Follow us on social media

Showing 45001 words to 48000 words out of 69924 words

Chapter 16 - Kurman Baki Writing Complete Hausa Novel by Safiyya Abdullahi Huguma


ya gaji

"Ki shiga ki gyaramin dakin nan" daga kai tayi ta kalli hajiyayye

"Don Allah qarasa ladanki mana 'yar hajiyayye" ta fada tana karyar da murya alamun lallashi.
Kai hajiyayye ta daga suka hada ido da saleem saita sunkuyar da kai. Bai dauka haukan Zainab
yakai har haka ba da zata aika masa bazawara gyaran dakinsa. Wani kallo ya jefeta da shi ya
saka kai kawai ya fita a sashen.
Karfe goma na dare ta shiga bedroom dinsa, idanunta a kanshi yana zaune daga gefan

gadonsa yana dan duba waya sama sama,shigowarta sai ya kammala abinda yakeyi din ya
ajjiye wayar. Idonsa yadan lumshe saboda yadda yakeji yana dan sara masa,a hakan maganin
da ruqayyan ta bashi ya sassauta akan lokacin da ya shigo gidan,sai ya maida bayansa yadan
jingina da gadon bayan ya zame kadan ya kwanta a rabin gadon bayansa. Lokaci lokaci yana
karantarta sanda take shige da ficenta abunta,ko sau daya bata nuna ta fahimci wani rashin
lafiya tattare da shi ba,duk da ko abinci ma kadan yaci don ruqayya yau bata samu zuwa cin
abincin ba,to shi dinma bakinsa ba taste shi yasa bai samu ci da yawa ba,kota wannan
bangaren a nasa ganin ya kamata ta fahimci akwai abinda yake faruwa amma hakan bai samu
ba. Ita kawai sabgar gabanta take,sauyawar miji ta kowacce siga bata daukeshi wani abu da
za'a bawa kulawa ba.

Ta nata bangaren Idanunta a kansa jifa jifa tana satar kallonsa,ranta da zuciyarta ba
abinda suke raya mata illa sauyawarsa na da nasaba da son bijire ma buqatarta,ita kuma taci
alwashin ba zata lamunci a danne mata haqqi ba,ire iren wadan nan abubuwan ma qila suna
daya daga cikin sanadin da ya sanya ruqayya ta rigata samun wani cikin.
Gadon ta iso ta zauna daga bayansa,zuwa sannan yaja blanket ya rufe har kafadarsa
saboda sanyi sanyi da yakeji na alamun ragowar zazzabin jikinsa bai tafi ba

"Ina da buqata" ta fada sankankan kamar me bada labari. Ya dade da sabawa da wannan
halayyar tata,sam bata da wani salon nunawa me gida buqata data wuce wannan

"Banajin dadi yau,nasha magani ina buqatar na huta" wani abune yazo yayi mata tsaye a wuya.
Ji take zuciyarta kamar zata fashe

"Eh,ai dama na fuskanci take takenka,to ko baka da lafiya nidai haqqina nake da buqata"
waiwayawa yayi kadan ya dubeta da kyau

"Kizo ki qwata idan kina iyawa" ya fadi cikin matuqar maqurar jin haushi. Mutum kamar
dabba,ace ko da yaushe shi kam baisan dai dai da ba dai dai ba,yana takaicin yadda sam
zainab bata gane lafiyarsa da lalurarsa indai ba kwanciya yayi magashiyyan ba,koda yaushe
tata buqatar ce s gaban tasa.
Bai gama wannan tunanin ba sautin kukanta ya karade masa kunnuwa,cikin muryar
kuka take cewa

"Ai dama na sani,koda baka fadi haka ba komai ya fito a aikace,ni nasan dama da gayya ka
yiwa ruqayya ciki ni baka yimin ba,to nima ciki nake da buqata haihuwa nakeso,banda ma
rashin adalci ni da nake gyaran nan aini yafi cancanta ace kafi maqalewa,ni ya dace ace ina da
ciki,amna saboda anqi Allah anqi ma'aiki sai gashi me ciwo daban me shan magani daban,Allah
zai saka min" tana kaiwa qarshe tana sauka daga gadon.

