, .....
Da sauri shugaban makarantar da sauran malamai suka firfuto daga abubuwa su "Malam lapiya ,lapiya?"
Jiri ne malam Lawal yaji yina ɗibansa dafa bango Ya shigayi yina shafawa saboda tsaf baya gani ,shikuwa kb ganin hakan sai ya sama kan mashin ɗaya ya haye yinata faman ƙyaƙyacewa da dariya ,Shugaban makarantar a kiɗime yace "Malam lafiya me kayi masa?" Tsuke fuska yayi kamar ba shine me ƙyaƙyacewa da dariyan nan ba ,wanda yasa gabaɗaya malam cikinsu kartawa cikin ciccijewa da hura hanci yace "Marin sa nayi na ɗauke masa gani ko sai akayi yaya?" Murmushin yaƙe shugaban makarantar yayi "Ahh bakomai..." Ya nufi wajen Malam Lawal da nufin ya kamosa ya zaunar dashi ,Kb durkowa yayi daga kan mashin ɗin ,kikaji ƙaran kambas ɗin sa ya bada sautin dimmm! Ai da gudu malaman sukayi cikin ajujuwan ɗalibai ,shikuwa daddagewa yayi ya sake kife malam Lawal da mari a ƙeya ,walllll malam Lawal yaga wani haske ya bayyana masa a ƙwaran ido kafin ya dawo yina gani dishi dishi
"Zaka sake dukanmun ƙanne?" Zubewa yayi akan gwuiwarsa "Don Allah kayi haƙuri masta akasi aka samu "
Sosa ƙeya kb yayi "shege kaji banbancin jahili da me ilimi ,Iyayenmu sun kaimu makarantar boko da na addini kuma munyi ,munsan sassan da In aka daka zai naƙasta mutum ,ya kaji marin da nayi maka a ƙeya bakaji ka daina gani ba?" Jinjina masa kai yayi alamun Eh
Dariya ya fashe dashi "kazalika da na so da wuri ɗaya a jikinka zan zabgawa wannan bahaguwar hannun tawa, Saidai ka buɗe ido ka jika a ƙiyama ,don haka a kiyaye na soke duka a makarantar nan in kunni yaji?..." Da sauri malam Lawal yace gangan jiki ya tsira"
Kaɗa kai yayi yina bubbuɗawa ya fice daga makarantar
Littafin ƳAN ASHAWO Isn't for free Drop your payment via this Account details 7782217014, Mohammad Hassana,Fcmb . Evidence of payment thru 09065990265
Regular group ₦300
VIP 500₦
Special ₦1000
*Garin Naji daɗi Yafi garin Na saba ,Kazalika tafiya da gwaninka Akwai matuƙar daɗi*
Thanks for voting and patronizing,Hrt u all❤️
[7/30, 10:09] أم افنان✍️💞: *ƳAN ASHAWO💅*
_(Romantic story)_
Free page
9️⃣&🔟
Oum Aphnan✍️
*___________________________________*
_Girl wid big liver_
Tahreem daga shigan ta Asibitin ta gane jiɗɗo,amma a hankali ta fara janta da labari don ta tabbatar da hasashenta ,ilai kuwa suna mazaunin cousins ne ,saboda ita Tahreem akwai bibiyan en uwa na cikin gari da jeji ,lanƙwashe ƙafa tayi babu kyara ta fara zayyanewa jiɗɗo Genesis ɗin su ,Sosai jiɗɗo taji ta sama sakeena(nutsuwa) a ranta ,saboda yanda take mata kwatancen rugarsu tana faɗo sunayen iyayenta ɗaya bayan ɗaya zai tabbatar mata da ita ɗin jininta ne...........
Daga wannan ranar kullum Tahreem sai tazo duba jiɗɗo a asibiti ,sosai ta sakar mata jiki take kula da ita baji ba gani abun har yina baiwa kowa mamaki,don tuni ta daina kyaran nazeefa akan rashin kawo mata sababbin yara da batayi ba ,a cewar ta jiɗɗo ita ɗai zata zame mata ɗaya tamkar da goma in Allah ya tarfawa garinsu nono....amma a gefe guda ,lamari ɗaya ne abun dubawa cikin sha'anin jiɗɗo wato urine incontinence. likitoci sun kasa gano dalilin da yasa wannan ɗirkekiyar take fitsarin kwance gashi in ansa mata cathetar sai ta fizge shi wai yina damunta ,bazata ringa yawo da jakan fitsari ba,haka dai jikinta yayi sarai ta daina firgita ta saki jikinta aka basu sallama ,suka taho gidan Tahreem.
****
TUSHE
Bughati club opp. twice Hotels,Gg street Abj.
