Chapter 8 of 14

MATAR HARIJI Haramtacciyar Soyayya By Maman Teddy

da wani likitan gargajiya, gdy yayi masa ya rakashi ya dawo suka shata filin dambe akan itafa bazatasha maganin bature ba saidai yaje rugarsu gurin Boka Bawa ya karbo Mata magani.

Kai abufa tun anayin na hankali har abu ya gagari kwandila ta rikice masa babu abinda takeyi sai kuka da surutai tana wani mimmiqewa, shikam wannan rana yayi danasanin tabata da yasan haka zata zame masa dama bai fara ba ya qyaleta yayita kallonta.



Ganin dai abin bana hankali bane yasashi fara yimata addu'a yana tofa mata tanata buge bugenta ya riqeta gam a jikinsa sun dauki tsayin lkc a haka sannan yaji ta fara keta gumi tana sauke numfashi ya kwantar da ita ya qara qarfin A.C ya zauna ya zuba Mata ido yana kallon kyawun surarta mace har mace sai gidadanci.

A ransa yana cewa wannan da ace kuma shidin wani cikakken namiji ne qila sai tayi sati tana aljanu, shima kwanciya yayi a gefenta ya rungumeta tsam a jikinsa da haka bacci ya daukesu, washegari lfy Lau suka tashi sai zazzabin dabai saukaba da kuma wani mugun tsoronsa da takeji.



Karanta Littafin>>> Macijine Shi Page 39-40 Hausa Novel



Excuse ya bayar a gurin aiki ya tsaya kula da ita takuwa narke ko miqewa yace tayi sai tayita kuka wai ita ciwo ya faffarkata ya yayyagata🤣

Kayy Lameer yana ganin tujara ko tabata bai isa yayiba saita rushe da kuka haka ya rinqa binta.

Kwanansu biyu a Lagos ya daukar Mata malama Salmah babbar macece mijinta ya rasu anan gaban quarters dinsu kadan to tanada ilimi sosai dan koyarwa ma take a wata secondary itace zata zama malamarta, duk wani Abu da yasan zaa buqata ya siya suka fara karatun addini dagashi har Malama Salma sunsha mamakin yanda ta iya tundaga izu daya har zuwa izu biyar duk wata aya da aka datso Mata saita cafe.



Gata Allah yayi Mata baiwar saurin fahimta ko a na bokon ma da wuri take gane abubuwa, bayan malamar ta gama ma ta tafi zama sukayi dashi yana qara koya mata.

Cikin abinda bai wucce wata gudaba ta iya rubutun hausa da karantawa duk abinda aka rubuta zata karanta, nan suka koma koya Mata turanci shima babu wata wahala ta fara iyawa ga karatun addinin shima shiga yake dake fresh brain dinta take gata gifted aikuwa yanajin dadin hakan sosai.



Gwanin dadi suke tafiyar da rayuwarsu da malamarta ta dauketa tamkar yarta ko girkin ma dayace zai kaita chattering school ta koya cewa tayi ya bari zatake koya Mata, idan suka gama karatun boko sai su shiga kitchen suyi girki kala daya da lemo shima don kada su cika ta kasa ganewa.

Duk bayan wata guda yake zuwa kano yayi sati ya dawo cikin wata ukun abubuwa da yawa sun faru Jiddoh ta fara wayewa ta gegije ta fara zama babbar mace saboda bayayi mata kiwon mugunta kuma bai qara yunqurin kusantarta ba ko wasannin ma da yake dan koya Mata har yanzu kuka takeyi tanace masa iskanci ne.



Daqyar da taimakon Malamarta ta daina ce masa Kado ta koma kiransa da babe aikuwa tunda babe ta zauna a gabanta a gaban uban kowa kiransa takeyi da babe shima yace mata babe.

A bangaren Mubaraka ma Abu da dama sun faru harga Allah ita mantawa ma takeyi da cewar mijinta yanada wata Matar bayan ita saidai idan farkanta daya kwallafa rai akan Baben yayan nasa yayi Mata mgn kasancewar shi yakan kirashi haka video call to wani lkcn idan yana gda zanganshi rungume da Hauwah din ko kuma yaji yana Kiran babe.



Hakance tasa kullum yake qara kwadaituwa da amaryar yayan nasa yakeso shima yaji abinda yayan nasa yakeji a jikinta.

Itakuwa Jiddoh harkan gabanta kawai takeyi Koda ya siya mata waya ma babbar gaske bata wani damu da itaba garama idan Zaliha qanwarsa ta kirata takan dade suna waya kasancewar bayan Lameer din da Alh Ali mahaifinsa sai Zalihan sune kadai suke sonta sauran duk yan partyn Mubaraka ne garama babban yanansu Hamza shikam babu ruwansa duk da Mubaraka ta kasance qanwar Matarsa.



Wata dawowa da zaiyi lkcn sunada wata bakwai da aure yace ta shirya su tafi tare aikuwa tayita murna harda kissing dinsa kasancewar malamarta ta koya mata kissa da kisisina sinka sinka Lameer yanashan shagwaba a gurinta kaya kuwa batasa manya saidai idan fita zasuyi.

Ranar juma'a bayan ya tashi daga aiki suka shirya suka tafi qauyanci da gidadanci duk babu sai wani yauqi takeyi tana narkewa a jikinsa shikuma sai tarairayarta yakeyi yana biye mata ko a mota drivern yasha kallo yanda suketa rungumar juna suna tsotse bakin junansu yana wani shafeta abin kamar a amurka, haka da suka hau jirgi ma ta lafe a jikinsa har yanzu mugun tsoron hawa jirgi takeyi shi kuwa ko a jikinsa kodan aikinsa ne tuqa jirgin oho.



Tun kafin su sauka kasancewar shigowar dare sukayi ya turawa Muneef saqon zuwansu yace yazo ya daukesa a airport, lkcn suna tare da Mubaraka suna qullah yanda zasuyi su dauke hankalin Lameer din dagakan cikin Mubaraka daya shiga wata na tara.

Kuka takeyi masa tana fada masa ta lura kamar Lameer bayason cikin nata kamar yanda yaso na Fadwah nan take bashi lbrn yanda sukayi tace “ranar dana fada masa inada ciki wata hudu a kwance yake amma zabura yayi ya miqe yace “yaushe na samu ciki da har yakai wata hudu?



Saida na tubure masa na rinqa kuka nace masa ashe duk zaman da mukeyi zargina yakeyi, to ganin na tashi hankalina Ina Shirin kiran Hajiya na fada Mata yasashi cewa shifa ba wani abu yaje zargi ba kawai dai mamaki yayi, to da qarya da qarairayi nace masa ai kwanciya yayi yanzu shine ya tashi"

Sauke numfashi Muneef yayi yace “dadina dake kinada kwanya sai ki tashi ki gyara gashinan isowa yanzu ya turomin saqon naje na daukosa a airport" a tsorace ta dafe qirji tace “na shiga uku yanzu jin dadina zai yanke kai nifa yanzu ko sha'awarsa banayi Allah"



Tafawa sukayi ya qifta mata ido yace “karki wani damu muna jorner" da haka ya fice itakuma ta tashi ta fara dauke duk wani abu dazai iya bashi damar gane wani abu, saida ta gama komai sannan ta shiga wanka ta fito ta zauna ta sheqa kwalliyarta ta fito parlourn ta harde.



Download>>> Kufan Wuta Hausa Novel By Safiya Huguma



____________Ya dauki kamar 30 minutes sannan jirginsu ya sauka mutane suka fara fitowa yana tsaye yana kallon masu saukowar can ya hango yayan nashi riqe da hannun wata balarabiyar yarinya yayi tawassali ga ubangijin daya halicci wannan kyakkyawar baiwa tasa, karkatar dakai yayi ya zuba musu ido shima Lameer din tunda ya hangishi ya lura da inda hankalin qanin nasa yafi karkata.

Nan danan wani mugun kishi ya taso masa ya janyota jikinsa hakan da yayi ya tabbatarwa da Muneef cewa Hauwah ce.

Numfashi yaja ya sauke ya zuba musu ido sunyi wani fresh dasu ba qaramin dacewa sukayi da juna ba kamar dama domin junansu aka haliccesu ga wani qara narkewa da takeyi a jikinsa tana shigewa shikuma sai biye Mata yakeyi.



Nandanan Muneef yaji wani shauqi ya shigeshi na ace shine take yiwa haka ba wannan rabin mutum din mijin nata ba, har suka iso baisani ba saida Lameer din ya mareshi yace “ubanme kake kallo ne?" Firgigit yayi ya dawo nutsuwarsa yace “oh sorry bansan kun iso ashe da gdan kake tafe gabadaya"

Murmushi yayi ya kalleta yace “kin ganeshi?" Yatsina fuska tayi kamar taga kashi haka kawai takejin haushinsa da tsanarsa tun ranar da sukaje neman aurenta taga ya kafawa nononta ido, girgiza kai tayi tace da cewa “Notthing"🤣



Sakin baki Muneef yayi shikuwa gogan ko a jikinsa yayi kissing dan qaramin bakinta yace “ok muje gida nayi miki wanka ki huta sai nayi miki bayaninsa Amma ai kin gane Zaliha ko?"

Murmushi tayi wani isasshe ta sake kwanciya a jikinsa daidai lkcn da suke zama a mota tace masa “tamace idan muka dawo zatayimin gyaran amare zata tsumani wai meye tsumi babe ni bangane hausarba?" Kallonta yayi da sauri yace “aa kada ki sake kisha tsumin nan zai iya zame mana matsala kinji?"



Turo baki gaba tayi tace “aa wlh nikam sai nasha tsumi ai magani ne nasan bai wucce maganin rana da basir ba" ya lura wauta a jinin Hauwah take shiyasa yayi mata Shiru ya qyaleta daga kan da zaiyi yaga Muneef ya saita mirrow yana qare musu kallo ya kuwa daka masa tsawa yace.

“Ka juya mirrow din nan bansan sa ido" da sauri ya juyashi yaci gaba da tuqinsa zuciyarsa na karanta masa wasiqar jaki har suka isa gidan yayi parking ya fito ya bude musu qofar suka fito ta kalleshi sheqeqe ta kawar dakai ya cije lebe yana tuno sanda yaganta a rugarsu kamar wata mahaukaciya amma yanzu yayansa ya wayar da ita iskancinta da wulaqancinta takansa ya biyo lallai kuwa sai yayi maganinta daga ita har mijin nata da yake daure mata gindi.



Kafin ya gama wannan tunanin sun bude qofar parlourn ya juyo yace dashi “ka debo kayan nan ka shigo dasu ka hauro dasu bangaren babe" bai iya cewa komai ba saboda baqin ciki suka shiga parlourn Mubaraka dake zaune tana jiran dawowarsa ta miqe da saurinta zata nufeshi wani mulmulelen abu yazo ya tokare mata qahon zuciya lkcn da tayi arba da Hauwah dake ta zuba mata murmushi tayi saurin daukar Fadwah data nufosu da gudu tana kiran “Dad yoyoyo" ta fara juyawa da ita tana dariya itama yarinyar tanayi suna hajijiya.



Tsayawa zatayi jiri ya debesu suka kuwayi baya luuuuuu zasu fadi yayi saurin taresu suka fada jikinsa ta rungumeshi sosai da hannunta daya dayan kuma tana rungume da Fadwah tace “pls help me Babe jiri nakeji kaini dakina" ai kafin ta rufe bakinta ya hadasu ita da yarinyar ya dagasu cak yayi sama dasu sunata dariya ita da Fadwah shima yana tayasu saboda sabon abune a gurinsa ganin yartasa cikin farin ciki haka shi zai iya cewa tunda yake Bai taba ganin Fadwah tana dariya irinta yau ba.

Daga Mubaraka har Muneef da yake shigowa sakin baki sukayi suka zubawa sarautar Allah ido shikam kusan akwatin hannunsa subucewa ya kusayi saboda mamakin yayan nasa “wai dama haka Yaya Lameer yasan darajar soyayya?"



Karanta Littafin >>> Macizai ne Page 1-10 Hausa Novel



Ya tambayi kansa tare da kallon Mubaraka data zube a qasa ta dora hannu aka zata rusa ihu, saukowar Lameer dince tasa Muneef saita nutsuwarshi ya kalleshi yace “ka kaimata kayanta sama"

Kamar Mai jiran umarni ya nufi saman ya bude qofar ya shiga suna baje a tsakiyar parlourn ta fuzge dankwalin da tayi rolling dashi ta ajiye a gefe suna after momy ita da Fadwah.

Ajiye akwatin yayi ya kwantar da kansa jiki molu din qofar parlourn ya zuba mata ido, jin kamar ana kallonta ne yasata dagowa itama Fadwah ta dago aikuwa sai yarinyar ta rushe da kuka tana shigewa jikinta ta miqe da sauri cikin masifa tace “dallah malam ubanme ka tsaya kana kallo anan ka wani kafemu da ido saikace maye harka tsoratamin yarinya aikin banza aikin wofi to wlh yau yata bazata kwana gurin waccen matarba a gurina zata kwana kuma ko ciwon kai naga tayi kaima ka kuka da kanka stupid kawai"🤔



_Hmmmm Jiddoh masifa Jiddoh bala'i Muneef dai jininku yasha bambam da Jiddoh_😆


Lameer dake shigowa ya tsaya ya zuba musu ido tace “yawwa babe wlh kajawa wannan wawan qanin naka kunne ya fita daga harkata banason gulma da munafurci yazo ya wani kafeni da ido dubi yanda ya tsoratamin yarinya nifa banason shisshigi wlh rashin mutum babu ruwana ni"

Figar Fadwah tayi taja uban tsaki tayi shigewarta dakinta ta ajiyeta a saman gado tace “aikin banza mutum sai shegen sa ido" wasansu sukaci gaba dayi.

Duban Muneef Lameer yayi yace “meye ya hadoku da itane?" Wani takaici ya hadiye yace “nima ban sani ba wlh"



Murmushi yayi yace “kayi hqr kasan yarinya ce" wani nunkin takaici muneef yaji ya taso masa wai wannan yar mitsitsiyar yarinyar data waye a gabansa itace take caccaba masa mgn saboda tasamu daurin gindi gurin mijinta bai Isa yace komai ba hakanan ya juya ya nufi upstairs din.

Koda ya sauka bai tsaya ya saurari Mubaraka da ta hade kai da gwiwa taketa sharbar kuka ba yayi ficewarsa daga gdan saboda tafasar da zuciyarsa takeyi, tanaganin ya fito ta sake rushewa da tana dafe inda Lameer ya mareta saboda kawai tace saidai yabar gidan da Hauwah bazata iya ganin wannan iskancin nataba.



Download>>> Dr. Bobby Complete Novel Document


Ta jima a zaune a gurin komai ya rikice mata daqyar ta tashi ta shiga dakinta ta cire kayanta ta kwanta tanata rera kukanta, kiran wayarta yasata tashi zaune daqyar ta daga tana ganin sunan Muneef ta kara a kunnenta yace “yarinyar nan taci uwar rashin mutunci waini tacewa wawa a gaban yaya amma bai iya cewa komai ba harma tana cemin zatayimin rashin mutunci wai nine maye kuma Yaya yana kallo qarshe ma dariya yayi yacemin nayi hqr yarinyace"

Haɗiye kukanta tayi tace “nifa dukana yayi abinda Bai taba yiminba mari har uku saboda na zageta nace Mata qazama kucaka baqauyiya" hawaye ta share tace “wlh bantaba tunanin Lameer yanada zafi haka ba har cemin yayi indai bazan zauna da matarsa ba saidai ni nabar masa gdansa wai baitaba farin ciki da aurena ba kullum baqin ciki nake qunsa masa"



Haka suka rinqa gulmarsu daga qarshe suka fara video sex saida suka gamsar da junansu.

Tana shirin ajiye wayar ya bude qofar ya shigo ya zuba mata ido tube haihuwar uwarta tayi saurin rufe wayar ta turata cikin shirginta, nazarinta yakeyi sosai yana mamakin yanayin daya tarar da ita a ciki juyawa yayi yace “idan kin gama abinda kikeyi ki kawomin coffee dakina"

Batace masa qalaba ya juya ya fice ya shiga dakinsa ya shiga wanka ya kwanta yana danne²nsa da wayarsa.



Ta jima kafin ta shigo cikin shirinta na bacci dauke da qaramin set na coffee ta ajiye masa a saman table din ta zauna ta zuba masa ido ko kallonta baiyi ba ya ya miqe ta zuba coffee din a cup ya dauka har yakai bakinsa ya kurba ya zuba mata ido yana nazarinta gabadaya batada walwala tasa kishi a ranta duk ta zuge.

Tasowa yayi ya zauna kusa da ita ya shafa cikinta yace “ya bby na?" Haɗiye wani yawu tayi cike da fargaba tace “la...lafiy....." Kukane ya qwace mata ya kalleta yayi murmushi yace “kin dorawa kanki kishin babe aranki ita batama san kinayi ba bata damu dakeba kin damu da ita meye yasane?"



Kuka ta sake rushewa dashi tace “marina fah kayi saboda ita kaje ka daukomin yata Lameer ban yarda da zamanta a gurin makirar yarinyar nan b..."

Saurin dakatar da ita yayi yace “karki shiga tsakanin yata da matata itama uwarta ce kulawar da zata samu a gurinta bazata samu irinta a gurinki ba saboda haka ki tsaya a matsayinki keba abin alfaharine a gurinki ba ta kama yarki ta riqe miki kullum Babe batada mgnr data wucce Fadwah nasan ba saboda kowa ta baro makarantarta ta biyoni Kano ba sai saboda Fadwah"



Tabe baki tayi tace “aidai nice na haifi abata ba uwar wani ta haifamin ba saboda haka dole abani abata wlh" miqewa tayi zata fita yabita da ido harta fice ya koma ya kwanta don yasan halin Hauwah duk bala'inta tafita.

Haurawa tayi cikin saa kuwa ta tarar da qofar a bude ta shiga parlourn ta zubawa parlourn ido abinda tunda take dashi bai tabayi musu ba shi tagani a parlourn manyan hotunansu shida Hauwah batasan sanda ta dauki cup ta jefi hoton dashi ba fuuuuuu ta nufi qofar dakin ta bude suna kwance tana rungume da Fadwah suna baccinsu cikin kwanciyar hankali sanye da baqar yalolowar rigar bacci ta baje gashinta a saman pillow.



Zuba mata ido tayi ko ita da take mace saida taji wani yarrr a jikinta balle kuma namiji, matsawa tayi tasa hannu zata janye Fadwah tayi saurin qanqameta ta fara shure² da qafa tace “nifa ka qyaleni nace ka tafi gurin matarka bazakazo ka dameni ba na gaji"

Fincikarta tayi da qarfi tace “ba tsinnanen mijin naki bane uwace tazo karbar yarta idan ba tsohon bafulacce ne ko tsohuwa me tallan nono da fura ta haifamin ba abani yata...." Ai bata gama rufe bakinta ba taji an shaqeta ta suka kama kokawa kafin kici wane wannan Jiddoh ta hada Mubaraka da bango ta hau kirbarta kamar Allah ya aikota babu kunya Mubaraka da taji wuya ta kama zunduma ihu.



Ihun ya rinqa jiyowa sama sama ya tashi ya fito da sauri ya kasa kunnensa ya jiyo muryar Mubaraka ce taketa zunduma ihu tana neman dauki da gudu ya nufi bangaren Hauwah yyana shiga yatarar da Hauwah tanata nadarta duk ta yaqushe mata fuska da faratanta.

Da sauri ya matsa ya janye Hauwah daga kanta yace “ya salam Hauwah meye hakan me kikeson yi bakiga abinda kikayi mata ba bakida hankali ashe Zaki kama dukan me tsohon ciki...."



Download>>> Attajiri Ko Almajiri Complete Novel Document



Rushewa tayi da kuka ta zame daga jikinsa ya matsa ya daga Mubaraka takaici kamar ya kasheshi wai duk girmanta ta tsaya Hauwah ta yimata wannan mugun dukan ko kunya babu sai kuka takeyi, takaicine yasashi daka mata tsawa yace “dallah malama fice mata daga daki godai godai dake ki tsaya wannan yarinyar ta kama dukanki kina ihu har masu gadi sunajinki don abin kunya"

Miqewa tayi ta matsa zata dauki Fadwah Hauwah tayi saurin miqewa ta dauke yarinyar tace “wlh bakeba ko ubanta bai Isa ya rabani da itaba a yau indai irin wannan yarinyar ce zakiyimin gori akanta ai nima macece saurin me kikeyi abinci ne inaci saboda haka kowanne lkc nima zan iya haihuwa ko babe?"



Harararta yayi ya nunawa Mubaraka hanya yace “fita muje kekuma bata yarta" qanqame Fadwah tayi ta dauki zani ta goyata tana kuka tace “wlh bazan bayar da itaba nima sai kayimin alqawarin zakayimin ciki na haifi nawa a daina yimin gori gashinan saboda bakasona ka tsaneni ita har kakuma bata wani babyn amma ni kaqi bani abinda zanci na samu ciki"🤔

Wani gumine ya karyo masa ya kalli Mubaraka da take tsaye qiqam yace “muje Mmn Fadwah ke kina da hankali wannan kiyi mata uzuri yarinya ce..." Tsalle tayi ta dire a gefe tace “tabdi wai yarinya ai wlh ko digon maniyyi ce saita