Wani dadi yaji yana ratsashi bayan tayi zuciya ta fita a dakin,ko banza zai samu yayi

bacci cikin salama,don haka ya sauko a nutse ya murza key ya rufe dakin ya dawo gadonsa
yayi kwanciyarsa,idanunsa a rufe amma cikin zuciyarsa yana wassafa irin kulawar da zai samu
inda ace kwanan ruqayya ne.

*******A harzuqe ta tashi washegari,don ko dakin bata leqa ba bare ta gaidashi. Abunda ya sake
dugunzumata kayan da tayi order tace tanaso da sunan kayan sallan yara da nata sun
iso,saidai kuma babu kudin da zata biya ta karba don duk sun tafi. Ita daya ta dinga qullawa
tana kwancewa,tasan tabbas dole kafin saleem din ya wuce umra zai nema ganin kayan
kowa,ita kuwa abun kunya ne ruqayya ta fiddo nasu ita ace ba abinda ta da nata sunbi ruwa.

Sai wajejen sha biyun rana ta shiga a tsaitsaye ta gaidashi,ta samu ya fito a wanka ma
yana shiryawa,gefe guda kwanukan abincin data aika haneefa takai masa ne na safe,da alama
ko tabasu baiyi ba bare yaci abinda yake ciki. Zuwa azahar ya fito da shirin fita ya ajjiye mata
kudin cefane ya wuce.
Qaramin tsaki taja sanda yake ficewa,ta dauki kudin tana juyasu sannan ta ajjiye.
Daidai sannan kira ya shigo wayarta.

Kiran raliya ne,abinda ya sanyata nutsuwa kenan ta kuma amsa kiran ba bata lokaci.

Qasa qasa takejin muryar raliyar,don sallamarta ma kaman a jigace take

"Me ya sameki ne raliya?,bana jinki sosai"

"Hala bakisha magungunan gurin basira ba?" Raliyan ta tambayeta tana numfarfashi

"Niko nasha don jiya ma kwanan asibiti nayi maimakon kwanan turaka"

"Madalla,mun samu qarin shaida,ashe matar nan bugaggiyar macuciya ce?,kin ganmu yanzu
haka gidanta muka nufa, billahillazi saita fito mana da kudadenmu,ashe ita ke hada abinta a
gida da duk abinda taga dama"

"Kan uba,lallai biri yayi kama da mutum,jiya da qyar na qwaci kaina raliya....."

"Ai ba'a bori da sanyin jiki,ki fito kawai mu hadu mu wuce gidanta,saita fito mana da kudinmu"

"Yanzu kuwa,mu zata gwadawa shegantaka?" Ta fada tana katse wayar. Tsam ta miqe,ta danyi
tunanin wacce qarya zata yiwa saleem ya aminta da fitarta?,don tasan ko giyar wake tasha bata
isa ta cewa saleem wai kudi maganin kayan matanta zata amso ba.

Lokaci ta duba,wata zuciyar ta gaya mata har taje ta dawo ba lallai saleem ya dawo
ba,tunda idan ya fita bai dawowa sai magarib,ita kuwa me zata zauna ma tayi har magariba.
Idan tayi wuta takai yamma,don ruwa ruwa zata zubawa basira rashin mutunci ta bata kudinta

ta wuce,ta samu ta sissiya wasu kayan da zata nunawa saleem.

"Umma ina zaki?" Haneefa da tayi tsaye a gabanta ta zuba mata ido tana kallonta sanda take
gyara zaman hijabin wuyanta ta fada

"Ku zauna keda.khalil,ko farfajiyar gidannan bance ku fita ba,yanzu zanje na dawo" tura baki
gaba yarinyar ta fara yi tana qunquni har uwar ta fice daga gidan.

