An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT COPY N COMPILED BY ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS WASAPP 08066360176 FOR MORE AISHATUL MUBEENA 1-20 [12:12AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ [1]-[5] Na Miss hafcy ©ONLINE HAUSA WRITTERS A fusace ya shigo gidan yana mita "Haba!! Mutum dame zeji? Da zafin talaucin dake damuna ko kuwa da Rashin haihuwa,,Nagaji da wannan rayuwar! "" Da sauri ta fito daga daki" Haba malam ai talauci ba hauka bane kuma haihuwa aiy ta Allah ce,,ka shigo gida bako salama kana fadan wannan maganganun ai komai yayi zafi maganinsa Allah"" Ya dago a fusace ya kalleta "ma'u kinga kimin shiru ki barni naji da abinda nake ji ace yau duk wahalar dana sha a kasuwa amma ba wani cinkin kirki dame zanji haba! Haba!!"" Ma'u tace "Amma ai be kamata wannn maganar ta dinga fitowa daga bakin kaba,,Kasani fa Allah yana cewa,, Acikin suratul baqarah Aya ta 153 "" innalla ha ma^as - sa biri n .""Ma'ana: Allah yana tareda masu haquri"",, Ya juyo ya kalleta toh sarkin wa'azi,, naji shikenan yanzu da abinda zan samu naci?? Tayi murmushi,,Dazu na sami 200 wankin danayiwa talatu shine na yi mana danwake har tumatir ma na bada aka siyo min"" Ya washe baki yauwa mata ta gari nagode an gaishe ki,,Suka shiga cikin dakin Bayan ta zuba mai danwaken a plate ya fara ci se santi yake yi can ya kalleta yace "Duk sanda nake cikin matsala in na tuna muna tare zan dawo na ganki se naji wani dadi a raina,,saboda nasan dole zaki faranta min rai" Tayi murmushi sannan tace "malam kenan nima ai duk hakan take" Yace "madalah ni yanzu matsala dayace take damuna wanan rashin haihuwar dan na tabbata daga gareni take mata nawa na aura bayanki amma har yanzu ba wada ta taba ko bari"" Ta nisa "Malam ba lallai bane hakan ne kawai dai mucigaba da addua,,,Se kaga cikin yardar Allah mun samu" Yayi murmushi yace toh mata ta gari na gode Allah ya amsa adduar mu tace "Amin malam" Bako sallama ta banko dakin,,ma'u da sauri ta tashi tana "Ahh iya ce? Sannu da zuwa,, iya ta balla mata harara "Dallah yimin shiru se shegen kinibibin tsiya ba wajen ki nazo ba wajen dana nazo" Ma'u ta sunkuyar da kai bata qara magana ba....Iya ta kalli Mal,, "Kai kuma mara zuciya kawai kaqi rabuwa da wannan matar me baqar kafa ta tsiya na gaji ace har yau banda jika,,nasa ka auri mata bata ko shekara ka saketa,, se wannan mayar matar taka,Naga alama so kake na mutu van sami jika ba "" Ta fashe da kuka,,Mal ya kalleta "Haba inna,,Ya kikeso nayi? Da sauri ta katse shi KA SAKI MATAR KA MAU SAKI 3! A firgice ya juyo ya kalleta "Haba iya,,ki tuna fa a duk matan da nake aura ita ce kadai me rupa min asiri take zaune dani a wannan quncin,Ga rashin haihuwa amma kuma kice na saketa haba iya!,, Iya ta juyo da mamaki "Auho lallai sule ka girma ka isa har ina ma magana kana maida min,,ta fashe da kuka ace dan dana haifa shi muke musayar yawu dashi na shiga uku ni tani!""Ya nisa sannan yace "iya ba haka bane ba wlhy abinda kika bukata ne bazab iya ba,"" Iya ta fusata "to kaje wlhy matar nan ta qara wata3 bata sami ciki ba se an raba auren nan,,,Tunda ban isa nasaka abu ka yi ba,,"" Ta fice cike da fushi Ma'u datake ta kuka ta juyo ta kalleshi "Bansan me nayiwa iya ta tsane ni haka ba,,Har yau ta kasa gane cewa haihuwa ta Allah ce"" Mal ya juyo ya kalleta "Kiyi haquri ma'u na Insha Allah matsalarmu ta kusa zuwa qarshe! Ma'u ta share hawayenta "Allah yasa ameen" Ta dauke kwanukan dake dakin ta fita dan wankesu shikuwa kishingida yayi akan yar katifar dakin ina jinjina maganar iya Share Recent Posts [12:13AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©ONLINE HAUSA WRITERS NA MSS HAFCY [6]-[10] ***ASALINSU**** Malam Sulaiman Abubakar me rariya Dan kasuwa ne sana'arsa bata huce Ta saida rariya ba, yana yin rariya ya kuma siyar a kasuwa sana'ar kuwa a wajen babansa ya gada,Alhaji abubakar me rariya marigayi,,,, Alhaji Abubakar me rariya yanada mata biyu da yaya guda 4 guda daya ta rasu,, Balki itace matarsa ta farko wadda ta haifa masa yaya biyu,,,Bashir da hauwa,Wanda dukansu sunyi aure cikin rupin asiri, Se kuma matarsa ta biyu Amina (Tani) Masifafiyar mata ce ta gaske ga rashin haquri Ta haifa masa yaya biyu Mal sule shine na farko se kuma habiba wadda ta rasu tun tana qarama,,,,,,,,, Mal Sule matarsa daya wanda suke zaune a halin yanzu, asmau ma'u wacce sukayi auren soyayya amma shiru kusan shekara 10 kenan suna tare Amma ko batan wata bata taba yi ba,,,Hakan yasa tani wadda suke cewa Iya ta takura masa akan se ya qara aure,, mata aqala sunkai 5 ta kawo masa in ya auri wanan ta fita se ta kuma samo wata yan mata da zawarori amma kuma sam basa zama Kuma a cikinsu ba wadda ta taba ko batan wata balle bari,,In suka gaji se su tafii,Ga talauci ga rashin haihuwa da kansu su suke neman saki, Wasu kuma in ya gaji da halayarsu se ya sake su Iya tayi masifar ta gaji,,,Tayi neman malaman akan nemawa tilon danta sule haihuwa amma har yanzu shiru Ma'u matace me haqurin gaske da tawakali tanada ilimin addini sosaii hakan yasa rashin haihuwar sam be dame ta ba Duk da talauci irin na mal sule amma Haka take haquri ta zauna dashi wataran ma da en dabarunta take ciyar dasu,Dan itama gidansu ba wasu masu arziki bane,Ga miji shima ba wani me arziki ba dan da sana'ar rariya kawai ya dogara ko noma ba yayi saida gonar gadonsa yayi,,Suna zaune yau da ci gobe babu. ********CIGABAN LABARI******** Ma'u da gudu ta fito daga daki tana kwarara amai a rariyar tsakar gida,,daidai shigowar iya kenan,,iya da sauri ta isa wajen ta "yar nan meya faru haka me kika ci" Ma'u Tana huci tace " Wlhy tun da safe nake jina wani iri ga zazzabi dazu kuma zuciyata ta fara tashi shine fa na fara jin amai har nazo nayi" Iya ta dago kanta" Yaushe rabon da kiga aladar ki? Ma'u tace "Watan daya huce dai bangani ba"" Iya ta duba idonta sosai aikuwa se ta saketa ta rangada guda ""Ayiriyiri" Yarinya ki godewa Allah ai alama ta tabbatar da cewa ciki gareki kai yau ni nafi kowa murna ayiriririiriiiii"" Ma'u ta zaro ido maganar iya se tazo mata kamar a mafarki ta dago cikin dashashiyar murya tace "Iya ciki fa kika ce?" Iya ta washe baki "Tabbas yar nan kiyi murna fa" Daidai lokacin mal sule ya shigo gidn dauke da rariya a hannunsa ya tsaya turus ganin iya tasa ma'u a gaba tana rangada guda ya matso yace "Iya me ya faru ne" Iya ta kuma washe baki "Yaro albishirin ka?"Da sauri yace goro iya" Iya tace "to matarka ciki gareta alama ta nuna!" Mal sule ya yarda rariyar dake hannusa se ganni Inna tai ya daga hannu sama yana godiya se kuma hawaye,,Ma'u da take tsugune kuka ta fara a hankali kukan murna! Yau dai Allah ya amshi addu'arsu! Mal sule a fili yace "Allah nagode maka,ya allah daka amshi addu'a ta, Ya Allah kasa dan dake cikin matata ya zamo namiji! Allah yasa namiji zata haifaa na samu magaji ameen!! Ma"u da sauri ta share hawayenta ta kalleshi "Haba malam Ai ba'a yiwa Allah haka kai dai kawai kayi fatan allah ya bamu nagari, inma namiji ne inma mace !" Ya juyo ya kalleta "A'a fa Ma'u ki banni na roqi Allah ya ban namiji dan ni banida wani buri daya huce na haifi da na miji ba mace ba!" Iya se a lokacin tace " fadi ka kara dana,me za'ayi da wata mace? Ina laifin da na biyu ta haifo mace amma wannan cikin Inshaa Allahu namiji ne ehe!" Ma'u ta tashi ta girgiza kai alamar kalaman basu mata dadi ba ta shige daki cike da farin ciki A zuciyarta kuma mamakin furucin su Mal take,tabar Mal da iya a tsakar gida suna ta Farin ciki da anashuwar abinda ya faru! Iya tace "ka dinga kula da ita bari naje na sanarwa da en uwa da abokan arziqi wannan abin alherin,Ai banga ta zama ba" Ta fice tana guda shima kuwa cewa yayi "nima banga ta zama ba kuwa nima bari naje na siyo mata kayan makulashe! Share Recent Posts WA GARI YA WAYA? 2 WA GARI YA WAYA? 1 WA GARI YA WAYA?? 3 Comments No comments yet. Why not make the first one! New Comment [] Name: Comment: (Some BBCode tags are allowed) Post Comment options Home Guestbook About Me Feedback Blogroll Feed: RSS / Atom Comment Feed: RSS / Atom Get a October 2016 October 13 Thursday 11:12 PM Go to top Visitor Counter : total-0060690 © 2016 Hafsat's Mobile Blog . fmb_Powered by Copyright 2016 mrs hafcy design by muhammad abba gana (09039016969) [12:14AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [15]-[20] Ma'u tana zaune tana cin tuwo mirar kuka da yajin dadawar da mamanta ta aiko mata, gefe guda kuma farfesu ne Goggo(k'anwar babansu,wadda tazo mata zaman wanka) ta kawo mata,suna zaune ita da goggon suna hira,Babyn na hannun goggo,, Salamar Mal sukaji,ya shigo fuska ba yabo ba falasa suka gaisa da goggo tace "Ahh angon k'arni ne ke tafe ashe" be amsa mata ba,tamai barka, ciki-ciki ya amsa sannan ta basu waje Ma'u da murmushi ta juyo ta kalleshi "Mal kenan,inata cigiyarka kazo kaga kyauta da Allah ya bamu,Yau dai Allah ya amshi addu'ar mu,se mu gode masa"a fusace ya kalleta "ke dallah sauraramin! Kin tashi kin haifo wata mace, zakimin dadin baki,bari kiji zuwan nan danayi abu biyu ne ya kawo ni, ki saurara da kyau kiji"" Ma'u tace "Ikon Allah mal meya yayi zafi haka? kuma ai bani ce ke bada haihuwa ba,Allah ne ke bayarwa" Ya katse ta"Abu na farko shine: kinga wannan(ya fito da dari biyar 5) ita kadai zan bada ayi hidimar suna da sauran abubuwa,Kaya kuwa kinsan na gama siya dan haka kyasan yadda kikayi,,Ragon dana siya ma,zuwa zanyi a cazamin aban tunkiya dan banga amfanin yankawa mace rago ba! Abu na biyu, nazo muyi salama domin tafiya zanyi bayan suna na dawo,Dafatan kin gane?, Ma'u bata san sanda ta fashe da kuka ba,, "Mal yanzu abinda kayi ya dace mal? Kayi mana aladalci nida yarka? ,, Ya katse ta "kinga ni bance kimin surutun banza ba,in kina da magana ki fada da sauri, dan tafiya zanyi gidan iya yanzu,,Ma'u ta cigaba da kuka bata bashi amsa ba Yana k'ok'arin fita ne cikin dashashiyar murya tace " Mal dan Allah ina neman alfarma a wajenka" ba tare da ya juyo ba yace "tame?" Ta cigaba"Inaso kayi ma yarinyar nan huduba kamar yadda Kowanne uba ya kamata yayiwa Dansa ko yarsa,Sannan kuma inaso ka dauketa ta ji dimin jinkin ka koda na minti 5 ne,,Ta fashe da kuka Ya danyi jim sannan ya gyada kai,ya koma ya zauna,Ya turbune fuska, ta dauko babyn, ta mik'a masa ya karba yana gun-guni,, "Ai se ki fadi sunan da zan samata," Ma'u ta juyo tace "Da nazata ai kaine zaka zaba" a fusace yace "ke bansan bata lokaci" cikin sanyin murya tace "AISHATUL MUBEENA"" Tsaki yayi ,toh shikenan,, Ya mata hudubar,ta dan dade a hannunsa sannan ya mik'a wa ma'u ta karba tana murmushin yak'e,tace "nagode mal Allah ya kiyaye hanya" yace ameen, yasa kai ya fita" Ma'u ta k'urawa AISHATUL MUBEENA ido kawai se jin sabon hawaye tayi na zuba,Tausayin Yarinyar duk ya cika mata zuciya,,,Goggo ta shigo ta tadda ta tana kuka,da sauri ta iso wajenta"Ma'u meya faru kike kuka?" Ma'u ta share hawayenta "bakomai goggo" Goggo tace "ban yadda ba,ki fada min abinda ke damunki,ko wani wajen ke miki ciwo?" ma'u tace "A'ah goggo kaina ne ke ciwo" goggo tace "kuma shine kike kuka,bari na dauko miki magani" ta tashi dan dauko mata maganin Iya tashigo kamar yadda tasaba yau ma ba sallama" ke ma'u dama nazo fada miki sak'o ne, mijinki yaban kudin,Shinkapa da kayan miya na taron suna,Dan haka bazan baki kudin ba kuje ke da daginki ku kashe a banza,dan haka ana gobe suna kome ake buk'ata se kiyi magana,,""Ma'u ta girgiza kai"A'ah iya ki barshi kawai,Ni bazanyi taron suna bama,Na hak'ura kawai Allah ya rayata,Tunda bezo a al'k'urani ba dole se anyi taron suna ba" Iya ta zaro ido ta dafe k'irji "Lallai yar nan kin rik'a wato ni kike fadawa magana a fakaice koh?" Se a lokacin goggo tasa baki " A'a a'a Tani karki soma,Yarinyar nan a kalamata ba wanda yayi kama dana zagi ko kuma na bak'ar magana, iya tace kwaji dashi dai dangin tsiya ta fita tana masifa",Ma'u ta fashe da kuka "oh ni asma'u ya zanyi? Da bak'in cikin mijina ko dana uwarsa? ® OHW AISHATUL MUBEENA 20-30 [12:15AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [20]-[25] Goggo da sauri ta katse ta"karki soma fadan wadanan maganganun Ma'u kinji,Kiyi hak'uri komai lokaci ne" Ma'u tace toh goggo insha Allah bazan kuma damuwa ba,Zanta addu'a Allah ya ganar da mal gaskia,,Goggo tace yauwa yar albarka.. Yan uwa da abokan arzik'i sunata zuwa barka,Yarinya tana ta samun kaya masu kyau,,rannar suna kuwa duk da Ma'u tace bazata yi taron suna ba mutane anzo dayawa...wata mak'ociyarta wadda suke mutunci sosai khadija shinkafa dafa duka ta yimata me dadi da zobo,dayake mijinta nada hali,Ma'u tayi farin ciki sosai da abinda khadija ta mata tayi ta godiya,,,dangi aka zo anata kwashar girki ana santi,hada su Iya,don ita har diba tayi ta kai gida kowa yaji sunan yarinyar AISHATUL MUBEENA Se ya yaba sunan ,,,Liman ne ya yanka tunkiyar suna, Iya kuwa ta tsaya tsayin daka akan naman k'iri-k'iri ta hana dangin Ma'u da sauran mutane taba naman,Daga ita se yan'uwanta ne suka sarafa naman,Wai kada su Ma'u su handame, ita ma'u ma ko a jikinta...yarinya ta samu kaya kuwa masha Allah daga ita har Ma'u itama tana samu kudi da atamfofi,tayi mamaki sosai dan bata taba zata zata samu abin alherin data samu ba Bayan suna mal ya dawo,Ba yabo ba falasa,Amma kuma sam yaqi yadda ya dauki yarinyar koda wasa,Tun Ma'u tana damuwa har ta dena,Ta cigaba da kula da yarta da ita kanta bayan tayi arba'in ta zagaya dangi yawon arbain shima da kyar ya barta,,Iya kuwa kullum cikin tsangwamar AISHATUL MUBEENA take,Har yanzu kuwa bata dauke ta ba,se dai ta kalleta daga nesa BAYAN SHEKARA BIYU Mal naezaune a kofar gida suna tadi shida wani abokinsa sanda,Wasu mata suka nufo gidan su 3,A tare suka gaida Mal ya amsa yana washe baki daya daga cikinsu tace" Mune masu yak'i akan cutar poliomyelitis wato cutar polio,Mun samu labarin kana da ya shine zamuyi mata rigakafi,"Mal ya kalleta "ke ni banda yaro a gidana ku fice min daga nan shashasahai kawai" Dayar tace "kaga malam dan munzo mu taimake ka kaida iyalinka,baka isa ka zage mu ba,ko dayake naga alama kai jahili ne!" Ya juyo ya kalleta" ke wallahi se na kwada miki mari,wa kike cewa jahili?" Tsaki tayi "kai mana" Taja sauran suka yi tafiyarsu ...yayin da suka bar mal da sanda suna ta balbalin masifa Ma'u duk taji abinda ya faru,AISHATUL MUBEENA tana tsakar gida abinta tana wasa, Ma'u kuma tana wanki a tsakar gida, mamakin halin Mal kawai take... Ya shigo yana balbalin masifa ko salama beyi ba, ta kalle shi "Mal wannan yar muce fa, tana da hakki akan mu,Ka tuna fa tunda muka haifi yar nan bamu taba kaita asibiti ba,ko cuta tai se dai inyi yan dubaru na,nice zuwa neman maganin gargajiya,Amma kai ko da wasa baka taba nuna damuwar ka ba,,,Sun biyo mu har gida don su mata rigakafin wannan muguwar cutar, sannin kan kane wannan cuta nakasar da yayan mutane take,akan me bazamu basu damaba? Basu nemi ko biyar daga gare mu ba fa,Mal nagaji da wanna halin naka nagaji!!! " ta fashe da kuka... Ya galla mata harar sannan yayi tsaki " Ma'u ki shiga taitayin ki fa,Ya isheki abinda kike yi,rigakafin ne nace baza'ayi ba!,Ai yata ce nina haife ta kuma na isa da ita har dake! Sh [12:18AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [25]-[30] Ma'u da sauri tadago kai ta kalleshi "au yarka?, se yau kasan cewa yarkace,Kai yanzu baka ji kunyar fada bama? Wallahi mal in baka canza halin ka ba Allah se ya tambayeka,Allah wadaran wannan mumunan halin naka!" Mal a fusace ya dago ya wankawa mata mari ji kake Tas!! Aishatul mubeena se data tsorata ta fara rusa kuka itama, Mal ya kalli ma'u ya cigaba"Naga alama kin fara raina ni a gidan nan,Wato yanzu har ina fada kina fada zan fara maganinki ne mara kunya kawai wadda batada tarbiya"" Ya sa kai ya fita daga cikin gidan a fusace......Ma'u ta share hawayenta tace "Allah ga baiwar ka,Allah ka raya wanna yarinyar ya Allah"" ta dauki aishatul mubeena ta fara rarrashinta tana hawaye ahaka har aishatul mubeena tayi bacci To rayuwa dai haka ta cigaba yau da dadi gobe babu dadi,Ma'u kullum cikin hak'uri take da mijinta da kuma uwar mijinta wanda suka zamo mata matsala a rayuwarta Yanzu dai shekarun AISHATUL MUBEENA 3 ta taso yarinya kyakyawa san kowa k'in wanda ya rasa,ga farin jini masha Allah,yara har fada ake akan daukanta saboda kullum tsaf da ita,Har ta fara magana sosai,abin mamaki kuwa itama tsoron babanta ma take dan tun tana k'arama tasaba tana zuwa wajenshi ze hantare ta hakan yasa ko kusa da shi bata san zuwa.. Yau AISHATUL MUBEENA ta tashi da zazzabi me zafin gaske ga ciwon kai se kuka takeyi,dagabaya kuma tace kafarta na mata ciwo ta kasa tafiya sam kafar ta rik'e ,,Ma'u ta rikice sosai ta rasa yadda zatayu ga yarinya tana ta rusar kuka, Data ga abin yayi yawa gashi tasan mal ko me zatai mai baze kulata ba se ta saba ta a baya ta shiga gidan khadija bayan sun gaisa ta mata bayyani,Khadija itama duk ta rude,Can tace "Inaga gwara mukai ta asibiti,Dan shine kadai mafita" ma'u tace "Toh shikenan ba matsala" khadija tasa aka hayo musu mota dan kai su asibitin garin dayake akwai wanta yana aiki a asibitin,,,Basu dade ba se ga mota ...nan nan da nan taja sukai asibitin Emergency aka shiga da ita aka shiga bata kulawa ta gaugawa,,Ma'u se kuka takeayi dan ita ganni take kamar mutuwa zatayi,,Khadija ce ke rarrashinta Bayan dan lokaci likita ya fito yana share gumi,Ma'u tana kuka tace "likita ya take? Ya jikin nata?" Likita ya ce a gskiya yanzu bamu gano komai ba,amma dai yanzu zamuyi mata test na aika lab,Se kujira kan result din ya fito" Ma'u tana kuka tace "toh likita Allah yasa muga alheri,," Yace ameen ya fice,Ma'u kukan nata ya k'aru sosaii; khadija itama se ta fara kuka dan suna bata tausayi sosaii, Tace "kiyi hak'uri maman mubeena komai yayi zafi maganinsa Allah,Inshaa Allah zata tashi cuta ba mutuwa bace !" Ma'u ta share hawayenta sannan tace "Toh khadija Allah yasa amma se nake ganni kamar bazata tashi ba!" Khadija tce"A'ah insha Allah zata tashi,Bari naje can gida sena na sanar dasu iya su san abinda ake ciki" Tana isa kai tsaye gidan iya ta shiga bayan sun gaisa ta sanar da iya,Abun mamaki iya se ta nuna damuwarta ba laifi ta sakko hijabi tace suje asibitin,sannan tabar sako da a nemo mal sule a fada mai halin da'ake ciki A kuma fada mai ya samesu a asibiti! Har suko isa ma'u kuka take se rarrashinta suke yi, a dan lokaci nan duk ta fita hayyacinta idanunwanta duk sun k'ank'ance saboda kukan datakeyi, Suna zaune se ga likita ya fito a razane ya kallesu yace............................ Share AISHATUL MUBEENA 30-40 [12:19AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [30]-[35] Likitan ya kallesu yace "ku biyoni office!" Ma'u ko takalmi bata sa ba ta bishi da sauri suma su khadija suka biyota Bayan sun zaune likita yaja numfashi sannan yace "ki nutsu ki fada min al'momin da ta fara kan ciwon yayi tsanani, Ma'u ta share hawayenta sannan tace "Ta fara da ciwon kai da dadewa amma jefi jefi in na bata magani takanji dadi,sannan takance kafarta na ciwo,to shine yau tun safe abin yayi yawa tana ta kuka,Ga zazzabi ga ciwon kafa" Likita ya share guminsa yana jinjina kai Likita ya maida numfashi sannan yace "Ana wa yarinyar rigakafin Cutar poliomyelitis (polio) kuwa?" (Gaban ma'u ya fadi)"A'ah ba'a taba yi mata ba" Likitan a fusace yace ' u see,kun ganni (ya daga murya) Duk k'ok'arin da gwamnati takeyi akan yak'i da cutar polio tana turo mutane su bi gida-gida dan yin rigakafin cutar,Kuna ina????Meyasa baku basu damu su mata ba,Dan nasan tabbas suna zuwa amma kuk'i basu dama,,,meyasa???!!!"" Ma'u ta fashe da kuka "Wlhy likita BA LAIFI NA BANE laifin babanta ne ba yadda ban yi dashi ba amma sam yak'i,," likita yace "Toh shikenan yanzu kun janyowa yarku,A iya gwajjin da mukayi.....Am sorry to say,, kwayar cutar polio ya riga ya gama bin jikinta,kuma kafarta ya taba "A YANZU HAKA YARKU TA RASA KAFARTA TA HAGU,ZEYI WUYA TA SAKE TAKAWA DA KAFAR !!DOMIN KWAYAR CUTA TA FI K'ARFI A KAFARTA!!! Innalahi waina ilaihi raju'n Khadija ta shiga maimaitawa iya kuwa kasa magana tayi,,Ma'u kuwa sulalewa k'asa tayi sumamiya!! Da sauri sukayo kanta nurses suka zo da gado aka dora ta Likitoci sun dade akanta,,Anci sa'a kuwa mal yazo shima yadan damu ba laifi ,Se wani kumbure- kumbure yake Likita ya fito yace," ku biyoni office",a gigice suka bishi ya kallesu cike da fushi yace "wai ku dan Allah meyake damun kune,? Matar nan tana da hawan jini amma baku taba kawo ta asibiti an gwada taba,Yanzu jinin ta ya hau over,,Allah ne yayi kiyaye da wlhy zata iya samun mutuwar barin jiki stroke! Suka zaro ido gaba daya banda mal,khadija tace "likita wallahi bamu sani ba,bata taba fada mana ba "likita ya nuna mal" kaine mijinta,, Ya galla masa harar sannan yace "Eh nine ya akai yi ne?" Likita a fusace yace "Amma wlhy baka da tausayi sam,wacca irin zuciya ce dakai?? Ka yi sanadin nakasa yarka sannnaan kana nema ka nakasa matarka ko ka hallaka ta har lahira,Kai wani irin mutum ne? Mal ya kalleshi kallo na rainin hankali sannan yace "Kaine bakada hankali,Ni nasan abinda nakeyi,kuma ba ruwanka da harkar gidana,mutumin banza kawai'' likita yayi murmushi "Ni bazan tsaya cacar baki da kai ba saboda ni bana cacar baki da jahilai irinku! [12:19AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [1:33PM, 12/02/2016] Miss Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [35]-[40] Mal yana nema ya cakumi wuyan rigar likita da sauri iya ta tare shi" Wlhy ka sake kayi fada dashi sena maka baki mara hankali kawai' Ya kalleta yayi tsaki sannan ya fice daga asibitin,likita girgiza kai yayoi cike da takaici ya cigaba da yi musu bayani An sanar da yan gidansu ma'u mamanta da goggo ne sukazo se kuka sukeyi da kyar aka lallasheshu,,,Ma'u kuwa bata dan fara dawowa daidai ba se datayi kwana2 a kwance Aishatul mubeena kuwa tana can an ware mata gadon ta daban likitoci ne kawai ke zuwa dubata Ma'u ta dan murmure,Tana shan magugunata sosai sannan likita ya mata nisiha sosai aka ta kwantar da hankalin ta,Addu'a ce ya kamata ta dinga yi,,Yawan damuwar datakeyi ne yasa ta hawan jini! Bayan ta dan warware hankalinta na kan yarta,,Hakan yasa tace suce wajen likita ya musu bayani,,bayan sun shiga,Ma'u cikin sanyi murya tace "Likita yanzu ba wani magani Da za'ayi mata ta sami sauk'i kafarta ta dawo daidai tunda naji kace kafarta Ta riga ta shanye" Likita ya nisa sannan yace "Malama ma'u kiyi hak'uri,Hanya daya da za'a iya maganin cutar shine....... RIGAKAFI! wanda ku kuma bakuyi wa yarku ba! Amma cutar polio in har ta riga ta kama mutum BATA DA MAGANI!!,Amma yanzu muna bata painkillers wanda zasu maganin wannan ciwon kai da zazzabi,da kuma ciwon kafar,,Kuma Alhamdulilah yanzu ta fara samun sauk'i,,,,Sannan batun kafarta na fada muku cewa bazata iya tafiya ba due to weakness na kafar,Yanzu zamu bata WHEEL CHAIR in ta k'ara girma kuma se ta fara amfami da FOREARM CRUTCH,lokacin kafarta ta dama ta k'ara kwari,Dan kunsan itace me lafiyar kuma yarinya ce,Kafar ba wani kwarin kirki tayi ba" Ma'u ta fashe da kuka yayin da mamanta,iya,Goggo,Da khadija suka Jin jina kai cike da tausauyi,,(Dan yanzu iya ta saduda ta gane laifinta,Har kuka tayi da tana bawa ma'u hakurin abinda tamata a baya) ,Likita ya cigaba "Ba kuka zakiyi addu'a zaki ki kuma godewa Allah dayasa nata yazo da sauk'i,Dan akwai wanda take ja musu paralys,Amma ita ai kafarta ta hagu kawai ta taba kuma zata iya komai dinta nrml,Nan da sati1 zakiga ta dawo daidai se dai kawai kafarta ta hagu da ta tabu ne!" Ma'u da murya kuka tace "shikenan likita,Allah ya raya ta,ya kuma sa k'arshen wahala kenan! Gaba ki daya sukace ameen,, Mama(maman ma'u tace) " Ma'u kiyi hak'uri ki fawala Allah komai,Yana tare dake kinji kiyi hak'uri duk da nasan kinayi ki dora akan wanda kike yi"Ma'u ta rungume mama "toh mama insha Allahu" khadija ta runtse idonta se hawaye tausayinsu duk ya cika mata ciki... BAYAN SATI 1 A yau aka salame su,Gwamnati ce dama ta dau nauyin duk wata dawainiyar sh,,Da zasu tafi aka basu wheel chair da kuma forearm crutch,kyauta shima,se godiya suke yi,,AISHATUL MUBEENA kuwa ta warware har dariyar ta takeyi,,Amma rannar data koma normal se data kalli ma'u tace "Umma,kinga kafata yadda ta dawo,A haka zatai ta zama?" Ma'u ta fashe da kuka a hankali duk da tana k'ok'arin kada ta gane ta dage tace "a'ah aishatul mubeena zata warke yi hak'uri,," Tayi murmushi tace "toh umma" A rannar da suka koma yan'uwa da abokan arziki suka dinga zuwa dubiya,kowa ya zo se yaji tausayin aishatul mubeena,ita kuwa dayake da yarinta haka take dariyarta tana harkar ta ba ruwanta,ita a wayonta ta zata kafar tata zata warke ne kamar yadda mamanta ta fada mata,,, Mal ne ya shigo gidan yana masifa 'Bazan iya bafa,baze yiwuba,Ayi ta zagina a gari anacewa inada ya gurguwa! Ma'u a fusace tace "Mal ya isheka fa,Waye ya ja mata? Ba kaine ba,Azzalumi kawai,Me bak'ar zuciya! Ya juyo da mamaki "lallai ma'u kin rik'a,Amma saurara kiji,Yau din nan zanyi maganinki!" Ma'u wani murmushin tak'aici tayi ta tana kallansa,,Ina sauraronka,, Yayi wata dariyar mugunta sannan yace............ Comment as: Publish Preview No comments: AISHATUL MUBEENA 45-60 [12:22AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [45]-[50] Likita ta ganni tsaya a jikin mota yana murmushi,,kasa magana tayi ta tsaya kawai tana kallansa cike da mamaki,,Dayaga shirun yayi yawa se yace 'Malama ma'u ya kika tsaya anan k'araso mana" jiki ba kwari ta karaso ya durk'usa ta gaishe shi ya amasa tare da murmushi sannan yace "nasan zakiyi mamakin ganina" Ta gyda kai alamar eh Ya cigaba"Hak'ik'anin gaskiya tunda na ganki ke da yarki nake tausayin ku,inason taimakon ku kuma Cikin ikon Allah Se akamin transfer na koma Asibitin aminu kano,Shine kwanaki na kawo ziyara garin nan se nake tambayarku se ake cemin ai kun rabu da mijiniki,,To gskia bazan boye miki ba tun daga nan nake jin sonki a zuciyata daga baya shine na yanke hukunci nazo na nemi amincewarki dan Da aure nake sanki ba da wani abu ba! Ma'u tayi murmushi "Toh likita zanyi shawara insha Allahu nagode kwarai,Se dai kuma bansan sunan ka ba", Likita yayi murmushi sannan yace " Sunana DR MUHAMMAD AMEEN" Ma' u tace "Toh Dr nagode,' yayi murmushi sannan yacr "Inason zanyi magana da magabatanki in har kin amince dan na dinga zuwa wajen ki" tace "Bakomai Insha Allahu ba matsala" yace "Masha Allahu amma nagode da wannan tarba me kyau da kika min,, ma'u tace bakomai ai,,,Yace "ina yartawa take? Ma'u tace tana ciki bari na fito maka da ita" yace toh ya bude motarsa ya dauke wata leda sannan ya kulle motar Ma'u bata dade ba se gata da aishatul mubeena tana turota,Ita kuwa tana murmushi tace "Ina wuni" yace lafiya lau my daughter, Ya jikin naki? Tace da sauki,, Ya mik'a mata ledar da kyar ta karba ma'u tai ta godiya Sun dan yi hira Kadan yana bata shawara akan yadda zata dinga kula da aishatul mubeena dagabaya sukai salama Bayan ta koma gida tayi wa mama bayanin komai mama ta ji dadi ta kuma ce zata fada wa kawaunan ta da kuma yaya basiru Abu kamar wasa zancen har ya mik'a yau Dr yazo da magabatansa bayan sun Gaisa kawu na katsina (Kawun su ma'u) yace,"Zamu iya sanin ka sosai" dr yayi murmushi yace "Nidai sunana DR MUHAMMAD AMEEN inada mata daya da yaya guda hudu : Ameen(Abba) ,Abdulhafeez,Se Husna da Aisha,,Ni baban likita ne yanzu a aminu kano ina zaune a kano da iyalaina unguwar lamido cresent,,Wayan nan kuma (ya nuna kawunansa) daya k'anin babana ne dayan kuma k'anin mamana ne wannan kenan Kawun katsina yayi murmushi "Masha Allahu"Yanzu zamu kirawo ita ma'u muji daga gareta kaga tunda bazawarace in ka amince yau se a daura auren,Amma se munji daga bakinta "dr ya gyda kai "toh bakomai" Yaya basiru ne yaje ya kirawota kanta na k'asa ta gaida su cikin girmamawa suka amsa ,,Kawun katsina yayi mata bayanin komai sannan yace "Yanzu yardar ki muke neman in kin amince se a daura aure!" Gaban ma'u ya fadi ashe dai da gaske ne ita bata zata abun ya kai ga haka ba har ana cewa za'a daura auren yanzu,,Ta sunkuyar da kanta tace.................. Like · 4 · Repl Share [12:22AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HASA WRITERS [50]-[55] Tace "To shikenan Allah ya zaba mafi alheri"Dr wani dadi yaji a ranshi,Tana gama fadan hakan ta fita daga falon,,kawun katsina yace "To Masha allahu tunda ta amince yanzu se muje masalaci tun dan naga ana kiran sallar la'asar bayan an idar se a daura auren,ince dai a shirye kuke(Ya kallesu)? Dr yace eh mal muje" Cikin K'ank'anin lokaci aka daura auren Muhammad ameen da Asma'u (ma'u) akan sadaki dubu10,Ango yayi alkwarin wani satin ze aiko da Kayan lefe se ta tare.. Tuni dama ya sanar da matarsa Hajiya Hadiza,Dayake tana da mutunci sosai kuma ba ruwanta addu'ar fatan alheri tayi masa,Ta kuma ce inshaAllahu zasu zauna lafiya,Indai ta bangarenta ne baza'a samu matsala ba Yau ne tariyar ma'u,Bayan tayi yar walima a gidansu,,Ita kadai aka kai gidan mijinta banda Aishatul mubeena a cewar mama insunyi sati 1 se akawota,Dan dr da kanshi yace ze dauke ta ya dau nauyin komai dinta kamar yarsa ta cikinsa Gida Masha Allah me kyau da shi bene ne sama da k'asa,Hajiya hadiza tana sama yayinda ma'u ke k'asa falo ne dan madaidaici da kuma dakuna biyu se kitchen da bandaki da dan tsakar gida ,,Dan yaya basiru da su kawun katsina sunyi mata kayan daki ba laifi,,,Kowa se yi mata murna akeyi mama ta mata nasiha sosai akan ta zauna lafiya da uwargida ta kuwa dauka dan ita ba ruwanta bata san hayaniya ma Dr ya tarasu yayi musu nasiha baki daya kuma sun nuna mai sun dauka suka mai alkwarin zasu zauna lafiya,, Bayan sati Dr da kansa yaje ya dauko aishatul mubeena da kayanta tana ta murna za'a kaita wajen ummanta,Rannar da'aka kaita suka fara sabawa da husna ;Sa'arta kuma akwai san mutane tafi aisha san mutane sosaii nan da nan suka saba kamar dama sun San juna,Husna tana shekara 4 ita kuma Aisha shekara 6 Suna zaune a falo dasu husna YA ABDUL ya shigo fuska ba yabo ba falasa, masha Allah kyakyawa ne sosai,Ga shi akwai tsayi,duk da befi shekara 15,Ya gaida Umma(ma'u)ta amsa da fara'arta tana mai sannu da zuwa dan boardn skul yake yi yau ya dawo,,Husna da Aisha da sauri suka taso zasu mai oyoyo cak! Suka tsaya sakamakon muguwar hararar da ya wurga musu,,"ku meyasa ba kuda hankali ne ni zaku zo kuna wa oyoyo ?banzaye kawae" ya fada cike da fushi daidai shigowa haj hadiza(ummi haka suke cemata) tace "kadai abdul Allah ya shirye ka ,kai da yan -uwanka Kana hantararsu kaji kunya wlhy" Yace "To ummi akan meye zasu zo suna min oyoyo se kace yaro sa'ansu!" Umma datake dariya se a lokacin tayi magana " Anty na ,ai da gskiyar sa ya girma fa" ummi tayi dariya "halinsa ne kenan fa,ni rasa gane irinsa,Haka yake,hira ma basa yi ,Suna mai magana ya hantaresu wai shi baya san raini,dadai, YA AMEEN,,kikace shine ba ruwanshi,yaranan kamar k'awayensa haka ya daukesu,,suyita hira suna raha abinsu abin sha'awa" umma tace " shima ai yanason su,Da alama magana ce bata dameshi ba ,(ta kalleshi)Rabu da ita Dana bari na kawo maka abinci kaci,, Yayi murmushi "Toh nagode" be sake magana ba ,umma ta tashi ta nufi kitchen dan zubo masa abincin,,,yayin da ya zauna a kujera yana jiranta,, se a lokacin ya lura da Aishatul mubeena dake kan wheelchair tayi tsuru-tsuru,dan har ta fara tsoronsa,, Ya kalli ummi da mamaki "Ummi wannan waccece?? L Share [12:23AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [55]-[60] Ummi tayi murmushi "k'anwarka ce,Yar antynka ce" yace "Allah sarki,But yana ganta a wheelchair ciwo taji ne? Ummi ta kada kai "A'ah polio victim ce! Ya zaro ido ya maimaita "polio victim kuma??!,garin yaya? Ya akai ta samu? Ummi tace "Kai kaga bansan tambaya nima bansani ba, Allah ne ya dora mata,ya isheka haka, yace toh ummi,, Kallo daya ya mata ya kauda kai a fili yace "Sannu kinji ya sunanki? A tsorace tace "Aisha..tul..mubeena" ya gyda kai "nice name" Daidai lokacin umma ta shigo da tray na abinci a hannunta ta dire mai a gabanshi yayi godiya ya kai loma daya kenan daga waje suka jiyo murya "Salamu alaikum Ummina my lovely sisters kuna ina?? Hakan ya tabbatr musu da cewa YA AMEEN ne,, Da gudu aisha da husna suka tashi suka nufi wajen sa, ya ware hannunsa suka taho da sauri suka rungume shi Yayi murmushi "Nayi missing dinku Deariz" suka amsa muma munyi missing dinka bros Ya rik'e hannunsu suka k'araso wajen su ummi , ummi tayi murmushi ta kalli umma "kingani ko dama na fada miki wuyata ya dawo,shi ba ruwansu ba kamar wannan sakaran ba!" Umma tayi murmushi ya k'araso wajen ummi ya rungumeta, Da sauri ta kwace "kaga ni bansan wannan shashashacin" yayi dariya " ummi nayi missing dinki dayawa" tace "nima haka dana" Yace "Finally dai mun gama secoundry skul Nan da yan shekaru zan zama PILOT,, Ummi tace "Insha Allahu munan muna ma addu'a yace "Dats my ummi" Ya juyo ya kalli umma ya gaisheta da girmamawa ta amsa,,Tare da yi masa sannu da zuwa da kuma murna kamala sakandire,,Yayi ta godiya,,Se a lokacin ya lura da Aishatul mubeena Ya kalle ta yace "Fine girl bakida lafiya ne? Ya na ganta a wheel chair? (Ya kalli su ummi)Umma tayi murmushi ta sunkuyar da kanta,, Da mamaki se sukaji tace "Ni polio victim ce!" A tare ummi da ya abdul suka zaro ido,,Lallai yarinyar nan daga fadan abu har ta gane ta haddace,, Haka Ya abdul yace a zuciyarsa"Ya ameen yace 'Eyyah Subhanalahi " ya kalli ummi " Ummi da gaske take? Umma da sauri tace"Da gaske take Ameen, kawai se ta fashe da kuka,, Ummi ta shiga rarashinta shikuwa ya ameen be san sanda hawaye suka fara zubo masa ba nan da nan tausayinta ya cika mai zuciya,, yaji kuma wani santa a zuciyarshi,,jinta yake tamkar k'anwarsa uwa daya uba daya ! ya matso kusa da ita yayi murnushi "Ya sunanki" ta wangale baki "Sunana Aishatul mubeena! Yace wow nice name " zaki sha sweet?" Tace ' eh" yace " toh zomuje na siya miki, umma da sauri tace" aah ameen ka bari ka huta mana, daga dawowarka? Yace bakomai umma yanzu zamu dawo Ai nan kofar gida ne,, Ya ja wheel chair din suka fita Jin haka husna da aisha suka ce zasu je suma,ba musu yace su taho yaja wheel chair din yana mata murmushi "Muje na siya miki sweet koh? Tace "Ehh tana wangale baki" suka fice Abdul kuwa tabe baki yayi, ya cigaba da cin abincinsa ,Umma kuma dadi taji a ranta sosai Basu dade ba se gasu sun dawo Kowa da sweet a hannunshi se wangale baki suke,,Aishatul mubeena ta kalli Ya ameen kainu wajen umma,,Yace toh yaja wheel chair din wajen umma ta wangale baki "Ummana kinga ya siyamin sweet" Umma tace"nagani angode" Ya ameen yace "Niwa? Ya sunana? Tace "Bansan sunan kaba ni" umma tace "Auu baki san sunan shi ba?" Tace "Eh ya sunanka" Yayi wani murmushi sannan yace... AISHATUL MUBEENA 60-80 [12:23AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [60]-[65] Sunana Ya ameen amma kin san me zaki dinga cemin? Ta gyada kai "A'ah" Yace toh ki dinga cemin "Bros" ya abdul dayakr k'ok'arin tashi ya fashe da dariya,"Wayaga bros! Su bros manya" ya tsuke fuska kamar ba shi yayi maganar ba sannan ya tashi ya fita,, Ya ameen yace "Ka dai ji dashi dan rainin hankali" Aishatul mubeena kuwa maimaita sunan ta shiga yi "Bro...s Yau ma kamar kullum bayan sallar magariba suna zaune gabadayansu a falon Abba suna hira ,,Ya ameen yace "Abba nikuwa inada shawara" abba yace inaji "Abba me ze hana aishatul mubeena ta dinga gwada tafiya duk da dai tafiyar bazata zama daidai ba? In ba haka wlhy tafiya da Forearm crutch din nan ze mata wahala sosai" Abba ya numafasa sannan yace "To ka dinga koyawa mata takawar muga,Indan tana takawa shikenan ba matsala idan kuma ta kasa kaga dole sai dai tayi amfani da forearm crutch din" yace to insha Allah za dinga gwada mata,, Umma tace "Angode fa Allah saka da alheri" yace "Bakomai umma" Yau da yama ya ameen Ya sauko da ita daga wheel chair din yana koya mata tafiyar,Ba laifi ta na dan k'ok'artawa yaji dadin Haka kullum addu'arshi Allah ya taimake ta,Ta fara cangala kafar tata dan a ganin shi hakan yafi da yawo da sanda" YAU DA GOBE SAI ALLAH yanzu dai Aishatul mubeena tana ss2,tana iya takawa amma saidai tafiyarta ba irin ta masu lafiyar kafa bace cikin ikon Allah tana iya cila kafarta tayi tafiya,,,, Ta k'ara girma ta zama yan mata,,Tana da shekaru 16 Duk da ba lallai ka gane hakan ba saboda yar k'arama ce kuma gata Ba k'iba saboda cutar polio ta k'ara motse ta,,Amma duk da hakan kyanta yana nan akwai kyau Masha Allah,,, Ya abdul yana final year dinshi a university inda yake karantar Engineering danshi dama burin sa kenan ya zama engineer yayin da Ya ameen Ya zama cikaken pilot har ya fara aiki ma Allah mai baiwa duk da nakasa irinta Aishatul mubeena,,Amma Kuma Allah ya bata kwakwala Tanada masifar k'ok'ari mussaman ma a fanni Ilimin addini harda na bokon ma,,,sannan kuma cikin ikon Allah,Allah se ya bata fasahar yin ZANE yanzun zata kalli abu ta zana shi tsaf kuma ya zanu sosai tayi fice A makarantarsu a harkar zane sosai,,Kuma cikin ikon Allah Ya ameen ne ya fara gano haka kuma ya bata kwarin gwiwa sosai,,Duk wani abu datake buk'ata a harkar zane da kudinshi yake siyowa ya bata! AISHATUL MUBEENA ce t zaune akan Farar kujera a compound din gidan,Kur'ani ne a hannuta tana karantawa a hankali,,, YA ABDUL ya shigo da motarsa ya faka ta a wajen fakin din motoci,,Sanye yake da Bakin wando da riga sky blue yayi bala'in kyau,,Ya k'ara girma ya kuma k'ara kyau A hankali ya tako wajen datake karatun yana sauraron k'ira'arta me masifar dadi,, Taji kamar alamar mutum da sauri tajuyo suka hada ido,,Bashiri ya kauda kai,,ya tsuke fuska yace " Ke me kike yi anan? Murya na rawa tace "Daman karatu nake yi," yace "Toh shi karatun ba'ayinshi a ciki ne? A sanyaye tace "Saboda naga suna kallo ne banason na dame su" yayi dan k'aramin tsaki sannan ya bar wurin,,Ita kuwa ajiyar zuciya tayi ta cigaba da karatunta Ba'a dade ba sai ga Ya AMEEN nan ya taho daga dakinsa yana ta mata murmushi(Dan bashida aiki week din) Tana ganinshi tayi wani yalwatatacen murmushi ya k'araso yana mata murmushi "SIS karatu ake ne? Tayi murmushi "ina wuni bros" yace "Lafiya lau sis karatu ake ne? Tace "Eh suratul khaf nake karantawa kasan yau juma'a kuma sannan jibi insha Allahu zamu yi musabak'a ! Ya wangale yabaki "Masha Allah my l sister am very very proud of you,,Allah ya bada sa'a insha Allahu ke zaki ci,, Tace "ameen nagode bros" Yace "Ga wani albishir din kuma;, tace inaji bros" yayi murmushi " Yanzu uncle hashim(teachern su aishatul mubeena) yace min aiy an zabe ki a gasar zanen da za'ayi a Schools din dake kano wanda kuma idan kinci shi ze bada damar ki wakilci kano gabadaya a gasar da za'ayi da states din dake nigeria.... Ta zaro ido da gaske bros? Yace "kwarai kuwa! Tace anya zan iya kuwa? " yace see you! Zaki iya mana insha Allahu se kin cinye mudai kawai mu cigaba da addu"a,, Tace "Nagode bros" Ya harareta "To meye na godiyar kinsan dai banaso Like · 3 · [12:24AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: by Hafsat ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [65]-[70] Ta sa hannu ta rufe bakinta toh shikenan na dena, yace "Yauwa ko kefa" Bayan sallar isha,Aishatul mubeena na zaune akan sallaya tana muraji'a,Husna ta shigo da kur'ani a hannunta,Ta zauna kusa da ita tace " Sis pls biya min nan,Ko sau daya ne" Aishatul mubeena na k'ok'arin dauka sai ga ummi nan ta shigo,Ta kalli husna" Ke husna me yasa zaki dinga damunta kinsan dai Musaba'ka garesu gobe ki barta tayi tilawa mana" Husna tace "Kai ummi kawai fa cewa nayi ta biya min shafi nan sau daya" Ummi tace "eh duk da haka,Kije umma ta biya miki mana" Aishatul mubeena tace 'Ummi dakin bari ma na k'ara mata" ummi tace "Aah dai gwanda ta barki kiyi karatunki" Husna na zumbure zumbure ta bar wajen......... To Yaune dai zasu tafi musabak'ar tun safe ta shirya tsaf cikin hijab har k'asa uniform din makarantarsu Tayi kyau sosaii,,Ya ameen ne da kanshi ze kaisu,, ita da su husna da kuma k'aninta Amir( Yaron da Umma ta haifa a gidan) dayake duk makarantarsu daya.... ,,(Da harda su umma za'a amma zasuje Gaisuwa zaria wani dan uwan abba ya rasu) A lokacin da suka isa Mutane an taru sosaii,Makarntar dazasu yi gasar da ita har daliban sun iso da kuma wanda zasu kara da Aisha....Bayan an bude taro da addu'a,Aka fara.... Cikin ikon Allah kuwa Aishatul mubeena tayi kok'ari sosai,,Gyra da aka mata basu da yawa,,bayan an kamala aka Aka kirawo malam salisu(Babban malami ne shi) dan yazo yayi jawabi sannan ya fadi sakamako,,,,,Sai da malam ya fara jawabi ya kuma ja hankalin dalibai da su dinga maida hankali wajen karatu sannan ya fara karanto sakamakon kamar a haka: "A musbak'ar Alkur'ani mai girma da muka gabatar tsakanin makarantar,khalid ibn walid islamiya da kuma Nana khadija Islamiya,, Makarantar nana khadija islamiya wadda ta samu wakilcin Aliyu sani tana da maki sha biyar (15) a cikin maki talatin( 30)A mata kabara,,(Dalibai suka dauka Allahu akbar) Sannan makarantar Khalid ibn walid islamiya wadda ta samu wakilcin AISHATUL MUBEENA MUHAMMAD AMEEN tana da maki..... ashirin da biyar(25) a cikin maki talatin(30)! ku musu kabara(Dalibai suka wage baki Allahu akbar) Aishatul mubeena dake gefe wata ajiyar zuciya tayi tare da Hamdala bata san sanda ta fara hawayen murna ba,, Mal ya cigaba ' Wannan ne ya tabbatar mana da cewa makarantar khalid ibn walid itace ta cinye wannan gasar karatun Alkur'ani me girma,, ku sake rangada musu kabara(Dalibai aka dau kabara da karfi,nima danake gefe wage baki nai nace Allahu akbar) Dan haka an shirya kyautuka masu tsoka ga wandanda suka yi Musabak'ar domin mu k'ara k'arfafa musu gwiwa dama sauran dalibai,, Dan Haka yanzu zan fara da Aliyu sani,, Alhaji Abdu mai nerori ya bada kyautar Dubu Da kuma Alk'urani me girma izu sittin ya kuma ce a bawa wanda ya zo ta biyu a wannan gasar karatun Alk'urani me girma,, Aliyu sani sai ka fito ka amshi kyautar ka,, Ba dadewa aliyu sani yazo ya karbi kyautarsa ana ta masa kabara Malam ya cigaba sannan Zamu kira AISHATUL MUBEENA MUHAMMAD AMEEN domin ta amshi kyaututukanta,,Ba'a dade ba sai gata ta taho tana cangala kafarta malam ya cigaba " Alhaji Audu mai nerori ya bada kyautar Naira dubu dari (100),Ga duk wanda yazo na daya Sannan Shugaban kamfanin jirgin **** ya bada kyauta kujerar umara shima ga wanda yazo na daya,Sai kuma haj asabe ta bada kyautar atamfa guda uku (3) itama ga wanda ya lashe gasar karatun alkur'ani Dan Haka Malama Aisha se kizo ki karbi kyautarki ta matso ta karba ana ta daukan hotonta mussaman ma da'aka lura da nakasar dake jikinta,, Ita kuwa se hawayen murna takeyi hannu na rawa ta karba aka dinga kabara,, Malam daga k'arshe yace,Dan haka sai muyi wa bayin Allah nan addu'ar Allah ya saka musu da alheri ya kuma k'ara budi.... Yayi addu'a sannan ya koma ya zauna.... Tana dawowa daga wajen Karbar kyautar kai tsaye wajen Ya ameen ta nufa ta mik'a masa kyautar sannan ta koma ta zauna ta kifa kai a gwiwa