FUREN ZUCIYA. Flower of the heart. By Nasreel R.L. A hausa love story……. Chapter 1; Riyadh Saudi Arabia. "Wani irin hucin zafi da dakin keyi sakamakon rashin window ko daya, ga wani jarababben yunwa da takejinshi kamar jikinta nacin kanshi yasa Miral mikewa jikinta dayake sanye da wani white cotton sleepwear daya koma creamy brown yayi paci paci a jike da gumi daya sa ya" maƙale a jikinta ya fito da Hadadden suffar jikinta. "Wani layi ne yake dibanta saboda yunwar dake neman hanata neman ma kanta mafita tayi saurin dafa bangon dakin dayake siminti ne kawai babu fenti. Wani irin warin ruma dakin keyi gashi dan karami dan baifi ya dauki mutun daya da kayanshi ba. Babu koda tabarma bare katifa a dakin, wani zanin gado ne daya ji jiki ya yayyage a shimfude dukda bawani fadi ne dashi ba amma ya mamaye rabin dakin. Kasan dakin simintin yadan burma ta wasu yan gurare ga ceiling din wanda ruwa ya dake shi alamun ruwa na zuba ta cikinshi duk ya daddago kamar zai fado" kasa. Dakyar ta samu jirin ya tsaya dukda hakan wani fatsi fatsi take gani. mikewa takarasa yi still hannunta na jikin bangon bata saki ba. "Doguwa ce ita a cikin mata, dan rigar bata karasa chan kasa ba dukda kuwa full size ne. Batada kiba kokadan dan har wani yawo takeyi a rigan, kirjinta kusan flat yake sai dan tudun da zainuna maka mace ce. Waist dinta so slim tommy dinta is flat kamar wanda bata cin abinci." Hips dinta ne kadai zakace da tsoka dan its wide and nicely shaped saitayi figure 8 shape effortlessly. "Tanada long oval face dake dauke da manya manyan idanu, eyeballs dinta are a rich shade of brown dayayi enhacing din overall features dinta. Hacinta irin botton nose dinnan ne mai tsawo saidai ba chan chan ba lips dinta are round and medium sized. her face is giving barbie and mulan saboda the eyes makes her look very cute saboda girmansu saidai shape dinsu kuma is upturned ta karshe saiya bata wani fierce no nonsense look dazaka zata irin marasa mutuncin" nan ne. Fatarta dayake mai haske saidai ba chan chan ba irin caramel African glowy skin dinnan. The shade very unique and glowy koda idan kasa ido ka kalla fatar zaka gane bata samun abubuwan dazai gyarata ko ginata. Jilbab blue ta dauka da shima ya kode wuyan yadan yage ta nade black curly hair dinta daya sauko har tsakiyan bayanta tasa wani ribon daya gama talewa ta daureshi ta dau wata black cap ta saka sannan tazura jilbab din daya sauka har kasa saidai baija kasa ba ya bayyanar da "slender kafafunta dake dauke da zara zaran slim yatsu, faratanta har kyalli sukeyi." Kofar dakin ta bude wanda yama sauko daga mazaunin shi saidai ta dagashi gefe ta fita. Long corridor ne gabanta dakinta shine na karshe agurin. Bagu haske kwata kwata a corridor din dan ba windows a bangaren sakamakon duk store rooms ne na ajiye kaya dabasu bukatan iska. Ita kanta dakinta store dinne aka mayar mata dashi daki idan zata kirashi da dakin kenan dan babu koda katifa a ciki. Dare ne dan haka gidan tsit bakajin komai sai karan tsintsaye da sautin wakan su ke tashi. Straight part din ta bari ta nufi main part na gidan. Ta kitchen entrance din yake dan haka nan ta shiga kitchen din ya tsaru iya tsaruwa sannan babba ne sosai. Ganin babu kowa a ciki kamar yadda take tsammani yasa ta salallaba a hankali ko takun kafafunta bakaji zuciyanta na bugun uku uku ta nufi wani katon smart double door samsung fridge ta budeshi a hankali. Fruits ne kala kala a cikinshi sunyi sanyi ga ruwa bottle water a jere a ciki suma sunyi sanyi zuciyanta na ayyana mata karta dauka kada a kamata saidai wani kugi da murdewa da cikinta yayi ya isar mata da sako. Dafe cikin tayi duk wani tsoro na fita daga kanta ganin zata iya mutuwa idan ta zauna haka yasa ta dago tafara daukan abubuwan dazasu kawar mata da yunwar data addabeta. Apple dayake favorite dinta ta dauka guda daya wanda zata iya irga sonawa a cikin yan "shekarun nan taci shi, sai ta hada da banana guda biyu dakuma strawberry biyu ta dauki ruwa guda daya." "Rufe fridge din tayi tana kallon abubuwan data kwaso, ko kusa bazasu cire mata yunwar dake jikinta da tun jiya da safe babu abunda ya shiga cikinta sai uban Aiki data jibga. Freezer dake gefen fridge din ta bude bayan ta rufe fridge din dan kozataga ragowar abunci. Cikin sa’a saiga wata biryani rice da half chicken a cikin package da alaman takeout ne akayi ordering ." . Ko ba’a fada mata ba tasan na Hanat ne dan ita ta anso mata shi dazu da aka kawo shi delivery. "Kura ma package din ido tayi tana kallon yanda aka chishi a wulakance, zuciyanta na wani irin ciwo ganin yanda su Hanat suke rayuwarsu yanda sukeso babu wata damuwa bayan ita saidai taci ragowarsu kamar wata mara galihu. Wani murmushin bakin ciki ne ya kufce mata, shin" meye marabarta da mara galihun? Masu Aikin gidan sun fita daraja da matsayi. "Daukar package din tayi hannunta na rawa dukda tanason ta kwantar da zuciyanta ta dauka babu tsoro dan Hanat bazata sake nemanshi ba, batacin abunda ko sanyi yayi bare kuma ace" ya kwana. Bazai wuce ma’aikata suci shi gobe ba kokuma a bawa dabbobi. Rufe freezern tayi ta juya zata koma dakinta saikuma wata zuciyar tace mata ta tafi laundry room mana yafi dakinta iska. Tasan yanzu kusan karfe 3 ne na dare dan haka tasan Hanat ta kwanta bata wuce 3 na dare. Kofar dazata sada ka da main palour ta kitchen din ta bude a hankali ta leka ciki. Duhu na ya sado ta daya tabbatar mata cewa babu kowa dan haka batareda cigaba da sandar datakeyi ba ta shiga tafiya normal ta nufi hanyar laundry room din dake kusan chan karshen falon tana dafa bango dan jirin dake fizgarta. "Sauke nunfashi tayi tanajin yawunta na tsinkewa rabon dataci abinci lafiyayye bare kuma harda nama ta manta shi, zuciyanta har wani iyo takeyi saboda nishadi. Yau kusan shekaransu biyu kenan a Riyadh tun zuwansu two years ago basu kuma koma GHAIR- MU’ADDAL ba. Tanaso ta tambaya ummi amma tana tsoron masifa, dukda tasan komawar bazata haifar mata da komai" ba sai tuna mata wani babi na rayuwarta da batada bukarya tunashi. Wani haske ne ya karede palourn dayasa ta datse idanunta dan sam batason haske saidai tuna inda take yasa cikin hanzari ta waro manya manyan brown eyes dinta dake daukeda zara zaran eyelashes dasuka sauka daidai kan Hanat dake mata wani irin kallo kamar zakin dayaga nama. "Wani baƙin murmushi be ya bayyana akan arab face na hanat, tanada kyau balaifi sannan batada tsawo sosai saidai tanada jiki ba laifi itaba siririya ba bakuma mai kiba ba, saidai tanada bust manya sunso suyima jikinta girma. Tanada irin witch face da kana ganinta kasan bataji, ga yanda tayi da fuska kawai kasan batada mutunci. Gashinta dayake bakikkirin yazubo har tsakiyan bayanta take wasa dashi, hannunta da yasha fake nails kamar zatayi fada da zaki ga" wasu rings a jere a yatsunta duka hudu tayi ma Miral alaman tazo da yatsa daya. Wani irin bugawa zuciyanta keyi jikinta yafara kyarma kamar wanda aka zubawa ruwan kankara. Lips dinta dake rawa ta bude zatayi magana saikuma ta rufe tama rasa mezatace. Tasan bada hakuri bazai kaita ko inaba duk rokonta dazatayi. Tana kallon yanda idanun Hanat ya sauka akan package din abincin kafin ta kara dago idanunta ta sauke su akan face na Miral. Wani bakin ciki ke dirar ma hanat a duk lokacin data kalli fuskar Miral. Face dinta na daya daga cikin abubuwanda ta tsana a duniyar nan. Bataga dalilin da Miral zata mallaki irin wannan kyawu da kallo daya bazakace mutun bace saboda madarar kyau. Sannan duk wanda ta tsaya kusadashi saiya disashe tazama tamkar wata tauraruwa da haskenta ke karuwa kullun akan raguwa. Wannan bakincikin yasa batareda tayi wani dogon tunani ba ta daga hannayenta dake dauke da zobuna masu kauri ta kifa ma Miral wani mahaukacin mari da yasa Miral wani irin kara dan saida taji wani abu ya fashe a bakinta. Bata yi wata wata ba ta kara sauke mata wani a dayen side na face dinta wanda saida Miral ta fadi kasa abinci da fruits dake hannunta suka watse a kasan. "Dafe fuskarta tayi dabama tajinshi a jikinta. Wani irin dau da zugi yake mata ga wani abu nabin hannunta datasan jini ne da ke fitowa daga goshinta daya bugu da kasan, kunninta yay wani dumm babu abunda takeji daga masifar da Hanat keyi sai kalma daya ‘kaskantacciya’. Wasu" hawaye masu zafi ne suka jero daga idanunta suna gauraya da jinin dake fita daga face dinta. "Kafa hanat tasa ta hambareta a hakarkarinta da saida taji nunfashinta ya dauke. Kasa ihu tayi dan azabar daya ziyarceta, dan ciwon da hanat taji mata sakamakon buga mata laptop datayi a" daidai gurin ko sati baiyi ba. "Muryan wata dattijuwa ne ya katse hanat dake Neman cigaba da bugun ta. Wani dogon nunfashi Miral taja jin muryan Ummi, aranta addua kawai takeyi Allah yasa yau ranta ba a bace yake ba ta rabasu da hanat. Karasowa tayi inda suke batada tsawo saidai tanada jiki sosai dan fuskanta a wani chure yake skin dinta wani reddish tana tafiya dakyar tana nunfarfashi jikinta" sanye da wani red burgujejen sleeping dress dayaje har kasa. Daidai inda Miral ke kwance ta tsaya tana bin abincin daya watse a kasa tana kara daure fuska. Miral da jikinta ke rawa tuni ya tsaya chak dan ganin yanda idanun ummi sukayi tasan yau babu sa’a kwata kwata. Yau kashin ta ya bushe yau babu mai chetonta a duniya. Kallon yanda ummi ta daura hannu akan kugunta tana mata wani mugun kallo yasa Miral mikewa zaune tana dafe ribs dinta datakejinshi kamar ana zuba mata wutan dalma daga kan gurin har zuwa cikin kirjinta da cikinta. Kasa rike ƙaran daya zo mata makwogwaro tayi cikin zafa ta rufe bakinta da dayen hannunta dan batason wani abu dazai kara harzuka dayansu. "Hanat ce ta juya ta kalli Ummi da gani bataji dadin zuwan Ummi ba dan tayi niyya cin uban Miral yau, takumasan Ummi bazata barta tayi mata dukan datakeso ba dan zatace tanada aiki