CHEF ZEEY Love in the Kitchen Azizat Hamza Ga duk wata mace mai sana'a. Allah Ubangiji ya dafa miki...AMIN HAKKIN MALLAKA ©AzizatHamza2025 "Wannan littafi hakkin mallakar AZIZAT HAMZA ne. Ba a yarda wani ko wata su ɗaura shi a YouTube, ko a" "ɗaura shi a shafukan facebook ko website na novels, ko kuma a maida shi Film, ko a kwafi labarin ba tareda izinin marubuciyar ba. Yin hakan zai sa a ɗau mataki na shari'a." ®ChefZeey2025 Za ku iya bibiyata ta waɗannan Manhajojin: ArewaBooks: Azizat Hamza Wattpad: Azizat Hamza TikTok: Marubuciya Azizat YouTube: Marubuciya Azizat Hamza WhatsApp: 08137311900 Marubuciya Azizat Hamza Azizat Hamza Azizat Hamza CHAPTER ONE ZEEY "Sunana ZIYADA SADIQ HARUNA a.k.a CHEF ZEEY. Ofcourse na je culinary school, dan haka, I am a" certified Chef. Certificate ɗina ma yana cikin folder a ƙasan gadon Kaka. "A hankali nake duba littafin da ke gabana, a lissafin dana gama yi kuɗin buɗe restaurant ɗina saura Naira" "Miliyan huɗu da dubu ɗari takwas da saba'in (#4,870,000) kacal." "Kenan na tara Naira dubu ɗari da talatin (#130,000) a cikin Miliyan biyar da nake nema. Classy" "Restaurant da za a riƙa siyar da abincin gargajiya zalla a garin Zaria na ke son buɗewa, at least daga" yanzu zuwa ƙarshen shekarar nan na ke fatan haɗa kuɗin. Wannan shine babban burina. "Watanni shida da suka wuce account ɗina na Instagram ya tafi viral, wannan ya sa na fara samun 'yan" chanji daga tallace-tallace da nake yiwa ƙananun 'yan kasuwa irin masu siyar da spices da kayan kitchen haka. Duk wanda ya ga numbers ɗin social media accounts ɗina zai ɗauka na fara samun wasu maƙudan "kuɗaɗe, irin na BLOW ɗinnan. Amma gaskiyar shine, ZIYADA SADIQ HARUNA a.k.a CHEF ZEEY bata blow ba. Followers ɗina dai sun ƙaru, amma kuɗin fa sai a hankali, musamman saboda masu kawo tallace- tallacen sun mugun rena ni. Dan kawai sun ga abincin gargajiya kaɗai na ke yi, kuma bani da fancy kitchen irin na manyan Food bloggers da suka yi fice sai suke ganin ko nawa suka bani kawai in karɓa in yi godiya." "Ba laifinsu bane, Instagram gidan aesthetic ne, gidan kwalliya, gidan gayu, gidan ƙarya, so babu wanda" "zai ɗauki maƙudan kuɗi ya bawa wata ƙaramar Chef da ke girki da murhun itace ta yi mata tallen kayanta. Sun fi son masu fancy kitchen. Chef Zeey bata da fancy kitchen. Ni da nake zaune da 'yar tsohuwata muna fama da kanmu ina na ga ta fancy kitchen. Amma Alhamdulillahi, ɗan abinda na ke samu yana rufa mana asiri, ba ga ni kaɗai ba, har da mutanen gidanmu." """Adda Ziya, wai inji Mamana wai ki bata aron dubu ɗaya idan kina da shi""" A fusace na ɗaga idanuna na kalli yarinyar da ta shigo min ɗaki hanci duk majina tana sanye da wani babban zani babu ko riga a jikinta. """Yanzu dan iskanci Atika kike ko waye...""" """Assima'u..."" ta gyara min tana wani zazzare idanu. Hannuna na kai na kwaɗa mata biron da nake" rubutu da shi """Ban hanaku shigo mana ɗaki babu sallama ba. Ana koya muku tarbiyan da zai gyara muku rayuwa" "amma sai shegen taurin kai""" Yarinyar ta wani zuba mini idanu ko a jikinta. """Koma ki je ki yi sallama!"" Na daka mata tsawa. ""Jibeta fiska duk majina, za a tashi da safe iyayenku ko" "fiska ba za su wanke muku ba""" """Salaama Aleekumm"" ta faɗa da ƙarfi sannan ta shigo ɗakin" """Bakinki ne Salama Alekum ɗin ai. Wai waya aikoki nema? Eh?""" """Mamana""" Na kalli yarinyar da kyau ko zan gane daga wani balbali ta fito. Yaran da ke gidanmu sun yi yawan da ba "iya ganesu nake ba, musamman ma ƙananan." """Mamanki ita ce, Amaryar Baffa Zakari?""" Sai da ta ja hancinta ina ganin green ɗin majina da ya maƙale mata a ƙofar hancin ya koma sannan ta ce """eh""" """Zo zo zo ki wuce ni bana son ƙazanta"" na jawo purse ɗina na cire gudan dubu ɗaya na miƙa mata. Na" "san idan dubu ɗayan nan ta fita ta fita kenan. Kaf matan gidan wacce ta ke da ɗan ƙoƙarin biyan bashi idan ta karɓi aron kuɗi a wajena Anty Hafsah ce, amma duk sauran idan zan fara lissafin ɗari biyu yau, ɗari biyar gobe, dubu ɗaya jibi da suke karɓa aro ba sa biya, ina ga sai ya cika littafi." A yanzu haka a FaceBook page ɗina ina da followers dubu saba'in (70k followers) FaceBook shi nafi "samun followers saboda a nan na fara food content ɗina. Sai kuma Instagram da nake da followers dubu talatin da takwas (38k Followers). Kar ku sha mamaki idan na ce muku a cikin wata shida na tara followers dubu talatin ɗinnan. Na yi shekara biyu ina posting a Instagram, ina samun followers kaɗan- kaɗan da ƙyar na haɗa 8k followers. Then, Boom!, wani video dana posting ni da Kaka muna yin kwaɗon rama da zogale sai ya tafi viral. Ban san mutane na son abincin gargajiya ba sai a wannan videon. Shikenan Instagram ɗina daga 8k followers sai ga shi wai video guda ɗaya tak ya kawo min mutane dubu talatin, har yau ina mamakin abin nan." Shi kuma YouTube na buɗe shi last year ne lokacin dana lura duk manyan food bloggers dana ke bibiya "sun koma can kuma kowa na faɗin YouTube suna bada kuɗi sosai. Kai! YouTube ya bani wahala, sai na" ɗaura video ya yi wata ban samu 1k views ba. A haka dai na yita gurgurawa har na samu 2k subscribers a shekarar amma kuma ban zama monetized ba saboda haka bana samun kuɗi. A YouTube dai videon "dana yi na Alalen gwangwani shi ya jawo na samu 6k subscribers a wata shida, ya zamana ina da 8k subscribers kenan kuma na shiga YouTube Partner program amma har yanzu saboda bana samun views ban samu adadin kuɗin da za su fara biyana ba." "TikTok kuma gidan rikici ne, har kirana suke da 'yar Talakawa a comment section, ko su kirani da 'yar" "gargajiya. A can followers ɗina yanzu haka sun kai 52k followers. Tare na buɗe da YouTube amma shi gudu yake kamar me. Ya ma fi Instagram saurin samun followers. Amma taron yu-yu-yu ne a can, dan wani lokaci har rufe comment nake saboda jarrabarsu. A TikTok har hashtag ɗin #ChefɗinTalakawa aka bani, da ka saka Chef ɗin Talakawa a TikTok videos ɗina zaka fara gani. Ban damu ba, dan ni ɗin Talaka ce, ni ɗin marainiya ce dana taso a hannun Kakata..." * Ina cikin buga lissafi Kaka ta kwala min kira daga tsakar gida """Ziyadatu, ba za ki fito ki wuce makaranta ba?""" """Kaks, Ina zuwa"" na faɗa ina rufe littafin dana ke lissafin kuɗi a ciki. Can ƙasan akwati na saka saboda" "'yan gulma da ɓarayin cikin gida. Idan kana zama a babban gida komai za ka yi sai kana taka-tsantsan. Idan aka san ina tara kuɗin restaurant ai labarina sai ya shiga kowani balbali a gidan nan, sannan masu karɓan aron kuɗi duk za su bi baya su zo su karɓe ɗan abin dana tara. Dama tunda aka ga na fara samun alkhairi a social media shikenan kowa ya saka mini ido." Black handbag ɗina da ke rataye jikin ƙusar da ke kusa da window na ɗauko sannan na ciro handouts "ɗina a ƙarƙashin pillow na sa a jakar. Jiya ina cikin karatu na yi bacci. Allah na gani ba zan iya tuno komai cikin abinda na karanta ba, komai ya gudu. Ƙarfe goma muke da test ɗin so na san dai ko a cikin Keke ne kafin na isa school zan ɗan yi bitar wasu abubuwan. Tunda na samu carryover biyu a shekarar farko na yi alƙawarin ba zan sake wasa da karatuna ba." "Jarrabawar soyayyar dana faɗa a lokacin ya sa na samu Carryover biyu a Level One, ban ma ɗauka zan" "cigaba da karatun ba saboda yadda na lalace a lokacin. Amma dana farfaɗo daga ciwon so sai na yiwa kaina karatun ta nitsu, babu ni babu soyayya har sai na cimma burina. Babban burina a rayuwa a yanzu shine: 1- na gyara shashin Kaka. 2- na buɗe restaurant. 3- na kammala Degree lafiya." "Sai dai at this point komai ma is proving to be difficult. Karatuna na shirin ƙwace mini, kuɗin restaurant" "ya ƙi haɗuwa, gyaran gida kuma... na gyara mana banɗaki daga pit zuwa water system, at least na ɗan yi wani abu ai..." Lokacin dana fito daga ɗaki sai na tarar Kaka tana tankaɗe garin Masara a tsakar gida. """Kaks, Tuwo za ki mana ne yau?""" """Garin da Ladidi ta aiko tun kwanaki ne na ce barin yi tuwo da shi kar ya lalace""" """Kaks, lallai a gaishe ki, kusan wata huɗu fa kenan da Umma ta aiko miki garin nan""" """Lah! na manta inda na ajiye ne. Sai jiya da yamma na gani a cikin jan Fantekan da ke ƙasan gado""" Wani tsumma da ke saman igiyar shanya na jawo na ɗisa ruwa daga butan Kaka da ke bakin ƙofar ɗaki na fara goge baƙin flat shoe dana saka dan ya yi ƙura sosai. "Ina gama gogewa na yar da tsumman dan sai wani maiƙo-maiƙon datti ya ke min a hannu, ko uban me" ma aka gobe da shi sai Allah. Na wanke hannuna da sauran ruwan da ke butan na yiwa Kaka sallama. """Kaks na tafi"" na faɗa ina ɗaga mata hannu." """A dawo lafiya, Allah ya bada nasara ya kuma kaɗe fitina""" """Amin, Kaka"" na amsa ina ficewa daga sashenmu..." *** JAYKAY A hankali ya ke saukowa daga matakalar da zai sadaka da babban falo. Meeting ya ke da shi da wasu investors ƙarfe tara na safe. Hajiyarsu ce a falon ita kaɗai tana shan green tea. """An fito"" ta faɗa lokacin da ya gaisheta" """Yes""" "Zama ya yi a kujera yana saka agogo yace ""Ina Janan?""" """Ai ina ga bata tashi ba"" Hajiya ta faɗa tana kurɓan tea ɗinta." """Bata tashi ba?"" ya duba agogon hannunsa, ƙarfe takwas ne na safe har da minti bakwai" """Kaima ka san halinta ai"" Hajiya ta faɗa tana ajiye mug akan saucer." "Miƙewa yai zai tafi ta kira shi ""Jamal""" Tsayawa yai cak ya kasa motsi yayinda ƙirjinsa ya fara cunkushewa yana masa wani suka. """Afuwan! Jalal, maganar Plaza ɗinnan ne, na ce har yanzu ba a yi komai akai ba""" "Sai da ya ɗau kusan sakan talatin yana ƙoƙarin saita nitsuwarsa kafin ya juyo ya kalleta ya ce ""idan na" "dawo za mu yi maganar, ban manta da Plazar ba""" "Hajiya ta sake ɗaukan mug ɗin da ta ajiye ta ce ""to sai ka dawo ɗin""" Wucewa ya yi ba tareda ya sake cewa komai ba. Yana fita ya shiga mota Direba ya ja mota suka bar cikin gidan. Sai da suka yi nisa da gidan sannan ya saka hannunsa a ƙirji yana furzar da iska. A duk lokacin da Hajiya ta yi suɓutan baki ta kira shi da Jamal sai hakan ya tuno masa da wannan mummunan rana da komai na rayuwarsa ya chanja. Shekaru uku kenan amma kullum ya tuna da wannan mummunan rana sai zafin abun ya dawo masa sabo. Duk sadda Hajiya ta kira shi da Jamal ji ya ke yi kamar gazawarsa ya sa ta ke auna shi da sunan ɗan'uwansa. Wataƙila hakan shi ya ke sanyaya mata zuciya. Wataƙila idan ta kira shi da Jamal zai rikiɗa ya koma Jamal ɗin na gaskiya. He was never her favourite. Jamal shine perfect son. Ɗan Albarka. Wanda kowa ya ke alfahari da shi a family. Ba zai taɓa mantawa da abinda ta faɗa masa ba ranan da ya ce mata zai auri Cassy. """Jamal ba zai taɓa kawo min suruka wacce bata Sallah ba"" abinda ta faɗa kenan, and it breaks him." Lokacin da aka saka bikin Jamal ta fi kowa farin ciki. As if a lokacin ne ɗanta zai fara aure. She was all "over the place tana ta shirye-shirye, yau Dubai, gobe India, jibi China, tana ta siyayyan biki." Lokacin aurensa da Cassandra saboda ma kar a yi auren tana kusa barin London ta yi ta wuce Nigeria. Jamal da Daddy ne suka zo kotun da aka ɗaura aurensu. Bayan auren Hajiya bata sake saka baki a maganar auren ba sai lokacin da Cassy ta haihu da ta zo ganin yaro. A lokacin ne ta maimaita masa abinda ta faɗa ranan da ya zo mata da maganan Cassy. """Kai da baka zama ka san dai kwacokam tarbiyyansa yana hannun uwarsa ko"" ta ƙare da faɗin ""Allah ya" "bashi hasken musulunci"" tsabar sanyin jiki bai iya amsa addu'ar ba. Jamal ne ya amsa yana yiwa yaron" "wasa yana faɗin ""Hajiya kar ki damu, Ni da hannuna zan riƙa tafiya da yaron nan Masallaci"" yai maganar" yana dariya. "Jamal kenan, Sarkin dariya. Har yanzu yana iya tuno sautin dariyar Jamal na ƙarshe a duniya." """Yallaɓai mun iso"" Direbansa ya faɗa ganin Ogan nasa bai fito daga motar ba minti biyu bayan ya yi" parking a parking space na Kamfanin. """Thank you, Abdullahi"" Jalal ya faɗa bayan ya farfaɗo daga duniyar tunani da ya tafi." Yana shiga Kamfanin mutane suka fara gaishe shi yana ɗaga musu hannu har ya shiga elevator ya wuce 7th Floor inda office ɗinsa ya ke. Yana zuwa Sakatariyarsa ta gaishe shi ta ce masa baƙin da za su zo sun iso. Karɓan file ɗin hannunta ya yi ya shige cikin office ɗinsa. Ƙaton Hoton da ya yi tozali da shi a office ɗinne ya sake tuno masa da rashin dacewarsa da wannan office ɗin. Kowa ya sani ba shi ya dace ya mallaki wannan office ɗin ba. Mamallakin Office ɗin Jamal ne. Shi yasa ya kasa cire hoton tun shekaru biyu da ya amshi ragamar tafiyar da kamfanin. Ji ya ke kamar idan ya cire hoton Jamal zai gani. Sannan Hajiya ba za ta ji daɗi ba. Shi ya sa ya kasa cirewa. Amma a kullum ya shigo office ɗin ya kalli hoton sai gabansa ya yi ras! Zama ya yi a kujera ya gyara tie ɗinsa sannan ya buɗe file ɗin da Sakatariyarsa ta bashi dan ya duba takardun kafin ya wuce ɗakin da zai gana da baƙi. Haka ya gama duba takardun har ya kai wajen da aka rubuta sunansa JALAL KABEER MAIYAƘI. A baya sunan Jamal ne a wajen ba nasa ba. A baya Jamal ne zai yi signing a wajen ba shi ba. """JayKay"" aka kira shi." Ya ɗago idanunsa ya kalli ƙofar. Mr Munir ne abokin Jamal kuma CFO na kamfanin. """Time"" ya faɗa yana nuna masa agogon hannunsa." """Oh, yes"" yai saurin saka biro a wajen sunansa ya yi signing. Sannan ya miƙe hannunsa riƙe da file ɗin ya" bi bayan Mr Munir suka fita. Za ku iya bibiyata ta waɗannan Manhajojin: ArewaBooks: Azizat Hamza Wattpad: Azizat Hamza TikTok: Marubuciya Azizat YouTube: Marubuciya Azizat Hamza WhatsApp: 08137311900 CHAPTER TWO ZEEY Ina jin Lecturer ɗinmu yana cewa kowa ya dena rubutu na ja wata siririyar tsaki a zuciyata. Haba Jama'a! Ta ya mutum zai iya amsa Questions uku masu 'ya'ya a minti shabiyar. Shima dai wannan Malamin ba so ya ke mu ci course ɗinsa ba. Allah na gani Question ɗaya na amsa da ƙyar. Kwata-kwata ba inda na karanta mutumin nan ya fitar ba. """Zeey, me kika rubuta? Ni fa babu abinda na sani, Ban rubuta komai ba"" Bestie na Faty ta faɗa gaba ɗaya" "ta rikice. Course ɗin da muka gama rubuta test ɗinsa 3 credit unit ne, kuma mutumin ba shi da mutunci." """Nima an gaya miki na rubuta wani abun kirki ne. Ke dai kawai Allah ya taimakemu ya bamu Assignment" "mu ɗan samu wani abu a nan in ba haka ba CA ɗin Dr Farouq zero za mu samu""" """Ni kinga gaba ɗaya wannan bikin da aka yanka mini ya bi ya hana ni karatu. Sai da na cewa Baby ya bar" "bikin nan sai na gama Makaranta""" """Tabɗi! Abeg! Gara da aka sa mana shi nan kusa, kinga next year idan za mu yi graduation kina nan da" "cute Baby girl ko Baby boy"" Faty ta kai min duka na sa mata dariya." "Fatima Jibril, ita ce Bestie na a gaba ɗaya duniya nan. Idan aka ce in kira sunan ƙawa guda ɗaya da zan so" "mu yi ƙawance har tsufa, to Faty zan fara kira. Faty mutum ce, Faty na da mutunci overrrr. Ba a iya shaidar mutum 100% saboda ɗan Adam ajizi ne, but gaskiya zan bawa Faty 99.9% cewa mutuniyar kirki ce." Za ku ɗauka mun jima tare da ita but a wajen registration muka haɗu lokacin muna Level One. Right "from day one muka clicking and tun daga lokacin Faty ta zame mun ƙawar arziƙi. Ko lokacin da matsalar soyayya ta sakani a gaba Faty was there for me. Lokacin da abubuwa suka mana zafi ni da Kaka Faty ta bani taimakon da ba zan taɓa iya biyanta ba. Lokacin dana fara ɗan posting video a FaceBook sama-sama haka, Faty ce ta bani ƙarfin gwiwa ta ce na cigaba watarana page ɗina zai yi girma har na fara samun kuɗi. Ita ta sa na fara posting a Instagram saboda ni lokacin ina ma na samu kuɗin datar da zan shiga IG. Faty za ta mini sub ɗin data ta ce Zeey ki dinga Posting a Instagram ɗinnan watarana za ki blow. Faty ce ta bani shawarar na je culinary school a Kaduna na koyi girki Professionally." "Kada kuce na cika ku da labarin Faty, gaskiyar shine, without Faty wataƙila da babu Chef Zeey." Ƙarfe uku muka baro cikin school. Kasuwa muka wuce saboda Faty ta ce za ta duba wasu kaya. Bikinta saura sati shida yanzu. Mun jima a kasuwa. Bamu muka dawo ba sai ana kiran Magariba. Na riga na kira Kaka na faɗa mata ina gidan su Faty dan haka bani da matsala. Ba wani kayan arziƙi muka siya ba duk yawace-yawacen da muka sha a cikin kasuwa. Sai da muka ci abincin dare kafin ta rakani har titi na hau Keke na taho gida. Ina zuwa ƙofar gidanmu na samu su Baffa Lawalli da Baffa Zakari da wasu maƙotanmu akan tabarma suna cin tuwo. Na haɗe fiska zan shige ba tareda na gaishe su ba Baffa Lawalli ya kira sunana. Na waske na ɗan risina na gaishe su. """Daga ina haka?""" """Gidan su ƙawata Faty, na rakata kasuwa ne siyayyan biki""" """To a kula, banda yawon dare""" "Har na shiga zaure ban dena jin haushin maganarsa ba, wai ""banda yawon dare"". Ƙarfe takwas ne fa" yanzun. Kumama in ba neman magana ba ai ya san su waye masu yawon dare a gidan. 