tana kuka,Ya ameen kuwa rarashinta ya fara "Haba sis ki dena wannan kukan mana Godewa Allah ya kamata kiyi ba kuka ba! Ta dago idonta ta share hawayen sannan tace " Toh bros insha Allahu na daina " yace "Toh yimin murmushi mana" Batasan sanda murmushi ya kubce mata ba,,Shima murmushi yayi yace "Yauwa ko kefa" mutane se zuwa yimata Allah sanya alheri suke mussaman ma dalibai da kuma malaman makarantarsu kai hadda baki.... Bayan an rufe taron Har zasu tafi gida tace a tsaya ta zata je ta dawo,Suka ce toh......Kai tsaye wajen shugaban makarantarsu ta nufa ta tsuguna har k'asa ta gaishe shi ,Ya amsa da murmushi "Tashi mana Aisha,Gaskiya kin burge mu sosaii muna alfahari dake Allah ya saka miki da alheri ya k'ara buda miki kwakwalki ,,kin k'ara fito da makarnatar mu ba abinda zamu ce miki sai godiya da fatan alheri"" Tayi murmushi "Malam aiy nice da godiya,Nice ya kamata nayi muku godiya ma,,Nagode nagode Allah ya saka muku da mafificin alheri Ameen" Malam yace "Ameen Aisha,Allah ya sa sauran dalibai suma suyi koyi dake" Tace "Ameen" sannan ta bude jakarta ta zaro envelop din nan da aka bata na Naira dubu dari(100).... Like · 2 · Reply · Ed [12:25AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [70]-[75] Ta mik'awa Malam Iro (Sunan shugaban makarantar tasu) murya a sanyaye tace "Malam ga wannan kai da sauran malamai ku kasa sauran abinda yayi ragowa kuma a siyo butoci da tabarmu akai massalacin makaranta " Malam ya zaro ido "Haba a'eesha(Dayake haka yake ce mata) Ai kudinki ne ba namu ba,Ki rik'e kudinki kinji Allah ya samu su albarka mukam mun gode bama karbi kudinki ba gaskiya" ta ja numfashi sannan tace "A'ah malam dan Allah ka k'arba,Ba a maida hannun kyauta baya!" Malam yayi murmushi " To sai da mu dauki dubu ashirin(20) ta ishe mu" tace "A'ah malam dan Allah ka karba duka" Yace "Toh shikenan raba a biyu ki bamu rabi Allah ya sa albarka" ta wangale baki " Yauwa malam gashi(Ta mik'a masa kudin duka) ya ciri dubu hamsin (50) kamar yadda Yace sannan ya mik'a mata yace "Gashi nan a'eesha mun gode sosaii Allah ya saka miki da alheri ba abinda zamu ce miki sai godiya" tayi murmushi "Godiya nake malam Allah ya biyaku" Sannan ta koma wajen motar tasu suka nufi gida Suna isa gida a harabar gidan ummi da sauri tazo ta rungume ta,Tana ta murna "yata kin burgeni gaskiya,Am soo proud of you My daughter,Ina alfahari dake Yata, aishatul mubeena tayi dariya "Nagode ummina" Umma itama ta zo wajen cike da murna Ta rungume yarta ta,Batasan sanda taji hawaye na zuba ba duk iya kok'arin datayi na ganni hawayen basu zuba ba amma sai da suka zuba,,A firgice ta kalli umman tata "Umma kukan me kike yi?" Da sauri ta share hawayen nata "Kukan murna ne mubeena kukan murna nakeyi,,Dama na dade ina jiran irin wannan rannar Sai yau Allah ya nuna min,, ina ma zanga........Da sauri ta canza zancen nata ,,muna alfahari dake Allah ya k'ara buda miki kwakwakarki,,Dake da sauran yan uwanki!" Su Husna dake tsaye suka ce Ameen..... Ya abdul ya fito daga dakinshi,Ya tsaya turus Yana kalonsu "Meya faru ne? Ummi da sauri tace "Abin arzik'i ne ya faru,,k'anwarka ce taci Gasar karatun Alkur'ani me girma " Yace "Masha Allah wacce a ciki?" Ummi tayi murmushi "yo waka sani banda mubeena,Kasan wadanan sakarkarun(Ta nuna su husna) Ba abinda suke tsinanawa" ya tabe baki "Okay" ummi tace Sai kayi mata murna ai,Ya juyo ya kalleta ya k'irk'iro murmushi yace "Congrats" yana rufe bakinsa da sauri ya koma dakinsa,,Ya ameen har a zuciyarsa beji dadi ba dan haka ya yanke hukuncin yaje ya sameshi ya mai magana,,Ya bishi dakinsu yayin dasu ummi suka shiga ciki (Abinda yasa suka san itace ta lashe gasar shine, Ya ameen ne ya kirasu ya sanar dasu,,jim kadan bayan an gama fadan sakamakon) Ya murda kofar ya shiga a zaune ya ganshi yana kallon system dinshi dake kan Bedside drower,,Ya shigo da salama sannan ya zauna a kusa dashi, Yace "Ahki(My brother dayake haka yake cemai) Gaskiya abinda kayi yau baka kyauta ba"" Ba tare da ya kalleshi ba yace "Me nayi" Ya ameen yayi murmushi,, "okay bakasan me kayi bama? Ya kallesa "Yes eh,Bansani ba" Ya ameen yace "To abinda kayi yanzu a harabar Gida nasan nasan cewa umma bataji dadi,Dan Allah ka dena yiwa yarinyar nan haka kodan nakasar ta ai ka sota,,Kamar k'anwarka fa take,,Dan Allah ki dinga janta a jiki ka dena hantararta dan Allah na rok'e ka" Ya abdul ya nisa sannan yace "To bakomai,Amma ni i dont knw why(Bansan meyasa ba) kwatakwata bata burgeni,Inaga jinin mu ne be hadu ba!! Kuma dama kasan halina ai,,ni ban cika san shigewa mutane ba and kar ka dauka wai ko dan ba blood sister dinmu bace,No ko su husna ma kasan ba wani sakar musu fuska nake ba Ya ameen yace "To shikenan amma ya kamata ka rage wannan halayar,Wani in ya fahimce ka wani baze bayi ba,Dats why(shiyasa) mutane ke maka Kallon me girman kai " ya abdul yace "Wannan ya rage nasu ni ban damu cuz nasan ba halina bane" lets keep this aside (mu aje wannan gefe) Wai ni ina maganar FATY ne naga yanzu baka maganarta,, Ya ameen ya bata fuska "kai ni daina min maganarta mu b'ata" ya abdul ya kalleshi da mamaki "Why meyasa" ya ameen ya nisa sannan yace "Waifa daga taga pics dinmu da Mubeena shikenan ta dau zafi, Wai budurwa tace,,inata k'ok'arin na mata bayani amma tak'i yanzu bata daga wayana ma" ya abdul yace "Tayiwa kanta,Amma i bet you dakanta zata dawo tace ku shirya" Ya ameen yace "oho mata" Ya kalli ya abdul "Kai dama wayo kake min ko da wasa baka min maganar budurwarka" ya abdul yayi dariya"Wayaga me budurwa,, Hhh ni banda budurwa ai" ya ameen yace "Ban yadda ba,Duk yan mata dake binka kace bakada budurwa wannan shayi ne kake mun" Ya abdul ya k'ara dariya sannan yace ................ Kuyi hak'uri kunji ni kwana2 biyu shiru Like · 1 · Reply · E [12:27AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [75]-[80] Yayi dariya sannan yace "Kasan Allah? Ni har yanzu ban ga wadda tayi min bane,Ni kaga ba kula mata ma nake ba,In banda yan-uwa sai kuma classmates," ya ameen yace "Kuji shi kamar gaske" ya abdul yace "Wallahi da gaske,," ya ameen yace " To shikenan Allah ya zaba mana mafi alheri, nidai kaga a shekarar insha Allahu zan yi aure na barka (yayi masa gwalo)" Ya abdul yayi dariya,,wayar sa ce tayi ruri da sauri ya dauka" Yace salamu alaykum" dayan bangaren akace "wslm abdul ka fito ina kofar gida" ya kashe wayar ya kalli ya Ameen "Hafeez ne frnd dina bari naje ltr zamuyi magana" Ya ameen yana k'ok'arin tashi yace "okay nima bari na tafi". Kai tsaye falon umma ya nufa inda ya tarada Nana(Aysha) Na chatn a waya,Husna na kitchen,Aishatul mubeena Na zaune Tana koyawa amir assignment,, Ya shigo yana murmushi hade da kallan Mubeena' Hafizar mu" tayi dariya "Kai bros" yace "Ko nayi k'arya?" Da sauri Nana tace "a'ah bakayi k'arya ba ya ameen, gaskiya ce" Yanzu kaga yan islamiyar mu sai cemin suke nace suna taya ta murna da fatan alheri, hadda masu sa pic dinta lokacin suna musabaqar a display Picture(Dp)kaga(Ta mik'a mai wayarta) ya karba "Masha Allah,Ai yau kwanan farin ciki za'ayi a gidan nan" Nana tace "Aikwa dai" Ya zauna akan kujera yana dana waya, Nana ta kalleshi "yauwa na tuna,Ya ameen kasan wata faty? " da mamaki yace "Yes nasanta" Nana tace " A layin nan take?" Da sauri yace "A'ah a unguwar nan dai suma suke,,me ya faru wai?" Tace "Amma ni bansanta ba,Wani ta aiko da sak'o dazu wai abaka,Am sorry mantawa nayi,, da sauri yace "sak'on me? Fada min" tace "bari na dauko maka" yace "yauwa" ala-ala yake ta kawo masa yaga ko mene ne Bata dade ba kuwa sai gata da yar k'aramar jaka a hannunta ta mik'a masa, cike da zumud'i ya karba yana washe baki, ,Mubeena kuwa bata ce musu komai ba shiru tayi kamar ma bata san abinda suke ba ,, Yana karba ya fice abinshi ya nufi dakinshi. Kan gadonshi ya baje da sauri ya dauko jakar yana bud'ewa wani kati ya gani ya sha kwalliya cikin hanzari ya bude ya fara karantawa kamar haka "" Remember the good times we had spent together,And the beautiful future we had dream of,,Darling i never wanted to create a distance between us...please let us bridges the gaps,,. Wani tsale murna yayi ya rungume kati a fili yace "Bakomai my faty na hak'ura!" Wayarsa ya dauko yayi dailing number ta,akace a kashe take,,Yayi tagumi yana sake kalan katin shi abin mamaki yake basa ma ashe dai abdul da gaske yake da yace da kanta zata dawo su shirya!,, Wayarsa yagani tana ruri da sauri ya dauka,, Ashe faty ce cike da murna Yake tambayarta ta canza number ne tace masa eh,, bayan sun gaisa tace "Kayi hak'uri ya ameen rashin fahimta ne ya kawo hakan, amma yanzu na gane komai,ina neman yafiyarka" yayi murmushi "Bakomai faty darling Allah ya barmu tare sweetheart" tace ameen dear suka cigaba da hirarsu ta soyayya. Aishatul mubeena bayan ta gama yiwa Amir assignment din ya tafi wajen su umma,,ta juyo ta kalli nana, "Ya nana wacce FATY wai" Nana tayi murmushi "inaga fa budurwasa ce !Dan dama rannar na labe naji suna hirarta shi da ya abdul ""Mubeena bata san dalili ba sai kawai taji gabanta ya fadi a sanyaye tace "Amma nikuwa bai taba fada min ba" Nana ta harareta da wasa "Ko ni dana girme ki be fada min ba saike yarinya" mubeena tayi murmushi "To yaya baba" nana tace "Kinsan mu akwai san girma" Mubeena tayi dariya ...Ta tashi ta shiga cikin daki ta zauna jikin gado tayi tagumi Tana tunane-tunane kala-kala a zuciyarta.. Umma ce ta shigo dakin,,kusa da ita ta zauna a hankali ta dube ta tace "me yafaru naga kin yi shiru kina tunani? Meke damunki?" Mubeena da sauri tace " bakomai ummana kaina ne ke ciwo kawai" umma tace "toh kuma ai se ki sha panadol,bari na dauko miki magani kisha" Ta tashi ta dauko mata,, ta k'arba da kyar ta sha maganin duk jinta take wani iri,, Ta d'an yi jim,Can ta tuno wani abu da sauri ta kalli umma tace "umma dan Allah wata tambaya zan miki amma dan Allah umma kimin alkwarin zaki bani cikakiyar amsar"" umma ta danyi jim sannan tace "inajinki indai inada amsar insha Allahu zan baki ita" Mubeena tayi murmushi "yauwa ummana" sannan tace.. "Umma DAN ALLAH WAYE MAHAIFINA? Gaban umma ya fadi sosaii cikin dauriya tace "Wai ke mubeena me ke damunki ne? Sau nawa kike tambayata nace miki Abba ne babanki,Abba shine babanki kar ki sake yi min wannan tambayar tunda kinsan amsar"" mubeena ta runtse idonta se hawaye,cikin murya kuka tace "Umma Abba bashine mahaifina ba, Na dade da sanin haka," Ummi cikin muryar masifa tace "to sai ki fada min waye Mahaifin naki,tunda ni baki yadda dani ba Mubeena ta fashe da kuka "Umma ba haka bane,Umma Dan Allah ki fada min,Kar kisa na fara tunanin ko ni yar shege ce,,Ba ta hanyar Aure aka haife ni ba!! Umma da sauri ta juyo idanunta fal da hawaye tace "Auzubillahi" "ke ba yar shege bace! Ke yar halak ce! Idan bakyason bacin raina to ko da wasa kar na kuma jin maganar nan,,tana gama fadan hakan ta fice daga dakin tana share hawayenta! Comment as: Subscribe to: Post Comments (Atom) Saturday, 15 October 2016 Posted by MissHafcy at 08:00 AISHATUL MUBEENA 85-105 [12:29AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©NA MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [80]-[85] Mubeena kuwa kukan ta ta cigaba dayi daga baya barci b'arawo ya sace ta. Da asuba ta tashi tayi sallolinta da kuma nafila,,Tana zauna tana karatun Alkur'ani har gari ya washe.. Bayan ta idar da karatun ta tashi ta nufi dakin Umma,,zaune ta tadda ita akan sallaya Tana addu'a,A bakin gado ta zauna tana jiran Umman ta kamalla addu'oin ta,, bayan Umma ta idar ta juyo ta kalli mMubeena,da sauri Mubeena ta k'ara duk'awa k'asa ta gaishe ta cikin sanyin murya "Umma ina kwana,kin tashi lafiya?" Umma tayi murmushi "Lafiya lau Mubeena" Mubeena tace "Umma dama ina neman yafiyarki naga jiya kamar na b'ata miki rai,insha Allahu baza ki sake jin maganar daga bakina ba" Umma tace "Ban yi fushi ba Mubeena,bakomai komai ya wuce" Mubeena ta washe baki "yauwa Ummana nagode sosaii" Umma tace "muje muyi karin kumalo(breakfast)" Mubeena tace "Toh" Bayan sun gama cin abincin,suna zaune ya Ameen ya shigo sanye da kayansa na pilot ya rik'e hular a hannunsa sai murmushi yake yi, Har k'asa ya duk'a ya gaida umma ta amsa da fara'arta,Mubeena ma ta gaishe shi ya amsa. Bayan sun gama gaisawa ya kalli Mubeena"Sis ni kinga yau zan koma aiki" ta canza fuska "Da gaske bro? ai nazata sai next week" yayi dariya "Yauwa dan Allah inaso ki maida hankali akan gasar zanen nan da za kuyi kinsan Ran monday zaku fara,Ku goma(10 )Aka zaba kuma a cikinku ne za'a zab'i ta d'aya( 1) Please inaso ya zamana kece ta dayar nan! Zaki iya, ga wannan(ya mik'a mata leda) duk wani items da zaki buk'ata a harkar zane yana ciki inaso ki fara practice tun yau,,Please ki dage " tayi murmushi "Toh bros nagode sosaii insha Allahu zan fara daga yau mu dage addu'a,insha Allahu bazan baka kunya ba." Yayi murmushi "Dats my sis,ki kuma sa a ranki zaki iya,indai kin yadda da hakan to baza ki samu matsala ba insha Allahu". Sai a lokacin umma tace "Gaskiyane Allah ya bada sa'a" Dukansu suka ce "Amin." Gabad'aynsu hadda Abba suka rako shi harabar gida,Mubeena kuwa daurewa kawai tayi dan ji take kamar tayi kuka idanunta sun yi rau-rau alamar me shirin yin kuka, shikuwa sai k'ara jadada mata yake akan ta dage sosai, itakuwa tana cemasa "insha Allahu zata dage sosai" su Abba suka mai fatan alheri suka kuma mai addu'ar Allah ya kiyaye hanya,sannan suka shige ciki,suka barshi daga shi sai Mubeena datake jikin motar tayi jim ta kasa magana ,daga baya ta kalleshi tace "Yanzu bros sai yaushe? " yace "Gaskiya for now bansani ba" tace "Okay Allah ya taimaka ya tsare ka Ameen,A dawo lafiya" yace "Amin sis nagode" har ta tafi sai ta dawo da sauri ta kalleshi "Ka gaida FATY in kunyi waya" bata ko jira amsar shi ba ta shige ciki, shikuwa mamaki yayi ,ko taya tasan faty budurwasa ce ? oho. Mota taja suka tafi.. Yau monday da sassafe suka shirya itada Amir suka tafi skul,Dayake dama can Husna da ya Nana sun fita aji a makaranta,su sunyi candy last year kuma Abba yace sam be yadda su fara unibasiti ba sai sunyi aure,Da kyar da taimakon su umma ma ya barsu suka fara zuwa Computer school. Tana zaune a kan bencin ta ita da k'awarta Asiya suna hira,dayake lokacin break ne,inda Mubeena ke bata labarin gasar zanen da za'ayi,, Uncle hashim ya shigo nan take ajin yayi tsit,suka tashi suka gaishe shi ya amsa sannan yace duk wanda ya kira sunansu su same su a Principals office, Ya fara kiran sunan kamar haka: "Nafisa Jameel, Auwal Isah, AISHATUL MUBEENA MUHAMMAD AMEEN,, Sai ku biyoni,"Yana gama fadan haka ya fita,yayin da yan ajin kowa ya shiga fadan albarkacin bakinsa,daga masu cewa laifi sukayi sai masu cewa suspension za'a basu, duk dai, Ita kuwa Mubeena sam bata damu ba dan tasan dalilin kiran,Suka jera ita da Nafisa sai yatsine take ita tana tak'ama an zo har aji an kira suna hada suna ta. A office suka tadda malamai da sauran Dalibai guda bakwai(7) suna jiransu,bayan sun gaida sauran malaman uncle hashim ya fara magana cikin harshen turanci kamar haka: "Mun tara kune anan ba dan komai ba dan wata gagarumar gasa da gwamnatin taraya ta shirya akan ZANE-ZANE,wato ART, ana neman kuma mutum d'aya mace ko namiji wanda ze wakilci kano baki daya,dan haka mukayi registar wannan makaranta, da farko dai a cikinku ku goma nan damuka zab'a, gobe zamu fara gasar mu a iya makarantar mu kuma duk wanda ya cinye shine ze wakilci makarantar mu a gasar da za'a yi da sauran makarantu guda biyar(5) da gwamnati ta tantance, idan Allah yasa wakilin makarantar mu ya samu ya lashe gasar to shine ze wakilci kano baki d'aya a gasar da za'ayi da sauran state (jihohi) dake k'asar nan tamu Nigeria,,da fatan kun gane?. Gaba ki d'aya suka ce "mun gane". Principal ya kuma musu wani k'arin bayani tare da yi musu fatan alheri daga baya aka salame su kowa ya koma ajinsu Nafisa sai wani iyayi take a zuciyarta kuwa cewa take aiy tasan ita zata lashe gasar. Suna shiga aji yan class suka fara tambayarsu abinda ya faru Nafisa ta k'arfi ta fada musu ,aikuwa suka d'au ihu "Se kinyi wallahi!!,se kin cinye nafisa!, ita kuwa sai busa hanci take yi, cikin murya isa ta fara magana" hmm ai ni dama sun ban mamaki,ai da basu b'ata lokacinsu ba wajen cewa sai anyi gasa sun zab'i gwani,suna b'ata lokacinsu ne amma kowa yasan nice zan cinye,ko ya kuka ce friends?" Suka kuma ihu "hakane Artist nafeesa, sai kinje abuja kin karbo mana award dinan! Share [12:30AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:53AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [95]-[100] Uncle Hashim murmushi yayi yace "To kunyi gueesin right" Nafisa kuwa iya kulawa ta kulu batasan sanda taji hawaye ba,dataga abin ya fara isarta sai ta fara zage-zage "wallahi bazan yadda ba! Wannan ma aiy sankai ne, aikin banza kawai,kuma...bata k'arasa maganar ba taji saukar mari a fuskarta ji kake tas! Kallo ya dawo kan Nafisa dake rik'e da kuncinta tana hawaye, sai a lokacin suka gane ashe anty sa'adah (english teacher dinsu) ce ta wanka mata mari,,wasu suka hau yi mta dariya yayin dana kusa da ita sukai tsit dan suna tsoranta. Anty sa'a taci gaba "ke waye sa'anki a cikinmu saboda tsabar rashin kunya mu sa'aninki ne?" Uncle Hashim ya k'araso wajen "bari ni da ita zanyi maganinta" ya kalli Nafisa dake ta sheshekar kuka yace "shige muje" ba shiri ta bishi Zuwa staff room...Dama lokacin tashi yayi dan haka aka sallami dalibai. Mubeena ce zaune ita da Asiya a bus stop din skul din, Mubeena da Amir na jiran drivernsu yayin da Asiya ke jiran skul bus din unguwarsu Asiya ta kalli Mubeena "gaskiya Mubeena kin burgeni, ni dama nasan ke zaki cinye,dama nice ke!" Mubeena tayi dariya "hmm Asiya kenan kema fa kinada taki baiwar fa" Asiya tace "tame fa?" Mubeena ta cigaba" na rubuta labarai mana novels ni kome zaki min bazan iya rubuta k'agaggen labari ba wallahi,ke kuwa fa kina iya k'irkira ki rubatasu kala-kala" Asiya tayi dariya "kema dai Mubeena nan abinda ni kadai nake rawa ta nake kida na, in na rubuta da sisters dina kawai nake bawa su karanta sai kuma ke" Mubeena tayu murmushi "duk da haka' Asiya tace "kodayake inmunyi candy inason na fara publishing din wanda wasu danake rubutawa wasu kuma na fara typing dinsu a whatsapp ko facebook wato online writeups" Mubeena tayi murmushi," lallai ashe kema kin kusa zama su' Benaxir,Lubbatu,Chuchu,Ybk,Jabo,Faty axland,etc danaji su Ya Nana na fadan su suna rubuta online hausa novels ,,kinsan su Ya Nana sun dage da karatun hausa novels,kullum zaki gansu mak'ale da waya suna karatun littafi" Asiya tayi dariya "lah ashe kema haka,wallahi nima sisters dina haka kullum cikin karatu a whatsapp har group garesu kala-kala na hausa novels" Mubeena tace "aiy suna k'ok'ari". Drivern su yazo suka wuce gida. Suna shiga gida Amir da gudu yayi falo yana kiransu umma,suka firfito a tsorace dan a zantonsu wani abun ne ya faru marar dadi...Yayi wani tsalle ya kalli umma "Yaya Mubeena ce tazo ta d'aya(ya nuna yatsan sa guda d'aya) Ummi ta wangale baki "Ai daman nasan a rina! ina 'yar tawa take? Mubeena ta k'araso tana murmushi "gani Ummina!" Ummi ta rungumeta tana murna "Allah ya sanya Alheri" Mubeena ta amsa, Ameen ummina! Amma kinsan meye? Ummi ta girgiza kai" next week zamu kuma yin wata gasar da Nafisa Jameel wanna wadda nake baku labarinta" Ummi tace "ai insha Allahu zaki samu nasar 'yata zamu dage da addu'a" Umma tace "kar kisa tsoro a ranki insha Allahu sai kin cinye gasar nan" Mubeena tace "Ameen my mother's" Umma ta cigaba "bari na kira Ameen na sanar dashi wannan abun arzik'in" ta shiga d'aki dan dauko wayarta. Murna wajen ya Ameen ba'a magana sun dad'e suna waya yana bata kwarin gwiwa akan ta dage zatayi nasara insha Allahu ta kuma dage da addu'ar daga k'arshe sukai sallama ta mik'awa Umma wayarta. Mubeena ce zaune akan carpet din falon Umma abinci ne a gabanta amma ta kasa ci tayi tagumi da alama akwai abunda take tunani, Umma ta k'araso wajen ta tace "Mubeena me ke damunki? Kinsa abinci a gaba tun dazu kink'i ci? Mubeena ta d'ago idonta sharkaf da hawaye tace "Umma wallahi wani labari aka ban yau in na tuno duk sai naji ba dadi" Umma ta kara matsowa kusa da ita "na mene?" Mubeena ta share hawayen nata sannan taba umma labarin da Asiya ta bata na yarinyar nan me cutar polio data ja mata paralysed,, Umma itama sai ta fashe da kuka ta tuno irin gwagwamayar data sha itama lokacin da Mubeena na k'arama,, Mubeena ta katse mata tunanin da cewa "Umma wannan dubu hamsin d'in dana samu a wajen musabak'ar nan nakeso kiban muje dake muyi mata siyayya kayan abinci da kayan sawa da kuma daiper size dinta,Atamfar nan kuma abani guda biyu na kaiwa mamanta d'aya sannan kuma aba Safi tella ta dinkawa yarnyar, mu kai gidansu" Umma tayi murmushi "Kaji d'iya ta kwarai Mubeena ke daban ce! Kinada zuciya me kyau Mubeena a kullum godewa Allah nake daya bani 'ya kamar ki, Mubeena Allah ya shi miki albarka ya kuma albarkaci rayuwarki," Mubeena ta ce "Amin Ummana nima ina alfahari dake, Allah ya saka miki da alheri ya biya miki duk bukatan ki duniya da lahira" Umma tace "Amin nagode AISHATUL MUBEENA" amma sai ki bari Abbanku ya dawo sai a sanar dashi koh? Mubeena tace "gaskiya kam Allah ya dawo dashi lafiya" [11:55AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [90]-[95] Mubeena tayi shiru can sai hawaye suka fara zirarowa,Asiya a rude ta fara share mata hawayen "yi hak'uri Aisha wallahi ba dan na saki kuka nayi wannan