gobe" karta illata ta. "“ Meya faru anan daugher?”, Ummi ta tambayi hanat. Kamar wanda take jira hanat ta anshe maganan batareda tajira Ummi takarasa ba a kufule kamar budurwan data kama saurayinta da wata tace “ Ummi wai wannan kazamar yarinyan nan sata tafara? Nadade ina fada miki dama yar iskan yarinyarnan is not innocent tana abubuwa simi simi tasan metakeyi ashe sata takeyi a gidan nan! Yan dauke dauke da akeyi nace miki banga abu kazaba kice maybe nayi misplacing" dinsu ne ashe ga barauniyar datake dauka nan. Yau zanci ubanta kuwa”. "Da fadin haka ta chakuma gilbab na jikin Miral tareda fincikota gaba tahau yi mata ruwan dundu a baya, dum, dum hannu bibbiyu. Miral batayi kokarin matsawa ba dan tasan hakan wani sabon matsalar zaija mata. Inda sabo ta saba da duka saidai sabawar bashi ya hanata jin zafin duka datake mata ba. Hawaye ke fita daga idonta ta rintse su tareda girgiza kanta tanajin yanda" dukan ke shiganta har cikin tsakiyar brain dinta. Ummi ganin hanat batada niyyan tsayawa yasa ta janyota baya tareda mata alaman ya isa. Umarni tabama Miral akan ta dago idaunta ta kalleta. Jiki na rawa Miral ta dago fuskanta dayake sharkaf da hawaye da jini nabin kusan rabin face dinta daga side dinda goshin ya fashe. Wani murmushi Ummi ta saki tana kallon cikin idanuwan Miral dake cike da hawaye sunyi ja jawur. Saurin sauke idanunta Miral tayi ganin irin kallon da Ummi takemata datakasa gane meyake nufi. Alaman ta mike Ummi tamata bata musaba ta mike a sanyaye ribs dinta kamar zasu fizge daga jikinta dakyar ta samu ta tsaya a tsaye tana kara danne ribs din. "“ cire hijab din malama”, Ummi tafada. Hannu na rawa tayi anfani da hannu daya ta cire jilbab din tana maida kallonta kasa takasa gane meyasa Ummi zatace ta cire hijab. Kodan tanason ganin ko ta dauki wani abune? Tun daga sama har kasa Ummi tabita da kallo kamar yau ta fara" ganinta. Idanunta suka tsaya akan kirjinta tawani tabe baki sannan ta karashe kallonta. Hanat kamar bakin ciki ya kasheta ganin surar jikin Miral data dade bata ganshi ba dan kullun cikin hijab take. Duk wahala dakuma azabar yunwa da take tabbatar ana mata a gidan amma still jikinta mai kyau ne. Tsaki tayi kawai ta juya fuu tanufi stairs tana hawa bibbiyu tana maganganu ita kadai kamar wata tababbiya. "Cikin zazzafar murya Ummi tace “ Daga yau idan nasake ji ko ganin irin abunda yafaru yau bazaki so abunda zai faru ba. Miral ni zakima sata a gida? Ni? Meye ban miki bah? Iyayenki sun wurgaki kan titi, ni nice na daukeki na taimaka miki nabaki gata na baki gurin zama, kika ce mun kin dena sata, infact ba cewa kikayi bake kikayi abubuwan dakikayi da ko dabba bazaiyita ga yan uwanshi ba? Cikinsu harda sata shine yau zaki nunamin halinki nanan koh? Toh nima" kenan wata ran zama dake zakiyi mun abunda kikayi ma yan uwanki na jini?”. "Kasa ansa wa Miral tayi jin komai na dawo mata sabo. Nunfashinta na kara karfi kirjinta nawani daurewa tanaji kamar an daure zuciyarta da igiyar dake dauke da kayoyi ana ja. Dafe kirjinta tayi da hannu biyu tama manta ciwon da ribs dinta keyi, kwakwalwanta na neman tunawa da memories dinda ta dade da burne su. Girgiza kai tafara yi kamar tababbiya panic na mamaye" ta. "Wani tsawa Ummi ta sakin mata “ Ba magana nake miki bah? Bude baki ki ansani before i make you regret this”. “ no, no no Miral take maimaitawa tama rasa mezatayi. Saida tadanyi yan mintuna kafin taji memories din na fading hankalinta na dawowa ga Ummi dake mata wani" mugun kallo. "Sauke hannayenta tayi daga kan kunnuwanta, cikin sanyi tafara furta sorry Ummi ta dakatarda ita tana fadin “ rike sorryn ki, bana bukata. Nasan mekike bukata, zamu taimaki juna kinji? Zakiyi mun wata babbar alfarma. Amma yanzu Ki kwashe wannan abuncin dakika zubar ki gyara gurin nan ki wuce ki kwanta kinada aiki gobe ba saurara miki zanyi ba”. Tana fadin hakan ta juya ta" hau stairs. Kasa ansawa tayi tunaninta ya tafi kan maganan datayi wai zasu taimaki juna. Toh ita metake dashi da zata taimake ta dashi? Ta dade a haka ganin bazata samu ansar tambayan nataba yasa ta dauki jilbab dinta ta mayar tareda bi ta kwashe fruits dasuka watse sannan ta tsugunna inda shinkafar ta watse itama tana kallon yanda ya barbaje gabadaya babu daman ta ci dan idan tasamu food poisoning ba lallai ne a kaita hospital ba gwara yunwa tasan duk yanda za’ayi zata samu ragowar breakfast dinsu hanat gobe. Naman kawai ta dauka ta ciccire inda ya taba kasa sannan ta dauki containar tasaka shi a ciki da fruits din ta mike ta nufi kitchen. Kan counter ta ajiye cikin sauri ta chinyeshi duk yunwar datakeji yatafi babu abunda ke yawo a cikin kanta sai maganar Ummi. Shin wani taimako zatayi mata? Meyasa zata sata cire hijab abunda bata taba sata ba? Wani irin kallo ne tabita dashi hakan? FUREN ZUCIYA. Flower of the heart. By Nasreel R.L. A hausa love story……. Chapter 2; Bugun kofar dakinta da akeyi a haukace ya tasar da ita doga bacci mai nauyi da takeyi. Ahargitse tamike duk jikinta yay tsami tanajin yanda ribs dinta yadauka azaba saidai bata bita kanshi ba ta nufi Kofa-ta janyeta gefe tana mutsike ido. daga daga cikin masu aikin gıdan ne tsaye ta kura mata ido tana taunar chewing gum kas-kas tana sanye da white tshirt da black knee-lenght skirt. "Tabe baki tayi ta juya tahau tafiya sannan ta furta “ kizo Ummi na kiranki a part dinta”. Da ok Miral ta ansa dukda tasan bajinta zatayi ba dan tayi nisa sannan ta koma cikin dakin taje dan lungu da kayanta suke. Kayan duka duka basufı guda 5 ba, kuma duk sıeeping dresses ne sai" abaya guda daya black data tsufa itama. Wata pink sleeping dress ta dauka sannan ta dau zani dake a kansu ta zura jilbab dibta ta fita daga part din. Straight part na masu aikin ta nufa dan yin wanka coz part dinda dake stores ne dan haka babu toilet a ciki saitazo nan. babu kowa a ciki kamar yadda tayi tsanmani dan kowa yatafi aikinshi. Karamin part ne dake dauke da dan madaidaicin palour dayasha furniture masu kyau da dakuna uku a ciki sai toilet na palour dayake kana shiga part din. toilet din ta nufa ta shiga tayi wanka a gurguge ta wanke jinin dake goshinta da fuskarta dayake tun jiya bata wanke ba. Dakyar ta iya wanke kan ciwon dake goshinta dukda ciwon bashida girma saidai ya suntuma sai azaba yakeyi musamman data samishi ruwa. Saida ta saka kayanta takuma wanke rigar data cire ta fito ta maida jilbab din sannan ta koma part din datake ta shanya rigar a jikin kofar dakinta tanajin yanda jilbab din jikinta duk warin abinci da jini da suka zubo mata jiya amma batasamu wankewaba dan jiya tana gyara palour ta dawo daki ta baje wani nannauyar bacci ya dauketa. A hanzarce take komai sannan cikin hanzarin ta nufi part na Ummi tana addua aranta Allah yasa kada tayi mata mummunan hukunci akan dadewar datayi dan tasan dole zata hukuntata. A palour ta sameta ta zauna a usual sofa datake two seater dake kallon tv dan bata iya zam a one sitter tayi mata kadan. tana sanye da wani red turkish evening gown dayasha adon embroidery kana ganinshi kasan designer ne. Wata matace a gefenta sanye da wata mahaukaciyar luxury black abaya da koda Miral batasan luxury brands ba tasan wannan kosu Ummi basasaka irinta. "Daure kanta yake da scarf dashima kana gani kasan bana kananan mutane bane, gaban gashinta a bude face dinta kusan half arab half japanese dan kamannin japanese din sunfi karfi a face dinta. Bazaka kira ta da kyakyawa ba saidai batada muni sam, fuskar ta a daure babu" "alaman dariya, kana ganinta kasan ba karamar mata bace kadaga irin zaman datayi." "Ummi ko sai smiling takeyi ear to ear kamar wanda take watching comedy show, dajin sallamar Miral tayi saurin daga idanunta ta sauke ma Miral wani mugun kallo kafin a kule tace “ dalla malama jiranki akeyi ubanwa kika ajiye kike wani sallalabewa agurin nan”. Da sauri Miral ta karasa gaban ummi dan nesa da ita ta tsugunna cikin sassanyar muryanta so soft kamar ana shafa maka feathers tace “ Kiyi hakuri Ummi, wanka na tsaya yi. ina kwana”. Sannan ta juya ta kalli matar dake opposite din Ummi kamar zata gaisheta, kamar wanda ta tuna wani abu saita" fasa ta dago idanunta daidai yanda zataga Ummi. Yarfa hannu Ummi tayi alaman ta gaidata sannan ta juya idanunta a kasa ta gaisheta. Bata ansa taba kawai binta da ido tayi dama Batayi tsanmanin zata ansa ba dan kusan duk kawayen Ummi banda kallon kaskanci babu abunda yake hadasu. Sunkai wajen 5 minutes amma ji Miral tayi kamar ta shekara goma a gurin har gwiwoyin ta sun fara sagewa tarasa meya kawota nan tunani takeyi ta tashi ta tafi ne? dan tanada aiki saidai ganin Ummi bata ce ta tashi ba yasa ta hadiye confusion dinta ta zauna. Chan kuma saiga muryar matan “ tashi tsaye”. Ta fada a harshen turanci. Mikewa Miral tayi still idonta a kasa. Ummi tace ta cire hijab na jikinta a sanyaye ta cire tanajin kirjinta na dukan uku uku jin yauma ansata cire hijab. Me hakan yake nufi? Dan tabe baki matar tayi tanabin jikinta da kallo sama da kasa kamar wani product dazata siya. Alama tayi mata da ta matso kusa dayake idanunta na kasa batagani ba. Tsawa Ummi tayi mata akan ta dago idanunta ta matsa da sauri jikinta na kyarma ta dago sannan ta matsa inda matar take ganin ta kara hade rai yasa ta kara matsawa dab da ita. Kare mata kallo tayi tas sannan tayi mata alaman ta matsa. Ummi ne ta tambayeta koh zata iya tafiya ta gyada kai dan haka ummi tace ta wuce ta jeta fara aikinta. Da sauri ta dauki jilbab din ta fita cikin hanzari zuciyarta na bugawa tana sauke ajiyar zuciya dan Allah Allah dama takeyi tabar palourn. A bangaren Ummi kuwa bayan Miral tafita ta juyo ta kalli matar gefenta cikin tausasa murya tace “ Miss kamila zatayi kuwa? Naga kamar batayi miki bah idan abunda zamu iya chanzawa ne sai musan yanda zamuyi tunda wuri”. "Dan kyabe baki matar takarayi tana wani mutsika face a gadarance tace “ Kin tabbata bata san namiji bah? Karki bani wahala kinsan inda hakan zai kaiki”. Da sauri Ummi tace “ A’a na tabbatar, dukda yarinyar tayi abubuwa a baya da bazasu furtu ba amma banda bin maza" intabbatar miki ma ko saurayi bata taba yi ba yarinya ce sosai”. "Dan jim Miss ayra tayi sannan tace “ shekaranta 18 kikace? Kin kuma dauketa na shekara biyu yanzu bayan barin gidan iyayenta, kin tabbatar bata taba sanin namiji ba, sannan kuma kince tayi munanan abubuwa kafin su koreta? Yarinya yar shekara 16 kenan a lokacin? Metayi ne" haka?”