Bata ma iya isa gidan raliya ba ta tsaya daga titi yayi mata waya,ba jimawa sai ga
raliyan tana tafiya iska na kadata,ta zabge lokaci daya da alama taji jiki itama yadda ya kamata.

Ba wanda ya iya magana a cikinsu don kowa idonsa ya gane masa,sai me napep kawai
da raliya ta tsare musu, raliyan ce ta bashi kwatance sannan suka hau tana daukan wayarta tayi
kira ta kara a kunne

"Rabi gamu nan akan hanya.....uhummm" ta fada tana yanke kiran.

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 22



Kusan dukansu a galabaice suke daga ita har raliyan,saboda ba wanda baiji jiki a
cikinsu,wannan ya sanya ko hirarma sama sama suke tabata,har zuwa sanda me napep din ya
ajjiyesu a qofar gidan. Zainab ce me qwari qwari a jikinsu,ita ta zaro kudin ta miqa masa yayi
gaba.
A qofar gidan suka samu rabi ita da wata,su dinma kana kallonsu kasan anji jiki

"Mu shiga kawai,mu shiga" Zainab da takeji kudinta kamar sunfi na kowa yawa ta fada,ko banza
tana saka ran samun koda rabin kudinne idan ma duka basu samu ba.

Tun daga soron gidan zakasan cewa tsafta ta tattara kayanta tayi gabas da gidan,tako
ina sunyi hannun riga basa hada hanya ba. Hatta da Zainab yau d'ari d'ari takeyi kada ta taka
kashin kajin dake karakaina abinsu cikin soron.

Sanda suka amsa sallama kuwa basira data karkace a gefen kwatar data raba gidan
biyu tana dahuwar kaza sam bata jiyosu ba. Hasalima waqe waqe take abinta cikin nishadi
gami da jin dadi,gefe guda kuma tana jin zuciyarta tayi fess,saboda dawa tayi nama,domin
kuwa dubu sha biyar ta karba a dahuwar kazar da duka dukanta naira dubu daya ce,sai tarin

tarkacen magungunanta da suke amfani dashi ita da yara da ta yiwa gamje gamje ta zuba suka
bada taste mara dadi,wanda shi makamin da zata bada hujjar cewa kazarta tasha hadin
maganin mata me inganci.

Cikin rawar jiki da washe baki ta miqe tana musu sannu da zuwa,cikin ranta tana jin
yau farar rana ce a tare da ita,don dukkansu ba wanda bata samu kudi dashi ba

"Sannunku da zuwa customer,eh lallai magunguna sunyi aiki, emergency ya kawo wuta yadda
ya kamata,sabon hadi kuka zo ayi muku kenan......ahayyeeeeee cassss,saini basira me gyaran
turaka......"

"Ke da'alla malama ki yiwa mutane shuru ko na zazzabgeki da mari,macuciya azzaluma,ke kisa
kikeyi ma inajin,kin bamu abinda kadan ya rage kwananmu ya qare" baya basira tayi baki galala
tana qarewa zainab kallo

"Ban fahimceki ba me kike nufi ne baiwar Allah?"

"Koma meye ki shiga ciki ki lalubo mana kudadenmu da dukiyoyinmu da kika karba billahillazi
ko na lahira ya fiki jin dadi"

"Ahto,don ba zamu dauki asara goma da ashirin ba,ba wan ba qanin?" Raliya da qafarta ke
rawa saboda rashin qarfin jiki ta fada rai a bace ta biyo bayan abinda zainab ta fada tana kada
hannu. Guda basira ta saki tana yarfa hannu gefe guda

"Ni zaki shigowa gida ki yiwa barazana?,to anqi a baki dukiyar taku....nace anqi a baku din duk
abinda zakuyi kuyi" bacin rai da kuma ganin samu da rashi duka lokaci daya yasa idanun
zainab suka rufe,ta tunzura da maganganun izgilanci da rainin wayon da basira ta fara kwararo
musu,sai kawai ta kaiwa basira duka. Cikin tsananin sa'a kuwa ta sameta a fuska,ji kake
qummmm......