tambayar ba kawai dai..." Mubeena ta katse ta "bake kika sani kuka ba Asiya... bari na fad'a miki" Asiya tace "toh inaji" Mubeena ta cigaba"cutar poliomyelitis (polio) ce ta maida ni haka! Asiya ta zaro ido "polio??,da kina k'arama ba'a miki rigakafi ba? Mubeena ta share hawayenta "eh,nidai kawai watarana na wayi gari naga kafana ta dawo haka,ba zan iya tuna abinda suka faru da ba,kuma banasan na tambayi Umma tunda naga itama basan zancen take ba" Asiya cikin sanyin murya tace "Allah sarki,Allah ya kiyaye gaba,ya kuma sauwak'e. Mubeena tace "Amin". Asiya ta girgiza kai cike da takaici tace "akwai wata yarinya a unguwar su cousins d'inmu itama polio ne, itafa ya ja mata paralysed,ga iyayenta talakawa ne,ko wheel chair ba tada, a k'asa zakiga sun shanya ta,tayi fitsari etc duk anan sai dai su gyra,yarinyar 12years amma ta k'ank'ance sai ki rantse bata fi 4-5years ba abun tausayi,rannar danaje gidan dubu d'aya(1000) ne a hannuna wallahi duka na basu naji tausayinsu ita da iyayenta,har takai ta kawo daga karshe maman bara takeyi saboda sukansu wani sa'in abincin da zasu ci gagararsu yakeyi,sun ban tausayi sosaii" ta k'arasa maganar tana kuka... Mubeena itama sai ta fashe da kukan, zancen ya matuk'ar bata tausayi,, ta dage tace "Allah sarki,shi yasa nake godewa Allah kullum dakuma iyayena,amma zaki gane gidan? Asiya tace "eh zangane kusa da gidan su cousins d'inmu ne" Mubeena tace "insha Allahu gobe zan zo ki rakani" Asiya tace "to bakomai Allah ubangiji ya kaimu" Mubeena tace "Amin." Akazo aka kirasu,Nafisa sai wani iyayi akeyi,bayan an musu bayanin komai aka raraba musu kayan da zasuyi zanen akace kowa ya zana abu mai kyau amma banda abu me rai,an basu minti talatin(30mint) nan da nan suka fara. Mubeena kuwa exactly abunda ta zana jiya (har ya Abdul yace yayi kyau daga k'arshe yace yanso tace ya dauka),ta zana ,tunda taji yace yayi kyau to tasan kuwa tabbas yayi din da gaske,, dan haka ta k'ara zana irinshi har yafi na jiya ma kyau... Lokaci ya cika,uncle Hashim ne ya k'arbi zanen aka bawa masana zanen da hukumar makarantar ta gayyato takanas don su duba su kuma fad'i sakamakon tun daga zanen daya zo na d'aya har zuwa na k'arshe....Bayan sun dade suna duba suka fadawa hukumar makarantar result din sannan suka tafi.. Uncle Hashim ne yazo yace musu su koma aji za'a had'a assambili na mussaman wanda anan ne za'a fad'i sakamakon. Nafisa tana shiga aji yan aji suka hau tafi suna mata kirari ita kuma sai busa hanci takeyi can tace "Sai ku shirya anjima za'ayi assambili anan ne zaku tabbatar dacewa nice na lashe gasar" Asiya ta tab'e baki "ba giringirin ba dai tai mai!" Nafisa tsaki tayi ta juya ta mata wani kallon raini sannan tace "ni bansan shishigi a rayuwata ita gurguwar da kike shigewa ai itama a bayana take wallahi,dukanku nan sai da ku zama 'yan amshin shata dan nice gaba da ku akomai" Mubeena murmushin takaici tayi ta sunkuyar da kanta. Asiya a fusace ta tashi "keee!! Ba'a aibata halitar Allah,ke in banda jahila/jahili ma wa yake yabon kansa? ,kuma da kike cewa gurguwa ai Allah ne ya haliceta haka,, a haka yaso ya ganta,kuma kema baki fi k'arfin Allah ya maida ke haka ba,wai ke da me kike tak'ama ne? eh? Nafisa a fusace tace "kut! Ke har kin isa ki zage ni,"tayi wani kukan kura zata wankawa Asiya mari,da sauri Asiya ta rik'e hannunta cak! Tace "karki kuskura ki taba min fuska,niba karya bace irinki bana dambe,"tana gama fadan haka ta zauna tabar Nafisa nata kumfar baki,,daidai nan teachern su ya shigo ,yana shigowa a fusace ya kalli Nafisa "get out!!" Simi simi tabar ajin tana gunguni. Malami suka dinga shiga aji-aji suna cewa dalibai sufito za'ayi asambili na musaman ba'a dad'e dalibai suka cika wajen assembly din Nafisa kuwa sai wani tak'ama takeyi. Uncle Hashim dayake shine me kula da harkar gasar ya fito ya fara jawabi kamar haka "Gud afternoon students,,abinda yasa muka tara ku nan ba dan komai ba dam mu fad'a muku sakamakon gasar zanen iya makarantarmu da muka gabatar yau,, a cikin mutane goma da suka yi participating a gasar mutum biyu zamu dauka wa'enda su kuma zasu yi tasu gasar next week,a cikinsu kuma mu dau wadda tazo ta d'aya dan ta wakilci makarantarmu,, wanda yazo ta goma(10) shine: Auwal Isah na tara(9 ) Jamila Muhd na 8 Iro Faisal................,,.wadda tazo ta biyu....Nafisa Jameel sai kuma zakaran wato wanda/wadda ta lashe gasar ......(ya k'ara daga muryarsa) AISHATUL....kan kace meye dalibai suka d'au ihu suka k'arsawa masa "Mubeena Muhd Ameen. [12:32AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:53AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [100]-[105] Umma tace "Amin, wannan satin insha Allahu inason muje k'auye wajen mama bata ji dadi ba ashe sai jiya yaya Basiru yake fad'amin a waya" Mubeena tace "eyyah Allah sarki Mamana Allah ya bata lafiya" Umma tace "Amin" . Abba ya dawo suka fad'a masa niyyarsu ta ziyarta iyayen yarinyar Abba yaji dadi kwarai ya k'ara musu dubu ashirin (20) akai,, ya dau waya ya kira Ya Abdul "Abdul Hafeez kana ina ne?" Ya Abdul yace "ina dakina" Abba yace "toh ka shirya yanzu zaka kai su Ummanku unguwa kasan driver yayi bulaguro" Yace "toh gashi nan". Ba dad'e ba kuwa sai gashi bayan ya gaishesu gaba d'aya,Mubeena ma ta gaishe shi ya amsa ba yabo ba falasa...Su Ya Nana ma sukace zasu bisu aikuwa suka shirya abinsu, Mubeena kuwa hijab dinta ta d'auko ash colour har k'asa tasa abinta hoda kawai ta shafa sai farin man leb'e ..ta fito suka shiga mota, se da suka fara zuwa wani babban mall suka siyo su kayan abincine,kayan makulashe, kayan sawa, daiper etc sun kashe kud'i dayawa ... dama already Mubeena ta taho da wheel chair dinta da take amfani da ita kan ta fara tafiya don ta bawa yarinyar. Sai da suka fara zuwa gida su Asiya suka dauko ta dan ta rakasu gidan,basu dad'e ba kuwa sai gasu a gidan, k'aramin gida ne na k'asa wasu wuraren na gidan ma duk ya rushe kana ganin gida kasan na talakawa ne futuk.. Da sallama suka shiga gidan a lokacin, wata matashiyar mata ta amsa musu da fara'a,yayin data aje tsintsiyar datake shara da ita,, "Sannunku da zuwa" ta fad'a tana fara'a, Umma, Mubeena, Ya Nana, Husna da kuma Asiya, Ya Abdul da Amir suna cikin mota su basu fito ba. Matar ta shimfid'a musu tabarma suka zauzauna, ta tashi ta nufi randar ruwa ta d'ebo musu ruwa a kwanon sha ta aje a gabansu, Sannan ta zauna suka gaigaisa, matar tace "sai dai kuma ban gane kuba, waccan kawai na gane(ta nuna Asiya) ko yan gidansu ne?" Umma tayi murmushi sannan ta fad'a mata dalilin zuwansu, matar sai hawaye kawai tace "Nagode kwarai Allah ya biyaku dama in Allah ya kawo makashinka sai ya kawo me ceton ka" Umma tace "gskiya ne, ina yarinyar" Matar tace " YUSRA tana cikin d'aki ku shigo" suka shiga dakin. A kwance suka tadda ita sai kallonsu takeyi ta kalli Mamanta "Mama suwaye?" Maman tayi murnushi "bak'i ne suka zo duba ki" A tare su Mubeena suka had'a baki "ya jikinki?" Tace "da sauk'i" Mubeena ta kura mata ido sai hawaye sharr ta sunkuyar da kanta tana kuka a hankali... ita kuwa Umma godewa Allah tayi da banda taimakon Allah ba da tuni itama suna cikin wannan halin... Umma ta dage ta ce "Ina mahaifinta?" Maman tayi murmushi takaici "Aiy bama tare yanzu nan gidan iyayen mune da suka mutu suka bar mana nida k'anina anan muke zaune, tunda muka rabu da mahaifinta be kuma waiwayar mu ba" ta fashe da kuka,, Umma ta runtse ido sai hawaye, a zuciyarta tace "ashe akwai masu hali irin nan Mal Sule a duniya? Allah wadaran wannan mumuman hali tur dashi! Itama da tuni fa tana cikin wannan hali kai dole ta godewa Allah daya musan yamata da mafi alheri" Umma ta share hawayenta tace " nima kinga 'yata nan itama polio ne amma ita kafarta ce kawai" Maman tace "Allah sarki ita yazo mata da sauk'i ma". Nan da nan wasu maza suka fara shigowa da kayayyakin da su Mubeena suka siyo,, Maman tsayawa tayi tana kallon ikon Allah ta kasa magana ma saboda tsabar murna,, Umma ce ta katse dacewa "gashi wannan kyautace daga AISHATUL MUBEENA ga wannan daiper sai ku dinga saka mata kinga kin huta da wanki kashi da fitsari sai dai kawai ki cire a tsaftace, ga kayan makulashe nan ana bata, ga Wheel chair nan shima a dinga dora ta ana zagayawa da ita itama ta zaga gari,, duk dai gasu duk naku ne malakinku ne ga wannan(ta mik'a mata dubu ashirin(20) da Abba ya bada) sak'o ne daga Abbansu kwayi wani abun dasu, Allah ya k'ara sauk'i" . Maman ta fashe da kukan murna "duk mukadai? Allahu akbar ashe akwai mutane irinku AISHATUL MUBEENA mun gode kwarai Allah ya biyaki ya daukaki bansan dame zan gode muku ba, bansan da wata kalma zanyi amfani na gode muku da ita ba, Allah ya biyaku, ya kare ku ya biya muku buk'atunku duniya da lahira, Mubeena da za'a sami mutane irinku da yan uwanku masu wannan masifafiyar cuta ta polio basu wahala ba,da basuyi bara akan titi ba, da kuma wasun su basu rasa ransu ba saboda wannan cuta,," ta k'ara fashewa da kuka. Mubeena ta k'araso wajenta ta rungume ta tana kuka "Maman ki dena kuka,a kullum raina yakan baci inda naga yan uwana masu irin wannan cuta suna wahala , inason in taimakawa yan uwa masu irin wannan cutar mussaman ma wa'enda basu da bud'i irinku,, kar ki gode min ki gode dan Allah" Maman tace "Allah sarki Allah me baiwa" Yusra dake kwance tace "mun gode Anty Mubeena". *** ina gayyatar ku zuwa sabon group din dana bude yau a facebook, masu yin facebook sai kuyi searching "MISS HAFCY NOVELS" Nagode Like · 2 · [11:53AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [95]-[100] Uncle Hashim murmushi yayi yace "To kunyi gueesin right" Nafisa kuwa iya kulawa ta kulu batasan sanda taji hawaye ba,dataga abin ya fara isarta sai ta fara zage-zage "wallahi bazan yadda ba! Wannan ma aiy sankai ne, aikin banza kawai,kuma...bata k'arasa maganar ba taji saukar mari a fuskarta ji kake tas! Kallo ya dawo kan Nafisa dake rik'e da kuncinta tana hawaye, sai a lokacin suka gane ashe anty sa'adah (english teacher dinsu) ce ta wanka mata mari,,wasu suka hau yi mta dariya yayin dana kusa da ita sukai tsit dan suna tsoranta. Anty sa'a taci gaba "ke waye sa'anki a cikinmu saboda tsabar rashin kunya mu sa'aninki ne?" Uncle Hashim ya k'araso wajen "bari ni da ita zanyi maganinta" ya kalli Nafisa dake ta sheshekar kuka yace "shige muje" ba shiri ta bishi Zuwa staff room...Dama lokacin tashi yayi dan haka aka sallami dalibai. Mubeena ce zaune ita da Asiya a bus stop din skul din, Mubeena da Amir na jiran drivernsu yayin da Asiya ke jiran skul bus din unguwarsu Asiya ta kalli Mubeena "gaskiya Mubeena kin burgeni, ni dama nasan ke zaki cinye,dama nice ke!" Mubeena tayi dariya "hmm Asiya kenan kema fa kinada taki baiwar fa" Asiya tace "tame fa?" Mubeena ta cigaba" na rubuta labarai mana novels ni kome zaki min bazan iya rubuta k'agaggen labari ba wallahi,ke kuwa fa kina iya k'irkira ki rubatasu kala-kala" Asiya tayi dariya "kema dai Mubeena nan abinda ni kadai nake rawa ta nake kida na, in na rubuta da sisters dina kawai nake bawa su karanta sai kuma ke" Mubeena tayu murmushi "duk da haka' Asiya tace "kodayake inmunyi candy inason na fara publishing din wanda wasu danake rubutawa wasu kuma na fara typing dinsu a whatsapp ko facebook wato online writeups" Mubeena tayi murmushi," lallai ashe kema kin kusa zama su' Benaxir,Lubbatu,Chuchu,Ybk,Jabo,Faty axland,etc danaji su Ya Nana na fadan su suna rubuta online hausa novels ,,kinsan su Ya Nana sun dage da karatun hausa novels,kullum zaki gansu mak'ale da waya suna karatun littafi" Asiya tayi dariya "lah ashe kema haka,wallahi nima sisters dina haka kullum cikin karatu a whatsapp har group garesu kala-kala na hausa novels" Mubeena tace "aiy suna k'ok'ari". Drivern su yazo suka wuce gida. Suna shiga gida Amir da gudu yayi falo yana kiransu umma,suka firfito a tsorace dan a zantonsu wani abun ne ya faru marar dadi...Yayi wani tsalle ya kalli umma "Yaya Mubeena ce tazo ta d'aya(ya nuna yatsan sa guda d'aya) Ummi ta wangale baki "Ai daman nasan a rina! ina 'yar tawa take? Mubeena ta k'araso tana murmushi "gani Ummina!" Ummi ta rungumeta tana murna "Allah ya sanya Alheri" Mubeena ta amsa, Ameen ummina! Amma kinsan meye? Ummi ta girgiza kai" next week zamu kuma yin wata gasar da Nafisa Jameel wanna wadda nake baku labarinta" Ummi tace "ai insha Allahu zaki samu nasar 'yata zamu dage da addu'a" Umma tace "kar kisa tsoro a ranki insha Allahu sai kin cinye gasar nan" Mubeena tace "Ameen my mother's" Umma ta cigaba "bari na kira Ameen na sanar dashi wannan abun arzik'in" ta shiga d'aki dan dauko wayarta. Murna wajen ya Ameen ba'a magana sun dad'e suna waya yana bata kwarin gwiwa akan ta dage zatayi nasara insha Allahu ta kuma dage da addu'ar daga k'arshe sukai sallama ta mik'awa Umma wayarta. Mubeena ce zaune akan carpet din falon Umma abinci ne a gabanta amma ta kasa ci tayi tagumi da alama akwai abunda take tunani, Umma ta k'araso wajen ta tace "Mubeena me ke damunki? Kinsa abinci a gaba tun dazu kink'i ci? Mubeena ta d'ago idonta sharkaf da hawaye tace "Umma wallahi wani labari aka ban yau in na tuno duk sai naji ba dadi" Umma ta kara matsowa kusa da ita "na mene?" Mubeena ta share hawayen nata sannan taba umma labarin da Asiya ta bata na yarinyar nan me cutar polio data ja mata paralysed,, Umma itama sai ta fashe da kuka ta tuno irin gwagwamayar data sha itama lokacin da Mubeena na k'arama,, Mubeena ta katse mata tunanin da cewa "Umma wannan dubu hamsin d'in dana samu a wajen musabak'ar nan nakeso kiban muje dake muyi mata siyayya kayan abinci da kayan sawa da kuma daiper size dinta,Atamfar nan kuma abani guda biyu na kaiwa mamanta d'aya sannan kuma aba Safi tella ta dinkawa yarnyar, mu kai gidansu" Umma tayi murmushi "Kaji d'iya ta kwarai Mubeena ke daban ce! Kinada zuciya me kyau Mubeena a kullum godewa Allah nake daya bani 'ya kamar ki, Mubeena Allah ya shi miki albarka ya kuma albarkaci rayuwarki," Mubeena ta ce "Amin Ummana nima ina alfahari dake, Allah ya saka miki da alheri ya biya miki duk bukatan ki duniya da lahira" Umma tace "Amin nagode AISHATUL MUBEENA" amma sai ki bari Abbanku ya dawo sai a sanar dashi koh? Mubeena tace "gaskiya kam Allah ya dawo dashi lafiya" Comment as: Publish Preview No comments: Post a Comment MissHafcy View my complete profile About Me ► 2017 (16) ▼ 2016 (34) ► November (1) ▼ October (33) WELCOME ASMAUL HUSNA 6 ASMA'UL~HUSNA ASMAUL~HUSNA 4 ASMAUL~HUSNA 3 ASMAUL HUSNA 2 ASMAUL HUSNA AISHATUL MUBEENA 155-160 AISHATUL MUBEENA 145-155 AISHATUL MUBEENA 110-140 AISHATUL MUBEENA 85-105 AISHATUL MUBEENA 60-80 AISHATUL MUBEENA 45-60 AISHATUL MUBEENA 30-40 AISHATUL MUBEENA 20-30 AISHATUL MUBEENA 1-20 WANI HANIN END! WANI HANIN 26-27 WANI HANIN 24-25 WANI HANIN 22-23 WANI HANIN 20-21 WANI HANIN 19-20 WANI HANIN 15,16,17&18 WANIN HANIN 12,13,&14 WANI HANIN 11 WANI HANIN 9&10 WANI HANIN 7&8 WANI HANIN 5&6 WANI HANIN 3&4 WANI HANIN 2 WANI HANIN 1 .... WANI HANIN Blog Archive Miss_Hafcy. Watermark theme. Powered by Blogger . More AISHATUL MUBEENA 110-140 [12:33AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:51AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS A tak'aice dai ansa rannar Ya Ameen da Faty, da kuma Aisha( Ya Nana) da Saifulah nan da wata biyu(2) ,, Su Umma kuwa sai shirye shiryen biki sukeyi.. Ya Abdul kuwa har ya gama karatunshi Abba ya samar masa aiki har ya fara yi dan haka ma ba kullum yake zama a gida ba. Baiwar Allah Mubeena kuwa tacan duk ta damu dan ta dad'e da gane cewa tana son ya Abdul ! amma sai take ganin abun da kamar wuya, na farko dai Umma tace mata Abba ne babanta to indai har kuwa Abba ne babanta to ba aure a tsakaninsu saboda wanta ne uba d'aya kuma ba aure a tsakaninsu k'anwa da wa.!.na biyu kuwa, tasan halin ya Abdul shida ko magana bata shiga tsakaninsu sai ta k'ure,, in ba kwanan nan dayake d'an sakar mata fuska,,kuma tasan ma baze rasa budurwa wadda yake so ba,,,,yadda yake d'in nan tubarkalah gashi kuma d'an gayu,, doleh 'yan mata suyi rububinsa... dan haka sai ta dinga addu'ar Allah ya cire mata sanshi a zuciyarta,, a kullum kuma tana k'ok'arin cire sanshi daga zuciyarta,, dan a iya tunaninta ko da da aure a tsakanin su, in ba wani ikon Allan ba,to ko a mafarki baza ta tab'a zama matarsa ba,, Ita dai kullum addu'arta shine Allah ya bata miji na gari ya kuma zab'a mata mafi alheri Yau saura befi kwana biyar (5) suyi gasar ba,kuma dama sun gama exams an basu hutu, dan haka lokacin hutu za'ayi gasar.. Mubeena na zaune a falo tana kallan musab'akar alkur'ani da akasa a sunnah Tv,, Umma ta fito daga d'aki cikin shirin fita unguwa, Mubeena ta d'ago ta kalleta "Umma fita zaki yi ne?" Umma tace "eh k'auye zani wajen Mama" Mubeena da sauri ta tashi "Umma dan Allah nazo muje? Na dad'e banga Mama ba" Umma tace to maza shirya muje,kafin rigimaman nan yazo(Amir) dama neman dalilin k'in zuwa islamiya yake yi" Mubeena tayi dariya sannan ta shiga dakinsu ta dauko hijab dinta ta bi bayan umma ,, suka yiwa su Ummi sallama sannan suka nufi k'auye. Bayan sun isa Mama tayi murna sosaii da ganin su, bayan sun gaisa sun sha ruwa , Mubeena nakan cinyar Mama suna wasan su na jika da kaka, Mama ta kalli Umma," Ma'u kinsan IYA ta samu mutuwar b'arin jiki kuwa? Gaban Umma ya fad'i , "subhanalahi,wacca iyan??" ta fad'a had'e da dafe k'irji, Mama tace " Iya dai surikarki, wallahi abun tausayi kuje ki duba ta dan Allah kullum fad'i take a kirawo mata ke da yarki ta nemi gafarar ku . Umma tace "Allah sarki Iya, a ina take zaune? Mama tace "inda dai kika santa tana nan' Mubeena dake kwance akan cinyar Mama da sauri ta taso ta tsutsura musu ido ,, ta kalli Mama tace"Mama wacce ce Iya?" Mama na k'ok'arin magana Umma ta dakawa Mubeena tsawa "bansani ba,dake muke magana,ban hanaki sa min baki in ina magana ba?" Mubeena ta sunkuyar da kanta , yayin da Mama tace "ke Ma'u wai meyasa kike haka ne? Daga tambaya saiki hayayak'o mata?" Umma tace "Mama haushi taban ai manya na magana ta dinga sako baki, bari na tashi naje na dubo ta"" ta tashi ta dauki jakarta tana k'ok'arin saka takalminta, Mama ta kalleta," Ma'u indai nina haifeki to ki tafi da Mubeena" Umma ta juyo jiki ba kwari tace "to se ki taso muje" bata jira amsar Mubeena ba ta sakai ta fita, Mubeena da sauri tasa hijab dinta tabi bayanta. Har suka iso gidan Umma bata yiwa Mubeena magana ba, da sallama suka shiga gidan amma suka ji shiru,, sai da sukayi sallama yakai guda hudu(4) sannan suka jiyo wata dashashiyar murya nacewa "Wa..alai..kum..us..salam...,k u..shigo..mana,, Umma ta kad'a kai sannan ta shiga dakin data juyo murya, Mubeena tabi bayanta. Umma ta zaro ido saboda abinda ta gani ya masifar tsorata ta, duniya kenan! ... IYA ce kwance akan wata yagalaliyar tabarma duk tayi fitsari akai, dakin in banda zarni ba abinda yake yi. Umma a firgice ta k'arasa wajen Mubeena ta bi bayanta, Iya ta k'are musu kallo sannan tace "Wannan kamar Ma'u nake gani kodai mafarki nakeyi? Umma ta runtse idonta sai hawaye 'Nice Iya!" Iya ta fashe da kuka "kece Ma'u ! ashe rai kanga rai? Ina jikar tawa take?" Umma ta nuna Mubeena "gata nan, tare muke ma" Iya ta k'ara fashewa da kuka "zo nan 'yar jikalle ta, ni bansan ma da wani ido zan kalle ki ba, randa aka haife ki nida mahai....." Umma ta da sauri ta katse ta "Iya komai ya wuce dan Allah a bar zancen nan baki yimin komai ba ni kuma koda kin min ma na yafe miki, garin yaya kika sami wannan ciwon?". Iya tana kuka tace "rannar ina zaune ni kad'ai a daki naji mage a gefena, kinsan dama ina tsoron mage ,to tun daga nan na tsorata sosai bakina ya juye magana ma na kasa yi, hannuna ma na kasa d'agawa balle na d'aga kafata,, Haka na kwana ina kuka bame ceto na,, washe gari makota da suka ji shiru suka zo suka bud'e kofar aka fito dani aka kaini asibiti anan akace mutuwar b'arin jiki nasamu,,shine nake kwance anan masa'udu (dan k'anwar iya) shine kawai yake kula dani,,, ta sake fashewa da kuka,, Umma ta fashe da kuka hakama Mubeena dama ga Mubeena da tausayi. Iya ce ta katse musu kukan da cewa "Ma'u baki fad'a wa jikartawa ni kakar ta bace ba? Dan daga ganin alama bata san nice na....Umma ta katse ta " Iya dan Allah ya isa haka, zancen nan ya wuce banse tasan komai ba ai" Mubeena duk ta rikice ta kasa gane maganar tasu, sun caja mata kwakwalwa....Iya cikin dashashiyar murya tace "Ma'u RANNAR WANKA BA'A BOYEN CIBI! Like · 2 · Reply · Edit · 3 February Khadija Muhamed [11:52AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [105]-[110] Mubeena ta shafa fuskarta" bakomai yusra Allah ya baki lafiya" yusra ta rik'e hannunta "Amin",, sukai musu sallama suka juya suka bar Maman nata kukan murna k'aninta mu'az yazo shima murna kamar me, ya dinga shiwa su Mubeena albarka,,dama kudin reg din makaranta yake nema ya cika dubu biyar(5000)amma ta gagara sai gashi Allah ya share musu kukunsu. A mota ne Umma ke ba ya Abdul labarin yarinya jaji tausayinta sosaii shima ya kuma ji dad'i da'aka musu wannnan taimakon..Suka aje Asiya a gida suka mata godiya sannan suka koma gida. Kwanci tashi ,gobe ne Mubeena da Nafisa zasuyi gasar su, Mubeena tayi practice sosai, a rannar raba dare tayi tana addu"ar Allah ya bata sa'a su Umma ma haka duk 'yan gidan ma, Ya Abdul ma yazo yayi mata fatan alheri,dan yanzu ba laifi yana sakar mata fuska. Da sassafe ta tashi ta yi sallolinta sannan tayi zikirorinta ta shirya suka huce makaranta...bayan an fito break 'yan class sun zagaye Nafisa dake wa