MAI DAKI... NA HAJ. HAFSAT C. SODANGI (Mrs. Yunus Abdullahi Dabai) 1 MAI DAKI... (1) "auwa'u Idris."" Nayi maza na" Lmike tsaye tare da amsawa saboda tun kafin ya kira sunana dama na "riga na harhada littattafaina, na zuba su a" cikin Jakata. Ya waiwayo ya zub. mun ido sannan ya ci gaba da kallon dogon littafin da ke ajiye "a kan teburin gaban nashi, wanda yake" littafin sunayen dalibai ne wadanda suka "biya kudin Makaranta, da kuma wadanda" ake bi bashi. Ya ci gaba da kiran sunayen daliban daya-bayan-daya duk wacce ya kira kuma to zata tashi. Sai da ya gama kiran sunayen ne sannan "ya waiwayo ya kalle mu ya ce, ""To" tsayuwar me kuma ku ke yi a nan? Cikin sauri kowacce ta fara nufar inda "yake, tana fada mishi uzurinta, wata ta ce" """Malam Babana yayi tafiya ya ce na bada" "hakuri kafin ya dawo, sati mai zuwa." 7 "Wata ta ce ""Malam ni Babana ya ce ayi" "hakuri kasuwa ce tayi gardama, zuwa wata" mai kamawa. Cikir sa'a kuma duk wacce ta kawo uzurinta yana sauraronta tare da ba wata dama. Sai dai ni kam ban ma doshi inda yake "ba, don kuwa a wannan karon ban san me" zan cewa Malam Ali ba. Ya waiwayo a karo na biyu ya sake "kallona ""To ke tsayuwar me ki ke yi a" nan? Ko kuwa kina da wani abin da ki ke son fada ne? "Na ce, ""A'a a hankali ya ce ai ke ko ma" me za ki ce mun a wannan karon babu abinda zai sa na saurare ki. Ni na dade ko ma na ce tunda nake a cikin Malamtaka ban taba haduwa da dalibar da ke cin garabasar karatu irin naki "ba. Haba! Wane irin abu ne wannan?""" Na rataya Jakata na juya tare da kokarin "fita a cikin ajin, cikin sanyin jiki lokacin" 8 "da naji an kira sunana cikin sauri, na amsa" tare da juyawa. Sadiya Tanimu ce dalibar da ke zaune a kujerar da ke bayana. """Ba ni littafina da ki ka karba dazu.""" Na dora Jakata a kan bencin da ke gabana na fara kokarin binciko mata littafinta na darasin English (Turanci) da na ara a safiyar yau don kwafar rubutun da aka yi a lokacin da bana nan. "Malam ya ce, ""Uhum, ba ka ji abin ba," zat tafi miki da littafi. Allah dai ya sauwake irin wannan abu to wai idan uba bai tsaya yaga ya ilmantar da ya yanshi a wannan zamani ba me zai yi mishi ne na gata kuma? Da irin wannan wahalar banzan da ki ke yi na kullum kina cikin wadanda ba su biya kudin Makaranta ba dama aure aka yi miki ki ka huta don ban san yadda za a yi kici jarrabawar gama Makaranta ba a irin wannan tambelen da karatunki yake yi. 9 Ni halina da Hausawanmu kenan wai ba za su tsaya suga sun biyawa ya'yansu "kudi sun yi karatu ba, amma idan an tashi" aurensu sai kaga mata ta sunkuya karkashin gado tana zaro 'yan marofiya da "masu hannun katako.""" "Yan aji suka kwashe da dariya," yayinda na mikawa Sadiya littafinta na kama hanyar barin ajin. """Ki hutar da kanki kada ki dawo, don" kuwa sai dai idan ban gan ki ba ko a ina ne kuwa za a kore ki gida. In tsaya cewa maganar Malam Ali bata "6ata mun rai ba ma to zance ne, kuma ku" "san kullum haka yake yi mun, idan yazo" ajinmu koran kudin Makaranta ba zai bar "ni da takaicin koran kawai ba, sai ya bini" da bakaken maganganu. Ni kuma ba abin in yi zuciya na ce na daina zuwa ba tunda idan na ce haka ba "zan yi karatun ba kenan, don kuwa ba biya" mun din za a yi ba. 10 Duk wadannan takaicin da nake sha "lada ne akan a ce an fara jarrabawa, ranar" da duk wani dalibi yake. dokin zuwanta saboda lokaci ne na nuna bajinta da kuma gwaji kan abin da aka koyar da kai da kuma gane irin fahimtar da ka yi. ab Sai dai ni takan zo mun ne cikin "tsananin fargaba, don kuwa rana ce ta babu" "sani babu sabo, idan har ana binka ko da" kwandala ce daya to babu ko shakka za a kore ka gida. Na rinka bin Malamai kenan ina kamun kafa wadanda za su tabuka mun wani abu ma wadanda babu wani taimako da za su yi mun ba. Wani lokaci ma kaga an bar wasu sun shiga ajin jarrabawar wata kila saboda su "din kudin zango daya ake bin su, ko kuma" wasu sauran canji da ba su gama biya ba N1 kuma a hana ni ko wani Malami ya tausaya yasa baki sai ka ji Malam Ali yana 11 cewa ai ko an barta ta shiga da alkawarin biya ba biya zata yi ba. Ana binta bashin da ya kai na shekaru "uku, don haka barta nan kawai ta karaci" zamanta ta tafi. Idan har akwai wani abu da nake burin "yin shi a rayuwata, to kuwa karatu ne, sai" dai ina ji ina gani abin yana nema yafi karfina. "Babana ba shi da karfi, ba zai iya biya" "mun kudin Makaranta ba, haka nan bai" ciyar da gida ba. Har a yanzu da muke mu "bakwai 'ya'yan Mamanmu, shi din" albashinshi a wurin da yake aiki bai fi Naira dubu goma sha biyar ba a wata. "To da me ya ciyar damu, da me ya biya" mana kudin Makaranta da kuma sauran hidindimu na rayuwa? Ta kai ma shi kanshi ya hakura da karatun kannena maza "ya saka su a sauran wurare irin su, koyon" dinki da kuma kanikanci don ganin ya 12 maida hankalinshi kan nawa karatun ni kadai amma abin ya gagara. Don kuwa da albashin nashi kafin wani watan ya zagayo an lamushe shi a bashi. Dan sauki-saukin da muke samu to na sana'ar dinkin da Ummanmu take yi ne inda wani lokaci takan samu tayi cikon cefane har ta adana mana dan abinda muke hidima da shi na sallah. ldan shekara ta zagayo babban abu guda daya kuma mai muhimmanci a wurinmu gaba daya shi ne muna da kwanciyar hankali da nutsuwa tare da addini mnai yawa a cikin gidan namu. Don haka zama muke yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Na kamo. hanya don komawa gida "zuciyata cike da kunci, don kuwa wani irin" nisa ne a tsakanin gidanmu da Makarantar wanda kuma a kullum da kafa nake zuwa nake kuma dawowa. 13 Sannan a mafi akasarin lokuta na kan "tafi ne ba tare da nayi karin kumallo ba," don kuwa na kan kasa hakurin jira don kada nayi latti. Tafiya zan kuma tafi ne ba tare da ko sisi ba har sai na dawo ne zan ci abincin da na samu an yi. Ina karyo kwanar unguwarmu na hango Abdussamad zaune kan dakalin shagon askin dake makwabtaka da gidan su. "Wani irin faduwar gaba na samu, nan" take na juya na koma ta daya hanyar duk kuwa da cewar ita din tafi nisa zan iya cewa kusan kullum aka koro ni kudin "Makaranta, to sai na ganshi matukar ba" komawa tashi Makarantar yayi ba. Na kane da niyyar na share shi nayi "kamar ban ganshi ba, don haka na" sunkuyar da kaina na ci gaba da tafiyata har na dan gota su. 14 "Sai naji ya ce ""Barka da dawowa, ranki" "shi dade. Cikin wayancewa na ce ""Af, ai" ban ganka ba ne. 9 Tare da dan murmushi. Ya mike ya nufo ni tare da kakkabe wandonshi yayinda yake karasowa inda nake. Ya dan tabe baki tare da cewa. """Da dai kamar ban sanki ba ne ki ka" "fada mun haka, to dana yarda." Na fara gaishe shi bayan mun faraa tafiya yana amsawa. Na ceAshe baka koma ba har yanzu? "Ya ce, ""A'a na koma jiya dai na sake" dawowa da yamma saboda wani yajin aikin da Jami'o'i suka fara satin can da ya wuce. "Na ce, ""Cabdijam! Abin dai babu dadi" "Ya ce, ""Eh to, kusan hakan, kin san" yanzu babu ranar komawa dai kenan "halin yajin aikin kasar nan, idan ba" matukar sa'a muka ci ba sai mukai watanni biyar nan gaba zaune Gwamnati 15 bata dauki wani kwakkwaran mataki a kai ba. "Tunda su babu ruwansu, don talaka ne a" matsala tunda mu ne muka cika "cikin Jami'o' i kasar, su nasu suna can Turai" "suna karatun cikin kwanciyar hankali, mu" kuma muna nan muna gwagwagwa. Karatun da zai dauke ka shekaru hudu idan ba matukar sa'a kayi ba sai ya kai ka shekaru shida kana yi ba ka gama ba. Shi yasa ai tun yanzu muke muku addu'a komai ya gyaru kafin zuwan naku "lokacin, sai dai banga alamar ke za ki yi" "nisa ba, nafi zaton aure za ki yi da alama." "Na kalle shi na ce, ""Uhum! Sai anjima." Na shiga gida saboda karasowar da muka yi kofar gidan mu. Akwai mutunc1 mai yawan gaske a "tsakanina da Abdussamad, don kuwa duk" "shariyata da mutane suke magana akai, shi" kam muna gaisawa har ma mu dan yi hira saboda shi ko na wuce shi to zai yi mun 16 magana har ta kai ma ba na ma iya wuce shin. "Makwabcinmu ne sosai, haka nan" Babana da Babanshi suna mutunci sosai a tsakaninsu. "Nayi sallama na shiga gida, yan" kananan kannena ne suke wasa a tsakar gida da alama Umma ta hana su fita zuwa kofar gida ne. "Tasi'u da Sabi'u, a guje suka taho suna" rige-rigen karbar Jakar Makarantana. Na mikawa Tasi'u saboda nasan Sabi'u ba iya "dauka zai yi ba, na kuma yi mishi dabara" ta hanyar daukanshi na cilla shi sama na cabke. Don kada ya saka mun rikici muka "karasa shiga dakı, suna yi mun hirar su ta" shirme Umma tana zaune a kan tabarma a "tsakar dakinta, yanka take yi na atamfa." "Na tsugunna nayi mata sannu da gida," ta amsa ba tare da ta tambaye ni dalilin 17 "dawowana ba, don ta riga tasan abinda ke" dawo da ni a irin wannan lokacin. """Shiga ki tube kayan Makarantarki ki" "saka na gida, ga dumame nan sai ki diba" "kici. Na ce, ""To." Sai dana gama cinye dumamena daa muka ci tare da su Tasi'u sannan na sake hada kwanukan da sukalalacena wanke na "sake gyara gidan, na wanke bayan gida" sannan na sake dawowa wurin Ummana "ce, ""Umma za a dora wani abu nea" wuta? "Ta ce, ""Dan saurara dai tukuna muga" "dawowar Auwalu ko?"" Na ce, ""To."" Na" mikena shiga dakina dake tsakar gida na dauko littattafaina na Makaranta don na dan yi bita. Har karfe daya na rana shiru Auwal bai "dawo ba, hakan ne ya sani sake tashi na" shiga cikin kicin dinmu na dauko dan sauran garin kwakin da ke ajiye don na jika musu. 18 Na kawo sugar na saka na mika musu cokala sannan na dauki buta don yin alwalar sallar Azahar. "Haka rayuwarmu take a gidanmu, kusan" kullum muna kwanciya ne da daddare ba tare da mun san abinda zamu ci idan gari ya waye ba. Haka nan idan safiyar tayi muka samuu "muka karya kumallo, to ba ma sanin abin" da zamu ci idan rana tayi. "Saukin abin ma shi ne, yanzu Auwalu" ya kawo karfi yana kuma matukar taimakawa. "Auwalu shi ne wana da nake bi, shi ne" kuma da na fari a wajen Iyayenmu baki daya. A yanzu haka makanike ne a cikin "babbar kasuwa, sai dai har yanzu ba" "kwarewa yayi ba, amma yana matukar" samun' alheri ba kadan ba. 19 Saboda sa'ar da yayi na haduwa da "shugaba na kwarai, illa ko yau ma shi ne" ya shigo da cefane a hannunshi Don haka na shafa fatiha cikin sauri na fito na karbe shi. """Akwai itace ne? Na ce, ""Bari na" "duba. Na leka kicin din na ce, Akwai," amma dai babu yawa. "Ya juya ya fita, yayinda ni kuma na fara" "kacaniyar dora girkin, ya sake shigowa da" itace kai biyu a hannunshi ya zuba tare da miko mun Naira ashirin. "Ki bai wa Tasi'u ya sayo miki maggi," "ni na manta ban siya ba. Na ce, ""To."" Ya" juya da niyyar komawa wajen aikinshi. Tuwon masara nayi tare da miyar "kubewa danya, saboda ita na gani a cikin" "cefanen, ta kuma yi dadi da yawa na tuka" don mu samu na dumamen safe. Na kwashe na adana na kowa tare da rufewa na janye itacen na dora ruwan 20 wankana a kan garwashin sannan na kawowa Umma nata. Sai da nayi wanka na yiwo alwalar "sallar La'asar, don kuwa zan iya cewaa" yanzu dabi'ata ce hakan saboda kusan kullum abincin yamma muke yi. Na idar da sallar La'asar na jawo kwalbar maina da Auwalu yake kawo mun mai kamshi. "Duk da ba wani mai tsada ba ne, shafa" shi yana sani naji ni'ima saboda kamshin shi. Na murza hoda da dan kwalli na jawo atamfata na daura sannan na fito nazo 1in da Umma take na zauna don naci nawa abincin. Muka dan fara hira wacce yawancinta "akan Makarantata ce. Tace ""Sai ki" "yawaita addu'a, Allah ya zabar miki mafi" "alheri a ciki, ko karatun idan zai yiwu." 21 ldan kuwa ba mai yiwuwa ba ne to sai kiyi aure a kai ki dakinki kema ki nutsu ki zauna a wuri daya. Babban burin Iyayena bai wuce na "ganin nayi karatu ba, ko da kuwa wacce" irin wahala za su yi don ganin hakan. Hakan ne yasa da Umma tayi mun wannan maganar gabana yayi matukar "faduwa, ta soma hakura kenan ko ya ya?" "Na ce, ""Umma aure fa ki ka ce?" "Ta ce, ""Eh shi na ce idan karatun ba zai" yiwu ba menene amfanin zaman gidan tunda kin riga kin isa auren. Shi ma Babanku ai ya nga ya fara hakura tunda naga an kwan biyu ba tare da yayi maganar Makarantarki ba. "Jikina yayi matukar yin sanyi, dafin" maganar Umma sai dai ban ce mata komai "ba, don ba maganata ba ce tunda ba zan" iya tuna ranardas wata magana makamancinyar wannan