Darene wajen ƙarfe goma da minti Ashirin ,Tahreem itake tuƙa motarta gefenta jiɗɗo ne sai zare ido take tana waige ² har suka isa gaban club ɗin ta faka motar ta fito jiɗɗo na Binta ƙafa² daka ganta kaga firgitacciya wanda bata saba shiga jama'a ba
Shigar doguwar rigar Atamfa jido tayi an mata ɗaurinta daidai da midi mayafinta ya rufe mata jikinta gabaɗaya ,tana biye da Tahreem da tasha matsu ta riƙe mata jakarta da wayoyinta ,can cikin club ɗin suka sama waje suka zauna ,da sauri ma'aikatan wajen suka zo tambayar su abunda za'a kawo ,saida Tahreem ta yamutsa fuska sannan ta faɗa masa kalar wine ɗin da za'a kawo mata ,sannan tace a kawo ma jiddo black tea.
Itadai jiɗɗo ta tafi kallon yanda duk mutanen wajen ke tikar rawa ,mace da namiji a tare wasu hannunsu da glass din giya ....Wani ɗan lukutin gaye ne ya zo inda suke yina tafe yina ɗan girgiza jiki alamun sautin dake tashi a club ɗin yina kai masa
"Hey" ya ɗaga wa Tahreem hannu ,saida ta masa kallon sama zuwa ƙasa ,sannan ta amsa masa da "Hii" washe baki yayi gabaɗaya sannan ya ce "Like I knw you?" (Kamar na sanki?) Caɓe baki tayi sannan ta ɗage duk kafadunta "Ko?"
Jinjina mata kai yayi alamun tabbatarwa "Ba kece jakadiyar matasa ba?"
Ɗan zancen zuci tayi "mtseww na riƙe muƙamai da yawa amma me yasa duk in za'a ce an Sanni sai ace sanda nike rike da mukamin jakadiyar matasa? This is so annoying" Ɗan showning tayi kamar bakomai a ranta "Ohyeah...yeah it's me" miƙa mata hannu da nufin suyi handshake yayi "Sunana Engnr Isma'il ma'aji,nice meeting you babes ina fata zamu zama Abokai" miƙa hannunta tayi suka gaisa fuskarta a sake "Thank you so much How do you do? I Tahreem...wannan kuma sister ɗita ce sunan ta jido"
Waigawa yayi ya kalli jiɗɗo da take fama da mug ɗin baƙar shayi "Hey sannu ko" washe masa dafaffun haƙoranta tayi "Yawwa hannu itadin er uwata ce da kakana da kakanta uwarsu ɗaya ubansu ɗaya sannan mamanta ..." Katse maganarta Tahreem tayi da sauri ta hanyar ɗauke hankalin Ismail da wata maganar "Ammm engineer kune da ƙasar nan fa ,amma naji ance engineering akwai wuya ina jinjinawa duk wani Engnr tun sanda zan shiga makarantar gaba da sakandire har na samu Admission amma aka tsorata Ni akan course din ,wai maza ne kawai suke shanyewa , sai naje na karanci sociology ....so I'm sociologist also psychologist now"
Ɗan tafa hannu yayi sannan yace "wow woww Ashe ba banzaba kika zama social gaskiya tsarin yanda kike tafiyar da lamarinki ya daɗe yina burgeni " cikin gadara tace "Dole ne ai in birge duk wanda na Zauna dashi na minti one" ɗaga mata gira yayi cikin gasgata maganarta "Oh I see... I see ,zan iya samun " bai ƙarasa maganarsa ba ya miƙa mata wayarsa (kenan yina nufin ta basa Number wayarta)
Ta wutsiyar ido ta ɗan saci kallon wayar ,saidai a take taji wani miyau ya wuce mata maƙoshi da gudu yina neman ƙwareta don haka da sauri ta soma tari ƙwaƙwal. Duk sakamakon ganin irin wayar da ta gani a hannunsa ,wayace ƙirar Goldvish revolution kimanin kudinta yakai $488,150
A ɗan ruɗe jiɗɗo ta miƙa mata ruwa tana ce mata "shori Anty" wani mugun harara ta zabga mata da ya sata shiru da sauri
Gyara natsuwarta tayi da sauri ,kafin ta basa Number da baki yina rubutawa ,itakuma a ranta zancen zuci take "Wannan yayi kama da ɗan fafa ,kuma kamar yina da ƙumbar susa,look like a sticky rich person ,dole I will flirt with him a little bit, in tatsi rabona ,in kuma holoƙo ne, Hmm...."
Ɗan sunkuyawa yayi saitin kunnen tahreem kamar na