mickey mouse din data zana musu fenti wai zasu sa a wall bangon class din ,bayan ta gama ta d'aga zanen "ya kuka gani friends?" Suka hada baki "Woww..yayi kyau sosaii amma da Mubeena ce ta zana munsan se yafi haka kyau" Nafisa ta juyo a fusace "lallai ma, in sha wahala in muku abu amma kuce da wata banza ce tayi sai yafi kyau?" D'aya daga cikinsu tace "a'ah kinga kar ki sake ce mata banza " Nafisa tace "an fad'a mata d'in, bari ku gani" nan da nana ta warce zanen ta yayaga shi, sannan ta fita daga ajin tana zage-zage,sukuwa dariya sukayi sukace "kanki kika cuta ai,wahalaliya kawai. Mubeena ce da Nafisa zaune suna jiran akawo musu abubuwan zanen, Uncle Hashim ya shigo ya raraba musu sannan yace mutum d'aya ta biyo shi saboda za'a raba musu aji gudun kar wani ya kwafi na wani, caraf Nafisa tace zata bishi ,hakan kuwa akaiyi yabar Mubeena da anty Sa'a sannan shi kuma suka tafi wani staff room d'in shi da Nafisa. Cikin minti talatin suka kamala zanen kowa yayi submitn,, suka koma aji ... aka bawa wanda suka duba zanen kwanaki dan su duba wannan d'in shima. Suna zaune a aji suna class work din maths Uncle Hashim yazo ya kira Mubeena anan ya tabbatar mata da cewa itace ta lashe gasar!! Wohoho murna wajen Mubeena kamar me ta rasa ma me zatai dan murna. Assamibili aka k'ara hadawa anan aka kirawo Mubeena gaban assambili aka sanar da sauran dalibai itace ta cinye gasar kuma ita zata wakilci makarantarsu a gasar da za'ayi nan da sati biyu2 dalibai aka d'au ihu ana Up Up Up Mubeena!! Mubeena kuwa sai murmushi take tana godewa Allah daya bata nasara... Nafisa dajin haka ihu ta saki ,tana wani fizge fizge daga k'arshe ta tada aljanun k'arya malamin islamic studies yasa prefect mata suka d'auke ta zuwa staff room dan yayi mata ruk'iya nan kuwa be san na k'arya ne ba. Mubeena kuwa se murna ake mata malamai kuwa sai wani nan-nan suke da ita kodayake dama can malamai suna santa saboda kwazonta...Nafisa kuwa da Ustaz(malamin islamic) ya gane cewa na k'arya ne,dorina ya dauko zabgegiya ya shiga lafta mata, bashiri ta tashi tana kuka sharaf sharaf tana bashi hak'uri,dariya yayi sanan yace ta koma aji, aka dinga mata ihu ana cewa me aljanun k'arya a rannar tayi alkwarin baza ta sake dawowa makarantar ba, dan abin kunya data aikita baza su barta ta zauna a makarnatar lafiya ba. Yau Ya Ameen ya ze dawo murna a wajen 'yan gidan kamar me,kowa ka gani yana cikin walwala hatta Ya Abdul... Mubeena kuwa cewa tayi a bar mata zata mai girki me dadi, dayake yanason abincin gargajiya fankaso da tuwo ta yi masa da miyar taushe dan ya fad'a mata a waya ya dad'e be cisu ba,, su ya Nana kuma suka yi masa kunun aya da zob'o. Bayan yayi parking din motar shi ya shigo gida Amir da gudu yazo ya rungume shi yana masa oyoyo , su Mubeena suka fifito suna masa sannu da zuwa shikuwa yana amsawa fuska d'auke da murmushi..ya k'araso cikin gida Umma da Ummi kuma na falo suna jiranshi suka yi masa sannu da zuwa sa kuma ya hanya. Ya amsa da "lafiya lau nagode,,kuma nayi missing dinku sooooooo much" a tare suka ce "muma munyi missing dinka". Bayan yayi wanka yayi sallah ya dawo ya zauna Mubeena tace abincinsa na kan dinning table( teburin cin abinci) yaje ya zauna yana budewa ya fara "wow nasan wannan aikin kine Mubeena", Ummi tace 'ai kuwa kamar kasani,kayan shan ne su Nana sukayi yimaka" yayi murmushi "amma kuwa nagode lovely sisters" Bayan ya gama cin abincin su Ummi ke sanar dashi Mubeena ce zata wakilci skul dinsu ba k'aramin murna yayi ba,a rannar ta faranta masa rai. Washe gari ya sami Umma yake fad'a mata cewa iyayen Faty sun takura masa daya turo dan nan da wata hudu (4) za'ayi bikin yarta kuma sunaso a had'a da na Faty...shikuma yana kunyar fad'awa Ummi da Abba,, Umma tayi murna dajin haka, ta kuma yimasa alkwarin zata fad'awa Abban sannan kuma indai ya shirya to ba matsala. yayi mata godiya ya tafi. Umma ta sami Abba ta fada masa yaji dadin haka dama yana shirin yi masa maganar auren dan a ganinsa lokaci yayi daya kamata ya zama cikaken mutum wato yayi aure...yace ta fad'awa ya Ameen d'in ya kwantar da hankalinsa zasuje shida yan- uwansa su nema masa auren insha Allahu.. [12:34AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:48AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [125]-[130] Wakilin shugabanin da suka shirya gasa wanda yazo daga birnin taraya Abuja wato MR MIKE da shugaban k'ungiyar masu zanen dake kano ALHAJI AL- AMIN BAWA sune suka fito dan fad'an result din bayan manyan-manyan kwararru a harkar zane sun duba sun fitar da sakamako, Alhaji Bawa shi zai dinga kiran suna yayinda Mr Mike ze dinga d'aga zanen dan kowa ya gani. Bayan sun yi d'an jawabansu, Alhaji Bawa ya fara magana kamar haka:" zamu fara da na sha biyar (15)" nan ya fara kiran sunaye yayin da Mr mike ke d'aga zanen, sai kuma wanda aka kira ya fito bainar jama'a. Sai mutane su tafa masa/mata . A haka dai yana fad'a har yazo ta biyu. Wanda ya kira dalibi Ahmad Huzaifa, aka d'aga zanen shi nan mutane suka fara ihu sosaii dan zanen nashi yayi bala'in kyau. Bayan nan yace yanzu za'a d'aga zanen wanda/wadda ta yazo ta d'aya, mutane kowa ya baza ido yana jiran ganin wani zane ne wanda ya zarce had'ad'un zanen da'aka nuna, da kuma wani tauraron ne ko kuma wata tauraruwar ce ta samu nasarar lashe gasar? Mr Mike wani had'ad'en ko nace gaba da had'ad'e zanen ya d'aga sama, zane ne wanda aka yishi akan al'adar bahaushe wato , da farko dai , bukka aka zana yar k'arama me bala'in kyau a gefen ta kuma tabarmar kaba ce wanda aka zana akushi da kwanon sha da kuma kwaryar akai, ga butar alwala a gefe, a d'ayan bangaren kuma atamfa ce aka zana da kuma dan kwali irin na da, sannan ga murajani da dai sauran kayan hausawa na mata. Zanen yayi bala'in kyau mutum in ya kalla sai ya rantse hoto ne aka d'auka a camera saboda tsabar tsaruwar da yayi. Nan da nan wajen ya gauraye da ihu kowa sai washe baki yake yi daga masu cewa "wow!" Sai masu cewa 'masha Allah" duk dai, Kowa burinsa be huce yaga wanda/ wadda yayi zanen ba. Yan jarida kuwa da sauran mutane sai d'auka hoton zanen suke. Mubeena kuwa suna hira da su Husna taga an d'aga zanen ta wani farin ciki taji wanda bata tab'a jinsa a rayuwarta ba,, ta runtse idonta sai hawayen murna, ta kuma k'i fadawa su Ya Abdul cewa zanen tane, sukuwa suna gefe sai fama zuzuta zanen suke,amma kowa a zuciyarshi, ji yake kamar zanen Mubeena ne. Alhaji Bawa ne ya dakatar da mutane daga hayaniyae da suke dakuma ihu, yayi gyran murya yace , "yanzu zan kira wanda yayi wannan zane, ina me farin ciki kirin AISHATUL MUBEENA Muhammad Ameen!". Murna a wajen su Husna kamar me ,sai kallon Mubeena suke suna k'ara kallonta, fuskarsu d'auke da farin ciki, Mubeena kasa tashi tayi da kyar suka lalab'eta ta tashi jiki ba kwari ta nufi inda aka kirata. Mutane dake ta jiran fitowar ta, sai hango ta sukai tana cangala kafarta dan zuwan wajen, mamaki duk ya cika su, amma wannan ta ciri tuta ashe dama da nakasasu masu irin talent irinta? Ihun mutane ya k'aru gaba d'aya suka tashi suna kallonta yayin da 'yan jarida suka cika wajen suna d'aukar ta hoto, da kuma hoto mai motsi(video). Isarta keda wuya , Mr Mike abinka da arne cak ya d'agata sama! Duk k'ok'arin datake dan ta kwace amma ya rik'e ta gam, cikin d'aga murya da hausar sa da wadda bata fita sosai yace " wannan itace ta lashe gasar, itace tazo ta d'aya!" Like · 2 · Reply · Edit · 6 February [11:50AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [115]-[120] Umma tace "hakane Iya amma..." Iya ta katse ta "dakata" ta janyo hannun Mubeena ta rik'e gam sannan tace "Aihatul mubeena nice kakar ki, nice na haifi mahaifinki SULAIMAN, nida mahaifinki mun kasance masu wata irin zuciya,masu butulci kuma wa'enda basu da godiyar Allah,, nan da nan ta fada mata komai tun daga auren Umma da Mal Sule har rannar da suka rabu" Mubeena ta fashe da kuka,kuka take sosaii haka ma Umma. Mubeena tana kuka tace "Umma dama na fad'a miki, na fad'a miki cewa Abba ba shine mahaifina ba!" Umma cikin tsawa tace " shine mahaifinki ! Abba shine mahaifinki! , shine yaso ki a lokacin da Mal sule ya k'i ki har yake ik'irarin cewa ke ba 'yarsa bace, shine ya ciyyar dake, ya tufatar dake, ya baki ilimi, daidai da rana d'aya bai tab'a nuna bambanci a tsakaninku ke da 'yan'yansa ba,, sabanin Mal Sule da ya firta da bakinsa kar na sake ko da wasa nace ke d'iyarsa ce , wanda shine sillar gurguncewa k'afarki, wanda besan cin kiba, besan shan kiba, besan wahala kiba, besan komai naki ba! Abu d'aya ne ya miki a rayuwa, shine sillar zuwan ki duniya , amma bayan haka ba abinda ya tsinana miki a rayuwa, wallahi kome Mal sule ze miki yanzu in aka d'auke Silan zuwanki duniya dayayi baze ko kusa yi miki abinda Dr Muhammad ya miki ba,, Mal Sule ya amsa sunan sa na cewa shine ubanki wanda ya haife ki kawai, amma ko kusa baze amsa sunan , wanda yayi wahala dake tun kina yar gwililuwa har yanzu, wanda ya ci dake, ya sha dake,ya tufatar dake,ya baki ilimi ya kuma baki tarbiya, Shine ya cika sharud'an zama uba wanda uban naki wanda ya haife ki ya kasa cikawa!(Ta sassauta murya ta) amma Mubeena kar abinda nida Iya muka fad'a miki ya sa ki tsani mahaifinki, ko kusa kar ki fara domin in badan shiba baza kizo duniya ba!....ta k'arasa maganar cikin sheshek'ar kuka. Kukan Mubeena ya k'aru sosai, tama kasa magana, sai sheshek'ar kukan data keyi,,, Umma ta kalli Iya dake ta faman sharbar kuka tace "Iya kiyi hak'uri ban fad"i maganar ba dan ta b'ata miki rai, gaskiya ce kawai na fad'a, Iya tace" baki b'ata min rai ba Ma'u, gaskiya ke kike fad'i, nayi dana sanin abinda na aikata a baya"" Ma'u tace "Iya bakiyi mana komai ba Iya wannan maganar ta huce saboda ni tun d'ad'ewa da kika nemi gafarata na yafe miki, dama ko baki nemi na yafe miki zan yafe miki dan wallahi ni tamkar Uwa na d'auke ki!" Ga wannnan ta aje mata bandir din yan dubu d'aya(1) sannan tace "gobe insha Allah zan aiko miki da sauran abinda kike buk'ata, kuma insha Allahu za mu dinga ziyartar ki akai- akai. Iya ta rik'e hannunta " Ma'u tsaya na fad'a miki wani abu,, yau tsawon shekaru goma(10) kenan ban sa Sule a idona ba, tunda yazo yace min ya tafi birni cirani na nuna ban amince ba amma sam ya k' jin maganata ya tafi ya barni, be kuma waiwayata ba, ko yana da rai? Ko ya rasu? Allahu a'alam,, amma dan Allah in Allah ya had'a ku dan Allah ma'u ku yafe masa ke da Aiha (Aisha), ki kuma ce nima na yafe masa, dan ina ji ajikina kwanan ya kusa k'are da k'yar na k'ara kwana a duniya ,nima ku yafe min Allah ya had'a fuskokin mu a aljana..." ta fashe da kuka,,,,jikin Umma da Mubeena yayi sanyi sosaii Mubeena tayi dauriyar cewa "ni na yafe miki Iya, kuma ki dena ambaton mutuwa insha Allahu zaki tashi, cuta ba mutuwa bace! " Iya ta girgiza kai "kayya! Suka mata sallama suna kuka tana kuka suka rabu. A gidan Mama ne, Mama ta kwantar da murya tayiwa Mubeena bayanin komai, Mubeena wani sabon kukan ta sake Mama na rarashinta, taji tausayin Ummanta sosaii sosaii ga wani sonta dake k'aruwa a zuciyarta,, sannan kuma taji tsanar Mal Sule a zuciyarta, ji take ba wanda ta tsana sama dashi..godewa Allah tayi daya bata uwa ta gari kamar Umma dan ita gani take tafi kowa dacen uwa a duniya! Haka suka koma gida dukkansu ba farin ciki da walwala.. ◆◆◆◆◆◆◆ Washe garin rana Allah yayi wa Iya cikawa,, su Umma sunji mutuwarta sosaii a wannan dak'in Allah yayi mata cikawa cikin dare. Da sassafe su Umma suka tafi suna ta kuka abun tausayi mussaman ma Mubeena, da 'yan gidan suka tafi gabad'aya har da Abba, dan shima yaji mutuwar dan ya santa, lokacin da 'aka kwantar da Mubeena a asibiti da cutar polio ta sameta,,sai da suka fara sauka a gidan Mama sannan sukaje gidan marigayiya Iya,, a lokacin ma ko wanka ba'a yiwa gawar ba, Umma da taimakon Mubeena su suka wanke gawar tas aka samata likafani aka fita da ita ,maza suka sallaci gawar aka kaita kuhewarta , Allahu akbar Allah kasa mu cika da imani, ka bamu kyakyawan K'arshe Ameen ya Allah.. Ba wani zaman makoki akayi ba tunda wa za'ayiwa gaisuwar? Dama Mal Sule ne kawai d'an data haifa kuma baya nan bai san ta rasu bama, 'yayan mijnata kuwa Bashir da Hauwa sun dad'e da dena kulata bama sa k'asar gabadaya. A 'yan- uwanta kuwa ita kad'ai tayi ragowa duk sun rasu,, sai dai sauran dangi da ba'a rasa ba..Masa'udu dama shi ake yiwa gaisuwar dan shine ya kula da ita tun data sami rashin lafiyar har ta warke, shima kuwa a rannar data rasu admission dinsa ya fito yaci Ahmadu Bello unibasiti zaria(ABU zaria) dan haka ya had'a kayansa ya tafi Umma kuwa kud'i me yawa ta bashi tace yayi harkar makaranta dashi ya yafi yana ta godiya. [12:35AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:46AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [135]-[140] Bayan an dawo hutun tak'aitacen lokaci. Aysha Amatulah: to barkan mu da dawowa. Hajiya Mubeena shin wai ta yaya kika tsunduma cikin harkar zane- zane? Mubeena: To agaskiya nidai na taso ne kawai na gani inayi, a lokacin inga abu ya min kyau sai na zana shi, cikin ikon Allah kuma sai kiga zanen ya fita sosaii...lokacin da ina primary kuma in kika duba littafai na na arts zaki ga inaci sosaii, koda merit za'a bada ma a Art ni ake bawa. Kuma akwai Yayana Ya Ameen shine ya cigaba da ban kwarin gwiwa har nazo matakin danake yanzu. Aysha Amatullah: madalah, to kafin ki fara wanan zane-zanen mene burinki a rayuwa? Mubeena: Burin na da shine na zama likita dan nima na bada gudunmawa ta wajen yak'i da wannan cutar sai kuma Allah beyi ba. Aysha Amatullah: to Allah zaba mafi alheri, meye ya fi b'ata miki rai da kuma abinda yafi faranta miki rai? Mubeena: Abinda ya fi b'ata min rai guda biyu ne na d'aya ya shafi personal life dina, na biyun kuwa shine, idan naga yan'uwana masu wannan cuta ta polio suna bara ko kuma suna cikin wani hali na rashin gata a gaskiya raina na sosuwa kuma ina iya k'ok'ari na dan ganin na taimake su. Sannan abinda yafi faranta min rai shine, ina tuno irin nasororin dana samu a rayuwa, sannan kuma ina ga masu irin cuta ta wato polio basa fuskantar wani k'alubale a rayuwa ,suna jin dadin rayuwarsu sannan suna samin gata daga wajen iyayensu dama al'uma baki d'aya, to nakan ji raina yayi fari . Aysha Amatullah: Allah sarki, yanzu zamu d'auki waya guda biyu(2) duba da yanayin lokaci, zaku turo sak'o ne ta wannan lambar 064**** sannan zaku kira mu ta 064****. Mutane an kira an mata fatan alheri, an kuma turo sak'oni ba adadi. Aysha Amatulah:wani kira zaki yi ga iyaye da kuma masu cutar polio? Mubeena: kiran da zanyi shine dan Allah iyaye su dinga bada yayansu a dinga musu d'igon rigakafi, sannan iyaye su dage su dinga gano talent din da suke dashi su k'arfafa musu gwiwa, bawai su dinga barinsu suna bara ba, da sauransu. Sannan irina masu wannan cuta ta polio, ganin suna da nakasa kar hakan yasa su fidda rai da rayuwa , su d'age suyi karatu suma su zama wasu a dinga damawa dasu, in hakan ya faru zan fi kowa farin ciki. Aysha Amatullah: to duba da yanayin lokaci mene sak'on ki na k'arshe? Mubeena: to Alhamdulilah ba abinda zance sai in godewa Allah da kuma iyayena nakan ji farin ciki sosaii in na tuno da iyayena,yayena da k'anina, da sauran dangi. Aysha Amatulah: to masu sauraron mu lokaci yayi halinsa , anan zamu k'ark'are wannan shirin, Hajiya Mubeena muna godiya da kika amsa gayyatar mu, da fatan duk sanda muka sake neman ki zaki amsa kiranmu. Mubeena: to nima nagode masu saurarona da kallona ina muku fatan Alheri,(tayi murmushi) sai anjima. Ahaka aka gama shirin, ta fito driver yaja suka tafi. *********** A yau ne aka d'aura auren Ameen Muhammad Ameen da Fatima Adam, Aisha Muhammad Ameen(Nana) da kuma Saifulahi Abdalah. Ansha biki sosaii an kuma kashe kudi dai-dai misali, Mubeena kuwa lemukan nan da'aka bata kyauta su ta bada akayi hidimar biki da su, sannan katuwar jaka da calanda me sunayen Allah ta musu a matsayin gudunmawa sun sha murna tare da yi mata addu'ar Allah ya saka mata da alheri. Bayan biki aka kai amarya Nana gidanta dake Hotoro, Sannan amaryar Ya Ameen Faty aka kaita gidan ta dake Janbulo. A yau su Mubeena sukayi final exam dinsu, sunsha kukan rabuwa da dalibai, Mubeena da Asiya ma ansha kuka, malamai sunyi bak'in cikin rabuwa da Mubeena sosai , hadda masu kwala, bayan sunyi sharing contacts driver yazo ya d'auki Mubeena suka koma gida, Mubeena cike da kewayar dalibai, malamai dama makarantar baki d'aya. Yau ta kama rannar lahadi kuma dama duk Lahadin k'arshen wata sukan je shopping... Suna cikin mota dan zuwa shopping d'in Abba ne ke driving dan yau yace sha'awar driving yake saboda ya d'ad'e beyi ba, Umma na gaba, yayin da Husna, Amir da Mubeena ke bayan mota Ummi kuwa taje bikin 'yar aminiyata. Suna tafe cikin raha da anashuwa. Can wata mota ta taho da gudun gaske, dai-dai lokacin da wani datijjon mutum yazo tsalaka titi, ai kuwa fuu motar ta bige shi, bata ko tsaya ba drivern mota ya k'ara falawa da gudu, cikin 'yan sakani aka dena hango motar sai k'ura da motar ta tayar... shikuwa dattijon mutumin nan yana baje a titi jini sai zuba yake. Abba da sauri ya fito daga motar yana salati suma su Umma suka fito dan ganewa idonsu, a firgice suka k'araso wajen da mutumin ke kwance cikin jini, Umma da ta k'araso wajen da sauri, dora idonta akan mutumin keda wuya ta kwala wani k'ara anan ta fad'i k'asa sumamiya! Lik [11:47AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [130]-[135] Nan take wajen ya d'auka sai ihu akeyi su Husna dake gefe sai dariya suke yi dan sunsan Mubeena yau ta shak'i haushi itada ko hannunta bata san wani namiji ya tab'a, sai gashi yau k'aton arne ya d'aga ta, shikuwa Ya Abdul ji yake kamar yaje ya wankawa Mr Mike mari dan haushi. Da kyar ta samu ya sauke ta k'asa, ai kuwa sai tabar wajenshi ta koma d'ayan banganren, sai d'aukanta hoto ake. Certificate aka bata ta, sannan aka buk'aci ta sa hannu taje ta saka kuwa, sannan aka mik'a mata shi, bayan nan aka shiga raba kyautuka ga wanda suka yi participating kyauta kuwa ta samu kala-kala, kamfaanin wani shahararen lemu ya bata da kuma sauran participant's d'in kud'i da kuma lemuka, kyauta dai iri-iri ta sha su wai kuma aka samun tab'i ne dan ba'a bata babbar kyautar tata ba. Check na miliyan d'aya(1) aka bata daga hukumar da suka shirya gasar sannan kuma k'ungiya masu zane dake kano suka bata kudi naira dubu d'ari(100). Mr Mike ne ya d'auko wasu sarkok'in medal's guda uku(3) 'yan k'anana d'aya na gold d'aya na silver na ukun kuma na bronze. Ta uku ya rataya wa bronze medal aka fara tafi ana d'aukan hotuna, sannan ya kira Ahmad Huzaifa ya rataya masa na silver, shima aka d'au tafi. Bayan nan kuma wakilin gwamnati ya tabbatar mata da cewa bayan ta kammala karatun sakandire gwamntani zata d'auki nauyin ta taje tayi course din zane a wata makatantar zane-zane(art school) dake amurka(America) Na gold din kuwa Mubeena ya ratayawa nan waje ya k'ara d'aukan ihu 'yan jarida nata d'aukan hoto da kuma hoto mai motsi(video) domin a yawancin kafafen yad'a labarai ta talabijin abin live ake nunawa. Su Abba dake zaune suna kallo LIVE murna a wajensu kamar me, sun ma rasa me zasuyi saboda murna, hak'k'ika wannan rana tana cikin rana mafi farin ciki a rayuwarsu, mussaman ma Umma da alk'warin da tayiwa Mal Sule ya cika yau, a zuciyarta cewa take dama Mal Sule ya ji ko ya ga wannan abin alherin. Bayan an kammala taro aka rufe taro da add'ua, nan aka fara d'aukan hotuna dasu Uncle Hashim da bakinsa ya kasa rufuwa saboda farin ciki, su Ya Abdul ma haka, kana ganinsu zaka gane irin halin da suke ciki. Zanen kuwa tafiya Mr Mike zeyi dashi, inda za'a kai shi wannan babban ART GALLERY dake Abuja. Su Alhaji Bawa basu so hakan ba dan su sunfi san a barshi a Art gallery din dake kano amma ba yadda suka iya. Fitowar su Mubeena ke da wuya wakilan 'yan jarida da gidajen radio sukawo mata caa akanta, sai tambayoyi suke mata tama rasa wadda zata amsa, can dai tace "Alhamdulilah ba abinda zance sai godiya ga Allah da ya bani nasara a wannan gasar, sannan ina godewa iyayena da suka bani k'warin gwiwa har nazo matakin dana ke yanzu! Nagode.". Tana gama fad'an hakan tayi hanyar motarsu. Zwan ta keda wuya ta tadda wakilan wani shahararen gidan TV suna jiranta, numfasawa tayi tace "wannan shine anyi gudun gara an tadda zago". Nan suka shiga yi mata magiya akan suna so su tautana da ita gobe, saboda gobe ne ta kama rannar masu cutar polio da duniya wato (WORLD POLIO DAY) wato ashirin da hud'u ga watan oktoba(24th october) bata musu musu ba kuwa ta amsa sunyi farin cika sosaii inda suka bata wani kati na gayyata. Farin ciki ya dawo sabo sanda suka koma gida su Umma hadda kukan murna, Ya Ameen dake can k'asar holland ya sami labari daya duba news ya kira su aka sha murna, makarantarsu kuwa dayake tana final year suka ce sun d'auki nauyin ta har ta gama su waec da neco duk zasu biya mata, saboda ta fito da sunan makarantarsu, bayan k'ananun kyaututuka da suka bata. Yau ta kama 24th october(World polio day), tun da safe ta ta shirya driver ya kaita dan Ya Abdul ya tafi wajen aiki. Tana zuwa dama ita suka jira, aka shirya komai tazo ta zauna akan kujerar da za'a tautauna da ita.