'Ya'yansa ne ba na kowa ba. A ƙofar ɗaki na tarar da Kaka tana zaune akan tabarma ta kunna radio tana ji. Wasu jikokinta kusan su "biyar suna gefe ta zuba musu tuwo a tray suna ci. Kullum abin kenan. Babu mai bawa Kaka naira biyar a gidan nan, amma da zaran ta yi girku sai su sako zugan 'ya'yansu su zo su cinye mata abinci." """Kin dawo?""" """Kaks, Na dawo"" na faɗa ina rataye gyalena a kan igiyar shanya. Wata ƙaramar kujerar katako na jawo na" "zauna na ce ""Kaks, kin ci abinci kuwa?""" """Dama na ce in jiraki ko za ki ci tuwon idan kin dawo mu ci tare""" """Kai Kaka! Kin san dai dole zan ci abinci a gidansu Faty""" """Garin na da kyau kuwa, Tuwon yayi danƙo sosai, barin zubo mana kema ki taɓa""" """Ki zubo to, amma kaɗan zan ci""" """Kaka Altine a ƙara mana miya"" wata daga cikin yaran da suke cin abinci ta faɗa tana turo tray ɗin gaban" Kaka da ta tashi za ta zubo mana tuwo. """Wallahi sai kun cinye gayan tuwon nan tas! Babu miyan da za a zuba muku. Oya ɗauki tuwon nan ki" "ajiye muku ku cinye"" na daka mata tsawa" """Adda Ziiyaa, dan Allahhhh""" """Barin saka musu kaɗan""" """Kaks ba za a ƙara musu komai ba. Nan gaba za su koyi yadda ake managing miya, ko kuma suje balbalin" "iyayensu a basu miyar a can""" Wayata ce ta fara ringing a jaka na ciro sai na ga sunan Alhaji Nafi'u. Na ja tsaki ina mayar da wayar jakata. Lokacin da Kaka ta zubo mana tuwo na wanke hannuna na fara ci. As usual tuwon ya yi daɗi. Girkin Altine mai tuwo ne fa. Kakata ta kaina. "Altine mai Tuwo ake kiranta, sama da shekara hamsin tana sana'ar sai da Tuwo. Tun kan ta yi aure ta ke" "taya mahaifiyarta sana'ar sai da Tuwo a Kano. Da ta yi aure a nan Zaria kuma, tun tana Amarya da ta fara sana'ar bata dena ba har sai da iftila'in jinya da tsufa ya hanata. Da sana'ar Tuwo ta gina kanta, da shi ta aurar da 'ya'yanta, da shi ta siyawa kanta daraja a wajen kishiyarta. Na ta so na ga Kaka tana siyar da Tuwo dan haka da kuɗin Tuwo Kaka ta reneni ta sakani a Makaranta." "So, idan na ce muku tuwon Kaka daɗinsa daban ne, to ku yarda kawai." "Ni dana ce kaɗan zan ci tuwon, sai ga shi da ni aka cinye shi tas. Dana gama ci na tattare wajen sai na je" na ɗaura ruwan wanka a 3kg gas dana siya mana kwanaki. Da ruwan ya ɗan yi lum-lum sai na juye na kai banɗaki na yi wanka. Lokacin dana fito daga wanka sai Kaka ta ce min wai Baffa Lawalli yana nemana. Tsaki na ja dan na san maganar ba zai wuce aron kuɗi ba. Kayan baccina riga da gajeren wando na saka sannan na ɗau ƙaton hijabi na sa a kai sannan na wuce ɓangarensu. "Mutum shi ba wata sana'ar kirki ba ya je ya zauna ya tara mata uku shi kaɗai, ga yara kullum haihuwarsu" ake. Allah dai kawai ya shirya. "Ɗakinsa na shiga bayan na gaishe da Uwargidansa Maman Suwaiba da ta ke tatar kamu a ƙofar ɗakinta," wajen duk ya yi caɓal-caɓal da ruwa babu kyan gani. """Baba, Barka da dare"" na gaishe shi bayan na tsugunna." """Barka da dare Ziyadatu, ya Makaranta?""" """Lafiya, Baba""" """Kin kusa gamawa ko?""" """Eh, daga mun gama wannan semestern za mu shiga ajin ƙarshe""" """Allah ya taimaka""" Na amsa da Amin. """Ɗan ƙara mini gudun fankan nan""" Ina tashi zan je na ƙara gudun fankar Nepa 'yan tsiya suka ɗauke wuta. """ 'yan iska, Yaushe ma suka kawo wutan har sun ɗauke"" Baffa Lawalli ya faɗa da ƙarfi kamar a ofishin" NEPA na ke aiki. Na dawo na zauna ina Allah-Allah ya yi ya sallameni. Ina gani ya fara neme-nemen mafifici bai samu ba. """Jummai, Jummai, ina mafificinkun nan ne?"" Ya ƙwalawa matarsa kira. Itace matarsa ta biyu. Ina ga yau" "girkinta ne. Matansa duka uku gatan ɗaki ɗaɗɗaya suka samu da su da 'ya'yansu, duk wacce ta ke da girki ita ce za ta shigo ɗakinsa ta kwana. Manyan yaransu Maza kuma na kwana a ɗakin Zaure." Har yau idan rikicin gidan ya tashi aka fara faɗan gado za ka ji matar Baffa Zakari tana mitar ai Baffa "Lawalli shi kaɗai ya cinye gidan, ɗakuna huɗu ya take shi kaɗai." Ni bana tunanin an shatawa Babana fili a gidan da sunan gado. Ina ga tun da ya rasu suka haɗu suka "laƙume filinsa da ke gidan. Shi ya sa fa nake son na samu kuɗin kaina. Bana so ko kaɗan na shiga maganar gado. Wanda ya ga zai ci ya ci, ai Allah ne ya ce a bayar idan suka cinye za su je su haɗu da Ubangijin da ya ce a raba gado." Ina tsugunne duk ƙafafuwana sun yi tsami Anty Jummai ta shigo ta duba masa mafificin a saman ƙaramin tsohon TV da ke ɗakin. Ta miƙa masa mafificin ta fita. Ina nan sai haɗa gumi nake cikin hijabi shi kuma ya dage sai fiffita ya ke bai ce da ni komai ba. "Sai can ya ce mini ""Yawwa! Ziyada ban sani ba ko akwai kuɗi a wajenki ki bani aron dubu hamsin""" Na zaro ido cike da mamakin yadda ya kira dubu hamsin ɗin kaman ya taɓa bani ajiya. """Baba, gaskiya babu kuɗi a wajena. Kwanaki na biya kuɗin Makaranta da su""" """To, to, ko dubu ishirin ba za a samu ba?""" "Na haɗe fiska na ce ""babu""" """To shikenan, je ki""" Na miƙe ina lissafin maƙudan kuɗaɗen da na ke binsa bashi har yau babu ranan biya. Ni Ziyada na sake bashi aron dubu hamsin. Allah ya kiyaye... "Har zan fita sai ya ce "" Wancan Alhajin da ya ke zuwa wajenki har yanzu kuna tare ko?""" """Baba na sallameshi"" na faɗa da ɗan ƙarfi dan bana son ya sa rai da Alhaji Nafi'u." """Kin Sallameshi saboda me?. Mutumin arziƙi Azumin da ta wuce rabin buhun sugar da katan ɗin taliya fa" "ya kawo mana""" """Ni dai na sallameshi"" na sake jaddada masa dan kar ya sa rai da kwaɗayin kuɗin Alhaji Nafi'u" Bai ce min komai ba nima na fita. Ina zuwa sashenmu na cire Hijabi na hau gado na kwanta na shiga CapCut na fara editing videon da zan ɗaura gobe. Saboda school yawanci a weekend na ke yin shooting ɗin video idan na samu time sai na editing na ɗaura. Sau biyu a sati na ke ɗaura recipe amma wani lokaci na kan ɗan ɗaura random vidoes na wasu abubuwan ko kuma idan Kaka tana wani abu sai na ɗauketa na ɗaura. Letter *Z* ne ya popping a saman notification bar ɗina. Ina ganin Z zuciyata yai wani ras. Ko ban duba "wa ya turo min ba, na san mutum ɗaya ne ke chatting ɗina da suna haka." Ban buɗe ba na cigaba da editing da nake yi sai ga wani saƙon ya shigo """Na san ba ki yi bacci ba, zan kira, plzzz ki ɗauka""" Ko gama processing kalmomin ban yi ba kiransa ya shigo. Na bi screen ɗin da kallo har yau ban chanja sunan dana saving contact ɗinsa da shi ba *My Ameen❤* Sai da ta kusa yankewa sannan na ɗauka amma na yi shiru... *** JAYKAY A gajiye ya shigo gidan. Today was super hectic. Amma Alhamdulillahi akwai positive response daga investors ɗin da suka zo. Idan har sun gama shawara there's possibility sati mai zuwa za su turo Lawyers ɗinsu a zo a yi yarjejeniya. Lokacin da ya shigo gidan main parlour ɗin babu kowa dan haka sai ya shiga ɗakin Hajiya ya sameta tana "sallar Magariba, bai jirata ba sai ya wuce nasa part ɗin dan ya yi wanka ya chanja kaya. Da ya fito daga banɗaki sai ya buɗe closet ɗinsa zai ɗau kaya, tsayawa ya yi cak yana kallon wajen, wasu kayan bacci guda biyu da aka jera kusa da pyjamas ɗinsa ne ya tuna masa da cewa yana da MATA. Matar da ke wata duniyar bata da niyyar rayuwa da shi a inda ya ke. Shekaransa biyu kenan da dawowa Nigeria permanently da zama. A cikin shekara biyun da yai a Nigeria Cassandra ta zo masa Nigeria ne sau biyu. A shekarar farko ta zo ne lokacin Christmas ta tafi bayan New Year. Kwanaki 15 ta yi a Nigeria kullum sai ta tuna masa da hakan. A shekara na biyu kuma ta masa kwana 10. Wannan shekaran ma ya sani bata da niyyar zuwa sai ƙarshen shekara kamar yadda ta saba." Yana tura mata ɗansu Junior London ya je ya mata vacation idan aka yi hutun Makaranta. Yanzu kamma "kamar yadda bata damu da yaron nasu ba shima yaron ya fara jin daɗin Nigeria, bai damu da rashin mahaifiyarsa kusa da shi ba. Idan ba an yi hutu ba baya ma maganar zai je London." "Wai shikenan, a haka za a cigaba da auren?." Ba zai iya abandoning Kamfanin da mahaifinsu ya kafa ya koma London ba. Balle ma bashi da wani "identity yanzu a can. Idan ya je baƙin cikin abinda ya rasa ne zai hana shi sukuni. Gara yana nan Nigeria kusa da Hajiya, kusa da ƙanwarsa ɗaya da ta rage masa. Kusa da 'yan'uwa da abokan arziƙi..." Wani baƙin comfy shirt mai laushi ya ciro ya saka ya haɗa da wata baƙar wando. Da alwalarsa dama ya fito saboda idan ya gaida Hajiya sai ya wuce Masallaci ya je ya yi sallar Isha. Lokacin da ya shiga ɗakin Hajiya sai ya samu ta idar da sallah tana jan carbi. "Ya gaisheta, ta amsa masa sannan ya ce mata zai je ya yi sallar Isha." "Ta ce da shi ""Muhammad yana ɗakinsa sai ka ɗaukeshi ku tafi tare"". Ya miƙe ba tareda ya ce komai ba ya" fita. Ɗakin Junior ya shiga ya kira yaron suka fito za su je Masallaci tare. Suna saukowa falo sai ga Janan ta shigo gidan tana maƙale da waya a kunnenta sai masifa ta ke yi. """Ya Jalal Barka da dare"" ta faɗa za ta haura sama ya ce mata" """Kin je office yau?""" """Na je manaaa"" ta faɗa sannan ta haura sama tana cigaba da wayarta." JayKay ya riƙe hannun ɗansa Junior suka wuce Masallaci... CHAPTER THREE ZEEY """Hellloo"" na faɗa da muryar bacci. Jiya ban kwanta da wuri ba sai ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Bayan" wayarmu da Yaya Aminu sai dana jima ina saƙe-saƙe kafin na samu na ƙarisa editing da nake yi. """Sayyada, ƙarfe bakwai saura baki tashi a bacci ba"" ai tunda ya ce Sayyada na ji duk wani baccin da ke" idona ya washe saboda ɓacin ran da ya taso mini. Haba! Sama da shekara ɗaya kenan amma mayen mutumin nan har yanzu bai iya kiran sunana ba. Idan "ba zai iya kiran Ziyada ba, to ya kirani da Ziya ko Zeey kamar yadda aka fi kirana da shi mana. amma ya wani kakaɓa mani Sayyada, kuma fa a hakan wai so yake ya aureni. Allah ya kiyaye na auri mutumin da ko sunana ba zai iya furtawa ba." Na haɗu da Alhaji Nafi'u ne a bakin ATM wata ranar Asabat ina cikin sauri zan cire kuɗi katin ATM ɗina "ya maƙale. Ga shi ranan Asabat, gashi ba ATM machine ɗin Bank da nake amfani da shi bane, ga shi ina" buƙatar kuɗi cash da gaggawa zan wuce Asibiti wajen Kaka. Haka na kama faɗin Innalillahi na rasa ya zan yi. Alhaji Nafi'u da shima ya zo cire kuɗi a ɗaya ATM ɗinne ya fito ya fara tambayata me ya faru. Na nuna masa machine ɗinne ya haɗiye min kati kuma ina buƙatar kuɗi. Haka ya shiga kwantar min da hankali yana faɗin za a iya resolving matsalar. Muka samu securityn Bank "ɗin muka masa bayani, ya ce mana gaskiya sai dai Monday mu dawo. Nan na sake rikicewa. Ƙarshe dai Alhaji Nafi'u ne ya bani aron kuɗin ya karɓi numbata ya kaini har gida daga nan muka wuce Asibiti. Ranan Monday ma sai ga shi ya zo har gida, ya ɗaukeni muka je Banki aka bani ATM card ɗina." Da zan mayar masa da kuɗin sai ya ƙi karɓa. Tun daga nan fa Alhaji Nafi'u ya manne min wai shi a dole sona ya ke. Tun day one da ya faɗi hakan na ce "masa bana ra'ayinsa ba zan iya aurensa ba, amma haka ya nace." Abinda ya sa ma ya fita min aka shine halinsa na burga da son nuna shi wanene. Ba wani kuɗi ne da shi ba amma sai shegen burga da kuma ƙarya. Wannan ya sa tun farko-farko na ce masa tafiyarmu ba zai yiwu ba. Amma kullum maganarsa shine ba zai taɓa haƙura da ni ba matuƙar ba aure na yi ba. Daga nan kuma ya fara cusa kansa wajensu Baffa Lawalli yana musu kyauta. Duk abinda ya musu sai ya faɗa min As if so ya ke na riƙa rubuta list ɗin alkhairin da ya ke yi musu ta dalilina. Idan 'yan mutuncina suna kusa na kan fita idan ya zo. Amma tunda muka yi faɗan ƙarshe da shi sai na dena fita. Ina godiya da alkhairin da ya yi mini a baya duk da ma ba ni ke tambayarsa ba ya ke yi. Amma tuni na haƙura da alkhairin Alhaji Nafi'u. Shi duk abinda zai maka to haka zai yi ta nanata maka ai ya yi maka kaza da kaza. Kyautarsa kullum tana zuwa da gori ne. Wannan ya sa fir na dena karɓan komai daga hannunsa tun ma kafin mu yi faɗa. Tsakanina da Alhaji Nafi'u babu yaudara. Tun ranan farko na ce masa ban amince da tayin soyayyarsa ba. Haka lokacin da yawan gorinsa ya isheni haka na zage na gaggaya masa maganganu na ce kar ya sake kawo min ko tsinke bana buƙata. Yai ta bani haƙuri amma ban sake karɓan ƙwandala daga wajensa ba. Wannan ya sa ya mayar da hankalinsa wajen yiwa su Baffa Lawalli hidima. """Sayyada, jiya ina ta kiranki kin ƙi ki ɗau wayata""" Ɗan tashi na yi zaune ina tsaki a raina. What is so hard a kiran suna ZIYADA """Alhaji Nafi'u me kake nema a wajena?""" """Allah Sarki Gimbiyata, ki yi haƙuri na tashe ki a bacci. Tun jiya na ke son jin zazzaƙar muryanki amma kin" "hanani""" "Na ɓata fuska na ce "" Alhaji idan baka da abin faɗa ni zan kashe wayata""" """Allah ya huci zuciyarki""" Chanjin muryarsa ya tabbatar min ya ji haushin abin dana faɗa. Ban damu ba tunda na masa kora da baki na masa kora da hali duka ya ƙi ya haƙura da ni. """Dama Baffanki Lawal ne ya kirani jiya ya ce na bashi aron dubu hamsin. To na tura masa kuɗin tun jiya" "na ji shiru har yanzu bai kirani ya ce min ya ga kuɗin ba""" """Kai! Innalillahi..."" na faɗa ina kama kaina. Wani irin zubar da mutunci ne wannan dan Allah. Shikenan" "'yan'uwan Babana babu abinda suka sani sai kwaɗayi, kwaɗayi, kwaɗayi." Saboda alkhairin da Alhaji Nafi'u ke musu ya sa na ke ɗan ɗaga masa ƙafa ban masa koran walaƙanci ba tuntuni. Kalmomin rashin arziƙin da Alhaji Nafi'u ya faɗa min watannin baya da tayin banzan da ya min ya ci a ce na yi nesa da shi tun da jimawa amma kwaɗayayyun 'yan'uwan Babana suna kashe mini gwiwa. Shi ya sa nake so na yi kuɗi. Shi ya sa nake so na buɗe restaurant ɗina. Shi ya sa nake so na fi ƙarfin walaƙanci. "Alhamdulillah yanzu ina samu, amma a lokacin dana ke cikin tsananin fafutukar ganin na gina kaina" Alhaji Nafi'u ya min gorin da ba zan taɓa mantawa da shi a rayuwata ba. """Sayyada kin ce ba za ki aureni ba. Ga shi dana ɗan riƙe miki hannu sai ki fara masifa. Mi kika ɗaukeni ne." "Watana nawa ina zuwa gidanku ina yiwa Baffanunki hidima amma ɗan kiss ɗinnan idan na ce ki min ba za ki min ba. Na san yanzu kin fara samun kuɗi kin fi ƙarfina, amma kada ki manta abubuwan dana yi miki a baya da wanda na ke yiwa 'yan'uwanki har yanzu...""" Kalamansa kenan a hirarmu ta ƙarshe a cikin motarsa. A ranan muka yi baran-baran na ce masa kar ya "sake zuwa wajena. Na ce masa ya lissafa duk abin da ya taɓa yi min Insha Allahu zan biya shi. Da ya ji haka sai ya fara bani haƙuri wai shi ba haka yake nufi ba. Dama halinsa kenan, sai ya gama min gori sai ya fara bada haƙuri." "Amma ranan kam ban saurareshi ba. Na shata layi tsakaninmu. Babu Ziyada, babu Alhaji Nafi'u." "A ranan bayan na shigo gida sai dana sha kuka kamar raina zai fita. Ban faɗawa Kaka abinda ya faru ba," na yi mata ƙaryar maraicin mahaifina ya saka ni kuka saboda abubuwanda su Baffa Lawalli suke min a gidan. "Yanzu ma cike da hawaye a idanuna na shiga Bank app ɗina na nemo account numbar Alhaji Nafi'u, dake" na taɓa mayar masa wani kuɗi da ya taɓa turo min na san ba zan rasa account ɗin a wajen History ba. Transfer ɗin Dubu hamsin na masa sannan na sharing receipt ɗin kuɗin ta whatsapp ɗinsa na rubuta "masa kuɗin da ya bawa Baffana ne, amma daga yanzu kada ya sake yiwa wani nawa hidimar kuɗi da" sunana. Kuɗin dana tara zan yi hidimar bikin Faty da shi na tura masa. "Ba nauyin kuɗin nake ji ba, ɗacin abinda Baffa Lawalli ya yi nake ji." "Ta ya zai je ya roƙi Alhaji Nafi'u aron kuɗi, Fisabilillahi!." Ina ganin kiran Alhaji Nafi'u na shigowa wayata na yi saurin katse kiran na dannawa numbarsa BLOCK. Wannan shine karo na ƙarshe da zan entertaining ɗinsa a rayuwata. Zafin maganganunsa na ranan suka sake dawo min. Wato idan ba zai sameni a mata ba to ya sameni a karuwarsa. Duk wata hidima da ya taɓa mini a baya ba dan Allah bane. Shi ya sa nake son yin kuɗi domin na tsira daga jarrabawar Talauci. Tun dana taso ina da himmar neman kuɗi. Ko shi Alhaji Nafi'un sai dai in ƙarya zai min ban taɓa "tambayarsa naira ɗaya ba, kuma ba da 'yan chanjin da ya ke bani na dogara ba." Ni fa a kan neman Halal babu aikin da ba zan iya ba. Kafin na zama CHEF ZEEY ɗin da aka sani yanzu ina da tarin backstory na irin ayyukan dana yi saboda in samu kuɗi. Lokacin ina Secondary daga JSS 1 har zuwa SS2 na yi aiki a Restaurant har guda biyu. Na yiwa wata mata Bayarabiya mai abinci aikin wanke-wanke da shara da serving customers. Da ta zo ta bar anguwarmu sai na koma wani fancy Restaurant da ake cewa Zikk's Foods. A nan na yi aiki a kitchen ina musu girki. Lokacin da Kaka ta dena Tuwo idan aka samu aikin yin Tuwon biki ni na ke zuwa na yi musu. Tukunya ko namba nawa ne ina tuƙawa babu matsala. Har yanzu part of side business ɗina bayan food content ana iya ɗaukana hire na je na yiwa mutane abinci. "Akwai wata Anty Shukura da muka yi aiki da ita a Zikks Foods tana da Catering service yanzu, idan aiki ya" samu tana kirana. Sannan daga Instagram da wata mata ta mun magana in zo har gida in koya mata abincin gargajiya sai na fara faɗawa mutane za a iya hiring ɗina koyar da girki. I'm not lazy. Ni ZIYADA bani da lalacin neman kuɗi. I Have To. Ina neman kuɗi ne saboda gudun walaƙanci. Saboda gudun mutane kamar Alhaji Nafi'u. Because ko Sule "ɗaya namiji ya baka one way or the other sai ya maka gori. Kaɗan ne masu yi dan Allah, babu gori, babu" walaƙanci... Raina a ɓace na fito daga ɗaki na ɗau buta na yi hanyar banɗaki. Kaka tana Dama koko a wani ƙaton bokiti. """Kin tashi. Ya ciwon kan?""" """Da sauƙi"" na shige banɗaki. Ɗazu da Asuba da Kaka ta tasheni sallar Asuba ce mata na yi kaina na ciwo" shine ta barni. Truly kaina na wani mugun sara mini ne tun jiya da dare da muka gama waya da Yaya Aminu. Dana fito daga banɗaki sai na ja ruwa daga rijiya na cikata butar na fara alwala. Kafin na gama yara har sun fara shigowa da kofi a hannunsu karɓan kunu. Na ja tsaki na shige ɗaki na shimfiɗa sallaya na tada sallar Asuba. Dana idar na jawo wayata na duba agogo ƙarfe 6:52AM. Allah ka yafe ni. Ban cika makara sallar Asuba haka ba. Kaka ce alarm ɗin dake tashina Sallah. Ko babu Alarm ƙarfe uku da rabi na yi tsohuwar nan take tashi ta fara hidima. jikinta ya riga ya saba da tashin dare. Addu'o'in dana saba na yi daga littafin Hisnul Muslim da ke wayata. Na haɗa da Salati da addu'ar RABBI "INNI LIMA ANZALTA ILAYYA MIN KHAIRIN FAƘIR. Wannan addu'ar ita ce sirrina. Sirrin rage mini ƙuncin Talauci. Da wannan addu'ar Food content creation ɗina ya fara bunƙasa. Tun daga lokacin dana fara ganin ƙarfin addu'ar, ban saketa ba har gobe. Da ita da addu'ar HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL sune sirrin samun nasarana." Na ɗan miƙe akan sallaya na shiga Instagram dan na yi replying DM's ɗina. Akwai wata mata mai siyar da spices a Kano da muka fara maganar zan mata talle ban sani ba ko ta ga reply ɗin dana mata jiya. Ina cikin danna waya Faty ta chatting ɗina ko na yi Assignment ɗin Dr. Bello na ce mata ban yi ba. Ba a jima ba Kaka ta ƙwala min kira ta ce na zo na juye ruwan wanka na. Muna da class ƙarfe 8AM amma a yadda maganar Alhaji Nafi'u ya ɓata mini rai ina ga sai dai na je class ɗin ƙarfe 10AM kawai... *** JAYKAY Idan aka tambayeshi me ya burgeshi gameda Cassandra Maria Morgan shekara shabiyu da suka wuce "har ya faɗa soyayyarta, har kuma ya ji ba zai iya auren wata mace ba sai ita ba zai iya bada" ƙwaƙwƙwaran amsa ba. Ba Love at first sight bane. Taimako ya mata lokacin da ta samu matsala da booking ɗin jirginta. An yi cancelling flight ɗinta saboda matsala ita kuma tana son zuwa ta je ta ga Kakarta da bata da lafiya a Asibiti. Kuka ta ke yi lokacin da ya zo wucewa wasu authorities suna bata haƙuri. Lokacin yana First Officer wato "Co-Pilot. Ya gama aikinsa zai fara hutunsa kenan a ranan ya haɗu da Cassy a Airport tana ta ihu. Ta bashi tausayi sosai, wannan ya sa ya tsaya ya ji bayaninta ya kuma yi 'yan kiraye-kiraye har ya sama mata wani jirgin na wani Airline ɗin daban." Suka gi exchanging contact ta tafi. A Lokacin da ta dawo London sai ta inviting ɗinsa for Lunch dan ta masa godiya. Ba su sake haɗuwa ba bayan nan amma suna waya lokaci zuwa lokaci. Bayan 'yan wasu watanni da ya sake samun hutu ya zo London sai suka haɗu a gidanta. "Cassandra tana da kyau sosai. Mahaifiyarta Spanish ce, Mahaifinta ne English. Ta fi kama da matan Spain" dan haka tana da albarkar ƙirji da ya ke iya ɗaukewa duk wani namiji mai lafiya hankali idan ya samu dama. Maybe ya faɗa soyayyarta ne. Maybe kuma kaɗaicin da suka samu ne Shaiɗan ya samu dama