Wani razanannen ihu basira ta saki tana dafe da fuskarta

"Da kin dauka da wasa mukeyi miki 'yar rainin hankali,maza wuce ki dauko mana kudadenmu
tun ban canza miki kamanni ba"

"Ni kika yiwa wannan dukan?"

"Nayi miki kuma na daki banza"

"Wallahi wallahi sai kinsan ba kowa ake tabawa a kwana lafiya ba" basira ta fada tana juyawa
afujajan zuwa dakinta

"Duk abinda Zakiya kiyi,ina nan ina dakonki,karki fito saida kudina" zainab din ta fada tana huci

gami da jan kujerar tsugunno da basira ta tashi a kai tana ci gaba da hayagaga da kumfar baki.

Har kusan minti biyar shuru babu batun basira suna tsaye carko carko suna maida
magana a tsakaninsu. Rabi ce ta dubesu cikin qosawa

"Ko zuwa zamuyi mu tafi matar nan ba ita ba dalilinta fa,kada muje ta shirya mana sharri"

"Wallahi indai ba batan dabo tayi tabar gidan nan ba inda zan motsa sai kudina sun fito,ta gama
zamanta ta fito ta sallameni koda kuwa ku tafiya zakuyi,ni na fita bariki wallahi" zainab ta fada
tana tafa cinya,tana jin kamar ta jawo basira ta bata kudadenta. Ko minti biyar bata rufa da rufe
bakinta aka bubbuga qofar gidan da qarfi,ta bude baki zatayi magana cikin fusata sallamar wata
mace me gurbatacciuar hausa ta sauka a kunnensu. Gajeriyar macace sanye da kaki na 'yan
sanda(uniform),baqa me fadi da qiba,tana takowa tinqis tinqis

"Hajaju........hajaju woooo" ta fada tana leqe leqe cikin gidan

"Madam,ganinan,bazan iya fitowa ba,ko tashi bazan iya ba,haduwa sukayi suka yimin dukan
tsiya,kin ganni a yashe a daki" maganar ta basira dake kwance a daki ta sanyasu kallon kallo a
tsakaninsu,suka kasa cewa komai,saidai kowa zuciyarsa ta cika da tsoro

"Aeaeaeae........sune wadacan mata na sakar geda ko?"

"Sune madam,sune" basira ta fada tana nishin qarya

"Angama" macen dan sandan ta fada tana fitowa.

Da daya da daya ta qare musu kallo tana muzurai idanunta a kansu

"Ku wuce mu tafi lafiya Allah ko na saka muku karfi" tace dasu

"Ina zaki kaimu madam?,me kuka mukayi?" Zainab tayi qarfin halin tambaya

"Tambaya na ma kikeyi?,to wa yabaki izinin shigowa gida ku dadaki matar gida kuma ku zauna
a ciki ba izininta?"

"Mu bamu daketa ba,kuma hakkinmu mukazo karba" zainab ta amsawa matar

"Hey shut up stupid,naga alama kin fisu kwarin ido......hey. ... Samuel shigo ciki" matar ta fada
cikin dan daga murya,nan take saiga matashin dan sandan ya sako kai,ya kuma taimaka mata
suka tasa qeyarsu zainab sai police station.

****Tunda yace mata zaizo ta kasa zaune ta kasa.tsugunne,kusan ta manta rabon da faisal
yace mata zaizo gidansu,ko yanzun ma tafi gasgata cewa aikin malam ne ya ciyoshi,don kuwa

tayi dahuwar borkono tsidugu da rubutu,ta saka wuqa a garwashin wuta me dauke da
sunansa,hakanan tasa anyi hatimi wanda aka buda aka rubuta sunansa a tsakiya dukka dai
gaba daya domin azalzalo zuciyarsa,sai gashi cikin nasara da bakinsa ya furta zaizo din,bayan
yazo din kuma yace akwai maganar da zasuyi wadda jikinta da zuciyarta sunfi gasgata mata
cewa magana ce ta aure.