(wasu gidajen radio suma sun juno dan masu saurarun radiyo suma suji) Me gabatarwa ta fara: Assalamu alaikum warahamatul lahi ta'ala wa barkatuhu masu kallo da sauraranmu. Barkan mu da sake saduwa a wannan shiri na mussaman da muke gabatarwa duk a rannar polio ta duniya duk shekara. A yau shirin namu yayi babban kamu, domin yau zamu tautauna da AISHATUL MUBEENA Muhammad Ameen, wadda itama ta zamo polio victim ta farko tada fara lashe gasar zane-zane dake gabatarwa duk bayan shekara hud'u a jihohi dama k'asa baki d'aya... Sunana Aysha Amatullah wadda zan gabatar da shirin, Hajiya Mubeena ko nace Artist Mubeena barka da zuwa. Mubeena: Barka kadai. Aysha Amatullah: shin zamu iya jin tak'aitacen tarihin ki? Mubeena: To Alhamdulilah, nidai sunana Aishatul Mubeena Muhammad Ameen an haifeni a garin Kano na taso a Kano, kuma a yanzu haka inada shekara sha bakwai next year zan shiga sha takwas(18), saboda ban fara makaranta da wuri ba yanzu dai ina ss3 a sakandire. Aysha Amatullah: Masha Allahu, shin kina shekara nawa wannan cuta ta sameki? Kuma mene ne dalili? Mubeena: A gaskiya wannan cuta ta same ni ina 3-4 years, dan dama kinsan a yara masu shekara d'aya zuwa biyar(1-5) tafi kamawa..kuma a gaskiya zan iya cewa wannan cuta kaddara ce daga Allah, dama can Allah ya riga ya rubuta cewa a haka zan tashi, cutar zata same ni. Aysha Miss Hafcy Newer Post Older Post Home Subscribe to: Post Comments (Atom) Saturday, 15 October 2016 Posted by MissHafcy at 08:01 AISHATUL MUBEENA 110-140 [12:33AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:51AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS A tak'aice dai ansa rannar Ya Ameen da Faty, da kuma Aisha( Ya Nana) da Saifulah nan da wata biyu(2) ,, Su Umma kuwa sai shirye shiryen biki sukeyi.. Ya Abdul kuwa har ya gama karatunshi Abba ya samar masa aiki har ya fara yi dan haka ma ba kullum yake zama a gida ba. Baiwar Allah Mubeena kuwa tacan duk ta damu dan ta dad'e da gane cewa tana son ya Abdul ! amma sai take ganin abun da kamar wuya, na farko dai Umma tace mata Abba ne babanta to indai har kuwa Abba ne babanta to ba aure a tsakaninsu saboda wanta ne uba d'aya kuma ba aure a tsakaninsu k'anwa da wa.!.na biyu kuwa, tasan halin ya Abdul shida ko magana bata shiga tsakaninsu sai ta k'ure,, in ba kwanan nan dayake d'an sakar mata fuska,,kuma tasan ma baze rasa budurwa wadda yake so ba,,,,yadda yake d'in nan tubarkalah gashi kuma d'an gayu,, doleh 'yan mata suyi rububinsa... dan haka sai ta dinga addu'ar Allah ya cire mata sanshi a zuciyarta,, a kullum kuma tana k'ok'arin cire sanshi daga zuciyarta,, dan a iya tunaninta ko da da aure a tsakanin su, in ba wani ikon Allan ba,to ko a mafarki baza ta tab'a zama matarsa ba,, Ita dai kullum addu'arta shine Allah ya bata miji na gari ya kuma zab'a mata mafi alheri Yau saura befi kwana biyar (5) suyi gasar ba,kuma dama sun gama exams an basu hutu, dan haka lokacin hutu za'ayi gasar.. Mubeena na zaune a falo tana kallan musab'akar alkur'ani da akasa a sunnah Tv,, Umma ta fito daga d'aki cikin shirin fita unguwa, Mubeena ta d'ago ta kalleta "Umma fita zaki yi ne?" Umma tace "eh k'auye zani wajen Mama" Mubeena da sauri ta tashi "Umma dan Allah nazo muje? Na dad'e banga Mama ba" Umma tace to maza shirya muje,kafin rigimaman nan yazo(Amir) dama neman dalilin k'in zuwa islamiya yake yi" Mubeena tayi dariya sannan ta shiga dakinsu ta dauko hijab dinta ta bi bayan umma ,, suka yiwa su Ummi sallama sannan suka nufi k'auye. Bayan sun isa Mama tayi murna sosaii da ganin su, bayan sun gaisa sun sha ruwa , Mubeena nakan cinyar Mama suna wasan su na jika da kaka, Mama ta kalli Umma," Ma'u kinsan IYA ta samu mutuwar b'arin jiki kuwa? Gaban Umma ya fad'i , "subhanalahi,wacca iyan??" ta fad'a had'e da dafe k'irji, Mama tace " Iya dai surikarki, wallahi abun tausayi kuje ki duba ta dan Allah kullum fad'i take a kirawo mata ke da yarki ta nemi gafarar ku . Umma tace "Allah sarki Iya, a ina take zaune? Mama tace "inda dai kika santa tana nan' Mubeena dake kwance akan cinyar Mama da sauri ta taso ta tsutsura musu ido ,, ta kalli Mama tace"Mama wacce ce Iya?" Mama na k'ok'arin magana Umma ta dakawa Mubeena tsawa "bansani ba,dake muke magana,ban hanaki sa min baki in ina magana ba?" Mubeena ta sunkuyar da kanta , yayin da Mama tace "ke Ma'u wai meyasa kike haka ne? Daga tambaya saiki hayayak'o mata?" Umma tace "Mama haushi taban ai manya na magana ta dinga sako baki, bari na tashi naje na dubo ta"" ta tashi ta dauki jakarta tana k'ok'arin saka takalminta, Mama ta kalleta," Ma'u indai nina haifeki to ki tafi da Mubeena" Umma ta juyo jiki ba kwari tace "to se ki taso muje" bata jira amsar Mubeena ba ta sakai ta fita, Mubeena da sauri tasa hijab dinta tabi bayanta. Har suka iso gidan Umma bata yiwa Mubeena magana ba, da sallama suka shiga gidan amma suka ji shiru,, sai da sukayi sallama yakai guda hudu(4) sannan suka jiyo wata dashashiyar murya nacewa "Wa..alai..kum..us..salam...,k u..shigo..mana,, Umma ta kad'a kai sannan ta shiga dakin data juyo murya, Mubeena tabi bayanta. Umma ta zaro ido saboda abinda ta gani ya masifar tsorata ta, duniya kenan! ... IYA ce kwance akan wata yagalaliyar tabarma duk tayi fitsari akai, dakin in banda zarni ba abinda yake yi. Umma a firgice ta k'arasa wajen Mubeena ta bi bayanta, Iya ta k'are musu kallo sannan tace "Wannan kamar Ma'u nake gani kodai mafarki nakeyi? Umma ta runtse idonta sai hawaye 'Nice Iya!" Iya ta fashe da kuka "kece Ma'u ! ashe rai kanga rai? Ina jikar tawa take?" Umma ta nuna Mubeena "gata nan, tare muke ma" Iya ta k'ara fashewa da kuka "zo nan 'yar jikalle ta, ni bansan ma da wani ido zan kalle ki ba, randa aka haife ki nida mahai....." Umma ta da sauri ta katse ta "Iya komai ya wuce dan Allah a bar zancen nan baki yimin komai ba ni kuma koda kin min ma na yafe miki, garin yaya kika sami wannan ciwon?". Iya tana kuka tace "rannar ina zaune ni kad'ai a daki naji mage a gefena, kinsan dama ina tsoron mage ,to tun daga nan na tsorata sosai bakina ya juye magana ma na kasa yi, hannuna ma na kasa d'agawa balle na d'aga kafata,, Haka na kwana ina kuka bame ceto na,, washe gari makota da suka ji shiru suka zo suka bud'e kofar aka fito dani aka kaini asibiti anan akace mutuwar b'arin jiki nasamu,,shine nake kwance anan masa'udu (dan k'anwar iya) shine kawai yake kula dani,,, ta sake fashewa da kuka,, Umma ta fashe da kuka hakama Mubeena dama ga Mubeena da tausayi. Iya ce ta katse musu kukan da cewa "Ma'u baki fad'a wa jikartawa ni kakar ta bace ba? Dan daga ganin alama bata san nice na....Umma ta katse ta " Iya dan Allah ya isa haka, zancen nan ya wuce banse tasan komai ba ai" Mubeena duk ta rikice ta kasa gane maganar tasu, sun caja mata kwakwalwa....Iya cikin dashashiyar murya tace "Ma'u RANNAR WANKA BA'A BOYEN CIBI! Like · 2 · Reply · Edit · 3 February Khadija Muhamed [11:52AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [105]-[110] Mubeena ta shafa fuskarta" bakomai yusra Allah ya baki lafiya" yusra ta rik'e hannunta "Amin",, sukai musu sallama suka juya suka bar Maman nata kukan murna k'aninta mu'az yazo shima murna kamar me, ya dinga shiwa su Mubeena albarka,,dama kudin reg din makaranta yake nema ya cika dubu biyar(5000)amma ta gagara sai gashi Allah ya share musu kukunsu. A mota ne Umma ke ba ya Abdul labarin yarinya jaji tausayinta sosaii shima ya kuma ji dad'i da'aka musu wannnan taimakon..Suka aje Asiya a gida suka mata godiya sannan suka koma gida. Kwanci tashi ,gobe ne Mubeena da Nafisa zasuyi gasar su, Mubeena tayi practice sosai, a rannar raba dare tayi tana addu"ar Allah ya bata sa'a su Umma ma haka duk 'yan gidan ma, Ya Abdul ma yazo yayi mata fatan alheri,dan yanzu ba laifi yana sakar mata fuska. Da sassafe ta tashi ta yi sallolinta sannan tayi zikirorinta ta shirya suka huce makaranta...bayan an fito break 'yan class sun zagaye Nafisa dake wa mickey mouse din data zana musu fenti wai zasu sa a wall bangon class din ,bayan ta gama ta d'aga zanen "ya kuka gani friends?" Suka hada baki "Woww..yayi kyau sosaii amma da Mubeena ce ta zana munsan se yafi haka kyau" Nafisa ta juyo a fusace "lallai ma, in sha wahala in muku abu amma kuce da wata banza ce tayi sai yafi kyau?" D'aya daga cikinsu tace "a'ah kinga kar ki sake ce mata banza " Nafisa tace "an fad'a mata d'in, bari ku gani" nan da nana ta warce zanen ta yayaga shi, sannan ta fita daga ajin tana zage-zage,sukuwa dariya sukayi sukace "kanki kika cuta ai,wahalaliya kawai. Mubeena ce da Nafisa zaune suna jiran akawo musu abubuwan zanen, Uncle Hashim ya shigo ya raraba musu sannan yace mutum d'aya ta biyo shi saboda za'a raba musu aji gudun kar wani ya kwafi na wani, caraf Nafisa tace zata bishi ,hakan kuwa akaiyi yabar Mubeena da anty Sa'a sannan shi kuma suka tafi wani staff room d'in shi da Nafisa. Cikin minti talatin suka kamala zanen kowa yayi submitn,, suka koma aji ... aka bawa wanda suka duba zanen kwanaki dan su duba wannan d'in shima. Suna zaune a aji suna class work din maths Uncle Hashim yazo ya kira Mubeena anan ya tabbatar mata da cewa itace ta lashe gasar!! Wohoho murna wajen Mubeena kamar me ta rasa ma me zatai dan murna. Assamibili aka k'ara hadawa anan aka kirawo Mubeena gaban assambili aka sanar da sauran dalibai itace ta cinye gasar kuma ita zata wakilci makarantarsu a gasar da za'ayi nan da sati biyu2 dalibai aka d'au ihu ana Up Up Up Mubeena!! Mubeena kuwa sai murmushi take tana godewa Allah daya bata nasara... Nafisa dajin haka ihu ta saki ,tana wani fizge fizge daga k'arshe ta tada aljanun k'arya malamin islamic studies yasa prefect mata suka d'auke ta zuwa staff room dan yayi mata ruk'iya nan kuwa be san na k'arya ne ba. Mubeena kuwa se murna ake mata malamai kuwa sai wani nan-nan suke da ita kodayake dama can malamai suna santa saboda kwazonta...Nafisa kuwa da Ustaz(malamin islamic) ya gane cewa na k'arya ne,dorina ya dauko zabgegiya ya shiga lafta mata, bashiri ta tashi tana kuka sharaf sharaf tana bashi hak'uri,dariya yayi sanan yace ta koma aji, aka dinga mata ihu ana cewa me aljanun k'arya a rannar tayi alkwarin baza ta sake dawowa makarantar ba, dan abin kunya data aikita baza su barta ta zauna a makarnatar lafiya ba. Yau Ya Ameen ya ze dawo murna a wajen 'yan gidan kamar me,kowa ka gani yana cikin walwala hatta Ya Abdul... Mubeena kuwa cewa tayi a bar mata zata mai girki me dadi, dayake yanason abincin gargajiya fankaso da tuwo ta yi masa da miyar taushe dan ya fad'a mata a waya ya dad'e be cisu ba,, su ya Nana kuma suka yi masa kunun aya da zob'o. Bayan yayi parking din motar shi ya shigo gida Amir da gudu yazo ya rungume shi yana masa oyoyo , su Mubeena suka fifito suna masa sannu da zuwa shikuwa yana amsawa fuska d'auke da murmushi..ya k'araso cikin gida Umma da Ummi kuma na falo suna jiranshi suka yi masa sannu da zuwa sa kuma ya hanya. Ya amsa da "lafiya lau nagode,,kuma nayi missing dinku sooooooo much" a tare suka ce "muma munyi missing dinka". Bayan yayi wanka yayi sallah ya dawo ya zauna Mubeena tace abincinsa na kan dinning table( teburin cin abinci) yaje ya zauna yana budewa ya fara "wow nasan wannan aikin kine Mubeena", Ummi tace 'ai kuwa kamar kasani,kayan shan ne su Nana sukayi yimaka" yayi murmushi "amma kuwa nagode lovely sisters" Bayan ya gama cin abincin su Ummi ke sanar dashi Mubeena ce zata wakilci skul dinsu ba k'aramin murna yayi ba,a rannar ta faranta masa rai. Washe gari ya sami Umma yake fad'a mata cewa iyayen Faty sun takura masa daya turo dan nan da wata hudu (4) za'ayi bikin yarta kuma sunaso a had'a da na Faty...shikuma yana kunyar fad'awa Ummi da Abba,, Umma tayi murna dajin haka, ta kuma yimasa alkwarin zata fad'awa Abban sannan kuma indai ya shirya to ba matsala. yayi mata godiya ya tafi. Umma ta sami Abba ta fada masa yaji dadin haka dama yana shirin yi masa maganar auren dan a ganinsa lokaci yayi daya kamata ya zama cikaken mutum wato yayi aure...yace ta fad'awa ya Ameen d'in ya kwantar da hankalinsa zasuje shida yan- uwansa su nema masa auren insha Allahu.. [12:34AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:48AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [125]-[130] Wakilin shugabanin da suka shirya gasa wanda yazo daga birnin taraya Abuja wato MR MIKE da shugaban k'ungiyar masu zanen dake kano ALHAJI AL- AMIN BAWA sune suka fito dan fad'an result din bayan manyan-manyan kwararru a harkar zane sun duba sun fitar da sakamako, Alhaji Bawa shi zai dinga kiran suna yayinda Mr Mike ze dinga d'aga zanen dan kowa ya gani. Bayan sun yi d'an jawabansu, Alhaji Bawa ya fara magana kamar haka:" zamu fara da na sha biyar (15)" nan ya fara kiran sunaye yayin da Mr mike ke d'aga zanen, sai kuma wanda aka kira ya fito bainar jama'a. Sai mutane su tafa masa/mata . A haka dai yana fad'a har yazo ta biyu. Wanda ya kira dalibi Ahmad Huzaifa, aka d'aga zanen shi nan mutane suka fara ihu sosaii dan zanen nashi yayi bala'in kyau. Bayan nan yace yanzu za'a d'aga zanen wanda/wadda ta yazo ta d'aya, mutane kowa ya baza ido yana jiran ganin wani zane ne wanda ya zarce had'ad'un zanen da'aka nuna, da kuma wani tauraron ne ko kuma wata tauraruwar ce ta samu nasarar lashe gasar? Mr Mike wani had'ad'en ko nace gaba da had'ad'e zanen ya d'aga sama, zane ne wanda aka yishi akan al'adar bahaushe wato , da farko dai , bukka aka zana yar k'arama me bala'in kyau a gefen ta kuma tabarmar kaba ce wanda aka zana akushi da kwanon sha da kuma kwaryar akai, ga butar alwala a gefe, a d'ayan bangaren kuma atamfa ce aka zana da kuma dan kwali irin na da, sannan ga murajani da dai sauran kayan hausawa na mata. Zanen yayi bala'in kyau mutum in ya kalla sai ya rantse hoto ne aka d'auka a camera saboda tsabar tsaruwar da yayi. Nan da nan wajen ya gauraye da ihu kowa sai washe baki yake yi daga masu cewa "wow!" Sai masu cewa 'masha Allah" duk dai, Kowa burinsa be huce yaga wanda/ wadda yayi zanen ba. Yan jarida kuwa da sauran mutane sai d'auka hoton zanen suke. Mubeena kuwa suna hira da su Husna taga an d'aga zanen ta wani farin ciki taji wanda bata tab'a jinsa a rayuwarta ba,, ta runtse idonta sai hawayen murna, ta kuma k'i fadawa su Ya Abdul cewa zanen tane, sukuwa suna gefe sai fama zuzuta zanen suke,amma kowa a zuciyarshi, ji yake kamar zanen Mubeena ne. Alhaji Bawa ne ya dakatar da mutane daga hayaniyae da suke dakuma ihu, yayi gyran murya yace , "yanzu zan kira wanda yayi wannan zane, ina me farin ciki kirin AISHATUL MUBEENA Muhammad Ameen!". Murna a wajen su Husna kamar me ,sai kallon Mubeena suke suna k'ara kallonta, fuskarsu d'auke da farin ciki, Mubeena kasa tashi tayi da kyar suka lalab'eta ta tashi jiki ba kwari ta nufi inda aka kirata. Mutane dake ta jiran fitowar ta, sai hango ta sukai tana cangala kafarta dan zuwan wajen, mamaki duk ya cika su, amma wannan ta ciri tuta ashe dama da nakasasu masu irin talent irinta? Ihun mutane ya k'aru gaba d'aya suka tashi suna kallonta yayin da 'yan jarida suka cika wajen suna d'aukar ta hoto, da kuma hoto mai motsi(video). Isarta keda wuya , Mr Mike abinka da arne cak ya d'agata sama! Duk k'ok'arin datake dan ta kwace amma ya rik'e ta gam, cikin d'aga murya da hausar sa da wadda bata fita sosai yace " wannan itace ta lashe gasar, itace tazo ta d'aya!" Like · 2 · Reply · Edit · 6 February [11:50AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [115]-[120] Umma tace "hakane Iya amma..." Iya ta katse ta "dakata" ta janyo hannun Mubeena ta rik'e gam sannan tace "Aihatul mubeena nice kakar ki, nice na haifi mahaifinki SULAIMAN, nida mahaifinki mun kasance masu wata irin zuciya,masu butulci kuma wa'enda basu da godiyar Allah,, nan da nan ta fada mata komai tun daga auren Umma da Mal Sule har rannar da suka rabu" Mubeena ta fashe da kuka,kuka take sosaii haka ma Umma. Mubeena tana kuka tace "Umma dama na fad'a miki, na fad'a miki cewa Abba ba shine mahaifina ba!" Umma cikin tsawa tace " shine mahaifinki ! Abba shine mahaifinki! , shine yaso ki a lokacin da Mal sule ya k'i ki har yake ik'irarin cewa ke ba 'yarsa bace, shine ya ciyyar dake, ya tufatar dake, ya baki ilimi, daidai da rana d'aya bai tab'a nuna bambanci a tsakaninku ke da 'yan'yansa ba,, sabanin Mal Sule da ya firta da bakinsa kar na sake ko da wasa nace ke d'iyarsa ce , wanda shine sillar gurguncewa k'afarki, wanda besan cin kiba, besan shan kiba, besan wahala kiba, besan komai naki ba! Abu d'aya ne ya miki a rayuwa, shine sillar zuwan ki duniya , amma bayan haka ba abinda ya tsinana miki a rayuwa, wallahi kome Mal sule ze miki yanzu in aka d'auke Silan zuwanki duniya dayayi baze ko kusa yi miki abinda Dr Muhammad ya miki ba,, Mal Sule ya amsa sunan sa na cewa shine ubanki wanda ya haife ki kawai, amma ko kusa baze amsa sunan , wanda yayi wahala dake tun kina yar gwililuwa har yanzu, wanda ya ci dake, ya sha dake,ya tufatar dake,ya baki ilimi ya kuma baki tarbiya, Shine ya cika sharud'an zama uba wanda uban naki wanda ya haife ki ya kasa cikawa!(Ta sassauta murya ta) amma Mubeena kar abinda nida Iya muka fad'a miki ya sa ki tsani mahaifinki, ko kusa kar ki fara domin in badan shiba baza kizo duniya ba!....ta k'arasa maganar cikin sheshek'ar kuka. Kukan Mubeena ya k'aru sosai, tama kasa magana, sai sheshek'ar kukan data keyi,,, Umma ta kalli Iya dake ta faman sharbar kuka tace "Iya kiyi hak'uri ban fad"i maganar ba dan ta b'ata miki rai, gaskiya ce kawai na fad'a, Iya tace" baki b'ata min rai ba Ma'u, gaskiya ke kike fad'i, nayi dana sanin abinda na aikata a baya"" Ma'u tace "Iya bakiyi mana komai ba Iya wannan maganar ta huce saboda ni tun d'ad'ewa da kika nemi gafarata na yafe miki, dama ko baki nemi na yafe miki zan yafe miki dan wallahi ni tamkar Uwa na d'auke ki!" Ga wannnan ta aje mata bandir din yan dubu d'aya(1) sannan tace "gobe insha Allah zan aiko miki da sauran abinda kike buk'ata, kuma insha Allahu za mu dinga ziyartar ki akai- akai. Iya ta rik'e hannunta " Ma'u tsaya na fad'a miki wani abu,, yau tsawon shekaru goma(10) kenan ban sa Sule a idona ba, tunda yazo yace min ya tafi birni cirani na nuna ban amince ba amma sam ya k' jin maganata ya tafi ya barni, be kuma waiwayata ba, ko yana da rai? Ko ya rasu? Allahu a'alam,, amma dan Allah in Allah ya had'a ku dan Allah ma'u ku yafe masa ke da Aiha (Aisha), ki kuma ce nima na yafe masa, dan ina ji ajikina kwanan ya kusa k'are da k'yar na k'ara kwana a duniya ,nima ku yafe min Allah ya had'a fuskokin mu a aljana..." ta fashe da kuka,,,,jikin Umma da Mubeena yayi sanyi sosaii Mubeena tayi dauriyar cewa "ni na yafe miki Iya, kuma ki dena ambaton mutuwa insha Allahu zaki tashi, cuta ba mutuwa bace! " Iya ta girgiza kai "kayya! Suka mata sallama suna kuka tana kuka suka rabu. A gidan Mama ne, Mama ta kwantar da murya tayiwa Mubeena bayanin komai, Mubeena wani sabon kukan ta sake Mama na rarashinta, taji tausayin Ummanta sosaii sosaii ga wani sonta dake k'aruwa a zuciyarta,, sannan kuma taji tsanar Mal Sule a zuciyarta, ji take ba wanda ta tsana sama dashi..godewa Allah tayi daya bata uwa ta gari kamar Umma dan ita gani take tafi kowa dacen uwa a duniya! Haka suka koma gida dukkansu ba farin ciki da walwala.. ◆◆◆◆◆◆◆ Washe garin rana Allah yayi wa Iya cikawa,, su Umma sunji mutuwarta sosaii a wannan dak'in Allah yayi mata cikawa cikin dare. Da sassafe su Umma suka tafi suna ta kuka abun tausayi mussaman ma Mubeena, da 'yan gidan suka tafi gabad'aya har da Abba, dan shima yaji mutuwar dan ya santa, lokacin da 'aka kwantar da Mubeena a asibiti da cutar polio ta sameta,,sai da suka fara sauka a gidan Mama sannan sukaje gidan marigayiya Iya,, a lokacin ma ko wanka ba'a yiwa gawar ba, Umma da taimakon Mubeena su suka wanke gawar tas aka samata likafani aka fita da ita ,maza suka sallaci gawar aka kaita kuhewarta , Allahu akbar Allah kasa mu cika da imani, ka bamu kyakyawan K'arshe Ameen ya Allah.. Ba wani zaman makoki akayi ba tunda wa za'ayiwa gaisuwar? Dama Mal Sule ne kawai d'an data haifa kuma baya nan bai san ta rasu bama, 'yayan mijnata kuwa Bashir da Hauwa sun dad'e da dena kulata bama sa k'asar gabadaya. A 'yan- uwanta kuwa ita kad'ai tayi ragowa duk sun rasu,, sai dai sauran dangi da ba'a rasa ba..Masa'udu dama shi ake yiwa gaisuwar dan shine ya kula da ita tun data sami rashin lafiyar har ta warke, shima kuwa a rannar data rasu admission dinsa ya fito yaci Ahmadu Bello unibasiti zaria(ABU zaria) dan haka ya had'a kayansa ya tafi Umma kuwa kud'i me yawa ta bashi tace yayi harkar makaranta dashi ya yafi yana ta godiya. [12:35AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:46AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [135]-[140] Bayan an dawo hutun tak'aitacen lokaci. Aysha Amatulah: to barkan mu da dawowa. Hajiya Mubeena shin wai ta yaya kika tsunduma cikin harkar zane- zane? Mubeena: To agaskiya nidai na taso ne kawai na gani inayi, a lokacin inga abu ya min kyau sai na zana shi, cikin ikon Allah kuma sai kiga zanen ya fita sosaii...lokacin da ina primary kuma in kika duba littafai na na arts zaki ga inaci sosaii, koda merit za'a bada ma a Art ni ake bawa. Kuma akwai Yayana Ya Ameen shine ya cigaba da ban kwarin gwiwa har nazo matakin danake yanzu. Aysha Amatullah: madalah, to kafin ki fara wanan zane-zanen mene burinki a rayuwa? Mubeena: Burin na da shine na zama likita dan nima na bada gudunmawa ta wajen yak'i da wannan cutar sai kuma Allah beyi ba. Aysha Amatullah: to Allah zaba mafi alheri, meye ya fi b'ata miki rai da kuma abinda yafi faranta miki rai? Mubeena: Abinda ya fi b'ata min rai guda biyu ne na d'aya ya shafi personal life dina, na biyun kuwa shine, idan naga