💞💓️ ZUCIYAR ALIYU CE💓💞 WhatsApp no:+234 8160983083 Chat with me YUSRAH MUSA ABUBAKAR DUTSE. ✍️MARUBUCIYAR ✍️ 1_Yarima Abdul-maleek 2_D'an millionaire 3_Safreeyyah 4_Royalty 5_Minister Ashraf 6_Me kamar sarki And now 7_❤️Zuciyar Aliyu ce❤️ Later 8_👑Yarima Aryan👑 Assalamu-alaikum yan uwa masoya barkan mu da shigowa wani sabon littafin nawa mai suna 💓Zuciyar Aliyu ce💓 humm ita fa yarinyar zuciyar Aliyu ce me kuke tunani a cikin wannan labarin abubuwan al'ajabi zasu faru ku dai ku kasance dani ku biyo ni mu shiga ciki tare yau za mu shiga duniyar nishad'i. In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE we love our NABI MUHAMMAD SAW no success without him he's the light of every darkness he've no limits ya rasulullah. STORY WRITTEN AND EDITING YUSRAH MUSA ABUBAKAR {maman Fatima Elham little Zaran aunty} I'm here to make u happiness educated hhhhhh! domin nifa I have no girman kai if u're fushi dani so wallahi u're just 'batawa kan k lokaci ni ta kowa ce. Godiya sosai sosai godiya masoya babu bakin da zanyi muku albarka dashi bisa kauna da kuke gwada min saidai nace Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa a duk inda kuke amin. Zarah Musa d'an Adam Naja'at Musa Abubakar Fatima Musa Abubakar Fatima batul Abdullahi Ru'kayyat Abdullahi Asma'u Abdullahi Ruwainah Abdullahi. Ranar kuce masoya maza kada kuyi sanya muyi rausaya 'yan uwa mu taho da baya baya mune muke cashewa a group. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 01 Parking yai da matu'kar 'karfi a cikin tabkekiyar babbar rumfar aje motocin dake 'katuwar harabar gidan su wanda da sauri wani mutum dake sanye da uniform yazo ya bude masa cikin girmama yace "u're welcome sir" fitowa yai cikin taku mai kyan burge mai kallon sa ya nufi kofar da zata kaishi cikin palor yana rike da rigar Army dinshi a hannunsa yaji mamaki har yana d'an zaro kyawawan idanuwan shi waje ganin babu wanda ya kula da shigowar shi hankalin su naga kallo wasu naga waya gyaran murya yai wanda a tare gaba d'ayan su suka juyo suna maida hankalin su kansa duk idanuwa suka zaro kamar zai fito waje dan tsoro da mamaki lokaci guda suka rud'e kowa ya gigice aje waya Afifah tai tana murje idonta ta bud'e ganin da gaske shine a tsaye ba gizo yayi mata ba yasa a rud'e tace. "Yaya discipline kai ne"?. A yadda tai masa maganar yasa ya sake zaro mata idon nasa ta gansu dakyau 'kila ko ta dawo hayyacin ta d'ora hannu tai aka da gudu tabar falon tai stairs tana cewa "wayyo Allah shikenan discipline ya dawo zaman bedroom ya dawo jama'a ku fito ku taya mu kallo" kai ya jinjina a ransa yace "hummm Afifah is so funny zan kama ki zaki bayani" wucewa yai zuwa ciki da kallo sauran suka bishi suna sauke ajiyar xuciya gashi 'kafafun su sunyi nauyi balle su tashi kafin ya dawo su gudu ita kam Momy lamarin su na bata dariya idan taga suna shiga firgici duk lokacin da suka ga Aliyu shigowar Daddy kenan ganin yadda yaran nasa suke yasa shi dakatawa yana karantar yanayin su domin ya sani matukar suna halin lafiya yana dawowa zasu tare shi da farin cikin su sa'banin yau da yaga damuwa a fuskokin su hannun karamar ya ri'ko yana mikar da ita tsaye yace. "Auta na miye yake faruwa ne"? Kafin tai magana Fati dake gefe tai wuf tace "Daddy ka taimake mu wallahi ya dawo" cikin rashin fahimta Daddy yace "waye ya dawo kuma"?. "Yaya boss" Elham dake gefe tai maganar kamar zatai kuka kallon ta Daddy yai da d'an mamaki a fuskarsa yace "wai Aliyu Haidar d'ina ne ya dawo gida d'ana ya dawo my son is back" duk zaro ido waje sukai jin abinda Daddyn yace ga kuma farin ciki ya bayyana a fuskarsa d'aya bayan d'aya ya kalle su yana murmushi yace "haba koda naji gaskiya shiyasa naga kun nutsu kowa ta kama kanta masha Allah yanzu wace a cikin ku zata je ta kira min shi"? Duk shiru sukai suna sunkuyar da kai aka rasa mai tari 'yar dariya Daddy yai yana girgiza kai yace. "Ke Elham je ki kira min shi". Kallon Daddy tai hawaye ya kawowa a idon ta lokacin data mi'ke da d'an mamki Daddy yace "wai duk meye hakan Aliyu Yayan ku ne d'an uwan kune fa amma sai ku ri'ka nuna damuwarku idan ya dawo me ya sa"? Goge hawaye Elham tai tana cewa "Daddy ba gudun shi muke ba lamarin yaya Aliyu ne sai shi". "Ok kinga bar kukan je ki kira min shi" wucewa tai yayin da Daddy ya bita da kallo yana murmushi kafin ya kalli sauran yaran nasa da duk sun kasa sukuni tafiya Elham take tana tsara da yadda zata iya shiga dakinsa tai masa magana a hankali ta bud'a kofar falon ta shiga ganin baya nan yasa ta wuce bedroom d'an kwankwasa kofar tai amma shiru ta sake ba amsa hakan yasa ta bud'e ta le'ka yana kwance a kan gado ya zubowa kofar ido yaga wanda zai shigo ganin ya ganta yasa ta tsaya daga jikin kofa tana cewa. "Yaya kazo Daddy na neman ka" tana fad'in haka ta juya da sauri tai waje kamar tana tafe yana bin bayanta haka ta ganshi a parlon daidai Afifah ta sauko ya jawota yana tuma mata dundu a bayanta 'kara ta saki ganin an fara daga kanta da gudu tai yin bayan Daddy tana 6uya Elham kam tunda ya fito jikin ta yad'au rawa bata farga ba ta ganshi a gabanta ri'ko hannun ta yai yana mi'kar da ita tsaye fuska a had'e sosai cikin fad'a ya soma magana. "Ke dan uban ki ni sa'an wasan kine da zaki min magana ta kofa"? Da mamaki Momy tace "yau nake ganin ikon Allah a gurin ka Aliyu to da ta ina zatai maka magana ta window"?. "No Momy yarinyar nan dan rainin hankali babu sallama taje tana min ihu a kofar bedroom harda gudu kamar taga mala'ika". "To da meye kai mala'ikan yara ne mana kaga sakar min hannun yarinya kar ka karya ta" Momy tai maganar tana kallon yadda idanuwan Elham d'in duk suka fito waje sakar mata hannun yai yana bata ran'kwashi mai zafi a tsakiyar kan ta wanda yasa da sauri ta dafe kan na ta kallon Afifah yai yana cewa "ke discipline ya dawo Fati matsalar ki ya dawo Elham damuwar ki ya dawo Husnah kukan ki ya dawo mai hana ku shan iska mai dad'i kamar yadda kuka ce ya dawo kusa Allah a ranku ban canza ba ina nan yadda nake yadda kuka sani har nafi da na dawo babu wacce zata sake jin dad'i a cikin ku" ri'ke ha6a Momy tai tana kallon sa tace "nikam yau nake ganin wata 'kaddara ayi mutum fad'a kamar kububuwa dan Allah ka rika shan ruwan sanyi Aliyu". "Momy wadannan yaran naki basa jin magana gabaki d'ayan su kuma zan saita musu zama badai farin ciki suke da tafiya ta ba gani na dawo babu me sake runtsawa mai kyau a cikin su har na koma". "Shikenan to idan ka gama fadan ka zauna mu gaisa daga dawowar ka duk ka hargitsa mana gida" zama yai suka gaisawa sukai masa sannu barka da dawowa domin ya dad'e baya gida sai yanzu ya samu yazo sosai suka saka shi a gaba cikin so suna kallonsa suna sake tambayarsa ya wajen aikin nasu shi yana fad'a musu abinda ya cancata ya fad'a akan aikin nasa wanda zai sanyaya musu rai amma ina soja ina samun kwanciyar hankali saida suka gama zancen nasu Daddy ya tambaye shi "Aliyu yaushe zaka koma amma dai bada wuri ba fatan zaka dad'e"?. "A'a Daddy karamin hutu na kar'ba maybe three weeks ma na koma" ya fad'a yana kallon Afifah da Elham lokacin da suka tafa cikin murna murmushi yai yana jinjina kai lallai yaran nan basu da hankali amma yana daidai da zamanin su maida hankalin sa kan Daddy yai jin yace "haba dai sati uku fa Aliyu da wuri haka shekarar ka uku da mun shiga ta hud'u fa baka zo gida ba sai yanzu amma kace sati biyu kawai zakayi meyasa baza ka dad'e ba"?. "Kuyi hakuri Daddy yanayin aiki ne haka" kai Daddy ya d'aga yana cewa "babu komai munsan da haka Allah ya taimaka ya kuma albarkaci rayuwarka da zuriyar ka". "Amin Daddy na gode" kiransa da akai a waya ganin mai kiran yasa ya mi'ke yana kallon Daddy yace "ina son zan fita". "Ok ba matsala Aliyu ka kula" murmushi Aliyu yayi domin dama yasan wannan a zaune take sai Daddy ya fad'a matu'kar zai fita sai yace masa ka kula saboda son da yake masa ganin Sameer ya sake kiran sa a karo na biyu yasa ya fita suna ganin ya bar gidan suka fara sauke ajiyar zuciya da sauri Afifah tazo gaban Daddy tana durkusawa tace "dan Allah Daddy idan Yaa discipline ya dawo kasa shi ya koma yai hutun sa acan" kallon ta Daddy yai kamar zaiyi dariya ganin duk tabi ta burkice yace "me kika ce Afifah Aliyun nawa zance ya koma inda ya fito yai hutun sa acan ko agola bazan yiwa haka ba balle shi d'an da na haifa d'ana nefa yaushe rabo na dashi ku bakwa taya ni kewarsa ne"? Tura baki Afifah tai tana cewa "amma Daddy kana ganin abinda yake mana daga dawowar sa"?. "Eh na gani ai baifi gyara ba dama kun manta yaushe rabon da ku shiga cikin nutsuwar ku kamar yau hakan ya min dad'i sosai ina so na ganku a nutse" yana rufe baki Afifah ta mi'ke tana cewa "tunda kace haka Daddy wallahi zaman lafiya na kawai naje na hada kayana gara na tafi gidan su Momy kafin yai hutunsa ya koma dan na tabbata idan na zauna ko burbushi na baza'a samu ba a gidan nan muddin Yaa discipline yana nan" ta fad'a tana nufar hanyar hawa stairs muryar Daddy taji yace "kada ki soma had'o kayanki a gidan nan zaki zauna babu inda zaki je har ya gama hutunsa ya koma" tuntu'be Afifah ta kwasa jin abinda Daddy yace yasa ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya kuma ita bata juyo ba cigaba Daddy yayi "Afifah idan baki tsaya kun fahimci juna ba a matsayin ku na 'yan uwa sai yaushe ko sai bayan ran mu sannan za kuyi zumuncin idan kunga babu mu? Ki nutsu ba wani abu bane bana so na sake jin wata magana ki dawo ki zauna cikin 'yan uwan ki" dawowa Afifah tai tana zama batare da ta sake cewa komai ba yayin da Elham ke mata dariya a boye ganin yadda take kumbura fuska tana cika da batsewa. Fitar Aliyu daga gida Sameer ne yai kiransa a babbar rumfar dake kafe a kofar gidan su ya ganshi har lokacin yana sake gwada kiransa ganin ya fito yasa ya kalle shi yana aje wayar yace "haba Aliyu tun d'azu inata jiran ka baka fito ba bayan kasan labari na kai min ka dawo ina barci bansan lokacin da nayi tsalle daga kan gado na sauko 'kasa ba saboda farin ciki amma ina ta kiran ka baka d'aga ba"? Karasawa Aliyu yai yana cewa "sorry kayi ha'kuri na tsaya gurin Daddy ne muna magana kasan sauka ta fa kenan ba jimawa nayi da zuwa ba" hannu Sameer ya mi'ko masa yana cewa "ok barka da zuwa gida bayan lokaci mai tsawo muje ka bani labarin inda kuke fatan komai lafiya"? Bai amsa masa ba sai wucewa da sukai Aliyu na cewa "am Sameer yaya ajiya ta take fatan tana lafiya right"?. Murmushi Sameer yai yana cewa "ayya Marshall albishirin ka ajiyar ka tana lafiya ina kula da ita yadda ya kamata babu wani abu daya same ta". "Ka tabbata"?. "Kwarai aboki na". "Bana son wasa Sameer please idan da matsala ka fad'a min na sani dan Allah"? "No nima da gaske nake maka ka yarda dani Marshall ba wasa abinda nake fad'a maka tsantsar gaskiya ne tana lafiya sosai". "Ok shikenan amma zan iya ganin ta yanzu kuwa ko sai zuwa jimawa"? Murmushi Sameer yai yana jinjina kai yace "eh zaka iya ganinta sosai mezai hana muje na nuna maka ita" fita sukai daga harabar rumfar suna tafiya wani gida suka shiga mai gate saidai ya tsufa har tsatsa yake kuma a hakan ta waje yafi ta ciki dama-dama domin gidan a ru'be yake ta ko'ina magidanta maza uku ne a gidan kowa da kofar sa da iyalan sa da tsohuwar gidan mahaifiyar su tana nan a raye itama da nata part d'in ba tsananin talauci ne ke damun gidan ba a'a ido ne yai musu yawa mazan gidan kowa bazai fidda kudi ya gyara shi kadai ba kuma su had'u su gyara rashin hadin kai ya hana d'aya headmaster ne na secondary daya Mopal ne dayan shine baya aikin gwamnati amma yana d'an kasuwancin sa ba laifi kuma yana samun kud'i shima gida ne daya tara mutane da mata da 'ya'ya masu yawa gidan ya tara gwarama akwai gulma munafinci yida wani hana zaman lafiya da akwai matan aure shida a gidan kowa macen shi biyu ga kuma samari da 'yan mata kofar tsohuwar gidan suka fara shiga da domin Aliyu ya gaishe da ita yara da yawa suka tarar zaune a gurin ta ganin tayi ba'ki yasa suka fara mi'kewa d'aya bayan d'aya suna fita zama sukai bayan sun gaisa kaka dake cin goro tace "Samar waye ne wannan d'in na kusa dakai"? Had'e rai Sameer yai yana kallon ta yasan dama sai tayi magana yace "kai hajiya wai dan Allah meyesa kike ce min wani Samar nifa bana son wannan sunan ki gyara" aje goron tai tana masa da'kuwa tace "naci gidan ku tun kafin na haifi ubanka nake rayuwa nasan komai shima nice na raine shi saida ya taso na nuna masa komai zakai min wata magana". "To hajiya ke d'ince da kayan haushi shi yasa ban cika shigo miki ba saboda fad'a muke idan ma nazo". "Karka sake shigowa daga yau ai ba kai kad'ai bane jika na gasu nan da yawa baza su 'kirgu ba saina za'ba". "Basai kin za'ba ba Hajiya kowa jikan kine". "Nidai akwai wadanda ba jikanu na ba domin ni jikanu na suna da farin jini". "To kuma waye mai 'bakin jini a gidan nan"?. "Ban sani ba matse ni saina fad'a maka" zaro ido Sameer yai yana cewa "wa nina isa na matse ki indai nima ba so nake su Abba sun matse ni ba kinga hajiya duk mubar wannan ga jikan ki yazo gaida ke" ya fad'a yana nuna mata Aliyu kallon sa Hajiya tai tana cewa "waye ne ban gane shiba d'an nan daga ina"? Samir ne ya bata amsa "Aliyu ne daga gidan Daddy Ahmed". "Tofa waye dad'i Ahmad kuma"?. "Bafa dad'i Ahmad ba Hajiya Daddy Ahmed nace". "To ai ban gane ba kamin yadda zan fahimta mana ni bazan iya fad'ar abinda kace ba" ganin zata d'ora masa wahala yace "Hajiya nan kusa damu nake nufi gidan Alhaji Amadu minister yanzu kin gane"? 'Yar zabura hajiya tai tana zaro ido cike dake da son zuciya tace "ayya yaron daya ya ke soja ne kaga marmari daga nesa ku ake wa kirari tuwon 'kaya Allah sarki yaro ashe ka dawo kullum saina yi sallar dare saboda kai da safe na sayo 'kosai nayi sadaka nace kuna can jeji ba gida ba gari fata na ka dawo lafiya sai kaga kwatsam kayya rayuwa" hajiya ta karasa maganar tana fashewa da kuka shiru Aliyu yai yana kallonta Sameer dake dariya yace "ki daina kuka hajiya ai tafiya ba mutuwa bace ba gashi ya dawo ba"? Kai Hajiya take girgizawa tana share hawaye da gefen zaninta tace "ka barni nayi Samar ka barni wannan abun kokawa dole ayi kuka a kai". "Shikenan to hajiya zamu tafi" mikewa sukai kud'i Aliyu ya ciro yana bawa Sameer ya mi'ka mata wanda dama tana goge idanu tana kallon shi ta tsananin yatsun ta da sauri ta kar'be tana masa godiya suna fita da sauri ta daga fulo ta saka tana cewa "haba malam zamanin nan saida basaja saida farauta ba gashi na samu kud'in 6atarwa ba daga zuwan d'an arziki Allah yasa gobe ma su sake shigowa" ta karasa maganar harda d'aga hannu sama ta shafa a fuskarta. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 02 Fitar su daga gurin Hajiya daidai 'yan mata biyu zasu shigo gidan su kuma suna shirin fita wacce tafi shishshigin da sauri ta tari Sameer tana cewa "Yaya Sameer waye wannan kamar Yaya Aliyu na gidan su Afifah ko"? Wucewa sukai Sameer na cewe "ba kama bace shine" zaro ido tai tana dafe'kirji tare da binsa da kallo tace "wow lokacin wanka yazo lokacin sa kyawawan kaya da lalle akai akai yazo zuwa gyaran jiki saloon ba kama hannun yaro bari naje gurin hajiya" tai maganar tana kallon wancan d'ayan data ta'be baki daidai sun ci gaba da tafiya kamar baza tai magana ba sai kuma tace "ai bake kad'ai ce kike son shi ba sannan ba ke kad'ai ce a 'yan matan gidan nan yake burge ki ba muje gurin hajiyan tare nima a wana 6angaren haka abun yake Ina jinsa a raina Allah ya baiwa me rabo sa'a domin nasan sama da mutum biyar ne ke sonsa a gidan nan kinsan da haka"? Kai Rasheedat ta jinjina tana cewa "eh tabbas na sani amma ina ganin duk na fiku son sa ai" da sauri Bilki tace. "A'a Rasheedat a yadda kike ji a ranki ba amma na tabbata idan bud'e tawa zuciyar za'ai sai kin tsorata saboda girman son da nake masa" murmushi Rasheedat tai kamar zata tanka mata sai kuma ta share har suka shiga gurin Hajiya dake kishingid'e a d'an parlonta tana sauraron radio kallonsu tai tana cewa "zancen me kuke kuda kullum kuna tafe kuna magana kamar wasu ta'ba'b'bu"? Zama sukai a gabanta Rasheedat na cewa "akan Aliyu ne dan gidan ministan nan alhaji Ahmed san kowa" jin abinda suka ce yasa Hajiya gyara zama ta tashi zaune tana kallonsu tace "to meya faru kuke magana a kansa"? tai musu tambayar tana sake zaune fulon da tasa kudin da Aliyu ya bata domin tasan matu'kar suka gani saita basu wani abu shiyasa take 6oyewa matsowa kusa da ita Bilki ta sake yi tana cewa " "babu komai Hajiya kawai son shi muke dukkan mu" zaro ido tai tana cewa. "Da gaske kuke yaran nan"?. "Allah hajiya". K'asa Hajiya tai da murya sosai gudun kar wani yazo shigowa yaji tace "yauwa 'yan albarka haka nake son ji kwanan nan zan ji'ke da kud'i idan d'ayar ku ta aure shi na tabbata yaron nan zai jiyar dani dad'i ku dage yasan daku yasan kuna son sa idan bai so wata ba zai so wata tunda naga yana da mutunci d'an arziki ne ya gaji halin mahaifin sa" ta 'karasa maganar tana d'auko kud'in daya bata ta nuna musu tana cewa. "Kun ga yanzu nan Samar ya kawo min shi kalli alherin daya min idan kuma akace yayi aure a gidan nan kullum jalaf d'in taliya da kifi ga zobo mai sanyi nasan shine abinci na dare da rana dan Allah yaran nan kada kumin bakin ciki kun ji"? Kallon juna sukai suna sha'kewa da dariya suka ce "sai hajiyan mu muna yinki za'ai yadda kike so" washe baki tai yauwa ko kufa haka nake son ji". Cikin wayo Bilki tace "amma hajiya kinsan bazai so mu a haka ba dole sai muna kyawawan shiga irin ta 'ya'yan masu kud'i muna kwalliya kuma ga shi bamu da kud'i yanzu ni saurayi na yayi tafiya" dariya Rasheedat tai tana cewa "nima nawa garan yayi tafiya shekaran jiya kuma banda ko sisi hajiya a cikin kud'in daya baki zaki bamu ko dubu biyar ce muje mu fara rage wasu abubuwan tunda kema kina son shiga cikin tafiyar" zaro ido hajiya tai tana mayar da kud'in ta cikin inda ta d'auko shi tace "caf dubu me zan baku dubu biyar naji kunce lallai yaran nan baku da hankali ko biyar bazan bayar ba balle dubu biyar kuje gurin iyayen ku su baku man dama dan ina so kuma nice zanyi muku jagorancin komai kenan"?. Hada ido sukai suna 'kiftawa Rasheedat tace "shikenan hajiya zamu nema amma ki sani idan yazo yace yana son mu ya aure mu kada muga yar 'kafar ki a gidan idan ma kinje zamu sa securities suyo waje dake mu nuna bamu sanki ba daga mu sai iyayen na mu tunda haka ne" shiru hajiya tai jikin ta yayi sanyi ganin batai magana ba Bilki tace "kefa Rasheedat ki rabu da ita da alama bata bu'kata dubu goman daya bata zata isheta rayuwa tashi mu je" ganin da Hajiya tai suna kokarin tashi da sauri tace "a'a ku tsaya badai dubu biyar bane gashi" ta fad'a tana d'auko kud'in ta basu badan ranta yaso ba tace "saidai na baku Kowaccen ku dubu biyu nima fa dubu goma ne kawai" kar'ba sukai suna mi'kewa Rasheedat tace "karki damu Hajiya dubu bibiyun ma tayi mana raba arne da makami ibada ce" a hasale Hajiya tace "kuma dan ubanki nice arniyar saboda ke ba 'yar mutunci bace"? Ta'be baki Rasheedat tana kallon ta da gefen ido tace "sai an kula kucaka take yanga ke kike yi mukam munyi nan" ta fad'a suna fita da ashar Hajiya ta raka su tana mi'kewa ta biyo bayansu tana cewa "ubanku ya make uwarku kuzo ku bani kud'i na shegu 'yan iskan yara matsiyata" cin karo da Haulat tai zata shiga gurin nata ganin su Rasheedat sun fita ga Hajiya na rako su da zagi tace. "Hajiya lafiya ke da waye"? Tsaki Hajiya tai tana cewa "ni da waye kuwa banda fitinannun shegun yaran nan Rasheeda da Balki" cikin gulma Haulat tace "tofa sun zo sun yi miki ha'incin nasu da suka saba ko muje ciki Hajiya rabu dasu dan Allah kinga kifi ne na kawo miki ko Umman mu bai baiwa irinsa ba saboda ina sonki jiya saurayi na ya kawo min da dare shine naci na rage miki" cike da zilama Hajiya tace. "Ina kifin yake bani shi nan 'yar nan irin ku ake so" murmushi Haulat tai tana jinjina kai tace "to mu koma ciki Hajiya akwai maganar da nake so muyi dake akan Aliyu" juyawa Hajiya tai tana dogarawa akan sandan tace "to kema dai akan Aliyun zaki min magana badai sonsa kike ba"?. "Eh sonsa nake man akwai wanda ya riga ni ne a cikin 'yan matan gidan nan"?. "Eh mana wadancan tantiran ma duk sonsa suke yanzu suka gama min lissafin zasu je su sayo kayan kwalliya da kayan sawa saida sukai min wayo d'an kud'in da Aliyun ya shigo ya bani dubu goma sun kar'be dubu hud'u" cikin zuga Haulat tace "kai ji mugaye 6arayi kuma kin basu"? Cikin takaici Hajiya tace "bayarwa na nawa saidai kar a 'kara a gaba na basu man" kai Haulat ta jinjina tana zama ta mi'kawa Hajiya ledar kifin tare da zuba mata ido saida taga ta fara ci tace. "Hajiya kinsan me nake tunani akan Aliyu"? Kai Hajiya ta girgiza tana cin kifi ko bakin magana bata samu ba murmushi Haulat tai tana cigaba tace "nima ina son Aliyu sosai kuma shima yana sona kullum muna waya dashi ban fad'a a gidan nan bane saboda kinsan akwai 'yan bakin ciki gashi yace aure na zaiyi Hajiya ki taya ni da addu'a idan nasamu ya aure ni kema kin warke domin bazan bari kici gaba da zama anan ba zan d'auke ki ki koma gurina muyi kyakkyawar rayuwa mai dad'i a gidansa komai kina zaune za'a akawo miki kici kisha kyauta ki kwanta a gado na alfarma Hajiya ke bakya son irin wannan daular ne"? Kai Hajiya ta d'aga tana cewa "ina so man wa ya'ki dad'i ne". "Tom kin gani Hajiya abinda nake son nuna miki kenan kuma ya fad'a min nan ba da dad'ewa ba mahaifan sa zasu yi magana amma yace bazai amince ya aure ni ba saina zama 'yar gayu irin sa". "Ban gane me kike nufi ba gayu kamar ya"? Cikin wayo Haulat tace "yace na samu kud'i na na sayo mayukan bleaching wanda zanyi fari sol kamarsa sannan na sayo kayan sakawa masu tsada na ri'ka cin kwalliya yadda baza'a kushe niba kuma iyayen sa zasu amince ya aure ni idan ya kaini gidan kinga Hajiya bai kamata nayi sake ba saboda nasan ko nawa zan kashe dana aure shi shikenan zan mayar da kud'i na harda riba zan samu" kai Hajiya ta d'aga tana cewa "tabbas haka yake to yanxu ya za'ai a ina xaki samu kud'in domin nima ina so naga d'aya daga cikin ku ta aure shi". "Abinda za'ai kawai yanzu wannan sauran dubu shidan zaki bani naje na sayo kayan kwalliya zan tambayi abban mu idan ya dawo ya bani kud'i na sayo atamfofi nakai shago ayi min manyan d'inkuna na alfarma watakil yadda nake da kyawun nan da yaga na koma haka kwanan nan ya aure ni na d'auke ki kikoma gurina da zama sai abinda kike so zaki ci" Haulat na rufe baki Hajiya ta saki dariyar farin ciki tana zura hannunta cikin fulon ta d'auko sauran dubu shidan ta mi'ka mata tana cewa "gashi nan kiyi sauri ki tashi kije kawai ki sayo komai gara kiyi auren nan mu bar gidan dama ba wanda yake so na sai ke duk 'yan 'kwal ubane babu tsiyar da suke bani tashi maza ki tafi shagon sannan wadannan 'yan iskan yaran kici ubansu idan kin had'u dasu kice su dawo min da dubu hud'u na" mi'kewa Haulat tai kamar zatai dariya ta danne da'kyar tana rufe baki saboda kar dariyar ta fito fili tace "to shikenan Hajiya karki damu zanyi miki maganin shegu dani suke zancen zasu san sun ta'bo min ke ki rabu dasu ina daidai dasu zan kar'bo miki kud'in ki bari naje na dawo" haka Haulat ta fita tabar Hajiya sai sambatun murna take tana hasko yadda zata ri'ka yiwa komai cin hauka tasan zata kwashi dad'i indai akai dace Haulat ta auri Aliyu tunda taga tana bata komai idan ta samo. Fitar su Balki daga gurin dariya suna dariya Rasheedat tace "wallahi dama yau haka na tashi ko sisi banda shi amma yanzu ga dubu biyu ziyau ta shigo mana ba aiki fari balle na ba'ki haka ake so muje muyi wanka muzo muci uwar dubu hudun nan kafin sauran 'yan matan gidan su dawo su saka mana ido" wucewa sukai kowa ta shiga 6angaren su. Daga gurin Hajiya dasu Sameer suka fito waje sukai ganin da Aliyu yayi Sameer bai nuna masa abinda ya tambaye shi ba yasa kalle shi yana cewa "kai Sameer wannan wanne irin wulakanci ne ka nuna min"? Kamar baisan akan me yake magana ba yace "da nayi maka me"?. "Da kai min ban sani ba cewa fa nayi muje ka nuna min ajiyar dana baka amma har muka fito banji kace komai ba"? Murmushi Sameer yai yana cewa "oh sorry buddy kayi ha'kuri zan nuna maka ba yau ba" wani kallo Aliyu yai masa yana cewa. "Ba yau ba sai yaushe"? Cikin tsokana Sameer yace "tommorow morning"? Jin abinda yace yasa ya had'ee rai yana cewa "tommorow morning kuma"? Shiru Samir yai bai bashi amsa ba kallon sa Aliyu yai ganin dariya yake masa yasa yadan daki kafad'arsa yana cewa "you're not so kind mutumi na kana bani ciwon kai wallahi meyasa kake min haka ne"?. "Babu komai Marshall insha Allah gobe da safe zan baka magani zaka warke daga ciwon kan daya same ka". "Meyasa baza ka nuna min yanzu ba sai gobe bayan kasan irin damuwar da nayi da abun"?. "Nasan ka damu gaskiya ne amma maganar Allah zan fad'a maka ajiyarka bata nan ta tafi D'an Yana tana gidan su mahaifiyar ta Amma jiya munyi waya da ita tace min nan da kwana biyu maybe zata dawo" numfashi Aliyu ya sauke jin abinda yace ya jinjina kai yana cewa "ok shikenan muje" wucewa sukai zuwa babbar rumfar kofar gidan su Aliyun domin su samu zama ayi hirar yaushe gamo da aka dad'e ba'ai ba. Ameerah na jin labarin cewa Aliyu ya dawo ta ciko trolley da kaya ta taho gidan cikin farin ciki da nuna za'kuwa ga soyayyar da take masa 'karara baya boyewa wace Amira? 'ya ce a gurin professor Bashir da hajiya Adama ala'kar abota ce tsakanin Daddy da mahaifinta kuma Abban Aliyu akwai shakuwa mai karfi yarda da amince wanda suka zama tamkar 'yan uwan jini wannan dalili yasa Amira ta taso da ciwon son Aliyu a zuciyar ta hakan yasa kullum tana zarya a gidan tun tana karama take burin aikin soja saboda Aliyu saidai dole ta hakura da aikin sakamakon cutar asma da take damunta bazata iya aikin ba saita sauya karatun zuwa bangare irin na babanta tayi zama da Aliyu a kasashe daban daban shine yake kula da karatun ta saida bayan ta kammala ya dawo da ita gida cikin aminci kamar yadda aka bashi amanar ta tun bayan rabuwar su basu sake haduwa ba shekara uku da rabi sai yanzu 'kawarta khulsum dake aiki a airport tai kiranta a waya ta sanar mata cewa taga Aliyu ya dawo shiyasa ta tattaro kayanta kamar yadda ta saba ta taho gidan wannan shine ala'kar ta dashi. Afifah tana zaune a bedroom taga an bud'o kofa zubawa kofar ido tai cike da fargaba farko ta d'auka Aliyu ne sai kuma taga Amira ta shigo bakinta ko rufuwa bayayi tsabar farin ciki jikin ta na mazari ga trolley sha'ke da kaya da mamaki Afifah tace "Amira yaushe rabon da na ganki kusan shekara uku fa tun lokacin da yaya discipline ya dawo dake gida sai yau anya kece kuwa nake gani ko mai sifar kice"? Murmushin Amira tana karsowa tace "yau kuma sai gani bayan wadannan shekarun naji labarin Aliyu ya dawo shiyasa kika gan ni yanzun ma nazo" kai Afifah ta jinjina dama tasan sai hakan saidai idan labari ne yakai mata anga dawowar Aliyun to wanne munafikin ne? Numfashi ta sauke tana 'kara 'karewa Amira kallo tace. "Waye ya fad'a miki"?. Zama Amira tai tana zuge zip din jakarta ta dauko phone d'inta zata kira Aliyu tace "ina da 'kawa a airport d'in daya sauka sunanta Ummu-Khulsum itace taga saukarsa shine ta kira ni tayi min albishiri a take data kira ni ta fad'a min nayi mata kyautar dubu hamsim sannan nayi wanka ko Daddy ban fad'awa ba na taho tsabar zumud'i sai daga baya zan kirashi na fad'a masa dukda nasan Aliyun zai je gidan ya gaisar dashi". Murmushi Afifah tai tana cewa "gaskiya ne yayi fa to sannu da zuwa kun had'u da Yaya discipline d'in kenan"? Kaita girgiza batare data d'ago daga kallon wayar tata ba tace "a'a ban ganshi ba maybe ya tafi wani guri bari na kira shi domin na matsu mu had'u" cikin tsokana Afifah tace "gaskiya ne ya kamata ku gaisa musamman yadda kuka dad'e kuna tare sannan tare kukai karatu tsawon shekaru sha'kuwa iya sha'kuwa dole ki matsu ku had'u amma yaushe zamu sha bikin ki ne"? Murmushin Amira tai har lokacin bata d'ago ba tace "taya zaku sha biki bayan baku shirya ba" da mamaki Afifah tace. "Ban gane ba kamar ya bamu shirya ba meye namu a ciki bayan anko ko a dangin mu angon yake"? Ta tambaye ta tana kallon ta rolling eyeballs dinta Amira tai tana kad'a kai tace "to da ina kike kaini a dangin ku yake man" da sabon mamaki Afifah tace "waye kenan"?. "A'a bazan fad'a ba zaki sani ba yanzu ba sai nan gaba fatana zaki taimake ni wajen cika buri na"? Nuna kanta Afifah tai tana cewa "ni kuma na taimake kifa kika ce"?. "Kwarai ki taimake ni man ko bazaki taimaka min d'in ba"?. "a'a mezai hana dan taimako kawai ba wani abu ba babu abinda zai gagara karki damu" cikin jin dad'i Amira tace "yauwa Afifah na gode har kinsa naji kamar komai ya faru ya 'kare please dan Allah Afifah kisa a kawo min abin sha mai sanyi man yanzu kinji"? Mi'kewa Afifah tai daidai zata fita tace "ok zansa a kawo miki" fita tai tabar Amira wacce ta kwanta tana kallon secreen din wayarta ganin kiran na shiga amma ba'ai picking ba karshe idan ta tura kira ma sai ai reject aje wayar tai tana jan tsaki wato Aliyu har yanzu yana nan kamar da bai canza ba lallai da 'kura a gabanta da alama zata sha fama dashi kafin ta shawo kansa......... 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YUSRAH MUSA PAGE 03 Har dare sosai Amira batai barci ba tana jiran dawowar sa bai shigo ba harta gaji ta tafi ta kwanta ko barci arziki bataiba tsanar damuwa washe gari da wuri tai wanka bayan tayi sallar asuba taci ado sosai tasa lace mai tsada ta kashe d'auri ita da kanta ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta ganin wani irin kyau datai tasan matu'kar sukai four eyes da Aliyu tofa bazai san lokacin dazai bita da kallo ba domin ta fahimci dole saida siyasa zata samu zuciyarsa da'kyar ta bari gari yai haske lokacin masu aiki sun gama aikin kayan breakfast har wasu sun karya amma banda ita saboda bata fita da wuri ba sai data daidaici kamar zata sameshi a parlon sannan ta fito. Tana zaune Afifah ta fito itama saboda tana part d'in Momy ganinta a zaune ita kad'ai ga yanayi mara kyau a fuskarta yasa ta karaso tana zama itama tace "yadai Amira ya haka"? D'agowa Amira tai cikin damuwa da rashin walwala tace. "Ya me"? Kallon ta sosai Afifah keyi tana nazarin ta da abinda yake damunta kafin tace "naga kinyi tagumi kuma da alama kamar baki breakfast ba meyasa baki ba ko akwai matsala ne"? Kai Amira ta jinjina tana sau'ke hannunta daga tagumin datai tana fitar da huci ranta a 6ace tace "eh Afifah banyi breakfast ba taya zan iya cin abinci a wannan yanayin bayan na shiga matsala". "Matsalar me wani abu ne ya faru"?. "Meye ma bai faru ba Afifah ni Aliyu zai wula'kanta har kamar ni na masa kira yakai ashirin daga jiya zuwa yau amma bai picking ko d'aya ba karshe har rejecting yake min ne yake nufi da hakan yaushe ya canza ki fad'a min Afifah lallai kuwa Aliyu ya d'auko damin da bazai sauke ba ya d'auko ya'ki zaisan yayi dani saina nuna masa fushi na Allah ya fito dashi lafiya ina nan ina jiransa nan da gobe wallahi sai nayi masa mugun rashin mutunci". Wani kallo Afifah tai mata jin abinda tace ta jinjina kai tana cewa "tabd'ijan babbar magana Amira shawarar dazan baki karki soma Yaya discipline ya canza ba wanda kika sani da bane shawara ce nake baki ki fita hanyarsa" a masife Amira tace "wallahi bazan rabu dashi ba Afifah saina idar masa da 6acin ran daya d'ora min" gyara zama Afifah tai tana cewa "to shikenan Allah ya taimaka nidai gaskiya ce kuma na fad'a miki amma naga da alama kafin ki tafi gidan ku so kike ya 6alla ki dan Yaya discipline ba irin wanda kika d'auka bane baya son raini ba'ai masa wargi humm Yaya discipline sha'anin sa sai sh........... Shiru Afifah tai tana rufe baki ganin Aliyu ya sauko daga stairs kuma ya kalleta yasa tad'an kau da kai kamar bata ga irin kallon daya aiko mata ba wucewa yai yana zama a dinning ya d'auki karamin kofi zai hada tea mi'kewa Afifah tai tana karasawa inda yake batare daya dago ba yace. "Meya faru kina neman wani abu ne"? Jada baya Afifah tai tana cewa "a'a Yaya dama kai zanyi serving". "I don't want bar nan kafin ke na 'balla miki 'kafar da kike magana akai" juyawa Afifah tai da sauri tabar gurin ta koma parlor tana zama a inda ta tashi d'aram Amira ta mike tana zuwa inda yake cikin shiahshigi tad'au plate tai serving d'insa Irish wanda yaji 'kwai tana direwa a gaban sa ta kama kujera ta zauna itama tana serving kanta tunda dama damuwa bata barta ta samu damar karyawar ba sai yanzu data ganshi ganin abinda take yasa fuska ba wargi yace. "Ke meye haka"? Bata bashi amsa ba saida takai loma bakinta sannan ta dago tana kallonsa cikin yanga ta sauya murya tace "da nayi me"?. "Do you want to know why"? Dan rainin wayo na miki tambaya kema ki min ni sa'anki ne"?. "A'a ba daya amma ai masoyi na ne kai ko ba haka ba"? Ba arziki tasa Aliyu kallonta jin abinda tace yace "waye masoyin naki"?. Fari tai masa da ido tana murmushi tare da rausaya kai tace "ina wani bayan kai Aliyu kaine da wa kake zato"? Kai ya jinjina sakamakon jin abinda tace wai sonshi take amma ta had'a kanta da aiki babba sannan ta d'orawa kanta damuwa saboda gaskiya bata da gurbi a zuciyarsa shifa yayi kyautar zuciyar tasa taya zai iya saka wata a ciki mutum d'aya ce mamallakiyarta baya jin akwai ta biyun ta........... "Aliyu baka ce komai ba ya aikin naka fatan ka dawo lafiya sannan abinda na fad'a kasan haka ne kaima shiyasa kayi shiru ko"? Kai ya girgiza mata yana cewa "ki daina zaton haka a ranki ki daina 'bata lokacin ki a kaina Amira" da mamaki tace. "Me yasa"?. "Bana so kiga kamar na cuce ki a gaba" girgiza kai tayi da sauri tana cewa "bazan ta'ba gani ba Aliyu ko maye zakai min dan Allah ka aure ni"? Tana rufe baki ya d'aga mata hannu yana cewa "listen up daina ro'ko na Amira karki 6ata lokacin ki a kaina ni ina da wacce nake so kin gane"? Zaro ido tai firgici dimuwa damuwa tashin hankali razana sune sukai mata dirar mikiya lokaci guda tea din data kurba ya 'kwareta ta soma tari mai karfi ba 'kak'kautawa tare da dafe 'kirjinta yana kallon ta baice 'kala ba har ta gama Afifah da ta taho da gudu tana bude fridge ta dauko mata ruwa tana kawo mata kallon da Aliyu ya mata yasa da sauri tabar gurin tana rike baki cikin mamakin wa Aliyu yake so dama yana soyayya amma bai ta'ba nunawa ba lallai kwanan nan zasu samu Aunty. Kasa d'aukar ruwan Amira tai balle ta sha ga zafin da 'kirjin ta ke mata kamar gidan gasa biredi hawaye ya cika mata ido yana gangarowa amma taga Aliyu kawai breakfast d'insa yake hankalinsa a kwance bai nuna alama damuwar abinda take ba kuka ta fashe dashi tana cewa "Aliyu dama kayi haka da niyya ne a zuciyarka dama son kashe ni ne 'kudirin ka shiyasa kayi min hakan"? Murya a tsawace yace "ke are you out of your sense ni kike fad'awa haka kinyi hauka ne"? Cikin kuka tace "ba hauka ne ya kama niba Aliyu kaine kake neman haukata ni da maganganun ka". "Da nace miki me"?. "Kana da wacce kake so". "Eh zan miki 'karya ne saboda ina gudun 'bacin ranki"?. "Kuma auren ta zakai"?. "To da me kika d'auka zan yaudare tane? Kaita girgiza ranta a 'bace tace "kawai ni ka bani amsa aurenta zakai"?. "Ban sani ba". Jin abinda yace yasa sabin hawaye suka fara zuba mata da'kyar muryarta na ma'kalewa tace "a ina take"?. "Meye matsalar ki da inda take"?. "Had'uwa nake so muyi da ita domin naja mata kunne a kanka ta fita layin da ba nata ba kafin tai asarar rayuwar ta dan wallahi saina kashe ta indai na gano wacece" mi'kewa yai cikin halin ko in kula alamun maganganun ta basu sha masa kai ba yace "look it up on Google madam zaki ga komai nata da adireshin ta da mahaifinta da inda suke sai kije ki sameta tana daidai dake" ganin zai bar gurin yasa a gigice Amira itama ta mi'ke tana shan gaban sa cikin kuka tace. "Meye sunan ta da ya zan gane ta"? Murmushin ganin haukan ta yai yana d'an girgiza kai yace "never mind 'yan mata karki damu kanki ba sunan ta zaki nema ba ita ya kamata ku had'u tunda wannan ne burin ki ko"? 'Kara ta saki mai 'karfi tana dukan dinning d'in a haukace tace. "Ka fad'a min sunan ta Aliyu fad'a min wace ita a ina zan sameta"? Lamarin Amira yana mugun bashi dariya matu'ka amma ya dake dan baya son raini ko tace da wasa yake mata yace "sunan ta Mrs. Aliyu Marshall anguwar da take gidan Aliyu d'akin da take rayuwa zuciyar Aliyu na gama fad'a miki komai a kanta da inda zaki sameta tana cikin zuciya ne idan kika sake min wata magana a kanta nan gaba saina 6alla ki" yana gama fad'a mata haka ya bi ta gefenta ya fita a parlon 'kamewa guri daya Amira tai ta daskare ta kasa motsin kirki numfashinta ya d'auke lokaci guda taga duk parlon yayi mata wani irin ba'ki bata ganin komai sai duhu ganin haka yasa Afifah tasowa zata zo gurin ta kafin ta iso taga Amiran ta yanke jiki ta fad'i 'kasa da gudu ta karaso tana kiran sunanta daidai Elham da Fati sun sauko da sauri suma suka zo inda suke. "Lafiya ita kuma wannan fa meye ya sameta"? Elham tai maganar cikin mamaki Afifah bata bata amsa ba sai kallon su datai tana cewa "ku taya ni mu d'auke ta kar Momy ta fito bansan me zance mata ba dukda nasan komai" du'kawa sukai suna d'ago ta sukai stairs da ita har bedroom suka ajeta akan gado zama Afifah tai tana cewa "Fati mi'ko min ruwa a fridge na shafa mata". "Ok" Fati tace tana mi'kewa ta d'auko mata Elham da take faman kallon Amiran tace "wai dan Allah Aunty Afifah meke damunta ne"? Sau'ke ajiyar zuciya Afifah tai kamar mai yin rad'a tace. "Ita da yaya discipline ne". Zaro ido sukai a tare suna cewa "yaya boss me ya hada su kuma"? Dariya Afifah tai harda tafi tana kallon fuskar Amira dake ri'ke shakaf da ruwa tace "maybe Amira tana son yaya discipline ne shi kuma ya fad'a mata da akwai wacce yake so". "Wacce yake so!?. Cewar Elham tana mi'kewa tsaye tsabar yadda maganar ta dirar mata kai Afifah ta jinjina irin tabbas d'in nan tace "eh wacce yake so akan haka ta fad'i kunsan ma wani goge hadda irin tasa da tace ina anguwar su take cewa yai tai sacin a Google zata gani ya sunan ta yace Mrs Aliyu Marshall anguwar su wai zuciyar Aliyu kiji fa"? Suma kallon juna sukai basu san lokacin da suka fara dariya ba kai Fati ta girgiza tana cewa. "Lallai Amira ta sayi damuwa da kud'in ta dan yaya boss ko mutuwa zatai ta dawo tunda yace bai yinta fa'kat karshen magana baya 'karya". "Kenan da gaske ne da yace yana da wacce yake so"? Elham ta tambaya tana ri'ke baki amsa Afifah ta bata "kai da gaske ne mana Elham mukam ai biki zamu sha koma wacece mu gwangwaje" mi'kewa Fati tai tana cewa "ai ko bari yanzun nan naje na fad'awa Momy dan a bari ya huce yana kawo rabon wani gara taji tunda zafinsa wannan labari ne me dad'i" daidai ta juya zata fita Afifah ta jawota baya tana cewa. "Da alama ki manta waye Yaya discipline ko gulmar sa zaki kai tab idan rabon shan na jaki ne yake rud'ar ki ga hanya nan Allah ya tsare zan dafa miki ruwan zafin da zaki gasa jikin ki" Afifah na rufe baki da sauri Fati ta zauna kamar an tura ta tana cewa "kan bala'i amma Aunty Afifah na gode kin taimake ni wallahi kin cece ni da naje ina ga yau Yaya boss farfesu na zaiyi a gidan nan". "Humm lallai yarinya iya farfesu indai ya tsaya iya haka ya miki da 'kauna idan bai saki a inji ya markad'a 'kasusuwan ki ba" dariya Elham tai tana cewa "nikam zaman bedroom d'in nan ya ishe ni bari na koma parlor yasan yanzu baya gidan zamu d'an huta kafin ya dawo" mi'kewa Fati tai tana cewa "nima bari na biyo ki" Afifah data ja bargo ta lullu'be Amira tace. "To wa zaku bari gadin mai suma wallahi nima gani nan bisa sawun ku muje idan ta farfad'o ta fito" saukowa sukai duk su ukun Afifah tai hanyar library ta dauko littafi ganin momy tana zaune a parlon yasa da saurin su cikin zumud'i suka karaso inda take suna zama kusa da ita TV suka kunna Afifah data fito tana zama a can gefe zatai karatu jin zasu takura mata yasa tace. "Malamai zaku iya kashe TV nan ko kuma ku sauya ku tafi wani parlon amma baku isa zanyi karatu ku 'kure volume ba" kafin suyi magana suka ji daga bayan su ance "this is not place for reading nan parlor ne gurin hutu zaki iya komawa inda kika fito can ne gurin karatu" d'aga ido Afifah tai ta gano Aliyu tsaye saman balcony yana watso mata kallon gargad'i bata sake magana ba ta aje book d'in alamar ta ha'kura. "Baza kije ki karatun ba kenan dan nayi magana shine kika aje book d'in saboda ga sa'an wasan ki ko"? Da sauri Afifah ta mi'ke tana d'aukar littafin zat bar gurin dakatar da ita yai "baki iya bada ha'kuri ba kenan ko wato ke jar wuya ce"? Dafe kai tai tana juyowa kamar zatai kuka tace. "Kayi ha'kuri". "Repeat". "Kayi ha'kuri". "Again". "Kayi ha'kuri dan Allah Yaya". "Yaya wa"?. "Yaya Aliyu". "Dama haka kike kira na"?. "Eh yaya kayi ha'kuri". "Ba discipline Daddy da Momy suka rad'a min ba"?. "Eh yaya kayi ha'kuri"?. "Kin iya bada ha'kuri kamar matar aure ta gari 6ace min da gani zan kama kine" wucewa Afifah tai tana d'an yin kasa da murya tace "oh ni naga ta kaina Yaya discipline akwai masifa harda ta saidawa a gurin sa so yake ya d'ora min hawan jini kamar yadda ya dorawa Amira". ZUCIYAR ALIYU CE @YMA DUTSE JIGAWA PAGE 04 Su kam su Elham da suka samu shiga ba'a biyo ta kansu ba yasa suka d'an sake har sun manta da tsayuwar Aliyu ta saman su zasu fara yiwa Momy shagwa'ba kenan suka ji murya ance "can you be quite or not? Which rubbish is this zaku sa min uwa gaba kuna mata ihu dama haka kuke mata saboda kunga bana nan to kusa Allah a ranku yau gani na dawo za kuci ubanku ne" a firgice duk suka kalli kofar palor suga da gaske ne mai wannan maganar ya dawo harda cikin mamaki suka zaro ido kamar yadda nasa suke a zare wanda basuyi zaton gani ba suka ganshi tsaye lokaci guda suka 'kankame Momy suna cewa". "Innalillahi wayyo Allahn mu wata damuwar is back shikenan d'ayan ma ya dawo yaya Afif" da gudu Afifah ta fito jin abinda suke cewa yayin da su kuma suka mi'ke suma da gudun sukai stairs rikicewa Afifah tai tare da tsayawa ta murtuke ido tana kallon sa tace. "Afif da gaske dama suke kaine"? Murmushin d'aya bata amsar tambayar ta yayi mata yana kallon Momy da itama murmushin farin cikin ganin sane a fuskarta hannu ya bud'ewa Afifah alamar tazo gare shi wacce da sauri ta buga tsallen murna tana dariya ta rungume shi sosai d'agowa tai har lokacin tana dariyar farin cikin ganinbya dawo tace "gaskiya nayi kewar ka bros d'ina yanzu lokacin mune nima d'an uwa na ya dawo zan sake na wala na sha'ki iska me kyau" ta fad'a tana juyawa ta kallo stairs hango su Elham tai suna faman le'kowa suna kallonsu batasan lokacin da sabuwar dariya ta sake 'kwace mata daidai Aliyu ya sau'ko ya karaso inda suke yana ri'ko hannun Afif cikin so tare da hararar Afifah yana mata nunin zai kamata ne yace. "Muje ka gaida Momy ke kuma zan ina nan zamu gauraya zan dawo kan kine Afif d'in bazai hana naci ubanki ba" ya fad'a suna wucewa inda Momy take zaune Afifah dake tsaye a gefe jin abinda Aliyu yace yasa tad'an 6ata fuska shiyasa fa tace idan yana gidan nan baya bari su sake gashi yanzu batai masa komai ba yace zasu gauraya aiko bazata yarda su had'u ba balle ya mata wani abu d'agowa tai ta kalle su suna zaune a kusa da Momy suna magana duk su ukun murmushi tai a ranta tace "perfect much gayun gidan sun gama kammala yanzu zaman bedroom ya fara gare min ni zan samu sauki ta bangaren Afif tunda Hassan d'ina ne saidai naji da takurar yaya discipline amma su Fati duk inda sukai ba sauki bari naje naga a wanne halin suke sarakunan matsorata" eucewa tai tana dariyar mugunta a ranta da yadda zata ga su Elham a d'aki tasan suna nan sun zubowa kofa ido kamar zasuyi kuka abinda tai zato ta gani domin tana bud'e kofa duk suka mi'ke a rud'e kowa ta rikice domin Elham kam har taje kofar bathroom ta bud'e zata shiga dariyar da Afifah tai yasa ta juyo taga ba Afif ki Aliyu bane sauke numfashi tai tana dawowa tace. "Kai dan Allah Aunty Afifah me yasa zaki tsorata mu wallahi na d'auka Yaya Afif ne ya shigo fa yadda yayi mana wannan tsawar da ace ba a lokacin ya dawo ba nasan sai yaci uban mu ba bedroom ba ko ramin gyare zamu shiga sai ya bimu" ta karasa maganar tana zama murmushi Afifah tai tana cewa "ai kuma duk da haka baki sani ba ko idan ya gama gaisawa da Momy nan zai taho tunda kinsan shi Afif kamar kurma yake fad'an sa baya mutuwa balle yaga Kuna neman d'orawa Momy hawan jini". "Humm insha Allahu babu abinda zai mana bari Daddy ya dawo muje gurin sa kawai a kashe maganar" Fati ta fad'a itama tana baro gaban mirror ta dawo bakin gadon su ta zauna kallonta Afifah tai tana jinjina kai tace "humm Allah yakai damo ga harawa idan baici ba yaci mugun duka wato baiyi miki wani abu ba zaki kai 'kararsa daga dawowarsa yau ko wallahi shawara zan baki ki rufawa kanki asiri kiyi shiru da bakin ki karki fad'awa Daddy". "To yanzu tsakani da Allah Aunty Afifah me mukai masa dan kawai mun yiwa Momy shagwa'ba har wani abu ne"?. "Ba wani abu bane a gurin ku amma shi a gurin sa wani abu ne saboda yaga kun girma sannan ko Asma'u bata haka balle ku yan mata ba wacce idan akai aurenta bazata zauna ba" Afifah na rufe baki duk suka zaro ido musamman Elham kamar an tsikareta da sauri ta girgiza kai tana cewa "wayyo please Aunty Afifah dan Allah ki daina fad'a kar d'aya daga cikin basawan nan yaji mun shiga uku kisa ayi auren mu lokacin mu baiyi ba". "Ba wani lokacin ku baiyi ba wallahi ba wacce idan akai aurenta bazata zauna ba a cikin ku". "Nidai banda ni" Fati ta fad'a tana sake gyara zamanta ta d'auki littafi ta soma karantawa amsa Afifah ta bata "harda ke man kece ma oganniya wacece a cikin mu take yawan son karanta littafan soyayya idan bake ba kuma anyi maganar aure kince wani banda ke"? Kai Fati ta jinjina tana cewa "kwarai banda ni dan wallahi Aunty Afifah yanzu tsautsayi yasa wani garawayis d'in yace yana sona ko yazo yasa ayi min aure dashi zaiga yadda ake hauka da d'anyan kai bazai iya zaman wata d'aya dani ba saboda damuwar dazan ta d'ura masa". "Tofa kamar wacce kalar damuwa kenan"? Dariya Fati tai tana cewa "idan yace nayi nace bazan ba idan yace na dafa abinci saiya dawo na d'ebo masa d'anye a plate na kawo masa idan yace ruwa na shiga toilet na d'ebo masa kinga ai ba wanda zai dauki wannan haukan komai son da ya ke min ko"?. "Tab mai sonki zai d'auka bazai ji haushin kiba duk lokacin da kikai wani abu dan ki 6ata masa rai shi Kuma a wannan lokacin zaiji duk duniya ke kad'ai ce kikai masa babu wacce yake so sai ke ai ance so hana ganin laifi komai zaki masa zai yarda hakan ma wani abu ne na musamma............................ Tarin da Amirah tai shine ya katse maganar da suke yi da sauri suka juya gurin daidai ta tashi zaune tana shirin sauka daga gadon duk kallonta sukai ganin yadda ta mi'ke tana had'a hanya tai toilet can ta fito alamar wanka tai ta wuce gaban mirror zata shirya Afifah ce tace "sannu Amirah" kamar bazata amsa ba saboda takaici sai kuma ta tuna ba itace tai mata haka ba Aliyu ne shiyasa murya a hankali tace "yauwa sannu" daga haka ba wanda ya sake cewa komai harta gama shirinta tasa doguwar rigar atamfa street gown ta d'aura d'an kwalin ta d'auki mayafinta da handbag zata fita tace "Afifah ina wayata"? Kaita girgiza tana cewa "maybe tana dinning ki duba idan kin fita na manta ban taho miki da ita ba" ok kawai shine abinda tace tana bud'e kofa ta fita jikinta gabadaya ba dad'i ya saki haka take jinta kamar mara lafiya irin zazza'bi-zazza6i na shirin kamata saukowa parlon tai a lokacin babu kowa daga Momy harsu Afif d'in wucewa dinning tai ta ganta a inda ta fara cin abinci lokacin da suke magana da Aliyu tuna abinda ya faru d'azu yasa sabon ba'kin ciki da takaici ya sake lullu'be ta da'kyar tad'au wayar tare da jan tsaki ta fita a parlon ba kowa a harabar gidan ma sai iya securities da yake bada mota tazo ba shiyasa kai tsaye ta fita daga gidan hango Aliyu tai sun taho wajen gidan tare da Sameer da alama daga gidan su Sameer d'in suka fito cije lips tayi tana kallonsa har suka karaso inda take. "Ina zaki je"? Aliyu ya tambaya yana kallonta ganin yadda tai mugun had'e rai fuska ba walwala tace "zan tafi gida ne" kaiya jinjina yana cewa "ok ki gaida Mama amma daga zuwan ki kwana d'aya zaki tafi"?. "Eh zan dawo akwai abinda na manta shi zan d'auko maybe zuwa magriba na dawo ko zaka kaini dama bada mota nazo ba saidai na tari napep dan Allah ka kaini kaji"? Shiru yai domin shifa bai son yawan wannan abubuwan tunda har yaji ta furta masa kalmar so gara ya ri'ka baya baya da ita saboda kar taga yana sake mata tayi tunanin ko shima yana son nata ne ya sani sun dad'e suna tare sun saba da ita ya d'auke ta tamkar Afifah domin tun bayan kammala secondary d'inta suke tare a school d'aya sukai karatu a India da kuma Spain sun zauna lokaci me tsawo shekaru kusan goma iya sabo dai wanda ya kamata sun yi shi amma bai ta'ba ji a ransa yana sonta da aure ba sannan baiji dad'in yadda ta bari zuciyarta ta kamu da sonsa ba yana ganinta d'aukawa kanta al'amari mafi wahala........................ 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 WhatsApp no:+234 8160983083 @YUSRAH MS ABUBAKAR PAGE 05 "Aliyu" ta fad'a tana kallonsa d'agowa shima yayi yana kallonta nata ya daina wancan tunanin da yake kamar zatai kuka tace "dan Allah ka kaini sai ka shigo ku gaisa da Maman namu" kaiya girgiza mata yana cewa "a'a ba yanzu nake son naje mu gaisa ba bari nasa driver ya kaiki" jin abinda yace yasa ranta na tafasa tace "a'a barshi na samu ne napep kawai nagode" ta d'auka idan yaji haka zai kaita sai taji yace "ok sai kin dawo" ya fad'a yana juyawa ya koma inda Sameer yake da kallo ta bishi hawayen damuwa sun cika mata ido ganin ya karasa rumfar ya zauna kar yaga shi take kallo ko tsaiwar me take a gurin yasa da sauri ta juya musu baya tare da bud'e handbag d'inta ta d'auko dan karamin handkicif ta goge hawayen fuskarta sannan ta wuce batare data sake marmarin juyawa ta kalli inda yake ba ta tari napep d'in ta tafi. Aliyu kam yana komawa inda Sameer yake ya kalle shi fuska shima sam babu walwala yace "Sameer wai dan Allah meyasa kake min haka ne kasan irin wahalar da zuciyata ta shiga cikin lokutan nan da garari ina cikin tashin hankali amma kai ko a jikinka abun bai dameka ba why"? Ya karasa maganar ransa babu dad'i ko kad'an da mamaki Sameer yace "Subhanallahi Marshall meya faru wani abu nayi maka ban sani ba"? Huci Aliyu ya fitar me zafi yana girgiza kai yace "meye ma bakai min ba Sameer yau kace zaka fad'a min inda zanje na sameta ka'ki ni ka fad'a min garin da tafi kawai zanje na ganta ka gane tunda kai baza kaje ba" dafe kai Sameer yayi alamar sha'afa da maganar da sukai shima yad'an girgiza kan yana cewa. "Sorry Marshall kayi ha'kuri dan Allah na kira wayarta tun jiya ta'ki shiga yau da safe kafin na fito mu had'u saida na kirata saboda nasan dole zaka tambaye ni ita amma labarin d'aya ne yau kuma wayar na rufe shine dalilin da yasa banyi maka maganar ba". "Ok sake kiranta yanzu maybe ta bud'e wayar". "Ok tom bari mu gani Allah yasa tana bud'en" Sameer yai maganar yana bud'e wayarsa ya sake kiranta ta shiga amma bata d'aga ba har kiran ya katse wani ya sake danna mata nan ma dai bata d'aga ba kallon Aliyu daya zuba masa ido yayi yana cewa "ka gani da idonka ko wallahi na kirata d'azun ma maybe bata kusa da wayar ne kayi ha'kurin zuwa jimawa saina sake gwada maka" Sameer na rufe baki Aliyu ya mi'ke yana cewa "bazan iya ba Sameer tashi muje ka tambayi mamarta kawai zanfi samun kwanciyar hankali akan wannan bugun da zuciya ta take yi dole sai naje naga likita ina ji a jikina kamar bani da lafiya" mi'kewa shima Sameer d'in yayi yana cewa "a'a Marshall 'kalau kake ka yarda babu abinda yake damunka sai ciwon so". "Kuma ciwon son ba cuta bane shine ma babbar illa wacce zata saka zuciyar mutum ta buga ya mutu kamar dai ni ka gane"?. "Eh na gane sosai". "No baka gane ba Sameer kuma bazaka gane ba sai ranar da so ya shige ka idan ma zaka fahimta kenan" murmushi Sameer yai yana kallon Aliyu daga baya kuma yace "ok muje gurin Umma d'in saina tambayi yaushe zata dawo d'in" d'an 'karamin numfashi Aliyu ya fitar bai sake cewa komai ba suka wuce saida sukai gaf da shiga gidan sannan ya tsayar da Sameer yana cewa "please Sameer fatan ba wanda yasan da maganar a gidan nan ko"? Kai Sameer ya jinjina yana cewa "tabbas ba wanda yasan kana son Zainab bayan ni domin ko ita kanta Zainab d'in bata sani ba saboda ban fad'a mata ba gara na bari idan lokacin daka d'iba yayi ka sameta da kanka ka sanar da ita hakan zaifi" "ok dama na d'auka ko mamarta ta sani ne amma tunda kace ba wanda ya sani naji dad'i yanzu zan iya shiga kaina tsaye cikin 'kwarin gwiwa" dariya Sameer yai yana cewa "kenan da ace sun sani baza ka shiga ba". "To Sameer na shiga nayi me indai ba gaisar dasu zanyi ba sun zama surukai na". "Gaskiyar ka wannan haka yake" Sameer na rufe baki suka ji ance "Yaya Aliyu ina yini"? Duk juyawa inda akai maganar sukai domin muryar mace ce ganin Haulat tsaye da jaka a hannunta alamar wani gurin zataje yasa Sameer sakar mata wata uwar harara yana cewa "gidan uban wa zaki je yanzu"? D'an zaro ido tai cike da rashin gaskiya tace "uhm uhm uhmm" ta kasa magana sai nishi da take kamar me jinya cikin fad'a Sameer yace "uhm me nace gidan uban wa zakije da jakar hannunki waye ya aike ki"? Baya ta matsa da sauri jiki na 6ari bata iya bashi amsa ba saboda ba inda aka aiketa kawai yawonta data saba fita zata tafi tsawa ya buga mata da karfi wacce tasa ta juya da gudu tai cikin gidan tsaki Sameer yaja mai mugun 'karfi alamar ransa ya 6aci sosai ko magana bai sake yiba sukai cikin gidan suma da yake mahaifin Zainab shine 'karami shiyasa kofarsa itace can ciki ta 'karshe lokacin da suka shiga iya mahaifiyar Sameer ce kad'ai tana wanke-wanke da sallama suka shiga ganin Sameer da wanda batai zato ba yasa ta washe baki tana mi'kewa tsaye tace "a'a Aliyu kaine d'an albarka kenan sannu da zuwa an dawo lafiya ku karaso man" ta fad'a tana shiga d'akinta bin bayanta sukai ta shimfid'a musu tabarma suka zauna Aliyu ya gaida ita cikin sakewa ta amsa sai faman jansu take da hira saboda tasan matu'kar suka fita yanzu sai sun had'u da Umma tunda taga bata fita ba amma tayi wanka anguwa zataje mi'kewa sukai zasu tafi itama data mi'ke suka fito tare saboda taji kamar alamun 'karar rufe 'kofa maybe ta fice d'in amma me suna fitowa taga kofarta a bud'e kenan ba d'akin ta ne aka rufe ba d'akin mahaifin su Sameer ne shine ya fita tunda taga ga alamar padlock nan a jikin murfin kofar d'akin nasa ya akai zai fita bai bada abinda za'a dafa ba saboda yau yaga ba ranar girkin Umma bace 'kwafa tai tana hararar murfin kofar kamar shine a tsaye a gurin da har zata bi bayansa sai kuma ta fasa ta zauna a gurin aikinta taci gaba da wanke kwanukan. D'akin Umma su Sameer suka shiga a lokacin ta gama shiri kenan ta d'auko 'yar kamar purse d'inta taji sallamar su amsawa tai tana le'kowa ganinsu yasa da fara'a tace "tofa sannu da zuwa Sameer karaso dashi man kamar wani ba'ko ka tsaya a waje ku shigo dan Allah" shiga sukai itama tabarmar ta shimfid'a musu suka gaisa sannan Sameer yace "am Umma nikam yaushe Zainab zata dawo ne ta tafi kawai tabarmu yau kusan sati uku ko wata guda zatai ne idan na gaji fa saidai kuga naje na d'auko ta" 'yar dariya Umma tai tana cewa "ayya Zainab nima bansan ranar da zata dawo ba tunda ba waya muke ba amma dai tunda hutu ya kusa karewa watakil ka ganta satin sama ta dawo". "Ok nayi kewar ta ne balle kamar can d'in babu network sai nayi ta kiranta wayar ya'ki shiga ko kuma idan ta shiga ma bata d'aga ba kodai a gida take barin wayar idan zata fita ne"?. "To Sameer Allah masani saidai idan ta dawo ka tambaye ta wallahi nima da ka ganni nan na matsu ta dawo saboda d'inkunan mutane wasu suna ta zuwa tambayar idan anyi musu nace bata nan kaga babu dad'i shiyasa nake so ta dawo duk da keken ma ya d'an samu matsala sai takai shi gurin gyara". "To Umma ta sake wani man ta ha'kura da wannan kwanan gida wunin garejin ba'a wata sai yaga gurin me gyara" murmushi Umma tai bata ce komai akai ba saboda ba kud'in gyaran kuma indai ya sani shine zai bata ta gyaro mahaifiyar sa na ganin kuwa sun shiga uku da zagi da gori iri-iri shiyasa ma batace masa babu kud'in gyaran ma shima daga haka bai sake magana ba sai mi'kewa da sukai ganin anguwa zata tafi karsu 6ata mata lokaci sallama sukai mata daga nan ko 6angaren Hajiya basu le'ka ba kawai sukai waje........... 📌AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE📌 @YMA DUTSE Ok PAGE 06 Fitarsu baifi da mintu biyar ba a fusace Asiya ta shigo tana buga murfin kofar su tace "ke Asabe ina Sameer yake"? D'agowa daga aiki Asabe tai tana cewa "ban gane Ina Sameer ba lafiya". "Au tambaya ma kike wai lafiya lafiyar ce ta kawo haka idan yana ji zan furta idan baya ji ki fad'a masa gargad'i na dashi akan Haulat ne daga yau karya kuskura ya sake koro min yarinya kamar wata akuya dan ta fita daga gida ina ruwansa da ita kowa yaci tuwon gidansu itama tana da yayun da zasuyi mata fad'an ai basai yayi mana shishshigi ba idan tsare gidan yake so ina yana da 'kannai shima yayi musu man amma banda Haulat duk inda taga dama zata fita taje bai isa ya hanata ba saboda ba shi zai aureta ba idan ya tare gida yace bazasu fita ba a gidan ubanwa zasu samu mijin auren dan kan uwarsa to ki fad'a masa sa'ko daga ni ba ruwansa da 'yata yaiwa d'an kowa a gidan nan bai dame niba amma banda tawa domin zamu kwashi damben tsiya dashi kin gane idan kunne yaji jiki ya tsira" tana fad'in haka ta juya fuuu tai waje shiru Asabe tai cikin takaici ranta na 'kuna wato da tacewa Sameer ya daina takurawa yaran gidan nan akan fitar da suke baiji ba gashi yanzu ya jawo mata magana bari ta gama wanke-wanke nan taje itama har kofarsu ta tsiyata Asiya sai hankalinta yafi kwanciya idan bata rama wannan cin mutuncin ba ba'kin ciki ne zai kashe ta. Fitar su Sameer kam basu zauna a anguwar ba mota Aliyu ya d'auko suka fita zuwa wani guri domin ya fad'a masa dama zasu je shiyasa ya fita da shirinsa su Afifah kam yau ranar 'yanci ce a gurinsu tunda gidansu Momy ya tafi maybe sai dare zai dawo musu sun san zasu sha'kata badon Afif yana nan ba. ANGUWAR HAUSAWA Saukowa yake daga stairs yana kallon fuskar Maminsa yadda take aiko masa da wani kallo murmushi yayi daidai ya karasa saukowa yazo ya du'ka ta gefen fuskarta ya mata kiss yana cewa "good morning Maah d'ina fatan kin tashi lafiya sorry na makara nasan nayi laifi kiyi hakuri yanzu zan tafi" kaita d'aga tana cewa "toya na iya Shareef ai dole nayi ha'kuri amma kai kamar karamin yaro kullum sai ana fama da tashinka daga barci bayan kasan kana da ayyuka"? Kunnuwansa ya kama ya ri'ke yana cewa "sorry Mami na bazan sake ba daga yau" mi'kewa tai tana nufar hanyar dinning tace "kazo kayi breakfast saika tafi tunda aikin gama ya gama". "A'a Mami na makara da yawa kawai bari na tafi" juyowa tai da sauri tana kallonsa lokacin da zai bud'e kofa tace "a ina kenan zakai badai abincin waje zakaje kaci ba"? Kaiya girgiza yana cewa "a'a Mami nasan bakya so ai saina dawo". "A'a indai haka ne tsaya na had'a maka a basket ka tafi dashi zaifi" takarasa maganar tana nufar hanyar kitchen tsayawa yayi yana sake kallon agogon dake d'aure a hannunsa ba karamin makara yayi ba yau gashi yana da aiki sosai idan yaje har gaggauta yayi ta gama had'o masa kamar yayi tsuntsu ya tashi haka yake ji tana kawo masa kuwa ya sake sakae mata sabon kiss yana cewa "thank you Mah d'ina Allah yasa na samu mace mai kyawun dabi'u irin naki" ya fad'a yana juyawa ya bud'e kofa ya fita murmushi tai tana kallonsa sakamakon kofar glass ce harya shiga mota sannan ta juya tana komawa insa ta tashi ta zauna. Sakamakon yasan ya makara sosai ya kwashi motar da gudu dan yaje da wuri yana parking kuwa yaga Baby a tsaye tana faman le'ke le'ke alamar jiran zuwansa take ganin yayi parking yasa da sauri ta gangaro daga inda take ta taho gurinsa cike da murmushi jin dad'in ganin nasa tana karasowa cikin shishshigi ta kar'bi basket d'in d'aya d'auko daga bayan mota tana shirin amsar sauran kayan dake hannunsa yace "no thank muje ko yau na makara" ya fad'a yana yin gaba da d'an sauri ta bishi har lokacin da murmushi akan fuskarta tace "good morning ya kake fatan ka tashi lafiya"? Bai tsaya da tafiyar da yake ba saboda saurin makarar dayai yace "lafiya kefa"?. "Nima ina lafiya baka tambaye ni jiya yaushe na tafi gida ba"?. "A'a wannan bai shafe ni ba akan me zan tambaye ki saboda kawai ina so naji yadda kika 'kare ai nasan ba anan kika kwana ba ko"?. "Eh man taya zan kwana a hospital niba midwife ba amma sai wajen bayan sallar isha na tafi gida ina zuwa Mom ta hauni da fad'a kamar zata dakeni da'kyar na samu na shawo kanta suka fahimce ni amma da cewa tayi da Yaya Hakim ya shigo zata fad'a masa". "Uhmmm" kawai shine abinda Shareef yace daidai sun kusa karasawa office d'insa ba zato yaji Baby dake bayansa ta danna wata ba'kar d'anyar ashar wacce yasa shi juyowa da sauri yaga meya faru basket d'in hannunta ya gani a 'kasa ga kayan nan sun tarwatse a gurin sannan ga wata budurwa a tsaye da takarda a hannunta kafin ya tambayi abinda yake faruwa Baby ta d'auke ta da mari cikin 6acin rai da tsawa "mahaukaciya ce ke ko kuma makauniya ce bakya gani ne tsabar shashanci da'ki'kiya kin taho kina kallon 'kasa kina iyayin kinzo ki buge ni da wannan banzan jikin naki yau sai kin biya wannan abincin" ta karasa maganar tana shirin kai mata mari na biyu dakatar da ita Shareef yayi ta hanyar cewa "no don't do that again karki 'kara marinta kin gane ni taiwa laifi bake ba bai kamata ki dauki hukunci a hannunki ba kalli fa itama tayi asara" kallon inda yake nuna mata tayi taga wayarta babba 'kirar Apple a 'kasa screen d'in ya fashe ta'be baki tai tana jan tsuka tace "sai me ni banji komai ba wallahi Allah ya 'kara inama ace idan ta bud'e taga taci secreen nan gaba saita kiyaye ta ri'ka kallon gabanta idan tana tafiya meye amfanin wadannan manyan idanuwan naki gashi harda glass amma a banza". "Baby kinyi hauka ne meye damuwarki da ita akan abinda bai Kai ya kawo ba sai maganganu marasa dad'i kike fad'a mata Ina ni taiwa idan ma 6arnar ce nace na yafe shikenan komai ya wuce muje" d'aukawa Baby tai tana tattara kulolin sannan ta zuba a basket d'in lokacin data d'ago kamar ta sake sharara mata sabon marin sai kuma taja tsaki ta wuce zuwa office d'insa shiru budurwar tai idonta cike da hawaye ba Marin datai mata ko fashewar wayarta ne ya 6ata mata rai ba kawai zagin datai mata batasan ita 'yar waye ba kawai ka kama zaginta badan bata son tashin hankali ba tana komawa gida saita sanar da Dad d'inta yau Baby bazatai kwanan gidan su ba sannan idan taga dama aikin da take ta'kama dashi sai tasa a cireta ta nuna mata karshen isar wace ita amma ba komai.................... Wayarta dake 'kasa Shareef ya d'auko ya saka 'karamin towel d'insa ya goge mata ya mi'ka mata d'agowa tai tana kallon sa tare da saka hannu ta kar'ba ranta na 'kuna da'kyar tace "na gode" ta fad'a tana juyawa ta wuce sosai ransa ya 6aci jin yadda tace masa ta gode d'in kowa yaji yasan ba kamarin ciwon abinda Baby tayi mata taji ba amma ta danne ta nuna godiyarta ga yar kulawar daya bata a fusace ya shiga office d'insa ganin ta tsaye yasa ya nuna ta da yatsa yana cewa "Baby daga yau kinyi na farko kinyi na karshe kar tsautsayi yasa na sake ganin idan nazo kinje tara ta ki barni komai nauyin kayan da nazo dasu na d'auko da kaina kin gane"? Had'e rai tayi tana cewa "yanzu Shareef saboda wancan yarinyar shine ka d'auki fushi dani ban kyauta ba kenan abinda nayi ban burgeka ba har kazo kana tuhuma ta"? Buga table d'in dake gaban kujerar da yake zama yayi muryarsa na nuni da tsantsan fushi yace. "How to impress you meye abun burgewar anan wannan jahilci kenan kika nuna ba komai ba" nuna kanta Baby tai tana cewa "Shareef ni ka kira jahila saboda nayi fad'a a kanka"? Sabuwar tsawa ya sake buga mata "you are no one but stupid and let me tell you today i am ending all this burden" ganin yadda yake fad'a yana mata tsawa yasa itama zuciya tazo mata wuya cikin d'aga murya tace. "Tell that to who is afraid Shareef na gaji da wannan tsawar da kake min saboda nayi wancan abun ne zaka sakani a gaba da fad'a kamar wani ubana na mareta kuma wallahi da nasan ita xaka baiwa gaskiya idan ka shigo saina sake marin ta" kaiya jinjina yana nuna mata hanyar fita yace "get out from my office" tsananin mamaki ne ya kamata har batasan lokacin da tace "Shareef na fitar maka a office kace akan wancan yarinyar ko sonta kakeyi ka fad'a min"? bai bata amsar tambayar ta ba sai sake nuna mata hanyar waje dayai yana cewa "as from today I don't want to see you in my office again har abada indai ba aiko ki akai ba kin gane"? Baki ta bud'e zatai magana ya daka mata tsaya. "Get of my sight kafin na 6alla ki" tsawar da bata saba jin irin taba a rud'e ta fice da gudu tana zubar da hawaye wani irin 'kak'karfan tsaki yayi tsabar yadda ta 'kona masa rai akan abinda bai kai ace damuwa ta shigo ciki ba tasa ya 'kara 6ata lokacin sa anan aje wayar hannunsa yai yana d'iban abubuwan daya kamata ya d'iba ya fita daga office d'in hango budurwar da Baby ta mara d'azu yayi tana tsaye tare da wani doctor abokinsa kamar zaije yayi magana da ita ya sake bata ha'kuri akan abinda Babyn tai mata domin gani yake kamar shine sila laifinsa ne da baizo da basket d'in ba da Baby bata d'auko ba sannan itama da bata bugeta ba har suzo a samu sa6ani wucewa yai saboda yana sauri bai tsaya a gurin su ba. Ita kam bayan sun gama maganar da suke saida ya rakata har inda motarta take driver yana ciki yana jiranta har zata shiga ta sake juyowa tace "Yaya Ammar yaushe ne ya kamata na dawo asibitin"?. "No shiga kawai kije gida zanyi magana da doctor Ishaq d'in duk abinda yake faruwa idan na dawo zamuyi magana dasu Abba kinji" kaita d'aga tana bud'e motar ta shiga suka fita daga asibitin kafin shi kuma ya juya zuwa 6angaren da yake. ZUCIYAR ALIYU CE @yusrah Musa Abubakar PAGE 07 Tafiyar Zainab tayi nisa domin har aka koma makaranta bata dawo daga d'an yana ba iya damuwa Aliyu ya shiga gashi baya so ya nuna damuwar tasa a fili yana iya bakin 'ko'karin sa ya danneta amma duk da haka idan ka kalleshi kallo d'aya zata fahimci halin da yake ciki na azabtuwa da jarabtar so yauma haka suna zaune tare da Sameer yana gwada kiran Zainab yace "Sameer kabar batun kiran nan kawai naga alamar gara muje can na gaji fa". "Sorry Marshall insha Allah ta kusa dawowa dan Allah ka rage yawan damuwar nan haka". "Taya kake tunanin damuwa zata barni kasan fa zuciya wata iriyar abace wacce idan taga abu tana so dole saika bata abun nan shine samun salamarka da kwanciyar hankali amma nifa gashi da bata samu abinda take so ba sai wahalar dani take kullum bata iya samun kyakkyawan barci". "Babu abinda zance saidai kayi ha'kuri nasan baka cikin yanayin jin dad'i amma insha Allahu zan sake kiranta nace mata Ya Sayyidi yace ta dawo islamiyya idan taji haka da sauri zaka ganta ta dawo". "Ok indai haka ne ka kira a waya man ka fad'a mata sannan ka tambaye ta ranar da zata dawo kar lokaci ya 'kure harna tashi tafiya bata dawo ba kaga bazan ji dad'i ba sosai iya nine nasan irin azabar da nake ciki idan kuma kana ganin muje can d'in ne a shirye nake"?. "A'a kayi ha'kuri insha Allahu bazata wuce cikin satin nan ba munyi waya da ita jiya na tambaye ta tace ta gama shiri maybe nan da two days ka ganta" numfashi Aliyu ya sauke yana cewa "Allah yasa abinda ka fad'a ya zama gaskiya domin maganar Allah Sameer bazan 6oye maka ba rashin ganinta da banyi ba Ina mugun azabtuwa zuciya ta baza iya d'auka ba kawai ina jurewa ne na danne yanzun kuma naga bazan iya ha'kurin ba". "Karka damu zaka ganta zuwa kwana biyun kamar yadda nace maka in Allah yaso". "Ok shikenan yana iya da lamarin ka Sameer Allah ya yarda kawai shine abinda zan iya cewa bayan hakan bani da bakin magana sai na ganta" dariya Sameer yayi cikin tsokana yace "sai dakai na gidana nidai indai dan nine na baka Zainab ka aureta". "Dama ko baka fad'a ba wannan yarinyar in Allah ya yarda matar aure nace ai". "Allah ma ya yarda Marshall lokaci ne kawai bai kai ba shima muna fatan zuwansa cikin gaugawa" "to Amin idan addu'a ce kayi min dan naga dariyar ka tafi yawa". "Da gaske fa addu'a ce nayi maka ta gari ma kuwa angon zee-zee" d'an murmushi Aliyu yai yana girgiza kai domin iya angon ta da yace masa ya d'an ji sassauci kuma zuciyarsa ta rage nauyin damuwar data d'auka ko sunanta yaji an ambata yakan ji tamkar ana shafa mata sansanyar ruwa a lokacin da yake jin zafi. @YUSRAHMS PAGE 08 D'AN YANA Zaune wata 'yar tsohuwa take a 'kar'kashin bishiyar zaitun mai yalwar inuwa a tsakar gida tana gyaran shinkafar tuwo lokaci zuwa lokaci tana d'agowa ta gano ko wutar na ci kasa ha'kuri tai ta d'an kallo kofar d'akin ta ganin takalmin wacce take tunani yasa tace. "Zainab Zainab kina ina ne"?. "Gani a d'aki kaka A'i ina zuwa yanzu sun dawo ne"? Wata sassanyar murya zazza'ka ce ta bata amsa yayin da ta fito sanye da bakar doguwar riga tana murmushi lokacin data kallo yadda tsohuwar take faman aikin gyara shinkafar kai masha Allah kyakkyawa ce fara da gani bata da hayaniya karasowa tai tana zama a kusa da tsohuwar tare da dauke turen shinkafar cikin tsokana tace. "Lallai kaka A'i akan kimin maganar cewa an kawo na fito na gyara shine kika d'ora da kanki kuma da wanne idon kike gyaran shinkafar"? Dariya kaka A'i tai tana cewa "da idanuwa na mana da naki na ara? Ki daina min kallo mai dindimi ras nake ganin ki". "Au ni da yaushe nace kina dindimi kaka A'i"?. "Ba fad'a kikai ba amma niyyar ki kenan duba min tukunyar inaga kamar ruwan yayi kadan" "ok tom kaka A'i Zainab ta fad'a tana mi'kewa zuwa inda murhun yake bata buda tukunyar ba ta tsaya tare da juyowa jin A'i tace "yaushe ma kika ce zaki tafi gida ne Zainab"? Kafin ta bata amsa wata budurwa ta shigo da sallama tana cewa "kai kakus miye zaki bata idan ta fad'a miki ranar da zata tafi d'in"?. "Babu fa kawai dai na tambaye tane saboda naji jiya d'an uwanta ya kirata a waya yana tambayar lokacin komawar tata". "To ba yanzu zata tafi ba saita dad'e mana rabin shekara zatai anan saiki sake sabon shiri". "Haka tace miki uwar ma'karyata kinga Najat ina raba ki da kiwon aura kina cewa aura ta haihu ko Zainab d'in ce zatai shekara kuma makarantar fa ko saita ha'kura saboda jin dad'i dama irinki ce an fad'a miki ita bata wasa da karatu ki koyi da ita"? Dariya Najat tai tana cewa "to me za'a fasa mutuwa ko hisabi"?. "Ba wanda za'a fasa saidai kimin shiru domin ba ke na tambaya ba sai naji daga bakin ta idan kuma kunyi maganar ne naji ko gaskiya ne"? Mikewa Najat tai tana shiga d'aki tace "eh man gaskiya na fad'a miki ai gata nan ki tambaye ta nikam shikenan bari nai baccin rabin lokaci kafin a gama yi mana tuwon shinkafa da miyar ganye muzo muci dad'i ko kakus"? Da kallo kaka A'i ta bita tana cewa "haka kika iya baki iya aiki ba sai ci kamar gara zan had'a ki da Balarabe ne bari yazo gidan gaishe ni ko zuwa jimawa ne" wuf taga Najat ta fito daga d'aki tana dawowa inda take zaune ta d'auki wu'ka ta soma yanka ganyen da za'ai miyar tana cewa. "Shikenan kakus na fito sai komai ya wuce basai kin fad'a masa ba kiyi hakuri so kike ya had'a ni da Yaya Auwal kisa yamin duka"?. "Ke kika sani yarnan ni bance yasa Auwalu ta dake ki ba amma dai idan baki tsaya kin koyi girki ba yanzu yaushe zaki koya"?. "Cab jimin tsohuwa ce miki akai ban iya girkin ba ko me duk abincin da ake kawo miki daga gidan mu nice nake dafawa ba Ummar mu ba kuma bari na baki mamaki Zainab zo ki zauna nayi mata tuwon nan yau dai tasan ni ba kanwar lasa bace wajen fannin girke-girke" tai maganar tana mi'kewa daidai Zainab ta dawo 'kar'kashin biyar ta zauna tad'an girgiza kai tana kallon Najat kafin tace. "Gashi can saiki kula" mayar da hankalinta kan kaka A'i tai tana d'aukar ganyen da Najat ta fara yankawa taci gaba tana cewa "am kaka ranar juma'a ta sama zan koma insha Allah". "To Zainab Allah ya kai mu". "Amin Kaka A'i"............ ✨✍️YUSRAH MUSA WRITER 1__Yarima Abdul-maleek 2___D'an millionaire 3____Safreeyyah 4_______Royalty 5____Minister Ashraf 6__Me kamar sarki And now Zuciyar Aliyu ce Later Yarima Aryan 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 PAGE 09 Kwana biyu tsakani Hajiya tana zaune Umma ta shiga zata gaishe ta bayan ta dawo daga bikin da taje a Katsina sallama tai ta shiga tana samun guri ta zauna cikin ladabi tace "Hajiya ina yini"? Kamar ba za ta amsa ba ta kalleta sau d'aya ta d'auke kai murya can 'kasa tace "lafiya" shiru Umma tai cike da damuwa ta rasa me taiwa Hajiya a gidan nan kowacce suruka zata zo ta gaisa ita ta amsa mata cikin sakin fuska amma banda ita............ "Yaushe wancan yarinyar zata dawo"? Taji muryar Hajiya ta katse mata tunanin da take yi numfashi ta sauke tana cewa "munyi waya da ita d'azu tace min sai juma'ar sama zata dawo amma nace ta taho jibi saboda an koma islamiyya". "Au ashe da ba'a koma makarantar ba baza kice ta dawo ba a gidanku zata je ta tare ana karanta mata rashin da'a ta fita duk sanda taga dama ta dawo lokacin datai ra'ayi saboda an koya mata karuwanci dama taya zata so zaman nan tunda anan akwai sa ido shiyasa ta'ki aure kenan tana can tana taro muku kud'i ko? To wallahi bari kiji idan baki kirata yau kince sa'ko daga ni nace ta dawo gobe ba tofa sai kin bar gidan nan dan wallahi a goben sai sun ganki sai nasa Abdullahi ya sakeki kuma saki uku ba d'aya ba balle kisa ran zaki dawowa mutane gida dan na fahimta dasa hannun ki Zainab take komai a gidan nan kuma wai a hakan ke d'in 'yar malamai ce 'yar malamai ko kuma 'yar malaun-malun mtswwww" idon Umma fal yake da hawayen damuwa da takaicin maganganun da Hajiya take fad'a mata to amma ya zatai da rayuwarta haihuwa ce ta bata sannan tasan cewa dama can Hajiya ba 'kaunarta take ba kawai Allah ne ya 'kaddara zaman aurenta a gidan badan haka ba yadda ta kafa mata 'kahon zu'ka take sukarta da muyagun maganganu da watace baza iya wannan ha'kurin datai ba sama da shekara talatin da biyar tana fama da kayan ba'kin ciki.................... "Tashi ki bani guri sannan kada Allah yasa kiyi abinda nace miki na rantse da Allah gobe indai banga Zainab ta dawo ba kema zamanki ya 'kare cikin gidan nan fatan kinji ni dakyau"? Shiru Umma bata ce mata komai ba sai mi'kewa datai ta fita daga sashin Hajiyan bata yarda kowa ya fahimci me yake faruwa ba duk da can ma ta je ta tarar Asiya da Asabe su na fad'a amma bata iya tsayawa ba saboda abinda ke ranta yafi gaban nasu su hayaniyar duniya ce da abin duniya yake rud'a su ita kuwa 'kiyayya ake nuna mata ake nuna 'yarta d'aya da take jinta tamkar da dubu. Tana shiga d'aki ta d'auki wayarta hawaye na zuba ta kira layin Zainab amma wayar a kashe aje wayar tai tare da ranka tagumi tai shiru kusan mintuna biyar daga baya ta sake d'auka da gwada jin a rufen ake sake ce mata yasa ta kira layin yayanta tace ya bada a kaiwa Zainab magana zasuyi Najat ya aika takai mata a lokacin ta gama linke kayanta kenan ta maida su cikin trolley Najat ta shiga da sallama tana cewa "Zainab ga Ummanki tana neman ki" fitowa daga d'aki tai tana cewa "Umma kuma lafiya dai fatan ba wani abu bane"? Ta tambaya hankalinta a tashe kai Najat ta girgiza tana mi'ka mata wayar tace "wallahi ban sani ba nidai kawai ina shigowa gidan mu naji babanmu yana waya yace nazo nakai miki ta kiraki bata sameki ba wayarki a rufe". "Eh na kaita shagon caji ne tun jiya da dare ta rufe bari na kirata zuwa jimawa nasan ta cika sai naje na kar6o" ta karasa tana bin bayan kiran da Umman tai jin ta d'aga yasa tace "assalamu-alaikum Umma ina yini"? Muryar Umma da alama damuwa tace "lafiya kalau Zainab na kira wayarki ban same kiba dama cewa zanyi gobe ki taho da safe kinji"? Da mamaki Zainab tace "Umma da akwai matsala ne naji kamar muryarki da damuwa ko"? Kai Umma ta d'aga tana cewa "eh d'azu bayan na dawo daga Katsina na shiga gurin Hajiya zan gaisar da ita shine take cewa na barki kin taho nan kin zauna idan baki dawo gobe ba nima sai tasa babanku ya sakeni a goben na taho nan saimu had'u mu zauna shiyasa nace ki taho goben da safe kinji" wani irin d'aci da zafi ne ya tsaya a 'kirjin Zainab wato har yanzu Hajiya bata canza halinta ba kenan tana zagin Umma akan ta rufe ido tai hawayen da suka cika shi suka fara fitowa waje a hankali ta jinjina kai tana cewa "shikenan Umma ba damuwa insha Allahu zan taho karki damu babu abinda zai faru nasan saboda ni Hajiya tai miki haka amma ba komai zan dawo Allah ya rufa asiri'' "Amin Zainab Allah ya miki albarka saikin dawo". "To Umma ki huta gajiya" katse wayar Zainab tai tare da saka hannunta duka biyun ta rufe fuskarta hawaye suna zuba ranta a mugun 'bace karshe kawai ta fashe da kuka da yake Kaka A'i da Najat suna waje babu wanda yasan abinda yake faruwa harta gama kukanta a lokacin ana kiraye-kirayen sallar magriba ta mi'ke daga d'akin ta fito ta baiwa Najat wayar tad'au buta tai alwala tana idarwa ta mi'ke ta d'auki kud'in da zata kar6o cajin tana kar'bo wayarta data dawo tai sallar isha sakamakon tasan kafin taje gida an riga anyi dare yaja ta shiga d'aki kawai suna zaune suna zance a waje sai ganinta sukai ri'ke da trolley tana ja da mamaki duk suke kallonta kaka A'i data aje carbin hannunta tace "a'a Zainab ina zuwa haka baki gama linke kayan bane"? Kaita girgiza tana cewa. "Na gama gida zan tafi" da sabon mamaki Kaka A'i ta zaro ido tana cewa "Subanallahi gida kuma Zainab a wannan lokacin ki bari saida safe man ko wani abu ne ya faru naga kunyi waya da Ummar taki yanzu"?. "A'a babu abinda ya faru kawai tafiya zanyi gobe da safe zan koma makaranta ne". "To amma Zainab wacce irin tafiya ce yanxu da dare me zai hana ki bari da safe idan kin karya saiki tafi kodai akwai abinda yake faruwa acan lafiya kuwa". "Eh lafiya babu komai Kaka A'i dan Allah kuyi hakuri ki barni na tafi yau insha Allahu babu abinda zai faru zanje gida lafiya nafi so naje yau bazan sake kwana anan ba" ganin da Kaka A'i tai kamar hankalin Zainab din a tashe gashi ta'ki ta tsaya akan saidai ta tafi yasa tace "to shikenan Zainab ba damuwa Allah ya kaiki gida lafiya ubangiji ya kare ki nagode ki gaishe da kowa" Kaka A'i na rufe baki Zainab taja trolley tai gaba tana cewa "na tafi" da kallo kaka A'i ta bita tana cewa "to Allah ya tsare amma wacce irin tafiya ce wannan da dare ba shiri ga shi ita Zainab ta kasance yarinya me zurfin ciki ba za ta ta'ba fad'a min abin da ya sa za ta tafi d'in ba Allah ya rufa asiri kawai" Kaka A'i ta fad'a cikin rashin kwancyar hankali da jimami................... See you tomorrow morning. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 10 Zainab na fita ta tari me mashin ya kaita tasha daga nan bayan mota ta tashi suka nufo Kano amma duk da haka bata iso da wuri ba sai wajen karfe goma da rabi na dare Umma tana d'aki a zaune ta zubawa guri d'aya ido taji sallamar Zainab d'in ta shigo da mamaki sosai ta d'ago tana kallon ta daidai ta karasa shigowa cikin d'akin ta saki hannun trolley ta cire hijab tace. "Sannu da gida Umma ina yini"? Har lokacin kallonta Umma keyi da mamakin da ya'ki 6oyuwa tace "Zainab lafiya na ganki yanxu meyasa baki bari sai gari ya waye ba"? Kaita girgiza tana zama tace "Umma hankalina ya riga ya tashi da abinda naji kin fad'a tunda naji haka nasan Hajiya ce tai wannan ba komai ba na tabbata na sake kwana a D'an Yana saina ganki sai tasan yadda tayi ta tura ki gida ni kuma hakan ne bana so shiyasa kawai na taho kuma koba haka bama ina son dawowar saboda kayan mutane wanda ban d'inka ba". "Tom ba damuwa tunda kin dawo naji dad'in hakan Allah ya rufa asiri" Amin Zainab tace tana mi'kewa ta d'auki trolley ta zata kai d'akin ta daidai Sameer ya shigo tsaye yayi yana kallonta cike da mamaki shima yace "a'a wata sabon gani Zainab yaushe kika dawo ban sani ba ko yanzu na ganki kina kokawa da akwati"? D'an murmushi tai tana cewa "eh ban jima da shigowa Yaya Sameer ina yini"?. "Lafiya kalau fatan kin dawo lafiya ya kika baro Kaka A'in taki"?. "Tana lafiya itama tana can na barota a 'yar barandar gidanta tana kan sallaya". "Ok masha Allah naji dad'in dawowar ki sosai dama d'azu na had'u da wannan yarinyar Hamimah tana tambaya ta wai kin gama musu d'inkin su nace a'a ban sani ba bakya nan saidai idan kin dawo ashema kina kan hanya". "Eh ai nata d'inkin na gama saura iya na 'kanwar su itama na yanka had'awa ne banyi ba saidai gobe da safe tunda ba makaranta zanje ba" kaiya jinjina yana shirin magana Asabe data fito ganinsa tsaye da kuma wacce suke magana yasa a masife tace "Sameer ina maganin da nace ka kawo min ko saina mutu sannan zaka fahimci bani da lafiya ka tsaya zancen banza da wofi wanda bazai amfane ka ba" ta karasa maganar tana zafgawa Zainab harara baiyi magana ba sai karasawa dayai yana mi'ka mata yace "kiyi ha'kuri gashi na taho kawo miki naga 'kanwata ta dawo shine na tsaya mu gaisa" tsaki Asabe tai tana juyawa ta shige d'aki shima Sameer d'in waigawa yai ganin ba Zainab alamar ta shige d'aki yasa shi komawa bakin kofar d'akin nata yana cewa. "Zainab". "Na'am Yaya Sameer" ta fad'a tana fitowa da 'karamin ba'kin mayafi a hannunta ta yafa shi a kanta "kina bu'katar wani abu ne"? Murmushin daba shiri tai saboda a rayuwa Sameer yana mugun burgeta yana sonta gashi dai ubansu d'aya amma baya nuna mata 'yan ubanci ba kamar Balki ba wanda ko kallon arziki ba ta yi mata sai habaici da ba'ka'ken maganganu................. "Zainab nace kina bu'katar wani abu ne"? Kaita girgiza tana kallon sa cikin girmamawa tace "a'a Yaya Sameer na gode da kulawa". "Ok bakya bu'katar komai kinci wani abu ne"?. "A'a". "Amma kikace bakya bu'katar komai please ki fad'a min abinda kike so na kawo miki bana so ki kwana da yunwa kinji"?. "To Yaya Sameer kawo min gurasa mai 'kuli kad'ai ta isa". "Ita kike so"?. "Eh itan ma tayi". "Ok bani mintuna ina zuwa" ya fad'a yana fita d'akin Umma ta koma ta d'auko handbag d'inta ta koma nata d'akin ta bud'e wayarta ta fara dubawa kafin ya dawo. Fitar Sameer kam kai tsaye wajen wani mutum me soya doya da naman kaji a anguwarsu ya nufa ya siyo mata abar da tace tana so ya kawo mata godiya sosai tai masa harya juya zai fita tace "Yaya Sameer dan Allah kar'bi wannan ka siyo min klin da 'yan abubuwa a shago da safe zan kaiwa Hajiya kasan indai taga na dawo ban bata abun sannu da zuwa ba saita fad'a ni kuma ba tafiyar shiri nayi ba" murmushi yayi yana cewa "a'a barshi karki damu idan na tashi shigowa gida zan taho miki dashi saiki bata". "To na gode Allah ya 'kara arziki" Amin yace yana fita itama ta tashi ta fita d'akin Umma ta shiga ta d'iba mata sannan ta koma taci iya wacce zata iya ci ta sake fitowa ta wanke hannunta ta komai fitilar wayarta ta kunna ta d'orata akan keken d'inkinta ta d'auko tsintsiya tai bismilllah ta share d'akin ta gyara katifarta ta fesa turare ta shimfid'a bedsheet tare da d'aukar wayar ta kashe fitilar ta kwanta. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA PAGE 11 Kusan sha biyu da rabi babansu ya dawo daga gurin sana'ar sa dama already kullum saiya shiga gurin Hajiya sannan zai karasa kofarsa shiyasa yauma dukda dare yayi da harzai wuce sai kuma ya tuna indai baije ba gobe saita masa tas da safe shiga yayi ya tarar batai barci ba suna zaune tare da Haulat da su Balki kusan 'yan mata shida sun aje babbar waya suna kallo da sallama ya shiga ya gaisar da Hajiya ya aje mata tsaraba kamar yadda ya saba kullum yad'an siyo mata abun motsa baki ya mi'ke zai tafi tace. "Abdullahi tsaya zamuyi magana dakai akan wancan yarinyar taka" jin abinda tace yasa saida gabansa ya fad'i tunda yaji tace haka yasan Zainab take nufi ya rasa me tai mata da jinin su baizo d'aya ba yarinya me cikakken hankali da nutsuwa wacce magana bata dameta ba amma Hajiya gabadaya tabi ta addabi rayuwarta ba dalili........................... "Abdullahi ka kira Zainaba ka fad'a mata sa'ko lallai in jini ta dawo gida gobe wallahi tallahi na rantse da Allah idan bata dawo a gobe ba saika saki uwarta tabi bayanta ka gane kuma ka jini"? Shiru yai ransa babu dad'i bai iya ce mata komai ba cikin fad'a Hajiya taci gaba "nayi magana kayi banza dani saboda ka zauna da marar tarbiyya ta koya maka tsiya da yadda ake wula'kanta uwa shine zaka nuna min"? Kaiya girgiza a damuwance yace "dan Allah kiyi hakuri Hajiya idan na shiga yanxu zansa ta kirata zata dawo goben" gyara zama Hajiya tai tana mayar da hankalinta kan kallon da suke yi tace "wannan kuma ya rage ruwanka tsabar shashanci na rasa wanne irin so kake musu da baka ganin aibun su kodai asiri sukai maka nasan wannan son da kake musu ba banza ba idan bakai a hankali ba wata rana za'ai bakai dan tuntuni na fahimta wannan talaucin da kake fama dashi sune sila basu da 'kashin arziki kaga fa duk sauran 'yan uwanka kowa aikin gwamnati yake yi kuma kaima kayi karatun nan amma auren dangin tsiya da ba'kin jini ya jawo maka ka 'kare a gaban bencin kayan miya ana mi'ko maka d'ari uku d'ari biyar ka na zubawa a leda kana mi'kawa" sosai ransa ya 6aci ganin yadda Hajiya take masa a gaban 'ya'yansa da 'ya'yan 'yan uwansa bai kamata ba..................... "Tashi ka bani guri kuma ka tabbata sa'ko na yaje gurin wannan uwar gulmar" yaji muryarta ta katse masa tunani mi'kewa yayi yana d'aukar kayan daya shigo dashi a hannunsa yace "saida safe Hajiya" kamar zatace masa kowa ya kwana lafiya shi yaso sai kuma a she'ke tace "toh" fita yayi ya wuce tasa kofar kai tsaye d'akin Umma ya shiga bai shiga d'akinsa ba saboda ranar a d'akinta yake har lokacin tana zaune a yadda take tayi tagumi hatta gurasar da Zainab ta kawo mata bata ko kalli yadda take ba balle ta samu damar ci sallamar dayai ce tasa ta d'ago tana d'an sakin fuskarta saboda karya fahimci halin da take ciki tace. "Sannun da dawowa" zama yai yana sauke numfashi ransa na sake 6aci ganin yadda ta jefasu cikin damuwa yace "kinyi magana da Zainab ne yau"? Kaita d'aga tana kallon sa tunda taji ya tambaya tasan daga kofar Hajiya yake shima yaje ta tsiyata shi kenan............................ "Tunda kinyi magana da ita gobe da sassafe idan kinyi sallar asuba ki kirata kice ta taho a goben karta 'kara kwana saboda Hajiya ta fad'a min wata magana da banji dad'in ta ba kuma tayi rantsuwa akai cewa indai bata dawo a gobe ba kema sai kin bita" yana rufe baki Umma tai murmushin da yafi kuka ciwo tana cewa "Zainab ta dawo tana d'akinta tun d'azu ta shigo". "Au ta dawo"?. "Eh ta dawo tana nan". Jin haka yasa ya mi'ke yana fita 'kofar d'akin Zainab yaje yana cewa "Zainab Zainab" daga d'aki tace "na'am Abba" tashi daga kwancen da take tayi tana zuwa bakin kofar ta bud'e tare da fitowa ta dur'kusa a gabansa tana cewa "ina yini ya aiki fatan ka dawo lafiya"?. "Lafiya kalau Zainab fatan kema kin dawo lafiya ya kika baro su Umman da wajen Alhaji Balaraben duk suna lafiya"? Kaita d'aga tana cewa "eh lafiyarsu kalau". "Masha Allah dama gaisawa kawai zamuyi naga lafiyarki tashi ki koma ki kwanta saida safe" mi'kewa tai tana cewa "Allah ya tashe mu lafiya Abba" Amin yace yana yin wajen kofar d'akinsa ita kuma ta koma d'aki ta kwanta kamar yadda take d'azu. ✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YMA DUTSE PAGE 12 Washe gari da asuba bayan Abba ya dawo daga masallaci sanin da yayi Zainab ta riga ta dawo shiyasa ya shiga 6angaren Hajiya zai gaida ita cikin 'kwarin gwiwa ba fargabar fad'an Hajiyan za tai masa daidai ya zauna sun gaisa tun bai sauke numfashi ba ya ji tace "Ina sa'kona Abdullahi" da 'yar alamar tambaya yace "wanne sa'ko ne Hajiya"?. "Au harka manta saboda an shanye ka baka damu da umarni na ba"? Cikin ladabi ya sake du'kawa yana cewa "kiyi hakuri Hajiya sa'kon ne na manta" cikin fad'a tace "ai gara daka manta amma bazaka manta ba daga lokacin dana mi'ko maka biro da takarda nace ka saki wancan matar taka zaka tuna ko"? Jin abinda tace yasa ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "kiyi hakuri Hajiya sha'afa nayi Zainab ta dawo tun jiyan anan ta kwana". "Au ta dawo tun jiyan shine saboda rashin arziki data gada a gurin uwarta shine bata zo ta gaida dani ba har yau zata shigo tazo ta sameni sai naci mutuncin ta"?. "Dan Allah Hajiya kiyi hakuri bansan bata zo ta gaida ke ba amma zan mata fad'a karta 'kara" tsaki Hajiya tai tana cewa "tama 'kara d'in man ni dama da ita da babu duk uwarsu d'aya yarinya ta'ki aure kun zuba mata ido babu ruwanku ko saita zama tsohuwa a gida ne ko kuma auren ne baza tai ba ko wanda zata aura ne bata dashi fad'a min naji"?. "A'a tana dashi amma ban sani ba ko basa tare yanzu". "Waye shi d'an waye a ina yake"?. "Ina jin kamar dai anan anguwar yake saidai bansan ta wajen wanne 6angaren ba abinda na sani kawai dai tace min malami ne a islamiyyar su". "Hum yayi kyau Allah ya kawota gurina zata sani ne sai naci mutuncin ta wanda ranta zai 6aci tayi zuciya ta fito da mijin aure inace ga Rafi'atu nan da Ralmat duk sa'annin tane kowacce tayi aure harda yara suke dashi amma ita ta tsaya ruwan ido indai tai za6en tumun dare wallahi a kanka masifa take bani ba kune zaku ri'ka sha'kar ba'kin ciki kuna mata aiken abinci daga Nan kunga babu amfani kenan kun siyar da akuya tazo tana gogar muku katanga" sosai ran Abba ya 6aci baya jin dad'i duk lokacin da Hajiya ta fad'i wani abu akan Zainab saboda shi yasan wace 'yarsa yasan irin hankali da nutsuwarta ya tabbata jinkirin aurenta alkhairi ne saboda kullum yana Mata addu'ar ta samu miji na gari yasan hakan ne yasa lokaci yake 'kara ja addu'ar sa ta kar'bu insha Allah Zainab zatai aure zata bar gidan nan duk daren dad'ewa............ "Na gama magana dakai tashi ka bani gu" yaji muryar Hajiya ta katse masa tunani kaiya girgiza yana mi'kewa zai fita ya aje mata d'ari biyar wanda tun bai gama kai ga ajewar ba tace "me zan gani wacce lalacewar ce wannan"? Ta fad'a tana d'ago da d'ari biyar d'in alamar batai mata ba shiru yayi ya rasa me zaice mata "dakai fa nake ka rasa me zaka bani sai d'ari biyar wadanda ban haifa bama suna min babbar kyauta har dubu goma Allah yayiwa yaron nan Aliyu d'an gidan Alhaji Amadu albarka ranar Samar ya kawo shi dubu goma 'kal-'kal suna walwali a mi'ke ya d'auka ya bani balle kai anya kuwa lafiyarka kalau"?. "Lafiya kalau nake Hajiya kud'in ne na siyo abun karyawa jiya da dare kuma yanzu zanje na bada kud'in abincin rana dana dare shiyasa kud'in suka 'kare babu wani a gurina iya d'ari biyar d'ince tai saura da nayi lissafi saboda jiya na bayar da kud'in sarin kayan miya bani da komai". "Fatara a kanka ta 'kare ne kullum da anyi magana sai kace baka da kud'i wannna kiran babun da kake shiyasa baka gaba abun ma ya shafi 'yarka ta'ki auruwa kowa zai wuce yana kallonka a gaban bencin tumatur kana cinikin naira dari biyu d'ari uku ba albashi kake d'auka ba waye dama zaizo yace yana sonta yasan ko kayan d'akin arziki ba samu zaiyi ba balle kayan gara" rufe ido Abba yayi yana girgiza kai zuciyarsa gaba d'aya ta 6aci da sauri ya fita daga gurin Hajiyan ko sallama baiyi mata ba yasan idan da rikicin tsufa a wadannan maganganun nata tofa akwai 'kiyayya ma yana so yasan meyasa bata son Zainab amma har yau ya kasa ya ganewa shi dai yana son kayarsa domin koda duniya ne suka taru suke 'kin Zainab shi kad'ai zai so abarsa domin cikin 'ya'yansa babu wanda ya shiga ransa kamar Zainab saboda ladabi da biyayyarta ga tarbiyya. Zainab tana d'akin ta bayan datai sallah bata fito ba saida gari yayi haske sannan ta fito ta shiga gurin Umma ta gaida ita saboda gudun laifi yasa tace mata ta tashi taje ta gaisar da Hajiya amma sakamakon ba tafiyar shiri tai ba bata siyo tsarabar komai ba yasa bata jeba ta bari Sameer ya shigo ta tambaye shi idan ya siyo mata idan kuma ya manta saita fita ta siyo da kanta domin da taje gurin Hajiya ba tsaraba gara ta ha'kura da xuwa gaida ita. Shi kam Sameer bai shigo gidan ba har wajen sha biyu sannan yazo mata da takarda a lokacin tana gurin wanke-wanke tana taya Umma ayyuka ya shigo tsayawa yayi daga wajen kofar shigowa yana cewa "Zainab zo nan" kallon inda yai maganar tai tana mi'kewa da fara'ar ta tace "Yaya Sameer ina kwana''? Kaiya d'aga yana cewa "lafiya na tashi akwai biro a gurin ki ne"?. "Eh da akwai baka zanyi"? Zama yai a kan wata farar kujerar roba dake kofar d'akin Zainab din yana cewa "uhm kawo min abu zanyi dashi" shiga tayi tana cewa "to bari na duba maka jakar islamiyya ta" yana zaune ta d'auko masa ta bashi zata koma gurin aikin yace "a'a Zainab dawo nan zo ki cike" jin abinda yace yasa da mamaki ta juyo tana kallon sa tare da nuna kanta tace "nice zan cike"?. "Eh kar6i" ya fad'a yana mi'ka mata 'kure takardar tai da kallo tana cewa "amma Yaya Sameer takardar ta mene zan cike"? Murmushi yai shima yana kallon takardar yace "form ne na makaranta" da sabon mamaki tace "form na makaranta kuma waye ya sai mun makaranta Yaya Sameer"?. "Ba ruwanki kawai kizo ki cike min" dawowa tai tana kar'ba tare da zama akan wata 'yar 'karamar kujera ta aikin gida ta fara cikewa fitowar Asabe kenan daga d'aki ta tashi daga barcin hutu ganinsa zaune ga Zainab na cike paper yasa ta aje butar data d'auka tana cewa "Sameer me kake anan"? D'agowa yayi yana kallon ta yace "ina kwana Umma"?. "Lafiya nace me kake anan"?. "Takarda ce na kawowa Zainab ta cike". "Takarda ta meye ko aikin polio ka samo mata"?. "A'a ba polio bane". "To takardar ta meye"?. "Form ne na makaranta" zaro ido Asabe tai tana cewa "form na makaranta karatu zata d'ora"? Amsa ya bata da "eh" daidai Zainab ta mi'ko masa takardar tana cewa "gashi Yaya Sameer na gode" ta fad'a tana mi'kewa ta koma gurin aikinta da kallo Asabe ta bita cikin takaici kafin ta dawo da hankalinta kan Sameer da shima ya mi'ke yana shirin fita tace "kenan kaine ka biya mata taci gaba da karatun"?. "A'a bani bane ni ina naga kud'in dazan biya mata tai karatun jami'a"? jin abinda yace ta sake jefa masa tambaya "ban gane bakai bane to waye ya biya mata"?. "Wani ne". "Wani kuma Sameer karka raina min hankali fa bana son munafirci uban wa take dashi wanda zai biya mata kud'i tayi karatu a wannan tsadar rayuwar"? Shiru Sameer yai bai sake magana ba taya zai fad'a mata cewa Aliyu ne ya siyawa Zainab makaranta bayan ita kanta Zainab d'in batasan yana sonta ba kawai zaman lafiya ya samu ya fita karma Asabe ta 'kureshi da tambayoyin har yayi 6arin zance juyawa yai zai fita ta ri'ko rigarsa tana cewa. "Sameer ka fad'a min gaskiya kona tsine maka waye ya siya mata makaranta kaine"? Kaiya girgiza yana cewa "wallahi Umma bani bane wani ne" a masife tace "to waye wanin inda kana da gaskiya ka fad'a min wanda ya siya mata munafirta ta kake Sameer wato kafi d'aukar Zainab wacce kuke uba d'aya da muhimmanci akan Bilki da kuke uwa d'aya uba d'aya ko". "Ba haka bane Umma dan Allah ki fahimta wallahi bani na siya mata ba nima d'an sa'ko ne" kallo inda Zainab take zaune Asabe tai tana ta'be baki tace "a iya sanina tunda Zainab ta taso ban ta'ba jin ance ga wani fitaaccen saurayi yazo gurin taba sai wannan fatararran malamin islamiyyar tasu waye sunan nasa"? Murmushin daba shiri Sameer yayi yana d'an girgiza kai yace "a'a bashi bane bansan ma wani Yaa sayyadi yana sonta ba sai yanzu naji a gurinki" yana fad'in haka ya juya ya fita cizon yatsa Asabe tai tana komawa ta d'auki butar da zata shiga band'aki tana cewa "humm zanga wannan munafikin ne ya siya miki makarantar idan tai tsami zamuji basai mun tambaya ba munafikai kawai daga ke har Sameer d'in zai dawo ya same ni ne shashashan yaro" shiru Zainab tai ko tari duk da taji zafin maganar da Asaben ta fad'a saidai ya zatai tunda uwace a gurinta bata da bakin da zata bud'e ta rama damuwarta Allah ya had'ata da alkhairinsa........................ Kwacaff taji 'kara a kusa da ita da sauri ta d'ago a tsorace tana kallon Asabe wacce ke tsaye a kanta tana sake turo mata kwanukan data d'ebo daga d'aki tace "yar aiki ki had'a da nawa kwanukan ki wanke dama hakan ne ya dace dake tunda kin 'ki aure saiki zama baiwar mu ashe ware nawa kwanukan kike saboda baki gaji arziki ba kodan ni ban haife kiba shiyasa kika ware nawa cikin naku kika mayar dasu gefe"? ta tambaye ta tana sake d'ebo su ta watso mata su cike da rashin son zaman lafiya shiru Zainab tai ko d'agowa batai ba balle tace wani abu sai kwanukan data tattara ta saka a kusa da nasu kafin ta gama itama ta wanke mata baki Asabe ta ta'be tana juyawa ta shiga d'aki tana rera wa'ka. Tas Zainab ta wanke mata kamar yadda ta wanke nasu ta d'auka har kofar d'akinta takai mata kamar dai babu abinda ya faru muryarta a daidai tace "gashi Maman Bilkisu na gama" ta fad'a tana ajewa saidai ko juyawa batai ba Asabe tace "shigo ki kawo min kamar yadda kika kaiwa taki uwar ko itama a kofar d'akin kika aje mata ki kace gashi ta fito ta d'auka"? Kai Zainab ta girgiza tana du'kawa ta d'auki kwandon ta shiga da sallama ta aje mata sannan ta fito ta d'auki nasu takai musu shi kitchen ta shiga d'akin Umma ta share ta share nata sannan ta share tsakar gidan ta wanke band'aki saida ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta shirya tana zaune lokacin tana shirin tashi taje gaida Hajiya tunda har yanzu bata samu ta shiga ba hijab d'inta ta d'auka da kayan tsarabar da tasa Sameer ya siyo mata ta koma d'akin Umma ta sanar mata zata shiga gurin Hajiya..................... We will meet again🤝. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH DUTSE Chat with me. +234 816 098 3083 PAGE 13 Ta fita daga kofarsu kenan taga Afifah ta fito ita kuma daga 6angaren Hajiya ga Balki da Haulat sun biyota kowacce tana so dole sai Afifah tasan da ita kodan su samu kusancin 'kawance su ri'ka shiga gidansu murmushi Zainab tai wanda ganinta yasa Afifah tahowa da d'an gudu tana rungume ta cikin farin ciki tace "kai Hajiya zee-zee nayi kewarki sosai wallahi matafiya kamar bazaki dawo ba gashi idan na kiraki ko kad'an bana samunki kullum wayarki a rufe meya faru ne"? Har lokacin da murmushi akan fuskar Zainab tace "ayya kiyi hakuri Afifah acan ne kwana biyu da zuwana na cire Sim tsautsayi wallahi shikenan na rasa shi babu inda ban duba ba ya fad'i shiyasa kika jini shiru sai d'ayan sabon Sim d'in da nayi lokacin dana kusa tafiya shi kuma sakamakon babu islamiyya yasa bamu had'u na baki ba" d'an had'e rai Afifah tai tana cewa. "Kuma wato shine kikai tafiya sama da sati hud'u ko sallama baki min ba ko kamar ni Afifan ki guda ko sanarwa saida na gaji nazo na tambayi Yaya Sameer yace min kina D'an Yana na gode" had'e hannunta Zainab tai tana cewa "ina neman afuwa nayi laifi Afifah nasan ban kyauta ba kiyi hakuri gani aina dawo ko kamar banje ko'ina ba yanzu haka zaki ji". "Uhm haka ne mu karasa d'akin naki ko,? dama ke nazowa sannu da zuwa saboda d'azu Yaya Sameer sun shiga gidan tare da Yaya discipline nake tambayar sa ke shine yace min kin dawo" da alamar tambaya Zainab tace "waye discipline kuma a gidan ku"? Dariya Afifah tai tana cewa "humm Yaya Aliyu nake nufi boss me zamani kenan". "Ok ya dawo ne"?. "Eh ya jima da dawowa ma neman komawa yake kwanan nan" numfashi Zainab ta sauke tana cewa "Allah ya taimaka". "Amin Hajiya zee-zee muje ki bani tawa tsarabar mana". "Tab waya fad'a miki na siyo kayan tsaraba nikam ban siyo komai ba saboda ba tafiyar shiri nayi ba kwatsam abun yazo min". "Au nan nufinki nazo miki sannu da dawowa har gida kice min babu kayan sannu da zuwa tab aiko dole ki bani wani abu". "Indai ba kaina zan baki ki tafi dani ba da gaske nake ban zo da komai ba kinga wannan ma klin ne saboda halin tsufa irin na Hajiya na tabbata naje gaida ita babu kayan sannu da zuwa saita maganta min sai d'azu Yaya Sameer ya siyo min a shago yanzu zan kai mata amma tunda kin zo min kawai mu komai nan da la'asar naje gurin nata" kai Afifah ta d'aga tana cewa "ok muje to" juyawa sukai suka koma kofar su Zainab d'in wanda Haulat taja tsaki tana cewa "gaskiya Zainab d'in nan anyi munafika mai mugun hali ji kawai ta ganmu tare maimakon tace mu tafi gurin Hajiyan gaba d'ayan mu sai tawani ce su tafi d'akinta" baki Balki ta ta'be tana juyawa zata koma tace "damuwarta ce ba tawa ba 'kawance ne idan naga damar yi da 'kanwar Aliyu ko bata so sai mun 'kulla kuma saina raba su itama ai zilama ce tasa ta le'ke mata kina gani fa hatta islmaiyya idan muka je suna tare ko'ina suna manne sannan idan an taso ma saidai su ware kansu su taho tare tsabar neman suna" bin bayanta Haulat tai suna komawa gurin Hajiya su Zainab kam suna d'akinta tun daga waje idan ka shiga kofar tasu zaka ri'ka jiwo muryoyinsu suna dariya da zance cikin nishad'i na an dad'e ba'a had'u ba Asabe na jinsu daga d'aki tana aiko musu da zagi wai sun dameta sun cika mata kunne da hayaniya kamar suna kasuwa. Afifah bata bar gidan ba saida akai kiran sallar azhar sannan tai sallah lokacin Umma ta gama abincin rana taiwa Zainab magana tazo ta d'iba musu abinci fur Afifah ta'ki ci saida 'kyar shima baifi loma biyar ba tace ya isheta rufewa Zainab tai tana mi'kewa zata raka Afifan kawai ta d'auki kayan da zata kaiwa Hajiya da nufin idan ta rakata ta dawo saita shiga ta gaishe da ita. Suna tafe suna d'an hirar da basa gajiya da yinta saida sukai nisa d'in har ta kusa rakata kofar gate d'in gidansu cak ta tsaya tare da cewa "Afifah bari na koma gida daga nan" juyowa Afifah tai tana kallon ta da alamar tambaya tace "haba Zainab ina laifin ki 'karasar dani har gida dan Allah tunda munzo nan kinji"? Kaita girgiza tana cewa "a'a daga nan d'in dai zan koma kiyi hakuri". "To saboda me"?. "Saboda bazan iya 'karasawar ba kalli man Yaya Sameer yana rumfar kofar gidan ku ga soldier's sannan kuma ga Yayan ki shima yana gurin" kallo gurin Afifah tai tana girgiza kai kafin ta sake juyowa inda Zainab d'in take tana cewa "me zasu tare miki zasu hanaki wucewa ne ba ruwan su dake sannan ba gurinsu zakije ba mu da zamu wuce kawai". "Nifa bazan 'karasa ba Afifah mu rabu anan na koma" ta fad'a tana kokarin juyawa ri'keta Afifah tai tana cewa "wallahi bazaki juya ba mu karasa". "A'a babu inda zanje fa ina da d'inkuna na mutane dana tafi na bari banyi musu ba kuma suna tambaya kawai jeki abinki sai mun had'u a makaranta" had'e rai Afifah tai tana cewa "kai dan Allah Zainab muje dan Allah wai yanzu na tako nazo gurin ki amma ki kasa rakani"? Shiru Zainab tai tana kallo wajen su Sameer tunanin ta yadda zata fara wucewa ta gurin take shiyasa taso ta juya tun anan duk da sukam hankalin su ba'a inda su Zainab d'in suke yake ba................. "Kawai ki koma kiyi d'inkin ki na tafi sai mun had'u a islamiyyar" Afifah ta fad'a tana yin gaba d'an kallonta Zainab tai tasan bata ji dad'i ba na 'kin raka ta din amma ya zatai bata son hakan saidai data wuce ta wancan majalissar mazan ba nikaf a fuskarta gara ta ha'kura duk muhimmancin abinda take son tayi tana kallo har Afifah taje kofar gate d'in gidansu aka bud'e mata ta shiga numfashi ta sauke tana juyawa ita ta koma gida. Shigar Afifah gida duk suna parlor a zaune wajen Momy shiyasa itama bata wuce ba ta zauna a gurin kallonta Fati tai tana cewa "kai wai harkin dawo daga gurin ta"? "Eh man aina dad'e ma a hakan 'kin rakoni tayi har kusan nan muka zo amma tace saidai na taho ita tana da ayyuka" kai Elham ta jinjina tana cewa "nifa tunda nake ban ta'ba ganinta a gidan nan ba Aunty Afifah meyasa bazata ri'ka shigowa bane"? Kafad'a Afifah ta d'aga alamar oho tana cewa "nima ban sani ba na kasa fahimtar dalili har gobe amma Amirah ta dawo daga gida ne naga kamar ba'kuwar mota a can"?. "A'a bata dawo ba saidai idan motar Yaa Afif kika gani". "Ok yana ciki ne"?. "A'a bai shigo ba tunda ni ban ganshi ba cewa nayi maybe ko tasa ce tunda ni banji Momy tace Daddy ya sayi mota ba balle kuma Yaya boss kinga kuwa ai saidai ta Yaa Afif d'in" mi'kewa Afifah tai zatai stairs harta fara takawa ta tsaya ta juyo tana cewa "Momy meyasa Amirah tun ranar data bar gidan nan bata sake dawowa ba"? Girgiza kai Momy tai tana cewa "taya zan sani tunda ba fad'a min tai ba ni washe garin ma bansan ta tafi gidan nasu ba domin ba had'uwa mukai ba" cikin kokwanto Afifah tace "to kodai hana ta komowa sukai a gidan"? "A'a bazasu hanata ba kawai dai ra'ayin tane ko kuma akwai uzurin da yasa bata dawo d'in ba inace tabar trolley nata anan ko dashi ta tafi"?. "Bata tafi dashi ba yana nan amma nayi mamaki da bata dawo ba tun a ranar ko washe gari ba bayan tasan Yaya discipline yana gari" da alamar tambaya Momy tace "kamar ya yana gari meyasa sai dan yana gari ne kad'ai zata zo gidan nan ta zauna bayan ta riga ta saba hakan ya zame mata jiki"? Dariya Afifah tai tuna abinda ya faru tsakanin ta da Aliyun ranar kamar zata cewa Momy ga dalili saboda Aliyu yace mata yana da wacce yake so sai kuma ta fasa fad'a kawai ta girgiza kai ta wuce. Wucewar ta da kamar mintuna biyar Aliyu shima ya shigo gidan amma ba tsayawa yayi a parlor ba wucewa yayi bayan ya wuce ne Fati ta sake matsawa kusa da Momy sosai tai 'kasa da murya saboda gulmar da zatai tace "Momy Yaya boss yana da budurwa ne"? Jin tambayar datai mata yasa Momy kallonta tana cewa "a ina kenan ni ban sani ba idan ma yana da itan kenan" kallon inda Aliyun ya shiga tai tana cewa "to amma meyasa idan baya nan Amirah ko ziyara bata zuwa gidan nan sai taji labarin ya dawo a ranar zaki ganta ta ciko akwati da kaya tazo meyasa"?. "Taya zan sani tunda ba fad'a min dalilin ta nayin hakan tai ba" numfashi Fati ta sauke tana cewa "alamar karfi dai tana ga mai 'kiba nasan ruwa baya tsami banza dole akwai wani abu a 'kasa bazai wuce tace nan gaba tana son Yaya boss ba" murmushi Momy tai tana kallon Fati datai maganar tace "ke kam kin cika sa ido tunda sun dad'e tare suna karatu sun saba mene damuwarki da tambaya irin haka idan ma soyayya suke naku addu'a ne Allah ya bashi mace ta gari wannan shine fatan mu" hannu Elham ta d'aga tana cewa "Amin Momy dan wallahi nikam haka kawai a raina banji Amirah tayi min ta zama matar Yaya boss ba gara wata dai". "Kuma watan kika san 'yar waye mayya ce ko kuma mai 'kulle 'kullen asiri ce mu shiga uku ba gara auren wacce ka sani ba" Fati tai maganar tana mayar da hankalinta kan Momy taci gaba "Momy koba haka magana ta take ba nasan dai duk tsiya da mutum ya auro macen da baisan halin gidansu ba gara ya auri wacce yasan komai nata"? Kai Momy ta d'aga tana cewa "eh haka abun yake wani lokacin amma fa koda 'yar gidan ya aura itama zata iya yi masa 'kulle 'kullen saboda duniya ba tabbas ba kowa ake yarda dashi ba amma watakil wacce zai auro daga can nisan duniya ya kawota cikin ku saita zame muku garkuwa ta zama silar wani abu naku wanda zaku ji dad'in sa koda ace bata nan zaku ri'ka tunawa da ita kuna alfahari da hakan" Momy na rufe baki Elham tace "yauwa Momy irin wannan mace nake so wacce zamu 'karu da ita Allah yasa Yaya boss yayi dace wallahi nasan zamu ji dad'i tunda bamu da Aunty ko d'aya ta 6angaren yayun mu" murmushi Fati tai tana cewa "hum Yaya discipline ance Aunty Afifah to Amin dai Allah ya za6a mana wacce zata zauna dashi damu tsakanin ta da Allah ba cuta ba cutarwa domin zamanin nan ya lalace kowa kansa yake so kowa kansa ya sani abun d'aukar alhaki shine ake ado dashi yanzu idan kaiwa mutum wa'azi akan ya daina wata mummunar dabi'a amsar dazai baka bazai wuce yace maka mutuwar yawa kaka bace ba shi kad'ai yake aikatawa ba" kai Momy ta jinjina tana kallon Fati tace "masha Allah Fatima Zarah Allah ya albarkaci rayuwar ku ya tsare ku a duk inda kuka tsinci kanku gaskiya naji dad'i daya kasance kunsan wasu abubuwa game da rayuwa sannan zakuyi hattara da taka tsantsan ba kowa ake yarda dashi a duniya ba koda 'kawaye akwai 6ata gari sai kun tsaya kun lura kun tantance wace ya kamata kuyi abota da ita wace ya kamata kuyi shawara da ita wace ya kamata ku ri'ka kawota gidanku wace ya kamata ku fad'a mata sirrin ku ko damuwar ku karki biye kowacce irin 'kawa duk sanda wata taso kuyi 'kawance da ita ku fara tsayawa ku karance ta sosai kuga ya dabi'ar ta take ya yanayin mu'amalarta da jama'a take ya tarbiyyarta da kamun kanta suke ta iya kame bakinta ko kuma kowacce kalar magana tazo fad'a take dole sai kunyi nazari ba lokaci guda zaku gane hakan ba domin akwai mayaudara masu fuska biyu ku kula ku kula kunji"? Duk kai suka d'aga mata cikin jin dad'i shiyasa suke matu'kar son su zauna tare da Momy a gida ranar da basu da karatu domin itama babbar makaranta ce wacce suke d'aukar manyan darasi a gurin ta kuma itama tana jin dad'in zama dasu domin sun iya magana mai kyau sannan tarbiyya da sanin darajar d'an adam wannan ba kama hannun yaro tana alfahari da wadannan yaran nata. J.W.A ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA PAGE 14 Batun Zainab kam bayan sun rabu da Afifah ta koma gida kai tsaye kofar Hajiya ta shiga domin ta samu ta gaisar da ita tayi sa'a kuwa ita kad'ai ce babu 'yan matan gidan ko mutum d'aya ta nan taji dad'i saboda gudun abinda zai faru tasan Hajiya baza tai shiru da bakinta ba saita fad'i wani abu da sallama ta shiga tana zama duk da taga kalar kallon da Hajiyan take mata muryarta a nutse tace "Hajiya ina yini fatan na same ki lafiya"? Wani irin kallon kasan ido Hajiya tai mata tana tashi daga kishingid'en da take ta yi tana cewa "ban wuni ba Zainaba nace ban wuni ba kuma lafiya bani da ita jinya nake fatan hakan yasa kinji dad'i dan naga abinda kike fata kenan nace bani da lafiyar ko"? Kai Zainab ta d'an girgiza tana d'agowa ta kalleta tace ''kiyi ha'kuri Hajiya ban samu na shigo miki tun safe bane saboda wani dalili kuma na taya Umma aiki ne d'azu na fito zan shigo 'kawata tazo min sannu da zuwa shine dalilin rashin zuwan nawa da wuri" baki Hajiya ta ta'be tana cewa "ke dai kike sani bai shafe niba Allah ya rufawa uwarki asiri kuma kin taimake ta da kika dawo wallahi da ace baki dawo d'in ba da saidai yau ki ganta tabi bayanki da takardarta a hannu kuma saki uku zansa ayi mata ba d'aya ba balle kisa ran zata dawo gidan sai naga zaki dawo gurin uban naki ko kuma zaki biye mata kici gaba da zama a can" sosai Zainab taji zafin maganar da Hajiya ta fad'a amma ta danne dan tasan dalili tace "Allah ya baki ha'kuri Hajiya ba 'kin dawowa nayi ba dama hutun islamiyyar da aka bamu nake so na 'karasa kuma dama jibi zamu koma" tashi zaune Hajiya tai tana cewa "kuma meye damuwa ta da hakan dan Allah Zainaba idan kin fita daga nan yanzu ki sake d'aukar akwati ki koma D'an Yana tunda acan aka yanke miki cibiya zan nuna miki 'karshen rashin mutunci na a gidan nan wato saboda kinga an zuba miki ido shine kika 'ki fito da mijin aure kullum kina yawo da nikaf kamar mai tsoron Allah ko dan ace ke ta 'kwarai ce taya zaki samu mijin aure kullum fuska tana rufe kamar 'yar garkuwa kodan kin ga ubanki bai Isa dake ba tunda ba mai kud'i bane talaka ne wani lokacin kece kike baku kud'in abinci ko idan jarin kayan miyarsa ya 'kare ki d'ora masa shiyasa kika raina shi kike ganin baida zarrar dazai fad'a miki magana kiji tunda ba wata tsiyar yake baki ba saidai ma shi yayi maula a gurin ki"? shiru Zainab tai ranta a 'bace maganganun da Hajiya take fad'a mata sunyi mugun 'kona mata zuciya da'kyar ta iya aje kayan data shigo mata dashi a leda tana cewa "ga ta ki tsarabar nan" zata mi'ke Hajiya tace "bana so tafi da kayan tsiyar ki dama kinji nace ki kawo min tsaraba ne me zanyi dashi anje uwar ki ta aika kin kunso mata asiri zaku yiwa Abdullahi ban yafe muku ba indai kuka sa d'ana ya daina min abin arziki" da mamaki Zainab take kallon Hajiya jin furucin da take na anje anyo mata asiri kawai dan ta 6atawa Umma suna humm ba komai wata ranar gaskiya zatai halinta akwai dai masu yowa asirin zasu bankad'a ne.......................... "Ke nace ki d'auke tsarabarki ki 6ace min da gani ko lokacin asirin har yanzu bai wuce ba akwai awannin da bokan naku yace miki idan kin zo guri na kiyi"? Jin abinda Hajiya tace yasa Zainab runtse ido tare da jinjina kai ta sunkuya ta d'auki kayan data shigo dashi ta juya zata fita tsaki Hajiya taja tana cewa "as as Allah ya raka taki gona dama ban gayyace ki ba dake da babu duk d'aya a gurina nifa ji nake a jikina kamar ke ba jika ta bace ma wannan yarinyar amma dai bari zan kira Abdullahi zamuyi magana dashi ya fad'a min gaskiya idan shigo-shigo ba zurfi akai masa bai sani ba ya auri uwarta da cikinta naji karshen batu na d'auki mataki dama idan ba tsohon munafirci ba ace daga Murjanatu da ita bata sake haihuwa ba sai uban 6aci da take yi humm zanci mutuncin ta ne bari ma a jima na tashi naje kofar tasu ke karma na bari sai anjima sannan maganganun dazan fad'a na manta zuciyar tawa ta wuce bari nabi bayanta yanzu" ta karasa maganar tana yun'kurawa ta mi'ke tare da d'aukar sandar da take dogarawa dashi ta fita tana tafe tana fad'a. Zainab tana shiga kofar su d'akin Umma ta shiga lokacin Umma tana zaune tana yanka ku6aiwar miyar ganin fuskarta ba walwala yasa tasan daga gurin Hajiya ta dawo sosai taji ranta babu dad'i kallon yadda tai shiru tana kallon guri d'aya tayi tana cewa "Zainab lafiya meya faru"? Kaita girgiza tana kar'bar wu'kar da sauran ku6aiwar duk da ta kusa gamawa muryarta a hankali tace "babu komai'. "Ba komai na ganki a haka fad'a min keda waye ko Hajiyan ce"? Numfashi ta sauke tana d'an rufe ido bata, ba ta amsa ba wanda hakan ya tabbatar mata da cewa Hajiya din ce ta fad'a mata wani abu mara dad'i "Zainab nace ko keda Hajiya ne sai yanzu kika je gurin nata"? Kai Zainab ta d'aga zatai magana sukaji muryar Hajiya tana cewa "eh dani ne mara mutunci wato nan d'in tuhumarta kike ita da waye kin sakata a d'aki kina karanta mata hud'ubar tsiya dani ne nace dani ne idan duka na zakiyi fito ki dake ne tunda dama kin saba zagina shiyasa yauma kika tura ta zage ni hakan bai ishe kiba yanzu kuma shine ku ka 'kule d'aki Kuna zagina saboda duk kanku ba 'yan arziki bane ko"? Shiru Umma tai batace komai ba saboda tasan sharri Hajiya take nema da ita shiyasa kome zatace batai magana ba.............. "Ba magana nake dake ba kina jina kika share ni saboda rashin arziki"? Hajiya ta sake fad'a tana d'aga sandar hannunta ta daki murfin kofar d'akin tana cewa "wai baki ji abinda nake fad'a bane"? Mi'kewa Umma tai tana fitowa waje inda Hajiyan take a tsaye ta dur'kusa har 'kasa tana cewa "ina yini"? A masife Hajiya tace "uban yini dama gaisawa nazo muyi kinga Hauwa ki kiyaye ni ki kama kanki zanci mutuncin ki a gidan nan fa" kai Umma dake dur'kushe ta girgiza tana cewa "kiyi ha'kuri Hajiya Allah ya baki ha'kuri" tsaki Hajiya taja tana juyawa zata bar kofar tace "zakiga nayi ha'kuri bari ya dawo zai zo ya sameni zaki bar gidan nan kwanan nan" mi'kewa Umma tai bayan fitar Hajiya zata shiga d'aki Asabe tai wuff ta fito waje tana dariya ta kalleta tana sakin gud'a "ahayye ayuririiiiiiiii gaskiya naji dad'in wannan al'amarin dama ashe abinda kike 'kullawa kenan asirin ki ya tonu gara da Hajiya ta gane yanzu kowa yasan halinki ashe D'an Yanan da take zuwa da sunan hutu duk 'karya ce asiri kike aikata tayo miki dan ki mallake miji ke kad'ai humm wallahi baki isa ba ni nan da kika ganni ina daidai dake" kallonta Umma tai cike da damuwa tace "bazan biye kiba Allah ya fitar da mai gaskiya a cikin mu nasan tsakani da Allah nake rayuwata a gidan nan ban ta'ba nufar wani da sharri ba ina ro'kon ubangiji ya saka min zargin da kuke min bazan ta'ba yafewa duk wanda ya jefani cikin 'kunci ba Allah ya isa" tana fad'in haka ta shige d'aki zazzafar gud'a Asabe ta sake saki tana cewa "yau ake nanaye a gidan nan ji min munafikar mace kamar ta Allah karki yafe d'in man dama kinji nace miki ina neman yafiyar kine kedai kije ki da borin kunyarki ganin asirin ki ya tonu duk kin bi kin rud'e to wallahi idan ma dani kike nikam nafi 'karfin ki saidai ba'kin ciki ya kashe ki na zame miki ciwon ido na zama 'kashin cikin turmi maganin wadan kare nan gani nan bari d'umamen mayya". Umman na jinta bata sake tanka mata ba sai Zainab data kifa kanta tana ta rusa kuka kallonta Umma tai itama idonta ya cika fal da hawaye tace "Zainab kiyi hakuri dan Allah karki d'orawa kanki hawan jini kisaka a ranki kamar babu abinda ya faru komai yai zafi maganinsa Allah babu wanda yake samun wata d'aukaka face an jarraba shi na sani baka samun farin ciki saika shiga 'kunci duk wanda kika ga ya samu wata rayuwa mai inganci idan kika bincika zakiga yasha matu'kar wahala kamar dai mu shiyasa nake sake fad'a miki kiyi hakuri insha Allahu akwai nasara ga duk wanda ya kasance mai ha'kuri ne kuma duk inda kika samu farin ciki dole yana tare da ba'kin ciki sannan idan kinga kin shiga wani 'kuncin rayuwa akwai sau'ki da jin dad'i a gaba kiyi hakuri ki daina kukan ki goge hawayen ki kinsan wannan kad'an ne daga aikin Hajiya zatai wanda yafi haka to tunda kin sani meyasa zaki 6ata lokacin ki kina kuka"? Kai Zainab ta girgiza tare da d'agowa ta goge hawayen fuskarta muryarta na rawar kuka tace. "Dole na damu Umma dole nayi ba'kin ciki duk gidan nan babu wanda Hajiya takewa haka saike sannan a jikanu ma nice abar zaginta bansan me nayi mata ba ta tsane ni koda ace ni agola ce kika zo gidan nan dani ya kamata ta bani daraja sannan ta d'auke ni matsayin jikarta balle a gidan nan kika haife ni anan na taso kawai dai idan mutum baiyi maka ba shikenan saika tsane shi me nayi mata idan laifi nayi mata ta fad'a min na bata ha'kuri na gyara man amma wadannan matsalolin sunyi min yawa". "Babu abinda ki kai mata sannan ba tsanar ki tai ba kamar yadda kike tunani ni nasan dalili laifi nane ya shafe ki sannan tana ganin kamar nice na hana kiyi aure saboda taga Hadiza Maryam da kuma Rafi'atu Aisha duk sunyi bayan sune sha'anin ki a gidan shiyasa ta d'auki abun da zafi batasan aure nufi ne na ubangiji ba sannan lokaci sai yazo da ayi ina fatan indai hakan zai gyara komai Allah ya kawo miki miji na gari kema kiyi auren nan kowa ya huta" numfashi Zainab ta sau'ke daidai anyi sallama suka amsa wasu 'yan mata biyu ne suka shigo gaida Umma sukai bayan ta amsa Zainab ta mi'ke domin tasan gurin ta suka zo kar6ar d'inki tace "muje ku kar6a Umma bari na dawo" to Umma tace su kuma suka fita d'akinta ta shiga ta d'auko musu tana cewa "saidai ban samu na goge ba sakamakon bana gari jiya na dawo ko zaku bari zuwa jimawa idan sun kawo nefa na goge muku ko zuwa yamma sai kuzo ku kar'ba"? Kai d'aya ta girgiza tana cewa "a'a wallahi barshi kawai zamu goge d'inkin yayi kyau sosai kawai saka mana a leda mu tafi" saka musu tai ta mi'ko musu suka bata sauran kud'in d'inkin ta sukai mata godiya bayan fitarsu ta aje kud'in tana komawa d'akin Umma ganin bata nan yasa ta fahimci maybe tayi kitchen shiyasa ta zauna jiran dawowar ta.................. ZUCIYAR ALIYU CE @YMA DUTSE PAGE 15 Fitowar Shareef kenan yaga Mami a dinning murmushi yayi yana karasawa ta bayan ya sunkuya yayi mata kiss a kumatu yana cewa "good morning mah fatan kin tashi lafiya"? Murmushi Mami tai tana girgiza kai daidai ya mi'ke ya zagayo ta gabanta ya samu kujera kusa da ita ya zauna kallonsa tai tana cewa "lafiya kalou na tashi Shareef yaushe zaka girma ne"? Jinjina kai yayi yana cewa "anya kuwa Mami zan girma"? Baki Mami ta bud'e tana dariya tace "tofa ban gane ba me kake nufi bazaka girman ba kenan" cire Bluetooth din kunnensa yayi yana cewa "gaskiya dai da alama domin koda ace yara na tara har lokacin ban girma ba tunda kuna nan nima ina da parents sannan kune kuka haife ni koda ace gemu na yana jan 'kasa a gurin ku ni yaro ne kallon da zakuyi min kenan koba haka ba"? Kai Mami ta d'aga tana cewa "tabbas maganarka nakan hanya domin har yanzun nan da muke magana nikam dama ban ta'ba ganinka a babba ba ko daidai da rana d'aya". "Yauwa kin gani Mami alamu dai sun nuna ni yaron ne da kuma har nake shirin d'auko miki suruka" zaro ido Mami tai tana kallon sa tace "da gaske Shareef"? "Kwarai Mami da gasken gaske saidai ban fad'a mata ba so nake saina gama wani abu tukuna". "Baka tsoro wani ya riga ka"?. "A'a babu wanda zai riga ni Mami saboda a jikina ina jin cewa wannan yarinyar mata ta ce" kaiii dariya Mami tai tana cewa "to Allah ya tabbatar mana da alkhairi me kake so nayi serving d'inka"? Ta tambaya tana d'agowa ta kalleshi amsa ya bata yana mayar da Bluetooth d'in kunnensa yace "abinda zaki ci Mami shi nake so" "to aini faten wake da bushashshen kifi nasa akai min kai kuma baka so". "Eh yau zanci saka min". Plate ta d'auka ta saka masa ta d'auko spoon ta aje masa daidai kiran Baby ya shigo wayarsa kallon wayar yayi yana d'auke kai dama yasan za'ai haka bazata ta'ba iya fushi dashi ba amma fa shi kam a nasa 6angaren yayi fushi da ita sosai tunda batasan darajar d'an adam zai nuna mata kuskuren ta koda gaba bazata sake makamancin irin haka ba koda ace baya gurin................. "Shareef kiran ka fa ake a waya baka gani bane"? Mami ta tambaye shi tana sake kallon wayar da akai kira karo na uku kai ya jinjina yana katse kiran yace "na gani Mami bana amsa waya idan Ina cin abinci su bari na gama" ok kawai Mami tace itama tana ci gaba da cin abincinta amma dai tsabar naci ba'a daina kiransa ba gudun kar Mami ta sake cewa wani abu yasa ya saka wayar a silent yana jan 'karamin tsaki saboda karta zargi wani abu ji yayi tace. "Na gani fa Shareef kiranka ake amma ka share kodai kiran ba mai muhimmanci bane"? Kaiya d'aga yana kallon sabon kiran daya sake shigowa yace "eh" murmushi Mami tai tana d'agowa ta kalleshi ganin yadda ya had'e rai tasan akwai matsala tsakanin sa da mai kiran shiyasa tace "amma ba mai muhimmanci bane aka dame ka da kira kai da kake da patient ai bai kamata ka ri'ka sharewa ba gashi naga number gurin aikinka ce ba family number ba please ka d'aga dan Allah kaji ko ba lafiya ba" numfashi ya sauke a hankali yana jinjina kai yace. "Mami ki yarda dani lafiya kalou kiran ba mai muhimmanci bane" kad'a kai Mami tai tana cewa "Ok shikenan na yarda" Mami ta fad'a tana d'auke hankalinta daga saitin sa amma tana hankalce jira take a sake kira ta fake shi ta d'auke wayar taji waye yake kiran ko gama shawara batai ba taga hasken secreen d'in wayar tasa tunda ya kashe ringtone d'in wuf tai ta d'auke yana shirin kashewa ta d'aga ji tayi cikin azama ance "hello Shareef Shareef dan Allah ka saurare ni karka kashe mun waya" d'agowa tai tana kallon Shareef wanda yai mugun had'e rai shima ya d'ago yana kallonta ganin irin kallon da take masa yasa yace "karki kiyi zargin komai Mami ba wani abu bane ki rabu da wannan". "Na rabu da ita alama ya nuna baka da gaskiya Shareef tunda gashi tun kafin nayi magana har ka harka ankara"?. "Ba ankara nayi ba Mami na fad'a miki gaskiya ta ne". "Oh na gane" Mami ta fad'a tana sake kallon secreen d'in wayar da akai sabon kira zatai magana yace "ki rabu da ita Mami wannan yarinyar bata da hankali" "na rabu da ita kuma Shareef wace Baby a ina take me zakai mata take ro'kon ka"? "Ki yarda dani Mami babu komai karki kiyi zargin komai tsakani na da ita bani da had'i da ita". "Dama kaji nace ina zargin kane kawai tsarguwa kayi" ta karasa maganar tana mi'ka masa wayar 'kin kar'ba yayi kawai yaci gaba da breakfast d'insa "amshi man" yaji Mami ta fad'a had'e fuska yai yana kar'ba zai aje tace "no kiranta zakai a gabana naji wace ita". "Oh my God Mami karki damu a kanta dan Allah" tsare shi da ido Mami tai tana cewa "saboda me baka so nayi maka tambaya a kanta"? "Saboda bana so kisan wace ita balle a gaba tayi tunanin zuwa gidan nan gurin ki nasan zata iya idan ta samu fuska". "Anya Shareef maganar nan taka akwai 'kamshin gaskiya kuwa"? "Akwai Mami ki yarda dani bata da wani dalili da zaisa ta kirani da safiyar nan" "Meyasa ka yanke hukunci bayan bakasan gaibu ba"?. "Saboda bata da wani dalilin da zaisa ta kirani ne kawai ba komai ba tunda yau ba ranar aiki bace" d'agowa Mami tai tana kallon sa daga baya tai murmushi tana cewa "baka da gaskiya Shareef akwai abinda kake 6oye min haka ne"?. "Babu abinda nake 6oyewa Mami ki yarda dani wallahi kawai 'yar gurin aikin muce ba komai ba had'uwar asibiti rabuwar can ba had'in biri da gada" kai Mami ta jinjina tana cewa "to meyasa take baka hakuri tayi maka wani abu ne"?. "A'a". "Ban yarda ba". "Da gaske nake Mami amma shikenan zan fad'a miki wace ita amma ba yanzu ba saina samu nutsuwa" murmushi Mami tai mai kama da dariya tana girgiza kai tace "zargi na ya tabbata kenan magana ta tana kan hanya ba komai ka samu nutsuwa sosai yadda ya kamata ina jiran ka" ta fad'a tana mayar da hankalinta kan abincin da take ci yayin da Shareef ya mi'ke yana shiga part dinsa yaje toilet yai brush ya fito yana sake fesa turare a jikinsa tare da tsayawa a gaban mirror yana dad'a gyara kansa a ransa yana tunanin meyasa Mami take zarginsa akan Baby kodai ta d'auka budurwarsa ce humm aiko zai sakewa Baby warning kar kuskure yasa ta sake kiransa a waya indai ranar weekend ne bazai yuwu ta jawo masa aiki ba a ri'ka tunanin ya fara soyayya alhalin ba haka bane yasan wuya Mami ta fad'awa Abban sa cewa yana da budurwa yanzun nan zaice yayi aure tunda dama yakai kusan wata biyar da kiransa ya tambaye shi yaushe ne zaiyi aure yace masa ko budurwa baida ita a lokacin Abba yace lallai-lallai ya samo wacce tayi masa yaji yana sonta ya aureta domin zama haka sam bai kamace shiba tunda babu abinda ya nema ya rasa..................... Ringtone d'in wayarsa ne ya katse masa tunanin da yake kallon secreen d'in yayi yaga still Baby ce yanzu ma take kira bai d'aga ba saida ta katse sannan yabi bayan nata kiran tana d'agawa tace "hello Shareef dan Allah ka............ "Baby" taji ya fad'a cikin tsawa wanda ba shiri ta d'auke wayar daga kunnenta tana kallon secreen d'in taga tabbas Shareef ta kira ba wani ba amma shine yake mata irin wannan tsawar d'an tsaki taja tana kallon wayar tata data kawo haske alamar ya katse kiran numfashi ta sauke tare da mi'kewa ta tafi jikin window ta d'aga labulen d'akin tana kallon compound d'in gidan ranta a 'bace yanzu ya zatai tasan kota sake kiransa bazai d'aga ba gashi yau weekend ne mahaifin ta yana gida bazai bari ta fita taje ko'ina ba taya zata had'u da Shareef gaskiya tana so suyi magana ta fahimta yadda ya kamata kar zuciyarta ta kamu da ciwo bayan baisan tana son shi ba gara ta fad'a masa a wuce gurin addu'ar ta dai Allah yasa kar yace a'a domin idan ya'ki amincewa tofa Abban ta yana son aura mata d'an gidan abokinsa ne wanda bata fatan faruwar hakan gashi yau kwanan biyar da dawowa Nigeria duk da tasan bai kammala karatun sa ba amma idan ya samu hutu yana zuwa gida yaga mahaifansa ya koma huuuuhhhhhh ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da sakin labulen ta dawo cikin bedroom d'in cikin rashin makamar abinda ya kamata tayi zama tai a gefen gadon ta tana tagumi can take mi'ke ta soma zaga d'akin zuciyarta cike da tunanuka iri-iri wanda ko kad'an bata da masaniyar ta yadda zata iya 6ullowa lamarin. 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YUSRAH MUSA ABUBAKAR PAGE 16 A 6angaren Shareef kam bayan ya daka mata tsawar bai sake ce mata komai ba saboda yadda yaji 6acin rai yana mamaye zuciyarshi ya tsani mutum mai masifae naci balle Baby da tun ranar data mari Nihal a gabansa yaji ta fice masa a rayuwarsa dan ya tsani yaga ana wulakanta mutum a take ransa zai 6ace shi mutum ne wanda yasan darajar mutane. A 6angaren Zainab kam alhamdulillah kamar yadda Sameer ya saka ta cike form d'in makarantar ta haka ta fara karatun ta cikin nasara da fatan alkhairi saidai ta 6angaren Hajiya taci ba'ka'ken maganganu da wulakanci daga ita harsu Umma saida sukai kuka tsabar irin ba'kin tozarcin da Hajiya tayi musu. Fitowar Bilki kenan daga d'aki ganin kwanukan Umma a kusa da nasu a gurin wanke-wanke yasa taja tsaki tana kallon kofar d'akin Zainab ganin takalman ta yasa tasan tana nan bata tafi school ba bakin kofar d'akin taje tare da cewa. "Zainab Zainab" A lokacin Zainab tana cikin karatu taji Bilki na kiranta dakatawa tayi tana mi'kewa ta karaso ta d'aga labule ganin tazo har kofar d'aki yasa tasan akwai abinda ya kawo ta kallonta tai sosai yadda ta had'e rai take girgiza cikin nutsuwa tace "meya faru"? Buntsura baki Bilki tai tana turo d'aurin kwali gaban goshi tace "kalli wancan kwanuka na tsohuwarki daga yau na saukewa kaina bazan sake mata wanke-wanke ba domin niba baiwar kowacce 'katuwar bace" jin abinda tace yasa Zainab tai murmushi tasan fitina take nema so take ta kula ta, ta zage ta shiyasa tace "idan dan wannan ne karki damu zan wanke mata idan kika gama naku" baki Bilki ta ta'be tana cewa "da dai yafi miki alkhairi sannan magana ta gaba shara ma daga yau bazan sake share dukkan kofar nan ba saboda ni ba jaka bace zan share iya kofar d'akin uwata idan kinga dama kema ki share naku idan baki ga dama ba ki barshi da datti" tana fad'in haka ta juya ta nufi gurin wanke-wanke da kallo Zainab ta bita tana d'an girgiza kai kafin ta saki labulen ta koma cikin d'akinta karasa kai surar da take yi sannan ta rufe al-qur'anin tayi addu'a tare da mi'kewa ta cire hijab d'in jikinta ta fita samun Bilki tayi a gurin tana wanke kwanukan su bata ce mata komai ba itama ta d'auki kujera ta had'a ruwan klin dana d'auraya ta fara wanke nasu ta gama ta d'auka takai kitchen sannan tazo ta saka ruwa ta wanke gurin ta share kofar tasu tas ta wanke ta tasaka tsumma ta goge tayis d'in daidai Umma ta fito ta kalleta cikin jin dad'i tace. "Sannu Zainab Allah ya miki albarka" murmushi Zainab tai daidai ta wanke 'kafarta da hannunta tace "amin Umma nagode" kai Umma ta d'aga tana wucewa ta shiga kitchen domin ranar aikinta ne bin bayanta Zainab tai tana cewa "wanne aikin zan kama miki"? Doya Umma ta nuna mata tana cewa "ki d'auki wu'ka saiki fita waje ki fere mana ita yau da ita za'a karya jiya baban ku ya shigo da ita da dare" kallon doyar kitchen d'in tai da d'an yawanta tasan zatakai kusan dubu goma ko tafi maybe 'yar ribar daya samu ce yayo musu cefane saboda suji dad'i suma tunda taga d'aurin kayan miya kuma ga d'anyan kifi ma a gefe numfashi ta d'auko tana d'auko babbar roba da wu'ka Umma ta d'iba mata iya wacce zasuyi amfani da ita waje ta fita ta zauna akan kujera a kusa da kitchen ta soma aikin fere ta domin yau sai karfe d'aya zataje lecture harta gama tana shirin mi'kewa Umma ta sake mi'ko mata guda d'aya tace a dad'a saboda saura kofafin ma akai musu abinda ka bayar shine rabonka tana cikin gyaran wacce ta mi'ko mata Sameer ya shigo da sallama hangota dayai yasa ya taho inda take yana zuwa ya tsuguna a kusa da ita yana cewa. "Yau kuma doya zamu ci kenan kece zaki dafa yau ba school ne"? Murmushi tai tana girgiza kai tace "a'a akwai amma ba yanzu zan tafi ba sai 'karfe d'aya". "Ok Allah ya kaimu wannan doyar wanne kalar samfurin dafi za'ai mata ne"?. "Nima ban sani ba saidai na tambayi Umma". "A'a basai kin tambaye ta ba kawai ni ban cika son faten doya bane gara sakwara yanzu abinda za'ai tunda sai karfe d'aya kike da school bari kawai na siyo 'kwai kiyi min yamballs" ya fad'a yana mi'kewa ya fita daidai Asabe kuma ta shigo kofar tun daga nesa take zaro ido tana kallon Zainab harta karaso ganin abinda take yasa tace "tofa wannan wanne irin kalar munafirci ne dama jiya an shigo da kayan abinci amma shine ko a sanar dani wato ga bora ko? Humm zai dawo gidan ina nan ina jiransa za'ai bala'i saidai a raba mana girki dan bazai yuwu a ri'ka cuta ta ina kallo ba" ta fad'a tana juyawa ta shiga d'akinta Umma tana cikin kitchen tana jinta batai magana ba balle Zainab da ko rufeta zatai da duka bazata tanka mata ba saboda albarkacin son da Sameer yake mata ko Bilki baya yiwa kulawar da yake mata shiyasa bazata ta'ba iya furtawa Asabe komai ba sai alkhairi. Zainab tana zaune Sameer ya dawo da 'kwai masu yawa har saida ta zaro ido tana kallon sa tace "Yaya Sameer wannan ai yayi yawa ka rage ka mayar da wasu sai ka kar6o mai da kud'in" murmushi yayi yana shima yana kallonta yace "ai ba nawa bane ni kad'ai akwai naki a ciki gudu goma ne nawa sauran na cikin kiret d'in naki ne" da mamaki tace "nawa kuma aini basai ka siyo min ba". "A'a nima ba nine na siya miki ba yanzu abinda za'ai ki d'ibi iya nawa nakin kuma saiki kai d'akinki ki aje kayanki idan kin tashi amfani dashi saiki d'auka" cikin rashin kwancyar hankali ta sake kallon 'kwan kafin ta d'ago ta kalli Sameer tana cewa "waye ya siya min 'kwai"? 'yar dariya Sameer yai yana cewa "ba ruwanki da wannan ke kam kawai kiyi abinda nace kafin Umman mu ta fito ta ganshi kinsan dai halinta idan ba so kike ta dugurguje su ba kowa ya rasa" jin abinda yace yasa Zainab ta mi'ke tana d'auka ta saka a cikin d'akinta amma data fito ba alamar Sameer d'in murhun gawayi ta d'auko ta d'ebi iya doyar da zatai masa yamballs d'in ta dafa ta da gishiri ta shiga kitchen ta fito da turmi ta d'ebo attaruhu albasa da maggi zama tai ta zuba doyar cikin turmin ta daka ta sannan ta d'auko roba mai fad'i ta zuba a ciki ta jajjaga attruhu da albasa ta zuba akan doyar ta kawo kori shima ta saka ta had'e ta gurin d'aya ta d'auko ta fara mulmulawa tana ajewa harta gama amma kuma bai kawo mai ba mi'kewa tai ta shiga d'aki ta d'auki wayarta ta kirashi yace sunje anguwa ne amma ta shiga d'akinsa akwai kud'i a cikin wani littafi ta d'auki yadda zata siyo man aje wayar tayi ta fito ta shiga d'akin nasa ta d'auko ta fito kenan Asabe ma ta fito daga nata d'akin ganin daga inda ta fito yasa ta zuba mata wani uban ihu tana cewa. "Wayyo jama'ar gidan nan ku kawo min d'auki na kama 6arauniya🙊 ta shigar min d'akin d'ana zatai masa sata" da mamaki Zainab ta kalleta amma batai magana ba sai Asabe data aiko mata da wani irin kallo tana cewa "uban me kika shiga yi masa a d'aki"? Kamar Zainab zata shareta sai kuma tace "am cewa yayi nayi masa yamballs ya kawo min 'kwai amma bai kawo mai ba shine na kirashi a waya yace min yaje anguwa ne amma na duba d'akinsa cikin littafi na d'auki kud'in shine yasa na shiga na d'auko ba wani abu bane"? Kai Asabe ta jinjina tana cewa "ko ba yamballs ba? Kai amma Sameer ya ji kunya au nan d'in har yardar dayai miki takai ya fad'a miki gurin ajiyar kud'in sa gaskiya Sameer bansan wanne irin shashashan 'kauye bane ayi mutum ba nutsuwa tsabar rashin sirri wai 'yar kishiya ya d'auki yarda ya baiwa har tasan gurin ajiyar kud'in sa amma ni ban sani ba" tai maganar tana cizon yatsa tare da d'agowa ta kalli Zainab cikin takaici tace "uban me kika tsaya kina kallona da wadannan manyan idon naki wuce ki bani guri makira kenan a haka fuska fal da annuri amma zuciyar tana nan ba'ki 'kirim shiyasa ma kika rasa mijin aure zalunci fal ciki wazai auri masifa ya kai wa mahaifansa" tari da bai kama Zainab ba bataiwa Asabe ba sai wucewa datai ta koma gurin aikinta duk da taji d'aci kalaman Asaben amma ya zatai hijab d'inta ta d'auka da kanta ta fita siyan man. Ayi ha'kuri yau typing d'in ba yawa ina uziri ne. STORY WRITTEN ND EDITING Yusrah Musa Abubakar. ZUCIYAR ALIYU CE. @YUSRAHMS PAGE 17 Asabe kam shiga d'akin Sameer tai tana bala'i tana bincike kamar tayi masa ajiya ganin kud'i kusan dubu ashirin a cikin littafin yasa ta d'ebe tareda d'aga katifarsa ko zata samu wani kud'in tabi duk ta birkice masa d'aki ta wargaza komai ganin iya wannan dubu ashirin d'in ne yasa ta fito daga d'akin batare data gyara masa komai ba ta shige nata d'akin ta bala'i da zage zage da habaici iri-iri an asirce miji da masifa d'an ma baza'a barta dashi ba shima ya juya mata baya. Dawowar Zainab batasan maiya faru ba balle ta shiga ta gyara masa d'aki saida ta gama soyawa ta shiga zata aje masa taga komai a wargaje littafin an yaga wasu fefofin tasan aikin Asabe ne to amma yanzu babu kud'in da yake cikin littafin idan ta gyara d'akin Sameer ya dawo zaice itace ta d'auke idan ta barshi a haka zaice waye ya shiga masa d'aki bayan ita bata da mafita gara ta barshi a hargitsen idan ya shigo ya gani tayi masa bayani d'aukar yamballs d'in tayi ta mayar d'akinta lokacin sha biyu tayi ta dafa ruwa akan sauran garwashin datai suyar ta shiga band'aki tayi wanka ta fito ita ma Umma sannan ta gama sakwarar miyar ma ta sau'ke ta fitowa tayi ta kar6o kwanukan Asabe dana Bilki da Sameer sannan ta dawo ta raba ta sakawa kowa ta fitar dana Hajiya da yake yau Zainab bata shiga ba da safe sun gaisa ba shiyasa yanzu tace tunda tayi wanka ta fito takai mata itama tazo taci kafin karfe d'ayan tayi. Saida ta shirya tsaf sannan ta d'auko hijab ta saka ta kar'ba ta tafi 6angaren Hajiya duk yaran gidan da 'yan mata suna nan sun cika kofarta kamar yadda suka saba dama ita kad'ai ce bata shiga saidai idan gaida ita zatai ko kuma wani uzuri saboda ayyuka sunyi mata yawa ba kamar sauran take ba zataje school zatai aikin gida ga d'inkunan mutane sannan tana koyarwa a islamiyya sufa sauran bai wuce daga school sai islamiyya ba kowace take aiki a cikinsu ba saboda sun d'auki rayuwar 'karya sun saka a gaba sun 'ki su tsaya iya matsayin da Allah ya ajesu. Da sallama ta shiga a lokacin Haulat tana basu labari suna dariya sun cika d'akin da hayaniya ko sallamarta basu jiba sai ha'kura tayi ta shiga tsit kowa yai shiru duk suka zuba mata ido ba wanda ya sake tari zama Zainab tai tana cewa "ina yini Hajiya"? Kamar bazata amsa mata a da'kile tace "lafiya" daga haka bata sake cewa komai ba kuma ko kallon inda Zainab d'in take batai ba shiru itan ma Zainab d'in tayi ranta babu dad'i can tace "ga abinci inji Umma tace a kawo miki" ta fad'a zata mi'ke kenan taji muryar Hajiya tace "tsaya ki tafi da kwanon" tsayawa tai Hajiya dake kallon wani d'an yaro zai kai shekara sha biyu a cikin yaran da suke gurin tace "Khaleel jeka waje idan kaga almajiri ka kira shi" to yace yana mi'kewa ya fita jin abinda Hajiyan tace yasa ran Zainab ya sake 6aci saboda ta fahimci baza taci abincin bane tana tsaye har yaje ya kira almajiri Hajiya ta d'auki kular tace "mi'ka masa ya juye" kar'ba khaleel yayi ya mi'kawa d'an almajirin dake waje ya juye ya mi'ko masa yace Allah ya kar'ba dawowa d'akin khaleel yai yana mi'kawa Hajiya kular kaita girgiza tana nuna Zainab tace. "Ga asararriyar da zaka baiwa nan mi'ka mata kayan tsiyarta ki fad'awa uwarki daga yau karta kuskura ta sake kawo min girkinta bana so bazan ci ba domin niba mayunwaciya bace ina da 'ya'yan da zasu kawo min idan sun girka ba iya Abdullahi ne d'ana ba" jin abinda tace yasa Zainab d'an juyowa ta kalleta idonta ya fara tara ruwa cikin 6acin rai ta kar'bi kular a hannun khaleel ta fita daga d'akin. Baki Haulat ta ta'be tana cewa "wallahi Hajiya Zainab d'in nan haushin da take bani kamar nasa bindiga na harbe ta kullum sai dare yayi kana son ka kwanta ka huta ita kuma sannan ne zata tsiri yin d'inki ta cika mana kunne da 'kara ba kofar mu d'aya ba amma tana mugun matsa min" karaf Bilki tace "to kema da kike wata kofar ta dame ki balle mu humm in Allah ya yarda saina lalata keken nan yadda ko masu gyara baza su iya gyara shi ba" dariya Rasheedat tai tana cewa "nikam ba ruwa na dajin wata 'kara ina can kofar mu Allah yasa bana ji balle gashi yanzu saurayi na ya turo mahaifansa nasan bikina bazai wuce nan da shekara d'aya ba Nima na shiga sahun su Aunty Arabiyyah" jin abinda tace yasa Hajiya cewa "kai kaiton abun da yafi karfinka wai suna ganin yarinyar nan dan masifa sun kasa sakata ta fidda miji 'kannin tama sai aure suke nikam nace Rafi'atu takai Zainab ne a haife"? Cikin gulma Bilki tace "Ina Aunty Rafi'atu zatai Zainab kusan shekara uku ne tsakanin su". Takaici ne ya 'kara kama Hajiya tace "kiji fa kiji fa amma har yanzu tana jangwa6e a gida shekara ashirin da hud'u ba aure". "Ai Hajiya indai kika biya Zainab da mahaifiyar ta ba aure take so tayi ba domin kwanan baya sabon murfin kofa suka baiwa Yaya Sameer kud'i ya siya aka kira wani mutum ya saka mata" Bilki tayi maganar tana dariya saboda ganin Hajiya ta zaro ido bayan 'karya tayi "kikace har murfin kofa aka saka mata"? Kaita d'aga tana cewa "kwarai Hajiya da idona naga wanda ya saka mata sai kallonsa take tana farfara masa ido dan yace yana sonta amma shi ko kallonta baiyi ba harya gama aikinsa ya tafi kyan d'an miciji ne da ita a haka ke kyace 'yar gidan gwamna kyau kamar balarabiya amma gashi wanda zaice yana sonta ma ta rasa". "Ba'kin jini gareta mukam muna dasu kuma sai munyi aure mun barta a gidan nan tunda har gobe bata da tsayayye" Haulat ta fad'a tana cije baki cike da mugunta a masife Hajiya tace "ai Kuma wallahi bata isa ba ko ta'ki ko taso sai tayi aure tabar gidan nan indai bata tsayar da mijin aure ba ni zansa ayi mini cikiyar kowanne irin mutum aka samu dole ta aure shi kuma ba saki saidai idan mutuwa yayi" dariya suka she'ke da ita cikin zolaya Rasheedat tace "ko makaho ne"?. "Ko kuturu ne saita aure shi" sabuwar dariya suka saki Zakiyyah na cewa "amma idan 6arawo ne fa Hajiya nan ya zaki"? Gyara zama Hajiya tai tana cewa "ko maye ne wallahi saita aure shi inyaso ya cinyeta a ranar da akai mata rakiya dan uwarta ni nagaji da wannan masifar jira nake a gama komai na auren Haulat nasa ai min cikiyar mai son 'yar sadaka ya kawo sadaki kawai a d'aura musu aure" shewa sukai suna cewa "sai dake Hajiyan mu Allah yaja zamanin ki" shiru Hajiya tai daga haka bata sake magana ba iya sune suka saka dabar gulmar Zainab d'in suna ta dariya. ZUCIYAR ALIYU CE DEDICATED TO 😭MY LATE FATHER😭 )(MUSA ABUBAKAR GIMBA)( Ina ro'kon Ubangiji ya garfarta maka Allah ya kai haske kabarin ka Allah ya yi maka rahma. IBRAHIM MUSA ABUBAKAR AISHAT MUSA ABUBAKAR ABDULLAH MUSA ABUBAKAR 🤲Ubangiji Allah ya ji'kan ku da rahma Allah ya haskaka kaburburan ku Allah ya sa aljannah ta zamto makoma a gare ku. @YUSRAH DUTSE PAGE 18 Zainab kam data koma bata fad'awa Umma abinda Hajiya tayi ba saboda kar ranta ya 6aci kitchen ta wuce ta ajiye kular ta fito ta shiga d'akinta ta d'auki iya abinda zata d'auka taiwa Umma sallama zata tafi school "Amma Zainab baki ci abinci ba zaki tafi"? Umma ta fad'a tana kallon ta kai ta d'aga ta na cewa. "Saina dawo zanci idan Yaya Sameer ya shigo ki fad'a masa yamballs d'insa yana d'aki na". "Tom Allah ya tsare ubangiji ya dawo dake lafiya" Amin Zainab tace tana fita daga kofar tasu ta tsaya ta saka nikaf d'inta saboda bata ta'ba fita waje fuskarta a bud'e zai wahala mutum yace yasan yadda fuskarta yake saidai idan ya santa lokacin da take karama. Sameer kam gidan su Amirah ya raka Aliyu ya gaisar da Maman ta sun dad'e acan amma har suka taho basu had'u da Amirah ba tana gidan kakanun ta bayan sun dawo Sameer yacewa Aliyu bari yaje gida ya d'auko musu yamballs saboda Aliyu yace yana so yaci irin girkin Zainab shiyasa ma ya'ki cin abinci a gidan su Amirah saboda kar yaji rashin dad'in sa Baisan meya faru ba sai da dare ya shigo gidan a lokacin an kawo nefa yazo saka caji yana bud'e kofar d'akinsa ya shiga yaga yadda yake a hargitse wani irin jada baya yayi yana kallon komai da mamaki ya akai Zainab tayi masa haka meyasa ta 6ata masa d'aki yasan tana da nutsuwa anya hakan zai faru? Sakin labulen d'akin yayi yana juyawa ya koma kofar d'akin Zainab zaiyi magana ta fito kusan karo sukai d'an ja baya yayi yana cewa "Zainab meya faru ne"? Cikin rashin fahimta tace "Yaya Sameer wani abu ne"? Ta tambaya hankalinta a tashe domin ta manta abinda ya faru d'azu "eh wani abu ne zo muje ki gani" ya fad'a yana juyawa ganin ya nufi d'akinsa yasa zuciyarta harbawa wato bai shigo gidan yaga d'akin ba sai yanzu to ita me zatace masa ganin ya tsaya a kofar d'akin yana kallon ta yasa da'kyar ta iya d'aga 'kafarta taje gurin d'age mata labulen yayi yana cewa "meya faru d'azu da nace kizo ki d'auki kud'in da zaki siyo mai"? Ji tayi hankalinta ya sake tashi muryarta na d'an rawa tace. "D'azu bayan kace min na shiga na d'auki kud'i a cikin littafin na d'auka na fito Umma Asabe ta shigo kofar ta ganni shine tace na shiga zanyi maka sata saboda naga baka nan nace Mata kaine kace na shiga na d'auko kud'i daga haka bata cemin komai ba na wuce na fita siyo man bansan abinda ya faru ba Yaya Sameer wallahi ba nice nayi maka haka da d'akin ba" tunda ta fara magana yake kallonta har takai karshe huci ya fitar mai zafi ransa a 6ace ya kalli littafin dake kasa da alama kud'in Asabe ta d'ebe kaiya jinjina yana cewa.. "Shikenan ba matsala jeki" jiki a sanyaye cikin rashin jin dad'i Zainab tace "bari na gyara maka d'akin" shiga yayi yana cewa "a'a karki damu zan gyara jeki" juyawa tai kamar mara lafiya ta koma d'aki shikam bai fito ba saida ya bincika ko'ina ganin babu alamar kud'in gashi har katifa a jingine take an d'agota ana neman kud'in ji yayi sabon 6acin rai yazo masa har wuya fita yayi ya shiga d'akin Asabe tana zaune ita da Bilki suna cin zazzafan tsire wanda yasha kayan had'i humm dama abinda yake zargi kenan kuma gashi tun ba'a je ko'ina ba ya tabbata tsaye yayi a kofar d'akin yana kallon ta yace. "Umma ya akai kika shiga d'aki na kika wargaza min komai nawa"? Jin abinda yace yasa ta zafga masa wata uwar harara tana cewa "uban me zanyi a d'akinka wata uwar ka ajiye dama ni kad'ai ce a kofar da zakai min sharri ga 6arayi can kaje ka tambaye su ko saini saboda raini"? A damuwance Sameer yace "ni bana nufin haka dan girman Allah Umma kud'in da kika d'auka kawai zaki bani domin ba nawa bane" a she'ke Asabe tace "wanne kud'i"?. "Dubu ashirin d'in da kika d'auka a cikin littafi" yana rufe baki ta mi'ke tsaye tana cewa "a cikin uban littafi da yaushe naje na d'auki kud'in ka a d'aki uban me zanyi dashi dama fatara nake"?. "Umma dan Allah ki taimaka ki bani kud'in nan wallahi ba nawa bane kud'in amana ne" a masife Asabe tace "ai ko saidai amanar ta cinye ka amma ni ban d'auki kud'i ba uban waye yace maka na d'auka"? Shiru yayi bai bata amsa ba taci gaba "wato Zainab ce ko saboda d'azu na kamata tana shirin shiga d'akin tayi bincike taga na ganta shine reshe ya juye da mujiya 'yar gadon masharranta bari naje na ci ubanta ko Hauwa bata isa tai min sharri ba balle ita da aka haifeta a gaban idona" tare kofar Sameer yai fuskarta a mugun had'e yace "karki fita daga d'akin nan Umma indai gurin Zainab zakije ki 'kyale na ha'kura kud'i kuma zan biya" wani d'an iskan kallo tayi masa tana cewa "au saboda zanje naci mata mutunci shine ka hana ni amma da itace tazo zata ci min mutunci bazaka hanata ba saboda ka zama sakarai ko"? Har lokacin shiru Sameer yai bai bata amsa ba karshe ya juya ya koma d'akin sa yana barin gurin itama Asabe ta fita da sauri taje kofar d'akin Zainab tana cewa. "Annamimiya fito min nan munafika wacce ta gaji ba'kin hali a gidan ubanki na shiga d'akin Sameer d'azu da yaushe na shigar masa d'aki fito ki fad'a min kona shigo d'akin nayi miki d'an banzan duka wallahi" ta karasa maganar tana d'aga murya sosai wanda yasa Umma fitowa da sauri Sameer ma yayo waje yana cewa. "Wai Umma me kike yi haka ne wannan fa ba girman ki bane taya zaki zo kina aika mata da zagi alhali tana matsayin 'ya a gurin ki". "Uban 'ya take a gurina wannan zan d'auka matsayin 'ya Allah ya suturu bu'kui inji kishiyar 'konanna wallahi Allah ya sauwake kai da Bilki dai dana haife ku na haife ku amma nikam ban haifi Zainab ba ga uwarta nan" ta karasa maganar cikin wula'kanci tana nuna Umma dake tsaye ta kasa magana kai Sameer ya girgiza yana cewa "da nasan abinda wannan tambayar zata jawo wallahi bazan tambayi kud'in nan ba gaskiya Umma ki gyara wannan ba rayuwa bace" yana fad'in haka ya juya ya koma d'aki da harara Asabe ta raka shi tana cewa "wannan ba rayuwa bace dan uwarka mutuwa ce mara mutunci har nice zan fad'i magana ka mayar min ina daidai dakai" juyawa 6angaren Zainab tai tana cewa "ke zo'kal'kalar banza mai had'a husuma masharranciya baki nasara ba saiki sauya tasha banza kawai" kan Umma ta koma tana nunata da yatsa tace "kema na dawo kanki kiwa 'yarki gargad'i karta kuskura ta sake min sharri idan kina bu'katar zaman lafiya a cikin gidan nan mtwwww" taja tsaki tana komawa d'aki. Hawaye ne shar shar suke zuba a fuskar Zainab irin maganganun da Asabe ta fad'a mata suna mata ciwo bata son ace abu yana had'ata da ita amma ina ko bata takale taba ita kuma zata ta6o ta................. Muryar Umma taji ta katse ta "Zainab ke d'in meya had'a ku nifa ban gane komai da take cewa ba a ina kika ganta ta d'auki kud'in"? Kaita girgiza tana goge hawayen fuskarta muryarta a hankali tace "d'azu ne da Yaya Sameer yace nayi masa yamballs ya kawo min 'kwai saiya manta ya tafi anguwa bai siyo farin man dazan soya masa ba shine na kirashi a waya na fad'a masa ni bansan ya tafi wani guri ba a lokacin ne yace na shiga d'akinsa na bud'e littafi akwai kud'i na d'auka na siyo na shiga na d'auko dubu d'aya Umma Asabe ta shigo ta ganni shine tace sata zanyi masa nace a'a kud'i yasa na d'auka zan siyo mai ne a lokacin ma ta zazzage ni daga haka nidai bansan komai ba hijab na d'auka na tafi na siyo man amma lokacin dana gama yamballs d'in na shiga d'akin zan aje masa naga an wargaje d'akin komai dabam shine na fasa aje yamballs d'in a d'akin nakai nawa d'akin na tafi makaranta yanzu kuma saiya kirani yake tambaya ya akai nace masa lafiya 'kalau nabar d'akin amma Umma Asabe ta shigo ta ganni daga haka bance masa komai ba bansan meya faru ba sai ji nayi tana zagina yanzu" numfashi Umma ta sauke tana girgiza kai tace. "Allah ya rufa asiri koma d'aki ai shi Sameer d'in yana da hankali yasan bazaki ta'ba yi masa haka ba karma ki d'orawa kanki damuwa ki 'kyale" Umma tai maganar tana komawa d'aki itama Zainab d'in nata d'akin ta koma shikam Sameer saida gyara d'akinsa tas ya mayar da komai daidai sannan ya fita daga gidan. Duk abinda akai Abban su Zainab bai sani ba daya dawo gida ma Umma bata nuna masa komai ba saboda bazai yuwu ya wuni yana fafutukar nema musu abinda zasu ci ba ya dawo gida dan ya huta kuma ta tada masa hankali ba amma me yana fara cin abinci kenan suna hira da Umma Zainab ta shigo ta gaida shi ta fita sai ganin Asabe sukai ta bamko muku kofa ta shigo ba sallama tana huci da mamaki Umma ta kalleta cike da fargabar Allah yasa ba abun d'azu zata fad'a ba karta taso masa da 6acin rai shi mutum mai sau'kin hali amma idan ka ta'bo shi zakaga tsantsan abinda ake kira da 6acin rai........ "Gaskiya na gaji da wannan na gaji da rashin adalcin da ake min a cikin gidan nan" sukaji ta fad'a da mamaki baba da baisan komai ba yace "akan me kike magana Asabe wanne irin rashin adalci akai miki kuma waye yayi miki"?. "Waye kuwa banda kai tunda kaji na ambaci adalci a gurin wa aka sanshi idan ba mai gida ba". "Ina jinki meya faru"?. "Meye ma bai faru ba taya za'ai jiya kayo cefane baka sanar dashi ba alhali nice uwar gida wannan ba adalci bane" kai baba ya jinjina yana cewa "ba rashin adalci bane Asabe ba abinda kike tunani bane a kitchen na saka kayan nan ba'a d'akin Hauwa ba kowa ranar girkinta ta d'auki abinda ya kamata ta dafa sannan naga jiyan ba girkin ki bane nata ne ke gobe zaki kar'ba shiyasa ban sanar dake ba amma idan kin d'auki hakan a rashin adalci kiyi ha'kuri" ya fad'a yana kokarin mayar da hankalinsa kan cin abincin sa ya sake ji tace. "Gaskiya baka kyautawa ha'kurin me zanyi bayan an gama dani komai baza'ai min na Allah ba ranar girki na saika bani abu mai wahala nayi ta faman shan wuya amma ranar girkin Hauwa da yake ta asirce ka kafi sonta sai abinda tace shi kake yi shiyasa ka siyo doya da kifi da kayan miya da su maggi da komai amma baka fad'a min ba saida na shiga kitchen d'in na gani kai gaskiya ana munafirci a gidan nan" ta fad'a tana dan'karawa Umma harara wacce fuskarta ta nuna alamun 6acin rai musamman ganin datai Abba yayi shiru tasan maybe ya gama 'kulewa ne numfashi ta sauke tana cewa. "Nidai Asabe tsakani da Allah nake zaune dake da zuciya d'aya ban ta'ba ji a raina daidai da rana d'aya na cutar dake kona nufeki da sharri ba sa6anin ke meyasa bazaki zauna kiyi nazari ki fahimce ni ba" hannu Asabe ta d'aga mata tana cewa "ke kinga bazan yi d'in ba badake nake ba ki rufe min baki adalci nazo ayi mun dan haka baza kisa mana baki a ciki ba indai kina da gaskiya saiki 'kyale ni" jin abinda tace yasa Umma jan bakinta tai shiru ya zama suyi maganar ita da Baban. "Magana nake yi ina so zan tafi" Asabe ta fad'a tana mayar da hankalinta kan Baba saboda kar tace da gaske baya yi musu adalci bayan ba haka bane ya d'aure duk da ta 6ata masa rai amma matsayin sa na mai gida kuma xaman lafiya da fahimtar juna yake bu'kata shiyasa ya danne duk abinda yake ji muryarsa a daidai yace "yanzu me kike so ayi miki ki fahimce ni kuma ki fahimci abokiyar zamanki me zakice"? Had'e rai Asabe tai ganin Umma ta d'ago ta kalleta kafin tace "ni bani da abun cewa saidai nace Allah ya isa Allah ya saka min cutar dani da Hauwa take yi domin yanzu ma wannan tambayar da kai min bakaga wata ba'kar harara data sakar min ba kawai na ha'kura da komai na barta da Allah idan munje can ayi masa sakamako a 'kwatar mun hakki na" tana fad'in haka ta juya da sauri ta fita saboda kar Baba yace ta dawo shiru d'akin ya d'auka daga baya Umma ta sauke ajiyar zuciya tana cewa. "Dan Allah kayi ha'kuri" kaiya girgiza batare da yayi wata magana ba ya d'ora cin abincin sa Umma taji dad'in hakan domin yadda ransa ya 6aci ta d'auka bazai ci abincin ba sai kuma taga ya d'ora daga inda ya fara shiyasa taja bakin ta tai shiru tana fatan Allah yasa kar idan ya gama ya sake kiran Asaben kawai a wuce gurin babban farin cikin ta ma shine jin ba tashin hankalin d'azu Asabe ta fad'a ba domin sai yafi 6ata ran Baba idan yaji sharrin da Asaben taiwa Zainab cewa ta shiga d'akin Sameer ta d'auka masa kud'i dubu ashirin. ZUCIYAR ALIYU CE.............. J.W.A @YMÄ YUSRÄH ÇË PAGE 19 Washe gari karfe bakwai Zainab ta gama shirinta zata tafi school bayan ta gaisa da babanta da Umma a lokacin Sameer baya gidan iya tea ta kar'ba a gurin Umma tasha a tsaitsaye ta fita 6angaren Hajiya ta shiga a lokacin ita kad'ai ce ta gaisar da ita duk da bata samu amsuwar arziki ba amma tunda ta saba wannan ba wani abu bane tana fita kofar gate d'in gidansu ta hango Sameer acan nesa wajen gidan su Afifah yana tsaye tare da wani mutum suna magana tsayawa tayi daga inda take bata cigaba da tafiyar ba addu'a take me napep yazo ta shiga kawai basai sun had'u ba amma dai shiru ba wulgu d'an napep saboda lokacin gari ya waye ba sosai suka fito ba har Sameer ya gama magana da mutumi ya taho bata samu ba karasowa inda take yayi yana kallon ta yace. "Yau da wuri zaki tafi makarantar"? Kaita d'aga ta kasa d'agowa ta kalleshi saboda abinda ya faru jiya murya a 'kasa tace "Ina kwana"? "Lafiya kalou nace yau kuna da lecture ta safe ne"? Kaita d'aga tana cewa "eh yanzu bakwai da rabi karfe takwas da rabi zamu shiga lecture d'in". "Ok abinci fa kin karya ne zaki tafi"?. "Eh nasha tea a gurin Umma yanzu". "Tea kuma Zainab aiba abinci bane mezai tare miki"? Shiru tai har lokacin bata d'ago ta kalleshi ba juyawa yayi yana kallon ko'ina ba mutane sosai yaci gaba "gashi masu abun saidawa basu fito ba balle na sai miki wani abu" jin abinda yace yasa ta girgiza kai tana cewa "a'a Yaya Sameer ba komai zan iya bari saina dawo naci abincin ko kuma naje cafeteria" "ok tom ba damuwa amshi wannan" ya fad'a yana mi'ka mata dubu d'aya kamar yadda ya saba kullum tsabar rud'ewa batasan lokacin data d'ago ta kalle shi ba duk da fuskarta da nikaf da sauri ta girgiza masa kai hawaye yana nema taruwa mata a ido tace. "A'a Yaya Sameer bazan kar6a ba jiya kayi asarar kud'i dubu ashirin ta dalili na ka barshi zanje da 'kafa babu nisa idan na fara tafiya kafin takwas da rabin na karasa school d'in" murmushi yayi yana kallon ta yace "karki damu kedai ki kar'ba kawai ai nine na baki kud'in jiya da aka d'auke ba nawa bane" zaro ido tai tana sake kallonsa tace "ba naka bane na waye kenan saika biya shi"? Kaiya jinjina yana cewa "tabbas ajiya aka bani Kinga kuwa ai ban isa naje nace ya 'karo wani kud'in ba wancan an sace" muryarta da alamar kuka tace "kuma kana da dubu ashirin d'in da zaka biya shine ko a cikin kud'in chemist d'inka zaka biya"?. "A'a ki kar'ba yanzu ki tafi karki latti" ya fad'a yana dad'a mi'ka mata dubu d'ayan kai ta girgiza tana cewa "ni bazan kar'ba ba kawai ka barshi" zata wuce yace "Zainab nayi miki tambaya"? Ji tayi gabanta ya fad'i wani yawu ta had'iye da'kyar tace "eh" numfashi Sameer ya fitar yana cewa "yanzu misali ace nine matsayin baban mu dan kud'i na ya 6ata idan na d'auka na baki baza ki kar'ba ba me ya sa? Kodan saboda bani da wadatar dazan baki ko kuma yaya"? Kaita girgiza tana cewa "Yaya Sameer dan Allah ka fahimce ni......... Katse ta yayi "na fahimce ki sosai fiye da yadda kike tunani amma saikin kar'bi wannan kud'in bana so idan na baki abu mu tsaya kina ja in ja sakamakon yanzu da wani ya fito daga gidan ya gani sai aje a fad'awa Umman mu ina shiga ta hauni da fad'a haka kike so"? Kaita girgiza masa "idan kina so na yarda amshi ki tafi" ya fad'a yana mi'ka mata hannu biyu ta saka ta kar'ba ba don ranta yaso ba tace "na gode" "ba matsala jeki sai kin dawo" wucewa tayi a sanyaye taci gaba da tafiya yana tsaye yana kallonta ta wuce kofar gidan su Aliyu kenan ya fito amma duk da haka saida ya ganeta a tafiyarta yasan school zata tafi hango Sameer yayi yana tsaye a inda sukai magana yanzu shima Sameer d'in ya ganoshi shiyasa ya dawo su gaisa. "Sameer ina Zainab zata tafi yanzu yau lecture safe take dashi"?. "Eh tace takwas da rabi zasu shiga" kallon agogon dake d'aure a hannunsa Aliyu yayi yaga takwas d'in ta cika harda mintuna kafin ya kallo inda Zainab d'in tabi yace "kafin taje school fa lokaci ya fita bari na tura driver ya kaita" ya fad'a yana juyawa cikin taku da sauri yaje yayi umarni a kaita yayiwa driver kwatancen irin kayan da ta kasa. Zainab tana cikin tafiya taga mota ta parking a kusa da ita kamar zata buge ta da sauri ta matsa gefe kad'an tana fad'in "Subhanallahi" sauke glass driver yayi yana cewa "ranki ya dad'e ki shigo na kaiki school d'in" wani irin zaro ido waje Zainab tai tana kallon sa da mamaki tace "na shigo ka kaini school waye kai"?. "Ranki ya dad'e babu bu'katar hakan wanda ya aiko ni yace karna fad'i sunan sa" jin abinda yace yasa Zainab sake 'kare masa kallo tana cewa "na gode ina da kud'in dazan hau napep" tana fad'in haka ta wuce taci gaba da tafiya da sauri driver ya fito da d'an gudu yabi bayanta daidai ta tsayar da d'an adaidaita yace "ranki ya dad'e dan Allah kizo na kaiki karki jawo min fushin uban gidana" kamar bazatai magana ba sai kuma tace "na gode" daga haka ta shiga napep mai napep yana shirin tayarwa cikin azama driver yace "malam d'an tsaya kinga Hajiya dan Allah ki fito daga napep d'in nan muje ga mota can na kaiki" kai Zainab ta girgiza gabadaya lamarin driver ya d'aga mata hankali domin harta fara zargi a ranta kodai wani ne ya aiko shi ayi kidnapping d'inta.................... "Hajiya ki fito muje" taji saukar muryar driver ya katse mata tunani a firgice tacewa mai napep "dan Allah rabu dashi mu tafi bansan shiba" jin haka yasa mai napep kallon driver da damuwa da bayyana 'karara a fuskarsa kamar zaiyi magana sai kuma yaga ba abinda ya shafe shi bane karya jawowa kansa bala'i tunda baisan waye shi ba sannan da ganin motar da yazo da ita kaima kasan ba motar 'kananun mutane bace fuuuu yaja napep d'insa sukai gaba yayin da driver yayi tsaye a gurin kamar ya fasa ihu karshe ganin ba yadda ya iya saboda ya nemawa kansa mafita saiya koma mota yad'an jinkirta kamar misalin yaje ya dawo sannan ya tada motar ya bar gurin kuma koda ya koma bai fad'awa Aliyu cewa ba shine ya kaita ba. Zainab kam da taje school ma kasa nutsuwa tayi ta kalli nan ta kalli can da'kyar ta tsaya tayi karatu yadda ya kamata lokacin da akai break kiran Sameer ya shigo wayarta tana d'agawa yace ta fito wajen aje motocin school d'insu yazo jin haka yasa ta mi'ke ta tafi wajen a tsaye ta same shi ri'ke da cooler a hannunsa da mamaki tace "Yaya Sameer amma dai ba abinci ka kawo min ba"? Murmushi yayi yana kallon ta yace "abinci ne mana kin fita gida baki karya ba ai dole na kawo miki indai ba so nake ki kamu da ulcer ba kar'bi ki koma cikin school ni tafiya zanyi" ya mi'ko mata kar'ba tayi cikin jin dad'in nuna kulawarsa gareta tace "na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" "Amin karki damu kin fi 'karfin komai yaushe za ku tashi"?. "Nan da awa hud'u ne". "Ok ba damuwa jeki sai kin dawo" "To Yaya Sameer na gode" ta fad'a tana juyawa saida yaga 'kulewar ta sannan shima ya koma cikin motar da suka zo duk abinda suke Aliyu yana zaune a cikin mota yana kallon su wata iriyar nutsuwa da farin ciki yana yawo a zuciyarshi ya rasa wanne irin so ne yake yiwa Zainab wani lokaci idan abun ya juyo masa ji yake kamar ya mutu a kanta kamar zaiyi hauka ya matsu yaga ta zama mallakin sa.................. "Aliyu muje ko" Sameer ya fad'a bayan ya shigo motar sauke numfashi Aliyu yayi yana kallon Sameer yace "Sameer dan Allah ka fad'a min wace Zainab"? Da alamar tambaya Sameer yace "kamar ya"? Sabon numfashi Aliyu ya sake fitarwa yana tada mota suka fita daga school d'in a hanya yace "ina nufin wace ita gani nake kamar tafi kowa ita d'in tamkar wani babban ginshi'kin abu ce wacce idan babu ita wannan abun bazai amfanu ba" ya fad'a ya juyowa ya kalli 6angaren da Sameer yake ya zuba masa ido ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba "Sameer Zainab zuciya tace Zainab rayuwa tace Zainab farin ciki nace Zainab abar nema nace sonta ya riga ya zama sinadarin dake sarrafa rayuwa ta dukkan zuciyata tata ce bazan iya saka kowacce mace a raina ba idan ba ita ba ina sonta da dukkan zuciyata ina tsoron rasa ta dan girman Allah Sameer ka taimake ni karka bari wani ya shiga rayuwar Zainab idan hakan ta faru zai zama sanadiyar rayuwa ta ina fatan zakai min wannan alfarmar"? Murmushi Sameer yayi yana jinjina kai ransa fari tas yace "insha Allahu Aliyu kamar yadda kake dakon 'kaunar Zainab kake sonta wata rana itama zata tsinci kanta kamar yadda kake ji nima ina tayaka da addu'ar ta zama abokiyar rayuwarka bazan ta'ba bari wani ya shiga cikin rayuwarta ba saidai idan ban sani ba ka kwantar da hankalinka". "Shikenan Sameer na gode zuwa karfe biyar na yamma zan koma gurin aiki shiyasa na sake tunatar dakai ka kula min da ita". "Insha Allahu Aliyu zanyi hakan zanyi iya bakin kokari na" ya fad'a daidai sun karasa kofar gate d'in gidansu Aliyu yai horn masu tsaron kofar suka bud'e ya shiga parking space ya tsaida motar tare suka fito shi da Sameer ta wata kofa ya bud'e suka shiga part d'insa tare domin ya sake bashi amanar kula da Zainab d'in. ZUCIYAR ALIYU CE YUSRAH MUSA 08160983083 @YMA DUTSE JIGAWA PAGE 20 Sai wajen karfe biyar Zainab ta dawo gida da yake dama ranar ba islamiyya tana aje jakarta ta fita ta d'ebi ruwa tayi wanka bayan ta fito ta shirya ta d'auki cooler ta shiga d'akin Umma a lokacin tana zaune tana waya da babarta Kaka A'i kar'bar wayar Zainab tayi suka gaisa bayan sun gama wayar ta mi'kawa Umma itama suka karasa sannan ta aje wayar a gefe tana kallonta tace "har kinyi wanka kin dad'e da dawowa ne"? Gyara zama Zainab tai tana cewa "a'a yanzu na shigo kawai dai zafi nake ji shiyasa na fara yin wankan". "Ya karatun fatan kina lura ko"?. "Sosai Umma ai bana wasa" "Masha Allah naji dad'i kije kitchen ki d'auko plate ga abinci a cikin cooler nan kizo kici dama yau abincin da kike so ne shinkafa da wake" girgiza kai Zainab tai tana mi'ko mata cooler data dawo da ita daga school tace "na 'koshi saidai zuwa dare kinga abincin da Yaya Sameer yakai min ma ban gama cinye shi ba" da mamaki Umma tace "Sameer yakai miki abinci to wannan cooler ta waye"?. "Oh ba ta nan gidan bace"? Zainab ta tambaya tana 'karewa cooler kallo amsa Umma ta bata "eh ba tanan bace kalli ki gani man ina muke da kuloli masu tsada irin wadannan saidai a wanke masa idan ya shigo a bashi watakil a gurin masu saida abinci ya siya miki" kai Zainab ta d'aga tana cewa "eh inaga hakan ne amma da sauran abinci fa a ciki" bud'ewa Umma tai taga had'add'an girki na gidan masu akwai zubawa abincin ido tai can ta d'ago ta kalli Zainab tana cewa "anya wannan a gurin masu saida abinci ya siya gaskiya bana jin hakan saidai idan a restaurant ko kuma hotel yaje ya siya baiyi kama da abincin shago ko gurin masu saidawa ba" murmushi Umma tai tana d'agowa ta kalle ta tana cewa. "Ikon Allah kenan soyayya gamon jini gashi tsakanin ki da Sameer kamar uwa d'aya ce ta haife ku wasu 'yan uban kuwa basu da buri sai ganin ka fito rana ka tozarta amma banda irin su Sameer" jin abinda tace yasa itama Zainab d'in tayi murmushi batare da tayi magana ba ta sake gyara zamanta tana kallon fuskar wayarta da message ya shiga bud'ewa tayi domin ta duba tare da mi'kewa ta fita ta koma nata d'akin. Sakamakon yau Monday da wuri Shareef ya shirya dan ya fita hospital gudun makara a lokacin daya fito daga part d'insa ko Mami bata fito ba sai iya masu aiki su biyu suna gyare-gyare a parlor wucewa yayi ya fita zuwa harabar gidan ya bud'e motarsa ya zuba takardun daya fito dasu a hannunsa kafin ya rufe ya sake komawa gidan daidai Mami ta fito ya shiga 'kare masa kallo tayi taga ya shirya tsaf yasha farar rigar likitoci kallon agogon parlon tayi tana sake kallonsa murmushi yayi yana cewa "good morning Mami na" kaita d'aga da alamar tambaya tace "amma dai ba hospital zaka tafi tun daga yanzu ba"? "Eh saboda gudun makara yasa na fita da wuri". "Ok abinci fa haka zaka tafi ba kayi breakfast ba"?. "Eh Mami zanyi acan". "Acan gurin wa"? Had'e hannuwansa yai yana cewa "please Mami ina da gaskiya" baki ta bud'e da mamaki tana cewa "tofa Shareef ban gane kana da gaskiya ba dama kaji nace 'karya kake kawai nace a gurin wa zakai break d'in ne"?. "Ina da abokai da yawa a hospital d'in". "Indai haka ne ka bari yanzun nan ko 'karamin abu ne mara nauyi na dafa maka kaci kafin ka tafi". "A'a Mami kawai ki barshi saina dawo". "Meyasa to bazaka tafi dashi ba"? "Babu komai dalili na mai 'karfi ne bana son 6acin rai a wancan ranar da kika had'a min basket na tafi dashi matsala ya zame min shiyasa yau bazan je dashi ba". "Matsalar me ya zame maka"?. "Humm kawai basai na fad'a ba na tafi saina dawo" ya fad'a yana shirin juyawa ya fita ri'ko hannunsa Mami tai tana girgiza kai tace "Shareef tsaya min ina zuwa" sakin hannun nasa tayi tana wucewa ta nufi kofar da zai kaita kitchen ta shiga kallon matar da take aikin tayi tana cewa "Laraba kin had'a wani abu ne"? Cikin girmamawa ta d'an risina tana cewa "ina kwana"?. "Lafiya kalou me kika dafa"?. "Yanzu na fara aiki Irish kad'ai na soya da 'kwai sai yanzu zan fara aikin" wata 'karamar cooler Mami ta d'auko tana cewa "ok sakawa Shareef anan zai fita hospital" kar6a Laraba tayi tana zubawa kamar rabin cooler tasa murfin ta rufe tare da mi'ko mata amsa Mami tai ta fita samun Shareef tayi zaune akan kujera a cikin parlon ya d'ora 'kafa d'aya kan d'aya mi'ka masa tai tana cewa "Allah ya tsare saika dawo" mi'kewa yai yana bud'e hannu ya rungumeta yana d'an lumshe ido fuskarsa da murmushi uwa kenan mahaifiya tafi 'karfin komai ba abun wasa bace duk yadda yaso ta barshi ya tafi ta'ki saboda bata so ya zauna da yunwa alhali ya mallaki hankalin kansa d'agowa yayi har lokacin fuskarsa da murmushin ya kalleta yana d'ago hannunta ya bata kiss yana cewa. "Na gode Mami babu kamar ki duk duniyar nan kinfi kowa ina son ki Mami na" ya karasa maganar yana sake rungume ta kansa Mami ta shafa tana cewa "karka damu Shareef kai d'ana ne nagari wanda za'ai alfahari dashi jeka tafi Allah ya tsare min kai" "Amin Mami" ya fad'a yana kar6ar cooler ya juya ya fita ya nufi motarsa ya bud'e kawai ya shiga yana aje cooler a d'ayar kujerar ta kusa da driver kafin ya kunna motar ya nufi gate mai gadi ya bud'e masa ya fita daga gidan. A shirye Afifah ta sau'ko daga stairs tana waya ta karaso gurin su Momy dake dinning suna breakfast zama tayi tana cigaba da wayarta harta gama bayan ta aje ta d'auko karamin kofi ta had'a tea ta fara sha tana dariya kai Afif ya girgiza yana cewa "wasu lokutan ina jin mamaki idan naga ke kad'ai kina dariya meyasa"? Kallonsa Afifah tai har lokacin bata daina dariyar ba tace "wallahi Amirah ce ta ban dariyar ba kowa ba wai akan ta tambaye Aliyu fa nace mata ai ya koma bakaji wani uban ihu data sakar min a kunne ba kamar zata fasa min kai haka ta hau salati wai kuma bayan ta dawo daidai tace min kodai da wasa nake mata nace mata a'a da gaske nake ya tafi shine kawai naji ta kama kuka wai ta rasa me yake damunsa yanzu tsakanin su ba amana tunda har zai iya komawa bai sanar da ita ba kuma ko a waya bai kirata ya fad'a mata ba tuna hakan yasa nake dariya ba komai ba" baki Fati ta ta'be batai magana ba Elham ma dai batace komai ba balle Asma'u da babu ruwanta idan suna magana. "Da kyau ya kyauta irin wadannan 'yan matan da basu san komai ba saidai su saka maka headache meye amfanin dan zakai tafiya saika fad'a musu amfanin me hakan zaiyi mata"? Afif ya fad'a yana d'aukar tissue ya goge bakinsa tare da mi'kewa yana d'aukar key d'in motarsa da glass d'insa dake aje akan dinning d'in yana shirin fita Afifah ta mi'ke tana cewa "please bro dan Allah muje kayi drooping d'ina a school saika wuce company kaga banyi breakfast ba a hanya saika siya min wani abu mai d'an dad'i-dad'i kaji" jin abinda tace yasa ya kalleta yana cewa "sannu uwar zilamammu waye zai siya min abun dad'in amma dai ba dani kike ba"? Kai ta d'aga tana cewa "dakai nake man waye nake dashi bayan kai"? Juyawa yayi zai fita yace "gara ma ki tsaya kiyi breakfast d'inki a gida kisa driver ya kaiki school nikam ba zanyi miki abinda kike so ba idan kika biyoni zakiyi wunin yunwa" ganin zai fice ya bud'e kofar parlor yasa Afifah d'aukar handbag d'inta tana bin bayansa tace "a'a da wasa kake yasin saika kaini kuma saika siya min abunda zan karya" tana fita Momy ta kalli su Elham tana cewa. "Ku baza ku bishi yayi dropping d'in naku ba in yaso lokacin tashi driver ya d'auko ku"? Kai Fati ta girgiza tana cewa "a'a gara mubi a huce driver ya kaimu hankalin mu kwance haka kawai zamuje muce ya kaimu shima Yaya Afif halin Yaya boss ne dashi abu kad'an yace anyi masa laifi ku karasa kawai mu tashi muje a kaimu" jinjina kai Elham tayi tana cewa "gaskiya ne Fati wannan haka yake mun riga munsan halin bosawan namu kinga gara mu kama kanmu tun kafin su kama mana ko"? "Haka ne wallahi tashi mu tafi kar lokaci ya fita" mi'kewa sukai a tare Asma'u da yake ita primary take yi Momy ta had'a mata basket d'inta na abinci ta tafi dashi a mota d'aya ake kaisu idan anyi dropping d'in Husnah sai a wuce a kaisu. HOSPITAL wata mace ce ta fito da sauri tana kokarin shiga wani d'aki a cikin asibitin Baby dake tsaye tana hangen ta inda zata ga Shareef amma shiru d'an tsaki taja tana kallon agogon hannunta tasan dai yanxu duk tsiya ya baro gida to a ina ya tsaya? Ya tambayi zuciyarta tare da cizon yatsa daidai wannan matar tazo zata wuce ganin inda zata shiga yasa Baby cewa. "Baki ji ba" dakatawa tayi tana juyowa tace "na'am dani kike"?. "Eh dake nake amma dai ba wannan d'akin zaki shiga ba ko"? Kaita d'aga tana nuna mata ruwan faron dake hannunta tace "nan zan shiga yarinya tace ba lafiya kuma tana ta kiran zata sha ruwa shine zan shiga na kai mata" yatsa Baby ta d'aga mata tana girgizawa tace "ba yanzu ba koma inda kika fito yau manyan likitoci suna zagaya patients ne" kallonta matar tai cike da tashin hankali tace. "Bakinta a bud'e yake kuma ya bushe saboda ta bakin take numfashi dan Allah ki barni ina bata zan fito" wani d'an iskan kallo Baby tai tana cewa "baki ji abinda nace miki bane ki koma inda kika fito nan da awa d'aya idan sun gama saiki dawo" tsananin mamaki ne ya kama matar har batasan lokacin da tace "anya kina da imani kuwa"? Wani irin zaro ido Baby tai tana nuna kanta tace "ni kike kira mara imani saboda na hanaki shiga? Shiru matar tai ta zuba mata ido kaita jinjina tana sake ri'ke murfin kofar tace. "Bazaki shiga ba saiki bari mai imani idan yazo ya barki ki shiga amma badai niba" jin abinda tace kuma ga halin da yarinyar tata take yasa ta sake kwantar da murya tace "dan Allah 'yata ki barni nakai mata wallahi rashin bata ruwa yana da babbar matsala kuma doctor ne ya fad'a min haka". "Wallahi bazaki shiga b................. Bata 'karasa ba taji anja kofar an bud'e 'kiiiiiii wanda ita da take jiki a jingine tai baya luuuu zata fad'i da sauri matar ta ri'ko hannunta tana dawo da ita ta tsayar ta numfashi Baby ta sauke yayin da doctor daya bud'e kofar ya fito ko inda Babyn take bai kalla ba ya wuce a abun sa sosai ran baby ya 6aci musamman da taga Ammar ne abokin Shareef tasan za'ai haka gabadaya hospital d'in nan su biyun nan sune 'yan jin kai wanda baka isa su tsaya su saurare ka ba 'kak'karfan tsaki taja tana d'aukar handbag d'inta data fad'i gefe matar dake tsaye a gabanta ta kalleta tana cewa. "Kin gani ko shiyasa a rayuwa ake so ka kyautata bakasan wanda kaima zai taimake ka ba gashi ina tsaye ina ta neman alfarma a wajenki kin 'ki yi min amma gashi wani yazo yayi silar fad'uwarki ni kuma na taimaka miki ko ta haka ya kamata ki d'auki darasi ki daina wula'kanci d'an Adam ba abun wula'kantawa bane kinji"? Maimakon Baby ta d'auki maganar da matar ta fad'a mata sai wani banzan kallo data watsa mata tana cewa. "Dama nace ki taimake nine mai yasa baki barni na fad'in ba taimakon ki bai 'kareni da komai ba sai takaici kar kisa a ranki naji dad'i balle kiyi tunanin zan gode miki mtwwwe taja mata tsaki" wuce tabar gurin tana masifa ji take kamar ta rufe matar da duka da kallo matar ta bita tana jinjina kai lallai ta dad'e bata ta'ba ganin mara tarbiyya irin Baby ba koda ace gidansu ba manya bai kamata ta aikata abinda ta aikata mata ba itama wucewa tai ta shiga ta baiwar 'yar tata ruwa duk da barci ya d'auke tama tun tana kiran ruwan shiyasa ta tasheta ta bata. Batun baby kam tana barin gurin kanta tsaye office d'in Shareef ta wuce harta rike handle d'in zata murd'a sai kuma ta tuna yayi mata warning kwanan baya cewa karta kuskura ta sake shiga masa office tsayawa tayi tana juya bayanta can take hango shi sun gitta su uku tare da wannan abokin nasa dayai silar ta kusa fad'uwa yanzu da kuma wata bururwa mai glass da takarda a hannunta da sauri tabi bayansu harda d'an gudunta amma bata gansu ba tsaye tayi tana kallon gabas da yamma ko zata hangon su saidai babu alamarsu kaita jinjina tana juyawa ta koma kofar office d'in nasa ta tsaya tasan duk tsiya nan da a tashi ai zai dawo tana so ta bashi ha'kuri ne akan abinda ya faru kwanan baya gashi shi kuma sai yawo yake mata da hankali. Haka ta wuni batai aikin daya kawota asibitin ba har aka tashi sai a lokacin taga Shareef ya rufo office d'insa ya fito numfashi ta sauke da sauri ta karasa tana cewa "Shareef dan Allah ka tsaya muyi magana" ko kulata baiyi ba har yaje gurin da motarsa take ya bud'e ya shiga ganin datai yana shirin rufewa ta ri'ke murfin motar tana girgiza masa kai tace "haba dan Allah Shareef ya kamata ka saurare ni man" kamar bazai magana sai kuma yace "kina da abinda zaki fad'a min"?. "Sosai ma nice nake da abun fad'a dan Allah Shareef kayi ha'kuri abinda ya faru kwanaki ka yafe ni nasan na aikata kuskure amma nayi maka alkawari insha Allahu bazan sake makamancin irin haka ba har abada fatan zaka yafe min"? Shiru yayi yana ri'ke da sityarin motar kusan mintuna biyu ya d'auka har ta fitar da rai akan zaice wani abu sai kuma taji yace. "Ok" yana fad'in haka yaja murfin motar ya rufe ya tada yabar gurin kamar Baby ta d'ora hannu aka tayi ta rusa kuka haka taji wani irin ba'kin ciki ya rufe ta me yake nufi da cewa ok anya Shareef ba so yake yaga gawarta ba ta sani tana matu'kar son sa tana so ta aureshi amma ya kasa tsaya ya fahimci irin halin da zuciyarta ta samu kanta a ciki saboda shi kawai akan 'karamin abu ya d'auke mata wuta data san haka abinda taiwa Nihal zai zama to da ta rabu da ita a wancan ranar ko kallonta bazata yi ba amma ba wanda yasan mezai faru a gaba zata zauna tayi nasari akan yadda zata shawo kansa tunda tana sonsa haka zata yi ha'kuri da duk abinda yayi mata kodan ta samu damar shiga jikinsa ta nuna masa manufarta a kansa huci mai zafi ta fitar tana kallon zanen tayun motarsa kafin ta juya ita ma ta nufi tata motar ta shiga tabar asibitin amma ta saka a ranta saita binciko gidan su gara tasan komai nasa idan ya'ki ha'kuri ya yafe mata saita koma 6angaren mahaifiyar sa duk tsiya idan yaga tana kyautata mata tun kafin ya aureta zai kamu da sonta.mm........................ YUSRAH MUSA ABUBAKAR ZUCIYAR ALIYU CE............. @DUTSE JIGAWA PAGE 21 Karfe takwas da rabi Zainab tana d'akinta tana d'inki Bilki ta banko kofa ta shigo ba sallama tana zuwa ta ri'ke kan keken tana cewa "gaskiya bazai yuwu ba haba wacce irin masifa ce wannan da safe baki barmu munji dad'i ba da rana baki barmu munji dad'i ba da daren ma muna so muyi barci dan jaraba bazaki barmu mu huta ba kamar a kanki aka fara neman kud'i to gaskiya bazai ta'ba sa6uwa ba wallahi dole kisan yadda zakiyi" ta karasa maganar tana sake ri'ke kan keken sosai harda jijjiga kallonta sosai Zainab keyi cike da mamakin ta tace. "Bilkisu sake min kan keke" a masife Bilki ta sake ri'kewa tana cewa "bazan sake ba wallahi bazan sake ba tun karfe bakwai nake so nayi barci amma dan mugunta 'karar wannan tsinannan keken ya hana ni yanzu kuma nayi magana harda wani na sake miki ban saki d'in ba ki 'kwace daga hannuna" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa ranta a 6ace ta kama hannun Bilki ta 6an6are daga kan keken nata sannan ta tattarata ta had'ata waje ta tura kofar d'akin tasa sakata ta ciki ta koma taci gaba da d'inkin ta. Bilki kam ganin abinda tai mata yasa bayan ta mi'ke daga fad'uwar datai ta kad'e jikinta komawa kofar d'akin tayi tana dannawa jin ta saka masa sakata ta ciki yasa tace "idan kin cika ke isashshiya ce kuma kin haifu a cikin uwarki ki bud'e min kofar nan na shigo wallahi saina 6a66alla keken nan" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa ta bud'e kofar tana kallon ta tace. "Na isa harna wuce inda kike zato na dan Allah Bilki indai kin haifu 'yar halak ce ki ta'ba min keken nan yau saidai ki kwana da kumburarran jiki wallahi saina miki d'an iskan duka a gurin nan" baki Bilki ta ta'be tana cewa "wallahi saina ta'ba ki dake ni ki daki masifa duk yadda kike jin rashin mutunci nawa ya dame naki ya shanye ba'ayi budurwar da nake tsoro ba kaf gidan nan ba babu 'yar iskan data isa na raga mata wallahi" murmushi Zainab tai tana jinjina kai tace. "Ai shiyasa nace ga keken nan idan kin isa ki ta'ba tunda bakya tsoron kowa yau zan nuna miki kalata" tsaki Bilki taja tana juyawa ta fita daga d'akin tana cewa "a tari gaba gamon mu dake bazai Miki kyau ba yau dai kinci sa'a barci🤣 nake ji amma badan haka ba wallahi saina nuna miki niba kanwar lasa bace" d'an karamin tsaki Zainab tayi tana komawa kan kekenta taci gaba da d'inki harta had'a rigar ta d'auko skirt d'in shima ta fara had'awa Sameer yayi sallama yana tsayawa daga kofar d'akinta yace. "Taso ki kar'ba Zainab zan wuce d'aki nane" mi'kewa tai tana zuwa kofar d'akin inda yake tace "barka da dare Yaya Sameer" kaiya d'aga yana d'auko kayan dake wata babbar leda ya mi'ka mata sannan ya d'auko kwalin indomie itama ya bata da mamaki tabi kayan da kallo kafin ta d'ago ta kalleshi tana cewa. "Yaya Sameer wannan fa"?. "Sa'kon kine" da sabon mamaki tace "sa'ko na kuma"?. "Eh". "To amma waye ya bani"?. "A'a kiyi godiya kawai Zainab amma karki nemi sanin wanda ya baki yanzu saboda tsaro ri'ke wannan" kallon hannun nasa tayi taga kud'i yakai wajen dubu ashirin haka ko talati bata kar6a ba ta girgiza kai tana cewa "Yaya Sameer kar kasa na kasa barci man wadannan abubuwan daga ina"? Murmushi yayi yana mayar da kud'in cikin aljihunsa yace . "Ok tom bari na aje miki kud'in a gurin na idan kin tashi bu'kata saiki fad'a min na baki wadannan kayan da kike gani wani bawan Allah ne ya umarce ni dana siya na kawo miki kyauta" cikin sabon rud'u Zainab tace "wani bawan Allah amma meye sunan sa"? Ta tambaya tana 'kure Sameer da kallo duk tunanin ta ko Yaa sayyadi ne ya bayar a bata amma kuma zuciyarta bata amince shi d'in bane.............. Ji tayi Sameer yace "karki damu ki kwantar da hankalinki zan fad'a miki sunan sa amma ba yau ba" yana fad'in haka taga ya wuce zuwa d'akin sa shiru tayi zuciyarta na harbawa cike da tsananin fargaba da'kyar ta iya d'aukar kayan jiki a sanyaye ta shiga dasu d'aki ta aje kwalin sannan ta zauna ta fara fito da kayan cikin ledar takalmi ne da handbag da kuma hijab sai nikaf guda biyu da sar'ka numfashi ta fitar tana sake bin kayan da kallo kafin ta d'auko d'ayar ledar ita kuma kayan kwalliya ne a ciki had'asu tayi guri d'aya ta d'auke tasa cikin wardrobe d'inta kasa komawa taci gaba da d'inkin tayi duk tunani yabi ya dama mata lissafi karshe fita tayi ta d'auki buta tayi alwala kawai tazo ta shimfid'a sallaya ta fara nafila tun lokacin da take yin bai 'karasa ba. Washe gari da sassafe bayan ta gama karatun al-qur'ani tayi azkar tashi tayi ta karasa skirt d'in da bata gama ba a lokacin da nefa na d'auki iron ta jona ta goge kayan ta saka a leda d'auka tayi ta fita d'akin Umma ta aje saboda mai su zuwa jimawa zata zo ta kar6a ita kuma makaranta zata tafi bayan ta aje kayan lokacin Umma tana karatu itama shiyasa bata gaida ita ba fitowa waje tayi ta shiga d'akin Abban su ta gaida shi taje kofar d'akin Asabe ma ta gaida ita duk da ba koda yaushe take amsawa ba wani lokacin kuma ta amma mata 'kasa-'kasa tsintsiya ta d'auka ta share kofar tas sannan ta had'a kwanuka ta wanke lokacin gari ya waye rana ta fito d'akin Umma ta koma ta gaida ita sannan ta fito ta zuba gawayi a mangal ta saka 'kyallen da take d'inki ta hura wuta sannan ta koma d'aki kafin ya kama. Fitowar Bilki ganin wani ya kunna wuta duk da tasan bazai wuce Zainab ko Ummanta ba amma tsabar neman rigima saita shiga kitchen ta d'auko yar tukunya ta cikata da ruwa haka kawai ba wani abu zatai dashi ba taje ta d'ora kafin ta d'auko brush da toothpaste ta d'auki buta ta tafi inda ake alwala daidai Zainab ta fito da mamaki take kallon tukunyar da aka d'ora taga bata Umma bace ta Asabe ce kuma tasan yau girkin Asaben ne shiyasa ma ta fito zata had'a d'an abinda zatai breakfast kafin ta tafi school domin duk ranar girkin Asabe bazata fito ta d'ora akan lokaci ba saboda kar Zainab ta tsaya karyawa kuma idan ta tafi bazata raba da ita ta baiwa Umma ba haka baban su ma wani lokacin saidai ya ha'kura da karyawar a gida idan ya tafi can gurin sana'ar sa ya karya duk da shi mutum ne wanda bai son cin abincin waje ko kad'an. Zainab tana kallon Bilki tana brush batai magana ba saida ta gama tazo zata wuce sannan tace "Bilki kece kika d'ora wannan tukunyar"? A gadarance Bilki tace "eh nice sai akai ya"?. "Babu abinda akai amma dai nice na hura wutar saboda sauri nake zan tafi makaranta ina so na had'a abun karyawa" ba'ki ta ta'be a she'ke tace "au saiki bari na gama uzuri na da mangal tunda na riga ki d'orawa kuma dai mangal d'in bana kowa bane na baban mune tunda shiyasa siyo balle kice zakiyi min gadara dashi" kai Zainab ta girgiza tana cewa "bazan miki gadara dashi ba kuma ni ban tambaye ki dan kiyi min rashin kunya ba kar kice zaki zage ni". "Idan na zage kin zaki dake ni ne"?. "Bazan dake ki ba amma dai na fad'a miki karki kuskura ki zage ni" harara Bilki ta sakar mata tana jan tsaki tace "kanki ake ji wawa da rad'a Nina wuce sai kici gaba da haushin ke kad'ai tunda kin zama karya" tana fad'in haka ta wuce d'akin su sosai ran Zainab ya 6aci shiyasa kawai da taji zuciyarta tazo wuya gashi ita ta hura wutar amma zata tsaya tanai mata raini shiyasa ta wuce kitchen ta d'auko tasu tukunyar ta zubo ruwa daidai yadda zata dafa indomie guda biyu tazo ta sauke tukunyar Bilki ta d'ora tata kafin ta koma d'aki. Duk abin nan da ake babu wanda ya sani tsakanin Umma ko Asabe balle Sameer da yake d'aki a 'kofar sa a rufe amma idon sa biyu duk yana jin abin da ya ke faruwa Bilki bata sake fitowa ba har ruwan da Zainab ta d'ora ya tafasa ta zuba indomie ta dafa ta shiga kitchen zata d'auko plate ta juye Bilki ta fito ganin tukunyar data d'ora a gefe yasa ta saki wara ba'kar ashar tana kallon kofar d'akin Zainab da gudu ta nufo gurin murhun tana zuwa tasa kafa tayi bol da tukunyar indomie ta zube a kasa ruwan tukunyar tata ta d'auka ta kwara akan garwashin mangal d'in ta kashe wutar sannan tasa takalminta ta tattaka indomie Zainab na tsaye tana binta da kallo na tsananin mamaki harta gama sannan ta d'ago tana huci tace. "Ke 'yar gidan mitsiyaciya wallahi kinyi kad'an 'karyarki tasha karya banza jaka saboda kinga ina d'aga miki kafa shine kowanne irin rainin wayo kika tattaro kaina zaki sauke shi to bari kiji ni nafi 'karfin ki idan ma ke mayya ce saidai kici kanki"........................ ZUCIYAR ALIYU CE.............. JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION. @YUSRAH DUTSE PAGE 22 Tana rufe baki ta ji saukar lafiyayyan mari a fuskarta mai mugun zafi ihu ta kurma tana dafe kumatunta duk zaton ta Zainab ce saida ta d'ago taga Sameer zaro ido tai zatai magana ya sake d'auketa da sabon marin tare da ri'ko hannunta kuka ta fashe dashi cike da tsoro ta soma zunduma kiran Asabe wanda gabadaya a gigice kowa ya fito daga Umma har Asaben ganin abinda yake faruwa yasa Umma tahowa da gudu tana zuwa ta kokarin kwace Bilki 'kin sakinta Sameer yayi Asabe itama dake ihu tana cewa. "Anya Sameer kana da hankali kuwa kashe min 'yar zakai akan 'yar wani wallahi wallahi bazan yarda ba dole wannan shari'ar aje gaban Hajiya tayi mana iyaka da ku matsiyatan mutane masu mugun hali" ta karasa maganar itama ta ture Umma gefe tayi taga-taga zata fad'i da sauri Zainab ta tare ta Asabe kam sai kici kicin kar6ar Bilki take a hannun Sameer wanda ke ta jibgarta ganin yana neman fitar mata da jini Asabe tace. "Sameer idan baka saketa ba saina tsine maka wallahi idan ka sake dukan ta bazan yafe maka ba har abada baza ka bari ba Sameer zanyi maka Allah ya isa fa"? Jin abinda tace yasa ya saki Bilki wacce jin ya sake ta yasa ta fad'i a kasa tana burgima da kururuwa har 'yan gidan suka jiwo nan da nan tasa kofar ta cika dam da mutanen gidan sai tambaya ake lafiya meya faru. D'ago Bilki dake kasa tana kuka Asabe tayi tana cewa "wallahi Sameer sai naci kan uwarka akan bambanci da kake nunawa yarinyar nan ba'kin mugu azzalumi ka tsaya kayi bincike ne daga fitowa zaka hau dukan ta sai kace wanda tayi maka sata kaga yadda kabi ka kumbura mata jiki"?. Dariya Rasheedat tai tana cewa "to da alama dai akan Zainab komai ya faru dan nasan ba wanda Sameer yake 'kauna a gidan nan kamar ita" ta'be baki Haulat tai tana cewa "ai kuma son na banza ne tunda yana bata komai amma ya kasa samar mata mijin da zata aura indai yana kaunarta ai bazai rasa wanda zai had'ata dashi ba ko a cikin abokan sa" jin abinda Haulat tace yasa sauran yan matan suka kware da dariya wanda hayaniyar da ake ya hana Sameer ko su Umma su ji abinda yake faruwa. Fitowa Sameer yayi yana d'aukar bokitin wanka ya fita daga kofar batare daya tsaya ya kalli kowa da duk da hayaniyar da ake yi tsakanin matan gidan da kuma Asabe da Umma Zainab dai da taga abun bana 'kare bane gashi kowa laifin Umma yake gani alhali batasan da komai ba yasa tabar gurin kawai ta koma d'aki tayi shiru zuciyarta na turiri da 'kuna can taji Asabe na cewa. "Muje gurin Hajiya na nuna mata na rantse da Allah akan wannan banzar yarinyar Sameer bai isa ya sake dukan ki ba tunda ni ban isa dashi ba zan kaishi gurin wacce zatai min maganin sa" numfashi Zainab ta sauke lokacin da taji sun bud'e kofa sun fita jiki a sanyaye ta mi'ke tana fita daga d'akin Umma ta hango tana share indomie da Bilki ta zubar da sauri ta karasa tana girgiza kai ta kar'bi tsintsiyar ta tattare tasa ruwa ta wanke gurin tasa tsumma ta goge ta tattare komai duk Umma na tsaye tana kallonta saida ta gama sannan ta d'ago ganin yadda Umma ke binta da kallo fuskarta a cike da tsananin damuwa yasa taji hawaye masu zafi suna taruwa mata a ido kasa tayi da kanta murya a tausashe tace. "Dan Allah kiyi hakuri Umma duk nice sila laifi nane wallahi da nasan idan nayi mata magana abun zaizo da haka dana ha'kura na tafi makarantar batare dana karya ba tunda Yaya Sameer yana bani kud'in napep dubu d'aya tana isa ta" ta karasa maganar hawaye yana shararo mata numfashi Umma ta sauke ba walwala ko kad'an tace "meya had'a kune Zainab ko laifin kine"? Kai Zainab ta girgiza tana goge hawayen fuskarta tace. "Wallahi Umma ba nice na fara kulata ba gawayi na zuba a mangal na hura wuta ina d'aki kafin na fito ita kuma ta d'ora tukunya akai shine dana tambaye ta take min rashin kunya gashi ni kuma sauri nake idan na tsaya lokaci zai 'kure min shine na sauke mata tukunyar a gefe na d'ora indomie idan ta dahu saina mayar mata to a lokacin dana gama dafawa na shiga kitchen zan d'auko plate na juye kawai ita kuma ta fito daga d'aki tazo tayi min bol da tukunyar indomie ta zube sannan ta d'aga ruwa ta kashe wutar ta fara zagi na ni ban san ma Yaya Sameer ya na d'aki yana jin mu ba sai naga ya fito ya na dukan ta" ajiyar zuciya Umma ta sauke tare da girgiza kai kamar itama ta fara zubar da hawayen ko ta samu d'an sassauci haka take ji tasan yau kam watakil bazata sake kwana anan ba saidai ta tafi D'an Yana domin indai Asabe ce sai tayi mata 'kazafin da Hajiya zata koreta daga gidan.................. Tunanin tane ya dawo jin maganar Sameer yana cewa "Zainab kiyi wanka muje na raka ki school d'in" yana fad'in haka ya shiga d'akin sa bayan ya aje bikitin da yayo nasa wanka a band'akin su na samarin gidan wucewa Zainab tayi ta d'auki baho ta saka ruwa ta kai bayi Umma kuma ta wuce d'aki data fito ganin kofar d'akin Sameer tayi ya rufe shiyasa data shiga nata d'akin da sauri ta shirya saboda kar yazo yana jiranta amma me ta saka hijab kenan ta d'aura nikaf naji wani yaro a cikin yaran gidan ya shigo d'akin tana cewa. "Aunty Zainab wai Hajiya tace kije yanzu" wani irin mummunan fad'uwa gaban Zainab yayi har saida ta dafe saitin zuciyarta tana jin yadda take harbawa da sauri rufe idonta data fara ganin ido tayi ga kanta yana juyawa tsabar tunanin abinda Hajiya zatai mata idan taje da'kyar tace. "Kace mata ina zuwa" to yace yana juyawa ya fita ita kuma ta d'auko jakarta da wayarta ta fito d'akin Ummanta ta shiga sai taga bata nan tayi tunanin ko tana band'aki ta d'an tsaya ta fito taji shiru har na d'an wani lokaci can ta kuma ganin yaron ya sake dawowa yace "wai tace ko baza ki zo bane ita tazo"? Jin sa'kon da Hajiyan ta aiko mat yasa ta fahimci to lallai itama Umman tana can bata bashi amsa ba a wannan karon kawai daya fita ta jawo kofar d'akinta ta rufe ta rufe da Umma sannan ta fita had'uwa sukai da Sameer ya shigo ganin yadda take a hangitse yace "lafiya meya faru"?. "Hajiya ce take nema na". "Take neman ki me zakiyi mata"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa "ban sani ba amma bazai wuce akan wannan abun daya faru d'azu bane". "Ok to baza kije ba wuce mu tafi" jin abinda yace yasa ta sake girgiza kai tana cewa "Yaya Sameer idan har na tafi makaranta banje gurin Hajiya ba akan Umma zata sauke fushin ta ni kuma bazan so hakan ba dan Allah ka jira ni yanzu zan fito mu tafi". Shima ya gamsu da hakan tunda yasan halin Hajiyan ya tabbata muddin Zainab bata je ba ta tafi school d'in nan tofa Abban su ma sai ransa ya 6aci idan ya dawo laifin har shi zai shafa shiyasa da tace bari taje shima yaga hakan shine yafi cancanta waje ya fita wajen samarin gidan inda suke zaune daya daga cikin sune ya bud'e rumfa yake siyar da shayi a gurin d'ayan kuma ya bud'e shago. Da sallama Zainab ta shiga gurin Hajiya duk da babu mai jinta saboda tsabar hayaniyar da suke yi masu gulma da masu had'a husuma suna gefe suna dariya gabadaya gurin ya cika dam gaban Hajiya Zainab taje tare da dur'kusawa tace "ina kwana"? Wani irin kallo Hajiya tayi mata tana cewa "munafika ina kwana kike tambaya ta? Yana kwano nace yana kwano ko baki ji ba yana kwano uban me Bilki tayi miki har kika saka Samar ya dake ta da sanyin safiyar nan saboda da ba'kin hali da muguwar zuciya to wallahi bari kiji idan dama kin 'ki yin aure ne saboda ki zauna ki zama shed'aniya a gidan nan baki isa ba bana son annamimanci ke kad'ai a gida kin bi kin hana mutane su zauna lafiya gashi ke ba wata uwar kike tsinanawa ba saidai kici ki kwanta ba aikin fari balle na ba'ki" jin abinda Hajiya tace yasa Haulat matsowa cike da gulma tace. "La Hajiya ta samu aiki fa dama bata fad'a miki ba"? Caraf Rasheedat tace "aikin me amma saidai wanke-wanke a gidan masu kud'i ko ba aikin gwamnati kike nufi ba"? Dariya Haulat tai tana cewa. "Ba aikin wanke-wanke ba ai an d'auke ta koyarwa a islamiyya yau kusan wata shida tana d'aukar albashi dama bata fad'a kin taya ta murna ba saboda karta baki d'an kud'in 6atarwa"?. "Taya zata fad'a kamar kin manta wace Zainab gadon ba'kin hali ce ai bata so a sani saboda kar wani yace tayi masa hanya" Zakiyyah ta fad'a tana ta'be baki taci gaba "kinga fa saboda kusan munafika ce kalli makarantar boko ma da nikaf take zuwa wai saboda kar maza suka fuskarta bayan jikin ma nasu ne". "Ai kuwa gashi nan shiyasa tayi ba'kin jini ba wanda ya ta'ba xuwa gidan nan yayi sallama da ita tunda ta d'ago". "To waye zai zo bayan yaga tana fita da siffar munafikai". "Ai kuwa zata tsufa a gida bata samu saurayi ba indai taci gaba da fita a haka nifa ke garama ki canza rayuwa ki bud'e fuskarki kowa ya gani kya samu wani sokon ya diba yakai gidan su". "Wazai d'auki masifa ya shiga uku indai ba so yake a raba shi da duniyar ba na tabbata wannan yarinyar zata iya kisa". "Kwarai kuwa tsaf zata kashe mutum ta binne batare da kowa ya sani ba tunda mugunta a zuci take". "Kai amma anyi asara kyawun d'an maciji baiyi ba". "To dai gashi duk kyawun nata ya tashi a banza ba wanda ya gani ya yaba". "Tirrr anji kunya kuma anyi asara ai bazata ta'ba samun mijin aure ba sai kowacce budurwa tayi aure a gidan nan ita kad'ai za'a bari tunda d'inkin ta yafi komai muhimmanci sai taci d'inkin ta zauna a tsakiyar uwa da uban kafad'arta tana gogan ta uwarta". "Hhhhhhhh" duk guri ya kaure da dariya suna nuna ta da yatsa d'aya a cikin matan gidan tace "zamu ga karshen 'karya ai za muga uban da zaizo yace yana sonta muna nan muna zuba ido muga d'an waye d'an sarki ne ko d'an gwamna ko kuma d'an waye"?. "Waye kuwa zai kawo kansa gurin ta a yadda take d'in nan ai saidai takai kanta gurinsa yanxu Kuna da tabbacin idan ta fita makaranta take zuwa"?. "Kuma fa haka ne wallahi watakil hotel take tafiya tana holewa da mazan banza shiyasa ma ta'ki aure ta tsaya yawon karuwanci a gari kai anyi asara girma ya fad'i". "Shawara ce zan baki ki daina wannan karuwancin kije ki samu miji ko d'an shaye-shaye ne ki aure shi domin dashi kika fi dacewa wanda zai je mashaya ya shawu ya dawo miki gida a buge ya kama ki yayi miki dukan mutuwa babu mai ceton ki". Subanallahi innalillahi wa inna ilaihi raji'un kowa dai da abinda yake cewa a gurin sun rufu akan Zainab suna ta fad'a mata ba'ka'ken maganganu marasa dad'i tsabar ba'kin ciki kuka kawai Zainab take wanda Umma ta tashi tabar gurin saboda ita ma kuka take kuma bazata so Zainab ta gani ba zata sake shiga wata damuwar ne babu yadda zasu yi komai da yake faruwa a gidan nan sun d'auke shi matsayin kaddara baza su gaji da yin ha'kuri ba domin shi ha'kuri baya 6aci Kuma abinda ha'kuri bai baka ba rashin ha'kuri bazai baka ba komai dad'ewa wata rana Zainab zatai aure zata bar gidan nan ta huta da masifar tsangwamar da ake mata........ AYI HA'KURI YAU ANAN ZAN TSAYA. 🗡️J.W.A🗡️ ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH YMA PAGE 23 Gajiya Sameer yayi ganin bata fito ba yasa ya dawo gidan da kan sa 6angaren Hajiya ya shiga har lokacin bata daina mata masifa ba ga sauran mutanen gidan suma kowa yana fad'ar ba'kin fata da mugun alkaba'i daga ba'kin su tsaki yaja mai mugun 'karfi yana zuwa ya hankad'e Rasheedat dake tsaye tana dariya ya karasa gaban Hajiya wacce ta d'ago tana kallonsa fuskarsa a mugun had'e ko gaisar da ita baiyi ba ya ri'ko hannun Zainab yana mi'kar da ita tsaye yace. "Muje". Cikin fad'a Hajiya tace "Samar ka kiyaye ni wato rainin naka har yakai haka ko tsabar mugunta akan wannan yarinyar ka kama Bilki da duka kamar zaka kashe ta bari uban naka ya dawo zan had'aka dashi yayi maka gargad'i karka sake ta'ba ta da sunan duka idan kuma ka'ki wallahi nan gaba ka sake dukanta da kaina zanje na d'ebo maka 'yan sanda saina had'aka da hukuma damu daidaita a gidan nan gara na sa akai ka gidan gyaran hali" zuba mata ido yayi har ta gama fad'ar abinda zata fad'a tsabar takaici da ba'kin ciki baisan lokacin daya sakar mata wani uban tsaki ba ya juya fuuu yabar gurin domin Zainab kam yana d'agata da sauri tabar sashen Hajiyan tayi waje. Bin bayanta yayi amma bai sameta a wajen ba tambayar d'aya daga cikin samarin gidan da yake zaune a waje yayi yace ga inda tabi da sauri shima yafi inda ya nuna masa a zaune ya same akan wani itace ta kifa kanta akan cinyarta tana rusa kuka mai ciwo karasawa yayi yana cewa "Zainab" a firgice ta d'ago duk ta ji'ke nikaf d'in nata da hawaye ganin Sameer yasa ta sake sakin sabon kuka tsananin damuwar da indai batai wannan kukan ba baza ta samu sassauci ba bakinsa ya cika da iska ya furzar tare da dun'kule hannunsa ya kaiwa iska naushi cikin rashin sanin abun yi agogo ya kalla ganin lokaci ya dad'a ja yace "Zainab kiyi hakuri da halin da kika tsinci kanki ya kamata ki cinye wannan jarrabawar taki akwai haske a gaban ki kina tare da nasara na rantse da Allah nan gaba Zainab duk mahassadan ki na gidan sai sunyi kuka da idanun su fiye da wanda kikai kiyi ha'kuri ki goge hawayen ki kinji"? Kaita d'aga badan kukan ya isheta ba sai domin abinda ya fad'a mata kuma bata so ya ri'ka shiga damuwa dalilin ta shiyasa ta d'auko d'an towel daga cikin school bag d'inta ta goge hawayen sannan ta mi'ke tana kallon sa da idonta dayai jawur tace . "Na gode Yaya Sameer" murmushi yayi yana nuna mata hanya alamar su tafi gyara nikaf d'inta tayi ta mayar dashi yadda yake ta rufe fuskarta sannan suka wuce duk yadda yasan zaiyi yasa ta d'an samu farin ciki saida yayi kafin ya siya mata abinda zatai breakfast sannan ya kaita har makarantar ya bata dubu d'ayan da yake bata kullum d'aya dawo gida yana shigowa sa'kon Hajiya ya same shi tana neman sa kai tsaye yace bazai je ba daya gama abinda zaiyi ma yabar gidan yaje ya bud'e chemist d'insa ya zauna yasa a ransa ko me zatai saidai idan har nan d'in zata biyo shi ta fad'a masa abinda take son fad'a masa ko kuma ta bari idan ya gama hucewa da ita duk ranar daya shiga gaida ita saita fad'a masa. Koda dare da Abba ya dawo yasha mugun fad'a a gurin Hajiya kusan awa biyu ta saka shi a gaba sai bala'i take masa akan indai yana son zama lafiya a gidan nan ya aurar da Zainab ta daina ganinta idan ya'ki zata saka ayi shelarta a masallaci ta sakar da ita tunda bata da wata daraja wannan maganganun sunyi wa Abba mugun ciwo a ransa domin kafin ya taso daga gurin Hajiya har zazza'bi ya rufe shi daya shigo kasa yin wanka yayi sai d'akinsa daya bud'e ya shiga da yake ba girkin Umma bane a d'akin Asabe yake shiyasa ma Umman tana d'aki bata san ya dawo ba har saida Zainab ta shiga gurin sa zatai masa sannu da dawowa taga yana rawa d'ari ta d'auki bargo ta rufa masa da sauri ta fita taje ta fad'awa Sameer yazo ya duba shi tsabar yadda ransa ke 'kuna daya zubawa fuskar Zainab dake zaune kusa dashi ido sai hawaye ne kawai yaji yana zuba masa Allah yana gani yana mugun son yarinyar nan baya so yaji ana sukar ta Hajiya mahaifiyar sace babu yadda zaiyi da ita amma da ace wani ne yake fad'a masa wannan maganar banzar akan Zainab saidai kotu ta raba su koda zai rasa komai nasa daya mallaka sai ya d'auki mataki akan duk mai muzanta masa kamilalliyar 'yarsa tun yana kallonta yana hawaye har barci ya d'auke shi juyawa Zainab tai tana kallon sa jin saukar numfashinsa sai kuma taga yayi barci amma ga hawaye nan a idonsa zaro ido tai tana sake kare masa kallo duk da batasan akan me yake kukan ba da tasan saboda ita ne batasan wanne irin hali zata tsinci kanta ba da mayafin jikinta ta goge masa hawayen ta sake gyara masa pillow da yake kai sannan ta d'aura masa net zata fita taji ya saki wani irin numfashi da sauri ta juyo tana dawowa inda yake ta dur'kusa a saitin fuskarsa wasu hawayen taga suna zuba kuma gashi barci yake sake cire mayafin nata tayi tana shirin goge masa Asabe ta shigo cike da son sharri ta saki salati tana cewa. "Laha'ilah ha'illallahu kashe shi za ki yi? Lahhh innalillahi na kama mashe'kiya tazo za ta danne masa kai da filo ya mutu ashe dama son kashe shi ki ke yi"? Ta fad'a tana tafa hannu mi'kewa Zainab tai batare da tayi mata magana ba tana shirin fita sha'keta Asabe tayi tana cewa "wallahi bazan barki ki fita ba sai kin fad'a min kashe shi zakiyi ko kuma uwar taki ce ta turo ki yi masa wani abu na asiri"? Nan ma shiru Zainab tayi batai magana ba Asabe dake ri'ke da kwalar rigarta taci gaba "idan ma kashe shin kike shirin yi dan ki samu gado shi dai fa'kiri ne kuma talaka babu abinda zaki samu idan ya mutu ma saidai sauran kayan miyar da yake siyarwa da gawayi da kwandunan da yake saro kayan miyar su kike bu'kata"? Ganin har lokacin kamar Zainab d'in bata mayar da ita mutum ba yasa cike da takaici Asabe ta turo ta waje tana cewa. "Asirin ki ya tonu Hauwa da kika aiko ta kashe shi ma na kamata ta saka tsumma ta danne masa hanci sai wutsul-wutsul yake da 'kafa Allah ya shigar dani d'akin wato kashe shi kuke son yi dad'in abun ma ba wata uwar ya tara balle ku samu gadon zilamammu kawai" ta karasa maganar tana hararar kofar d'akin Umma daidai ta fito bata kalli Asabe ba sai Zainab dake tsaye ta kalla tana cewa. "Zainab ki shiga d'aki ki kwanta dare yayi" to Zainab tace tana juyawa ta shiga d'aki kamar yadda Umma ta umarce ta itama Umman juyawa tai ta koma nata d'akin suka bar Asabe a tsakar gida sai faman surfa masifa take tana d'aga murya wai Zainab ta shiga d'aki ta dannewa Abban su kai zata kashe shi saboda su samu gado. ZUCIYAR ALIYU ZAINAB CE😍. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• J•W•A ______________Y ____________________M ___________________________A ♥♥YUSRAH♥♥ Chat with me. +234 816 098 3083 @Y♠M♠A DUTSE PAGE 24 Washe gari da Abba ya tashi zazza'bin ba sosai ya sake shi ba shiyasa ma bai tafi gurin sana'ar sa ba daya d'an daddafa bango yaje ya gaida Hajiya ya bata d'an wani abu saiya dawo yasa Asabe ta fito masa da tabarma waje ya kwanta a barandar kofar d'akinsa yana kwance Sameer ya shigo gai dashi ya siyo masa kayan karyawa daga waje ya d'aga shi da kansa ya zauna ya bashi sannan ya sake duba shi Zainab ma ta fito tayi masa sannu zata tashi yace ta kira masa Umman ta sannan Asabe ma yai kiranta ya kira Bilki duk suka taru a gabansa kallon su ya fara yi d'aya bayan d'aya har yakai kan Zainab sannan ya tsaya yayi shiru ita kam kanta yana kasa batasan yana kallonta ba saida taji yace. "Zainab". D'agowa tayi tana kallon sa cikin nutsuwa tace "na'am Abba". "Meya had'a ki da Bilkisu jiya bayan fita ta daga gida"? Duk gurin babu wanda ya kawo akan abinda ya tara su kenan domin Asabe ita tayi tunanin ko wasiyya ma zaiyi musu🙊 sai kuma taji batu sa6anin wanda take zato d'an shiru Zainab tayi domin bata so a sake tada maganar har abada badan yanzun da yake son sanin dalili ba muryarta a hankali ta soma magana. "Baba jiya da safe bayan na tashi ina sauri zan tafi makaranta shine na kunna wuta a mangal zan dafa indomie naci kafin na tafi na shiga d'aki kafin na fito Bilki ta d'ora tukunya da ruwa a ciki shine na tambaye ita ta d'ora tace min eh ni kuma a lokacin sauri nake yi domin zan iya makara shiyasa na sauke tata tukunyar na d'ora na dafa indomie kafin na d'auko plate na juye tazo tayi bol da tukunyar indomie ta zube Kuma ni bance mata komai ba ta fara zagi na har Yaya Sameer yaji yana d'akin sa shine ya fito ya dake ta wannan shine abinda ya faru" tana rufe baki Asabe tace. "Sannu munafika wato karyar da kika shirya kenan bayan kin mammari Bilki kalli fa yadda bakin ta ya kumbura saboda dake idanuwanta duk sun kumbura suma amma saboda babu Allah a ranki sai kinyi mata sharri"? Shiru Zainab tayi batai magana ba sai Abba daya kalli Sameer yana cewa. "Kai meyasa ka dake ta bayan baka san komai ba"? Gyara zama Sameer yayi yana cewa "Abba ina daga d'aki ina jin irin zagi da cin mutuncin da takewa Zainab bayan itace mara gaskiya raina ne ya 6aci shiyasa ina fitowa na mare ta hakan ma da naji ban huce ba na sake dukanta" kai Abba ya jinjina yana mayar da hankalinsa kan Bilki wacce kamarta ta canza tsabar dukan da Sameer yayi mata jiya yace. "Ina jinki ke meyasa ita ce ta fara hura wutar amma kika zo kika d'ora tukunya kuma kika zubar mata da abinci meyasa"? Shiru Bilki tai tunda tasan ita ce marasa gaskiya ko ina aka je ganin batai magana ba yasa Asabe cewa "ke dan ubaki ba magana ake miki ba banza kina ji kowa yana fad'ar 'karya dan ya kare kansa amma dan sakarci kinyi shiru wato kin kar6i laifin da ba naki ba kenan"? Ta karasa maganar a masife yayin da har lokacin Bilki batai ko tari ba takaici ne ya rufe Asabe tana shirin magana Abba yace "duk yadda akai kece baki da gaskiya a wannan lamari dan haka ki baiwa 'yar uwarki ha'kuri yanzun nan kafin ranki ya 6aci" tun kafin Bilki tayi magana Asabe tace. "Wannan wanne irin abu ne taya za'a dake ta sannan yanzu ace ita ce mai bada ha'kuri wato itace mai laifin kenan a cikin su gaskiya bazai yuwu ba" batare da Abba ya kallo inda take ba yana kallon fuskar Bilki da tayi kasa dakai yace "ban sako dake ba da 'ya'ya na nake magana ta". "Kuma tsakani da Allah shikenan bazan fad'i gaskiya ba saina bari ina kallo bayan cutar ta da akai azo a tilasta mata bada ha'kuri" fuskarsa Abba a had'e yace "Bilkisu baki ji abinda nace ba zaki bata ha'kurin ne ko nima saina dad'a marinki akan wanda Sameer d'in yayi miki" yana rufe baki da sauri Bilki tace "kiyi ha'kuri". "A'a ba irin wannan ha'kurin nake so ki bata ba ban gamsu ba a tsaye kikai maganar babu ladabi balle kwantar da harshe tana matsayin yayarki so nake ki fad'a yadda xan ji raina ya yarda" shiru Bilki tayi tana kallon kasa ta'ki magana alamar bazata bada ha'kurin yadda yace ba. "Bilkisu". Taji Abba ya kira sunanta kasa d'agowa tayi ta fuskance shi balle kwarjininsa yasa ta bata ha'kuri domin a yadda take ji yanzu a ranta ko kisa ne zata iya kashe Zainab ba tare data damu ba......... "Bilkisu". Ya kira sunanta a karo na biyu da'kyar tace "na'am" babu ma wanda ya jita domin a ciki ta amsa marin da Sameer ya sakar mata yasa ta fasa 'kara da gudu ta tashi daga kusa dashi tana kuka nuna yake da yatsa yana huci zaiyi magana Asabe tace "kai jama'a ni kam na shiga uku a gidan nan gaskiya wallahi kai dai Sameer kayi asara anyi mugun mutum anan kana 6ata min rai da wannan dabi'un na ka wacce irin masifa ce wannan jiya kayi mata duka bata gama warkewa ba yau ma kazo ka mareta to ka daki Allah ya isa" ta karasa maganar tana zafga masa wata uwar harara ji take kamar ta tashi ta rufe shi da duka ko ta huce wannan takaicin da yake d'ura mata Sameer kam bai kula zancen da Asabe take ba tsabar yadda ransa yake tafasa sai kallon Bilki dake gefe tana kuka yayi yana cewa. "Zaki dawo nan ki zauna ne ko saina tashi naci ubanki" da sauri ta dawo ta zauna a kusa da Asabe cike da tsoro tana matsar hawaye. "Wallahi sai kin gane kuren ki zan kama kine" ya sake fad'a yana cije lips tsaki Asabe tayi tana cewa "kayi asara dai Sameer wallahi a rayuwarka kaji kunya tunda ka d'auki 'yar uba ka bar 'yar uwarka kayi babbar asara ma wacce babu ribaa cikin ta ita wacce kake yi dominta ai ba gani take ba kuma ni na fad'a maka wata rana saita guje ka da zarar ta samu wata ni'ima zata manta dakai ya zama daga ita sai uwarta kaine sakarai shashasha ta mayar dakai mahaukaci shiyasa ka kasa ganewa amma ban sani ba ko kaima asirin tayi maka shiyasa idonka ya rufe ka koma 6angaren ta dan nasan duk rintsi babu inda ake samun 'yan uban suna irin wannan kyakkyawar mu'amalar da kuke yi dole akwai wani 6oyayyan abu kuma saina bincika ko menene idan na gano ba haka kawai suka barka ba wallahi hukuma ce zata raba ni dasu............ "Asabe ya isa haka" Abba ya fad'a fad'a ransa a 6ace ganin yadda ta mayar dasu biyo ta nan ta bud'e baki sai magana take kowa yana sauraron ta gashi sun tura mata aniyarta ta inda yake son Umma ke nan koda Asabe zata rufe ta da duka indai yace karta kulata tofa baza ta biye mata ba amma ya tabbata idan Asaben ce a matsayin Umma baza yarda ta ri'ka mata irin wannan wula'kancin tayi shiru ba. "Kayi ha'kuri Abba a manta da komai laifi duka na Bilkisu ne ba kowa ba domin duk inda za'a je itace mara gaskiya" Sameer yana rufe baki Asabe tace "inji uwar ka munafiki waya sako dakai a gidan uban wa kasan laifin Bilki ne"? Shiru Sameer yayi domin koma mene ne ita mahaifiyar sa ce dole yayi taka tsantsan karya kauce hanya duk abinda ake yi Abba yana lura da Bilki hankalinsa yana kanta yana kallon yadda take murgud'awa Sameer baki tana maganganu 'kasa-'kasa saita d'ago ta harari Zainab ta ta'be baki kai ya jinjina yana kallon ta da mamakin raini irin nata baisan yaushe ta koyi fitsara ba yasan dai da ba haka take ba ya akai ta canza rayuwarta kodai rashin zaman da yake a gida shine ya kawo hakan ajiyar zuciya ya sauke yana cewa. "Bilkisu ki bata ha'kurin abinda kikai mata jiya kafin ranki ya 6aci a gidan nan" ya fad'a yana kallon ta ita kuma Sameer ta kalla ganin yadda ya had'e rai yana watso mata mugun kallo yasa tace "kiyi ha'kuri" Kai Zainab ta girgiza tana cewa "babu komai ya wuce". "Shikenan Allah ya rufa asiri Bilkisu Zainab yar uwarki ce kuma yayarki ce jinin ku d'aya bana son wannan zaman takun sa'kar da kuke yi daga yau karna sake jin wani tashin hankali ya faru a tsakanin ku zaku iya tafiya" godiya sukai masa suka mi'ke kowa ya bar gurin har Zainab ta shiga d'akinta sai kuma ta sake fitowa ta dawo inda yake tace. "Baba kana bu'katar wani abu ne ka karya"? Murmushi yayi tun kafin yayi magana suka ji muryar Asabe tace "to munafika ai ba a d'akin uwar taki yake ba da zaki zo kina tambayar sa ya karya ko bai karya ba idan bai karya d'in ba wata uwar zaki kawo masa" shiru Zainab tai bata kalli inda Asabe take ba sai tashi da tayi ta koma d'aki ta d'auko hijab d'inta da nikaf ta saka ta fita. Asabe kuma kitchen ta shiga ta dama masa kunu ta fito tana cewa "kai da baka da lafiya haka zaka sha kunun ba sugar idan mu lafiyar mu kalau kai fa"? Ta karasa maganar tana karasowa ta aje kofin a gefensa tace "gashi nan" tun bata mi'ke ba yace. "D'auke bazan sha ba na 'koshi" kai Asabe ta d'aga tana kallonsa daga baya ta mi'ke tana cewa "saboda nayi fad'a akan gaskiya ta shine zakai fushi dani"? Shiru yayi mata kamar bai ji ba taci gaba "tabd'ijan lallai akwai 'kura a gidan nan akwai ba'kar guguwa an shanye min d'a sannan mijin ma baza a barni naji dad'in sa ba wallahi duk wanda yaje yayi min 'kulunboto yazo ya baiwa Abdullahi yasha ya tsane ni Allah ya isa tsakani na dashi" tana rufe baki yace. "Ba wanda ya shiga tsakanin mu halin ki ne ya haifar miki da wannan matsalar domin halin mutum shine sabulun wankan sa kar kiyi zargin kowa ki zargi kanki". "Ba wani hali nane ya jawo min kawai dai kace rashin adalcin naka daka saba min shi zakai na gaji gaskiya na gaji amma ba komai muje zuwa zan d'auki matsakin daya dace da kowanne tunda har anyi min shedar rashin arziki idan na fito muku da kalata zamu fi daidaitawa" tana fad'in haka ta d'auke kofin kunun data aje masa ta juya d'akin ta dashi tana tafe tana balbalin fad'a da kallo Abba ya bita tare da dafe kai ya girgiza kad'an ya sauke numfashi ya rasa da me zaiji idan yaje gurin Hajiya ta balbale shi saboda shi talaka ne ba'a cin dad'i a kofar sa sauran suna kai mata nama da kaji sannan abincin su yafi na kofarsa had'uwa tunda su suna d'aukar albashi idan ya shigo kofarsa domin ya huta nan ma Asabe ta tada tata masifar ta hana shi jin dad'i indai kaga yana zumud'in dawowa gida da wuri tofa saidai idan ranar a d'akin Umma yake shine kawai zai ci abinci cikin salama ana hira da dariya yayi barci cikin farin ciki ya tashi da annashuwa amma ba dai Asabe ba yana nan a kwance Zainab ta dawo ta shiga d'aki ta cire hijab d'inta ta fito da klin a hannunta tana zuwa ta wuce d'akinsa ta d'ebo kayansa masu datti ta kai gurin da ake wanki ta saka kujera ta zauna yana kallonta ta wanke masa kayansa tas ta shanya sannan ta wanke kafarta ta tashi ta d'an d'ora ruwa yayi d'umi tayi wanka ta shirya ta hau kan keke ta fara d'inki kafin wani lokaci tunda ba girki Umma bane balle tace zata kama mata yan wasu ayyukan. ZUCIYAR ALIYU CE. ♪♦Fatima Zarah Shamsuddeen ♪♦Ramlat Ikram Ibrahim Lele @YMA DUTSE PAGE 25 Nihal tana tsaye a jikin motar su driver yana ciki a zaune hangen ta inda zata ga Zarah ta 6ullo take yi amma babu alamarta gashi ta barsu suna jiranta kamar wanda tayi shanya d'an tsaki taja tana sake kallon kofar shiga school amma dai labarin d'aya ne ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa ta bud'e mota ta aje takardun hannunta da handbag d'inta sannan tacewa driver. "Dan jira na shiga na duba inda tayi kamar fa ciki naga ta koma" kai ya d'aga yana cewa "ok madam ba damuwa" wucewa tayi tana shiga cikin school d'in ita kad'ai sai magana take "wanne irin iskanci ne a gurin Zarah yarinya rashin ji yayi mata yawa kullum sai ana jiranta kamar wata uwar mutane"? Ganin datai har 6anfmgaren da take karatun taje bata nan yasa ta dawo tana cewa. "Wai bata dawo ba"? Kai driver ya d'aga yana cewa "ban ganta ba bari na fito mu gani" d'an tsaki Nihal tayi tana kallon lokacin da driver shima ya tafi yana d'an hahhangawa ko zai ganta ita ma wani gurin ta sake shiga ta duba ta nan ma babu ita fitowa tayi a lokacin Shareef yayi parking da motarsa zai shiga gurin ya ganta farko yayi tunanin tare da yayanta Ammar take sai kuma yaga ita kad'ai ce yana so zaiyi magana mai muhimmanci da yarinyar nan amma sai ya fara samun Ammar d'in tukuna yana daga cikin mota yana kallonta kuma yaga yadda take waige-waige alamar akwai abinda take nema kamar zai fita yaje inda take sai kuma ya fasa yaci gaba da zama a cikin motar. Baby da Badiyah su na tsaye a gurin da Nihal ta shiga su kuma za su fito da alamar abu suka siyo hannun su ri'ke da ledoji ta'be baki Badiyah tayi tana kallon inda Nihal take tace "kinga irin 'yan 'karyan nan haushi suke bani kiga dai wancan budurwar yadda ta saka glass saboda iyayi sai wani sham 'kamshi take sai kace 'yar gwamna kuma maybe idan kika bibiya 'yar talakawa ce aron kayan take yi dan tazo ta burge samari" juyawa Baby tai tana cewa "a Ina kika ganta"? Da hannu ta nuna inda Nihal ke tsaye zaro ido waje Baby tai tana cewa "wancan ai yarinyar da Shareef yayi fushi dani a kanta ne". "Waye Shareef kuma"?. "Wani guy ne a hospital d'in mu yake masifar jin kansa tayi yawa a kanta nake ta faman binsa Ina bashi a ha'kuri amma ya'ki ya saurare ni bari naje naci uwarta kona huce takaici na" ta fad'a tana shirin fara tafiya da sauri Badiyah ta ri'ke ta tana girgiza mata kai tace "a'a kada kiyi haka bana son abun jawo rigima wannan ba girman ki bane" fisgewa tayi tana cewa "ke wallahi sai naje naci ubanta maybe idan nayi haka ta kiyaye ni a gaba". Nihal kam bata lura da su Baby ba hankalinta yana kan Zarah data fito tare da wata 'kawarta taga ice-cream suke je siya ba komai ba suna karasowa ta soma mata fad'a "haba Zarah me kike yi haka kinsa hankali na ya tashi dama nan kika taho siyan ice-cream kuma maimakon ki fad'a min kika barni nayi ta neman ki"? Ta'be baki Zarah tai tana cewa. "Akan me zan fad'a miki sai kace wata uwata dole sai nace miki na tafi siyan ice-cream yanzu da kika ganni dashi ai ya baki amsar tambayar ki ko"? Kai Nihal ta jinjina tana kallon ta tace "bansan yaushe kika koyi raini ba amma bari muje gidan wallahi saina had'a ki da Yaya Ammar yayi min maganin ki" tana rufe baki Zarah ta murgud'a mata baki tana gatsinin ta ran Nihal a 6ace ta d'aga hannu zata mareta a fuska hannu Zarah ta saka za ta tare marin kawai bata sani ba ta buge glass d'in dake fuskar Nihal ya fad'o kasa da sauri Nihal ta sunkuya tana laluben ta inda zata ji glass d'in ta d'auko jin bata ta'bo shi ba yasa tace. "Zarah ki d'auko ki bani baza kizo ki mi'ko min ba" tsaye Zarah tai tana gefe tana kallonta ta'ki magana Shareef dake cikin mota tsananin mamaki ne ya kusan sumar dashi ganin da glass d'in ya fad'i tana laluben sa alamar bata gani kenan sai dashi dama ciwon ido take shiyasa yake yawan ganinta a hospital, baki Badiyah dake tsaye ta bud'e tana kallon su ganin yadda Nihal ta gigice yasa tace. "Ayya Allah sarki ashe bata gani saida glass d'in ni kuma har nayi mata muguwar fassara astagfirllah Allah na tuba bari naje na d'auka na bata wannan 'kanwar tata anyi mara kunyar yarinya" ganin da Baby tayi zata tafi inda Nihal take yasa ta ri'ke ta tana cewa "wallahi baza ki taimake ta ba na tsane ta bana son ganinta da nasan zan had'u da ita bazan zo gurin nan ba" da mamaki tace. "Haba Baby ke fa musulma ce sannan taimako take nema". "Ai ba a wajen ki take neman taimakon ba ko ke kad'ai ce mai rai a gurin". "Ni banyi la'akari da kowa da yake nan ba zanje na taimake ta Allah yana taimakon bawa ne matu'kar bawan yana taimakon d'an uwansa musulmi kin gane"? Kai Baby ta girgiza tana cewa "ban gane ba" zaro ido 'kawar tayi da mamaki zatai magana suka ga Shareef wanda basu san da zuwansa gurin ba sakamakon bada motar sa ya fito ba ta Mami ya d'auko da sauri suka ga ya fito daga cikin motar ya karasa ya d'auka ya saka towel ya goge yace. "Kar'bi" ya fad'a yana kara Mata a hannunta kar'ba tayi ta mayar dashi idonta tana sauke ajiyar zuciya tace "na gode" kai ya d'aga mata zai juya tace "amma kamar kaine wanda nayi wa laifi a hospital kwanan baya ko"? Jin abinda tace yasa ya kalleta yana girgiza yace. "No baki min laifi ba ki saka a ranki kece da gaskiya bayan wayarki data 6aci wanne rashin gaskiyar za'a baki". "Shikenan na gode". "Karki damu" yana fad'in haka ya koma ya kulle motarsa ya shiga gurin ko lura da baby baiyi ba wacce tsananin rud'ewa ta kama ta ita kam Nihal tana ganin ya bar gurin itama ta juya ta fita domin Zarah tun ganin datai yazo ya d'auki glass d'in da gudu ta bar gurin saboda kar Nihal ta saka glass d'in taga tana nan ta'ki mi'ko mata. A mota ta samu Zarah sai kallonta take bayan ta shiga bata kula ta ba har driver ya tu'ka motar suka bar gurin suna zuwa kuwa sukai sa'a Daddyn su yana nan a parlor Nihal ta tsaya bayan ta gaisar dashi tace "Daddy daga yau warewa Zarah nata driver da zai ri'ka zuwa d'auko ta domin na gaji da halinta tun ina dannewa yau ta kaini bango". "Me ya faru"?. "Wai Daddy yarinyar nan ta buge min glass ya fad'i tana ji ina ta 'kwalla mata kiran tazo ta mi'ko min ta'ki sai wani saurayi ne ya taimaka min". "Subanallahi ita Zarah d'in"?. "Eh Daddy wallahi na gaji da halinta na rashin ji bazan iya ba kawai a samar mata wanda zai ri'ka d'aukar tsiyar ta amma bani ba". "Ok na fahimta ina ita Zaran take"?. "Ana yin parking da motar ko bari ya kashe batai ba ta bud'e murfi ta fito ta kofar baya ta shigo part d'in mu". "Shikenan yanzu tashi kuje kuyi wanka da sallah kuzo kuci abinci ita kuma nida ita ne ki rabu da ita zanyi maganinta sannan daga yau driver na shine zai ri'ka kaita" murmushi Nihal tai cikin jin dad'i tasan ko ba komai an wuce gurin tunda har Daddyn yace haka tasan idan zai tafi gurin aiki tare zasu tafi ya sau'ke ta haka idan an tashi zai tura driver ya d'auko ta ya dawo da ita gaskiya bazata taji dad'i ita kad'ai ba amma tunda haka ta za6a shikenan....................... ZUCIYAR ALIYU CE............... YMA DUTSE JIGAWA VNTRS. .................PAGE 26 Su Afifah suna zaune a parlor gaba d'ayan su harda Afif daya dawo daga gurin aiki ko part d'insa bai shiga ba saboda ya d'ebo yunwa yana zaune tare da su Momy ana zance suka ji sallamar Amirah kowa zuba mata ido yayi harta karaso ta zauna Momy ta fara gaisarwa sannan suka gaisa da Afifah sauran ma suka gaishe ta. "Fati tashi ki d'aukowa Amirah lemo da cup man" to Fati tace tana mi'kewa shiru Amirah tai so take ta tambaye su ina Aliyu kuma tana tunanin ta yadda zata tambaya d'in da kamar a bedroom suke su kad'ai zata iya tambayar Afifah. Har Fati ta d'auko juice da kofi ta kawo mata bata sani ba saida Momy tayi mata magana sannan ta dawo daidai cikin hayyacinta amma data zuba ma kur6a d'aya tayi ta aje tai shiru kallonta Momy tayi cikin kulawa ganin ta d'an rame kad'an tace. "Amirah ko baki da lafiya ne"? Kaita d'aga a sanyaye muryarta a hankali tace "wallahi nayi zazza'bi kwanan nan shiyasa yau ma a kwancen nake kawai dai cewa nayi bari nazo na gaishe ki saboda na d'an yi yawo jini na ya tsinke". "Kin kyauta kuwa ni da naga shiru-shiru ma baki dawo ba nasa Afifah ta kira ki kika ce lafiya kalau kina dawowa shiyasa daga haka na bar batun". "Eh a lokacin nayi tafiya ne naje Abuja gidan Aunty Fadeelah ban dad'e da dawowar ba na fara zazza'bin kuma asma ta ta tashi". "Ayya babu wanda ya sani ai da za'a je a dubo ki kuma baki kira Afifah kin fad'a mata ba Allah ya 'kara sau'ki". "Amin" Amirah tace tana kallon Afifah tayi mata magana da ido kaita d'aga tana mi'kewa suka hau stairs tare bedroom d'insu suka shiga akwatin Amirah dake aje Afifah ta d'auko tana kawo mata zama a gefen gadon Amirah tayi tana zuge zif d'in ta soma fito da kayan tana cewa "dole idan na koma na baiwa mai yi mana wanke ya d'auraye min su saiya goge min sun d'an yi 'kura". "Wai nikam Afifah ina Aliyu ne naga motarsa a parking space amma kuma naga an rufeta da rigar rufe mota ko ya koma ne"?. "Eh ya koma bai kira ki ya fad'a miki ba"? Shiru Amirah tai tana kallon waje daya daga baya tace "taya zai fad'a min ban sani ba sai yanzu dana kasa ha'kura na tambaya amma ko ba komai ya kirani kota waya ne ya fad'a min nayi masa fatan alkhairi". "Maybe zai kira ki daga baya" Afifah ta fad'a tana dariya numfashi Amirah ta sauke tana cewa "wanne irin zai kira ni tun da bai kirani ba sanda ya tafi sai yanzu ya dad'e fa da tafiya ko"?. "Ya dad'e man dama ai ba wani dogon hutu ya d'auka ba sai ranar daya sake dawowa kuma" kai Amirah ta kad'a tana cewa "Allah ya dawo dashi lafiya" daga haka bata sake cewa komai ba ta fara kad'e kayanta tana linkesu tana mayarwa cikin trolley Afifah kuma ta shiga wanka sakamakon lokacin tafiya islamiyya ya kusa sanda ta fito Amirah harta gama ta rufe akwatin da wayarta a hannunta tana dubawa jiran Afifah tai ta shirya ta saka hijab d'in islamiyyar da nikaf ta d'auki jakarta sannan suka fito tare ganinta da akwati yasa Momy cewa. "Wai tafiya dashi zakiyi shikenan kuma na d'auka kinzo ki d'an yi mana sati d'aya ne"?. "A'a wallahi Momy zan dawo nayi muku satin amma ba yanzu ba". "Ok to mun gode ki gaida maman naki". "To Momy insha Allahu zata ji" kallon Afifah Momy tayi tana cewa "Afifah kiwa driver magana ya kaita" kai Amirah ta girgiza tana cewa "a'a da mota nazo tana harabar gidan". "Ok to ba damuwa ki gaida gida" to tace suna fita tare da Afifah ita ta shiga motarta Afifah kuma ta fita daga gidan har tayi tunanin zuwa gidan su Zainab ta gani ko bata taho islamiyyar ba sai kuma ta fasa ta wuce kawai saidai tana shiga ta hangota suna tsaye tare da wata suna zance murmushi tai bayan ta karasa tayi musu sallama d'age nikaf d'in tayi tana kallon Zainab tace. "Hajiya zee zee ikon Allah kin shigo islamiyyar ma bazaki cire nikaf d'in nan ki d'an huta ba"? Kaita girgiza tana cewa "Afifah bazan iya cire nikaf a ko'ina ba saidai a gidan mu balle nan islamiyyar ba maza ne"? Dariya tai tana cewa "da maza man amma ai ba ruwan su da hakan". "Waya fad'a miki babu inda shed'an baya zuwa ya haddasa fitina shiyasa nake kokarin kare kaina daga shiga fitinar tasa" kai Afifah ta jinjina daidai ya sayyadi ya shigo da littafai a hannunsa fuskarsa fal da gashi irin na ustazai yasha jallabiyya da rawani a kansa yana karasowa suka dur'kusa suna gaida shi amsa yai yana cewa. "Malama Zainab Abdullahi ki shiga ajin da kike koyarwa ki kar6i hadda" kaita d'aga cikin ladabi tace "to sayyadi insha Allah" saida ya wuce sannan suka mi'ke da yake ajin su Afifan take koyarwa nan suka shiga duk su ukun saida ta fara kar'bar haddan kowa ya biya tukuna sannan tayi musu sabon d'ori suna biyawa har akai kiran sallar la'asar kowa ya fita zasu yi alwala Afifah dake tsaye bayan ta gama alwalar ta baiwa Zainab butar taje ta d'ebo ruwa a famfo ta dawo ido ta zuba mata taga yadda zatai domin kullum haka ake fama bata son aga fuskarta ko kad'an tsayawa tayi ta duba gabas yamma kudu arewa ganin ba namaji a cikin malaman islamiyyar sai zallar mata yasa ta cire nikaf d'in ta mi'kawa Afifah wacce tayi dariya tana kallon yadda fuskarta tata take dad'a wani irin yellow tsabar sabon saka nikaf kaita jinjina tana cewa. "Allah mai iko kenan kowa da kiwon daya kar'be shi wai makwafcin mai akuya ya sayi kura" mi'kewa Zainab tai bayan ta shafa addu'a tace "ke kuma dawa kike wannan karin maganar"? Ta fad'a tana kar'bar nikaf d'in ta mayar kai Afifah ta girgiza tana cewa "dawa nake kuwa banda ke"?. "Ni kuma da nayi me"?. "Da naga kina wasu abubuwan da suke bani mamaki". "Haka ne"? Da kyau muje kar a shiga sallar muna nan" Zainab ta fad'a tana d'aukar carbinta data aje a gefe ta mayar shi yadda yake a yatsarta ta zura shi sannan suka wuce bayan an idar da sallar kowa ya koma cikin aji aka ci gaba da karatu sai da rana tayi sanyi sosai jikin magriba daidai lokacin tashi ya sayyadi ya le'ko yace tayi musu addu'a sai gobe kuma. Addu'ar tayi suka shafa sannan d'aya bayan d'aya suka fara fitowa suna fita daga islamiyyar saida kowa ya tafi ya sayyadi ya tura gate d'in ya rufe shima ya nufi hanyar anguwar su. AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE. J.W.A Yusrah Musa Abubakar @♠Y♠M♠A♠ DUTSE PAGE 27 Zainab tana shiga ta tarar da Umman ta a kofar kitchen tana zaune akan kujera tana mulmula tuwon shinkafa shiga d'aki tayi ta aje jakarta ta cire nikaf da hijab d'in sannan ta fito tayi mata sannu da gida ta kama mata aikin ita kuma Umma ta mayar da hankalinta kan miya saboda kar Abba ya dawo daga gurin sana'a bata gama ba lokacin anyi kiran sallar magriba Zainab ta saka dukkan tuwon a cooler ta saka murfin ta rufe ta tashi taje tayi alwala ta shiga d'aki bata sake fitowa ba saida taji sallamar babansu ya dawo ta fito tayi masa sannu da dawowa ta koma bayan isha tana zaune a d'aki Umma ta le'ko tana cewa. "Zainab kizo ki d'auki abinci man" kaita d'aga mata tana cewa "ina zuwa Umma wannan atamfar nake so na karasa yankawa gobe idan Allah ya tashe mu lafiya dana dawo daga makaranta saina fara d'inkin ta" sakin labulen Umma tai tana cewa "to shikenan gashi nan dai a d'aki ni gurin Hajiya zanje" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa cike da fargaba ta fito tana cewa. "Me zaki yo acan"? Umma dake kokarin saka hijabi tace "bani kad'ai bace taron matan gidan ne gaba d'aya bansan me ya faru ba" numfashi Zainab ta sauke tana cewa "Allah yasa alkhairi ne" daga haka bata sake cewa komai ba har Umma ta fita ita kuma ta koma d'aki samun kanta tayi da kasa ci gaba da yanka atamfar duk jikinta yayi sanyi tasan kiran nan ba kiran alkhairi bane Allah yasa ba akan Umma ko baban su abun zai 'kare ba shiru ta zauna har Sameer ya shigo ganin kofar ba kowa yasa yace. "Zainab". "Na'am Yaya Sameer" ta fad'a tana fitowa kallonta yai ganin yadda fuskarta ta nuna alamun da akwai damuwa yace "ina yan kofar suke"?. "Suna gurin Hajiya". "Gurin Hajiya kuma me take musu"?. "Wallahi Yaya Sameer ban sani ba amma dai naji Umma tace taron na duka gidan ne". "Na duka gidan har yaran gidan kenan"?. "A'a nufi iya su matan gidan dasu Abba". "Ok na fahimta yau me aka dafa"?. "Tuwon shinkafa ne"?. "Da wacce kalar miya"?. "Miyar ganye" "ok" kawai yace yana wucewa ya shiga d'akin sa ita ma nata d'akin ta koma kafin Umman ta dawo. Batun su Umma suna can sun hallara maza su uku mata su shida Hajiya tana zaune daga kan kujera su kuma suna 'kasa a zaune kowa yayi shiru suna sauraron su ji dalilin da yasa ta tara su kallon su Hajiya ke yi d'aya bayan d'aya kafin tayi gyaran murya tana cewa. "To jama'a salamu alaikum" amsa mata sukai "wa alaikum salaam" kafin taci gaba "nasan wasu daga cikin zasu yi mamakin me yasa na tara ku anan wasu ransu bai so ba amma ni na zama ciwon ido zama dani sai mai ha'kuri ba wani abu ne yasa na tara ku magana ce akan 'ya'yan ku dama ku kanku wanda yaji hukuncin da zan yanke baiyi masa ba sai yakai ni hukumar kare hakkin d'an adam tunda naga so kuke kuna kallo 'ya'yan ku su maida mana gida gidan karuwai to wallahi baku isa ba 'ya'ya sun kawo mizanin aure sun zama gird'a gird'a kamar shanu kuna kallon su kun 'ki ku tsaresu su fad'a muku gaskiyar samarin su na kwarai yau zan kawo karshen komai ta kanka zan fara kai Habibu kaine babba a gidan nan kuma kana samun kud'in da zakaiwa 'ya'yanka kayan d'aki meyasa ka barsu kara zube ka'ki musu aure"?. Ajiyar zuciya Habibu ya sauke yana cewa "kiyi hakuri Hajiya ba nine na'ki musu aure ba lokacin sune baiyi ba ina gasu Rafi'atu da Aisha da lokacin su yayi na aurar dasu". "Au abinda zaka ce kenan? Lallai kuwa naji naka" juyawa tai tana cewa "sai kai Aminu meyasa ka'ki kayi wa Atika da Zakiyyah da Rasheedah aure"? Kai ya girgiza yana cewa "Hajiya bani da amsar tambayar ki domin ban 'ki yi musu aure ba komai nufin Allah ne" kai Hajiya ta jinjina tana kallon Abdullahi ta ce "to masu damar ma anyi musu maganar basu aurar da 'ya'yan su ba sunce lokaci ne baiyi ba ina ga kai Abdullahi saidai kar kaji nace haka zuciyarka tayi fari ka sake baiwa Zainab lasisin zama a gidan ka baka isa ba" mayar da hankalinta kan gaba d'ayan su tayi tana cewa. "Ku bani hankalin ku nan yanzu zan fad'a muku hukuncin dana yanke tunda ku kun garara kuma kar wanda ya kuskura ya musa min dole ku bi abinda zan fad'a ko ranku baya so sannan ko ba kayan d'aki sai kun aurar da yaran nan in yaso ku kaisu da tabarmi". "Ban tari numfashin ki ba amma Hajiya ina ganin da kin bari kowa a cikin mu muje munyi magana da yaran idan suna da samari a waje sai musan wanne kalar mataki zamu d'auka" kaita girgiza tana cewa "bakin al'kalami ya riga ya bushe na gama yanke shawara da zuciya ta umarni zan baku ba neman yardar ku nake ba "Isma'il d'an wajen Habibu ya auri Bilkisu Yusuf d'an wajen Habibu na d'akin Mairo ya auri Rasheedah Samar ya auri Zakiyyah Zaidu shi kuma ya auri Zainab Abdul-Razza'k ya auri Safiyyah wadannan yaran dana lissafa su nake so na bud'e ido naga kowa da mijinta tunda Haulat da Atikah su an gama komai na bikin su kun ji abinda nace"?. Kowa a gurin 'kamewa yayi aka rasa wanda zai fara 'kin yarda ya mayarwa Hajiya magana sai Asabe wacce ta gyara zama tana cewa "Hajiya ina da magana gaskiya hukuncin da kika yanke akan Sameer bai dace ba a rasa wacce za'a 'ka'kaba masa duk yawan yan matan gidan nan sai Zakiyyah yarinyar da ba ganin girma na take ba bata ta'ba gaida ni ba tunda nake gaskiya bazai yuwu ba" caraf Mairo tace "dama uwar me Zakiyyah zatai da d'anki 'yata tafi karfin auren had'i kuma tafi karfin auren talaka irin Sameer" a masife Asabe tace "wallahi 'karya kike Sameer ba talaka bane duk samarin gidan nan ba wanda ya isa ya fad'a masa samun kud'i saidai Zaidu tunda shi yana koyarwa". "Au ashe dai da wanda ya fishi ai na d'auka shine millionaire gidan"?. "Dallacan gafara rufe min baki kafin na fasa shi wallahi baki isa jamila ta auri Sameer ba kin ji na rantse". "Kuma nima sai aka fad'a miki zan amince shi Sameer d'in na bari ya aure ta ne Allah ya tsari gatari da saran shuka yafi karfin wacce taba damu da zuwa islamiyya ba shiba jahila zai aura ba". "Kece babbar jahila jakar 'kauye" mi'kewa Asabe tai jin tana zaginta ita ma Mairon ta mi'ke zasu fara fad'a Hajiya tace "wallahi duk wacce tsautsayi yasa hannunta ya fara sauka akan d'aya yau saidai ta tafi gidan ubanta sakinta zansa ayi kuma kuyi fad'an na gani" jin abinda tace yasa kowa ta tsaya tana huci suna aikawa da juna mugun kallo. Ganin guri yayi shiru yasa Adama itama tace "nima fa wallahi ta Asaben Yusuf bazai auri Rasheedah ba" caraf Asiya tace "balle kuma ni wallahi bazai yuwu ba anfi cutar Zaidu a rasa dawa za'a had'a shi sai Zainab kusan sa'ar sa Allah ya sauwake gaskiya a duba wannan al'amarin abar kowa yaje ya nemo matar aurensa da kansa". "Ban bari kowa yaje ya nemo d'in ba hukunci na riga na gama yankewa babu wanda ya isa karya min ku tashi ku bani guri" ba wanda yayi motsi a cikin su Hajiya ta sake cewa "baku ji bane nace ku tashi ku bani guri" tashi sukai zasu fara tafiya Habibu yace "ku tsaya" kallonsa Hajiya tayi tana cewa "uban me zasu tsaya suyi maka" cikin nutsuwa yace "magana zamuyi ta fahimta Hajiya yadda kowa bai goyi bayan wannan hukuncin naki ba matu'kar akai aurarrakin nan masifa da fitina aka had'a baza su ta'ba zaman lafiya ba tunda kowa ba cewa yayi yana son kowa ba Hajiya mai zai hana ki bamu lokaci kowa ya tara 'ya'yansa muyi musu magana su fitar da mazajen aure suma samarin su fito da matayen aure ina ganin hakan yafi akan wanda kika fad'a ko ya kuka ce"? Duk kaurewa sukai kowa yana cewa "yayi a bamu lokaci gaskiya gara hakan" shiru Hajiya tai tana binsu da kallo daga baya kuma tace. "Shikenan na baku lokaci amma wallahi gaba bazan yi muku uzuri ba ko kuna so ko bakwa so idan na tashi saidai kuji an d'aura domin zanje gurin liman da kaina na masa bayani ko kuma nasa 'ya'yan naku ayi shelarsu masu son 'yan sadaka suzo su kawo sadaki". "Insha Allahu Hajiya hakan bazai faru ba". "Idan Kun kiyaye kenan naji fitsararrun matan naku suna wannan maganar zaka ce hakan bazai faru ba humm ina daidai da kowanne shege ku tashi ku bani guri na gaji da ganin ku" duk mi'kewa sukai kowa yana mata saida safe ko karasa kallon su batai ba balle ta amsa har suka fita karshe da zagi ta raka su daga 'ya'yan nata har surukan. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH Y♣M♣A PAGE 28 Washe garin da akai wannan rikicin da yake Zainab bata sani ba taje gaida Hajiya ai kuwa saida tayi dana sanin zuwa saboda irin maganganun data ya6a mata marasa dad'i shiyasa koda ta dawo kofarsu kawai ta shiga d'aki ta kwanta tunda ba school zata je ba gashi zazza'bi na neman rufe ta balle tace zatai d'inki harta lullu'ba barci yana neman d'ebeta ta tuna bataiwa Umma aiki ba da sauri ta tashi tana fita ta kallo gurin wanke-wanke ga sharar kofar ba'ai ba tsintsiya ta d'auka ta fara yin sharar sannan ta had'a kwanukan duka ta kai inda zata wanke ta ta had'a ruwan klin da wanda zata d'auraye ta wanke harda na Asabe da suke gurin takai mata d'aki kamar yadda ta saba sannan ta d'auke nasu ma daga gurin ruwa ta dafa zatai wanka ta zuba shi a bokiti har zata kai band'akin ta fasa ta tafi kofar d'akin ta dashi ta aje ta shiga d'akin sabulun wankanta ta bata ganshi ba dole ta d'auki hijab ta fita zata siyo wayarta na kan window ta kunna wa'azi bata kashe ba ta barta a gurin ta fita jinjina kai Bilki dake tsaye ta window tana le'kenta ta yi ganin ta fita ya sa da gudu ta fito daga d'akin su tana zuwa ta d'auki wayar Zainab d'in ta jefa ta a cikin ruwan bokitin da sauri ta juya ta koma d'aki tana dariya harda tsalle ganin shikenan ta lalata mata wayar tasan duk tsiya wannan wayar ta gama yawo domin kafin taje ta dawo ruwan ya gama ratsa ta. Da yake shagon kusa da gidan su ta ganshi a rufe yasa ta wuce d'ayan ta siyo tana shigowa gida kawai taga wayarta a cikin ruwan bokitin dake kofar d'akin zaro ido tai da sauri tasa hannu ta d'aukota ta fara gogewa ruwa har tsiyayowa yake ta cikin wayar tsananin mamaki ne ya kama ta taya za'ai wayar ta fad'o ta fad'a ruwa bayan acan cikin window ta d'ora saida idan wani ne ya jefa mata shiru tayi mugun takaici ya gama cika ta har hawaye ne taji suna taruwa mata a ido yaushe ta siya wayar duba sittin da biyar amma har zata lalace gwada kunnawa tayi amma ta rufe ta'ki bud'ewa d'aki ta shiga kawai hawayen ba'kin ciki suna zuba mata ta dad'e tana kukan ta sannan taga kukan ba magani zaiyi mata ba abinda ha'kuri bai baka ba rashin ha'kuri ma bazai baka ba Allah ne ya hore mata ta siya yanzu ma shi zata ro'ka ya sake hore mata duk ta tana zubin adashi a gurin auntyn ta Murjah taso ya kasance ita ce karshen d'auka amma yanzu dole taje ta kar'bo ta siya waya idan ba haka ba dame zata ri'ka assignment.................. "Zainab Zainab". Taji muryar Sameer yana kiran ta tashi tashi da sauri tana goge fuskarta ta fita yana tsaye a can wajen kofar d'akin sa kallonta yayi yana cewa "ina kika je naga kin wuce d'azu"?. "Na je siyo sabulu ne kuma na dawo kaga wayata nazo na tarar ta fad'a ruwa". "Subanallahi a ina kika barta harta fad'a ruwa"?. "Nidai akan window na tafi na barta dana dawo nazo na same ta a cikin ruwan da zanyi wanka dashi" jin abinda tace yasa Sameer yayi shiru yana kallon kofar d'akin Asabe babu takalminta amma yaga na Bilki zato zunubi koda ya kasance gaskiya amma ya tabbata Bilki ce zata jefa wannan wayar a ruwa saidai baya son data hankali shiyasa ya kalli Zainab d'in yana cewa. "D'auko min wayar mu gani" juyawa tayi ta koma ta d'auko masa ya kar'ba yana jin har lokacin da sauran d'umin ruwan a jikin wayar kai ya jinjina yana cewa "ok bari na kaita gurin masu gyara su duba miki Allah yasa ta tashi" amin Zainab tace shi kuma ya fita daga kofar yana fita Bilki dake d'aki ta kwashe da dariya wanda Zainab tana jinta bud'e labule tayi ta le'ko waje tare da yiwa Zainab wani tantirin kallo sannan ta sake labulen ta koma tana cewa. "Ya da min irin wannan kallon kar dai kiyi min sharri cewa nice na jefa miki waya dan nasan ku gadon munafirci ne ni nafi 'karfin 'karyar ki" jin abinda tace yasa Zainab kallon kofar kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta koma d'akin ta tunda tasan yanzu da tayi magana ko itace mai gaskiya ana zuwa gurin Hajiya zata yi mata tas a gaban kowa sabulu ta d'auko tazo ta d'auki ruwan har ya fara hucewa ta shiga tayo wankan ta ta fito dan ita sai yanzu ta tuna ma su Umma anguwa suka tafi. Sameer kam yana fita yaje bakin chemist d'insa ya d'auko mashin d'insa ya tafi gurin gyara mata yana tsaye me gyaran yana kunce wayar Aliyu ya kira shi gefe ya koma ya zauna akan mashin d'in nasa yana d'agawa yace "hello Marshall ya gari ya kake kwana biyu shiru lafiya dai"? Daga can 6angaren Aliyu dake zaune sanye da uniform d'insa na army ya saka photon Zainab a gaba yana kallo saida ya shafo fuskarta dake jikin photon ya sauke ajiyar zuciya sannan yace. "Alhamdulillah ko kaje wani wuri ne nake jin kamar kana guri me hayaniya"?. "Wallahi nazo wani waje na kawo gyaran waya ne". "Wayar wa"?. "Wayar Zainab ce". "Ok meya samu wayar"?. "Wai ruwa ta fad'a d'azu da safe shine ta d'auke ta'ki kawowa yanzu dai na bar me gyaran yana kuncewa yaga matsalar". "Ruwa kuma yanzun ta gyaru ko a'a dame take yin assignment d'in school"?. "A'a yau ne fa ta lalace ba dad'ewa akai d'azu da safe ne". "Ok amma ta gyaru ne ko ya duba bazata tashi ba"?. "Wallahi ban sani ba yanzu na bada ya kunce ta dai na dawo gefe sakamakon kira na da kayi". "Shikenan kuyi cinikin ta da me gyaran a haka ka siyar da ita zan baka kud'i ka siya mata wata sabuwa saboda aikin school d'inta". "A'a Marshall basai ka siya mata wata ba dan Allah ka barshi wannan d'in ma insha Allahu zata gyaru". "Na riga nayi niyya karka 6ata min niyya ta ba ro'ka tayi ba sannan kome na baiwa Zainab a rayuwa ba fad'uwa nayi ba abun alfahari zai zama gare ni idan naga tana amfani da kaya da na tabbata daga hannu na ya fita yaje gurin ta sannan a yadda nake jinta a zuciya ta ko raina ne zan iya bata indai zatai farin ciki da hakan" murmushi Sameer yayi yana cewa "na sani Marshall amma abubuwan ne sun yi yawa daga wancan kayi wancan shiyasa nace basai ka siya mata ba". "Sameer a gurin ka ne abubuwa sukai yawa amma a gurin Aliyu bai sa hannu akan hidima da Zainab ba tamkar banyi mata komai a rayuwa ba haka nake ji fatan ka gane"? 'yar dariya Sameer yayi yana jinjina kai yace "eh na fahimta ai dole na gane Marshall". "Ok zan turo maka kud'in saika sai mata wata d'in kawai" Sameer baya son yawan jayayya shiyasa da Aliyun ya dage saiya siya matan yace "shikenan ba damuwa ba matsala Marshall Allah ya kara bud'i" "Amin zai shigo yanzu insha Allah" yana fad'in haka ya kashe kiran shiru Sameer yayi kawai yana mamaki har baisan lokacin da yayi murmushi. Bayan sun gama wayar ko minti goma ba'ai ba Sameer yaji alert ya shigo wayarsa yana dubawa yaga Aliyu yayi masa transfer dubu d'ari biyu da hamsin zaro ido yayi a rud'e bai san lokacin daya danna kiran shi ba Aliyu na d'agawa yace. "Marshall wannan kud'in kuma fa sunyi yawa waya fa zan siya mata ba saniya ba" mi'kewa Aliyu yayi daga can 6angaren da yake da photon Zainab a hannunsa yaje ya mayar dashi inda ya d'auko batare daya baiwa Sameer amsa ba wanda Sameer duk zaton sa ko ya kashe kiran ne saida ya duba yaga ba katsewa yayi ba shiyasa ya sake cewa "hello Marshall kana jina"?. "Eh ina jin ka meya faru"?. "Nace wannan kud'in sun yi yawa a siyan waya kud'in me ka turo haka ko duk wayar za'a siya dashi"?. "Da kud'in me na turo maka kud'in wayar ne man ka siya mata me kyau ta dubu d'ari biyu da hamsin d'in nan dan Allah Sameer gara ta ri'ke babba wacce zata fi jin dad'in ta" kai Sameer ya girgiza yana cewa "amma Marshall.................. "Amma me? dan Allah Sameer kayi shiru kar kasa naji ba dad'i kayi abinda nace kawai sai anjima" yana fad'in haka ya katse kiran shiru Sameer yayi ya rasa wanne irin yanayi yake yanzu idan ya koma gida me zai cewa Zainab taya zaiyi mata bayani yadda zata fahimta waya bata 'karamin kud'i ba dole zata nemi jin waye ya siya mata anan ya zaice wacce kalma zai fad'a Aliyu ya jefa shia tunanin ta yadda zai iya kai mata idan ya siya da wacce kalma zaiyi furuci? Ganin bashi da amsa yasa ya tashi daga kan mashin d'in nasa ya koma gurin mutumin ya tambaye shi yaya batun wayar bayan mutumin ya duba wayar yace. "Mai gida saidai ka barta anan fa baza ta gyaru a yau ba da ruwa a cikin ta sosai" kai Sameer ya d'aga yana cewa "ok zan dawo na kar6a daga baya idan nazo saika fad'i kud'in gyaran na baka Allah yasa ta gyaru". "To ba damuwa insha Allahu zata gyaru karka damu". "Ok tom sai na dawo" Sameer ya fad'a yana zuwa ya d'auki mashin d'insa daga gurin me gyaran da ya tafi shagon saida wayoyi ya shiga ya siya mata sannan ya fita ya hau mashin d'in ya tafi gida da tunanuka kala-kala a ransa lokacin daya shiga kofarsu Zainab tana waje ta shimfid'a babbar tabarmar Umma tana yanka kayan d'inki ganin sa yasa ta aje almakashin tana cewa. "Yaya Sameer ta gyaru"? Kaiya girgiza yana karasawa inda take yace "Zainab wayarki baza ta gyaru a yau ba amma ga wata" da mamaki ta d'ago tana kallon ledar da yake mi'ka mata sannan ta kalle shi tana cewa "wata kuma Yaya Sameer ina kaga kud'in siyan wata wayar da ka bari an gyara min wancan d'in" kaiya girgiza yana kallon ta yace "bani na siya miki ba" jin abinda yace yasa Zainab d'agowa a firgice tace. "Waye ya siya"? Kai tsaye ya bata amsa "wanda ya biya miki makaranta ne" mamaki ne 'karara ya bayyana a fuskar ta har bata san lokacin da tace "wai Yaya Sameer waye wannan da yake min abubuwa me yasa baza ka fad'a min shi ba"? Murmushi taga yayi mata yana jinjina kai yace. "Lokaci ne baiyi ba Zainab idan lokacin daya d'iba yayi shi da kansa zai bayyana miki kansa basai na fad'a miki shi ba" shiru tayi zuciyarta na bugawa da 'karfi gaskiya wadannan al'amuran suna mugun bata tsoro taya wani zai ri'ka mata abubuwa na ban mamaki akan wanne dalili gashi Sameer da yasan komai ya'ki ya fad'a mata to waye zai fad'a mata bayan shi................ "Amshi" taji ya katse mata tunanin tsabar yadda ta'ki a gigice har wata 'yar zabura tayi tana kallon sa wayar yake mi'ko mata 'kin kar'ba tayi sai kai da take faman girgizawa muryarta har rawa yake tace "Yaya Sameer ka mayar masa kayarsa gaskiya bazan iya kar'ba ba tafi 'karfi na nagode". "Na mayar masa kuma? kema kinsan abinda bazai yuwa bane ba kyau mai da hannun kyauta baya kiyi hakuri ki kar6a dan Allah haba Zainab so kike wani yaji maganar da muke daga ni har ke mu shiga uku a gurin Hajiya domin sai tayi mana rashin mutuncin da kare bazai lasa ba sannan kinsan Bilkisu tana d'aki ita ma babbar masharranciya ce zata iya zuwa ta fad'awa Hajiya harda 'karin abinda ba'ai ba saita fad'a dan haka ki kar'ba kawai ina son zan koma chemist". Jin abinda yace yasa jiki a sanyaye tasa hannu ta kar6a tare da mi'kewa ta kai d'aki ta fito ta karasa yankan kayan da take yi sannan ta tashi ta koma d'akin kallon ledar wayar kad'ai tayar mata da hankali yake da'kyar ta iya fito da ita tana kallon photon wayar da yake jiki kwalin taga ga kud'in da aka siya nan dubu d'ari biyu da hamsin kamar za ta fasa ihun tsoro da'kyar hannunta na rawa ta bud'e ta ciro ta sai sha'ki take ido ta zuba mata hankalinta in yayi dubu ya tashi waye wannan mutumin wai meye haka ne ita fa ta rasa ganewa wannan al'amarin yaushe ne zata fahimta tasan Sameer bazai mata wasa ba kuma ba tsokanarta yake ba bashi da kud'in dazai ri'ka yi mata wadannan abubuwan tabbas akwai mai yi mata to abun tambayar waye shi a ina yake yaushe zata san shi meyasa yake mata hakan waye zai bata wadannan amsoshin? Ta tabbata ko Sameer ta tambaya bazai fad'a mata ba saidai yace akwai lokacin yaushe lokacin zai zo.............. Sallamar Umma ce ta katse mata tunanin da take yi alamar sun dawo daga anguwar gaba d'ayan matan gidan suka ji tashi tayi da wayar a hannunta ta shiga d'akin Umma a lokacin Umma ta cire hijab ta ajiye ganin ta da yanayin ta kamar bata cikin walwala yasa cikin fargaba tace "Zainab lafiya ko wani abu ne ya faru Hajiya tayi kiran ki ne"? Kaita girgiza a damuwance ta mi'ka mata wayar tana cewa "ga abinda ya d'aga min hankali Umma" kallo Umma tabi wayar dashi ba tare data kar'ba ba tace "wannan wayar kuma fa daga ina"? Jikin a sanyaye Zainab tace. "Yaya Sameer ne ya kawo min". "Sameer kuma ina taki wayar"? Numfashi Zainab ta sauke tana cewa "d'azu bayan fitar ku anguwa ta fad'a ruwa shine na bashi ya gyaro min kuma daya dawo maimakon na ganshi da tawa sai yace wai baza ta gyaru a yau ba amma ga wata" da mamaki Umma tace "ga wata kamar ya siya miki yayi"?. "A'a wai wanda ya siya min makaranta ne ya bashi kud'in ya siya min" zaro ido Umma tai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un wai dan waye wannan me miki wadannan abubuwan meyasa Sameer bazai fito fili ya fad'a miki ba wannan abun ya zarta hankali bari naje na kaina gurin nasa naji abinda yake faruwa" ta fad'a tana d'aukar hijab ta kar'bi wayar a sanyaye Zainab ta kalle ta tana cewa. "Yana chemist fa" Umma data gama saka hijab tace "eh ai can chemist d'in zanje" fita tayi ta bar Zainab shiru a d'aki ta rasa me yake mata dad'i. Umma kam da saurinta ta fita daga gidan kana ganinta kasan hankalinta ba'a kwance yake ba a lokacin da taje tayi sa'a kuwa shi kad'ai ne ba kowa da sallama ta shiga tana aje masa wayar tace "Sameer waye ya siyawa Zainab wannan wayar? Kace wanda ya siya mata makaranta ne haka ne"? D'an murmushi yayi yana d'aga kai yace "eh Umma haka ne d'azu wayar tace ta fad'a a ruwa na shiga gidan ta bani na kai a gyara mata acan yayi kirana a waya nace na kawo mata gyaran waya ne shine yayi transfer na siya mata wata na kawo mata nima da nasan idan nace wayarta ce ta 6aci zai zaice zai siya mata wata wallahi Umma bazan fad'a masa ba". Da alamar tambaya Umma tace "to wai Sameer waye shi"? Shiru yayi ya rasa me zaice mata domin bai da amsa ita ma Umman ta fahimci hakan sosai shirun ya ratsa gurin can ya d'ago yaga yadda ta 'kure shi da kallon jiran amsa numfashi ya fitar a hankali yace. "Umma aboki na ne kuma yana son Zainab ne amma yace baya so a sani yanzu sai ya tashi zaiyi auren zai zo ya bayyana mata kansa alkawari na d'auka masa cewa bazan ta'ba fad'a mata shi ba sai lokacin daya d'iba da kansa ya cika zuwa da kai yafi sa'ko sannan duk abinda da kika ga yana yi mata yace min bai saka hannu a cikin yi mata hidima ba shiyasa nake rasa abun cewa a duk lokacin da Zainab ta tare ni da tambayar waye shi dan Allah Umma kiyi hakuri bazan iya fad'a miki shi ba saboda alkawarin dana d'auka masa insha Allah yana nan zai zo gare ku" tunda ya fara magana jikin Umma ke rawa har ya kai karshe waye wannan yake son Zainab a ina yake dama sonta yake?.............. Kai ta girgiza tana sau'ke ajiyar zuciya mai 'karfi tace "kuma Sameer idan lokaci yayi ya bayyana tace ba ta son sa fa shine abun damuwar"?. "In sha Allahu Umma Zainab ba za ta 'ki ba saboda ina da tabbacin hakan ba za ta ta'ba juya baya ba za ta amince masa shine ya dace da rayuwar ta" kad'a kai Umma tayi ba tare da sanin abun dafawa ba tace "shikenan Allah ya rufa asiri ubangiji ya za6a mana abinda ya fi alkhairi a rayuwar mu bari na koma kawai" tana fad'in haka ta juya ta bar chemist d'in sansanyan numfashi Sameer ya fitar bayan ta tafi ya kira Aliyu. "Marshall akwai matsala fa dama na fad'a maka in dai na siya mata wayar ne dole zata nemi sanin waye kai kuma gashi hasashe na ya tabbata yanzun nan Umma ta bar chemist d'in nan tazo jin waye ya siya mata". "Kuma ka fad'a mata"?. "A'a taya zan fad'a mata bayan alkawari mu kai dakai cewa kaine da kanka zaka fad'a mata kuma saina karya maka alkawari". "Yanzu ka fad'a mata wani abu ta yadda zata fahimta ne"?. "Eh nayi mata kyakkyawan bayani nasan ta yarda kuma idan ta koma gida zatai wa Zainab bayani ita ma zata fahimta". "Ok yayi ina so ne saita gama school d'in idan ta samu offer ta fara aiki saina fito mata da maganar son ta sannan koma menene sai ayi kawai". "Allah ya yarda Aliyu muna godiya".. "Karka damu kaina nake wa domin ko me Zainab zata zama dai muna tare idan na aure ta sai ranar da kuka ganta idan na 6oye ta duk ranar da tazo gida baza ku gane ta ba saboda yadda kamannin ta zasu canza tayi kyau akan wanda take dashi ta 'kara haske tayi 'kiba sosai" dariya Sameer yayi yana cewa "Allah yasa Marshall zan fi kowa jin dad'in hakan wallahi har na matsu lokacin nan yayi Zainab ta zama matarka". "Na fika damuwa da hakan Sameer yanzu maganar nan da muke da kai ji nake kamar nayi tsuntsuwa nazo na ganta kawai ko zuciya ta zata samu salama daga tafasa da 'kaunarta take yi". "Lokaci ne yana nan zuwa". "Haka ne dalilin da yasa bazan sake zuwa gida pass ba sai ta gama school d'inta". "Ok tom Allah ya dawo da kai lafiya". "Amin na gode Sameer" yana fad'in haka ya katse kiran murmushi Sameer yayi yana aje wayar a gefe daidai wasu mutum biyu sun shigo ya tashi yana kallon a yadda aka ri'ko d'ayan da gani baida lafiya sosai.................. JGW STATE. ZUCIYAR ALIYU CE. @YUSRAH MUSA PAGE 29 Umma tana komawa a yadda ta bar Zainab a d'akinta anan ta dawo ta same ta tayi tagumi ta zubawa guri d'aya ido ko sanin tayi sallama ba tai ba saida ta kira sunanta sannan ta d'ago tana sau'ke ajiyar zuciya mi'ka mata wayar Umma tai tana cire hijab ta aje tare da zama ta kalle ta tana cewa "Zainab naje gurin Sameer yayi min bayani abokinsa ne yake miki wadannan abubuwan sannan yace min sonki yake amma ba yanzu zai bayyana miki kansa ki ganshi ba ni dai da ace akwai abinda zan iya yi gara koma waye ya fito mu ganshi tsoro na nan gaba Zainab kice bakya son shi bayan duk wannan d'awainiyar da yayi miki"? Shiru Zainab tayi ta kasa magana gaba d'aya bata san me zata ce ba waye abokin Sameer a ina yake duk iya zurfafa tunanin ta bata gano ko waye ba............. "Zainab" Numfashi ta fitar tana kallon Umma a sanyaye jikinta ba wani sauran 'karfi tace "na'am" ita ma Umman zuba mata ido tayi tasan tana cikin halin rud'ani ta yadda duk abinda zata fad'a mata ba lallai ta fahimce ta ba shiyasa kawai tace mata "tashi kije koma waye Allah yasa shine mafi alkhairi a rayuwarki idan babu alkhairi Allah kar ya shigo dashi cikin rayuwarki balle har a samu matsala nasan dama bazai wuce hakan ba domin ruwa baya tsami banza duba irin abubuwan da yake miki dole saidai so d'in ni kam Allah yasa kar Hajiya taji labarin siyo miki wayar nan tazo ta d'aga mana hankali" ita dai Zainab tari da bai kama ta ba bata yi ba 'karshe ta mi'ke ta fita daga d'akin tana jin yadda wani zazza'bin fargaba da damuwa ya lullu'be ta lokaci guda. *** ** *** Kwanaki sun sake ja lokaci yana ta tafiya abubuwa suna ta faruwa tun Hajiya tana fad'a da zage zage har tazo ta zuba musu ido taga iya gudun ruwan su so take su kaita bango rana d'aya ta fito tayi musu uwar watsi ta gigita musu lissafi daga iyayen har 'ya'yan nasu zata nuna musu duk abinda suke ji dashi nata yafi nasu idan rashin mutunci ne tun kafin a haife su ta iya idan wula'kanci da fitina ne ma duk saidai su biyo bayan ta. Tana zaune ita kad'ai babu kowa Zain ya shiga gaida ita yana zama ko ina kwana bata bari yace ba tace "Zaidu d'aga idon ka ka kalle ni nan" da yake d'an zamani ne tar ya d'aga idonsa ya zuba mata taci "Zaidu kuna son gani kalata a gidan nan kuna son ganin rashin mutunci na zan gwada muku ni ba tsohuwar kwantu kwan bace" da mamaki Zain yace . "Me kuma ya faru Hajiya"?. "Au meya faru kake tambaya ta"?. "To ya kike so nace Hajiya ke fa kina da d'orawa mutum laifi daga shigowa ta ko bari na gaida ke baki yi ba kin kama balbala min bala'i". "Dan ubanka ni nake balbala maka bala'in"? Shiru yayi bai amsa mata ba taci gaba "batu nake akan maganar aure dana had'a ku kai da Zainab har yanzu tsabar raini banji tsinannan da yazo yace min ya amince a cikin ku ba"? Wani irin kallo yayi mata jin abinda tace lallai ma Hajiyan nan da neman rashin zama lafiya take ta'be baki yayi yana cewa. "Ni dai banda ni a cikin su kiwa sauran dai amma ban da Zaid". "Uban wa ka fi"?. "Me kike nufi ni dai karki saka ni a cikin wannan shirmen banga mai yi min auren had'i ba wallahi". "Sai ni dan ubanka". "Kinsan Allah Hajiya bazan auri kowacce yarinya a gidan nan ba gara ma ki sani". "Ni kuma saina aura maka in yaso ana shafa fatiha ka furta mata kalmar saki". "Ai kuwa zan furta". "Da naci 'kwal ubanka wallahi" kallon mamaki Zaid ya bita dashi ganin tunda ya zauna take masa zagi na tsamar nama yace "wai ke Hajiya dan Allah haka ake rayuwa ne ke haka akai miki auren dole ne ko me da kika matsa sai munyi gadon ki kike so muyi ko me"?. "uban wa ya fad'a maka auren dole a kai min ni auren so nayi da kakan ku". "Kuma mu kike neman 'ka'kaba mana abinda ba mune mukai ra'ayi ba"?. "K'warai kuwa sakawa tace umarni na ne dole ka auri Zainab saina aura maka ita" kaiya jinjina yana she'kewa da dariya yace "waye zaki aurawa Zainab d'in amma dai bani ba"?. "To da ubanka zan d'aura idan ba da kai ba"?. "Caf lallai Hajiya wacce irin magana kike yi wannan mara dad'in ji kema kinsan abunda bazai yuwa bane wallahi. . "Kuma dan ubanka ni kake cewa caf fad'a min dalilin da yasa baza ka auri Zainab d'in ba"?. "Saboda babu soyayya tsakani na da ita kuma bayan haka ni ina da wacce nake so". "Yar gidan uban waye a ina take"?. "Yar gidan baban ta ce a sabuwar 'kofa suke da zama" yana rufe baki Hajiya tace "to wallahi bari kiji ko a gidan uwar wa take ba sabuwar 'kofa ba dole ka barta ka auri Zainab ko kuma ka had'a ka aure su duk su biyun ranar d'aya a cikin biyu ka za'bi d'aya ko rabuwa da wancan ko auren su biyun lokaci guda ina jin ka"? Ta'be baki yayi yana cewa. "Ni bani da 'karfin da zan auri mata biyu rana d'aya dame zan ji da yi musu lefe ko da kud'in sadaki ko kuma gini na da ban 'karasa ba? Gaskiya bazan iya ba". "To tunda haka ne sai ka bar waccan yarinyar ka auri iya Zainab domin gida bai koshi ba kaga ai baka isa ka d'auko mana yar wani gidan ka kawo ta ba so nake suma sauran su shigo nayi musu magana ku taru ku rufawa junan ku asiri idan ku 'ki humm abun bazai muku kyau ba". "To wai Hajiya ni ban gane inda kika dosa ba meye hakan ne wai"?. "Taya kuwa zaka gane abinda nake nufi ka tsaya kana min fitsara mara kunya kawai tashi ka bani guri kafin na buga maka wannan sandan" ta fad'a tana d'ago masa shi yasan ba 'karamin aikin ta bane ta buga masa d'in shiyasa bai sake magana ba ya mi'ke ya fita daga gurin Hajiya kofar su ya shiga a lokacin mamarsa tana d'aki yaje ya same ta. "Lafiya naga ka shigo ranka a 6ace"? Yana daga tsaye ba tare daya zauna ba yace "gaskiya Mama bazai yuwu ba bazan iya wannan masifar ba zan nemi transfer aikina na koma kaduna kawai" jin abinda yace yasa ta kallon sa da mamaki tace. "Saboda me zaka nemi transfer ana zaune 'kalau"? Bud'e hannu yayi cikin fad'a ya fara magana "ba kowa ba saboda Hajiya haka kawai daga na shiga gurin ta na gaisar da ita wai ta tsare ni da maganar aure dole saina had'a lefe na auri Zainab bayan ni ba sonta nake ba sannan tayi min girma sa'ata ce fa shekara ta ashirin da biyar ita da had'u dame na fita haka kawai za'a d'ora min aiki" zaro ido Asiya tai tana cewa. "Meee Hajiyan ce tace kayo lefe ka auri Zainab"?. "Eh man yanzu fa daga gurin ta nake fita zanyi amma wannan maganar data fad'a min yasa bana jin zan iya karyawa idan na fita shiyasa ma na dawo" a masife Asiya tace "kuturun ubancan akan wata shegiya zaka hana kanka sukuni wallahi bazai yuwu ba tashi kayi fitar ka babu wani transfer aiki da zaka yi sannan Zainab tunda baka sonta kar ka yarda su aura maka ita ko tsine maka zatai bazai bika ba dan naga Hajiya niyyar ta kenan idan kaci gaba da jayayya da ita". "Wai taya ma zatai min haka nifa ina da budurwa 'yar sabuwar 'kofa ce kuma ita nake so ba wai Zainab ce bana so ba ni auren had'i ne bana ra'ayi". "Ka daina wani 6ata bakin ka kana maimaita magana tunda baka so ba wani shege da zaiyi maka abi da baka ga dama ba ka manta da wata Hajiya ka daina tada zancen dan Allah yanzu nafi tunanin gigin tsufa ne yasa take yin duk wadannan abubuwan abinda za'ai kawai kayi wa babanku magana akai maka kud'in gaisuwa can sabuwar 'kofan kayi auren ka kawai shine magana ina ruwanka da wata Zainab yadda take ganin tana da ilmi gashi tana da hanyar samun kud'i ai raina naka arzikim zatai ko ka aure ta ba za ta baka daraja ba kayi tafiyar ka kaje ka karya ka manta da batun". "Ok tom shikenan Mama hakan zanyi kawai a wuce gurin nayi maganin ta" yana fad'in haka ya fita Asiya da tabi kofar daya fitan da kallo tsaki taja tana cewa "wallahi indai ina raye babu wanda ya isa ka auri Zainab a gidan nan idan guguwa suke bu'kata ni masifa ce zanyi maganin duk d'an iskan da yake neman saka ka Zainab cikin rayuwar Zaid haba dan jaraba mutum da ransa da lafiyar sa a nemi hana shi ya sha'ki iska me kyau" ta karasa maganar tana jan tsaki ji take kamar ta tashi taje ta yiwa Hajiya magana akam takura Zaid da take sai kuma ta fasa domin tasan sharrin ta yanzu Habibu yana dawowa zata had'a mata bom abinda batai bama saita fad'a. Ko da dare bayan sallar isha da Hajiya taga Habibu bai shigo ya gaida ita ba yasa ta saka akai mata kiran sa lokacin bai jima da dawowa ba ko wanka baiyi ba saboda gudun laifi yasa ya amsa kiran nata yana shiga da'kyar ta bari suka gaisa kamar wani zai riga ta tace "Habibu ashe har yanzu baku fi 'karfin 'ya'yan ku ba ace kamar ni Zaidu d'azu zai ciwa mutunci akan nace ya auri Zainab yana fad'a min wata banzar magana wai akwai wacce yake so 'yar sabuwar 'kofa ce"? Jin abinda tace yasa ran Habibu ya soma 6ata ya gaji da maimaita wannan maganar shiyasa yace. "Hajiya dan Allah tunda duk yaran nan basa son za6in da kikai musu ki barsu kowa ya za6o da kansa a gani na hakan zai fi zaman lafiya dan wallahi idan kika matsa akai auren ba bazai yi 'karko ba babu jin dad'i kullum ana cikin sasanto da rabiyar fad'a ne" kai Hajiya ta jinjina tana kallon sa ya d'auka ta gamsu da maganar da yayi mata ne sai kuma yaji tace. "Habibu kasan abinda kake fad'a kuwa na riga na yanke maganar auren nasu yanzu kuma ka zo min da batun wai wani Zaidu yana da budurwa kai ma abinda zaka ce min kenan baza kuyi abinda nace ba"?. "Ba haka bane Hajiya su fa yaran zamani ne dan Allah ki barsu kowa ya samo matar aure kar ki matsa ayi had'in nan za'a samu matsala ba karama ba gaba ce abun ji muddin hakan da faru sai anyi dana sani akan gagarumar matsalar da zata faru a gaba". "Matsala daga wajen ka kenan tunda naga alamar kaine baka so da ace ka tilasta masa ka nuna 6acin ranka ya isa ya tsalle maganar kane shi d'in banza amma kaima ka nuna baka bu'katar abinda nace shiyasa duk sauran ma suka juya min baya". "Ba haka bane Hajiya anan ina iya bakin kokari na duk dan a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin mu dake da kuma 'ya'yan mu kamar yadda muke a baya amma indai kika matsa sai anyi auren nan wallahi ba karamin ya'ki da tashin hankali za'ai ba bama ga yaran ba harma da iyayen su mata tunda ba so suke ba kina kallo ranar da kikai maganar ba wacce ta yarda" yana rufe baki Hajiya tace. "Duk tsinanniyar da bata so ku saketa ta bar gidan saita koma gidan su taje can tayi isar ta amma ba'a nan ba indai ina raye a wannan gidan ba shegiyar da zatai mulki" murmushin fitinar Hajiya Habibu ya saki ganin bata rasa abun fad'a ko za'a kwana ana zance yace "yanzu dai Hajiya me za'ai"?. "Me za'ai kake tambaya ta Habibu me nake so ayi kuwa bayan wanda na fad'a ko Zaidu baya so sai ya auri Zainab kana kallo yadda suka bar yarinya ta lalace wai itace harda koyarwa ga wani sabon salon 'karya da suka d'auko har wata makarantar boko take zuwa labari yazo min wayar hannunta ma ta dubu d'ari biyu da hamsin ce uban waya siya mata ta kafe a gida ta kama sana'a itace had'a man shampoo da baseline itace yin gireba tuwon madara tsami gaye gullisuwa da iloka tana bi tana rabawa masu shago suna mata balance d'in kud'in ta kamar wata ma'aikaciyar gwamnati ta manta da maganar aure tsabar shashanci kuma shi Abdullahi d'in ya sani amma saboda tana d'ora masa jari idan ya karye shiyasa baya so ta bar gidan sai anyi magana yace aure lokaci ne zan nuna masa cewa nata lokacin yayi ba tare daya sani ba zanje nasa a d'aura mata aure da duk wanda naga dama saiya dawo daga gurin sana'ar sa ya tarar anyi mata rakiya idan nayi haka zan gani zai zo ya hauni da fad'a ne ko kuma zai bita gidan auren nata yace a sake ta ne". "A'a bazai yi haka ba amma kema dan Allah Hajiya na ro'ke ki kar kiyi haka". "Kai karka dame ni sai na yi hakan idan kuma kana da ikon hana hakan sai na ji"?. "A'a mu umarnin ki muke bi duk abinda kike ce shi za'ayi ko muna so ko bama so" a she'ke Hajiya tace "a hakan ko duk kuna bin umarnin nawa kuka kasa saka y'ay'an ku su bi magana ta"?. "Ki yi ha'kuri Hajiya zan zauna da su za mu tattauna duk abinda muka yanke zan zo na fad'a miki kin ji"?. "Shikenan zan gani ai idan ma 'karya ka ke yi" kai Habibu ya girgiza yana mi'kewa yace "saida safe za mu yi magana da su ranar weekend" Hajiya batai niyyar magana ba saida taji abinda yace da sauri ta kalle shi tana cewa "yanzu kai ranar weekend zakai magana dasu har wani lokaci kake sakawa sai kace gwamna? To ni a gobe nake son kuyi meeting d'in ka gane"? Kaiya d'aga yana cewa "to shikenan Hajiya za mu yi yadda ki ka ce" daga haka bai sake cewa komai ba ita ma Hajiyan haka ya juya ya fita daga gurin ta kofar baban su Zainab ya tsaya yana sallama. "Assalam-alaikum Abdullahi ka na ciki ne"? Abba dake d'akin sa a zaune jin sallamar babban yayan na su yasa ya mi'ke yana d'auke labule ya le'ko ya na cewa "eh ina nan Yaya bismilllah 'karaso" ya fad'a ya na shirin kokawa yaji Habibu ya ce "a'a basai na shigo ba fito magana za mu yi" jin abinda ya ce yasa Abba baro kofar d'akin yana d'aukar takalman sa ya saka ya fito a tsaye ya same shi a gurin a kidi'ime ya ce. "Allah ya sa dai lafiya Yaya na ga kamar fuskar ka da damuwa"?. "Eh to lafiya ba lafiya ba dama Hajiya ce ta kira ni d'azu tana sake jaddada min aure tsakanin Zaidu da Zainab ko d'aya daga cikin su ba ya so sai anyi har ta na ikrarin laifin mu ne da ace mu na bin umarnin ta su ma ba za su juya ma ta baya ba yanzu ya kake ganin za'a yi"? Shiru Abba yayi ya na tunanin ta yadda zata su 6ullowa al'amarin can ya ce "to Ina ganin kawai abinda za'ai shi ne ka samu Zaidu d'in ka 'kara fad'a masa ni ma zan yi magana da Zainab kamar hakan idan mu kayi shi ne mafita daga mu har yaran a gurin Hajiya idan kuwa aka samu sa6ani dama zata ce ba mu so ba taya yaran za su so amma ya ka ce"? Jinjina kai Habibu ya yi yana cewa "tabbas abunda ya kamata ayi kenan kafin mu yanke hukunci shikenan Allah ya rufa asiri dama kiran da na yi maka kenan gara na fad'a ma ka tun yau kafin gobe da safe ka je gurin Hajiya ta ji labarin ban fad'a ma ka ba ta tsiyata ni" yana rufe baki su ka saki dariya dukkannin su saboda tuna yadda Hajiya ta sako su a gaba da fitina iri-iri ta na caza mu su kai Abba yace. "Ba damuwa Allah ya tashe mu lafiya" "Amin" Habibu yace ya na juyawa zuwa kofar sa shi kuma Abba ya koma d'akin sa har ya kwanta ya sake tashi zaune ya yi shiru ya na tunani tabbas ya na so yaga Zainab a d'akin mijin ta amma irin wannan auren had'in ba tunda ba su suke son juna ba akwai matsala koda Hajiya za ta ce ya goyi da bayan 'yar sa indai Zainab ba ta son auren Zain ba zai yarda ta takura kan ta ba saboda ya na sone tayi rayuwar aure mai cike da farin ciki a gidan auren ta ba rayuwar aure mai cike da 'kunci ba sauke ajiyar zuciya yayi ya na tashi ya sake fita kofar d'akin Zainab ya je ya tsaya yana cewa. "Zainab kin yi barci ne"? Jin muryar Abba yasa ta tashi zaune daga kwancen da ta ke ta na cewa "a'a Baba ido na biyu". "To maza ki zo yanzu d'aki na magana za mu yi" jin abinda yace yasa ta mi'ke tana d'aukar hijab d'in ta tace "to Baba ga ni nan" jin shiru yasa ta fahimci ya koma fita ta yi ko takalmin ta bata d'auka ba ta shiga d'akin nasa da sallama tana dur'kusawa cikin ladabi ta ce. "Ga ni Baba". Kallon ta ya yi zuciyar sa falda tunani yace "amm Zainab dama tambayar ki zanyi ki na da saurayi ne"? Ba tai tunanin abinda zai tambaye ta ba kenan shiyasa a firgice ta d'ago ba shiri ta na kallon sa shi ma yaga yadda ta firgita d'in da yatsa ya nuna mata wata farar kujerar roba dake kusa da ita ya ce "zauna a kan nan saboda kar kafin mu gama zancen 'kafar ki tayi ciwo" jiki a sanyaye ta tashi ta koma kan kujerar ci gaba Abba ya yi. "Ina fatan ba ki yi mamakin wannan tambayar da na yi miki ba saboda kin san da ajiyayyiyar maganar ko"? Kai ta d'aga a hankali ta ce "eh". "Yauwa yanzu kiran da Yaya ya yi min duk akan hakan ne Hajiya ta sake kiran sa ta yi maganar dole sai Zaidu ya aure ki amma ni ban isa na hana Hajiya abinda ta ga dama ba kamar yadda su Yaya ba su da ikon hakan sai abinda ta ce shiyasa na ga ya kamata na kira ki mu tattauna domin wannan al'amari ne mai girma kuma mai cike da sar'ka'kiya da 'kalubale yanzu ki na da wanda ki ke sone ko a'a"?. "Eh da akwai". "A ina ya ke"?. "Malamin islamiyyar mu ne". "To amma ya na zuwa gurin ki ne"?. "Eh ya na zuwa amma sai lokaci zuwa lokaci". "Da gaske da aure ya ke son ki ko kuma kawai zuwa ya ke"? D'an shiru ta yi kamar mai tunani ta rufe ido ta na sakin numfashi ta ce "kwarai da gaske ya ke so na". "Shikenan na fahimta amma duk da haka ba zan fad'awa Hajiya ba sakamakon ta na jin wannan labarin sai mun nemi nutsuwar mu mun rasa domin ta daina bari na huta har sai ta ga kin yi aure kin bar gidan nan ni kuma kullum ina tashi da dare yayin da kowa yake barci na tsaya tsayin daka nayi ta ro'kon ubangiji ya baki miji na gari wanda zai ri'ka ki da kima ya girmama ki kuma ya ji tausayin ki shiyasa ba na so ace Hajiya ta matsa akan auren ki da Zaidu domin tunda ya furta akwai wacce ya ke so kin ga an samu akasi" ya d'an yi shiru ya na kallonta sannan ya ce "shikenan ba komai dama dalilin kiran kenan tashi ki je" mi'kewa ta yi jiki a mace da'kyar ta iya ce masa "saida safe" kai ya d'aga ya na bin ta da kallo yace "Allah ya tashe mu lafiya". Fita ta yi ta koma d'akin ta amma tunanin maganar da su kai da Abba ya hana ta samun sukuni balle ta iya runtsawa sai juyi da ta ke faman yi har lokacin ya fara ja dare yana yi ba ta ji barci yazo mata ba 'karshe tashi ta yi ta fita tayo alwala ta zo ta fara nafila domin ta ro'ki ubangiji ya za6a ma ta abinda yafi alkhairi a rayuwar ta................... 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 30 POV AMIRAH Tun da Aliyu ya tafi Amirah ba tai kiran sa ko sau d'aya ba saboda ya 6ata mata rai sosai rashin sanar mata komawar ta sa gashi d'an zuwan da yake su gaisa da mamar ta wannan karon bai zo ba shiyasa ta d'auki niyyar har ya dawo ko shekara d'ari zai yi a can ba za ta ta'ba kiran sa ba dole ta koyi ri'ke mutunci da kimar ta matsayin ta na mace koda ace ita ce take son sa ba shi ne ya ke son ta ba duk inda aka san mace an san ta da kamun kai in dai ba ballagaza bace. Tana kwance a bedroom tana barci safe Aliyu ya yi ta kiran ta kusan kira uku amma ba answer sakamakon barci take sai da 'kanwar ta Nana ta shigo ta ga ana kiran ta 'karasawa ta yi ta duba ganin me kiran yasa ta d'an bubbuga pillow da ta ke kwance a kan sa ta na cewa. "Aunty Amirah Aunty Amirah ki tashi wai har yanzu ba ki tashi daga barci ba sai kiran wayar ki ake yi" juyi Amirah tai cikin muryar barci ta ce "waye ya ke kira na"? Sake kallon secreen d'in wayar Nana ta yi gudun kar ta yi mistake ganin dai Aliyun ne a rubuce yasa ta ce "Aliyu na gani" ta fad'a tana d'ago ma ta wayar zaro ido Amirah tai ta na cewa "Aliyu kuma duba min kira nawa ya yi"? Sake duba secreen d'in ta yi ta na cewa "kira uku ne kuma wannan ba number Nigeria bace" jin abinda ta ce yasa a zabure Amirah ta tashi zaune ta na cewa. "Mi'ko min wayar" mi'ka ma ta tayi jiki na rawa ta kar'ba ganin da gaske Aliyu ne ya yi mata kira uku yasa ta dafe kai ta na cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu ba lallai ya d'aga ba idan na kira shi amma bari na gani" gwada danna kiran nasa tayi ta shiga tana ta ringing ba'a d'aga ba dama ba ta jin a ran ta zai d'aga mata kiran har ta katse za ta sake kira ta ga nasa kiran ya shigo abun nema ya samu da sauri ta d'aga tana cewa. "Hello Aliyu barka da safiya" bai amsa mata ba sai tambaya da ya jefo mata "a ina ki ka aje wayar ki ina ta kira ba ki min picking ba"? Jin abinda ya ce yasa ta gyara zama ta na cewa "kayi ha'kuri dan Allah wallahi barci na ke saida Nansy ta shigo sannan ta tashe ni ban san ka na kira ba domin ko ringtone d'in ban ji ba". "Ok dama irin agogon nan da ki ka gani tun mu na Spain a lokacin da ki ka gama karatu kuma zan siya miki na manta ke kuma har mu ka taho baki tuna min ba d'azu na je shopping na gan shi, shi ne na siya miki amma guda biyu ne d'aya na ki d'ayan kuma ki kaiwa Afifah" jin abinda ya ce yasa ta zaro ido tana cewa "dan Allah Aliyu¿ Wow gaskiya na gode sosai wallahi naji dad'i Allah ya saka da alkhairi". "Amin". "Yaushe za ka dawo kenan"?. "Ba yanzu ba bayarwa zan yi a taho muku da shi da akwai wani aboki na d'an Lagos ne zai taho kwanan nan zan ba shi ya taho da su idan ya zo gida daga nan zan bashi number ki da address sai ya baiwa masu mota a taho miki da shi idan ki ka d'auki na ki saiki kaiwa Afifah d'ayan" kaita d'aga tana murmushi cike da jin dad'in yadda ya nuna ma ta kulawa ga abinda ta dad'e ta na so ta ce "Allah ya 'kara arziki na gode Aliyu na gode sosai da kulawar ka gare ni". "Ba godiya tsakanin mu" ya na fad'in haka ta ji wayar tace d'it d'it alamar ya katse kiran sauke numfashi tai tana kallon agogon dake bangon bedroom d'in nata ta ga 'karfe goma da rabi na safe tashi ta yi ta sauka daga gadon ta shiga toilet tai wanka da brush ta fito ta shirya ta fita zuwa parlor ba kowa shiyasa kawai ta wuce dinning ta yi breakfast daga nan ta mi'ke ta d'auko mayafinta ta tafi gidan su Afifah domin ba za ta iya ha'kuri har sai agogon ya zo ba gara tayi mata albishir tun kafin zuwa kyautar ta na shiga kuwa tayi sa'a da yake weekend ne duk su na parlor harda Daddy da sallama ta shiga bakin ta ya'ki rufuwa tsabar farin cikin da ta ke ciki zama ta yi tana gaisar da Daddy ya amsa sannan ta gaida Momy ganin su na gurin yasa ba ta fad'awa Afifan ba ta bari su shiga bedroom kawai wayar ta ce a hannun ta tana chatting har Daddy ya tashi ya bar parlon sai lokacin ta samu damar d'agowa tana kallon Afifah wacce ke gefe d'aya ta na haddar karatu ta ce. "Afifah albishirin ki"¿ Da mamaki Afifah ta d'ago ta na kallon ta tace "albishiri na kuma ni Afifan"¿ kai Amirah ta d'aga da murmushi tace "eh ke Afifan man please ki ce min goro dan Allah wallahi abun dad'i zan fad'a mi ki dalilin zuwa na ma kenan". "Ok goro fad'a min ya akai"¿ Gyara zama Amirah tai ta na cewa "d'azu mu kai waya da Aliyu ya ke fad'a min ya siya ma na wani agogo ni da ke" da alamar tambaya Afifah tace "ban gane ba wanne irin agogo kuma"?. "Agogo dai irin wanda ki ka sani na kwalliya". "Kuma shi Yaya discipline d'in ne ya ce miki har da ni ya siya ko ke ce ki ka fad'a"?. "A'a shi ne ya fad'a min dama tun mu na Spain na ga agogon na ce masa ina so to ya manta bai siya min ba wai sai d'azu ya je shopping ya ganshi shi ne ya siyo su guda biyu ya ce zai baiwa wani abokin sa d'an Lagos ya taho da shi idan yazo daga Lagos d'in zai bashi number ta da address sai a sako a mota a kawo ma na" d'an zaro ido Afifah tai ta na cewa. "Kai da gaske"?. "Da gaske man". Murmushi Afifah tai ta na girgiza kai ta mayar da hankalin ta kan littafin dake hannunta ta na cewa "ni kam jin wannan maganar na yi kamar tatsuniya zan yarda ne kawai idan na ga sa'kon ya zo" tana fad'in haka ta ci gaba da karatun ta kallon ta Amirah ta yi ta na cewa "amma dai kin san Aliyu ba ya 'karya ko ya ta'ba miki alkawari ya sa6a"? Kai Afifah ta girgiza ba tare da ta d'ago ba ta ce "ni na fad'a miki kar ki had'a ni da shi na shiga uku kawai dai mamaki na yi sakamakon jin abinda ki ka ce min" Afifah na rufe baki Elham ta ce. "To idan haka ne me ya sa mu bai had'o da mu ba sai iya Aunty Afifah"? D'an ta'be baki Amirah ta yi tana cewa "wannan kuma shi za ku tambaya ni kam iya sunan ta na ji ya kama". "Ke ma dai Elham da kayan haushi ki ke bayan kin san waye Yaya boss me ye abun cewa bai had'o da mu ba dama za mu had'a kan mu da su ne"? Fati ta yi maganar ta na kallon yadda Amirah ta ke wani kad'a kai ta na yau'ki alamar su ne na gaban goshi a gurin Aliyu su ne masu lokaci da su ya ke ra'ayin sa kai Elham ta jinjina ta na cewa. "Na san da haka amma ya kamata a ri'ka yin abinda 'kuda zai bi". "Kar ki wani d'aga hankalin ki idan ya kawo mu su mun ga kalar sa sai mu fad'awa Daddy mu kuma ya siyo ma na dad'in abun mu na da uba balle mu yi kuka". "Ke Elham dama mu sa'annin ki ne da zaki nemi dole sai an yi miki abinda a kai mana"? Jin abinda Amirah tace yasa Elham kau da kai ba tare da ta amsa ma ta ba domin ta san ba mutunci gare ta ba yanzun nan sai ta kwakkwara ma ta ashar ba kunya ko a gaban Momyn ne balle ba ta nan ta tashi. Ba wanda ya sake magana ma akan hakan har Momy ta fito tare da Husnah su ka fita anguwa ta bar iya su kad'ai mi'kewa Amirah ta yi akan kujerar da ta ke three seater ta saka pillow kujerar ta kwanta ta koma barcin ta............. J.W.A ZUCIYAR ALIYU CE **** YUSRAH ** MUSA **** @YMA DUTSE JIGAWA PAGE 31 Yau Zainab ba da wuri za ta tafi school ba shi yasa ta rage d'inkunan mutane kafin ta tafi sai da akai kiran sallah ta tashi ta yi wanka ta yi sallah ko abinci Asabe ba ta gama had'awa ba da yake Sameer ya siyo mata katon d'in biscuit da lemo wani lokacin da shi ta ke tafiya idan ta dawo ta ci abincin bayan ta gama shiryarwa ta shiga d'akin Umma ta yi ma ta sallama ta fita har za ta wuce 'kofar Hajiya amma sakamakon ta san in ba ta shiga ta gaida ita ba sai ta yiwa Umma shi ya sa kawai ta shiga a waje ta same ta ta shimfid'a sallaya ta zauna akai da radio a gefen ta ta na sauraron labarai 'karasawa ta yi ta dur'kusa har 'kasa ta ce. "Hajiya ina yini"¿ Kallon ta Hajiya ta yi ta kalli school bag d'in ta da littafin dake ri'ke a hannu ta kamar ba ta san inda za ta je ba tace "ina za ki je na gan ki da littafi har da jaka ko D'an Yanan zaki koma"¿ Girgiza kai Zainab ta yi duk da ta san gatse Hajiyan ta yi mata amma sai ta ce "a'a makaranta zan ta fi" humm hali a jikin rai ta na rufe baki Hajiya ta ce. "Yanzu ke Zainab an ya rayuwar da ki ka d'aukarwa kan ki hakan a gare ki daidai ne wannan rayuwar ki ka za6a a ganin ki makaranta tafi aure makarantar da ki ke zuwa ba za ta kankaro mi ki da mutunci ba amma aure fa" shiru Zainab ta yo kan ta a 'kasa ba ta iya cewa komai ba domin ba ta san me za ta ce ba Hajiya ta ci gaba "Fad'a min idan kin gama karatun kuma fa me za ki samu wanne ci gaba zai kawo mi ki ko wata tsiya aka ce miki za ki samu idan kin yi karatun ko kishi kike da su Zaidu to ai su maza ne iyali za su ri'ke ke kuma da zaki auri wani me za ki yi"? Har lokacin Zainab ba ta iya cewa komai ba. "To bari ki ji wallahi tallahi na rantse da Allah idan tsautsayi yasa ki ka d'aukowa mutane abun kunya sai kun bar gidan nan ke da uwar ki ba za ku sa duniya ta zage mu ba tunda baki da aiki sai shige da fice ki na cud'anya cikin samarin banza duk ranar da na ji labarin ciki a tare da ke na lahira sai ya fi ki jin dad'i da kaina zan kira mi ki hukuma su tafi da ke su yanke miki hukuncin kisa domin shi ne ya dace da ke wai wanne irin shashanci ne wannan so kike sai kin zama tsohuwa kin diddige sannan ki auri tsoho ko kuma sai kin yi shekara talatin a gidan nan baki tafi d'akin mijin ki ba fad'a min ko Dan a jinin ku masifar take yayarki Murjah ma kafin ta fidda miji saida mu ka sha wahala kuma ke ma gashi duk hud'ubar Hauwa ce dad'in abun ma Allah ya rufa asiri daga ke ba wani gara da bata hayayyafa sosai da mu ba haba me za'ai da ba'kin gado gadon tsiya irin wannan wallahi gara da yaran da ta haifa duk suka mutu ku biyun da ku kai saura gashi kun zame mana annoba d'aya ta wuce saura ke". Sosai idon Zainab ya cika da hawaye sosai kawai ta yi shiru ta na saurarar Hajiya wacce ita ma daga haka ba ta sake cewa komai ba. "Ba ki gaji da zama a gaban nawa bane ko me tashi ka ban guri idan kin ga dama kar ki yi auren ki ci gaba da karatu har sai kin ga 'karshen biro da takarda 6acewa gani na" mi'kewa Zainab ta yi jikin ta babu 'karfi balle 'kwarin gwiwa ta fita ta na sharar hawaye had'uwa su kai da Sameer ya shigo ganin ta tana kuka yasa ya ce. "Zainab me ya faru lafiya kukan me ki ke"? Kai ta girgiza ba tare da ta yi magana ba sake kallon ta ya yi yana cewa. "Ki fad'a min mana"?. "Ba komai Yaya Sameer ni da Hajiya ne ka ga kuwa wannan sababban abu ne tsakanin mu ba wanda za'a yi tambaya a kan sa bane" tsaki ya ja yana cewa "dama na san sai dai Hajiyan gaskiya wannan tsohuwar ta na da matsala a rayuwa humm yanzu school za ki tafi"?. "Eh". "Ok ba damuwa kar6i" ya fad'a ya na zaro mata dubu d'aya a aljihun shi har za ta yi magana sai kuma ta fasa kawai ta kar6a ta yi masa godiya saboda ya sha fad'a mata idan ya ba ta ba ya so ta ri'ka cewa a'a tun da ba shi ya ke bata ba ciki ya shige ita kuma ta fita. YUSRAH YMA DUTSE ** * ** WRITER Yarima Abdul-maleek D'an millionaire Safreeyyah Royalty Minister Ashraf Me kamar sarki And now Zuciyar Aliyu ce Later 👑Yarima Aryan👑 @DUTSE YMA JIGAWA PAGE 31 Sakamakon yau weekend ne ba ranar aiki bace kuma Baby ta tabbata idan ta kira Shareef ba lallai ya d'auki kiran na ta ba shi ya sa ta yanke shawara kawai bari ta je gidan nasu domin tasan gidan wata rana an tashi daga asibiti ta bi bayan sa a mota ta ga gidan su ta so fad'a masa tsoro ya hana ta shi ya sa yau ta ke so ta yi masa bazata. Shiryarwa ta yi duk da zuciyar ta tana d'ar-d'ar ba ta san wanne irin kallo zai yi mata ba idan ya gan ta a gidan su sai dai takai ma'kura ne ta kasa jurewa da shariyar da ya ke mata son sa ya na neman yi mata illa amma daga zarar ya ga ta fara zuwa gidan su ta na yiwa mahaifiyar sa alkhairi komai d'auke kan sa dole ya dawo ya kula ta kuma ya so ta 'karshen zancen ya aure ta wanda hakan shine babban burin ta. Ba ta je da mota ba kawai napep ta hau ta gidan a lokacin iya Mami ce a parlon tana zaune ta ji sallamar Baby. "Assalamu-alaikum" d'agowa ta yi tana kallon ta tace "Amin alaiki salam shigo man" karasawa shigowa parlon ta yi tana dur'kusawa cikin tsananin ladabin neman gurin zama ta ce "ina yini Mami"?. "Lafiya kalau". "Dan Allah nan ne gidan su Shareef"?. "Eh nan ne Allah ya sa lafiya"? Numfashi Baby ta sauke ta na cewa "eh lafiya dama na zo gaishe da ke ne". "Ok ayya to sannu na gode ki zauna mana ki ka dur'kusa tashi ki zauna" daga can inda ta ke ta baro ta karasawa shigo ainihin inda Mamin ta ke ta zauna tana d'an kallon gidan Mami kuma ta mi'ke ta na cewa "bari na dawo ina zuwa" hanyar kitchen ta wuce Baby kam ganin ya rage sai ita kad'ai kai ta jinjina tana ri'ke baki tace. "Tabd'ijan dole Shareef ya ri'ka d'age min kai ya na wulakanta ni ashe d'an manya ne kalli gida dan Allah kamar wanda akai ginin da diamond humm ai kuwa na ga gurin zuwa wallahi daga yau na saka d'ambar kawowa mahaifiyar ka ziyara har sai ka amince min na zama surukar gidan na............... Shiru ta yi jin takun tafiya yasa ta nutsu Mami ce ta dawo tana zama ta kalle ta tana cewa "yi ha'kuri na bar ki ke kad'ai na shiga kitchen ne gurin me aiki" kan Baby a 'kasa ta'ki d'agowa ta fuskanci Mami dan Mamin tace tana da kunya a sanyaye tace "ba komai Mami". "Amma ba ki fad'a min daga inda ki ke ba"?. "Daga tudun yola na ke ni abokiyar aikin Shareef ce hospital d'in mu d'aya to kullum yana yawan bani labarin ki da irin son da yake miki shine nace bari na zo na ga Mamin nan nasa na kawo miki ziyara" kai Mami ta jinjina ta na murmushi tace "masha Allah gurin ku d'aya ke nan gaskiya na ji dad'i sosai kuma na yi farin ciki ashe har a hospital an san ni"?. "Mun sanki sosai Mami saboda yawan ambaton ki da ya ke yi koda yaushe yace Mami komai Mami duk wani motsin sa Mami za ki ji ya ce gaskiya kin yi dace wallahi Shareef d'a ne na gari mai kishin iyaye mai son walwalar su". "Ai haka yake ko a gida ma bashi da motsi sai ni ina matu'kar alfahari da shi". D'an shiru Baby tai tana kallon photon sa dake manne a parlon yayi kyau sosai numfashi ta sau'ke tana cewa "amma Mami sai yaushe zai yi aure"?. "Ban sani ba domin ina tunanin ko budurwa bai da ita har yanzu ni dai ina so ya kawo 'yata gidan nan amma har gobe idan na yi masa magana sai dai yace akwai lokaci ko sai yaushe lokacin zai zo oho". "Ai Mami yadda Shareef ya ke da d'auke kai gaskiya zai dad'e bai yi budurwa ba balle ya yi aure saidai idan ku ne za ku yi masa domin ko kallon 'yan mata ba ya yi balle ya samu wacce za tai masa shawara kawai ku ne zaku matsa masa". "Wannan gaskiya ne mu na ta zance baki fad'a min sunan ki ba"?. "Suna na Humairah amma Baby ake ce min kowa da haka ya san ni shi kan sa Shareef d'in idan ba Baby ki ka ce masa ba bai san ni da Humairah ba" kai Mami ta jinjina daidai Rabi ta fito da kaya a hannun ta daga kitchen ta zo ta aje kallon ta Momy tai tana cewa. "Kawo mata nan muna zance ba sai ta je dinning ba" to Rabi ta ce tana d'aukowa daga can take kawo gaban Baby ta aje ta bud'e fridge ta d'auko mata juice da ruwa shi ma ta aje sannan ta koma kitchen d'in. "Bismilllah Baby ga abun ta6awa nan ki ci" kai baby ta girgiza tana cewa "a'a alhamdulillah na gode tafiya ma zan yi". "Ah ya tafiya kuma mu na 'yar hirar mu ki bari sai zuwa jimawa man" gyara zama Baby tai domin dama ba niyyar tafiyar ta ke ba kawai dai kar Mami d'in ta ga za'kewar ta ta yi yawa shi ya sa ta ce hakan amma tun da ta bu'kaci ta ci gaba da zama bari ta zauna d'in. "Amma Mami na ce kamar Shareef ba ya gidan nan ko"?. "Eh ba ya nan ya je anguwa tun d'azu ya fita". "Zai dad'e ne kafin ya dawo"?. "Eh to maybe ya jima d'in dan fitar ta sa sa'a ce yanzu zan iya ce miki ba zai dad'e ba sai kuma ya dad'e d'in ko kuma na ce zai dad'e ki ga ya dawo haka na ke fama da shi" kai Baby ta jinjina ta na d'an sakin murmushi tare da mi'kewa ta ce "bari na tafi Mami sai na sake dawowa". "Ba za ki tsaya ya dawo ba"?. "A'a ba sai mun had'u ba kawai dama bazata na so nayi masa sai dai ma had'u a hospital ranar Monday". "Ai da kin tsaya amma dai ba damuwa na gode sosai Baby na gode Allah ya yi miki albarka". "Amin Mami ki huta lafiya sai wani lokaci". "To ki gaida gida sai na gan ki". Fita Baby ta yi tana sake waigowa ta kalli gidan kamar kar ta tafi haka ta ke ji saidai ba za ta so Shareef ya dawo ya same ta a gidan ba in dai ba so take ta shiga uku ya yi mata wula'kanci ba Allah ya sa hakan ma kar ya tare da maganar ta zo gidan su ranar Monday ko kuma ya yi mata iyaka da gidan. Numfashi ta sauke lokacin da ta fita daga gidan ji ta ke kamar ta fita daga wata ni'ima ne gaskiya ba ta san wanne irin azababben so ta kewa Shareef ba tana tsoron kar son sa ya zama ajalin ta tsaye ta yi a bakin titi kawai ta na kallon anguwar daga baya kuma ta tsare d'an napep ta shiga ta tafi. Barin ta anguwar bai fi da minti talatin ba Shareef ya dawo gida sai dai ya ji mamakin yadda ya ga Mami tana bin sa da wani kalar kallo daga baya ya ga ta yi murmushi ta na d'an girgiza kai kallon ta ya yi yana cewa. "Mami akwai magana a bakin ki ko"? Kai ta jinjina tana cewa "kwarai ma kuwa maganganu masu yawa". "Me ya faru"?. "Ai d'azu bayan tafiyar ka nayi ba'kuwa". "Ba'kuwa dai"?. "Eh man". "Amma daga ina ta ke"?. "Ta ce min hospital d'aya ku ke aiki kuma ka na yawan yi mata zance na shi ya sa tace bari ta zo ta gan ni ta gaida ni". "Ni d'in da yaushe na ke maganar ki da wata a hospital har ta zo gidan nan ba tare da na sani ba"?. "Ce min ta yi bazata take son ta yi maka ba nacin da ban yi akan ta jira ka dawo ba ta ce a'a tafiya za ta yi". "Wacece wannan yarinyar Mami"?. "Ta ya zan san ta Shareef bayan ko ta'ba ganin ta ban yi ba sai yau" shiru ya yi yana tunani shi fa ba ya kula 'yan mata a hospital wacce ma'karyaciyar aka samu ta zo gurin Mami ta yi masa sharrin ya na zancen ta idan ya je ko dai Baby ce? Ya tambayi zuciyar sa ai kuwa ba wacce za ta yi masa haka sai ita amma me yasa ta yi masa hakan wannan yarinyar muguwar 'yar rainin hankali ce wato ta nan ta 6ullo masa uban wa ya fad'a mata address d'in gidan su har ta zo ta shirga masa 'karyar da bai san ya yi b..................... "Shareef ka na lafiya"? Yaji muryar Mami ta katse shi kai ya jinjina "eh Mami lafiya ta 'kalau me ne sunan yarinyar da ta zo d'azun"? Dariya Mami tai tana kallon sa tace "dama na san sai haka ta ce min Humairah sunan ta amma am fi sanin ta da Baby" hummm hasashen sa ya zamo gaskiya kenan wato Baby ce dai ta zo ai kuwa zai gyara mata zama dole ya gargad'e ta ya taka mata burki kar ta sake wannan gangancin in dai ta na son zama lafiya. "Na fahimta Mami ziyara ta kawo miki kenan ko ni tace miki ta zo nema"?. "A'a ziyara ta kawo min ta ce saboda yawan ambato na da ka ke yi yasa tace ita kuma sai ta zo ta gan ni" Mami na rufe baki Shareef ya furzar da iska ran sa ya soma 6aci jin 'karyar da ta zo ya yarfa sai dai ba ya bu'katar Mami ta fahimta kar ta yi tunanin ko da akwai wani abu a tsakanin su bari kawai ya share hakan zai fi, bai sake magana ba duk da abun yana ran sa kuma ya yi 'ko'kari ya danne ya fuskanci Mami su ka ci gaba da hirar wani abu can daban kamar yadda koda yaushe su ke yi domin ba ya so ta sake masa magana akan Babyn ko da nan gaba ne. J♠W♠A Sayyidah Fad'imah R.A ❤️Ahlin girma mafi tsarki Nana Allah ya kadaita ki babu me matsayi irin naki Nana gashi mijin ki ne zaki Haidara sirrin ma'aiki na❤️. ** ** =====♣YUSRAH♣===== @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 32 Zainab tana kwance a d'akin ta misalin 'karfe tara zuwa da rabi Umma ta shigo d'akin tana tsayawa a jikin keken d'inkin ta tace "Zainab har kin kwanta baki ci abinci ba"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa "yau abincin ne bana son ci". "Ke nan a haka za ki kwanta da yunwa"?. "A'a Yaya Sameer na ke jira ya shigo na ba shi kud'i ya siyo min awara kuma har yanzu na ji shiru". "To ai shi Sameer ya shigo ya d'auki abincin sa ya sake fita" tashi zaune ta yi tana cewa "to gaskiya ban ji shigowar sa ba ne". "Eh lokacin ki na sallah ne daman kuma ba zama yayi ba ya juya dan dama abincin kad'ai ya zo d'auka ko d'akin sa bai shiga ba" jin abinda Umma ta ce yasa Zainab mi'kewa dan ta san ba sake shigowa zai yi ba sai lokacin kwanciyar sa yayi hijab ta saka tana cewa "bari na je ya raka ni na siyo kawai na dawo" ta fad'a tana d'aukar kud'in ta fita daga 'kofar ta su Umma kuma ta koma na ta d'akin. Tayi sa'a kuwa ba ta had'u da kowa ba daga samarin gidan har 'yan matan ba kowa saidai shagon 'kofar gidan yana bud'e yayan Rasheedat ne a ciki shi ma kuma ba ganin ta ya yi ba wucewa ta yi ta 'kara gaba kad'an ta had'u da Sameer shi kuma ya na tahowa gida tsayawa ya yi yana kallon ta da mamaki ya ce "dama ke ce na yi tantama farkon da na hango ki na san babu abinda zai fito da ke 'karfe goma ta kusa ina zuwa yanzun"?. "Yaya Sameer dan Allah ka raka ni na siyo awara a can layin kar na kwana da yunwa har na kwanta naji ba zan iya ba dama ina ta jiran ka sai da Umma ta shiga d'aki na yanzu ta ke fad'a min har ka shigo ka d'auki abincin ka". "Eh ai na le'ka d'akin da ki ke na ga ki na sallah ne shi ya sa na fito abinda aka dafa d'in ne bakya so"?. "Ai ni Yaya Sameer ka san ban damu da tuwon shinkafa ba bana son shi". "Ok jira na zo mu tafi" ya fad'a yana shiga gidan ita kuma ta koma gefen hanya ta tsaya jiran sa ya d'an jima sannan ya fito suka wuce daidai Haulat ta sauka a Napep ta ga giftawar su iya Zainab da hijab d'in ta ta gane amma tsabar gulma ko tsayawa ta ga tare da Sameer take ba ta yi ba da sauri ta sallami mai napep ta shiga gida kamar zata tashi sama haka ta fad'a kofar Hajiya 'kwalla mata kira "Hajiya Hajiya kina ina Hajiya yau na ga abinda ya fi 'karfin ido na ki na ina ne Hajiya"? Hajiya dake d'aki a zaune jin kira kamar zata tsaga gidan yasa ta mi'ke tana cewa "ga ni 'yar jarabar kira me ye hakan ne zaki zo ki na min kira na d'aga hankali"? Da gudu Haulat ta fad'a d'akin tana cewa "Hajiya albishirin ki yanzun nan na ga Zainab ta yi bayan layin nan tare da wani namiji Ina tunanin ma kamar shi ne kwarton na ta da take zuwa gurin sa kullum da dare yana iskanci da ita yana bata kud'in da take kashewa" zaro ido Hajiya tai tana cewa "kwarto kuma mun shiga uku ke Haule ba na son 'karya fa a ina ki ka gan ta"?. "Ba fa 'karya na ke miki ba Hajiya da ido na na gan ta su na tafiya ita da shi sun yi wancan layin nan ki zo muje kar suyi nisa" jiki na 6ari Hajiya ta d'auki mayafi takalmin ma ba iri d'aya ta saka ba kowanne daban-daban ne suka fita tare da Haulat a lokacin fitowar Rasheedat daga kofar su kenan ta hango su suna sauri za su yi kofar gate da gudu ta taho tana cewa "Hajiya ina zuwa haka ko anguwa za ku je na zo nima na raka ku"? Jikin Hajiya ya na mazari tace "ina wata anguwa Haule ce ta ga Zainab sun yi bayan layin nan tare da wani kwarto shi ne ta fad'a min can za mu tafi" zaro ido Rasheedat tai tana cewa "kai kwarto kuma bari mu ma mu je kar mu tsaya a bamu labari gara ayi komai a gaban mu" bin su ta yi su ka fita daga gidan daidai Zaid shi kuma ya na shirin shiga tsayar shi Hajiya tai tana cewa. "Yauwa Zaidu gara da mu ka had'u da kai dama dole sai dai mu je tare da namiji dan abun ya fi 'karfin mata" tsayawa Zain ya yi yana cewa "me ya faru Hajiya ina za ku je a haka". "Wai Zainab ce ta bi wani saurayi su kai bayan layin nan Haulat ce ta gan ta yanzu can za mu je taho dan Allah ka raka mu yadda za ka kama tsinanne ka yi masa duka ka sumar da shege" kai Zain ya jinjina yana cewa. "Shi ke nan mu je" wucewa su kai su na tafe Hajiya sai fad'a ta ke tana zage-zage Zaid da ke murmushin jin dad'i yace "kin ga Hajiya ta nuna miki wace ita ashe dama 'yar iska ce ki ke so na aure ta ta zama uwar 'ya'ya na"?. "Taya na san 'yar iska ce ba dan yau da asirin ta ya tonu aka gan ta ba waye ya san tana zuwa gurin samari da dare ba na jin uban ta ya san da wannan labarin amma uwar ta zata sani tunda ba uwar arziki ba ce watakil ma ita ce ta ke saka ta yawon dan ta ri'ka samar mata kud'i tun da ba sana'ar uwar komai ta ke yi ba". Kai Zaid ya jinjina ya na cewa "humm ai kuwa sai na gasa mata magana wacce za ta saka ta kasa jin dad'in zaman duniya bari mu je gurin dama ai nasan munafirci ne ya sa ta ke saka wannan nikaf d'in ba dan ta tsare mutuncin ta ba ne kawai dan ta mayar da mutane shashashu ne ace ta na tsoron Allah bayan gashi duk dare mazan banza ta ke bi wallahi yau sai ta gane ruwa ba sa'an kwando ba ne bari mu je ba 'kwarton nata ba har ita zan had'a naiwa d'an banzan duka" ya fad'a suna shan kwanar layin Hajiya dake ta faman sauri kamar za ta kifa ta ce "kai dai muje kawai burina na ga wanne d'an matsiyatan ne ya ke bata kud'i har ta iya fitowa da dare ta zo gurin sa" ta'be baki Zaid yai ya na cewa "Hajiya ko bai bata kud'i ba Zainab za ta iya bashi kanta kyauta kar ki ja akan hakan" zaro ido Hajiya tai ta na shirin magana Haulat ta ce "yauwa mun kusa ku taho dai" ita ce a gaba ba su yi nisa da shiga layin ba su ka fara hango su daga can nesa tare da Sameer sai dai ba su gane shi ba da yake da nisa tsakanin su shi kam har ya raka ta sun siyo sun dawo da mamaki yake kallon Hajiya tun daga nisa ya gane ta. "Su kuma wadancan ina za su je haka a wannan daren gayyar su guda"? Da alamar tambaya Zainab tace "su wa ye"? ta fad'a tana kallon sa domin ita ko kad'an ma ba ta lura da wasu su Hajiya da suke tahowa ta gaban su ba saida Sameer ya nuna mata gaban na su da yatsa yana cewa "ga su can su Hajiya ne" kallon gurin ta yi ta ga yadda suka d'ebo gayya haka kawai ta ji fargaba lokaci guda ta dirar mata ta san ba lafiya ba babu abinda zai fito da su yanzu kuma abun mamakin har da Hajiya ma. "Amma me ye zai fito da su yanzu"? Ta sake fad'a cike da zulumi kafad'a Sameer ya d'aga yana ta'be baki yace "oho mu su wannan matsalar su ce koma menene ya fito da su d'in" shiru Zainab ta yi tana kallon su daidai sun had'u aka tsaya ana kallon kallo tsakanin su ba wanda ya yi magana sai Zainab da ta ga duk ita suke kallo me ye hakan Sameer ne ya fara magana "Hajiya ina zuwa haka da sauri"? Zainab ta nuna da yatsa tana cewa "ga wacce mu ka biyo ina saurayin da su ke taren fatan ka yi masa duka ba ka barshi ya gudu ba"? Da mamaki Sameer ya ce. "Wanne irin saurayi ki ke magana kuma Hajiya"? Wani kallo ta yi masa ganin kamar hankali ya ke son raina mata tace "au me ka ke nufi kai ma munafirtar tawa za ka yi saurayin da aka gan ta yanzu da shi sun yo nan layin tare maganata ta tabbata kenan Zainab bin maza ki ke da uban wa aka gan ki yanzu kin yi bayan layi iye"? Hajiya ta fad'a tana kallon Zainab wacce ta zaro ido a rud'e jikin ta ya fara d'aukar rawa tsabar yadda maganar an gan ta tare da wani saurayin ta daki ran ta had'e rai Sameer ya yi yana cewa. "Wai Hajiya wa ye ya je yace miki an gan ta da wani ta yi bayan layi har ki ka yarda ki ka fito"? A masife Hajiya ta ce "uban ka ne yaje ya fad'a min wato nan kare ta ka ke yi saboda kar mu zarge ta kenan ko me"?. "Ni nace miki kare ta na ke yi ba kawai dai zan fad'a miki gaskiyar abinda baki sani ba kuma baki da tabbaci a kan sa". "Me kake nufi Samar yanzun ba zuwa kayi ka taho da ita ba"?. "Daga Ina na je na taho da ita"? Cikin fad'a Hajiya tace "daga d'akin tsinannan saurayin da aka ce an gansu tare yanzu" tsaki Sameer ya ja yana cewa "wai Hajiya wa ye ya fad'a miki tare da wani aka gan ta ni ne fa ba wani ba ne" yana rufe baki Haulat dake gefe tana aikowa da Zainab harara da sauri ta matsa kusa da Hajiya tana cewa "wallahi Hajiya ba gaskiya ya fad'a miki ba kare ta yake amma ni naga wanda suka tafi tare shi wancan gajeren wando ne a jikin sa🙊 kawai dai ban san shi bane amma shi ne d'an iskan nat......................... Tun bata gama fad'ar abinda ta ke shiryawa ba taji saukar mari me mugun zafi Sameer ya sauke mata shi a fuska 'kara ta fasa cike da azaba ta ja baya tana fashewa da kuka nuna ta da yatsa ya yi yana cewa "ke 'karamar mara kunya ki gyara kalaman ki akan 'yar uwa ta bata kasance 'yar iska ko mazinaciya kamar yadda ku ke neman d'ora mata sharri ba na rantse da Allah daga rana irin ta yau duk tsinanniyar yarinyar da ta sake cewa ta ga Zainab ta yi wani layi da saurayi sai naci bura uban ta ina daidai da ku matsiyatan yara marasa mutunci" yana rufe baki Zaidu yace. "Kaine babban matsiyaci amma ba 'kanwa ta ba amfad'a mata 'yar iska ce ba ta yi bane"? ya fad'a yana kawo masa mari zai ramawa Haulat ri'ke hannun sa Sameer ya yi ransa a mugun 6ace ya yi masa wani irin kallo yana cewa "kai Zaid ka kama kan ka kar ka kuskura tsautsayi yasa bakin ka ya sake furta kalmar iskanci akan Zainab ka iya bakin ka kafin na fasa maka kai wallahi dukkannin ku ina daidai da zamanin kowanne shege zaku gani kuma" fisge hannun sa Zaid yayi yana huci. Ganin kamar ya fusata shi ya sa yace "rama mata za ka yi? To bismilllah ga fuska rama ma ta wallahi yau da kaga ikon Allah saidai kayi kwanan asibiti" yana rufe baki Zain yace "saidai mu yi kwanan asibiti tare yaro wallahi baka da 'karfin da ka isa ka min dukan da za'a kai ni asibiti kai kuma ka zauna a gida saidai a kai mu tare domin ko a dawa giwa ta san zaki ka gane"? kai Sameer ya jinjina yana cewa "ban gane ba amma idan kai d'an halak ne ka d'aga hannu ka mare ni sannan ne zan san ka cika ni kuma wallahi tallahi na rantse da wanda numfashi na yake hannun sa yau sai kayi kwanan asibiti mari ka gani" ya fad'a yana mi'ko masa fuska shiru Zain yayi yana huci domin yasan tsaf Sameer zai aikata abinda yace tun da masifaffe ne shiyasa da yaji ya fad'i haka kawai ya ja tsaki mai 'karfi yana hararar Zainab cikin son huce haushin sa ya ce. "Yar iska kawai uban wa zai aure ki kin gama zubar da kimar ki a gurin wasu Allah ya sauwake min auren mace me fuska biyu irin ki"? 'Bangaren da Hajiya take tsaye ya juya yana cewa "yanzu Hajiya a hakan kike so na aure ta Allah ya rufa asiri tun wuri ta nemi mijin aure d'an iska irin ta kafin lokacin ya 'kure ma ta amma ni dai nafi 'karfin auren mace 'yar duniya mai fuska biyu da safe ta saka dogon hijab har jan 'kasa yake ta rufe fuska da nikaf kowa yana mata kallon mutuniyar arziki amma da dare ta tafi gurin maza ta na basu jikin ta su na biyan ta tirrr....................... Sha'ko wuyan sa Sameer yayi yana cewa "gurin mazan uwar ka ta je nace gurin mazan uwar ka ta je da uban wa ka ta'ba ganin ta tare da shi fad'a min ko na kashe ka a gurin nan" ya fad'a cikin tsawa yana wujijjiga shi ganin zasu fara fad'a a layi su jawo hankalin jama'a gurin a zo ana tambayar me ya faru lafiya ya sa hajiya tace "kai ku saki juna bana son hauka idan kun je gida kwa yi a can" tura Zaid Sameer yayi yana nuna shi da yatsa yace "wallahi ba 'kyale ka na yi ba sai na nuna maka iyakar ka" tsaki Zaid yayi yana cewa. "Sai mu nunawa juna iyaka kai dai Sameer ko 'kasa ce abinci na ba zan tsaya ka min duka kamar yadda ka ke d'auka a ran ka ba aure kuma nace bazan aure ta ba idan akan haka ka ke jin haushi na ma wallahi ba zan auri Zainab ba" yana fad'in haka ya bar wajen ashar Sameer ya sakar masa ya na cewa "uwar ka Zainab za ta yi da kai wallahi tafi 'karfin auren jaki irin ka zuba ido ka ga irin mijin da za ta aura kaf yaran gidan nan ba wacce zata samu irin sa daga wadanda sukai auren har na bayan ta". Kallon sa Hajiya ta yi bayan wucewar Zaid tace "Samar ba za ka fad'a min gaskiyar a inda ka samo ta ba"?. "Hajiya wallahi Allah kenan kin ji na rantse tare da ni mu ka tafi awara na kara ta ta siyo kin gani" ya fad'a yana nuna mata ledar dake hannun Zainab a ri'ke kallon Zainab Hajiya ta yi tana cewa "amma me ya sa tun da ake maganar ba ta ce komai ba ta yi shiru"?. "To Hajiya me zata ce"?. "Da tana da gaskiya ai za ta yi magana za ta musa zargin da ake mata amma ta yi shiru ta na sauraren mu"?. "Ke dai Hajiya tun da ba'a iya miki Allah ya sauwake kawai shine abinda zan ce amma yadda ku ke d'aukar Zainab ba haka ta ke ba baza ku gane ba sai gaba idan lokaci ya zo muje" ya fad'a yana kallon Zainab jiki a sanyaye ta wuce ta fara yin gaba shi kuma ya juya inda Haulat take tsaye ta gama kukan ta ta share ya ce "zanyi miki gargad'i daf da duka daga yau idan na sake jin kin je kin ce wa Hajiya wai kin ga Zainab ta yi wani layi tare da saurayi hummmm matakin da zan d'auka a kan ki ba zai fad'u ba zaki gani ki ci gaba da mata sharrin" yana fad'in haka yabi bayan Zainab wacce ke tsaye a d'an nesa da su tana jiran sa ya je su fita. Tsaki Hajiya ta yi tana kallon Haulat wacce ta yi shiru ta ce "wai ke dama dan uban ki da Samar ki ka gan ta amma shi ne ki ka ce min wani saurayi ne gashi kin sa a daren nan na fito waje Allah ya 'kara da ya mare ki ina ma dukan tsiya ma ya miki shegiya ma'karyaciya" murgud'a baki Haulat tai tana hararar Hajiya fuuuuu ta wuce tana cewa "duk sharri na ban kai ki ba mutum bai yi abu ba ki ce yayi idan 'karyar ce ma gurin ki na gada" ta fad'a tana nufar hanyar gida d'aga murya Hajiya ta yi yadda za ta ji ta ta ce "Asiya ce ma'karyaciya ba ni ba bankad'add'iyar yarinya kawai" dariya Rasheedat da ke gefe a tsaye ta yi tana cewa "muje gida Hajiya duk sun tafi sun bar mu" juyawa Hajiya ta yi suna tafiya ta ce "ai ba 'yan arziki bane ta ya za su jira mu kowa ya na ji da ba'kin hali". Komawa su kai Hajiya da yake dama a kwance take d'azun ma shiyasa ta koma ta kwanta Rasheedat da Bilki da Zakiyyah suna waje a kofar d'akin ta a zaune suna zance dariya Rasheedat tana cewa "ke Bilki ban ba ku labari ba" cike da son jin me akai Bilki tace "me ya faru bana nan fad'a min"? Sabuwar dariya Rasheedat ta sake yi tuna abinda ya faru da irin gwaramar da akai tace. "Humm ku dai ku bari kawai d'azun nan Haulat ta shigo da gudu ta na cewa Hajiya kiyi sauri mu je wallahi ga Zainab can tare da wani saurayi sun yi bayan layi mu ka tashi Hajiya har da tuntu'be ta ke yi mu ka samu Yaya Zaid a waje shi ma ya bi mu ashe 'karya Haulat take tare da Yaya Sameer su ka je ya raka ta siyan awara tabd'ijan baki ga gwaramar da akai a gurin ba saura kad'an Yaya Sameer ya yi wa Yaya Zaid dukan mutuwa wallahi sannan ya mari Haulat d'in ta yi ta kuka ni kwa ina gefe ina dariya abu na" zaro ido Bilki ta yi tana cewa "ke dan Allah da gaske ki ke Rasheedat"?. "Wallahi da gaske na ke mu ku d'azu ai mun yi kallo ku na nan ba ku sani ba naso ace naje da waya ta na yi musu video". "Me ya sa ba ki zo kin kira mu ba ku ka tafi iya ku ai mu ma da mun yi kallon. "Taya zan tsaya zaman kiran ku ina sauri kar ayi ba ni hum nan gaba nasan Haulat ko da kud'i ba za ta yiwa Zainab ko Yaya Sameer 'karya b............... "To 'yar munafika annamimiya munafirci na ki ke kenan mitsiyaciya," suka ji muryar Haulat wacce ta shigo kofar Hajiya yanzu ta ji abinda Rasheedat ta ke fad'a duk juyawa su kai su na kallon ta daga baya Bilki ta yi dariya ta na cewa. "A'a Hajiya Haulat iyayen 'yan sharri ashe d'azu mari kika sha a gurin Yaya Sameer fatan fuskar ba ta kumbura ba yatsun sa sun fito"? Wata ba'kar harara ta sakar mata tana cewa "ban sani ba ke ma" baki Bilki ta ta'be tana cewa "kar Allah ya sa ki sani ai dama Yaya Sameer d'in su ne maganin munafikai irin ku" a masife Haulat tace "ke kin ga kar ki 'kara fad'a min magana munafirci aka kai ki komai sirrin kofar ku sai kin fad'a hatta jefa wayar Zainab da ki kai a ruwa sai da ki ka fad'a mana dan bana son tashin hankali ne amma wallahi da gobe sai na fad'a mata". "Idan kin fasa fad'a mata Asiya cikin shege tayi ta haife ki" jin abinda Bilki tace mata yasa ta fasa shiga d'akin Hajiya a fusace ta juyo suka hau damen fad'a wanda hatta Hajiya da ta fara barci saida su ka tashe ta da sauri ta bud'o labule ta na cewa "kai kai uban me haka zaku baro iyayen ku ni ku zo ku cika min kunne da fad'a ba za ku bari ba"? ko sauraron ta ba su yi ba ga Rasheedat a gefe sai dariya take ta'ki tashi ta raba su ganin haka yasa Hajiya d'auko sanda tana fitowa ta yo wajen su tana cewa "tselan uwa ku tsinannun yara ina magana shine ku kai kunnen uwar shegu da ni kamar yadda iyayen ku mata su ka raina ni kuma haka" ganin da sukai tana shirin rad'o mu su sandan yasa suka saki juna kowa ya na huci kallon su Hajiya ta yi tana cewa . "Fad'an uban me ku ke yiwa mutane da daren nan"? Ran Haulat a 6ace ta ce "wai tsabar rainin hankali ina shigowa na ji su na munafirci na wai wani d'azu Sameer ya mare ni saboda na yiwa Zainab 'kazafi" "Ba ki yi bane dan uban ki ina ni ma har sani ki kai na sha wahalar fita ki kace zaki raka ni inda kika ga sun yi ashe 'karya ki ke kuma dan su na maimaita zancen shi ne zaki kama ta da kokawa"?. "Bazan kama ta da kokawa ba uban ta ne yace ta ce min Sameer ya mare ni d'azu harda wani ko fuska ta ta kumbura yatsun sa sun fito". "Ta fad'a ya mare ki ni ma na fad'a d'azu Samar ya mare ki dan ubanki ki yi wani abu akai na sake jin kin yi magana a kofar nan wallahi sai na fito na shirga mi ki wannan sandan a bayan ki" tana fad'in haka ta koma d'aki tsaki Haulat ta ja me 'karfi ta na hararar kofar d'akin Hajiya kafin ta juya inda Bilki ta ke tana cewa "ke kuma zamu had'u ne wallahi sai mun fidda rainin da ya ke tsakanin mu" ita ma ta na fad'in haka ta juya fiiii ta fice daga kofar ita dai Rasheedat da take ta yi musu dariya ganin Haulat d'in ta ji haushi ta fice ta ce. "Gaskiya 'yan gidan nan suna burge ni masifa ko gidan haya iyakaci kenan haba ace kullum idan rana ta fito kafin ta fad'i sai an samu wandanda su Kai tashin hankali idan kuwa ba'a yi da rana ba sai anyi da dare kafin a kwanta barci a gidan nan ba'a rasa abun yi" ta'be baki Bilki tai tana cewa "waye zai zauna a raina shi ke yadda 'yan gidan nan ba mutunci ne da su ba daga manyan su har 'kananan su idan su ka ga kai ba mafad'aci bane tuni za'a sakaltar da kai gara ka nuna kai ma masifaffe ne da bala'i ya gan ka saida ya sara maka sai ka nuna haka sannan za ka daidaita da kowa" kai Rasheedat ta jinjina tana cewa "gaskiya ne shiyasa ai mu ka raina Zainab saboda ita ba mai son hayaniya ba ce". "Wannan kuma ita ta so sai kin je 'kofar mu ma kin ga yadda na ke mata rashin mutunci son raina da rashin kunya ko tari ba ta yi min ke ko 'karasa kallo na ba ta yi" kai Rasheedat ta girgiza tana cewa. "Uhm gaskiya dai a gidan nan indai ba sharri za ka yi mata ba bata da wata matsala Allah sarki wallahi har na ji tausayin ta ya kama ni" zaro ido Bilki tai tana cewa "ke Zainab ba abar tausayi ba ce garama kar ki wahalar da kan ki saboda ita" da mamaki Rasheedat ta ce. "Me ya sa ki kace haka"?. "Kina gani a gidan nan ita kad'ai ta ci gaba da makaranta saboda ba kud'in da za'a biya mana mu dora ita kad'ai ce take sana'o'i kusan shida amma ki ce tana baki tausayi hum idan ba ki sani ba bari na sanar da ke kece babbar abun tausayi" dariya Rasheedat ta yi tana cewa "saidai abun taushe ba abun tausayi ba sana'a mu na da hanyar yi dan dai ba mu da jari ne amma ai ke Yaya Sameer ne zai ba ki" zabura Bilki tai tana cewa. "Wanne Yaya Sameer d'in amma dai ba na gidan nan ki ke fad'a ba"?. "Wai da shi". "Cafd'i wallahi ko mutuwa zan yi Yaya Sameer biyar d'in sa baya d'agawa ya bani tunda na ke dashi bai ta'ba min wani abun arziki ba amma ya yiwa Zainab ya fi 'karfin a 'kirga". "Jinin su ne yazo d'aya" cewa Rasheedat tana hamma alamar barci kai Bilki ta girgiza tana cewa "ke ba wani had'uwar jini sai dai had'uwar asiri a banza ba zai ri'ka kulawa da ita yana mata abubuwa ba alhali suna uba d'aya ni da muke uwa d'aya ya ri'ka share ni ki na ganin fa kowacce 'kofa a gidan nan had'e kai 'yan d'aki d'aya su ke yi amma ban da Yaya Sameer shi kam da 'yan uba yake nasa sha'anin domin kwanan baya gidan Murjah yayar Zainab d'in ya je amma bai le'ka gidan Auntyn Aisha ba kin ga ko ta nan ai kinsan ba son Allah ya kewa 'yan d'akin su Zainab ba asiri ne yake yawo a jikin sa a halin yanzu nasan da mutuwa za'a bashi za'bi tsakanin ni da Zainab cewa zaiyi mutuwar ta d'auke ni tunda ba 'kauna ta ya ke ba yafi son ta dad'in abun ma ba aure tsakanin su uban su d'aya amma ba dan haka ba yadda yake mata wannan shishshigin 'karshe ba zai wuce yace yana son ta ba wallahi wani lokacin idan ya yi mata wani abun kamar na yi ta kuka haka na ke ji tsabar ba'kin ciki da takaici" tana rufe baki Rasheedat ta fara dariya tana kallon ta tace. "Hum ai kuwa aiki ne bai ishe ki ba nidai da ace Yaya na ne yake irin wannan abun ko 'karasa kallon sa ba zan yi ba saboda damuwa zan ri'ka d'orawa kai na shi kuma ba tare da ya damu ba maybe ma shi Yaya Sameer d'in bai san kina damuwa da hakan da yaje yiwa Zainab d'in ba". "Uhum wallahi yana sane kawai dan ya 'kuntata min ne ba komai ba shi ya sa nima idan na ga ya fice nake ramawa a kan Zainab d'in tun da ba wata tsiyar ta isa ta min ba". "Akwai ranar da zaki daina ai idan ta yi aure ta bar miki gidan". "Anya Zainab za ta yi aure kuwa? Miji ya'ki fitowa"? Kai Rasheedat ta d'aga tana cewa "daina mata fata za ta yi man akwai lokaci nikam bari kiga na d'aga wannan zancen da mu ke ba 'karewa zai yi ba idan zamu kwana a nan ni kam bari ki ga na tashi ta tafi kofarmu na kwanta barci na ke ji kar na fara gyangyad'i" ta fad'a tana mi'kewa ita ma Bilkin mi'kewar ta yi suka fita tare kowa ta tafi 'kofar su.................. ZUCIYAR ALIYU CE YUSRAH MUSA DUTSE NAJA'AT MUSA ABUBAKAR ✨ SALEEM MUSA ABUBAKAR ✨ FATIMA MUSA ABUBAKAR ✨ AISHAT MUSA ABUBAKAR ✨ ABUBAKAR MUSA ABUBAKAR @YMA DUTSE PAGE 33 Yau Shareef bai je hospital da wuri ba duk irin jiran sa da Baby ta yi amma shiru sai wajen 'karfe tara da rabi ya zo amma sakamakon yana da ayyuka yana zuwa ya wuce a ta'kaice ba ta samu had'uwa dashi ba sai 'karfe d'aya da rabi sannan sun gama komai ya dawo office ta je. "Barka da rana Shareef ya kake"? Bai d'ago ba wayar sa ce a hannun sa yana dubawa ya ba ta amsa. "Lafiya". Numfashi ta sauke tana cewa "fatan ba wata matsala na ga kamar fuskar ka da damuwa"?. "Ni ma fad'a mi ki"? Ta sake ji ya bata gajeruwar amsa cije baki ta yi kamar za tai shiru sai kuma ta sake cewa "ya Mami fatan ta na lafiya"? Jin abinda ta ce yasa ya d'ago ya kalle ta tare da aje wayar yana fuskantar ta sosai yace "dama ina so na kashe miki warning akan zuwa gurin Mami da ki kai ranar Saturday kar ki dad'a zuwa bana so bana bu'katar ki sake zuwa gidan mu" da mamaki Baby ta ke binsa da kallo ta ce. "Amma saboda me"?. "Tambaya ki ke me ya sa"?. "Dole na tambaya Shareef me ye laifi na a ciki dan kawai na je na gaisar da ita"?. "zuwan ne bana bu'katar ki 'kara yi kin gane"? Shiru ta yi ta zuba masa ido ta ma rasa abinda za ta ce masa ba wanda ya sake magana a cikin su tsawon mintuna can tace "Shareef idan har zuwa gidan ku da nayi shine ya 6ata maka rai kayi ha'kuri ba zan sake ba daga yau insha Allahu amma kai ma ya kamata ka yi min adalci ba fa a rayuwa haka kaga yadda ka saka ni a garari kuma dan na yi abun arziki sai ka d'auke shi da fushi"?. "Na fad'a miki a karo na uku kar ki sake zuwa gidan mu balle ki yi min 'karya a gurin mahaifiya ta". "K'arya kuma Shareef"?. "Eh ba ki yi bane kin ce idan na zo hospital bani da zance sai nata kullum idan muna tare ita na ke furta miki yawan ambaton ta da na ke yi yasa ki kace dole sai kin je kin gan ta da yaushe mu kai haka da ke a ina na samu lokacin da zamu zauna har na fad'a miki irin wadannan maganganun? Ya isa haka ki bari bana so idan kina son zama da ni lafiya kar na sake jin labari ko a mafarki ne kin 'kara zuwa gidan mu kin gane"? Rasa abinda za ta ce masa ta yi shi yasa kawai ta yi shiru gabadaya wani irin yanayi ya lullu'be ta ta gaza gane wanne irin mutum ne Shareef ta na so tasan a inda matsalar ta ke ta gyara amma har gobe ta rasa, kai ta girgiza tana sake d'agowa ta kalle shi ta ga ya mayar da hankalin sa kan wayar sa ta tabbata tun da ya yi mata iyaka da gidan su idan ta 'kara zuwa abun bazai mata kyau ba zata yi 'ko'kari ta danne duk wata damuwa ta d'an share shi na tsawon wata guda maybe idan ta cire shi da damuwa da shi a ran ta za ta samu lafiya kar ta je ta jawowa kan ta ciwon da ya fi 'karfin ta ko wanda zai hallakar da ita, mi'kewa ta yi tana d'aukar jakar ta da key d'in motar ta ba tare da ta sake ko da tari ba ta fice ko kad'an bai damu da yanayin da ta shiga ba shi yasa a rayuwa kar ka damu da mutumin da bai damu da kai ba ko dashi ko ba shi za ka iya ingantacciyar rayuwa mai kyau wacce ta fi wadda kake tunanin yi da shi. Afifah yau tana dawowa daga school ta ga sa'kon da Aliyu ya bada a kawo musu ita da Amirah har ya iso cike da murna ta kar6a tana ihu ganin yadda yanayin sa yake daga photon sa na jikin kwalin tun kafin ta bud'a lallai wannan agogon mai mugun tsada ne zata sha wanka da kayan ta. Tana bedroom ta yi wanka da sallah kenan ta saka kaya tana zaune a gaban mirror Aliyu ya kira ta tasan bazai wuce ya tambaye ta ko Amirah ta kawo mata ba shiyasa tana d'agawa ta ce "hello Yaya Aliyu Ina yini naga agogon ya zo". "Eh nace Amirah ta kawo miki ta kawo d'in"?. "Eh ta kawo min lokacin ma ban dawo daga school ba sai yanzu Momy ta bani ita Amiran ta tafi na gode sosai Allah ya 'kara arziki". "Ok kin bud'e shi ne"? Kai ta girgiza tana cewa "a'a ban duba ba". "Yayi kyau gara da baki bud'e ba domin ba naki bane ki kaiwa Sameer yanzun nan kuma wallahi idan yace min kin 6arka gidan agogon nan na dawo sai jikin ki ya fad'a miki" zaro ido waje Afifah tai kamar zata fasa ihun takaici wannan agogon na mata ne akan me zaice ta kaiwa Sameer gaskiya badan babu yadda ta iya ba babu inda zata je amma tasan tunda yace haka zaman lafiyar ta kawai ta kaiwa Sameer d'in............... Ba ki ji abinda na ce bane"? Kamar za tai kuka ta ce "na ji". "Ok ki kai masa" yana fad'in haka ta ji ya kashe kiran cije yatsa ta yi tana sake kallon agogon tace "kan bala'i wai da gaske Yaya discipline ya ke yanzu wannan agogon tsakani da Allah ai na maza ne idan na kai masa shi ma sai dai ya bada kyautar sa innalillahi gaskiya Yaya discipline ya gama da rayuwa t............ Ringtone d'in wayar ta taji da sauri ta duba shi ne ya sake kira kamar kar ta d'aga tsabar takaici bari ta yi saida ta kusa katsewa sannan ta d'aga ji ta yi yace. "Kin tafi ne"? Da sauri ta ce "a'a ban tafi ba ina bedroom" ta d'auka cewa zaiyi ta barshi basai ta kai masa ba idan ya ji ba ta tafi ba sai kuma ta ji yace "baza ki tashi ki Kai masa ba kenan wato dan kin ga bana kusa shi ne za ki min raini ko"? Turo baki tai tana tashi ciki-ciki tace. "Ka yi ha'kuri". "Ban ha'kura ba ki je ki kai masa idan kin dawo ki kira ni ki sanar da ni" d'it d'it taji wayar ta katse d'aukar hijab d'inta ta yi tana tura baki ran ta a had'e sosai ta fita parlor iya Fati da Momy ne Husnah da Elham ba sa gurin ganin yadda ta fito tana cika da batsewa yasa Momy cewa. "Afifah ya haka ke da ki ka shigo ki na murna me ya faru lafiya"? Agogon ta d'agowa Momy tana cewa "ina lafiya Momy haka kawai Yaya discipline tun kafin agogon nan ya zo ya kira ni ya fad'a min Amirah za ta kawo min ina ta saka rai nawa ne sai yanzu da yasa aka kawo min wai ya kira ni yanzu ba nawa bane naje na kaiwa Sameer kuma fa agogon mata ne kin gani" ta fad'a tana mi'kawa Momy kallon agogon Momy ta yi tana cewa. "Ok tun da dai ga wanda yace ki kaiwa kije ki kai masa saiki fad'a masa cewa kema kina son irin sa idan zai dawo ya taho miki da shi". "Uhm uhm nidai daya bar min wannan d'in yafi amma shikenan lamarin Yaya discipline sai shi Fati taso ki raka ni" mi'kewa Fati tai tana cire mayafin da tayi rolling a kanta dashi ta yafa suka fita tana tambayar Afifah "to wai Aunty Afifah ni ban gane ba me yasa zaice ki kaiwa Yaya Sameer bayan shi namiji ne kuma dai wannan agogon mata ne" cike da jin haushi Afifah tace. "Oho masa shima Yaya Sameer d'in wa yasan me zaiyi da shi daina taso min da kayan takaici kar na fara hawaye a layi" murmushi Fati tai tana kallon ta ta ce "ki gwada cewa ya bar miki man nasan Yaya Sameer zai baki" kai Afifah ta girgiza tana cewa. "A'a tunda Momy tace na fad'a masa ya taho min dashi gara hakan da nayi abinda idan ya dawo zai ci ubana duk da nasan Yaya Sameer in dai nace masa ina so zai bar min d'in" ta fad'a daidai sun shiga chemist d'in da sallama ta mi'ka masa tana cewa "Yaya Sameer gashi inji Yaya Aliyu yace a kawo maka" kar6a yayi yana murmushi ya kalli agogon kafin ya d'aga kai yana cewa "ok tom na gode dama yanzu ya kira yace kin kawo min nace a'a ashe kina kan hanya". Jinjina kai Afifah tai tana cewa "ki ji dan Allah Fati wai kafin nazo harya kira yana tambaya"? Dariya Fati ta yi bata ce komai ba Afifah taci gaba "yanzun nan ni d'in ma mukai wayar dashi amma har ya kira ka"?. "Eh Aliyu ne fa kad'an daga cikin aikin sa ne wannan" ya fad'a yana aje agogon d'an ta'be baki Afifah tai tana cewa "ai shikenan na kawo na huta da naci Fati mu je Yaya Sameer sai anjima". "Ok ki gaida Momy kafin na shigo na gaida ita". "Za ta ji insha Allahu" ta fad'a su na fita suka koma ba su samu Momy a parlon ba babu kowa shiyasa Afifah ta wuce dinning taci abincin rana Fati kuma ta shige ciki bata tsaya a parlon ba Afifah ta dad'e sosai kafin ta ji 'karar bud'e 'kofa Momy ce ta dawo ta na zama tace. "Au har kun dawo ke nan"?. "Eh tun d'azu wai nan d'in kafin mu je har ya kira shi yana tambayar sa na kai masa". "Ai kuwa dama zai kira shi kin san waye Aliyu fa shi ya sa na ce miki ki kai masa kawai idan kina so ki fad'a masa ya taho miki dashi idan ya tashi dawowa". "Ni fa na ha'kura Momy kawai ya wuce tun da ban samu wannan d'in ba Yaya Sameer ya ce yana gaida ke kafin ya shigo". "Ina amsawa ai dama ya dad'e bai shigo ba saboda ya ga yanzu ba Aliyu kuma da ya duba ko da ace Aliyu ba ya duniya shi me shigowa gidan nan ne kullum balle yana raye ko dan abinci ma sai dai a bishi chemist d'in da shi ya daina zuwa ya kar6a" kai Afifah ta d'aga tana tasowa daga dinning table dawo parlor gurin Momy tana cewa. "Ai yana da kunya ne shi yasa". "Eh gaskiya kam ya na da kara da wani ne haka zai ri'ka shigowa koda yaushe ba ruwan sa". AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE. @YUSRAH DUTSE PAGE 34 Kiran wayar Afifah da akai shi ya dakatar da zancen da su ke yi ta d'aga daga can 6angaren Amirah dake zaune akan gado ta d'ora pillow akan cinyar ta ta ce "hello Afifah ya kika ga agogon ya yi miki kyau da kika d'aura"? Ta'be baki Afifah tai tana cewa "wanne irin kyau d'in bayan ashe dama ba nawa bane d'azun nan ya kira ni yace na kai wa Sameer". "Sameer kuma shi me zaiyi da abun mata"?. "Oho nima na kasa gane wannan al'amarin". "Kenan dama ba ke ya siyawa ba amma yace na kawo miki"?. "gashi nan kuma ya fad'a ni kam ai na kai masa kuma na ha'kura ko siyowa ya yi ya taho min da shi ba zan kar6a ba" dariya Amirah tai ta na cewa "ki ce na fara shiri idan ya baki bakya so zan zo masa sannu da zuwa sai na kar6a". "Sai dai ke d'in amma ni kam ina da zuciya" sabuwar dariya Amirah ta sake yi tana cewa "ahh mu kam bamu da zuciya musamman a gurin mutane irin Aliyu" kai Afifah ta jinjina tana cewa "ai kuwa kin had'a kan ki da aiki duk wanda zaki nuna masa kome ya yi miki daidai ne zaki kwashi takaici da ba'kin ciki a gurin sa musamman lokacin da ku ka samu sa6ani yana sane zai ri'ka yin abinda ran ki baya so saboda kawai ya ba'kanta miki". "Ke Afifah wa ya fad'a miki mutane irin su Aliyu su na haka ai duk wanda ki ka ga yana wula'kanta d'an Adam bai san darajar kan sa bane amma in dai mutum ya na da hankali bazai tozarta d'an uwansa musulmi ba". "Haka ne kin yi gaskiya ke ma kin zo da magana a nan sai anjima". "Ok zuwa dare maybe zan sake kiran ki". "Ba matsala" Afifah ta fad'a tana sau'ke wayar ta kalli Momy tana cewa "ki ji Amirah da wata magana dan Allah haka kawai zan li'ke a abinda ba'a saka da ni ba bazan iya irin wannan rayuwar ba ko kowa bai ganin kima ta ni zan yi 'ko'kari na kare kimar tawa domin duk daren dad'ewa za'a samu wanda zai ga kimar tawa kuma ya martaba ni" murmushi Momy tai tana jin ta bata ce komai ba. Sameer kam duk wunin yau yana chemist tunda ya bud'e bai samu ya koma gida ba sai dare daya rufe chemist d'in ya tafi gida Zainab ta riga ta yi barci shiyasa ya bar agogon sai da gari ya waye kafin ta tafi school tana zaune a 'kofar d'akin ta akan sallaya tana karyawa da indomie ya zo gurin yana tsugunawa a gaban ta d'agowa tai tana kallon sa tace. "Ina kwana Yaya Sameer"? Kai ya d'aga mata yana d'aukar fork d'in da ya gani a aje akan indomie domin ita da hannu ta ke ci loma biyu yayi ya aje fork d'in yana cewa "da me kika dafa"?. "Ba komai indomie ce kad'ai sai Maggi da albasa da attaruhu". "Ok ta yi dad'i kuwa" ya fad'a yana bud'e ledar ya fito da agogon yana bata yace "ri'ke kar6i wannan" da mamaki Zainab ta ce "wannan agogon kuma fa daga ina"? Kai tsaye ya bata amsa. 'Ke ma kin san waye zai ba ki aboki na ne man" jin abinda yace yasa taji numfashin data sha'ka ya tsaya mata a 'kirji 'kure agogon tayi da kallo kafin ta d'ago ta kalli Sameer wanda yace "yayi kyau ko sai kisha kwalliya da abun ki" yana fad'in haka ya mi'ke zai fita da sauri tace. "Yaya Sameer" dakatawa ya yi yana cewa. "Umhum ya a kai"? A rud'e tace "wai dan Allah waye wannan abokin na ka"? Jin abinda tace yasa ya juyo yana kallon ta gabadaya tashin hankali yaci karo dashi akan fuskarta wanda bazai iya gane yanayin da take ciki ko ya kwantanta ba... "Ina jin ka Yaya Sameer ka fad'a min" kai ya jinjina yana cewa "ok karki damu zan fad'a miki amma ba yau ba dan Allah Zainab ki nutsu da aboki na ki tsaya da zuciyar ki guri d'aya shine masoyin ki na hakika mai kaunar ki ta gaskiya wanda yake burin ki zama uwar 'ya'yan sa ya kamata ki gane hakan ki daina tambaya a kan sa da sannu zai zo miki ki na zaune" hawaye ne shar shar taji yana zuba mata ta soma girgiza kai tana kallon sa ta kasa magana da sauri ta mi'ke ta wuce d'aki gudun kar wani ya shigo ya ganta tsaye Sameer ya yi a wajen kamar zai le'ka d'akin ya yi mata magana sai kuma ya fasa ya fita. Zainab kam ka sa jurewa ta yi sai da ta yi kuka me isarta sosai sannan ta fito ta wanke idon ta indomie d'in da bata karasa ci ba ta ha'kura ta shirya ta d'auki jakarta tai wa Umma sallama ta fita gudun kar ta shiga gurin Hajiya ta sake saka mata wata sabuwar damuwar wacce gara ta yanzun da ta ke ciki hakan yasa ta fice ta je ta kar6i dubu d'aya kamar yadda ta saba a gurin Sameer ta tafi shi kan shi yasan tana ciki damuwa domin ko iya godiya ba ta masa ba kawai yana bata ta juya ta fita a wajen chemist d'in Napep d'in daya aje wasu mata biyu shi ta tsayar ta shiga su ka tafi. K'arfe biyar da rabi aka tashi ganin lokaci bai 'kure mata ba kuma har zata iya zuwa gidan Aunty Murjah ta kar6o d'inkin su gashi ya fi kusa daga school d'in nasu akan ta ce sai ta dawo gida kawai da ta fito daga ciki ta tare me Napep ta ce ya kaita gadon 'kaya ta yi sa'a kuwa lokacin dawowar Aunty Murjah kenan daga anguwa ta sauka a Napep ita ma ta sauka da mamaki Aunty Murjah tace. "Tofa Hajiyar kulle yau kece a gidan nawa ashe yau za'ai ruwan sama" d'an murmushi Zainab ta yi tana kallon Aunty Murjah wacce ta juya tana bud'e musu kofar gidan suka shiga a parlor Zainab ta zauna ita kuma ta wuce ciki ta rage kayan jikin ta sannan ta fito. "Ina Yaya Auwal d'in ko baya nan"? Kai Aunty Murjah ta d'aga tana cewa "yana Abuja yau kwanan sa hud'u sun tafi shi da wani abokin sa Mukhtar wanda ki ka ta'ba zuwa gidan nan ya gan ki yace yana son ki kika 'ki" d'an jinjina kai Zainab ta yi tana cewa. "To tsakani da Allah Aunty Murjah ina zan kai wannan buhun mutumin nan haba dan Allah kina ganin sa wani shirgege da shi" dariya Aunty Murjah tai tana juyowa ta kalli Zainab tace. "Oh kice saboda 'kibar sa ki ka 'ki amince masa ai kuwa da ya sani sai ya sha maganin slimming ya zafge kodan ke saboda yana matu'kar son ki dan dai kin 'ki ne da yanzu idan yara ne ma kina da d'aya ko biyu" tana rufe baki ta sauke ajiyar zuciya mai 'karfi har saida Aunty Murjah ta kalle ta tana dariya tace. "Ya dai"?. "Please dan Allah Aunty Murjah ki daina fada kar ki sa na daina zuwa gidan ki Allah dama yanzun ma dan nasan lokacin da bazan samu Yaya Auwal a gida bane balle ace shi wancan Mukhtar d'in ya zo ya gan ni". "Humm shikenan zan bari sai sun dawo na ce kizo ki wuni min sai ku had'u Allah ina so ki auri Mukhtar ko dan ki taho kusa da ni kin ga gidan sa daya kammala ginawa anan zai zauna iyayen shi suna Sharad'a". "Hum'um ni fa ko tare da su zai zauna ba ruwa na wallahi haka kawai wannan gayen baya burge ni" dariya sosai Aunty Murjah ke yi tana kallon ta cikin tsokana tace "kai Zainab duk wankan da ya ke d'auka"?. "Yo ni tun da ba yimin yayi ba ai ko kyan sa bana gani balle kuma na tsaya kallon wanne kalar wanka yake d'auka". "To kin ga indai haka ne ki bari sai ranar weekend ba ki zo min ki wuni shima zan fad'awa Daddyn Ikram ya fad'a masa sai ya zo ku gaisa". "Da wa zai gaisa amma ba da ni ba"?. "Da ke man ji wani iskanci zan ce ya zo ya gaisa da ni ne". "Ai kuwa in dai da nine zai dad'e bai gaisa ba balle ma ni bana samun lokaci a weekend kullum ina d'inki ne ko had'a baseline da shampoo shiyasa ma ba zan iya zuwa ko'ina ba" da hannu Aunty Murjah tai mata jinjina tana cewa "uhm kina lokaci Hajiya Zeey yayi kyau masu sana'a goma maganin me gasa yanzu ya ake ciki ko dama zuwa ki kai mu gaisa ko kuma tun da Sweet baya nan ki tsaya ki kwana ko"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa. "So ki ke yau a saka ni a lasifika kenan ana cewa na tafi gurin saurayi na kwana ko"?. "Kamar ya wanne irin saurayi kuma"?. "Aunty Murjah ke ma kin sani ai tun da ki kai aure ki ka bar gidan nan Hajiya ta sako ni a gaba maganar yau daban ta gobe daban wai na'ki aure kamar yadda ke ma saida aka sha fama a kanki ta rasa wanne irin hali ne damu mun gado uwar mu ke fa maganganu marasa dad'in ji ni wani abun ma bazan iya maimaitawa ba saboda takaicin sa". "Subanallahi Hajiyan ce take fad'ar hakan"?. "Hajiyan to tsaya ki ji me kankat abun da zai baki ba'kin ciki yau kwana uku anyi tuwon shinkafa da dare ni kuma bana so sai na fita na je Yaya Sameer ya raka ni bayan layin mu gurin Maman Sabeer me awarar nan kin san ta ai"? Kai Aunty Murjah ta d'aga tana cewa "tabbas na san wannan matar tun mu na yara take awarar saidawa har yanzu bata daina ba ke nan"?. "Eh bata daina ba tana yi tofa gurin ta ya raka ni wajen 'karfe tara zan siyo awara ashe wai Haulat ta gan ni ita kuma saukar ta kenan daga Napep babu wanda yasan inda ta je tun safe har dare amma da yake ita 'yar gaban goshin Hajiya ce ba wanda ya kula ta sai ni tana sauka ta tafi ta cewa Hajiya wai ta ganni tare da wani saurayi na yi bayan layi kuma gajeren wando ne a jikin sa hankalin Hajiya a tashe harda gayyato su Yaya Zaid wai ya taho ya daki 'kwarto kawai sai ji nayi Yaya Sameer yana cewa meya fito da Hajiya yanzu Ina kallo gurin su na gan su gayyar su guda muka had'u ta ri'ka fad'a min magana shi ma Yaya Zaid haka har da fad'a su kai da zage-zage a gurin shi da Yaya Sameer ya ri'ka kira na da 'yar iska wa zai aure ni shi dai Allah ya rufa asiri ya zauna da ni hum abun dai babu dad'i 6atacciya aka yi ranar". Aunty Murjah dake dafe da kunci kai kawai take girgizawa har Zainab ta yi shiru sannan tace "kai Subanallahi innalillahi wa inna ilaihi raji'un wacce irin masifa ce wannan shi Zaid d'in uban wa yace ya aure ki har zai ri'ka fad'a ba'kar magana"?. "Waye kuwa bayan Hajiya wai haka kawai ta kama lissafin samarin gidan da 'yan mata akan kowanne ya auri d'an wani 'kofar kuma duk ciki ba wanda ya amince domin kin san Allah Aunty Murjah da na auri Yaya Zaid tunda bai san daraja ta ba gara na auri wannan abokin Yaya Auwal d'in nasan zai ri'ke ni da mutunci tun da yana so na". "Gaskiya ne Zainab amma ban ji dad'in wannan abun ba Allah ya rufa asiri da yake na dad'e ban je gida ba shiyasa ban san abinda ya ke faruwa ba sai yanzu amma in sha Allahu Sweet yana dawowa zan tambaye shi na je na kwana d'aya na taho Allah ya sa ya barni na kwana". "Amin idan bai bari ba sai ki wuni". "A'a ki yi min addu'a ma ya barni dan na fi son kwanan" mi'kewa Zainab tai tana cewa "to Allah yasa ya barki d'in bari na tashi na tafi domin ba zama nazo ba gashi har an kira sallah". "To me ye a ciki sai ki tsaya kiyi sallar kya tafi ni sai na kai ki a motar Sweet ma da kaina dan kar su tuhume ki". "A'a wallahi kar ki wahalar da kan ki d'inki Ikram kawai zaki d'auko min na tafi da ki ka ce kuna da bikin 'kanin mijin ki shi na zo kar6a". "Ok kin san me ya faru ma? Ashe da ya siya mana atamfar sai ya kai shagon d'inki wani telan 'kanwar sa ne zai d'inka mana amma dama ina da wata atamfa da nake so ki d'inka min ni da Ikram d'in bari na d'auko miki ita kawai ki tafi da ita" ta fad'a tana mi'kewa ta shiga bedroom ta d'auko mata ta saka a cikin leda ta kawo kar'ba Zainab tai tana cewa. "Ni ina Ikram d'in ne ban gan ta ba"?. "Tana gidan kakarta tun jiya da Salimat ta zo suka tafi harda uniform d'in ta maybe sai ranar Monday idan an kaita school daga can ta taho". "To shikenan Aunty Murjah ni kam na tafi sai na gan ki". "Wai dan Allah Zainab ba za ki tsaya na dafa abinci ki ci ba ko taliya ce gashi harda kifi na siyo zan yi miya dan Allah ki dawo ciki saurin me ki ke ne"?. "Hum Aunty Murjah 'kyale ni na tafi na tabbata yanzu haka ma jiran komawa ta ake tun da bana kaiwa sama da shida a makaranta yanzu kuwa gashi bakwai ta kusa" ta fad'a tana bud'e kofar parlon ta fita suka nufi 'kofar waje nan ma ta bud'e ta mata sallama ta fita................................ ZUCIYAR ALIYU CE STORY WRITTEN ND EDITING YUSRAH MUSA ABUBAKAR. @YMA DUTSE JIGAWA PAGE 35 Lokacin da ta fito daga gidan Aunty Murjah ganin lokaci ya ja yasa ta tare Napep tun daga layin suka fito ya kai ta gida d'akin ta ta fara shiga ta aje jakarta da atamfar da ta kar6o ta fita ta yo alwala ta dawo d'aki ta yi sallar magriba tana idarwa ta ji an kira isha tashi ta yi taci gaba saida tai sallama ta yi addu'a ta shafa sannan ta tashi ta fita a waje ta ga Umma ta fito da kwanuka daga d'aki ta kai gurin wanke-wanke da mamaki Umma ta ke kallon ta tace. "Yaushe ki ka shigo"?. "Ban dad'e ba na je gidan Aunty Murjah ne bayan an tashi daga school na je hana ni tahowa ta yi wai sai na kwana a can nace mata a'a saboda ina da ayyuka a gida kuma ko ba haka ba ma kin ga ban fad'a a gida ba". "Eh gara da baki kwana ba gaskiya da a kaina abun zai 'kare Hajiya tana ji zata ce ba gidan Aunty Murjah ki ka je ba wani gurin ne daban". "Humm shi ya sa ai ban zauna d'in ba ita ma tace min zata samu lokaci ta zo ta gaishe ku ta dad'e ba ta zo ba". "Gaskiya ta dad'e kam Allah ya kawo ta lafiya ya su Ikram da Aiman d'in". "Duk basa gidan ita Ikram tana gidan kakar ta shi kuma ban ganshi a gidan ba kuma ban tambayi in da yake ba". "Shikenan to ki zo ki ci abinci" Umma ta fad'a tana shiga d'aki bin bayan ta Zainab tai tana cewa "me aka dafa"? Zama a bakin gado Umma tai tana cewa "gashi nan a cikin cooler jallof d'in shinkafa ce" bud'ewa Zainab tai tana d'agowa ta kalle ta tana cewa "amma dai ba ke ce kika dafa ba"?. "Uhm ba ni bace Asabe ce ni sai jibi zan kar6i girkin ai tunda kwana uku-uku ne" maida murfin Zainab ta yi ta rufe tana cewa "ni ba ci zan yi ba". "Kin ci kenan a gidan Murjanatun"?. "A'a ko ruwa ban sha ba ni sai da ki ka fad'i haka ma na tuna ban bud'e fridge d'in ta ba maybe ta yi kalolin zobo da juice iri-iri na taho da shi kuma har kayan had'e-had'en na gani ta shigo da su". "Ba rabon ki sai kin sake komawa". "Ni kam ba zan koma a kwana kusa ba". "Me ya sa"? 'yar dariya Zainab ta yi tana girgiza kai ta'ki cewa komai saboda kar tace saboda abokin mijin Aunty Murjah ne Umma ta yi mata fad'a ita ma Umman daga haka ba ta sake magana ba har wani lokaci tunani ma take a ran ta taje ta samu Sameer ya siyo mata wani abu a waje amma tsoron abin da ya faru ran nan ya sake faruwa kawai ta fasa 'karshe ma tashi ta yi ta fita ganin takalmin baban su yasa ta fasa shiga na ta dakin ta tafi d'akin sa ta shiga ta gaida shi tana fitowa Sameer ya shigo da leda a hannun shi shima ya shiga d'akin Abban ya aje masa ya fito kallon sa Zainab ta yi tana cewa. "Yaya Sameer ina yini"?. "Lafiya ya akai yau baki dawo da wuri ba"?. "Na je gidan Aunty Murjah ne shi ya sa ban dawo ba me ka siyowa baban mu"? Murmushi yayi yana kallon ta yace "shiga ki tambaye shi ko ki ce ya sam miki kad'an" kai ta girgiza tana langwa6ar da kai ta ce "a'a saboda samun lada ka siyo masa ni kuma saboda da rashin kunya da zilama ban siya na 'kara masa ba sai na je ya bani". "Ai ba rashin kunya bane kuma ba zilama bace soyayya ce ke ma ba za ki ci shinkafar ba kenan"?. "Wallahi Yaya Sameer ba ta yi min bane haka kawai na ji bana son cin abinci me nauyi irin su shinkafa da taliya ko dai su doya". "Uhm ka ga babbar yarinya sai 'kwai da 'kwai ke nan"? Ya fad'a cikin tsokana yana kallon ta dariya ta yi tana girgiza kai tace "a'a ni na isa nace sai haka bani da gashin wance ban isa na yi kitson wance ba ni da ba 'yar kowa ba mahaifi na talaka ne bana kai kaina inda Allah bai kai ni ba". "To yanzu fad'a min me ki ke so sai na kawo miki". "Idan zan samu awara na ke so irin ta ranar ka ji". "Tom ina dawowa Allah ya sa ki gan ni da wuri" ya fad'a yana fita kamar za ta ce masa ya jira ta su fita tare ta kar6o amma tsoron abin da zai faru irin na wancan karon yasa kawai ta shige d'aki tana d'aukar wayar ta ta kwanta ganin kiran Afifah kusan uku yasa ta bi bayan kiran amma ta ji bata da kati kuma Sim d'in ta baya flashing dole sai dai gobe sa had'u dan gaskiya ba zai yuwu komai ta ri'ka d'orawa Sameer ba kuma shi Yayan ta ne ba yaron aiken ta ba gashi yanzu ta ce ya siyo mata awara ta ya sai ya siyo ya kawo mata zata sake cewa kati ina dahuwar hankali ayi ta da ruwa. Pillow ta jingina a jikin bango ta jingina a jikin sa ta d'an kwanta ta kunna kallo kafin ya dawo bai dad'e ba ta ji ya shigo yana aje mata ledar ya ce gashi nan kar ki tambaye ni komai akan wannan daga baya kin san ba arziki na bane" yana fad'in haka ya fita saboda ya tabbata idan ya tsaya sai ta yi masa tambaya akan hakan. Aje wayar ta yi ta jawo ledar kusa da ita ta bud'e zaro ido tai da mamaki ta na kallon abin da ya ke ciki rufe baki ta yi tana mi'kewa da sauri ta le'ko waje ko za ta ga takalman Sameer d'in idan ba fita yayi ba amma sai ta ga 'kofar d'akin sa a rufe alamar ba zama ya yi ba fita ya sake yi, komawa ta yi tana zama a fili tace. "Wannan wanne irin abu ne na tabbata Yaya Sameer ba zai siyo min kaza guda ba kuma kazar ma mai tsada kai innalillahi wai waye abokin nan na sa ne yaushe gaskiya za ta bayyana a gare ni ina jin tsoron wannan al'amarin hankali na ba'a kwance ba ta ya zan ci na ji dad'in ta"? Shiru ta yi ta rasa me za ta yi can ta mi'ke tana d'aukar ta ta shiga d'akin Umma ta na ajiyewa tace. "Umma kin ga na ce Yaya Sameer ya siyo min awara idan ya fita saboda ba zan ci shinkafa ba amma kin ga daya fita sai na ga ya kawo min wannan kuma ya ce wai kar na yi masa tambaya a kan haka tun da na san wanda zai ba ni" kallon ta Umma ta yi tana cewa "me ye a cikin nan d'in"? Jiki a sanyaye ta ce. "Kaza ce". "Kaza kuma"? Umma ta fad'a tana bud'awa ta ga tabbas kaza ce babban gashi sai 'kamshi ta ke d'agowa tai ta kalli Zainab wacce ke tsaye damuwa 'karara ya bayyana akan fuskar ta tace "wannan d'in ma daga abokin na sa ne"?. "Eh". "Waye shi"?. "Nima ban san shi ba yace min baya gari wai sai ya dawo zai sanar min" numfashi Umma ta sauke tana cewa "to Allah ya bamu ji da gani na gari Ubangiji ya dawo da shi cikin alkhairi" shiru Zainab ta yi ta na kallon guri d'aya kallon ta Umma ta sake yi tana cewa "d'auki abar ki ki tafi man ki ka tsaya" kai ta girgiza tana cewa. "Ni ba zan ci ba". "To waye zai ci miki idan ma ba ki ci ba zaki kwana da yunwa ne". "Gara kwana da yunwa akan cin abin da hankali na bai kwanta a kan sa ba". "Me ye abun rashin kwancyar hankalin zai sako miki maganin wani abu ne Sameer d'in ne fa ya siyo ba shi wancan abokin na sa bane ki d'auka ki ci zuciyar ki d'aya". "To ai tayi min yawa ko rabi ba zan iya cinyewa ba ki raba ta biyu kin d'auka" kai Umma ta girgiza tana cewa "a'a je ki da kayar ki ni na ci abinci". "Ta yi min yawa ne". "Na sani ki je da ita idan baki cinye ba da safe sai ki d'umama ta" shiru Zainab ta yi ta kafe Umma da ido kamar me nazarin wani abu zuwa can ta dur'kusa tana raba ta gida biya ta saka rabi a kwano ta mi'ke da d'ayar tana cewa "gashi nan sai da safe" tana fad'in haka ta fita ta koma d'akin ta kawai ta aje ledar ta kwanta ta bud'e wayar ta taci gaba da kallon ta har dare ya ja wajen sha d'aya sannan ta kashe ta fita ta yo alwala ta zo ta saka rigar barci ta kwanta ta rufe ido barci ya fara d'aukar ta taga tarrr a idon ta da sauri ta bud'e ta ga ashe nefa ce aka kawo ta manta ba ta kashe 'kwan ba tashi ta yi ta saka caji bata kashe nefar ba saboda dama akwai d'inkin da za ta sakawa stones d'aukowa ta yi ta zo ta fara jerawa tana saka iron tana dannewa har ta gama na rigar ta saka a skirt ta sake d'auko doguwar riga guda d'aya ita ma ta saka mata wajen 'karfe d'aya a lokacin bata gama sakawa a doguwar rigar ba ma ta ha'kura sakamakon dare yayi ta mi'ke ta sake sabuwar alwala ta zo ta yi nafila da yake daren juma'a ne ('yan uwa ku ri'ka yin wannan nafilar daren juma'a raka'a biyu ce "FATIHA DA IZAZUL SAU GOMA SHA BIYAR" raka'a ta biyu ma "FATIHA DA IZAZUL SAU GOMA SHA BIYAR" idan kayi sallama sai ka karanta "YA HAYYU YA K'AYYUM YA ZULJALALU WAL IKRAM 'KAFA D'ARI (100)" Idan kayi haka Allah zai tsare ka da azabar kabari da 'kuncin sa da nau'o'in azabarsa Kuma Allah zai haskaka 'kabarin ka ba za ka mutu ba sai ka ga mazaunin ka a aljannah, dan Allah 'yan uwa ku ri'ka yin wannan nafilar DAREN JUMA'A). Sai da ta idar sannan ta tashi ta cire kayan ta mayar da rigar barcin ta ta kwanta bata dad'e ba barci ya d'auke ta........... J*W*A Ina jinjina ga 'yan ANNURI WRITER'S ASSOCIATION home of hospitality and harmony gidan kar6ar mutane hannu biyu da zaman lafiya ANNURI haske le'ka gidan kowa ko da ma'kiya na kallon ka ramin kura sai 'ya'yan ta. SAFIYA ALIYU WAKILI ZARIA ina mi'ko gaisuwa mara adadi tare da fatan samun nasara da kwanciyar hankali a gare ki Maman khaleel Allah ya ja kwana marubuciyar littafin "MASAUKIN SO". Tare da FATAHIYYAH MUHAMMAD YAKASAI oum Yasmeen marubuciyar littafin "UWAR GAFALALLU" ina mi'ko gaisuwa da jinjina. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 36 Washe gari juma'a bata da lecture a school shi ya sa ya wuni ba ta je ko'ina ba ta 'karawa sakawa mai doguwar riga stone sannan ta yanka wasu ma ta fara d'inkawa a wunin dai babu inda ta je har dare sai d'ari biyar da ta baiwa Sameer ya siyo mata kati ta saka su kai waya da Afifah. Sai ranar asabar da safe sakamakon za ta je islamiyya ta yi wanka da safe ta shirya har ta d'aura nikaf d'in ta ta d'age ta d'auka agogon da Sameer ya bata ta zuba masa ido ji take kamar ta saka kamar kuma kar ta saka mayarwa ta yi ta aje tana kallon sa tare da sauke ajiyar zuciya ta saka hannu a hankali ta sake d'auko sa ta fitar da shi daga cikin kwalin da yake ta d'aura a hannun ta na dama yayi mata kyau sosai kuma ya amshi farar fatar ta sakamakon Brown ne d'aukar jakar ta tayi ta fita. Da ta je wucewa kamar ta shiga gidan su Afifah ta gani idan bata tafi ba su tafi tare sai kuma ta fasa ta wuce tana shiga gate d'in islamiyyar ta hango ta alamar ita ma bata dad'e da zuwa ba domin jakarta na hannun ta ko aji bata shiga ganin Zainab d'in yasa tace "Aunty Zee-Zee ashe kina tafe yanzu na ke tambayar Rasheedat da Zakiyyah 'yan matan gidan ku ai suka ce min kina gida"?. "Eh ina gida sun zo kenan"?. "Uhm har sun wuce ajin su tun d'azu". "Ya Sayyidi fa ya zo ne"?. "Ban sani ba wallahi tun da nima yanzu na shigo ko ajin ban shiga ba". "Tom mu je ajin" wucewa su kai ta fara yin d'orin surar da yake sakamakon ita kad'ai ce ta ke d'aukar ajin sai 'karfe d'aya su ka tashi Afifah dake tsaye tana jiran Zainab ta gama had'e abubuwan ta su tafi ita kuma ta na du'ke tana tattare littafan karaf idon Afifah ya sau'ka akan agogon da ta kai wa Sameer zaro ido ta yi tana kallon Zainab wacce ta d'ago za su tafi ta ce. "Lahhhh Aunty Zee-Zee wannan agogon ke Yaya Sameer ya barwa dama"? Ta fad'a tana ri'ko hannun Zainab d'in ta d'an shafa shi cike da sha'awa kallon ta Zainab ta yi da alamar tambaya tace "ta ya ki ka san Yaya Sameer ne ya ba ni"? Murmushi Afifah tai tana sakar mata hannu bayan ta d'auki jakar sun fita daga islamiyyar tace. "Saboda nice na kai masa shi a cikin kwalin sa shi ya sa na fad'a" da mamaki Zainab ta kalli Afifan wacce ita ma take kallon ta tace "ke kuma"?. "Eh man ni ce na kai masa wallahi ina son agogon nan har na d'auka nawa ne kawai ina ta murna daga baya murnan ta koma ciki aka ce na tashi na kai masa" a razane Zainab ta sake cewa "amma waye ya baki ki kai masa"? D'an murmushi Afifah ta yi ba tare data duba yanayin rud'anin da Zainab d'in ta shiga ba tace. "Humm Yaya discipline ne ya aiko su guda biyu tun daga can inda yake d'aya ya baiwa wata Amirah 'yar gidan abokin Daddyn mu wannan d'in kuma na d'auka nawa ne saboda tun kafin ya yo aiken ni yace a baiwa idan an kawo ina ta murna kawai ina zaune nayi ready zan bud'e ya kira ni a waya yace na kaiwa Yaya Sameer yana chemist ashe rabon ki ne ke Yaya Sameer zai barwa ai dama nace na mata ne shima sai dai yayi kyauta dashi" shiru Zainab tai gaban ta na faduwa a ranta tace. "Hakan yana nufin Aliyu ne ya aikowa Yaya Sameer kenan ya ce a bani kar fa ace shine yake min duk wadannan abubuwan ba dai shine yake so na ba"? Jin abinda zuciyar ta tace yasa a razane ta girgiza kai tana kallon Afifah wacce hankalinta yake kan wata 'kawarsu da ta biyo bayan su suka taho tare iya su kad'ai su ke magana amma ban da ita da take tafiya tana had'a hanya da'kyar ta yiwa Afifah sallama lokacin ta wuce gida ita kuma ta mi'ke kai tsaye chemist d'in Sameer ta wuce gabadaya fuskar ta a 6ace ya yi mamakin ganin ta a haka domin ko kad'an bai kawo a ran sa maganar agogo za ta yi masa ba shi ya sa yace. "Zainab lafiya akwai matsala ne na gan ki a haka ba daga islamiyya ki ke ba"? Kai ta d'aga ta na ciro masa agogon da yake d'aure a hannun ta tace "Yaya Sameer waye ya baka agogon nan ka ba ni"? Bin agogon ya yi da kallo kafin ya mayar da hankalin sa kan ta yana cewa. "Me yasa ki ka tambaya kuma bayan abu ya wuce"?. "Saboda ina son sani dan Allah ka ji Yaya Sameer ni a guna bai wuce ba ka fad'a min ko na samu kwanciyar hankali"? Kar6ar agogon ya yi yana bud'e zip d'in jakar ta ya saka a ciki ya na cewa "kar ki damu za ki sani amma ba yanzu ba sai lokacin daya d'iba ya cika shi da kansa zai bayyana miki kansa ki gan shi nan ba da dad'ewa ba ya na tafe kin ji ko"? ya fad'a yana harhad'owa wanda ta samu a zaune magani kallon sa take da idonta wanda suke gani dishi-dishi gabadaya kan ta juyawa ya ke ta rasa me ya ke mata dad'i za ta samu kwanciyar hankali ne kawai idan Sameer ya fad'a mata wanda ya bata wannan agogon . Saida ya baiwa mutumin magungunan ya yi masa allura ya tafi sannan ya kalli Zainab ya na murmushi zai yi magana ta girgiza kai tana cewa "Yaya Sameer Aliyu ne ya baka yace ka ba ni"? Yayi mamaki da yaji ta kama sunan Aliyu lokaci guda waye ya fad'a mata fargaba yaji ta kama shi amma dan kar ya sake d'aga mata hankali akan yadda ta ke ciki sai ya dake yana 'kure ta da kallo yana d'auke gira yace. "Wanne Aliyun ki ka fad'a"? Muryar Zainab har rawa take da'kyar ta ce "Aliyu Yayan Afifah" huci ya fitar ya na sake duban ta yana cewa " "Waye ya fad'a miki"? Kai ta girgiza ta na cewa "ba kowa bane ya fad'a min ganin sa Afifan tayi a hannu na d'azu na je islamiyya da shi ina tattare littafai tace Aliyu ne ya aiko su guda biyu daga inda yake d'aya ya baiwa 'yar abokin baban su d'ayan yace a kawo maka haka ne"? Jin ta kamo magana daidai ya san babu ta yadda za'ai ya kawo mata wata hujja shi ya sa yace. "Eh haka ne abin da ta fad'a mi ki" wata irin bugawa zuciyar Zainab ta yi kan ta ya d'auki ciwon damuwa lokaci guda ta nemi dukkan nutsuwa da jarumtar ta ta rasa runtse ido ta yi ta na son hawa hawayen daya taru mata a ido fitowa ta ce. "Kenan Yaya Sameer Aliyu Yayan Afifah shi ne abokin naka da ya ke so na"? Shiru yayi bai bata amsa mata jin bai yi magana ba ya sa ta bud'e ido tana kallon sa ta ce "Aliyu shi ne ya ke min duk wadannan abubuwan"? Nan ma shiru ya yi bai bata amsa ba sake dafe kanta ta yi jin ta ko'ina ciwo ya ke mata addu'a ta fara karantawa a cikin ranta tana wannan hali ta ji muryar Sameer ya ce. "Zainab kar ki rud'a kan ki akan haka kar kisa cewa Aliyu ne ya ke miki duk abinda na ke baki bana so ki fitar da wannan zancen har wani yaji zaki jawowa kan ki matsala a gidan nan ki na zaune lafiya wallahi iya bakin mutune ma ya ishe ki ke ma sheda ce". "Kenan hakan ya nuna da gasken shi ne ya ba ni"? Kai ya jinjina yana cewa. "Zainab ki na ji.................... ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA DUTSE PAGE 37 Katse shi ta yi "Yaya Sameer idan shi ne ka fad'a min na daina tunani ina wahalar da kai na" ganin da yai ba za ta bar zancen ba yasa ya had'e rai yana cewa "Zainab kin san ba na son irin wadannan abubuwan ko na fad'a miki abin da ya kamata kin kasa ganewa idan kuma na baki number sa ne sai ki kira shi ki tambaye shi da kan ki kiji idan shine ya baki ma zai baki amsa tunda naga kamar haka kike so ko"? Kaita girgiza a damuwance tace. "A'a a'a ba sai ka bani ba abun ne ya d'aga min hankali akan me Aliyu zaice yana so na shi ba sa'an aure na bane". "Saboda me"?. "Saboda ya fi 'karfi na ni y'ar talaka ce shi kuma fa d'an minister guda bayan haka bamu kasance mutane irin su ba kai ma ka sani Yaya Sameer". "Zainab so ba ruwan sa da duk wadannan abubuwan da kika lissafo sannan so yana da abun mamaki kuma shi ne zai kai ki inda baki ta'ba tunanin zaki je ba a rayuwar ki kamar dai hakan babu yadda zaki yi idan Ubangiji ya 'kaddara miki cewa shi ne mijin naki" ya na rufe baki a rud'e ta fara girgiza kai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un wacce irin makauniyar 'kaddara ce wannan ta same ni abin da ban ta'ba kawowa a raina ba shi ya same ni Yaya Sameer bazan saka hakan a rai na ba balle ya dame ni indai akan Aliyu ne". "Me ya sa Zainab""?. "Saboda d'an mai kud'i sai 'yar mai kud'i haka nima ina matsayin 'yar talaka ya barni na auri d'an talaka daidai da ni ba zan kai kaina inda Allah bai kai ni ba zan tsaya iya matsayi na ni ba zan auri Aliyu ba" tana fad'in haka ta juya ta fita daga chemist d'in murmushi Sameer yayi bayan wucewar ta ya girgiza kai duk da bai so tasan cewa Aliyu ne ya bata wannan agogon ba kwata-kwata sha'afa yayi da ya san zata saka har Afifah ta gani da ya barshi a gurin sa daga baya idan tasan Aliyun ne yake son ta sai ya d'auka ya bata sai dai mai faruwa ta riga ta faru yanzu kuma za'a shiga sabon babin abubuwan tunda har ta fara zargin Aliyu ne yake son ta komai zai ba ta da Aliyun za ta danganta shi ta daina zargin wani. Saboda Zaid ya san in dai Hajiya ta ji labarin ya had'o kayan lefe za ta ce babu in da za'a fita dashi sai dai ya auri Zainab shi ya sa su ka bari saida dare Asiya ta saka su ka fita da shi daga gidan aka kai gidan wata aminiyar ta washe gari da safe sai ta saka Adama da Mairo su je su had'u a gidan ta a kai lefen kawai idan ta ji an kai duk tsiya ai ba za tace a dawo da su ko aje a kar6o ba. Amma me a garin fita da shi Rasheedat ta na waje tare da saurayin ta kuma ta ga lokacin da Asiya ta tsayar da me Napep ta shigar da akwatunan guda uku ta shiga su ka wuce kai ta jinjina bayan sun gama maganar da za su yi sun yi sallama da sauri ta fad'a gida kai tsaye ta wuce 'kofar Hajiya cike da gulma ta yi sa'a kuwa iya Hajiyan ce ita kad'ai a waje ta shimfid'a 'katuwar tabarma tana zaune cire takalman ta ta yi tana zama tace "Hajiya albishirin ki"? Kallon ta Hajiya ta yi tana cewa "ba na son yawon munafirci fa kema kar ki zo ki fad'a min irin abin da Haule ta fad'a ran nan ki sa na fita a banza". "A'a Hajiya ba wannan ba ne wani abu na gano miki yanzu". "Me ya faru"? Cire hijab Rasheedat ta yi tana cewa "ki ce min goro mana sai na fad'a miki"?. "Ke ba na son shashanci wai me ya faru ko munafirci na ki ka ji tsinannun matan gidan nan su na yi". "A'a gagarumin abu na gano miki wanda yafi gulmar ki wai kin san Yaya Zaid ya had'o kayan kuwa"?. "A'a ta ya zan sani dama ya had'a ba su zo sun fad'a min ba saboda 'yan ba'kin ciki ne gado ba'kin hali Asiya ce ko"? Dariya Rasheedat ta yi tana cewa "au nan d'in jira ki ke su zo su fad'a miki sun gama had'awa? Tabd'ijan ai kuwa gara ki daina saka rai indai ba bayan auren zaki je gidan nasa matar tasa ta nuna miki kayan ba" wani kala Hajiya tai tana cewa. "Ban gane ba me ki ke nufi"?. "Bari na fad'a miki gaskiya Hajiya domin ko kowa zai ci amanar ki ban da ni maganar Allah yanzun nan na ga Umman Yaya Zaid ta fita da akwatuna guda uku daga gidan nan ta tare me Napep ta shiga ban san inda za ta kai su ba" a zabure Hajiya ta dafe 'kirji ta na zaro ido tace "ke 'yar nan da gaske ki ke yi kuwa"?. "Wallahi Hajiya da gaske na ke da idanu na na gan ta lokacin da ta hau Napep d'in" kai Hajiya ta jinjina tana cewa "wato akwatin Zaidu za su kai wani gurin ba tare da na sani ba ko"?. "K'warai Hajiya ni ganau ce ba jiyau ba alamu ya nuna ba su mai da ke komai ba baki da amfani tun da da sauran ran ki ma sun daina saka ki a cikin al'amarin su balle kuma nan gaba so su ke ki mutu ma na sani". "Kan bala'i ai kuwa sai nace uban duk shegen dana samu da goyon bayan sa a gidan nan bari Habibun ya dawo sai naci uwar matarsa yau sai ta bar gidan nan sai dai ta yi kwanan Hotoro tun da mitsiyaciya ce" jin abinda ta ce ta had'o abun har da Habibu kuma in dai ya san ita ta had'a bomb d'in uban ta zai ci shi ya sa cewa "amma fa Hajiya kar kice nice na fad'a miki" a masife Hajiya tace . "Saboda me"?. "Saboda za su ji haushi na". "Na buge uban wanda yaji haushin naki dan uban su tashi ki raka ni 'kofar ta ku kafin Habibun ya dawo ya sai naci mutuncin duk wanda na samu da hannunsa a cikin lamarin tashi mu je"................... ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH YMA PAGE 38 Gyara zama Rasheedat ta yi tana cewa "ni dai gaskiya Hajiya ba zan je ba haka kawai ba za a gan mu tare ki jawo min duka a gurin baban mu ba". "Yadda ya ban haushin nan ya dake ki ai sai na tsine masa ta so mu je". "A'a Hajiya ki zauna bari Zakiyyah ta shigo sai mu raka ki mu biyu kin ji"?. "Ba na so idan ba za ki raka ni ke kad'ai ba ki barshi bari na je" ganin ta mi'ke tana shirin saka takalmi ya da hankali a tashe Rasheedat ta ce "kin ga Hajiya ki zauna bari na je na gano miki idan abban namu ya dawo sai na zo na fad'a miki ki je" jin abinda ta ce yasa Hajiya fasa fita amma ba ta zauna ba tace "shi ke nan dubo min" da sauri Rasheedat ta mi'ke saboda tana son fitar da kan ta ta d'auki hijab ta maida ta saka takalmi zata fita Hajiya ta ce "kuma kar ki dad'e kiyi sauri ki dawo ki fad'a min dan a wuya na ke" fita Rasheedat ta yi amma da ta je 'kofar ta su kasa shiga ta yi tana tsaye ta bayan ta taji an ce. "Waye wannan"? A firgice ta juya ganin baban su ya sa ta matsa gefe tana cewa "sannu Baba" kallon ta yayi yana cewa "yauwa tsaiwar me ki ke anan"? Cike da rashin gaskiya ta ce "uhm uhm am wannan da.dama wai Hajiya ce tace na zo na kira ka" da mamki ya ce "Hajiya kuma? Me ya faru"? Kai ta girgiza tana yin 'kasa da kai gani ta ke kamar zai gane da'kyar ta ce. "Ni ma ban sani ba kawai cewa ta yi na kira ka" juyawa ya yi yana nufar 'kofar Hajiya d'in ya bar Rasheedat a gurin a tsaye wacce tsoro ya hana ta koma ta raka6e ta ji me Hajiya za ta ce masa kuma ta kasa shiga 'kofar ta su saboda gudun kar sai ta shiga d'aki ta je Hajiyan ta fad'a masa ita ta kai gulmar ya shigo ya dake ta ci gaba ta yi da tsaiwa a gurin ta na jiran ta ga a yadda zai fito ta na tsaye ta ga Asiya ta dawo daga kai akwatunan ta shiga 'kofar ta su kai ta jinjina tana sake sabuwar tsaiwa tun da har ta ga ta dawo yanzu sabuwar guguwa za ta tashi. Habibu kam yana shiga Hajiya ta rufe shi da fad'a "yanzu kai Habibu saboda bankad'a ta same ka ka na kallo Zaidu bazai rufawa 'yar uwarsa asiri ya aure ta ba shi ne da nasa a had'o akwati ku kai taro ba tare dana sani ba kuka d'auke kuka kayi gidan wadancan budurwar tasa ko"? Da mamaki Habibu ya ce "Hajiya wa ye ya fad'a miki"?. "Au waye ya fad'a min ka ke tambaya ba abinda na ce ayi zakai ba? To bari ka ji ba sabuwar 'kofa ba ko tsohuwar 'kofa wancan budurwar ta ke ku je ku kar6o kayan ku dawo da shi" shiru Habibu ya yi cikin rashin sanin abun yi ya sani yanzu muddin ya fad'i wani abu in dai ba batun da Hajiya ta ke so bane shi za ta d'orawa laifin komai......... "Wai ina magana ka yi shi ko ba ka ji abin da na ce ba"? Ya ji Hajiyan ta sake jefo masa tambaya kai ya girgiza ya na cewa "shikenan Hajiya ba damuwa in sha Allahu zan yi masa magana za'a kar6o" ya na rufe baki tace "idan ya'ki kar6owa ma sai ya had'o wani ya auri Zainab ko zai mutu na gama yanke magana tashi ka bani guri". "Ki yi ha'kuri Hajiya". "Zan ha'kura ne kawai idan ka saka d'an ka ya yi min abin da na ke so" jin abinda ta ke sake maimaitawa ya san indai ba Zain ne ya auri ba bazai ta'ba hutawa ba kuma kome zai ce mata bazai fita daga zargi ba fita yayi ya koma 'kofar sa a d'aki ya samu Asiya shi ya sa ya zauna yayi mata bayanin yadda su kai da Hajiya su kai da Hajiya sannan ya tambaye ta duk inda ta kai akwatunan ta dawo da su kawai Zain ya ha'kura da wancan yarinyar ya auri Zainab d'in nan komai ya wuce. Kai Asiya ta girgiza ta na cewa "yanzu tsakani da Allah ba za ka iya tausar Hajiya ta ha'kura da batun zuwa a kar6o kayan nan ba wacce irin rayuwa ce wannan"?. "To ya zanyi Hajiya ba za ta ta'ba ha'kura da batun nan ba tun da ta saka a ran ta" baki Asiya ta ta'be tana cewa "an riga an kai kayan fa ta ya za'a koma a kar6o"?. "To me ya sa ku ka bayar da kayan aka kai ba tare da kun sanar min ba hakan kun yi daidai kenan"?. "Ka yi ha'kuri ba dan na 6ata maka rai ba ne saboda gudun fad'an Hajiya ne ya sa nayi haka kuma gashi mun gudu ba mu tsira ba ba yadda za'ai mu saka a koma a kar6o kayan nan". "Ki na ji Asiya ni fa baza ku jawo min matsala ba indai batu akan Hajiya ne ban san yadda zan yi da ita ba" ganin kamar goyon bayan Hajiyan ya ke akan abin da ta ke so yasa Asiya cewa "da yadda zakai man rayuwa ba'a dole shi fa Zaidu yace baya son had'in auren gida ka ga kuwa ai abu ba mai yuwa ba ne tun da shi zai zauna da ita ba mu ba kuma yace ba ya so" numfashi Habibu ya sauke gabadaya sun saka shi a hau duk gurin wanda ya je daga Hajiyan har Asiya kowa murd'add'an kan sa ne kallon yadda take ke huci ya yi yana cewa. "Yanzu ya ku ke so ayi ke da Zaidun"? Gyara zama Asiya ta yi tana cewa "kawai yanzu abu mai sauki zuwa za ka yi ka fad'awa Hajiya gaskiyar abin da Zaidu ya ce shi bazai auri Zainab ba wannan shi ne magana" kallon mamaki ya mata ya na cewa "me ne kin san abin da ki ke fad'a kuwa ni ne zan tunkari Hajiya da wannan maganar so ki ke ta tsine min"?. "A'a ni ba haka na ke nufi ba amma................. "Amma me? Kin ga Asiya idan ke bakya gudun 6acin ran Hajiya ni ina gudun sa saboda mahaifiya ta ce idan ta min baki zai kama ni dan haka ba ruwa na shawara ta rage ta ku idan Zaidu ya shigo ko da safe ne ki fad'a masa sa'ko daga Hajiya ya sake sabon lefe na auren Zainab ko ku je ku kar6o wancan da ku ka kai idan kun 'ki zan yi mata bayani domin na fitar da kai na" yana fad'in haka ya mi'ke ya fita daga d'akin ya tafi na sa baki Asiya ta ta'be bayan fitar sa tace. "Wallahi tallahi na rantse da Allah ba lefen da zai sake had'owa tsinke ba zai 'kara siya ba ban ga ta yadda za'ai na amince ya auri Zainab ba tun da ba ya sonta baza'a takura masa ba ai ba shi kad'ai ne namiji a gidan ba ni na goyi bayan sa ko da Hajiya zata saka a sake ni sai dai a sake ni d'in akan na bari Zaid ya auri Zainab.................... ZUCIYAR ALIYU CE 🖋️J♣W♣A🖋️ @YMA YUSRAH DUTSE PAGE 39 Zaid kam bai shigo 'kofar su a daren ba sai washe gari da safe ya shigo gaisar da Asiya ta tsayar da shi ta ke maimaita masa yadda su kai jiya da Habibu akan kayan lefen da Hajiya ta samu labarin an had'o shi ya sa tun daren jiya ta d'ebe akwatunan daga gidan ta kai gidan aminiyar ta. Jin sa'kon da Hajiya ta bayar a fad'a masa ya sa yace "wallahi Mama babu inda za'a je a kar6o wani akwatuna na riga da na bayar a kayi kawai tsabar zubar da girma sai ku koma ku kar6o wai me yasa Hajiya ta ke min haka ne ba wanda ta takurawa a gidan nan sama da ni kowa an bar maganar auren da zai yi amma ni ta dage sai na auri Zainab wallahi Allah ba zan auri yarinyar nan ba". "Kai kar ma ka 6ata bakin ka nima ina goyon bayan ka kuma ko a gaban Hajiyan ne ta kira ka kar kaji wani tsoro ko shakka ka fad'a mata cewa kai baza ka auri Zainab ba baka son ta mu gani me zata ce maka duk tsiya ai ba za ta kore ka daga gidan ba dan na ga gadarar ta kenan da an yi magana za ta ambaci gida kamar ita ba za ta mutu ta bar shi ba ko me za tace maka kar kayi shiru ka mayar mata da martani". "Balle ma me zata ce duk abin da zata fad'a ina daidai da ita". "Yauwa Zain na san idan ka yi kmata 'karyar baka da kud'in da zaka sake yin sabon lefe zata iya cewa kawai ka bada sadaki a d'aura muku ba sai ka yi mata lefen ba idan ka je ka fad'a mata abin da yake ran ka kai Zainab d'in ce ba ta yi maka ba idan ka 'ki kana kallo ko Abban ku sai ta saka ya biya maka sadaki an aura". "Kai haba wallahi fa bazan aure ta ba tunda na rantse akan hakan ko tsautsayi yasa an je wajen aurin aure na naji an sake aura min ita wallahi ina dawowa gida zan rubuta mata takarda saki uku sai dai na bar gidan nan akan haka". "Allah ma ya sauwake akan wata baza ka je ko'ina ba kana nan zama diss ba yadda za'ai da kai wallahi ka zama ciwon ido zama da kai sai ha'kuri nan gani nan bari d'umamen mayya" mi'kewa Zain ya yi yana cewa "har na ji rai na ya 6aci iya wannan maganar da mu ke bari na je gurin Hajiyan yanzu" kallon sa Asiya ta yi tana cewa. "Me za ka je fad'a mata"?. "Zan fito fili na fad'a cewa ba zan ta'ba auren Zainab ba har abada koda ta rasa mijin aure ne garama ta daina min tallar ta saboda ba na so kuma ba zan yi abinda zai takurawa rayuwa ta ba ina matashi wannan tsohuwar ba za ta d'ora min ciwon zuciya da hawan jini ba" kai Asiya ta jinjina har da sakin murmushi tana cewa . "Yauwa d'an albarka je ka da kan ka kar ka yi sanyi ka bud'e murya yadda za ta ji ka sosai ka fad'a mata ba ka son auren dole da take neman 'ka'kaba ma ka" bai tsaya jin 'karshen abin da zata fad'a masa ba ya yi waje kan sa tsaye 'kofar Hajiya ya shiga tana ganin sa ta fara hararar sa shi ma had'e rai ya yi sosai ya tamke fuska ko ina kwana bai ce mata ya fara magana. "Hajiya na ji sa'kon da ki ka baiwa Abban mu ya fad'a min amma ni Zain............. Tun bai fad'i abin da zai fad'a ba ta tare shi da fad'in "eh ba dole na bashi sa'ko ba na ga kun mayar da ni tsohuwar banza wacce ba ta da daraja a idon ku har kamar ni ce zan ce ku yi min abu amma ku 'ki yi kun kyauta kenan a ganin ku saboda rashin tarbiyya"?. "Me ki kace mu yi mu ka 'ki yi? ke ma fa Hajiya ba haka ake rayuwa ba an ta'ba so dole ne da za ki ce sai na so Zainab na aure ta ni ba na son ta kuma ba zan ta'ba son ta ba har abada akwai wasu mazan a gidan nan ki neme su ku tattauna maybe ki samu wanda zai kar6i ta yin ki amma ba dai ni ba" gwalo ido Hajiya tai tana kallon sa tace "au ba za ka aure ta d'in ba kenan ka bujirewa umarni na"?. "Ni fa Hajiya kar ki nemi d'ora min laifi na fad'a miki iya gaskiya ta ne bazan auri Zainab ba kawai bazan aure ta ba ina nufin bazan iya ba, bana son ta bana sha'awar zama da ita" kallon sa sosai Hajiya ke yi daga baya ta jinjina kai tana cewa "shikenan Zaidu ka kyauta kar Allah ya sa ka aure ta d'in tashi ka bani guri marar mutunci fitsararre" tashi Zain ya yi yana nufar 'kofar fita yace "kome za ki ce ta haushi ta biyo aure dai nace bazan aura ba". "Kar ka aura d'in man bankad'add'e Allah ya sa matar da zaka auro ta ri'ka yi wa Asiya dukan tsiya kai kuma tana kwara maka ruwan sanyi idan ka na barci kuma ta mayar da kai mijin tace ta ri'ka saka ka shara da wanke-wanke zan yi ta addu'a in Allah ya yarda ba za ka ji dad'in auren da za ka yi ba tun da ka 6ata min rai" shi kam Zaid ba jin ta yake ba domin ya riga ya yi tafiyar shi. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH JIGAWA PAGE 40 Tashi Hajiya ta yi ko takalmi ba ta d'iba ta saka ba ta fita ta shiga 'kofar su Zaid a lokacin Asiya tana waje tana wanki ko sallama babu ta na shiga tace. "Ke Asiya wato ke ce ki ka zuga Zaidu yaje yayi min rashin kunya akan nace ya had'o wani lefen ya auri Zainab ko? Tunda kika hana shi auren ta insha Allahu matar da zai auro miki sai ta zame miki masifa da bala'i sai kin shiga uku a wurin ta yadda ki ka wulakanta ni ki ka raina ni ke abinda za ta yi miki sai ya ninka nawa sau dubu matsiyaciyar mace kawai" tana fadin haka ta juya ta fita baki Adama ta ri'ke bayan fitar Hajiya ta fito daga d'aki tana kallon Asiya wacce ke hararar 'kofar da Hajiyan ta fita tace "amma mu dai mun shiga uku a gidan nan dan masifa uwar miji ta hana ka sukuni tunda na shigo gidan nan ban ta'ba ganin ranar da ta fito ta fad'i Hajiya ba tayi fad'a da surukar ta ba ke ma abun ya juyo miki kamar yadda ta ke takurawa Hauwa" ta6e baki Asiya ta yi tana cewa. "Ai ni kuma nafi 'karfin ta ina daidai da ita duk abinda take ji dashi na fita 'karshe bai wuce ta ce Habibu ya sake ni ba ni kuwa ban damu ba tunda d'ana ya d'ago ya mallaki gidan kansa inda zan zauna dai ba rasawa na yi ba balle ta ce dole sai a inuwar d'an ta kad'ai zan rayu ni ma Allah ya yi min arzikin d'an" kai Adama ta girgiza tana cewa. "A'a in sha Allahu ba za ta ce ya sake ki ba kawai dai bala'i ne ba za ta daina miki ba sai dai idan mutuwa ta yi dan nasan ko ranar d'aurin auren ma sai ta zo ta yi miki ga dangi sun cika gida sannan ko haihuwa matar tayi nan ma sai ta tuna baya ta zage ki ta ce da yanzu Zainab ce ta haihu da shi kece ki ka hana". Mi'kewa Asiya ta yi tana d'iban kayan data d'auraye ta fara shanyawa tana cewa "na hana d'in nima hanau ce ta hana ni kin ga nifa yanzu lamarin Hajiya baya sha mun kai domin tun ina jin shakkar ta yanzu ta saka ko kad'an bana tsoron ta kina gani fa har so take wani abu ya had'o mu da ita nayi min tas to ni ma yanzu ba 'kyale ta zanyi ba jira nake babban abu ya had'o ni da ita na zage ta tas yadda a gaba zata kiyaye ni" jin abin da Asiyan ta ce yafi 'karfin d'auka ya sa Adama cewa. "Uhm mu kam babu abin da za mu ce saidai Allah ya rufa asiri" ta fad'a tana wucewa ta d'auki buta ta shiga band'aki. Batun Hajiya kam tana fita daga 'kofar su Zain 'kofar su Zainab ta wuce nan ma ta soma 'kwallawa Umma kira tun kafin ta 'karasa shiga "Hauwa Hauwa" da sauri Umma ta fito daga d'aki tana zuwa kofar shigowa lungun nasu tare da dur'kusawa ta ce "gani Hajiya" kallon ta Hajiya tai tana cewa. "Duk abinda ya kamata ace na yi matsayi na na kaka a wurin Zainab nayi 'ko'kari akan ta samu mijin aure idan baku gode min ba baza ku tsine min ba yanzun nan daga kofar Habibu nake wancan mitsiyaciyar ta hana Zaidu ya 'karo lefen da zai auri Zainab to yanzu dai ban san yadda zaku yi da 'yar ku ba shawara ta ragewa me shiga rijiya ko ya saka igiya ya shiga ko ya dirga idan kuma zaku je ku fad'awa liman ya cikita muku ko za'a samu mai auren ta nan ma dai ku kuke yi ni na gama iya nawa tashi ki je" tana fad'in haka ta juya ta tafi tashi daga tsungunen da take Umma tai ran ta babu dad'i ta kalli kofar d'akin Zainab ta ga takalmin ta yana nan maybe ta ji wannan maganar kamar zata bud'a ta le'ka ta amma tunanin irin halin da zata riske ta a ciki yasa kawai ta koma d'akin ta jiki a mace. Zainab kam tana kwance a d'aki ta zubawa celling ido tana jin komai abin da Hajiya ta ke cewa numfashi ta sauke ba ta iya aikata komai ba ta rasa me ya kama ta tayi a wannan lokacin kuka ko tunani ko me ta na jin yadda Asabe ke gud'a tana shewa ta na faffad'awa Umma maganganun banza marasa dad'i amma ko kad'an ba ta ji muryar Umman ba cije lips tai lokacin da taji Asaben tace "ai ba lallai Zainab ta samu mijin aure ba watakil a haka zata 'kare rayuwar ta a gida kawai abinda yafi sauki zan ba ku shawara ku siyo mata kayan d'akin ta ta jera abun ta ta ri'ka kallo ko ya rage mata rad'ad'in rashin auren da take ji ko dan ina kud'in kayan d'akin tunda daga ke har shi ba arziki gare ku ba me ku ka tara mu na nan mu na jira za mu ga ta inda mijin na ta zai fito kuturu ne ko makaho ne wa ya sani" ta 'karasa maganar tana she'kewa da dariya ta sake sakin gud'a kamar za ta cire hanci saboda farin cikin abinda ya faru yanzu. Humm Allah sarki duniya mai cike da abubuwan mamaki da al'ajabi duk wadannan maganganun da Asabe ke yi Umma ta na jin ta amma tsabar ha'kuri ko cira kai ta kalle ta ba ta yi ba balle ta mayar da martani sai Zainab dake d'aki hawayen damuwa su na ta zuba mata Allah ya gani ba za ta iya wannan masifar ba in sha Allahu ana yin hutun makaranta za ta tafi D'an Yana ba za ta dawo ba sai hutu ya 'kare idan ba haka tai ba ba'kin ciki sai ya saka zuciyar ta ta buga a gidan nan................... 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 ><°°>< YSRH @JIGAWA STATE PAGE 41 Kamar yadda Hajiya ta ce ba za ta sake magana ba akan auren Zain da Zainab haka ne ya faru duk abin da ake ta na shan kallon su sai dai ta d'au fushi ta cika ta yi dam duk ranar girkin Asiya idan an kai mata ba ta ci sai dai ta kora yaran da ya kawo ya mayar bata huce ba har lokacin bikin ya yi hatta goro da aka bata da ta amsa bayan fitar Habibu ta taso ta zo ta watsawa Asiya a kan ta ta juya ta fitce tana cewa ko ba ta ta'ba cin goro ba baza taci na auren Zain ba. Aunty Murjah ba ta samu damar shigowa ba ranar da aka fara bikin sakamakon can ma wani bikin ne da su shiyasa ta bari sai ranar dinner ta d'an le'ko musu ta wuni a d'akin Zainab su na ta hira da dariya musamman da Aunty Murjah ta ke ce mata Mukhtar ya na neman ta ya kamata ta je su gaisa. Da lokacin tafiya dinner yayi babu yadda Aunty Murjah ba ta yi ba Zainab ta ce ita babu inda za ta je da ta yi wankan ta ma keken ta ta hau take rage d'inkuna Umma ba ta san bata je ba duk zaton ta da taji Aunty Murjah ta na mata sallama tana cewa sun tafi ta d'auka da Zainab d'in ne d'age labulen d'akin ta yi tana le'kawa ta ce. "Zainab ke baza ki je gurin dinner ba naga kinyi wanka na d'auka ma tafiya zaki yi sai kuma naga kin hau keke kina d'inki dama ba tare da Murjanatu za ku tafi ba"? Kai ta d'aga tana cewa "eh Umma gaskiya ba zuwa zan yi ba". "Amma me ya sa kowa fa ya tafi ke kuma ki na gida babu dad'i me ye dalilin da za ki ce baza ki je ba"?. "Wallahi babu komai kawai son zuwan ne bana yi musamman kin ga harkar da ya shafi kid'a ne ba abun burgewa anan". "Amma Zainab wannan rashin zuwan naki baza ki ta'ba fita ba 'yan gidan nan za su yi tunanin ko damuwa ce ta hana ki zuwa ko 'kin amincewa da Zaidu ya yi ya aure ki kishi ya sa ba za ki je ba kodai wani abu ne" murmushi Zainab tai ta na cewa. "Damuwar me ne zai saka har na yi abun da zai takura min in dai ina son zuwa". "Gani za su yi kamar saboda baki yi aure ba ne su kuma suna matsayin 'kannin ki shiyasa kike 'ki zuwa gashi harda Haulat yanzu kowa d'auka zai yi kina daga cikin wad'anda suke yi ba'kin ciki shiyasa baki je d'in ba balle gashi abinda ya faru tsakanin ki da Zaidu ke bakya tsoron hakan ne"? Shiru Zainab tai tana kallon wayar ta da ta kawo haske alamar kira domin ta saka ta a silent *bro S* ne yake kiran ta tasan bazai wuce akan bai ganta a gurin dinner d'in bane ita kuma gaskiya duk wani abu daya shafi harkar kid'e-kid'e ta tsana d'agawa ta yi Umma kuma ta saki labulen tana barin 'kofar d'akin tun kafin Zainab ta yi magana Sameer yace. "Zainab kina ina ne tun d'azu sai neman ki nake yi a gurin amma ban gan ki a ko'ina ba kina ta wajen ina ne na kasa samo ki"? Numfashi ta sauke tana cewa "Yaya Sameer ina gida ban zo ba". "Me ya sa ba ki zo ba"?. "Babu komai". "Bakya ra'ayin zuwan ne ko kuma yaya"?. "A'a kawai dai ba na son jin 'kara ne gashi ta wayar ma ina jin tashin sa balle wanda ya je gurin gara na zauna a gida na yi d'inki na ya fi min alkhairi" ji ta yi yace "ok sai mun dawo mu kam sai mun ga abin da ya turewa buzu nad'i" yana fad'in haka ya kashe wayar yana amsa kira da alama wani ne yake kiran sa a wurin dan ta jiyo sanda aka ce Sameer d'an murmushi tai tana girgiza kai wato sai sun ga abinda ya turewa buzu nad'i kenan rawa Yaya Sameer zai yi ko me? Dariyar da ba shiri tayi tana ci gaba da d'inkin ta kafin ya dawo ta san zai d'auko video ta kar6a ta gani". Kamar mintuna talatin ta ji sallamar Sameer da mamaki ta tsayar da d'inkin da ta ke dan ta ji kunnen ta ne ko kuma shi d'in ne ji ta yi yana magana da Umma a ranta tace "Subanallahi Allah ya sa ba zuwa ya yi mu tafi b........... Tun kafin ta 'karasa addu'ar da ta ke yi ta ji yace "Zainab ki na ina"? Numfashi ta sauke tana cewa "ga ni a d'aki". "Ok fito mu tafi gurin dinner d'in nan" jin abinda yace yasa ta d'an 6ata fuska ta na mi'kewa ta fito waje ya na tsaye a kusa da 'kofar d'akin nata ganin ta fito ya sa yace "koma ki d'auko mayafi da handbag d'in ki mu tafi saboda na d'auke ki na dawo". "Ni fa Yaya Sameer.............. "Kar ki ce min ba za kije ba dan Allah taho mu tafi gashi kin yi wanka ba tsayawa zaman jiran ki zan yi ba kawai sai dai ki saka anko". "Ni ban yi anko ba" . "me ya sa"?. "Saboda ba'a kawo min ba lokacin da Haulat ta siyo atamfar ankon ta shigo ina ji ta zo ta nunawa Bilki ta fita ba tai min magana ba shiyasa nima ban yi ba ni bana abin da ba'a sako da ni ba kuma Atikah ma haka ba wanda ya tambaye ni idan zan yi" kai ya d'aga ya na cewa "ok na gane yanzu dai d'auko mayafin ki mu tafi". "Gaskiya Yaya Sameer sai dai na saka hijab" zaro ido ya yi yana kallon ta da mamaki yace "hijab kuma Zainab ba fa islamiyya za ki je ba gurin dinner za mu je haba ke kuwa yau d'ayan" d'an dafe goshi ta yi kamar za tai magana sai kuma ta fasa ta koma d'aki bisa dolen ta ta d'auko mayafi da handbag d'in na ta kamar yadda ya ce kai ya jinjina ya na murmushi ya ce "yauwa 'yar 'kanwa ta ko ke fa mu je" ita dai Zainab ba dan ran ta ya so ba ta bi bayan sa suka fita ta d'auka mashin d'in sa za ta gani sai kuma ta ga mota a wajen da alamar tambaya ta kalle shi gira ya d'auke yana cewa. "Aboki na ne tare mu ka zo zan d'auko mashin ya ce na barshi mu je a motar sa sunan sa Äl'ämëëñ" kai ta d'aga ba ta yi magana ta ya bud'e gaba ya shiga ita kuma ta shiga baya tana shiga ta zaro Nikaf d'in ta ta d'aura dan ba za ta iya shiga wannan uban taro kowa ya na kallon fuskar ta ba balle wai yau ita ce ta fita da mayafi humm ji ta ke kamar ba ta saka komai ba. Ko kad'an Sameer bai kula ba saida suka je gurin ta fito ya ga fuskar ka rufe da Nikaf baki ya bud'e ya na cewa "kai ke dama kin taho da Nikaf to me akai kenan ai da kin sako hijab d'in ki ma kawai ya fi" ya fad'a suna shiga ita dai ko tari ba ta yi ba da suka shiga ma a can gefe ya nuna mata kujera ta zauna da lallami da'kyar ya samu ta cire Nikaf d'in amma a tsarge ta ke gani ta ke kamar kowa ita ya ke kallo su na zaune suna zance abokin sa da ya raka shi yanzu shine ya zo gurin yana zama a d'ayar kujerar ya kalli Zainab wacce ta yi 'kasa da fuska ganin irin kallon da ya ke mata Sameer ya kalla ya na cewa. "Ya kai Sameer wannan Ladyn fa 'kanwar ka ce"? Kai Sameer ya jinjina ya na kallon yadda ta ke 'kara yin 'kasa da fuskar ta ba ta so Al'ameen ya kalle ta (Bari nayi tsokana Al'ameen A. Prince🤴 nake nufi😃). Sameer ya ce "eh 'kanwa ta ce" gyara zama Al'ameen ya yi yana cewa "amma gidan ku d'aya ko kuma biki ta zo"?. "Uhm gidan mu d'aya". "Ok abin da na yi tunani kenan dan na ga kuna kama da ita cousin sister d'in ka ce"?. "A'a wannan ta fi 'karfin cousin sister uban mu d'aya kawai bari na 'kare maka karshen zance" zaro ido Al'ameen cike da farin ciki ganin shikenan fa'kat 'karshen zance yace "wow alhamdulillah ashe yau na yi tsintsuwa irin wannan kyau da hankali haka fatan zaka ba ni ita Sameer"? Kad'a kai Sameer ya yi yana kallon Zainab wacce tun lokacin da Al'ameen ya zauna ta sunkuyar da kai ta'ki d'agowa ya ce. "Eh to gaskiya ba ni da tabbaci akan haka" da alamun tambaya Al'ameen ya ce "me ya sa kace ba ka da tabbaci"? Kai tsaye Sameer ya ce "saboda tana da wanda za ta aura" yana rufe baki Zainab ta d'ago da sauri ta na kallon shi ganin yana kallon ta yasa ta yi wani irin da fuskar ka kamar za ta yi kuka murmushi yayi kamar bai ga abindm da ta yi ba ya ci gaba. "Da gaske na ke maka Al'ameen wallahi akwai wanda ya ke son ta kuma auren ta zai yi" huci mai zafi Al'ameen ya sha'ki iska ya fitar ya na 'kure Zainab da kallo ya ce "innalillahi wayyo Allah na gaskiya na ji ba'kin ciki ban ji dad'i ba ina ma ace na riga wancan yanzu idan na ro'ke shi zai iya bar min ita"? Kai Sameer ya girgiza ya na cewa. "A'a gaskiya ba zai iya bar maka ba". "Ko na ce zan bashi duk abin da ya ke so yana da sana'a ne ko ya na da fili ka fad'a masa duk abin da ya ke so ni zan ba shi ko jari ya ke nema in dai zai bar min ita ka fad'a masa ka bashi number ta ya kira ni sai mu had'u"? Murmushi Sameer ya yi ya na girgiza kai yace. "Shi ma ba baya bane yana da komai Al'ameen ba abin da ya nema ya rasa duk abin da ka lissafo ya na da su shi ma sai dai ya baiwa wani mu ma a 'karkashin inuwar sa mu ke". "Da gaske Sameer"?. "K'warai na fad'a maka gaskiya ne saboda kai aboki na ne babu rufewa tsakanin mu". "Gaskiya ne na gode Sameer amma ba ta da 'kanwa ka ba ni"?. "Ba ta da wata 'kanwa ita kad'ai ce sai Bilki ita kuwa ba ta da hankali ba zan so ka auri yarinya irin ta ba" murmushi Al'ameen ya yi yana kallon Sameer ya ce. "Humm ko dai hana ni ka ke son yi ba shi ya sa kace haka"? Dariya Sameer ya you yana cewa "kai a'a ba haka ba ne ka yarda da ni da gaske na ke fa". "Na yarda kai Sameer shi ke nan na gode amma kai sai yaushe za mu zo na ka bikin ka ga anan saina za6i matar auren da kai na". "Aure na akwai dogon lokaci domin ko kad'an ba ni da budurwa balle na yi batun auren ka gan ni iya fili na siya ko ginin ban fara ba". "Sai yaushe za ka yi to"?. "Ba rana sai na shirya". "Tom Allah ya kai mu" hankalin sa ya mayar kan Zainab wacce ta ke sauraron duk wata hira da su ke ya ce "big girl sai an jima ina ro'kon Ubangiji ya bani matar aure mai hankali da cikakkiyar nutsuwa irin ki" ya fad'a yana mi'kewa da murmushi akan fuskar sa ya kalli Sameer ya na y "na wuce sai mun sake had'uwa". "Ok Al'ameen na gode" hannu ya mi'ka masa su ka sake gaisawa sannan ya wuce kallon Zainab ya Sameer ya yi bayan wucewar Al'ameen ya ce "ba dan an riga shi ba wannan abokin na wa mutumin kirki ne da shi zan aura miki" kai Zainab ta jinjina tana cewa "waye ya riga shi? Ni fa bani da kowa" ta fad'a ta na had'e rai dariya yayi yana mi'kewa ya ce. "Lokaci ya yi mu je mu tafi gida kar magriba ta yi mu na nan maganar ba ki da kowa kuma bai taso ba domin ki na da kowa ta so mu je" tashi ta yi su na fita daga gurin ya je ya d'auko mashin d'in sa ta hau su ka tafi a hanya Sameer ya ke cewa. "Ki kace baki da kowa Zainab ina ki ka jingine wancan abokin na wa"? D'an yatsina fuska ta yi tana cewa "Yaya Sameer ni kam ban mayar da maganar Aliyu ya na so na komai ba" da mamaki ya ce. "Kai lallai ma saboda me"?. "Saboda ba na jin a raina cewa shi miji na ne". "Au wai akan haka ne dama? Za ki ji daga ranar da aka d'aura miki auren da shi" ya na rufe baki ta ta'be baki ta na cewa "hummm hum'um". "Ya na ji kina jan numfashi me ya faru fad'i man"?. "Me zan fad'a"?. Na ji kin ce humm na san akwai magana a bakin ki shi ya sa na ce fad'i". "Ni ba wani abu zan fad'a ba" daga haka ta sauya zauncen da cewa "Yaya Sameer ka san me wannan mashin d'in na ka idan ka hau yana maka kyau". "Da gaske ai kuwa shi ya sa nake son abu na yanzu addu'a na ke ma Allah ya hore min na yi gini na sai mota ko"?. "Ba aure za ka fara yi ba"?. "Eh zan yi amma ba yanzu ba sai na gama komai na nutsu saboda kar na rame kin san yadda ango ya ke komawa kuwa idan aka kusa aure wani sai kin tausaya masa musamman talakawa irin mu haka za ki gam mu kamar skeleton" ya rufe baki Zainab ta fara dariya Zainab tana cewa. "Kai Yaya Sameer me ne abun ramawa a nan"?. "Akwai ramewa man ka yi wancan ka yi wannan duk lokaci guda ki tuna abubuwan da suke jira na gini lefe sadaki kin ga kuwa ai ni nake da aiki" kai ta jinjina ta na cewa "uhm haka ne gaskiya da aiki Allah ya bud'a maka 'kofofin samu ka yi abubuwan da ba ka yi ba". "Amin" ya ce yana parking a 'kofar gate d'in gidan Zainab ta sauka shi kuma bai sauka ba ta bud'e masa gate d'in ya shigar da mashin d'in cikin gidan saida ya kai shi har 'kofar d'akin sa sannan ya yi alwala ya fita ita ma tana aje handbag d'inta fitowa ta yi ganin lokaci ya na neman fita an jima da yin sallar magriba d'in da sauri ta yi alwala ta je ta yi sallar tana zaune akan sallayar akai kiran sallar isha ta tashi ta yi tayi shafa'i da wutiri sannan ta yi addu'a ta tashi ta cire hijab kenan ta ga Aunty Murjah ta bud'o labule ta shigo ta na sauke numfashi kallon ta Zainab ta yi tana cewa.............. ZUCIYAR ALIYU CE WRITTEN Yusrah Musa. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 42 "Y'an dinner sai yanzu kenan"? Sabon numfashi Aunty Murjah ta sake saukewa tana cewa "uhm ke dai bari ai saida aka tashi sannan mu ka taho da har zan kira Sweet nace yaje mu tafi ta can kuma na tuna da kaya na anan bayan haka ban yi muku sallama ba" juyowa Zainab ta yi tana kallon ta da murmushi ta ce. "Ai da kin tafi ba komai za mu fahimce ki" zama ta yi tana cewa "ai ina son dawowa gidan ne ba dan haka ba sai ranar da mu ka had'u". "Sallah ya kamata ki fara yi na ga kin zauna"? Zainab ta fad'a tana kallon yadda Aunty Murjan ta ke neman kwanciya ta ci gaba "daga gurin dinner ki ke ba wa'azi ba balle ki ce can ma lada ki ka samo dan Allah ki tashi" tashi zaune Aunty Murjah ta yi ta na mi'kewa ta cire rigar da ya ke jikin ta ta na ajewa ta ce. "Ke ni fa hutu na ke ba don haka ba ai kema kin san ba zan zauna ban yi sallah ba ko"? Kai ta d'aga tana cewa "haka ne bari na tambayo Umma me ta dafa" dakatar da ita Aunty Murjah ta yi "kin san abin da ta dafa ke ma ai sai dai ki je kalan magana ni kam ba zan ci tuwo ba zo kiyi mana wainar fulawa kawai". "Ai kuma ba fulawa fa a gidan nan" kallon ta Aunty Murjah ta yi ta na cewa "kin yi sallar isha d'in"?. "Eh na yi tun kafin shigowar ki". "Ok bari na tashi mu je mu had'o kayan yi muzo muyi kawai tun da nasan ba za'a rasa gawayi ba" kai Zainab ta d'aga ta na cewa "eh buhu guda Abban mu yake ajewa sai ya 'kare ya kawo wani". "Ok bari na yo wanka idan na fito sai mu je dan yanzu wani irin zafi na ke ji ta ko'ina a jiki na gashi babu nefa balle mu kunna fanka" ta fad'a tana d'aukar zanin wankan Zainab ta fita. Kusan awa guda ba ta dawo ba har sai da Zainab ta gaji da jira ta na shirin tashi ta fita taga inda ta tsaya sai kuma ga ta ta dawo". "Kai Aunty Murjah wannan wankan na ki kamar ki na canza fata"? Goge jiki Aunty Murjah ke yi da d'an farin towel ta na cewa "ai ni ko a gida haka na ke wanka na ban iya kware-kware ba". "Lallai Yaya Auwal ya na ganin duniya" dariya Aunty Murjah tai tana juyowa ta kalli Zainab tana cewa "kamar kin sani dan kwanan baya ma haka ya ce wai idan mutum gudawa ya ke na shiga band'aki saidai mutum yayi a jiki ban fita ba". "Hum ai gaskiya ya fad'a irin wannan dad'ewa haka kamar me wankan mutum nawa"? Hijab Aunty Murjah ta saka ta na cewa "mu bar zancen nan mu je a had'o kayan wainar nan dan rabo na da abinci tun rana shi ma ina sauri ban tsaya na ci me yawa yadda zan 'koshi ba". "Ba ki ci a gurin dinner d'in ba ne"? Zaro ido waje Aunty Murjah tai tana cewa "uwar me zan ci a gurin me suka kai wanda bana ci a gida na har zan yi sha'awar cin sa a gurin" murmushi Zainab ta yi suna fita daga gidan shagon 'kofar gidan a nan suka tsaya suka siyo fulawa da manja sannan su ka koma ba wacce ta shiga d'aki duk 'kofar kitchen su ka tafi suka zauna akan kujera Zainab ta d'auko mangal ta zuba gawayi ta had'a musu wuta Aunty Murjah kuma ta jajjaga musu taruhu ta yanka albasa ta saka maggi ta 'kwa6a musu su ka fara soyawa. "Zainab yaji fa ko babu"? Aunty Murjah ta tambaya ta na kallon ta kai ta d'aga tana cewa "eh babu amma bari na tambayo miki Umma ko za'a samu" ta fad'a tana shirin mi'kewa "a'a zauna ki soya mana bari ni na je" komawa Zainab ta yi ta zauna ita kuma ta mi'ke saidai ba yaji a gurin Umma gashi gaskiya ita ba za ta iya ci babu yaji ba ganin Asabe ta shigo zata shiga d'aki ya sa tace. "Umma Asabe dan Allah ko kina da sauran yaji ki bani zan ci waina"? Kai ta d'aga tana cewa "bari na duba" baki bud'e Zainab ta kallo kofar d'akin ta ga ta shiga wato bari ta duba ko dan ita ba'a gidan ta ke ba shi ya sa baza ta yi mata wula'kanci ba ta tabbata da ace ita ce ta ro'ka ko kallon ta baza ta yi ba Aunty Murjah ta na tsaye ta bud'o labule ta mi'ko mata gabadaya robar yajin tana cewa "je ki da shi idan kun gama kya dawo min da shi" kar6a Aunty Murjah ta yi tana cewa "yauwa Umma Asabe na gode" zaro ido Zainab ta yi tana jinjina kai amma ba tai magana ba gudun kar da tace wani abu Asaben ta fito ta hau bala'i ana zaune lafiya dawowa Aunty Murjah tai ta zauna tana cewa. "Kai haba malam sai yanzu nasan ina cin waina" murmushi Zainab ta yi tana d'auko wacce ta soya ta sake aje mata tana cewa "lallai Aunty Murjah kin taki sa'a". "Sa'ar me"?. "A'a ba sai na fad'a ba kawai gara na yi shiru domin yin shirun nawa ya fi alkhairi". "Ok yayi" kawai Aunty Murjah ta ce tana ci gaba da cin wainar ba kamar Zainab da ta ji ba tai mata ba har suka gama soyawa suka tashi Zainab ba ta ce komai ba Aunty Murjah ta mayarwa Asabe yajin ta ta had'a mata da wainar sannan ta shiga ta kai wa Umma ma sauran suka wuce da ita d'aki akan keke ta aje plate d'in ta na cewa "to masha Allah sai yanzu na ji na dawo daidai Allah yasa su kawo nefa wallahi da zafi ko dan na ci abu me d'umi yanzu ne" ta fad'a tana d'aukar wani mafici na roba ta fara fifita da shi ita kuma Zainab ta d'auki littafin ta ta fara assignment d'in da bata samu ta yi ba dama ta bari da la'asar za ta yi sai kuma Sameer ya zo suka tafi dinner har Aunty Arabiyyah ta shigo su ka sake sabon zama ita da Aunty Murjah su ka yi ta hira Zainab ta na gefe tana jin su sai dai idan an yi abun dariya ta d'an yi murmushi 'karshen wannan wainar Aunty Arabiyyah d'in ce ta cinye ta. ZUCIYAR ALIYU CE @YMA DUTSE PAGE 43 Washe gari da safe ba wanda ya tashi sai wajen sha d'aya da rabi a lokacin Sameer ya shigo da firiza ya aje ta a 'kofar d'akin Zainab da katon d'in lemuka guda biyu da ledojin pure water ya wuce na sa d'akin sai da ya yi abin da zai yi ya fito sannan ya fito yana dawowa 'kofar d'akin Zainab ya dafe fridge d'in yana cewa. "Zainab kin tashi ne"? Jin shiru yasa ya sake cewa "Zainab Zainab" kamar a mafarki haka Zainab ta ji muryar Sameer sama-sama ya na kiran sunan ta da sauri ta yaye bargon da suke barcin da shi wanda hakan ya yi silar tashin Aunty Murjah cikin magagin barci ta ce "Zainab lafiya irin wannan zabura haka kin tsora ta ni"? Kai ta d'aga tana mi'kewa ta ce "eh lafiya kamar muryar Yaya Sameer na ke ji a waje ya na kira n................... "Zainab" ta sake jin ya kira ta ba ta 'karasa fad'awa Aunty Murjah maganar ba ta ce "na'am Yaya Sameer" ta fad'a tana fita a tsaye ta same shi har lokacin hannun sa yana dafe da firizar. "Ina kwana Yaya Sameer"? Kai ya d'aga ya na cewa "lafiya klou ina Murjah"?. "Ta na d'aki". "Ok sorry ki na barci na tashe ko? Ga alama nan na ga idon ki ya yi ja ki taso Murjanatun ta taya ki ku shigar da wannan fridge d'in d'akin ni zan fita" jin abin da ya ce yasa da Aunty Murjah fitowa da gudu turus ta yi ta tsaya daga ita har Zainab d'in su na bin firizar da kallo cike da tsananin mamaki cak Zainab ta yi ta kasa motsin kirki tsoro da tashin hankali ya rufe ta kai Aunty Murjah ta jinjina ta na kallon Sameer ta ce. "Wannan fridge d'in kuma daga ina Sameer"? Murmushi ya yi ya na kallon Zainab shi kuma ya ce "ita wacce na kawowa ta san daga in da ta ke wani ne ya bayar a ba ta saboda yanzu lokacin zafi ne ta ri'ka shan ruwan sanyi haka ya ce sa'ko ne daga gare shi" da sabon mamaki Aunty Murjah ta ce. "Wani kuma"?. "Eh aboki na ne ki taya ta ku shiga da ita d'akin" ya na fad'in haka bai sake kallon yanayin da Zainab d'in ta ke ciki ba ya fita juyawa Aunty Murjah ta yi da tsantsan mamaki ta na kallon Zainab wacce ta 'kame kamar wacce ta suma numfashi ta sauke ta na cewa "ke Zainab waye abokin sa har ya siya miki fridge saboda ki ri'ka shan ruwan sanyi son ki ya ke ko me"? Shiru Zainab ta yi tana kallon fridge d'in jikin ta sai rawa yake ko maganar da Aunty Murjah take mata bata ji tsabar rud'ewa ganin ba ta cikin hayyacin ta yasa ta dafa tana cewa. "Zainab wai lafiya ba ki ji abin da na ce bane"? Kai Zainab ta girgiza hawaye yana neman fara zubo mata da sauri ta shige d'aki ta bar Aunty Murjah a tsaye a gurin shiru Aunty Murjah ta yi gabadaya kan ta ya kulle ta kasa fahimtar komai Umma dake d'aki tana jin su ita ma hankalin na ta a tashe yake musamman jin wai firiza aka kawo wa Zainab saboda kawai ta ri'ka shan ruwan sanyi wai waye wannan abokin Sameer d'in ita ma yanzu gaskiya tana son sani ko dan samun zaman lafiyar su kafin a fara zagin su a gidan nan ko a d'auka da gaske asiri ta ke tura Zainab D'an Yana mi'kewa ta yi ta na fitowa ta kalli Aunty Murjah wacce har lokacin ta ke tsaye a wajen ba ta bi bayan Zainab ba kallon firizar ta yi ta na cewa. "Murjanatu ina Zainab d'in"? Sauke ajiyar zuciya Aunty Murjah ta yi ta na cewa "ta na d'aki Umma wai lafiya na ga ta shiga damuwa dan Sameer ya kawo mata wannan fridge d'in"? Jiki a sanyaye Umma tace "Murjah dole Zainab ta damu dole ta shiga tashin hankali idan na fara lissafo miki abubuwan da Sameer yake kawo mata yana cewa abokin sa ne ya ke mata wai son ta yake amma yafi so sai ta gama makarantar da take yi yanzu idan ya dawo sai ya fito ya nemi auren ta kuma makarantar ma shi ne ya biya mata wannan dalilin ya sa ki kaga ta shiga damuwa". "Na fahimta to waye shi abokin Sameer d'in a ina ya ke wannana na ke son sani"? Kai Umma ta girgiza ta na cewa "wallahi ni ma har gobe ban san waye shi ba Sameer ne ya sani kuma ya'ki fad'a mana ya ce abokin na sa ba ya so a san shi da kan sa ya ke so ya zo ya bayyana ya gabatar ma ta da kan sa" sabuwar ajiyar zuciya Aunty Murjah ta sake saukewa ta na cewa "ko dai akan haka na ga yanzu ta shiga wani irin yanayi". "Ba dole ta shiga yanayi ba Murjah ni kai na kullum hankali na a tashe ya ke idan na ji Sameer ya kira sunan ta saboda nasan abu zai bata ke fa hatta kud'in da take hawa Napep ta je makarantar kullum dubu d'aya wancan abokin na sa ne yake baiwa Sameer d'in yana bata kwalin indomie chocolates biscuits haka zaki gan su kala-kala ya kawo mata wai kawai ta ri'ka ci ban da kayan sakawa fa" Kai sosai Aunty Murjah ta ke jinjinawa ta na kallon Umma tace "gaskiya dole ta shiga damuwa musamman da ba a san waye ba shi ne abun matsalar yanzu bari Sameer d'in ya shigo na tambaye shi" murmushi Umma ta yi ta na cewa. "Ko kin tambaye shi ba zai fad'a miki komai ba sai dai ya ce da lokaci ko me za ki yi ba zai fad'a mi ki ba". "Ok shikenan Allah ya kai mu lokacin Ubangiji ya sa shi ne miji na gari mafi alkhairi a rayuwar ta". "Amin shi ne kawai abun fatan yanzu ki shiga d'akin ki mata magana ta fito ku d'auke tun kafin a zo a gan ta magana ta fita" Umma ta fad'a tana juyawa ta koma d'aki Aunty Murjah kuma d'akin Zainab d'in ta shiga ta gan ta ta kwanta akan katifa ta na kuka zuwa ta yi ta d'ago ta tana goge mata hawayen tace............. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH DUTSE PAGE 44 "Zainab tun da kin san ga wanda ya ba ki meye abun da zai sa ki damu kan ki dan Allah ki daina kukan nan" kai ta girgiza muryar ta da alamar kukan ya kama ta sosai ta ce "Aunty Murjah na kasa fahimta na kasa gane komai kyautar yau daban ta gobe daban abubuwan masu tsada yanzu kuma komai ya wuce yadda na ke tunani firiza fa ya siyo min dan kawai ana zafi na ri'ka shan ruwan sanyi abun nan yana bani tsoro wallahi". "Na sani amma tun da ki ka ga Sameer ya mayar da hankali akan abun na tabbata yana da muhimmanci kuma in sha Allahu alkhairi ne dan haka abin da na ke so da ke ki yi hakuri yanzu ki tashi mu je mu shigo da ita ciki" Aunty Murjah ta na rufe baki da sauri Zainab ta girgiza kai ta na cewa. "A'a ni ba na so kawai bari Yaya Sameer d'in ya shigo na ce ya d'auka ya mayar masa ko ya saka a chemist d'in sa amma ni dai ba na so" da mamaki Aunty Murjah ta ce "ya kai chemist kuma? A'a ba wani chemist da zai kai ta wallahi tana nan a d'akin ki mazaunin ta ya ke dan haka ki kwantar da hankalin ki tashi mu shigo da ita ciki ki ri'ka zuba pure water d'in ki da abubuwa ki na sha haka kawai zaki mayar da hannun kyauta baya ba zai yuwu ba gara da ban tafi gida jiya ba na dawo nan ashe alkhairi ne ya dawo da ni za'a yi wannan abun a gaba na" ita dai Zainab ko motsi ba tai ba daga haka kuma ba ta sake magana ba duk abin da Aunty Murjah ta ke ta na jin ta. Shigar Umma da Aunty Murjah d'aki bayan sun gama magana da sauri Bilki ta fito daga d'akin su tana kallon firizar takaici da ba'kin ciki ya gama rufe ta yatsa ta ciza tana hararar kofar d'akin su Zainab da sauri ta fita daga 'kofar ta su ta tafi gurin Hajiya har da gudu kamar wani ne zai riga ta ta na shiga ta ce "Hajiya albishirin ki kin san Zainab ta na da saurayi me kud'i kuwa"? Kallon yadda ta ke haki Hajiya ta yi ta na cewa. "A ina ta yi saurayi me kud'in? Taya zan sani tunda ba shigowa guri na take ba bayan haka Hauwa tana jin haushi na na takura mata can ta yi aure yaushe za su fad'a min 'yan gadon ba'kin hali ne fa" tsaki Bilki ta ja kamar za tai ihun takaici ta ce "to wallahi yanzu ma maganar da na ke miki ba ki ga wata 'katuwar fridge da Yaya Sameer ya kawo mata ba da katon-katon na lemuka da ledojin pure water wai abokin sa ne ya ke son ta kuma shi ya siyo mata ta ri'ka zuba kayan sanyi tana sha yanzu lokacin zafi ne" gwalo ido waje Hajiya ta yi ta na cewa. "Aw kawai tsabar jin dad'i dan ta ri'ka shan kayan sanyi ya siyo mata 'katuwar firiza ki ka ce waye wani abokin Samar kuma a ina ya ke ko Aliyu ne"? Da alamar tambaya Bilki ta ce. "Wanne Aliyun"?. "D'an gidan Alhaji Ahmad d'in nan Minister nan nake fad'a mana ko shi ne tun da na ga shi ma abokin na sa ne"? Ta'be baki Bilki ta yi tana yatsina fuska ta ce "kaiiii a'a cafd'i me Aliyu zai yi da Zainab ya na d'an me kud'i baban sa Minister mu kuwa baban mu da ya ke sana'ar kayan miya da gawayi gaskiya ba shi bane saidai idan wani ne daban". "To yanzu ina firizar ta ke"? Cike da munafirci ta ce "ta na can a d'akin ta har sun jona ta sun siyo ruwa sun zuba da lemuka sun zuba su na ta dariya da shewa Umman su kuwa har da rawa ta na cewa ina Hajiya ta zo taga arzikin Zainab ya fara sauka d'an ba'kin ciki sai dai ya mutu tun da gashi ita ma na ta masoyin ya bayyana" gwalo ido Hajiya tai tana cewa. "Iye haka Hauwan ta ce a kai na"?. "K'warai haka ta ce kuma ba 'karya na ke ba su na can su na ta gulmar ki wai dama a gidan nan ba wanda ki ka takurawa irin 'yan d'akin su" cikin fad'a Hajiya ta ce "ka ji matsiyata in ji uban su na ke takura musu ko dan sun saba yi min sharrin 'yan gadon ma'karyata, yanzu ki ka ce har sun siyo ruwa sun zuba a firizar wanne za'ka'kurin ne gwanin zuba ruwan? Murmushi Bilki ta yi tana gyara zama ta ce. "Waye kuwa bayan Aunty Murjah ke ma Hajiya ai kin sani sai dai ita". "Au Murjan dama ta dawo gidan nan jiyan ba ta tafi ba shi ya sa ta ce dad'a kwana dan ta yi wa mutane rashin arziki tashi ki kira min ita dan uban ta" Hajiya ta fad'a ta na kallon Bilki wacce ta girgiza kai ta na cewa "kai Hajiya gaskiya idan na je za su ce nice na zo na fad'a miki". "To su fad'a man dan uban su tsoron su ki ke kome za su dake ki ne"?. "Ni ba tsoron su na ke ba amma za su iya fad'awa baban mu kuma yace kar na sake yiwa Zainab rashin kunya kuma kar na sake shiga safgarta" cikin fad'a Hajiya ta ce "kuma ina ruwa na tashi ki kira min Murjanatun na ce ko"? Tashi Bilki ta yi tana fita tare da tsayawa a 'kofar Hajiyan ta 'ki zuwa kiran Aunty Murjan ganin khaleel ya fito daga 'kofar su zai yi hanyar waje ta ce. "Kai khaleel zo na aike ka kaje 'kofar mu kace wai Hajiya ta na kiran Aunty Murjah" to yace yana juyawa ganin ya shiga yasa da gudu Bilki ta fice daga gidan dan kar ma su zarge ta. Su Aunty Murjah su na d'aki su ka ga khaleel ya shiga yana cewa "Auntyn Ikram wai Hajiya tana kiran ki" kallon juna su kai da mamaki Zainab wacce ke gefe daya tayi tagumi jin ance kira daga Hajiya yasa tace "kin gani ko Aunty Murjah na san ba zai wuce ace wani ne ya je ya fad'a mata an kawo min firiza ba gashi har ta turo a kira ki meye laifin ki a nan"? Mi'kewa Aunty Murjah ta yi ta na d'aukar mayafin ta ta ce "sai me waya damu? bari na je naji me za ta ce min zan ga uban da ya kai saran na ki cewa an kawo miki fridge tun da ba uban mai fad'ar ne ya siya ba" kai Zainab ta girgiza ta na cewa. "Dan Allah Aunty Murjah kar ki biye mata idan har ki ka tafi akan Umma za ta sauke fushin ta" huci Aunty Murjah ta fitar ta na cewa "wallahi Zainab sai na fad'i gaskiya sai dai ta tsabar 'kiyayya ta dafa Umma ta cinye bayan tafiya ta amma ba zan 'kyale ba wannan cin fuskar ya yi yawa ai dai iya 'yan d'akin mu ta ke wa bari na dawo" fita ta yi tana d'aukar takalman ta daidai Umma ta fito daga kitchen ta gan ta tsayar da ita ta yi da cewa. "Murjah ina zaki je"?. "Zan je gurin Hajiya ne Umma ina dawowa yanzu" tana fad'in haka dan kar Umman ta sake jefo mata wata tambayar ya sa da sauri ta fita daga 'kofar saboda ran ta a 6ace ya ke har matsuwa ta yi ta shiga gurin Hajiyan ta na zuwa kuwa ta same ta a 'kofar d'aki ta na hutawa zama ta yi ta na cewa.................... 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @DUTSE JIGAWA PAGE 45 "Hajiya ga ni" kallon ta Hajiya ta yi ganin yadda ta had'e fuska ya sa ta fara magana "wato Murjah kamar yadda ki kai wa mutane itama wannan yarinyar haka take nufi ko uban waye ya kawo mata firiza d'azu wai abokin Samar ne ko? Shi ma Samar d'in munafiki yanzu da zan kira shi ba zai fad'a min waye ba saboda da ya iya 'kulle-'kulle ke ki fad'a min waye ya kawo mata"? Kai Aunty Murjah ta girgiza cike da takaici ta ce. "Dama na san ba zai wuce akan haka ba matsala ta da ke Hajiya saurin d'aukar zuga yanzu wanne munafukin ne har ya zo ya fad'a miki an kawowa Zainab firiza saboda tsabar sharrin harda wani ta fara siyar da pure water da zobo da kunun aya daga kawo tan yanzu har ta fara wad'annan sana'o'in sai kace wata inji haba jama'a wacce irin masifa ce wannan"?. "Aw Murjanatu nan d'in zuwa ki kai ki zage ni kenan saboda na ta'bo 'yar uwar ki Hauwan ce ta aiko ki ko kuma rashin kunyar ta ki ce ta juyo kai na"?. "Ni fa Hajiya gaskiya na zo fad'a miki ba wai goyon bayan Zainab ko kuma na miki fitsara kamar yadda ki ke tunani bane gaskiya kuma dole na fad'e ta saboda ina gani ba za'a yiwa 'yar uwa ta 'kazafi ba". "Iyeeh maza ki ci gaba da fad'ar gaskiyar d'ora daga inda ki ka tsaya nace ci gaba da zagi na Murjanatu uban wa ki ka ji yace 'kazafi akai mata ko akan hakan ki ke shirin zagin na wa"?. "Hajiya kar ki sa mutanen gidan nan su d'auka da gaske zagin na ki nayi kawai raina ne ya 6aci akan wannan rainin wayon da ake mana ta ya baki san komai ba bayan yanzun nan Sameer ya shigo da firizar ko d'aki Zainab ba ta shigar da ita ba tana nan a waje inda Sameer d'in ya aje ta ko ta'ba ta ba ta yi ba amma har an samu wani d'an Allah bani mu huta gori d'in ya zo ya ta da fitina to duk wanda ya zo ya fad'i wannan maganar kar Allah ya bar shi ya kwana lafiya Allah ya tsine masa Ubangiji ya tarwatsar aniyar sa duk wanda ya ke son ganin ba'kin cikin Zainab in sha Allahu shi ne zai shiga cikin masifa da bala'i sai yaga 'karshen sa kowanne tsinannan ne ma" ta na fad'in haka ta mi'ke ran ta a 6ace sosai ta fice daga 'kofar Hajiyan ganin ta fita ya sa Hajiya mi'kewa ta na shirin bin bayan ta shigowar Bilki da sauri shi ya hana ta fitan kallon Bilki ta yi tana cewa. "Je ki kira min Samar duk inda ya ke ya zo yanzu ina neman sa"? "Tom Hajiya bari na kira miki shi" Bilki ta fad'a tana juyawa ta fita Hajiya kuma ta koma ta zauna kafin Sameer d'in ya zo dan tasan tun da har Aunty Murjah ta na gidan yanzu idan ta je 'kofar ma akwai me tarewa Umma shi ya sa ta ha'kura sai bayan ta tafi. Sameer kam da sa'kon Hajiya ya iske shi ma bai zo ba saboda shi kan sa yasan dalilin kiran ba zai wuce akan firizar d'azun ba ce dan haka ya bari sai da akai sallar magriba ya shigo 'kofar ta ya fara shiga domin ya ji me ya sa take neman sa samun ta ya yi tana sallar nafila ya jira ta yi raka'a shida ta yi sallama ko addu'a ba ta tsaya yi ba ta juyo tana kallon sa tace. "Sannu isashshe sai yanzu sa'kon na wa ya riske ka ko kuma saboda tsabar ba ka mayar da ni mutum ba ya sa da aka fad'a maka ba ka zo akan lokaci ba"? Kai Sameer ya jinjina ya na cewa "ki yi ha'kuri Hajiya ban samu na zo bane tun lokacin da ki ka aika saboda ina ta duba marasa lafiya ba damar na rufe chemist d'in na zo". "Yayi kyau dama tambayar ka zan yi Samar uban waye ya siyawa Zainab firiza"? Kallon Hajiya ya yi kamar zai fad'i wata maganar daban amma saboda baya son hayaniya ya sa kawai ya ce mata. "Aboki na ne" sabuwar tambaya ta sake jefo masa. "Waye abokin ka"? "Aboki na man abokai na da yawa idan na fad'a miki sunan sa ma ba san shi ba". "A ina ya ke"? Kafad'a Sameer ya d'aga ya na cewa. "Yana ko'ina". "Ban gane ya na ko'ina ba"?. "To Hajiya idan na fad'a miki in da ya ke amfanin me hakan zai yi miki"?. "So na ke na bashi umarni ya turo iyayen sa in dai da gaske ya ke ba mayaudari ba ne". "Da gaske ya ke man auren ta zai yi in sha Allahu Hajiya ki kwantar da hankalin ki ya kusa dawowa gari Zainab ta kusa ta bar gidan nan ta koma gidan mijin ta" yana rufe baki Hajiya ta d'aga hannu sama ta na sake ri'ke carbin ta da kyau ta ce. "Allah Amin Allah ya sa naga wannan ranar" sauke hannu ta yi ta na kallon Sameer ta ce "idan ma 'karya ka ke Allah ya biya bakin ka" mi'kewa ya yi ya na cewa "balle ma ba 'karyar na ke ba gaskiya ce na fad'a miki akwai mai son ta da aure kuma shi ne ya aiko ni da sa'kon fridge d'in" kai Hajiya ta d'aga ta na cewa. "Shikenan ba damuwa Allah ya bayyana shi sai ya zo d'in mu na nan mu na jiran sa". "Yauwa ko ke fa Hajiya Amin har kin sa na ji dad'i amma kullum ace sai an samu sa6ani haba wallahi abun nan ya na mugun 'kona min rai gida d'aya jini d'aya 'yan uwan juna babu bare amma had'in kai ya yi 'karanci duk laifin ya na gurin............... Katse shi Hajiya ta yi "ka ga Samar ka yi tafiyar ka na gane komai ya wuce na fahimta". "Ok sai da safe" ya fad'a ya na fita 'kofar su ya nufa daidai Aunty Murjah ta fito daga d'akin Zainab ri'ke da jakar kayan ta Auwal da ya zo d'aukar ta shi kuma ya shiga d'akin Umma su na gaisawa kallon ta Sameer ya yi yana cewa............................ ZUCIYAR ALIYU CE J.W.A @YUSRAH YMA PAGE 46 "Tafiya za ki yi ne dama motar da na gani a waje ta Daddyn Ikram ce"? Kai Aunty Murjah ta d'aga ta na cewa "eh dama mun yi da shi yau zai zo ya d'auke ni shi ya sa jiyan ma na dawo" kai ya d'aga yana cewa "ok ki gaida gida" ya fad'a ya na wucewa fitowa Auwal ya yi suka gaisa sannan suka fita su uku Zainab za ta yi musu rakiya zuwa 'kofar gida d'akin Zainab Sameer ya shiga ya na bud'e fridge d'in ya ga duk an saka lemukan da pure water murmushi ya yi dan yasan wannan shirin ba Zainab bace sai dai Aunty Murjah d'aukar juice guda d'aya ya yi ya fita daga d'akin ya shiga na sa. Su Aunty Murjah kam fitar su Auwal ya ce su shiga gurin Hajiya su gaisa da ita iya su biyun suka shiga Aunty Murjah za ta yi masa rakiya amma Zainab kam ko da wasa ba tai marmarin shiga ba, a d'aki su ka samu Hajiya ta na kwance da radio a kusa da ita ta na saurara jin sallama yasa ta rage volume tana cewa. "Waye a waje? Ku 'karaso man" Aunty Murjah ce ta fara shigowa sannan shi ma ya shigo ya dur'kusa ya gaida Hajiya gaggawa Aunty Murjah ta ke ya tashi su tafi saboda kar Hajiya ta 6aro wata maganar amma Hajiya sai jan sa ta ke da hira da labarai ganin dare ya na sake yi yasa Aunty Murjah ce wa. "Sweet ya kamata mu tafi goma ta kusa tara da mintuna" kai ya jinjina yana mi'kewa tare da saka hannu a aljihu ya ciro dubu uku ya ajewa Hajiya ya na aje mata tun kafin ya ce wani abu ta d'ebe ta na cewa. "Allah ya yi maka albarka irin ku ake so wanda su ne na Allah bakwa gajiya da kyauta Allah ya 'kara bud'i ka ji? Ubangiji ya tsare ka daga sharrin ma'kiya". "Amin Hajiya na gode sai wata ran" ya fad'a ya na fitowa ya saka takalman sa ita ma Hajiyan mi'kewa ta yi har 'kofar fitowa daga lungun ta ta rako shi ta na masa addu'a kamar ba za ta daina ba sannan ta juya ta koma ciki waje suka fita Zainab dake ri'ke da jakar ta ta mi'ka mata tana murmushi ta ce. "To Allah ya tsare Momyn Ikki sai ranar da na sake zuwa miki Yaya Auwal ku gaida gida" kai ya d'aga yana cewa "mun gode Hajiya Zainab sai kin zo mana ziyara domin mu fa har yanzu ba mu ha'kura ba muna ciki" kamar Zainab ba ta san akan me yake magana ba ta ce. "Ku na cikin ina"? Murmushi ya yi ya na kallon yadda ta juyar da kai ya ce "ke ma kin sani ai da tare da Mukhtar d'in zamu taho dan kawai ya zo ya gan ki sai kuma uzuri ya tare shi" kai ta jinjina tana cewa "gara da bai samu damar ya zo ba dan da ya biyo ka ma ba gani na zai yi ba" da mamaki ya kalle ta ya na cewa. "Saboda me bayan ga ki a tsaye ina kallon ki amma ki ce shi ba zai gan ki da ace ya zo d'in"?. "Saboda ba zan fito ba ma balle mu had'u da shi har ya yi tunanin ko da gaske ina jin wani abu game da shi" d'an zaro ido Auwal ya yi ya duban ta ya ce "haba dan Allah Zainab aboki na ne fa yana matu'kar son ki wallahi dan kawai kin 'ki ba shi fuska ne amma da yanzu ya aure ma na ke kin tafi gidan sa kin ga wannan zuwan da na yi shima da sai dai kawai ya zo ya d'auke ki ku tafi gidan ku ko"? Kusan dariya ce ta so ya 'kwacewa Zainab da sauri ta danne tana cewa. "Hummm tabd'ijan" kawai shi ne abin da tace ta na kallon Aunty Murjah wacce ke tsaye jikin motar ta na dariya da har ta za yi magana sai ta fasa kawai ta ce "ku gaida gida a gaisar min da Ikram" kai Aunty Murjah ta d'aga ta na cewa. "Zata ji in sha Allahu sai da safe" ta fad'a ta na shiga mota Auwal da ke tsaye ya na d'an kad'a key d'in motar ta sa sake kallon Zainab ya yi yana cewa "to 'kanwa ta kuma wife to be d'in babban aboki na mun tafi". "Uhum mu kwana lafiya ku gaida gida" ta na fad'in haka ta juya ta koma shiga motar ya yi Aunty Murjah da ke kallon 'kofar gate d'in gidan na su tace "kai gaskiya Zainab sai a hankali ita fa gaskiyar abin da ya ke ran ta take fad'a" kai Auwal ya jinjina ya na cewa "ni ma na ga alama gaskiya Mukhtar ba zai ta'ba samun kar6uwa ba duba da lokacin da aka d'iba kawai sai dai ya yi ha'kuri" numfashi Aunty Murjah ta sauke tana cewa "uhm Allah ya kyauta mu je" tada mota yayi yana cewa "ta gidan Mama za mu bi mu tafi da Ikram saboda ta d'an jima a can ya kamata ta dawo gida haka". "Ka bari gobe da safe idan na yi abinci sai mu je tare na gaida Maman idan na wuni da yamma idan ka dawo daga wajen aiki sai ka je ka d'auko mu ko"?. "Ok tom shikenan hakan ma ya yi" ta fad'a ya na jan motar su ka bar gurin su kai gidan su..................... AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE. ♥ZUCIYAR ALIYU CE♥ @YMA DUTSE PAGE 47 Sameer kam tun da ya shiga d'akin sa bai fito ba har Zainab ta dawo ta kwanta ya dad'e daga baya ya fito d'akin Asabe ya shiga ta na zaune ta gan shi d'an hararar sa ta yi musamman tuna d'azu da ta dawo daga anguwa Bilki ta fad'a mata ya shigowa da Zainab firiza kamar za ta yi masa magana akan hakan sai kuma ta share ta na d'auke kan ta daga saitin sa Sameer ya na tsaye bai zauna ba ganin ta na kallon juice d'in da yake hannun sa yasa ya ce "ga shi Umma idan na fita daga nan na shiga na d'auki wani" wani d'an iskan kallo ta yi masa ta na ta'be baki tare da nuna kan ta tace "wa ni? Allah ya rufa asiri na sha abin da ya fito daga hannun wad'ancan mutanen har abada" jin abin da ta ce yasa Sameer kallon ta ya na cewa. "Kai dan Allah Umma wai me yasa ki ke haka ne"? Harara ta sakar ma sa cike da takaicin ya za6i 'yar kishiya akan wacce su ke d'aki d'aya ta ce "au kai ka ke cemin? Iya kai ban da 'kafofi kaga Sameer ka fita safga ta ka kiyaye ni na fad'a maka hummm". "Ki yi ha'kuri dan Allah Umma ban fad'i hakan dan na 6ata miki rai ba" "Shikenan zan huce ne kawai idan ka fita ka siyo min nama ko kifi" jin abin da ta ce yasa ya saki murmushi ya na laluba jikin sa ya ce "ba damuwa Umma zan siyo miki amma yanzu ba kud'i a jiki na wallahi". "Kan uba lallai ma Sameer ka mugun raina min hankali amma da wancan yarinyar ce tace haka jikin ka yana 6ari za ka fita ka siyo ka kawo mata saboda gudun 6acin ran ta ko"?. "A'a Umma ba haka ba ne ita ma duk abin da za ki ga na kawo mata ba kud'i na bane sa'ko ne aka bani na bata ina na ga kud'in da zan ri'ka mata irin wad'annan abubuwan in dai zan samu kud'i kamar haka na fara gini man" wani karkataccen kallo ya sa, Asabe ta yi masa ta na cewa. "Ma'karyacin banza uban waye zai baka ka bata da gaskiya ne ka fad'i waye yake aiko ka mana amma saboda ka san 'karya ka ke ina gashi har yau ban ga idon wanda ya ke aiko ka d'in ba" murmushi ya yi yana kallon ta ya ce "wallahi da gaske na ke Umma amma tun da ba ki yarda ba bari na fita ko ATM d'ina sai na je da shi na siyo miki". "Kai ka sani wannan matsalar ka ce" juyawa ya yi yana fita daga d'akin ta na jin sanda ya ke kiran sunan Zainab tsaki ta ja tana cewa "na rasa wacce irin maita ce wannan dan bala'i ace in dai ka shigo sau goma saika kira sunan ta kamar tare aka haife ku? Aikin banza mtwwww ta sake jan tsaki ta na kwanciya jiran dawowar sa take ta tsawatar masa akan wannan shishshigin da yake ya fara isar ta................................ Yau ba yawa typing d'in ZUCIYAR ALIYU CE Yusrah Musa Abubakar ce. #Team Zainab #Team Aliyu ♥Y♥S♥R♥H♥ @YMA JIGAWA PAGE 48 POV SHAREEF Yana zaune a parlor tare da Mami su na magana ta kalle shi tana cewa "Shareef ni kuwa kamar kwanan baya ka ce min ka samu wacce kake son aura daga haka kuma ban ji ka sake cewa komai ba ko dama da wasa ka ke yi"? Kai ya girgiza ya na cewa. "A'a ban fasa ba kuma ba da wasa na ke ba". "To amma daga ihu d'aya sai murya ta dashe gaskiya ni fa na matsu na gan ni da suruka ta"?. "Zaki gan ta Mami har sai kin gaji da ganin ta idan na aure ta". "Anya zan gaji da ganin 'yata kuwa? Yadda ban ta'ba jin na gaji da ganin ka ba ita ma haka to amma a ina ta ke ko yarinyar nan da ta ta'ba zuwa gidan nan ta gaida ni"? Da sauri ya girgiza kai yana cewa "nooo Mami ba ita bace haba dai ni Shareef na auri wannan yarinyar Allah ya rufa asiri" da mamaki Mami ta ce. "Me ya sa"?. "Haba Mami akwai dalili man ni ba irin ta na ke son aura ba saboda ba zan iya da matsalolin ta ba". "A haka kuma lokacin da ta zo min yarinya me hankali da nutsuwa kamar ba ta da wata matsala"? Kai ya jinjina ya na cewa "fuska biyu gare ta Mami dan baki zauna da ita na d'an wani lokaci ba shi ya sa ki ke ganin kamar ba ta da wani matsala d'in amma a zahiri kuwa wannan yarinyar da ki ke gani humm ba ta da kyau". "To Allah ya kyauta wancan surukar ta wa a ina ta ke"?. "Tana anguwar su". "Ina ne anguwar su kuma"? Sake cewa ya yi "anguwar su can man na ke fad'a Mami anguwar su fa" cikin rashin fahimta Mami ta ce "ikon Allah Shareef kenan ai kowa ma ya na da anguwa sunan ta zaka fad'a min". "Neehal". "Nihal sunan ta"? Kai ya jinjina na tare da ya yi magana ba Mami ta ci gaba "a wacce anguwa ta ke"?. "Zan fad'a Mami amma ba yanzu ba". "Sai yaushe"?. "Idan na dawo daga hospital zan fad'a miki" ya fad'a yana mi'kewa tsaye da kallo ta bishi tana cewa "ka yi alkawari"?. "In sha Allahu Mami zan fad'a miki ina dawowa tun kafin na shiga part d'ina". "Shikenan ba matsala Allah ya dawo da kai lafiya ina sauraro". "Ok Mami ki wuni lafiya" ya fad'a ya na fita murmushi Mami ta yi bayan fitar sa ta yi shiru kawai kamar me tunani ta dad'e a haka daga baya ta sauke numfashi jin 'karar bud'e gate da rufewa ya sa ta fahimci an shigo gidan to amma waye zai zo a wannan lokacin Shareef dai yanzu ya fita balle ta ce shi ne to ko Alhaji ne ya dawo shi ma kuma me zai dawo yi? Ta na shirin tashi ta le'ka ta ga sun shigo da sallama Daddyn Shareef a gaba sai wasu maza mutum biyu a bayan sa d'aya tsoho d'ayan kuma ya kai misalin magidanci kallo d'aya Mami ta yi musu ta ji yawu bakin ta ya 'kafe numfashin ta yana neman tsayawa har ba ta san lokacin da ta zabura ba zama Daddy ya yi shi ma jikin sa sanyaye ya ce. "Kin ga wad'anda ba ki ta'ba tunanin zuwan su a irin wannan lokacin ba ko? Ni ma ina zaune a office akai min aiken ana sallama da ni ina fitowa na gan su ashe yau kwanan su biyar ma da shigowa Nigeria d'in" numfashi Mami ta sauke ta na cewa "sannun ku da zuwa Baba Sadoh" ta kalli d'ayan ta na cewa "Amru ku ne na ke gani ko mafarki na ke yi"? D'an murmushi Baba Sadoh ya yi ya na d'aga kai yace. "Eh mu ne dama mun d'an shigo ne gobe maza mu tafi mu koma Niger d'in shi ne nace wa Amru mu 'karaso mu gaisa da ku ba dan haka ba ma yau zamu tafi" hawaye ne ya fara cika idon Mami ta na jin yadda ran ta ke sosuwa da tuna ba ya tace. "Yauwa gara da ku ka zo dama tun da aka haifi Shareef bai ta'ba sanin a ina dangin mahaifiyar sa su ke ba bai ta'ba kawowa a ran sa ba ni ce na haife shi ba, lokaci ya yi da ya kama ta ace ya san komai" jin abinda ta ce yasa Baba Sadoh saurim girgiza kai yana cewa "a'a a'a ba wannan ya kawo mu ba ki ci gaba da ri'ke Shareef matsayin ke ce ki ka haife shi kar ki fad'a masa wannan maganar mu ba mu zo dan tarwatsa muku farin cikin ku ba gaisawa kad'ai mu ka zo yi domin koma mene ina tuna kalar ri'kon mutunci da amana da ku kai wa 'ya ta shi ya sa bana so na zama silar shigarku damuwa domin na zo na same ki cikin farin ciki ne". "Ba tarwatsa farin ciki ba ne lokaci ya yi daya kamata Shareef ya gana da ku dan Allah ku bari mu fad'a masa gaskiyar lamari idan bai sani ba shi ke nan fa a haka zamu ci gaba da tafiya ku kuma sai dai ku ha'kura da shi". "Dama mu mun dad'e da ha'kura da shi Shareef d'an ki ne na halak kar ki damu bayan me d'an da kanta ta furta kalmar ta yafe miki shi yaushe zamu karya wannan alkawarin tun da dai mun zo kuma mun gan shi hankalin mu ya kwanta ba sai ki fad'a masa ba dan Allah ki ci gaba da zama matsayin mahaifiyar sa kar ku bari ya gane ba kece kika haife shi ba har abada" kuka sosai Mami ke yi gabadaya hankalin ta nema ya ke ya bar jikin ta gaskiya ta na jin takaici ba'kin ciki da d'aci a duk lokacin da ta tuna cewa ba ita ce ta haifi Shareef ba amma a wannan karon ba za ta bari son zuciya ya hana ta fad'a masa gaskiya ba............... "Ki daina kuka haka mu za mu tafi sai Allah ya sake 'kaddara saduwar mu idan da rai a gaba" Baba Sadoh ya fad'a ya na mi'kewa ya kalli Daddy Amru kam ya na gefe yana sauraron su bai ce komai ba amma shi ma yana so ya ga d'an gidan 'kanwar ta sa ko sau d'aya ne a rayuwa........,... ZUCIYAR ALIYU CE NAJA'AT MUSA ABUBAKAR ✨ @YUSRAHMS PAGE 49 Bayan fitar su ma Mami ba ta iya yin shiru ta daina kukan ba musamman ta san indai Shareef shi ma ya fahimci ba ita ce ta haife shi ba sai shiga mummunan tashin hankali amma dai duk da haka ta na so a cire batun komai a fad'a masa ko da mene zai faru ita dai zata fad'a masa gaskiya kafin ya samu labari a gurin wa su hakan zai yafi 6ata masa rai akan idan su ne suka fad'a masa. Shareef kam bai samu damar dawowa gida ba sai jikin magriba a lokacin Mami ta na parlor jiran dawowar ta sa take yi sai kuma gashi ya yi sallama amsa masa ta yi tana 'karasowa bisa al'ada da d'abi'ar sa ya zo ya mata kiss ya na cewa "barka da yini Mami na fatan na same ki lafiya"? Ya fad'a yana zama a kusa da ita ya ri'ke hannun ta hawaye ne suke neman zubo mata ta yi saurin dannewa da'kyar ta ce. "Lafiya kalau Shareef ya wajen aikin na ku"?. "Lafiya Mami ai yau na sha wahala sosai a gajiye na dawo ga yunwa ma na ke ji bari naje na yi wanka da alwala idan na dawo daga masallaci sai naci abinci me aka dafa Mami"? Ya fad'a ya na mi'kewa 'kin d'agowa ta yi ta kalle shi saboda hawaye zasu iya fitowa daga idon ta tace. "Abin da ka ke so ne Rabi ta dafa maka". "Wow thank you Mami na gode da kulawa bari na je nayi wankan ina zuwa" wucewa ya yi yana hawa stairs d'agowa ta yi tana binsa da kallo kuka na neman 'kwace mata shi ya sa ta mi'ke ita ma ta tafi part d'in ta kafin ya fito ya same ta a haka ta ji yace a gajiye ya ke ga yunwa kar ya gan ta cikin matsala ya kasa cin abincin zata bari sai ya nutsu ta fad'a masa komai. Tun da ya fita bai dawo ba sai bayan sallar isha a lokacin Mami ita ma ta dawo parlon ta na jiran sa ya zo yaci abinci Daddy dama wani lokacin a nasa dinning d'in na part d'in sa can ake kai masa abinci ba kullum ya ke zama yaci a main parlor ba, su na zaune ta yi serving d'in sa yana ci ita kam ta kasa koda loma d'aya sai kallon Shareef kawai take ta na juya maganganun da za ta fad'a masa ba ta so ta gan shi a cikin damuwa amma ya zama dole a wannan karon ta fito masa da 6oyayyen sirrin da bai sani ba............ "Mami ya akai bakya cin abincin kina ta ri'ke da spoon"? Ta ji muryar ya katse mata tunani kai ta jinjina ta na cewa "ji nayi bana son ci". "Me ki ke so Mami fad'a min na siyo miki ko na tashi na dafa miki sabon abinci kar ki kwana haka"?. "A'a Shareef gabadaya yunwar ce ba na ji ba komai ba ne". "ba ki da lafiya"?. "Lafiya ta 'kalau". D'agowa ya yi yana kallon ta bisa tsautsayi idon su ya had'u da ta juna d'auke idon ta tayi da sauri tana kaiwa gefe daidai Daddy ya fito Shareef da ke kallon ta da mamaki ya ce "Mami lafiya na ga idon ki yayi ja kuma ya kumbura kamar wanda ki kai kuka"? Jin abinda yace yasa Daddy kallon ta ya ga ta sunkuyar da kai kuma ba ta yi magana ba zama ya yi a kujerar parlon ya na cewa. "Shareef zo nan" tashi daga dinning d'in ya yi yana zuwa gurin Daddy ya zauna a kusa da shi ita ma Mamin ta mi'ke jikin ta na rawa ta je in da suke hawaye Shareef ya ga suna zuba a fuskar ta wanda a rud'e ya mi'ke ya na ri'ko ta yace "Mami wai lafiya kuwa kukan me ki ke dan Allah ki yi shiru haka za ki d'aga min hankali na" ya fad'a yana goge mata hawayen kai Mami ke girgizawa ta na jin yadda ya saka ta a jikin sa cike da kulawa da so ta ya zata iya fad'a masa wannan maganar bata so ya shiga wani hali yanzu me ye madafa me ya kamata ta yi? samun kan ta tayi da fashewa da kuka tana cewa. "Dole na yi kuka Shareef dole na yi ba'kin ciki akan abin da ban san yadda zan kwatanta maka ka fahimta ba Shareef ina neman yafiyar ka Shareef ka yafe min dan Allah"? Ta fad'a tana had'e hannuwan ta cikin rashin fahimta ya ce. "Kamar me kenan Mami wani abu ne ya faru ni babu abin da ki kai min ki daina kukan nan dan Allah" kai ta girgiza sabin hawaye masu zafi da 'kuna su na sake kwararo mata tace "a'a Shareef zaman lafiyar mu da ga ni har kai shine kar ka so sanin abin da ya saka ni a cikin wannan damuwar domin kai ma za ka samun kan ka a irin haka". "Saboda me Mami damuwar ki damuwa ta ce fad'a min dan Allah kin ji"?. "Tabbas a wannan karon ma kuma damuwar ta wa damuwar ka ce kai abun ya fi shafa ma ban san ta yadda zan yi maka bayani ka fahimce ni ba a yau ina matu'kar jin kunyar ka Shareef". "Ni fa Mami ban gane ba dan Allah ki daina kukan haka ki fad'a min abin da ya faru"? Kai ta girgiza Daddy da ke zaune ya na kallon su ya ce "Shareef samu guri ka zauna ni zan yi maka bayani ka ji" jin a yadda Daddy ya yi maganar ya sa Shareef kallon sa ya ga shi ma damuwa ne tsantsa a fuskar sa to wai me ye haka ne amma dai koma menene ya faru ba abu ne me dad'i kuma me sauki ba.......... "Ka na ji d'azu bayan fitar ka mun shigo gidan nan tare da kakan ka da kuma yayan mahaifiyar ka" d'an shiru Daddy ya yi yana girgiza kai wanda a 6angaren Shareef ya kalli Daddy da mamaki yana cewa "wanne kakan nawa Daddy mahaifin ka ya rasu tun kafin a haife ni mahaifin Mami na taso na tarar shi ma kuma yanzu ya rasu to wanne kakan na wa ka ke fad'a"? 'kak'karfan ajiyar zuciya Daddy ya sauke yana cewa "kakan ka wanda ya haifi asalin mahaifiyar ka na ke nufi". "Mahaifiya ta kuma Daddy"? Ya fad'a cike da tsananin mamaki tare da juyawa 6angaren da Mami ta ke zaune ta na gurzar kuka ya ce "dama Mami ba ke ce ki ka haife ni ba ko me ban fahimta ba"? Kasa magana Mami ta yi saboda a wannan lokacin ba ta san me za ta ce masa ba ko ta ina za ta fara ba kukan da ta ke yi ba zai bar ta ta iya yi masa bayani ba Daddy da ya fahimci halin rud'un da ta shiga ya sa yace. "Shareef Mamin ka ba za ta iya yi maka magana ba a halin yanzu ni ne zan yi maka bayani ka saurare ni da kyau kuma ka fahimci abin da zan fad'a maka kamar yadda ka ke tambayar Mamin dama ba ita ce ta haife ka ba? Eh gaskiya ne ba ita ba ce kawai dai ita ce ta ri'ke ka kuma ta raine ka tun kana jarari har zuwa yanzu da muke wannan maganar mahaifiyar ka sunan ta "Aishatu" ita 'yar Niger ce shekaru masu yawa da su ka wuce sun zo nan tare da mahaifin ta da kuma mahaifiyar ta sun zauna tsawon lokaci ni kuma lokacin shekara ta biyar da auren Mamin ka Allah bai ba mu haihuwa ba tun daga 6ari da ta yi sau biyu da mu ka je asibiti aka ce mahaifar ta ce da matsala ba za ta iya d'aukar ciki ta ri'ke shi har ya kai lokacin haihuwa ba babu irin 'ko'karin da likitoci ba su yi ba amma abun ya ci tura wannan dalili ya sa muka ha'kura mu ka mi'kawa Ubangiji kukan mu muna wannan yanayi Allah ya had'a ni da Aishatu na aure ta ita ma dai mun shekara biyu tare ba ta haihu ba sai daga baya a cikin shekara ta uku lokacin mahaifan ta sun sake zuwa Niger sun dawo a san nan ne Allah ya azurta ni da samun haihuwar ka mu na cikin farin ciki ya juye ya zame mana kuka domin bayan Aishatu ta haife ka ko awa uku bata sake yi a cikin duniya ba amma kafin ran ta ya fita ta bud'e baki ta ce ta barwa Mamin ka kai har abada ta ri'ke ka matsayin ita ce mahaifiyar ka koda ka d'ago kar ka san cewa wata ce daban ta haife ka ba Mamin ka ba wannan dalili ya sa bayan rasuwar Aishatu da mahaifin ta ya tattara ya koma Niger bai sake dawowa ba sai wannan shekarar shi ma yanzun ba zuwa ya yi dan ya gan ka ba ko a tona wannan maganar ba a'a ya zo ne bisa kasuwancin da ya ke kuma gobe ma zai koma Shareef Mamin ka mahaifiyar ka ce amma ba ita ce ta haife ka ba jin hakan kar ya saka ka cikin ba'kin ciki ko damuwa mun yi 'ko'karin mu ri'ke sirrin har abada amma Mamin na ka ita tace ya kamata mu fad'a maka ka san gaskiya wannan shine dalilin da yasa ka ga Mamin ka ta na kuka" daga haka Daddy ya yi shiru shi ma hawayen ne a fuskar sa saboda ganin irin tashin hankalin da yake tare da Shareef a lokacin da ya ke jin wannan maganar Mami kawai ya 'kure da ido kamar bai ta'ba ganin ta ba sai yau wani takaici da d'aci su na shiga zuciyar sa turiri na fita yanzu dama Mami ba ita ce ta haife shi ba a hakan shi d'an kishiyar ta ne amma ya d'ago cikin tsananin so da gata? "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya fad'a a fili kuma da 'karfi yana dafe kan sa wanda yasa Mami a razane ta mi'ke da sauri ta na zuwa in da yake da dafa shi cikin kuka ta ce......................... ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH YMA PAGE 50 "Shareef dan Allah kai................. Ba ta fad'i abin da ta ke son fad'a ba ya d'ago cikin gaggawa yana girgiza kai ya tashi ya rungume ta yana rufe mata baki cikin wani irin yanayi yace "a'a Mami kar ki yi magana ba sai kin ce komai ba dan Allah na gane yanzu ni d'an ki ne ke ce mahaifiya ta Mami ke ce ki ka haife ni" ya 'karasa maganar yana runtse ido kawai shi ma hawaye ya soma zuba masa sun dad'e a haka daga baya ya sake ta yana sake share mata na ta hawayen Daddy da ya ke zaune yana kallon su gabadaya tausayin dukkan su biyun ya rufe shi "innalillahi wa inna ilaihi raji'un lahaula wala 'kuwwata illah billahil aliyul azim" kad'ai ya ke maimaitawa ya san ba wanda bai shiga yanayi a cikin su ba dole su na bu'katar hutu ko da zai ci gaba da bayani dole sai dai gobe idan kowa ya d'an dawo cikin hayyacin sa zai saka Shareef a gaba su je ya gano kakan sa da kuma yayan mahaifiyar sa kafin su tafi duk da maybe fitar asuba za su yi. Washe gari tun da aka fito daga masallaci bayan sallar asuba Daddy da Shareef su ka wuce masaukin su Baba Sadoh amma babu alamar su domin 'kofar a rufe ta ke key tunani Daddy yayi ko dai tun daren jiya su ka tafi saboda kar su d'agawa Shareef hankali in dai haka ne shi zai d'auki Shareef d'in ya kai shi har Niger d'in ya gano su saboda ya kamata. Ba kowa ba wanda za su tambaya shiyasa Daddy ya ce kawai su tafi gida a lokacin Mami fitowar ta parlor kenan ta gan su sun shiga tsayawa ta yi ba tare da ta zauna ba take bin kowannen su da kallo a sanyaye tace. "Kun had'u ne"? Zama Daddy ya yi yana girgiza kai ya ce "a'a da alama basu kwana a Nigeria ba tun daren jiya su ka tafi saboda gudun had'uwa da Shareef ko kuma irin matsalar da za su fuskanta musamman saboda shi da ke da kuma ri'ke alkawarin Aisha" jin abin da Daddy yace yasa Mami kallon Shareef ta ga ita ya ke kallon jikin ta a sake ta ce. "Shareef na san nice na jawo komai amma ina neman afuwar ka da ace tun tasowar ka na fad'a maka abun ba zai maka ciwo kamar yanzun da ka mallaki hankalin kan ka ba ka yi ha'kuri dan Allah" murmushi ya yi ya na 'karasawa in da take tsaye ya kama hannun ta na dama ya yi masa kiss sannan ya d'ago ya na d'an kwantar da kan sa a kafad'ar ta yace. "Barka da safiya Mami na fatan kin tashi lafiya"? Jin abin da ya ce yasa daga Daddy har Mamin su ka fara bin sa da kallon mamaki ganin irin kallon da su ke masa duk su biyun ya sa ya sake yin murmushi ya na cewa "Mami yau zan fara zuwa zance gurin 'yar ki bari na je nayi wanka na zo ki koya min yadda ake hira" ya na fad'in haka ya juya ya nufi stairs ya na 'kulewa Daddy ya sauke numfashi ya na cewa. "Shareef akwai damuwa a ran sa tun daga jiya zuwa yau domin da dare wajen 'karfe biyu na je na le'ka bedroom d'in sa ta window na gan shi a zaune ko barci bai samu yayi ba amma saboda ba ya so ya gan ki cikin damuwa kamar yadda ya ke ciki hakan ya sa ya danne abun duk da ya na cin ran sa kawai dan ya gan ki cikin farin ciki wannan shine siffar namiji kuma d'a na gari wanda ya yi ri'ko da tarbiyyar da ki ka ba shi" hawaye Mami ta ji ya fara zubo mata amma saboda ta san a kowanne lokaci za ta iya ganin Shareef ya fito ya sa da sauri ta goge ta na girgiza kai ta ce "da na sani 'keya ce ba wanda ya ke ganin ta da nasan nan gaba abun nan zai dame ni wallahi tun yana d'an yaro da na fad'a masa cewa ba ni ce mahaifiyar sa ba ni kaina da ban samu kaina cikin wannan takaicin da tashin hankalin da nake ciki yanzu ba amma mai faruwa ta riga ta faru da baya idan ta wuce ta na dawowa da na gyara wannan kuskuren da na yi" kai Daddy ya girgiza yana cewa. "Baya ba ta dawowa abin da yafi alkhairi kawai ki danne kamar yadda shi ya yi 'ko'kari ya danne ki manta da wannan al'amarin mu koma yadda mu ke da rayuwar farin ciki hakan shine zai taimakawa dukkannin mu amma idan ba ki d'aure ba Shareef ma ba zai ta'ba mantawa ya sake ran sa ba duk da yana 'ko'karin yin hakan" kai Mami ta d'aga ta na goge hawaye bisa dole ta maye gurbin da murmushi dole ta danne kamar yadda Daddy ya ce kodan Shareef d'in................ ZUCIYAR ALIYU CE J♣ W♣A @YUSRAH YMA PAGE 51 Amirah ta na bedroom a kwance su na waya da Aliyu sai ta ke tambayar sa "Aliyu sai yaushe za ka dawo gida ne"?. "Ba rana". "Me ya sa"?. "Saboda lokacin dawowar ta wa baiyi ba zan zo amma ba kwana kusa ba". "Gaba za ka yi kamar shekara na wa kafin ka zo"?. "Wannan kuma ban sani ba sai abin da ya faru wani abu ne"?. "A'a kawai dai na yi kewar ka ne sosai so nake na gan ka ido da ido sosai fa na ke jin kewar ta ka musamman idan na zauna ba abin da na ke tunani sai rayuwar da mu kai a Spain gwanin burgewa". "Da kyau ki huta lafiya" ya fad'a ya na 'ko'karin kashe wayar da sauri ta ce "ahh Aliyu wai har ka gaji da yin wayar da ni"?. "A'a me ki ka gani"?. "Na ji kuma ka na shirin kashewa"?. "Eh zan sauka akwai abin da zan yi kuma kira na ake yi daga wajen aiki na yau daji za mu shiga" kai ta d'aga ta na sake sabon juyi ta ce "ok ba damuwa Allah ya fito da ku lafiya" "Amin thank" ya na fad'in haka ta ji d'it d'it aje wayar ta yi a gefen filon da take kwance akai ta na sauke numfashi ta yi shiru kamar me tunani sai kuma ta saki murmushi ita kad'ai ta fara magana. "Aliyu kai ne mafarki na lokaci ya yi da zan fito na bayyana maka soyayya ta tun da naga kamar kai ba ka da ra'ayin furta min ba da wanda na dace na zama matar sa sai kai kuma in sha Allahu kai zan aura" tashi zaune ta yi ta na kallon agogo ganin har sha biyu na rana ta san yanzu ta na fita Mama fad'a za ta yi mata shi yasa ta mi'ke ta je tayi wanka da ta fito sai ta dau'ki takardun jarrabawar ta kamar gaske ta fita da su parlor ba Mama ba Nansy murmushi ta yi ta na samun kujera kawai ta zauna tana aje takardan a kusa da ita ta bud'e wayar ta ta hau WhatsApp ta fara chatting da 'kawayen ta. ** ** Sakamakon yau weekend ba aiki ga shi Baby ta kwana ta na mafarkin Shareef hakan ya sa da gari ya waye ta yi tunanin zuwa har gida ta gan shi har ta gaisar da Mami amma me? Tuna ya ce mata kar ta 'kara zuwa gidan su ya sa ta ja dogon numfashi tana d'auko wayar ta ta zubawa number sa ido ta dad'e daga baya ta danne kiran sa amma har ta katse bai d'aga ba ta sake kiran sa nan ma bai d'aga ba ji ta yi hankalin ta ya d'an fara tashi sake kiran sa ta yi karo na uku sai ta ji d'it alamar ya katse zaro ido ta yo firgice ta na kallon secreen d'in sai kuma ta ga na sa kiran ya shigo d'agawa ta yi ta na cewa. "Hello barka da safiya Shareef ya ka ke"?. "Lafiya ki na kira ina wanka ne shi ya sa ban d'aga ba yanzu na fito" jin abin da ya ce yasa ta sauke ajiyar zuciya cikin jin dad'i ashe ba 'kin d'aga mata ya yi ba baya kusa ne tace "ok ba damuwa dama abu zan tambaye ka". "Me ne"?. "Shareef dan Allah idan ba damuwa ka zo ina jiran ka za mu yi magana"?. "A ina kenan"?. "A inda ka ke so mu had'u". "Kamar ya ban gane ba"?. "Ina nufin ko gidan mu ne zaka iya zuwa dan girman Allah ka ji wallahi muhimmiyar magana za mu yi". "Ok ba damuwa amma yanzu ba zan samu lokaci ba akwai in da zan je maybe sai wajen 'karfe uku ko biyar zan zo idan na kusa shigowa zan kira ki na fad'a miki" cikin farin ciki Baby ta ce "wayyo na gode Shareef sai na gan ka". "Ok" ya fad'a yana aje wayar shiryawa ya fara yi sai da ya gama sannan ya d'auki wayar ta sa yana fita saukowa daga stairs ya ke yi yana kallon agogon dake d'aure a hannun sa ganin ba Mami yasa ya nufi hanyar kitchen yasan ba zai wuce ta na can ba iya Rabi ya tarar ta na aiki ba Mami fitowa ya yi ya dawo parlon kenan ya gan ta ta shigo ta na cire mayafin da ke kan ta tare da sauke numfashi ta na kallon sa ta ce. "Wannan wanka haka ina za ka je"?. "Gurin 'yar ki" jin abinda yace yasa ta saki murmushi ta na cewa "humm dama na san sai dai can d'in Allah ya sa rabon ka ce". "Amin Mami daga ina ki ke ko dai anguwa ki ka je"?. "Eh na je asibiti ne an kai Tasnin ba ta da lafiya" d'an zaro ido ya yi yana cewa "Subanallahi cousin sister na ba lafiya me ya same ta"? "Tasnin 'yar gidan 'kanwar Mami ce". "Ina ganin ko haihuwa ce ko kuma lokaci bai 'karaso ba bana ce ba na baro su yanzu dai jikin da sauki". "Ok alhamdulillah bari na je ni ma na duba sister na ta ya zan iya nutsuwa abokiya ta tana can a gadon asibiti Mami na tafi" murmushi Mami ta yi tana bin sa da kallo ta ce "ok sai ka dawo ka gaida min surukar ta wa". "Za ta ji Mami" ya fad'a ya na fita motar sa ya d'auka daga gida gidan su Neehal ya fara zuwa su ka tafi tare asibitin a lokacin Tasnin ta na zaune da Umman ta su na ta zance kamar ba ita ce majinyaciya ba ganin Shareef ya sa ya murje ido ta na cewa "mu gudu ko mu tsaya mafarki na ke ne jama'a d'an uwa rabin jiki yau kai na ke gani yaushe rabon duniya da ayyaraye"? D'an hararar ta ya yi yana cewa. "Kuma tsakanin ni da ke waye za'a wa irin wannan murje idon"?. "Kai man rabon da na saka ka a ido na har na manta". "Yau kin gan ni ai kema kin san ba zan je gidan auren ki ba tun da ni ne babba kuma ni namiji ne ko"?. "Duk da haka amma kamata ya yi a sati ko sau d'aya ne ka ri'ka zuwa". "Ba zan zo ba" ya fad'a ya na mayar da hankalin sa kan Umman ta ya ce "barka da safiya Umma ya mai jikin"?. "Lafiya kalau Shareef ga ta nan alhamdulillah". "Allah ya 'kara sau'ki". "Amin wannan fa ko rakiya ta yo maka"?. "Eh ta rako ni na duba gawa ta'ki rami ne" ya fad'a ya na kallon Tasnin wacce ta yi dariya ta na cewa "wace gawa ta'ki rami amma dai ba da ni kake ba"?. "Eh da ke nake yarinya ga matar da zan aura nan" zaro ido waje Tasnin ta yi tana duba Neehal da mamaki tace "kai dan Allah da gaske kake babban Yaya"?. "Da gaske man Auntyn ki ce". "Wow masha Allah dad'i kashe ni kaji har na daina jin zazza'bin da na ke ji saboda farin ciki alhamdulillah sannu Aunty in-law ya kike"?. "Lafiya kalau ya jikin na ki"?. "Jiki alhamdulillah na samu sau'ki Yaya Shareef ashe kwanan nan zamu sha biki"?. "A'a ba kwanan nan ba". "saboda me"?. "Saboda ba na so baki haihu ba ayi bikin na fi so sai kin samu lafiya dad'in yadda zaki je ki yi shagali a biki na ko"? Kai ta d'aga tana cewa "yauwa babban Yaya haka nake son ji Allah ya kai mu da alkhairi". "Amin bari mu tafi" jin abinda ya ce yasa Tasnin 6ata fuska tana cewa "haba dan Allah ya tafiya kuma daga zuwan ku". "Eh zan je na mayar da ita gida ne". "Amma dan Allah idan an bani sallama za ka kai mun ita har gida mu sake gaisawa"?. "Ok in sha Allahu". "Ka yi alkawari"?. "Kar ki damu zan cika miki ke dai Allah ya baki lafiya shine burin mu". "Amin na gode Aunty na kin gaida gida sai na gan ki". "To Allah ya sauwake" Neehal ta fad'a ta na gyara glass d'in fuskar ta kud'i Shareef ya ajewa Tasnin da d'an fruits kayan 'karin jini na mai ciki sannan su ka tafi ya mayar da Neehal gida su ka gama maganar da za su yi sannan ya koma gida.................... ZUCIYAR ALIYU CE @YMA DUTSE PAGE 52 Kamar yadda ya cewa Baby sai wajen 'karfe uku bai samu dama ba sai bayan sallar la'asar ya je gidan su humm samu yayi ta yi masa hidima ta kece raini abubuwa kala-kala ta d'au wanka ta na zaune ta na jiran sa ta ga kiran sa ya shigo alamar ya 'karaso tashi ta yi tana d'aukar mayafin ta ta fita yana waje a tsaye jikin motar sa hum kamar a mafarki haka ta ke gani wai yau Shareef ne ya zo gurin ta har gidan su day sallama ta karasa ta na kallon yadda ya d'au wanka ta ce. "Sannu da zuwa Shareef bismilllah 'karaso ciki"? Kai ya girgiza ba tare da ya kalle ta ba yace "no ki barshi ba sai na shiga ciki ba za mu iya yin maganar mu anan". Kai Shareef dan girman Allah ka zo mu shiga ciki". "Me wai kina nufin gidan ku zan shiga"?. "Eh amma ai ba cikin gidan ba sashin saukar ba'ki za mu je baya ala'ka da cikin gidan". "Ok". "Yauwa mu je" ta fad'a jiki na mazari ta yi gaba lock ya sakawa motar sa sannan ya bi bayan ta tsayawa ta yi tana cewa "ka shigo da motar ta ka harabar gidan man idan zaka tafi shikenan" kai ya girgiza ya na cewa "a'a bar shi kawai ai ba zama zan yi ba" jin abinda yace ya sa ta sauke numfashi duk da dama ta san sa'a taci ya zo mai gari ta 'kwallawa kiran ya fito da sauri ya zo yana cewa "ga ni Hajiya". "Ka fita waje ka kula da motar da ta ke 'kofar gidan nan kafin me ita ya fito". "To Hajiya" ya fad'a ya na juyawa ya fita "mu je Shareef" Baby ta ce tana ci gaba da tafiya kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa suka shiga ya ga yadda ta had'a abubuwa na alfarma iri-iri duk saboda shi zama yayi Baby data kasa nutsu jiki na rawa ta ce. "Barka da zuwa gidan mu Shareef me zan yi serving d'in ka komai da ya ke nan na yi ne saboda kai" murmushi ya yi yana d'an girgiza kai tare da kallon ta yace "na gode da kulawa". "Kar ka damu Shareef ko me na yi maka ban fad'i ba zaman tare ne ya kawo haka". Kai ya jinjina bai sake magana ba juice ta zuba a cup tana mi'ko masa har zai girgiza mata kai amma sakamakon na dad'i ya sa ya kar'ba ya d'an kur6a ya na cewa "thank you" ajewa ya yi yana cewa. "Uhum ina jin ki maganar me ki ke so mu yi da ke"? Gyara zama Baby ta yi tana sauke numfashi me nauyi tare da yin shiru ta na tunanin ta ina zata fara da wacce kalma za ta yi masa bayani yadda zai fahimce ta sosai.............. "Baby" taji ya kira sunan ta da sauri ta d'ago ta na barin tunanin da ta ke yi tace "na'am". "Na ce me kike son fad'a min ki ke nema na har gidan ku"? Zazzafan huci ta sake fitarwa ta na kallon sa a sanyaye ta ce "duk da ban san ta inda zan fara yi maka bayani ka fahimta ba amma Shareef ina cikin matsananciyar damuwa a kan ka na rasa sukuni na rasa walwala duk saboda kai kullum ina tunanin yaushe ne zan daina shiga wannan halin amma na duba babu rana idan har ba samun ka na yi na fad'a maka ba" shiru ta yi ta kasa ci gaba Shareef da ya 'kure ta da kallo ya ce "uhum ina jin ki ci gaba" kai ta girgiza tana dafe goshin ta tare da runtse ido ta bud'e ta na cewa. "Shareef ina son ka". Bai yi mamakin jin hakan daga gare ta ba domin dama tun da tace za su yi magana abin da ya kawo a ran sa kenan gashi kuwa hasashen sa ya tabbata kai ya jinjina bai yi magana ba Baby ta sake cewa. "Shareef ina son ka kasan tun yaushe na ke son ka? Huuuuuhhh ta sauke numfashi muryar ta ya fara rawa ta ce "tun lokacin da na fara ganin ka wannan dalilin ya sa na dage sai da ka san ni sannan na 'kulla ala'kar mutunci da kai a tunani na ta wannan hanyar ce kai ma za ka ji kana so na amma na ga tsawon shekaru ba wani canji shiyasa na kasa ha'kuri na fallasa maka asirin zuciya ta wallahi Shareef kai ne buri na kai na ke so ka zamo miji gare ni dan Allah kar ka ce a'a" ta fad'a ta na had'e hannun ta gurin d'aya alamar ro'ko kai ta ga ya girgiza ya na cewa. "Dole na ce a'a". A zabure ta ce "me ya sa"?. "Saboda ni ban ta'ba jin hakan a rai na ba". "A'a Shareef dan Allah ka daina cewa ba ka ta'ba ji ba zaka ji daga baya indai ka amince min zaka tsinci kan ka kamar yadda na ke a yanzu ina son ka son me mugun 'karfi wanda ban ta'ba yiwa wanin ka ba tun da nake ban ta'ba had'uwa da wanda na ji zan iya auren sa na zauna da shi ba sai kai please Shareef ka ce zaka aure ni kana sona"? Cije lips ya yi yana sake girgiza ma ta kai yace. "Baby bazan iya soyayya dake ba balle rayuwar aure bana ra'ayi dan Allah ki fahimta bazan iya za6arki matsayin uwar 'ya'yana ba idan nayi hakan banyi musu adalci ba" rud'e Baby tace "haba Shareef me kake fad'a ne haka meyasa ba za ka iya soyayya dani ba balle ka aure ni ina da tauya ne"? Kai ya jinjina yana cewa "tawaya me girma ma kuwa ke ba ki gani ba ne"? jin abinda yace yasa ba arziki Baby ta fara kallon jikinta taga ta inda tauyar da yake fad'a take amma dai bata gani ba d'agowa tai tana kallon sa sai taga ya saki murmushi yana girgiza mata yatsar hannunsa alamar ba daidai ne abinda take hasashe bashi bane yace. "Ba tauya a halittar jikinki ba nake magana tauya a dabi'un ki da mu'amalar ki da mutane ina hankalce dake sannan ina lura da duk wani motsin ki na gama karantar halayyan ki tabbas idan na aure ki ban yiwa yaran dazan haifa adalci ba ko kad'an". "Me ye da dabi'un nawa Shareef"?. "Wannan kuma kanki zaki yiwa wannan tambayar ba ni ba domin kinfi kowa sanin wacece ke nima na fahimce ki balle kuma ke kanki". "Indai nice bana jin ina da wata matsala Shareef kawai ka fito fili kace so na ne baka yi bawai baza ka iya soyayya dani ba". "Ba haka bane kar kiyi min gurguwar fahimta na fad'a miki gaskiyar abinda yake cikin raina ne ko mace yanzu ba ai mata auren dole balle namiji". "Me hakan yake nufi"?. "Bazan aure ki ba kuma kar fad'ar hakan ya sa ki kawo wani abu daban a ran ki". "Dalilin ka nake son sani kawai ba abin da zan kawo a rai na ba". "Bana maimaita magana saboda na fad'a miki hujja ta kin gane"? Shiru tai ta zuba masa ido zuciyarta tana tafasa da yasan yadda take azabtuwa da tsananin sonsa da baiyi mata jayayya akan son da tace tana yi masa ba taya zai fahimta taya zata gwada masa ya gane wacce hanya zata bi ita fa bata jin koda duniya ne suka taru akan ta rabu da shi zata iya.............. Maganar da kika kira ni muyi kenan ko da wata"? Taji ya katse mata tunani d'agowa tai tana kallon sa ta kasa cewa komai sai da ido take binsa gira ya d'auke yana cewa "ki huta lafiya" yana fad'in haka ya juya zai bar gurin da sauri ita ma ta mi'ke muryarta kamar zai fashe tace. "Shareef dakata" tsayawa yayi ba tare daya juyo ba yace "uhum" ajiyar zuciya ta sauke tana takowa inda yake ta zagayo ta tsaya a gabansa yadda zai ganta ta fara magana "Shareef ya kamata ka tausayawa rayuwa ta ka dubi son da nake maka karka barni na fad'a gagari dan Allah ka samu lokaci ko nan da wata guda ne ko shekara ka zauna kayi nazari a kaina komai kake so nayi alkawari zanyi maka zan gyara halaye na". Kaiya girgiza yana kallon ta kamar yadda ta kafe shi da ido yace "maganar zaki canza halayen ki wannan ba gaskiya bane domin hali tamkar zanen dutse ne bashi shafuwa koda kinyi kokarin canzawar daga baya zaki koma kan halin ki da ace zaki canza Baby da yanzu kin canza shekara ta nawa dake a hospital d'in nan ina fad'a miki abinda ya kamata ina miki nasiha amma bakya d'auka na gwada ki ta hanyoyi da yawa amma baki iya cinye jarrabawar da nayi miki ba some times nakan yi wani abu saboda naji me zaki ce a kai saina tarar kin 'kalubalancin abun koda ya kasance gyara ne ga rayuwarki sannan idan naga kuskure na nuna miki maimakon ki min godiya saidai ki nuna kinji haushi da tunatarwar da nayi miki yanzu Baby me irin wadannan halayen ce kike so na aura a tunani na ko baki furta min ba ni nazo miki da kalmar soyayya zaki ce a'a baki dace dani ba naje na nemi mace ta gari wacce idan na fad'a mata magana zata ji idan na bata umarni zata yi aiki dashi yanzu tsaya nayi miki misali kamar wannan budurwar da kika bugeta ranar da naje da basket hospital kece da laifi gashi wayarta ya 6aci maimakon ki bata ha'kuri sai bala'i kike mata harda marinta kuma ina miki magana kina dad'a daga muryarki akan tawa hakan gani kike ado ne? Na fad'a miki wani abu da zai baki mamaki kwanan baya mun had'u da ita a wani wuri abinda tace min tana sake bani ha'kuri akan wannan abun daya faru tsakanin ki da ita gashi ke da muka shiga office ina miki fad'a sai kika nuna abinda kikai shine daidai ko"? Hankali tashe ta ce. "Ban yi tunanin hakan wani abu bane"?. "Baki tunanin hakan wani abu bane ashe idan yayan ki yana miki fad'a a gidan ku bakya tunanin kiyi shiru ki saurare shi sannan ki bashi ha'kuri ko kece da gaskiya"? Shiru tayi jikinta yana tsumma ta sunkuyar dakai hawaye sai faman zuba mata yake da tasan Shareef yana komai dan ya gwada tane da ta zama cikin mata masu ha'kuri data kame kanki ta danne kowanne irin abu idan ya taso gashi yanzu tana gani duk yadda take son shi ya nuna halinta bazai barshi ya aure ta ba kuka ta fashe dashi tana girgiza kai ta kasa magana. "Kuka bazai miki amfani ba kamata yayi kije ki zauna kiyi nazari sosai ki gyara halayyarki ki ri'ka kallon mutum da kima domin d'an Adam ba abun wula'kantawa bane kamar yadda ke kika d'auka" sosai ta ke kuka tana girgiza kai cike da tarin nadama tace. "Wallahi Shareef na tuba daga yanzu na gane na amince ni ce na zalunci kai na kuma zan gyara kamar yadda ka ke bu'kata amma dan Allah kar ka fitar dani a cikin rayuwar ka hakan zai cutar dani kar ka watsar da ni". "Ai dama bance zan watsar dake ba maganar da kika zo min dashi ne yasa nima na fad'a miki abinda ya kamata ace kin sani game da ni ba zan iya rufe miki gaskiya ba ko dan mutunci da sanayyar da ya ke tsakanin mu" huci mai zafi ke fita daga jikin Baby tsabar irin tafasar da zuciyar ta ke yi ta ce "in dai ba za ka watsar dani ba to Shareef ka kar6i soyayya ta ka ji"?. "A'a wannan kuma ba zan iya ba kawai ki yi ha'kuri Baby za mu ci gaba da mutunci idan kin bu'kaci hakan amma ba maganar so ba kin gane"? Shiru Baby ta yi ta kasa cewa wani abu daga haka gabadaya hankalin ta neman fita daga jikin ta ya ke yi shi ma daga haka bai sake mata magana akan komai ba sai mi'kewa da ya yi yana cewa. "Zan tafi ki kula" ya na fad'in haka ya juya ya bud'e 'kofa ya fita hannu Baby ta d'ora a ka ta fasa ihu me 'karfi wanda ba san ta yi ba tsabar rud'ewa da cikin azama ta yi saurin rufe bakin ta tana fatan Allah ya sa kar a jiyo daga cikin gidan su kai ta kifa akan kujera kawai ta yita kuka domin idan ba kukan ta yi ba baza ta ta'ba jin sassauci a zuciyar ta ba.............. ZUCIYAR ALIYU CE •♣ YSRH ♣• @YUSRAH YMA PAGE 53 Yau Zainab ba za ta samu damar zuwa school ba sakamakon tun dare da zazza'bi ta kwana gari ya na wayewa ta soma kwara amai da sauri Umma ta fito ta na zuwa in da take a dur'kushe ta na ta amai kwaaa kwaaa yellow shar alamar malaria ce d'agota ta yi ta jingina ta a jikin ta ta na cewa. "Sannu Zainab zazza'bi ki ka tashi da shi sannu bari Sameer ya tashi daga barci sai ya duba ki" numfashi kawai Zainab ta ke yi sama-sama kamar minti biyu Umma ta na 'ko'karin mi'kewa ta kai ta d'aki sabon amai ya sake 6alle mata wannan karon har jikin Umman ta 6ata juyi Asabe ta yi daga kwancen da take jin 'karar amai ya sa ta zaro ido ta na tashi zaune tare da dirowa daga kan gado da gudu ta fito waje ta na yin inda ta ga Umma da Zainab d'in a dur'kushe 'karasawa ta yi ta na tafa hannu ta ce. "Laha'ilah ha'illallahu Zainab amai ki ke wato ciki ne da ke"? Ba wanda ya kula ta ta ci gaba "kan uban nan wallahi ba ku isa ba gara da asirin ku ya tonu yau kowa zai sani ashe dama ke 'yar iska ce? Humm aiko baki Isa ki haifa mana d'an shege a cikin gidan nan ba, ba za ki sa yaran mu su rasa mazajen aure ba sai dai ki tafi D'an Yana can dangin gyatumar ki, ki haifa musu tsiya a can yanzun kuwa zan tara mu ku jama'ar gidan nan kowa ya zo ya gani da idon sa kar a 'karya ta ni daga baya" ta na rufe baki ta d'ame iya 'karfin ta, ta fasa wani uban ihu ta na cewa. "Yekuwa jama'ar gidan nan kowa ya fito yau ya ga abin da Zainab ta ke aikatawa" ta fad'a ta na fita daga 'kofar ta su ta sake yin sabon ihu ta na cewa "wai ba, mutane a,gidan nan ne ba za ku fito ku yi kallo ba wayyo Allah jama'a ku fito wayyo yau wa su asirin su ya tonu" haka ta yi ta bin 'kofa 'kofa ta na hela tuni kuwa kowa ya fara fitowa yara da manya kowa tambaya ya ke. "Me ya faru asirin su waye ya tonu"? Nuna 'kofar shiga lungun su Asabe ta yi ta na cewa "cikin shege ne da Zainab tun jiya da dare take amai har yau yanzu ma su na nan a waje tare da munafukar uwar ta tana faman kwara aman kamar ba za ta daina ba" jin abinda Asabe ta ce ya sa kowa ya zaro ido wasu na cewa. "Ciki? Tabd'ijan dan'kari yau ake bala'i bari mu je" rudududu suka fara gudu su na shiga 'kofar su ka je su ka zagaye Umma da Zainab kowa ya na salati kai Asiya ta jinjina ta na cewa "Allah ya so Zaidu da ya'ki auren yarinyar nan da yanzu an cusa masa d'an wani an d'ora masa bala'i" kai Asabe ta jinjina ta na cewa. "To kin gani dai gashi nan ciki gare ta da aka so lalla6a ku ki kar'bi jikan da bai fito daga jinin d'an ki ba ni fa dama abun nan yana bani mamaki kwanakin nan na ga yarinyar nan ta yi wani irin fari ta sake ja d'auu idan ta fito rana ka kalle ta har d'auke maka ido ta ke tsabar yalo da haske ashe hasken ciki ne 'kayan kwad'ayin da ake siyowa aci ba'a banza ba kullum ba'kar leda ta na tafe da tofe-tofen yawu". "To wai tsaya an fad'owa Hajiya ne"? Cewar Mairo wacce ke tsaye ta na dariyar farin ciki kai Asabe ta girgiza ta na cewa "ina za'a fad'o mata idan ba so kike mu ma mu shiga uku ba kina ganin fa laifi ko ba naka bane idan ta ga dama sai ta 'ka'kaba maka dan kawai ta samu hanyar da zata ci maka mutunci". "Wallahi ko ma meye sai an fad'o mata dole ta sani wannan babbar matsala ce ba abu ne wanda za'ai shiru a rufa asiri a kan su ba". "Dama wa zai rufawa Hauwa asiri a gidan nan? Sai dai munafiki irin ta amma indai mutum yasan gaskiya bazai yarda da wadannan mutanen ba". "To yanzu dai kawai aje a fad'owa Hajiya ta zo taga komai da idon ta" cewa Asiya ta na fita daga 'kofar da sauri Umma da ke zaune tare da Zainab a jikin ta bata cewa kowa komai ba sai mi'kewa da ta yi ta na d'ago Zainab ganin yadda su ka zagaye su kamar wanda su kai sata ya sa ran Umma ya yi mugun 6aci ba tare da ta yi magana ba ta hankad'a su gefe za ta wuce caaaa su ka yo kan ta kowa na fad'ar tsiyar da ya d'ebo a bakin sa ya na sauke mata jin hayaniya yasa Sameer tashi ya fito wajen ganin yadda 'kofar take fal da mutane ga Umma a tsakiyar su ta na ri'ke da Zainab wacce idon ta ke rufe hawaye ya na zuba cike da mamaki ya 'kasaro ya na cewa. "Umma lafiya"? Tun kafin Umma ta yi magana Asabe ta yi caraf ta ce "shashashan banza wato ita zaka tambaya lafiya a tunanin ka zata fada maka gaskiya ne? To yau Allah ya toni asirin mayyar ta ka ciki gare ta gashi nan amai ta ke" a rud'e Sameer ya ce "ciki kuma"? Tsananin mamaki ya gama rufe shi da 'karfi Asabe ta ce "eh cikin shege ma kuwa ga ta nan ai idan kana tunanin 'karya ko sharri akai mata" shiru Sameer ya yi yana kallon Zainab wacce har lokacin hawaye basu daina zuba mata ba kuma ba ta bud'e idon ta ba ya ce. "Wannan ba gaskiya ba ne hakan ba zai ta'ba faruwa ba har abada wallahi duk wanda ya fad'a muku ma ya yi 'karya". "Ni ce na fad'a ni ce ma'karyaciyar kenan tun da duk mutanen wajen nan ba wanda ya sani sai da na je na fad'o musu". "Amma Umma me ya sa za ki yanke hukunci akan abin da baki tabbatar ba babu kyau shedar zurrr" a masife ta ce "kai dan kan uwar ka na yi shedar zurrr d'in sai kasa a yanke min hukunci". Bai kula zancen da take masa ba sai kallon Umma da ya yi yana cewa "Umma ki mayar da ita d'aki bari na je chemist na d'auko kayan aiki na zo na duba ta" yana fad'in haka ya koma d'akin sa ya d'auko key d'in chemist d'in ya fito ya saka takalmin sa ya fita a hanya ya had'u da Hajiya ta fito za tai 'kofar ta su ganin sa yasa tace..................... ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA PAGE 54 "Kai Samar tsaya uban waye ya yiwa Zainab ciki"? Jin tambayar da ita ma take masa ya sa ya ta'be baki ya na wucewa ya ce "ki je ki tambaye ta man" ya na fad'in haka ya fice kai Hajiya ta jinjina ta na ci gaba da tafiya ta ce "za ta ci uban ta ai wallahi yau sai ta fad'a min tsinannan da ta je ya bata kud'i ta bashi kan ta ko na yi mata duka da wannan sandan" 'kofar ta shiga ganin yadda ta ke cike da mutane ya sa tace. "Ina me cikin ta ke ko na'kuda ta ke yi"? Jin tambayar da ta yi yasa wasu daga cikin 'yan matan gidan su ka rangad'a gud'a a fusace Hajiya ta ce "mitsiyata dan tselan uwa ku da ku ke shewa da farin ciki shashashu ba ku san idan labari ya fita waje ba saurayin da zai sake zuwan gidan nan neman aure ba mahaukatan banza ina magana ku na dariya ai lalacewar har da kowacce sai dai ta zauna a gaban uwar ta ta tsufa ba miji". "Ni kam aure sai na yi wallahi ko d'an shaye-shaye ne balle ma Allah ya rufa asiri wacce nan idan kin ji ana cewa ta gaban jirgi ta gaban mota ni ce" Rasheedat ta yi maganar ta na nuna kan ta kallon ta Hajiya ta yi ta na cewa "zan ci uban ki ne 'yar marar kunya kawai bari a gama wannan abun wallahi sai na miki duka a gidan nan" hararar ta Rasheedat ta yi tana cewa. "Allah ya sauwake na bari har na zauna ki dake ni kamar 'kasa ce abinci na" kai Hajiya ta jinjina ta na cewa "wallahi tun da na rantse ba zan yi kaffara ba sai dai ki bar gidan nan har abada amma sai na dake ki" ta na fad'in haka ta shiga d'akin Zainab iya Umma ce a ciki sai Asabe dake tsaye ta ri'ke labulen 'kofar d'akin ta na jijjiga ta na harare-harare zama Hajiya ta yi akan kujerar d'inkin Zainab ta na kallon Umma ta ce. "Kin zo kin saka yarinya a gaba kin yi tagumi dan munafirci kamar ba ke ce ki ka d'ora ta akan wannan mummunar hanyar ba yau wa gari ya waya wa"? Kan Umma a sunkuye cike da damuwar maganganun 6atancin da 'yan gidan su ke fad'a akan Zainab wanda ba gaskiya ba ne hawaye ne ya ke ta zuba mata takaici ya hana ta iya d'agowa balle ta yi magana har Sameer ya dawo d'akin ya shigo zai fara duba ta Hajiya ta ce. "Kai Samar ban yarda da kai ba kar ka fara duba ta ba baza ka ta'ba fad'a min gaskiya ba" jin abin da tace yasa Sameer had'e fuska ya na cewa "ai dama ba sai na fad'a miki gaskiya ba ni dai damuwa ta 'yar uwa ta, ta samu lafiya" ya fad'a ya na dur'kusawa a kusa da Zainab ya fara duba ta waje Hajiya ta le'ka ta na kallon Zakiyyah da ke tsaye a 'kofar d'akin ta ce. "Ke Abdul-Razza'k ya tafi asibiti ne"?. "Ban sani ba ko ya tafi kira miki shi za'a yi"? Zakiyyah ta fad'a cike da gulma ta na le'ken d'akin ta ga ina Zainab d'in muryar Hajiya ta ji ta ce "eh kira min shi ki ce ya zo ya duba Zainab ya taho da abun gwajin ciki" dariya Bilki ta yi jin abin da Hajiya ta ce harda girgiza ta na cewa "ayuririiiiiiiii wayyo Allah na dad'i kashe ni ashe kwanan nan za mu ci ragon suna" wurgo mata sanda Hajiya ta yi tana cewa "a gidan uban ki za ku ci ragon shegiyar yarinya mara kishin zuci" ta'be baki Bilki ta yi tana cewa. "Ina ruwa na da ita da zan damu dan ta yi ciki dama ni nace ta je tayi"?. "Da baki ce ta je tayi ba ina uban ku d'aya kuma yayar ki ce duk tsiya idan ana gulmar za'a ce 'yar gidan Abdullahi ta yi cikin shege abun bai shafe ki ba"?. "Caf wallahi Hajiya bai shafe ni ba babu had'in hanyar mota data jirgi dan mu na uba d'aya ta yi abun kunya ba dalilin da zai sa na damu kai na akai". "K'warai kuwa ba abin da yayi miki zafi ai ba ke ce kika sa taje gurin samarin banzan da suke bata kud'in ta na bushasha ba" Asabe ta fad'a tana gyara tsaiwar ta ran Sameer a 6ace ya d'ago ya na cewa "wai dan Allah me ye haka Umma"? Kamar Asabe ta buge shi haka ta ji lokacin da yai maganar ta ce "uban ka ne haka nace uban ka ne ba zan fad'i abin da ya ke raina ba saboda tsoro ko me"?. "Saidai uban ki ne haka ba uban sa ba" Hajiya ta fad'a ta na aikawa da Asabe harara hannu Asabe ta d'aga ta na cewa "Hajiya ba ruwan ki anan tun da ba dake na ke ba magana ce tsakani na da d'ana" baki Hajiya ta bud'e za ta yi magana sallamar Abdul-Razza'k yasa ta yi shiru shigowa ya yi ya na kallon dukkan su ya ce. "Me ya faru Hajiya ki ke tura nema na lafiya"?. "A'a ba lafiya ba ka ga yarinyar nan zaka duba min" kallon Zainab dake kwance ya yi ya kalli Sameer wanda ya ke duba ta yace "kuma Hajiya bayan ga Sameer nan shima fa likita ne gashi ya na duba ta" kai Hajiya ta girgiza ta na cewa "ai ban yarda da shi bane bakin su d'aya ko da matsala zai iya 6oye min shiyasa na sa a kira ka d'auko na ka kayan aikin ka duba ta yanzu" da har zai sake magana amma gudun abin da Hajiyan zata ce yasa ya fita ya koma kofar su ya d'auko kayan aiki shima kallon Sameer Hajiya ta yi tana cewa. "Kai Samar tashi ka baiwa 'kwararre guri ya bincika min sosai" kai Sameer ya jinjina kamar zai yi magana amma gudun hayaniya ya sa ya matsa kad'an ya barwa Abdul-Razza'k gurin shi ma du'kawa ya yi ya fara duba ta kamar yadda Sameer d'in ya yi sannan ya ce. "Hajiya ba komai ba ne zazza'bin malaria ne kawai ya ke damun ta" yana rufe baki ta ce "karya ka ke" da mamaki ya juyo inda ta ke ya na cewa "ban gane 'karya na ke ba kamar ya"?. "K'arya ka ke man naga ka kalli Sameer kafin ka yi min magana" baki ya bud'e cike da mamaki ya na kallon ta yace " da yaushe ki ka ga na kalli Sameer d'in ni fa Hajiya ba na son irin haka dama na san 'karshen abun nan sai mun yi fad'a kin ce a duba ta kuma na fad'a miki abin da ya ke damun ta kin ce 'karya na ke me yasa"?. "Dole na ce 'karya ka ke domin kai ma ka 6oye min da kai za'a had'u aci amana ta ba ka fad'a min gaskiya ba ciki ne da Zainab". "Ciki kuma Hajiya"?. "Eh ciki duba min watan sa nawa". "Ke d'in waye ya fad'a miki ciki ne da ita". "Ciki baya 6oyewa duk tsiya dole zai nuna kan sa idan lokaci ya yi ga shi nan ance amai ta ke ga zazza'bi kuma na ce ciki kai ma kana neman mayar dani 'karamar yarinya wacce ban san me na ke ba kubar gani na tsohuwa ban fara gigi ba har yanzu kalau na ke kuma ina ganin kowa tas kamar idon yara" d'an kamarin tsaki Abdul-Razza'k ya yi ya na cewa. "Wai Hajiya me ki ke yi haka ne a iya aman ta fa wannan zazza6in malaria ne ba ciki ba meyasa kike son 6atawa yarinyar nan suna ne wallahi ba abin da ya ke damun ta zazza'bi ne kawai ni ban ga komai ba haba dan Allah" nuna shi da yatsa Hajiya ta yi tana cewa. "Kai Abdul-Razza'k ka kiyaye ni ka fita ido na bana son fitsara irin ta 'ya'yan Asiya ko kai ma d'an uwan Zaidu ne"?. "Hajiya dole na fad'a miki gaskiya ko bakya so ni ba rashin kunya zan yi miki ba abin da na gani shi na fad'a miki Zainab ba cikin komai a jikin ta malaria ce kawai ya saka ta yalon amai amma idan ba ki yarda ba zanyi mata gwajin cikin"? Gyara zama Hajiya ta yi ta na cewa "da dai yafi amma wallahi ba zan ta'ba yarda ba ciki ne da ita ba sai na ga zahirin ba ta haihu ba yarinyar da ta ke yawo da samari masu gajerun wanduna da dare................... "Oh my God innalillahi wa inna ilaihi raji'un Hajiya ya isa haka dan Allah ki yi shiru wannan ba tsari ba ne tun da so ki ke kiga zahiri bari na zo" tashi ya yi ya fita Sameer ya na gefe a zaune ya tsume ran sa in yayi duba ya 6aci ji yake ba dan Hajiya mahaifiyar mahaifin sa bace da ace wata daban ta yi wannan maganar sai ya mata dukan mutuwa sai dai idan hukuma ta kama shi ayi masa d'aurin rai da rai amma saboda kar ya yi magana turirin da yake ran sa ya fito ya nuna 6acin ran sa a fili ga Asabe ta na gurin shi ya sa ya yi shiru kawai har Abdul-Razza'k ya dawo da wata 'yar siririyar roba me d'an jan murfi ya bai Zainab ya ce ta tashi ta je ta kawo masa fitsari ya gwada duk da Zainab tasan ba wanda ta ta'ba baiwa kanta ta yarda da kanta amma sai da taji zuciyarta ta hau dukan d'ari-d'ari da'kyar ta mi'ke jikin ta ya na rawa ta fita ta ga waje ma har lokacin 'yan matan gidan su na kofar sun yi tsit kowa jira ya ke yaji salatin Hajiya ko na Asabe cewa cikin ne da Zainab ganin ta fito ta yi hanyar band'aki yasa suka bi ta da kallo har ta fito ta zo ta sake wucewa ta kai masa komawa ta yi ta kwanta ta na addu'a a zuciyar ta Umma ma gabadaya ta rud'e PT Abdul-Razza'k ya d'auka ya d'an saka ya dagwalo ya d'ago shi ya zuba ido kafin ya ja tsaki me 'karfi ya na mi'kawa Sameer ya ce. "Kalli da idon ka, ka gani na rasa me ya ke damun 'yan gidan nan kamar rashin tarbiyya a kan su ta 'kare" kar'ba Sameer ya yi shi ma yaga dai layi d'aya PT d'in ya nuna ba layi biyu ba kai ya jinjina ya na cewa "Allah na gode maka d'an ba'kin ciki sai ya mutu duk wanda ya ke son ganin ba'kin cikin Zainab sai dai ya ci kan sa Allah ya fitar da ita daga zargi kuma sai Allah ya saka mata sharrin da akai 'yan ba'kin ciki kuma sai su yi tono su binne kan su alkaba'in da suke nema bai samu ba" kallon sa Hajiya ta yi tana cewa. "Uban wa yace maka ba'kin ciki ake mata uban me ku ka gani a jikin wannan d'an siririn abun munafikai har ku ke fad'awa mutane magana" mi'kewa Abdul-Razza'k ya yi yana cewa "ba kin ce a duba miki idan ta na da ciki ba? To bata da shi" ya na fad'in haka ya juya zai fita Hajiya ta ce "kai Abdul-Razza'ku ba na son 'karya ka fad'a min gaskiyar abin da ka gani". "Ai Hajiya gaskiyar abin da na gani na fad'a miki daga 'kin gaskiya kuma kowa ya san sai 6ata wallahi tallahi na rantse da Allah wanda ya halicce ni Zainab ba ta da ciki zazza'bin malaria ne ya kama ta sosai shi ya sa ku ka ga tana amai" sauke ajiyar zuciya Hajiya ta yi tana cewa "shikenan na yarda na san kana da hankali ba za ka min rantsuwa akan 'karya ba shi ya sa nasa aka kira ka amma da Samar ne ya fad'a min ba zan ta'ba yarda ba". "Humm Allah ya rufa asiri Allah ya shiryar da 6atacce" Abdul-Razza'k ya na fad'in haka ya fita daga d'akin cike da takaicin jin ba ciki ba ne malaria ce Asabe ta harari Umma wacce ke gefe ta na goge hawayen fuskarta kamar za ta ja tsaki amma saboda kar ace ta na daga cikin 'yan ba'kin cikin gidan yasa ta saki labulen dake ri'ke a hannun ta tun d'azu ta fice fuuuu daga d'akin su ma na wajen jin abun da Abdul-Razza'k d'in ya fad'a yasa d'aya bayan d'aya su ke mi'kewa su na fita kowa murna ta koma ciki. "Kin gani ko Hajiya kin ga irin abin da nake fad'a muku wai ana zuwa idan aka fad'a muku magana ba bincike sai ku hau ku zauna yanzu gashi kun zarge ta akan abin da bata aikata ba sai ku nemi yafiyar ta" Sameer ya yi maganar ya na tattare kayayyakin sa hararar sa Hajiya ta yi tana cewa "uban na nemi yafiyar ta dama ni ce nayi mata sharrin ina d'aki a zaune aka je akai kira na nazo kuma dan na sa an bincike ta meye abun laifi a nan har zan nemi wata yafiya"? Mi'kewa Sameer ya yi yana cewa "shikenan tun da ba ki ga abun neman yafiyar ba ni dana gani na fad'a miki amma tun da kin ce ke ba ki yi komai ba, ba damuwa" shi ma yana fad'in haka ya fita mi'kewa Hajiya ta yi ita ma zata fita ta kalli Umma ta na cewa. "Hauwa Allah ya rufa miki asiri yau da ace ciki ne da yarinyar nan daga ke har ita yau sai dai ku yi kwanan D'an Yana dan wallahi ba ku isa ta haifa mana shege a gida ba to amma tun da maleriya ce Allah ya kawo sau'ki" ta fad'a ta na shirin fita sai kuma ta juyo ta na kallon kwalin sweet dake can gefen Umma ta ce "Hauwa me ye a cikin nan"? Kallon kwalin Umma ta yi tana cewa.. "Chocolates ne a ciki da biscuits" dawowa ciki Hajiya ta yi tana cewa "chocolates da biscuits mi'ko min bibiyu" bud'ewa Umma ta yi ta d'ebo mata ta d'auko leda ta saka a ciki ta mi'ko mata kar6a Hajiya ta yi tana cewa "saura lemuka da pure water nima yau Allah ya rubuta zan ci arzikin duk da ran ku bai so ba bud'e ki d'ibo min tun da aka kawo mata firizar nan daga ke har ita ba ku ta'ba tunanin d'aukar wani abu ku kai min ba sai yau da rabo ya shigo da ni" Umma ba tayi magana ba duk dan a rabu lafiya nan ma ta sake tashi ta bud'e fridge d'in ta d'ebo mata kai Hajiya ta jinjina ta na cewa. "Ahh lallai kam ta yaya Zainab za ta yi aure bayan ba ta rasa komai ba ga sana'o'i ga kuma wadannan gatan da take samu daga aljanin ta tun da nasan da mutum ne yake bata wadannan abubuwan da yanzu ya bayyana mata kan sa Allah yasa ba ba'kin aljani ne ya aure ta ba kar ya hana ta aure" ta fad'a ta na zaro alawa d'aya ta 6are ta saka a baki ta na cewa "garin dad'i ba kusa ba ana shan irin wannan dad'in a gidan nan amma ban sani ba humm! Na gode ni zan tafi Allah ya sauwake zan dawo anjima na sake duba ki lokacin na shanye alawar sai na 'kara kar6ar wata tun da na gani ai na daina barin ku, ku huta" ita dai Umma tari da bai kamata ba ba ta yi ba har Hajiya ta bar 'kofar ta na fita Asabe ta bankad'o labule ta koma d'akin ta na kallon Umma ta ce. "Na san 'karya Sameer da Abdul-Razza'k su ke yi da suka ce Zainab ba ta da ciki dan su kare ta ne amma ai duk inda cikin gaskiya ya ke baya 6uya mu nan mu na zuba ido duk wani motsin ku muna hankalce da shi duk ranar da na ga Zainab ta fita daga gidan nan ko biyu bana rabawa asibiti ki ka tura ta taje a zubar da cikin humm ga sakamakon kwad'ayi nan kun fara gani in dai nadama ce ba ku fara shiga ba sai nan gaba ma aure dama ba ku so ta yi ba kuma ba za ta ta'ba yi ba" ta na fad'in haka ta juya ta fita kai Umma ta girgiza ta na cewa "bakin ki ya fad'i a 'kasa in sha Allahu Zainab za ta yi aure duk daren dad'ewa" ta fad'a ta na sake jan bargo ta lullu'be ta kafin ta koma ta zauna ta yi shiru ta na kallon ta cike da tausaya mata kullum addu'ar ta Ubangiji ya ba ta miji na gari wanda zai ri'ke ta tamkar 'yar da ya haifa ya nuna mata gata domin wannan damuwar da ta sha ta gushe fatan ta Allah ya sa kafin ta bar gidan nan kar ba'kin ciki ya saka ta kamu da hawan jini. 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YUSRAH MUSA PAGE 55 Koda lokacin tafiya islamiyya ya yi ma bata samu lokaci ba sakamakon zazza'bin bai sauka ba waje Umma ta fito mata da shimfid'a ta kwanta a 'kofar d'akin ta tana nan a kwance ganin Bilki ta fito daga d'aki da shirin islamiyya ya sa Zainab tashi zaune tana jingina da jikin bango ta ce. "Bilkisu islamiyya za ki je"? Jin abin da tace ya sa Bilki hararar ta tana cewa "a'a gidan rawa zan je" numfashi Zainab ta sauke sakamakon jin irin amsar da ta bata da har za ta 'kyale sai kuma ta ce "dan Allah idan kin je ki fad'awa Yaa Sayyidi ba ni da lafiya" taki Bilki ta ta'be tana cewa "wallahi ba zan fad'a ba ina ruwa na da wani Yaa Sayyidi" ta fad'a ta na shirin fita da kallo Zainab ta bita tana cewa. "Bilkisu yanzu ba za ki fad'a masa ba ni da lafiya ba"? Kai ta jinjina tana cewa "eh ba zan fad'a ba sai akai ya"? Shiru Zainab ta yi ba ta sake magana ba tsaki Bilki ta ja ta na ficewa tana fita Asabe ta fito daga d'aki ta kai kwanuka gurin wankewa sannan ta juyo tana zuwa kan Zainab ta tsaya tare da kallon ta tace "ke a tunanin ki Bilkisu 'yar aiken ki ce? Tsabar rainin hankali ita ce za ta fad'awa wani Yaa Sayyidi ba ki da lafiya? Ai da tace za ta fad'a masa na fito sai na yi mata dukan ala tsine a gidan nan yadda ba ki d'auke ta 'kanwa a gidan nan ba har abada ba za ta yi miki kallon yaya ba ai ba ita kad'ai ce take zuwa islamiyya a gidan nan ba da za ki ba ta wani banzan sa'kon ki uban wa ya hana ki zuwa ai ba zazza'bin gaskiya ki ke ba wannan zazza6in na ciki ne kuma in sha Allahu sai kin haife shi" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin Zainab kam dama tun da ta fara magana kan ta yake 'kasa har ta gama ta juya kuwa ba ta d'ago ba domin ta tabbata ko Umma da ta na nan ba za ta tankawa Asaben ba balle ita da ta ke matsayin 'yar cikin ta kuma ko ba haka bama yadda Sameer ya ke son ta ya ke kula da ita bai kamata ace ta na yiwa Asabe rashin kunya ba duk ranar daya shigo ya tarar da hakan ba zai dad'i ba wannan dalilin ya sa ko Asabe za ta rufe ta da duka ba za tace ma ta komai ba.................. Kiran wayar ta da akai ta mayar da hankalin ta gurin Sameer ne d'agawa ta yi tana cewa "assalamu-alaikum Yaya Sameer ina yini"? Jin ta ambaci Sameer ya sa Asabe daina wanke-wanken da ta ke ta tsaya tare da juyowa ta na kallon ta, ta ji me za tace Zainab kam hankalin ta ba'a kan Asaben ya ke ba balle ta san me ya ke faruwa kawai da Sameer ya ce mata ya jiki ta ce. "Da sau'ki". "Zazza'bin ya sauka ko har yanzu da saura"?. "A'a ya sauka ba zafin jikin sai juwa da na ke ji idan na mi'ke tsaye". "Ba ki ci abinci bane"?. "Eh". "Me ya sa to ba'a yi bane"?. "An yi shinkafa ce da wake salad ne babu shi ya sa ban ci ba" jin abin da ta ce ya sa yace "ok ina zuwa" ya na fad'in haka ya katse aje wayar Zainab ta yi Asabe da ta gama wanke kwanukan ta na shirin barin gurin ta ce "to munafika gadon 'karya da sharri inji uban waye ya ce ba'a siyo salad ba har ki ka fad'a masa kodan dama 'karya abincin ki ce" shiru Zainab ta yi ba tai magana ba Asabe data shiga kitchen ta d'auko salad a leda ta wurgo mata ta na cewa "kin ce masa ba salad saboda ga gidan fatararru yanzu wannan uban meye a ledar inace uwar ki ce ta yi abinci da shi jiya tsabar ba'kin hali ta'ki yanka shi yadda zai isa ta 6oye kuma gashi asirin ta ya tonu har salad d'in ya fara zama yellow ba ta d'auke ba" tafa hannu Asabe ta yi tana cewa "kai jama'a gaskiya akwai azzalumai a gidan nan ni dai ana zalunta ta ba abin da zan ce sai Allah ya saka min daga ke har uwar taki idan an gan ku shiru-shiru ba'a san lunbu-lunbu ne ba uwar 'kai'kayi sai mutum ya zauna da ku zai ga sharruka iri-iri gashi a haka gani ake kamar ni ce na ke cutar ku saboda ni ina da baki hummm kowanne shege haka nan zai gan ni ya, barni dan na zama ciwon ido zama da ni sai ha'kuri" ta fad'a tana komawa cikin kitchen d'in ita dai Zainab har lokacin ko tari ba ta yi ba sai dai ta ji mamakin ya akai da salad d'in amma ba'a yanka ba ai duk zaton ta babu shi ya sa ta'ki cin abincin da ta san da akwai koda kan ta za ta iya yankawa tun da Umman ba ta nan sallama Sameer ya yi yana shigowa ya zo ya aje leda a kusa da ita sannan ya shiga kitchen Asabe ta na tsaye ya gaida ita ba ta amsa ba sai tambaya da ta jefo masa ganin ya d'auki plate da wu'ka da cokali tace. "Kai uban me za ka yi da su"?. "Zan yankawa Zainab salad ne ta ci abinci". "Humm dama na san sai dai Zainab d'in da nice nake jinyar nan Sameer ko kallo na ba za ka yi ba amma da ya ke Zainab 'kanwar uwar ka ce daga tace maka ba za ta ci abinci idan ba salad ba shine har ka rarumo ru'kui-ru'kui jiki na rawa ta kawo mata kuma hakan bai isa ba saboda ta mayar da kai bawan ta sai ka yanka mata" kallon ta Sameer ya yi yana cewa. "Umma wannan fa duk ba abun fad'a ba ne dan na kyautatawa 'yar uwa ta". "Sannu me 'yar uwa sakaran banza da an yi magana ka ce 'yar uwar ka zan ga tsiyar da za ta tsinana maka nan gaba da ka nace sai ita aikin banza kawai" juyawa ta yi ta bar gurin Sameer dai bai sake magana ba ya yanka mata salad d'in ya d'ebo gishiri kad'an ya wanke mata ya yanka mata cocumber tumatur da albasa ya aje mata ledar da ya shigo da ita ya bud'e ya d'auko wani 'katon kifi a ciki ya 6are shi ya fitar mata da 'kayar sannan ya zuba mata abincin ya shiga d'akin ta ya d'auko mata pure water a fridge ya kawo mata tare da zama a gefen shimfid'ar ya na cewa. "Ki ci man ki ka tsaya ki na kallon abincin"? Kai ta d'an girgiza ta na cewa "ba zan iya ci ba" da mamaki Sameer ya ce "ba za ki iya ce ba kuma"? Nan ma kai ta sake d'agawa ta na d'an zamewa daga zaunen da take zata kwanta ganin haka ya sa Sameer cewa. "A'a la'asar ta yi koma ki zauna kar ki kwanta rana ta yi 'kasa" d'agowa ta yi ta dawo zaune yadda ta ke duk da ta na son kwanciyar abincin Sameer ya gauraya mata cikin kulawa da lallami na mara lafiya ya soma ba ta ya na cewa "kin ga ki d'an kar6a ki ci ko loma d'aya ce" idan yaga ta kar6a sai ya sake d'ebowa ya ce "yauwa 'kara d'aya" da haka kamar da wasa har ta ci da yawa ya bata pure water ta sha murmushi ya yi yana kallon ta ya ce. "Yauwa to alhamdulillah" mi'kewa ya yi ya na cewa "idan an jima ki d'auki d'ayan kifin da ya ke ledar ki cinye shi kafin na shigo bari na koma na baro chemist d'in a bud'e" kai ta d'aga a hankali ta ce "na gode Yaya Sameer Allah ya saka da mafificin alkhairi" "Amin ya ce ya na fita daga 'kofar ta su Asabe da ta yi shiru ta na kallon su ganin ya fita ya sa ta taso da gudu ta na zuwa ta yi wuff kamar shaho ta d'auke ledar kifin ta na hararar Zainab ta ce. "Mayya ba ni wato bayan wanda ki ka ci harda saura ya rage miki zuwa jimawa ki ci, humm ni dai wannan abu ya na ba'kanta min zuciya amma ba komai in dai asiri ku kai masa zan je awarware daga ranar asirin munafiki zai tonu" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin ta shige d'akin ta numfashi Zainab ta sau'ke tare da rufe ido kawai ta yi shiru kamar me barci............................... ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA PAGE 56 Ganin da Afifah ta yi Zainab ba ta je islamiyya ba har aka tashi shi ya sa da taga tawagar su Bilki za su tafi gida ta tare su ta na cewa "am dan Allah yau ya akai Zainab ba ta zo islamiyya ba"? Dukkan su Bilki su ke kallo ganin ta'ki magana ya sa Rasheedat cewa "sai dai ki tambayi Bilki ita ce 'kofar su d'aya" jin abin da Rasheedat ta ce ya sa Bilki zafga mata harara ta na cewa "ni ma ban san dalilin ta na 'kin zuwan ba". "Ok ba ta gidan ne ko ta yi tafiya"? Afifah ta sake tambaya kai Zakiyyah ta girgiza ta na cewa "in dai ba d'azu ta tafi ba gaskiya Zainab ta na nan da yake bata da lafiya tun safe ta ke amai ina ga shi yasa ba ta zo ba" d'an zaro ido Afifah ta yi ta na cewa "Subanallahi wayyo Aunty Zee-Zee dama ba ta da lafiya? Allah sarki Zainab d'ina shi ya sa na yita kiran ta a waya na ji a rufe ashe ita ta kan ta, ta ke yi bari na wuce na dubo ta" jin abin da Afifan ta ce ya sa suka fara kallon kallo tsakaninsu su na ta6e baki Bilki kuwa ji ta yi kamar ta d'auke Afifah da mari tsabar takaicin yadda ta damu da Zainab d'in, tare su ka shiga gidan Bilki da Afifah su ka wuce can 'kofar har lokacin Zainab ta na waje ba ta koma d'aki ba Abba ya na kusa da ita ya na mata sannu dawowar sa kenan daga gurin sana'ar sa ko d'aki bai shiga ba ganin ta yi ba'kuwa ya sa ya mi'ke dur'kusawa Afifah ta yi ta gaida shi ya amsa ya na nufar 'kofar d'akin sa zama Afifah ta yi tana kallon ta ta ce. "Sannu Aunty Zeey ya jikin na ki"? D'aga kai Zainab ta yi ta na cewa "da sau'ki Afifah", "Allah ya 'kara lafiya ashe tun safe ba ki da lafiya ban sani sai yanzu da mu ka taho na ke tambayar 'yan gidan nan suka ce min tun safe ki na kwance har da amai ki ke". "Uhm zazza'bi ne". "Yaya Sameer ya duba ki"?"eh tun safen ya duba ni na samu sau'ki ba kamar d'azu da ko zama gagara ta ya yi ba" zaro ido waje Afifah tai ta na cewa "zama ya gagare ki? Caf Allah ya rufa asiri Allah ya kawo sauki". "Amin" Umma ce ta fito daga d'aki ta na cewa "Afifah ashe ke ce ki ka zo"?. "Ni ce Umma ina yini"? "Lafiya kalau ya mutan gidan na ku"?. "Lafiya kalau su ke ya me jikin"?. "Ga ta nan da sauki". "Allah ya 'kara sau'ki" "Amin an gode sosai Allah ya yi albarka" Umma ta fad'a ta na wucewa ta d'auki buta za ta yi alwalar sallar magriba kallon Zainab Afifah tai ta na mi'kewa ta ce "Aunty Zee bari na tafi kin ji an fara kiran sallah" kai Zainab ta d'aga ta na cewa "to Afifah na gode ki gaida Momy"?. "To in sha Allahu za ta ji sai da safe" ta fad'a ta na fita bayan Umma ta yi alwalar dawowa gurin ta ta yi tana cewa "zaki iya tashi ki yi alwalar ne"? "Eh zan iya" ta fad'a ta na tashi tsaye duk da har lokacin ba ta jin 'karfin jikin ta ko kad'an shimfid'ar Umma ta d'auke ta mayar mata d'aki sannan ta fito ta shiga na ta ita kuma Zainab ta yo alwalar ta zo ta shiga za ta yi sallar. Afifah ta na komawa gida ta tarar da Momy a parlor ta na zaman jiran dawowar ta ganin ta shigo ya sa Momy kallon ta tana cewa "Afifah a ina ki ka tsaye ne sai yanzu ki ka shigo gida har an fito daga masallaci bayan ba ki saba yin hakan ba"? Kai Afifah ta d'aga ta na cewa "tun lokacin da aka taso na taho Momy na wuce gidan su Zainab na dubo ta ne". "Ba ta da lafiya"?. "Eh ashe tun safe ta ke zazza'bin ni ban sani ba da yake na kira wayar ta a kashe na d'auka ba ta da caji ne ashe ba ta jin dad'i ma ita". "Ayya Allah ya sauwake idan na samu lokaci ko gobe ne zan je har gida na duba ta Allah ba ta lafiya". "Amin" Afifah ta ce tana wucewa part d'in su Momy ma tashi ta yi ta koma na ta dama dalilin fitowar da ta yi rashin ganin shigowar Afifan a lokacin da ta saba ne amma tun da ta dawo kuma ta ji inda ta je ba matsala. Da yake tun da daren da Zainab su kai waya da Aunty Murjah ta fad'a mata ba ta da lafiya shi ya sa washe gari da safe wajen 'karfe goma da rabi na safe ta sake kiran ta, ta duba ta sannan ta ce mata da dare za su shigo tare da Auwal su sake duba ta Afifah ma ta sake shigowa da safen kafin ta tafi school ta duba ta harda Fati da Elham su ka zo da kayan dubiya. Sakamakon shi ma Yaa Sayyidi bai san ba ta da lafiyar ba a jiyan ya ga yau ma still ba ta le'ko islamiyyar ba shi ya sa ya tambayi Afifah ko lafiya ta fad'a masa ai ba ta jin dad'i ne tun daren shekaran jiya sosai ya yi kewar rashin zuwan ta musamman ajin da ta ke d'auka dole jiya da yau duk shi ya ke shiga mu su.............. ZUCIYAR ALIYU CE STORY WRITTEN ND EDITING YUSRAH MUSA ABUBAKAR✨ @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 57 POV. YAA SAYYIDI Da ya koma gida bayan sallar magriba ya shigo anguwar ta su amma a d'an nesa da gidan ya tsaya saboda haske kiran ta ya yi a waya ta fito ya duba ta ba ta ta'ba tunanin zai zo har gida ba ta d'auka tun da ya kira ta d'azu shikenan idan gobe ta koma islamiyyar ya duba ta. A lokacin ta na kan sallaya ta yi sallah kenan ya yi kiran ta, tashi ta yi ta d'auki Nikaf ta d'aura ta shiga d'akin Umma ta sanar mata sannan ta fita had'uwa su kai da Sameer da mamaki ya kalle ta ya na cewa "Zainab ina zuwa haka ke da ba ki da lafiya"? Numfashi ta sauke a hankali ta ce "Yaa Sayyidi ne ya kira ni a waya ya ce na fito ya na waje ya zo duba ni" jin abin da ta ce ya sa Sameer ya kalle ta da sauri cike da mamaki ya ce. "Wai Yaa Sayyidin dama har yanzu bai daina zuwa gurin ki ba"? Kai ta d'aga ta na cewa "eh ya na zuwa amma ba koda yaushe ba sai lokaci zuwa lokaci" 'kak'karfan numfashi Sameer ya sauke ya na kallon ta ya ce "tabd'ijan amma akwai............... Koda shikenan je ki kawai idan kin dawo gida sai mu yi maganar kar na tsayar da ke shi kuma ya na jiran ki ba damuwa je ki kawai" ya fad'a ya na wucewa shiru Zainab ta yi a ran ta, ta na cewa "tabbas akwai abin da Yaya Sameer ya hango min wanda ni ban gano ba amma bari idan na dawo zan tambaye shi" bud'e 'kofa ta yi ta fita a inda ya saba tsayawa idan ya zo anan ta same shi yasha wankan jallabiyya shi yasa mutumin nan ya ke burge ta kuma ta ke jin cewa za ta iya auren sa ko mata uku ne da shi ta shiga gidan matsayin ta hud'u ta amince sallama ta yi su ka gaisa ya kalle ta shi ma cike da burgewa ko'ina a rufe ya ce. "Fatan kin samu sau'ki ko ashe ba ki ji dad'i ba"?. "Wallahi ban ji dad'i ba jiya a kwance na wuni shi ya sa ban samu na shigo islamiyya ba yau ma kuma na tashi babu 'karfin jiki shi ya sa ban zo ba na bari sai gobe". "To Allah ya kai mu ai haka Afifah Ahmad ta ke fad'a min yau da na tambaye ta ki na ina na san dama ba za ki ta'ba yin tafiya ba ki fad'a min ba". "Ba tafiya na yi ba zazza'bi ne ya same ni". "Shikenan ba damuwa Allah ya 'kara lafiya dama kawai cewa na yi bari na shigo na duba ki daga nan sai na je gurin wani malami da ya ke bayan layin ku mu gaisa da shi ga wannan" ya 'karasa maganar ya na d'auko ba'kar ledar da ke gefen sa ya mi'ko mata kai ta girgiza ta na cewa "lah a'a ka barshi ba komai iya duba ni da ka zo ka yi ma na ji dad'i sosai". "A'a ki kar'ba ai niyya na yi ba saka ni ki kai ba sannan kin san ba kyau mai da hannun kyauta baya ko"? Shiru ta yi ya ci gaba "dan Allah Zainab ki kar'ba na tafi" ya fad'a ya na sake mi'ko mata da'kyar ta saka hannu ta d'an risina ta kar6a ba don ran ta ya so ba sai dai dan kawai ba ta son musu. "Na gode sosai Yaa Sayyidi Allah ya saka da alkhairi". "Amin ba damuwa sai da safe na tafi" ya na fad'in haka ya juya ya tafi ita kuma ta shiga gida ba ta samu Sameer ba domin har ya gama abin da zai yi a lokacin ya fita d'aki ta koma ta jira sallar isha lokacin ta ya 'karaso ta yi sannan ta d'an kwanta kafin su Aunty Murjah su zo kwanciyar ta ke da wuya barci ya fara d'aukar ta, ta ji sallamar su tashi zaune ta yi ta na kallon kofar shigowa d'akin ta gani ta yi an bud'o labule Ikram ta shigo da murnar ta, ta zo ta zauna a kusa da ita ta na cewa. "Aunty Zainab ina wuni"? Murmushi Zainab ta yi tana d'aukar ta, ta d'ora ta akan cinya ta ce "lafiya kalau Ikiki na ina ki ka bar Daddyn ki"? D'aga yatsa ta yi ta na cewa "a can"?. "A can gida ku ka baro shi"? Ikram na wasa da kayan 'kyallayen d'inki ta ce "eh Aunty Zainab za ki d'inkawa baby na kayan ta"?. "Aw Baby ce da ke"?. "Eh Daddy ne ya siyo min". "Lallai Daddyn nan na ki ya na son ki to ina Momyn na ki"?. "Ta na d'akin Umman ta" d'an zaro ido Zainab ta yi tana kallon ta tace "ke ba Umman ki ba ce"? "Eh ni Momy ce Momy na" kai Zainab ta jinjina ta na d'auko biscuit mi'ka mata daidai Aunty Murjah ta shigo da sallama ganin ta a zaune yasa ta ce "ahh masha Allah ashe kin samu lafiya"? Ta fad'a ta na zama kusa da ita ta ce "sannu ya jikin"? Murmushi Zainab ta yi tana kallon ta tace. "Da sauki ina yini"?. "Lafiya kalau ya 'karfin jikin"?. "Na samu lafiya wai ku kad'ai ku ka zo ban da Abban Ikram"? Kai Aunty Murjah ta girgiza ta na cewa "tare mu ka zo man" "Kai amma Ikki ta ce min iya ku ne"?. "A'a ba mu kad'ai ba ne ya na gurin Abban mu" mi'kewa Zainab ta yi tana d'aukar mayafi ta ce "bari na je mu gaisa da shi" tashi Aunty Murjah ta yi tana cewa "mu je ina son za mu gaisa da Hajiya" kallon ta Zainab ta yi kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa su ka fita ganin takalman Auwal a 'kofar d'akin Abban su ya sa ta fahimci har lokacin ya na d'akin waje su ka nufa Aunty Murjah ta shiga 'kofar Hajiya ita kuma ta tsaya tare da Ikram har Auwal ya fito Aunty Murjah ta na ciki 'karasowa inda Zainab ta ke ya yi yana cewa. "Sannu 'yar 'kanwa ta ashe ba ki da lafiya ai ban sani ba sai da na dawo princess ta ke fad'a min kuma gashi ke da baki da lafiya amma ki ka fito rakiya"? D'an murmushi Zainab ta yi daidai Aunty Murjah ta fito ta ce "ai da ya ke zazza'bin dare na yi daga shekaran jiya zuwa yau ne". "Allah ya kawo sau'ki ko dan ya kawo ma tun da gashi kin ware" kallon Aunty Murjah ya yi yana cewa "mu je dare ya na dad'a yi" kai ta d'aga su na fita a lokacin Ikram ta na kafad'ar Zainab ta yi barci jikin motar su ka zo Aunty Murjah ta bud'e baya ta shiga da mamaki Zainab ta kalle ta za ta yi magana ta ga an bud'e murfin gaban motar an fito zaro ido ta yi tare da d'auke numfashi ganin da wanda su ka zo............... Ya na ri'ke da murfin motar ya kalle ta da murmushi ya ce "barka da dare malama Zainab ya jikin na ki"? Har lokacin numfashin ta bai dawo daidai ba da'kyar ta iya ce wa. "Da sau'ki". "Masha Allah Ubangiji ya 'kara afuwa". "Amin na gode". "Na so ace mun d'an samu zama ni da ke mu tattauna amma ba lokaci sai dai idan na ji ni free zan sake dawowa in sha Allahu sai mu yi magana ko"?. "To" ta sake cewa muryar ta bai fita sosai kai ya jinjina yana komawa cikin motar ya zauna murmushi Aunty Murjah ta yi tana kallon ta tare da mi'ko hannu ta ce "kawo ta mu tafi" kai Zainab ta girgiza ta na d'an 6ata fuska ta ce "Aunty Murjah dan Allah ki bar Ikram a nan tun da gobe asabar ce ba school jibi zan kawo mi ki ita har gida da kai na Yaya Sameer ne zai rako ni". "Ai kuma akwai islamiyya"? Zainab za ta yi magana Sameer ya karaso gurin sakamakon ba ya nan su ka zo fitowa Auwal ya yi yana bashi hannu suka gaisa cikin tsokana ya ce. "A'a me gida Alhaji Sameer kana sha'anin ka sai yaushe za mu zo biki ne ko ba rana"? Dariya Sameer ya yi yana cewa "wanne biki amma ba nawa ba"?. "Na ka mana yaushe ne"?. "Tab ba rana ni da ko gini ban fara ba ka ga ina batun aure a gu na"? Da mamaki Auwal ya ce "kai haba dai"?. "Wallahi da gaske ne ke maka iya fili na ke da shi sai daga baya zan fara aikin sa" kai Auwal ya jinjina ya na cewa "ok Allah ya taimaka Allah ya kai mu lokacin". "Amin na gode" ya fad'a ya na juyawa inda Zainab ta ke tsaye ya ce "ya jikin na ki gaskiya ke 'yar gata ce sai zuwa duba ki ake uhm mu je a bani nawa abun dubiyar na san ya nan a d'aki jibgi-jibgi" dariya Aunty Murjah ta yi ta na cewa "tabbas ya na nan lodi-lodi ku je ka kar'bi rabon ka". "Hum ki ji fa har albishir ake min please Zainab mu je dan Allah" ita kuma Aunty Murjah ta ke kallo tare da cewa "to Aunty Murjah dan Allah na tafi da ita kwana biyu kawai kin ga fa ta yi barci"? Tun kafin Aunty Murjah ta yi magana Auwal ya ce "ba damuwa je ki da ita". "Yauwa Yaya na gode in sha Allahu jibi da kai na zan kawo ta sai da safe Yaya Sameer mu je ku gaida gida" ta na fad'in haka ta juya su ka shiga gida tare da Sameer saboda ya kar'bi Ikram tun da ta yi barci kuma Zainab d'in ba lafiya ce da ita ba har d'aki ya shiga ya kwantar da ita ganin dare ya d'an fara yi yasa daya fito ya d'auki bokitin da zai yi wanka ya fita daga 'kofar ta su. Sosai Zainab ta sha mamakin ganin babbar leda a ajiye a kusa da katifar ta kenan Aunty Murjah ce ta shigo da ita d'aukowa ta yi ta na shirin bud'ewa ta duba sai kuma ta ga kiran Aunty Murjan ya shigo d'agawa ta yi ta na cewa "hello Aunty Murjah wannan ledar ke ce ki ka shigo da ita"?. "Eh ni ce dama na manta ban fad'a miki ba shi ya sa na kira ki duba ledar nan za ki gan ta a d'akin ki kayan 'karamar ledar na mu ne na babbar kuma na masoyin ki ne Mukhtar" ta na fad'in haka ta yi dariya tare da kashe wayar dan ta san in ba haka ta yi ba sai ta yi mata 'korafi shiru Zainab ta yi hankalin ta a tashe ta kasa saka hannu ma ta bud'e ledar balle ta ga abin da ya ke ciki matsawa ta yi daga gurin ta koma kan katifa ta cirewa Ikram kayan ta sannan ta gyara mata kwanciya kafin ta tashi ta fita daga d'akin..................... 💓 ZÜÇÏYÄR ÄLÏYÜ ÇË💓 ♣Y♠ü♥s♣r♠ä♥h♣ ♣M♠ü♥s♣ä♣ ♣Ä♠b♥ü♣b♠ä♥k♣ä♠r♥. @YUSRAH MUSA ₱AGE 58 Washe garin ranar asabar da yake ba school za ta je ba islamiyya ce shiyasa ta dafa ruwa da wuri ta yiwa Ikram wanka ga shi ba'a zo mata da kaya ba dad'in abun ma akwai irin wanda idan sun zo su ke barin sa shi ta birkito a cikin kayan ta, ta saka ma ta. Su na d'aki Momy ta shiga tare da Husnah ta yi sallama Umma dake waje ta na shara ganin wacce ta shigo ya sa ta mi'ke tsaye cike da mamaki ta ce "a'a Hajiya Barakah ke ce a gidan na mu yau da kan ki"? Murmushi Momy ta yi tana cewa "wallahi ni ce ai dole in zo na duba 'yata ta na ina"? Aje tsintsiyar Umma ta yi tana cewa "bismilllah 'karaso" shiga d'akin Umma ta yi suka gaisa ta na cewa. "Ya mai jikin kuma ai jiya ina ta jiran Afifah na ga ba ta koma gida da wuri ba ashe nan ta zo duba ta fatan ta warware"? Kai Umma ta d'aga tana cewa "alhamdulillah jikin ta ya yi sau'ki sosai ya kwanan yaran". "Masha Allah haka ake so yara su na lafiya ta na ina yanzu"?. "Ta na d'akin ta tare da Ikram" mi'kewa Momy ta yi tana cewa "ok bari na je na duba ta Husnah tashi mu je" fita su kai Umma ta bud'e labulen 'kofar d'akin Zainab ta na cewa "Zainab ki na ciki ne ga Maman Afifah ta zo duba ki" sakin labulen Umma ta yi tana cewa "bismilllah Hajiya Barakah ki shiga ta na nan" komawa Umma ta yi ta ci gaba da shara Momy kuma ta shiga d'akin Zainab da 'yar fara'a Zainab ta ce. "Lah Momy ke ce sannu da zuwa" ta fad'a tana tashi ta d'auko sallaya ta shimfid'a mata zama Momy ta yi bayan sun gaisa ta ce "ya jikin na ki da sau'ki ko"? Kai ta d'aga ta na cewa "eh na samu sau'ki ina kwana"?. "Lafiya 'kalau Zainab Allah ya 'karo miki lafiya kin ji". "Amin Momy na gode" ta fad'a ta na ri'ko hannun Husnah ta ce "Husnah har da ke aka zo ina su Elham da Fati"?. "Su na gida Aunty Zainab ya jikin"? "Jiki alhamdulillah Husnah da sauki" mi'kewa Momy ta yi tana cewa "Auta tashi mu je" tashi Husnah ta yi su ka fita daga d'akin a lokacin har Umma ta gama sharar da ta ke yi ganin su ya sa ta ce "kun fito"?. "Eh za mu tafi Allah ya sauwake". "Amin Hajiya mun gode Allah ya saka da alkhairi". "A'a ba komai Zainab ai 'ya ta ce dan na zo duba ta dad'i na ji yara su na yabon ta sosai kuma su na matu'kar jin dad'in karatun ta a islamiyya kullum sai sun fad'a shi ya sa ni ma har ta shiga rai na sosai" murmushi Umma ta yi cikin jin dad'i daidai Momy ta juya za su fita a 'kofar ta ce "sai anjima a sake yi mata sannu idan ta fito". "To in sha Allahu Hajiya mun gode Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a ta na shirin shiga d'aki Asabe ta fito tana kallon ta tace "oh! Ni 'yasu na shiga d'aka ni jikar mutum hud'u anya Hauwa ki na neman zaman lafiya kuwa ashe asirin naki har ya bar kan mu 'yan gida ya koma kan masu kud'in anguwar nan meye had'in biri da gada ki fad'a min in dai ba sharrin asiri ba ko a mafarki wannan matar ba za ta tako gidan nan ba balle har ta yi magana da ke ta na matsayin matar minister ke kuma matar me siyar da kayan miya da gawayi" juyawa Umma ta yi tana kallon ta jin abin da ta ce ya sa ta girgiza kai cikin takaici ta ce. "Ai ke Asabe na dad'e da jingine ki a gefe duk wani abu da zaki fad'a a kai na ko 'ya ta sai dai na kalle ki da ido" a masife Asabe ta ce "yo ai dole kin kalle ni da ido man tun da kin gama dani kin cuce ni kin raba ni da miji na kin raba ni da d'ana bani da ma'kiyiya sama da ke a duniya duk wani ma'kiyi na sai dai ya biyo bayan ki" numfashi Umma ta sau'ke tana cewa. "Allah ya kyauta sannan Allah ya tsare ni da wadannan mugayen abubuwan da kike siffata ni da shi ban kasance mai aikata shirka ba ban ta'ba zuwa gurin malami ba balle boka sharrin da kike min idan ban yafe miki ba sai Allah ya saka mun" Umma na rufe baki Asabe ta yaryara gud'a mai zafi ta na cewa "ahayyye ayuririiiiiiiii ji ba'kin munafirci da baki aikata ba zan fad'a ne? Dad'in abun ma kin yi kuma dole na fad'a ko zaki mutu Allah ya sauwake na yi wa tsogalgalar mace sharri irin ki ni zuciya d'aya nake zaune da ke kece kike nufi na da sharri kuma sai dai ya koma kan ki" ta fad'a ta na tofar da yawu ganin da Umma ta yi kawai Asabe neman ta take da fad'a ita kuma ba za ta biye mata ba sai kawai ta ce "ki fad'i komai ki zauna lafiya domin ni ba zan kula ki ba amma zan ro'ki Allah ya fitar da me gaskiya tsakanin mu" ta6e baki Asabe ta yi tana cewa "ai kuma ni ce me gaskiyar ke wacce gaskiya ki ke da ita 'yar d'an Yana". "Kan ki ake ji". "Ke ma ana jin naki kan shi yasa na ga 'yar ki ta'ki auruwa saboda kowa yana gudun d'iban annoba ya kai gidan sa kar a mallake shi da asiri". "Ki fad'i komai Asabe ba zan tanka miki ba Allah ya fiki" ta na fad'in haka ta wuce d'aki ita ma Asaben ba ta sake magana ba ta ci gaba da aikin had'a kayan karyawar da ta ke yi da gudu Ikram ta d'auko kofi ta yo waje duk kiran da Zainab ke mata ba ta koma ba har 'kofar d'aki ta biyo ta tana cewa "Ikram ke Iki ina za ki je dawo min da kofin nan" Ikram ba juya ba gurin Asabe ta zo tana mi'ka mata tace "a zuba min shayi na" d'agowa Asabe tayi tana kallon ta tare da fisge kofin ta yi jifa dashi tana cewa "to 'yar gidan maciya bamu da shayi a gidan nan ban dafa ba matsa ki ban guri 'yar gadararru harda wani a zuba miki shayin ki uban shayin ki za'a zuba miki Auwal ya siyo Lipton din ya kawo ne"? Shiru Ikram ta yi ta zubawa Asabe ido wanda ya sa Asabe cewa. "Mayya ko cinye ni za ki yi naga ki na yi min irin wannan tsinannan kallon"? Jin abun da Asaben ta ke fad'a akan yarinyar da bata fi shekara hud'u ba ya sa Zainab fitowa ta tsaya daga wajen 'kofar d'akin ta tace "Ikram zo nan". Hararar ta Asabe ta yi tana cewa "eh tazo nan d'in domin ko wuni za ta yi anan bazan bata wannan shayin ba saina gama had'a komai na baku rabon ku idan kuma wuta ce a cikin tama saidai ta cinye ta 'yan masu da gadara haka kawai da gidan uban ta tsabar son a sani ku ka kar'be ta wallahi kun kar6i banza ba zan ta'ba raba abinci da ita ba har tabar gidan nan yadda nake zuba muku haka zan zuba ba ruwa na da wata yarinya idan kun ji haushi ku mayar da ita gidan uban ta" ita dai Zainab ko tari ba ta yi ba ta d'auke Ikram daga gurin suka koma d'aki ta zaunar da ita ta d'auki biscuit ta 6are ta bata kar6a ta yi tana ci ganin haka yasa ta d'auko mata buredi ma ta aje mata a gefe sannan ta d'auki indomie guda d'aya ta fita zata dafo mata ganin abin da za ta yi yasa Asabe ta6e baki ta na cewa. "Eh da hakan ku kai dai yafi domin shi kansa mai gidan ko biyar bai dad'a a kud'in abinci ba yadda ya ke bayarwa haka ya bada balle kuce ya had'a da nata kud'in harta bar gidan nan ni dai bazan ta'ba raba abinci da ita ba idan kun ga taci sai dai ranar girkin munafikar kakar ta" sosai takaici ya rufe Zainab amma har lokacin bata yi magana ba shigowa Sameer ya yi yana waya ganin Zainab d'in a waje ya sa yayi wajen inda take ya na cewa. "Eh a'a kar ka kashe na shigo ga ta nan bari na ba ta" mi'ka mata ya yi yana cewa "kar'bi za'a duba ki" har zata tsaya tambayar waye sai kuma ta fasa ta kara a kunne tare da yin sallama ya na dafe da saitin zuciyar sa ya na jin yadda ta ke bugu sakamakon jin muryar ta kawai gaida shi ta yi duk da ta so ta d'auki muryar shi a lokacin da ya amsa mata sallamar amma ta kasa gane weye......................... "Ya jikin na ki fatan kin samu lafiya"? Ta ji ya katse ta kai ta d'aga a hankali kamar ya na gurin ta ce "da sau'ki". "Alhamdulillah Allah ya 'karo sau'ki ko kina jin wani abu har yanzu"?. "A'a na warke na samu lafiya". "Ok ya yi kyau Allah ya 'kara lafiya". "Amin na gode". "Ba komai ba godiya tsakanin mu baiwa Sameer d'in" mi'ka masa ta yi ya kar6a yana murmushi ya kara a kunne yana cewa "ok" "ok eh shikenan sai zuwa jimawa" daga haka ya sauke wayar yana kallon ta yace "ina Ikram ko bata tashi a barci"?. "A'a ta tashi tana d'aki indomie na ke dafa mata". "Ok" kawai ya ce ganin ya na shirin fita kuma bai fad'a mata waye ya duba ta ba ya sa ta ce "Yaya Sameer" dakatawa ya yi tare da juyowa ya ce "na'am". "Waye wannan da ya duba ni"? Murmushi ya yi yana cewa "Aboki na ne man" da alamar tambaya tace "Abokin ka"?. "Uhm ya akai"? Jiki a sanyaye ta girgiza kai 'kare mata kallo ya yi daga baya ya yi yana sake yin sabon murmushi daidai Ikram ta fito tana jefar da ledar biscuit d'in da taci hannu Sameer ya bud'e mata yana cewa "oyoyo 'yar Abban ta yau kin kwana a gidan mu ko zo nan" 'karasowa ta yi ya d'auke ta ya na kallon Zainab yace "bari mu dawo" ya fad'a su na fita daga 'kofar yatsa Asabe ta ciza kamar za tai hauka ganin yadda suka bi su ka kanainaye mata d'a huci kawai ta ke fitarwa jira take ya dawo ta yi masa zagin 'kare dangi Zainab kam indomie ta juye mata ta tafi d'akin kafin su dawo............. ZUCIYAR ALIYU CE ❤️️YMA DUTSE JIGAWA STATE Ni YUSRAH MUSA ABUBAKAR ina alfahari da jiha ta domin ba ni da kamar ta duk in da naje a fad'in duniya ❤️JIGAWA❤️ zan dawo ga shi abun sha'awa a cikin Nigeria mu ne muke da gada sannan mu ke taka kan ❤️DUTSE❤️ idan ka ji ana cewa birnin daraja wanda ya cika ya batse da al-umma to fa ♥JIGAWA STATE CE♥ ga haske a cikin ❤️JIGAWA❤️ ga kuma adon ❤️DUTSE❤️ ta ko'ina garin dad'i ❤️JIGAWA❤️ kafin Allah. ❤️JIGAWA❤️ jiha ta ce abar alfahari na ce sannan mu na zaune lafiya da juna ba ma rigima ko tashin hankali ni fa idan an ce ❤️JIGAWA❤️ har wani tunkaho na ke ji Masha Allah ina godiya ga Allah swt da ya kaddara min kasancewa ta cikin ❤️JIGAWA❤️ ba karamin falala ba ne gare ni. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 59 Ta na zaune ya shigo ya na aje Ikram da abin da ya siyo mata kallon sa Zainab ta yi tana cewa "lah Yaya Sameer wai abun karyawa ka siyo mata kaga fa taci biscuit ga buredi kuma kaga indomie ma ita na dafowa" kai ya d'aga yana cewa. "Ba ta 6aci ba ki aje mata wannan d'in kafin a gama girkin rana sai ta ci tun da yarinya ce kowanne lokaci za ta iya neman abinci ki saka mata a cooler sauri na ke zan koma chemist". "To Yaya Sameer an gode Allah ya 'kara arziki". "Amin" ya na fad'in haka ya juya ya fita daidai Asabe ta fito daga d'aki ta gan shi ya na shirin ficewa da sauri ta ce "kai Sameer zo nan" komawa ya yi inda take ya zauna a kusa da ita ya na cewa "ga ni Umma" wani irin kallo Asabe ta yi masa ta na cewa. "Wai me ka ke son mayar da kan ka ne soko shashasha saki tumaki 6allo jakuna kake son mayar da kan ka akan wadannan mutanen ko me? Da mamaki Sameer ya ce "da na yi mefa Umma"? cikin takaici ta ce "da ka yi uban ka wato ma saboda ka na son mayar da ni shashasha shi ne ka ke tambaya ta wai me ka yi ko"? Had'e hannu Sameer ya yi yana cewa "Umma dan Allah kiyi ha'kuri idan na 6ata miki rai yanzu ana jira na a chemist zan shigo zuwa jimawa sai mu yi maganar kin ji" kai ta jinjina tana cewa "shikenan je ka" tashi ya yi ya fita Asabe da ta gama had'a komai ta kallo 'kofar d'akin Umma ta na cewa. "To isashshiya na gama idan kin ga dama ki fito ki d'auke mu ku" ta na fad'in haka ta bud'e labulen d'akin ta, ta shige kai Umma dake kwance a d'aki ta girgiza tana sake gyara kwanciyar ta kusan mintuna goma ba wanda ya fito domin Zainab duk zaton ta ko Umma ta fito ta d'auke sai da ta fito sannan ta ga komai a gurin zuwa ta yi ta d'ebe ta shigar da shi d'akin Umma ta tarar barci ma ta ke kawai ta ajiye ta fita ta koma d'akin ta, ta d'auki kayan d'inki ta soma duba wanda ba ta d'inka ba ko zuwa jimawa ne sai ta yi. NA'IBAWA Saukar wata mace a Napep kenan bayan ta biya me Napep d'in kud'in sa ta 'kwan'kwasa wani gida dake rufe tare da d'an komawa baya ta tsaya kafin a zo a bud'e mata jin shiru yasa ta sake 'kwan'kwasawa daidai an bud'e 'kofar ta kalli wacce ta bud'e tare da sakar mata harara ta na cewa "wato ke idan aka zo gurin ki sai mutum ya 'kai'kashe baki zo kin bud'e masa 'kofa ba ko wannan da abun cutarwa ne ya biyo ni sai dai ya kashe ni ai" dariya ta yi tana matsawa ta ce "haba ke kuwa 'kawa ta ai kema kin san ba halina ba ne ban ji da wuri ba ina kitchen Nassar ya na parlor yana kallon cartoon shi ne ya fad'o min fa". "Humm lallai ya yi". "Shigo man ki ka tsaya a nan"? "A'a ba zan shigo ba kuma idan Yaa Sayyidi ya na nan fa ni da na zo mu yi magana". "Hum'um da yana nan ma ba ruwan sa dake balle baya nan sai ka ce yau ki ka fara zuwa gidan ki shigo dan Allah mu je". "Ok mu je to tun da baya nan" shiga su kai sakamakon Nassar ya na parlor ya na kallo su ka wuce can cikin bedroom su na zama Samirah da ta aje mayafin ta ta ce "lallai 'kawar arziki gaskiya ba amana wallahi ba amana yanzu tsakani da Allah ba dan na ji labari ba da shikenan sai dai daga baya na zo miki jaje duk tsiya ai mu ne 'yan danna 'kirjin ko"? Cikin rashin fahimta Sabirah ta ce "ban gane danne 'kirji ba? 'kirjin wa za ku danne"? Dariya Samira ta yi tana cewa "ina wata bayan ke"?. "Har yanzu ban gane abin da ki ke nufi ba fa ni me ye had'i na da danne 'kirji"?. "Ki na da had'i dashi man tun da mijin ki ya fara 'ko'karin neman aure" zabura Sabirah ta yi tana zaro ido ta ce "ban gane ba aure ya ce miki zai 'kara aure fa? Amma ya kasa fad'a min waye ya fad'a miki"?. "Ina zaune na ji zancen ya same ni shi ne ma dalilin zuwa na, na ji inda gaske ne". "Gaskiya duk wanda ya fad'a miki ma bai ji daidai ba saidai idan wani Yaa Sayyidin ake nufi amma ba wannan ba". "Yauwa abun ya bani mamaki shi ya sa har na kasa ha'kuri na zo fa" dariya Sabirah ta yi tana cewa"ya 'kara aure a ina zai saka ta bayan ba fili ne dashi ba kuma shi ba wata 'kwak'kwarar sana'a ba". "Ki ka sani ko had'a ku zai yi"?. "Ya had'a wa? Ai kuwa da yaga tashin hankali dan wallahi sai na 'kone duk shegiyar da ya aura sai dai ni ma a kashe ni". "A'a hakan ma ba zai faru ba tun da jita-jita ba gaskiya ba ne mu bar maganar kawai" mi'kewa Sabirah ta yi ta na cewa "ki dawo parlor fankar d'akin ta lalace kuma akwai zafi bari na je kitchen na duba kar abincin ya fara 'konewa saura kad'an ruwan sanda na fito" tashi ta yi su ka fita tare ita tayi waje Samirah kuma ta zauna a parlor ta na d'auko wayar ta daga handbag ta saka caji.................................. ZUCIYAR ALIYU CE ≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈ J.W.A @YUSRAH YMA ₱AGE 60 A ranar Sabirah ba ta samu sun yi magana da Yaa Sayyidi ba sakamakon bai dawo gida da wuri ba sai washe gari da safe bayan ya yi wanka ya shirya ya taje gemun sa ya debi littafai zai fita ta ce "Abban Nassar wai da gaske ne ka na neman aure"? Jin tambayar da ta yi masa ya sa ya tsaya ya na jinjina kai yace "eh gaskiya ne" zabura Sabirah ta yi ta na cewa "aure za ka 'kara me nayi maka meye na rage ka dashi ka ke son yi min kishiya"?. "Dama waye ya fad'a miki sai mace tayi laifi sannan ake mata abokiyar zama ra'ayi ne yasa zan 'kara saboda ina so ba wai dan kin gaza da yi min wani abu ba". "Ai kuwa wallahi ba zai yuwu ba gaskiya ba zan iya ba wannan ai masifa ce haka kawai ina zaune ni kad'ai ban damu da kowa ba za ka d'aga min hankali". "Ke ki ka d'agawa kan ki hankali tun da ke ce ki ka fara tada maganar ba ni ba". "Me ka ke nufi"? "Zan ba ki amsa idan na dawo" ya na fad'in haka ya juya ya fita rasa in da za ta saka kan ta taji dad'i ta yi kenan jita-jitan da Samirah taji gaskiya ne tun da akwai 'yar uwar su Yaa Sayyidi da ta ke aure a makoftar su wato a nan ta ji labari, da sauri ta d'auki waya ta na danna kiran Samirah ta shiga amma ta na ta ringtone ba'a d'aga ba har ta katse sake kira ta yi nan dai no answer wani irin takaici ne ya rufe ta aje wayar tare da cizon yatsa ta ce "humm ba dai aure za ka 'kara ba? Zan ga tsinanniyar da za ta aure ka idan kwanakin ta ne a kusa sai na kashe ta walla.................. Kiran wayar ta da akai shi ya katse mata tunanin da take yi da sauri ta d'auka ganin Samiran ce ta biyo bayan kiran ta na d'auka ta ce "hello Samirah hasashen ki ya tabbata ashe da gaske ne neman auren ya ke yanzu na tambaye shi zai fita ya ce min eh". "Kan bala'i aure dai kuma yanzu ke ya za ki yi"?. "Akwai yadda zan yi man kinsan anguwar da yake neman auren har gida zan je na ci wa yarinyar dazai aura mutunci na yi mata barazanar kisa idan ta aurar min miji shikenan abun da na ke so haka kawai ba hannun sa ne ya cud'i bayan sa ba d'an albashin da ya ke d'auka mu na samu ya na isar mu ya taro aure haka kawai mu dawo zaman 'kaili 'kalula". "Gaskiya kam gara ki je da kan ki ta ga idon ki, ki nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane" kai Sabirah ta jinjina ta na cewa "shikenan ga ni nan yanzu zan shirya na fito mu tafi shi ma ai ba makaranta ya tafi ba maybe akwai abin da za suyi na ga ya d'auki littafai har za mu dawo" ta na fad'in haka ta kashe kiran tare da shiga bedroom a gurguje ta d'auko hijab da kud'i ta fito da key ta rufe gidan sannan ta tari d'an Napep ya kai ta rijiyar lemo gidan su Samirah ita ma a lokacin ta shirya kawai fitowa ta yi su ka tafi domin ta san anguwar kuma da suka sauka su ka yi tambaya aka nuna musu gidan shiga su kai da Rasheedat su ka fara cin karo zata shiga 'kofar Hajiya caraf Sabirah ta ri'ke mata hannu tana cewa. "Ke tsaya ke ce Zainab"? Cike da mamaki Rasheedat ta girgiza kai ta na cewa "a'a ba ni ba ce wacce 'kofar ta 'karshe za ku shiga da alama ku ma ta kar6i kud'in d'inkin ku kuma ba ta yi mu ku ba ko"? Tsaki Sabirah ta ja ta na wucewa ta ce"dallacan ban guri uban d'inki zan kar6a na rasa wacce zan kawowa d'inki sai ita" dariya Samirah ta yi ta na cewa "ita abun da ya dame ta kenan amma ai ba gurin ta ki ka zo ba da zaki huce haushin ki a kan ta"?. "Eh ba gurin ta na zo ba amma tun ki ka gan ta a gidan ai watakil 'kanwar ta ce" ta fad'a ta na tura murfin kofar shiga lungun su Zainab ta ce "assalamu-alaikum"! Asabe da ya ke ranar girkin ta ce ba kowa a kofar duk su na d'akin ita kad'ai ce a waje ta na aiki d'agowa ta yi jin anyi sallama ga kuma ba'kuwar fuska da bata ta'ba gani ba ya sa ta ce "wa alaikum salaam ba'ki da ranar nan haka sai da muka kusa sau'ke tukunya mu da ko 'kwayar shinkafa ba ma dad'awa akan abun da mu ke dafawa🙊" ta6e baki Sabirah ta yi tana cewa "ke ce karayayyiya kuma mayunwaciya uwar me zan yi da abincin wannan gidan ko an ba ni aina zubar balle ma Allah ya sauwake" kai Asabe ta jinjina tana kallon ta tace "humm dama na san za'ai haka tun da ki ka fara magana na san cewa ke dangin Hauwa ce daga zuwan ki har zaki fara yi min rashin arziki". "Ke ki ka san wata Hauwa har ki ka damu Ina ruwa na da ita" hararar ta Asabe ta yi tana cewa "to dai kar ki kuskura ki zage ni" a masife Sabirah ta ce "idan na zage ki za ki dake ni ne". "To shikenan zage ni ki gani" bud'e baki Sabirah ta yi za ta yi magana Samira ta rufe mata bakin ta na girgiza kai ta ce "ba gurin ta mu ka zo ba gurin 'yar ta ne". "Wacece 'ya ta" Asabe ta tambaya cike da fargaba domin ta san Bilki ba ta gida tun safe ta tafi gidan da take wanke-wanke da shara ko dai wani abu ta yi aka kawo 'karar ta? Ji ta yi Samira ta ce " 'yar ki Zainab" ta6e baki Asabe ta yi tana sauke ajiyar zuciya jin ba Bilki suke nufi ba cikin jin dad'i ta ce "a'a a'a Allah ya tsari gatari da saran shuka Zainab ba 'ya ta bace ni ban haife ta ba ga d'akin gyatumar ta nan ku shiga". "Ba shiga za mu yi ba kawai ki mana magana da ita". "Cafd'i ni ce zan yi muku maganar da ita ma kenan saboda tsabar samun gu akuya da tu'kin tuwo idan ku ba za ku yi mata magana da kan ku ba sai dai ku kwana a nan" ta na fad'in haka ta shige kitchen tsaki Samirah ta ja ta na cewa "ni fa na tsani harkar rainin wayo a rayuwa ta wannan matar ba mutunci ne da ita ba". "Bar ni da ita ina daidai da zamanin ta assalamu-alaikum wai ba kowa ne"? Sabirah ta dad'a fad'a ta na gyara tsaiwar ta fitowa Umma ta yi tana cewa "amin alaikum salaam su waye"? Jijjiga Sabirah da ke tsaye ta yi tana cewa "mu ne fito ki gan mu" da mamaki Umma take bin su da ido ba ta ta'ba ganin ko mutum d'aya ba a cikin su. "Sannun ku da zuwa daga ina"?. "Daga ko'ina ina 'yar ki Zainab take"? Da sabon mamaki Umma ta ce "lafiya dai ko"?. "Lafiya za ta kawo ni gurin Zainab ne har abada yanzu a duniya ina da wata ma'kiyiya sama da ita ne" d'aurewa Umma kai Sabirah ta yi shi ya sa ta kalle ta sosai ta na cewa "to me yayi zafi haka ko kun samu sa6ani da ita ne"? Tsaki Sabirah ta ja tana cewa "ni na ta'ba ganin ta ne ma da har zan samu sa6ani da ita ba dan yanzu da ta shigo rayuwa ta ba kawai ki fad'a min inda zan same ta" numfashi Umma ta sau'ke ta na cewa. "Ta je siyo kayan d'inki" ta na fad'in haka Zainab ta bud'o 'kofa da sallama ta na aje Ikram da ke hannun ta na 'ko'karin cire hijab Sabirah ta ce "ohhh yanzu na fahimta ko ba'a fad'a min ba ke ce Zainab tun da na ganki da nikaf ga hijabi har 'kasa haka ne"? Da mamaki Zainab ta kalle ta tana cewa "eh ni ce" zabura Sabirah ta yi tana cewa "au ke ce tsabar tsaurin ido ki ke ce min wai kece munafika dama kece annamimiyar da take son auren miji na? Hmm ai kuma kin yi kad'an wallahi kin yi tsararo ba ki kai ba tun wuri kafin lokaci ya 'kure miki ki je ki samu mijin aure domin Yaa Sayyidi yafi 'karfin ki babu 'yar iskan data isa na had'a kishi da ita idan tsautsayi ne ya ke kiran ki bismillah ki auri mijin nawa ni kuma na d'au alkawari sai na fard'e ki da wu'ka idan kunne ya ji jiki ya tsira idan kuma ki na ganin na yi 'karya ne dan Allah kar ki fasa ki aure sa zan nuna miki 'karshen ki" ta na fad'in haka ta juya fuuuu ta fice daga 'kofar Samirah ta bi bayan ta shiru Zainab ta yi cikin wani irin yanayi gabadaya ta rasa me ya ke mata dad'i ace ba dama saurayi ya fara neman ta sai an samu sa6ani Umma kam jin abinda Sabirah ta zo ta amayar a ya sa tace. "In dai dan Yaa Sayyidi ne ba shi kad'ai ne namiji ba insha Allahu Ubangiji zai kawo miki miji na gari ki na zaune tun da ta iya zuwa har gida tayi miki haka ina kuma da kin je gidan? Ba komai Allah ya rufa asiri" ta na fad'in haka ta juya d'aki Zainab ma jikin ta a mace da'kyar ta shiga na ta d'akin ta kwanta domin yadda jikin ta ya ke rawa ko ta hau kan keke ba za ta iya d'inkin ba dole sai ta samu nutsuwa. ZUCIYAR ALIYU CE ................PAGE 61 "A'a kai jama'a dad'i na da gobe saurin zuwa ayuririiiiiiiii wayyo dad'i zai kashe a gidan nan wato dai da alama fa Zainab ba za ta yi auren ba da gaske tun da gashi duk wanda ya fito sai an wargaje maganar wato ashe wannan matar Yaa Sayyidi ce ta zo har gida ta yi muku wankin babban bargo haka na ke so wallahi humm in dai zaman gida ne yanzu ta fara mu je zuwa bari na yi sauri na gama abinci na kai wa Hajiya daga nan sai na gulmata masa hehehehhhh" ta karasa maganar ta na fashewa da dariyar mugunta ba wanda ya fito balle su tanka mata kawai sun bar ta da fitowar rana da fad'uwar ta. Su na Napep Sabirah ta ke cewa "kai sai yanzu na ji dad'i da naje na kaddamar musu da zan bar abu a raina yayi ta damu na" dariya Samirah ta yi tana cewa "ai kin ban 'ko'kari ban ta'ba tunanin za ki iya fad'a irin haka ba sai da na gani". "Humm Samirah 'kyale ni kawai rai na ne ya 6aci da yawa babu wanda za'ai wa haka ya yi shiru balle ni Ina son Yaa Sayyidi sosai kamar rai na kuma yaushe zan bari wata ta shigo rayuwar mu na je ta raba mu shi ya sa tun abun baiyi nisa ba na yiwa tukar hanci" daidai me Napep ya tsaya su ka sau'ka Sabirah ta bashi kud'in sannan su ka shiga gidan. Yaa Sayyidi kam tun ya fita da safen sai bayan sallar magriba ya dawo a lokacin Samirah ta tafi bai zo ya same ta ba sai Sabirah da take ta faman cika ta na batsewa yasan akan maganar da su kai da safe ne shiyasa ma bai kula ta ba da yayi wanka ta kawo masa abinci ta d'auka zai tambaye ta fushin me take amma sai ta ga ya yi burus da ita cikin takaici ta ce. "Abban Nassar ashe dama waccan yarinyar ka ke so Zainab? Jin abun da ta ce ya sa ya fasa kai lomar abincin ya tsaya ya na cewa "ya akai ki ka sani"? Ta'be baki ta yi ta na kawar da kai ta ce "zancen duniya ba ya 6uya ai daka 6oye min ma an fad'a min wacce ita shi yasa na taka naje har gidan su nayi mata gargad'i" zaro ido Yaa Sayyidi ya yi ya na aje cokalin tare da d'aukar ruwa ya kur6a jin har lokacin abincin da ya ma'kale masa bai wuce ba ya ce. "Me ki ka fad'a mata"?. "Wannan kuma tsakanin mu ne". "Wai Sabirah ki na da hankali kuwa waye ya zuga ki kije gidan su Zainab kin yi hauka ne"?. "Idan haukan na yi ma kai ne sila ba kowa ba tun da hankali na ka aure ni kai ka ke son mayar dani me 'karamin ta6in kai kuma wallahi ka ji na rantse ba zan yi kaffara ba indai tsautsayi yasa ka aure ta sai na kashe ta" ta na rufe baki Yaa Sayyidi ya yi mata wani irin kallo ya na cewa "ai kuwa da ke ma sai an kashe ki" kafad'a ta d'age ta na cewa "ban damu da irin hukuncin da za'a yanke min ba in dai itan tabar duniyar hakan na ke so" ta na fad'in haka ta tashi ta bar gurin da kallo Yaa Sayyidi ya bi ta tare da yin shiru kamar me tunani daga baya ya mi'ke yana fita daga gidan ya tafi masallaci sai da akai sallar isha sannan ya dawo gida ya d'auki mashin d'in sa ya tafi anguwar Zainab a lokacin ta kunnawa Ikram kallo a wayar ta taji ana kiran ta ganin wanda yake kira yasa ta sa Ikram ta mi'ka mata wayar ta d'aga suka gaisa ya ce ta fito waje ya zo numfashi ta sau'ke tana ajewa Ikki wayar sannan ta d'auki hijab ta shiga d'akin Umma ta fad'a mata zata fita kallon ta Umma ta yi tana cewa. "Wannan Yaa Sayyidin ba shi ne wanda matar sa ta zo d'azu ba"?. "Eh shi ne" da mamaki Umma ta ce "amma kuma za ki je"? "Ai kuma Umma ba laifin sa ba ne maybe ma bai san matar tasa ta zo ba sai da ya koma gida". "To shikenan sai kin dawo Allah ya tsare". "Amin" ta ce ta na juyawa ta fita akan mashin d'in sa ta same shi a zaune sallama ta yi su ka sake gaisawa kafin ya kalle ta ya na cewa "wai d'azu da gaske mata ta tazo gidan nan"? Kai Zainab ta d'aga tana cewa "eh ta zo ashe ta fad'a maka kenan"?. "Ta fad'a min ai na d'auka da wasa take ashe da gasken dai tazo? Subanallah Allah ya rufa asiri shi ya sa da ta fad'a min na kasa nutsuwa dole sai na zo na baki ha'kuri dan Allah ki yi ha'kuri kin ji". "Ba komai a take na manta da abun ni ban ri'ke ta ba". "Yauwa masha Allah na ji dad'i sannan alfarma na ke nema kar wannan barazanar da ta zo tayi ya dame ki har tasa ki ji a ran ki cewa kin fasa aure na"?. "In sha Allahu hakan ba zai faru ba matar mutum kabarin sa idan akwai rabon aure tsakanin mu babu wani abu da zai hana" murmushi Yaa Sayyidi ya yi tare da shafa gemun sa ya ce "Alhamdulillah malama Zainab na ji dad'i sosai da ya kasance kin fahimce ni kuma na gode yanzu bari na koma gida dama dalilin zuwan nawa kenan" kai ta d'aga ta na cewa "shikenan ka gaida gida na gode sai da safe" ta fad'a ta na juyawa zuwa gida d'akin Umma ta fara shiga ta tarar da ita ta na karanta wani littafi na addini mai suna miftahul ibadat jin sallamar ta ya sa Umma ta d'ago ta na kallon ta tace. "Har ya tafi ne"?. "Eh ya tafi yanzu" jinjina kai Umma ta yi tana cewa "Allah ya kyauta Ubangiji ya 'kara rufa asiri ya za mu yi da rayuwar mu idan shi ne mijin na ki dole mu ha'kura ko ba ma so amma ni dai gaskiya Zainab lamarin yarinyar nan da tazo d'azu ya ban tsoro amma dai ba komai Allah ya tsare ki daga sharrin ta" jiki a sanyaye Zainab ta ce "Amin" kamar mara lafiya ta juya ta fita daga d'akin ba kuzari ko kad'an musamman yadda ta ga Umma ta damu akan abinda matar Yaa Sayyidin ta zo ta yi mata d'azun ta sani abun ya d'agawa Umman hankali kuma ya dame ta tun da har ta'ki ta manta, gaskiya ita kam indai Umma ba ta son auren nan gara ta ha'kura Allah zai kawo mata miji na gari duk daren dad'ewa duk mai ha'kuri ya na cin riba sannan indai har ka ro'ki Allah zai amsa maka idan ka tsaya a kofar sa zai kar6e ka idan ka nufe shi zai cika maka burin ka idan ka dogara da shi zai isar maka babu wani abu da ya ke faruwa ba tare da sanin sa ba shi ne sarki guda d'aya mai bud'awa gwanin jin 'kai mai tausasawa babu abin da ya 6uya gare shi dukkan fitar nishi da numfashi ya na sane ka dagora da shi ka ro'ke shi komai zai amsa maka ya biya maka bu'katun ka ya fitar da kai daga damuwa da ba'kin ciki shi ne Ubangiji abun nufi da bu'kata shi ne madogara shi ne mari'ka shi ne mafaka kuma shi ne matabbata daga gare shi mu ke sannan gare shi za mu koma, ya Ubangiji ka yi ma na rahma ka yalwata mu dukkan mu, mu bayi gare ka ne ya Allah ka gafartawa iyayen mu😭 Amin,,🤲. ❤️ZUCIYAR ALIYU CE❤️ JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION. J.W.A gidan kar6ar mutane hannu biyu da zaman lafiya. @YUSRAH DUTSE PAGE 62 Washe gari lahadi da ya ke a ranar Zainab za ta mayar da Ikram gida shi yasa bayan ta dawo daga islamiyyar wajen 'karfe biyu da rabi su ka je gurin wata me lallai a anguwar ta biya akaiwa Ikram su ka dawo gida ta iya kitso ta yi masa sannan ta yi mata wanka ta shirya ta dama ta fad'awa Sameer shi ne zai raka ta su mayar ta. Bayan ta shirya ita ma ta saka hijab da nikaf ta d'auki wata handbag d'in ta me d'an girma ta zubawa Ikram biscuits da chocolates sannan ta fito a lokacin Ikram ta na tsaye a gaban Umma wacce take zaune ta na tu'ka tuwon masara kallon ta yi bayan ta 'karasa gurin ta ri'ko hannun Ikkin ta na cewa. "Umma bari na je Yaya Sameer ya na chemist mun yi magana dashi shi ne zai raka ni na mayar da ita" kai Umma ta d'aga bayan ta gama tu'kin ta rufe tukunyar ta na cewa "to ba damuwa sai kun dawo Allah ya tsare" sai kuma ta kalli Ikram ta na murmushi ta ce "yar Abban ta yau sai kwanan gida ko ba za ki tsaya na gama tuwon ki ci ba"? Kai Ikram ta d'aga ta na ri'ke hijab d'in Zainab ta ce "gida zan tafi gurin Momy na". "Shikenan to ki gaida ita in ji wa zaki ce". "Cewa zan yi in ji Umman Aunty Mami" d'an murmushi Zainab ta yi tana kallon Ikki ta ce "wacece Aunty Mami kuma"? Nuna ta ta yi ta na cewa "ke ce Aunty Zainab zan cewa Momy na Umman Aunty Mami ta na gaida ita" dariya Umma ta yi tana "lallai Ikram ya yi kyau to ki gaida Yayan ki" to ta ce Zainab ta na ri'ke da hannun ta su ka fita daga 'kofar daidai Sameer ya shigo ya hango su. "A'a wai har kun shirya"?. "Eh tun d'azu dama gurin ka za mu fita ka kai mu ai". "Ok ai kuma ko wanka ban yi ba ya za'ai kenan"?. "Sai mu koma mu jira ka, ka yi" kai ya d'aga ya na cewa "shikenan mu je to" juyawa ta yi su ka koma Umma ta na d'aki ba ta san sun dawo ba sai da ta fito ganin takalmin da Zainab d'in ta saka a 'kofar d'akin ya sa ta ce "Zainab ki na ciki ne"?. "Eh ina ciki" da mamaki Umma ta ce"ya akai ku ka dawo bayan kun riga kun tafi kuma ko wani abu ku ka manta"?. "A'a Yaya Sameer mu ka dawo jira zai yi wanka". "Oh bai yi wanka kenan ya fita shikenan Ikram yau ma anan za ki sake kwana ba za ki ga Momyn ki ba" dariya Zainab ta yi ta na kallon Ikram wacce ta 6ata fuska ta na turo baki alamar za ta yi kuka cikin lallahi ta ce "yi shiru Ikki na da wasa Umma ta ke miki kar ki yi kuka yanzun nan za mu tafi gurin Momyn ki na mayar da ke kin ji"? Kai ta d'aga ta na goge ido alamar ya fara yi ma ta 'kai'kayin hawaye ta ce. "Mu tafi yanzu mu tafi gurin Momy na" ganin za ta d'aga ma ta hankali ya sa ta mi'ke ta na sakin nikaf d'in ta su ka fita waje daga d'akin har lokacin Sameer bai gama shiryarwa ba amma dai ya fito a wankan numfashi Zainab ta sau'ke ta na zuwa wajen 'kofar d'akin na sa ta ce. "Dan Allah Yaya Sameer ka yi sauri yarinyar nan za ta fara mun kuka" daga cikin d'aki ya ce "Subanallahi kuka kuma? Haba 'yar Abban ta gani nan yanzu zan fito mu tafi" Umma kam da take ta ayyukan ta ganin inda Ikram ta tafi ta tsaya a can wajen 'kofar shigowa lungun alamar ta matsu su tafi ya sa ta ce "Allah sarki Ikram anan za ta sake kwana ba mai a mashin d'in dawo ki zauna a nan idan na gama tuwo ki ci gobe sa mayar da ke" Umma na rufe baki ba zato su ka ji Ikram ta fasha kuka ta na zaman 'yan bori a gurin da sauri Zainab ta taho ta d'aga ta sai harharba 'kafa ta ke ta na ihu fitowa Sameer ya yi yana girgiza kai ya ce "kai gaskiya wannan yarinyar akwai caza kai wannan ai sai ta sakawa mutum ciwon kai ta na da rigima" dariya Umma ta yi ta na kallon yadda har lokacin ta'ki ta yi shiru sai faman jijjigen ta Zainab ke yi kamar wata jaririya ta ce. "Yau za mu huta sai dai ta je ta yi wa iyayen ta" kai ya jinjina yana cewa "sai mun dawo". "To Allah ya tsare Ikki ki gaida Abba da Momy ko"? Ta fad'a ta na kallon Ikram wacce ta yi shiru ta na kallon ta, fita sukai shi kuma ya d'auki mashin d'in na sa ya fita da shi zuwa 'kofar gida Zainab ta saka Ikram a tsakiya sannan ta hau bayan ta su ka tafi. Da yake dama Aunty Murjah ta san za su zo ita da Sameer su kawo Ikkin shi ya sa ta fad'awa Auwal shi kuma ya fad'awa Mukhtar zai zo su gaisa duk da Zainab ba ta sani ba sai da su ka je, su na zaune a parlor bayanta sun gaisa Zainab ta ce "to Aunty Murjah gashi na cika alkawari na dama kyan alkawari cikawa kamar yadda na d'auka na dawo miki da Ikki ki har gida" murmushi Aunty Murjah ta yi tana kallon ta tace "ai kuwa tun d'azu Mukhtar ya zo gidan nan saboda na fad'a masa yau zaki dawo da ita yace za ku yi magana suna ta jira ganin baki zo ba basu dad'e da fita ba shi da Sweet" da mamaki Sameer ya kalli Zainab wacce ta had'e rai ya na cewa. "Waye wani Mukhtar kuma" dariya Aunty Murjah ta yi ganin yadda Zainab ta ke dad'a cika ta ce "Mukhtar abokin Sweet ne ranar da mu ka je duba ta tare da shi ne dan dai ya na cikin mota ne a lokacin da ka je gurin na mu amma da za ka gan shi" kai Sameer ya jinjina ya na cewa. "Son Zainab d'in ya ke ko kuma yaya ban gane ba"?. "Eh man son ta yake sosai da gaske kusan shekara guda tun da ya gan ta tazo gidan nan da ace ta bashi fuska da yanzu an jima da yin bikin su domin tun a lokacin ya nuna min shi da gaske ya ke yi matsalar daga ita ne" ta'be baki Sameer ya yi yana cewa "ai kuwa ya had'a kan sa da wahala Zainab akwai wanda za ta aura ba rabon sa bace gara ki fad'a masa tun wuri ya nemi matar aure kafin lokacin ya 'kure masa" bud'e baki Aunty Murjah ta yi da mamaki ta zaro ido ta kalli Zainab wacce ta yi shiru kamar ba ita a gurin mai da hankalin ta kan Sameer ta yi ta na cewa. "Dan Allah Sameer da gaske ka ke kodan ka dakatar da Mukhtar ne"?. "A'a ba dan na dakatar da shi bane gaskiya na ke fad'a miki akwai wanda za ta aura" cikin matsuwa Aunty Murjah ta ce "to Masha Allah haka ake so ai waye wanda za ta aura dama kin tsayar da miji amma ba ki fad'a min ba da sai lokaci ya 'kure ko kuma ya"? Dad'a 6ata fuska Zainab ta yi tana juyawa musu baya ta'ki magana kai Sameer ya jinjina ya na cewa "ni za ki tambaya domin ni ne na san shi ba Zainab ba" dariya Aunty Murjah ta yi tana cewa. "Ah ah ban gane kai zan tambaya ba ita ba kenan ka fita sanin sa"?. "K'warai domin ita wacce ki ke tambayar ita ma ba ta san waye ba". "Ji Kayan tashin hankali ba ta san shi ba me akai kenan waye zaiyi irin wannan auren ka bar ta kawai ta auri Mukhtar d'in ya fi". "A'a an riga shi". "To in dai haka ne sai ka fad'i wanda ya riga shi mu ji waye"?. "Wani 6oyayyan masoyi ne ba yanzu za ki san shi ba sai ya bayyana" kai Aunty Murjah ta girgiza ta na cewa "kai dan Allah Sameer please ka barta ta auri Mukhtar ka ji" saurin girgiza mata kai shima ya yi yana cewa "a'a akwai wanda zata aura ki fad'a masa kar ma ya ji cewar ya na da rabo an riga shi" ha6a Aunty Murjah ta ri'ke ganin yadda su ka d'aure mata kai ita Zainab ta juya musu baya shi kuma Sameer ya dage akwai wanda za ta aura, huuuuuhhh ta sauke ajiyar zuciya ta na cewa. "To fa babba magana ni da aka ban sa'ko ya zan yi wannan al'amarin da nauyi" Zainab ta kalla ta na cewa "yanzu dai abin da za'ai idan ya dawo sai ki fad'a masa da kan ki domin ni ba zan iya ba ina jin kunyar sa" ta na rufe baki Sameer ya mi'ke ya na cewa "wallahi bai isa ba tashi mu tafi tun bai dawo ya same ki ba balle zuciyar sa ta ji dad'i idan ya gan ki" dariya Aunty Murjah ta yi tana kallon sa tace "kaii Sameer wannan har ka fi mai son Zainab d'in kishi irin wannan fad'a daga na fad'i haka ka tashi a zabure kamar an watsa maka ruwan wuta dan Allah ku tsaya man mu na hirar mu". "Kin san Allah tafiya za mu yi da gaske fa nake miki ba zai dawo ya same mu ba Zainab akwai wanda za ta aura idan ma kin fad'a masa ya'ki yarda shikenan shi ya sani dabara ta rage ta shi ko ya ha'kura ko kuma ya ci gaba da wahala idan yaga ta yi aure ya yarda tashi mu tafi Zainab ko dai ke ma ki na son sa ne kar na bada kai na"? Kai Zainab ta girgiza ta na mi'kewa ita ma Aunty Murjan tashi ta yi ta rako su har harabar gida suka hau mashin suka fita daga gidan suka barta ta na ta dariya.......... ZUCIYAR ALIYU CE J♣W♠A🤙 Story.Written.Editing “‰YUSRAH MUSA ABUBAKAR @YMA DUTSE JIGAWA PAGE 63 Su na cikin tafiya Zainab da ta sauke daddad'an numfashi ta ce "na gode Yaya Sameer gara da ka fad'a mata haka nima na huta Allah da gaske ko kadan mutumin nan bai yi mun ba" jinjina kai Sameer ya yi yana cewa "balle kuma ni gara da bai yi miki din ba ai da ko yayi miki dole ki bar shi" murmushi Zainab ta yi tana cewa. "Saboda me"?. "Saboda Aboki na man yaushe ina kallo zan bari wani Tom ko Jerry d'in zai zo ya na hira da ke bayan shi ya na so". "Ni fa Yaya Sameer abokin nan na ka bana saka shi a layin mutane da ace da gaske mutum ne da yanzu shi ma ya bayyana kan sa shekara kusan nawa ka na fad'a sai dai kullum ka ce zai bayyana har yanzu ya'ki bayyana d'in watakil ido ya bud'e maka kake ganin kamar mutum ne shi, ni dai ba ruwa na ba gara Mukhtar d'in ba tun da shi na gan shi da ido na kuma nasan mutum ne iri na da nayi soyayya da aljani fa"? Dariyar da ba shiri ta saka Sameer ya yi yana jinjina kai yace "da kyau kaiii da kyau tambaya me armashi, albishirin ki? To ki kwantar da hankalin ki ya kusa zuwa kwanan nan za ki gan shi in sha Allahu kun kusa had'uwa sai ki shirya tarbar sa" ya na rufe baki Zainab ta ja dogon numfashi ta na cewa. "Uhmmmmm!!" "Uhmm! kamar ya me ya faru"? Kai ta girgiza tana cewa "a'a babu komai" ta fad'a daidai sun 'karasa wani guri ya yi parking sau'ka ta yi shi ma ya sau'ka da mamaki ta kalli gurin ta na cewa "Yaya Sameer me za ka yi anan" key d'in mashin d'in ya cire ya na mi'ka mata ya ce "ri'ke min wannan ki jira ni yanzu ina zuwa" juyawa ya yi ya shiga cikin gurin ta na tsaye ya d'an jima kafin ta gan shi ya fito da plasma a hannun sa da mamaki ta kalle shi ta na cewa. "Yaya Sameer me za ka yi da plasma kuma ko a d'akin ka za ka saka"? Kai ya girgiza yana kar6ar key d'in ya tada mashin d'in ya na cewa "a'a ba tawa ba ce sa'ko ne dama yau zan zo na kar6a shiyasa na ce idan za ki dawo da Ikram ki yi min magana sai mu taho tare hau mu je" kai Zainab ta d'aga ta na hawa ya saka plasma d'in a gaban sa su ka d'auki hanyar gida. A 'kofar gidan ya aje ta, ta shiga sannan ya yi parking da mashin d'in shi ma ya shiga ya fara aje TV din ya dawo waje ya shigar mashin d'in ciki a lokacin an kusa kiran sallar magriba ya yi alwala ya fita daga gidan bai dawo ba sai bayan sallar isha su ka shigo tare da wani mutum sannan Zainab ta na d'aki ta ga Sameer ta yi ya shigo ya aje plasma d'in ya na cewa "ki fito daga nan ki shiga d'akin Umma wanda zai had'a miki TV ya zo" zaro ido ta yi a firgice ta nuna kan ta ta na cewa. "Wai ka na nufin dama na wa ne"? Kai ya d'aga ya na cewa "eh man in ji aboki na ba" dafe kai ta yi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ni dai ina cikin matsala wai Yaya Sameer wanne irin mutun................. "A'a ba sai kin ce komai ba na gane ki kwantar da hankalin ki ai na fad'a miki ya kusa zuwa ba za'a dad'e ba za ku had'u" ya na fad'in haka ya fita shiru Zainab ta yi zuciyar ta na bugawa da 'karfin gaske har Sameer ya shigo da mutumin ba ta iya tashi ba sai da ya sake le'kawa ya mata magana sannan ta mi'ke da'kyar ta na jan 'kafa ta fita ta shiga d'akin Umma, ita ma Umman ta na kallon ta kuma ta ga a yadda ta shigo sai dai ba ta da bakin magana akan wannan al'amari tun abun ya na damun idan ta gani ko tsoron a je a fad'awa Hajiya yanzu har ta watsar ko fargaba ba ta ji. Har mutumin ya gama aikin sa Sameer ya biya shi ba wanda ya fito sai dai su na jin maganar su dad'in abun ma Asabe ba ta gidan ta yi tafiya ana biki a dangin su da ace ta nan da yanzu ta had'a musu kururuwa ta kirawo mutanen gidan nan, jin da Zainab ta yi shirun ya yi yawa yasa ta fahimci sun fita har Sameer d'in mi'kewa ta yi jikin ta a mace ta fice ta koma d'akin ta kawai kallon iya TV d'aga mata hankali ya ke rasa inda za ta saka kan ta, ta ji dad'i ta yi ta na jin lokacin da Sameer ya shigo ya na tambayar Umma abincin sa ta fito ta saka masa. Ta na kwance idanun ta a rufe sai haske ta gani d'auu da sauri ta bud'e ido ta ga nefa aka kawo ga shi harda sabuwar 'yar yawo ta gani a gurin Sameer ya cire wancan tsohuwar ya saka mata sabuwa numfashi ta sauke tare da mayar da idon ta ji tayi Sameer yace. "Yauwa an kawo nefa Zainab ki na d'aki ne"? Sake bud'e ido ta yi a hankali ta ce "eh ina nan". "Ok" ya ce tare da yin shiru can kuma ta ji sallamar sa ya shigo ya na cewa "amma ba ki gwada kunnawa kin gani ko da akwai matsala ba"? Ya fad'a ya na kunnawa ya d'auki remote ya jawo kujerar da take d'inki ya zauna akai ita dai ta na gefen katifar ta da waya a hannun ta ba ta ce komai ba Sameer kam fita yayi ya koma d'akin sa ya d'auko abincin sa ya dawo d'akin domin so ya ke ya gani idan da matsala gari na wayewa zai kira mutumin ya zo ya sake saitawa sai kuma ya ga komai normal". ZUCIYAR ALIYU CE WRITTEN BY YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨ @YUSRAH MUSA DUTSE PAGE 64 Duk abin da ya ke faruwa Bilki ta na daga d'aki ta na jin su kai ta jinjina cike da takaici ta fito daga d'akin tare da takowa cikin sand'a a hankali ta le'ka window ta ga yadda TV take walwalin sabuntaka ji ta yi sabon ba'kin ciki ya rufe ta kamar ta d'auko katon dutsi ta jefa TV ya fashe tsaki taja ta na fita daga 'kofar tasu ta shiga gurin Hajiya ta yi sa'a ita kad'ai ce kuwa babu kowa ganin ta tayi ta baje naman kazar da Aminu ya siyo mata sai dagwargwaza ta ke zama Bilki ta yi tana cewa. "Tabd'ijan Hajiya ban ba ki labari ba kin san................... Tun kafin ta fad'i abin da take son fad'a Hajiya ta tare mata numfashi da fad'in "wani abu ne ya faru a gidan nan"? . "K'warai kuwa Hajiya gagarumi ma". "A ina su waye"? Cizon yatsa Bilki ta yi tana cewa"a 'kofar mu man d'azun nan Yaya Sameer ya shigo da wata 'katuwar TV na d'auka shi ya siyo wai ashe ta Zainab ce mai sakawa har yazo ya saka mata a d'akin ta ya saita mata tashoshi yanzun nan da aka kawo nefa Yaya Sameer d'in ya shiga d'akin ya kunna ba ki ji yadda 'kara ta ke tashi ba a 'kofar mu kamar gidan DJ" zaro ido Hajiya ta yi ta na daina cin naman ta ce. "TV kuma uban wa ye ya siya mata"? Kafad'a Bilki ta d'aga ta na cewa "taya zan sani Hajiya mafita d'aya ce kawai ki kira shi Yaya Sameer d'in ki takura masa ya fad'a miki wanda ya bashi ya kawo mata duk tsiya ai shi ya sani dashi ake had'a baki ana duk wata barna ta 'kofar mu domin duk wani abu da za ki gani a gurin Zainab shi zai kawo ya ce in ji abokin sa gashi har gobe abokin na sa ya'ki ya bayyana a san waye ai ko ta nan Hajiya ya kamata ki san 'karya su ke kawai raina ma na hankali za su yi dan kin ga misali kwanan bayan nan lokacin da ba ta da lafiyar d'in nan da ace ciki ne da ita wallahi Yaya Sameer za ku ritsa ya fad'a muku gaskiyar komai tun da duk wani abu da za'a kawo shi ne manaja da hannun sa komai zai zo gurin ta a hakan dan ma ba'a 'kofar ki ke ba da takaici ne zai kashe ki idan ki ka ga irin bushashar da ya ke kawo mata kala-kala naman kaji da na shanu kayan 'karfi zaki gan shi ya kawo mata ko chocolates da biscuits sai kace yarinya balle kuma su Faro da yogurts wadannan ai idan ana sallah ba'a magana Hajiya ku da ba ku sani ba shi ya sa hankalin ku ya ke kwance amma mu da muke 'kofar za'a kawo komai a gaban mu ba'kin cikin da mu ke sha'ka ya yi yawa ga masifar rowa ko zaka mutu ba za ta baka ba" ko kad'an bakin Hajiya ya'ki rufuwa tun da Bilki ta fara magana har ta kai 'karshen kai kawai take jinjinawa ta ce. "Kan bala'i dama irin abubuwan da suke faruwa kenan a 'kofar ta ku ban sani ba ko shi yasa na ga kwanan nan Abdullahi ya yi 'kiba har da naman wuya ashe dad'i ya ke ci ni ina nan a 'kai'kashe wato ga tsohuwar banza wacce ba ta da daraja sai a idanunsa bare humm ya yi kyau koda na ji shiyasa idan na tambaye shi kud'i ba musu yanzu zai d'auka ya bani ashe sabuwar rayuwa ya canza? Ai kuwa zan ci mutuncin sa zai zo ya same ni tashi ki je ki kira min Samar d'in shi ma wani munafikin ya zo na ji uban waye ya ke aiko shi da kaya gurin Zainab d'in yau sai na ci uban sa tashi ki kira min shi na ce". Zaro ido Bilki tayi tana cewa "tab ni ce zan kira shi so ki ke ya karya a gidan nan gashi Umman mu ba ta nan Baban mu kuma ba laifin sa ya ke gani ba gaskiya indai nice na kira shi cewa zaiyi ni na fad'a miki ki bari d'an wata 'kofar ya shigo sai ki aika masa". "To shikenan Allah ya kawo wani d'in yau ba zan yi barci ba sai na yi magana da Samar a gidan nan ko da ace zan samu nutsuwa" tashi Bilki ta yi ta na cewa "bari na nemo miki wani yaron sai ya kira miki shi" to Hajiya ta ce Bilki kuma ta fita ganin babu kowa ya sa ta le'ka 'kofar su Zakiyyah 'kanin Rasheedat ta gani a zaune ta ce. "Yauwa kai Adam ka je Hajiya ta na kiran ka yanzu" ta na fad'in haka ta juya 'kofar su ta koma da sauri ta fad'a d'aki a lokacin Sameer kam ya dad'e da fita a gidan Zainab kuma barci ma ya d'auke ta, sallama Adam ya yi shigo ba wanda ya amsa tun da duk sun yi barci shi kuma Sameer ya na waje le'kowa Bilki ta yi ta na cewa "Adamu ka tafi chemist d'in sa ya na can baya gida" ta na fad'in haka ta saki labulen ta koma fita ya yi daga gidan ya tafi chemist d'in ya fad'awa Sameer Hajiya ta na neman sa bai yi mamaki ba kuma ya na ji yasan dalilin kiran ba zai wuce wani ne yaje ya fad'a mata ya kawowa Zainab TV ba, humm mutanen gidan nan su na da abun haushi bari ya je yaji me za ta ce masa tun da dama dare ya fara yi goma har 'yan mintuna rufe chemist d'in ya yi ya tafi gida gabadaya idan ya fito daga gurin Hajiya kawai sai yayi kofar su. Ya na shiga kuwa abun da ya ke tunani ko sallama da yai ba ta amsa masa ba ta fara magana "kai Samar 'karshen alewa 'kasa yau sai ka fad'a min uban waye abokin ka wanda ya ke aiko da abubuwa ka ke baiwa Zainab haukan ya yi yawa abun ya wuce inda hankali zai d'auka alhali ku na da nagaba da ku amma ba mai tambayar ku saboda ba sa son su 6ata muku rai tun da zilamammu ne ku na d'an ba su wani abu ko kwanan baya ka shigo da firiza yau kuma har da kayan kallo duk waye ya ke aiko ka"? Kallon ta ya yi yana jinjina kai ya ce "tsinannan munafikin da ya ke zuwa ya fad'a miki gulmar ya zo kenan ya yi kyau amma ya manta bai fad'a miki har da katifa ba da yadin gado da fanka duka na kawo mata"? Zaro ido Hajiya ta yi tana cewa "au har da katifa da fanka kuma wai har da yadin gado kamar wacce ta kama d'akin mijin ta? na shiga uku ina raye a gidan nan an mayar da ni gawa wacce babu ita a duniya" tsayawa ta yi tana kallon Sameer ta ce "Samar uban waye yake aiko ka, ka fad'a min tun mu na mu biyu kafin na tara maka jama'a kasan Allah daga shi ba wani idan ba ka fad'a min ba sai nasa dukkan samarin gidan nan sun ri'ke min kai na ba su igiya su d'aure ka nasa Habibu da Aminu su yi maka dukan tsiya idan ba ka fad'a min ba" ta na rufe baki Sameer ya she'ke da dariya ya na dafe goshin sa tare da ri'ke ciki kai Hajiya ta jinjina ganin yadda ya ke dariyar ko tsayawa ba ya yi yasha numfashi ta ce. "Hummm! dole ka yi dariya tun da ga mahauciya ta na maka magana ka mayar da ni ban san abin da na ke ba" tsagaitawa ya yi yana zama a kusa da ita ya ce "Hajiya kin sani dole na zauna" ya fad'a tare da gyara zaman sa ya ci gaba "ni fa dariyar ce tazo min lokaci guda sakamakon nishad'in da nake ciki amma ba abun da ki ka fad'a ne ya sa ni dariya ba sannan maganar kayan da ake kawowa Zainab wannan gaskiya ne haka yake wanda ya ke son ta ne yake siya mata kuma auren ta zaiyi ya kusa zuwa kwanan nan za ku gan shi in sha Allahu". "Wanene shi"?. "Ki yi ha'kuri Hajiya ba zan iya fad'a miki ba za ki san shi amma ba yanzu ba sai lokacin da ya zo" ido Hajiya ta zuba masa ganin haka yasa yayi murmushi ya na cewa "ki yarda da ni gaskiya na ke fad'a miki" kai ta girgiza ta na cewa. "Ka ga Samar ba na son munafirci ka fad'a min waye"?. "Kaiii Subhanallahi Hajiya ki na da son ayi ta maimaita magana nace ba zan yi iya fad'a miki ba idan na yi haka ban ri'ke amanar da na dauka ba". "Har wacce amanar ce wannan kuma idan ba mutum ba ne ya za ka biya bashin aljani da ka ke d'auka irin wad'annan dukiyoyi"?. "Mutum ne man". "A ina ya ke d'an waye a garin nan"?. "Dan Allah Hajiya ki bar yi min tambaya a kan sa domin ko kashe ni za ki yi ba zan fad'i waye ba duk ranar da ya bayyana kwa gan shi" ya fad'a ya na mi'kewa hararar sa Hajiya ta yi tana cewa "kar ka fad'a d'in d'an me ba'kin hali wata uwar zan ce idan ka fad'a min ko kana tunanin zan cinye shi mayya ce ni"?. "A'a ni fa Hajiya ba ki ji haka daga baki na ba, duk abin da zan ce miki ba za ki ta'ba fahimta ta ba kawai sai da safe" ya na fad'in haka ya juya ya fita ya bar Hajiya ta na fad'a kamar ba za ta daina ba daga baya kuma tayi shiru tun da wanda ta ke fad'an dan shi ya tafi ba jin ta ya ke ba. ** ** YUSRAH MUSA ** ** Chat with me. +234 8160983083 WhatsApp number YMA DUTSE JIGAWA STATE. 1_💓Mai alfaharin jiha ta ce 2_🚗Ko'ina na ke inda zan zarce 3_🇳🇬A cikin Nigeria mu ke da gada mun taka kan Dutse 4_🌃Birnin daraja daya batse 5_🏜️Ga haske 6_🏞️🏔️Ga adon Dutse👍💙💃💚 💛JIGAWA TARON ALLAH💛 @YUSRAH MUSA PAGE 65 Baby ba ta ta'ba tunanin da gaske Shareef zai iya auren wata mace bayan ita ba saboda ganin irin sha'kuwar su ta d'auka idan yaga ta nutsu ta kame kan ta zai tausaya mata amma ta ga ba canji jiya iyau, Kamar kullum yadda ta saba yau ma lokacin da ta zo hospital ta ga motar sa amma kuma ta yi iya neman ta bata gan shi ba har ta ha'kura ta samu guri ta zauna tana zaune tayi tagumi 'kawarta Badiyah ta karaso gurin tana zama tace "ke Baby ina ta neman ki ashe ki na nan ban sani ba"? Kallon ta Baby ta yi cikin yanayi na rashin jin dad'i za ta yi magana Badiyah ta ce "tsaya ma na tambaye ki wai dama Shareef aure zai yi ne"? Sake d'agowa Baby tai jikin ta yayi mugun sanyi da'kyar tace "taya kika sani waye ya fad'a miki"? Wani d'an littafi ta d'auko daga jakar ta wanda bangon sa yake d'auke da sunan su alamar an yi mu su engagement mi'ka mata ta yi tana cewa "waye ya fad'a min kuwa bayan ga sheda nan na gani da ido na kalli man" kar'ba Baby tai hannunta na kakkarwa ta fara dubawa wani irin zaro ido waje tayi tana zabura a rud'e tace. "Mene wacece Nihal Alhaji Mustapha kuma"? Kai Badiyah ta girgiza tana cewa "oho duniya da fad'i taya zamu santa tunda ba a hospital d'in nan take ba amma dai kamar naji ance 'kanwar Doctor Ammar ce fa" kamar idon Baby zai fito waje ta ce. "Kanwar Ammar kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku" ta fad'a tana dafe kanta da yake juyawa tare da komawa da sauri ta zauna tana ri'ke kan da hannu biyu ta runtse ido sakamakon wani irin ciwo daya sara mata lokaci guda dafa ta Badiyah tai tana cewa. "Baby kina lafiya kuwa meya faru"? D'agowa Baby tai tana kallon Badiyah maimakon ta bata amsar data tambaye ta sai kawai ta fashe da kuka mamaki ne 'karara ya bayyana a fuskar Badiyah harta kasa gane me hakan yake nufi karshe tunani ya bata kodai son Shareef take shine dalilin wannan kukan nata shiru tayi ta zuba mata ido harta gaji ta share hawaye tana sau'ke ajiyar zuciya. "Wai Baby me ya ke faruwa ne kukan me ki ke yi"?. "Dole na yi kuka Badiyah 'kanwar Ammar fa me saka glass d'in nan wacce kwanan baya muka ganta tare da kanwarta harta buge mata glass d'in ya fad'i Shareef ya fito ya d'auka ya ba ta" kai Badiyah ta jinjina ta na cewa "kenan dama son ta ya ke" zazzafan huci Baby ta fitar tana sake kallon littafin memo d'in ta cije lips cike da takaici ta ce. "Taya zan sani bayan ba fad'a min yayi ba amma sai dai daga baya yake sonta domin ranar haduwar su ta farko bai santa ba a kanta har fad'a mu kai da shi ban manta ba" d'an murmushi Badiyah ta yi ta na cewa "abun mamaki zuciya kenan mai son abinda take muradi daga had'uwar su shikenan nan ya kamu da son ta irin haka ake so wallahi ka so mutum dan Allah" jin abinda Badiyah tace yasa Baby sake cije lips d'in ta har ta fara huda shi da ha'kori amma ko zafin ba ta ji rad'ad'in da ya ke cin zuciyar ta yafi wanda ta ke ji akan lips d'in na ta kallon Badiyah kawai take cikin takaici tace "na rasa me yasa Shareef yayi min haka meye bana dashi meye zanyi ya burge shi ya rasa a inda gayun nasa zai 'kare sai a kan nakasasshiya me ciwon ido ki na kallo fa a ranar da 'kanwar ta ta, ta buge mata glass d'in bata gani fa saida shi in ta cire kamar dare haka take ba ta ganin komai" jinjina kai Badiyah ta yi tana cewa. "Eh a hakan yaji zai iya zama da ita baki san dalilin sa ba akwai abinda yasa ya za6i ya aure ta kuma ya kamu da son ta". "Ba wani dalili Badiyah dan ya wula'kanta ni yayi haka nasan shine dalilin sa ba komai ba yana so ya nuna min idan ni bansan ciwon kaina ba ga wacce ta cancanta zamowa abokiyar rayuwarsa ne". "To ke meye ruwan ki a ciki ko son sa ki ke"?. "Ke za'a yi wa wannan tambayar idan ina son sa ma kin sani idan ba na son sa nan ma kin sani shekarar mu nawa tare da ke a hospital d'in nan ina da wata 'kawar bayan ke"?. "A'a ba ki da ita amma Baby a tunani na sirrin zuciya sai me ita taya ba ki ta'ba fad'a min ba kawai zan san ki na son sa? Amma yanzun na fahimta sai dai zan baki shawara dan Allah ki cire damuwar dake damun ran ki wai tsaya ma na tambaye ki kina kallon fuskar ki a mirror kuwa kin ga yadda ki ka koma kamar skeleton". "Hummmm!!" Kawai shi ne abin da Baby ta ce domin a halin yanzu yadda take ji ba ta san da yadda zata kwatantawa Badiyah ta fahimta ba ita kuma da take jin zafin da ciwon ba ta san ya zatai ba sake sau'ke ajiyar zuciya ta yi ta na mi'kewa ta ce "ina zuwa yanzu zan dawo". "Ok" Badiyah ta ce Baby kuma ta bar gurin cikin hospital d'in ta shiga sosai ta ri'ka tambayar doctor's da nurses ta na neman sa har sai da ta samo shi ya na can yaje wajen wani abokin sa a 6angaren 'yan surgery tuni zuciyar ta ta fara tashi ta na yun'kurin amai sakamakon kallon mutanen da su ke gurin gabadaya abun ba kyan gani da'kyar ta wuce ta shiga ciki su na office tare su na magana ta shiga da sallama tare da tsayawa daga jikin kofar ta na kallon Shareef wanda shi ma yake kallon ta tace. "Shareef dan Allah ina so za mu yi magana". "Ok nan ma maganar mu ke ki jira ni a waje ina zuwa". "Wai a gurin wad'annan 'yan surgery masu 'konannan jiki zan jira ka"?. "Eh idan ba za ki iya ba ki tafi can wajen office d'ina ina zuwa". "Gaskiya sai dai na tafi can d'in na jira ka amma wa zai iya kallon wannan kayan 'kyan'kyami haka" kai ya jinjina yana d'agowa ya kalle ta ita kuma ta juya ta fita ta bar sashin a wani guri inda wasu kafafun kujeru su ke ta zauna ta na jiran sa kafin ya fito jin ana kiran wayar ta yasa ta fito da ita daga cikin jakar ta ganin Badiyah ce ya sa ta ja tsaki ta na maida wayar ta d'auko ruwa ta bud'e robar shi ma kur6a kad'ai ta yi ta mayar ta d'aure ta d'auki karamin towel ta goge bakin ta tare da kallon agogon da yake hannun ta taga lokacin tashi ma ya yi dafe goshi ta yi tana buso iska daga bakin ta tare da mi'kewa ta fara zaga gurin kafin ya fito ta d'an jima amma har lokacin shiru tunani ta fara yi kodai ba zai fito bane shanya ta ya yi ta na cikin haka ta hango shi sun fito tare da wancan doctor d'in ya mi'ka masa hannu sun gaisa ya koma Shareef kuma ya taho wajen inda ya gano ta numfashi ta sau'ke ta na d'aukar jakar ta, ta nufe shi fara tafiya su kai akan doguwar verandah irin ta asibiti. "Uhum fatan dai lafiya ina jin ki me ya faru"? Dakatawa da tafiyar da take ta yi ta na fuskantar sa sosai ta zuba mi shi ido kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce. "Shareef da gaske ne"?. "Da gaske ne me"?. "Da gaske ne aure za ka yi"? Zaro ido ta yi farko da ta ga ya girgiza masa kai ta d'auka ko bai san da zaman wancan littafin ba har ta fara jin sanyi a ran ta sai kuma ta ji ya ce. "Ana aure da wasa ne"?. "Kenan abin da na gani d'azu ba 'karya ba ne"?. "Me ki ka gani"?. "Memo na engagement d'in auren ka da wannan yarinyar". "Wacce yarinya kenan"?. "Kai zan yiwa wannan tambayar tun da ka fi ni sanin ta ai" kai ya jinjina su na ci gaba da tafiya ya ce "ya yi kyau" daga haka bai sake magana ba ita ma shiru ta yi tunani iri-iri sun cika mata zuciya har su ka 'karasa ya rufe office d'in sa sannan su ka je wajen aje motoci tana tsaye ya shiga ya tafi ba maganar da ta sake had'a su kamar ta had'iyi zuciya ta mutu haka take wani irin takaici da d'aci ya na ma ta yawo a ma'kogoro da'kyar ta tafi gurin motar ta ita ma ta shiga ta nufi gida tu'kin ma ba sosai take kula da titi ba hankalin ta duk nema ya ke ya fita daga jikin ta kafin ta je gida zazza'bi ya rufe ta, ta na parking kuwa ko key ba ta zare ba balle ta tsaya d'aukar handbag kawai kofar parlon su ta bud'e ta shiga Mom d'in ta tana zaune ganin a yadda ta shigo tana layi kamar wacce tasha abun maye yasa tasowa da sauri ta na cewa "Subanallahi Baby ke Baby lafiya"? Ba ta iya ba ta amsa ba sakamakon idonta ya gama rufewa ba'ki kawai take gani luuuu hajijiya ta d'ebe ta tayi baya zata fad'i da sauri Hajiya Fatima ta tare ta tana ri'ke ta a jikinta tare da 'kwalla kiran........🖋️ Typing sai gobe in sha Allahu. ZUCIYAR ALIYU CE. ................PAGE 66 "Aminah Aminah ki na ina sauri ki zo" da sauri wata mace ta fito daga wata kofa da kayan aiki a jikinta da alama kitchener ce karasowa tayi tana cewa "gani ranki ya dad'e" a rud'e Hajiya Fatima tace "d'auko min ruwa a fridge yanzu kiyi sauri Baby ce ta ke suma" juyawa tayi ta gudu ta d'auko mata kar6a tayi ta bud'e ta d'an tsiyaya ta shafa mata a fuska ta 'kara shafa mata shiru kamar gawa sai numfashin ta da yake kai komo shi ne kad'ai zai tabbatar maka tana da rai kusan awarsu guda sannan ta sauke nannauyan numfashi amma ba ta bud'e ido ba cikin kulawa Hajiya Fatima ta d'an girgiza ta tana cewa. "Baby Baby bud'e idon ki" a hankali Baby ta ke jin tashin maganar mahaifiyar tata da'kyar ta bud'e idonta da sukai nauyi suka zama ja tana kallon ta kafin ta yun'kura a hankali ta tashi zaune d'aga ta Hajiya Fatima ta yi ta 'karasa shiga da ita parlon ruwan dake gora na hannun ta, ta mi'ka kur6a d'aya tayi ta aje tana dafe kai ido Hajiya Fatima ta zuba mata tana mamakin meya sameta ta fita lafiya 'kalau ta dawo a haka. "Baby ki na lafiya"? Kai ta girgiza numfashin ta na fita da zafi ta ce "Mom kai na ciwo ya ke kamar zai fashe jiki na da zazza'bi na dawo zuciya ta zafi ta ke min" ta fad'a ta na dafe saitin zuciyar ta zaro ido Hajiya Fatima ta yi tana kallon ta ta ce "Subanallahi har da zafin zuciya Baby wai me ya same ki ne nasan dai lafiya kalau ki ka fita daga gidan nan ko wa ya 6ata miki rai fad'a min"? Shiru Baby ta yi hawaye ya na zuba mata da ace yadda take samun komai daga gurin mahaifan ta yadda ba ta san rashi ba ina idan ta sanar musu su yi 'ko'kari su taimake ta kar ta rasa Shareef a rayuwa yardar sa da auren sa kawai yanzu shi ne matsalar ta............... "Wai Baby ba za ki fad'a min abin da ya ke damun ki ba ki na ganin kukan shi ne mafita"? Kai baby ta girgiza ta na cewa "koda na fad'a miki ba ki da maganin matsala ta Mom duk duniya ba wanda zai iya min maganin ta sai Allah". "To ai ke ki na da matsala kuka ba zai kai ki ba tashi za ki yi kije ki yi alwala sai ki yi sallah ki fad'awa Ubangiji damuwar ki zai yaye miki duk wani ba'kin ciki da ki ka tsinci kan ki haba dan Allah kamar bakya zuwa islamiyya ya kamata ki dawo hayyacin ki mana komai yai zafi maganinsa Allah ne ki share hawayen ki, ki tashi ki je kiyi sallah" kai Baby ta d'aga tare da mi'kewa ta shiga part d'in ta shiru Hajiya Fatima ta yi cike da tunanuka iri-iri a ran ta akan abin da ya ke damun Babyn tun da har ta ga ta'ki fad'a mata to fa ba 'karamin abu bane. Ta na nan a zaune har Daddy ya shigo shi ya sa ko numfashi bai gama saukewa ba ta fad'a masa komai ya ce ta kira masa Babyn tashi ta yi ta shiga kamar yadda take tunani haka ta tarar ta a zaune ta zuba uban tagumi da hannu biyu ta yi shiru kai ta girgiza ta na cewa. "Baby". Shiru ba ta amsa mata ba alamar tunanin da take ta yi zurfi 'karasa shiga Hajiya Fatima ta yi ta na d'an girgiza ta ta ce "Baby" a firgice ta d'ago da jan idon ta tana kallon Hajiya Fatima wacce ta ce "wai ke meye haka ne sai kin kashe kan ki yau d'aya mtwwww ki zo Daddyn ki ya dawo ya na son ganin ki" ta na fad'in haka ta juya ta fita ajiyar zuciya Baby ta sau'ke tare da mi'kewa jiki a sanyaye ta fita tun su ka ganta duk su ka zuba mata ido kowa cike da tsantsan mamakin yadda ta mayar da kan ta abar tausayi lokaci guda, zuwa ta yi ta zauna tare da yin 'kasa da kan ta tace "Daddy ina yini"? Kai ya jinjina ya na cewa "lafiya 'kalau daughter me ya same ki ne yau"? Jin tambayar da ya yi mata yasa ta 'kara 'kasa da kan ta ba ta ba shi amsa ba". "Ok ba za ki fad'i abin da ya ke damun ki ba sai na kira miki Hakeem ko"? Jin ya ambaci Hakeem yasa ta girgiza kai da sauri ta na cewa "dan Allah Daddy ka yi ha'kuri". "Na ji amma zan ha'kura ne kawai idan har ki ka fad'a min gaskiyar lamari me ya ke damun ki"? Hawaye ne ya fara zuba mata bakin ta ya'ki bud'uwa balle ta samu damar iya fad'a masa kuka kawai ta fara yi tun ta yin sa a hankali ciki-ciki har ya fito fili daskarar da su ta yi suka saka ta a gaba kamar TV su na kallon ta babu wanda ya ce ta yi shiru a cikin su waya Daddy ya d'aga ta ji zai yi kira cikin kuka ta ce. "Dan Allah Daddy kar ka kira Yaya Hakeem ka bari zan fad'a maka ba ni da lafiya zazza'bi na ke yi"? Ta na rufe baki cikin fad'a Hajiya Fatima "aww zazza'bi zazza'bi ki ka ce shi ne ya ke damun ki wato Baby ba za ki fad'a ma na gaskiya ba ko"? Sosai ta ke kuka Amma taya za ta iya fad'a musu gaskiyar lamari su gane akan namiji ta mayar da kan ta haka, ganin ba daina kukan za ta yi ba ya sa Daddy mi'kewa ya na cewa "tashi mu je". "Ina za ku je Alhaji" 'kofar fita Daddy ya nufa ya na cewa "zan kai ta asibiti ne idan mu ta'ki fad'a mana tun da ba mu kai ba likita zai fad'i duk abin da ke damun na ta" jin abin da ya ce yasa Baby girgiza kai a susuce ta ce "Daddy please let me tell yo................. Tsawar da ya buga mata ya sa ta sake rud'ewa da gudu ta mi'ke tana 'kan'kame Hajiya Fatima cikin tsoro ta sake fashewa da kuka huci Daddy ya fitar ya na nuna ta da yatsa zai yi magana Hajiya Fatima ta yi masa nuni da ido alamar ya yi ha'kuri kar ya ce komai amma duk da haka sai da ya ce. "Ni za ta mayar 'karamin mutum har ina tambayar ta me ke damun ta tayi banza kin san........ "Alhaji please dan Allah shittttt" Hajiya Fatima ta fad'a ta na d'ago da Baby ta goge mata hawayen sannan ta ce "ki je ku tafi" kai Baby ta d'aga cikin tsoro ta kallo Daddy wanda ya ja tsaki ya na juyawa zai fita ya ce "ina jiran ki a mota" bin bayan sa ta yi su ka fita ta d'auka ko a mota zaiyi mata wata tambayar sai kuma ta ji ya share ta har ya kai ta wani private hospital aka duba ta iya dubawa akai mata binkicen tsaf sannan ya ke6e da doctor d'in ya fad'a masa komai mamaki kamar zai kashe Daddy haka ya 'kure Baby da kallo kamar ba zai daina kallon ta ba daga baya ya jinjina kai ya na yiwa Doctor godiya su ka fito su ka dawo gida. Kamar yadda takaici ya kama Daddy a hospital ita ma haka Hajiya Fatima ta ji bayan ya yi mata bayani kallon Baby wacce ta sunkuyar da kai ta yi tana cewa "tabd'ijan anya Baby kina da hankali akan saurayi ki ka d'orawa kan ki hawan jini waye shi a ina ya ke me ya ke da shi wanda ki ka nace a son shi har cuta ta shige ki"? Shiru Baby tai kan ta a 'kasa ta kasa d'agowa ta fuskance su saboda kunyar abinda ta aikata cikin fad'a Hajiya Fatima ta ce "wai ba magana nake miki ba waye shi ko ba ki jini ba"? Rawa muryar Baby ya ke da'kyar ta iya ce wa. "A.a.h.hospital d'in mu ya.ya.ke". "Humm a hospital d'in ku ko? Da kyau kin kyautawa kan ki ai shi ya na can lafiyar sa kalau hankalin sa kwance ke kuma ga ki kin kamu da jinya uban waya fad'a miki ana damuwa da wanda bai damu dakai ba ko tare ki ke da mutum ya nemi fita daga rayuwar ki ke kiyi gaggawar cire shi in da hali ma ki dad'a masa da kud'in mota uwar me zai baki shi wancan yaron me ki ka nema ki ka rasa da har za ki hallaka kan ki a banza shashashar yarinya kawai wannan ai ba ki san ciwon kan ki ba kuma bakya kishin kan ki da ki na son kan ki da arziki ba za ki fara son wanda ba ya son ki ba aikin banza aikin wofi ki ci gaba kar ki fasa son shi ki gani idan riba za ki samu ke idan ba tsabar gidahumanci ba ke fa mace amma ki ka kasa ri'ke martabar ki to ga Daddyn ki nan ki tambaye shi wuyar da yasha kafin na amince masa kuma ba wai dan ba na son sa sai domin mata an san mu da aji amma ke dai Baby kin ji kunya saboda wani namiji har ki ka damu da shi ciwo ya kama ki kai jama'a wannan asarancin har ina domin wannan kam asara ce ba komai ba"? Ta 'kasara maganar tana sakar mata harara ganin da Alhaji Abubakar yayi ran Hajiya Fatima ya 6aci sosai gashi ta saka ta a gaba da fad'a hakan ma zai sake haddasa mata wani ciwon shi ya sa ya ce "ya isa haka Fatima kiyi shiru na fahimta zan yi magana da ita daga baya wannan abun mu bar shi matsayin jarrabawa dan haka Baby kiyi 'ko'karin ciyewa karki bari shed'an yaci nasara a kanki aiki kuma daga yau na soke shi a wancan hospital d'in zan sa ayi miki transfer zuwa wani daban". Shiru Baby tai hankalinta a mugun tashe domin maganar gaskiya koda ace zata iya ha'kura da Shareef baza taso a cire ta daga hospital ayi mata canjin wani ba amma yanzu baza tayi jayayya ba zata yi ha'kuri zuwa d'an wani lokaci idan komai ya lafa ta samu Daddyn ta ro'ke shi ya barta taci gaba da aikinta acan indai ba haka ba gara ta ha'kura da aikin gabadaya akan ayi mata transfer ta koma wani gurin............... "Baby" ta ji ya kira sunan ta a hankali ta ce "na'am Daddy". "Kin ji hukuncin da na yanke ko"? Nan ma kai ta d'aga da'kyar ta ce "eh Daddy". "Ok yayi tashi ki je kuma ki kula sosai wajen shan maganin ki kin ji"? Kaita d'aga ta na mi'kewa a sanyaye ta shiga bedroom d'in ta Hajiya Fatima wacce ta had'e rai bayan wucewar Babyn ta ce "ni fa wallahi yarinyar nan ta bani takaici lokacin da ka ce doctor yace wai ciwon so ne ya haddasa mata hawan jini shi kad'ai ne namiji a duniya ga masoya nan da yawa sai kace wacce ta yi kwantai ko am fad'a mata mun gaji da ita ne har za ta fara neman kai namiji ya na mata yawo da hankali". Murmushi Alhaji Abubakar yayi yana kallon ta yace "baki ji ba aka ce soyayya gamon jini to jinin ta ne ya kaita inda zata sha wahala shiyasa ba don haka ba zai amince mata ko kad'an banga laifin sa ba domin ba'a so dole kamar yadda ita ta d'auka a ranta" da mamaki Hajiya Fatima ta ce. "Yanzu kenan da ace mutuwa ta yi ma za ka ce laifin ta ne"? Kai ya jinjina alamar confirm ya ce "kwarai ma kuwa to tsaya na tambaye ki laifin waye a cikin su shi ko ita na tabbata duk tsiya ya san tana son sa kuma ba zai bar ta tayi ta sonsa ba tare daya fad'a mata ba gaskiyar yana sonta ko baya sonta ba wai ke kin manta wace Baby ne akan naci"? Ajiyar zuciya Hajiya Fatima ta sau'ke tana cewa "idan na fahimta dai goyon bayan yaron da ko sanin sa ba kai ba ka ke yi akan 'yar da ka haifa haka ne"?. "No Hajiyan fassara ban goyi bayan sa ba kada ma kiyi wannan tunanin gaskiya ce nake fad'a a matsayin na uban dukkan su biyu ni d'an wani ma nawa ne kin gane"? Gyara zama ta yi tana cewa "shikenan" kawai shine abinda tace tana yin shiru daga haka kallon ta ya yi yana cewa. "Shikenan kin ji haushi kenan"?. "A'a ko d'aya". "Sai biyu"?. "Kamar ya"?. "Kamar yadda ki ka ji nace ba ko d'aya ki kace ba shiyasa nace miki sai zero tun da ko d'aya babu" 'yar dariya tayi tana kallon sa tace "kai wallahi Alhaji kana da barkwanci idan mutum ya zauna dakai ko mai 'kin son dariyar sa sai yayi". "Uhm gara na kasance me baiwa mata ta nishad'i idan ban saka ki dariya ba wa zan saka"? . "Babu fa ni d'in ce dai". "To kin gani yanzu tashi mu je ki had'a min ruwan wanka" "ok to" ta fad'a tana mi'kewa gaba ya wuce ta bi bayan sa su ka shiga part d'in sa. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA 08160983083 WhatsApp number. J.W.A PAGE.............67 Yau Zainab ba ta kwanta da wuri ba domin saida ta gama d'inkawa wasu 'yan mata biyu d'inkin su, su ka jira ta saka musu stone sannan su ka kar6a su ka tafi shi ya sa da ta yi wanka kawai ta domin idon ta har rufewa ya ke tsabar yadda barci ya cika su. Aliyu bai fad'awa kowa zai dawo gari ba ya yi saukar dare ya kira daga gida aka je airport aka d'auko shi lokacin duk 'yan gidan sun yi barci shi ya sa ya na shigowa bai nemi kowa sun gaisa ba sakamakon a mugun gajiye ya ke ga shi kuma dare ya riga ya ja sosai wanka ya yi ya kwanta shi ma. Duk da irin barcin da Zainab ta ji ya na damun ta da dare amma asuba na yi ta tashi ta yi alwala ta yi raka'atanil fajri ta yi 'yan addu'o'i sannan masalatai sun fara shiga sallah ta mi'ke ta bi masallacin kusa da su bayan an idar ta sake yin addu'a jin yadda idon ta yake zafi ta san barcin ne bai ishe ta ba shi ya sa ko sallayar ba ta nad'e ba hijab kad'ai ta cire ta koma ta kwana a take kuwa barci ya sake kwashe ta. 😃Dream works😃 Farkawar ta kenan ta d'ora idon ta akan fuskar Aliyu wanda ya ke barcin sa hankali kwance hannun sa ta kalla ganin yadda ya zagaye ta a jikin sa ya rungume d'an murmushi ta yi ta na shafa gashin girar sa tare da busa masa iska a hankali d'an motsawa ya yi amma maimakon ta ji ya sake ta sai ta ga ya sake sabon juyi ya na dad'a jan ta tare da cusa fuskar sa a gefen wuyan ta shiru ta yi ta zuba masa ido kamar me tunani can kuma ta juyar da hankalin ta kan agogo ta ga sha d'aya saura minti biyu rufe baki ta yi tare da yun'kurawa za ta tashi ya ri'ke ta, duk tunanin ta ko tashi ya yi sai taga idon sa a rufe har lokacin kama hannun nasa ta yi a hankali ta janye shi daga ri'kon da ya yi mata ta mi'ke ta na d'auke 'kafa saboda kar ta tashe shi ta shiga toilet murmushi Aliyu ya yi lokacin da ya ji ta rufe 'kofa dama ba barci ya ke ba tun lokacin da ta shafa gashin girar sa ya tashi kawai dai ya'ki bud'e idon ne kuma ya'ki nuna mata ya tashi d'in ta na fitowa ta sake kallon kan gadon ta ga ya sake salon sabuwar kwanciya ajiyar zuciya ta sau'ke ta na wucewa ta tafi gaban mirror ta d'auki 'karamin towel kenan za ta fara goge ruwan jikin ta, kawai ta gan shi tsaye a bayan ta da mamaki tace "Wai dama ba barci ka ke ba"? Gira ya d'auke ya na cewa "uhmm ta ya zan iya barci bayan kin tashi a kusa da ni ki dawo mu kwanta" ya fad'a ya na juyawa ya koma gadon ya kwanta ta cikin mirron ta kalle shi ta na cewa "na ga sha d'aya ta yi ne kuma ban je na gaida Momy ba". "Ok ki na nufin yanzun hakan wanka ki kai gurin Momy za ki je? Ai kuwa wannan wankan na ki bai wanku ba domin yanzu zan sake 6ata shi" tsayawa ta yi ta na aje towel d'in da ta gama goge jikin ta ce "da me kenan"? Ta tambaya tare da juyowa ta na kallon sa murmushi ta ga ya yi mata yana tashi daga kwancen da ya ke ya taho gaban mirror inda ta ke tsaye ya na 'karasowa ya ri'ke towel d'in ke d'aure a jikin ta ya ja zaro ido ta yi ganin ya na neman kissing d'in ta tace "A'a Aliyu kar k............................... Kai ya girgiza mata ya na janye hannunta da ta ri'ke na sa ba tare da ya yi magana ba ya matso ta jikin sa sosai ya manna ta ya na d'ago fuskar ta ya ri'ke lips d'in ta ya fara kissing d'in ta. 🙊Hummm!!! kan babbar butar shayi🙉 wannan mafarki ya yi dad'i d'and'anon shi coiiii🙈. ME KU KE TUNANIN ZAI FARU IDAN ZAINAB TA FARKA DAGA WANNAN ZAZZA'KAN MAFARKIN NA TA?😁 MU JE ZUWA NEXT PAGE. 💓 ZUCIYAR ALIYU CE 💓 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION. J.W.A @YUSRAH MUSA PAGE 68 Wani irin tsalle Zainab dake kwance akan katifar ta, ta yi ta na cillar da bargon da ta rufu dashi tare da fasa wata firgitacciyar 'kara a gigice ta ce "wayyo Allah na shiga uku Aliyu me ye hakan wayyo Allah wayyo Umma ki taimaka min ya shigo min d'aki" gabadaya tabi ta firgice ko sanin cewa a cikin d'akinta ta ke ba ta yi ba sai had'e kai da gwiwa da ta yi ta na 'kan'kame jikin ta guri d'aya Umma ta na d'akin ta, ta jiwo 'karar ta da sauri shigo d'akin ta na cewa. "Zainab Zainab lafiya ihun me ki ke me ya faru"? Ganin ta tayi a takure a can jikin bango jikin ta sai kakkarwa ya ke "Zainab lafiya kuwa"? Umma ta sake tambayar ta tana 'karasawa ta d'ago da fuskar ta wacce ta ji'ke da hawaye da mamaki Umma ta ce. "Subanallahi wai me ya faru ne kukan me ki ke"? Kasa magana Zainab ta yi sai kai da take girgizawa hawaye sharr sharr ya na zuba mata ganin ba ta ce komai ba ya sa Umma ta ce "to ba ki fad'i me ya ke damun ki ba kuka maganin me zai yi miki na tambaye ki kin yi shiru"? Da'kyar ta na shashshe'ka ta ce. "Ba komai". "Ba komai kuma amma ki kai 'kara gashi na shigo na same ki kina kuka sai ki ce ba komai ki fad'a min me ya faru"? Sake girgiza kai ta yi ta na cewa "ba komai Umma mafarki na yi"? Baki Umma ta bud'e ta na kallon ta tace "mafarki kuma"?. Kai ta d'aga sabin hawaye masu zafi su na 'kara gangaro mata dafa ta Umma ta yi ta na cewa "wanne irin mafarki da har zai sa ki kuka"?. "Umma mafarki ne kawai abin da ya faru a mafarkin ne ya d'aga min hankali har na yi 'karar ban sani ba kuma sai da na farka na gane ba a gaske ba ne" kai Umma ta jinjina ta na "amma da alama kamar mummunan mafarki ki kai ko tun da na ga ki na kuka". "Eh Umma ba me kyau ba ne ki taya ni da addu'a Allah ya sa ya tsaya a iya mafarkin kar ya zama gaskiya domin ba na fatan hakan a rayuwa ta" kai Umma ta d'aga ta na cewa "shikenan ba komai Allah ya rufa asiri Ubangiji ya sa ba gaskiya ba ne" da sauri Zainab ta ce "Amin" tun da ta san addu'ar iyaye akan 'ya'yan su kar6a66iya ce juyawa Umma ta yi ta fita ta na cewa. "Allah ya kyauta kar ki saka mafarkin da ki kai a ran ki duk da ba gaske ba ne amma wata rana ya na zama gaskiyar" shiru Zainab ta yi ta zubawa guri d'aya ido bayan fitar Umma kawai abun ya fara dawo ma ta sabo gani ta ke kamar a gaske ne komai ya faru runtse ido ta yi ta na cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un mafarkin Aliyu kuma me ye had'i na da shi da har zan saka shi a rai na, na yi mafarkin sa kuma mafarkin nasa ma na rasa wanne kala zan yi sai na gan ni matsayin matar sa? Matar sa fa"? Tuna abin da ya faru a cikin mafarkin ya sa wasu zafafan hawaye su ka fara zuba mata ji ta ke dama da ta yi sallar asuba ba ta koma barcin nan ba da ace irin wannan mafarkin za ta yi gara ta ha'kura da kwanciyar. °°°•••°°°•••°°° Fitowar Fati kenan daga part d'in su ta na hamma za ta nufi dinning ta tsaya cak ta 'kame guri d'aya ganin wanda ya ke zaune a dinning d'in tare da Momy rufe baki ta yi ta na zaro ido a hankali ta juya cikin sand'a ta koma bedroom d'in su da gudu ta na shiga ta fara 'kwalla kira. "Aunty Afifah kin tashi ne ko har yanzu barcin ki ke na zo miki da albishirir"? Afifah da ke kwance jin yadda Fatin ta ke 'kwalla mata kira kamar ba lafiya ba ya sa ta ce "ga ni fa ya akai? na tashi man" kai Fati ta jinjina ta na waiwayen bayan ta kamar shi ne ya biyo ta ta ce. "Aunty Afifah kin kuwa san Yaya boss ya dawo" tashi daga kwancen Afifah ta yi ta na zaro ido ta ce "wanne Yaya boss d'in amma dai yanzu ya dawo ko"?. "A'a ina yanzu ai ina ganin a gida ya kwana". "Ganin sa ki kai da idon ki"?. "K'warai a parlor ba ya na zaune a kusa da Momy a dinning su na breakfast yanzun nan ban 'karasa ba na dawo na fara miki ki fita da shirin ki" dafe goshi Afifah ta yi ta na cewa "Subanallahi ji Yaya discipline da wani tsari shi d'in meya dawo da shi"?. "Ta ya za mu sani maybe hutu ya sake zuwa bari na koma domin breakfast zan yi yau da yunwa na tashi jiya na kwanta ban ci abinci ba" ta fad'a ta na 'ko'karin fita sai kuma ta sake juyowa ta na cewa "please Aunty Afifah ki wanke fuskar ki sosai kar ya gane barcin safe ki ka koma tun da kin san ya hana" mi'kewa Afifah ta yi ta na cewa "tabbas na sani ga Yaya discipline akwai saurin gane yanayin mutum bari kawai ko zuwa jimawa na fita sannan idon na wa ya gama wartsakewa". "Ok" Fati ta ce ta na bud'e 'kofa ta fita tare da le'kawa ta ga iya Momy ce a parlon sai Elham sauke ajiyar zuciya ta yi ta na cewa "yauwa masha Allah haka na ke so" 'karasa fitowa ta yi tana gaida Momy sannan ta wuce dinning Elham da ta bi ta da kallo ta ce. "Ke Teemoh kin san Yaya boss ya dawo kuwa" kai Fati ta jinjina ta na zama ta ce "ni kuwa na san ya dawo tun da na gan shi da ido na". "Au kin gan shi kenan"?. "Na gan shi man tun d'azu ina fitowa fa na gan su tare da Momy a dinning shi ne na juya na je na fad'awa Aunty Afifah" dariya Elham ta yi ta na cewa"au ta sani kenan ai da kin 'kyale ta kamar yadda kowa ya fito ya gan shi ita ma ta fito su had'u". "A'a ba zan iya yi wa Aunty Afifah haka ba da amana me 'karfi tsakanin mu kuma nasan ita ma da ita ce ya dawo ban sani ba za ta fad'a min". "Da gaske? Sannu radio me jini". "Ba wani maganar radio me jini wannan taimakon kai da kai ne". "Uhmm na ji wannan saura wanne"? Tun kafin Fati ta yi magana Momy ta ce "gara ki tsaya ki nutsu ki yi breakfast me kyau da ki ka zauna ki na biye Elham ita ta yi na ta ke kuma ta dame ki da tambaya ki na bata amsa abincin ko dad'in sa ba za ki ji ba" kallon Elham Fati ta yi taga ta na masa dariya harara ta saka mata ta na cewa. "Zan rama ko ba yau ba" gwalo Elham ta yi mata ta na cewa "ai kuwa ba ki isa ki rama ba sai dai ki rame ki 'kai'kashe". "Tom shikenan za ki gani" ta fad'a ta na mayar da hankalin ta, ta share Elham d'in kamar yadda Momy ta ce su na zaune Afifah ta fito ita ma ta na le'ke-le'ke kallon ta Momy ta yi ta na cewa "lafiya"? Kai ta girgiza ta na cewa "ina ya ke"?. "Wa ye"?. "Yaya discipline". "Ok ko saboda shi ki ka fito ki na wannan le'ken"?. "Dole na le'ka Momy kar na je ya na kusa". "A'a shi kam ba ya nan ya fita tun d'azu" ajiyar zuciya Afifah ta sau'ke ta na cewa "yauwa har na ji dad'i haka na ke son ji bari mu zo mu bararraje mu ci abin da ran mu ke so cikin kwanciyar hankali". "Idan ya na nan ma ba zai hana ki yi abun da ki ke so d'in ba". "Eh amma ba kamar yadda mu ke free haka ba Allah ya sa wannan karon ma Afif ya dawo ni sai na huta" kai Fati ta girgiza ta na cewa "a'a ba Amin ba wallahi haba Aunty Afifah ya dawo ki samu hutu mu kuma mu shiga rud'u mutum biyu sun had'e ma na lokaci guda ko"? Murmushi Afifah ta yi ta na cewa. "Eh man 'yar gari ashe kin gane indai ni zan huta komai normal ne" numfashi Fati ta sauke ta na cewa "a gurin ki ba amma mu kuma fa mu yi yaya kenan"?. "Oho ku, ku ka sani wannan matsalar ku ce in kun ga dama ku bar gidan ko ku yi zaman ha'kuri da su". "Ahhh lallai kam to ai tun da haka ne sai mu kama kan mu kafin Yaya ki sa Yaya Afif d'in ya dawo" Fati ta fad'a tana mi'kewa ta bar gurin dinning d'in ta tafi cikin parlor inda su Momy su ke ta na jin Afifah ta na mata dariya ta 'kyale ba ta sake bi ta kan ta ba. Zainab kuwa tun da ta gama kukan mafarkin da ta yi ta mi'ke ta fito waje ta d'an taya Umma ayyuka da su ka gama ta koma ta gyara d'akin na ta, ta saka turaren wuta ta saki labulen window da na 'kofa wata 'katuwar tabarmar Umma ta d'auko ta shimfid'a a waje ta fito da keken d'inkin ta aje saboda haka kawai yau ta ji ta na son zaman waje ta yi d'inki duk da akwai sanyi bayan sun karya ta had'a kwanukan ta wanke ta kai kitchen wankan safe ta yi harda 'yar kwalliyar ta lipstick da powder ta saka kwalli sannan ta saka doguwar riga fara tas ta yi rolling da mayafin rigar shi ma fari akwai adon golden a jikin sa kamar yadda ita ma rigar akwai stone a jere ta gaban rigar fitowa ta yi bayan ta gama shiryarwa ta hau keke ta fara d'inki. Bilki da ta fito daga d'aki da jaka a hannun ta zata bi Asabe gidan su tun da ta tafi biki ba ta dawo ba shi ya sa yau ta shirya idan ta je sai su taho tare ganin yadda Zainab ta d'au wanka ya sa ta ta'be baki sai da ta zo saitin ta sannan ta tsaya ta na mata kallon uku saura kwata ta ce "hum'um an ji kunya dai wallahi anyi asara duk wannan kyawun a banza sai dai aci kwalliya ba gurin zuwa kuma ba wanda zai gani ya yaba balle ya ji kin burge shi kodan dama wa za ki burge sai dai ki burge keken na ki idan kuma neman saurayi ki ke ai ba wanka za ki yi ki zo ki hau kan keke ba gari zaki mi'ke ki shiga watakil idan kin dace ko d'an bola ki samu ya aure ki" jin abun da Bilki ta ce ya sa Zainab d'agowa ta na kallon ta tace "ke Bilkisu ki kama kan ki ban damu da ke ba kar ki kuskura tsautsayi yasa ki sake fad'a min irin wannan maganar wallahi kin ji na rantse sai na miki mugun duka a gidan nan" dariya Bilki ta yi ta na cewa. "To fa sannun ki da 'ko'kari wa za ki wa mugun dukan amma dai ba da ni ki ke ba domin ni dai ba zan 'kyale ki ba sai dai mu daku tare amma ke dai ba zan ta'ba tsayawa ki iya duka na ba" kai Zainab ta jinjina ta na mayar da hankalin ta kan aikin ta ta na cewa "tun da ki na ganin ba zan iya d'in ba ki ci gaba idan kin isa ki sake fad'a min wata banzar magana anan wajen ki ga yadda zan yi da ke" nuna kan ta Bilki ta yi ta na cewa "ba yadda za ki dani nan gani nan bari ni Bilkisu na fi 'karfin ki fad'a da ni sai kin shirya domin yanzu na yi miki nisan da ko kin hau tsani ba za ki taro ni ba 'karshen wasan ba zai wuce ki had'a ni da Yaya Sameer ya dake ba to bari ki ji 'karyar ki tasha 'karya mai duka na a yanzu sai ruwan sama amma ba dai wani d'a ba". "Ya yi kyau tun da har kin yarda da kan ki ba me iya dukan ki sai ruwan sama dan Allah ki sake fad'a min irin maganar da ki ka fad'a min lokacin da ki ka tsaya anan ni kuma yau sai na targad'a ki a gidan nan" bud'e baki Bilki ta yi za ta yi magana Sameer ya shigo da sauri ta ja bakin ta tayi shiru tare da barin gurin kallon ta ya yi yana cewa "ke ina za ki je na gan ki da jaka"? Jin tambayar da ya yi mata ya sa ta fara sosa jiki ta na cewa. "Uhmm uhmm". "Ke ina wasa da ke ba tambayar ki na ke ba gidan uwar wa za ki je yanzu har da d'iban kayan a jaka"? Ja da baya Bilki ta yi tana cewa "gurin Umma zan je sai mu taho tare" hararar ta ya yi ya na cewa "kin san inda za ki je d'in amma tsabar raini na tambaye ki kika kasa ba ni amsa ki fad'a min gaskiya kafin ki ji duka". "Wallahi Yaya Sameer can zan je". "Ok kuma tsaiwar me ki ke d'azun dana shigo na gan ki a gaban Zainab"? Zaro ido Bilki ta yi tana fatan Allah ya sa bai ji komai ba ta ce "uhmm gaishe da ita na yi kuma shi ne na ke tambayar ta ina da atamfar da zan bata ta d'inka min idan zan samu da wuri"? Ta fad'a tare da d'agowa ta kallo Zainab wacce ita ma da saurin ta d'ago ta na kallon ta jin ba'kar 'karyar da ta sharara wai gaida ita za ta yi kai wannan yarinyar akwai sharri buhu-buhu kai ta girgiza ta na ci gaba da d'inkin ta ba ta bi takan maganar da Bilkin ta yi ba ji ta yi Sameer ya ce. "Munafika ke d'in ce zaki gaisar da Zainab 'karya ki ke yi" "Da gaske na ke kuma ka tambaya ta za ta fad'a maka" kallon Zainab wacce gabadaya hankalin ta ya na kan d'inki ya yi yana cewa "wai haka ne abin da ta ce"? Murmushi Zainab ta yi ta na jinjina kai ta ce "ni ba zan ce komai ba". "Humm dama na san za'ai haka" juyawa ya yi ya koma waje Bilki ta bud'e baki za ta yi magana ta gan shi wuff ya sake shigowa ya wuce d'akin sa d'an 'kasa ta yi da murya ta na kallon Zainab ta ce "wai dama za ki iya rufa min asiri ko da ace na yi miki 'karya"? Kallon Zainab ta yi jin tambayar da ta yi kamar ta share ta sai kuma ta ce. "Me ye riba ta idan na tona miki asiri ya dake ki ko kuma ya yi miki wani abu ta sila ta ni bana irin wannan sharrin a rai na kin gane"? Kai Bilki ta jinjina ta na ta'be baki ta ce "ya yi kyau masu kyakkyawar zuciya ni kam da ni ce wallahi ba ki isa na rufa miki asiri ba" murmushi Zainab ta yi ta na cewa "ai ni dake ba d'aya bane je ki da halin ki" tsaki Bilki ta ja mai 'karfi har Sameer ya jiyo daga d'akin sa ya ce "waye wannan ya kewa mutane tsaki"? Tabd'i da gudu Bilki ta fita daga 'kofar wanda ya sa Zainab ta yi dariya wato yarinyar nan 'yar rainin hankali ce ga fatsara da rashin kunya ga kuma uban tsoro. Fitowa Sameer ya yi ya na saka takalman sa ganin Bilkin ta fice kuma ya san ita ce ta yi tsakin, humm za ta dawo gidan ta same shi ai ba tabbata za ta yi acan d'in ba idan ta je kallon Zainab ya yi yana shirin fita ya ce "wai yau ko anguwa za ki je"?. "A'a ba inda zan je lecture ne kuma sai 'karfe d'aya da rabi zan tafi" "Ok ai da naga kin ci kwalliya ne haka shi ya sa na yi tunanin ko akwai inda zaki je d'in"?. "A'a d'inki kawai zan yi". "Ya yi kyau bari na koma chemist ban rufe ba kuma na baro shi ba kowa". "To Yaya Sameer Allah ya taimaka" "Amin" ya fad'a ya na fita Umma kam ta na can nesa da su ta na aiki ba ta san me ya ke faruwa ba tasowa ta yi daga gurin ta dawo wajen 'kofar d'akin ta, ta zauna za ta yanka albasa d'an kallon ta Zainab ta yi ta na cewa "wai Umma yanzun har abincin rana za ki d'ora"? Kai ta d'aga tana cewa. "Eh man gara na gama da wuri ai na huta kuma kin manta Hajiya idan ka kai mata abinci a makare sai ta yi maka tas kamar za ta dake ka sannan ta kar'ba idan ma za ta ci kenan" "hummm Allah ya rufa asiri" kawai shi ne abin da Zainab ta ce ba ta sake magana ba. Fitar Sameer kam ya na komawa chemist ya ga Aliyu a ciki ya na zaman jiran sa shiga ya yi shi ma ya na zama akan kujera ya ce "barka da dawowa Marshall ashe har ka fito tun wuri haka na d'auka yau wuni za ka yi a gida ka na hutun gajiya sai kuma na ga ka fito"? Kai Aliyu ya d'aga ya na cewa"ta ya zan iya wuni a gida ba tare da na fito na ga zuciya ta ba yanzu haka ba abin da na ke muradi kamar na gan ta fatan ta na nan ba ta je ko'ina ba"?. "Eh ta na nan ba inda ta je dama D'an Yana ne gurin zuwan na ta kuma ka ga ba'ai hutu ba balle ace ta samu d'an lokacin da za ta je d'in" ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya na mi'kewa ya ce "mu je" da alamar tambaya Sameer ya ce "ina mu je"? Kai tsaya ya ce "gidan ku"? Zaro ido Sameer ya yi yana cewa "kai Marshall da gaske sai ka iya shiga". "K'warai ba abin da zai hana tun da ba sani akai ina son ta ba gaba ne dai zan daina shiga" jinjina kai Sameer ya yi yana mi'kewa ya ce "shikenan mu je" fita su kai daga chemist Sameer ya rufe sannan su ka tafi kamar yadda ya saba in dai ya shiga gidan 'kofar Hajiya su ke fara shiga ai kuwa ta na ganin su ta zaro ido ta na bin Aliyu da kallo ta ce. "Ikon Allah wa na ke gani kamar Aliyu" zama su kai ya gaisa da ita sannan ya ce "eh Hajiya ni ne" ri'ke baki ta yi ta na cewa "ohh Allah mai iko dama ka dawo ne d'an nan ya fama da 'ko'kari"?. "Alhamdulillah Hajiya na same ku lafiya"?. "Lafiya 'kalau Aliyu Allah ya yi maka albarka tun da har ba ka ta'ba mantawa da ni duk lokacin da ka dawo sai kazo ka gaisar da ni". "Ba komai Hajiya ai ke kaka ta ce" kai Hajiya ta jinjina cikin jin dad'i ta ce "kwarai kuwa ni matsayin kaka na ke a wajen ku" kallon Sameer ta yi ta na cewa "kai Samar ba dan darajar Aliyu ba yau ka shigo min yaushe rabon da na gan ka tun ranar da mu kai maganar akan video da ka kawowa Zainab" juyawa 6angaren Aliyu ta yi ta na cewa "ka gan shi nan Ali sai mu kwana gida d'aya mu tashi yaron nan Samar bai le'ko ya ga lafiya ta ba ko tunani ya ke zan ro'ke shi ya bani wani abu ne oho masa". "Kin gani ko Hajiya ai ke matsala ta da ke zargi ni da yaushe na fad'a miki haka maganar ba na shigowa gurin ki wannan gaskiya ne sai lokaci zuwa lokaci amma ai na san ki na lafiya tun da da ace ki na ciwo zan ji labari a gurin 'yan gidan ko". "Ai ka ji shi ko Ali nema min jinya ya ke saboda ba ya so ya shigo ya gan ni cikin walwala gaskiya Samar ka nuna min matsayi na yanzu dole na san irin zaman da na ke da kai". "Wanne irin zama ki ke yi da ni"?. "Ka fi ni sani ai ba sai na fad'a maka ba". "Ok shikenan Aliyu tashi mu tafi Hajiya idan za ka kai dare anan ba za ta daina maka zance ba yadda ka gan ta nan ba ta rasa abun fad'a duk rintsi". Mi'kewa Aliyu ya yi kamar yadda ya saba ya aje mata kud'i su ka fita daga gurin ta sai albarka ta ke yi mai shi ya sa take son zuwan Aliyu ba ya ta'ba fita sai ya aje mata abun arziki. Fitar su daga gurin Hajiya kai tsaye 'kofar su Sameer ya nufa har lokacin Zainab ta na yadda take ta na d'inki........ "Assalamu-alaikum" da sauri ta dago jin muryar namiji ba zato ta na d'agowa idon ta ya sauka akan fuskar Aliyu su ka had'a ido ya d'au wanka da wani irin mugun sauri ta sauke kan ta 'kasa jikin ta ya d'au rawa haka kawai mafarkin da ta yi d'azu ya fad'o mata gani take kamar da gaske ne musamman da ta gan shi sai ta ke ganin kamar shi ma ya yi mafarkin irin na ta shigowa su kai Sameer ya na cewa. "Ina Umma ta ke"? Ya tambaye ta ya na kallon yadda ta kasa ci gaba da abin da ta ke yi d'an daidaita nutsuwar ta, ta yi da'kyar ta iya ce masa "ta na d'aki" sannan a hankali ta ce "Ina kwana" Aliyu ya san da shi ta ke ba Sameer ba shi ya sa ya ce. "Lafiya". Ya fad'a ya na wucewa numfashi ta sauke lokacin da suka shiga d'akin Umma da har za ta tashi ta shiga d'aki idan sun fita ta fito ta ci gaba sai kuma ta fasa ta kalli 'kofar d'akin Umman haka kawai ta zubawa takalmin Aliyu ido ganin yadda ya ke d'aukar ido ya na she'ki wai yau Aliyu ne a gidan su har cikin d'akin su ita dai damuwar ta Allah ya sa ba shi ne ya ke mata kyautukan nan ba, sai kuma zuciyar ta, ta ce "idan kuma shi ne fa ya za ki yi"? ji ta yi numfashin ta ya na neman daina tafiya yadda ya kamata cikin azama ta girgiza kai da sauri ta kawar da tunanin a ran ta sannan ta daina kallon gurin gabadaya ta na nan a zaune sun d'an dad'e daga baya ta ga sun fito za su fita. "I love you Zainab" Aliyu ya fad'a a zuciyar shi wanda ya yi daidai da kamar ta ji a fili ya fad'a kawai ta d'ago gani ta yi ya kalle ta sannan su ka fita da Sameer su ka bar ta zuciyar ta na harbawa cike da tunani "me ya sa Aliyu ya ke mata irin wannan kallon kodan yau ya gan ta ba nikaf ne kenan fuska ta yake kallo"? Hannu ta saka ta na shafa fuskar ta ta tabbas fuskar ta ya ke kallo innalillahi ai ba ta san za su shigo ba da ba za ta fito waje ta yi d'inki ba gara ta yi abun ta a d'aki................... "Zainab kin ga Aliyu d'an albarka kalli shigowar su abin da ya bani" ta ji muryar Umma ta katse mata tunanin da ta ke yi kallon hannun ta tayi ta ga kud'i ga kuma turare da alama zai yi tsada domin ka na ganin sa ka san ba turaren 'yan ya ku bayi ba ne, saboda kar Umma ta fahimci a rud'e ta ke ya sa dole ta d'an saki fuska ta yi murmushin da iyakacin sa la6en ta, ta na jinjina kai amma ba ta yi magana ba komawa Umma ta yi ta aje ta na fitowa ta d'ora aikin ta. Komawar su chemist Aliyu da ya tsaya daga 'kofar shiga ya ce "Sameer wai dama har yanzu Zainab ba ta daina d'inki ba"? Kai Sameer ya d'aga ya d'aga ya na kallon sa ya ce "eh ba ta daina ba ta na yi duk ranar da ta samu lokaci idan ba school ko kuma da dare kafin ta kwanta". "Har da dare lokacin da ya kamata ta kwanta ta huta gaskiya ya kamata ka fad'a mata ta daina wannan aikin 'karfi ne da 'kafafun ta take takawa abun ya na juyawa akan kud'in da baifi dubu nawa ba ni bana son ta ri'ka shan wahala" ya fad'a fuskar sa na bayyanar da rashin jin dad'in da zuciyar sa ke ciki murmushi Sameer ya yi ya na cewa. "Ai kuma ta riga ta saba ba za ta iya dainawa ba ko na fad'a mata" huci Aliyu ya fitar ya na cewa "a nan kenan amma idan na aure ta wallahi ba zan bari ta yi ba ko ta je da shi sai dai ta ri'ka kallon sa da ido ko na yi kyauta da shi" dariya Sameer ya yi jin abun da ya ce kuma ya ga da gaske ya yi maganar ya ce. "Ba na jin za ta amince koda auren na ta ka yi" ya fad'a ya na tabbatar da hakan a ran sa ya tsaya akan cewa lallai Zainab ba za ta ta'ba amincewa ta rabu da keken ta ba. "Idan ta'ki yarda sai ta fad'a min nawa ta ke samu a wata sai na ri'ka biyan ta kawai" zaro ido Sameer ya yi ya na cewa "to fa abu ya yi nisa kenan"?. "Da gaske na ke Sameer hakan ya fi min kwanciyar hankali ba zan iya jurar ganin wadda na ke so ta na wahala ba mun yi waya da Amirah tun ina can zuwa nan da kwana biyu za mu je gidan su na gaida Mama sakamakon wancan zuwan da na yi har na tafi ban je ba za su ga kamar yanzun saboda ba ala'kar karatun Amirah a hannu na ne shi ya sa na daina zuwa gurin su" kai Sameer ya jinjina ya na cewa "ok ba damuwa Allah ya kai mu". "Amin bari na koma gida gurin Momy za mu yi magana da ita sai na fito" "ok ka gaida ta" fita Aliyu ya yi ya tafi gida ya bar Sameer ya na mamakin maganar da ya fad'a na cewa ba zai iya barin Zainab ta ci gaba da d'inki ba gara ta fad'a masa nawa ta ke samu a wata ya ri'ka biyan ta. @YUSRAH Yau weekend Shareef ya na gida bai fita ko'ina ba ya na zaune a parlor ya d'ora laptop d'in sa akan table ya na duddubawa Nihal ta kira shi bai d'aga ba ya katse ya kira ta d'agawa ta yi sun fara magana kenan Mami ta fito ganin ta ya sa Shareef cewa Nihal ta kashe kiran ya na zuwa zai kira ta daga baya, aje wayar ya yi bayan ya ji ta katse sannan ya bar kallon laptop d'in ya tattara dukkan hankalin sa da nutsuwar sa ya na cewa. "Barka da kwana Mami na fatan kin tashi lafiya"? Murmushi ta yi ta na kallon sa ta jinjina kai alamar eh ta ce "lafiya 'kalau na tashi Shareef dawa ka ke waya da safen nan"?. "Surukar ki ce Mami". "Shareef" ya ji ta kira sunan sa "na'am Mami" numfashi ta sauke ta na cewa "dama tambayar ka zan yi ina yarinyar nan ne ban sake ganin ta ba tun sau d'aya"? Da alamar tambaya ya ce "wacce yarinyar". "Humairah na ke fad'a" gani ta yi ya d'an dafe kai alamar tunani can ya ce "Mami wacece Humairah kuma a ina ta ke"?. "Wannan yarinyar 'kawar nan ta ka fa"?. "Wacece 'kawa ta kuma ni ba ni da 'kawa mace" baki Mami ta bud'e ta na kallon sa ta ce "amma wannan yarinyar da ta ta'ba zuwa gidan nan kwanan baya da d'an dad'ewa ta kawo min ziyara har ta ce hospital d'in ku d'aya"? Dogon numfashi ya ja ya na cewa. "Ok Baby ki ke fad'a"?. "Eh yauwa ita fa na ke nufi wai ta na nan kuwa har yanzu ta na aiki a hospital d'in na ku"?. "Eh ta na yi". "Ayya Allah sarki me ya sa ba ta sake zuwa gaishe da ni ba ne"? Kai Shareef ya girgiza ya na cewa "a'a Mami" da mamaki Mami ta kalle shi ta na cewa "kamar ya a'a ko kai ka hana ta"?. "Eh ni na dakatar da ita". "Haba Shareef akan me"?. "Akan wani dalili Mami ina da babbar hujja ta na hana zuwa d'in" "hujjar ka ta me"?. "Mami dole na hana ta ni ba na son d'anyan kai tsabar rashin hankali yarinyar wai ashe so na ta ke nan d'in zuwan da ta yi ta zo ne saboda ta gabatar miki da kan ta ku saba dan ta shiga jiki na". "Kamar ya ban gane ba"?. "So ta ke ta zama surukar ki"? Dariya Mami ta yi ta kallon sa cikin tsokana ta ce "au masha Allah ashe ma suruka ta ce ban sani ba ita ma auren ta za ka yi kenan rana d'aya da na Nihal ko sai daga baya za ka aure ta"? Girgiza kai ya yi da sauri ya ce "a'a ni ba ni da ala'ka da son da take min kuma na fad'a mata gaskiyar akwai wacce zan aura domin ina yaro na ba za ta saka na auri mata biyu ba saboda ba na son hayaniya". "Haka ne amma ni a nawa ganin tun da ta na son ka ba za ta d'aga hankalin ta a gidan ka ba musamman idan ka fad'a mata sharud'an ka na tabbata za ta amince kuma za ta bi umarnin ka". "A'a Mami ni gabadaya yarinyar ba ta yi min ba ne saboda wad'ansu halayen ta marasa kyau na yi iya 'ko'kari na ta gyara tun shekarun baya amma ta'ki shi ya sa na watsar da ita kawai kuma sai yanzu sama ta kai za ta zo ta ce na aure ta ai Mami ki kwantar da hankalin ki ni wacce za tai miki ladabi ta ba ki girman ki na ke da burin aure ba wacce ni ma idan na fad'a ma ta magana ba za ta saurare ni ba ita kuma irin wad'annan matan ce" jinjina kai Mami ta yi ta na cewa "subanallah Allah ya rufa asiri ni kam gaskiya da na gan ta haka ban ta'ba tunanin za ta aikata wani abu mara kyau ba sai dai hali ba a kamanni ya ke ba Allah ya kyauta ka yi breakfast ne"?. "A'a zan yi sai anjima" mi'kewa Mami ta yi ta tafi dinning ta na cewa "ok ba damuwa ni bari na yi tun da anguwa zan tafi". "Ina za ki je". "Zan je na sake gano jikin Tasnin". "Har yanzu ba ta warware ba ne"?. "A'a ta samu sau'ki ai da yake ka ga idan ba haihuwa ta yi ba ina za ta samu lafiya". "Ok tun da haka ne kawai bari ni ma na zo na yi sai mu tafi tare na kai ki na gano ta sister guda ba lafiya" ya fad'a ya na rufe laptop d'in shi ma ya tafi dinning Mami za ta yi serving d'in ya ri'ke hannun ta ya na cewa "a'a zauna da kai na zan yi serving d'in ki wannan hakki na ne domin tun ban san waye ni ba ki ke feeding d'ina har na d'ago ni ma ya kamata na rama miki" ya fad'a ya an amsar serving spoon d'in ya saka mata ya aje a gaban ta sannan shi ma ya zuba na sa kallon sa Mami ke ta yi kawai ta na tuna baya ta na jin takaici da ba'kin ciki idan ta tuno cewa ba ita ce ta haifi Shareef ba yadda ya ke son ta ya ke nuna mata kulawa, hawaye ne ta ji sun cika mata ido amma gudun kar ya gani ya damu ta yi saurin gogewa, ganin ba ta fara ci ba ya sa ya d'ago ya na kallon ta ya ce. "Mami ya ba ki fara ci ba ko bashi ki ke so ba"? Murmushin dole ta yi ta na d'an sake fuska ta ce "a'a zan ci man". "To ki ci dan Allah Mami mu tafi" kai ta d'aga ta na d'aukar spoon ta d'iba sai da ya ga ta fara ci sannan shi ma ya ci gaba. **** Kamar yadda Aliyu ya cewa Amirah nan da kwana biyu zai shigo gidan su ya gaida Mama haka ta yi sabon kitso ta je ta yi jan lalle ta bari ba'kin ko ranar da zai zo ta yi, gari na wayewa ta kira shi ta ji yaya zai zo ne ko ya fasa ya ce mata zai zo amma sai 'karfe biyu ai kuwa ranar kamar sallah haka ta ke jin wani irin farin ciki ya cika ma ta zuciya yau Aliyu zai zo gidan su, hummm ai kuwa za ta dage ta had'a masa abinci me shiga rai haka ta gayyaci Nansy su ka tafi ta yo siyayyar abubuwan da za ta yi amfani da su ta dage tun safe take shirye-shirye sha biyu daidai ta fara had'a masa savoury stuffed yam balls da porridge with ganache mix domin ta san ya na son wannan duk abubuwan da ta san favorite foods d'in sa ne sai da ta yi ma sa sannan 'karfe d'aya da rabi ta na yi tayi sallah ta d'auki hijab d'in ta, ta je wani shagon lalle da ke anguwar ta su a gaggauce aka zana mata ba'ki sakamakon an riga an yi ma ta jan, ana gamawa ta dawo gida ta yi wanka Nansy dai ta na zaune ta na bin ta da kallo har ta gama shiryarwa ta d'auko wayar ta ta na danna kiran Aliyu. "Hello Aliyu kun taho ne"?. A lokacin Aliyu ya fito parlor daga part d'in sa kenan ta kira shi agogon hannun sa ya kalla ya na cewa "a'a ina gida amma yanzu zan taho" murmushi ta yi ta na cewa "yauwa ina jiran ka" "ok" ya fad'a ya na sauke wayar ya 'karasa fitowa ainihin cikin parlon duk yaran gidan su na gurin Momy a zaune ganin sa ya sa su kai tsit kowa ya yi shiru su na jiran su ji me zai ce mu su. "Kai ZAMAN uban me ku ke yi anan ba ku tashi kun yi shirin islamiyya ba ko duka ku ke jira"? Da sauri su ka fara girgiza kai d'aya bayan d'aya su ka fara tashi su na girgiza kai su ka bar gurin har rige-rigen shiga part d'in su, su ke kallon sa Momy ta yi ta na cewa "Aliyu ina zuwa na ga ka d'au wanka haka kamar wani ango"? Ta fad'a da murmushi "Momy gidan su Amirah zan je na gaida Mama saboda wancan zuwan da na yi har na tafi ban je ba" kai ta d'aga ta na cewa "ok eh gaskiya ne ya kamata ka je Allah ya kiyaye sai ka dawo" "Amin" ya ce yana fita daga parlon ya fito harabar gida ya d'auki motar sa ya kai ta waje sannan ya kira Sameer ya ce ya fito su tafi a lokacin Sameer shi ma ya yi wanka ya gama shiryarwa ya fito kenan ya ga Umma ri'ke da cooler abinci kallon sa ta yi ta na cewa. "Amma ba fita za ka yi ba ka ci abinci ba"?. "Eh Umma fita zan yi wani guri za mu je" kai ta d'aga ta na cewa "to shikenan ga abincin ka zan saka maka a d'aki idan ka dawo". "Ok Umma na gode" ya fad'a ya na wucewa Zainab da ta fito daga d'aki za ta yi wanka ta yi shirin islamiyya ganin sa da kwalliya ya sa ta ce "Yaya Sameer ina zuwa"? "Anguwa za mu je". "Kai da wa"?. "Tare da Aliyu za mu je gidan su wata yarinya ko za ki raka mu"? Ya na rufe baki da sauri ta girgiza kai ta na cewa "a'a Allah ya kiyaye sai ka dawo" kallon ta ya yi ya na cewa "ok ba za ki raka mu ba"?. "Ni ba inda zan je da dai kai kad'ai ne zan iya zuwa sai dai kuma islamiyya zan tafi". "Ai mu biyun ma za ki iya raka mu kin ga mu, mu na gaba ke ki na baya ana tafiya ana hira ko"? Zaro ido ta yi za ta yi magana sai kuma ta fasa ta wuce dariya ya yi ya na cewa "me ya faru na ga kina zare ido"?. "To tsakani da Allah Yaya Sameer na rasa da wa zan had'a tafiya sai Aliyu"?. "Eh me ye a ciki"?. "Akwai man ni dai a nawa 6angaren har abada ba na fatan tafiya ta had'a ni da shi". "Kaii saboda me"?. "Ni dai kawai na fad'a" kai Sameer ya jinjina da murmushi akan fuskar sa ya ce "ai kuma ba ki sani ba idan 'kaddarar ki ce dole sai kin had'a tafiyar da shi ko bakya so". "Hum'um Allah ya sauwake wallahi dan Allah Yaya Sameer ka daina fad'a" . "Ok shikenan na daina fad'a sai na dawo za mu samu zama mu yi magana" ya na fad'in haka ya fita daidai kiran Aliyu ya sake shigo ma sa ya d'aga ya na cewa "sorry Marshall afuwan gani nan" 'karasa fita ya yi daga gidan da sauri saboda biyu har ta cika ya je ya same shi a mota ya na shiga su ka wuce. "Sorry na bar ka, ka na ta jira na" Aliyu hankalin sa ya kan titi ya ce "ba damuwa ni ma damuna Amirah ta yi ni kuma ba na son takura shi ya sa ka ga na sake kiran ka ka ga tsaraban da zan kai mata nan tun safe na saka a motar saboda kar na manta amma yanzu ma za mu sake bi na dad'a mata wani abu" murmushi ya yi ya na cewa "hummm ni ma da Zainab mu ka tsaya bayan na shirya na fito dalilin da ban 'karaso da wuri ba kenan" kai ya jinjina ya na sauke numfashi ya ce "ok ta na gidan har yanzu ba ta tafi islamiyya ba"? "Eh lokacin da na fito za ta shiga wanka". "Sun gama exam"?. "Sun gama yau kusan kwana goma sha da har zan kira ka na fad'a maka amma sakamakon na san sai ka ce ta yi murnan graduate kawai na yi shiru abu". "Saboda me ka 6oye min Sameer yanzu a rayuwa komai na ke saboda ita ne tun da ita ce komai na wa a rai na, na ke jin ta idan ka fad'a min ta gama dan kud'in da zan ba ta, ta yi graduate shi ne ka 'ki fad'a" kai Sameer ya girgiza ya na cewa "gaskiya Aliyu abubuwan ne na ga sun yi yawa daga wannan sai wancan ka na 'ko'kari ya kamata ka ri'ka hutawa". "Kai ne ka ke ganin ina wahala amma ni indai akan Zainab ne gani na ke har yanzu ban yi ma ta komai ba Sameer ka san yadda na d'au wannan yarinyar a rai na kuwa? Ba za ka ta'ba sani ba kuma ba za ka fahimta ba ni kad'ai ne na ke jin abin da na ke ji" tsayawa yayi ya na girgiza kai shi kad'ai huuuuuhhh ya fitar da numfashi me 'karfi ya na cewa "Sameer lokaci ya yi da ya kamata na bayyana kai na Zainab ta san ina son ta ko zan samu sauki dama school na ke jira ta kammala yanzu ta gama a irin wannan lokacin shi ne daidai da na aure ta domin dama kawai na biya mata ta yi karatu ne saboda ni da kuma yara na ba dan ta yi aikin gwamnati ba babu abin da za ta nema ta rasa a guri na babu ce kawai ba zan ba ta ba ita ma da ana ganin ta zan ba ta" kai Sameer ya jinjina ya na cewa. "Masha Allah ashe kwanan nan za mu sha biki"?. "In sha Allahu domin ba zan bari auren ya ja lokaci ba" ya fad'a ya na horn a 'kofar gate d'in su Amirah me gadi ya bud'e masa su ka shiga Amirah kam dama tun da su ka gama waya ta na tsaye a jikin window ta na jiran shigowar sa ganin motar sa ta shiga ya sa ta ji kamar ta saki gud'a jiki na rawa ta bar jikin window d'in ta d'auki mayafin ta, ta na kallon Nansy ta ce "ke sun 'karaso" kai ta d'aga da wayar ta a hannun ta, ta na chatting ta ce. "Ok sannun su da zuwa". "Ba za ki taso mu je tarar su ba"?. "A'a je ki kawai zan fito daga baya" d'an ta'be baki Amirah ta yi kamar za ta sake magana amma tuna maybe yanzu sun shigo ya sa ta bud'e 'kofa ta fita a can main parlor ta tarar da su suna gaisawa da Mama murmushi ta yi cikin zumud'i ta 'karasa tare da zama ta na cewa "sannun ku da zuwa ya gida Samer har da kai kenan"? Kai ya d'aga ya na cewa. "Eh tare mu ka zo". "Sannun ku to ku taso mu 'karasa" ta fad'a ta na mi'kewa dakatar da ita Aliyu ya yi da cewa "zuwa ina kenan"? Juyowa Amirah ta yi ta na kallon sa yadda ya d'au wanka ajiyar zuciya ta yi ta na cewa "dinning za mu je ku ci abinci". "A'a mun gode"? Zaro ido Amirah ta yi ta na cewa "kai dan Allah Aliyu ka zo ko ruwa ne ku sha" sake girgiza ma ta kai ya yi yana cewa "a'a" kamar za ta fashe da kuka tsabar takaici ganin duk wahalar da ta yi a banza amma in dai ba su ci ba yau idan ta shiga d'aki ta rufe har dare za ta kai ta na kuka........... Ji ta yi Mama ta ce "a'a Aliyu tashi ku je ko ruwa ku sha domin an yi tanadin ku sosai ta zauna ta shirya mu ku abinci da abun sha ba za ku tafi ba sai kun ci" jin abin da Mama ta ce ya sa Amirah sakin wani daddad'an numfashi ta na kallon Aliyu ta ce "yauwa ta so dan Allah ku 'karaso" gani ta yi, ya yi shiru tamkar bai ji abin da ta ce ba mi'kewa Mama ta yi ta na cewa. "Aliyu ku 'karasa dan Allah ku fa ba ba'ki ba ne a gidan nan gidan ku ne amma sai jayayya ake da ku" ta na fad'in haka ta bar parlon ta shige part d'in ta shiru parlon ya d'auka Amirah ta na tsaye ta na jiran ta ga sun taso amma kamar an dasa su dawowa Amirah ta yi ta na kallon Sameer ta ce. "Dan Allah ku ta so mu je" d'an murmushi ya yi, ya na d'aga mata kai ya ce "ok mu na zuwa" ajiyar zuciya ta sauke ta na juyawa ta tafi wajen dinning d'in kafin su 'karaso Aliyu kam ko kad'an bai da niyyar tashi sai ma d'ora 'kafa d'aya kan d'aya da ya yi, ya na d'auko wayar sa ya fara dubawa Amirah da ta zauna ta na jiran ta ga sun taso hango shi ta yi ya na danna waya kawai alamar ba zuwa dinning d'in nan zai yi ba kamar ta d'ora hannu ta fasa 'kara da ihu haka ta ji ido kawai ta zuba masa hucin takaicin sa ya na fitowa daga zuciyar ta, kusan minti biyar Nansy ta fito ta gaisar da su ganin Amirah a dinning ta mugun had'e rai kamar ta je ya yi ma ta magana sai kuma ta fasa ta juya ta koma part d'in su . "Aliyu ba dan ni ba dan girman Allah ka taso ku 'karaso dinning d'in nan ka ga idan ka tafi ba ka ci komai ba ka tuna ba ni ba hatta Mama ba za ta ji dad'i ba kuma ka ga ta yi maka magana kafin ta tashi dan Allah ku 'karaso ka ji"? Amirah ta yi maganar ta na jin kamar ta tashi ta je ta fisgo shi, gani ta yi ya mi'ke ya na tahowa har ba ta san lokacin da ta saki ajiyar zuciya ba wacce shi kan sa ya ji ta zama ya yi Sameer da ya taso daga baya ganin yadda kowanne ya had'e rai a cikin su sai abun ya ba shi dariya kai ya girgiza ya na zama ya kalli Aliyu zai yi masa magana ya nuna ma sa da ido alamar ya yi shiru kar ya ce komai murmushi Sameer ya yi bai fad'i abin da ya ke son fad'a ba, Amirah ta yi serving d'in su duk abubuwan da ta yi ba wanda ta rage sai da ta zuba mu su kafin ta koma ta zauna cikin jin dad'i. Saboda kar ta ce ya wula'kanta ta ya sa ya ci abinci kawai ba wai dan ya na ra'ayi ba ita dai Amirah ta na zaune ta zuba ma sa ido ta na murmushi kamar ta d'auko wayar ta, ta yi ma sa video amma gudun kar ya gan ta a samu matsala ya sa ta ha'kura can kuma ta kalle shi sosai ta na cewa. "Amma dai Aliyu fatan abincin ya ma ka dadi ko"? Bai amsa mata ba Sameer da ya ke lura da yanayin kowanne a cikin su ita ta na cike da farin ciki da shaukin shi kasancewar sa a gidan su kuma a na sa 6angaren ya kame cikin attitude sam ya'ki ba da fuska balle a yi maganar arziki kai Sameer ya jinjina ya na dariya ya ce. "Marshall da kai fa take ka amsa mata shin abincin ya yi maka"? Ganin har lokacin ya yi banza kamar ba da shi ake ba ya sa cikin tsokana Sameer yace "ni bari na wakilce shi tun da naga shi ba zai amsa ba gaskiya abincin ya yi bala'in dad'i sosai yadda ba kya zato dad'in ne ma ya sa Aliyu rud'ewa ki yi hakuri Amirah dad'in abincin ne yasa ki ka ga bai iya yi miki magana ba" murmushi jin dad'i Amirah ta sake yi jin yabon da Sameer d'in ya yi ta, ta kalli Aliyu ta na cewa. "Dan Allah da gaske ka ke Sameer abincin ya yi dad'i sosai ni ce fa na dafa da kai na ba 'yar aiki ba na iya kenan"? Kai Sameer ya jinjina mata shi ma yana murmushin ya ce "ai wannan dalilin shi yasa ki ka ga Aliyu bai amsa miki ba ya na zilama santi ba zai bar shi ya amsa miki ba" Sai lokacin Aliyu ya d'ago tare da kallon Sameer sakamakon jin abin da ya ce shi kam Sameer dama ya na gama fad'ar haka ya kau da kai ya na dariya dama da niyya ya fad'i haka dan ya ji me Aliyun zaice mata ne ya d'auka zai yi magana sai kawai ya ga ya aje spoon d'in hannun shi tare da mi'kewa ya bar gurin ya nufi hanyar fita daga parlon cikin gaggawa Amirah ta mi'ke a gigice ita ma da sauri ta na cewa. "Aliyu ya haka na ga za ka tafi ko akan abin da Sameer ya fad'a ne? Please ka yi ha'kuri ka dawo ko 'koshi ka yi shi ya sa tashi"? Banza ya yi ta na tsaye ta ga ya bud'e 'kofa ya fita da gudu ta bi bayan sa har harabar gidan inda ya aje motar sa ta na huci da mamaki ta ce "wai me ya faru ne na ga ka tashi tafiya za ku yi"? Kamar kar ya kula ta sai kuma ya ce. "Eh tafiya za mu yi mun gode" shi ne amsar da ya bata ya na bud'e murfin motar tare da shiga ya zauna kallon sa ta yi ta na cewa "to amma Aliyu ai ba ka biya kudin abincin ba za ka tafi". "Me na biya ki dama restaurant na zo ko hotel"? Ya fad'a da mamaki sosai a fuskar sa kai ta girgiza ta na cewa "a'a amma Aliyu............. Katse ta ya yi "amma Aliyu me? Kin ga Amirah ba na son wasa ki rabu da ni kar ki 6ata min rai". "Ba wasa na ke maka ba idan saurayi ya je gurin budurwa ta masa liyafa ko ya ci ko bai ci ba biya ya ke". "Waye zai biya kin? Dama na ce ki dafa min abinci ne bayan ma ko dad'i bai yi ba" had'e rai ta yi jin abin da ya ce wato ma bai yi dad'i ba kai ta jinjina kamar ta ja 'kwafa sai kuma ta fasa ta na cewa "to yanzu ni dai ba wannan ba ka biya kawai kafin ku tafi". "Na biya me kin yi hauka ne"? Amira za ta yi magana Sameer da ya ke tsaye a can gefe ya na dariya 'karasowa ya yi ya na cewa "kai fa malam ba wani hauka da ta yi haka ake yi" ta'be baki Aliyu ya yi ya na cewa. "Haka ake me"?. "Haka ake biyan 'yan mata idan an ci abincin su" Sameer na rufe baki Aliyu ya ce "ba zan biya ba saboda ba ni nasa ta ba ra'ayin ta ne za ka iya shigowa mu wuce idan kuma ba bu'katar hakan na tafi dan na ga kamar dad'in tsayuwa da ita ka ke ji". "A haba kai fa Marshall? Kai ma ka na ji". "Ka ga ni kar ka damu da ni ka ji da kan ka idan kuma ta yi maka ne na saitawa kai na hanya na bar ka tare da ita"? Dariya Sameer ya yi ya na girgiza kai ya ce "a'a ni bance maka haka ba malam daga fad'ar gaskiya kar ka fassara ni" ya fad'a ya na juyawa gurin Amirah wacce ta kafe Aliyu da kallo ya ce "kin ga Amirah ki yi ha'kuri abincin ki ya yi dad'i kuma mun gode nawa ne kud'in da za'a biya ki"?. "Kawai kai dai ka bayar yadda ya kamata ai ba nice zan fad'a ba abin da ku ka ji zuciyar ku ta yanke mu ku shikenan" d'auko kud'i Sameer ya yi wanda ya kasance na Aliyu ne canjin da su ka yo mata shopping ya ba ta kar6a ta yi ta 'kirga ganin dubu goma ya sa ta d'ago ta na cewa. "Wannan ai ko kud'in drinks ba ku biya ba dubu goma kawai me zan yi da ita"? Kallon mamaki Sameer ya yi mata jin abin da ta ce lallai ta d'auko da zafi ya ce "ai ba iya shi kad'ai mu ka zo miki da shi ba" ya fad'a ya na bud'e motar ya d'auko mata shopping din ya na cewa "haka ne kin yi gaskiya Amirah sai dai ba komai ake nema a samu ba kin gane" mi'ko mata ya yi amma kunya ta hana ta kar6a kuma ta kasa cewa komai balle ta yi godiya ganin irin kayan kud'in da su ka jibgo mata ga shi ita kuma ta bada kan ta da'kyar ta ce. "Thanks na gode sosai Aliyu"hannun Aliyu ya na ri'ke da sityarin motar ba 6agaren da su ke ya ke kallo ba ya ce "ba ni za ki godewa ba wanda ya ba ki" ya na fad'in haka ya tada mota shiga Sameer ya yi ya na rufe murfin Aliyu ya ja motar ya nufi 'kofar gate da kallo Amirah ta motar har su ka fita sannan ta d'ebe kayan farin ciki da murna ta shige gida. A hanya bayan sun taho Sameer ya ke cewa "kai amma fa ka iya kafce Marshall" kallon sa Aliyu ya yi cikin alamun tambaya ya ce "wanne irin kafce"?. "Irin wanda kai wa Amirah yanzu". "Haka ne"?. "Eh mana da dukkan alamu Amirah fa ta na son ka matu'ka son da ta ke maka ga shi nan har ba ya iya 6oyuwa". "To amma kai me ka gani dangane da ni"? Jin tambayar da ya yi masa ya sa Sameer kallon sa cikin tsokana ya ce "ni dai ban ga wani abu ba ta yi maka kenan"? Kai tsaye Aliyu ya ce "a'a". "To ka na son ta"? Nan amsar d'aya ce "a'a" da 'karfi Sameer ya ce "amma tun da ita ta na son ka za ka iya auren taaa"? Yana rufe baki Aliyu ya taka wani irin burki wanda sai da Sameer ya bugi kujera juyowa ya yi yana kallon sa dariya Sameer ke yi har da ri'ke ciki ya kasa magana ganin yadda Aliyu ya yi da fuskar sa dafe saitin 'kirjin shi ya yi jin yadda zuciyar sa ta ke bugawa ya sa ya d'ago ya na kallon Sameer ya ce. "Amma wallahi kai dai Sameer ba ka da mutunci wata rana in dai ina yawo dakai sai dai aga gawa ta saboda maganganun ka masu kama da saukar tsawa" rufe baki Sameer ya yi ya na cewa "sorry Marshall dama na jarraba ka na yi". "Kuma ka rasa ta yadda zaka jarraba ni sai da haka"?. "To ai na ga ba wani abu ba ne a ciki dan kawai na tambaye ka". "Eh ba wani abu bane mana tambaya mai muhimmanci ya kamata ka yi min". "Wacce iri kenan"?. "Ka fi ni sani" "Ohoo so ka ke nace maka ka na son Zainab? Ta yi maka? Za ka aure ta abin da ka ke son ji kenan ba"?. "Eh shi ne nake so naji ba waccen shirmen ba". "Shikenan to yanzu dai tada mota mu yi sauri mu isa gida". "Ka na da uzuri ne"?. "Ni ko na ke da uzurirrika zan bud'e chemist kuma kai ma ka manta za ka had'u da Zainab". "Haka" Aliyu ya fad'a ya na tada mota su ka ci gaba da tafiya suna karya kwanar anguwar su kuwa sai gan ta ita da Afifah sun fita daga gate din islamiyyar su d'an murmushi Aliyu ya yi ya na tsaida motar ya ce "ya ka gan ta Sameer"? Ya fad'a ya na sauke numfashi tare da d'an lumshe ido jin yadda lokaci guda bugun zuciyar sa ya canza sakamakon ganin ta kad'ai da ya yi ido shi ma Sameer d'in ya zuba ma ta yadda suke tafiya a tsari cikin nutsuwa ita da Afifah kafin ya juyo ya kalli Aliyu da shi ma ya bud'e na sa idon ya na ci gaba da kallon ta ya ce "ita ce yarinyar da ta saka na rasa nutsuwa ta ita ce duk duniya na ke fatan mallakar ta nake addu'a saboda ita a kowacce rana da son ta nake rayuwa ba na jin bayan Zainab zan iya son wata yarinya a duniya ya Allah ka taimake ni Ubangiji ka 'kaddara yarinyar nan ta zamo mata ta" ya 'karasa maganar ya na fitar da huci me zafi wanda ya sa Sameer juyowa ya kalle shi da murmushi kawai amma bai yi magana ba da yake dama Aliyu iya tsayawa ya yi ba kashe motar ya yi ba sai ya ja kawai su ka ci gaba da tafiya su ka sake zuwa su ka wuce su Afifah a hanya da mamaki Afifah da ta bi bayan motar da kallo ta ce. "Wannan Yaya discipline ne to ina ya je na ga kuma da ya tsaya a can"?. "Maybe shi d'in ne sun je anguwa tare da Yaya Sameer" Zainab ta fad'a ta na d'an sauke ajiyar zuciya kai Afifah ta d'aga ta na cewa "eh tabbas motar sa ce na yi mamakin tsayawar sa a can ne amma d'azu ina gida lokacin da ya shirya za su tafi". Daidai sun fito daga motar ganin yadda kowanne ya d'au wanka ya sa Afifah ta ri'ke baki ta na cewa "to fa irin wannan d'aukar zafafan wanka haka sai ka ce angwaye" Zainab kam da mamaki ta ce "wai dama Afifah Aliyu ya na irin wannan shigar amma rai da rai sai dai ki gan shi daga shi sai vest da three quarter d'in wando sai kace wanda ya rasa kayan sakawa"? Dariya Afifah ta yi ta na cewa "ai indai lamarin Yaya discipline ne sai ha'kuri haka ya ke ya na son wannan shigar". "Ai kuma kamata yayi ki fad'a masa ya daina" Zainab na rufe baki Afifah ta zaro ido ta na "ni wa? Rufa min asiri so ki ke ya ci uba na kenan". "Dan kawai kin fad'a masa gaskiyar idan ke ki na tsoro ki fad'awa Momy man ita ai za ta masa magana" "to ban 'ki ba sai dai Momyn ita ce za ta fad'a masa yanzun dai ga su can sun alwalar la'asar sun yi masallaci sai anjima Aunty Zee ko sai gobe ma kai zan ce tun da ba 'kara had'uwa za mu yi ba" "to Afifah Allah ya ba mu alkhairi" shiga gida Afifah ta yi Zainab kuma ya wuce. Aliyu su na fitowa daga masallaci gida ya shigo a lokacin Momy ta na zaune ita da Husnah zuwa ya yi ya zauna a kusa da ita ya gaisar da ita kallon sa ta yi bayan ta amsa ta ce "har ka dawo daga gidan su Amiran dama ba dad'ewa za ka yi ba kenan"?. "Ai na dad'e Momy na yi 'ko'kari tun da na kusa awa biyu". "Awa biyu ka ce Aliyu ita kuma Amiran da ta ke zuwa ta yi mana sati biyu cif a gidan nan fa"? "Kuma ni ai ba zan had'a kai na da ita ba ba ta da aikin yi ni kuma ba mashiririci ba ne". "Meye abun shiririta a ziyara"? "Babu Momy amma ni da ita akwai bambanci ita mace ce ni namiji ne"? "Haka ne dama Aliyu ina ta so na tambaye ka wani abu tun wancan zuwan da kayi wai ba za ka yi aure bane"? Bai ta'ba tunanin abin da za ta tambaye shi ba kenan shi ya sa ta na fad'a ya d'ago ya kalle ta kai Momy ta girgiza ta na sake cewa "na ce ba za ka yi aure ba ne"?. "Zan yi Momy". "To ai na ga shiru-shiru ne lokaci sai sake ja yake na d'auka tun wancan zuwan na ka zaka ce min aure za kayi kafin ka koma sai kuma naga sa6anin abinda nake tunani gashi ka sake tafiya yanzu shekara uku ka dawo wannan karon babu inda za ka tafi har sai ka fad'a min budurwar ta ka an gama magana kafin ka tafi"? Murmushi yayi yana d'agowa ya kalli Momy ya ga ta girgiza masa kai ta na cewa "ba kallo ba da gaske nake Aliyu ko baka da wacce kake so ya kamata ka nema kafin ka tafi Allah maganar gaskiya ina so kayi aure to kai ma baka yi ba wa yake batun Afif tun da dama shi ba isa auren ya yi ba kai ne dai ya kamata ka yi ka ji"?. "Kar ki damu Momy na fad'a miki akwai wacce na ke so dama lokaci ya yi d'in da zan bayyana muku ita dalilin da ya sa ban yi maganar ba school ta ke yi yanzu kuma ta gama" "yauwa alhamdulillah a ina take"?. "A nan garin". "Ok wacce anguwa"?. "Zan fad'a miki daga baya idan na gama shawara" "tom Allah ya za6a maka mafi alkhairi wacce ta dace da rayuwar ka". "Amin Momy na gode" ya fad'a tare da mi'kewa ya nufi part d'in sa Elham dake ra6e da gudu ta karaso gurin ganin ya tafi dariya ta zauna ita kad'ai ta na yi Momy dake kallon ta da mamaki tace "ke kuma fa lafiya sai kace sabuwar kamu"?. "Dole na yi dariya na 'kara Momy farin ciki na ke da naji Yaya boss yace yana da budurwa kwanan nan zamu samu Aunty ashe"? "Aw kin ji maganar da mu ka yi da shi kenan? "Kwarai Momy kowacce kalma na ji tun daga farko har 'karshen" jinjina kai Momy ta yi ta na "ya yi kyau saura kuma ki fad'a har ya ji ni babu ruwa na ina kallo zai daki banza" zaro ido Elham ta yi ta na cewa. "Ni kuwa ina zam fad'a ai ba wanda zai ji mutuwar sarki a baki na wallahi bazan ta'ba fad'a ba duk ranar da maganar ta fito fili kowa ya ji yanzu nasan ina fad'a abun ya koma kunnen sa cewa zai yi waye ya fad'a a ce nice ya ci ubana" hakan dai ya fi miki alkhairi ki yi shirun da bakin na ki" Momy ta fad'a daga haka ba ta sake magana ba ita ma Elham d'in haka. ** *** ** Yau Baby ba ta je hospital ba sakamakon zazza'bi da ta tashi da shi a bedroom ta wuni har magriba ba ta samu ta fito parlor ba sai da Daddy ya dawo sannan Hajiya Fatima ta shiga ta yo mata magana sai lokacin ta fito duk da zazza'bin bai gama sakin ta ba zama ta yi ta na gaida shi ya amsa ya na kallon ta ya ce. "Baby ko bakya jin dad'i ne"? Kai ta d'aga hawayen shagwa'ba su na zubo mata ta ce "tun safe da shi na da zazza'bi" "Subanallahi zazza'bi Allah ya sauwake dama magana mu kai da aboki na Mustapha na fad'a masa matsalar da ta ke damun ki amma ya ce na bar ki, ki ci gaba da zuwa aikin ki kar na yi miki transfer shikenan ya wuce ki koma bakin aikin ki idan Allah ya kai mu gobe kin ji"? Kai ta d'aga shi kuma ya ci gaba "sannan Baby magana ta 'karshe ya ce ya na nemawa d'an sa auren ki" wata iriyar zabura Baby ta yi jin numfashin ta ya na neman barin jikin ta da wani irin mugun sauri ta fara girgiza kai ta kasa magana 'karshe ta fashe da kuka ta na cewa "a'a Daddy ni ba zan yi aure ba kawai zan ci gaba da aiki na har iya tsawon rayuwa ta ba zan auri kowa ba" zaro ido Hajiya Fatima ta yi ta na kallon ta, ta ce "kin yi hauka ne uban ba za ki yi aure ba kai ka ga shashashar yarinya idan kin 'ki yin aure saboda shi ki na tunanin shi zai fasa na sa auren saboda ke ne, ina ruwan sa da ke, ke ce ki ke naki yi shi kam ai ya na can hankalin sa a kwance ya na rayuwar sa cikin jin dad'i da walwala ke kin zo ki matsawa kan ki a banza" kai Daddy ya jinjina ya na cewa "bakya son sa Baby amma ai da kin bari kun had'u ko ma menene daga baya sai ki yanke hukunci" har lokacin kuka Baby ke yi ta ce "ni Daddy ba sai ya zo guri na ba, ba na bu'katar ganin sa". "Ok ba damuwa tashi ki je" mi'kewa ta yi ta na jin yadda sabon zazza'bi ya dad'a lullu'be ta lokaci guda a hankali ta bud'e 'kofa ta shiga tare da rufowa tsaki Hajiya Fatima ta yi bayan wucewar Babyn ta ce "anya wannan yarinyar ba ta fara samun 'kwacewar kai dalilin yaron nan ba, ace tsabar hauka har da wai ba za ta yi aure ba a rayuwar ta hummm ai kuwa ba ta isa ba sai ta yi". "Dama ai ba wai yin ne ba za ta yi ba a'a yanzu ta na kan zafin abun idan ta huce ita da kan ta za ki ga ta na batun auren sannan ko da ace ta 'ki amincewa ta yi d'in ni kam ba zan bar ta ba wannan d'an gidan abokin na wa ya na hankali sosai da shi zan had'a ta tun da har mahaifin sa ya furta ni kuma Mustapha ya fi 'karfin komai a guri na" numfashi Hajiya Fatima ta sau'ke ta na cewa "Yauwa masha Allah yanzu na ji magana" "Au duk maganar da mu ke da ba ki ji ba kenan"? Dariya ta yi ta na cewa "a'a na ji sai dai ba irin wacce na ke son ji ba ce amma abin da ka fad'a yanzu ya wanke min zuciya". "Da sabulu na wanke miki zuciyar na ki ko da Klin"? Jin abin da ya ke ya sa kawai ta fara dariya ta na cewa "gaskiya Alhaji ba ka da dama wannan idan ka zauna da me cutar hawan jini tuni zai warke saboda abun dariyar ka gaskiya ka na saka ni nishad'i sosai" kai ya jinjina ya na cewa "alhamdulillah ai ni kullum abin da zai faranta miki shi na ke so kin ga yanzu misali ki d'auki wannan maganar da mu kai a matsayin........................ Kiran wayar sa da akai shi ya hana ya fad'i maganar da ya ke fad'a ya d'aga kiran Hajiya Fatima ta na gefe ita kad'ai sai murmushi ta ke ran ta fal da farin ciki. Sanin da Amirah ta yi Aliyu ya na gari Shi ya sa kwana uku tsakanin zuwa gidan su da ya yi ita ma ta zo sai dai ta yi mamaki domin tun ta zo a parlor ta ke ita da sauran yaran amma ko kad'an ba ta ga ya fita ko ya shigo ba, ba ta san a ina ya ke ba yanzu har su ka baje su ka bar ta a gurin Afifah ta ce mata ta karasa bedroom d'in su amma saboda so take ta ga ba kowa ya rage sai ita kad'ai ta shiga part d'in Aliyu 'kin 'karasawa ta yi ta ce ta yi gaba ta na zuwa daga baya. Sun dad'e da barin parlor amma dai shiru ta na ta zauna ta d'auka ya na nan a part d'in sa fitowa ne baiyi ba gajiya ta yi ta mi'ke ta shiga gurin su Afifah tare da aje handbag d'in ta da mayafin ta kwanciya ta yi akan gadon ta rufe ido na d'an mintuna har barci ya fara d'aukar ta amma sakamakon mafarki da ta yi ga Aliyu tsaye tare da mace da sauri ta bud'e ido a gigice ta mi'ke tana d'aukar mayafin na ta ko yafawa ba ta yi ba ta fita daga 6angaren su Afifah da sauri ta nufi parlor ganin ba kowa ya sa ta ja dogon numfashi ta lalla6a tana waige-waigen ko wani yana kallon ta lura da tayi babu kowa yasa wuf ta fad'a part d'in Aliyu a guje tana shiga parlon sa domin ta duba idan yana nan bata samu kowa ba shiru amma dai ta ga wayar sa da laptop d'in sa akan table 'karasawa ta yi ganin photon mace akan fuskar laptop d'in d'an du'kawa ta yi tana 'kure photon da kallo gaban ta na mugun fad'uwa zuciyar ta na bugu kamar ganga ta dafe 'kirji ta na cewa "na shiga uku wace wannan a ina take kar dai ace ita Aliyu ke so? Lokaci guda ta ji kan ta yana juyawa idon ta ya na neman rufewa sake bud'e idon ta sosai ta yi akan photon ba ta ta'ba ganin wannan budurwar ba taya zata nemo ta wa zata tambaya wa ye ya san ta a ina take"?. Wayar sa da ka kawo haske alamar shigowar message ya sa ta mayar da hankalin ta gurin nan ma dai wani photon macen ta sake gani akan secreen d'in wayar da sauri ta d'auka hannun ta ya na rawa ta kalli photon lokaci guda ta zaro ido waje numfashi ya na fita da mugun gudu ganin wacce ke fuskar laptop d'in na sa ita ce akan wayar ma kenan dai hakan ya na nufin ita ce wacce Aliyu ya ke so ko ba'a fad'a mata ba kusan su6ucewa wayar tayi daga hannun ta cikin sauri Amirah ta ajiye jikin ta yana rawa sosai hawaye ya cika mata ido ta fara girgiza kai ta na cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku me yake shirin faruwa ne dama da gaske Aliyu yake da yace min yana da wacce yake so ban ta'ba yarda ba saida na ganta da ido na a ina wannan budurwar take ta ya zan same ta"? kuka ta fashe dashi tana dur'kusawa a gurin tare da kife kanta a jikin table d'in wanda laptop da wayar suke kai kawai ta fara kuka mai 'karfi sai da tayi ta gaji sannan ta d'ago idonta yayi jajur ta mi'ke fuska a murtuke ba rahma a ranta ta fara magana. "Wannan yarinyar ce Aliyu yake so dama a kanta ya 'ki saurarar tawa soyayyar? Kan bala'i ai kuwa wallahi bata isa ba ni na fara sanin Aliyu kafin ita ni na fara son sa ni na zauna da shi tsawon lokaci watakil ma sannan bai san da zaman ta a duniya ba bazai yuwu ina kallo wata jakar 'kauye tazo ta aure shi ba, inaaa! never in history zan binciko ta duk a inda take a fad'in 'kasar nan sai naje na same ta ko ta bar min Aliyu ta je ta samu wani ko kuma na sanya ta cikin masifar da duk dangin ta idan sun taru basu isa fitar da ita daga cikin bala'in da zan jefa ta ba" ta karasa maganar tana cije lips ta jinjina kai d'auko wayar ta tayi saboda tasan Aliyu baya saka password a wayar sa da sauri ta tura photon sannan ta aje masa wayar ta juya ta fita ko sallama ba ta yiwa Momy ba ta fice ta d'auki motarta ta koma gida a lokacin Nansy tana bedroom d'in kawai sai jin Amirah ta bud'o kofa tana kuka ta yi da mamaki ta d'ago tana kallon ta har tazo ta fad'a gado tana sake fashewa da sabon kuka sosai Nansy ta zuba mata ido tana kallon ta matar da ta bar gida cike da farin ciki kuma me yasa ta dawo ta na kuka lallai akwai dalili amma bari ta tambaye ta tashi tayi ta karasa tana dafa ta cikin kulawa ta ce. "Aunty Amirah lafiya kuwa"? Kai Amirah da ke kwance tana faman kuka ta girgiza ba ta iya magana ba yadda kukan ya ke zuwa ma ta ba 'kak'kautawa "Aunty Amirah dan Allah ki daina kukan nan tunda baya magani ki fad'a min me ya 6ata miki rai na san dai lafiya 'kalau ki ka bar gida"? Tashi zaune Amirah tayi tana goge hawayen fuskarta da towel d'in ta dake aje akan gadon muryar ta a dashe tace "Nana ni da Aliyu ne shi ne silar kuka na" "Subanallahi Yaya Ali-Zaki shi ne ya 6ata miki rai kuma"?. "Kwarai Aliyu ne saboda yau na ga abin da ya kusa tarwatsa min rayuwa ta ina jin zuciya ta kamar ta buga a halin yanzu domin bana ganin komai daidai" zaro ido Nansy tai tana sake sabon zama tace "ni fa Aunty Amirah ban gane ba ki yi min bayani yadda zan fahimce ki wani abu ne ya faru tsakanin ku"? "Tabbas Nana abu ne ya faru da nasan idan na shiga part d'in sa abin da zan gani kenan da nasan zan ci karo da ba'kin ciki da tashin hankalin da zai hana ni zaman lafiya da ban je gidan ba ma kwata-kwata na yi dana sanin zuwa na gidan su Aliyu yau kuma zan dad'e ban koma ba" kai Nansy ta girgiza ta na cewa. "Haba Aunty Amirah akan me"? "Nana ko ke ce idan na fad'a miki abinda ya faru ba za ki sake marmarin zuwa gidan akan lokaci ba". "Ok me ya faru ina jin ki"?. "Basai na fad'a miki ba saboda bana son abun tashin hankali ko kuma su Mama da Daddy su ji labarin rai na ne zai sake 6aci fiye da yanzu kawai ki 'kyale ba zan iya fad'a miki ba sai a gaba" "shikenan ba damuwa Allah ya rufa asiri" Nansy ta fad'a tana mi'kewa ta fita jim kad'an ta dawo da ruwa a hannunta tana mi'kawa Amirah kai ta girgiza mata batare da ta yi magana ba Nansy dake tsaye da kofin ruwa tace "idan ki ka sha ruwan sanyi zai rage miki rad'ad'in da ki ke ji a cikin ran ki shiyasa ma na kawo miki" jin abinda tace yasa Amirah kar6ar ruwan tayi kar'ba d'aya ta mi'ka mata tana cewa "Ki d'auko min paracetamol a cikin drawer yanzu nasha naji na fara jin sanyi maybe zazza'bi ne zai kama ni" ta fad'a tana kwanciya "ok bari na dubo miki" Nansy ta fad'a tana aje mata ruwa ta fita tun da zata sha magani zuwa tayi ta d'auko ta kawo mata ta tashi tasha sannan ta koma ta kwanta ta yi shiru idon ta a rufe kawai photon d'azu take gani fuskar Zainab dake d'auke da murmushi da sauri ta bud'e ido har da kamar ta firgita nannauyan numfashi ta sauke tana sake sabon juyi ta zubawa guri d'aya ido kawai ta rasa abinda yake mata dad'i Nansy tana gefe tana kallon ta ba tare da tasan taimakon daya dace ta bata ba tunda ta'ki fad'a mata abinda ya same ta balle ita kuma ta san me zatai mata ganin ta juya mata baya yasa ta le'ka fuskarta ta gani ko barci tayi sai taga idon ta biyu ganin hakan ya sa kawai ta tashi ta fita a bedroom d'in jin 'karar bud'e 'kofa da rufewa yasa Amirah jan 'kwafa tana cewa. "Wallahi Aliyu ka yi da 'yar halak zan nuna maka ba'a biyu dani koma wace wannan budurwar zan nemo ta zan tsananta buncike a kan ta har sai na samo inda ta ke zan iya kawar da kowa dan na mallake ka a shirye nake na fara ya'ki domin na 'kwatowa kai na soyayyar ka a kan ka saidai a mutu wannan alkawari nane kuma sai na cika shi saika aure ni Aliyu na rantse bazan yi kaffara ba sai na aure ka ko ka na so ko ba ka so" ta 'karasa maganar ta na sake sabon juyi a ran ta ta ce. "To amma ban san ta ba ban ta'ba ganin ta ba ban san a wacce jiha ta ke ba ta ya zan nemo ta? Ta tambayi zuciyar ta can wani tunani ya fad'o mata mi'kewa ta yi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta duk da kana ganin ta kasan ta yi kuka ko bata fad'a maka ba saboda kar Mama ta gane shiyasa ta d'auki ba'kin glass ta saka a idon nata ta d'auki handbag d'inta da wayar ta ta fito Nansy tana ganin ta, ta fito da sauri ta ce "Aunty Amirah ina zuwa kuma bayan kin ce zazza'bi ki ke ji"? "Zan je wani wuri ne yanzu zan dawo" da mamaki Nansy ta ce "ai gidan su Yaya Aliyun za ki sake komawa" kai Amirah ta girgiza ta na cewa "a'a ba can bane nan anguwar ne ina dawowa ba dad'ewa zan yi ba". "Ok bari tun da haka ne na zo na raka ki"? Da sauri Amirah ta ce "a'a ina dawowa kar ki biyo ni" tana fad'in haka ta fita daga parlon ta yi waje wani shagon photo a bayan layin su ta je photon Zainab data d'auka na wayar ta ta nuna masa tana cewa "S.S Smart dan Allah wannan photon nake so ka wanka min kamar guda goma ka gane"? Kai ya d'aga ya na kar6ar wayar ya ce "ok yanzu ma kuwa tsaya ki tafi da shi" murmushi Amirah ta yi tana samun kujera ta zauna ba jimawa ya fito ya mi'ka mata wayar ta sannan ya bata photunan guda goma cif kamar yadda tace bud'e handbag d'inta ta yi ta zaro kud'i dubu goma ta mi'ka masa tana tashi tsaye tace. "Kai ma ga ladan ka nan duk d'aya na d'auka shi matsayin dubu d'aya goma saboda girman abin da zan yi" "yauwa irin ku ake so Hajiya Amirah na gode sosai Allah ya biya ki". "Amin kar ka damu" ta na fad'in haka ta juya ta tafi daga nan shagon data fita kai tsaye facemask ta saka a fuskar ta akwai wasu 'yan 'kwaya da suke taruwa a wani guri can gefen anguwar su gurin su ta je ta same su sun taru kuwa da d'an yawan su ta ce. "Aiki na ke so kuyi min kowanne ku zai samu dubu hamsin wanda kuma ya samo min abinda nake so nayi masa alkawari rabin million d'aya" su na jin ta ce haka kowa ya d'ago a zabure ya na cewa "wanne kalar aiki ne wannan da za'a ba mu kud'i masu yawa haka ki fad'a mana kawai babu wani abu da baza mu iya yi miki ba" kai ta jinjina ta na bud'e handbag d'in ta, ta d'auko photunan Zainab guda tara ta mi'kawa ogan su tabar d'aya a handbag d'in nata tana kallon sa tace "ka rabawa yaran ka d'ai-d'ai duk wanda ya ri'ki photo d'aya yana da dubu hamsin wannan budurwar ta jikin photon ita nake so ku samo min kawai idan kun samo min ita na yi muku alkawarin zan ba ku rabin million d'aya". "Za'ai yadda ki ka ce zamu nemo miki ita za mu kamo ta mu kawo miki ita nan ko 'yar waye ita a garin nan sai mun samo ta sannan duk tsaron da aka zuba mata ba zai hana mu samu nasarar d'auko ta ba mu kawo miki ita" wani irin daddad'an numfashi Amirah ta sauke ta na cewa "ok ka bani number ka ni ma bari na, baka number na ta yadda idan kun samo min address d'in ta sai ku kira ni ku fad'a min". Takarda da biro ta d'auko ta rubuta musu sannan ta biya su kud'in neman kafin su samo mata ita ta cika musu alkawarin rabin million d'in da ta yi musu kar'ba yayi yana jinjina kai yace "shikenan Hajiya in dai ita ce wannan karki damu zamu nemo miki ita" juyawa ya yi ya na cewa "kai Laburos ku taso mu je yau mun samu na busawa Rakwah kai kuma shiga ka fito mana da Napep mu tafi". Amirah tana tsaye har suka fito da Napep sai da taga sun shiga sun bar gurin ta cije lips tare da sakin murmushi tace "tun da na biya wad'annan 'yan 'kwayar na tabbata maybe a yau buri na zai cika ina da tabbacin zasu nemo min ita dole ta bar min Aliyu idan ta'ki ta bakunci lahira domin zan saka suyi mata mugun fayd'e a cikin wannan kangon bari daga nan na samu Napep ya kai ni gidan su Afifah ba zan koma gida ba zuwa zan yi na nuna mata photon nan maybe ita ma ta san ta" fitowa ta yi daga kangon ta tari me Napep ya kaita a lokacin Afifah tana bedroom su Momy suna parlor ta wuce tana shiga tun kafin ta zauna ta d'auko photon tana cewa. "Afifah kin san wannan"? Kar6a Afifah tayi tana kallo ganin wacce ke jikin photon yasa ta zaro ido waje tare da hangame baki Amirah da take kallon ta ganin ta zaro ido yasa ta fahimci ta san ta kenan humm akwai 'kura kai ta jinjina ta na cewa. "Ya kin san ta ne"? Har lokacin Afifah ba ta iya rufe bakin ta da kyau ba ta ce "eh na san ta man Aunty Zee ce" hura hanci Amirah ta yi ta na cewa "wacece Aunty Zee kuma"? "Wata 'kawa ta ce" d'an zabura kad'an Amirah ta yi jin zatayi karamin hauka a susuce tace "kawar ki ce"?. "Eh man 'kawa tace a ina ki ka samu photon ta"? Daurewa Amirah ta yi duk da yanayin tashin hankalin da take ciki ba ta baiwa Afifah amsa ba sai tambaya da ita ma ta yi mata "a wanne anguwa ta ke"? Ita ma Afifan kai ta girgiza ta na cewa "a'a ni tambayar ki na ke inda ki ka samu photon" ta'be baki Amirah ta yi ta na cewa. "Tsintar sa na yi man a ina ki ke tunanin zan samu ni da ba ta'ba ganin ta na yi ba balle na san ta kawai na gan shi a 'kasa ne ana takawa na d'auke" da mamaki sosai Afifah ta sake kallon photon ta na cewa. "Ki ka tsinta kuma"?. "K'warai a kan hanya ba". "Tabd'ijan dan'kari abun mamaki gaskiya Aunty Zainab ba za ta zubar da photon ta haka kawai a layi ba" huci Amirah ta yi ta na kallon Afifah ta ce "naji kina ce mata Aunty Zainab ko budurwar Aliyu ce"?. "A'a ba budurwar sa bace dama haka nake kiran ta tun da dad'ewa kuma bayan haka dama ai ta fi ni ba sa'a ta bace kawai dai mu na mutunci ne". "Ok ya yi shi ke nan sai ki bata abun ta tun da dama tsintar sa na yi". "A ina kika tsinta ne anan anguwar"? "A'a a titin bayan anguwar mu wajen wa su 'yan 'kwaya". "Kai Subanallahi 'yan 'kwaya kuma? Gaskiya wannan abun mamaki ne sosai da al'ajabi amma shikenan bari kawai na aje shi a guri na" jin abin da ta ce ya sa Amirah cewa "a'a ki tashi mu kai mata kawai har gidan su me za ki yi da shi idan kin ajiye a gurin ki gara ki tashi na raka ki, ki ba ta abun ta maybe ma ta fad'a miki yadda akai photon na ta ya je anguwar mu" girgiza kai Afifah ta yi ta na cewa. "Uhm uhm gaskiya ba zan je a ba idan na kai mata zata damu sosai gara nayi shiru da baki na ba za ta ta'ba sani ba har abada" ganin da Amirah ta yi za ta rusa mata tsari ta ce "saboda me ba za ki iya kai mata ba? Ai gara ki kai mata". "A'a fa ba zan kai ba". "To ki nunawa Aliyu man". "Shi kuma me ye had'in sa da wannan photon idan ya tambaye ni a ina na samu fa" kafad'a Amirah ta d'aga ta na cewa "sai kice masa nice na tsinta a wajen bayan layin anguwar mu". "A'a gaskiya ba zan kai masa ba ina ruwan Yaya discipline anan"?. "Da ruwan sa man ba kince 'yar nan anguwar bace maybe ai ya san ta". "Eh ya santa man sosai ma tun da mu na mutunci" kai Amirah ta jinjina jin abin da Afifah ta ce kamar ta fad'a mata gaskiyar abin fa ya faru sai kuma ta yi shiru kawai ta ce "hummmm" alamar da magana fa wanda sai da ta saka Afifah ta kalle ta ganin irin kallon da take mata yasa ta saki fuska da murmushi saboda kar ta zargi wani abu ta ce "gaskiya kuwa kyakkyawa ce masha Allah" ita ma Afifan murmushin ta yi tana cewa "hum kyau sai kin gan ta a fili ma har d'aukar ido take musamman ki ganta ba Nikaf". "Oh har nikaf take sakawa"? "Ai ita kullum jikin ta a rufe yake ko mayafi bata sakawa hijab ma har kasa yake zuwa mata sannan kafarta da safa ba abin da zaki gani a jikin ta koni da muke islamiyya d'aya kuma muke 'kawaye ne idan ba a gurin alwala ba bana ganin fuskar ta kwata-kwata" kai Amirah ta jinjina mamaki ya gama cika mata zuciya a ran ta tace "to in dai haka ne bata bayyana fuskarta a fili ba taya Aliyu ya san ta shida ya dad'e baya kasar nan sannan da ya gama karatu ma ya dawo ba zama yayi ba ya fara aikin soja sai yayi shekaru bai zo ba gida ba"? Ashe a fili ta yi magana ji ta yi Afifah ta ce. "Nima ban san da yadda akai ya san ta ba" d'an huci ta fitar tare da rufe ido Allah ya sa ba wani abun tashin hankali ta fad'a ba balle har Afifan ta gane sake cewa ta yi "kwarai ki ka ce Zainab sunan ta ko?. "Eh Zainab sunan ta". "Kuma inkiyar gidan su fa"? Ta tambaya ta na 'kure ta da kallo ta ji wacce amsa za ta ba ta "eh to anan anguwar dai kamar an fi cewa gidan su Alhaji Habibu headmaster ko kice gidan su Aminu d'an sanda ko gidan su Sameer me chemist in dai mutum d'an anguwar nan ne kina fad'a masa haka gaskiya gidan su ba a 6oyayye bane" wani irin murmushi farin ciki Amirah ta yi tana jinjina kai tace "ok ya yi nifa tafiya ma gida zan yi". "Ki tafi gida dai yanzun"?. "Eh man". "To amma d'azu ina kika je ba sallama na neme ki na rasa ko dama ba gida ki ka tafi ba"? "A'a gida na je ai shine na tsinci photon a hanya". "Ok na gane sai dai duk da haka ya kamata ki zauna zuwa la'asar sai ki tafi ko"? "A'a tafiya fa zan yi Afifah". "Kai dan Allah Amirah ki zauna please mu na 'yar hirar mu yanzu za ki ga fa la'asar d'in ta yi ba wuya kin ji"? Ganin da ta yi Afifan ba ta son tafiyar ta ya sa ta ce "ok" tare da komawa ta zauna "yauwa ko ke fa bari na zo" Afifah ta fada tana mi'kewa ta fita Amirah kuma ta cire mayafin ta tana cewa "humm masha Allah dama anan anguwar take harna zauna wahalar da kaina ina ba da kud'i a nemo ta zan je na same ta dole ta rabu da Aliyu ko bata so in ta'ki na aikata inda idan an tafi ba'a dawow............. Kiran wayar ta da akai ba'kuwar number yasa ta d'aga ta na cewa "hello waye"? daga can 6angaren ta ji an ce "Hajiya ni ne wanda ki ka baiwa number ki d'azu mun samu wani mutum yace ya san ta har gidan su ma ya sani" kai Amirah ta jinjina ta na cewa "ok nima na samu wacce ta santa an fad'a min har adireshin gidan su amma duk da haka ina zuwa gurin ku yanzu domin aikin bai 'kare ba". "To Hajiya mu na jira" aje wayar ta yi tana mi'kewa da sauri ta d'auki mayafin ta ta mayar shi kafad'a ta d'auki handbag ta fita parlor da mamaki Afifah wacce ta d'ebo musu kayan cinye-cinye daga kitchen ta ce "ina zuwa haka kuma da sauri"?. "Gida zan tafi". "Wai Amirah ba za ki zauna ba"? "Eh tafiya zan yi zan dawo yanzu Nansy ta kira ni ta ke fad'a min wani d'an uwan Maman mu ya zo gidan ya na nema na zan je mu gaisa sakamakon mun dad'e ba mu had'u ba" kai Afifah ta d'aga ta na cewa "ok tom shikenan sai kin dawo" ta na rufe baki Amirah ta yi waje cikin gaggawa ta tari d'an Napep ta shiga kai tsaye gurin 'yan 'kwayar ta koma ta kar6i photunan tunda ta gama aikin ta dasu ta tafi gida ta 'kone photunan dan wanda ta baiwa Afifah ma d'auko kayan ta amma shi ba ta 'kone shi ba tun da aikin bai 'kare ba. Da daren ranar da'kyar Amirah ta iya runtsawa tsabar yadda ta matsu gari ya waye ta je ta samu Zainab tun kafin asuba ta tashi ta zauna har akai kira duk ta na zaune sai da ta ji za'a shiga sallah sannan ta tashi ta yo alwala ta yi sallah gari ya na d'an yin haske ta shiga wanka shaf-shaf ta fito ta shirya a lokacin Nansy ta tashi a barci ita ma ta yo alwalar kallon Amirah ta yi ta na cewa. "Dan Allah Aunty Amirah idan kin tashi ki ri'ka tashi na sallar asuba d'in nan" tsaki Amirah ta yi ta na cewa "uban wa yasa ki saki baki ki na barci wato ni ce baiwar ki me tashin ki daga barci? Ba zan tasa ba idan kin ji haushi ki koyi tashi da kan ki" ta fad'a ta na juyawa ta ci gaba da shiryarwa Nansy ba ta ce mata komai ba ta juya ta fara sallah ganin haka ya sa Amirah d'aukar handbag d'inta ta yi waje ta d'auki mota ta bar gidan a d'ari. Lokacin da ta zo anguwar tambaya ta yi tayi akai mata kwatance ta zo har 'kofar gidan sannan 'karfe bakwai daidai ba ta fito daga motar ba ta ci gaba da zama har kusan bakwai da rabi sannan ta bud'e murfin motar ta fito waje tare da jingina a jiki ta na 'karewa gidan kallo ganin yadda gate d'in ya yi tsatsa ga shi duk fentin gidan ma ya kod'e kamar ba'ai ba tsaki ta ja ta na zubar da yawu tare da d'aukar towel ta toshe hancin ta da shi ta na cewa. "Yanzu dama Aliyu ya rasa in da zai ji ya na son matar aure sai a irin wannan da'ki'kin ru6a66en gidan da talauci ya gama samun gurin zama a cikin sa? Anya nan ne gidan kuwa wancan budurwar ta jikin photon ba ta yi kama da 'yar talakawa ba ko dai wad'anda na tambaya ba su fad'a min gaskiya ba amma bari tukuna na fara aikawa idan ba nan d'in ba ne sai na ji" ta na rufe baki ta ga wani yaro almajiri ya fito daga gidan da robar barar sa a hannun sa alamar abu ya kar6o Kiran sa ta yi bayan ya zo ta ce. "Kai a nan gidan ka ke"? Kai ya girgiza ya na cewa "a'a daga makarantar mu na ke zuwa ni almajirin gidan ne aiki na ke musu" da mamaki Amirah ta ce "almajirin gidan me na sama ya ci balle ya baiwa na 'kasa yanzu wannan fatararren gidan har d'an aiki su ka ajiye amma dai aikin zubar da shara ka ke mu su ko"?. "Eh da zubar da shara da d'iban ruwa" . "Humm na canka daidai kenan dama sai dai zubar da sharar kuma idan ka zubar me su ke baka". "Abinci su ke ba ni safe da rana". "Ok yanzu wannan abinci ne kenan ka kar'bo bud'e mu gani" bud'e murfin robar ya yi taga tuwon masara da miyar ku6ewa ta sha manja jawur da ita amma tsabar wula'kanci da sauri ta ja baya ta na sake toshe hanci harda yun'kurin amai bud'e jakar ta, ta yi ta d'auko sweet ta jefa a bakin ta tare da sauke ajiyar zuciya ta ce. "Allah ya tsare gidan da ake karyawa da tuwo anan Aliyu ya 'karar da soyayyar ta sa wato ma budurwar da ya amince da ita rainon wahala ce humm" yaron ta sake kallo ya na tsaye bai tafi ba kafin ta kalli gidan a 'kyamace ta ce "shiga ka ce wai ana sallama da Zainab a waje idan ka fito zan baka dubu d'aya ka ji"? Da sauri yaron ya d'aga kai ya na cewa "to" ya juya ya shiga gidan a 'kofar su Zakiyyah ya ke aiki dan haka can ya fara nufa had'uwa su kai da yaron 'kofar zai fita ya ce. "Nan ne 'kofar su Zainab"?. "A'a ba nan ba ne zo in nuna maka" juyawa su kai tare da yatsa ya nuna masa ya na cewa "ka ga wancan 'kofar ta 'karshe can za ka je" wucewa almajiri ya yi ya na shiga in da aka nuna masa ya ce "assalamu alaikum wai Zainab ta na nan"? Juyawa Zainab dake gurin wanke-wanke ta yi ta na cewa "eh ina nan waye ya aiko ka"?. "Nima ban san ta ba wata ce ta na waje ita ce ta turo ni" kai Zainab ta d'aga duk da ta ji mamaki da aka ce wata ce a waje ta ce "kaga ka je kace mata ta shigo" to ya ce ya na fita Zainab da har lokacin ta kasa daina mamakin wacece ta tsaya a waje take neman ta maimakon ta shigo gidan ta san dai ba Afifah ba ce kuma ba su yi alkawari da wata ba balle ta ce ko d'inki aka kawo mata to kodai matar Yaa Sayyidi ce? Tabbas ita c......... Dawowar yaron yasa Zainab kallon sa ta ce "ya akai ta na ina"? "Tana wajen wai tace ki fito". "Na fito sai kace wata namiji zan fito mata waje idan bazata shigo ba ko ma wacece ta koma inda ta fito je ka kawai" juyawa yaron ya yi zai tafi Umma ta fito daga d'aki ta dakatar dashi da cewa "kai tsaya kace tana zuwa" jin abin da Umma ta ce ya sa a damuwance Zainab tace "Umma". "A'a Zainab ke ce ya kamata kice wa wani babu kyau wula'kanta d'an adam kije ki gani idan jira ta ke ki fita ki shigo da ita fa? Ba lallai ta ta'ba shigowa gidan ba tashi ki je" mi'kewa ta yi duk da ran ta bai so ba amma ita ma yanzun kuma ta yi tunanin ko jira ta ke ta fita ta shigo da ita sai dai ta yi mamaki ne saboda ba'a ta'ba yi mata hakan ba duk masu kawo mata d'inki kan su tsaye su ke shigowa, d'aki ta shiga domin ta d'auko hijab ran ta fal da wasuwasi yayin da Umma ta maye kujerar ta da ta tashi za ta 'karasa wanke kwanukan. Fita almajirin ya yi Amirah na ganin sa ta ce "ka ce ta fito waje ina jiran ta"? "Eh na fad'a mata yanzu za ta fito" numfashi Amirah ta sauke cikin jin dad'i ta ce "yauwa ga dubun ka amma ba zan ba ka ba sai ka zubar da wannan tuwon anan gurin ka je ka sayi abinci me kyau wanda zai bi lafiyar ka ka ci ko? Ganin almajirin yai shiru ta ci gaba "kaga idan ka zubar zan 'kara maka wata dubun ka had'a guda biyu ka ji"? Kai ya girgiza ya na cewa "a'a ni ina son tuwo na kuma Malam ya fad'a mana ba kyau wula'kanta abinci" jin abin da ya ce ya sa Amirah kallon sa ta ce "ok kar6i ka je" mi'ka masa dubun ta yi ya kar6a ya yi mata godiya ya juya ya tafi da kallo Amirah ta bi shi ta na jinjina kai dama ta saka ya zubar ne ta yadda idan Zainab ta fito za ta ya6a mata magana akan haka ta caccaka mata rashin mutunci wanda har ta mutu ba za ta manta ba sai kuma akai sa'a yaron me hankali ne. Fitowar Zainab da dogon hijab d'in ta kamar kullum tana shirin sa nikaf Umma da ta kalle ta ta ce "haba Zainab nan da 'kofar gidan sai kin saka Nikaf kuma fa yaron yace mace ce ina shigowa da ita za ki yi kawai"? Sauke ajiyar zuciya Zainab ta yi ta na aje Nikaf d'in akan keken d'inkin ta dake kofar d'aki sannan ta fita kusan karo su kai da Asabe wanda da sauri Zainab ta matsa mata hanya cikin ladabi amma duk da haka sai da ta biyo ta saitin ta, ta bangaje ta na cewa. "Ni sa'ar kice za ki tare min hanya ba dake nake kishi ba da tsohuwar kine dan haka ki fita idona mara kunya kawai" kallon mamaki Zainab ta yi ma ta ba tare da tace komai ba ta bi ta gefen ta, ta wuce kallon ta Asabe ta yi ta na cewa "ke sumore ina za ki je yau kuma babu dan gadon (nikaf) ko kanki ya gwaro da bango shine zaki koyi fita haka babu nikaf d'in ki nunawa samari fuskar ko Allah zaisa wani ya kwashi tsiya yakai gidansa"? Tari da bai kama Zainab ba ba tai mata ba ta na jin ta amma ta share duk da ya da girma da Asabe take a gurin ta daidai da ranar daya ba ta ta'ba mata rashin kunya ba tana mata kallon uwa matsayin ta na matar ubanta fita Zainab ta yi daga gidan can ta hango Amirah tsaye a jikin mota da waya a kunnen ta alamar magana ta ke duddubawa Zainab ta yi ko za ta ga me kiran na ta domin ba ta ta'ba kawowa a ran ta cewa Amirah ba ce tun da ba sanin ta, ta yi ba kuma ba ta'ba ganin ta, ta yi ba amma ba kowa sai ita d'in dai 'karasawa ta yi gurin ta har lokacin wayar ta ke ba ta daina ba za ta yi magana ta ga ta d'aga mata hannu alamar ta dakata takaici ne ya kama Zainab sosai domin ta tsani rainin wayo ita kuma wannan budurwar kamar ta ga haka abun ya ke ba ta'ba ganin ta tayi ba sai a yau juyawa ta yi za ta tafi ta ji Amirah ta kamo hijab d'in ta kallon ta tai sai kawai taga ta girgiza mata kai ta na sauke wayar tare da zare glass d'in idon ta, ta ce. "Barka da safiya malama Zainab na san ba ki san ni ba baki ta'ba gani na ba sai yau hakan zai baki mamaki amma wata 'yar bazata nazo miki da ita kalli ki gani" ta fad'a tana nuna mata photo a wayarta kallon photon Zainab ta yi sosai idan ba gizo idanuwan ta ke mata ba Aliyu ne zaune tare da wannan budurwar a wani kyakkyawan guri da alama ba Nigeria bace wata 'kasar ce domin ta bayansu ta ga yanayin gine-ginen 'kasar sannan ga fararen mutane a bakin ruwa su kai photon. "Wannan ya baki amsar tambayar da ke zuciyar ki ta ko ni wacece kuma daga ina na ke haka ne"? D'agowa Zainab ta yi ta na kallon ta tace "to me ye had'i na da wannan"?. "Au tambaya ki ke me ye had'in ki da shi? To amma tsaya ma dai tukuna na tambaye ki kar na yi kwafsi ba ke ce Zainab ba"?. "Eh ni ce" wani irin kallo Amirah ta yi mata ta na cewa "ke ce kuma amma za ki bani irin wannan amsar ba ki ga abin da na nuna mi ki ba"?. "Na gani me ye damuwa ta da shi"?. "Ok ba ki da damuwa da hakan amma ta ya zan yarda da ke ko ki na tunanin wannan kakkaucewar da ki ke ba zan iya gano ki ba ne kin wani fuske kamar ba ki san komai ba ni za ki rainawa hankali"? Sosai ran Zainab ya soma baci jin zata mayar da ita shashasha kamar yadda ta mayar da kanta ta ce "ke saurara kin ga dan Allah ban san akan me ki ke magana ba za ki iya tafiya bani da lokacin wannan banzan shirmen". "Shirme? Ni ce nake miki shirme? Har yanzu baki fahimci maye ma'anar zuwa na nan wajen ba kenan amma ki kalle ni da kyau kin san dai matsayi na da girma na nafi 'karfin tsayuwa a irin wannan 'kofar gidan amma na cire duk wani girma nazo saboda mu daidai ta dake ki fita daga cikin rayuwa ta" da mamaki Zainab ta nuna ta da yatsa ta na cewa "rayuwar ki"? Jinjina kai Amirah ta yi ta na cewa. "Eh rayuwa ta ko har yanzu ba ki gane ba tun d'azu dana nuna miki photo na da Aliyu"? Shiru Zainab tai domin kanta ya gama kullewa ta rasa abun da Amirah ta ke nufi ganin haka ya sa Amirah yin murmushi ta na cewa "ko har yanzu ba ki fahimta bane bari na sake nuna mi ki dalilin zuwa na gurinki da kuma abin da za mu yi magana a akan sa" sake kunna wayar ta yi ta na juyo mata da ita yadda za ta gani sosai ta ce "ga abin da ya kawo ni gurin ki" kallon secreen d'in wayar ta yi taga photon Aliyu ne wanda ya ke shi kad'ai da kayan dai da bata son ganin sa da su wato 3Quarter ba'ki sai farar singilet ya na zaune akan kujera da wata flower a kusa da shi tsabar takaici Zainab ba ta san lokacin da ta ja tsuka ba tana kau da kai fuskar ta a had'e ta ce "wai ke me ye haka ne"?. Sauke wayar Amirah ta yi ta na kallon ta, ta ce "fatan kin san waye wannan da matsayin sa kin san ya fi 'karfin d'iyar talaka irin ki dan haka na zo na miki gargad'i a kan sa ne ki fita hanyar sa domin shi d'in da ki ke gani ya kasance masoyi na ne ni kad'ai zai aura mu yi rayuwa tare ba zan ta'ba had'a kishi da kowacce yarinya ba duk matsayin ta balle kuma 'yar talaka irin ki" wani razanan nan kallo Zainab ta yi mata ran ta a mugun bace jin zata raina mata hankali a gidan uban wa take son Aliyu waye ya fad'a mata har zata zo tana mata ihu Allah ya sauwake ta rasa wa za ta aura sai Aliyu tabd'ijan tashin hankali ai gara ta zauna haka babu aure har abada.................... "Tambayar ki fa nake kin yi shiru ki bani amsar da nake son ji" zuciyar Zainab na turiri ta ja tsaki ta na cewa "ba ni da lokacin amsa wannan wofantacciyar jakar da'ki'kiyar tambayar ta ki kin gane ina da abubuwa masu mahimmanci daya fi wannan shirmen banzan ina ruwa na da wani Aliyu me ye had'i na da shi ba ala'kar komai tsakanin mu na rasa wanda zan aura sai shi? Ba had'in hanyar mota da jirgi zan tafi Idan kin ga dama ki ci gaba da tsaiwa a nan har 'karshen rayuwarki" tun da ta fara magana Amirah ta bud'e baki da ido ta na kallon ta nuna kan ta tayi ta na cewa. "Keee ni ki ke fad'awa haka"?. "Amfad'a miki hakan d'in ke wace ba haihuwan ki akai ba kamar kowa ba fad'a min dame ki ka fi wani? kin ga dan Allah ki kama kan ki bada iri na ake wannan shashancin ba bana iya jure magana da ta6a66iya". "Ni ce ta6a66iyar"?. "Tambayi kan ki ni ba ni da lokacin ki sannan zan gargad'e ki daga yau kar ki kuskura ki sake had'a ni da Aliyu idan ran ki yayi dubu sai ya 6aci domin zan d'auki matsakin da ba ki ta'ba zato ba" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin ta yi shigewa gida 'kamewa guri d'aya Amirah ta yi tare da d'auke numfashi na wani d'an lokaci tsananin mamakin Zainab ya kama ta kai ta jinjina ta na sauke ajiyar zuciya lallai tana da aiki a gaban ta da Aliyu da Zainab kusan halin su d'aya akan iya fad'ar magana amma ta san yadda za ta bi da su shiga motar ta tayii ta bar gurin amma ta san a ran ta sai ta sake dawowa gurin Zainab nan da 'yan kwanakin nan ba za ta'ba kwantar da hankalin ta ba sai ta ga Zainab ta amsa mata babu ita ba Aliyu domin yanzu ma ba ta yarda ba soyayya su ke ba gani ta ke kamar ta 6oye mata gaskiya ne. Zainab kam ta na barin gurin Amirah da ta koma gida ganin Umma ta 'karasa wanke-wanken ya sa ta cire hijab d'in ta, ta na zama a kujera ta fara d'inka kayan data yanka.. Amirah gida ta koma amma sakamakon jin zuciyar ta sai bugawa ta ke ta kasa samun kyakkyawar nutsuwar da za ta iya yin breakfast ma 'kara mi'kewa ta yi ta na d'aukar key d'in motar ta, a hankali ta bud'o 'kofa ganin ba kowa maybe Nansy ba ta gidan tun ba ta gan ta ba tun shigowar ta, da sauri ta fita harabar gida ta sake d'aukar mota ta yi gidan su Aliyu ta so ace ya na nan ta je ta same shi yau ayi ta, ta 'kare amma ganin ba alamar sa ya sa ta wuce zuwa gurin Afifah ta yi sa'a kuwa ita kad'ai ce ta na kwance akan gadonsu da littafin linguistic students a hannun ta, ta na karantawa zama Amirah ta yi ta na huci gabadaya kishi ya rufe mata ido takaici ya gama cika ta da'kyar ta ce. "Afifah dama da gaske ne Aliyu ya na da budurwa"? Ba tare da Afifah ta daina karantun ba sama-sama ta ce "me ya sa ki ka tambaye ni"? Fuskar Amirah a tamke ta ce. "Saboda ina so na sani"? Kai Afifah ta girgiza ta na cewa "ni wallahi Amirah ban sani ba idan ya na da ita d'in ko ba shi da ita Allah masani" Afifah na rufe baki Amirah ta ce "ya na da ita man". "Ok shi ne ya fad'a miki ko ganin ta ki kai"? "Hum'um Aliyun ne zai fad'a min ganin na yi da ido na" jin abin da ta ce ya sa Afifah tashi zaune da sauri ta na zaro ido da mamaki ta ce "kai dan Allah tare ki ka gansu". "A'a". "To ya akai ki ka san budurwar sa mu kuma ba mu sani ba"? Cije lips Amirah ta yi tuna yadda su kai da Zainab d'azu da ta je gurin ta, ta ce "saboda bai shafe ku ba" komawa Afifah ta yi ta kwanta ta na cewa "ai kuwa dai ina ya shafe mu Allah ya taimaka ashe Aunty na ta kusa zuwa gidan na mu kenan tun da har magana ta fara fita manyan 'kawayen Yaya discipline sai ku fara shiri domin gaskiya bikin na ku ne" ta fad'a ba tare da ta kalli yanayin da fuskar Amirah take ba wacce ta cika da 6acin rai kamar zuciyar ta ta fashe haka take ji a wannan lokacin musamman da Afifah tace Auntyn ta, ta kusa zuwa gidan wani irin ba'kin kishi ne ya sake lullu'be ta ta ji ran ta ya cika da fushi ba tare da ta sake cewa Afifah komai ba ta mi'ke ta bar bedroom d'in ita ma Afifan sakamakon ba ta so idan ta na karatu ta ri'ka tsayawa ko tambayar inda za ta je ba ta yi ba har ta fita. Amirah kam da ta fito cikin sauri kamar za ta tashi sama ta yo harabar gidan daidai Aliyu ya shigo ta 'karamar 'kofar gate d'in numfashin ta na fita da a sukwane cikin azama ta yi wajen inda ya ke tsabar sauri kamar za ta kifa takalman 'kafar ta ma da ya ke masu santsi ne ji ta ke sun hana ta tafiya da kyau zubar su ta yi ta tafi haka ba takalmi gudun kar ya bud'e 'kofar da ya ke iya shiga part d'in sa idan ba ya son bi ta parlor kuma Momy ta na nan balle ta zagaya ta shiga da 'karfi ta ce. "Aliyu tsaya dan Allah ina so za mu yi magana" ta fad'a muryar ta na rawa dakatawa ya yi ya na kallon ta tabbas ba ta cikin yanayi me kyau ka na ganin ta ka san cewa a hargitse ta ke 'karasawa gurin sa ta yi ta na huci da'kyar ta ce "Aliyu ashe dama wannan ce budurwar taka da ka ke 6oye min da ka 'ki fad'a min ma ni da na damu na san wacece ita na binciko ta da kai na" jin abin da ta ce ya sa shi kallon ta ya na cewa. "Wacece a ina ki ka gan ta"? Kau da kai Amirah ta yi duk da ta na son kallon na sa amma 6acin ran da ta ke ciki ba zai bari ta ji dad'in kallon na sa ba. "Tambayar ki fa na ke wacece a ina ki ka gan ta"?. "A gidan su" da mamaki Aliyu ya kalle ya na cewa "a gidan su kuma"? Kai ta jinjina "k'warai gidan su zuwa na yi mu yi magana da ita a kan ka duk da ta 'ki ba ni had'in kai". "Mee? Kin yi hauka ne me ki ka ce mata"? Had'e rai ta yi ta na cewa "wannan kuma bai shafe ka ba tsakanin mu ne". "Please Amirah me ki ka fad'a mata"? Ta'be baki ta yi ta na cewa "ka je ka tambaye ta man ai ka fi ni kusa da ita saboda tsabar ta raina min hankali ni za ta yiwa karatun ta na goge hadda har da nuna min ita ba wani abu tsakanin ku saboda ga mahaukaciya ni kuma sai na yarda ta na wani abu kamar wacce ba ta san komai ba ni za ta mayar 'karamar yarinya har da wani wai ba ta san ka ba kar na raina mata wayo babu soyayya tsakanin ku mtwwww" ta fad'a tana jan tsaki tare da bud'e wayar ta, ta nuna masa video da ta yi wa Zainab ba tare da ta sani ba a lokacin da su ke maganar kar6a Aliyu ya yi ya na kallo kafe shi Amirah ta yi da ido ta na jiran ta ji me zai ce murmushi ta ga ya yi tare da jinjina kai ya mi'ka mata wayar ta bayan ya yi delete d'in video sannan ya ce. "Ya yi kyau tabbas kin yi 'ko'kari ya kamata a jinjina miki" ya na fad'in haka ya wuce ta zai bud'e 'kofa da sauri ta sake shan gabansa idon ta ya fara kawo 'kwalla ta ce "Aliyu wai me ka ke yi haka ne, kenan ka za6i bare sama da ni shekarar mu nawa a tare ka san ni ka san hali na babu wani abu nawa wanda ya yi saura ba ka sani ba a ina matsalar ta ke ka fad'a min na gyara dan Allah" had'e rai ya yi ya na cewa. "Ba ni hanya na wuce kin ji na ce ki na da wata matsala ne"? Kai ta girgiza a rud'e ta ce "to indai haka ne dan me za ka yi soyayya da wancan budurwar"?. "Wa ya fad'a mi ki soyayya mu ke yi da ita"? "Ba fad'a min a kai ba da ido na, na ga photon ta akan fuskar laptop d'in ka da kan secreen d'in wayar ka ko nan za ka ce min ba ita ba ce"? Tamke gira ya yi ya na cewa "eh ita ce man ki na tunanin zan 6oye miki ne"?. "Aliyu me ka ke nufi na ga gidan su ba gidan arziki bane ba 'yar mai kud'i bace hatta gate d'in gidan ya yi tsatsa ya lalace fentin gidan duk ya kod'e ga shi abincin da su ka karya da shi yau ma tuwon masara da miyar ku6ewa ne wanda ya kwana me ye abun so a irin 'yar wannan gidan a yadda ka ke da kyau da ajin nan kamata ya yi ka samu 'yar manyan mutane irin ka, ka aura wacce ta dace da tsarin rayuwar ka domin yanzu auren 'kwarya tabi 'kwarya ake yi"?. "A ina kenan"?. "A ko'ina ma kuma ka tambaya ka ji d'an mai kud'i irin ka sai da 'yar mai kud'i iri na sannan d'an talaka sai ya auri 'yar talaka irin sa an raba kowa ya auri sashin sa" zuba mata ido ya yi yana kallon ta kamar me nazarin maganar ta daga baya ya yi murmushi ya na nuna ta da yatsa ya ce "kenan yanzu campaign ki ke yi wa kan ki a waje na"? Ba kunya ta jinjina kai ta na cewa. "K'warai kuwa ka na tunanin zan ji nauyin fad'a maka abin da ya ke damun zuciya ta ne"?. "Hakan gani ki ke kin burge"?. "Tabbas". "To me ye ribar ki a nan"? "Riba ta shi ne ka yarda da abin da nace ka bani soyayyar ka da zuciyar ka ni kuma na yi maka alkawarin zan kula da kai fiye da yadda ka ke tunanin waccan budurwar za ta yi maka za ka samu farin ciki da kwanciyar hankali tare da ni" kai ya girgiza ya na gyara tsaiwar shi ya ce "Amirah ba zan 6oye mi ki ba ina da zuciya a 'kirji na amma tamkar babu ita domin na riga na yi kyautar ta na dad'e da mallakawa wata ita babu gurbin da zan iya saka soyayyar kowacce 'ya mace bayan ita ina so ki fahimci abin da na ce miki ita wancan yarinyar da ki ke magana a kai 'yar talakan wanda ba komai ba ita ce rayuwa ta burin na ta zama uwar 'ya'ya na duk wani motsi da son ta na ke yi bana jin koda mutuwa ta yi zan iya maye ta da wata ita kad'ai ce a gaban Aliyu ita ce mudubin da yake duba rayuwar sa ita d'in ba iya zuciyar sa bace duniyar sa ce gabadaya kin gane" Juyi sosai kan Amirah ke yi ta na kallon sa dishi-dishi numfashin ta ya na neman d'aukewa da'kyar ta ke jan iska sosai yadda zuciyar ta ta ke bugawa kuwa zai wahala idan nan gaba bata samu ciwon zuciya ba wani irin yawu mai d'aci ta had'iye da'kyar ta ce. "Aliyu ka na fad'ar wad'annan kalaman ne dan ka ga yadda zan yi"? "A'a ba ina fad'a ne saboda dad'in baki ba ina fad'a miki abin da ya ke zuciya ta ne Amirah ki tsaya iya matsayin ki na 'yar gidan abokin mahaifi na kar ki sa kan ki inda Allah bai kai ki ba tun da mu ke da ke ban ta'ba ji a rai na daidai da rana d'aya na aure ki ba kawai dai na d'auke ki matsayin 'kanwa gare ni ba kamar ke yadda ki ke d'auka a zuciyar ki ba kin gane" shiru tai ta kasa magana sai huci da turiri da ya ke faman fitowa daga ran ta kamar ta mutu ta huta haka take ji hawaye fal idon ta, ta ce. "Dan Allah Aliyu da gaske ne ya akai har ta yi nisa a cikin zuciyar ka haka ka ba ta babban matsayi ba tare da na ankara ba har ta yi min nisan da ta sa na kasa banbamce fari da ba'ki mene asalin ta yaya ka d'auke ta ita d'in wacece"? Kai tsaye ba tare da wani gargada ba ya ba ta amsa. "Zuciyar Aliyu ce" zaro ido waje ta yi ta na kallon wannan hawaye ta ya'ki dannuwa sai da su fito waje shar-shar su na bin kuncin ta, ta kalle shi ta na cewa "Aliyu ita d'in zuciyar ka ce"? "Eh ita d'in she's my whole life ba iya zuciya ta ba ce" baki ta bud'e za ta yi magana ta kasa kai ya girgiza mata ya na cewa "kome zan fad'a miki yanzu ba za ki fahimce ni ba amma daga baya za ki gane gida za ki tafi ko wani wurin za ki je daga nan"? Tsabar takaici ko iya bashi amsa ba ta yi ba sai wucewa da ta yi da sauri taje ya d'ebi takalmin ta nufi gurin motar ta, ta bud'e ta shiga kawai ta kife kan ta, ta kama kuka sai da ta yi me isar ta idon ta ya yi jajur ta koma sauke ajiyar zuciya sannan tai wa motar key ta bar gidan koda ta koma gida su Mama duk suna parlor da ta yi sallama gudun kar su ga idon ta kawai ta wuce da sauri ta shiga part d'in su jin numfashin ta ya fara sama-sama alamar Asmar ta na son tashi ta d'auki anhela da sauri ta bud'e murfin ta fesa a bakinta sau uku sannan ta aje tana huci toilet ta wuce ta wanke fuskar ta, ta fito tare da zuwa gaban mirror ta zubawa kan ta ido tai shiru kamar me tunani can ta ja tsaki mai 'karfi tana baro gaban mirron ta dawo bakin gado ta zaune tare da dafe kan ta da hannu biyu kawai maganar da su kai da Aliyu d'azu ne take dawo mata sabuwa tana mata yawo a cikin 'kwa'kwalwar ta sabin hawaye ne masu zafi suka ci gaba da zuba mata gudun kar Nansy ta shigo ta same ta yasa ta tashi ta sakawa kofar lock sannan ta dawo ta fad'a gado tana fashewa da kuka tayi ta yi kamar baza ta daina ba daga baya dole ta yi shiru 'karshe barcin damuwa da ba'kin ciki ya d'ebe ta wanda ko nisa barcin nata bai yi ba ta fara mafarkin Aliyu suna tare da Zainab a gida d'aya ita kuma ta je ta zuba musu ido ta na gefe tana kallon su a firgice ta farka tana tashi zaune ta soma kalle-kalle ganin a d'akin ta take yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da runtse ido jin yadda kanta yake wani irin mugun sara mata da ciwo idonta a rufe ta koma ta kwanta domin duk ciwon da kan na ta ke mata bai kai maganganun da sukai da Aliyu d'azu ciwo ba kuma wannan ciwon kan kawai zai warke ne idan har Aliyu ya daina furta mata kalmar cewa ba gurbin da zai saka wata a zuciyar sa. *** * ** Sakamakon Zainab ta riga ta yi graduate yanzu ba school ta ke zuwa ba sai iya islamiyya shi ya sa kullum ta na gida sai lokaci zuwa lokaci ne ma dai ta ke d'an zuwa gidan Aunty Murjah ta wuni ta taho d'inkunan mutane da su ke hannun ta, a ta ke son 'karasawa yanzu D'an Yana take son zuwa idan an yi hutun islamiyya can ne ta dad'e ba ta je kuma Aunty Murjah ta fad'a mata idan ta saka lokacin tafiya ta kira ta fad'a mata za su tafi tare ita ma ta yo kamar kwana uku sai ta taho ta baro Zainab d'in a can. Ta na zaune a d'aki ta na had'a shampoo ta kunna wa'azi a wayar ta Afifah ta kira ta murmushi ta yi lokacin da ta d'aga ta ce "hello Afifah ya ki ke"? "Lafiya lau Aunty Zainab kwana biyu shiru idan babu hello ai akwai hay ba 'kira mai zaici gawayi"?. "Tofa da na yi me"?. "Kai ji dai ina ta kiran wayar ki a rufe kuma kin san Yaya discipline ya na gari ba zai bar ni na fito ba shi ya sa ban zo naga ko kalau ki ke ba" "Ayya Afifah yi hakuri lafiya 'kalau na ke waya ta ce shekaran jiya haka kawai ta d'auke ita kad'ai na baiwa Yaya Sameer ya duba min jiya kuma ta wuni a rufe shi ya sa ki ka kira ba ki same ni ba. "Oh na san dai halin lafiya ba za ki bar wayar ki ta kwana a rufe ba dama na kira ki ne dan Allah littafi na ya na gurin ki"? "Eh ya na nan littafan na ki ai guda biyu ne ba d'aya ba". "Yauwa to dan Allah ta ya zai same ni yanzu ni ba za a bar ni na fito a kawo" kai Zainab ta d'aga ta na cewa "tom bari na nemi yara sai na ba su, su kawo mi ki yanzu" ta na rufe baki da sauri Afifah ta ce. "A'a Aunty Zee". "Kamar ya a'a"? "Uhmgaskiya a'a ni ke nake so ki kawo min da kan ki". "Amma me ya sa sai ni Afifah shampoo na ke had'awa" marairaicewa Afifah ta yi ta na cewa "dan Allah Zainab kwana biyu ba mu had'u ba yau kam ki zo ki d'an ta ya ni hira ban san me ya sa ba bakya son shigowa gidan mu ba"? Shiru Zainab tai cikin rashin jin dad'i za ta iya rantsewa ba ta shiga gidan su Afifah sau uku ba tun da take a rayuwar ta yanzu har ta manta ma yanayin tsarin sa................... "Kin yi shiru Zainab ko na turo su Fati su zo su kar6a min"? "A'a kar ki damu ba sai kin turo su ba gani nan zuwa yanzu zan kawo mi ki" murmushi Afifah ta yi ta na cewa "yauwa masha Allah ko ke fa Aunty Zee-Zee na har kin sa na ji dad'i ina jiran ki" ta na fad'in haka ta sauke wayar ta na mi'kewa ta ce "alhamdulillah bari na hada mata liyafa domin a rayuwa ta ina tunanin kamar yau ce rana ta farko da Zainab za ta shigo gidan mu". "Wacce Zainab kenan" Elham tai maganar ta na kallon Afifah "Zainab fa ta gidan su Yaya Sameer man abokin ya discipline ai kun san ta a islamiyya tun da ta na shiga ajin ku". "Oh malama zaki ce min sai nafi ganewa ayya ai Aunty Afifah kin yi dacen 'kawa sosai bari ma ni na dauko littafi na daga ta zo ta dora min kafin lokacin tafiya islamiyya ya yi". "To kin gani dai bari ni na sama mata abubuwan tarbar ba'ko domin tun da mu ka taso ban ta'ba ganin ta a gidan nan ba yau d'in ma kamar mafarki na ke ji sai dai idan na gan ta ta zo da gasken d'in sannan ne zan yarda" dariya Fati ta yi ta kallon ta tace "kai wallahi Aunty Afifah ke ma dai". "Ah to dole nace haka kunga laifi na ne"?. "Ina a'a bari mu ma mu taya ki had'awa" mi'kewa su kai cikin zumud'i Afifah ta ce "yauwa 'yan 'kannai na ku mu je" gabadayan su, su ka nufi kitchen Aliyu na kallon su kome suke sai dai ya ji d'an mamaki da ya ji suna cewa wai Zainab za ta zo gidan anya ba kunnen sane bai ji daidai ba idan kuwa da gaske za ta zo d'in yana fatan Allah ya sa har ta tafi Amirah ba za ta zo ba domin akwai matsala idan su ka had'u anan tun da 'yan gidan ba su sani ba gashi ita ma Zainab d'in ba furta mata ya yi ba da zarar Amirah ta ta'bo ta fad'a hakan zai wargaza masa tsarin sa". Tashi Zainab ta yi bisa dole dan kada Afifan ta ji babu dad'i shi ya sa za ta je sai dai ba ta so tana baya baya da Afifah ne saboda ba ta son ayi mata kallon mai son zuciya tun da ita 'yar talaka ce su kuma masu kud'i ne sannan masu mu'kami sanannu d'an gyara jikin ta yi ta shafa powder da d'an lipstick ta d'ebo litattafan daidai zata fita kofar su ta had'u da Umma da mamaki ta ce. "Umma ina ki ka je harda hijab"? "Mun shiga gurin hajiya ne taron mu tai matan 'ya'yan ta wai kwana biyu ta ga sun daina bata kud'in kashewa ko mune mu ka hana su ba ta" murmushi Zainab tai ta na d'an girgiza kai ta ce "wato hajiya ba za ta ta'ba daina rigima ba saima abinda ya 'karu tun da kullum tsufa take haka za ku yi ta hakuri da ita". "To ya mu ka iya Zainab Hajiya uwa ce dole mu bita duk yadda ta ke so kawai dai fatan mu shi ne mu rabu da ita lafiya" d'aga kai Zainab ta yi ta na sauke ajiyar zuciya ta ce "Umma zan fita" da mamaki Umma ta kalle ta tana cewa "Zainab ina za ki je"?. "Ehmm dama neman ki zan je na fad'a miki zan d'an shiga gidan su Afifah ne na kai mata littafin ta". "To shikenan sai kin dawo kar ki dad'e kin ga d'inkunan mutane sun yi yawa ga bikin gidan Dattijo ya kusa kuma ko mutum biyu ba ki wa ba". "Eh Umma ba zan dad'e ba yanzu zan dawo in sha Allahu" ta na rufe baki su ka ji daga bayan su ance "lalalahhhhh kai jama'a gaskiya zilama ba tai ba a rayuwa wato Zainab gidan wannan Minister d'in Alhaji Ahmad za ka shiga ko harda fakewa da daukar littafi dan munafinci bayan maula za ki je Allah ya sauwa'ke a haka za ki 'kare ba aure sai yawo a gari kamar ledar pure water" had'e rai Umma tai ta na nuna Asabe da yatsa ta ce "Asabe ki iya bakin ki akan 'yata domin baki isa ki ramar min ita ba alhamdulillah ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli ya ci riba kuma riba mai yawa ma kuwa bari ki ji na fad'a miki kaf gidan nan daga wad'anda su kai auren har da 'yan matan ba za a ta6a samun wacce za ta kama 'kafar Zainab ba a komai ta wuce in da bakya tunani ba dan cin fariya ba na fad'a miki haka sai gaskiya" ta'be baki Asabe tai ta na saki gud'a da shewa ta ce "ahayye nanaye yau nake ganin sabon salo kiran sallah da usur ji min mace wato ke ce mai goya mata baya shi ya sa ta'ki aure sai cin kud'in wannan bawan Allan ku ke me ye ma sunan sa? Yaa Sayyadi malamin islamiyyar ku ko"? Ta fad'a tana kallon Zainab wacce ta sunkuyar da kan ta 'kasa. "kuka ki ke ne dan na fad'i gaskiya"? D'ago fuska Zainab tai tana kallon ta tare da girgiza kai za tai magana Umma ta dakatar da ita "tafiyan ki Zainab ke 'ya ce a gurin ta koda bata son haka ni ce daidai da ita" wucewa Zainab tai cikin damuwa domin ba ta son yiwa Umman musu shi ya sa da tace ta tafi kawai ta wuce d'in amma ba dan haka ba yau sai ta fad'awa Asabe maganar da har ta mutu ba za ta ta'ba mantawa da ita ba. Ta na turkarar 'kofar fita tun daga ciki ta fara jiyo muryar Bilki da Rasheedat a waje suna dariya wato su dai wad'annan suna son zaman 'kofar gida sai kace wasu maza ta na bud'e 'kofa ta ji Bilki ta ce "wow! Dan Allah Rasheedat ki kalle shi gwanin burgewa kyakkyawan saurayi d'an gayu ga kud'i gaskiya fa ya had'u sai dai bani da 'kwarin gwiwar zuwa inda ya ke tun da yana tare da wad'ancan mu'karraban na sa da kamar shi kad'ai ne yau sai na je gurin sa na gwada sa'a ta" dariya Rasheedat tai tana cewa "ke Bilki mai zai kai mutum can su karya masa 'kafa mu dai tsaya daga nan mu yi ta kallon abun mu, mu na jin dad'i" 'karasa bud'e 'kofa Zainab tai ta fito tare da kallon su ganin ba ma su lura da ita ba gashi sun tare hanyar fitar yasa tai gyaran murya domin su matsa mata daga hanya ta wuce amma a banza ba su ji ta ba mamaki ne ya kama ta harma ta kalli inda suke kallo dan ta ga abin da ya d'auke musu hankali Aliyu ta gano zaune akan kujera cikin katuwar rumfar kofar gidan su ya sha ado da kayan gado wato dai shi waccan a haka rayuwar sa zata 'kare kullum da 3Quater kamar dashi aka haife shi ga Sameer a gefen sa da kuma wani soja Mansur shi ma d'an anguwar ne guri d'aya su ke aiki da Aliyu sai dai shi Mansur bai dad'e da shiga aikin ba d'an tsaki ta ja za ta wuce ta gefen su Rasheedat tace. "Ahhh me ye abun tsakin dan kawai mun kalli abin da yai mana"? Hararar ta Bilki ta yi ta na cewa "'kwarai ko ke nasan kin 'kyasa shi dan kawai ace miki ta Allah wato malama shine ki ka 'ki nunawa zuciyar ki ta na dan'kare da soyayyar sa ai Aliyu 'karshe ne" wani kallo Zainab tai musu saidai damuwar da ke tare da ita ba za ta bari ta musu magana ba kawai ta wuce. "Au ai da kin yi magana mu na daidai da kowacce budurwa a gidan nan yau da sai mu ba ki kunya wajen nan za mu cire miki hijabin da Nikaf d'in a layi kowa yau ya zo ya ga abin da ki ke 6oyewa" tana jinsu ta share domin rashin tarbiyyar ba a su bane a uwayen sune da basu ba su ta gari ba tana cikin tafiya ta kusa kofar gidan kafin ta 'karasa kawai taga an sha gabanta tana dagowa taga Mansur d'an team d'in su Aliyu ne ran ta a bace ta ce "wai maye haka ina tafiya za ka tare ni a layi"?. "Ki yi ha'kuri amma yalla6ai ne ke son magana dake" had'e rai ta kuma yi "waye wani yallabai"? Nuna mata Aliyu ya yi ya na cewa "sir Aliyu Ahmad na ke nufi" wani irin fad'uwa taji gaban ta yayi akan wanne dalili Aliyu zai ce yana son magana da ita yana wancan gun bayan ga Sameer shima duk su na tare 'kara had'e rai tayi tana cewa. "Ka bani hanya na wuce". "Zan barki ki wuce ne kawai idan har kika saurare shi" cike da takaici tace "bazan saurare shi d'in ba ka bani guri na wuce bana son irin haka" "Na fad'a mi ki zan barki ki wuce ne kawai idan ki ka saurare shi". "Wai Mansur meye haka ne ka ban hanya na wuce bani da lokacin sa" hard'e hannu a 'kirji ya yi yana cewa "kai uban gidan nawa"? "Koma waye na ka kaga malam ka matsa min na wuce ko nayi maka kama da irin matan dake tsayuwa a layi suna magana ne"? Kai ya girgiza ya na cewa "a'a baki min kama dasu ba nafi kowa sanin ki Zainab kuma zan bada sheda a kanki ke kamila ce kuma me saukin kai". "Naji to ban hanya na wuce". "Karki sa nai laifi ki taimaka min ki je" "A'a ni baza ni gurin sa ba me zanyi mai"? "Dan Allah Zainab ki rufa min asiri ba ki san waye sir Aliyu ba tun da ba tare da shi ki ke ba rashin zuwan ki zai iya haifar min da hukuncin sati ina wahala kin ji"? D'agowa tai ta kallo inda Aliyu ke zaune ta cikin nikaf d'in ta taga ya d'auke kai daga saitin su kamar bai san da tsayuwar duk su biyun ba haushi ne ya 'kara kama ta za ta wuce da sauri Mansur yace. "Zainab dan Allah ki rufa min asiri ki je dan Allah ba dan ni ba wallahi idan ba ki je ba ina cikin matsala" tsayawa tai tare da juyowa tace "shikenan karka damu saboda kai ya ci albarkacin ka amma in dai dan shi ne ba zan ta'ba zuwa ba" zaro ido Mansur yai tare da saurin girgiza kai ya na cewa "ki daina cewa haka idan yaji sai hukunci na yafi na 'kin zuwan ki" sauke ajiyar zuciya tai ba tare da ta sake ce masa komai ba ta soma takawa a hankali ta kusa isa rumfar ta ja ta tsaya cak ta kasa d'aga 'kafar ta taci gaba sakamakon wani irin kallon da ta ga Aliyu ya na mata ji ta yi 'kafafun ta sun yi mata nauyi sam ba za ta iya 'kasarawa ba gashi yana cikin rumfar sai taje har can fasa kasawa tayi kawai ta juya ta nufi gate d'in gidan mi'kewa Aliyu yai ya na bin bayan ta ba tare data sani ba balle ta tsaya amma da ta je securities sun hana ta shiga saita cire nikaf gurin wa tazo 'yar waye ita wa take nema daga ina take?. Tambayoyi masu ban haushi suka ri'ka yi mata wacce bata basu amsar ko d'aya ba kawai gara ta koma gida ta kira Afifah ko su Elham su fito su zo su kar'ba mata amma indai saita basu wad'annan amsoshin ne data shiga gidan ta ha'kura har abada ji ta yi d'aya daga cikin su ya ce "kin ga madam idan baki da amsar tambayar mu zaki iya barin gurin nan ba kalar gurin tsayuwar kowa bane" taji muryar wani security wanda yake tsaye daga gefe fuskarsa a had'e ba alamar wargi sosai ran ta ya sake 6aci jin abin da yace da sauri ta juya za ta bar gurin kusan karo su kai da Aliyu wanda yake tsaye a bayan ta cikin tsananin firgici ta ja da baya da sauri a razane ta yada littafin hannunta sosai jikinta ya d'au rawa wanda kana gani kasan ba 'karamar tsorata tayi ba ita ba ganinsa ne ya tsorata ta ba karon da suka kusa yine innalillahi wa inna ilaihi raji'un da yanzu jikin mu ya had'u? Ta fad'a cikin ranta numfashinta har lokacin yana fita da sauri kamar wacce tayi gudu a 6angaren Aliyu ido ya zuba mata sosai yana kallon ta cikin wata iriyar tsaftacecciyar soyayyar ta da yaji tana sake tunkaho shi musamman a yanzu daya samu kusanci da ita ji yake inama ace matarsa ce inama ace ya riga ya aureta inama ace ita mallakinsa ce kullum addu'ar sa kenan baida burin daya wuce ya ga wannan rana numfashi ya sauke tare da kallon littafin da yake 'kasa kafin ya du'ka ya d'auko bai bata ba ya danna wani abu dake ri'ke a hannun shi kamar na'ura saiga gate d'in ya bud'e da kansa tare da fitar da wani sauti wasu fararen fitilu dake jikin gate d'in suka kawo haske 'kamewa masu tsaron kofar sukai tare da bashi girma juyawa yayi yana bata littafin har sannan jikinta bai daina rawa ba da'kyar ta iya saka hannu ta karba cikin sauri ta shige gidan saida ya bari ta wuce ya kallesu fuskarsa a murtuke yace "wannan yarinyar 'kanwa tace kada ku sake hana ta shiga daga yau gidan su ne" cikin girmamawa su ka ce "Yes Sir". Juyawa yai bai shiga gidan ba ya koma gurin Sameer wanda yake kallon su yana mamakin wanne kalar so Aliyu yake wa 'yar uwarsa bai ta'ba gani ba Aliyu yayi matukar damuwa da Zainab sonta a cikin jininsa da ruhinsa yake yawo. Da sallama ta shiga katafaren parlon wanda Afifah dama tana jiran tane ta d'au ado kamar saurayin ta ne zai zo ganin ta daidai ta sauko daga stairs hango Zainab da tayi yasa da gudu ta sauko tana rungume ta tace "oyoyo oyoyo Aunty Zee-Zee oyoyo gaskiya na yi murna sosai yau kin zo min ziyara sannu mu 'karasa parlon" kai Zainab ta d'aga ta na cewa. "To mu je amma ina Momyn ku ta ke"?. "Tana part d'in ta". "Gaishe da ita nake son yi kafin na tafi". "Ok muje part d'in na ta sai ki gaida ita" Afifah ta fad'a tare da ri'ke hannun Zainab wacce ta dakata ta na cewa "tsaya Afifah da kin kira ta parlon kamar hakan ya fi ko"?. "Me ya sa"?. "Saboda kin ga ba ki sani ba ko tana wani uzuri ne kar mu katse ta sannan kin ga ba sanarwa za mu shiga ai babu dad'i" girgiza kai Afifah tai ta na sake jan ta tace "kai a'a babu abin da take mu je" har Zainab za ta sake magana sai kuma ta yi shiru shiga su kai suka same ta a parlor tare da Daddy suna zaune abin da Zainab ta yi gudu kenan ga shi kuwa ya faru Husnah ta na gefe ta na rubutu 'kwace hannun ta Zainab ta yi da sauri za ta juya Afifah ta ri'ke ta ta na cewa. "Haba dan Allah Aunty Zee ki tsaya ku gaisa man bayan ga shi har da Daddy" tsayawa tai tana juyowa ta yi sallama amma ta'ki yarda ta fito normal su gan ta tana bayan Afifah kamar wacce tai laifi ko ta ke jin tsoro murya 'kasa-'kasa tace "Afifah ban san Daddyn ku yana nan ba ke kuma baki fad'a min ba me ya sa za ki min haka? Kin sa naji kunya wallahi" 'yar dariya Afifah tai zatai magana Momy tace. "A'a malama Zainab kin shigo kenan ai Afifah ta fad'a min zaki zo tun d'azu"? Dur'kusawa Zainab tai tana gaida su amma dai ta'ki fitowa daga bayan Afifan sai kare kan ta take kamar mara gaskiya murmushi Momy tai tana cewa "Ya kike ra'bewa ki shigo sosai mana karaso nan" Zainab na dur'kushe a gurin murya a nutse tace "Daddy ina kwana"? sai a lokacin Daddy ya d'ago shima yana kallon yadda take faman jan Afifah tana 6oyewa kai ya girgiza yana cewa "nidai bazan kar'ba daga nan ba" jin abinda yace yasa dole ta mi'ke tana d'an karasawa cikin parlon ta d'an zauna a kasan carpet ta gaida su da fara'ar su suka amsa mata lallai yarinyar nan akwai nutsuwa sanadin ra6arta da Afifah keyi a islamiyya yasa itama ta kasance mai hankali suna godiya da samunta matsayin 'kawar 'yar su. "Zee-zee taso mu je part d'in mu" Afifah ta fad'a tana kallon yadda ta sunkuyar da kai 'kasa ta'ki d'agowa saida tai magana sannan ta mi'ke suka fita da kallo Momy ta bisu tana d'an yin murmushi bayan sun fita Daddy ya kalli Momy da Asma'u ta mi'ko mata rubutun datai tana duba mata yace "ni dai ina yiwa Aliyu kwad'ayin yarinyar nan sai dai kin san jiki da jini ba lallai shi kuma tai masa ba" numfasawa Momy itama ta yi ta na cewa "haka ne amma ai ba shi zamu biya ba mezai hana kawai muyi magana a junan mu damu da iyayen ta a aura masa ita ba dole sai yana sonta ba kyawawan halayenta sune zasu sanya ya damu da ita idan ma dai yana da wacce yake so daga baya saiya aureta" jinjina kai Daddy ya yi ya na cewa "haka ne kema kin kawo magana amma bana son abinda zai zama damuwa a tare dasu damu gara a fara tuntubar sa idan yana ra'ayi shikenan idan yace a'a sai a 'kyale shi ni Ina ganin kamar hakan zaifi sau'ki akan mu je gurin iyayen ta kai tsaye". "Ai ko nasan Aliyu da son mace mai tarbiyya bazaice a'a ba domin yasha fad'a min kud'i ba su bane samun mace ta gari shi yake so saboda tarbiyyar 'ya'yan sa kuma ma bayan haka yace min yana da wacce ya ke so". "Wacce ya ke so kuma a ina take"? "Ni kaina ban sani ba domin bai fad'a min ba sai dai na sake tambayar sa". "To ki tambaye shi ina fata ta kasance wannan yarinyar ce ina so ta zama d'aya daga cikin ahli na" hannu Momy ta d'aga tana cewa "Amin Alhaji Allah ya amshi ro'kon ka" murmushi Daddy yayi yana kallon ta ya ce "ya amsa ma in sha Allahu yanzu idan ya shigo kiyi min magana da shi kice ina neman sa idan kina ganin kamar a naki 6angaren da matsala". "Ba wata matsala amma dai gara ka tambaye shi da kanka". "Ok shikenan idan ya shigo ki fad'a masa ya same ni a part d'ina yanzu zan fita ko zuwa dare ne idan na dawo za mu yi magana da shi" ya fad'a yana mi'kewa itama Momy mi'kewar tayi suka fita tare tayi masa rakiya suka bar iya Asma'u a parlon tana ci gaba tracing d'in rubutun da take yi. Su Zainab kam suna fita parlor ta mayar da nikaf d'inta kan fuskarta kamar yadda yake dariya Afifah tai tana kallonta tace "kai dan Allah a gida ma bazaki cire ba nan fa ba layi bane ko dama haka kike zama ko a gidan ku"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa. "A'a". "Oh meyasa anan ba za ki cire ba kodan saboda akwai samari a gidan"? "Eh" shine amsar da ta bata "to ai kuma iya Yaya discipline ne a gidan shi kuma ya riga ya sanki Afif ne ma dai zan ce da sau'ki kuma shi da baya nan garama ki cire abin ki kisha iska". "A'a basai na cire ba". "Kai wai da gaske ki ke, me ya sa bakya son a kalli fuskar ki ne Zainab"? "Saboda na tsare kai na daga shiga fitina ina yiwa wanda zai aure ni tattalin kai na da taya shi kishi kar kowanne d'a namiji ya ga fuskata sai shi" dariya sosai Afifah keyi tana tafi tare da jinjina kai tace. "Gaskiya ne Zainab ni kai na da nake mace kuma 'kawar ki zan iya 'kirga sau nawa naga fuskar ki ba dan kina yin alwala ba kuma saboda mutane kar su gani bakya yin alwala sai kowa ya gama shima ba dan nasan muryar ki ba fuskar dai zai min wahalar ganewa ko dan ina ganin ta a islamiyya lokaci zuwa lokaci ko Yaa Sayyidi shima alwala za ki yi kika cire nikaf ya ga fuskar ki shikenan ya rud'e ya kamu da son ki haka ne"? "Hummm" kawai shi ne abin da Zainab ta ce wanda yasa Afifah dariya tana cewa "humm me"? "Ba komai" ta fad'a daidai Fati da Elham sun fito ganin har tazo yasa suka karaso suna cewa "Aunty Zainab ina kwana"? A sake tace "lafiya kalau ya ku ke"? "Muna lafiya" Fati ta d'ora da cewa "dan Allah Aunty Zainab na d'auko littafi na, na d'an biya ki ji ko ina da gyara"? Tun kafin Zainab ta yi magana Afifah ta harari Fati ta na cewa. "Ke ba d'ori ta zo yi muku ba kar ku takura ta ki bari sai kin je islamiyyar man" murmushi Zainab tai tana cewa "a'a bari na d'ora mata d'auko Fati" jin zata biya mata yasa Elham ma tashi kowa ta d'auko na ta al-qur'anin su ka dawo d'age nikaf d'in Zainab tayi sannan ta fara gyara musu Afifah dake gefe tana murmushi so take ta yi dariya tasan tana yi indai Zainab ta fahimta yanzun nan zata mayar da nikaf d'in ta yadda yake Aliyu kam daga kofar gidan su tashi yayi domin ya shigo gida zai d'auki abu kawai tun yana wajen kofar parlon su kafin ya bud'e yake jiwo tashin karatun ta tsam ya tsaya a guri d'aya yayi shiru yana saurarar ta daga baya kuma ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "alhamdulillah" sannan ya bud'e kofar ya shigo idon sa ne ya sauka akan kyakkyawar fuskar ta da ke bayyane rabon da yaga fuskar ta a fili kamar haka har ya manta wani abu yaji ya sake dira a cikin zuciyar shi ji yake ina ma yadda take zaunen nan ace ba zuwa ta yi zata tafi ba kyan abun ace ta riga ta zama matar sa a gidan sa take ya aure ta kawai abin da ya kawo a ransa ke nan Zainab bata lura da wucewar sa ba saida ya d'auko abinda zai d'auka ya dawo zai fita jin 'karar bud'e 'kofa yasa ta d'ago karaf su ka had'a ido da sauri ta d'auke kai gaban ta na fad'uwa ta mayar da kallon ta kan al-qur'anin da'kyar tace. "Ina kwana"? K'ofar fita ya nufa can 'kasa ta ji muryar sa yace "lafiya" numfashin da ya tsaya mata a 'kirji ta samu ta fito da shi tana d'an daidaita nutsuwar ta ta ci gaba da yi musu gyaran saida suka gama Afifah ta tashi tana cewa "Zainab ta so mu koma bedroom d'in mu tun da gashi tun ba'a je ko'ina ba abun da kike gudu ya faru taso mu je" kai ta girgiza tana mi'kewa ta ce "a'a tafiya zan yi na baro d'inkunan mutane da dama kuma an kusa bikin". "Kai dan Allah Aunty Zee please mu karasa ki wuni man" zaro ido Zainab tayi tana kallon ta tace "wuni fa ki kace? A'a tafiya zan yi" ta fad'a tana yun'kurin nufar kofar fita da sauri Afifah ta ri'ko hijab d'in ta tana girgiza mata kai tace "wai dan Allah Zainab me ya sa bakya son zuwa gidan mu kuma yau ina ta murna kin zo sai ki ce tafiya za ki yi................ Muryar Momy ce ta katse maganar da Afifah ke yi "Ina zata je amma ba har gida za ta tafi ba"? Kai Afifah ta d'aga tana cewa "eh wai sai ta tafi nace ta tsaya ta wuni ta'ki" "A'a haba Zainab daga zuwan ki ki bari man ko zuwa jimawa sai ki tafi" "Nima fa abun da nace kenan ta tsaya ta wuni". "Ko bata wuni ba amma tunda yanzu 'karfe sha biyu tayi ta bari idan tayi sallah taci abinci sai ta tafi bari na zo" ta fad'a tana nufar wata 'kofa kallon yadda Zainab ta yi shiru Afifah tai tana cewa "kin ji ko Zainab dan Allah ki dawo ki zauna kin ga Momy ma ta saka baki baza ta ji dad'i ba idan ki ka tafi" dole babu yadda Zainab ta iya duk da ta na son tafiyar amma tun da har da Momy ita ma ta saka baki ya za ta yi bedroom suka wuce acan ma da'kyar ta cire hijab d'in jikin ta gabadaya tafi so ta koma gida ko dan kar a kai gulmar ta gurin Hajiya jan ta Afifah ta yi tayi da hira har ta d'an ware sukai zance da aka 'kare lunch ta je ta d'ebo musu yin duniya Zainab taci abincin nan ta'ki saida Afifah ta rantse cewa indai bata ci ba sai ta zuba mata a cooler ta tafi da shi jin haka yasa taci abincin su na gamawa ta yi alwala tayi sallah shaf-shaf ta d'aura nikaf ta tashi daga kan sallayar Afifah data fito daga toilet ita ma tayo alwalar ganin yadda har ta gama shiri yasa ta saki murmushi ta na girgiza kai batare da ta ce komai ba ta d'auki hijab d'in ta ta saka. "Afifah zan tafi" taji muryar Zainab juyowa inda take ta yi tana cewa "ok bari na yi sallah sai na raka ki" tana fad'in haka ta juya ta fara sallah tsaye Zainab tai har Afifan ta idar tayi addu'a sannan ta tashi ta d'auke sallayar tana cewa "mu je to" sauke numfashi Zainab ta yi tana bud'e kofar suka fito daga part d'in su Afifah duk sauran suna dining Momy Aliyu Elham Fati da Asma'u suna cin abinci sallama ta yiwa Momy da sauri ta fita saboda ta ga yadda Aliyu ya ke bin ta da wani kallo wanda yake firgita mata lissafi a ranta tana tunanin watakil baza ta sake shigowa gidan ba sai dai idan Aliyu ne ba ya nan tsayar da Afifah Momy ta yi tana cewa. "A cikin dogayen rigunan nan guda biyu da Daddy ya siya miki kwanan baya naga baki saka su ba ki d'auko mata d'aya ai za ta yi mata daidai" kai Afifah ta d'aga tana cewa "to" tare da juyawa ta koma bedroom d'in su ta d'auko harda turare ma ta had'o mata guda d'aya ta sa'ko su a wata 'yar jaka da nufin daga baya ta kawo mata jakar fitowa tayi tacewa Momy "bari na je ta raka ta" ta fad'a tana bud'e 'kofar parlon ta fito harabar gida amma abun mamaki duk zaton ta Zainab tana harabar gidan tana jiran ta sai ta ga bata nan wucewa ta yi ta fita ko alamar ta babu humm Zainab kenan har ta gudu gida bari na bita wucewa tayi ta bi bayan ta a lokacin da ta shiga da Rasheedat suka fara karo ta na tsaye tare da Zakiyyah da sauri cikin shishshigi tace "Lah Afifah ina yini"? "Lafiya kalau ya kike"? Ta fad'a tana d'an tsayawa kad'an cikin cushi Rasheedat tace "ina lafiya kwana biyu ban gan ki ba fatan ki na lafiya"?. "Eh lafiya alhamdulillah" tana fad'in haka ta wuce da kallo Rasheedat ta bita tana cewa "wallahi a rayuwa ina so mu yi mutunci da wannan Afifan ko dan na ri'ka shiga gidan su amma sam daga gaisuwa bata tsayawa ayi wani zance da ita" dariya Zakiyyah tayi tana kallon Rasheedat tace "eh idan kin duba ita da masu aji take harkar ta". "Su wa ye masu ajin"?. "Zainab man a gidan nan da wa take 'kawance bayan ita gurin wa kika ta'ba gani ta tako ta zo idan ba ita ba"? Ta'be baki Rasheedat ta yi tana cewa "ai itan ma a shishshigin ne ya sa tayi suna a gurin ta idan ba haka ba tana matsayin 'yar mai kud'i zata zo har gida neman ta ne"?. "To indai da shishshigi Zainab ta samu suke 'kawancen ke wa ya hana ki yi mata ke ma kuyi"? Zakiyyah ta fad'a tana kallon Rasheedat wacce ta ce "ai ina mata kawai har yanzu ban samu 'kofa bane". "Hummm" kawai shine abinda Zakiyyah tace domin ita kam har ga Allah bata ga abun shishshigi a wanda ba ta kai yake ba duniya da fad'i idan wani ya'ki kuyi 'kawancen wani kana zaune zai zo ya kawo maka katin gayyatar ka yi abotar to meye a ciki. Afifah kam tana shiga da sallama d'akin Zainab ta shiga ta same ta har ta hau kan keke tana d'inki murmushi ta yi tana cewa "kaga Hajiya chef Tailor mad'inkiya tsakani da Allah Zee-Zee baki kyauta min ba daga bari na zo na raka ki shikenan nan ki ka gudo"? "Eh akwai dalilin da yasa na yi hakan"?. "Wanne dalili"?. "A'a basai na fad'a miki ba". "Ok shi ke nan Momy tace a fad'a miki ta gode sannan ga wannan" ta fad'a tana fito da doguwar rigar da turare ta aje mata zaro ido Zainab ta yi tana girgiza kai tace "a'a Afifah na gode dan Allah ki mayar mata" da mamaki Afifah tace "kamar ya na mayar mata"?. "Saboda ni ban je dan na saka ta wahala ba" "Kuma amfad'a miki dama ita ce ta ba ki rigar tawa ce fa Daddy ne ya siya mana kowa bibbiyu kwanan baya shine na d'auko miki". "Duk da haka ki koma da ita na gode" mi'kewa Afifah ta yi tana kallon ta tace "wallahi tunda na kawo miki ita bazan koma da ita ba saidai ki mayarwa Momyn da kan ki ni na tafi sai zuwa jimawa idan mun je islamiyya" tana fad'in haka ta fita ta saka takalmin ta ta koma gida. Aliyu kam sakamakon Momy ta ce masa Daddy yana neman sa shiyasa ya fasa zuwa in da zai je ya jira shi tukuna ya dawo idan su kai maganar ya tafi kar yazo yana neman sa Daddy kuwa bai dawo ba tun sha biyu da ya bar gida sai dare bayan sallar isha ya shigo shiyasa Aliyu ya bari da yayi wanka ya huta ya je a lokacin shi kad'ai ne yana garden a zaune sakamakon ko'ina da haske tarrr kamar da rana yana karkashin wata bishiya akan kujera da securities mutum biyu a tsaye suna gadin sa da sallama Aliyu ya je gurin amsa masa Daddy yayi yana nuna masa d'ayar kujerar dake gurin zama yayi shi kuma Daddy yayi wa securities d'in nuni su d'an basu guri za suyi magana matsawa su kai d'an nesa da su kafin su yi abin da za su yi kallon Aliyu Daddy yayi yana cewa "Aliyu dama tambayar ka nake so na yi magana ce akan aure shin ka shirya yi yanzu kana da wacce kake so"? Aliyu bai ta'ba kawowa a ransa wannan tambayar da Daddyn zai yi masa ba shiyasa ya d'ago yana kallon sa kai Daddy ya d'aga ya na cewa "eh kalle ni da kyau na ce akwai wacce kake so ko a'a idan baka da wacce kake so ni na samo maka" jin abinda Daddy ya ce daga 'karshe ya sa cikin fargaba Aliyu yace "a ina take Daddy"?. "Ba ruwan ka da inda ta ke da farko ka fad'a min wacce kake so ko babu"? shiru Aliyu ya yi zuciyar sa na harbawa addu'a kad'ai yake Allah yasa ba Amirah Daddy ya hango masa ba Allah yasa ba ita zai ce ba....................... "Aliyu". "Na'am Daddy". "Nace ka fad'a min in da yarinya take 'yar waye a wacce anguwa ta ke"? Numfashi da huci ya fitar lokaci guda yana d'an rufe ido ya bud'e tare da girgiza kai duk Daddy na hankalce da shi yace "uhum ina jin ka"? "Daddy a nan anguwar ta ke". "A nan anguwar ta wajen ina"?. "Gidan su Sameer 'kanwar sa ce". "K'annin nasa mata guda nawa ne"? "Su biyu ne Bilkisu da Zainab". "Ok na gane wacce daga ciki ka ke so"? "Zainab ce" baki Daddy ya bud'e yana kallon sa da mamaki ya ce "bayan neman ka da Momyn ku ta ce ina yi ta fad'a maka wani abu ne"? "A'a babu abin da ta fad'a min kawai cewa ta yi ka na nema na". "Ok shikenan dama dalilin kiran kenan tun da na ji a inda take ya wadatar tashi ka je" har ya mi'ke zai tafi ya sake tsayawa yace "amma Daddy ban fad'a mata ba". "Me ya sa zaman jiran me ka ke "?. "Lokaci na ke jira". "Oh! nan d'in baka fad'a mata ba idan kuma da wanda zata aura fa"? "Babu Daddy ai tasan da zama na saidai ba ta san ni bane kar ku shiga maganar har sai naje na same ta da kaina" murmushi Daddy yayi yana cewa "Ok yayi ba damuwa je ka" wucewa Aliyu yayi ya fita daga garden d'in sosai Daddy yayi mamakin jin abinda ya ke so ya tarar da shi a inda ya dace shi ke nan ba wata shan wahala ko aikin da na sani bai dad'e ba a garden d'in bayan sun gama maganar da Aliyu shi ma ya tashi ya shigo part d'in sa daidai Momy ta shigo ko bari ta zauna bai yi ba ya ce. "Ashe kin ji wai dama ita ce yake so da na tambaye shi ni da na ji ya kira sunan ta ma farko zargi na yi ko kece kika fad'a masa"? Dariya Momy tai tana 'karasowa ta zauna ta ce "wallahi a'a ban fad'a masa komai ba kawai da nace yaje kana neman sa shikenan humn gaskiya abun nan yayi mun dad'i sosai ba gamu ko Aliyu ba hatta a gurin su Elham nasan zata samu kar6uwa sosai suna yawan yabon halayen ta yanzu idan suka ji ita Aliyu zai aura farin cikin da zasu yi ba zai fad'u ba. "Haka ne amma saboda saka ido irin na mutane kawai zan kira mahaifin ta nan gidan mu yi magana ni da shi yafi sau'ki cikin sirri akan a taka zuwa gidan su" kai Momy ta d'aga ta na cewa "eh gaskiya hakan zaka yi nima bana so maganar ta fita da wuri saboda 'yan ba'kin ciki da ma'kiya ko mahassada ka san babu abin da ka yiwa mutum amma sai ka ga baya 'kaunar ya gan ka cikin walwala". "Gaskiya ne kin san abin da Aliyu ya ce? Wai shi bai fad'a mata ba lokaci ya ke jira". "Ka ji shi da wani shirme lokaci ya ke jira sannan ya fad'a mata idan wani ya riga shi fa, lalacewar agogo ba ya hana lokaci tafiya" Momy ta fad'a tana kallon Daddy wanda ya jinjina kai ya na cewa "ni ma dai abin da na gani kenan amma shi wai jiran lokaci ya ke ko wanne irin lokacin ya ke nufi"?. "Lokacin sa na shirme man ya ke nufi kaga idan da wanda zata aura shikenan ya tashi a tutar babu yanzu kawai abin da za'ai ka rabu da shi ka yi magana da iyayen ta kawai hakan ya fi". "Ni ma nafi yarda da hakan a raina domin a bari ya wuce ya na kawo rabon wani tsaya kawai na saka a kira min shi yanzun nan mu yi magana tun da ba dare ne ya yi ba" Daddy ya fad'a ya na mi'kewa ya fita daga parlon na sa wani security ya samu ya aika shi cikin sirri ya ce yaje yayi masa magana da baban Sameer yace yazo yana neman sa da yaje 'kofar gidan a lokacin da 'yan 'kananan yaran gidan a waje d'aya ya aika yace "ka je kace ana sallama da mahaifin su Sameer" "to" yace ya na tashi ya shiga gidan a lokacin Abba yana zaune yayi shimfid'a a kofar d'akin sa sakamakon yanayi na zafi Umma ta kawo masa abinci zai ci yaron ya shiga yace "Baba wani mutum yana neman ka a 'kofar gida" da mamaki Abba yace "wani mutum kuma baka san shi ba"? "Eh yace na kira ka". "To kace gani nan ina zuwa" to khaleel ya ce yana juyawa ya fita shiru Abba yayi yasan shi dai bai da ba'ko sannan ba zuwa gurin sa ake ba wa yake dashi aikin me yake da zai samu jama'a har su ri'ka biyo shi gida shi da ba ma'aikacin gwamnati b................... Ya na cikin tunani ya ji muryar Asabe ta ce "ka tashi ka je man kana ji ana neman ka in kaji kira an samu amma ban da kiran d'an sanda irin su Aminu" Asabe tai maganar tana kallon yadda yayi shiru har lokacin bai motsa ba taci gaba "kar kasa idan alkhairi aka kawo maka ma mutumin yayi zuciya ya tafi watakil sadakar kud'i ko kayan abinci ne ko kuma ma suturar sawa dan Allah ka tashi ka je watakil gobe da kaji za mu karya da safe idan kud'i aka kawo maka" kallon ta Abba yayi bayan ya mi'ke a damuwance yace. "Ke abin da ya ke ran ki kenan"? Kai Asabe ta d'aga ta na cewa "tabbas abin da ya ke rai na kenan kuma na fad'a wa ya'ki dad'i sai dai idan bai samu ba" bai tanka mata ba sai takalman sa da ya saka ya fita a can gefen gidan nasu ya hango mutumin a tsaye har tsoro abun ya bashi shi fa bai ta'ba ganin sa ba Allah ya sa ba makirci aka had'a masa ba balle ya gan shi da shiga irin ta masu aikin d'amara 'kasawa yayi ya na addu'a a ran sa yayi sallama amsa masa security d'in ya yi yana cewa "kai ne Abdullahi mahaifin Sameer"? Kai Abba ya d'aga gaban sa na fad'uwa musamman da ya ga mutumin da uniform gashi ya ambaci sunan Sameer Allah ya sa ba wani laifin Sameer d'in yayi aka kama shi ba ji yayi yace. "Ok dama Alhaji Ahmad ne ya aiko na kira masa kai" da alamar tambaya Abba yace "wanne Alhaji Ahmad d'in"? "Wannan nake fad'a na nan anguwar yana cikin gida shine ya aiko a kira ka magana za ku yi" da sabon mamaki Abba yace "ni kuma suna na ka ji ya ambata Abdullahi ko Habibu headmaster ko kuma Aminu d'an sanda wanne ya ce"?. "A'a Abdullahi mahaifin Sameer ya ce idan kai ne mu je"? Jiki a sanyaye Abba yace "shi ke nan nine mu je d'in Allah ya sa lafiya" ya fad'a suna wucewa sosai jikin sa ya d'au rawa ganin gidan suka shiga inda bai ta'ba zuwa ba shi da ba kowa ba abun tambayar ya akai Alhaji Ahmad ya san sunan sa kuma yasan shi ne mahaifin Sameer? Har cikin parlon Daddy ya kai shi sannan ya fita Abba jikin sa na rawa yake shirin zama a 'kasan carpet Daddy yace "a'a a'a haba bismilllah ga kujera ka zauna" ya fad'a yana nuna masa kujerar dake kusa da shi da'kyar ya zauna yana kallon table d'in dake gurin an cika su da kayan cinye-cinye gwanin sha'awa ga kaji nan yana gani kamar a banza numfashi ya sauke yana d'an girgiza kai. Fuskantar sa Daddy yayi yana mi'ka masa hannu yace "barka da dare malam Abdullahi" hannun Abba na ma'kyar'kyata ya mi'ka masa suka gaisa numfashi Daddy ya sauke yana cewa "nasan ka ji mamakin me yasa nake neman ka duk da ni ya kamata na taka naje inda ka ke to amma gudun maganganun mutane yasa na ce ka zo nan mu tattauna ya fi sirri sosai akan a gan ni acan kofar gidan dole kowa zai so sanin abinda ya kai ni ko"? Kai Abba ya d'aga ya na cewa. "Eh gaskiya ne haka ne". "Yauwa masha Allah dama dan Allah Malam Abdullahi alfarma na ke nema a wajen ka" baki Abba ya bud'e ya na cewa "alfarma a waje na ranka ya dad'e ni fa"? ya fad'a yana nuna kan sa da mamaki jinjina kai Daddy ya yi yana cewa "kwarai a wajen ka alfarma me daraja ma nake nema Kuma abu ne me muhimmanci Aliyu ne yake son yarinya d'aya daga cikin yaran ka" a susuce Abba yace "a cikin yara na wacece"?. "Am Zainab sunan ta'" cak numfashin Abba ya tsaya tsoro ya gama cika shi taya za'ai shi da ya ke talaka Aliyu zai ce ya na son Zainab wannan al'amarin abun jawo maganganun mutane ne idan su ka ji ba zai ta'ba hutawa ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya fad'a a fili ya na dafe kan sa da hannu biyu gumin firgici ya fara fito masa ya ji Daddy ya ce. "Malam Abdullahi na san za ka d'an ji mamaki amma ba abun mamaki bane wannan lamarin Ubangiji ne sannan 'yar ka ta cancanti a so ta fiye da tunanin me tunani domin dukiya da mulki ba su ne kwanciyar hankali ba mace ta gari wacce ta fito daga babban gida mai cike da tarbiyya irin na ku tabbas bazan 6oye maka ba, ba Aliyu ba ni ma ina son wannan yarinyar ta shigo cikin ahli na dan Allah da fatan zaka amince domin na ga kamar ba kayi na'am da maganar ba"? Shiru Abba yayi jikin sa yayi mugun sanyi Daddy yaci "ko dai akwai wanda za ka ba ta ne kayi mata miji"? A hankali ya girgiza kai ya na cewa "a'a ban yi mata ba amma gaskiya wannan abun da ka zo min dashi akwai tashin hankali da damuwa sosai a cikin sa". "Saboda me"?. "Yanzu da zarar wannan maganar ta fito kowa cewa zai yi ba haka kawai Aliyu ya gan ta yace yana son ta ba"?. "Kamar ya kenan ban gane ba"? "Za'a ga yadda na ke talaka ba komai ne dani ba kamar ku ace d'an da ya fito daga gidan nan ne yake son 'ya ta"? Kai Daddy ya girgiza ya na kallon Abba wanda ya cire hular kan sa tsabar zafin da ya d'auka ya ce "Malam Abdullahi mu fa daraja da kimar ka da ta 'yar ka mu ke dubawa ba talauci ba arziki da talauci duka na Allah ne kuma shine yake jarabtar bayin sa da su dan ya gwada imanin su akam me Ubangiji ya yi maka ni'ima ka ke son bijire masa ni dai na fad'a zan sake fad'a ina son wannan yarinyar ta shigo cikin ahli na saboda hankalin ta da nutsuwarta da kuma tarbiyyar ta dan Allah Malam Abdullahi kar ka ce a'a"? Nannauyan numfashi Abba ya sauke yana kad'a kai cikin rashin sanin abun yi yace "to shikenan Allah ya za6a mana abinda ya fi alkhairi idan matar sa ce Allah ya bashi ita babu komai amma yanzu zan je gida zamu tattauna da mahaifiyar ta". "Ok ba damuwa ina godiya sosai idan na ga kwana biyu baku gama yanke shawara ba saidai ka gan ni a 'kofar gidan da kai na naje ro'kon ka" Daddy ya karasa maganar yana murmushi shi ma Abban murmushin dole yayi cikin ya'ke ya ce "insha Allahu da zarar mun gama magana da ita zan sanar da kai". "Ok ba damuwa Malam Abdullahi bismilllah fa abinci ka shigo hankali na ya d'auke mu ta magana" girgiza kai Abba ya yi da fara'ar sa ya ce "a'a Alhaji alhamdulillah alhamdulillah na gode sosai zan tafi duk yadda mu kai da mahaifiyar ta in sha Allahu za ka ji" ya fad'a ya na mi'kewa shi ma Daddyn mi'kewa yayi ya sake bashi hannu suka gaisa sannan suka fita tare ya d'an taka masa zuwa bakin gate aka bud'ewa Abba ya fita shi kuma Daddy ya koma ciki.............. 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 Mai son complete document d'insa yai min magana ta WhatsApp number zai same shi akan Naira d'ari bakwai complete har 'karshe. WhatsApp no. +234 8160983083 #700 Acc. 2410673902 Nm. Yusrah Musa Bnk. Zenith Bank Me kamar sarki 300 Minister Ashraf 300 Safreeyyah 400 Royalty 500 YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨ DUTSE JIGAWA STATE 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