da ta danganci aure ta hada ni da ita ba. 22 Aunty Hauwa'u kizo in ji Yayan su Lubabatu. Na waiwayo na zuba ma "Tasi'u ido, na ce ""In zo fa ka ce?" "Ya ce, ""Eh shi ne ya aiko ni gashi nan" "ma a zaure. Umma ta ce ""To ki ka sani ko" wani abu zai tambaye ki? "Na ce, To bari naji naga bai taba" "aikowa gidanmu a kira ni ba."" Hijabina na" sako na fita kofar gida inda yake tsaye. Wata gaisuwar muka sake yi yana "kallona ""Ya na ganki fuskarki wata iri?" "Na dan yi murmushi na ce, ""Ai da ka" "kirani ne baka ji yadda zuciyata tayi ba, sai" da gabana ya fadi. "Ya ce, ""To da alama dai ba ki da" "gaskiya kenan."" Na ce, ""A'a rashin" gaskiyar me? Na dai dauka wani abu ne ya faru kuma ka san ban saba hakan ba. 99 Ya "ce, ""Eh to, ai komai dama farashi ake yi" ko? Ua juya inda su Tasi'u da Sabi'u suke harkokinsu ya mika musu Naira ashirin ya 23 ce a siyo biskit suka karba tare da fallawa da gudu don sayowan. Ba wai don yazo wurina ko kuma kofar "gidanmu ba ne yasa shi yin hakan, dama" can dabi'arshi ce inda duk ya gan su to zai saya musu ko biskit ko cakulet. "Ya waiwayo inda nake ""To ya ya" "yanmata ya karatu? Na ce, To mun" "gode Allah, ni yanzu kina aji nawa ne?""" "Na ce, ""SS1."" Ya ce, ""Dama nayi zaton" "kina tafiya ne tare da su Luba, sai dai a" hanya za ki tsaya tunda ban ga alamar kina mayar da hankali tare da bada himmar yin "karatun ba.""" "Na ce, ""Me yasa ka fadi haka? Ya ce," A'a na gane kamar aure ki ke so. Wayancewa nayi tamfar maganar bata bata mun rai ba. Kuma kafin na samu amsar ba shi sai na hango Babanmu yana tahowa daga wurin "aiki kuma yake na ce ""Ni zan shiga gida" ga Baba nan ya dawo. 24 Har kasa Abdussamad ya tsugunna ya "gaida Babana, sannan ya wuce ni kuma na" shigo gida ina yi mishi barka da zuwa. Ban wuce dakina ba abincin Babanmu na dauko na kai mishi dakin Umma tare da ruwa. Yana sanye da kayan gida da alamar har ya cire na aikin shi sannan na sake mishi sannu da zuwa na wuce dakina. Washegari da sassafe kamar kullum sai "da na hada mana abin karyawa, kunu da" dumamen tuwo sannan na saka uniform dina na dauko hanyar Makaranta. Kamar daga sama ina shiga ajinmu "kafin na zauna sai ga Malam Ali ya shigo," "ya ce ""Maras zuciya, ai dama nasan yau" ma sai kin dawo shi yasa na bugo sammakon zuwa ajin naku don na gani. Ba kuma zan bar ki ko darasi daya ki "samu ba. Juya kawai ki tafi."" Na juyo na" "kamo hanyar dawowa gida, yau kam ta" lungun unguwarmu na biyo don kaucewa idon Abdussamad. 25 Ban tsaya yin komai ba kan yar yamushashshiyar katifata na hau na kwanta ba zan iya cewa ga iyakacin abinda "Zuciyata take gaya mun ba, illa iyaka dai" "kawai nasan babu mamaki, ni din ba zan" samu cikar burina ba ne a rayuwata shi ne "na ni din na zama Nos, wato Malamar" jinya. Nayi kuka har na gaji ban san sanda "barci ya dauke ni ba, na dai farka ne naji" ana kiran sallar azahar. Na mike tare da yin salati da na tuna ko "abincin rana ban dora ba, tunda idan ina" gida ni ce mai yi. Na fito cikin sauri na samu har Umma ta riga ta sauke tana rabo. "Shinkafa da wake ne, da mai da yaji." Nayi mata sannu sannan na shiga bandaki don kama ruwan in alwala. Har na gama hidimomina na gida yau ko waiwayon littafan Makarantana ban yi "ba, don kuwa na fara fidda rai abinda" kwata-kwata ban saba yi ba kenan. 26 Dabi'ata ce kullum Zan yi bitar littattafai na koda nake da matsala wajen biyan kudin Makaranta ni din ina cikin daliban aji da suke da matukar kokari. Tunda har Malamaina ma sun shaida "hakan, to amma ya zan yi? Malam Ali ya" "taso ni a gaba, bana kuma ganin laifinshi" tunda aikinshi yake yi. Duk wadannan tunanina ne kafin "wayewar gari, don kuwa tsintar kaina nayi" "da fara shirin Makaranta, har na fito tunda" sammako nayi ina yiwa Babana sallama wanda a yau din zan riga shi tafiya. "Ya ce, ""Ke Hauwa'u ba Ummanku jiya" ta ce mun satin nan kaf idan ki ka je Makaranta koro ki ake yi ba? "Na ce, ""Eh haka ne Baba."" Ya ce, ""To" amma a hakan ke gara miki kiyi ta zuwa ana korarki? Maganar gaskiya shi ne nayi niyyar baki wani abu ki kai Makarantar taku. 27 To sai dai mu mamatsalar wurin aikin mu yawa ce da ita tunda wannan watan shi ne wata na wajen uku da ba a bamu "albashi ba, amma daga zarar an bamu wani" abu zan ba ki ki kai musu ko da babu yawa ne. Sai ki ba su hakuri yau din idan kin "je.""" "Na ce, ""To Baba."" Na fito daga gida ina" tafiya tare da tunanin maganar Babana ni ba abin in ce mishi ai yanzu ta kai ma ko saurarona basa yi ba. sli Babu amfani tunda ba da gangan yake Rin biya ba. Na shiga aji na zauna a darare ganin har "karfe tara tayi Malam Ali bai zo ba, sai na" waiwaya bayana inda Sadiya Tanimu ke zaune. "Saidai ban ganta ba, don haka na ce wa" wacce suke zaune tare rmai suna Zubaida. DunsDon Allah dan bani aron littafinki ná Chemistry na dan fara kwafa kafin a tashi. 28 Ta kalle ni ta dan tabe baki tare da "girgiza kanta kafin ta ce, ""A'a a gaskiya ba" "zan miki karya ba, ba zan iya ba haka" kawai azo a kore ki na manta ki wuce mun da littafi. Bari dai wacce ta saba baki tazo don naga itama kamar ke karatun ba damunta "yayi ba, bambancinku kawai ita ana biya" "mata kudin Makaranta.""" Na juyo na ci gaba da wasu sabgogin ba tare da na tsaya bai wa Zubaida amsa ba. Ba a ko kai mintina biyar ba bayan nan sai kawai Malam Ali ya shigo. Tun kafin ya fara kiran suna na mike na kamo hanyar "dawowa gida, zuciyata cike da kunci da" 6acin rai. Har naZO zan shiga gida sai naji ana "kirana,Abdussamad ne. Na tsaya ya" karaso inda nake. "Hauwa'u kenan, yau ma kin kasa zama" ne kiyi karatun har zuwa lokacin tashi? 29 Wani gululun bakin ciki ya taso ya "tokare ni, wai wannan me yake nufi ne?" Na dago kaina da niyyar ba shi amsa. Sai dai na kasa saboda dama kiris nake "jira, don haka da na lura kawai kuka zai" kubucemun sai na shige gida ba tare da na sake sauraronshi ba. Ina shiga gida wurin Umma na wuce na "durkusa, kuka na kama yi babu" "kakkautawa, ba tace mun komai ba sai da" nayi ya ishe ni ina share hawayena sai ta "ce ""To ni kam Hauwa'u ai bani da abin yi" miki da ya wuce na ki hakura da wannan sintiri da ki ke yi ana koro ki ba tare da fashi ba. Ki dan saurara kema ki samu nutsuwa amadadin wannan zirga-zirgan da ki ke yi. Idan Babanku ya samu kudi ai ya gaya miki zai ba ki dan wani abu ki kai musu ko? Kafin karshen wata muga abinda "Allah zai yi.""" 30 Na dawo daki na debi kayan wanki na fitar na hado da na su Tasi'u gaba daya na "fara yi, sai wajen Azahar na gama nayi" wanka na nemi wuri na zauna da niyyar hutawa a ka yi sallama da ni. "Na riga nasan Abdussamad ne, don" haka kamar ba zani ba sai kuma na dauki gyalena na fita. Yana tsaye a kofar gidanmu sanye da wandon Jeans da riga shirt fitted na gaishe shi a dake. "Ya ce, Hakuri nazo baki don naga" "kamar dazu na bata miki rai, kiyi hakuri" "ban yi da nufi ba. Na ce ""Babu komai." "Ya ce, ""Kin tabbata?" "Na dan yi murmushi na ce, ""Uhum!""" saboda yanayin yadda ya yi tambayar. Ya "ce, ""Ban san dalili ba Hauwa'u, sai nake" ganin kamar ni din ina da ruwa a cikin al amarin karatunki. Don kUwa ko babu komai ai ke kanwata "ce. ko ba haka ba? Na ce, ""Eh haka ne." 31 "Ya ce, ""To 1dan mutum ya samu halin yin" abu to baya sakaci da wannan damar har ta kubuce mishi. Kiyi amfani da kuruciyarki ki taimaki kanki kiyi karatu. Muka shiga wata hirar "ta daban, yana tambayata wasu abubuwan" ina ba shi amsa har Babana ya dawo. Yau ma ya gaishe shi ya wuce na biyo shi a baya yana tambayataYau an bar ki kin yi karatun ko kuwa an sake koro ki? "Na ce, An koro ni Baba. Ya ce,To" "sai kiyi hakuri muga abin da Allah zai yi.""" "Na ce, ""To." Har satin ya kare ban koma Makaranta "ba, haka nan kullum bayan sallar La'asar" Abdussamad yana zuwa mun hira. Ranar Lahadi da yamma kwatsam sai "ga Sadiya Tanimu, na tare ta cikin farin" ciki ba kadan ba. Makwabtanmu na tura "aka sayo mun Zobo mai tsabta," 32 Na kuma yi sa'a dafaduka muka yi ma1 Kyau ta kuma yi dadi na kai mata dakina bayan sun gaisa da Umma. Tana cin abincin muna dan hira tana bani labarin abubuwan da suka faru bana "nan, da irin gwajin da aka yiyyi a aji." Naji wani iri a raina. Ta tashi zata tafi na mike da niyyar yi mata rakiya. Da nisa sosai na kaita har kusan barin unguwarmu gaba daya. Ta wuce ni kuma na kama hanyar dawowa gida. Baiwar Allah salamu alaikum. Jin "yanayin sallamar ne ya sani juyawa, wani" mutum ne a tsaye sanye cikin farar shadda jamfa da wando. Na amsa tare da nufin ci gaba da tafiya. Dan dakata mana yanmata. Tun daga dan nesa fa nake bin ki ban dai yi miki magana ba ne saboda ganin yanayinki. Na san ba yarda za ki yi ki tsaya cikin "mutane ba, shi yasa ban tsaida ke ba sai da" 33 naga mun zo nan wurin. Sunanki nake so ki fada mun. "Na ce, ""Hauwa'u. 99 Ya ce, Gidanku" fa? Ba tare da yin wani dogon tunani ba "na yi mishi kwatance.Ya ce, ""To ya" gode. Na dawo gida na ci gaba da harkokina. Har a yau Monday ma ban yi nufin "zuwa Makaranta ba, saboda maganar da" Babana ya yi mun na jiranshi zuwa karshen wata don ganin abin da Allah zai yi. "Da yamma ne aka yI sallama da ni," "cikin zuciyata Abdussamad ne, don haka" hijabina na dauko na fito ga zatona "Abdussamad din ne, Sai kawai naga" mutumin jiya. Yau ma sanye yake cikin tafafe na "kamala, jamfa da wando, rigar half jamla" ta matukar yi mishi kyau. 34 """Ina wuni? Na fara gaishe shi cikin" "girmamawa, don kuwa ba karamin yaro ba" ne. "Lafiya Hauwa'u, yaya karatu? Na ce," """Mun gode Allah.""" """A aji nawa ki ke a Makaranta? Na" "gaya mishi ya dan yi murmushi ""Kina da" "saura dai ashe."" Muka dan yi hirar karatu" "kadan, abinda ya sa na saki jiki da shi." """Kina da sha'awar yin karatu mai zurfi" ne? Ko za ki tsaya ne daga gama "Secondary?"" Na ce, ""Idan na samu halin ci" "gaba haka nake so.""" "Ya ce, Eh yana da kyau, kin san" karatun 'ya mace ba karamin abu ba ne ga "ya'yanta, da kuma mijinta baki daya." "A daidai lokacin ne Abdussamad yazo," ganinmu yasa shi juyawa ya tafi. Mutumin ya kalle ni yana dan murmushi. Ina fata dai ban tsarewa saurayin naki "wuri ba'? Na ce, ""A'a ba saurayina ba ne." "Ya ce, ""Menene, abokinki ne?""" 35 "Na dan yi murmushi, ya dan yi ajiyar" "ZUciya ya ce, ""To Malama Hauwa'u, ni dai" "kin ganni ba yaro ba ne karami, don haka" ya kamata ki gane ba da wasa ko yaudara nazo wajen ki ba. Na gan ki ne na yaba da halinki da kuma dabi'arki ta nutsuwa da na gani a "tare da ke. Ni ba mutumin garin nan ba ne," nazo wani dan aiki ne wanda nake ganin kamar zai dauke ni tsawon shekaru uku zuwa hudu. "Sunana Ishak, ina kuma aiki ne da" Ma'aikatar noma wato (Ministry of Agriculture). Ina fata zan samu hadin kan da nake nema a.tare da ke? Ina so na gaya miki ba zan tauye ki na "hana ki karatunki ba, don kuwa kina da" kuruciya sosai. ldan aka yi miki hakan ba a yi miki adalci ba. Don haka ina so kiyi tunani mai yawa a kai zan dawo rana ita yau din nan don jin abin da ki ke ciki. 36 "Na ce, To. Y asa hannu ya miko mun" "kudi, ya ce ""Ungo wannan. Na dan yi jim" "kamar ba zan karba ba, ya ce ""A'a karbi" "kawai.""" "Na ce,To na gode. Sannan ya bude" bayan motar shi ya sauke mana doya manya goma da buhun shinkafa da wata leda babba baka. Yayi sallamaya tafi. Na dade a wurin a tsaye kafin na shiga gida. "Ummma ta zubawa kayan idanu ta ce," """Ikon Allah! Shi kuma wannan ko waye" "sai Allah. Na zauna na jawo ledar na bude," zannuwa ne masu kyau guda biyu da kayan shafa masu daraja. Sai da Babana yaci abincine sannan ya "kira ni na same shi a zaune. ""Ke Hauwa'u" ashe dama kin fara tsayuwa da samar1 ne ni ban sani ba? "Naji wani iri a cikin jikina, na kuma" "rasa abinda zan ce mishi. Ya ce, Ke ía" nake sauraro don ni nayi zaton shi wanan 37 yaro Abdussamad da nake ganinku da shi ba wani abu ba ne a tsakaninku face makwabtaka da mutunci. To shi kuma wannan a ina ki ka same "shi?"" Nayi wa Babana bayanin komai" "game da mutumin, har da ranar gamuwvata" da shi da kuma abinda ya gaya mun da kan "shi ya ce ""To tashi ki tafi.""" Na dawo dakina na zauna bayan na kai1 wa Umma har da kayan atamfofin da kudin wanda ta mika su ga Babana gaba daya. Washegari Abdussamad bai zo ba "kamar yadda ya saba, sai bayan kwana" biyu ne inda dawowa daga siyo sugan da "naje yi a shagon unguwarmu, na ganshi" tsaye kusa da shagon "Ya ce, ""Hajiya Hauwa'u. Na ce Ni" din ce kuma Hajiya a yau? Ya ce Eh "mana, ba dole nace FlajIya ba, wannan irin" luntsumemiyar mota haka a1 kin san mai niya ake cewa llajiya ba wanda yaje ba 38 Kin ga yanzu dole mu rinka yi a hankali kenan tunda Tunku ma yasan shurin da yake yi wa kashi. "Na ce, ""Haka ne."" Ban tsaya cigaba da" "jin abinda yake fada ba, tunda na fahimci" so yake ya soka mun magana sai kawai nayi gaba. Ranar da Ishak ya ce zai zo kuwa sai "gashi ya dawo, na kuma isar da sakon" Mahaifina a gare shi ta yana son ganinshi. Bai tsaya wani dogon bata lokaci ba ya "ce, zai jira shi ba sai yaje ya dawo ba, don" haka shigowa gida nayi na bar shi da nufin shi na sai yaga Babana kafin ya tafi. "Hakan kuwa aka yi, ban san yadda suka" "yi ba, bani kuma da damar tambaya, don" haka harkokina kawai nasa a gabana. Na dai yi nufin tambayar Umma ko Babana zai bani kudin nan naje na biya "kudin Makaranta dashi, sai dai na gagara" saboda nauyin da nake ji. 39 "Ban yi zaton zuwanshi a washegari ba," kwatsam sai ga shi. Ina tsaye yayin da yake jingine jikin motarshi ya ceNa dawo ne yau don nayi miki magana kan al'amuran da muka tattauna da Baba. Muyi magana da ni da ke saboda fahimtar juna. Jiya ganin da nayi mishi ya bani izinin turo magabatana don daidaita "maganar aure.""" Cikin wani irin mummunan faduwan "gaba na dago kai na kalle shi, karo na" farko da nayi hakan a karo na uku da fara Zuwanshi gidanmu. "Yana cikin matsakaitan mutane, shi din" "ba kyakkyawa ba ne, haka nan ba za a kira" shi mummuna ba. "Shi da kanshi ya lura da canzawata, ya" "ce ""Shi yasa na ce zan ganki don mu" tattauna a tsakaninmu. Kina da matsala a kan turo magabatana da zan yi? "A hankali na girgiza kaina alamar a'a," don kuwa babu wani hukunci da Babana 40 "Zai zartar na sa kafa na shure shi da sanina," kuma ina cikin hayyacina ba. "Ya ce, To ya naga yanayinki ya" canza? Ban san dalili ba sai na samu "kaina da ce mishi ""Karatu nake yi."" Ya" dan yi murmushi. Don ta wannan nayi wa Mahaifinki alkawarin zan sa ki a Makaranta kiyi ta "karatun har ki gama, bayan wannan kuma" "sai me? na ce, ""Babu."" Ya ce, ""To ni" ranar Jumma'a zan tafi Kaduna gida wurin "iyayena, don mu zanta kan maganar." "Na ce, ""To Allah ya kiyaye hanya."" Ya" "ce, Amin. Ya miko mun kudi a" hannunshi na karba tare da godiya. Duk yadda na kai da daurewa da na zauna gaban Umma zan yi mata magana sai kawai na fashe da kuka. 9T6 Menene kuma na kuka? Ta tambaye "ni fuskarta a yamutse. Na ce ""Umma daga" "zuwa biyu sai kawai maganar aure, ko" 41 "gama saninshi bamu yi ba, sannan" "karatuna fa?""" Tayi shiru ta ci gaba da saka maballan "gar da na samu ta gama, an kai kamar" mintina biyar sannan ta fara yin magana. """Babanki ba shi da halin daukar" "dawainiyar Makarantarki, kema kin san da" haka. A yanzu ma da ki ke Makarantar Secondary abin ya gagara ballantana kin shiga wacce ki ke burin yi ta koyon jinya. Idan da kina da zurfin tunani kema ya kamata ace kin fahimci hakan. ke kadai ce "a cikin ku bakwai ki ke ka ratun nan," amma a biya miki kudin Makaranta ma abin ya gagara. Babanku yana zuwa wurin aikin nan da yake yi ne kawai ba wai don kudin da ake ba shi ba tunda a yanzu ba biya ake yi ba sai don kawai kada ya zauna a gida ba tare da yana da abin yi ba. Ba kuma zai yiwu ya ce takamar ke da shi kuna son kiyi karatu ya yi ta ajiye ki a 42 "gida ba, ke mace ce. Kin kai lokacin aure" tunda kuma sh1 ya ce ya yaba da kamalar mutumin. "Ina ganin shi kenan magana ta kare, ya" kuma yi alkawarin zai tsaya yaga kin yi karatun da ki ke son yi. Na tashi na dawo dakina na kwanta "saboda yanayin da jikina ya yi mun, aure a" yanzu? Babu abinda ke zagaya mun kwakwalwata irin ko wata guda ban yi da sanin mutumin ba. To amma tunda dai yayi alkawarin zan "yi karatu shi kenan magana ta kare, dama" burina kenan idan na samu hakan kuma zan yi murna. Bayan nan ban sake zuwa Makaranta ba saboa abinda Babana ya ce kenan a jinkirta aga yadda maganar zata kaya. Na ci gaba da karatun a dakina. Sati biyune kawai bayan nan iyayen Ishak suka zo an sasanta da su har an daidaita lokacin aure don suma suna son shi da gaggawa. 43 Sun kuma zo da kayansu na na gani ina So. Tun daga lokacin da maganar aurena ta yadu ban sake ganin Abdussamad na gaishe shi ya amsa ba wani lokacin ma yana hango ni yake kaucewa. "Ban san abinda yake nufi ba, don haka" nima sai kawai na share shi. Shirye-shirye na nima nake yi da iyakacin karfina tunda dai ba zance bana "son Ishak ba, kamar yadda ba zan ce ina" Son shi ba. Babban burina dai da nake hangowa kamar nishadi. Ishak da kanshi ya shaidawa iyayena ba ya bukatar wata doguwar dawainiya da ta danganci kayan "daki, shi gidanshi akwai komai." Don haka shirin da Umma ma take yi ya dan yi sauki kokarinta kawaina ganin ta hada mun kayan kicin ne ta kuma saya mun sabon Keke gau a kwalinshi. Tunda nima ta koya mun dinki na kuma iya daidai gwargwado. A shirye-shiryen da 44 aka yi mun a gida kuwa har da na zuwan "garin ma garin Babana Birmin Kudu, duk" kuwa da suma za su zo bikin. An yi mun shirye-shirye masu yawa daga gida amma duk da haka sai da Ishak ya kawo kudi masu yawa ya kara mun. Zan iya cewa tun da aka fara maganar aurena da shi al'amarin da yanayin "gidanmu gaba daya ya canza, don kuwa" duk zuwan da zai yi zai kawo kudi masu dan dama ya bani. Haka nan ba zai rasa abin amfani da zai sauke mana ba. Tun da farko da Babana yana karba ya hana ni am fani da kayan da yake bani. Amma da aka zo magana tayi karfi sai ya bar ni har da kayan da yake kawo mun na zannuwa yana karba yanzu duk ya dawo mun da su. "Ni kuma na kai an diddinke mun su, ina" ta kwalliyata gwanin sha'awa. Wani lokaci 45 sai nayi tunani na ce to a waje ma ya wadata ni haka ina kuma ga naje gidan shi. Kwanaki uku kawai nayi a birnin kudu duk kuwa da yawan 'yan uwan Babana da ke garin saboda gabatowar bukina na gaiyato kawayena irin su Sadiya da wasu daga cikin ajinmu da na san muna mutunci da su. Na kuma gayyato Lubabatu kanwar Abdussamad da muke unguwa daya da su gashi kuma dama tare muka tashi tunda sa'o'i muke. Ina zaune a dakina ina shafa mai na mai tsada Ishak ne ya ke saya mun shi wanda a yanzu ya mayar mun da jikina tamfar wacce aka ciro daga cikin kwai saboda laushi da kyau. Dama gani ba fara ba haka nan ba baka "ba. Kalar jikina ita ce tafi daukar hankali," amma ba ya ga haka bani.da tsawo sai dai kuma idan ba tsayuwa kusa dani kayi ba. 46 "Zai vi wuya ka gane haka, don kuwa" gabo6ina suna da zubin na dogayen mutane. Lubabatu ce tayi sallama ta shigo ta zauna muna gaisawa tana tambayata "shirye-shiryena, ina yi mata bayani." "Zuwa can ta ce, To ai gaskiya" Hauwa'u ni dai hakuri za kiyi ba zan samu zuwa ba shi yasa naga da ki ga shiru ban zo ba gara na gaya mii kawai. "Na ce, Saboda me Luba? Ta ce, TO" "Yaya Abdussamad ne ya hana ni ya ce," idan kuma nazo to zai lauki kwakkwaran mataki a kaina. Nayi shiru ina dan tunani a raina na rasa abin da na yiwa Abdussamad da yake sa shi yin irin wadannan abubuwan da yake yi mun a wannan lokacin. "Na ce,To babu komai Luba na gode," amma kin san wani abu? Ni fa ban san "abinda na yi wa Abdussamad ba, amma" zan shigo gidan naku dan anjima kadan. 47 "Ta ce,A'a rabu da shi kawai. Ni na" "riga na fahimce shi, shi a tunaninshi" sauraron shi da ki ke yi Jira yake yi ya gama karatu kuyi aure. Wanda Umma ma ta gaya mishi ke mace ce ba tun yanzu ba to bai yarda ba. "Yaushe za'a ce ke kin jira shi, shi da yake" aji uku na Jami'a a yanzu ko bautar kasa "bai je ba, ballantana har ya samu aiki kuyi" aure? "Na ce, ""Duk ba haka ba ne ma Luba, ni" "bai taba ce mun yana sona ba, mutunci ne" "kawai na dauka a tsakani.""" "Ta ce, ""Tabdijam! Ke kenan amma" "kowa ya sani.""" Bayan tafiyar Luba shiru na yi ina tunani ban san abinda ya hana ni fahimta ba sai a yanzu ne nake fahimtar wasu abubuwan. To amma koda na gane hakan tun farko ko kuma ace shi ya gaya mun da kanshi 48 zai yiwu na jira shi? na yi wa kaina tambayar. A take kuma na baiwa kaina amsa ba zai yiwu ba don kuwa a yanzu ma auren nawa ya dauro ne saboda wasu dalilai. Da dai ace muna da wadatar da zan yi karatuna ne ba tare da wata matsala ba to da sai in ce zan yi ta jiran Abdussamad har ya yi karatunshi ya gama muyi aure. Don kuwa wane mutum na ce bana sonshi dan gaye ne. Duk da iyayenshi ba masu kudi ba ne Abdussamad dan gata ne. Haka nan shi ne dan farin namiji a gidansu. Nayi maza na cire tunaninsu shi "da kanwarshi a cikin raina, na ci gaba da" "harkokina, saboda hakan shi yafi mun." Kayatacciyar walima aka shirya ana gobe daurin aurena. Babu abin da bai ji ba a wurin walimar. Ana cikin walimar ne kuma 'yan uwan Ango suka iso da La'asar aka farata ba a gama ba sai gab da sallar Magriba. 49 A wurin su Sadiya nake jin labarin irin kawataccen kayan auren da aka y1 mun kamar zan yi dokin gani sai kuma naga to "al ma nawa ne, dokin me kuma." Na tsaya cewa Ishak ya kawata bikin nan ma tamkar na bata ne. Nayi kwalliya iri-iri ba a magana. Ranar Asabar da aka daura aure aka kai ni gidan aka watse saboda wadanda suka zo daga wasu garuruwa da za su koma a ranar Lahadi don samun damar komawa wuraren aikin su wadanda suka saura daga "yan biki kawai, yan uwan Umma ne da" yan uwan Babana wadanda a gidanmu suke. Na bude idona ina kallon dakin shiryayyen daki na zamani irin wanda mafarkina bai taba nuna mun shi a matsayin nawa ba. A takaice dai gidan yayi matukar haduwa daidai da rayuwar 'yan boko. Bani 50 kadai ba nasan Ummana da Babana ma za Su samu nutsuwa a yanzu. "Naci amarcina yadda ya kamata, abin" ba a cewa komai ga kuma karin nutsuwa da na samu ta bangaren abinci da kuma wurin zama sai abin ya hadu ya sani nan "da nan nayi wani irin canzawa, nayi kyau" ba kadan ba. SKullum idan 'na tashi nake tsab tace gidana na fara da abincin karyawa wanda shayi ne da biredi wani lokaci ya ce da kwai zai ci wani lokacin kuma ya ce da sauran farfesun dare zai ci. Kasancewar kusan kullum yana kawo kaji ko kuma kifi ko nama ya dai danganta da abin da yake so sannan na fara gyaran dakin kwanciyarmu wanda kullum na gyara shi sai na tsaya na kare mishi kallon saboda sha'awar da yake bani. Kullum kuma burina Umma tazo ne taga inda nake kwana amma har yanzu wajen watana daya shiru bata zo ba. 51 Sai na tsabtace toilet din da ke cikin bedroom din na kalkale tiles din bango "zuwa na kasa yayi tas, sannan na fito falo." "Nan ma haka kafn na shiga kicin, nan" ma na gyare shi na goge tiles din shi nayi wanke-wanke na goge cabinet sannan na fito na wanke tsakar gidan nan tas. Nasa sandar goge-goge nayi mopping din ko ina. Bana gajiya saboda yadda yin hakan yake yi mun dadi a cikin raina. Bayan duk na gama hakanne sai kuma na dauko kayanmu da muka cire na wanke su na goge. Ban cika yin abinci da rana ba saboda "baya dawowa da rana sai dare, don haka" sai kawai na sha shayi ko dan wani abu mai sauki sai da daddare ne nake yin girki Kullum cikin raina dai ina tsara yadda "zan rinka tafiyar da al'amuran gidana ne," idan na koma Makaranta. 52 A yau kuma nayi nufin yi mishi maganar tunda idan ba batan lissafi nayi "ba, to ina cikin wata na uku ne da aure." Sai da na gabatar mishi da abincin shi shinkafa da miya da salad na ajiye mishi "kunun zaki a gefe, sannan na koma na" zauna na ci gaba da kallon abinda ake yi a TV. Ishak ba mutum ba ne mai hira zan iya cewa abinda aurenmu ban sani ba ko da can kafin auren ban lura na gane hakan ba ne. Kullum dai idan zai dawo to ka'idarshi zai yi guzurin Jaridar da zai karanta ta ranar kafin zuwan shi wurin kwanciya. Idan kuma ya kwanta ranar ba shi da bukata ta to zai yi juyawar shi ne ya kalli bango nima nayi tawa kwanciyar ban kuma taba daukan hakan a matsayin wata matsala ba. Idan kuma ranar sati ne to kuwa haka "zai wuni yana kallon Jaridar shi ta sati," 53 idan kuma yamma tayi to zai fita ba zal dawo ba sai sha daya ko da rabi idan ya yi dare kuwa har sha biyun dare. To zan iya cewa wannan ita ce babbar matsalata da shi amma nauyinshi ya hana ni yi mishi magana. Sai dai maganar Makaranta ta ce a yau nayi nufin yi mishi magana saboda tafiyar lokaci. Saida ya gama cin abincin shi na kwashe kwanukan sannan na dawo na zauna can gefe na ce mishi cikin ladabi. """Don Allah ina so ne nayi maka wata" "magana idan ba za ka damu ba."" Ya dan" kawar da Jaridarshi daga kan fuskarshi ya "ce, ""Uhum ina jin ki.""" "Na ce, Dama maganar Makaranta ta" nake so nayi maka don yanzu na kai wata shida bana zuwa kada lokaci ya yi ta "tafiya.""" Yayi shiru zuwa wani lokaci da har na fara gundura da shirun nashi sai da ya 54 daga Jaidar ya ci gaba da dubawa sannan "ne ya ce ""Ba yanzu ba.""" "Na ce, Na'am!"" saboda yanayin da" amsar tashi tazo mun. Na ce miki ba "yanzu ko da matsala ne?""" "A hankali na ce, ""A'a babu."" Ya ce," "To madallah."" Sannan ya ci gaba da" kallon Jaridarshi. Daki na shiga na kwanta sai dai na kasa hana kaina kukan da yazo mun. Ba yanzu ba sai yaushe? Sai dai ba zai yiwu nayi mishi irin wannan tambayar ba. To waye zai tambayan mun shi? Ai sai daini din don kuwa ni ce nake zaune tare da shi. Hakan ne yasa ni mikewa daga kan gadon na fito falon na sake neman wani wuri na zauna. Na ce To yaushe ka ke ganin ya dace kenan na koma Makarantar? Ya janye Jaridar daga fuskarshi ya zuba mun ido yana kallona. 55 """Ke! Tashi ki bani wuri, ke kuma" wacece da za ki yi mun titsiye? Shashashar yarinya kawai. Wadanda ya zamarwa dole ma ba su "tsaya sun ga kin yi karatun ba ballantana ni.""" Mikewa na sake yi na hau gado na kwanta. Har aka kira assalatu ban runtsa "ba, kuka kawai nake yi kukan sharbe." Wane irin abu ne kuma haka meke faruwa ne? Shin me Ishak yake nufi? Na mike daga kan gadon na nufi bayan gida nayi wanka sannan na dauro alwala. Har yanzu barcin shi yake yi cikin kwanciyar hankali. Nayi sallolina na nafila raka'a biyu sau uku sannan na zauna na dan yi karatun Kur'ani.kafin aka fara kiran sallah. Lokacinne ya tashi ya shiga bayan gida yayin da ni kuma na tada sallar nafila ta "raka'atul fijri, sannan nayi sallar asubahi." 56 Na durkusa na gaishe shi kamar yadda na saba sannan na shiga kicin don kokarin yin abin karyawa kada ya makara. Ba tun yauba na sha yin tunanin shiga gidajen makwabta da muke unguwa daya da su saboda mu'amalla da Jama'a. Ban kuma samu damar yin hakan baa duk kuwa da cewar su sun shigo ba sau daya ba ba sau biyu ba. Haka nan ma yayan su. Baran ma dai Hindu wacce nasan ko bata gime mun ba to zamu yi sa'a da ita don a yanzu a SS 2 take kenan da muna tare a Makaranta. Don haka ko a yau da nayi nufin na sha kunun gyada da safe sai na tashi domin na leka sudaga nan kuma na samu wanda zai siya mun gyada da kamu. Ba a yi hanzarin tambayar Ishak ba amma a a raina sai na kuduri aniyar idan ya dawo daga wurin aiki sai na sanar da shi. 57 sNa fito na rufe ko'ina na cikin gidan sannan na nufi gian su Hindu wanda yake kallon namu gidan nayi kyakkyawan sallama a tsakar gidan wanda hakan yasa Momy mahaifiyarsu ta leko. """A'a'a Amarya ce yau a gidan namu?" "To shigo daga ciki mana."" Na bita muka" "shiga falon na zauna a kasa ta ce ""A'a" "zauna a kan kujera mana.""" Na mike na gyara zamą a kan kujerar sannan na gaisheta cikin girmamawa ta amsa tare da yin yar hira kadan wacce mafi yawancinta kan al'amuran gida ne. "Na ce, Hindu bata nan ko? Ta ce, ""Eh" "ba su dawo daga Makaranta ba, saboda" "tana tsayawa lesson.""" Ban. wani tsaya bata lokaci ba na mike don dawowa gida har kofar gida ta rako ni da yar leda a hannunta ta miko mun nayi godiya na nufi gida ina tunanin inda zan samu abin da na fito nema. 58 Wanda ba zai yiwu kuma na kara yin gaba ba. Wani abin mamaki shi ne ban lura na hangi motar Ishak ba sai da nazo shiga gida. Wani irin mummunan faduwar gaba ne ya same ni sai dai kawai sai naga to ai ba nisa nayi ba sai nayi mishi bayani. "Na shiga dakin cikin murmushi na ce," "Lah ban yi zaton zaka dawo yanzu ba, shi" "yasa... "" kan na gama maganata ya ce" """Dama idan na fita yawon ki ki ke tafiya?" lye? Inà ki ka je? Na ce miki daga ina ki "ke, kaga mun shegiya 'yar matsiyata." "Raina yayi mummunan baci na ce ""A'a" "ni kada ka sake zagina ka hada da iyayena," "me nayi da zafi haka?""" "Ya ce, ""An zage su matsiyata me za ki" yi iye na ce me za ki yi idan an zage su su "din banza su din wofi.""" Wannan shi ne na farko kuma na karshe na gaya miki idan ki ka kuskura ki ka sake 59 ita na dawo gidan nan ba kya nan sai nayi "miki abinda ba ki yi zato ba.""" Ya juya ya fita ina jin shi ya sakala kwado ya rufe gidan ta baya. Na zauna a wurin nayi kuka irin wanda ban taba yi ba a rayuwata. Dama haka auren yake? Na san iyayena talakawa ne wadanda ba su da komai amma ba haka yana nufin Ishak ya zage su ba ne tamkar sun dauke ni sun ba shi ni auren da ko wata biyar bai yi ba. "Tausayin Babana ya sake kama ni," mutum mai kokari da bai taba zuwa kofar "gidan wani neman taimako ba, ya dogara" ga Allah ne da kuma dan abinda yáke samu a wurin aikinsa. Hakanne yasa mutanen unguwarmu har da ma su kudin suke matukar girmama shi. Na lallaba na mike da nufin shiga kicin nayi girkin abincin dare. Na kuwa samu ya kawo wani cefanen abinda a yau ya daina birge ni. 60 "Na dauko na fara rarrabawa, ina ajiye" "komai a wurinshi, na zaro ledar da naji" "danshi, kifi ne manya masu kyan gaske" guda uku. Na bude frizer na ajiye guda biyu na fara gyaran dayan da alama shi yake son ci da daddare. Farfesun kifi nayi mishi wanda bai yi "romo mai yawa ba, sai nayi coconut fried" ice na ajiye a food flask ganin har na gama bai dawo ba duk kuwa da daren da nayi sabodamakarar da nayi wajen farawa. Har nayi sallar Isha'i shiru bai dawo ba. Bai saba yin dare a waje ba idan ba kwanakin sati ba ne wato Asabar da Lahadi. Tun ina sa ran dawowan shi har na hakura na hau gado na kwanta. Can cikin dare na ji motsin shi. Na mike na same shi tsaye yana cire riga da niyyar canzawa don kwanciya. 61 Na fito falo na dauko abincinshi na "kawo mishi, bayan nayi mishi sannun da" ko kallona bai yi ba. Na ajiye abincin da farfesun na koma gefe na zauna yadda na saba yi. Ya gama shirin shi ina tunanin zai zauna yaci abincin ne sai kawai naga ya hau gado ya kwanta. Na dan daure na ce ba za ka ci abincin ba ne? Bai ce mun komai ba duk kuwa da nasan idonshi biyu saboda haka sai na tattara na kai kicin na zuba cikin wani abin na saka a fridge don gudun kada ya lalace. Na dawo dakin na gyara na sake kwanciya sai dai a yanzu kam ban samu yin barcin ba. Kan kace meye wannan sai na fara jin saukar numfashin Ishak yau ma haka na kwana ban yi barci ba. Sai dai duk tsawon lokacin tunani nake yi na ya kamata naje gida naga iyayena 62 haka nan na sanar musu da abinda yake faruwa. Hakanne yasa da na gama gaishe shi da safe na roki ya bani izinin zuwa gida bai bani amsa ba haka nan bai tsaya karyawa ba yayi ficewarshi. Da wani bacin ran na wuni wanda yau duk da dadin da gyaran gidan nan yake yi mun yau haka ya zauna sai da naga La'asar tayi sannan na mike don shirin abincin dare. "Shaf, na mance da abincin jiya da Ishak" "bar ci ba, don haka na nufi kofar gida don" na samu yaran da zan baiwa abincin. Sai dai a kulle na ganshi ta baya. Sai kawai na dawo na kama aiyukana. Kamar yadda jiya bai dawo ba sai tsakar dare haka nan yau ma. Sannan bai ci abincin ba ya sake kwanciya. Gari ya waye na sake yi mishi maganar zuwa gida yau ma bai ce mun "komai ba, ya fita ba tare da ya karya ba." 63 Na dai lura idan nace zan zauna ina "kunci da bakin ciki to zan nakasa kaina," sai kawai na nemi samun saukin damuwata ta wata hanyar. "Ni ba ma'abociyar kallon fim ba ce," amma yau sai na shiga laluben drawer da ke jikin TV stand din don neman kaset din kallo. s1Na yi dace da wani mai suna Why did I get married too?' sunan shi ne ya dauki hankalina da na saka kuma sai na samu kaina da nutsuwa don yin kallon. Kawaye ne guda uku sai dai kowacce da irin matsalar aurenta. Na dan ji dadin yin kallon don ya rage mun damuwa. Ban ki yin abinci ba don ganin ba ya ci kuma ina ta tara shi a fridge. Tuwo nayi miyar kubewa bushasshiya na ajiye kamar yadda na saba. Ban kwanta ba zama nayi na jira dawowarshi. Shima yau bai vi dare sosai "ba, don kuwa sha daya da kwata ya dawo." 64 Babu irin tunanin da ban vi ba amma ina kasa sanin abin vi a kan matsalar. Zaman auren da nayi ba mai yawa bane ballantana har nayi wayon zama da miji. Amma sai na kudure a raina a yau idan ya dawo zan san abin yi akai shi ne kuma na ba shi hakuri. Ganina da yayi zaune a falon bai tsaya ba wucewa yayi zuwa cikin daki yadda ya saba. "Na bishi na sake yi mi1shi sannu, sannan" na tsugunna a gefe na ce Don Allah idan nayi maka laiti ne ka yafe mun abinda nayi maka. Ba kuma zan sake ba da ikon "Allah.""" Wannan magiyar da nayi mishi ita ce tasa shi ajiye rigar barcin da ya dauko zai saka ya kalle ni. To kenan har kin isa na zage ki ki rama. Iye! Ke kuma wacece a cikin mata? Duk da bacin ran da maganar tashi ta sa ni wacce a take kuma na kasa danne 65 hawayen da suka fara zuba a idona hakurin na ke ba shi kafin daga baya ya ce "ya wuce amma kadá ki sake ko da wasa.""" "Hakan bai sa yaci abincin ba, amma bai" dame ni ba. Na hau gado na kwanta. Washegari na lura ba shi da niyyar buga sammak0 irin na sauran kwanakin. Don haka na shirya mishi abin karyawa. Ya fara ci kenan ya kalle ni Na baki mintina goma kI shirya na sauke ki a "gida.""" "Ban san sanda na fara godiya ba, duk da" cewar mintina goman ba 1sa na za su y ba. Na riga nayi wanka don haka atamfata na dauko Exclusive na daura da gyalenta "da set din takalmi da Jaka 'yan taly, sai" yan canji na da ba su fi Naira dubu daya ba. Da wasu yan abin kwalam da nake ajiyewa idan ya kawo sun ban sha'awa na karewa dakin kallo na rasa abinda zan kaiwa Umma. 66 Don haka na bude akwatin aurena da zannuwa suke ciki na dauko mai kyau na fara nadewa ban san ya shigo ba ya ce """Me za ki yi da ita? """ "Na rasa abinda zan ce, ya ce To" mayar. Na sake budewa na mayar gwiwata a sanyaye. A kofar gida ya ajiye ni na shiga rabona da gidanmu watanni biyar. Haka na Umma da Babana. Gani na rinka yi kamar ba ni ba. Haka nan Umma ta rinka ina ta ka saka da ni. Ta zuba mun ido ko kyaftawa bata yi. Ni kuwa kunya duk tà kama ni. Farin ciki mai yawa Umma ta nuna na ganina. Ita ma na ganta tayi kyan gani ba kadan ba. Na bude Jakata na ciro ma su Tasi'u Bueno cakulet da biskit kwali biyu na "mika musu suna ta murna, wanda iyakacin" kuma abinda na riko nusu kenan. 67 Ni ce na tashi yau ma nayi mana girkin rana muna ta yar hirar mu da Umma. Wacce ganin irin murnar da take yi ne yasa ni kasa gaya mata mnaganar da ke cina a cikin raina. Wato maganar Makarantata. Ba zai yiwu na dakushe mata wannan farin cikin da take ciki na ganina ba. Karfe hudu da rabi daidai sai ga sallamar dan aika wai na fito na dauko gyalena na zo inda Ishak ke hakimce a "cikin mota na dan risina ta gefe na ce ""Ai" na dauka zaka shigo ku gaisa da Umma ne ko da ba za ka bar ni na jira dawowan "Babana ba.""" "Ya ce, A'a ba zan shiga ba, fito" "kawai. Na ce, ""To."" Na koma na ciro ""yar" Naira dari taran da nake ta nuku-nuku na "kasa bai wa Umma, na mikawa su Tasi'u" nayi wa Umma sallama na fito zuciyata kamar ta fashe. 68 "Muka iso gida ya ajiye ni ya juya, ni" kuma na shiga kicin da nufin dorà abincin dare. Tunani nake yi na yadda zan rinka "taimakon iyayena, don kuwa ba zai yiwu." na zauna a haka ba. Ishak ba ya bani ko sisi zan iya cewa tun bayan aurena a shi sile biyar bata shiga tsakanina da shi ba. Haka nan duk wani abu na amfanin gida shi ke kawowa bani da wata hanya da zan bi na samu kudi da zan iya yi musu wani abu. Ya zama mun dole nasan abin yin. Tun daga ranar da na samu matsala da Ishak kan zuwana gidan su Hindu ban "sake ba, sai dai da yake ya daina kulle ni" "bayan na roki yayi mun hakan, to ita takan" shigo. Mafita daya ce shi ne na dan rinka taimaka musu da dan abinda za su ci "wanda shi kam ina da shi, don haka da" Hindu ta shigo na roke ta ta gayawa Mominsu ina son aikanta gidanmu. 69 Na debi shinkafa mudu biyar da su "Taliya da cous-cous, man gyadan (Turkey)" da soyayyen nama da sauran abubuwan amfani na hada mata rigijif ta kai ta dawo. ow Zuciyata tayi mun dadi naji sanyi na dan yi wani abu. Sai dai babban abin "takaicin shi ne, bayan kwanaki biyu kawai" da faruwar hakan sai naji wa'azi a Rediyo ana yi na matar da ta yi wa miji kyauta da "abinci ba tare da ya sani ba, irin" hukuncinta. Sai dai har idan ta tabbatar da shi din "ma zai yi hakan, to sai tayi da nufin Allah" ya ba shi ladan. Nayi shiru a raina ina tunanin to shi zai yarda da hakan ko kuwa shisshigi nayi? Ba zai yiwu na gaya mishi ba kada na Ballo "wa kaina liki, tunda dai an ce haramun ne" gara kawai na nemi hanya da zan nemi "nawa ita ce ta hanyar dinki tunda na iva," kuma ina da keken yin dinkin. 70 Sannan unguwarmu sabuwar unguwa "ce, da alama za a samu alheri idan mutum" ya ce zai yi wata sana'a. Washegari asabar don haka Ishak yana gida da rana. Sai da na gama aikace- aikacena na gida sannan nazo falon da yake na zauna na fara yi mishi magana kan tunanin da nayi na dinki tunda na iya. "Amsar da ya bayar a gajarce ce, ita ce" idan ina gidanshi to ba zan yi dinki ba. Ba zai lamunci irin wadannan abubuwan na nuna karanta ba. "Ba ni da abin fada, don haka naja" bakina nayi shiru. Kamar yadda shima ya yi. Bani da wani abu da nake yi da ya wuce aikin gida da girki. Wannan a yanzu nake rayuwa akai babu abinda yafi damuna irin tsayawar karatuna. Ba zan ce Ishak ya yaudareni da "1yayena ba, don kuwa matsayj shi ya" wuce hakan mijina ne. 71 Sannan babu wanda zai kalle ni ya ce Ina da matsala don kuwa a bayyane yake na samu canji. Kana kàllona ka san ina "cikin wadata," Sai dai to iyavena fa? Wannan shi ne babbar matsalata. Yau ma zama nayi da nufin jiran dawowar Ishak na nemi i2inin zuwa gida a washegari don kada ya ce ban fada mishi da wuri ba. Ina matukar kewar Babana saboda zan iya cewa tun da aka yi aurena rabona da "shi, a yanzu kuma wata na bakwai nake" ciki. Na jira shi har na gaji na hau kan doguwar kujerar dake dakin na kwanta. Bai shigo ba sai karfe goma sha biyu daidai. Na mike zaune saboda jin motsin da nayi na kuma yi mishi sannu' ya amsa: Ban tsaya zancen kawo mishi abinci ba don 72 kuwa ma a yanzu idan ya dawo ba yaci ko "na kawo mishi," Ban yi mishi maganar ba sai da ya kammala shirin kwanciya sannan na fara kokarin yi mishi maganar. Bai bar ni ba saboda dago mun hannu da yayi alamar dakatawa. Wai ke ba ki da wata magana ne sai ta gidanku? Mits! Yayi tsaki ya yi kwanciyarshi. Sai mutum ya wuni aiki amma idan ya dawo gida a maimakon a barshi ya huta wai sai a tasa shi a gaba da surutan banza. Ya ja abin ruhuwarshi ya kwanta. "Na riga na saba da dabi'un Ishak, don" haka a yanzu ba su cika damuna ba. Washegari har na gama mishi shirinshi na karyawa da sauran abubuwan shi na tafiya aiki a raina ina tunanin zai yi mun maganar zuwana gida da nayi mishi bai ce komai ba ya tafi. 73 A duk 1ökacin da ya tafi aiki na kan "dauki wayata na kira Hindu ta taya ni hira," hakan ne yasa muka yi wata irin shakuwa ba kadan ba. Hindu wayayyiyar yarinya ce ba kadan "ba, haka nan yanayin irin gidajen da muka" tashi ma ba daya ba ne. "Don kuwa kamar yadda nake ""yar talaka" ita kuwa ya ce ga babban Ma'aikacin "Gwamnati, Mominsu ma wayayyiyar mace ce." Wunin da nake yi da ita a cikin gida yayi matukar taimaka mun kwarai da gaske kan al'amurana. Ban taba zama na "fada mata wani abu game da mijina ba," amma sai ta gane hakan. "Wanda yasa ta yi mun magana, ban" saurari abin ba don ganin da nake yi mata na cewa ita din ko da muke kusan sa'o'in juna ita ba macen aure ba ce. 74 Haka nan kullum Umma tana gaya mun na rike sirrina. Don haka ko da ta yi mun magana murmushi kawai nayi. An dan dade kafin na samu Ishak ya bani izinin zuwa gida. na zaune cikin motar daidai ya tsaya a kofar gidanmü na "ce mishi ""Ko za ka bar ni ne zuwa dare" "don na gaisa da Babana?""" "Bai ce komai ba, nima kuma ban sake" yin magana ba. Hira sosai muka yi da Umma ina mata korafin ba a taba kawo min su Tasi'u ba "Tayi murmushi ta ce, ""To sai ki gayawa" "Babanku tukunna. Na ce, ""To."" Babana" ba karamin jin dadin ganina ya yi ba. "Yayi ta murmushi ba iyaka, yana ta dan" yi mun tambayoyi ina ba shi amsa tare da jaddada tambaya daya da yake yi min. Babu matsala dai ko Hauwa'u? Na "ce, ""A'a babu."" Ya ce, ""To ki yi ta hakuri" "kin ji, shi zaman tare hakuri ake yi.""" 75 "Na ce, ""To Baba."" Kamar na danne" abinda ke damuna sai dai na kasa. Na ce """Baba sai dai maganar Makarantata ne har" yanzu shiru. Nayi mishi bayanin yadda muka yi da "Ishak ya dan yi shiru zuwa can ya ce, ""Too" babban al'amari a wurin mu ai shi ne ki zauna lafiya a dakin aurenki. Kuma ga dukkan alamu kina da kwanciyar hankali. Ita maganar karatu tana zuwa ne daga baya. Amma tunda dama can yasan da maganar ina ganin bari ni da kaina nayi "mishi tuni muji abin da zai ce.""" Tun kan Ishak yazo daukana nayi wa Babana magana akan ina bukatar su Tasi'u "su zo min kwana biyu, ya ce ""To.""" Ba a wani dade ba rannan kawai da rana sai ga Yaya Auwalu da su Tasi'u da dan kayansu a kullin leda. 76 "Murnata bata boyuwa, na rasa inda zan" ajiye su. Nan da nan na shiga kicin na fara ajiye musu dan abinda nake dashi. Muka yi hira da Yaya Auwalu sosai daga ni kuma ya yaba da inda nake don kuwa bai taba zuwa ba shima sai yau. Ya jima sosai kafin yayi mun sallama "ya tafi, ya bar mun Tasi'u da Sadisu akan" za su y1 mun sati guda. Muka wuni muna harkokinmu ba kadan ba cikin raha da jin dadi. Hindu kuma tazo ta debe su ta kai wa Mominsu suka gaisaa suka dawo tare da kaninta Abubakar. Da daddare kuwa hira muka sha ba "kadan ba, nayi dariyar abubuwan da suke" bani labari har na gaji. Rabon da naji dadi irin a yau har na manta. Ba su yi barci da wuri ba saboda kallon da suke yi sai wajen karfe goma na dare kafin nan kuwa ni kaina na gaji. Nayi wanka na gyara na hau gadona na "kwanta, kan ka ce meye har nayi barci" 77 abinda ya hana ni jin dawowar Ishak don kuwa ban farka daga barci ba sai da naji "kiran sallar Asubahi," Da sassafe Ishak ya fita wanda shi ne dalilin da ya sa ban tuna gaya mishi zuwaan su Tasiu ba sai bayan tafiyarshi. A yau mna wuni muka yi muna harkokinmu. Nayi mana abinci mai dadi dafadukar taliya da taji hanta ga kuma "farfesun kayan ciki, don kuwa nasan babu" abinda suke so irin taliyar. Yau ma sai da muka yi hirarmu wajen karfe goma sannan na shinfide su a dayan dakin na gyara musu komai na fito na hau gadona ina tunani a raina irin kewar da zan ji ranar da su Tasi'u za su koma gida. Idan da da hali da na roki Umma ko Babanmu su bar mun su Tasi'u. Kwanciyar nayi da nufin na yiwa Ishak "maganar idan ya amince to, tunda muna da" wadatar waje. 78 Yau ma ban san sanda ya dawo ba saboda barci mai nauyi da ya dauke ni. Can cikin barcina naji kamar ana kirana. Na bude ido cikin sauri saboda gane ba mafarki nake yi ba. Sadisu ne. Sai dai ba ni kadai ce na tashi ba har da Ishak. """Menene ya faru Sadisu? Ya ce," """Aunty zan yi fitsari ne."" Na mike cikin" sanyin jiki saboda irin kallon da Ishak "yake yi mun, na dawo dakin da suke nasa" shi a bayan gida yay. Na sake shimfide shi ina kara jaddada musu in sun ji wata bukata ba sai sun tashe ni ba su shiga bandaki kawai su yi. Na kuma gaya musu hakan tun kafin su kwanta amma kuma sha'ani irin na yaro. "Na shigo dakin, Ishak yana zaune a kan" bakin gadon nayi nufin wucewa naje na "kwanta, duk kuwa da sanin da nayi na" cewa ni yake jira. 79 "Sai, dai yanayin shi da ke sani cikin" "faduwar gaba. ""Zo nan. Abinda yace mun" kenan. Na nemi wuri a kasa na zauna. Me wadannan yaran suke yi mun a gida? Lafazin da yayi amfani da shi yasa na rasa "abunda zan ce, ko kuma ta inda zan fara." "Cikin daga murya ya ce, ""Ba ki ji" "abinda na ce ba ne ko ya ya? Na ce, ""Eh" "naji, ba ka gane su ba ne? Su Tasi'une fa" da Sadisu kannena. """Hala kin ga alamar makanta ne a tare" "da ni ko? Nayi maza na ce ""A'a ba haka" "ba ne.""" Idan na ce zan tsaya fadin irin tashin hankalin da na gani ranar a tare da lshak to nayi karya. Duk kuwa da irin bayanan da nayi mishi wanda ko saurarona bai yi ba. Maganar kuwa da muka wayi gari da ita "ita ce, ta bai yarda su sake kwana mishi a" "gida ba, maza-maza na sa a mayar da su" kwana biyun da suka yi ya isa haka. 80 Bai ci komai ba ya fita. Bai bani kudin "motar mayar da su ba, duk kuwa da yasan" banida ko asi. Nayi iyakacin kokarina wajen juriya kada 'yan yaran nan su fahimci wani abu. "Tasi'u bai fi shekara shida ba, shi kuwa" Sadi yafi uku amma bai cika hudu ba. Yan kannena da nake da su amma wai Ishak ba zai iya mu'amalla da su ba. To sai da wa? Ko da yake ni din ma da ya aura ga irin yadda yake tafiyar da ni. Sanin hakan da nayi bai hana ni bakin ciki mai yawa ba. Biye mishi zan yi? Ko kuwa dai zan nemi mafita ne? Na gama ayyukana nayi lullubi tare da rufe gidan na shiga gidan su Hindu. Mominsu tana daki nayi sallama na "shiga, na bar su Tasi'u a wajen yara suna" wasa. Ban boyewa Momi komai ba. Ta tashi ta shiga daki ta dauko kudi "masu yawa ta bani ta ce ""Ki koma gida" 81 idan Hindu ta dawo zan turo miki ita sai ki bata ta mayar da su gida. "Kiyi hakuri, ki kuma yiwa mijinki" iyakacin biyayyar da za ki iya idan har bata sabon Ubangiji ba ce. Kada ki să damuwa a ranki ko kuma ki "ce wai za ki yi fushi da shi kin ji ko?"" Na" "ce ""Eh.""" "Na dawo gida na ci gaba da kwanciya," don kuwana rasa kuzari tunani iri-iri a cikin raina. To da Ishak ya yi mun haka a kan kannena shi nashi 'yan uwan baya tunanin za su iya zuwa ko kuwa idan suka zo ya ya yake so ayi? "Na sake yin shiru, to a zaman da nake" yi ma zan iya cewa bai taba yi mun wata magana ta game da 'yan uwanshi ba kamar yadda ban taba ganin wani yazo ya ce shi abokin shi ne ba. 82 Nayi saurin mikewa na zauna ina wasu "yan anane-tunane a raina, tambayoyi iri-" iri da nake bukatar na samu amsarsu... Sallamar Abubakar kanin Hindu ne ya katse mun tunanina. Ya miko inun bakar "leda ya ce ""Ga shi in ji Momi. Na karba" ina dubawa. Littattafai ne na Hausa da alama ta bani ne na samu na karanta ni ba ma'abociyar "karatun ba ne, amma sai naga barı na ajiye" kada ta ce na gwasaleta. Na mike don samarwa kaina abinda zan Ci tunda yamma ta fara yi. Chives kawai na soya da kwai naci na sha shayi aka: sannan nayi sailar Magriba. Ina idar da saliah sai kawa naji "sallamar shigowar Ishak, mamaki ne yayi" "Ihatukar kama ni, zan iya cewa tunda, aka" yi aurenmu ya koma aiki bai taba dawowa kafin ayi saliar isha'i ba. Asali na ya dawo karie tara yayi sauri. Na mike ina nade dardumar sallah tare da 83 "yi mishi sannu da zuwa, bai amsa ba don" dama nasan hakan ne zai biyo baya. Saboda zai yi mun abu wanda zai sani bakin ciki amma shi ne kuma mai yin "fushi idan har ba hakun na bashi ba, kuma" to ba zai taba saukowa ba. Sai dai a wannan tunda dai nasan ban yi "mishi wani laiff ba, to nima ban shirya" bada hakurin ba. Na shiga kicin cikin sauri nayi mishi "abinda zai ci, fried rice da farfesun danyen" kifi wanda duka aikin bai dauke ni awa guda ba. Na kawo na ajiye mishi. Sai dai ban ganshi a falon ba. Na shiga cikin dakin kwananmu nan ma hakan. buruntun da naji a daya dakin ne yasa ni lekawa. Gyarawa yake yi yana kakkawar da wasu abubuwa duk da dai har da ba a wani amfani da daki banabarin shi da datti. Ine tsaye ina kallon 'irin gyaran da yake yi na shiga daki na dauko wani zanin 84 gadon na shimfida akan gadon na sa tsintsiya na share dakin. Bai ce mun kala ba ya shiga asalin dakinmu ya fara kwaso kayan shi yana maida su daya dakin. Aikin da ya dauke shi har karfe goman "dare, don kuwa tsinke nashi sai da ya" "dauke ya kai shi daya dakin, kuma ya" gyare shi tsaf ina zaune a. falon ina kallonshi. Ya shiga bandaki yayi wanka ya bada tea yasha bai ko kalli abincin da na ajiye mishi ba ya shiga sabon dakinshi ya kwanta. Ba sai na jira an yi mun wani bayani ba nima da kaina na fahimci abinda hakan "yake nufi, nima sai na shiga tsohon" dakinmu ko kuma na ce na asalin na kwanta. "Al'amarin Ishak ba na karewa ba ne," kuma na lura idan na ce zan zauna ina 85 kwana ido biyu saboda bacin ran da yake sa ni to zan wahala ba kadan ba. Kwana da kwanaki muna cikin wannan hali ya mayar da wancani dakin na shi nima kuina ga nawa. Tsakanina da shi gaisuwa ce ta sate ta dare kuwa bana ma sanin sanda yake dawowa. Nayi iyakacin addu'o'in da zan yi a kan hakan ban ga canji ba. Gyaran daki nake yi lokacin da na sake cin karo da littattafan Momi. Na bude daya na fara karantawa. Wunin ranar bata kare ba sai da na gama shi tas na dauko na biyun shima haka. Cikin kankanin lokaci sai na koma wurin Momi neman kari. Kullum da safe idan na gama aikina na gida sai na zauna nayi ta karatuna bana tashi sai sallah ko cin abinci. Sai ya zamana na koyi abubuwa in-iri wadanda wani bai taba zaunar da ni ya koya mun ba. 86 Abubuwa da suka danganci zama da "miji, zama da mutane, girki, kuia da kai." "gyaran jiki, kai abubuwa daban-daban." "Idan nazo wani wajen naji takaici, wani" "wajen nayi dariya, wani wajen naji tausay1," wani wajen kuwa naji kamar labarina ake bayarwa da' Ishaf. Don haka ga abinda zan yi. Damuwata "tayi matukar raguwa, na kuma y1 niyyar" yin amfani da shawarwarin da Marubuta suke bayarwa da suka danganci zama na aure na kuma Zubar da na banza. Tsawon sati biyun da muka yi a hakaa "muka yi ta da Ishak gaisuwar safe, dn uwa" da daddare kan ya dawo nayi barci. Amma na kuduri aniyar gyaran aurena don na fahimci ba haka ake auren ba. Aure yana yin nasara ne idan har akwai kyakkyawar alaka ta addini da "zamantakewa a tsakanin ma'aurata, uwa" uba: kuma soyayya ta gaskiya da take haifar da yafiya a kowanne lokaci. 87 Sannan Annabi (S.A.W) ba haka yayi "Zama da nashi 1yalin ba, don kuwa babu" wani mutum da zai nunawa matarshi kwatankwacin irin soyayyar da ya nuna ga iyalinshi. "Babu kyamata, babu hantara bare" tsangwama a cikin al'amarin aure. Miji da mata (ma'aurata) duka su baiwa junansu "lokaci na hira, kulawa, da tausayawa" wacce suke haifar da karin soyayya da fahimta a tsakani. Na jawo akwatin kananan kayana na bude ina dubawa tare da tunanin wacce zan yi amfani da ita. Duk da ina jin kunyar yin hakan amma idan har zai kawo mun gyara ga aurena to ko meye zan yi idan ba sabon Ubangiji ba ne. "Rigar bata wuce mun iya gwiwa ba," haka nan shara-shara ce don kuwa kusan koma: nawa a bayyane yake. 88 Na gyara gashin kaina wanda na wanke shi da man wanke gashi na (Trichup)na kuma shafe shi da kayan gyara iri-iri. Duk da ba wani tsawo ne da gashin nawa ba ya yi kyau ba kadan ba. Ga jikina da yayi luwai-luwai saboda jin dadi. Maganar gaskiya ita ce Ishak ya wadata ni da abubuwan jin dadi da suka danganci abinci da na gyara. Sai dai a yanzu na fahimci ba su ba ne masu muhimmanci wanda bai bani ba shi "ne komai, wato soyayyarsa da lokacinsa." Na kuma kuduri aniyar nema ta hanyar da ta dace. Na dawo falo na zauna na ci gaba da "yan karance-karancena, don kada barei ya" dauke ni. Yau sha daya saura kwata ya dawo. A lokaci na dawowar Ishak kuwa to ya dawo da wuri. Ya shige dakinshi ban ce mishi komai ba kamar yadda bai kalle ni ba. 89 "Gabana sai faduwa yake yi, kodai na" "kyale shi ne kawai? Kai a'a, na dauki" abincin da na ajiye mishi wanda ni kaina rabon da nayi girkin gidan da shi har na manta saboda ba ya ci. Nayi sallama a daidai. kofar dakin na shiga ba tare da na jira amsawar shi ba. "Wanka yake yi, don haka na zaunaa" bakin gadon ina jiran shi. Ya fito yana goge kanshi da karamin tawul nayi mishi sannu na kuma gabatar mishi da abinci. Bai ce mun komai ba sai da ya zo zai kwanta. "Ya ce, ""Ni fa kwanciya zan yi ko za ki" "je dakinki ne?"" Wani abu ne ya tokare ni a" "wuya, na mike na dawo dakina na kwanta." Don takaici sai kawai na fashe da kuka. Me ke faruwa ne'? Shin fita hanyar Ishak zan yi ko ya ya? Abu daya ne ya sani na ji sanyi da naje debe kwanukan abincin da na kai mishi naga ya dan ci. 90 Yau ma shiri sosai nayi mishi ban damu "da korata da yayi ba jiya, don kuwa gyara" nake so. Kuma na kuduri aniyar yi ta kowacce hanya in dai ba fin karfina abin ya yi ba. Ganin da nayi ya dan ci abincin yasa ni yin niyyar yi mishi wani abincin da nufin neman burge shi. Sai dai kash! Ban ma san abincin da yake so ba. To amma na cire wannan tunanin a raina kawai nayi abincina mai kyau kuma na burgewa na dan hada mishi da kunun zaki. Yau ma irin kwalliyar jiya nayi. Ban kuma yi barci ba har ya dawo. Dakin shi na bishi yana kokarin daure igiyar rigar barcinshi na ajiye tiren da ke dauke da food flask da sauran plate da cokula na Juya na je na dauko Jug din da na ajiye na kunun zaki na dawo. "Ina shigowa ya ce, ""Ki kwashe" kwanukan nan ki fita da su ba zan ci abinci 91 "a wannan daren ba."" Raina bai baci ba, na" "ce ""To ga kunun zaki mai sanyi ne sosai.""" Na kalli yanayin shi yana daga kwance hakan ne yasa na jawo kofi na tsiyaya mishi kunun na mika mishi. Kamar dai ba zai karba ba sai ya mike ya zauna ya karba ya kara miko mun kofin "na kara, mishi na tashi da niyyar fitar da" kwanukan abincin da ya ce ba zai ci ba. "Har na juya ya kira ni ""Zo ki zuba mun" "kadan."" Na ce ""To."" Kadan din na zuba" mishi na kara mishi kunun zakin sannan na jira ya gama na kwashe kwanukan na fitar. Ban koma dakin ba nawa na shiga nayi kwanciyata. Da sassafe ban koma barci ba sammako nayi na yi mishi abin karyawa cikin sauri na kawo mishi. Har ya gama shiri lokacin da na shiga. Kwalliya sosai nayi ya kalle ni ya kalli "tiren kayan karyawan. Na ce ""Ko za ka" "karya ne kafin ka fita?""" 92 Bai musa ba zama ya yi na zuba mishi ya karya har ya mike sai ya kalle ni """Unguwa za ki je? Na ce, ""A'a."" Ya ce," """Au to na dauka ko kin fara fita ne ba ki" "tambaye ni ba.""" "Na ce, ""A'a ba za a yi hakan ba."" Yau" wuni nayi cikin jin dadi a raina. wajen karfe uku da rabi yaron da ya saba aikowa da cefane yayi sallama. Na zauna ina duba cefanen yadda ya saba kawowa ne bambanci kawai shi ne kafar Saniyan da na gani a ciki. Na dauko "wayata duk da ban taba yin hakan ba, ban" kuma san ya ya zai dauki hakan ba. "Tana yin kara ya dauka, ""Lafiya?" "Tambayar tayi mun wani iri, amma sai na" "daure na ce ""Dama zan tambaye ka ne," kafar Saniyar da na gani za ka ci abincin "dare a gida ne?""" """Da can sauran cefanen da ake kawowa" "tambaya ki ke yi?"" Na ce, ""Aa."" Ban" saurari jin karashen maganar ba na kashe 93 wayar saboda abinda naji a cikin zuciyata na tamkar ina kokarin cusa kaina da yawa a wajen Ishak. Na hada kayan kawai na sanya kowanne a mazauninshi na kuma wanke kafar da niyyar yin miyar ganda da ita. Sai da na hada komai sannan na dora tuwon shinkafa. Na gyara kicin din na kammala komai a mazauninshi. Na dawo daki nan ma na kara kikkintsa abubuwan da suke bukatar kintsi. Sai da na gama ayyukan abinci sannan na shiryawa Ishak nashi abincin a inda na "saba, tare da sauran kunun zakin jiya" wanda ya kara jika. Yayi dadi ba kadan ba. Na shiga wanka na hado da alwala nayi sallar Magriba sannan na zauna domin nayi shafa. Yau ana idar da sallar Isha'i kawai sai ga Ishak shi kanshi ya gane nayi mamakin "hakan, sai da ya gama shirinshi kafin ya" fito ya zauna a falon. 94 """Kawo mun abincin nan wurin"". Na" shiga dakinshi inda na ajiye abincin nashi na fito dashi na zuba. Ba karamin abinci "yaci ba, don kuwa miyar tayi dadi ba" kadan ba. Na gama kwashe kwanukan sannan na dawo ina kallon tashar da ya kamo ta Aljazeera yana sauraron labarai. Sai wajen karfe goma sannan na mikKe don kwanciya. A raina nasan 1dan na ce zan jira Ishak ban san lokacin da zai kwanta ba. Haka nan kwanakin da nayi ina zaman jiran dawowarshi sun sa barci ya kama ni da yawa. Na gama shirina na zauna a bakin gado ina addu'o'ina da na saba yi na "kullum kafin kwanciya, sai ya shigo." """Zo mana."" Na mike na bishi.ba zai" yiwu na ce Ishak yana neman mata ba don kuwa ban gani da ido ba bani kuma da wanda zai fada mun. 95 Amma idan abin shi ya motsa mishi na fushi ko halin da ya saba yana jimawa ba tare da ya neme ni ba sat da tun da na samu na fara shawo kanshi ta wannan hanyar al'amuran gidana sun dan fara yi mun sauki. Na farko dai ya daina zaman karfe sha "daya ko sha biyu a waje, idan yayi dare to" "karfe goma, duk kokarin da nayi kuma na" ganin na gane ko na fahimci abin da yake yi a wajen na gagara. Tun da na lura da shi na gane ina janye "hankalinshi da irin shigar da nake yi mishi," kullum da irin wacce nake canzawa. nKo da ba ya cewa komai kuma ina gani a aikace. Sai dai abubuwa kullum da irin wacce take zuwa. Shirin da nayi musamman don naje gida "yau amma sam 1shak ya ki yarda, duk" kuwa da na gaya mishi cewa Umma zanje gayarwa saboda rashin lafiyar da take yi. 96 Har Hindu da Móminta sun je sun dubota amma sam shiya ki barina ya kuma ki żuwa shi ya dubota. Kullum sai dai na kirata a waya. Na záuna na buga tagumi duk wani abu da nake Rokarin ya rage mun Bacin rai ya ki. Da ya dawo kuwa ban fasa yi mishi abinda na saba ba. Amma gari na wayewa "da na kara rokonshi ya ki, ban ce mishi" komai ba. Yana fita sai na shirya na dauki gyalena burina bai wuce naga halin da Umma take "ciki ba, tunda ni dai zamana da ita ban" taba jin tayi wata rashin lafiya ba. Don haka hankalina a tashe yake ba kadan ba. "Jikin nata babu dadi sosai, amma duk" da haka ban zauna ba don kuwa kwata kwata ban fi awa daya ba na dawo. Na dawo duk da dai ban ji dadin ganin "da na yi wa Umma ba, na samu saukin" 97 damuwar rashin Zuwa dubata da.ban yi ba kwana da kwanaki. Ban dade da shigowa ba sai ga Ishak ya shigo ina yi mishi sannu bai tsaya amsawa ba sannan yanayinshi gaba daya ya canza. Ina ki ka je? Shi ne tambayar da ya fara yi mun. Nan da nan na kama inda- inda kan in san abinda zan ce tuni ya dauke ni da mari kauu! "Duka Ishak ya yi mun mai shiga jiki," sannan yayi ficewarshi ya komawurin aiki. Tun daga lokacin wani irin zazzabi yaa rufe ni wanda yafi kama da na bacin rai da bakin ciki. Bai dawo ba sai can cikin dare. Ina zaune a tsakiyar gadona har a lokacin kukana bai kare ba. "Washegari, kuwa ga zazzabi, ga karin" "tsamin jiki, Don haka ko, tashi nayi abin" karyawa ban yi ba. Sai da naji yunwa tana neman nakasa ni ne na tashi na lallaba na hada tea na sha. 98 Har dare yau ma ban samu nayi abinci "ba, don kuwa ko sallah da kyar nake iya" mikewa nayi. Haka nan yau ma da ya dawo sha dayan "dare bai leko ni ba, dakinshi ya shige da" gari ya waye ya yi sammako kamar dai dabi'arshi ta da. Nayi kukan takaici har na gaji nayi "shiru, Ishak wane irin mutum ne wanda ko" kadan bai san hakkin zaman aure ba? Amma kuma shi yana so ya sanyawa mutum dokar rashin adalci kuma yabi. Lallabawa nayi na shiga gidan su Hindu duk da sanin da nayi me hakan yake nufi idan har ya gane. "Momi tana ganina ta fara salati. ""Ba ki" "da lafiya ne Hauwa'u? Na ce, ""Eh Momi." "Hindu nake nema."" Ta ce, ""To je ki gida" "gata nan.""" "Hindu ce ta gyara mun gida ko ina," sannan na sa ta tayi mun faten tsaki don abinda zan iya ci kenan. 99 Na kuma yi matukar sa'a na samu na sha sosai nayi wanka na dan samu karfi a jikina. "Ita ce kuma ta taya ni nayi girki sosai," tuwon semovita miyar kubewa danya da taji tantakwashi da naman rago na' hada komai na ajiye wa Ishak a wurin cin abincinshi na shige daki na kwanta. Duk da dan (Paracetamol) din da na "samu na sha jikina bai yi sauki ba, sai" dada tsananta yake yi. Da sassafe na lallabo na shiga dakin Ishak yana zaune yana duba wasu takardu rabon da na saka shi a idona kwana hudu kenan yau. Yanayin da ya ganni a ciki bai hana shi yamutsa fuska ba. Wane irin abu ne haka ke wai wacce irin yarinya ce? Kin ga yadda ki ka yi wujiga-wujiga kuwa? Don Allah can wuce ki gyara jikinki kafin ki zo mun nan muryata tana rawa ta "ce, ""Ba ni da lafiya ne." 100 To idan ba ki da lafiya sai ki zo mun haka? Mits! Fita don Allah kije kiyi wanka "wawiyar yarinya kawai.""" Dawowa daki nayi na zauna sai da nasha kukana ya ishe ni sannan na mike na lallaba nayi wanka na saka doguwar riga mai gyale na zauna na hada tea din da zan sha. "Ruwan lipton ko birebi ban iya ci ba, na" koma na sake kwanciya don ko Paracetamol din da zan sha ba ni da shi ya kare. Ishak bai fito ba sai wajen sha daya kasancewarta Asabar. Sanye yake da Jeans blue a shirt long sleeve wuce muje. Hijabi na dauko muka fita zuwa asibiti. Muna zaune a gaban Likita bayan ya "tabbatar mana ciki ne da ni karami, ya" kuma rubuta mana prescription na magunguna wadanda muka karba a chemist din asibiti muka kamo hanyar komawa gida. 101 Tsananin zazzabin da ke damuna vasa ban ma lura na gane hanyar da Ishak yab ba sai da ya ce mun fita ki shiga ina jiranki. "Na duba naga a kofar gidanmu muke," cikin sauri na bude kofar motar na shiga. "A kicin na samu Umma taji sauki sosai, na" durkusa a gefen kicin din tana kallona. """Hala kema ba ki da lafiyar ne ko naga" "kin zama haka?"" ban bata amsa ba sai" kuka da na fara yi mata. """To menene kuma na kuka ai hakuri za" "ki yi ba a yiwa ciwo kuka Hauwa'u, ki" zama jaruma. Ban daina kukan da nake yi "ba har ta gaji ta.ce ""Ko dai kina da wata" "matsala ne?""" "Ban san me zan cewa Umma ba, ta gaji" "da tambayata ta ce ""Uhm, hakuri fa ake yi" "da komai ma da ki ka gani na duniyar nan," ballantana zaman aure. Kada ki sa wa kanki wata damuwa game da lamarin mijinki tunda dai bai 102 gaza miki da komai ba. Bai zama lallai sai ka samu yadda ka ke so a kowanne lokaci "ba, kin gane.?""" Na tashi na yi wa Umma sallama na fito muka dawo gida da Ishak. Wanda tsawon watanni goma sha daya da nayi da shi a matsayin matarshi ta aure bai sa shi ya yi tunanin rana daya yaje ya gaisa da iyayena da suka ba shi aurena ba. Har kuma da rashin lafiyar da Ummana tayi. Ciwo sosai nayi na wajen wata kusan "guda ina kwance ko aikin gida bana iyawa," sai Hindu ta shigo tayi mun. Ban samu saukin laulayin da naketyi ba "sai ana gab da sallah, ba ta fi sati biyu ba." A cikin akwatina na dauki atamfa daya da shadda mai laushi na bayar aka kaiwa Umma don ta dinka atamfar ta bayar da "shaddar don a dinka wa su Tasi'u, tunda" bani da kudin da zan saya musu. 103 Ni kam Ishak yayi mun har kala biyu "masu kyau sosai, ban ma san da su ba sai" da ya karbo su daga wurin Tela. Daga ni har shi din shirin sallar muke yi ba kadan ba. Ta bangare na dai wannan ita ce sallar da zan yi ta farko a dakin aurena. Shi kuma yayi sayayya na abinci ba "kadan ba. Nayi cincin, cake, sannan nayi" miya mai dadin gaske da taji naman Saniya. Sannan na soya naman kajina gaba daya. Ga kunun zakin da nayi wanda ya ji kayan yaji sosai da busasshen dankali. Hindu ce ta shigo da sassafe tun kafin a tafi sallar Idi ta rinka mika mun abincin gidajen makwabta saboda sammakon da nayi na gamawa. Tayi sallama a bakin kofä saboda sahin "da tayi Ishak na nan, na amsa mata na fito" "ina tambayarta akwai,sauran gidan da ba a" baiwa ba ne? 104 "Ta ce, ""A'a."" Na ce, ""To don Allah idan" kin yi wanka sai ki kai mun na gidanmu "Ta ce, ""To.""" Na shiga daki da shiri na shiga wanka. Ke zo nan. Ishak ne ya kira ni. Kwanakin baya ba na hana yarinyar nan shigowa gidan nan ba? Ba na ce bana so ba? Gidannan wai shin ba gidana ba ne? Idan na ce bana son abu menene dalilin "da yasa ba za a bari ba, ki kiyaye ni fa! Me" take zuwa ku ke yi? Gulma ko ba ki munanan shawarwari da koya miki "dabi'un banza? To ya ishe ni haka.""" Karo na farko da al'amarin Ishak ya gundure ni na zuba mishi ido ina kallonshi. Yana dandanna wasu lambobi ne a "waya, alamar zai yi kira. Kamar na ba shi" amsar maganganunshi sai naga ba zan iya ba. Yayi mun kwarjini da yawa sai kai na wuce shi na shiga bandaki nayi wankana na fito. 105 Lokacin nan kuwahar ya gama shirinshi. Jamfa ce a jikinshi dogųwa ta yadin shadda geitzner ja. Tayi mishi wani irin kyau. Ban taba ganin ya saka babbar riga ga wata kila don baya ra'ayinta. Yana rike da hularshi yana kokarin karyata haka kawai na ga kalanta bai yi mun ba. Na mika hannu na dauko watamai ruwan ja da brown da wani ratsin nace ko za ka ajiye wannan ne ka saka wannan zuba mun ido ya yi yana kallona. A hankali na ce mishi na gane kamar tafi shiga da kayan. Ya mika hannu ya karba bayan ya ajiye ta hannun nashi. Ya karyata ya saka a kannan shi sannan ya feshe jikinshi da turare. Yayi mun kyau a idona. Ina matukar son yin mu'amalla mai kyau da Ishak irin wacce nake ji ana "bada labari," 106 Don na san rayuwa ce da take faruwa a "zahiri. Ya juyo da kallonshi gare ni, nima" shi nake kallo. """Zan tafi hawan Idi, ana saukowa zan" "dawo, don zan yi baki daga office dinmu." Ayi mun shiri na abubuwan ci sosai don "suna da yawa.""" "Na ce,To Allah ya bada sa'a."" Ya" "kuma amsa mana lbadunmu. "" Ya ce," """Amin.Ya fita." Zama nayi na yi kwalliya ta burgewa ba "kadan ba, na dauko yadin material wanda" Ishak ya karbo mun daga gun Tela na saka ya kuma karbi jikina ba kadan ba. Gashi kuma na fara yin kibar ciki ga fatata da ta yi haske tayi laushi zan iya cewa ban taba yin kyau irin hakan ba. Hindu ta shigo ita ma tayi kwaliya sosai "ta shadda da ta sha ado. Ta ce, ""Kai Aunty" "Hauwa, kin gan ki kuwa? Kin ga irin kyan" da ki ka yi? 107 "Nayi murmushi na ce, Haba Hindu," "har na kai ki? Ta ce, ""Haba wane ni, keta" dubi kalari kin san yadda ado yake yi wa "farin mutum kyau kuwa?""" "Na ce,""Ke kuma ga ki doguwa kin san" kyau yana ga dogon mutum. 99 Gaba daya muka yi dariya. Na ce mataTo barka da "sallah, Allah ya maimaita mana.""" "Ta ce,""Amin."" Ta kwashe manyan food" flask guda biyu da na cika da abincin "gidanmu, daya dai miya ce da taji nama" don kuwa raba miyar nayi biyu na juye rabi. Dayan food flask din kuwa soyayyen naman kaji ne da cincin da kek. Na saka mata a nan ne don kaninta ne zai rike gudun bari. Ban zuba shinkafa ba don nasan Umma zata dafa. Na shiga shiryawa Ishak abincin bakinshi komai na tanadan mishi. Karfe goma daidai ya shigo gidan. Nayi mishi barka da sallah ina kallon shi ga 108 zatona zai yaba kwalliyata tunda ko da ba dabi'arshi ba ce yin hakan. Ai kuma yau sallah. Bai ce mun komai ba har na gama shirya mishi abincin shi. "Ya ce ""Da kin bari sai sun zo muci tare.""" "Na ce, Ai ba ka da tabbacin lokacin" zuwan nasu tunda yanzu ne ma aka sauko "daga Idi, kaci ko babu yawa zai rage maka" "yunwa."" Sai dai na daure ne kawai nayi" mishi wadannan bayanan. Don tuni zuciyata ta fara hankoron fushi. Na shiga daki na zauna a bakin gado naga abin bai yi mun ba. Na gaji da abubuwan ko in kula da Ishak yake yi mun ko ma meye zai faru kawai ya faru a yau dinnan. B Ban san lokacin da na ganni zaune kan kujerar da ke gabanshi ba. Na kare mishi kallo yana cin abincin shi cikin nutsuwa kana kallon shi ka san ba shi da matsala. 109 Ya dago ya kalle ni Yaya lafiya? kullum salon tambayarshi kenan. Ban ce mishi komai ba ban kuma daina kallon nashi ba. Kina da matsala ne? ko wani abu yana miki ciwo. Wani tunani yazo mun cikin raina da kuma yasa na fasa yi mishi magana na mike da nufin komawa daki. Hauwa'u na juyo tare da amsawa. A tun farkon zamana da Ishak zan iya kirga adadin lokutan da ya kira sunana. Zo ki kwashe wadannan kwanukan na "gama."" Na zo ina kwashewa., Dan" sassaucin da na samu na mu'amalla ni kaina nasan don juna biyun da nake dauke da shi ne wani lokaci ya kan tambaye ni akwai matsala ne ko kuma wani abu yana yi miki ciwo? Haka nan ya rage yawan dadewa a waje karkari ya kai karfe goma shi kenan. Na gama kwashewa da karin gyaran wurin na dawo dakina na kwanta don 110 dan samu na huta ayyukan da na kwana biyu ina yi. Ya shigo dakin sanye da farar singilet da wandon kayan da ya cire ya miko mun kudi bandir din Naira dari sababbi fil da su. Na mika hannu na karba ina jira yayi "mun bayanin abinda za a yi. Ya ce, ""Ki" ajiye barka da sallanki ne. in tsaya cewa kudin nan sun yi mun dadi ma bata baki ne. Sai dai kan nayi mishi godiya aka fara buga sallama. Ya juya ya shiga dakinshi don dauko rigar shi da ya tu6e. Ni kuma na jawo gyalena mahadin material din jikina na yafa na fito har ya ba su izinin shigowa. Lallai kam bakin Ishak da yawa. A can gefe na zauna müka gaisa da su. Ban tsaya kallonsu ba amma nasan sun kusa goma. Ban iya komawa ba lokacin daa 111 na shiga kicin tunanin yadda zan yi na kat musu sa'a shima ya fito ya zo kicin din. Bani abincin kawai ba sai kin shiga ba tunda kun gaisa.Ya fara kwasa yana shigarwa sannan na hada Plate-Plate da kofuna na sake mika mishi ya shiga. An dai kai kamar mintina talatin na "motsin plate da cokula kawai nake jiwowa," yayin da nake zaune a single dakin dake tsakar gidan. Kafin daga baya hira ta barke. Ina sauraronsu kowa da abinda yake fada game da abincin yayin da ake sakawa wasu waigi. Hira sosai şuka shiga yi daga baya da ta kunshi wajen aiki da kuma wasu al'amura. Koda nake kwance a kan gadon dakinnan na kasa barci duk kuwa da irin gajiyar da "nayi saboda muryar Ishak da nake jiyowa," Da yadda yake dariya da wasu "abubuwa. Mamaki ya kama ni, dama yana" 112 hira da mutane da ni ne.bai yi ko kuwa ya ya? Ba su tashi tafiya ba sai wajen azahar "suka fita gaba daya don yin sallah, bayan" sun nemi nazo muyi sallama ya ce musu nayi barci. Na dawo dakin na sake gyara shi tsaf "kamar ba a yi komai a ciki ba, sannan nayi" sallah na hau gadona na sake kwanciya. Ishak bai dawo ba sai wajen hudu da rabi. Na mike na bishi dakinshi baya ciki alamar yana wanka na zauna a bakin gadon ina jiran fitowar shi. Tunda ya fito nake bin shi da kallo har "ya sanya short da jallabiya fara sol, sannan" ya sake kallona. Ga wannan suka ce na baki goron sallah. Yana miko mun kudi na kalli "kudin a hannunshi da yake miko min," sannan na kalle shi shima ni yake kallo. 113 """Ya ya dai akwai matsala ne?"" Na ce," """Eh akwai, wannan ma da ka bani da safe" "gasu nan na dawo maka da su bana so.""" "Ba karamun kada shi maganata tayi ba," don tsawon zamana da Ishak ban taba amsa mishi magana ba ballantana nayi jayayya da shi. Kuka na fara yi a daidai lokacin da na "fara magana. ""Ni ba zan iya irin wannan" rayuwar ba. Dama abinda yasa nake ta "hakuri na dauka haka ka ke, haka" dabi'arka da halayyarka suke. To ashe ni kadai ka ke yi ma. "Ya ce, ""Wacce irin banzar magana ce" "wannan, ke lafiyarki kuwa?"" Na ce," """Lafiya kalau, na dai gaji ne. Ban taba" saka kaya a gidan nan ka ce yayi kyau ba. Ban taba yin girki kaci ka ce yayi dadi "ko bai yi ba, ban taba yin wani abu da" nufin na burge ka ka yaba mun abinda nayi ba. 114 Ni a kullum a wajen ka a kushe nake. Bana gwaninta a wajenka sai kuskure. Ni kulluma wajen ka mai laifi ce ni. Ba ka ganin nawa da mutunci saboda "ni, babu wani mutum da zai shigo cikin" gidan nan da sunan wurina yazo ba tare da ka wulakantashi ni kuma ka bata min "ba...""" """Ke dakata! cikin tsawa ya dakatar da" "ni. ""Ita ce ta turo ki ki zo ki titsiye ni?" Kina nufin kin isa ki sa ni nayi abinda ban yi niyya ba? Wannan abin da ki ka zo ki ke yi ba zai sa na canza daga dokata ta kada wani ya shigo mun gida ba ko wanene ba tare da yardata ba. Kuma tunda yanzu na kara gane aibun hakan nasan abinda zan yi kenan har kin fara bin shawarwarinsu ne kina titsiye ni "akan abin da bana so. To babu laifi.""" """Ba titsiyeka nayi ba, kuma ni babu" wani wanda yasan abinda muke yi 115 ballantana har ya bani shawara a kan abinda zan yi. Amma wacce irin rayuwa ce wannan? Za ka iya zama da abokai kuyi hira kuyi dariya tare amma ni matarka ta aure ba ka da lokacina? Idan gari ya waye ka fita ba zan sake saka ka a idona ba sai wani wayewar garin? Amma ni kana saka mun takunkumi "na yin mu'amalla har da 'yan uwana, to..." kafin na karasa tuni ya dauke ni da marin da na kife a kasa. """Ki rinka fahimtar lokacin da mutum yá" "gundura da abu."" Ya watsar mun da kudin" a wajen ya dauki mukullin motarshi yayi waje. A hankali na mike na goge hancina da "naji alamar ruwa-ruwa yana biyowa, jini" ne. Ban ci gaba da kukan da nake yi ba sai dai duk da gargadin da zuciyata take yi mun kan abinda nayi nufin yin ban fasa ba. 116 Wannan karon shi ne karo na uku da "Ishak yake dukana, Jakata na dauko har na" fito na nufe ko'ina sai na tuna ko kudin mota ba ni da shi. Dawowa nayi na bude dakin Ishak har yanzu kudin suna watse a kasa na sunkuya na dauki gudan dubu guda uku a kudin da bakin shi suka ce ya bani na sake shig dakina na dauko kaya set daya na sake fita a gidan bayan na rurrufe ko ina na tafi gida. "Ba karamin mamakın ganina suka yi ba," don kuwa ban gaya musu zuwana ba. Babana muma yake yi daga ganinshi "kuma na san ya dan samu canji, don kuwa" yayi fes da shi. Umma atamfar da nayi "mata ce a jikintą, haka nan su Taşi'u." "Umma ta zubo mun abinci ta ce ""Ga shi" "nan duk da dai daga gidanki yake."" Na dan" "yi murmushi na ce ""Umma ba ni, naki" "mana na ci,""" 117 "Ta ce, ""Fuwo ne miyar taushe."" Na ce," Eh bani kawai. Cin abincin nayı sosai "sannan na sha kunun zaki. Ta ce, ""Amma" ai ba yau muka yi da ke za ki zo ba ko? "Lafiya dai ko?""" Na dan yi shiru ban ce wa Umma koai "ba. ""Idan akwai wani abu kiyi magana" "mana, naga kamar ranki a bace yake.""" Na rasa ta inda zan fara yin maganar "nan take kuma na kama kuka, sosai da" sosai. Sai dai na kasa cewa Umma ga matsalata. "Ta ce, ""To ko nayi, iki magana da" "Babanku ne? Na girgiza kai na ce, ""A'a.""" "Ta ce ""To ki share hawayenki kiyi hakuri" "kowacce mata da ki ka gani, da irin" matsalarta. "Shi aure haka yake, kina hango na wani" ne wani kuma yana hango naki. Ki daure ki zamo mai sirTi a tsakaninki da mijinki. Babu mai ganinki ya ce kina da matsala "kwata-kwata, tunda mijinki ba gaza miki" 118 "ba, bai kuma yi tsari ba a ce tun yanzun" kin koyi kai kararshi ba ki iya warware wa kanki matsalarki ba tare da wani ko wata ya fahimta ba. Ki tashi ki koma kada ki dade kuma ya "zama matsala, tunda dai da'alama ma ba ki" "sanar da shi zuwan ki ba.""" Sai da Umma tayi wannan maganar ne naji gabana ya yi matukar faduwa. Na koma gida idan Ishak ya dawo kuma muyi ya ya kenan? Ban bari Umma ta fahimci halin da "nake ciki ba, dauko kudin dake Jakata nayi" na bata biyu na baiwa su Tasi'u canjin kudin mota ta dari takwas na rage kudin da za su mayar da ni gida. Fitowar da zan yi kenan na hango motar "Ishak ta karyo kwanar unguwarmu, cikin" sauri na koma gida. "Umma ta ce ""Lafiya?"" Na ce, ""Gashi" "nan zuwa shima."". Ta ce, ""To, to Allah" 119 yasa kalau. Umma ce da kanta tayi mishi shimfida suka gaisa. Sannan aka kira Babana da ke tare da wasu daga cikin makwabtanshi suna tattaunawa. Gaisuwa sosai suka yi sannan ya kawo goron sallah ya baiwa su Tasi'u. An dan jima kafin ya nemi na fito mu tafi. "Bai ce mun komai ba har muka iso gida," daidai an fara kiran sallar Magriba. Bayaan gida na wuce nayi alwala na fito don bada farali. Shima a dakin shi yayi sallah. Ban fito ba don kuwa na riga na kudurawa rainaa zan zauna ne da lshak irin zaman da yake "so muyi da shi, tunda dai haka ya zaba." Lekowa yayi dakina ya kira ni na shiga "yana tsaye. ""Kwashe mun kudin nan. Na" sunkuya na kwashe su gaba daya.. "Ya ce, ""To zauna."" Na nemi wuri a kasa" na zauna. Tashi ki zauna a bakin gado. Nayi kamar yadda ya ce shima yazo bakin gadon kusa da ni ya zauna. 120 """Na dauka kina da tarbiyya hakan ne" yasa ban taba yin zaton za ki yi abin da ki ke yi a yau ba. Sake gaya mun abubuwan da ki ka ce ba kya so wadanda nake yi miki sai na kula nan gaba na daina. "Amma abinda ba zan lamunta ba shi ne," ki kara zuwa mun cikin fusata irin na yau ki ce za ki gaggaya mun bakaken maganganu kin gane ko? Ba ke ce za ki koya mun yadda zan rinka mu'amallata da wasu ba. Ina so ki san ke din ba za ki taba zama "mai sa ni ko mai hana ni ba, koyi samuna" cikin nutsuwa kina yi mun magana ta yadda zan gane har kullum cewa ni ne mijinki ba ke ce mijina ba kin gane ko? Dokata ba za ta sauka ba na cewar ban son shigowar waccan yarinyar cikin gidana ba don a zahiri ga abinda ki ka yi mun a yau wanda a da ba ki taba yi mun "ba, gabanin fara mu'amallarki da ita." 121 "Na dago ido ina kallonshi ""Zan kuma" dauki mataki da kaina ba sai kin shiga matsala tunanin fuskantarta ba. Ba zan lamunci masu son shiga lamarin aurena ba. Na kuma yafe miki fita da ki ka yi ki ka je gida a yau ba tare da kin nemi izinina ba sai dai ina so ki san kin fitan ne a madadin "wunin da za.ki je na gaisuwar sallah.""" Na mike da nufin fita a dakin. Ya ce """Dawo ki zauna. Na dawo na hau gadon" na kwanta sai dai kuka na kama yi saboda tukukin da zuciyata take yi mun. Washegari da safe kamnar ba zan yi "kwalliyar ba, sai kuma naga kaina kawai" "nake yi wa, don haka sai na yi kwalliyata" na sanya atamfa super exclusive holland wacce ya yi mun a sallar. Kadan ya rage na ce tafi yi min kyau a "jikina a kan material din da na saka jiya," "ita ma kalarta mai kyau ne kwarai, ruwan" kwai da jajja da kore kadan. 122 Adon atamfa tana matukar sanya mutum kwarjini ba kadan ba. Na kammala shirina na fita kicin ko bi ta kan Ishak ban yi ba. Sai da na gama ayyukana na kicin sannan na shiga dakinshi don na kwaso abubuwan da ya yi amfanida su da kuma gyaran bandakin shi. "ldon shi biyu na same shi, sabanin dazu" da yake barci. Na shiga bayan gidan na gama gyarawa sannan na zo don komawa duba girkina. """Zo mana."" Na juyo na ce ""Ga ni. """ Magana yake son yi sai dai ya rasa ta inda "zai yi ta, abinda na fahimta kenan." Ya dai zuba mun ido sai da na gaji na "ce ""Ka kira ni. Ya ce, ""Eh na gane baki" nuna mun kwalliyar taki ba ballantana na "ce tayi kyau, ko ba haka ki ka ce na ringa" "yi miki ba?""" Na juya nayi tafiyata ba tare da na ce "komai ba, ina gab da gama abinci ne naji" 123 ana ta6a kofa. Na leka ta wurin da ake ganin mutum. Gabana ne yayi mummunan faduwa a "madadin farin ciki, Sadiya Tanimu ce. Na" "dawo kamar na kyaleta ta gaji ta tafi, sai" kuma naga bai dace ba. Dakin Ishak na shiga har yanzu yana kwance na rasa yadda zan yi nayi mishi bayanin don nasan yadda yake daukan baki. Sai shi ne ya yi mun tambayar tashi ta "fama Ya ya dai?"" Na ce, Nayi bakuwa ne" "kawata ta Makaranta ce tazo.""" "Bai sake kallona ba ya ce, ""To menene" "ki bude mata mana."" Na juya na koma" muka rungume juna cikin tsananin farin ciki. Ta rike baki daidai ta shigo falo ta ce """Kai Hauwa'u, kin gan ki kuwa? Kin yi" "wani irin kyau abin ma ba a ko magana.""" "Na dan yi murmushi na ce ""Sadiya" "kenan. Ta ce, ""Uhm, Allah dai ya samu a" 124 "danshinku. Na ce, To Amin. Kin san" kuwa ban taba tunanin zuwanki ba. "Ta ce, Yaushe kuwa za ki yi tunanin" zuwana? Ai ke kam Hauwa'u ba ki da "kirki, daga kin yi aure sai ki ki mutane?" "Na ce, Ayya, ba na samun fita ne. Ta" "ce, Eh ai ban ga laifinki ba ko kadan ko ni" nayi aure na samu wadata haka ina za ni? Ai sai kawai nayi zamana na yi ta shan gara. Na mike don kawowa Sadiya abinci da kayan shaye-shaye da ciye-ciye saboda hirar tata ba wani dadi take yi mun ba. Don nasan Ishak yana jinta. Tana nufin kenan don ka samu gidan miji mai wadata shi kenan babu ruwanka da sauran mutane? "Yan uwanka, 1yayenka da abokan" arziki. Idan kuma ya zamana shi ba shi da lokacinka kamar Ishak fa? Sai ka yi ta rayuwa kai kadai takamar ya wadataka' 125 Lalura kuma idan ta same ka fa? Na debo abinda zan kawo mata na ajiye a gabanta tana tambayana maigidan yana nan ne? "Na ce, Eh yana barci. Na mike na shiga" dakin Ishak na zauna kusa da inda ya ajiye kanshi don nayi maganar da zan yi a hankali. "Na ce, Za kủ gaisa ne? bai ce mun" komai ba har na gaji da zamana na fito na dawo falo muka ci gaba da hirar mu. "Na ce, Sadiya ya Makaranta? Ta ce, Ga" mu nan mun usa gamawa muna ta shirin "zana jarrabawa, Malam Ali kuwa kullum" sai ya tambaye ki. "Na ce, To da yake tambayata ai sai ki ce" mishi iyayena sun dauki shawarar da kullum yake ba su sun kuma aurar da ni. "Tayi dariya, Ke Malam Ali fa" shakiyanci kawai yake yi miki. Amma ke kin zauna kenan ba za ki koma Makaranta ba? 126 Ke kina ganin hakan ya yi miki daidai? Yanzu fa watan gobe ne za mu rubuta jarrabawa kowa kuma sai ya kama gabanshi a yi ta tafiya babu ke. Karatu ai shi ne adon mace a duk lokacin kuma da ta rasa shi to tayi babbar "asara, don kuwa ko aure ki ke yi ai ba kin" rinka zama ke kadai ba kenan wata rana za a yi miki kishiya ki ka san wacce za a auro miki? "Na yi nufin katse Sadiya na ce, Ke" Sadiya bar wannan maganar haka muyi wata kuma. Na dauko wata hirar ina "tambayarta, Ni kuwa ina Zubaida?" "Ta tabe baki ta ce, Uhum, tayi aure ita" ma har ma ta haihu ai tsiranku babu yawa. Kema dai da alama cikin ne da ke tunda gashi nan har ya fito. Aini kam yanzu idan nayi aure family planning zan yi kafin na gama karatuna sannan na fara haihuwa. Na ce To idan mijin naki bai yarda da hakan ba fa? 127 "Ta ce, To yaushe dama zan sanar da shi," ai tuni zan je nayi abina bai ma san lokacin ba. Ke! Cikin saurina waiwaya Ishak ne a "tsaye cikin wani irin bacin rai. ""Tashi ki" "fita a gidan nan.""" "Sadiya ta fara kokarin gaishe shi," """Common get out, idiot! 'yan banzan yara" "kawai marasa kunya.""" "Sadiya ta mike sum-sum-sum ta fita, ni" kuwa jikina sai bari yake yi ga kunya ga "takaici, ""Ke kuma."" Yana nuna ni da dan" "yatsarshi ""Ki kiyaye ni na gaya miki." Ki san irin mutanen da za ki rinka kawo "mun gidana. Wanene Malam Ali?"" Cikin" kuka na fara kokarin yi mishi bayani. """Shut up dalla kiyi mun bayani. Na ce," "Malamin mune na Makaranta. ""Menene" gaminki da shi da take yi miki maganar shi "iye?""" Taratsatsin bala'in da na gani a wajen Ishak ranar ba kadan ba ne. Na lallaba na 128 "hau gadona na kwanta, don kuwa na ga" da irin wadannan abubuwan. Har hutunshi na sallah ya kare ya koma "bai yarda ya kai ni gida ba, wai a madadin" zuwan da nayi babu izininshi. Yanzu kuwa kullum idan zai fita a gida "kullewa yake yi, ya yi tafiyarshi da nayi" "mishi magana akan illar yin haka sai ya ce," Idan ina da matsala nayi mishi waya ba zai "ji kuiyar zuwa ba, na ce To." Don haka yanzu ni kadai ce nake wuni a cikin gidan ko dan littattafan da nake samu na daina. A yanzu da nake cikin watanni na "takwas cikina ya bayyana sosai, kowa." yana gani nima kuma ina matukar jin shi a "jikina, don kuwa abubuwa suna dan yi" "mun wahala, kuma ba ni da mataimaki." "Shi kanshi Ishak ya lura da hakan," amma ba zai iya hakura da halinshi ba. Tashin da muka yi yau ba mai dadi ba ne a wurina. 129 Don kuwa jikina yayi nauyi ba kadan "ba, da kyar nake motsawa. Ishak da kanshi" ya ce muje asibiti. Muna zaune gaban "Likita ya ce, Yaron a karkace yake" sakamakon da scanning dina ya bayar kenan. Don haka za a yi kokarin gyara mishi "kwanciya, don haka Ishak yaje gidanmu" "ya sanar da Ummana, sannan ya dawo." Ina zaune a bakin gadon dakin da aka "bani shi kuma yana zaune a kan kujera," yanzu ya ya ki ke ganin zamu yi kenan "tunda dole naje wurin aiki, kina ganin ba" ki da wata matsala a kan hakan? "Na ce, Eh Umma zata zo ai. Ya ce, To" tunda haka ne bari na jira zuwanta kada a "bar ki ke kadai.""" Sai washegari da safe ne aka yi mun gyaran tare da kyakkyawan kashedin kada na rinka aiki komai kankantarshi. Kwana daya na kara a ka sallamo ni na dawo gida. 130 Da safe Ishak ne ya tashi ya hada mana "abin karyawa, ya share dakin gaba daya ya" shirya cikin sauri ya fita. "Na sha shayina na koma na kwanta," wajen karfe daya sai ga dan aiken da ya saba aikowa ya kawo mun abinci. Na bude "take a way ne na abinci mai kyan gaske.""" Shinkafa fried rice da sálad da kuma kwatan kaza. Da yamma kirana ya yi yana "tambayata abinda zai taho mun da shi, na" ce ni a koshe nake zan sha tea. Duk da hakan bai fasa kawo mun wani irin gashi ba na bankararren kifi da aka gasa da lemon tsami yayi mun dadi ba kadan ba. "Don haka na ci sosai. A daren yayi ""yan" aikace-aikacen da zai yi bai kwanta ba sai wajen karfe goma da rabi saboda wankin da yayi na under wcars din shi. Sanin halayyar Ishak yasa nake ta jin shakkun yi mishi magana akan shawarar 131 "da. nayi aina, sai dai duk da hakan ban" fasa ba.s "Ina kwanoe & gefehshi na ce, Ko zan yi" wa Umha magand ne ta samo mana wacce 2amu rinka. żarňa tare runda ka ga ni ko wannan aikin ma da ka ke yi ba kai ne ya kamáta kayi ba. "Ya ce, Kin ji nayi miki wani kora a" "kan hakan? Na ce, To naji ba ka yi ba" amma idan naæo haihuwa fa? "Ya ce, Sai ki bari idan haihuwar tazo" "kiyi magana, ba zan tsaya na yi ta jayayya" dashi ba don haka naja bakina nayi shiru. llai ko ba a fi sati guda ba bayannan sa na tashi da wani irin ciwon mara ma "musaltuwa, nayi ta wani irin murkususu ni" "kadai a daki, don kuwa Ishak baya nan bai" dawo daga wurin aiki ba... To bari mu jira dawowar Ishak din "muma, sai in ce mu hadu a littafi na biyu." Taku; Haj. Hafsat C. Sodangi 130