yan'uwana masu wannan cuta ta polio suna bara ko kuma suna cikin wani hali na rashin gata a gaskiya raina na sosuwa kuma ina iya k'ok'ari na dan ganin na taimake su. Sannan abinda yafi faranta min rai shine, ina tuno irin nasororin dana samu a rayuwa, sannan kuma ina ga masu irin cuta ta wato polio basa fuskantar wani k'alubale a rayuwa ,suna jin dadin rayuwarsu sannan suna samin gata daga wajen iyayensu dama al'uma baki d'aya, to nakan ji raina yayi fari . Aysha Amatullah: Allah sarki, yanzu zamu d'auki waya guda biyu(2) duba da yanayin lokaci, zaku turo sak'o ne ta wannan lambar 064**** sannan zaku kira mu ta 064****. Mutane an kira an mata fatan alheri, an kuma turo sak'oni ba adadi. Aysha Amatulah:wani kira zaki yi ga iyaye da kuma masu cutar polio? Mubeena: kiran da zanyi shine dan Allah iyaye su dinga bada yayansu a dinga musu d'igon rigakafi, sannan iyaye su dage su dinga gano talent din da suke dashi su k'arfafa musu gwiwa, bawai su dinga barinsu suna bara ba, da sauransu. Sannan irina masu wannan cuta ta polio, ganin suna da nakasa kar hakan yasa su fidda rai da rayuwa , su d'age suyi karatu suma su zama wasu a dinga damawa dasu, in hakan ya faru zan fi kowa farin ciki. Aysha Amatullah: to duba da yanayin lokaci mene sak'on ki na k'arshe? Mubeena: to Alhamdulilah ba abinda zance sai in godewa Allah da kuma iyayena nakan ji farin ciki sosaii in na tuno da iyayena,yayena da k'anina, da sauran dangi. Aysha Amatulah: to masu sauraron mu lokaci yayi halinsa , anan zamu k'ark'are wannan shirin, Hajiya Mubeena muna godiya da kika amsa gayyatar mu, da fatan duk sanda muka sake neman ki zaki amsa kiranmu. Mubeena: to nima nagode masu saurarona da kallona ina muku fatan Alheri,(tayi murmushi) sai anjima. Ahaka aka gama shirin, ta fito driver yaja suka tafi. *********** A yau ne aka d'aura auren Ameen Muhammad Ameen da Fatima Adam, Aisha Muhammad Ameen(Nana) da kuma Saifulahi Abdalah. Ansha biki sosaii an kuma kashe kudi dai-dai misali, Mubeena kuwa lemukan nan da'aka bata kyauta su ta bada akayi hidimar biki da su, sannan katuwar jaka da calanda me sunayen Allah ta musu a matsayin gudunmawa sun sha murna tare da yi mata addu'ar Allah ya saka mata da alheri. Bayan biki aka kai amarya Nana gidanta dake Hotoro, Sannan amaryar Ya Ameen Faty aka kaita gidan ta dake Janbulo. A yau su Mubeena sukayi final exam dinsu, sunsha kukan rabuwa da dalibai, Mubeena da Asiya ma ansha kuka, malamai sunyi bak'in cikin rabuwa da Mubeena sosai , hadda masu kwala, bayan sunyi sharing contacts driver yazo ya d'auki Mubeena suka koma gida, Mubeena cike da kewayar dalibai, malamai dama makarantar baki d'aya. Yau ta kama rannar lahadi kuma dama duk Lahadin k'arshen wata sukan je shopping... Suna cikin mota dan zuwa shopping d'in Abba ne ke driving dan yau yace sha'awar driving yake saboda ya d'ad'e beyi ba, Umma na gaba, yayin da Husna, Amir da Mubeena ke bayan mota Ummi kuwa taje bikin 'yar aminiyata. Suna tafe cikin raha da anashuwa. Can wata mota ta taho da gudun gaske, dai-dai lokacin da wani datijjon mutum yazo tsalaka titi, ai kuwa fuu motar ta bige shi, bata ko tsaya ba drivern mota ya k'ara falawa da gudu, cikin 'yan sakani aka dena hango motar sai k'ura da motar ta tayar... shikuwa dattijon mutumin nan yana baje a titi jini sai zuba yake. Abba da sauri ya fito daga motar yana salati suma su Umma suka fito dan ganewa idonsu, a firgice suka k'araso wajen da mutumin ke kwance cikin jini, Umma da ta k'araso wajen da sauri, dora idonta akan mutumin keda wuya ta kwala wani k'ara anan ta fad'i k'asa sumamiya! Lik [11:47AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [130]-[135] Nan take wajen ya d'auka sai ihu akeyi su Husna dake gefe sai dariya suke yi dan sunsan Mubeena yau ta shak'i haushi itada ko hannunta bata san wani namiji ya tab'a, sai gashi yau k'aton arne ya d'aga ta, shikuwa Ya Abdul ji yake kamar yaje ya wankawa Mr Mike mari dan haushi. Da kyar ta samu ya sauke ta k'asa, ai kuwa sai tabar wajenshi ta koma d'ayan banganren, sai d'aukanta hoto ake. Certificate aka bata ta, sannan aka buk'aci ta sa hannu taje ta saka kuwa, sannan aka mik'a mata shi, bayan nan aka shiga raba kyautuka ga wanda suka yi participating kyauta kuwa ta samu kala-kala, kamfaanin wani shahararen lemu ya bata da kuma sauran participant's d'in kud'i da kuma lemuka, kyauta dai iri-iri ta sha su wai kuma aka samun tab'i ne dan ba'a bata babbar kyautar tata ba. Check na miliyan d'aya(1) aka bata daga hukumar da suka shirya gasar sannan kuma k'ungiya masu zane dake kano suka bata kudi naira dubu d'ari(100). Mr Mike ne ya d'auko wasu sarkok'in medal's guda uku(3) 'yan k'anana d'aya na gold d'aya na silver na ukun kuma na bronze. Ta uku ya rataya wa bronze medal aka fara tafi ana d'aukan hotuna, sannan ya kira Ahmad Huzaifa ya rataya masa na silver, shima aka d'au tafi. Bayan nan kuma wakilin gwamnati ya tabbatar mata da cewa bayan ta kammala karatun sakandire gwamntani zata d'auki nauyin ta taje tayi course din zane a wata makatantar zane-zane(art school) dake amurka(America) Na gold din kuwa Mubeena ya ratayawa nan waje ya k'ara d'aukan ihu 'yan jarida nata d'aukan hoto da kuma hoto mai motsi(video) domin a yawancin kafafen yad'a labarai ta talabijin abin live ake nunawa. Su Abba dake zaune suna kallo LIVE murna a wajensu kamar me, sun ma rasa me zasuyi saboda murna, hak'k'ika wannan rana tana cikin rana mafi farin ciki a rayuwarsu, mussaman ma Umma da alk'warin da tayiwa Mal Sule ya cika yau, a zuciyarta cewa take dama Mal Sule ya ji ko ya ga wannan abin alherin. Bayan an kammala taro aka rufe taro da add'ua, nan aka fara d'aukan hotuna dasu Uncle Hashim da bakinsa ya kasa rufuwa saboda farin ciki, su Ya Abdul ma haka, kana ganinsu zaka gane irin halin da suke ciki. Zanen kuwa tafiya Mr Mike zeyi dashi, inda za'a kai shi wannan babban ART GALLERY dake Abuja. Su Alhaji Bawa basu so hakan ba dan su sunfi san a barshi a Art gallery din dake kano amma ba yadda suka iya. Fitowar su Mubeena ke da wuya wakilan 'yan jarida da gidajen radio sukawo mata caa akanta, sai tambayoyi suke mata tama rasa wadda zata amsa, can dai tace "Alhamdulilah ba abinda zance sai godiya ga Allah da ya bani nasara a wannan gasar, sannan ina godewa iyayena da suka bani k'warin gwiwa har nazo matakin dana ke yanzu! Nagode.". Tana gama fad'an hakan tayi hanyar motarsu. Zwan ta keda wuya ta tadda wakilan wani shahararen gidan TV suna jiranta, numfasawa tayi tace "wannan shine anyi gudun gara an tadda zago". Nan suka shiga yi mata magiya akan suna so su tautana da ita gobe, saboda gobe ne ta kama rannar masu cutar polio da duniya wato (WORLD POLIO DAY) wato ashirin da hud'u ga watan oktoba(24th october) bata musu musu ba kuwa ta amsa sunyi farin cika sosaii inda suka bata wani kati na gayyata. Farin ciki ya dawo sabo sanda suka koma gida su Umma hadda kukan murna, Ya Ameen dake can k'asar holland ya sami labari daya duba news ya kira su aka sha murna, makarantarsu kuwa dayake tana final year suka ce sun d'auki nauyin ta har ta gama su waec da neco duk zasu biya mata, saboda ta fito da sunan makarantarsu, bayan k'ananun kyaututuka da suka bata. Yau ta kama 24th october(World polio day), tun da safe ta ta shirya driver ya kaita dan Ya Abdul ya tafi wajen aiki. Tana zuwa dama ita suka jira, aka shirya komai tazo ta zauna akan kujerar da za'a tautauna da ita.(wasu gidajen radio suma sun juno dan masu saurarun radiyo suma suji) Me gabatarwa ta fara: Assalamu alaikum warahamatul lahi ta'ala wa barkatuhu masu kallo da sauraranmu. Barkan mu da sake saduwa a wannan shiri na mussaman da muke gabatarwa duk a rannar polio ta duniya duk shekara. A yau shirin namu yayi babban kamu, domin yau zamu tautauna da AISHATUL MUBEENA Muhammad Ameen, wadda itama ta zamo polio victim ta farko tada fara lashe gasar zane-zane dake gabatarwa duk bayan shekara hud'u a jihohi dama k'asa baki d'aya... Sunana Aysha Amatullah wadda zan gabatar da shirin, Hajiya Mubeena ko nace Artist Mubeena barka da zuwa. Mubeena: Barka kadai. Aysha Amatullah: shin zamu iya jin tak'aitacen tarihin ki? Mubeena: To Alhamdulilah, nidai sunana Aishatul Mubeena Muhammad Ameen an haifeni a garin Kano na taso a Kano, kuma a yanzu haka inada shekara sha bakwai next year zan shiga sha takwas(18), saboda ban fara makaranta da wuri ba yanzu dai ina ss3 a sakandire. Aysha Amatullah: Masha Allahu, shin kina shekara nawa wannan cuta ta sameki? Kuma mene ne dalili? Mubeena: A gaskiya wannan cuta ta same ni ina 3-4 years, dan dama kinsan a yara masu shekara d'aya zuwa biyar(1-5) tafi kamawa..kuma a gaskiya zan iya cewa wannan cuta kaddara ce daga Allah, dama can Allah ya riga ya rubuta cewa a haka zan tashi, cutar zata same ni. Aysha Amatullah: to madalah, wani kalubale kika ko kike fuskanta? Mubeena: Alhamdulilah a gaskiya nidai k'alubalen dana fuskanta be huce lokacin da ina k'arama ba, lokacin danake koyan tafiya, amma bayan haka ban fuskanci wani k'alubale ba gaskiya. Aysha Amatullah: to masu kallo da sauraranmu, kunji yadda hirar mu ke kasancewa, yanzu zamu je hutun tak'aitacen lokaci Share Comment as: Publish Preview No comments: Post a Comment MissHafcy View my complete profile About Me ► 2017 (16) ▼ 2016 (34) ► November (1) ▼ October (33) WELCOME ASMAUL HUSNA 6 ASMA'UL~HUSNA ASMAUL~HUSNA 4 ASMAUL~HUSNA 3 ASMAUL HUSNA 2 ASMAUL HUSNA AISHATUL MUBEENA 155-160 AISHATUL MUBEENA 145-155 AISHATUL MUBEENA 110-140 AISHATUL MUBEENA 85-105 AISHATUL MUBEENA 60-80 AISHATUL MUBEENA 45-60 AISHATUL MUBEENA 30-40 AISHATUL MUBEENA 20-30 AISHATUL MUBEENA 1-20 WANI HANIN END! WANI HANIN 26-27 WANI HANIN 24-25 WANI HANIN 22-23 WANI HANIN 20-21 WANI HANIN 19-20 WANI HANIN 15,16,17&18 WANIN HANIN 12,13,&14 WANI HANIN 11 WANI HANIN 9&10 WANI HANIN 7&8 WANI HANIN 5&6 WANI HANIN 3&4 WANI HANIN 2 WANI HANIN 1 .... WANI HANIN Blog Archive Miss_Hafcy. Watermark AISHATUL MUBEENA 145-155 [12:37AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MSS HAFCY ®ONLINE HAUSA WRITERS [140]-[145] Abba cikin rud'ewa ya d'auko wayarsa yayi dailing numbern drivern asibitin shi, ya mai kwatacen inda accident d'in ya faru, yayinda ya d'auki Umma ya sata a motar su, su Mubeena kuwa duk sun rud'e. Sai da suka jira Motar asibiti tazo, da taimakon mutanen wajen aka sa mutumin a Mota suka bi bayan su Abba dan zuwa asibiti. Emergency aka shige dasu, Umma kuwa bata dad'e ba ta farfado dan haka aka kaita resting room, shikuwa mutumin likitoci suka duk'ufa akansa ana duba shi. Bayan Umma ta farfad'o ta dawo dai-dai sai kuma kuka, kuka take sosaii tama kasa magana, Abba dake gefenta sai lalashinta yake, su Mubeena kuwa suna reception suna jira. Abba cikin sanyin murya yace "Asma'u wai meya faru ne? Kinada alak'a da mutumin nan ne ko kuwa me? Daga ganin mutum sai ki yanke jiki ki suma, ke da kike da hawan jini, Allah ya taimaka ma jininki be hau sosaii ba.....Asma'u magana fa nake miki kin min shiru, kukan nan ba abinda ze amfana miki dashi fa". Umma kasa magana tayi kawai sai runtse idonta tayi tana kuka a hankali, wata Nurse ta shigo sanye da kayan Nurses ta kalli Abba " Doctor, Dr.Faruk ya gama dubashi mun samai bandage da komai, yanzu ma mun canza masa daki, kuma da alama ya dawo hayyacinsa ma, Abba ya kalleta "okay nurse Sadik'a, muje d'akin naga jikin nashi" zumbur Umma ta mik'e tana k'ok'arin binshi, Abba ya juyo da mamaki " Asma'u ina zaki?", ta kalleshi "inda zaka je" murmushin tak'aici yayi, sannan yace" to muje", yana gaba, tana binshi a baya har suka isa zuwa d'akin mutumin. Yana kwance idonshi na kan celling sai zubar da hawaye yake yi, Umma ta k'araso wajen sa a nutse, tace "ya jiki?" yana had'a ido da ita ya kauda kansa cikin muryar sa da bata fita yace " Ma'u yau gizon naki da kike min hadda magana? Kodai mafarki nakeyi? Ina ne nan?. Ma'u tayi wani murmushin tak'aici sannan tace "ba mafarki kake ba, kuma ba gizo nake maka ba, kalle ni da kyau kagani, nice dai Ma'u mahaifiyar nakashashiya, nice dai Ma'u wadda ka tsana kake hantara saboda kawai ta haifa maka d'iya mace kuma nice dai Ma'u wadda ka wulak'anta daga k'arshe ka sake ta, nice dai Ma'u tsohuwar Matar azzalumi MALLAM SULE, ta fashe da kuka.. Abba ya dafa kafad'arta yace "ya isa haka Asma'u muje gidan ki d'an huta, anjima ma dawo muyi maganar (ya kalli Mal Sule, Allah ya k'ara sauk'i) suna k'ok'arin fita ya kalleta yace, "and inaso ki share hawayenki", ta kalleshi "toh" sannan ta share hawayen, Abba yace to muje ta shige suka tafi. Bayan sun shiga gida Umma kai tsaye dakin ta ta shige ta kwanta, zuciyarta fal da tunane-tunane kala-kala, Mubeena ta turo kofar d'akin ta shigo, a kan gado ta tadda ta tayi tagumi, Mubeena ta zauna a bakin gadon tace " Ummana wai meya ke damun ki ? Waye wannan mutumin? Meya miki? Har ganinsa ya sa ki suma? Umma ta juyo ta kali Mubeena sannan ta dafa kafad'arta tace " Mubeena wannan mutumin bakowa bane illa MAHAIFINKI Mal Sule! , Mubeena ta zaro ido "mahaifina kuma?" Umma tace " tabbas" Mubeena ta d'an yi jim sannan ta tashi da sauri ta nufi d'akinta, tana zuwa ta haye kan gado ta fashe da kuka, a daren rannar kuwa gabad'ayan daga ita har Umma kasa runtsawa sukayi. Washegari........ Da sassafe suka tashi suka shirya gabad'aya 'yan gidan suka d'unguma suka tafi asibitin Abba, Mubeena cike da d'okin taje taga wannan babanta da baya santa. A kwance suka tadda shi, yau ma kansa na kan celling sai hawaye yake, daga ganin bayan damuwar dake tatare dashi akwai zafin ciwo ma, yana kallonsu ya kauda kai , Mubeena ta k'araso wajenshi da sauri dan ya bata tausayi sosai, bakin gadon shi taje ta zauna cikin sanyin murya tace "Baba ya jiki??? *****ku yi hak'uri na rashin jina da kukayi kwana biyu, wayata ce ta sami matsala shiyasa, Nagode.*** [12:38AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ [145]-[150] ©MISS HAFCY ®NWA Ya juyo cike da mamaki, cikin muryarsa da bata fita yace "Allahu Akbar, Alhamdulilah ashe akwai rannar da nima zanji d'an ko 'yar dana haifa ta kirani da Baba?" Mubeena tace " ai dama can kane bakso kaji ba da'ace kaso kaji da baka wulak'antani nida mahaifiyata ba" ya kauda kansa "hak'ika nayi kuskure babba na kasance mutum mara godiyar Allah, dan Adam butulu, ku yafe min dan Allah" ya fashe da kuka. Mubeena ta runtse ido sai hawaye ta kalleshi "ai saika fara nemin gafarar Allah domin Allah gafurur rahim ne" Abba yace "Mal ya jiki?" Mal Sule yace "jiki da sauk'i". Mal Sule yace " ni naga rayuwa, naga sakayata, Allah yaban 'ya mace amma fir nak'i gode masa sai ma sab'o dana dinga yi kala-kala, ya kalli Umma datayi shiru tana sauraransa, Bayan rabuwar mu dake, a k'auye duk inda na nemi aura ba'a bani, saboda abinda na aikata ya baza gari sosaii mutane sai suke kyamar hadda jini dani,,, rannar sai na yanke shawarar komawa birni wajen yayana Bashir, anan ya bani kudi da d'an dama yace naje na ja jari, naje na sami d'an k'aramin gida me d'aki biyu da bandaki na bud'e shagon kayan masarufi na sami mata na aura, amma shiru ba haihuwa data gaji tayi tafiyar ta, a tak'aice dai wallahi sai dana auri mata sunkai biyar(5) ciki harda masu ciki guda biyu2, wai dan duk su haifi d'an a gidana na rene shi ya zama d'ana, amma abin mamaki a cikinsu ba wadda ta tab'a haifar cikin a raye a mace suke haifosu. Daga baya auren ya gagara jari na ya cinye na zamonto banda komai,na koma gidan yayan nawa shima na tadda basa k'asar ma gabadaya,,, rayuwa tamin zafi abincin da zanci gagara ta yake, tun daga nan na fara nadamar abinda na aikata, nakuma tabbatar da cewa hak'in ku ne ku da Iya yake bina, na taho neman ku shine mota ta kad'e ni kuka taimakeni" ya fashe da kuka. Gabad'ayansu jikinsu yayi sanyi, kowa yayi shiru Mubeena cema ke kuka a hankali, ya kalli Mubeena 'yata ki yafeni, ki yafeni dan Allah kar na mutu da hakk'in ki akaina na cuce ki, na cutar da rayuwarki,(ya juya wajen Unma) Ma'u kema ki yafeni dan Allah, a lokacin da kike ce akwai rannar da zanyi nadama bazata min amfani ba ban yadda ba, sai gashi yau ga rannar nan tazo, ki yafeni, kuma dan Allah ki kaini wajen Iyata itama na rok'i gafararta, kar na mutu da hak'inta akaina" Umma tana hawaye tace "bakomai na yafe maka , Allah ya yafe mana baki d'aya, Amma Iya babu, Allah yai mata rasuwa, sai dai kan ta rasu tace ta yafe maka" ya fashe da kuka " wayyo Allah na iya ta rasu? Innalalhi waina ilaihi raju'un KAICONA! Na cuci kaina,, Umma tace "ga dai 'yarka kamar yadda na fad"a maka zata zamanto abar kwatance kuma duniya ta santa akan abin alheri to Allah yayi, yanzu duk shafukan jaridar daka duba zaka labarinta, gidan rediyo dana talabijin dama..." Abba ya katse ta "ya isa haka ! Me ya kawo wannan zancen kuma, komai ya wuce mubar maida hannun agogo baya". Ya kwantar da murya yace "kuyi hak'uri kai kuma tunda sun yafe maka har Iyan ma ta yafe maka, ka gode Allah,k a kuma cigaba da nemi gafarar a wajen Allah domin kamar yadda 'yarka ta fad'a ma Allah gafurur rahim ne"" Allah ya sawwak'e, mu bari mu tafi,(ya kallesu)"kuzo mu tafi" Mubeena ta share hawayenta tace "ni ku barni anan zanyi jinyarsa" da mamaki suka juyo "me?" Tace "cewa nayi zanyi jinyarsa" Mal Sule yayi tari "a'ah zan zauna nan ma nagode d'iyar kirki, Allah ya shi miki albarka, tace "amin, amma zan zauna d'in anan,,da kyar ya rok'e ta ta hak'ura tace zata bisu. Da kuma alk'warin kullum zasu dinga zuwa suna duba shi. Yau kimanin kwana biyar5 kenan da ganin Mal Sule, a ranna ta biyar d'in kuwa Allah yamai cikawa sun sha kuka sosaii da sosaii mussaman ma Mubeena data rasa Uba, haka dai suka sha kukansu su gaji suka daina. Tare dayi masa addu'oi kala-kala. ********** Admission d'in Mubeena ya fito nan da wata d'aya zata tafi America. Abba ne zaune a falonsa gefensa Ummi ce tana karanta jarida,,ya d'an yi jim sannan yace "nikuwa Hadiza wata shawara na yanke, amma bansani ba ko ke zata miki,, Ummi tace "tame fa?" Abba yayi gyran murya sannan yace "Akan yarinyar nan ne Mubeena kinsan admission d'inta ya fito nan da wata d'aya1 zata tafi America gashi shekara biyu 2 ne sai nake ganin kamar be dace mu barta ta tafi ba muharami ba,kuma kinsan ta isa aure shekara sha takwas da d'ori ai ba kad'an bane, dan haka na yanke wata shawara...... Ummi ta gyra zama tace "gaskiya ne wannan, amma shawarar me ka yanke?" Abba yayi murmushi " ina so zan had'a ta aure da Abdul- Hafeez ne!, kinga dama already an sa rannar Husna sai a had'a a d'aura auren tare! Ummi da mamaki tace "gaskiya ne, amma a gaskiya sai a kira su yaran aji ta bakinsu in sun amince falilahil hamd in basu amice ba kuma shikenan sai asan abin yi" Abba yace " dad'i na dake garaje baki tsaya kinji me zance ba kin tari numfashina, dama ya za'a yi na d"aura musu aure ba amincewarsu? Kuma bazan musu auren dole ba, yanzu dai je ki kira min 'yar uwarki Asma'u itama muji ta bakinta, Ummi a sanyaye ta nufi part d'in Umma ta kira ta suka nufo wajen Abba a jere. Abba yayi mata(Umma) bayanin abin itama tayi mamaki sosaii dan a ganinta Abdul ya wuce ajin Mubeena amma dai sai tacewa Abba Allah zab'a mafi alheri yaji dad'i sosaii. Abba dakansa ya d'au waya ya kira Ya Abdul ya kuma ce masa yazo yana son ganinsa, yace gashi nan, sannan ya sa Umma ta kira Mubeena suka zauna suna jiran Ya Abdul. Mubeena cike da fargabar ko wani laifin ta aikata.. Be dad'e ba ya shigo sanye da shadar light bleu, Abba ya kalleshi " kai dai Abdul Hafeez har yanzu baka girma ba?, kasa shadda manyan kayanmu na hausawa, kuma kana yawo kai a haka ba hula, ina hularka? Ya sosa k'eya "tana daki wallahi ina sauri ne dats y kaga na barta, yi hak'uri", Abba yace bakomai zauna nan muyi magana. Ya zauna, sai a lokacin ya lura da Mubeena dake kan kujera kanta a sunkuye kallo d'aya yayi mata ya kauda kai. Abba ya fad'a musu hukuncin da ya yanke,dum! Gabansu ya fad'i gabad'aya, Mubeena kuwa murza idonta anya ba mafarki nake ba? Ta fad'a a zuciyarta, shikuwa Ya Abdul suman zaune yayi yama kasa magana, Abba dayaji shirun yayi yawa yace "ya dai? Ya kukayi shiru?" Ya Abdul ya dage yace " Allah ya zab'a mafi alheri" Abba yace "Amin Alhamdulilah" kefa? Mubeena tace "Allah zab'a mafi alheri na amince, Abba yaji dad'i sosaii ya kuma cewa su Umma su fara shirya shiryen biki. Abba ne ya sanar da Ya Ameen shima yaji dad'i sosaii dan dama ya dad'e yana wannan tunanin, ya fad'a wa Faty matarsa dake d'auke da ciki itama tayi murna sosaii, ta kuma musu fatan alheri. Umma ta sanar da daginta, suma sukayi fatan alheri, dagin marigayi kuwa dama basan nan, kuma dama bama su wani saba ba dan in ta gansu yanzu ma bazata gane su ba. Shirye shiryen biki akeyi sosaii, amare kuwa suna ta shan gyra kala-kala Ya Nana da itama ke dauke da ciki itama ta taimaka musu da shawarari da magunguna da sauransu. Abin mamaki kuwa Mubeena da Ya Abdul har hira sukeyi sun fahimci junasu ba laifi. ◆◆RANNA BATA K'ARYA SAI DAI UWAR D"IYA TA JI KUNYA◆◆ A yau ne aka d'aura auren ABDUL HAFIZ MUHAMMAD AMEEN DA AISHATUL MUBEENA M. AMEEN akan sadaki dubu hamsin (50) da kuma na Husna Muhammad Amin da angonta Al'amin Jafaru akan sadaki dubu arba'in(40) .mutane dayawa sun hallaci d'aurin auren. Bayan d'aurin aure ba ai wata bidi'a ba yini kawai akayi sai kuma kamu kan d'aurin auren , dagin su Al'amin ne ma suka shirya dinner suka gayyaci amaryarsu Husna taci kwaliyarta taje kuwa. Mubeena kuwa kallo d'aya zaka mata kasan tana farin ciki, dan ta godewa Allah