Cikin wancan satin data shaidawa isma'il bata aurenshi yayi haquri yace ba komai Allah
ya hada kowa da rabonsa sai jikinta dukka yayi sanyi daga baya,har ta dinga ji cewa kamar tayi
gwari,kamar bata kyauta ba,kamar tayi wata asara,amma yanzu faisal ya wanke mata zuciyarta
fesss da zancan zuwansa.
Kwalliya ta zauna ta dandasa 'yar ubansu,itama umma bata zauna ba,tana ta aike siyo
drinks da sauransu. Ta tatse jakarta yau tas,don hatta kudin da yaa bashir ya bata dazun duka
sun narke.

Turaren da malam ya bata hadi da kwalli duka ta dauka tayi amfani dasu,da taga
akwai sauran lokaci sai ta dauko carbinta ta zauna tana fuskantar gabas ta soma qarasawa don
jiya bata samu kammalawa ba.

Ba dadewa suraja ya shigo yace ana sallama da ita. Kafin umma ta amsa ita ta rigata,ta
ajjiye carbinta ta dauki mayafinta da duka duka bai wuce ayi dankwali dashi ba ta yafa ta fito
kai tsaye ta wuce umman tana cewa

"Bari na shigo da shi"

Wani sanyi ne ya sauka a ranta sanda ta ganshi a tsaye jikin motarsa yana danne
danne, exactly irin mijin da takeso. Kallonta yayi yadan saki murmushi ta maida masa

"Bismillah,ka qaraso" ta fada tana juyawa ciki ya bita a baya yana qare mata kallo,don sosai
straight gown din jikinta ta fitar da shape din mazaunanta,uwa uba kuma a yanzun da tasha
supplement na qiba ta sake cika,kai ba zakace itace wasila 'yar ficika da ake tsokana ba,don
har nankarwa yanzu gareta(stretch marks).
Idanu ta juya masa a shagwabe sannan ta miqe tana fadin

"Ina zuwa" sai tayi cikin gida yayin da shi kuma ya bita da kallo. Bayason su rabu amma kuma
bai shirya aurenta ba kwata kwata,yanason macen da tafi wanann quality,duk wasu alamu da
zasu nuna budewar idanun mace akwaisu a tattare da ita,duk da a iya saninsa bata taba zina
ba,amma wasu abubuwan nata suna nuni ne da qarancin tarbiyya.
Bata zauna ba sai data jere komai,komai tanayi ne cikin gwalangwaso iyayi da
sanabe shi kuwa yana biye mata. Hira suka shiga yi kadan kadan,komai a shagwabe take masa
hadi da kashe ido da karyar da murya kamar ba zatayi magana ba,abinda yasa ya dinga jin

feelings a kanta kenan.

Sama sama yaci abincin,duk da baici da yawa ba amma hakan ya mata dadi,tasan
indai ya shiga cikinsa magana ta qare,sai daya nutsa yana goge hannunsa da tissue sannan ya
dubeta

"Waseela,inaso muyi magana ta fahimtar juna ni dake"

"Tun dazu nake jira naji maganar ai" ta fada tana sakin murmushi gami da gyara zamanta

"Kome zan fada miki ki dauka muqaddarine daga Allah,kuma shine qaddararmu da ni
dake,amma kuma abinda zan fada din bawai yana nufin yankewar mu'amala tsakanina dake
ba....." Maganarsa ta qarshe ta sanyaya faduwar gaba,amma ta dake taci gaba da sauraronsa.

"Wasila aurenmu ni dake bazaiyiwu ba,saboda yanxu haka kakata ta dage ta tada rigima harda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login