. "Dan jan nunfashi ummi tayi sannan tace “ Ina tabbatar miki Miss kamila yarinyar nan 18 take, sannan a shekara sha hudu na dauketa, abunda tayi duk babu wanda bai dagama hankali ba dan babu mai zaton yarinya kamarta zatayi, a tana sheru 13 tana shirin shiga 16 tadawo" makaranta ranar…..”. "Katse ta Miss arya tayi tace “ banason ji, munada bayanan ta already babu abunda yake a boye a gurinmu, sannan duk abunda tayi matsalar tace. gobe zansa azo a duba mun ita idan abunda kika fada gaskiya ne. Idan har akaga cewa she is pure toh zamu aiwatar da plan din. Zaki kawo mun ita ghair muaddal, daga nan zan dauketa, daga ranar dana dauketa ban sanki ba, baki sanni ba Halima, bamuyi maganar yarinyar nan dake ba, bakuma wani zaiji zancen nan ba." Bakuma zaki saka a ranki cewa zata dawo ba dan ta tafi kenan”. Gyada kai Ummi tayi sannan ta cigaba. "“ sannan naga ciwo a goshinta, face dinta a kumbure yakuma faffashe, banason sake ganin wani tabo ko ciwo a jikin yarinyarnan bama anfani da masu ciwo, sannan a bata abinci mai gina jiki zansa a kawo supplement dan she’s too skinny for my liking”. Tana gama fadin hakan kuma ta tashi ta dauki channel bag dinta. Ansawa da ok Ummi tayi tabude baki kamar zatayi magana saikuma ta fasa tadan sunkuyar dakai tana wani dan smile kamar wanda ke son yin wani abu" yakasa. "Dan juyowa Miss Kamila tayi ta kalleta cikin wani annoyed voice tace “ kyautar ki sai bayan komai ya tafi daidai, idan an tabbatar mun gobe gaskiya kike fada toh ranar da kika danka mun yarinyar nan a ghair muaddal ranar abunda kike buri zai cika, sannan koda kuwa kin chanza ra’ayinki mun riga mun ansheta, bama chanza magana, sannan idan kikayi yunkurin tona maganar dake tsakaninmu toh lallai kinsan waye mu, bama fadan hukunci, saidai hukuncin mu" "nada tsanani, wanda sukayi yunkurin yaudaran mu basu shaba”." Tana fadin hakan tayi wucewarta ta fita ta exit. Har waje Ummi ta rakata zuwa garage inda wata Arniyar bentley take a parke ga wasu bodyguards su biyu a gefen motar. Bata ko kalli Ummi dake mata sallama ba daya dage cikin bodyguards din ya bude mata kofar baya ta shiga sannan ya shiga mazaunin driver dayen bodyguard din ya shiga gaba suka ja motar da gudun gaske suka fice. Sauke wata nannauyar ajiyar zuciya Ummi tayi sannan ta juya ta shige gida ranta fes dan tasan yau burinta ya cika. "A bangaren Miral kuwa aikinta ta fara yi dukda takasa cire tunanin abunda yafaru tun daga daren jiya zuwa yau. Har yanzu maganar Ummi nacewa zasu taimaki juna take tunani. A iya saninta babu abunda zataiya taimakon Ummi dashi, kudi Allah ya bata, yaya bataso tun bayan data samu hanat tace bazata kara ba, kuma ta ishe ta dabakinta ta fada batason kari, tanada miji mai sonta, ga kawaye da yan uwa masu sonta. Babu wani abu datake da bukata da zata iya" batashi. Dan haka sosai abun ya girgiza kuma ya razana kwajwalwar ta. "Gakuma wasu sabbin questions din dabata da ansar su. shin waye wannan mata datazo yau? Meyasa Ummi zata bukaci ganinta takuma sanyata cire hijab matar ta kare mata kallo? Kodai siyar da ita Ummi zatayi ne?. Dan dariya ne ya kubce mata a tunanin datayi saurin denashi sakamakon zafi daya ziyarce ta a fuska dan marikan jiya har yau kamar sabo take jinsu. Babu yanda za’ayi Ummi ta siyar da ita. Bayan Ita Ummin da kanta ta dauketa dukda batada niyya da farko? Kuma itadin dukda ba sonta takeyi sosai ba ai yayar mamanta ce, aunty dintace bazata" taba yin hakan ba. Barta dai da yi mata azaba amma baza ta taba siyar da itaba. "Wanke hannunta tayi tareda karasa jera plates din data wanke a cikin dishwasher, dan haka Ummi tasata duk wanke wanke da akeyi a gidan ita takeyi idan tagama wankewa saitasa a dishwasher yakara wankewa. Tasan salon kawai wahalar da itane dan babu wasu ayyuka a" gidan masu aiki keyin yawancin su. "Wucewa tayi tafara gyaran kitchen din a hankali dan duk wani motsi datayi saitaji ribs dinta na ansawa, addua kawai takeyi Allah yasa ya warke da kanshi dan tasan ba kaita hospital za’ayi ba indai ba gani sukayi ciwon na neman kasheta ba. Saida ta gyara shi tsaf sannan ta nufi wani mini fridge da ake ajiye leftover abinci da ba’a sawa a main fridge, cikin sa’a taga wani plate na scrambled eggs dadan yawa da sausages wajen 5 cikin sauri kamar wanda za’a kwace mata ta" dauko shi ta juyeshi a cikin wani rubber container dan ba’a barinta taci a plates na yan gida. Straight dakinta ta nufa ga yau da alaman ana rana dukda bata leka waje ba a yanda dakinta yawani dau huci kamar oven ga babu window bare tasamu wani ventilation wani dum ta shiga kawai ta zauna kan yagalgalallen bedsheet dake shinfide akan simintin dakin. A hankali tasa hannu tafara cin eggs din saida ta gama ci sannan ta dauki sausages din suma taci. Alhamdulillah tayi tana godema Allah atleast yau tasamu abunda zata kai bakinta kafin ta fita sharan waje. Tunawa da bata dauko ruwa ba yasata sauke ajiyan zuciya tun batayi wani komai ba harta gaji. Dan kwanciya tayi tana maida nunfashi tunane tunane na dibanta saidai jin yanda hucin zafin dakin ya rufeta yasata mikewa tareda daukar container ta fice daga dakin dan yau bazata iya zaman dakin ba a cikin zafin nan gwara ko kitchen ne taje ta zauna tasha iska. Koda ta koma kitchen saitaga har chefs sun fara preparations na lunch dan haka bata yi kokarin zama ba kafin Headservant ta shigo tayi mata bala’i akan kitchen ba gurin zama bane. Abun "shara ta dauko kawai ta nufi waje, fili ne babba sosai ga wani open garage a karshe mike idan" ka shigo gate din gidan da motoci guda 4 a parke Mercedes biyu sai lambo biyu daya pink daya black. Body guards ne guda hudu biyu a gurin gate biyu kuma suna zagaye babu wanda ya nuna ya ganta cikinsu sai guda daya dake bakin gate daya kureta da ido tunda ta fito. Yi tayi kamar bata ganshi ba yanda tasaba dan idan da sabo ta saba. Daga gurin motocin tafara sharowa irin dogon tsintsiyan nan da ake using dinsu a tsaye. Ko rabi batayi ba tafara nishi tana gumi dan wata irin rana ake kwallawa kamar ana dafata. ji tayi kamar ta cire hijab dinta saidai sanin wannan mutumin nanan yasa mata ido bazai barta ta iya cirewa ba dan a hakan ma idanunshi kamar ya chinyeta. Da kyar tanayi tana zama ta huta tasamu ta karasa saidai batakai har gurin gate dinba ta kwashe adan nesa ta shige cikin gida. Nishi takeyi da karfi da karfi duk nunfashi daya sai kirjinta ya ansa. Ta jike sharkaf da gumi sai diga takeyi. Straight dakinta ta wuce a kofar data shanya rigan data cire ta tsaya tadan huta sannan ta ja rigar data kusa gama bushewa ta fita tayi part na masu aiki. Dayake kusan sun gama aiyyukan su banda masu girki dan haka a palour ta gansu wajen su 3. "Gaishesu tayi a hankali basu ansa ba babu ma wanda ya juyo ya kalleta kawai ta shige toilet din. Daya daga cikinsu ne wata yar budurwa cikin daga murya tace “ kada ki taba mana ruwan heater dama, ba tsoho ya siya ba”. Tana fadan hakan kuma Suka wani kwashe da dariya harda" tafawa. "Tajisu sarai saidai tayi kaman bata jisu ba, dukda sosai abun ke damunta saidai tasan yes da gaskiyar su tsohonta bai siya ba, dan a cewarshi mutuwarta shine babbar kyautar da zata mishi. Haka ta kunna ruwan sanyi dan da tayi niyyan tayi wanka sosai saidai ganin bazata samu ruwan zafi ba kuma tana tsoron mura kawai ta dauraye gumin jikinta ta sanya rigarta ta wanke" wandata cire tareda jilbab din sannan tafito. A kofar fita part din sukayi karo da wata yarinya da bazata wuce 17 years bahaka. Yar head servant ce dukda ita ba aikin takeyi ba kawai dai takanzo ta yini a gidan ta tafi da dare. Sauke kanta Miral tayi tana dan rabeta ta wuce. Saurin riko hannunta khalisa tayi tana dauke da murmushi akan cute arab face dinta tadan jawota baya tabude baki zatayi mata magana kawai Miral ta fincike hannunta idanunta suka wani yi ja sukayi ciki ciki tareda cikowa da hawaye tafara girgiza kai tareda yin baya baya daga khalisa kamar taga aljana. "Danne kunnuwanta tayi hawaye na gangarowa daga idanunta bakinta na rawa tana furta “ no no, ban aikata ba wlh, Layla ki fada musu gaskiya Layla , Layla”. Tarinka maimaita hakan a dimauce khalisa ta matsa baya tana zazzaro ido batasan metayi ba, waye kuma Layla? Saurin shigewa ciki tayi sauran maids din dake zazzaune a cikin palourn suka juyo suna kallonta dayan cikinsu kawai ta fashe da dariya harda rike ciki tana fadin “ Jama’a akwai mahaukata fa a gidan" "nan, Layla dake ake fah”." Ta fadi hakan tana nuna ta gefenta da alamun itace Layla. Dan zazzaro idanu tayi tana nuna kanta kafin ta kwashe da wata shegiyar dariya tana fadin “ Ni Layla menayi? Yaushe nazo gidan nan ko wata daya banyi ba shegiyar yarinya ko magana bata taba hadamu ba. zata fada uban me nayi mata kuwa yau”. Da fadin haka ta mike a zabure sauran biyun na dariya kamar zata kashesu suka mike suka bita suka nufi Miral datake zaune a kasa ta janye gwiwoyinta zuwa kirjinta ta kifa kanta akan gwiwoyinta sai surutai takeyi tana girgiza kai. FUREN ZUCIYA. Flower of the heart. By Nasreel R.L. A hausa love story……. Chapter 3; "Su Layla basu karasa inda takeba Khalisa tayi saurin tsayawa a gabansu tayi musu tsakani, cikin dan daga murya tace “Yane badaku takeyi ba, babu ruwanku da ita”. Wani kallo wanda ke bayan Layla tayi nata sama da kasa kafin tace “ ke yarinya matsa mana anan kafin bakinki yayi" jini banason rashin kunya anan niba sa’ar yinki bace”. Kallo khalisa tabisu dashi tareda folding hands dinta a kirji tana kara gyara tsayuwanta alaman bafa zata matsa ba. Gaba Layla tayo kamar zata daketa saikuma dayar dabata yi magana ba tun tuni saidai dariya tayi saurin riko ta tana mata kallon warning. Layla sarai tagane me take mata warning akai. Tasan idan har ta taba khalisa toh lallai yau head servant zata nuna musu masifarta na da ba komai bane dan wlh saita sa an kore su. suda samun wani aikin kuma sai "wani ikon Allah, sannan ana biyansu sosai anan bakuma wani aiki sukeyi ba." Kamar bazata hakura ba dai ganin ita zata chutu hakan yasa kawai ta juya tana ballawa Khalisa harata aranta tana fadin zasu hadu da Miral saita gyara mata zama. "Khalisa ganin sun koma a hankali ta tsugunna dan nesa da Miral sannan cikin tausasa murya tace “ Miral kiyi hakuri, bansan mena miki ba ni kawai kawance nakeso muyi naga bakida kawa ko daya, amma yanzu kiyi hakuri bazan sake ba idan ma wani abu nayi miki. tashi ki tafi daki" kada wayannan marasa mutuncin suyi miki wani abu”. Kamar Miral batajita ba dan still girgiza kanta takeyi tana furta abubuwa dabama zaka gane komai daga cikinsu ba. Takai wajen 5 minutes agurin kafin ta dago kanta da fuskar ta tayi sharkaf da hawaye idanunta sunyi ja fatar face dinta shima yayi ja kamar tomato. A sanyaye ta mike idanunta a kasa ta dauki jilbab da rigar daya fadi kasa ta fita daga part din. Dakinta ta wuce ta shanya kayan a jikin kofa sannan ta shige kawai ta kwanta kan bedsheet din tana shasheka tareda maida ajiyar zuciya. Ko 15 minutes batayi ba bacci ya dauketa bata tashi ba sai washe gari wajen karfe 6am na safe. Wani irin ciwo jikinta kemata batasan ko dan tun jiya da rana take bacci bane kokuma dan cewa kan cement ne da bedsheet kawai take kwance? Mika tayi sannan ta mike aranta tana fadin yau babu zafi sosai saikuma ta tuna maybe dan safiya ce rana bata kwallo ba. Mikewa tsaye tayi tareda jujjuya wuyanta daya sage kamar an buga mata katako a gurin. Wata yauwa ne ta ziyarceta cikinta yayi wani kara tanajin hanjin cikinta kamar an daure mata su. Saurin daukan jilbab daya bushe akan kofa tayi ta zura hannunta nadan rawa kwata kwata batajin kwari a jikinta. Kitchen ta nufa ta tarar chefs na cooking breakfast kanshi natashi taji yawunta yawani tsinke. Kara cikinta yakara yi da sauri ta fita daga kitchen din ta wuce waje ta zauna a terrace dan saita jira sun gama idan da ragowa da ba’ayi serving ba saita dauka. Wajen 10 minutes tayi amma jitake kamar yunwar zata kasheta idanunta sun dan cicciko da kwalla. "Kamar tayi ihu takeji, a rayuwanta ta tsani yunwa. Zata iya jure komai amma banda yunwa duk kankantan yunwa saita gigitata. Jin an bude gate yasa ta juya don ganin waye, ganin khalisa ne yasa tayi saurin dauke kai tafara wasa da siraran yan yatsunta dake daukeda farata masu kyau" daidai hannunta. "Tanajin yanda ta karaso har inda take saidai bata dago ba harta tsaya dan baya da ita kadan idanunta a kanta. Dan sauke ajiyan Zuciya Khalisa tayi sannan tace “ Hello, Miral”. Tana fadin hakan kuma ta cigaba da tafiya zuwa cikin gidan. Dan dagowa Miral tayi jin tabude kofa a tunaninta ta shige tana kallon kofar kuwa suka hada ido. Taso tadauke kai saikuma tadan yi dan guntun murmushi tareda daga mata hannu tanajin nauyin abunda tayi mata jiya dan ita" batamasan tayi bah. "Smile din Khalisa ta mayar mata sannan ta shige tareda rufe kofa. Miral ta juya ta cigaba da wasada yatsunta tana tunane tunanen yanda rayuwa ta kawota nan. Ba uwa ba uba babu ya babu kanwa. Ba kawa babu maisonta, toh inma tanadasu mezasu kara mata banda ciwo?" Ciwon da har abada bazai taba warkewa bah? Nunfashi ta sauke tareda mikewa ganin rana yafara dukantanta gari yafara zafi ta shige ciki. "Kitchen ta shiga wanda ta tarar da head servant a ciki tana ba maids orders din ayyukan da za’ayi, alamun chefs sun gama kenan. Kallo head servant ta wurgama Miral tareda dauke idonta tana yamutse fuska. Babbar matace zatakai maybe 50 years tamada bitch face irin me tsorata yara ga wani black lipstick datasa a bakinta da kwalli daya dambaro batada tsawo ko" kadan ranta a hade kamar mala’ikar mutuwa. Sunkuyar dakai Miral tayi sannan ta nufi side din kitchen da ake wanke wanke ganin har an fitoda plates da mugs da sauran abubuwa na wankewa yasa ta nade hannun jilbab din ta wanke komai tas tas sannan ta sakasu a dishwasher ya gama ta kashe lokacin head servant da sauran maids din duk sun tafi yin ayyukan su. Fridge din leftovers ta bude saidai yau babu sa’a dan babu koh faranti a ciki tawani waro ido da nandanan yaciko da kwalla tai narai narai da fuska kenan yanzu bazata samu breakfast ba? Kodai ta duba main fridge ne? Saurin girgiza kai tayi tuna shekaran jiya bazataso a kara kamata tana daukar abinci ba. Kamar daga sama taji an kwalo mata kira tayi saurin mikewa daga tsugunnen datake ta mike tajuya inda taji muryan. Daya daga cikin maids din gidan ne tace mata taje ciki Ummi na kiranta. Da ok ta ansa aranta tana tunanin mekuma zatayi ma Ummi? Ko wanki zatayi? Amma kuma ai ko kwana uku batayi dayi mata wanki ba. Kauda tunanin tayi ta wuce palour tana tafiya a hankali dan jikinta babu kwari kwata kwata. A kujerar datake zama ta sameta a hakimce fuskarta dadan sarari dan yau ba’a murtuke takeba. Gakuma wata mata gefenta sanye da jeans da blouse ta rufe face dinta da face mask da wani shades a idanunta babu abunda kake gani a bayan wuyanta. Gaban Ummi ta tsugunna ta gaisheta kanta a kasa Ummi tayi mata alama ta gaida matar. Juyawa tayi ta gaisheta batareda ta dago kai ba sama sama matar ta ansa sannan ta juya ta kalli Ummi cikin harshen turanci tace “ Can we start? I don’t have time to waste”. Gyada mata kai Ummi tayi matar ta tambaya a Ina zasuyi? "Dan jim Ummi tayi dan batayi wannan tunanin nan ba, ganin kada ta batama matar lokaci kawai tace suje guest room dake anan kasan. Mikewa matar tayi Ummi ma ta mike tace Miral ta biyosu. Tashi tayi tanajin yanda kirjinta ke bugun uku uku mekuma za’ayi yau? Yanzu tsoro yafara shiganta meke shirin faruwa ne? Me Ummi zatayi da ita? Suwaye wayannan dake zuwa" ganinta haka?. Ganin an nufa guest room yasa taji toh kodai aiki zatayi ne? Questions sunfi dari suke shigo mata gashi babu mai ansa mata. A daidai kofa ta tsaya Ummi ta shige chan cikin ta zauna bakin bed tana nunfarfashi tsabar kiba. Wata jaka matar ta ajiye a kan gadon tareda budewa ta fara fiffito da wasu karafuna da kayayyaki kana gani kasan kayan hospital ne kaman za’a duba mara lafiya. Juyowa tayi ta kalli Miral tace ta cire hijab din jikinta tazo ta kwanta. "Wani irin faduwa gabanta yayi kwakwalwarta takasa daukar me akece. Wani irin kallo tayi ma Ummi dabata masan tayi ba dayasa Ummi ta daka mata tsawa, batasan lokacinda tazo ta" kwanta kan gadon bah. "Matar tace ta tashi ta cire hijab, jikinta na karkarwa ta mike ta cire hijab din sannan ta koma ta kwanta. Ganin matar ta matso dab da ita sannan tasa hannu ta daga rigarta zuwa cikinta yasata sakin wani ihu ta zabura ta damke rigar ta rufe jikinta dan babu komai a jikinta bayan rigar" batada undies. Wani gigitaccen mari Ummi tasakin mata dasaida ganinta da jinta gabadaya ya dauke. Duk kawai taji tama kasa motsi dan ba’a taba mata mari irin hakan ba. Hannu Ummi tasa ta damko wuyanta tareda baya da ita ta kifo kan gadon ta kwantar da ita dakyau da saida ta fizge hannun Miral daga jikin rigar ta kwayeshi har zuwa cikinta kafin Miral ta dawo daidai. Jin hannun Ummi akan wuyanta kamar zata kasheta dukda ba matse mata wuyan tayi sosai ba amma ta sakin mata nauyin hannunta dayake kamar dutse tsabar nauyi. Dakyar take jan nunfashi tana jin yanda matar tasa hannunta akan naked private part dinta. Mani marayan kuka ta saki tareda fara shushura kafa tana shasheka dayasa Ummi ta shake wuyanta sosai da tuni ta nutsu jin kamar ranta na fita daga jikinta yasa Ummi tadan saki kadan yanda zata ita nunfashi amma bata saki gabadaya bah. "Ko minti daya ba’ayi ba matar ta ja mata rigar tarufe sannan ta kalli Ummi tace “sakin mata Wuya kada ki illata ta nagama, basai nayi wani further examination bah Hymen dinta is intact, dan haka ac….”. Shiru tayi dan ganin sign da Ummi tayi mata tagane ba’aso yarinyar tasani. Dan haka saita chanza maganar kawai tace “ a ina take kwana?” Tafada tana shafa fatar kafar" Miral. Sakin wuyanta Ummi tayi sannan ta tambayi Miral. Cikin wata wahalalliyar murya datake breathless very soft tace “ A store room na storage area”. Dan shiru Ummi tayi dan batamasan a ina take kwana ba sai yau. A iya saninta a palourn masu aiki da akace mata tana kwana batasan yanda akayi takoma wani store room ba. Gyada kai matar tayi sannan tace “ akwai zafi ne a dakin sosai? Ya ventilation din yake?”. Miral ta ansa mata da cewa akwai zafi sosai sannan babu window. "Kallon Ummi tayi sannan tace “a chanza mata daki, infact ta dawo nan damuke ta zauna na lura babu kowa dake anfani da dakin. Skin dinta is rough duk kananan kurajen zafi kinsan kuma bama daukar wannan koh? Dan haka ta dawo nan da zama in the meantime kuma akwai meal plan da supplements dazata rinka using. Kada ta rinka fita rana sai karfe 6 na safe na 20 minutes kawai bayan haka ta zauna a cikin daki ba aiki na lura hannunta is not as soft as we want alamun tana aiki da ruwa sosai ko wanki. Sannan kayanta might be contributing to rough skin din dikda skin din nata nada kyau dan inba medical professional ba bazaka gane akwai" something wrong with it bah. Sannan kwana nawa zaku kara anan din?”. "Dan gyada kai Ummi tayi dan sam zuciyar ta bata so hakan ba. Tunda dai tana iya kwanan store room din koba window ai yafi ta rabu da ita dai a chan din, amma babu komai. Nanda 1 week zasu koma Ghair muaddal ta yarda kwallon mango ta huta da kuda, dan haka kawai saita ce toh tunda dama babu kowa a guest room din sannan akwai wani koda tayi baki. Dan haka ta" ansa ma da matar 7 days zasu kara. Da haka matar ta kwashe kayanta ta mayar cikin bag din sannan ta juyo tayima Miral one final look ta cikin shades dake face dinta ta fita. Binta a baya Ummi tayi da sauri dan sauri. Tafiyar nasu ba daya ba. Ganin bazata iya kamo matar bane yasa ta kirata da Miss! Miss! Tsayawa da tafiyar datakeyi matar tayi tareda juyowa ta kalli Ummi ta cikin shades ummi tayi saurin karasawa inda take tana nishi tace “Yanzu tunda kun tabbatar yaushe ne kukeso a kawo muku ita? Nanda 7 days zamu tafi Ghair muaddal shin a airport zaku ansheta? Kokuwa zan tafi da ita har gidan iyayenta ne dan chan muke sauka”. "Shiru matar tayi kamar bazata ansa ba chan kuma tace “wannan maganar ba’a hannunki yake ba, duk lokacin da muke so zamu zo mu dauketa, bama sa lokaci dan mu mukeda lokaci ba lokaci keda muba”. Tana fadin hakan kuma ta cigaba da tafiyarta. Ummi taso ta tambayeta ta ina zata samesu ko subata number amma sanin bazasu bata ba yasa kawai ta juya. kan sofa ta zauna tana cizon thin lips dinta tana abun sosai yayi mata ciwo sunki su ansa mata kowani question datake musu. Babu wanda yake treating dinta da wannan rasin mutuncin banda su dan kowa yasan waye su a duniya bama guri daya ba. Mijinta nada one of the biggest car manufacturing company a duniya. Kowa cikin respect yake dealing da ita amma su basada" wannan. "Sannan ma babu abunda yafi mata ciwo sai ganin cewa sufa wayannan ma dasuke zuwa kananan rank ne a kungiyar, bama manyan bane amma suna jinsu kamar duniya na juyi ne saboda su. Ita babu abunda ke damunta ma sai alkawarinta, batasan yaushe zasu dauki yarinyar ba dan haka bata san yaushe zai shigo hannunta ba harsai sun dauketa. Kamar tayi ihu haka takeji ta zaro wayarta ta kira head seevant a kawo mata abinci dan wata mahaukaciyar" yunwa takeji dukda ko 1 hour da gama breakfast batayi ba. FUREN ZUCIYA. Flower of the heart. By Nasreel R.L. A hausa love story……. Chapter 4; A bangaren Miral kuwa kuka takeyi sosai ta nade jikinta akan bed din kamar ball jikinta na kyarma brain dinta takasa daukar abunda ya faru. Wani irin zafi zuciyarta keyi shin wannan wani irin keta haddi ne? Mezai kawo wannan abun? Meyasa Ummi zatayi mata hakan? Kawai idan ta tuna yanda taji hannun matar akan sirrinta na ya mace harta iya bude baki ta fada ma Ummi wai She’s Untouched saitaji wani ƙuna a zuciyarta kamar ta hadiye zuciya ta mutu. Meke shirin faruwa da itane? Saida taci kukanta ta gaji sannan ta mike tareda share hawayen face dinta dayayi ja sabon kumburin mari ya fito akan wanda Hanat tayi mata daya kusa warkewa. Sai a lokacin ta tuna a inda take. Bin dakin da kallo tayi ba yau tafara shigowa guest room dinba saidai duk shigowan datakeyi na gyara ne idan Ummi zatayi baki. Yau tafara mishi kallon kurilla dan kuwa ya hadu dakin sosai dukda interior dinshi is simple. "Komai a dakin brown ne da touch of white. Queen sized bed ne da takejin laushin katifar kamar ta kwanta a kan audiga. Full sized wardrobe ne ta left side, opposite gadon kuma full length mirror ne da dresser da babu komai akai banda lotion biyu dakuma bodywash daya da turaren" Reef da duk ba’a taba suba. Ta right side kuma frame ne said kofar toilet. Ajiyar zuciya na ba adadi ta sauke tanajin yanda jikinta ke kara lumewa a katifar. Rabon da ta kwanta kan katifa ta manta jikinta duk sai taji wani iri dan yafi sabawa da kasa. Ga AC dake tashi dakin yayi sanyi dayasa tayi yunkurin janyo white comforter dake folded neatly a karshen gadon. wata zuciyar tace mata kada ta taɓa. Haka tajanyo jilbab data wurgar a gefen gadon ta saka tareda kudindine jikinta a ciki. "Tunanin maganar matar tayi nacewa a barta anan saboda jikinta yayi kyau. Mezasuyi da kyan jikinta kuma? Tunawa tayi Ummi tace sauran sati daya su koma Ghair muaddal, kenan da ita za’a koma? Me komawar zai haifar mata? Shin zasu karbeta? Bayan duk ab… saurin katse" tunanin tayi tasa hannu ta buge kanta kamar hakan ne zai tsayar mata da tunanin. Jan nunfashi tayi tareda saukewa kawai ta janyo comforter ta cire jilbab din jikinta ta rufe jikinta da confortern ta daura kanta akan lallausar pillow wani laushi da dumi daga kan confortern har zuwa pillow da katifar ya ziyarceta batasan sanda ta lumshe idanu ba tareda sakin wani moan da saida taji tamanta duk wani matsala datake dashi. Wani tunani ne yazo mata toh kodai saboda zasu koma Ghair muaddal ne yasa ta kawo wata ta dubata? Kodai aure zata mata? Dan dariya tunanin yabata dan tasan bazata iya aurar da itaba dan babu wanda zai aureta kowa yasan me babanta yace akan ta dakuma duk wanda ya rabi kanshi da ita. Toh kodai sunce a dawo da ita gida ne? Kodai sun gano gaskiya ne? Kokuma Ummi nason ta maidata ne kada ace tayi abusing dinta? "Tunane tunane, question bayan question haka suka rinka jerawa a cikin brain dinta batasan" lokacin da wani daddadan bacci ya kwashe taba. Jin kamar ana bubbuga ta yasa ta mikewa a sukwane tana zazzaro idanu. Layla tagani akanta fuskarta daure tamau kamar ta shanu sai huci take tana harararta. Dauke ido tayi tana sosa kai dan jitake kamar a mafarki take kamar kuma a gaske dan yanda sanyin dakin ke shigarta ya rikita mata brain dinta data riga ta saba da azabar zafi a koda yaushe. "Tsawa tsawa fada fada Layla ta kira sunanta daya tabbatar mata da ba bacci takeyi bah ta tashi. Dago ido tayi ta kalleta ganin irin kallon datake mata kawai ta sauke idonta cikin muryar jin bacci tace ‘na’am”. Tsaki Layla tayi sannan a kufule tace “akace wai makaho an samu idanu, ga abunci nan da na tabbatar baki taba cin irinshi ba ance ki cinye tas, banmaga dalilin da Ummi zatace a fada miki hakanba dan kowa yasan kedin yar yunwa ce kuma barauniya, dan haka yau ba sai anyi halin beran ba. Sannan ga supplement pill nan kisha daya daga kowanne" container”. Tana gama fadin haka tay tsaki ta juya ta fice. "Ciccikowa idanun Miral sukayi da kwalla jin yanda ta kirata da barauniya, ita duk zagin daza’ayi mata baya damunta amma sunan barauniya na daya daga cikin abubuwan dake mugun damunta. Gashi wannan tasan tabbas tayi, ta saba daukar abinci, amma Allah na gani sai" batada yanda zatayi yunwa zata mata illa take dauka. "Tuna hakan yasa taji wani zafi a zuciyanta. Yaushe ne wannan rayuwar kunci da kaskanta zai kare? Share hawayen daya zubo tayi tajuya ta kalla tray din abincin da aka ajiye mata a kan side bed drawer. Mashed potatoes ne a plate da chicken soup a bowl sai tiriri sukeyi, ga cup of warm milk a gefe da bottle of chilled water. Saikuma wasu containers da babu label ba komai" bare ta karanta da alamun sune supplements din. "Sosai yawunta ya tsinke takasa dauke idanunta akan abincin rabonda taci abinci lafiyayye daba ragowa ba sannan kuma complete ta manta. Bawai bata samun mashed potatoes din bane ko chicken soup din, kawai dai da wuya tasamu complete food saidai idan tasamu mashed potatoes toh bazata samu soup ba. Saidai kuma tana dadewa bata samu chicken soup ba dan" "gabadaya akeyi so masu aikin gidan suke ci, kafin yazo kanta ya kare." Wai yau ita aka kawoma abinci a cikin daki take kwance kan lallausar gado tanashan AC? Anya ba mafarki takeyi ba? Jin cikinta yafara murdawa ne yasa ta sauke kafarta kasa sannan ta dauki spoon daga kan tray din tafara tuttura abincin da sauri da sauri kamar mai tsoron a kwace mata. "Ko 5 min batayi ba tagama ci cikinta ya cika sosai data manta yaushe rabon da cikinta yacika haka, ga abincin da zafinshi da bazama ta iya tuna ya abinci mai zafi ke tasting ba. Madarar kawai yarage half cup bata shanye ba sai supplements din. Tunanin shan supplements din takeyi dan batasan na menene bah. Gashi babu label ko rubutun komai a container. Daukan gudadaya tayi ta bude taga babu wani yawa a ciki basufi guda ten ba kawai ta dauka daya dan za’a iya ganewa idan bata dauka ba dayen ma ta bude ta dau daya tayi ta toilet tay flushing" dinsu dan bazatasha abunda batasan mezaimata ba. Bin Toilet din da ido tayi bashida girma sosai saidai ba karami bane daidai na guest rooms dai. Ji tayi tanason tayi wanka saidai tuna batada kaya anan yasa ta fasa kawai ta fito tadawo ta kurbe milk din dakyar dan cikinta yacika sosai ta cire bottle of water din daga kan tray sannan ta saka jilbab ta dauki tray din ta fice daga dakin. "Kitchen takai tray din Sannan ta fara wankewa. ummı ce ta shigo kitchen din da saurı kaman an wurgota. TSawa ummi ta daka mata ""uban waya Saki wanke wanke? neman sai dole anyı mıkı fada koh! zakı ajiye ko sanayı mıkı dukan mutuwa"". Saurı mıral tayı ta ajıye tana mamakın yanda ummj ta harzuka akan wanke wanke. Kamar ba ita tasata rinka wanke wanken ba a baya. Wanke hannu tayi. ummı ta wuce daga kitchen dın, miral Saida tabarı tayı nisa sannanta" juya ta nufı dakinta. Kayanta ta kwaso kaf dinsu dama ba yawa ne dasu ba. batada komaı banda yan kayan Sawan dan haka bata tsaya komai ba ta koma main Part zuwa sabon dakinta aranta tana tunanin ko ıya yaushe zamanta anan dakin zai kasance. Tana Shiga ta tarar da wata suitcase a gefen gadon dakin. Kamar bazata bude ba kuma ta dagota zuwa kan gadonta ta bude ZiP din. "Cıke take fam da kayan sawa. Dogosu tafara daya bayan daya. dogayen rıguna ne daidai sıze dinta na pure cotten kusan ırınna jikinta Saidaısu sababbıne gal sannan sunfı najıkınta kyau da alamun kuma sunfisu tsada saboda design dinsu. Wajen guda 12 ne sai wasu abayas suma guda 12 a ciki da underwears bras 12, pants 24. Binsu da ido tayi tans tunanin ina suka san size dinta saidai tuna matar nan babu abunda bata gani a jikinta ba yasa tayi saurin cire tunanin a ranta dan batason kara tuna abun, tasa aranta cewa bai taba faruwa ba bakuma zata sake" tunawa ba. Nunfashi mai karfi ta sauke sannan ta maida kayan ciki ta rufe. Kan bed din ta koma ta kwanta har yanzu ji takeyi kamar a mafarki. "Haka rayuwa ta kasance mata harna tsawon kwana biyar tana daki bata fita sai safe tayi 20 minutes kachal sannan tadawo cikin dakin gashi kullun ana kawo mata breakfast, lunch, dinner har daki abinci masu kyau da lafiya tareda gina jiki bata komai saidai ta zauna tayita tunani." Ayyukan data sabayi ma yanzu batayi jikinta yayi wani irin kyau fatarta ta kara haske har wani healthy glow takeyi sannan Ummi tasa an fitar da tsofaffin kayanta so wayannan sababbin dresses din take sawa. "Dukda tanajin kamar kamai ya lafa Ummi sau daya take zuwa dakin ta dubata kota bata umarnin wani abu sannan ta duba ko tasha supplements din wanda har yanzu basha takeyi ba flushing dinsu takeyi amma batajin koda digon kwanciyar hankali a cikin zuciyarta. Takasa tasa ranta cikin salama dan bataga inda wannan chanjin zai kaita ba. Gabadaya Ummi ta chanza mata dukda ba kirki take yi mata ba amma kuma sam bata dukanta yanzu, sannan idan ta shigo saita tsareta da ido sosai tana kallonta, sai taji wani iri dan bata gane kallon menene take mata" ba. Bakuma ta kara haduwa da Hanat bah shine babban abunda take godewa Allah dashi a cikin zaman dakin datakeyi dan ta tabbatar da tacigaba da aikinta dole su rinka haduwa and haduwa da Hanat bad news ne dan in babu mari akwai duka kokuma ta hada mata su gabadaya. Kwance take yau kan gadon dakin ya dauki sanyi da harta fara sabawa da sanyin da dakin keyi dan tarage shigewa comforter all the time. Zaman kadai kwata kwata baya damunta dan inda sabo ta saba. Saidai yau kawai ji tayi zaman yayi mata yawa duk jikinta yayi tsami dan tariga ta saba da ayyuka jikinta na motsawa yanzu kuma banda kwanciya sai zama. Tashi tayi tana tunanin ko tayi wanka ne saikuma ta fasa ganin batawani dade dayin wankan ba dan still ma towel ne a jikinta takasa chanza kaya tsabar yanda taji jikin nata babu kwari. Gaban mirror taje ta tsaya tana kallon kanta. Sosai face dinta tadan cicciko skin dinta yana wani glowing kamar wanda akama gyaran amare tayi haske sosai duk wani tan na aiki cikin rana yafita daga jikinta da wayannan kananan kurajen zafin duk sun tafi. "Idanunta dasuke dan ciki-ciki yanzu sun cicciko sosai daya kara ma face dinta wani cuteness da haiba, brown eyeballs dinta ya kara haske farin dake surrounding idanun nata shima ya washe saidai still oily look dakuma tired eyes din nata nanan. Lips dinta sun kara pink kamar tasa" lipstick looking so soft and moist har dan red-red sukeyi. "Sosai ganin yanda takoma a cikin yan kwanakin nan yabata mamaki dakuma tsoro. Bata cika kallon mirror ba amma tasan dai dole da bahaka take ba, dan zata iya cewa tun bayan tabaro Ghair Muaddal rabon data samu kwanciyar hankali dakuma bukatar ta kalli kanta a mirror ta" manta. "Turo kafar akayi da wani violent push da saida kofar ta bugi bango ta komawa wanda ya turota. Wani razana Miral tayi, tayi saurin juyowa ta kalli kofar dan ganin waye ya bugota haka kamar" za’ayi mata sallamar mutuwa. FUREN ZUCIYA. Flower of the heart. By Nasreel R.L. A hausa love story……. Chapter 5; "Sosai Hanat ke kallon Miral ganin yanda tsantsan kyanta ya fito. Wani bakinciki taji ya daki zuciyarta da saida idanunta suka rikida suka koma ja, gashi yanda Miral take cikin towel santala santalan sexy legs dinta duk a waje so nicely shaped ga manya manyan light brown eyes data" waro mata tana kallonta tayi looking so bewitching. "Ajiyar zuciya Hanat tasaki tana jin yanda zuciyarta ke tafarfasa gashi Ummi tayi mata warning me tsanani akan dukan Miral, bakuma tasan meyasa Ummi zatayi mata hakan ba, dan a tunaninta kodan za’a mayar da ita gida Ghair Muaddal ne saidai kuma Layla ta fada mata babu wanda zai anshe ta koda an kawo ta. Sosai abun yaba Hanat mamaki gashi Ummi takasa gaya mata dalilin kawai dai tafada mata saboda ita takeyi sannan idan lokacin yazo zata gode mata" dakanta. Tuna hakan ne yasa ta kwantar da wutar bakin cikin dake ruruwa a cikin zuciyarta ta zayyanar ma Miral sakon da Ummi ta aikota dashi tana danasanin shigowa dama yar Aiki ta fadamawa. “Kallon uban me kikemun haka ne barauniya?”. Saurin sauke ido Miral tayi tana addua Allah ya rabata da Hanat lafiya batason a taba mata lafiyar jikinta yanzu. "“Ki hada e naki e naki gobe zamu wuce Ghair Muaddal, kiyi shigan arziki dama kan ace muna musguna miki, mai kama da maza kawai”. Ta fada tana kallon kirjin miral da yanzu yadan ciko" bakamar da ba sannan ta juya ta fita tareda buga kofar shut a bayanta. "Miral dake kallon kasa jin ta fice yasa ta dago tanajin wani iri a zuciyarta takasa gane mema takeji. Wai gobe zasu koma Ghair Muaddal. Shin dadi takeji ne kokuwa tsoro ne, tanaso taji dadi da tasan yanzu komai ya nuna kanshi cewa dawoda ita gida za’ayi toh kenan sunaso tadawo tunda har Hanat tace tayi shiga mai kyau kada a gane ana musguna mata. Wani feeling ne ya mamaye zuciyanta mai kama da happiness da excitement, kenan sun yafe mata? Kodai sun gano gaskiya ne? Dama shiyasa Ummi tadawo da ita nan kenan ake bata ci da sha harda" su supplements dan tayi kamar ana kula da ita? Kara kallon kanta tayi a mirror a take kuma taji tanason tayi looking best dinta inzata koma. Kallon kurilla tayima jikinta saidai duk towel din yarufe komai babu abunda take gani sai chinyoyinta dayake mirror din ba har kasa bane. Zare towel din tayi a hankali tana kallon kofa kada a shigo daga ita sai wata half vest data gani a cikin suitcase din sai pants jikinta yaciko shima sosai ko ina yayi bul bul sosai shape dinta yakara fita waist dinta still so small and flat hips dinta da su sukafi cika a cikin jikinta da butt dinta so round and shapely shape yafito asalin pear dinshi dukda bawani kiba ne tayi ba. "Chest dinta ta kalla da shima yadan ciko amma ba sosai ba, ta tuna maganar Hanat wai mai kama da maza tasan da kirjinta takeyi, wani iri taji tuna yanda kirjin yanmata yake ita nata har yanzu kamar bazasuyi girma yanda ya kamata ba. Tunani takeyi kodai tasha supplements dinne tunda zai iya yuwuwa ne kiba ne dan boobs dinta su kara saidai kuma tasan batasan na" menene ba bazatayi gangancin shaba. "Sakin towel din tayi gabadaya kawai ta wuce ta bude suitcase tafara daddaga abayoyin ciki. Luxury abayas ne irin wayanda Hanat kesawa, sababbi ne duka tabisu tana kallo daya bayan daya sosai sukayi mata kyau da batasan sanda wani smile ya bayyana a face dinta ba. Colors uku ne, wajen guda 8 black ne saidai kowanne design dinshi daban, guda 2 kuma pink sai 2" white. Daya daga cikin black din ta dauko da aciki tafiyi mata kyau da haduwa sosai tasha beads akan embroidery design na jiki baiyi too much ba baikuma yi kadan ba. Camisole dake hade da kowanne abaya ta dauko na black din ta zura sannan ta zura abayan gudu-gudu tayi gun mirror tana kallon kata ba karamin kyau tayi ba sosai black din yayi complementing skin dinta. "Smile ne akan face dinta ear to ear data kasa boyeshi tayi sarin komawa ta dauki mayafin abayar ta daura a kanta tayafa shi. Sai kallon kanta takeyi ita kanta tasan tayi kyau tawani juya idanu tareda fashewa da dariya kawai hango kanta takeyi a Ghair Muaddal tareda familyn ta itama tazama kamar yanda su Hanat dasu solail suke. Tunani take inama da kayan makeup, da" ko kwalli ne tasa. Komawa tayi kan suitcase din pocket dabata ma lura dashi ba sai yanzu ta bude yan kayayyaki ne a ciki daga lip gloss sai kwalli sai scrunchies guda 3 na daure gashi basuda kauri sosai sai kuma set biyu na jewelry kana gani kaga pure gold ne guda daya dayen kuma silver chain ne mai wani diamond shape crystal da tana gani tasan diamond din gaske ne. Ganin harda jewelries yakara tabbatar mata da lallai gida zata koma dakuma dukka alamu zasu karbeta. Face na layla ne ya fado mata arai kwatsam. Tunani takeyi shin zataga Layla a gidan? Sunanan har yanzu? Umm Layla ma nanan? Ko asirinsu ya tonu shiyasa akace a dawo da ita? Shin layla sunyi regretting abinda suka mata itada umm Layla? Ko za’a sata school itama su shiga tareda solail da Hanat University of Ghair Muaddal? Ganin tunane tunanen Layla na neman fidda ita daga cikin farin cikin datake ciki yasa kawai ta cire abayar ta saka doguwan riga a jikinta ta koma gado tana sauke nunfashi duk wannan excitement din na fita daga jikinta dan duk yanda taso tacire tunanin Layla da Umm Layla takasa. Tana cikin haka bacci ya kwashe ta. "A bangaren Ummi kuwa sosai suke ta shire shirye itada Hanat datake jin kanta kamar zaiyi hayaki komai ya kwabe mata. Yau mijin ta MR. Omar Zolkrov watanta uku bataji daga gareshi ba, yadena daukar wayanta, data fara kiranshi da wayar Hanat ma saiya dena dauka saidai ya kira yarshi kawai da kanshi cikin dare ko idan tana school danma kada taganshi tayi mishi magana. Sosai abun ke damunta bawai yau suka fara fada a tsakaninsu yatafi yayi watanni" baiyi mata magana ba baikuma dauki wayarta ko yabari ansan inda yake ba. "Saidai tana ji a jikinta wannan din na daban ne dan tasamu labarin a yanzu hakan yana Ghair Muaddal, sannan kuma an ganshi da wata yarinya wanda shine yafi daga mata hankali dan a duniya zata iya jure komai musammam ma akan mijinta Omar dan kodan yanda mutane a friend circle dinta suke zama jealous and pink with envy yanda tasamu miji mai kudi kamar Omar. Bawai su mazagen nasu basuda shi bane shi Omar yakai wani matsayi a duniya da kudi kadai bazai siya ba, dan haka dole duk yanda zatayi tazama ita kadai, sannan sucigaba da" zama sai yanda takeso zatayi shi. Babban tashin hankalin nata shine maganar tafito fili kafin mutanen dasuka yi mata alkawari guda Biyu kachal da bata bukatan wani abu bayansu na cewa mijinta zai zama nata ita kadai sai yanda tayi dashi ko yanaso ko bayaso kuma babu asiri ko laya dazasuyi anfani dashi a cewarsu sunfi karfin wannan. Sannan kuma zasu mallaka ma Hanat Imad wanda bayan Crown Prince na Ghair Muaddal shine second in line to the throne. Abu daya dayasa zuciyar ta ta kasa kwanciya dukda tasan lallai dole zasuyi mata hakan dan idan abunda ya wuce wannan ma zasu iya ba kananan mutane bane kungiya ce suke da ita babu Wanda yasan mesukeyi saidai ta gagari duniya da koda ansan abunda sukeyi duk wata kasa ko kungiyan security duk girmanta da shahara a duniya saisun shafe ta dan haka babu wanda yake shiga sabgar su. Matsalar kawai shine sunkasa su fada mata yaushe ne takamai-mai zasu biya mata bukatunta. A cikin contract din sun bayyana cewa harsai sun dauki Miral zasu cika mata alkawarin dasuka dauka. Amma kenan yaushe ne zasu dauketa? Sunki fada. Gashi batada yanda zatayi tayi contacting dinsu. "Tunani takeyi shin mezasuyi ma Miral din? Saidai tasan batada ansar wannan kuma koda ta tambaya ba ansa mata zasuyi ba. Abu daya datasani wanda yaje baya dawowa duk rintsi ko tsiya shiyasa babu wanda zaizo yace ga abunda sukeyi, dan ba’ayi wanda ya shiga ya fito ba bare yafada abunda ke wakana a cikin kungiyar. Sannan bazaka taba cewa ga inda suke ba," basuda inda zaka duba kace anan suke. Shiyasa kamasu ma ba abunda zai yuwu bane. Hanat dake dakinta bayan ta fita tabar Ummi tagama mata complain akan daddynta da ita ko a jikinta a cewarta matsalarsu ce ba nata ba sunsaba. gabadaya hankalinta nakan zuwa Ghair Muaddal gobe. Abubuwan dazatayi sai replaying dinsu takeyi akai kamar film hardaddiyar fuskar nan nata yau banda dariya babu abunda ke kanta. "Hango kanta takeyi gata ga Solail da Layla sun fara zuwa University of Ghair Muaddal. Ga classy rich girls like her da wanda suka fita suzama kawaye. Friends life, night parties, rich handsome boyfriends, girls night da duk batayi anan ba dayasa takejin nan din is boring dan duk ta raina yaran dasukeyin high school dasu shiyasa koda tayi graduating last year taki fara" school ta dage saida Daddynta ya yarda taje Ghair Muaddal. "Bata kwasa komai ba dan tun achan tasa anyi mata shopping anyi stocking kayanta a gidan su Solail dan achan zata zauna Ummi dawowa zatayi. Tunanin Miral tafarayi, tunda itama gidansu zata koma kenan zai zama a gidansu Miral zata zauna kamar yanda itama Miral take a gidansu yanzu?. Wani iri taji a zuciyanta dan kwata kwata ganin Miral takeyi a matsayin kaskantacciyar baiwa da babu wanda keso dan haka kwata kwata bataji tanason zama a gidansu ba. Wata zuciyar ne tace mata ai koda a gidan su Miral din ta zauna tafi Miral matsayi dan Solail tafada" mata bazasu karbeta ba. Dan dariya tayi tuna yanda taga Miral dazu cikin farinciki. Tasan bazai wuce tana tunanin zata koma gidansu bane itama tazama classy gorgeous rich babe kamar ita da solail. Wani kwashewa da wata azzalumar dariya tayi tana hango fuskar Miral idan sukaje taga ba yanda tayi tunani bane. Kan bed dinta ta fada tareda daukar latest iPhone dinta ta shiga Instagram ta dauki hoton freshly done nails dinta dasukayi tsawo da tsini kamar zatay dambe tayi caption ‘ Bye to my old life✌’. Ko 5min ba’ayi ba saiga likes da comments rututu kowa nason yaji metake nufi. Tanada wajen 10m followers a instagram kawai. Tana posting pics dinta sosai da lifestyle dinta datasan kowa na envying. Abunda yafi zama viral shine car collection dinta a cikin underground garage datake sa followers dinta su zabar mata motar dazata hau for the day. Sosai takeson attention din da take samu a social media dan tana ganin yanda mutane keta tambaya tayi wani murmushin gefen baki aranta tana ayyana bazatayi posting wani abuba sai bayan two days dan tasamu comments dayawa na masu guessing mezai faru. "Call din daddynta ne yashigo wayarta, da mamaki take kallon call din na ringing dan sunyi waya jiya bawani waya sosai sukeyi ba. Gyaran murya tayi sannan ta tashi zaune ta dauki call din." Voice call ne a nutse tayi mishi sallama kamar ba Hanat ba. Bai ansa gaisuwar ba ya tambayeta ina Ummi. Gaya mishi tana daki tayi voice dinshi sak na Hanat saidai kanaji kasan na miji ne. Ok ya ansa shiru baice komaiba harta zata ya kashe zata cire wayar a kunninta yace “Ki gaisa da new mom dinki”. Wani durum kirjinta yayi saida ta hadiya iska tama kasa ansawa. "Muryar dataji tashigo daga wayar yasa kanta bugawa. Aunty dinta, no. Cousin din mamanta dasuka dauka kamar Uwa. Magana takeyi amma kwata kwata Hanat takasa ma gane metake fadi. Muryar daddynta dataji yasata dan dawowa daidai yana tambayanta meya faru. Ba komai tace mishi tabashi hakuri kawai ta kashe wayar ta mike da gudu ta fita daga dakin sai dakin" Ummi. [tohfah guys. Mekuke tunanin zai faru? Wannan wani irin set up ne mijin Ummi zai auri cousin dinta? Shin Ummi zata bar hakan ta faru kuwa?]. FUREN ZUCIYA. Flower of the heart. By Nasreel R.L. A hausa love story……. Chapter 6; The next day; "Miral tunda ta tashi takejin wani nauyi a zuciyarta, Takasa gane ko farin ciki takeyi ko bakin ciki da zuwan wannan ranar. Gabadaya tunaninta ya karkata ga yanda zasu tarbeta. Anxiety ya mamayeta sai ayau takejin anya kuwa zasu karbeta?. A haka tayi wanka ta shirya tsab cikin black abaya datayi rolling mayafin a kanta ta dauko yan kayan make up tayi simple makeup" dayayi mugun mata kyau yakara fito fa kyanta na aynihi. Flat shoes ta saka ta kalli kanta a madubi she looks like a model she looks so classy and young skin dinta ya kara kyau yana glowing takasa dena kallon kanta. Sosai kamarta da mummynta ya fito a face dinta dayasa taji wani bakin ciki ya sauko mata a zuciyarta tunawa da mommynta datayi. Me kamar ta taimaketa dashi? Sanda sukayi watsi da ita kamar ba yarsu ba?. Saurin dauke kanta tayi daga mirror din ta koma kan bed ta zauna tana kallon luggage dinta data ajiye a gefen bed din tana tunanin yaushe zasu tafi dan bataga kowa ba daga Ummi har Hanat ko breakfast ba’a kawo mata ba yau bare a fada mata yaushe za’a tafi. Mikewa tayi tafara sassarfa a dakin tayi nan tayi chan sam babu wani nutsuwa a zuciyarta. Wajen ten minutes tayi tana haka kagin ayi knocking kofar batareda an jira ansarta ba aka bude kofar aka shigo. Wata maid ce ta shigo dakin dauke da tray a hannunta. Kan side bed ta ajiye tray din sannan ta juyo ta kalli Miral tace “ Madam tace a fada miki nanda 8 zaku tafi”. Ok Miral tace mata sannan ta tambayeta ko karfe nawa ne yanzu? Ansa mata tayi da yanzu 7:30am ne. Miral tace tagode sannan maid din ta fita. Sauri Miral tayi tazo gurin abincin dama dan yunwa yunwa takeji ta zauna tafaraci. Yau tea akayi da scrambled eggs sai baguette bread anyi slicing dinsu an shafa thin layer of salted butter akai. "Sosai Miral taji dadin breakfast din dan its her favorite breakfast. Tas ta chinye shi dukda yawan eggs din ya cika medium sized bowl amma saida ta chinye, saidai taji dama bata chinye ba" saboda wani cika da cikinta yayi kamar zai fashe nunfashinta na fita da karfi da karfi. Mikewa tayi a hankali dan wani gajiya ne ya diran mata cin abincin datayi. Zazzagayawa tayi a dakin dan abincin yadan sauka sannan ta dau ruwa tasha kadan ta cigaba da zagayawa. Takai wajen 15 minutes sannan aka turo maid tafada mata tafito za’a tafi sannan maid din ta ansa luggage dinta ta fita. "Binta a baya Miral tayi sukayi waje, an fitoda motoci guda uku biyu ciki irin high landers dinnan ne for security sai ta tsakiyarsu kuma benz ce latest edition. A daya daga cikin highlandern maid din ta saka mata kayanta sannan ta bude mata kofar ta shiga kujeran baya. Gaban cikinta driver" ne sai wani security a gefenshi dukkansu sanye da black and white. "Tashin motar drivern yayi kafin a bude gate a fara fita, sai a lokacin su Ummi suka fito tareda shigewa benz din suka jero waje . Sauke ajiyan zuciya kawai takeyi tarasa nutsuwarta zuciyarta" sai bugawa takeyi. Airport na riyadh suka nufa a gujen gaske babu abunda ke tsayar dasu sai traffic ga Miral sosai take tsoron gudun da sukeyi gabadaya abincin cikinta juyamata sukeyi. Ajiyar zuciya ta sauke ganin finally sun isa Airport din. Sauka sukayi zuwa private VIP lounge securities din na tafe da kayansu. Su kadai ne a ciki Ummi ta zauna a daya daga cikin sofas din Hanat na gefenta. Shigansu lounge din kwata kwata baiyima Miral dadi ba dan lounge din is shaped kamar circle sannan bashida girma na family daya ne dan haka dole a inda suke zata zauna. Danne abunda ke zuciyarta tayi ta saukar da kanta ta shigo ciki a hankali dan nesa da Ummi ta tsugunna ta gaidata. Ummi dake sanye da wata peach abaya datasha beading da dark beige colored stones sai walwali sukeyi anyi design din butterfly daya mamaye kusan rabin abayar tun daga kasa har zuwa wajen waist dinta. Tayi rolling mayafin a kanta da shikuma yakeda design din butterflies din kanana an wawwatsa su. Idanunta dakagani kasan batayi bacci ba sunyi ja sunkuma kumbura saidai ta dambara kwalli tayi wani heavy make up daya kara fitoda kibar face dinta sam babu kyan gani tayi wani kubul kubul kamar an hura ballon ga wrinkles dasukayi forming a goshinta da gefen idanuwanta saitayi kamar ta kara shekaru goma akan shekarunta. "Ansawa tayi sama sama sannan ta dago ta kalli Miral data dan dago manya manyan doe eyes dinta ta kallo Ummi da saida Nunfashin Ummi ya tsaya. Bata taba ganin tsantsan kyan Miral ba irin na yau, tasani dan sani yarinyar nada kyau bana misali ba, saidai last time data ganta da nutsuwarta dakuma haiba a face dinta bata wuce 16 years ba, dan haka a yarintar ta take yanzu tayi wani irin Bala’in cika ido, tazama classy ga kwallin datasa a idanunta yafito da idanunta da sune best features dinta kana kallonta eyes dinta zaka fara gani gasu they look so" bewitching and alluring. "Lips dinta dasuka sha lip gloss akan natural pinkish red color dinsu sai kyalli sukeyi they look so fresh, soft and suffle. Saurin dauke idonta tayi daga kan Miral dan ji tayi inama yarta ne da wannan kyan? Inama ace Hanat dinta ce da shikenan batada bukatar har saita bata lokacinta" akan wayancen mutanen duk namijin da takeso zata samu. Daidai ta dauke idanunta ya sauka akan na hanat da itama daidai lokacin ta dauke idanunta dasukayi ja daga kan Miral. Ta rasa meke mata dadi a duniya tunda tsautsayi yasa ta daga idanunta suka sauka akan Miral. Wani hucin bakin ciki ke dukan mata zuciya babu abunda takeso a zuciyarta kamar ta mike ta yayyaga fuskar Miral. Wasu kwalla taji suna kokarin zubo mata tayi saurin mikewa zata fita. Riko ta Ummi tayi da sauri sannan tace ma Miral “ ke tashi ki fita daga nan zan kiraki idan lokacin tafiya yayi”. Ok Miral ta ansa mata dashi cikin siririn voice dinta sannan ta mike ta fice. Kallon Hanat Ummi keyi Tana ganin yanda wasu zafafan hawaye ke zarya a face dinta. Tasan sarai meke damun yar nata. Hakuri tafara bata tana shafa mata baya dan banda wannan babu abunda zata iya mata. Saida Hanat ta tsaida kukan nata tsab sannan ta dago face dinta daga shouldern Ummi tana share hawayen daya bata mata face duk make up dinta ya baci yayi smudging. "Ajiyar zuciya take saukewa daya bayan daya tana kallon kofar da Miral ta fita daga ciki tana balla mata harara kamar da Miral din take. Lallashinta sosai Ummi tafara yi saidai ganin bajin rarrashin takeyi ba yasa tace “ Hanat my daughter karki bari wannan dan abun ya bata miki rai, bata fiki da komai ba infact kin fita komai, duk Kyan nan na mujiya ne bakiga make up ne a face din nata ba? Idan ma tafiki kyau saime? Me kyan ya anfana mata? Babu, saidai masifa daya kawo mata. Dan haka ki share hawayenki nanda yan kwanaki za’a shafe babinta daga doron" kasa”. Juyo da face dinta Hanat tayi ta kalli Ummi idanunta a ware da duk kwalli da eye makeup yayi "smudging, cikin muryarta data dan shake saboda kula tace “ Ummi ban gane ba, mekike nufi" "za’a shafe babinta? Kasheta zakuyi?”. Dan dariya Ummi tayi sannan tace “ No daughter, ba kasheta zamuyi ba, saidai mutuwa tafi abunda zata gani sauki. Kedai ki cire damuwa a cikin ranki, nafada miki komai a duniya nada ranarshi, ita Miral din dana dauka dukda baso nayi ba kin zata a banza ne? No. Bana taba yin abu babu dalili, saidai anfaninda zata min yanzu yasha" banban da anfanin da nazata zatayi mun a chan baya”. Kura mata ido Hanat tayi tadan hade gira dan kwata kwata bata gane ina maganar Ummi ta "dosa. A kule tace “ Ummi nifa ban gane me kike so kice ba, kawai ki fada mun ni kidena wahalar dani”." "Dan sauke nunfashi Ummi tayi sannan tace “ Kintuna ranar dana dawo da Miral gidana ko? A lokacin da iyayenta sukasa a fitar da ita daga gidansu duniya tayi abunda taga dama da ita ko tayi rai ko ta mutu, naga opportunity na dauketa na ajiye a gurina dan nasan watarana dole zasu zo nemanta dan a cikin fushi sukayi hukunci musamman ma sister na dan wace uwa ce zatayi ma yarta wannan hukuncin a shekar sha shida kawai? Saidai sun tabbatar ma da kowa cewa da gaske sukayi hukuncin dan kuwa basu nemeta ba har tsawon shekara daya. Lokacin nayi danasanin daukar ta, saidai kuma nabarta tacigaba da zama saboda wata friend dina data bani labarin wata Organization, bazan shiga cikin meta fada mun ba kokuma menene organization din, basai kin sani ba. Amma dai kisani cewa samun Imad damuke son kiyi toh Miral ce silar, sannan daddynki zai dawo da kafafunshi har inda nake sai yanda nayi dashi" saboda Miral”. "Shiru Hanat tayi tana kallon Ummi da mamaki fal cikin ranta “ Ummi kenan tsafi za’ayi da ita?”. Girgiza kai Ummi tayi sannan tace “Nikaina bansani ba daugher, iya abunda nasani zan mika yarinyar, nayi ma friend dina tambayar nima tace mun ba tsafi bane, wai sun wuce suyi tsafi da mutun. Sannan banaso naji maganar nan a ko ina, ko waye kuwa duk ranar da maganar nan ta fita ki kaddara keda Imad Babu ku, sannan kina ji kina gani wata za’a kwace miki daddynki, duk wannan designers din da status dinki, daji dakikeyi ke yar The Billonaire Umar Ayuro ce kowa" yasan an kwace miki daddynki”. Sosai kan Hanat ya daure da tama kasa processing abubuwan dataji. Saidai abu daya tasani taji dadi sosai da za’a dauke Miral sannan kuma ta tafi kenan. Bata san me Miral tayi mata ba amma ta tsane ta a rayuwarta babu wanda takejin bakin shi a duniya kamar Miral. A bangaren Miral kuwa koda ta fita waje babu wani abu a zuciyarta ta samu wani dan bench ta zauna adan nesa da lounge dinsu Ummi tana kallon mutane dake ta shigowa harabar gurin a nesa dasu dan ba wanda keyowa nan yawanci suna shiga Public lounge wasu kuma Vip lounge suke shiga. Dan swinging kafafunta tafara yi tana cizan lips dinta gabadaya tazama bored so kawai takeyi suzo su tafi. She feels so on edge da dukda tana fargabar abunda zata tarar idan sunje din amma tafi bukatar su tafin kawai akan tazauna jira anxiety ya kasheta. Kamar an ansa mata wish din nata kuwa daya daga cikin securities din yace mata tazo su tafi. Mikewa tayi dadan saurinta ta shiga cikin lounge din da yayi leading to private boarding room daga nan direct suka yi cikin wani medium sized private jet suka tashi. "Solid 18 hours sukayi daga saudi zuwa Ghair Muaddal. Rabin tafiyar nasu Miral ta kasa bacci fargaba ta cika zuciyarta. Takasa nutsar da Tunaninta gabadaya a hargitse take jinta. Anxiety, nervousness har wani amai amai takeji duk saboda fargaba. Ko abinci da flight attendants suka kawo takasa ci. Tana so tayi convincing kanta cewa zasu karbeta sannan sun yafe mata amma" wani bangare na zuciyarta nason hanata gamsuwa. "Zuciyarta na fada mata babu abunda zaisa Ummi ta tafi da ita Ghair Muaddal indai ba iyayenta sun yafe mata bane saidai kuma idan ta tuna irin zafi dasuka dauka da yanayin hukuncin dasuka yanke akanta bata tunanin zasu yafe mata. Wani tunanin neya fado mata, toh kodai sun gano gaskiyarta ne? Ko sun gano cewa Layla karya tayi mata? Sosai ta gamsu da hakan dan" dama duk wuya duk rintsi gaskiya zata fito. "Ganin tasamu ansa yasa tunane tunane da fargabar suka dan nutsa ta samu barci ya dauketa. Bata tashiba saida suka sauka a kasar GHAIR MUADDAL. A Airport na boardern kasar suka sauka. Babban border ne da kana shiganta kasan ba karamin guri kazoba, baka isa ka wuce ta batareda proper lisence da tabbatar da tsaro ba. Anan duk wata private jet da commercial daba na kasar ba suke sauka harsai an tabbatar da shigan su cikin kasar. Criminals da masu" smuggling idan akwai border da basa koda nufarta to bordern Muaddal ne. "Open space ne da a tsaye bazakaga karshensa ba. Ga walls dinshi are Triple motion sensing, sound muffling fencing ne da duk abunka bazaka iya tsallake shiba sannan na waje bazai iya jin abunda ke wakana a ciki ba haka na ciki bazaiji meke faruwa a waje ba. Kasan shi anyi flattening dinshi kamar kasa saidai ba kasa bane dan a bushe yake sannan kura bata tashi," saidai mota bata iya tafiya akai dan hana masu shiga da mota. Bulletproof untinted Busses ne ke yawo a ciki akan wani lane da akayi layinshi in zigzag da "white road paint, drones ne baja baja ke yawo a sama, ga poles dake jere da ultra smart facial recognition AI cameras 360 coverage." "Security personnels ne a baje a gurin da masu patrol dakuma stationary ones dake tsaye kowannen su na sanye da black fit dakuma velvet red caps da red belts. Jikinsu gabadaya is armed with tactical gears, sub machine guns, assault riffles, heavy machine guns, sniper rifles" "and authomatic grenade launchers, and so on." Kai dakaga level of security na gurin duk wani tunanin yin badaidai ba saiya fita a ranka. Sai kaji kamar mai laifi tun kafin kamayi wani abun. "Wani square cubicle suka shiga yayi scanning dinsu sannan suka fito aka anshi wayoyinsu da kayansu sannan suka shiga wata white millitary Bus, wata different Bus din ta dauki kayansu." Guri daya suka zauna a layi na uku a bus din ga wasu mutane a gabansu. Hanat ta zauna a window seat sai ummi a gefenta sannan Miral a sit dake dayen side din da space din wucewa ya raba su. Sosai abun yake cinma Hanat rai takalli Ummi tace “Ummi nifa "shiyasa banason zuwa Ghair Muaddal fah, kalli yanda aka gwamutsamu da mutane wai meyasa private cars dinmu bazasu zo su daukemu bah? Duk sai an wahalar da mutane a" bordern nan kafin ma a shiga”. Hanat tafada tana turo baki tareda yamutsa face. "Girgiza kai kawai Ummi tayi bata biyewa Hanat ba dan gabadaya a gajiye take. Kowa yasan Ghair Muaddal kasa ce da ba’a yimata sakai. Komai nata na daban ne, babu ruwansu da cewa kai dan wane ne ko kai wane ne, indai zaka shiga kasar saika sauke kanka, motsi kadan kayi yanzu zasu jefaka cikin maximum security prison da idan ka shiga koda kanada gaskiya saika yi" spending atleast 6weeks a ciki kafin ka shiga trial. Duk wanda yasan Ghair Muaddal kuwa yasan akan ka shiga trial saboda ana zargin ka da wani laifi a border toh gwara a kasheka kawai. Gakuma prison dinsu idan ka shiga toh fitowar ka intact yanda ka shiga saidai wani ikon Allah kawai. Ba baya manyan criminals ke tsoron "shigowa kasar ba, dan yawancin masu shiga cikin prison dinta a haukace suke fitowa." Sunyi tafiya na wajen 15 minutes dan a zigzag suke tafiya bordern babu titi straight dan a hana gudu a ciki sannan suka kai department of security straight to secondary inspection da ana gamashi sai shiga cikin kasar. For more Information contact me via my WhatsApp at 09024295046. "//ghair muaddal: kasace mai tarin arziki da su kansu basusan yawan arzikin kasar ba, bakuma a tabayin kasa mai arziki kamarta ba." //miral shoud be wearing red shiry and trousers and so should all the girls. Things; ● Sarmul quwaa- capital ● Khairat- couzin din hanat. Corr- "● Solailis17Hanat19layla18,Mihrima21,Tahira22,Deniz23" ● rymno(phonecompanyghairmiaddal).