ba adadi saboda cika mata burinta da yayi. Ta kuma yiwa babanta da kuma kakarta addu'a sosaii. Sannan a kullum addu'ar tashine Allah ya basu zaman lafiya mai d'orewa.. An kai amarya Husna gidan mijinta sun sha kuka rabuwa da gida, Mubeena kuwa dama tana gida sai nan da kwana biyar (5) zasu lula k'asar America shima Ya Abdul cikin ikon Allah kamfanin dayake aiki suka tura shi wani course can America hakan yazo daidai, abinsu dagwas! Yau zasu tafi k'asar America kukan wajen Mubeena kuwa kamar me, dan a daren rannar kasa bacci tayi tana tunanin rabuwa da iyayen nata, amma ba yadda ta iya, idanuwanta kuwa duk sun kumbura saboda kuka.. Mr& Mrs Ameen, Abba, Umma, Ummi, Amir da Ya Nana sune suka musu rakiya zuwa airport,, da kyar aka banbareta daga jikin Umma, Umma na kuka itama tanayi haka suka rabu, Ya Abdul ya kama hannunta suka shige jirgi abinsu, nikuwa ina binsu a baya har muka shiga jirgi, jirgi ya lula damu sai k'asar America..... [12:39AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®NWA [150]-[155] Bayan sun sauka ne motar kamfanin su Ya Abdul tazo ta d'auke su ta kaisu masaukinsu, inda zasu zauna , gida ne d'an k'arami falo sai d'akuna gida biyu d'aya babba d'aya k'arami sai kuma tiolet da kitchen da dinning,,,Mubeena ce ta kai kayan d'akin dan gida baya bukatar gyra saboda ko ina tsaf dashi. Yayin da shi kuma Ya Abdul ya fita nearby restaurant dan yayo musu take'away ya dawo , a lokacin har ta fito daga wanka ma tana kan kafet tana sallah , gannin haka yasa ya aje abincin akan dinning shima ya shiga band'akin d'ayan dakin dan yin wanka da sallah. Ya d'an jima sannan ya fito sanyen da wando 3 quater iya gwiwa da riga armless, ya tadda ta tana kan kujera tana dana laptop din dake kan centre table,, ya zauna kusa da ita, ta juyo tace "sannu da fitowa Yaya" yayi d'an murmushi "yauwa Mubeena ya gajiyarmu?" Tayi murmushi "aiy ta tafi" yace "i see, me kike yi a system ne? Naga alama dai baki gaji ba" Tayi murmushi "A'ah Yaya kawai dai naga ba abinda zanyi ne shine nake duba school din da yanayinta, ashe ma next week ne za'a fara registration" yace "Gud Allah ya kaimu" tayi murmushi "Amin". Ya dauko musu abincin suka ci, sannan Mubeena ta shige d'aki dan shirya kayanta a wadirop (wardrob e) ta barshi nan yana kallo a Talabijin(TV). Da daddare ma fita yayi yaje ya siyo su pizza, shawarma, da roasted chicken, sannan da su ice cream, lemuka da yagut(yaghurt) ya shiga d'akin nata. Tana zaune akan dressing mirrow, tana taje yalwatacen gashinta, rigar bacci ce a jikinta iya gwiwa pink, tana da d'an kauri ba sharara ba, ya tsaya kawai yana kallonta, ita bata san ma yanayi ba, sai data duba mirrow din da kyau ta ganshi tsaye kunya ta kama ta sosaii tayi saurin d'auko hijab d'inta dake kan gado tasa, dariya abin ya bashi ma, yayi murmushinsa me ban shawa'a sannan a zauna kan carpet din d'akin had'e da aje ledojin hannunsa. Cikin sanyin murya yace "Mubeena" da sauri tace na'am, yace "sakko muci" ta k'araso wajen sannan ta duba ledodin, murmushi tayi "nidai shawarman nan zanci kawai na sha ice cream ya isheni, cuz dazu na ci abinci" yace "okay Gud." Ya d'an yi jim kamar zece wani abu can dai ya fasa ya aje mata ice cream d'in da shawarma d"aya sannan ya kwashi sauran ledodin ya tafi d'aya d'akin ya zauna ya cika cikinsa sannan ya koma falo ya d"an yi kallo dagabaya ya koma d'aki ya kwanta abinshi, itama kuwa rufe k'ofar ta tayi tayi kwanciyarta. Sai daya dad'e akan gado yanata tunane-tunane kala- kala sannan daga baya bacci b'arawo ya d'auke shi,,, Asuba ta gari ango mijin amarya Washegari da safe ta fito sanyen doguwar riga red da adon golden tayi bala'in kyau, da niyyar gyra gidan , da mamakin ta sai ta tadda wata mata tana shara da alama dai mai aiki ce, suka gaisa anan take fad'a mana cewa ita mai aiki ce sunanta Kim dayake matar nada faran faran nan da nan suka saba suna hira kamar dama can sun san juna. Tana gama gyran sukayi salama ta tafi, ita kuwa Mubeena wayarta ta d'auko ta sa number Husna ta kira ta, bugu uku ta d'auka, Mubeena tayi dariya " 'yar rainin hankali bakya neman mutane koh?" Husna tayi dariya " ke waketa ta neman mutane inata mijina, ai in gaya miki aure da d'adi wallahi" Mubeena ta bud'e baki "lallai Husna ko kunya bakyaji kike fad'an haka,ko kin manta ni surukar kice? Ta fad'a da zolaya,, Husna ta tuntsure da dariya " yo wayake ta surika a wannan harkar? Yauwa ban labari nasan Yayl Abdul daga gani baze yi sanya ba, wai shin ya kuka k'are ne?" Mubeena tayi tsaki 'ke ni banda lokacin ki, ki gaida mijin naki sai anjima" Husna tace "zeji yanzu ma jira na yake a d'aki" Mubeena ta kashe wayar tana dariya tayi mamaki sosaii yadda aure ya canza Husna matar da ko irin maganar akayi sai ta nuna bata san komai ba bataso ashe dai ashe dai. Yau kimanin sati d'aya kenan da zuwansu amma kuma har yanzu ba abunda ya shiga tsakinunsu sai dai su ci abinci wani sa'in tare suyi kallo amma dare nayi kowa ze tafi d'aki ya kwanta abinshi. Yau Mubeena ta fara zuwa makarantarsu tunda suka ganta nakashashiya suke ji da ita, dan su basa wulak'anta irinsu sai ka sonsu dasuke yi, hakan ba k'aramin dad'i ya mata dan ganin yadda mutane ke nan-nan da ita kamar wata 'yar sarki ko shugaban k'asa,, tayi k'awaye sosaii mata malamansu ma suna shiri sosaii da su. Ya Abdul shima ya fara zuwa wajen aikinsu, tare suke fita wani sa'in ma tare suke dawowa, wataran inda time itace ke musu abinci wani lokacin kuma sai dai su siyo ko kuma suje can wajen cin abincin su siyo. Yau ma kamar kullum bayan sallar isha, Ya Abdul yana zaune a falo yana kallon wani series film, Mubeena ta shigo falon sanyen da wata doguwar riga wadda ta kama ta ta kuma bayyanar da surar jikinta riga ta k'arbi jikinta sosaii, tunda ta shigo yake kallonta har ta lura ta sunkuyar da kanta cike da kunya, a haka ta k'araso har kujera mai facing dinshi ta zauna ta fara kallo abinta, shikuwa dena kallon yayi ya tsura mata ido cike da sha'awa data lura kallon yayi yawa sai kawai ta tashi ta nufi d'aki tayi kwanciyarta dan bazata iya jura kallon dayake mata ba,, shikuwa be ji dad'in tafiyar data yi ba, ya tashi ya kashe TV din ya nufi d'akinta har ze shiga sai wata zuciyar tace masa "aa" jiki ba kwari ya koma d'akinsa ya kwanta. Yau Friday, a gajiye ta dawo daga school wajen k'arfe biyar da rabi 5:30 gashi ba laifi an d'an yi zafin rana kad'an tana zuwa ta shige d'aki a kan gado ta cire kayanta, ta janyo towel ta shige band'aki dan ta watsa ruwa, bayan tayi wanka ta fito sanye da towel iya gwiwa ta tsaye a bakin gado tana taje gashinta, dai-dai shigowar Ya Abdul kenan ya tsura mata ido yana kallonta nan take yaji sha'awarta ta mamayeshi,ita kuwa sunkuyawa tayi zata d'auki ko mayafi ne ta rufa ai kuwa towel ya sauko k'asa ta zaro ido ganinta tsurara haihiwar uwarta a gaban Ya Abdul, da sauri ta sunkuya zata d'auka da sauri shima ya sa hannun ya janye da towel d'in, rungume tayi nan ya fara kissing dinta ta koina ita kuwa sai turjewa take tana bashi hak'uri, nan dai labari ya canza nidai rufe musu d'akin nayi na fito abina. A rannar dai ta sha wahala sosaii dan a rannar suka zama cikakun ma'aurata, sai shimata albarka yake yana kuma jin wani sabon santa a zuciyarsa itama kuma haka. Kwanci tashi sunkai shekara d'aya 1 a America suna zauna zama cike da so da kuma kyautatawa juna, sai dai 'yan abun da ba'a rasa ba, dan hausawa sunce zo mu zauna tamkar zo mu sab'a ne... Yau Mubeena ta tashi da wani zazzab'i me zafin gaske ga amai datake ta kwararawa tun safe Ya Abdul kuwa duk ya rud'e ganin ta a wannan hali,, d'aukanta yayi sukutum ya kirawo drivern motar kamfaninsu ya sata a ciki suka nufi asibiti bayan an duba ta anan ne aka tabbatar da cewa ciki gareta har na wata biyu 2 zokaga murna wajensu a rannar sunyi kwanan farin ciki. Dan dama sun daidai suna tsumaye da har sun fara damuwa ma ganin Mubeena shekara d'aya amma har yanzu shiru ba ciki, dan ita Husna ma har ta haifi d'anta santalele namiji yaci sunan baban mijinta. Basu je gida ba kuwa har yanzu Ummi ce tace subari sai ta haihu sai su dawo. Kullum tana samun kulawa wajen mijinta tana motsawa zece"meya faru?" Ita kuwa saitayi murmushi tace bakomai Yau Mubeena ta tashi da ciwon nak'uda cikin dare a rude ya kira drivern kamfaninsu yazo ya kaisu asibitin da take awo,, aka shige da ita d'akin haihuwa ba ta dad'e ba kuwa cikin ikon Allah ya sulub'o 'yayanta guda biyu maza. Aka sanar da uban 'yaya murna a wajensa kamar me, sai sumbatun murna yake yana kuma mamakin wai yau shine da 'yaya har guda biyu,, nan da nan aka sanar dasu Umma suma murna ba'a magana...Ya Abdul ya shirya musu tafiya kwana biyu da haihuwarsu suka dawo nan gida Naija. Yara tubarkalah masha Allah masu kamada Ya Abdul sak, kullum suda Mum d'insu suna samun kula sosaii sai bulbul suke abinsu. Ran suna yara suka ci suna Sulaiman da Muhammad anace musu SAHAL DA SUHAIL,, ansha shagali sosaii anci ansha don rannar murna ce, anyi rabo kayayaki ba'a magana,, kowa ya watse ciki da murna da kuma fatan Allah ya raya mana 'yayan mu Suhail da Sahal. Share Comment as: Publish Preview No comments: Post a Comment MissHafcy View my complete profile About Me ► 2017 (16) ▼ 2016 (34) ► November (1) ▼ October (33) WELCOME ASMAUL HUSNA 6 ASMA'UL~HUSNA ASMAUL~HUSNA 4 ASMAUL~HUSNA 3 ASMAUL HUSNA 2 ASMAUL HUSNA AISHATUL MUBEENA 155-160 AISHATUL MUBEENA 145-155 AISHATUL MUBEENA 110-140 AISHATUL MUBEENA 85-105 AISHATUL MUBEENA 60-80 AISHATUL MUBEENA 45-60 AISHATUL MUBEENA 30-40 AISHATUL MUBEENA 20-30 AISHATUL MUBEENA 1-20 WANI HANIN END! WANI HANIN 26-27 WANI HANIN 24-25 WANI HANIN 22-23 WANI HANIN 20-21 WANI HANIN 19-20 WANI HANIN 15,16,17&18 WANIN HANIN 12,13,&14 WANI HANIN 11 WANI HANIN 9&10 WANI HANIN 7&8 WANI HANIN 5&6 WANI HANIN 3&4 WANI HANIN 2 WANI HANIN 1 .... WANI HANIN Blog Archive Miss_Hafcy. Watermark theme. Powered by Blogger . More AISHATUL MUBEENA 155-160 ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY ®NWA [155]-[160]. ◆◆ BAYAN SHEKARA BIYU◆◆ Wani hadad'en falo na shigo falon babba ne sannan an k'awata shi da zane-zane kuwa kala- kala na paintings sai kamshi falon yake. A zaune na tadda Mubeena ta k'ara kyau ta k'ara k'iba ta k'ara fari,ta zama cikakiyar hajiya, tana zaune Sahal na hannunta shima ya k'ara girma kamaninsa da mahiafinsa sun k'ara fitowa, tana bashi abincin yara( Cereal), yayin da shi kuma Suhail na gefe akan wani mashin na wasan yara yana ta gwarancinsa, wata yarinya ta fito daga d'aki yarinyar tana bala'in kama da Ya Ameen, ganinta yasa Sahal da Suhali suka fara murna suna wangale baki, ta k'arso wajen Suhail dake kan keke, ta fara masa wasa, sannan ta kalli Mubeena " Anty Mubeena kawo na had"a masa cereal din na bashi " Mubeena tayi murmushi " zaki iya kuwa Namesy(dayake sunan Mubeena Ya Ameen ya samata) tace zan iya mana ina bawa Maama(k'anwarta) Mubeena tace "To wataran kya bashi shi na fara bawa kan na bawa Sahal anjima in yaji yunwa kya bashi" taui murmushi "yauwa anty Mubeena". Ya Abdul ya shigo shima ya k'ara zama babban mutum ya k'ara kyau sosaii kana ganinshi kaga wanda naira ta zauna masa,,, sanye da shadda golden yayi kyau sosaii, ya kalli Mubeena "Oya Momin twins time ya kusa yi fa mu kad'ai ake jira " tayi murmushi "sorry Dadyn twins kaga ni a shirye nake, Baby Sahal naga yana kuka da alama yunwa yake ji shine na had'a masa cereal na bashi, (ta mik'a masa shi) karbe shi na sa mayafi na, ya k'arbe shi yana masa wasa shikuma yana dariya, sannan yaja hannun Little Mubeena sukayi wajen mota ita kuma Mubeena ta d'auko mayafi da jakarta sannan ta d'auki Baby Sahal suka nufi wajen mota. Basu zame ko ina ba sai wata katafariyar makaranata koyon zane-zane wadda Aishatul Mubeena ta gina kuma a yau ne za'ayi taron bud'e makarantar. Isarsu keda wuya suka yi parking motarsu a filin parking sannan suka iso wajan da'aka tanada dan bak'i, mutane ancika kowa jiransu yake family din su gabad'aya suna can suna jiransu, sukai ta gasawa da mutane anata Allah sanya alheri. A kofar makarantar aka sanya wata igiya me bala'in kyau tasha ado aka zagaye gate din data ita, Mubeena rik'e da Suhail da Ya Abdul rik'e da Sahal suka k'araso bakin gate din yayin da Ya Ameen da Little Mubeena suka mik'a musu wani dan faranti d'auke da almakashi me shegen kyau, suka k'arba suna murmushi yayin da yan jarida suka kara matsowa dan daukan hotuna da rahoto, Mubeena ta karb'i almakashin Ya Abdul ya dafa hannunta suka kamo hannun 'yayan nasu suka dora akai mutanen dake gurin suka k'irga d'aya har zuwa uku sannan suka yanka igiyar, nan aka d'au tafi suka shiga cikin makarantar Su Abba suka bi bayansu sauran mutanen ma haka, dan ganin makarantar. Makarantar kuwa Masha Allah tayi kyau gashi komai da'ake bukata akwae, bayan mutane sun zagaya makarantar sukaita sa albarka anan ne kuma Mubeena tayi jawabi akan makarantar a karshe tace duk wani polio victim wato mai cutar shan inna dayake sha'awar harkar zane to ze shigo kyauta ne! Bata bukatar ko sisi daga wajen masu cutar polio nan mutane suka dinga tafawa suna shi mata albarka, daga baya aka koma akaci akasha sannan aka watse. Little Mubeena tabi iyayenta suka koma gida dan gobe Monday akwai school. Suna cikin mota kan hanyar dawowarsu gida, Mubeena ta kalli Ya Abdul dake tuka motar tace " Baban twins nikuwa zaka gane gidan su Yusran nan kuwa daka tab'a kai mu da d'adewa?" Ya d'an yi jim sannan yace "eh toh bari mu gwada" ya juya kan motarsa sannan yayi hanyar gida, sun sha wahala kam kan sun gane gidan sai da taimakon kwatance, abin mamaki kuma suka tadda gidan ya canza ya k'ara kyau an canza fasalin gidan ma, Mubeena na rik'e da Sahal Ya Abdul kuma na rik'e da Suhail, Mubeena ta fara shiga gidan shikuma Ya Abdul ya tsaya a kofar. Da sallama Mubeena ta shiga gidan, sai datayi salama kusan biyu sannan aka amsa, Maman ta fito sanye da doguwar riga tana ganin Mubeena ta fad'ad'a fara'arta da sauri ta k'araso ta rungume Mubeena da murnarta, sannan ta k'arbi Sahal " mashaAllah, shigo mana Mubeena sannnu da zuwa", Mubeena tace yauwa sannan suka shiga wadatacen falon gidan, Maman ta karbi Sahal tana tamai wasa shikuma yana dariya, Maman tace "sannu ke kad'ai ke tafe?" Mubeena tace "a'ah da mai gidana suna kofar gida" Maman tace "yo kuma kya barshi nan tsaye ya shigo mana, bari na lek'a nace ya shigo" Mubeena tayi murmushi toh, Maman ta lak'e suka gaisa sannan tace ya shigo, ta kawo musu ruwa da lemo sannan ta dawo ta zauna itama, tana rik'e dasu Suhail sai wasa take musu " ikon Allah Mubeena ashe har kinyi aure hadda 'yaya bamu sani ba" Mubeena tayi murmushi " eh wallahi kinsan sha'anin ne kuma ma kinga bayan biki mukaje can America mu yi shekaru kana muka dawo bamu dad'e da dawo bama" Mamn tace " Allah sarki Allah ya taimaka, naji dadin zuwan ku wallahi," , Mubeena tace "mungode, nikuwa ina Yusrah tunda muka shigo ban ganta ba" Maman tayi murmushi " tana can cafe d'insu itada k'anina Bello" Mubeena da mamaki tace "cafe?" Maman ta cigaba "aiy bayan zuwan ku d'inan kun mana abin alheri k'anina yayi amfani da kudin wajen yin harkar makarantarsa to dama Computer science yake karanta kuma yana shekarar k'arshe lokacin, to cikin ikon Allah sai ya gano cewa itama Yusrah akwai basira a fagen computer abu kamar wasa in ya dauko ze koya mata cikin ikon Allah sai yaga ma wani wajen ma tafi shi kwarewa ,to shine ya bada shawarar yana so ya bud'e cafe mukai cikwi cikwi da d'an abinda ya rage mana muka siyar akasai komai da'ake buk'ata ya bude shagon yanzu cikin ikon Allah shagon yana nan ya bunkasa, kuma sannan k'anin nawa ya samu aiki a wani babban kamfani,, har yayi aure ma, yana nan da matarsa hada d'a, ya gyra mana wannan gida nima yaban jari yanzu ina harkar bussiness na kaya ina sa ran ma a wannan shekarar zanje Dubai dan na saro kayan da kaina na kuma bud'e shagon, kunji ikon Allah koh? Mubeena tayi Murmushi" Alhamdulilah, amma gaskiya naji d'adi sosaii, Allah shine abin godiya, dama ance mahakurci mawadaci, kinga da bakuje kun k'ask'antar da kanku kunyi bara ba, Allah ya hore muku ya bud'a muku har kuma nasan kuna taimakon wasu, a gaskiya naji dadi Allah ya sanya alheri yasa albarka a ciki, dukansu suka ce "Amin" Ya abdul shima yayi murna kwarai da jin hakan, Mubeena tace "ina cafe d'in yake ?muje inga kawartawa" Maman tace "to muje in raka ku" suka fito a tare dan zuwa cafe din. A kan hanya ne Mubeena ta bata labari makarantar ta data bud"e yau, ba k'aramin dadi Maman taji ba ta kuma yi alkwarin zata ziyarci makaranta gobe. Sun d"an yi 'yar tafiya sannan suka isa wajen Katafaren shago ne babba shaguna uku ne aka had'e suka zama guda d'aya, asaman shagon an rubuta " YUSBELL INTERNET CAFE" suka shiga wajen ma'aikatan se aiki suke wajen fal da mutane customer's can ciki wani ya nuna musu yace Hajiyar tana can, suka k'arasa wajen. A kan wheel chair d'inta suka tadda ta tana dan system din dake gaban ta, ta k'ara cikowa ba laifi, ta zama 'yan mata, tana juyowa suka had'a ido da Mubeena ta saki murmushi, farin ciki ya bayyana a fuskarta k'arara, da mamaki tace "kamar Aunty Mubeena nake gani ko me kama da itace?" Mubeena tayi murmushi had'e da dafa ta "itace Yusra" Yusra tayi murmushi "sannu da zuwa Anty, nayi murna kwarai dana had'u da dake, ya bayan saduwa, nan suka fara hira Sun dad'e suna hira kana Mubeena ta bata shawarari sannan sukayi exchanging contacts, da kuma alkwarin zasu dinga ziyarta juna jefi-jefi, sukayi salama su Mubeena suka koma gida. ◆◆◆◆◆◆◆ Wasa-wasa dai makarnata tana ta samun budi makaranta ta sharara sosaii mussaman ma saboda k'wararun malaman da Mubeena da samo take kuma biyansu albashi me tsoka, itama kanta tana koyarwa in ta samu lokaci. Wani abin sha'awa shine yadda polio victims wato masu cutar shan Inna suke makaranta kusan kaso biyu 2 a cikin biyar 5 sune, wannan ba k'aramin dad"i yake sa Mubeena ba , saboda ita dama mussaman dan su ta bud'e makarantar. Ya Abdul shima yana ta samun cigaba da d'aukaka uwa uba ga mata ta gari daya samu, yanzu shima ya bud'e kamfaninsa na kansa, kudi suna ta shigo mai ya zama babban alhaji haddda su tumbi irin na manyan masu kud'i yayi(Lol). Mubeena ce zaune a d'akinsu Suhail bayan ta gama saka musu kayan bacci kowanensu ta kwantar dashi a gadonshi, ta tofe su da add'ua sannan ta musu good nyt ta kashe musu fitila ta kulo d'akin. Kai tsaye d'akinta ta shige ta watsa ruwa ta shafe jikinta da mai da turaruruka masu kamshi, ta taje kanta ta raba shi gida biyu ta d"auko wata arniyar rigar bacci da ita gwanda babu ta saka tayi brush ta kuskure bakinta da mouthwash sannan ta d'auko wani cewing gum me k'amshi pineapple ta wurga a bakinta tana taunawa a hankali, ta k'ara feshe jikinta da turare sannan ta kulo d'akin ta nufi d'akin Ya Abdul. A kwance ta taddda shi a kan gado ganin ta shigo d'akin yayi murmushi yayi ta karaso tana rangwada sannan ta kwanta gefensa ya jayota jikinsa "ya akai ne Hun?" Tayi murmushi "bakomai" ya kad'a kai sannan yace " i Luvv you soo much my dear wife, ur my everything," ta cakule shi a kumatu sannan tace "Me too my man,my husby, my heart desire, i soo much love you yaya nah, Allah ya barmu tare" yace "amin" had'e kashe musu wutar d'akin hakan yasa nima na fito nace: ALHAMDULILAH!!! Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai da yabani ikon kamala wannan littafi nawa me suna AISHATUL MUBEENA, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabmu Annabi muhammad (swa) da sahabansa da alayensa baki d'aya. SADAUKAWA: na sadaukar da wannan littafi ga d'aukancin masu Cutar Shan Inna(POLIO) dake fad'in duniyar nan musulmai....sannan ina kira da babbar Murya ga iyaye da su dinga bada 'yayansu ana musu d'igon rigakafi domin ance prevention is better dan cure, sannan ina kira ga gwamnati (Duk da suna iya bakin k'ok'arinu) da sauran masu hannu da shuni dake wannn k'asa tamu da su dinga taimakwa talakawa wad'anda wannan cuta ta riga ta lahanta, Alhamdulilah tunda yanzu an cire kasar mu Nigeria daga sahun k'asashen dasuke fama da wannan cuta amma duk da haka akwai mutanen da already wannan cuta ta riga ta musu illa a jikinsu, kuma basu da gata talakawane, ga kuma rashin sana'a sune a k'arshe suke k'arewa da bara-barece akan hanya saboda basu da hali basu da yadda zasuyi su ciyar da kansu balle har su samu suyi ilimi, ba sana'a sannan kuma ba kudi, kuma a cikinsu ana samun dayawa masu baiwa daban-daban(talent) amma saboda kulawa dasu da ba'a ayi ba'a gano hakan, Allah ya bamu yadda zamu iya ya k'arawa gawamnati dama sauran masu hannu da shuni damar taimaka musu Amin. Sannan wanda wannan cuta ta riga ta lahanta ina me jajanta musu da iyayensu Allah ya basu hak'uri jurewa kuma su sani bawai dan Allah baya san su bane ya dora musu wannan cuta A'A kawai dai kowanne d'an adam da abinda Allah yake jarabtarshi dan ya gwada imaninsa, to su jarabtar tasu kenan,, Allah ya bamu ikon cin jarabawar daya d'ora mana Amin... Ina godiya ga duk wandada suka bi wannan littafi tun daga farkonsa har zuwa k'arashe duk da tashon lokacin dana dauka kan na gama shi, ba abinda zance sai Allah yabar so da kauna da kuma d'akon zumunci.Amin Domin tsokaci ko kuma gyra kawai- 09097136605 Anan Ni Miss Hafcy nakece muku BISSALAM......s e mu had'u a sabon littafina nan gaba Nagode da kulawarku, LOVE YOU ALL Sh Comment as: Publish Preview No comments: An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT