Back to novel

Chapter 15 of 20

RUGAR SAJE Farashin Tsira by Nusaiba Ayuba

da zafin rai yace"bazan iya taba wannan najasar ba Mamah, kiyi hakuri amman wllh bazan iya dora hannuna akan Maryam ba, da aure na.....da aurena fa take...."



Kuka ne yake son kwace masa yai saurin barin dakin, da sauri Mamah ta karasa wajen Mairoji ta tallafeta, wayarta ta janyo ta kira Hibbatu kanwarta da daman tana gidan, cikin lokaci kadan ta shigo, ganinsu ahaka ba karamin rudewa tayi ba, da sauri ta dau wayarta ta kira likitansu tamai kwatancen gidan akan lallai yazo yanzo, ita Mamah ma sai yanzu tunanin kiran likita yazo kanta, cikin abin dabaifi muntina ba kuwa yazo, da sauran wasu likitocin mata biyu dan Hibbatu tamai dan takaitaccen bayanin abundayake shirin faruwa.





Kusan awa aka dauka kafin aka samu komai yai normal,nan suka sanar dasu ai cikin ne yai barazanar fita, amman yanzu an samu ya zauna, sai dai za'a kiyaye sosai banda daukar abu mai nauyi da kuma aikin karfi, har sai kicin yai wata hudu zuwa biyar kafinanan yayi kwari, kafin nan kuwa tuni zance ya baza Maryam ba lafiya za tayi bari, Sakeena na kan gaba wajen nuna tashin hankalinta, har da fake tear dinta kuwa, nan dai ta zauna tare dasu Mamah da Ummie dataki matsawa konan da can, suna haka yan daurin aure suka dawo, anan mazan gidan suka san san abundake faruwa, sai dai Mamah bata fadawa kowa musababin abun daya janyo hakan ba, ta dai ce musu Maryam din ta zame ne abandaki.



Malik kam, yana komawa daki, ya zauna bakin gado ya dafe kansa, tunani yake mai ya kaisa aikatawa matarsa abar sonsa haka, ko banza ai tana dauke ne da gudan jinisa, kuma ita din zabin sace, bai kamata ya mata wannan bahagon hukuncin ba, wayarsa ya janyo zai kirata yaji sallama hade da nocking, ajiyewa yayi yaje ya bude, Sakeena ya gani ya matsa mata ta raba ta gefensa ta shige, gefen gadon ya koma ya zauna, itama ta zauna kusa da shi, sai data gama karantarsa ssannan ta dan sassauta murya tace"kaje ka duba Mairoji kuwa?, tana jin jiki fa, kamata yiyi ace kaine yanzu awajenta ba wani ba, kai kana matsayin mijinta amman ace wani can daban yaje yana bata kulawa, hakan aganina bai dace ba, duk dadai dan uwane shi ma, amman ai kafi kowa kusanci da ita."



Kallonta yayi idonsa kam akanta, cikin kaushin murya yace"waye wani din dake wajen nata?, mai yake yi, mai ya kaisa?."



Mirmushi tayi aboye tace "ah'ah, bafa wani bare bane, Ya Saddiqu ne naga yaje sai shige mata yake ita kuma sai kara narke masa take, abun daya kai ya kamata tana yiwa ba wani ba, amman fa ban fada maka dan kaji haushinta ba, kar ka jaza mun ace na hada fada."



Bai bari ta karasa ba ya mike ya fice da sauri, dariya ta sheke da ita sannan tabi bayansa dan bata son kallo ya wuce ta, dai dai ya bude dakin ya sa kai kenan, Mamah ta dagota shi kuma Saddiqu ya na gyara mata zaman filon, ita kuma Mairojin tana kallon Saddiqun ne damai dan murmushi da jinjina kai alamar godiya, kofar ya buga da karfi ya karasa shigowa yana nuna kofar da hannu yana kallon Sddiqun, cikin tsananin bacin rai yace"fita ko kuma wllh afita da gawarka, ke kuma..!"

ya nuna Mairoji da tayi tsuru da ita yace"ki tattara ki koma gidanku, ai nan ba gidanku bane, gidanmu ne ki koma inda kike da gado akula dake akara miki tarbiyya, idan kinyi hankali sai ku neme ni, kai kuma wllh ko ka fita ko na illataka anan wajen inga dan abun uban daya tsaya maka."



Murmushi Saddiqu yayi ya juya ya fita, Mamah kam dan takaici kawai tsawaya tayi tana kallonsa, tana tunanin wannan Malik nata ne ko sauya mata akayi da wani, tsawa ya kuma dakawa Maryam yace"watau ga dan iska ina magana kin tsare ni da ido, nace ki tashi ki bar mana gida tunda bakida gado anan."



Jikinta na rawa ta yunkura zata tashi Mamah ta maidata, cikin muryar da ba yabo ba fallasa tace"koma ki kwanta, matukar na isa dake ban yadda ki taka kafarki ko kofar dakin nan bakinji ni?."



Kai ta gyada tana satar kallon Malik da yake aika mata da muyagun kallo, cikin bacin rai yace "Mamah ke bakiji irin warin da take ba, gaba daya dakin fa wari yake, wllh tun daga bakin kofa nake jin warin da ke tashi ajikinta, pls ki baeta ta tafi kawai, in dan ta nine wllh na yafe ta bana bukatarta arayuwata ko kadan."



Haka ya gama babatunsa Mamah dai bata kulasa ba, sai dan kansa sannan ya juya zai fita tace "idan ka fita ka jamin kofar, kuma idan na kuma ganinka adakin nan, ban yafe maka ba, matukar bani na neme ka ba, kana iya tafiya."



Shi ji yake ma ko ajikinsa , ko tsine masa zatayi bai damu ba indai akan wannan yarinyar ne, haka ya fita yana gunguni, kuka Maryam ta fashe dashi tana kallon Mamah, hararata Mamahn tayi tayi tace "ke ni yimin shiru, sai e dan ya ce baya bukatarki arayuwarsa, ke da kike da manyan yara masu sonki da gaskiya, idan ma sakinki yayi ai ba rarasa manemi zakiyi ba, bana son wannan kukan naki, kullum ina fada miki ki mika lamuranki zuwa ga Allah, inshaAllahu zakiga sakamakon duk wanda aka zalunta."



Da kyar dai ta samu ta rarrashe ta sannan ta fita dan lokacin mata yan zuwa yini sai shigowa suke, haka yinin ranan ya kasan cewa Maryam ba dadi, ta kira wannan ranar da ko wane irins suna, karshe ta lakaba mata ranar yanke farin ciki.



Da yamma tayi aka dauko amarya, anan part din Khausar din zata zauna dan an ware mata falo da bedrum biyu, sai dai kichen ne yake ahade, sai kuma babban falon part din nasu da kowace zata iya zama tayi harkokinta aciki ba tare da takurawa yar uwarta ba.





  *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _29_



Bayan kwana biyu da yin bikin an gama watsewa, kowa ya kama gabansa, zuwa wannan lokacin duk wanda ya kalli Malik sai ya tausaya masa, saboda wata mahaukaciyar rama da yai, gaahi in dai zai zauna shi kadai, to bashida aiki sai na tunani ko kuma shi kadai ajisa yana kananun surutai, a hankali idan aka fahimcesa kamar yana cikin damuwar da babu mai taimaka masa ne, cikin sati biyu duk ya fita hankalinsa, tun Abbah baiyi magana ba sai da ya magantu, haka Mamah sosai hankalinta ya tashi, sai dai bata kulashi amman ta dage sosai da addua.



   Bangaren Mairoji kam, ita tuni ta manta da wani sabani daya shiga tsakaninta da Malik din, neman hanyar da zata ganshi take, dan rabon dasu hadu tun ranar da abun ya faru, sai dai ta gansa daga nesa, yanda  taga yai wawuyar rama, ga kasumba daya tara, shi da ko saje baya ajiyewa yana taruwa yake cireta, ta tausaya masa matuka ita da za'a barta da sun tattara sun koma ina yaso sa sasanta tsakaninsu.





**

Yana zaune kamar ko yaushe, ya buga tagumi Sakeena ta shigo, harta zauna bai sani ba, sai data cire masa tagumin sannan ya kalle ta adan firgice, numfashi ya sauke yana jin wata yar shakkarta, harararsa tayi cikin bada umarni tace,

"Wato kazo ka zauna kowa ya ganka yace ina takura maka ko, salon iskancin daka koya kenan yanzu, salon ana mun wani kallo daman ga waccan matar da ba sona take ba, sai afkin munafurci data hada aka lika min kishiya, dan bakin hali ita bata zauna da kishiya ba ni tasa an hadani da ita dan tsana."

Kallonta yayi adan fusace kamar yana son mata masifa amman bakinsa ya kulle, tsaresa tayi itama da ido tace"me..? karya nayi kome, da tana so na ne?, ai ita bataki yau ka sake ni ba, da zaka wani bini da ido kamar ga wata sa'arsa tana magana."



Kai ya dan sunkuyar yana ji wani tukuki yana taso masa, tashi tayi ta fara hada kaya tace"kana gani ina aiki amman ko ka karba ko?, yayi maka kyau."

Tashi yai jikinsa asanyaye, ya karbi kayan yaci gaba da hada mata, sai daya gama tana kallonsa ranta fes, sannan cikin sanyin murya yace"na gama."

Tsaki tayi tace"to da ka gama hadan nawan, naka wa zai hada maka, kana wani abu kamar karamin yaro, maza ni ka hada kayanka so nake mu bi jirgin yamma zuwa Lagos daga nan mu wuce inda muka fi wayau."



Jikinsa asanyaye ya hada duka kayansa, har wanda ma baya amfani dasu sai datasa ya hada, yana gamawa ya dan kalle ta adan duburburce yace,

"zanje naiwa Abbah da Ya Ahmad sallama, tunda basu san yau zamu koma ba."



Wata uwar ashariya data narko sai daya runtse idonsa, cikin masifa da tsoron karyewar aikinta tace"babu wajen ko wane munafiki da zaka, ina sune masu tirsasaka daman kana yin abunda ransu keso, to wllh baka isa ba babu inda zaka, ka wuce ka shirya kawai mu tafi."



Bai mata musu ba ya nufi bandaki, amman sai ta dakatar dashi, daya fada matama wanka zai , sai cewa tayi ya barshi yayi idan sun sauka Lagos, haka yasa kayansa yana jinsa duk atakure, shi ya dunga jidar kayansu yana kaiwa mota sannan yazo yace mata ya gama, suna fitowa kuwa sukayi kicibus da Khausar, zata shiga wajen Mamah, kallonsu tayi tace.

"ah'ah Malik sai ina kuma, tun dazu naga kana saka kaya amota ko har zaku koma ne?."

Ta maida tambayar kan Sakeena da take jijjiga tana jiran atabata ta sauke, dauke kai yai bata bata amsa ba, shi kuwan Malik satan kallon Sakeenan yayi sannan ya kalli Khausar yadanyi yake yace"matar Yaya, zamu koma ne, kinsan ina da abubuwa da dama acna, ga batun bude kamfani da mukayi hadin gwuiwa da , da Ansar dan tsohon gwamnan jihar Kano, kinga dole ana bukata ta acan ai mun dan kwana biyu."



Tsawa Sakeena ta daka masa da tasa ko Khausar sai data dan razana, kallon mamaki tayi mata, sannan ta kalli Malik da ya sunkui da kai kamar ma jikinsa rawa yake, cikin masifa Sakeena tace,

"In banda barbadanci waya tambayeka, ko abun data tambaya kenan zaka tsaya yi mata wani bayani kamar ance maka ya akayi, nifa wllh wannan salon daka dauko ne bai minba, ehe dole ma kka sake lale, dan bazai sabu ace ko wanne shirgi sai ka fadawa sirrinki ba abunda na ce maka kar wanda yasan da batun amman shi ne dan rashin jin magana kake fada mata kuma bama tambayarka akayi ba, dalla ni wuce muje."



Haka ya wuce ya nufi mota, sai dataga shigarsa sannan ta kalli Khausar data saki baki tana kallon sabon abu, murmushi Sakeenan tayi tace"ina dai wajen uwar mijinki zaki shiga, idan kinje ki fada mata mun wuce, ita da ganin danta kuma maybe sai dai ahoto, eh to zamu iyayin kara, idan wani agidannan ya mutu muzo gaisuwa mu koma, ita kuma wadda.kuka lakaba mai, ki fada mata ta jira takardar sakinta, zata sameta har gida, kuma idan ta hauhu ta nemawa dan nata uba, dan wannan uban yayana ne kadai ba da wata can ba."



Tana gama fada tayi wucewarta wajen mota, ta shiga suka tafi, sosai Khausar ta shiga rudani, da hanzari ta shiga wajen Mamah, a falo ta tarar dasu ita da Ummie da Maryam, zama tayi tana sauke numfashi, kafin wasu irin kwalla masu dumi suka sauko mata, da hanzari Mamah take tambayarta meya faru, kukan ta fashe dashi, duk sun rude sai tambayarta suke, ita Maryam har tana duba jikin Sultana ko wani abu ne ya samu yarinyar, sai da tayi kuka mai isarta sannan ta kalli Mamah tace,

"Dan Allah Mamah mu tashi tsaye akan mazan gidan nan, ban san wacce annoba ce ta kunno mana kai ba, Mamah muna cikin tsaka mai wuya, tun ranar da aka kawo Laura ban kuma ganin idon Ahmad ba har yau, sai dai naji fitarsa da dawowarsa, idan naje bangarensa kuma ba za'a buden ba balle na shiga na gansa, ga Malik shi kuma yanzu matarsa tasashi agaba wai sun tafi, Mamah wannan wacce irin kaddara ce tayi mana sallama acikin gidan nan, ya zamuyi?."

Kuka ta kuma fashewa dashi, daga ji kasan daga kasan zuciyarta yake, kuma abun na matukar damunta, ajiyar zuciya Mamah ta sauke tana dan satar kallon Mairoji, sannan ta kalli khausar din tace,

"To kuma meye abun kuka anan Fateema, ki kwantar da hankalinki, duk rintsi duk tsiya da tsiyatsiya rabo ya gifta tasakaninki da Ahmad, ko yaki ko yaso dole dai ku nashi ne idan ma bai kula dake ba, dole ne ya kula da yarinyarsa, kuma komai nisan jifa dole kasa dawo, yanda kika zo kina kukan na, insha Allahu wata rana zaki zo kina dariya, da farin cikin ki dage da addua, kinji karki sa abun aranki, kinga shayarwa kike, dan Allah kar ki dorawa kanki damuwa da tunani kinji yarinyata, ki bar kowa da Allah, shi ne kadai zai.miki magani ya kawo mana mafuta akan lamarin."



Da kalamai masu dadi da nasiha ta samu ta kwantarwa da Khausar dun hankali, sai dai duk yanda suka so ayi zanyi Malik ki tayi, haka suka hakura, sukaci gaba da shirarsu, sai dai Maryam bata tofa ko uffan sai binsu kawai take da ido.





***

Bayan wata uku,cikin Mairoji ya fito sosai, sai dai yayi wani irin girma, watansa shida, amman da ka ganta zaka zzata ta shiga watan haihuwarta ne, kulawa kam tana samu daga ko wanne bangare, duk sati Daddyn Yusra, wato babanta yana zuwa kawo mata rubutu duk ran juma'a, ga malam saje da shima ko yaushe yan mata rubutun baki, domin duk wanda yaga yanda cikin yai girma sai ya tanka, Goggoji taso ta zauna bangarenta, amman Mamah taki dan itama Goggojin tana bukatar mai kula da ita, dan ta manyanta sosai ga matsalar kafa da take fama da ita.

Uncle Malik ya samu aikin koyarwa da wata makaranta akasar Egypt ta hanyar wani malamin makarantar abokinsa ne tare suka dau karatu asaudiyya dashi , cikin abun da baifi wata ba ya gama komai na tafiya, hatta karatun yaransa ma can zai koma, haka ma Mairoji ya karba mata transfer zuwa can, ranar wata talata kuwa suka daga, sai dai banda Mairoji da sai ta haihu tukun zataje ta fara nata.





***

Yana kishingide afalonsa yana murza tabarsa acikin wata yar farar takarda, wayarsa dake gefe tayi kara, dagawa yayi ya saka ta a amsa kuwwa, tare da yin sallama, adaya bangaren aka amsa sannan ya fara magana,

"Ranka ya dade, abubuwa fa sai cabewa suke, bawan Allahn nan abun yamai yawa dan yanzu takai ko wajen buga kwallo bai fiya zuwa ba sai an taki babbar sa'a, gashi yanzu wannan abokin nasa ma ya dawo gidan da zama, wllh abun ya kazanta, yallabai ina tausayawa halin da Malik yake ciki, yana cikin jarrabawa."



Iska ya fesar asannan cikin nitsattsiyar murya yace"Gimba, kuna bashi ruwan rubutun nan kuwa?."



"Eh ranka ya dade, har kamfanin da suke buga masa ruwa naje na samu shugaban wajen na masa bayanin yanda muke son abun ya kasance, to da yake ma na sakar masa kudi sosai, shi ne muke kai rubutun saisu hada da ruwan su buga masa nasa daban akawo masa, kuma na tabbata yana sha, tunda babu wanda zai gane ba normal ruwa bane."

Kai ya gyada kamar yana ganisa yace"yayi kuci gaba da kokarinku anan, nima zan sabunta nawa aikin, nida nayi wayo gari gari, jeji jeji babu irin kalar asirin da ban sani, da kuma magungunan karyawa, tun ran daurin auren dan uwansa na gane an jefesa da bakin sihiri, amatsayina na dan uwansa, kuma wanda ya auremin wadda nafnafiso arayuwa, zan taimaka masa, badan shiba sai dan Allah da kuma darajar Maryam, ku ci gaba da aikinku , kuma ka kuma samin ido akan wannan Khabir Khan din."



Daga can bangare ya amsa da "an gama ranka ya dade, Allah ya bada nasara".

Amsawa yai da ameen sannan ya kashe wayar ya fada wani nazari, badan kar abun ya zamo tashin hankali ba, da zai samu Hajja Yargana da zancen, akan su karya asirin da suka sa akawa Malik din, shi kuma zai rufa musu asiri, amman zai kyale su ne har sanda asirin zai karye da kansa, sannan sai su gane cewa yana sane da duk wani kullinsu, idan ta kama ya toni asirin ma sai ya tona.





**

" Gid'ad'o, mai kake nufi dani ne, me hoton Ummie yake yi awayarka, kar dai kace min amanata kake ci?."



Kallon wayarsa dake hannunta yayi ya dauke kai yana Allah wadai da wannan halin a Salma, sai shegen bincike awaya wai ita lallai bata son ganin hotunan yan mata awayarsa, zuwa yai ya karbe sannan ya koma ya zauna ya ce,

"Kina da matsala ne da ita?, naga yar uwata ce, me dan kinga hotonta awayata, laifi ne?."



Ranta a banmce tace"ai wllh ko ka goge sa, ko na fasa wayar, dan yar uwarka ce, ai naga akwai sha'awa atsakaninku, tunda dai ba muharraman juna bane, kawai nidai ka goge wllh ko kuma ka shiyi tashin hanklia agidannan kenan."



Dariya yasa, yana kallonta yace"to fa, sabon fi'ili tonwai idan ma neman aurenta nake meye naki aciki, nifa mijin mata hudu ne, kuma inada wadatata ina