akansa. Maybe sha'awace kawai tsakanin namijin da bai taɓa yin hakan ba da kuma macen da ta ke buƙatar su yi hakan. He felt guilty bayan abinda ya gitta tsakaninsu. Amma a wajen Cassandra dama ta jima tana muradin hakan saboda tuni ta yi nisa a soyayyar Jalal Maiyaƙi. Daga wannan lokaci dai guragurbin soyayyarsu ta samu gindin zama a zukatansu. Shekara biyu bayan haɗuwarsu ya gabatar wa iyayensa cewa zai auri Cassandra. Lokacin Daddynsu yana da rai. Shi bai objecting auren kamar yadda Hajiya ta yi ba. Nauyin alƙawarin da ya yiwa Cassandra ya sa ba zai iya juya mata baya ba. Wannan ya sa ya dage cewa "ita ɗin kawai zai aura, ko Hajiya tana so, ko bata so." Yanzu da ya ke riƙe da waya yana kiran Cassy shine komai ke dawo masa. Shi ba dutse bane. Shekaru uku "da suka wuce duka a rikice ya ke saboda mutuwar ɗan'uwansa, amma yanzu da ya ɗan fara sassautawa ransa yana buƙatar kulawa, yana buƙatar nitsuwa da matarsa. Zuwan sau ɗaya a shekara ba tsari bane da zai iya jura." Dole ne su yi magana. Dole ne su samu mafita. Musamman yanzu da Hajiya ta fara kawo masa maganar Saudah. Ba zai iya auren Saudah ba. Ba zai ma iya auren kowacce macce ba matuƙar yana auren Cassandra saboda auren Kotu suka yi. Akwai abubuwa da dama da za su rushe idan ya ce zai yi wani auren ko kuma ya ce zai saki Cassandra. Har lokacin da wayar ta gama ringing ba a ɗauka ba. Jalal yai ajiyar zuciya yana cire wayar daga kunnensa... CHAPTER FOUR ZEEY """Sannu kin ji, Sannu Ziyadatu. Wannan jinya duk wata Allah ya kawo miki sauƙinsa""" Wani sharp zafi na ji a tsakiyar marata. Na ɗan boƙare bayana kamar mai yin sujjada na tsaya a haka har sai da zafin ya sake ni sannan na gyara kwanciyata akan pillow ina cigaba da fitar da nishi. Ya Allah! Duk macen da bata ciwon cikin period ko kuma zuwan period baya bata wahala to ta godewa Allah. Tun da Magaribar jiya na ke jin cramps. Na sha pain reliever na ɗan samu relieve kaɗan na yi bacci ina addu'ar Allah ya taimakeni kada ciwon ya tashi min tsakar dare. Ai kuwa ƙarfe biyun dare na tashi da amai da gudawa. Sai da na amayar da komai na cikina amma still ban dena jin aman ba. Sau uku kenan ina sintirin banɗaki. A daren Kaka ta je ta ɗauko gas ta kawo na kunna mata dan bata iya kunnawa ba ta ɗaura min ruwan zafi. Ruwan zafin na ɗan sha kaɗan na sake watsa wasu maganin da ban san adadinsu ba a baki saboda na samu na ji relief da wuri. Ina da aiki gobe. Akwai kayan da aka kawo min zan yi video na yi tallensa sannan akwai matar da ta biya ni kuɗi 'yarta za ta yi aure tana so na je na koya mata yadda ake abincin gargajiya. Ina kwance Kaka ta dinga matsa min marata da ruwan zafi har sai da ruwan ya yi sanyi. Haka na dinga jujjuyawa ina nishi har Asuba kafin na ɗan samu relief har bacci ya ɗaukeni bayan na sake shan wasu pain relievers ɗin dan na amayar da wanda na sha. Ban tashi ba sai ƙarfe tara na safe. Ƙarfe goma zan je gidan matar nan ga kuma na yiwa vendor ɗin da ta turo min garin kununta alƙawarin yau zan mata video na posting. Ina tashi daga kan gadon idona ya kai kan stain ɗin dake bedsheet. Nan take raina ya sake ɓaci. On top kana fama da ciwon mara da ciwon kwankwaso haka za ka yi ta fama da matsalar stain. "Yaye zanin gadon na yi na ajiye gefe, idan na gama tsaftace kaina zan dawo ta kansa. Na buɗe akwatina" na ɗau pad da pant na wuce banɗaki. Ina ciki Kaka ta ƙwanƙwasa min ta ajiye min ruwan zafi kusan cikin bokiti. Na ji daɗin ruwan dan duk da har yanzu ina jin ciwon ciki jikina ya ɗan warware sosai bayan na yi wanka da ruwa mai zafi. Na fito looking clean and ready to face the day. Ina shiga ɗaki na ga Kaka ta riga ta shimfiɗa sabon bedsheet akan gadon ta ɗauke wanda ya yi staining ɗin. Anya zan iya surviving a wani wajen idan babu Kaka? Kaya na saka sannan na kira matar da zan je gidanta na ce ta yi haƙuri zan ɗan zo da latti ta expecting ɗina zuwa ƙarfe shaɗaya ba goma ba kamar yadda muka yi magana. """Ziyadatu za ki ci ɗumame ne?"" Kaka ta ƙwalo min kira" """a'a"" na faɗa ina ɗan matsa marata" In dai ina period to ranaku ukun farko bana iya cin komai. Ko zan ci sai dai na forcing kaina na ci cokali biyu ko uku haka idan ba haka ba sai amai. Kwalin garin kunun da aka aiko min na fito da shi na buɗe ina tunanin ya za a yi na yi videon. Dana gama ɗan joting abinda zan yi sai na fito da ringlight ɗina da ƙaramin tripod da kwalin garin kunun. """Yanzu za ki yi musu bidiyon?""" """Yanzu zan yi, Kaka. Tun jiya ta ke ta min masifa wai ta aiko kaya ban mata video ba""" Roughly na faɗawa Kaka yadda zan yi and she was on board muka fara recording. Kusan shekara uku "kenan ina food content ta riga ta gane yadda na ke abubuwana, duk da ma dai watanni shida da suka wuce ne na fara ɗaukan abin seriously har na sayi tripod. Ringlight kuwa dama Yaya Aminu ne ya siya min tun da jimawa." Bana nuna fuskata shiyasa ɗaukan videon ya ke min sauƙi. Kaka ce ta yi kunun ni kawai ina saita mata yadda komai zai tafi ne. Muna cikin yi yaran gidanmu suka fara taruwa wai Anty Ziya ta fara bidiyo. Sun saba ganina ina yi fa amma kullum zan yi haka za ka ga suna shigowa gulmar abinda na ke yi. """Wai ba za ku je Islamiyya bane kam!"" Na korasu ganin sun fara distracting ɗina. Idan ina period ba" ƙaramin masifa na ke ba. I guess gaskiyar Likitoci da suke cewa period yana sakawa mata mood swing. Muna gama recording na zauna a tabarma a ƙofar ɗaki na fara editing videon while Kaka ta juyewa yaran kunun da muka yi ta ajiye min kaɗan in case zan sha. Dana gama editing sai na shiga ɗaki na kulle na riƙe wayata na fara yin voiceover. Ba ni da microphone "yanzu, da ina da wani wireless microphone amma ban san wa ya taka min transmitter ɗin ba ya zo ya dena yi." Ina gama voiceover na ƙarisa editing ɗin na posting videon tareda tagging wacce ta aiko min kayan. By the time na gama shiri na fito ƙarfe shaɗaya ta cika. Haka dai na fito da sauri na samu Keke na wuce "gidan matar. I make sure na ɗauki extra pad dan baƙona ɗan iska ne, zai iya disgracing ɗina a ko'ina. Mata masu heavy bleeding suna fama..." *** Matsalar gida a GRA shine buga gate. Lokacin dana isa gidan sai dana yi ta faman buga gate kafin daga baya har na ji haushi zan tafi aka buɗe. Kuma fa na yita kiran matar tun kafin na iso amma bata ɗauka ba. """Wa kike nema?"" Wani yamutsatstsen tsoho ya tambayeni fiskarsa a ɗaure. Da alama shine Maigadi." """Hajiya Maryam"" ""ta san da zuwana"" na ƙara da haka dan kar ya ɗauka maula na zo yi gidan." Wani kallon sama da ƙasa ya min kafin ya ce na shigo. Kai Allah ya tsinewa Talauci. Yanzu dan zan shiga gida mai GATE shine ake min wannan walaƙancin... """Ai mun yi ta jiranki. Kin san ni bana so ana wasa da lokaci"" matar ta kalleni sannan ta ce ""I DON'T LIKE" "IT""" """Dan Allah ki yi haƙuri, Hajiya. Wani uzuri ne ya riƙe ni"" na faɗa a taƙaice saboda na san ni ce da laifi" tunda dai ƙarfe goma na safe muka yi zan zo. "Kitchen ɗin gidan ta wuce da ni sannan ta ce bari ta kira min Hayfa, wato 'yarta da zan koyawa girki." Na tsaya a kitchen ɗin na fara duba ledojin ingriedients ɗin da suka siyo dan na tura musu list last week. Na fi minti ishirin ina tsaye kafin Hayfa ta fito sai wani tura baki ta ke irin an takurata ɗinnan. Da headphone a kunnenta ta shigo kitchen ɗin ko magana bata min ba. Na yi ƙoƙarin gaisheta ma amma ko amsawa bata yi ba. Ta ja kujera ta zauna sai danna waya ta ke yi. Ni dai biyana aka yi dan haka babu ruwana da attitude ɗinta. Zan yi abinda aka ce na yi ne na tafi. "Miyan kuka zamu fara yi amma ko kallo ban isheta ba, duk bayanin dana ke yi mata akan yadda ake" miyar kuka ta yi yauƙi ta yi daɗi hankalinta na kan wayarta. Sai da Hajiya Maryam ta shigo ta mata masifa ta karɓe wayan daga hannunta kafin ta taso daga kan "kujeran ta tsaya kusa da ni. Daga masifar da Hajiyar ke yi na fahimci wanda Hayfan za ta aura a ƙasar waje yake da zama, kuma specifically zan koya mata abincinmu na gargajiya ne saboda yana so sosai. Da alama babban mutum za ta aura dan na ji Hajiyar na faɗin kada ta manta da mahimmancin wannan auren." "A yadda na ɗan fahimta, kamar yarinyar bata son auren. Ita kuma Hajiyar ta ɗauki maganar auren kamar" "ranta. Koma wanene za ta aura dai ban sani ba, dan basu faɗi sunansa ba." "Na dai fahimci wani abu kafin na tafi, wato suma mutanen gida mai GATE suna fama da tasu matsalar..." *** JAYKAY "Yau Sunday, yana gida tun safe babu inda ya je. Bayan ya karya keɓewa ya yi a ɗakinsa shi kaɗai kamar" maye yana tunani. Wannan kaɗaicin shi ya ke tuna masa da abinda ya rasa lokacin da ya ajiye takardar aikinsa. Kafin ya dawo Nigeria bai san komai ba sai tuƙin jirgi. It's all he ever knows. It's all he ever wants. Tun yana yaro yake son jirgi. Ko a toys ɗinsa jirgi ya fi so. Yana shekara takwas ya tabbatarwa iyayensa cewa Pilot ya ke son zama idan ya girma. Yana gama Secondary School Daddy ya tura shi Oxford Aviation Academy ya fara Pilots training a can. Yana samun Commercial Pilot License ɗinsa ya samu aiki da British Airways a matsayin First Officer. Shekara da shekaru yana aiki da su har ya excelling zuwa Senior First Officer. Lokacin da ya samu Airline Transport Pilot License (ATPL) ɗinsa kuma aka promoting ɗinsa zuwa Captain. Shi Captain ne for good 5 years kafin wannan accident ɗin da ya faru shekaru uku da suka wuce wanda ya chanja komai na rayuwarsa. "Ranan Alhamis ne, ba zai taɓa mantawa ba. Yana iya tariyo abinda ya faru tiryan-tiryan kamar yau abun" ke faruwa... *** SHEKARA UKU DA SUKA WUCE Captain Jalal Maiyaƙi yana shiga cockpit wajen zamansa a cikin jirgi ya fara yin system checkings na "ƙarshe. Bayan ya gama duba komai tun daga flight plan, har zuwa adadin fuel levels da ake da shi. Sai ya fara addu'o'in da ya saba duk lokacin da zai tashi." Wayarsa ce ta yi vibrating yai kamar ba zai duba ba sai kuma ya ciro wayar yana tunanin wataƙila Jamal ne ya ke son faɗa masa cewa ya isa Abuja lafiya. Bai kamata ya duba wayarsa a wannan lokacin ba. Bai kamata ya amsa waya ba a irin wannan lokacin. Amma ganin sunan ɗan'uwansa ke kira sai ya ce bari kawai ya ɗauka ya faɗa masa zai kirashi idan suka sauka. "Lokacin da ya ɗau kiran maimakon muryan Jamal sai ya ji muryan wani yana faɗin ""Hello, Hello, Allah" "yiwa mai wayan rasuwa. Muna hanyar Asibiti da sauran waɗanda suka yi hatsarin amma shi mai wayar ya cika ku samemu a Asibitin...""" """Captain"" Copilot ɗinsa ya kira shi." A birkice ya juyo ya kalleshi ƙwaƙwalwarsa bai gama processing abinda ake faɗa masa ba. """Are you Okay?"" Copilot ɗin ya tambaya." Gyaɗa kai ya yi ya mayar da hankalinsa wajen jirgin yana kashe wayar tasa gaba ɗaya. Hankalinsa rabuwa ya yi kashi-kashi. Waye ya kira shi da wayar Jamal? Wani irin prank zai masa da cewa wai mai wayar ya rasu. Ina Jamal ya ke?. Sun yi waya da Jamal jiya da daddare akan zai je Abuja gidan Uncle ɗinsu wajen matar da zai aura sati uku masu zuwa. Har ya yi taxi a runway aka bashi clearance suka tashi hankalin Captain JK Maiyaƙi baya jikinsa. Tarin tambayoyine marasa amsa suka cika masa kwanya. A haka dai ya cigaba da tuƙa jirgin har Allah ya kaisu lafiya. Sai dai saboda bashi da nitsuwar zuciya sai ya yi misjudging altitude ya sauka da sauri wanda hakan ya sa jirgin ya bugi ƙasa da ƙarfi har sai da tayoyin jirgin suka fashe. Fasinjojin jirgin suka ruɗe kowa ya fara ihu. Babu wanda ya ji ciwo amma kowa ya tsorata da fashewar tayar hatta sauran Crews ɗin dake cikin jirgin sun ɗan girgiza. Emergency crew ne suka shigo da sauri aka fara duba mutane ana fito da su a hankali """Are you okay, mate?"" Copilot ɗinsa ya tambaya yana dafa kafaɗarsa." Captain Jalal ya gyaɗa masa kai. Wayarsa ya ciro ya kunnata. Numbar Jamal ya sake kira amma sai ya jita a kashe. Nan fa hankalinsa ya sake tashi. Ya kira numbar Hajiyarsu amma ba a ɗauka ba. Numbar Uncle Idris ya kira ya kuwa ci sa'a aka ɗauka. Sunan Jamal ya fara ambata yana tambayar ko ya isa Abuja lafiya. Daskarewa ya yi a wajen lokacin da ƙanin mahaifinsu ke faɗin Allah ya yiwa Jamal rasuwa motarsa ta yi hatsari. Har Airline safety officers suka zo suka tafi da shi for questioning komai duhu ya ke gani. "Jamal ya rasu kaman yaya? Jamal fa, Jamal ƙaninsa, his best friend, his best buddy." Tambayoyin da officers ɗin suka masa da kuma wayarsa da aka karɓa ne aka gano cewa already kafin a tashi maganar mutuwar ɗan'uwansa da aka masa ya taɓa shi. Nan take aka bashi temporary suspension for negligence. "Bayan ya gama serving suspension ɗinsa sai ya applying zai dawo tuƙi, amma Aviation Authorities suka" "hana shi dawowa saboda lokacin da aka masa Medical assessment an tabbatar yana fama da depression saboda rasuwar ɗan'uwansa kuma ya ƙi ya je ya yi therapy. Saboda mahimmancin Aviation Safety Laws sai aka ƙi mayar masa da license ɗinsa na tuƙin jirgi. Option ɗin aiki off-air suka bashi, suka ce ya koma ɓangaren Air Traffic control ko kuma Flight Instructor amma ya ƙi. Wannan ya sa shi rubuta resignation letter ya basu." Shekara uku da suka wuce kenan da faruwar hakan. Bayan ya ajiye aikinsa ne ya dawo Nigeria saboda ya "kula da Kamfanin da mahaifinsa da kuma ƙaninsa suka bari. It was not easy for him. Kula da kamfani, matsalar aurensa, surutun Hajiya, da kuma rayuwa da sanin cewa Jamal ya tafi kenan ba zai sake dawowa ba..." CHAPTER FIVE ZEEY A gajiye na shigo gidanmu da yammacin ranan Lahadi. Ƙarfe biyar da kusan minti arba'in da tara kenan. "Daga GRA nake gidan Hajiya Maryam da nake koyawa 'yarta girki. Two weeks kenan da fara class ɗin kuma saura sati biyu mu gama, dama class ɗin na wata ɗaya ne, duk weekend muke yi." "Ba laifi Hayfa ta fara sake fiska da ni, and tana ɗaukan class ɗin serious saboda Hajiya da ta kasa ta tsare" "akan sai ta koya. Hasashena ya yi gaskiya, Hayfa bata son mutumin da za ta aura. From 'yan maganganun dana tsinta a zuwan da na yi gidan na fahimci akwai wacce Hayfan ke so amma iyayenta basa son shi. Kamar dai Saurayin ba shi da kuɗi ne. Shi kuma wannan da ake ƙoƙarin molding masa Hayfa saboda ta" fitting irin macen da ya ke so tabbas ba ƙaramin mai kuɗi bane duba da cewa su Hajiya Maryam ma suna da kuɗin babu laifi amma suna so su yi abinda zai faranta masa rai. Girki a wajena ba abun wahala bane duba da cewa tun banida wayo na ke yi. Amma a wajen Hayfa da ta "tashi da masu yi musu aiki a gida dole ta kalleshi a matsayin aikin wahala. And a fahimtata cuisine ɗin turawa ta ke son ci har ma ta ce min ta iya dafa dayawa daga ciki. Amma dangin Tuwo namu na gargajiya bata iya ba, dan ba ci take ba." Hayfa ta bani tausayi. Aure za ta yi saboda biyayyar iyaye ba wai saboda soyayya ba. Nima mai maganar "ban san wani irin aure zan yi ba idan lokaci ya yi. Currently bani da Saurayi, and technically mutum ɗaya na taɓa soyayya da shi. Ba zan ce babu masu sona ba, cikin mutanen Anguwa, School, har ma da masu bina DM suna mini tayin soyayya. But right now gaskiya ban shiryawa soyayya ba, balle kuma aure." "Ban sani ba ko zan iya soyayya a gaba ba, amma a yanxu soyayya shine ƙarshe cikin lissafina." At 24 na sani da na ƙare Makaranta su Baffa Lawalli za su min chaaaa! akan maganar aure. A yanzunma dai ana kan yin maganganu ƙasa-ƙasa akan na ƙi aure na sako Boko da neman kuɗi a gaba. "Sai dai fa su yi haƙuri, dan ni da batun aure sai na cimma burina na mallakar Restaurant a garin Zaria..." Ina shiga sashenmu dana ga wani baƙin takalmi da ya lotse ta tsakiya a ƙofar ɗakin na san Umman Fada ce ta zo. Umma Halima ita ce ƙanwar Babana da suke uwa ɗaya uba ɗaya. Tana auren wani Bafade a cikin Fadan Zazzau shiyasa kowa ke kiranta Umman Fada. "Da Sallama na shiga ɗakin, na tadda Umman Fada tana cin tuwo. Tulelen cikinta dana gani ya sani" mamakin wannan rashin lissafin irin nata. Ga shi nan fama suke da mijinta amma sai zubo 'ya'ya ta ke. Yanzu wannan cikin idan ban manta ba haihuwa na bakwai ko na takwas kenan. """Ziyadatun, idonki kenan?"" Ta faɗa tana suɗe hannunta." Umman Fada da Baffanmu Adamu da ke Katsina ke kirana da ZIYADATUN. Ance Babana ya saka mini suna ZIYADA ne saboda na yi tsawon rai. Lokacin da iyayena suka yi aure ba a damu da gwaji kafin aure ba. Wataƙila da sun yi gwaji da sun gano cewa dukkansu AS ne wanda hakan ke nuni da cewa akwai high chance na za su haifi 'ya'ya masu sickle cell. Kafin a haifeni sai da Ummana ta haifi 'ya'ya uku suna mutuwa. Bayan ta sake yin wani ɓari sai aka samu cikina. Kaka ta ce lokacin da aka haifeni Babana babu abinda ya ke faɗa sai addu'ar na yi tsawon rai. "Lokacin da Ummana ta ke haihuwa suke mutuwa babu abinda ba a faɗa ba. A ce Aljanu, a ce jifa, a ce" "mayu, kai har cewa aka yi Kaka ce ke cinye yaran. Sai a yaro na uku da aka haɗa da Asibiti kafin aka tabbatar musu yaron sickler ne. Kafin ni babu yaron da ya kai shekara biyu cikin 'ya'yan da suka haifa. Shiyasa lokacin da na cika shekara uku ba ƙaramin murna iyayena suka yi ba, duk da kuwa lokacin haihuwata an tabbatar musu a Asibiti cewa ni AS ce ba Sickler ba kamar sauran." Kafin na cika shekara huɗu Umma ta sake haihuwa. Sulaiman sunansa. Iya abinda zan iya tunowa gameda Sulaiman shine kullum bashi da lafiya. That's the only memory da nake iya tunawa akansa. "Bayan rasuwan Sulaiman zaman iyayena sai ya ƙi daɗi, ƙarshe har ya kai ga saki. Kaka ce ta riƙe ni" yayinda Babana ya ke gwada mini tsantsan soyayya. Har Private School ya sakani maimakon sauran yaran gidan da suke zuwa Makarantar Gwamnati. Shekara ɗaya da rabi da rabuwan iyayena ko wani auren Babana bai yi ba Allah ya masa rasuwa. Hatsarin mota. Dama Babana Direba ne... Wanka na yi na chanja kaya zuwa wata doguwar rigan material mai hannun shimi da nake sawa a cikin "gida. Fitowa na yi ƙofar ɗaki na joining Kaka da Umman Fada akan tabarma, cikin akwai zafi, NEPA sun" ɗauke wuta. Umma ta ce yaushe zan je wajen Umma a Kaduna na ce mata kafin Azumi zan je idan muka gama bikin ƙawata Faty. Sai bayan Isha Umman Fada ta tafi ita da zugan 'ya'yanta guda huɗu da ta zo da su. Bata tafi ba sai dana "bata cash ɗin dubu biyu da alƙawarin zan aika mata dubu biyar ta account ɗin babban ɗanta. Na tambayeta ina account ɗinta da Yaya Aminu ya buɗe mata farkon fara aikinsa da Bankin FCMB, tace mini wai account ɗin ya samu matsala an rufe." "Na rakata har bakin titi bayan ta yiwa sauran 'yan gidan Sallama, na tara mata Keke na biya kuɗi sannan" na juyo. Ina shigowa wani ɗan gidanmu ya biyoni wai ana min magana a waje. Sharewa na yi dan na san ba zai wuce ɗaya daga cikin 'yan zaman Majalisa dana wuce bane. Bani da lokacinsu. Ina alwalar sallar Isha Faty ta kirani. Kaka ta miƙo min wayar na karɓa ina ƙoƙarin swipping in ɗau kiran amma ruwan da ke yatsata ya hana shi yi. Na goge hannuna a jikin rigana amma kafin na ɗauka kiran ya yanke. Sake kiranta na yi dan na san ta yi fushi dani. Yau ya kamata in rakata Kasuwa amma saboda zan je gidan Hajiya Maryam na ce mata ta yi haƙuri. """Bestie dan Allah ki yi haƙuri, yanzu na ke cewa Kaks dana yi Isha ke zan kira sai kuma kika rigani""" "Ta ce ""ba wani, cewa fa kika yi daga GRA gidanmu za ki zo amma na ji ki shiru har dare""" """Sorry, Bestie Wallahi ban bar gidan da wuri bane, kuma ina zuwa gida na tarar Umman Fada ta zo""" """Yanzu dai ki yi sallah sai ki kirani mu yi magana""" """Ki ce akwai labari kenan""" Kafin na ƙare maganar ma ta kashe wayar. Sake alwala na yi daga farko dan ban san daga ina na tsaya ba. Bayan na yi sallah mun fi minti arba'in muna whatsapp call da Faty. Rikicin da suka yi da wasu Anties "ɗinta akan siyayyar da ake ta ke faɗa min, wai ita ce za ta yi aure amma duk abinda za a siya ba choice ɗinta ake dubawa ba sai abinda suka ga dama suke siya. Na dai bata haƙuri na ce mata dama biki ya gaji haka. Na ce mata ta bari gobe za mu haɗu sai mu ƙarisa maganar." Social media pages ɗina na shiga ina ta reply comments ɗin mutane da duba DM's ɗina. Sai dana ji na fara kallon rubutu bibbiyu kafin na haƙura na ajiye wayar na fita na je na yi fitsari na dawo na ja mana ƙofa na saka sakata na kwanta akan gado. Tsohuwata tuni ta yi bacci abinta. Lokacin dana rufe idona maimakon bacci sai lissafin kuɗaɗen dana tara da kuma wadda na ke shirin tarawa suka fara zuwa mini. Na fara plus da minus na kuɗaɗen da ke accounts ɗina. "Bikin Faty zai ci min kuɗi, but it's worth it. Faty ta worthing ko nawa zan kashe mata. Azumi ya kusa, zan" yiwa Ummana cefanen Azumi ga kuma kayan sallah da zan mata da ita da ƙannena biyu da ta haifa bayan ta sake wani auren a garin Kaduna. Ga ƙananun bani-bani daga 'yan gidanmu. "Wash! Allah ya cigaba da buɗa mini kawai, ina ɗan samun kuɗin amma buƙatun sun yi yawa." Ina ta lissafi har bacci ya ɗaukeni ba. *** JAYKAY Breakfast suke yau safiyar Monday shi da Hajiya da Janan da kuma Junior da shima ya ke cikin uniform zai tafi Makaranta. Wayarsa ce ta fara ringing. C. MARIA da ya gani a jikin screen ɗin wayar ya saka shi ɗaga ido ya kalli Hajiya wacce hankalinta ke kan "abincin data ke ci. Miƙewa ya yi ya ɗau wayar tareda barin wajen dinning ɗin. Kwana nawa kenan yana so ya yi magana da Cassandra amma bata bashi dama ba, daga ta ce tana meeting da client ɗinta sai kuma ta ce ta gaji za ta kirashi idan ta huta." """J Love"" muryanta ya doki kunnensa lokacin da ya ce 'Hello' bayan ya koma falo can nesa da su Hajiya" kada su jiyo shi. """I'm sorry J Love, I've being meaning to call you, I was just super busy, work has...""" Katseta yai ta hanyar faɗa mata cewa zai je office idan ya samu dama zai kirata su yi magana. Lokacin da ya koma dinning ya zauna suna haɗa ido da Hajiya ya ji gwiwarsa ta yi sanyi. Yadda ta kalleshi ya san ta fahimci da Cassandra yai waya. Bata ce komai ba amma gaba ɗaya sai ya ji ya rasa appetite ɗinsa. Tea kawai ya kurɓa ya miƙe ya ce zai wuce office. """Yaya Jalal ka jirani mu tafi tare pleaaaase"" Janan ta faɗa tana rushing abincin da ta ke ci." """Ki zauna ki ci abincinki a hankali, ba kina da motarki ba""" "Hajiya ce ta yi maganar. Janan ta ce ""Na manta ban ce Isa ya kai min wajen Mechanic ba, jiya da nake" "dawowa daga Mall ta bani ciwon kai kafin ta tashi""" """5 minutes"" Jalal ya faɗa sannan ya bar wajen." Bai kai ma lokacin ba Janan ta fito suka shiga mota Driver ya wuce da su Kamfani. A cikin motar hankalin "Janan na kan wayarta yayinda na shi hankalin ya tafi zuwa neman mafita wa kansa gameda aurensa da Cassy. Dole ne su nemi mafita mai ɗorewa, wannan rayuwar da suke ba rayuwane da za a kira shi da aure ba. Ko lokacin da ya ke Captain da baya samun isashshen lokaci duk sanda ya samu hutu baya wasa da zuwa wajen matarsa da ɗansa. But this! This is different. Zaman da suke yanzu it's like kowa zaman aikinsa ya ke yi. Shi ba zai iya barin Nigeria ba saboda Kamfaninsa, sannan itama Cassandran ta ce ba za ta iya barin Fashion brand ɗinta ba, and certainly ba za ma ta iya zama a Nigeria ba." There has to be a way. Ba zai samu mafitar wannan matsalar ba har sai dukkansu sun cire son zuciya... CHAPTER SIX ZEEY Hassada mugun ciwo. Yau ina shiga sashen Baffa Lawalli sai na ga abin mamaki. Cousin ɗina Mardiyyah ce ta ke content irin nawa. Taliyan murji za ta dafa kuma uwarta ce ke riƙe da wayar Vivo na Mardiyyan tana recording komai. Yara sun tafi Makaranta dan haka sashen nasu ya yi shiru. Nima Kaka ce ta aikoni in karɓi abu a wajen Maman Suwaiban da babu abinda zai kawoni. Ikon Allah! Tunda Ziyada ta fara samun alkhairi da girke-girken Hausawa da ta ke nunawa ai dole suma su fara ko za su samu kuɗin da ta ke samu. Hmm! Allah ya basu sa'a. "Ina ga mantawa suka yi shekarana huɗu ina yin food content bana samun komai, sai wata shida da suka" wuce da Allah ya ɗaukaka min abin kafin na fara samun alkhairi. Ko magana ban musu ba na faɗi saƙon da ya aikoni na karɓa na wuce. Mardiyyah sai wani rarraba idanu ta ke irin na kamata red-handed ɗinnan. "Ba yau ta fara kishi da ni ba. Tun lokacin soyayyarmu da Yaya Aminu ta saka mini ƙahon zuƙa, a wai wai" "da nake ji wai itama son shi ta ke. Ba sa'ata ba ce, dan zan iya bata 2yrs ko ma ya fi. Shekaranta huɗu kenan da gama Sakandare, ba Makaranta, babu komai. Though na ji an ce tana koyan ɗinki yanzu." Ina komawa sashenmu na faɗawa Kaka abinda na gani. As usual Kaka bata ɗau abin da zafi ba sai cewa "ma ta yi "" kowa rabonsa zai ci. Allah ya basu sa'a""" """Kaks, kin san fa hassada suke min saboda sun ga na fara samun alkhairi""" """Ziyadatu kenan, na san me kike tunani ai. Kin san mutane nawa suka fara sai da Tuwo a gidan nan" bayan na fara sun ga ina samun alkhairi. Ba a cikin gidan nan bama hatta a layinmu zan iya irga miki "mutane uku da suka fara sana'ar Tuwo bayan na fara. Daga ƙarshe wa kika tashi kika gani yana sana'ar?""" """Ke"" na faɗa saboda tun da na taso ita kaɗai na gani tana sana'ar Tuwo." """To kin gani""" "She's right. Mardiyyah za ta iya fara food content saboda ta ga ina yi, amma wannan ba zai hanani" "cigaba da samun ɗaukaka a harkar ba, na riga na yi mata nisa." """Yanzu Kaka sanda kika fara tuwo a gidan nan sai da aka samu wanda suka fara sana'ar? Baaba Tabawa" "ce ko?""" "Kaka ta yi murmushi ta ɓantari goron dana karɓo mata daga wajen Maman Suwaiba ta ce ""ke dai bari" "kawai. Komai me wucewa ne, ba ga shi ya wuce ba""" """Ya wuce kam. Amma ni dai sai kin bani labarin komai idan na dawo daga gidansu Faty""" Black hand bag ɗina na ɗauka na mata sallama na fita. Kaka kenan. Ita sam bata da hayaniya. An ce babu "irin muzgunawar da Uwargidanta bata mata ba. Mahaifiyarsu Baffa Lawalli ta rasu lokacin ina JSS 2. Masifaffiyar mata ce ta ƙarshe. Baaba Tabawa ake kiranta. Ita ce Uwargida a wajen Kakana Malam Haruna, an ce tsabar yadda ta hana shi ƙara aure bai iya auren 'yar Zaria ba sai a Kano yai nemansa a ɓoye har magana ta faɗa ya auro Altine ƙanwar abokinsa." "Baaba Tabawa ta haifi 'ya'ya bakwai, ɗaya ya rasu tun yana jariri. Umma Hadiza ita ce babba, sai Baffa" "Lawal, Baffa Adamu da ke Katsina, Baffa Mamman, Baffa Zakari da kuma Umma Binta." "Ita kuwa Kakata Altine 'ya'yanta biyu ne suka yi tsawon rai, Babana da kuma ƙanwarsa Halima. Sauran" tun suna jarirai suke mutuwa. Wataƙila suma Sickle cell ɗinne ya ke kashe su. Ba za mu taɓa sani ba tunda ba Asibiti suka je ba. Haihuwa shida ta yi a gidan amma biyu ne suka zauna. Wannan ya sa lokacin da Ummana ta ke haihuwa suke mutuwa mutane suka fara cewa Kaka Altine ta cinye nata 'ya'yan ta zo tana cin jikokinta. Abin haushin har bayan an tabbatar da cewa yaran suna mutuwa ne saboda suna da sickle cell mutane ba su dena kallon Kaka a matsayin Mayya ba... "Daga gidanmu kai tsaye gidan su Faty na wuce, Biki ya matso kusa shirye-shirye sai ƙara kankama ya ke." Lokacin dana isa gidan ko zama ban yi ba muka wuce Kasuwa. Bayan mun dawo muka wuce gidan da za a kaita. Ana gyaran gidan shine ta cewa Ango tana so ta yiwa masu aiki bayanin yadda za a buga mata cabinets ɗin kitchen. Amaren zamani babu kunya. Two weeks to aure amma mun zo ganin gida kafin a kawota gidan officially a matsayin Amarya. "Kitchen ɗin ɗan ƙarami ne, bana tunanin mutane biyu za su iya tsayuwa a cikin kitchen ɗin, amma akwai" wani ƙaramin lungu wanda ya ke kamar store. Ni na bata shawara nace ai mata shelves a wajen saboda ya zamo kamar mini pantry haka. Ina yawan ganin manyan food bloggers suna da pantry a kitchen ɗinsu. Da ke ba ai lissafin hakan da ma'aimakatan ba sai suka ce wai sai an ƙara musu kuɗi. Faty ta kira Ango ta "faɗa masa, Ango ya ce hannunsa is tight gaskiya a bari sai bayan biki a yi. Faty ta ce bata san zance ba dole a mata Kitchen ɗin da ta ke so." Ƙarshe dai ita ce ta transferring cikaton kuɗin. Ba mu bar gidan ba sai kusan ƙarfe shida na yamma. """Bestie ki ji Baby da wani magana fa, wai in bar gyaran kitchen sai bayan biki. Yo masu zuwa gulman" "gidan Amarya ba da kitchen suke farawa ba""" "Da ke a gajiye nake sai na ce mata tunda ta biya kuɗin ai shikenan, gobe ma za a kammala aikin." """Abubuwa nawa zan biya masa da kaina. Ke dai Bestie ki bar maganar kawai""" Na kalleta da mamaki sai kuma na juyar da kaina ina kallon titi. Mu uku ne a cikin Keken dan haka na san ba za ta so bani labarin a cikin mutane ba. "Faty Makeup artist ce, kuma Alhamdulillah tana cikin top 5 makeup artist da ke garin Zaria." Tana da studio wanda ta buɗe kusan 2 years ma kenan. TYMA GLAMS sunan studio ɗinta. Ban san me yasa ta choosing ta auri Munir ba cikin manemanta. Tana da manyan masu kuɗi da ke sonta sosai amma daga ƙarshe ta choosing Munir bayan alamu sun nuna ta fi shi samu. Na taɓa tambayarta 'Why Munir?' Lokacin da aka kawo sadakinta duba da cewa basu jima da haɗuwa ba dududu watansu huɗu da haɗuwa ya turo iyayensa. "Amsarta a lokacin shine ""Bestie, shi kaɗai ne ya zo min da maganar aure kai tsaye. He was open, bai" "ɓoye min iya samunsa ba, bai zo min da ƙarya ba. Lokacin da na tambayeshi ko zai bari na cigaba da" "sana'ata shi kaɗai ne ya bani assurance cewa babu matsala zai bari""" Munir Malamin Sakandare ne yana aiki da State Government kuma yana da shagon ɗinki suna ɗinkin Maza zalla. "Na gamsu da dalilanta. Ta choosing stability sama da komai. Amma duk da haka Munir yana da tauri," "hannunsa a dunƙule yake. Ko Faty bata faɗa min ba na san har da kuɗinta a cikin gyaran gidan da ake yi, har ma da wasu abubuwan da na san ba za ta taɓa faɗa min ba saboda kar na yi zargin ita ke sponsoring auren." "Babu ruwana da tsarinsu, afterall su biyun ne za su zauna a gidan. Kuma su biyun ne za su ci moriyar" "auren idan Allah ya albarkaci auren nasu. So, it's fair." Ita aka fara saukewa sannan aka wuce da ni anguwarmu. Ina cikin Keke Yaya Aminu ya kirani. Everytime na ga kiransa sai zuciyata ta yi bugun da bata saba yi ba. Kamar ba zan ɗauka ba sai na ɗauka. Kusan 3yrs kenan da muka dena soyayya officially. It was difficult a ce kana son mutum amma kana gani ka haƙura da shi saboda harafin A da S da Likita ya alaƙantaka da su. "Ce mi shi na yi ina hanya ya ce mini gobe shima zai shigo Zaria, na ce Allah ya kawo shi lafiya." "I should be Happy, bayan kusan wata nawa zan sake ganinsa, amma sai na ji blank." "Bana farinciki da zuwansa. Like, ina so ya zo, amma bana jin wani ɗokin zuwansa kamar da. Wataƙila" zuciyata ta fara gajiya da adana soyayyarsa ne shi yasa wasu abubuwan suka dena tasiri akaina kamar da. Wataƙila kuma alama ce da ke nuna cewa it's time to finally move on. Ni da yaya Aminu ba za mu taɓa kasancewa ƙarƙashin soyayyar da za ta kaimu inuwar Aure ba... *** JAYKAY Yana zaune a ɗaki yana duba wasu reports Junior ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da bindigar wasa. Ya zo "gaban Baban nasa ya fara harbinsa paw, paw, paw, yana dariya." Jalal ya ɗaga hannu kamar ya yi surrender Junior ya cigaba da dariya yana faɗin Captain ya kama criminal. """Come here"" Jalal ya jawo shi ya rungumeshi sosai. Idanunsa suka kawo ruwa tunowa da yai da maganar" da suka yi da Cassy. Lokacin da ya ce mata idan har ba za ta bashi lokacinta ba zai ɗau mummunan mataki. "Ce masa ta yi ""Are you planning to Divorce me?""" Amsarsa a lokacin shine 'NO' saboda maganar saki magana ce da ke da sarƙaƙiya. Auren kotu suka yi dan haka dole yai taka-tsantsan. Ce masa ta yi kar ma ya fara kawo maganar SAKI dan kuwa idan ya ce zai saketa tamkar ya yi bankwana ne da ɗansa Junior. Ita za ta riƙe full custody ɗinsa har sai ya kai shekara shatakwas. Wannan abin ya ke tsoro tun lokacin da Hajiya ta fara masa maganar ya auri wata matar a nan Nigeria. "Idan Cassandra ta ji labarin ya yi aure zata filing for divorce, kuma babu makawa zai loosing custody na yaronsa ne. Idan hakan ta faru, tabbas ba lallai ɗansa Muhammad Jalal Maiyaƙi (Junior) ya taso a Musulmi ba. Hakan kuma zai ƙonawa Hajiya rai. Abinda ta ke gudu masa kenan lokacin da ta ƙi aurensa da Cassy tun farko." """Dad, Anty Saudah ta zo, wai GrandMa ka zo ka gaisa"" Junior ya faɗa da gurgurarriyar Hausarsa da ke" sirke da harshen Bature. Jamal ne ya dage masa akan ya koyawa ɗansa yaren Hausa. """Ka dinga yiwa Muhammad magana da Hausa saboda ya iya. Idan baka masa yanzu ba zai taso bai iya" "yaren Babansa ba""" Wannan ya sa ya rinƙa yiwa Junior magana da Hausa har yaron ya fara ji duk da kuwa Cassy bata so. Tun da yaron ya dawo Nigeria ma Hajiya Hausa ta ke masa ko Janan ta hanata yiwa yaron Turanci wannan ya sa yaron ya fara sabawa da magana da Hausa. """Je ka ce musu ina zuwa"" ya kissing goshin yaron sannan ya maida hankalinsa kan takardun dake" gabansa. Jamal ne ya takura masa akan sai ya yi MBA. As if ya san ba zai jima a jagorancin Kamfanin ba. Bai taɓa saka interest akan Kamfanin Daddynsu ba. Jamal shine a fore front na komai. Lokacin da yai MBA ɗinma ya yi ne dan Jamal ya takura shi ba wai dan yana tunanin zai yi amfani da karatun ba. Sai gashi karatun da kuma Company journals da Jamal ya ke rubutawa su suka taimaka masa ya ke tafiyar da Kamfanin a yanzu. Kusan 20 minutes da tafiyar Junior kafin ya sauko ƙasa. Hajiya da Saudah suna hira a falon. Janan ta naɗe kanta a kujera tana chatting. """Yaya Jalal, barka da yammaci"" Saudah ta gaishe shi lokacin da ya iso tsakiyar falon." """Barka, ya su Uncle?""" """Suna lafiya, sin ce a gaisheku"" ta faɗa tana wasa da ƙasan veil ɗinta." """Saudah ta zo mana hutu. Ga tsaraba ta kawo mana. Muhammad ma ya samu Jirgi da Bindiga"" Hajiya ta" faɗa tana kallonsa. Ya san me Hajiya ke shirin yi. Ta taɓa shipping masa idea ɗin ya ce mata ba zai taɓa yiwuwa ba. Lokacin da Jamal ya rasu weeks to his wedding. Mutane sun yi ta faɗin cewa ko za a mayar da auren kansa. But lokacin Saudah bata da nitsuwar da za a ce za a mata aure. Sannan Hajiyar da ake tunanin za ta kawo maganar ma shock ɗin mutuwar ya hanata yin komai. Watannin farkon mutuwar Jamal Saudah was a mess. Sai da aka turata Dubai wajen Sister ɗinta saboda "ta samu sauƙin tunani. Last year ta dawo Nigeria, lokacinne kuma Hajiya ta ɓaro masa maganar Saudan." "Koda a ce yana da halin yin wani auren a yanzu, Saudah ba macen da zai iya aura bane. Yes, ita cousin" "ɗinsa ce. Tana da kyau, tana da hankali. But ba zai taɓa auren matar da ƙaninsa ya so aurenta ba. Zai riƙa kallonta ne a wacce ya aura saboda ba Jamal. Haka itama za ta kalleshi ne a mijin da ta aura saboda babu ƙaninsa. Ba zai iya irin wannan auren ba. Jamal is too Precious a wajensa da zai masa wannan cin amanar." A ɓangaren Saudah tunda ta dawo Nigeria ta dawo da walwalarta and time to time tana chatting ɗinsa "su gaisa, daga take-taken chats ɗinta ya fahimci she's ready ta switching zuwa aurensa idan har zai amince. Ba zai yi blaming ɗinta ba, shekara uku is enough ta gama mourning Jamal. She has to move on da rayuwarta. Sai dai ba da shi za a yi hakan ba. Ta samu wani daban ya cike mata gurbin Jamal, ba shi Jalal ba..." CHAPTER SEVEN ZEEY Ina cikin school Yaya Aminu ya kirani wai ya iso school ɗinmu. Practical muka tsaya yi shiyasa na kai har 6 a school. Da aka gama practical ɗin sai na tsaya rubuta report kafin na tafi gida dan na san next week bani da time saboda bikin Faty. Itama kujuba-kujubar bikin ya sa bata tsaya yin practical damu ba tun ƙarfe shabiyu ta tafi gida. Na san ya ce mini zai shigo gari yau amma ban ɗauka zai zo ya sameni a school ba. Kwatancen inda nake na masa na ce ya bani minti biyar gani nan fitowa. Lokacin dana fito ina riƙe da farin Lab coat ɗina ina kalle-kallen arean wajen ko zan hango shi. Na san dai ba zai wuce da machine ɗin gidansu zai zo ba tunda tasa machine ɗin tana Yola inda yake aiki. Ɗaga wayata na yi na kira shi. """Yaya ban ganka ba..."" ban gama maganar ba na ganshi ya fito daga cikin wata mota. Ɗaga mun hannu" ya yi yana murmushi. Mai da wayata na yi cikin bag na ƙaraso wajensa ina tunanin ƙila aron mota ya yi dan zai zo ya ɗaukeni. """ 'yan Boko. Ya school?"" Ya faɗi maganar har lokacin fiskarsa ɗauke da murmushi. Once upon a time" murmushinsa na tayar min da butterflies a cikina. Once upon a time murmushinsa na melting min duk wani ɓacin rai dana ke tare da shi. Kallon-kallo muka tsaya yi. Yaushe rabon da muga juna haka. Tunda aka masa transfer zuwa Yola kusan shekara ɗaya kenan. Ya zo Zaria sau ɗaya amma lokacin ina Kaduna wajen Ummana. "He looks...HANDSOME kamar yadda na san shi. Ga shi nan sanye da blue shirt babu tie, ya ɗan loosing" "botina biyun farko. Baƙin wando, da baƙin takalmi sai sheƙin polish ya ke. Da ka gan shi ka ga Banker." "Handsome Banker. Ga tsayi, ga dimple, ga..." """Na kawo miki Amarya"" yaya Aminu ya katse mini gulmarsa da zuciyata ke yi." Yadda ya nuna motar yana murmushi ya sa na kai hannuna baki na riƙe. """Don't tell me...""" """Yes, mun yi Amarya""" Na fara bin motar da kallo ina masa Congratulations. Toyota Camry ce 2012 model. Kalar ruwan toka ta "sha wanki abunta. Ba sabuwa bace, amma daga gani bata wani jima ba." """So, ya kika ga Amaryar tawa?""" """Ta yi kyau. Kai, I'm so happy. Allah ya sa albarka ya kaɗe duk wani sharri da ke tattare da ita""" Yaya Aminu ya amsa da Amin. Lokacin dana shiga cikin motar zan zauna sai yai saurin saka hannu ya ɗauke baƙin suit ɗinsa da ke wajen ya mayar kujerar baya sannan na zauna. Na fara kallon cikin motar ina yabawa. """Ba sabuwa bace, Wani colleague ɗina ya siyeta 7 months kenan shine ya siyar mini""" """Ai yaya ba za ka ce ba sabuwa bace wannan, ga shi komai neat. Gaskiya Congratulations""" """Thank you, My Dear""" "Ɗan kallon juna muka yi briefly kafin ya ɗauke kai ya ce ""bari mu je mu celebrating dan ke kika fara" "ganinta""" """Da gaske baka kai gida ba?""" """Ina zan kai gida bayan Uwargida bata sa min Albarka ba"" yai maganar yana dariya." Maimakon na yi dariya sai na juyar da kaina ina kallon titi. Ba abin dariya bane. Dukkanmu mun sani ba zan taɓa zama Uwargidansa ba. An ce yanzu masu Genotype AS da AS za su iya haihuwan lafiyayyun yara idan za su yi preimplantation "genetic screening yayin IVF. Shekaru uku baya na yi ta research akan research akan haihuwa through IVF, halarcinsa, yadda ake yi, a ina ake yi, dama success stories na waɗanda suka haihu ta dalilin IVF kuma suka samu lafiyayyun yara ba masu ɗauke da ƙwayar sickle cell ba." "Zamani ya kawo mana cigaba, sai dai wannan cigaba ta masu kuɗi ne. Ta masu kuɗin da za su iya biyan" miliyoyin Naira dan a musu treatment ɗin IVF ne. Wataƙila da ni ba marainiya bace kuma Babana ba Direba bane. Wataƙila da yaya Aminu wani CEO ne ko ɗa ga wani hamshaƙin Attajiri da yanzu an wuce wajen. Da yanzu bamu watsar da soyayyarmu saboda Genotype ɗinmu ba. "Kun san soyayya. At a point cewa ma na yi zan haƙura da haihuwa, idan ya so bayan mun yi aure da" wasu shekaru sai yaya Aminu ya auro wata matar mai AA ta haifa masa lafiyayyun yara ni kuma sai a bani ɗaya daga ciki. A lokacin giyar soyayya ke cina I was ready to share him da wata duk da ina da zafin kishi. Shima a nasa ɓangaren ya kawo shawaran mu yi aure mu haƙura da haihuwa sai mu adopting yaro mu "riƙe, but we both know ba abu ne mai yiwuwa ba." """What if ba mu da matsalar genotype and muka yi aure Allah ya jarrabcemu da rashin haihuwa? Kin san" "hakan yana faruwa. My Dear let's just get married and pretend Allah ne bai bamu haihuwa ba""" Kalaman yaya Aminu kenan a ƙoƙarinsa na son sama mana mafita akan matsalar da muka tsinci kanmu. "Babu mafitar da ba mu kawowa kanmu ba. But daga ƙarshe, muka rungumi gaskiyar da ke gabanmu," "rabuwar ce Alhairi, and the earlier muka rabu, the better." Bayan mun haƙura da soyayya sai muka yi ƙoƙarin komawa Friendship kamar yadda muka faro kafin "soyayya ta shiga, but hakan sai ya gagaremu. Zama Friends da mutumin da kun riga kun crossing layin soyayya, is difficult." Daga lokacin zuwa yanzu ba zan iya bawa alaƙarmu suna ba. Mu ba Masoya bane dan mun riga mun "haƙura da juna, and then mu ba Friends bane saboda jirgin Friendship ɗin ya jima da sinking. Maybe mu" tsaya a ƙarƙashin inuwar Cousins tunda nan ne asalin farkonmu. Ni da Yaya Aminu Cousins ne. Gara a barshi a haka kawai. Dai dai wani sabon restaurant ya karya kwanar motar ya samu waje ya yi parking. Kusan a tare muka buɗe ƙofar motar muka fito. Na ɗan jira shi ya zago ta wajena sannan muka shiga "rastaurant ɗin. Na ɗan saci kallonsa lokacin da ya ja kujera zai zauna. Ɗan tumbi na noticing ya fara ajiyewa. I was surprised dan the last time dana gan shi ba shi da tumbi. Wannan karan gaskiya Bankin da ya ke aiki da su yana samun abun nunawa. Lokacin da ya fara aiki da FCMB shekara huɗu yana waje ɗaya ba promotion ba komai, daga nan ya koma Sterling bank yai shekara biyu da su. A farkon last year ya samu offer da Union Bank da ke Yola ya karɓa ya tafi saboda a can ɗin zai fi samun promotion kuma salary da benefits ɗinsu ya fi yawa. To gashi har ya sayi mota. Masha Allah!." "Idan ba ƙasar tamu ba, ina mai Degree a Chemistry ina aikin Banki. Amma aka ce duk condition da ka" "tsinki kanka to sai ka adopting ka saje ka bi Yarima ka sha kiɗa. I remember lokacin da ya ke mini lesson ɗin Chemistry da Physics gabannin in rubuta jarrabawar WAEC ɗina na farko. Yaya Aminu gurun Chemistry ne sosai, daga ƙarshe sai gashi ya ƙare a aikin Banki. Nima mai maganar ba ga ni ina karatun Microbiology ba amma na faɗa harkar Food Content, in dai na buɗe restaurant ɗina ma. Ajiye takardar Degree ɗin zan yi a ƙarƙashin gado na cigaba da neman kuɗi." Ko Menu ɗinsu ban kalla ba na cewa waiter ɗin a bani Fried rice da chicken. Shi kuma yaya Aminu ya ce a "bashi jollof rice. Kafin a kawo abincin sai na fara ƙarewa restaurant ɗin kallo ina lura da decor da kuma tsarin wajen. Idan zan buɗe restaurant ɗina ba irin wannan fasalin zan masa ba. Kaman ya san tunanin buɗe restaurant nake sai ya tambayeni ""ya batun buɗe restaurant ɗinki, nawa kika tara yanzu?""" Ɗan murmushi na yi sanin cewa bai manta da babban burina ba. Once in a while idan muka yi waya ko chatting mu kan ɗan faɗawa junanmu plans da goals ɗinmu na rayuwa. Old habit ne da tun kan mu fara soyayya muke yi. Lokacin da nake rubuta JAMB bana samun admission shi ya ke ta ƙarfafa min gwiwa akan na sake rubutawa kada na haƙura koda ba zan yi amfani da karatun ba samun shaidar karatun na da mahimmanci. "Babban dalilin faɗa masa ma shine, idan ban faɗa masa ba, a cikin sauran 'yan'uwana babu wanda ya ke" da hankalin da zan iya taɗi makamancin wannan da shi. "Kaka ce kawai nake iya faɗa mata komai, amma itama akwai abubuwan da kona faɗa sai dai ta ji kawai" amma bata da ilimi ko wayewar da za iya bani shawara akai. 'Yan gidanmu kam yadda nake da Mahassada da ko'ina da an ji na furta zan buɗe retaurant ai shikenan na shiga uku ƙila a kira meeting akaina a ce on kawo kuɗin dana tara za a sai gado da katifa a mini aure... """Kin san ko"" yaya Aminu ya katse min tunani. ""Duk sadda na je cin abincin a restaurant a Yola sai na yi" "tunaninki""" """Kana lissafin yaushe zaka fara cin abinci a Restaurant ɗina ko? "" na yi maganar ina dariya. Kafin yai" magana aka kawo mana abincinmu. Muka fara ci a hankali. Loma ɗaya da na yi na gane Fried rice ɗin bai yi daɗi ba. Ba kowanni restaurant ne suka iya dafa fried rice mai kyau ba. Lokacin da na yi aiki a Zikk's Foods wane mutum ya ci Fried rice ɗin gurin bai yaba ba. Lokacin da muka ƙare cin abinci yaya Aminu ya biya sai muka tafi. "Gidansu ya wuce da mu, ya ce zai je ya nunawa iyayensa mota. Can ƙasan zuciyata sai na ji babu daɗi" cewar ni ya fara nunawa motar kafin Ummansa. Lokacin da muka isa gidan muna fitowa yaran da ke ƙofar gida suka yanyameshi suna masa oyoyo. Ban "jira shi ba na shige gidan dan na gaishe da Umma Hadiza. Na jima ban zo gidan ba, na san za ta mini gori ta ce saboda yaya Aminu na zo." Compared to sauran 'yan'uwan Babana da suka gaji baƙin halin Baaba Tabawa ita Umma Hadiza tana da sauƙin kai. Duk sadda ta samu shigowa babban gida za ta shigo sashen Kaka ta zauna har ta wuni a wajen. Ita kaɗai ce ta ɗauki Kaka a matsayin uwa bayan rasuwar Baaba Tabawa. Sai kuma Baffan Katsina da shima babu laifi yana bawa Kaka darajar uwa a gidan. Sallar Magariba na samu tana yi dan haka na jira ta idar muka gaisa. Muna cikin gaisawa yaya Aminu ya shigo. Ya mata Albishir da cewa Allah yayi ya sayi mota. Ya bata key ɗin motar ta riƙe a hannunta sannan ta fara kwararo masa addu'a. Lokacin da ya ce ta fito ta ga motar sai ta ce bari Malam ya dawo ta faɗa masa. Na taɓe baki ina mamaki. Gaskiya tarbiyyar zamanin su Umma Hadiza daban da tamu. Yanzu wai ta fita ƙofar gida ta duba motar ɗanta shine wai sai Malam ya dawo ta faɗa masa. Cabɗi!... *** JAYKAY Jalal bai shigo gida ba sai wajen goma na dare. Bayan ya tashi a office Plaza ya wuce saboda ya duba "aikin gyare-gyare da ake yi. Komai na Plazar ya kammala sai ɓangaren restaurant kaɗai shine har yanzu ba a gama finalizing yadda za a tafiyar da restaurant ɗin ba, da kuma wajen Gym wanda basu samu instructor mace ba. Hajiya ce ta ce a yi gym na mata a wajen, amma kuma matar data ɗauko za ta kula da wajen ta ƙi karɓan offer ɗin har yanzu. Plazar nasu ya ƙunshi ɓangaren Event center, Restaurant, Salon da Makeup studio, Gym na mata da kuma mini shopping Mall. Project ne da Jamal ya fara, bayan rasuwansa aka ajiye aikin. Sai last year Hajiya ta sa shi dawo da aikin gadan-gadan. Ga shi yanzu har ya ci 70% na aikin. Da a ce ma an gama ɓangaren restaurant ɗin da za a iya buɗe Plazar nan kusa." Lokacin da ya shigo falo bai yi tunanin zai ga kowa a falon ba sai kuwa ya ga Saudah ita kaɗai a falon tana kallo. """Sannu da dawowa"" ta faɗa ta taso za ta karɓi jakarsa ya dakatar da ita." Jiki a sanyaye ta koma ta zauna. """Hajiya ta yi bacci ne?""" """Bata jima da shiga ciki ba""" "wuceta ya yi ya nufi ɗakin Hajiya. Ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, daga ciki Hajiya ta ce ya shigo. Lokacin da" ya shiga zaune ta ke kan kujera tana karatu idanunta sanye da reading glass ɗinta. Gaisheta yai ya ce mata daga duba Plaza ya ke shi yasa bai shigo da wuri ba. Ta ce masa babu komai. Da zai fita sai ta ce masa ya shiga ya duba Junior da yamma bai je Islamiyya ba saboda zazzaɓi. Sun kai shi Asibiti an duba shi an basu magani. Godiya ya mata ya ce zai duba shi. "Har ya kai baƙin ƙofa zai buɗe ta kira sunansa ""JALAL""" Juyowa yai a hankali. Ganin kamar magana ta ke so da shi sai ya dawo ya zauna a inda ya tashi. Ajiye littafin hannunta ta yi sannan ta cire reading glass ɗin ta mayar da shi cikin gidansa. """Maganar aurenka na ke so mu yi"" ta faɗa tana kallon ƙwayar idanunsa." Wani ƙullutu ya haɗiye yana fargabar abinda zai fito daga bakinta. """Idan na ce zamanka a gidan nan babu mata baya damuna to na yi ƙarya. Nan ba London bane, mutane" "na magana. Wallahi tun ina kau da kai akan abinda mutane ke faɗa har abin ya fara damuna nima. Ban san wani irin yarjejeniya ke tsakaninka da Cassandra ba, amma gaskiya a tafiyar da kuke wannan ba aure bane." """Ka godewa Musulunci da ya baka damar auren fiye da mace ɗaya. Idan ita ba zata biyoka Nigeria ba, sai" "kai ka auri wacce za ta zauna a nan saboda mutane su dinga kallonka da mutunci""" "Wannan karan sassauta muryarta ta yi sannan ta ce ""ni ban ce dole sai ka auri Saudah ba. Ban kuma ce" "dole sai ka aura daga cikin Family ba. Abu ɗaya na ke so, wannan karan ka daure ka auro Musulma 'yar Nigeria. Idan da hali ta kasance 'yar yankin Arewa. Kai ko ba a Arewa ta ke ba I won't mind in dai Musulma ce kuma 'yar Nigeria""" Wani ƙullutun ya sake haɗiyewa wanda ya hana shi yin magana. "Shirunsa ya sa ta cigaba da magana, wannan karan da sigar magiya." """Kai kaɗai ne yanzu babu Jamal, Janan za ta yi aure next year. Gidan ba zai mana daɗi ni da kai da" "Muhammad kaɗai ba. Shi kansa yaron yana buƙatar ka sama masa ƙanne""" Yana so ya faɗa mata tsoronsa akan rabuwa da Cassandra amma kuma ba zai bari ta ganshi a namijin da "bai kai ya zartar da hukunci a rayuwarsa ba. And worse of it, ba ya so ta ce masa 'da Jamal ne, da tuni ya yi kaza'. Wannan ya sa ya haɗiye bayaninsa ya ce ""ki yi haƙuri, Hajiya. Insha Allahu kafin shekaran nan ya ƙare zan yi abinda kika ce""" """Yawwa! Yanzu na ji magana. Kar ka manta saboda kai Saudah ta zo gidan nan. Idan ba ka ra'ayinta kada" "ka sa mata rai ka ɓata mata lokaci, she's being through pain already""" """Na fahimta"" Jalal ya faɗa tareda miƙewa..." CHAPTER EIGHT ZEEY Yau za mu ƙarƙare class ɗinmu da Hayfa. Sati uku muka yi maimakon sati huɗu da aka saka. Nima dama "ina tunanin zan ɗau excuse saboda bikin Bestie na da za mu fara ranan Laraba sai kuma Hajiyar ta kirani da kanta ta ce tana so mu ƙare class ɗinmu a satin nan saboda ranan Tuesday ita da Hayfa za su je Dubai. Ai kuwa na ce ba matsala tunda nima zai zo min da sauƙi kenan, zan samu na sake a yi hidimar biki ba tareda wani abu ya riƙeni ba." Jiya Saturday da na zo ban tafi ba har kusan ƙarfe tara na dare saboda mun yi tuwon Biski. Gaba ɗaya ilahirin gidan ya buɗe da ƙanshi. Lokacin da aka gama hatta Hajiya Maryam sai da ta yaba da tuwon wai rabonta da cin tuwon Biski tun bata yi aure ba. Hayfa kam ko a jikinta sai cewa ta ke ita bata da patient ɗin wannan ɗawainiyar. Na ce mata in har kuwa ba za ta yi haƙuri ba tuwon ba zai mata yadda ta ke so ba. Ta ce min oho dai tunda ba ita za ta ci ba. Duk da dai bata son tuwo amma yadda ƙanshin tuwon ya cika mata hanci sai da ta gutsiri kaɗan ta ci. Ta ce wai ƙanshin ya fi taste ɗin daɗi. Na ce ba ta san daɗi ba kuwa. "Alhajinsu na nan, kuma shima an zuba masa tuwon shi da wani abokinsa. Wallahi har da neman ƙari" kuma babu saboda ba dayawa na yi ba. Nima na so na ajiye kaɗan in kaiwa Kaka amma duka komai ya ƙare. Da ke dama duk abincin da muke yi na class ɗin masu gadi da Direbobinsu ake bawa shi yasa komai nake kaɗan-kaɗan amma Tuwon Biskin da na yi sai ya yi Albarka tunda masu gidanma sun ci. Ina kitchen Hajiya Maryam ta zo wai Alhaji ya ce a kawo musu tuwon shi da baƙonsa wai ƙanshin tuwon ya hana su sakewa. Na yita murmushi ni kaɗai. Ashe dai masu kuɗi ma na son abincinmu na gargajiya. "Yau Sunday ba zan daɗe ba, dan Dambu kawai za mu yi, da shi zan ƙarƙare mata class ɗin. Tun da na ce" "Dambu zan yi Hajiya Maryam ta ce na yi dayawa wai ta jima ba ta ci shi ba. Ni abin ma sai yake bani mamaki, suna da kuɗi suna da mai aiki amma ba za su riƙa dafa irin waɗannan abincin ba. Koda ya ke mai aikin nasu ba Bahaushiya bace, intercontinental girki ta ke musu. To idan har suna son namu na gargajiya mi yasa ba za su ɗauko wacce za ta riƙa girka musu duk lokacin da suka buƙata ba?. Ko dai ni ce ban san ya masu kuɗi suke lamarinsu ba?. To ma ta ina zan sani ni dana taso gidan Talauci. Wallahi ko, ba dan Kaka ba, da a miskiniya zan taso bayan Babana ya rasu. Kuɗin Makarantana Kaka ce, kayan sawa da abincina duka Kaka ce. Allah Sarki lokacin da ta ke sana'a Wallahi ko nawa ne za ta cire ta yi mini hidima da shi. Jarrabawar WAEC ɗina na farko ita ta biya mini. Da zan gyara NECO dan da jarrabawar NECO nake amfani yanzu shine yaya Aminu ya biya mini." Su fa mutanen gidanmu kowa ta kanshi ya ke yi. Ba dan na dage sai na yi Boko bama dan ta su ne kawai "na je na yi aure. A gidanmu wanda ya damu da Boko shine Baffa Mamman, ya ɗan yi Diploma ya samu aiki a ABU as non Academic Staff, daga baya ya samu ya haɗa Degree a wajen. Ina ga ba zai wuce shekara uku bama da kammala Degree ɗinsa. Ya yi ta encouraging ɗina akan na yi karatu lokacin dana dage ina JAMB bana ci. Shi dai akwai bada shawara, amma sisinsa bai taɓa bani wai dan na yi hidimar karatuna da shi ba." A cikin irin mutanen dana taso kenan. So ni ban san yadda masu kuɗi suke lamarinsu ba. Amma a ɗan "zuwana gidan nan, na fara fahimtar wani abu daga irin rayuwarsu." "Yau ma kamar jiya, tun dana fara turara Dambu gidan ya buɗe da ƙanshin Gyaɗa da Zogale. Kun san abu" "da masu kuɗi Dambun namu ya ji hanta dumu-dumu. Ga extra veggies da zan sake zubawa idan ya kusa yi, na haɗa saboda komai ya tafi dai-dai da irin cimarsu." Ina cikin kitchen ina danna waya Mai aiki ta shigo wai in je Hajiya na kirana. Dama tun ɗazu na ke jin voices kamar Hajiyar tana tareda baƙuwa. "Ajiye wayar na yi na fita daga kitchen ɗin na wuce falo. Hajiya Maryam ce da wata kyakykyawar mata, da" ka ganta ka ga gogaggiyar 'yar Boko. Za ta iya kaiwa 50 koma 60 amma jikinta sam bai nuna tsufanta ba. """Ita ce Chef Zeey ɗin?"" Matar ta tambaya. Hajiya Maryam ta jefawa tambayar dan haka sai na ja na yi" shiru ina ta blushing. """Ita ce, Hajiya Layla. Ai jiya hatta Alhaji sai da yayi santin Tuwon Biskin da ta yi""" "Sai a lokacin matar ta kalleni da kyau fiskarta a sake ta ce ""Masha Allah, ai na kusan shekara ina" "following videos ɗinki a Instagram. Chef Zeey ina Kaks?""" Dariya na saka saboda bata manta yadda nake kiran Kaka a cikin videos ɗina ba. Shi yasa har a comment section idan ni na yi girki ba a ga hannun Kaka ba sai a riƙa tambayata ina Kaks ta shiga. """Kin san Hajiya Maryam na jima ina cewa zan mata magana tunda a Zaria ta ke amma sai na basar ashe" "da rabon za mu haɗu ne"" ta kalleni ta ce ""gaskiya content ɗinki yana nishaɗantar dani, keep it up"" murmushi ya suɓuce mini na fara yi mata godiya." Yanzu wai wannan haɗaɗɗiyar matar ne ta ke cewa ina burgeta. Kai akwai daɗi fa wani da yake "bibiyarka a social media ya nuna har a zahiri shi fan ɗinka ne. Musamman idan wanin babban mutum ne. Duk da ban san wacece matar ba, amma yanayinta kaɗai idan ka kalla za ka san babbar mata ce da duniya ta san da ita." """Ai ina shigowa gidan nan da na ji ƙamshin Dambu ke na fara tunawa kwanaki na ga kin saka recipen a" "YouTube, shine ta ke ce min ai ke Chef Zeey ɗin ce a Kitchen. Gaskiya i'm happy to meet you. Gashi Hajiya Maryam ta ce yadda muke gani a video haka girkinki ke da daɗi a zahiri""" "Hajiya Maryam ta ce ""gaskiya ba laifi. In dai girkin gida ne ki bar wa Chef Zeey""" Har na koma kitchen ban dena blushing ba. Jina nake kamar wata celebrity. Ashe dai manyan mutane ma na kallon videos ɗina. Gaskiya dole na ƙara himma wataƙila na samu wanda zai min hanya Ɗangote ya bani tallen gishiri da Taliyarsa. Na sa dariya ni kaɗai. """Wai abin nan ba zai yi bane. Tun awa nawa muke ta jira"" Hayfa ta faɗa duk ta ƙagu a gama class ɗin da" muke yau. """Kar ki damu mun kusa gamawa"" ta ɗan ja wani ƙaramar tsaki ta cigaba danna iPhone ɗinta. Jiya" daɗewar da muka yi a kitchen ya dameta. "Ba zan yi wasa da damata wajen ƙara burge wannan Hajiya Laylar ba, dan haka dole na bi komai a" "hankali, babu rushing-rushing." Lokacin da muka gama na serving Hajiya Layla da kaina na kai mata na tsaya a wajen ina jira ta taɓa ta ji "ko ya yo daɗi. With Hajiya Maryam ban taɓa damuwa da yabawarta ba dan ba ci ta ke yi ba, ita damuwarta 'yarta ta koyi girkin ne. Jiya ne dai Tuwon Biskin da na yi ya tado musu sha'awar cin abincin gida." "Loma ɗaya Hajiya Layla ta kai ta ce ""Masha Allah! Na jima ban ci Dambun da ya mini irin wannan ba""" "Lokacin da ta kai loma na uku sai ta ce ""Allah ya jiƙan Kakata Jamila, a wajenta na koyi cin Dambu""" Hajiya Maryam ta sa dariya nima na yi dariyar saboda gaskiya ba ƙaramin daɗi na ji ba jin cewa girkin da na yi ya tashi kanta. Lokacin da Hajiya Layla za ta tafi sai ta ta bani kati da ke ɗauke da suna da numbarta. Mun yi maganar "zan zo gidanta gobe nai mata Tuwon Biski itama. Ta ce min rabonta da cin tuwon ya fi shekara ishirin. Ban yi mamaki ba. Ina ruwan masu kuɗi da Tuwo, Tuwon ma na Biski." Ta ce min idan na zo akwai maganar da za mu yi ɗanta yana son buɗe restaurant wataƙila zai iya ɗaukana aiki. Na ce mata nima ina da burin buɗe restaurant amma wanda za a riƙa yin abincin gargajiya zalla. """I like the idea, Ziyadaah"" ta ja ƙarshen sunan, sai hakan ya ƙarawa sunan daɗi. Karo na farko da ta kirani" da sunana ba Chef Zeey ba tun haɗuwarmu da ita kenan. Ina shiga kitchen na buɗe katin na karanta sunan da ke jiki LAYLA J. MAIYAƘI. Da sauri na kwafi numbar na saving a wayata. Bayan na gama tattara kitchen ɗin sannan na fito na yiwa Hajiya Maryam sallama. Hayfa kam tuni ta koma ɗakinta dama a matse ta ke. Da zan wuce sai Hajiya Maryam ta ce min idan na je wajen Hajiya Layla na yi mata tallen class ɗina tana da 'ya Janan wataƙila ta sakata yin class ɗin. Na yi mata godiya na fita. Kai anya ba zan ƙara kuɗin class "ɗina ba kuwa, tunda dai sun ga aikina yana kyau." Kai! ko Hajiya Layla ba ta ce za ta biyawa 'yarta Class ɗina ba zan iya koyawa 'yarta a kyauta. Matar ta burgeni ne. Ya jima ban haɗu da matar da lokaci guda ta shiga raina ba irin Hajiya Layla. Dana isa gida na faɗawa Kaka abinda ya faru na ce mata Hajiyar ma na gaisheta ta ce tana amsawa. Da "na ce ba zan sake yin aiki ba tunda satin bikin Bestie za a shiga amma gobe dole na je gidan Hajiya Layla, irin mutanen nan idan suna sonka za su iya buɗe maka ƙofa dan su ɗaga ka. Ga shi dai daga haɗuwa har tana cewa ko za a ɗaukeni aiki a restaurant ɗin da ɗanta zai buɗe." "Kafin na kwanta na shiga IG na searching sunanta, ai kuwa sai ga shi nan ta fito. Kamar yadda na yi" "hasashe babbar mata ce. Wikipedia na shiga a Google na karanta labarinta tsaf. A Zaria aka haifeta, bayan aurenta da Alhaji Kabeer Maiyaƙi sai ta koma London da zama, a nan ta yi karatu har matakin Phd. Lokacin da mijinta ya dawo Nigeria da zama gaba ɗaya shine ta ke shuffling tsakanin London da Nigeria, amma bayan rasuwar mijinta sai ta yi retire ta dawo Nigeria da zama gaba ɗaya. An ce tana da 'ya'ya uku amma ɗaya ya rasu a hatsarin mota shekara uku da suka wuce." "Wani abin da ya bani dariya gameda ita shine, a wani videonta dana ke kallo ana hira da ita ta ce sunan" "Kakarta ta ci wato Jamila, ake kiranta da Layla amma tun tasowarta take ƙin suna Jamila saboda basa" shiri da Kakar tata. """Na yi ƙoƙarin maida sunana Layla kawai na cire Jamilan amma mijina Allah ya jiƙan rai har ya rasu Jamila" "ya ke kirana, baya son Layla shi yasa na bari"" a dai-dai wajen ta yi murmushi. Irin murmushin da ya fi kuka ciwo ɗinnan. Ni da nake gani a waya ma sai da idona ya ciko da ƙwalla." """Saboda son sunan da ya ke, yaron dana fara haifa sunan Jamil ya saka masa, unfortunately ya rasu few" "weeks bayan haihuwarsa. Na zo na sake haihuwa ya saka masa Jalal, then Jamal, akan autata sai ya mayar mata da sunana Jamila"" wannan karan dariyar da ta yi dariya ne har zuciyarta." """Amma itama kamar ni, ta fi son a kirata da ɗayan sunanta ba Jamila ba""" Mai yin shirin ne ya katseta da cewa suna Jamila dai ya ƙi karɓuwa a gidan Alhaji Kabeer Maiyaƙi. "Cikin dariyar Hajiya Layla ta ce ""ka san bayan rasuwarsa menene abu ɗaya da na fi missing?"" idanunta ya" "ciko da ƙwalla ""yadda yake kirana da JAMILAH"" hawaye ne ya gangaro mata, aka miƙa mata tissue ta" "fara gogewa, a dai-dai wajen videon ya yanke." Nima sai ga shi ina goge hawayen. Dama ga ni da saurin kuka idan na ga abun tausayi. "A nawa ɓangaren, cikin abinda na missing bayan rasuwar Babana, shine yadda idan ya kira sunan ZIYADA" a kowanni lokaci fatan na yi tsawon rai ya ke mini. """Husnan wa Ziyada'... daga nan aka ce ya ɗauko sunan. Babana ba Malami bane, a tafsiri ya ji ma'anar" "'ZIYADA' kuma ya saka min saboda na yi tsawon rai, na samu alkhairi, na samu rayuwa mai kyau..." Haka dai na kwanta cike da tunanin labarin Hajiya Layla Maiyaƙi... CHAPTER NINE JAYKAY Hajiya tana dawowa daga gidan ƙawarta ta kira Jalal da ke supervision Plaza ta ce masa ta samu Chef da za ta musu aiki a restaurant. Shi duk yadda ta ke ta bayanin abincin gargajiya bai fahimci inda ta dosa ba. Restaurant ɗin da za su buɗe fine dining ne ba wai shagon abinci kamar na Mama put ba. Ya dai ce mata idan ya shigo gidan zai sameta su yi magana. Completely shi yama manta da maganar da suka yi. Amma yana shigowa da ya gaisheta sai ta ke ce masa me ya ke gani gameda hiring Chef Zeey su mayar da Restaurant ɗin wajen yin traditional food. """Hajiya, akwai plan a ƙasa, mun riga mun yi nisa, I don't think it's a good idea mu chanja tsarinmu a" "wannan gaɓar"" ya faɗa a nitse kamar ba ƙorafi ya ke ba." """Daɗina da kai kenan, idan ka kafe a abu shikenan. Ɗan'uwanka is more open to new ideas"" hakan da ta" faɗa zafinsa dai-dai yake da ta ɗau guduma ta buga masa a dai-dai ƙirjinsa. Everytime ta auna shi da Jamal haka yake ji. """Ni dai na inviting ɗinta za ta zo gobe, ka yi tunani akai. Ka gwada jin idea ɗin daga wajenta ka gani ko" "abu ne da za ka yi aiki da shi. Yanzu ni sau nawa nake tashi da marmarin abincin gida in rasa wajen siya sai dai ko a taho da shi daga family house. I think her idea is very creative""" So yake ya ce mata ba creative idea kaɗai bane zai tafiyar da restaurant amma sai ya yi shiru. Duk abinda zai faɗa ba fahimta za ta yi ba musamman da ta riga ta nanata cewa Jamal yana son new ideas. """Zan yi magana da ita"" ya faɗa bayan dogon shiru." """Ko kai fa. Allah ya sa a dace"". Ƙasa-ƙasa ya amsa da Amin sannan ya tashi ya fita." Da safe bai yi mamaki ba da Hajiya ta sake nanata masa cewa ya dawo da wuri saboda su yi magana da Chef Zeey. Yana jin Janan da Saudah suna yiwa Hajiyar tsiya wai tun jiya da ta ci abinci a gidan Hajiya Maryam take ta waƙar Chef Zeey. Ya kaɗa kai ya fita. To ko suma za su taya shi jimamin wannan lamari ai. Lokacin da ya samu sarari a office sai ya shiga Instagram dan ya ga wacece Chef ɗin da Hajiyar ke maganar a damƙa wa restaurant. A bayanan Hajiyar ya fahimci a Instagram ta santa tun ma kafin su haɗu a gidan ƙawarta. Video ɗaya ya kalla ya fita daga wajen yana mamakin me ya hau kan Hajiya haka take ƙoƙarin kawo masa tarkace cikin harkarsa. "Videon da ya gani ba da waya mai kyau aka ɗauka ba, it was blurry. Wajen da ake girkin duk ƙasa da su" "randa su rijiya, typical gidajen ghetto." Ta ina mai irin wannan content ɗin za ta heading restaurant ɗin da ya ke son buɗewa. Anya ma Chef ɗin ce kamar yadda Hajiyar ke ta faɗa. Koda zai yi amfani da maganar Hajiya ya mayar da "restaurant ɗin strictly traditional cuisine, to ba zai iya ɗaukan wannan matar ba, dan bata dace da shirinsa ba." Bai bari maganar ya jima a ransa ba ya watsar da komai akan koma wacece ya riga ya gama assessing ɗinta tana zuwa zai ce mata ba zai yi aiki da ita ba. Ba sai Hajiya ta gane ba ya san me zai yi ya koreta a rufe maganar. "Ƙarfe huɗu saura ya dawo daga Masallaci kenan zai koma office Hajiya ta kira shi, wai yana ina, ya zo" "Chef Zeey ta jima a gidan, ta gama abinda ya kawota shi ta ke jira. Ya ce mata yanzu zai zo." *** ZEEY Gidan Hajiya Layla ya ninka gidan su Hayfa girma da kyau. Ban zama 'yar ƙauye ba sai dana shiga kitchen ɗinsu. Allah ina ga sashen Kaka tsulum zai shiga kitchen ɗin har a samu sauran space. Babu abinda babu a kitchen ɗinnan. Irin kitchen dana ke gani a Pinterest da manyan food bloggers ɗin kudu ne. Da ni ke da kitchen ɗinnan ai katifa kawai zan shimfiɗa na rinƙa kwana a wajen. Idan za ka kwana kana girki a irin wannan haɗaɗɗen kitchen ɗin Allah ba za ka gaji ba. "Hajiya da ta lura na faɗa kogin soyayyar kitchen ɗinta sai ta ce ""gashi duk kyan kitchen ɗinnan ni da" "Janan ba girki muke a ciki ba""" Hangame baki nayi da ta faɗi hakan. Idan ina da irin kitchen ɗinnan ai babu abinda zai hanani girki sai ciwo. """Lokacin da zan yi aure aka kaini wajen Kakata wai ta koya mini girki muka yi ta faɗa na gudo. Da na je" "London kuma su ba irin abincinmu suke ci ba dama bana son wahala sai na koma cima irin tasu. Kin san a lokacin Alhaji idan ya ji ta cin Tuwo ko wani abu sai dai ya siya a African restaurant ko kuma ya yi da kansa""" Na zaro ido ina mamaki. Cabɗi! Wai 'sai shi ya yi da kansa'. Har na hango Baffa Lawalli ko Baffa Zakari "suna tuƙa tuwo. Abinda ba zai taɓa faruwa ba kenan, ko a mafarki." Haka ta riƙa nuna min komai na kitchen ɗin. Ta haɗa ni da mai aikinta ta ce ta gwada min inda ake saka "komai da yadda ake konna burner ɗin. Akwai wata ma da ta shigo, na ji Hajiyar ta kirata da Saudah. Tana kallona ta ce ""ke ce Chef Zeey da Hajiya ke ta maganarki tun jiya?"" na gyaɗa mata kai." Na fahimci kallon reni a idanunta. Wato irin ban worthing Hajiya ta yi maganata ba ɗinnan. Lokacin da mai aiki ta buɗe min freezer inda suke ajiye frozen foods ɗinsu sai dana nemi tsari da talauci "sau goma a zuciyata. Wato nama ne da kifi danƙare a ciki sun yi ƙanƙara. Akwai naman Sa, Akwai gudar Akuya da aka yanka gida takwas, ga naman rago, ga naman Kaji. Hassana mai aikinsu ta ce min akwai naman Talo-Talo dana Zabi, ba wai Kaza kaɗai bane a wajen. Ni sai na rasa ma wanne zan ɗauka. Ba ni zan ci abincin ba amma ni ke ruwan ido. Su kam na san nama bai damesu ba." Hajiya Layla ta ce na yi mata Tuwon Biski da miyar Kuka amma gaskiya zan haɗa da wani abun. Yadda kitchen ɗin yake ƙal-ƙal da tsari sai na rasa ma a ina zan haɗa kurho ɗin gawayi da zan turara tuwon kamar yadda na yi a gidan Hajiya Maryam. Ai kuwa ina tambayar Hassana ta ce sai dai mu fita ta baya ina kunna gawayi a nan zan fara jin ƙara winwinwin. Ta nuna min wani abu wanda na fahimci smoke detector ne. Muka fita ta baya na je na haɗa wutan. Cikin tsari da ƙwarewa na fara komai. Ina tuwo ina prepping "miyan kukan da zan yi, ina so shima sai ruwan kukan ya dahu da kyau kamar yadda Kaka ta koya min kafin na zo na kaɗata." Kafin na ƙare girkin Janan 'yar Hajiya ta dawo. Ita da Saudah ne suka shigo kitchen ɗin wai tana son "ganina. Itama irin kallon da Saudan ta mini ɗazu shi take min, in fact nata ma ya fi muni. Ko kaɗan bata da daraja mutum kamar Hajiya. Kallon 'yar aiki ta ke mini ba Chef ba." "Ta yatsina fiska ta ce ""Yanzu wannan ɗinne Hajiya ke cewa za ta koya mini girki. Thank God Mi Amor" "baya son Tuwo balle ta ce saboda shi in koya""" Saudah dai dariya ta yi ta bi bayanta suka fita daga kitchen ɗin. Gwiwata sai ya sace iissssssss kamar an sace balon-balon. Ashe dai yadda Hajiya ta ke da fara'a ba haka sauran 'yan gidan suke ba. Da alama dai daga yau idan na fita ba zan ƙara zuwa ba. Kafin su fara min kallon 'yar Maula. Halal nake nema ba roƙo na zo yi ba. Lokacin dana gama wanke kitchen ɗin ni da Hassana sai na koma falo na zauna ina jiran ɗan Hajiyar da zai zo mu yi maganar restaurant. Ina zaune ina kallo a falo sai ga wani yaro ya shigo falon sanye da Uniform ɗin Makaranta a jikinsa. Yaron "kyakykyawa da shi, daka ganshi ka ga ruwa biyu. Ga gashin kansa baƙi siɗik a kwance lub irin na Turawa." """Hi, Sannu"" ya faɗa yana ɗaga min hannu." """Sannunka handsome boy, an dawo daga Makaranta?"" Ya gyaɗa kai sannan ya wuce sama da gudu." "Yaron ya burgeni, dan ban ɗauka ya iya Hausa ba." Can ina zaune duk na ƙagu mutumin dana ke jira ya zo sai Hajiya ta sauko ita da yaron ɗazu wanda nake da tabbacin jikanta ne ta ce yau za ta koya masa cin Tuwon Biski. "Wajen dining suka nufa ta dishing masa. Ina ji tana tambayarsa ko abincin ya yi daɗi, na leƙa na ga yaron" yana gyaɗa mata kai. Har yaron ya gama cin abinci wanda na ke jira bai dawo ba. "Hajiya ta zo ta zauna ta kira shi a waya. Ban san me ya faɗa ba, na dai ga ta cire wayar ta ɓata fuska." """Hajiya barin je na tattara kayana idan ya so yana zuwa ɗin sai na wuce""" """Ki yi haƙuri na riƙe ki Ziyadaah. Ki shiga kitchen ki ɗauki duk abinda kike so kin ji""" Na miƙe ina mata godiya. Tun ɗazu ta tura min alert ɗin kuɗin aikin dana yi. Nauyin alert ɗinne ma ya sa na shirya jiran ɗan nata ko zai kai ƙarfe takwas na dare bai dawo ba. "Da zan wuce kitchen ɗin sai ta ce na buɗe freezer na ɗebi naman da zai isheni. Allah Sarki matar arziƙi," kamar ta san naman nan dana gani yana raina. Babu kowa a kitchen ɗin. Tunda muka tattare kitchen Hassana ta koma ɗakinta. Itama duk yadda ta ke ganin wai ban kai ta girki ba da ta ci tuwon dana yi sai data ce dole Hajiya ta kirani na zo na mata girki. "I think waccar Saudar ma ta ci amma ita Janan bata ci ba, ban ma sake ganinta ba tun da ta leƙoni ta min" kallon banza. Talaka ya samu ganima dole yai bushasha. Ni da Hajiya ta bani damar ɗiban nama ba sai na buge da cika leda ba. Sai dana cika leda mai yellow da baƙi da nama amma still idona bai haƙura ba. Hassana ta ce idan naman yai wata bai ƙare bama ita da sauran ma'aikatan gidan suke rabawa a sake kawo wasu. "A yadda na ke ganin naman nan kuwa, ko kullum za a riƙa girki da shi zai iya kaiwa wata uku ma." Wannan greed ɗin ya tunzurani na sake ɗauko wani baƙin ledan cikin tarkacen dana zo da shi daga gida na sake sa hannu ina ƙoƙarin ɓanɓaro gudar kazar saboda ta yi ƙanƙara. Da ƙyar na cirota na ɗago zan sata a leda """U'u'um""" """Wayyo!"" Na saki ledar hannuna a tsorace saboda gyaran muryan da na ji a bayana babu shiri." A hankali na juyo cike da kunyar abinda aka kamani ina yi. Ga nan leda cike da nama a saman island ɗin kitchen ɗin ga ni nan kuma ina shirin cika wata ledar. "Hannunsa ɗaya riƙe da baƙin suit ɗinsa, ɗayan hannun kuma yana cikin aljihun wando." Kallon-kallo muka tsaya yi ni da shi. Na san kallon ɓarauniyar nama yake mini. Sai na ji wani kunya ya rufe ni. Ina so na ce masa Hajiya ce ta ce na ɗiba amma bakina ya kasa maganar sai rarraba idanu kawai na ke yi. "Juyawa yai zai tafi na ce masa ""Ha, Haajiya...Hajiya ce ta ce...""" A nan muka kawo ƙarshen Free Pages na littafin CHEF ZEEY: Love in the Kitchen ©AzizatHamza2025 CHAPTER TEN JAYKAY Yana jinta tana ƙoƙarin yi masa bayani amma ya shareta ya fice daga kitchen ɗin. Ya riga ya gama making "decision ɗinsa, wannan fake Chef ɗin babu abinda za ta masa. Maybe idan yana buƙatar buɗe restaurant" na 'yan Maula da Maroƙa then zai iya employing ɗin service ɗinta. """Jalal, kun haɗu ko?"" Hajiya ta tambaye shi yana ƙoƙarin hawa sama." """I think..."" fitowar Ziyada daga kitchen ɗin ya sa shi maida dubansa gareta. A tsorace ta ke, sai rarraba" idanu take kamar za ta yi kuka. Whether Hajiya ce ta bata damar ɗiban nama ko kuma sace naman take ƙoƙarin yi ba damuwarsa bane. "A Shekara biyu da yai a Nigeria yana running Kamfaninsu ya fahimci halayen akasarin Artisan 'yan Nigeria na rashin gaskiya da cin amana. Ko aikin plaza da ake yi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ana kawo complain ɗin sata da wasu ma'aikata ke yi. Yau wannan ya zari abu ɗaya ya siyar gobe wani ya siyo abubuwan da basu da quality ya kawo bayan an bashi kuɗin masu quality. So, Chef ɗin da ke satan nama a gidan da tayi aiki, to him halin rashin gaskiya irin na 'yan Nigeria ne." """Hajiya zan tafi, an kirani a gida, Kaka na nemana"" ta yi maganar muryarta na rawa." """Lah! Kaks ta ji ki shiru kenan. Ba matsala Ziyadah, ina ga kawai Jalal zai kiraki cikin satin nan sai ku yi" "maganar""" Bai ƙarisa jin maganarsu ba ya fara hawa stairs. He's already tired. Ba dan Hajiya da ta dameshi da kira ba da ba zai dawo yanzu ba. Yana shiga ɗaki sai ya cire kayansa ya shiga banɗaki ya sakewa kansa ruwa. Bai sauko ƙasa ba sai da ya shirya fita sallar Magariba. Kiran Junior ya yi suka wuce Masallacin tare. Da ke sun rasa jam'i wani ne ya ja su sallar Magaribar suka yi sallar su kusan biyar. Tsayawa ya yi har aka yi isha saboda yana so idan ya shiga gida ya je ya ƙarisa aikin duba report da bai samu ya yi ba. Lokacin da suka fito daga Masallaci sai Junior ya ce ya kai shi shan ice cream. Jalal ya ce masa to. Lokacin da suka shiga gidan sai suka samu Janan da Saudah sun ci kwalliya za su fita. "Ya tambayesu ina za su je, suka ce masa za su je cin pizza, wai Hajiya ta hana a yi musu girki su kuma ba" za su iya cin Tuwon da aka yi ba. Nan Junior ya kama tsalle wai shima zai ci Pizzan. Jalal ya kalli Junior ya ce ya bisu kawai. Lokacin da suka fita har zai haura sama sai ya ce bari ya haɗa coffee ya haura sama da shi saboda ya ji daɗin aiki. Yana shiga kitchen ɗin sai ya samu Hassana tana mayar da nama daga cikin leda zuwa Freezer. Kenan yarinyar can bata ɗauki naman ba. """Yallaɓai, barka da dare, akwai abinda za a maka ne?""" Ɗaga mata hannu yai ya nufi gaban coffee maker zai haɗawa kansa coffee. "Ƙasa-ƙasa yake jin Hassana na faɗin ""Ziyada za ta ji babu daɗi idan ta isa gida ta lura bata sa nama a cikin" "kayanta ba. Kai! Ba rabonta bane""" "So, ZIYADA sunanta. Ya ɗauka Zainab ne saboda yadda Hajiya ke ta nanata masa Chef Zeey tun jiya." Ya gama abinda zai yi ya fita daga kitchen ɗin ya bar Hassana mai aiki tana goge-goge. "A can ƙasan ransa sai ya ji babu daɗi da yarinyar ta bar naman saboda shi, musamman da ya fahimci" Hajiya ce ta bata damar ɗiba. Ya girgiza kansa kawai ya kurɓi coffee yana mai cigaba da aikin da ya ke. ZEEY Zuciya babu daɗi. Yin zuciya wa abinda kake so akwai cin rai. Gani nan ina kwance amma ƙarfe ɗayan "dare bacci ya ƙi zuwa mani. Tunanin naman dana yi fushi na bari a gidan Hajiya Layla ne a raina. To ni inama ruwana da shi da zan haƙura da naman saboda ya ganni. Ai ba sata na yi ba, cewa aka yi na ɗebi nama yadda zai isheni." Kallon da yai min ne na rashin yarda duk ya sa na ji gara kawai na haƙura da naman. Ko lokacin da zan fita da ɗan Bagco bag ɗina Hajiya na cewa ban de manta komai ba na ce mata ban manta ba. Direban gidan ta sa ya kawoni gida. Ina zuwa na samu yaya Aminu ya zo yiwa 'yan gidanmu Sallama gobe zai wuce Yola. Ina ji Kaka na masa tsiya wai har yanzu bai kawo mata kishiya ba amma ban tanka musu ba. Lokacin da muka keɓe dan ya min sallama ce masa na yi kaina na ciwo muka yi sallamar a gurguje ya tafi. "Da gaske ne kaina na ciwo saboda gajiyar aiki dana kwaso, amma musabbabin rashin jin daɗina saboda" "haushin rashin ɗaukan naman da ban yi bane. Da yanzu na gama soya naman nan, koma na yi dambun kaji da shi. Wani ɗaci ya taru min a wuya ya hanani sukuni sai juyi na ke akan gado." Tin dana dawo nake jira na ga ko Hajiya za ta kirani ta ce mini na yi mantuwa za ta aiko Direba ya kawo "min kayana amma shiru. Saboda na ankarar da ita ma sai na yi mata text na tura ina mata godiya bisa karamcinta. Gajeriyar amsa ta turo min wai ""you're welcome, Dear"". Text message ɗin ya sake tunzurani. Na dinga jin haushin kaina ni kaɗai. Koda ya ke ba laifinta bane. Ita kam ta yi nata da ta ce min na je na ɗebi abin dana ke so. Ni ce dai zuciya ta ɗebe ni na bar kayan saboda ɗanta ya min kallon ɓarauniyar nama." "Shima ɗan nata shegen girman kai, ina ƙoƙarin yi masa bayani ko kallona bai yi ba ya fita daga kitchen" ɗin. Gaskiya Hajiya Layla bata ci sa'ar 'ya'ya masu hankali ba. Na rufe ido ina tuno yadda komai ya faru. Wani tingling na ji a zuciyata lokacin dana tuno handsome face "ɗinsa. Na girgiza kai, handsome or not handsome yana da girman kai, ni kuma bana harka da masu girman kai. Besides ma na san babu abinda zai sake haɗa mu. Maganar restaurant ɗinsu ba zai yiwu ba. Zan cigaba da neman kuɗin da zan buɗe nawa restaurant ɗin kawai." "Ina son yin bacci, amma bacci ya ƙi zuwa. Duk wannan dogon mutumin ne ya jawo mini. Da wani ƙwala-" ƙwalan idanunsa a wajen. Na ja tsaki a raina na sake juyawa a karo na ba adadi tunda na kwanta akan gadon. Ya jima ban ji wani namiji ya tsaya min a rai ba. Bayan rabuwarmu da yaya Aminu kulle zuciyata na yi gaba ɗaya na jefar da key ɗin zuwa lokacin da abubuwa za su daidaita mini har na yi tunanin soyayya da aure. Hana ƙarya lokacin da nake level 2 akwai wani Lecturer ɗinmu da na ji yana ɗan burgeni kaɗan. Shima kuma tunda ya tafi ƙaro karatu na watsar da batunsa. Dama kawai crushing nake ba wai ina sonsa ko wani abu bane. Wayyo Allah! Ashe ba maganar nama bane kawai ya tsaya mini a rai. Ya Allah! Na girgiza kaina saboda na dena day dreaming abinda ba zai yiwu ba. Saurin kawar da tunanin da ke ƙoƙarin shigo mini kai na yi na koma lissafin hidimar bikin da ke gabana. "Gobe Talata zan je gidansu Faty mu fara shirye-shirye. Ranan Laraba za ta yi bridal shower, Ranan Alhamis za a yi kamu. Friday kaman yini kawai za a yi a gidansu, sai kuma Asabat za a ɗaura aure a kuma yi reception. Ta so a yi dinner ranan Friday amma mai girma Ango ya ce ba za a yi ba wai baya so. Ni dai na san saboda bashi da kuɗin yi ne." "Ina tausayawa Bestie, ta saka kuɗi sosai a hidimar bikin nan. A matsayina na aminiyarta na yi ƙoƙarin" bata shawarar ta rage kashe-kashen kuɗin nan saboda bayan biki zata ji jiki idan ba kuɗi. But sai ta nuna mini babu yadda za a yi Tyma Glams guda ta yi biki a garin Zaria kuma a ce bikin ba zai kece reni ba. "Iyayen Faty dai ma'aikatan Gwamnati ne. Babanta na aiki a Ministry ita kuma Mamanta na aiki a Asibiti," "duk da kusancinmu har yau ban sani ba ko Mamanta Nurse ce ko kuma Matron, ni dai na san a Asibiti take aiki. A rayuwata ban cika bin ƙwaƙwƙwafin mutane ba, musamman abinda ya danganci iyaye ko asalin mutum." Ban san yaushe na yi bacci ba. Na dai ji sama-sama Kaka na tashina da Asuba wai na tashi na yi sallah. Sake rungumar pillow na yi saboda kamar ma yanzu ne baccin ya fara mini daɗi. """Ziyadatu, ki tashi ki yi sallah sai ki koma baccin kin ji""" """Zan tashi, Kaka"" na sake ƙudundunuwa cikin bargo na rufe idona na cigaba da bacci. Alarm ɗina na" ƙarfe biyar da rabi ne ya fara ƙara. Na sa hannu na lalubo wayar na dismissing alarm ɗin. Ganin dai ba daɗin baccin zan ji ba idan ban yi sallah ba sai na tashi zaune ina murza idanuna. Na ɗan mammatsa yatsun hannuna suka bada sautin ƙat!. Na sake yiwa yatsun ƙafan ma haka sannan na tashi daga kan gadon na fito ƙofar ɗaki na ɗau buta na wuce banɗaki. Bayan na yi sallar Asuba na kwanta a sallaya ina karanta Azkar a wayata sai ga text ɗin yaya Aminu yana min ya jiki tareda cewa yanzu zai kama hanyar Yola. Na tura masa addu'ar Allah ya tsare masa hanya. Daga reply ɗin text sai na buɗe data na na fara bibiyar messages ɗin da ke shigowa. Ina jan carbi da "hannu ɗaya ɗayan hannun kuma ina danna waya. Lissafin Azkar ɗin dana ke yi ne ya ƙwace mini wannan ya sa na yi Astagfirullah na ajiye wayar a gefe na maida hankali kan Azkar ɗin. Allah dai ya yafemu gaba ɗaya, waya ba ƙaramin ɗauke mana hankali yake ba." Da na ƙare Azkar sai na sake hayewa gado na kwanta dan gaskiya bacci bai isheni ba. Ko wanka ban yi ba ƙarfe tara na safe ina sharan ɗaki Faty ta kirani wai ina nake ta jini shiru. Na ce ta yi haƙuri zan zo zuwa shaɗaya idan na karya. A gurguje na ƙarisa sharan na je na yi wanka na fito na saka ɗumamen tuwo a gaba na fara ci. Call it "Talauci, amma ni duk abinda zan ci da safe in dai ba ɗumamen tuwo bane baya riƙe mini ciki. Maybe saboda da shi aka sabar min ne. Idan kuka ga ban ci ɗumame da safe ba to kodai babu ɗumamen ne, ko kuma bani da lafiya ko kuma ba a gidanmu nake ba." "Wataƙila idan na yi kuɗi zan dena son ɗumame in koma breakfast ɗin 'yan gayu, but for now, ɗumame" any day. Lokacin dana isa gidansu Faty sai na samu aiki na jirana jingim. Ta ce ni zan mana abincin bridal shower "so dole na fara haɗa komai kafin goben. Snacks za mu yi da kuma Fried rice. Haka na cire hijabi na naɗe hannun rigana na fara kwaɓa Donut, dana gama sai na haɗa samosa sheets na saka fillings ɗin a ciki muka kai gidan maƙociyarsu za ta saka mana a freezer gobe da safe sai dai kawai a soya." Bayan na gama wannan muka fara fitar da souvenirs da za ta rabawa ƙawaye gobe a wajen bridal "shower. Mu biyu muka yi aikin da ƙanwarta Basma. Sai gobe ƙawaye za su fara zuwa kuma ta fi trusting ɗina akan kowa. Unlike ni da nake da 'yan tsirarun ƙawaye ita Faty akwai ta da mutane. Ni ce best Bestie ɗinta yanzu, amma tana da wasu Bestie ɗin bayan ni. Wasu na sansu muna mutunci sosai, wasu kuma kawai gaisuwa ne idan an haɗu. Amma a hidimar bikin nan idan akwai wacce Faty ta trusting da shirye- shirye, to ni ce." Ba mu muka gama jigila ba sai gabannin Magariba. Ta yi-ta yi na kwana na ce ta yi haƙuri gobe zan shigo "mata da sassafe. Ni da kwana a gidansu sai ranan Jumu'ah zuwa wayewar Asabat da za a ɗaura aure. Na ƙi kwana ne saboda ni tun asali idan ba ya kama dole ba bana son kwana a gidan mutane. Duk inda zan je a gidan 'yan'uwanmu in dai a Zaria ne bana iya kwana, duk min dare zan dawo gida na kwana kusa da Kakata. Dalili na biyu kuma shine saboda gidan an ɗan fara cika. Ɗakin nasu da suke kwana su biyu da ƙanwarta Basma yanzu akwai jakukkunan mutane sun kai uku a ɗakin ni kuma a rayuwata bana son takura." Da ƙyar dai ta yarda bayan na mata alƙawarin ƙarfe shida na safe ina gidansu. Ni kaɗai na fito na ce ba sai ta rakani ba. Na tsare Keke na taho gida. Ina shigowa na shiga banɗaki na yi fitsari. Na riƙe fitsarin ne tun daga gidan su Faty. Ɗazu dana shiga "banɗakinsu zan yi, sai na samu 'yan biki sun ɓata banɗakin shiyasa ban yi ba." Dana fito daga banɗaki sai na jefa guga a rijiya zan ja ruwan wanka sai na ji sallamar yara. """Adda Ziya, wai ki je in ji wani mai mota a waje""" """Kai Yakubu, wani mai motan ne yake nemana?""" """Wallahi wani mai haɗaɗɗiyar mota ne ya ce mu kiraki, yana waje yace mu kira masa Chip Zeey""" """Bakinka ne Chip Zeey ɗin ai. Ka je kace musu ina zuwa""" Shi da zugan yaran da suka shigo suka fita da gudu. To ni Ziyada waye zai zo nemana da Mangaribar Allah. Jin suna neman Chef Zeey ya sa zan fita saboda "kar alkhairi ya wuce ni, wataƙila masu son a yi musu aiki ne ko kuma talla." Fasa jan ruwan na yi na koma ɗaki na ɗau dogon blue hijab ɗina mai hannu na saka. Ban saka ko bra ba "amma shimin da nasa ya packaging ƙirjina da kyau. Ina da ɗan ƙiba, amma daɗin abin nonuwana a tsaye suke. Beside ma akwai duhu babu wanda zai lura baƙin vest ne a jikina da zani, daɗin hijabi kenan, sai ya ɓoye maka komai ka fito with confidence abinka. Na fita ba tareda na yiwa Kaka magana ba dan tana Sallah. Idan na ce zan mata magana yanzu za ta fara tafi a Sallah. Tsohuwata sai a hankali." Ban gane motar ba. Da na yi tunanin ko Hajiya Layla ce ta aiko min Direbanta ya kawo min naman dana "manta jiya, amma kuma ba irin motar da a kawoni gida da ita bane jiya. Wannan motar da nake gani ta fita haɗuwa." Ina ƙarisowa wajen motar Direba ya fito ya zago inda nake muka gaisa ya ce saƙo ya kawo min. Ni dai na zubawa sarautar Allah ido har ya buɗe boot ɗin motar ya fito min da manyan ledoji guda biyu. "Tsayawa na yi ban karɓa ba dan kar na karɓi kayan sata na ce ""Malam yi haƙuri ban gane ba, wannan" "saƙon daga ina ne?""" """Yallaɓai Jalal... "" sai ya gyara maganarsa ya ce ""Daga gidan Hajiya Layla ne aka ce na kawo miki""" Tabbas na ji duka suna biyun da ya faɗa. Yallaɓai Jalal da Kuma Hajiya Layla. """Gashi, ina sauri ne"" ya faɗa yana sake miƙo min ledojin. Sai a lokacin na karɓi ledar a hannunsa na ce ya" yiwa Yallaɓai da Hajiya godiya. Daga yanayin nauyin ledojin na fahimci nama ne. Ina zuwa ƙofar gida su Yakubu suka tareni wai za su "riƙe min ledar na ce su bari. Haka na shiga da kayana ciki na wuce sashenmu. Torchlight ɗin wayata na kunna na haska ledar and hasashena ya yi gaskiya, Kaji ne a cikin ledar farko. Na fara bubbuɗewa, manyan Kaji guda biyar sai ɗaya ledan kuma naman Sa ne ban san ko kilo nawa bane a ciki amma dai" "dayawa. Dariya kawai na fara ni kaɗai a ƙofar ɗaki. Ko saƙon daga Yallaɓai Jalal ne, koma daga Hajiya" Layla ne. Yau kan zuciyata fari ƙal zan kwanta. Gajiyar dana kwaso daga gidan su Faty tuni ya washe. Na shiga na faɗawa Kaka daga gidan Hajiya Layla "ne aka kawo min nama. Wankan da ban yi ba kenan. Sallah kawai na yi na zo na hau gyaran nama. Magulmatan gidanmu har da turomin 'ya'yansu wai su tayani aiki. Ai kafin ma su fara tunanin wani abu na ce musu na bikin ƙawata Faty ne dana gyara gobe zan packaging na aika musu. Idan ba haka ba yanzu za ku ga ana miƙowa Kaka kwano a sam musu nama, dan sun san ni kam ba zan basu ba." "Ban gama aikin suya da dambu ba sai kusan ƙarfe biyun dare. Lokacin dana yi wanka na zo zan kwanta," bayana kamar zai tsage gida biyu. Ina kwanciya akan gado bacci ya tafi dani... CHAPTER ELEVEN ZEEY Ni dana ce zan je gidansu Faty ƙarfe shida na safe sai gashi ban bar gidanmu bama sai ƙarfe takwas da "kusan minti talatin. Wallahi gajiyan soye-soyen jiya ne ya sani makara. Ga ni 'yar Talaka amma jikina baya son wahala, dik sadda na sha aiki haka yanzu jikina zai fara ciwo." Da safe da Kaka ta ga yawan naman da dambun dana yi sai ta fara ƙoƙarin convincing ɗina wai na ɗibawa "'yan gidanmu naman. To in faɗa muku Wallahi muna cikin maganar sai ga Maman Suwaiba da kanta ta zo da 'yar kwano wai dan Allah in sanmata ko ɗan hanji ne za ta watsa a miyar kukan da za ta yi da rana. Wannan matar da kwaɗayi. Innalillahi!. In dai kana neman kwaɗayi to ita ce Oga kwata-kwata. Ga ta bata da zuciya kamar sauran matan. Sauran matan za ka iya hanasu abu su haƙura, amma Maman Suwaiba idan ta fara maka sintiri tana aiko maka 'ya'yanta sai ka bata dan dole." """Saboda ke zan basu, Kaka. Kuma Wallahi saura ki ce musu naman namu ne duka.""" """Ki ce musu na bikin ƙawata Faty ne"" na sake jaddada mata." """Idan kika aika musu ma ai babu wacce za ta dawo""" """Kaka kenan, kamar baki san halinsu ba. Ga shi nan a cikin kwalla zan tura ƙarƙashin gado, Allah idan na" "dawo na samu kin sake bawa wani a cikinsu zamu yi faɗa""" """Ba zan basu ba"" Kaka ta faɗa tana yagar cinyan kazar dake hannunta." Cikin wasu takeaway na aikin abinci da na yi kwanaki na zuzzuba musu naman dan su sake tabbatar da cewa na bikin Faty ne. Har na shirya na tafi banda soyayyan hanta dana ci da ruwan Lipton ban iya cin naman ba. Jiya da nake soyawa na ɗan taɓa yanzu kuma warin suyan ya hau mini kai. Shiyasa ma na yi dambun dayawa saboda zan fi cinsa idan na dawo. Ban turawa Hajiya Layla saƙon godiya ba dan ban gama tabbatar da ita ta aiko saƙon ko kuma ɗanta ne ya aiko ba. Da alama dai siya aka yi ba wai an ɗebo daga cikin na gida bane. Dana isa gidan su Faty sai na samu har Sumayya ta iso. Muna shiri da Sumayyan dan haka ni da ita muka "fara shirin yadda za a tafiyar da abincin bridal shower. Na ce mata ita ta soya mana Samosa ni kuma zan mana fried rice ɗin. Da ke na ɗebo ruwan nama daga gida da ita na dafa mana shinkafar. Shiyasa tun kafin ma na zubata cikin veggies dana soya da ya ji hanta sai ƙanshi shinkafar ta ke. Kan kace me wajen ya baje da ƙanshi. Ƙawaye suna ta zuwa. Wasu su sameni su ce za su tayani aiki, na ce musu kar su damu. Wasu kuma su wuceni suna min kallon mai aikin abinci. Ban ji haushinsu ba tunda ba ƙarya suka yi ba, aikina kenan dafa abinci. Ba dan yanzu da harkar content ya ɗauke min hankali ba ai ina zuwa girka abincin biki sosai." Ƙarfe goma na safe aka ce za a fara bridal shower ɗin amma ba a fara bama sai past 11AM. Lokacin da suka fara ni ina ƙoƙarin kwashe abinci a take-away. Dana gama na je na yi wanka na chanja kaya na dawo cikinsu aka cigaba da games ɗin da ake yi dani. Abinci ya yi daɗi kowa ya yaba. Ƙarshe har nema aka zo ana yi daga 'yan bikin da suka zo. Mu dai dama namu na ƙawaye na riga na packaging ma kowa. Waɗanda suka biya kuɗin bridal shower har da souvenir aka saka musu. Da yamma lis ina ƙoƙarin dawowa gida sai ga kiran Hajiya Layla. Na ɗau wayar muka gaisa. Ta ce mini ta yi magana da ɗanta Jalal ya ce na zo interview ranan Asabat a Plaza ɗinsu. Na ce mata ta yi haƙuri Asabat muna da biki ba zan samu zuwa ba. Ta ce min babu komai za ta bawa Jalal nambana sai mu fixing wani lokacin. Na yi mata godiya. Jin bata yi maganar nama ba sai nima na yi shiru. "Da dai na ce ba zan sake yin maganar restaurant ɗinnan ba, amma tunda Hajiya Layla ta nace da" "maganar zan sake duba yiwuwar abin. Koma menene dai yanzu kam sai bayan biki, ni kaina yanzu ban ganewa kaina ba balle batun wani interview." Haka na share zancen na wuce gida. Da dare ƙarfe takwas dai-dai sai ga text ya shigo wayata daga baƙuwar number. Wai ana gayyatata interview ranan Asabat ƙarfe goma na safe a JK PLAZA. A ƙarken text ɗin kuma sai aka rubuta J.K. MAIYAƘI. Na maimaita sunan a fili JK Maiyaƙi. Na gyara kwanciyata akan sallaya inda na yi sallar Isha sannan na rubuta masa amsar saƙonsa nima a "ƙarshe sai na rubuta nawa sunan Chef Z.S. Haruna. Idan professionalism ne nima na iya. An ce yanzu a harkar kasuwanci sai da packaging, ko Branding nema ake cewa, duk dai. Dan haka nima nake branding kaina a matsayin Chef a koda yaushe." Microbiology nake karantawa a Jami'a amma ni yanzu lissafina ya koma kan Kasuwanci da harkar girki. "Shiyasa bana wasa da bibiyan littatafai da kuma YouTube videos da ake koyar da Kasuwanci. A harkar Food Content kuma na fi maida hankali wajen bibiyar 'yan Kudu saboda na ga su sun fi ɗaukan abin a matsayin business kuma za ka ga komai na su da tsari. Mutanenmu na nan kuma sai girman kai, lokacin da video na ya tafi viral na ɗan fara bibiyan wasu dan su nuna min yadda ake neman talle daga hannun manya-manyan Kamfanoni irinsu Dangote da Hollandia amma babu wacce ta kulani. To ni suma ce in" "biya kuɗi za su faɗa mini mana, amma babu wanda ya responding mini. Ko harkar tallen nan ma da" "dikake nake komai, sai ɗan abinda na ke koya daga gefe a wajen manyan Food content na Kudu." "Allah ma ya sa dalilin yaya Aminu na taso da son karatu da bincike, dan haka na san a hankali dai nima" zan gama gane komai gameda harkar Food Content ɗinnan. Karatu shi ya banbantani da sauran 'yan gidanmu. Har yanzu ni kaɗaice mace a cikin gidanmu da ta ke "Jami'a. Akwai kuma Aisha 'yar wajen Baffan Katsina da take NCE yanzu, ina ga ko ta gama ko kuma ta kusa gamawa, ban dai sani ba. 'Yan gidan namu ne zumuncinmu sai a hankali." Ina gama tura masa reply na manta da batun interview na cigaba da lissafin hidimar da ke gabana. Ranan "Jummu'ah aka yi Kamu kuma ya yi kyau ba kaɗan ba. Har video na yi na saka a duka social Media pages ɗina. For the first time kenan da nake saka hoton fiskata a shafukan Chef Zeey. Kun san idan mutum ya yi make-up, ji yake idan bai ɗan ɗaura hotunan an kalla ba kaman bai mori make-up ɗin bane. To nima da aka min make-up sai na ji gara na nunawa duniya fiskata. Gani ina tare da ƙawa mai yin make-up amma ni bana yi. Ina ga banda a bikin nan sau ɗaya na tsaya aka min professional makeup a rayuwata. Lokacin dana gama culinary school a Kaduna da za mu yi graduation." "Amarya Faty ta yi kyau ba kaɗan ba. Ranan Bridal shower da Kamu duk ita ta yiwa kanta kwalliya, amma" yau ɗaurin aure wata ƙawarta itama make-up artist ɗince ta tsantsara mata kwalliya na gani na faɗa. Muna cikin shirin tafiya wajen da za a yi reception bayan an ɗaura aure sai ga test daga J.K. Maiyaƙi wai yana jirana for the interview tun awa ɗaya daya wuce. Cabɗi! Wani interview kuma ana zaune lafiya. Ba na rubuta masa reply akan muna da biki ba zan samu zuwa ba a mayar da shi Sunday. Na sake duba wajen messages ɗina dan na tabbatar da text ɗin dana tura sai na ga ashe text ɗin bai tafi ba. Subhanallahi! Na riƙe baki... *** JAYKAY Zai iya cewa tun da yake a rayuwarsa ba a taɓa ɓata masa lokaci irin na yau ba. Gashi nan a cikin restaurant side dake cikin Plaza for over an hour yana jiran yarinyar nan babu ita babu dalilinta. Ba dai wani wrong impression ta samu akansa ba dan ya sa an aika mata da nama. Ya faɗawa Direbansa "ya ce mata daga wajen Hajiya ne saƙon ba daga shi ba. To, ko dai ba hakan ya faɗa ba?." Saboda Hajiya yasa aka aika mata naman. Washegarin ranan da abin ya faru da ya fito zai karya sai ya ji "Hajiya da mai aikinsu na maganar yarinyar ta manta bata tafi da naman data ɗiba ba. Har Hajiyar ke cewa ba rabonta bane, idan ta sake zuwa sai a bata." "He felt guilty, tunda ya san saboda shi yarinyar ta ajiye naman ba wai saboda mantuwa ba. Shi yasa ya" "bawa Direbansa kuɗi ya ce ya siya ya kai mata. Bai ma tsaya saurarenshi ba lokacin da ya ke tambayarsa kwatancen address ɗin, cewa ya yi yai wa Direban Hajiya magana ya san gidan." Bayan ya dawo daga office ma still da maganar Chef Zeey Hajiya ta tareshi wannan ya sa shi faɗa mata "cewa dole ne yai mata interview saboda ya gane ko ta dace a ɗauketa ko bata dace ba. Ya yi hakan ne saboda ya samu damar kashe maganar gaba ɗaya. Idan ya faɗawa Hajiya ya yi mata interview kuma bata qualifying ba babu abinda Hajiya za ta iya, dole ta haƙura da local Chef da ta ke ta ƙoƙarin cusa masa a lissafinsa. And with this zai samu damar focusing akan abubuwan da suka dace. A yadda ya tsara za a buɗe Plazar ne nan da wata uku idan komai na Restaurant ɗin ya kammala. Chanja tsari a dai-dai wannan gaɓar zai komar masa da shirinsa baya ne kawai." Yana shirin tashi daga inda ya ke zaune ya ga shigowar text wayarsa. Tsaki ya ja bayan ya gama karanta text ɗin. Yarinyar nan ta rena shi. Shi take cewa tana wajen biki ya yi haƙuri sai gobe. Tun Thursday ya tura mata text na invitation ɗin interview ɗin amma sai yau Asabat bayan lokaci ya ƙure ta ke ce masa tana wajen biki. A yadda bata ɗaukan abu da mahimmancin ake so ya barta ta running restaurant ɗin da suke tunanin shi zai fi kawowa Plazar kuɗi idan aka buɗe. Ba zai ma yiwu ba. "Shi baya son reni, and clearly yarinyar nan ta rena shi. Zai faɗawa Hajiya kawai yarinyar bata zo ba which" means bata da interest akai a wuce wajen kawai. Ya miƙe ya fita yana jin haushin kansa da ya ɓata lokaci yana jiranta. Lokacin da ya je gida sai ya samu mutanen gidan basa nan. Hajiya wai ta tafi biki. Janan bai san ina ta je "ba, itama wata ayawon ce." """Yaya Jalal ko na kawo maka abinci"" Saudah ta katse shi." """No, Thank you"" ransa a ɓace yake ba ta cin abinci ya ke ba." """Ni ce na yi girkin fa. Barin zuba maka kaɗan please ka ɗan taɓa. Idan ka ci na san sai ka bani aiki a" "restaurant ɗin da za a buɗe"" ta ƙarisa maganar tana murmushi." Ya fahimci abinda ta ke ƙoƙarin yi. Ba za ta samu attention ɗinsa ta haka ba. Ba za ma ta taɓa samun "attention ɗinsa bane saboda har gobe kallon budurwar Jamal, kuma cousin ɗinsa ya ke. Dole ya furta mata wannan da bakinsa kada ta cigaba da ɗaukan wrong impression akansa." """Erm... Saudah""" """Yes, yaya J"" ta amsa tana kallonsa fiskarta cike da murmushi." """Har yanzu ina tareda Cassandra""" "Saudah ta sauke idanunta ta furta ""I know"" a hankali" """ ba sai na spelling komai ba kin san me nake nufi. Kada ki zauna a gidan nan saboda ni, abinda Hajiya ke" "son haɗawa tsakaninmu ba zai yiwu ba. I'm Sorry Saudah""" "Ya lura da hawayen da ya zubo mata lokacin da ya gama maganarsa, amma babu abinda zai iya yi akan" "haka. Wuceta ya yi ya haura sama. Part of him ya ji relief na cewa ya fayyace mata gaskiyarsa, ɗaya part" ɗinsa kuma yana jin tausayinta. "Yana shiga ɗaki wanka ya yi, ya ce bari ya ɗan kwanta jiya bai yi bacci da wuri ba ya bi dare yana duba" wasu ayyuka. Kafin ya kwanta ya ɗau wayarsa ya ɗan leƙa social media. Zuciyarsa ce ta riya masa ya sake leƙa shafin Ziyada. Hotonta ya fara cin karo da shi wanda ta ɗaura mintuna takwas da suka wuce. Wato ta ɓata masa lokaci tana can tana ɗaura hotuna a social media ko?. Zai bata mamaki kuwa. Haka kawai sai ya samu kanshi da ƙurawa hoton ido. Sai yanzu ya samu damar ƙare mata kallo. The last "time da ya ganta kallon yarinya ya mata, probably under 20, amma a wannan hoton ya ɗan lura da girmanta, probably tana mid 20's ɗinta. Ya jima yana kallon hoton, yana bin fiskarta da kallo tun daga cikar gashin giranta har ya kai kan full lips ɗinta da suke so attractive kamar suna jawoshi ya kissing ɗinsu..." Vibration na kira ne ya shigo wanda hakan ya sa shi yin firgigit har wayar ta faɗa saman ƙirjinsa. Ya ɗau wayar yana mamakin kansa. Bai taɓa tsayawa kallon hoton wata mace haka ba. This is not him. Ya kawar da tunanin ta hanyar kiran numbar Hajiya da ta kira shi... CHAPTER TWELVE ZEEY Mun gama biki lafiya. Da ni aka kai Amarya muka tsaya aka yi siyen baki abokanan Ango suka wuce da "mu gida. Amarya ta ce wai na tsaya na kwana, na ce mata ba dani ba. Yadda Ango ke ta rawar jiki lokacin da ake siyan baki a hannu yake. Kar na kwana a gidan sabbin ma'aurata kunnena ya jiyo mini abinda bai kamata ba. Na san itama ta faɗa ne kawai abinda Anty's ɗinta suka yita ɗirka mata tun da aka shiga satin biki ai ba zai barta ta tuna da ni ba idan ta shiga hannun Ango." Nima wani abokin Ango mai suna Bashir ya sakani a gaba wai sona yake. A motarsa aka kawoni gida kusan ƙarfe goma da rabi na dare. Da ke akwai mutane biyu da zai kai nambar wayata kawai ya karɓa suka wuce. Na dai bashi numbata ne kawai saboda surutunsa amma ba wai dan ya min bane. Da zan shiga gida na haɗu da Baffa Lawalli ya fara faɗa wai daga ina nake. Kuma fa tun jiya na je na same shi har ɗaki na ce za a yi bikin ƙawata zan kwana a gidansu kuma da ni za a kai Amarya. """Ni bana son yawon dare, ki kiyaye"" na ce masa ya yi haƙuri Abokanan Angon ne basu zo da wuri ba." "Yana ganin ledoji a hannuna sai ya sake fiska ya ce ""ba za a bamu kayan bikin bane""" Kwaɗayi dai a wajen Bawan Allah nan. Da shi da uwargidansa ban san wa ya fi kwaɗayi ba. Na dai miƙa masa leda ɗaya wanda ke ɗauke da take-away da aka saka snacks da nama da kuma Coca- Cola guda ɗaya. Na haɗa shi da shi ya je can ya ƙarata na wuce sashenmu. "Kakata ko shiga ɗaki bata yi ba, Allah Sarki! tana zaune a tabarma tana jirana." Rediyon data kunna ma ya dena yi sai shu-shu-shu yake amma bata kashe ba. """Kaks na dawo""" """Ziyadatu kun yi dare gaskiya, Sannu da dawowa""" """Wallahi Kaka Ango da Abokanansa ne 'yan renin hankali, wai fa kuɗin siyan baki dubu goma suka bamu." "Da ƙyar suka ƙara dubu biyu akai. Mijin Faty ba dai maƙo ba, Kai! Faty zata ji jiki a hannunsa, ita kanta da" "ta ji yadda ake ta jayayya ranta sai da ya ɓaci, kamar zata yi kuka""" "Kaka ta ce ""Kul! ke kin san wa za ki aura ne?. Ki yi mata fatan alkhairi ki yi shiru""" """Haba Kaka! Labari fa nake baki""" """Hadisi ya ce faɗi Alkhairi ko ka yi shiru""" """Allahu Akbar, Malama Altine Mai Tuwo na ji wa'azi, zan gyara. Allah ya bawa Faty da Angonta zaman" "lafiya. Ba shikenan ba"" na ƙarisa maganar ina dariya." "Idan ina son tsokanar Kaka, Altine Mai Tuwo nake kiranta." Ban kwanta ba sai dana watsa ruwan zafi. Alhamdulillahi dai tunda an gama biki lafiya. Na bautu ba "kaɗan ba a bikin nan. Na saka kuɗi, na saka jiki, na saka zuciyata a wannan hidimar. Na tsayawa Bestie ta ko'ina ban bari ta ji kunya ba. Bikinta ya yi tashe a social media musamman a shafukan masu Make-up da suka nuna mata solidarity suka yita posting videos da hotunan bikin." *** JAYKAY """Saudah ta koma Abuja"" Hajiya ta yiwa Jalal magana lokacin da suke karyawa." "Ya sani saboda maganar da ya mata jiya ne ta tafi. But, da ta tsaya jiran gawon shanu, gara ta tafin kawai." A hankali zata samu wani namijin da ya fishi. """Oh! Hope ta isa gida lafiya?"" Yai tambayar dan magana ba wai dan a bashi amsa ba." """Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi"" Hajiya ta faɗa fuskarta babu daɗi. Ko bata furta ba ka san ta ji zafin" rashin yiwuwar wannan haɗin. """Amin"" Jalal ya amsa ƙasa-ƙasa." Shiru ne ya biyo bayan haka. Yana shirin miƙewa saboda ya gama cin nasa abincin Hajiya ta tambayeshi maganar Chef Zeey. Yai shiru ya rasa abin da zai faɗa. Idan ya ce mata ya soke interview ɗin ya san Hajiya ba za ta ji daɗi ba. "Ga maganar Saudah da bai gama lafawa ba zai sake ɓata mata rai. Bai san mai yasa Hajiya ta damu da yarinyar nan ba. There's nothing special about her. A'a, akwai wani abu guda, sexy lips ɗinta da suka saka shi wasu irin mafarkai jiya da dare. Amma kam idan qualified Chef suke nema da zai tafiyar da restaurant ɗinsu to wannan yarinyar da Hajiya ke ta waƙar sunanta tun ranan Monday bata da irin skills da qualification da yake buƙata." """Zan mata interview yau"" ya faɗa bayan ya saita tunaninsa." """Ban ce dole sai ka ɗauketa ba Jalal, amma Dan Allah ka nitsu ka fahimci idea ɗinta kafin ka yanke" "hukunci""" """I'll do that"" ya faɗa yana miƙewa tsaye." Sai bayan ya fita daga gidan sannan ya turawa Ziyada text akan ta same shi a JK Plaza ƙarfe goma na safe. "That is, nan da awa ɗaya kenan..." *** ZEEY Da ciwon jiki na tashi safiyar yau. Da ƙyar ma na tashi na yi sallar Asuba ƙarfe bakwai har da 'yan mintuna. Babu inda baya mini ciwo musamman kafaɗuna da kuma bayana. Sai bayan na samu na gasa jikina da ruwan zafi around 9 na safe sannan na bawa yunwar cikina mahimmanci. Bana tunanin throughout jiya na ci abincin kirki a wajen biki. Daga cikin tukunya na ke cin ɗumamen tuwo da Kaka ta rage min. Da ke ya ɗan yi sanyi sai na sake "ɗumamawa na zuba enough nama saboda na ji daɗin ci. Na barshi ya sake tafasa har sai da miyar ya fara ƙonewa sannan na sauke. Ɗazu na duba cikin kwallar da muke ajiye kayan tea amma babu komai sai TopTea da Milo, babu madara. Babu yaro kusa balle na aikesu siyan madara. Sai kawai na juye Milo da sugar a cikin ruwan zafi. A ƙofar ɗaki na zauna akan tabarma ina cin ɗumame ina korawa da ruwan zafi ina danna waya. Ashe dai hotunan dana saka a shafukana suna trending. Na fara bin comments ina karantawa, wasu na yi dariya wasu kuma na ja tsaki." Wasu dai a rayuwarsu basa jin daɗi har sai sun kushe halittar mutum. """Dama Chef Zeey lukuta ce"" comment ɗin da ya fi bani haushi kenan. To uban wa ya taɓa ce musu ni" "siririya ce. And idan ba mutane da neman magana ba har ni ɗin wani ƙiba ne da ni da za a kirani da Lukuta. I'm just a bit chubby ne fa. Na sake kallon kaina. Wani tight tshirt na saka da zani. In ba pencil ake so na zama ba ai wannan jikin ya yi. So portable, so sexy. Masha Allah, ina da gaba da baya mai ɗaukan hankali. Ba zan kira kaina da kyakykyawa can ba, amma idan ina waje aka kira mata goma aka ce a ware kyawawa na tabbata zan faɗa a tsakiya ne kona biyar kona shida, ina da confidence akan haka. Koma yanene ni na san I AM BEAUTIFUL a yadda na ke." Ɗumamena har sai da ya yi sanyi ban gama ci ba saboda na tsaya danna waya. Can dana ankara sai na "ajiye wayar gefe na cinye tuwon na lashe tukunyar tas, har ɗan ƙanzo-ƙanzon da tuwon ya fara yi sai dana kankara da cokali na cinye. Na ƙurɓi sauran ruwan Milo sannan na tattare wajen na kai wajen wanke-wanke. Allah Sarki 'yar tsohuwata sai da ta yi wanke-wanke tas kafin ta wuce Islamiyya. Tunda aka buɗe Islamiyyar safe na matan aure da manyan Mata a saman layinmu Kaka ta je ta yi register duk Asabat da Lahadi tana wajen." Tukunya da kofin dana yi amfani da su na tsugunna na wanke sannan na shiga kitchen na sa su a kwando. "Ina ga ɗaki zan shiga na sake kwanciya dan jikina bai gama warwarewa ba. Kai, koma dai kayan wanki" zan kwaso na zo na dirje su tunda akwai rana. Tun da aka shiga satin biki ma ban yi wanki ba. Ina cikin wannan lissafin na ga wayata ta yi haske a kan tabarma. Na jawo wayar sai na ga notification ne na text message. Ina karantawa na furzar da iska. Wannan maganar Restaurant dai idan ban je na ƙarisa shi yau ba haka mutumin nan zai yi ta damuna. Wai fa cewa yai na zo JK Plaza for interview ƙarfe goma. Na duba agogon "wayata, goman da ya ce ma saura minti ishirin da tara." "Ɗaki na shiga na fara neman kayan da zan saka. Duk kayana masu hankali sun yi datti ban wanke ba, sai" "kawai na nemi mafaka a wajen wani maroon jilbab ɗina gogagge a ƙasan Akwati. Waccar Sallan na ɗinka su kusan kala huɗu. Ɗaya Umman Fada ta ɗauke, ɗayan kuma da na je Kaduna sai na manta a gidan Ummana." File ɗin dana ke ajiye duk wasu credentials ɗina na jawo daga ƙasan gado. Aiki a restaurant ai ba shaidar degree ko sakamakon WAEC ake nema ba ko?. "Na ciro certificate ɗina na Culinary school. Na ɗauko na Baking and Pastry wanda na yi a nan Zaria, shi" kam ma ya jima dan ina ga ina SS2 na je na koya a wajen wata mata ta bamu certificate. Na ciro recommendation letter da aka bani a Zikks Foods dana yi aiki na haɗa da shi. Ina da experience dayawa amma sai dai na faɗesu da baki saboda su basu da certificate. Na nemi copy ɗin CV na sama da ƙasa amma na rasa. Na ja tsaki dan yanzu sai na tsaya na printing a hanya kafin na wuce tunda ina da shi a waya. Dana gama haɗa komai sai na cire zanin dake jikina na saka wani baƙin wando da jan top dana samu "wankakke a cikin jakar Ghana must go da nake saka kayan zaman cikin gida. Na goga Roll-on, sannan na" ɗan fesa body spray kaɗan. Na fito ɗauke da file ɗina da jaka sannan na jawo ƙofar ɗakinmu na saka masa kwaɗo. Na fara tunanin "ina zan ajiyewa Kaka key. Duk inda muka saba ɓoyewa 'yan gidanmu sun sani. Da sun ji babu kowa za su zo su ɗau key su shiga su mana sata. Ni yanzu bayan nama, ina da cash a jakata da zai kai dubu goma dan haka dole na nemi safe waje na ajiye key inda ba za su gane ba." To kuma kar Kaka ta zo ta yi ta nema. "Ƙarshe na yanke shawarar zan bawa ƊanLiti mai shagon kusa da gidanmu, idan Kaka ta zo wucewa sai ya" bata. I think wannan zai fi. Kai Jama'a! JK Plaza ya haɗu iya haɗuwa. Lokacin dana sauka a gate ɗin Plazar sai dana tsaya na ƙarewa wajen kallo. Gaskiya sun kashe kuɗi a wajen nan babu ƙarya. Wajen masu gadi na nufa na ce musu na zo wajen Mr Jalal ne. """Yallaɓai Jalal ai yana ciki tun ɗazu. Ki miƙe straight, ƙofar da kike gani ki shiga yana ciki"" ɗaya daga cikin" masu gadin ya min kwatance. Na riƙe file ɗina da kyau na gyara hannun handbag ɗina sannan na nufi inda suka nuna min. Wajen shiru kaman babu kowa. An ƙawata cikin restaurant ɗin da kujeru na alfarma masu kyau. Gaskiya idan aka buɗe wajen nan zai ja hankalin mutane. Akwai Laptop a kunne da kuma ruwan gora a saman ɗaya daga cikin table ɗin da ke tsakiyar hall ɗin restaurant ɗin. Ko ina ya shiga oho? Na zauna a kujera opposite da inda ya zauna na ajiye file ɗina akan table ina sake ƙarawa cikin restaurant ɗin kallo. Waya yake yi lokacin da ya fito daga wani lungu wanda nake tunanin hanyan kitchen ne. Na ɗan saci kallonsa kafin na sunkuyar da kai nima ina danna waya. Grey T-shirt ne a jikinsa da ya ɗameshi ya bayyana shape ɗin saman jikinsa. Sai baƙin jeans. Ban kai ga duban takalmin da ya saka ba amma kaman sneakers ne. Ƙanshin turarensa ya dominating warin sabon waje da cikin restaurant ɗin ke yi lokacin da ya zauna a kujera. """Chef Zeey, ko?""" """Yes"" na faɗa ina gyaɗa masa kai" """pitch me your idea """ "Na buɗe baki na rufe dan ban san ta ina zan fara ba. Daga zuwa, ba gaisuwa, ba komai, sai kawai na" pitcing masa idea ɗina. """Kina da 5 minutes"" ya faɗa tareda ajiye wayarsa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mini ido." """Arhm, Arhm..."" Subhanallahi! yanzu ta ina zan fara yi masa bayani da zai fahimci irin abinda na ke so." "Ɗaga mini gira ɗaya ya yi, idanunsa na mini kallon ba ni da abin faɗa ɗinnan." "Na yi gyaran murya sannan na fara masa bayanin irin restaurant ɗin dana ke son buɗewa, dama nawa" na tara a cikin kuɗin restaurant ɗin. """So, idan na fahimceki da kyau. Miliyan biyar ne zai buɗe miki restaurant?""" """Like irin for a start ɗinnan a hankali kuma...""" """Kina ga Miliyan biyar zai running wannan wajen?"" Ya katseni da tambaya." Na kalli gefe da gefena. Na san decoration ɗin da aka yiwa restaurant ɗinma kaɗai zai iya cin Miliyan "biyar ko kusa. Na ce masa ""dama ba wai restaurant me girma zan buɗe ba, ina son dai-dai...""" """Ghetto"" ya faɗa yana mini kallon reni." """Ban gane ba?""" """Kina son buɗe restaurant a Ghetto area da miliyan biyar. Good, za ki samu kasuwa idan abincinki yana" "da daɗi kamar yadda Hajiya ta faɗa. But...""" Ya saka hannunsa duka biyu akan table ya ɗan matso da fiskarsa yana kallona sosai. """Idea ɗinki bai dace da restaurant ɗin da muke so mu buɗe a wannan Plazar ba. I wish you success a duk" "sadda kika buɗe restaurant ɗin da ya dace da idea ɗinki""" A fusace na tattare file ɗina da jakata na yi hanyar waje. Dan iskanci ni zai kira ya renawa hankali. Dama ba so yake na yi masa aiki ba. Idan ba dan Hajiya ba mi zai sa na zo wajensa. An faɗa masa yunwar aiki a restaurant nake yi ne. Ɗan renin hankali kawai. Masifar da ke cina kenan lokacin dana fito daga restaurant ɗin amma sai na kasa tafiya. Idan ban faɗa masa abinda ke raina ba yau da ƙyar zan iya bacci. Na koma da baya na buɗe ƙofar na shiga ciki. Yana danna laptop ɗinsa ya ɗago ganin na nufoshi rai a ɓace. """Eh ɗin zan buɗe restaurant a Ghetto. Na ga ai mutane ke zama a wajen ba Aljanu ba. Da kake cewa idea" "ta bata dace da restaurant ɗinka ba kada ka manta bani na kawo kaina nan ba. Hajiya ce ta nuna tana so na yi aiki a nan saboda ta yarda dani. Kai kuma Mr High and Mighty da baka yarda da abincin gargajiya ba ka sani mu masu son gargajiya ba za mu mutu ba. Ba fancy dining za ka buɗe ba Allah ya sa Palace dining za ka buɗe""" """Sai wani maimaita Ghetto kake yi kamar wani ƙanjamau, to barin faɗa maka, ni ZIYADA SADIQ HARUNA" ina alfahari da ghetto saboda daga nan na fito. Kuma ba maula na zo yi wajenka ba balle ka ce zaka "walaƙantani""" Na yi juyawata ina faɗin Iskancin banza kawai... CHAPTER THIRTEEN JAYKAY Har ta buɗe ƙofa ta fita bai dena kallon bayanta ba. This is the first time a rayuwarsa da wata mace ta tsaya a gabansa ta faɗa masa magana irin haka. Ba wai mamakin rashin kunyarta ya ji ba. Mamakin ƙarfin hali da rashin tsoronta ya ji. Shi Captain JK Maiyaƙi wannan 'yar yarinyar ta tsaya a gabansa ta gaggaya masa magana haka. Good riddance. "Gara da ya mata haka, at least yanzu za ta fahimci tazarar da ke tsakanin abinda ya ke shirin yi da kuma" abinda ta ke tunanin yi. "Yanzu ta ina za a fara serving tuwo, da ɗanwake da Fate a babban waje irin wannan?." Target audience ɗinsa ba mutanen ghetto bane. Fahimtar hakan da Hajiya bata yi bane ya sa take ƙoƙarin haɗa shi da local Chef ɗinnan. Ƙoƙarin cigaba da aiki ya yi a Laptop ɗinsa amma maganganun Ziyada sai ringing suke masa a kunne. Ga kuma fiskarta da ya ke masa gizau yadda ta ke masifa. Yadda movement ɗin lips ɗinta suke bala'in ɗaukan hankali. "Lips ɗinta an yi su dan kiss ne, ba dan masifa ba. Yai saurin girgiza kai da wannan banzan tunanin da ya" zo masa. Gaskiya daɗewar da ya yi babu mace ya fara taɓa shi. Ta ya masifar wannan yarinya zai zama masa so attractive. Thank God ma ba zai sake ganinta ba. Babu wata alaƙa da za ta sake haɗa su dan haka wani banzan tunani ma akanta ba zai sake shigo masa ba. Bai jima a wajen ba ya fara tattare Laptop ɗinsa zai tafi gida dan aikin da ya ke son yi a wajen ma ya fara gagararsa. Zai koma inda fiskarta ba zai riƙa yi masa gizau ba. Yana cikin tattare wajen sai ya ga takarda a ƙasa gefen inda Ziyada ta tashi. Ya tsugunna ya sa hannu ya ɗau takardar ya fara karantawa. CV ɗinta ne da ke ɗauke da wajajen da ta yi aiki da kuma experience ɗinta a harkar girki. Bayan ya gama karanta takardar sai ya sa a jaka kusa da Laptop ɗinsa. "Duk da dai Local Chef ce, experience ɗin da ta ke da shi yana da matuƙar amfani. Idan har ta buɗe" restaurant kamar yadda ta ke iƙirari to tana da experience da za ta iya running wajen. Har ya wuce gida tunanin Ziyada ne fal a ransa. *** ZEEY "Tun dana fito daga JK Plaza nake tafiya raina a ɓace, na kama tafiya cikin sauri fuuuu kamar zan tashi" "sama. Sai da na yi tafiya mai nisa ban tsare Keke ba, masu Keke na mini horn amma ban tsai da su ba. Wani zafi nake ji a zuciyata, duk dana amayar da abinda ke raina sai nake ganin kamar akwai abinda na manta ban faɗa ba. Inata sake playing abun dana faɗa masa a raina amma zuciyata bata huce ba." Ina ta sauri har sai da na kusa faɗawa kwalbet ban sani ba saboda hankalina ya yi gaba. Wannan ya sa dana kai junction sai na tsaya na tari Keke na wuce gida. "Ɗan iska, mai keken ma wai in zai shiga dani har cikin layi sai na ƙara masa kuɗi. Da a hayyacina nake sai" mun yi rikici amma na ce masa mu je kawai. Muna isa ƙofar gidanmu tun ma kafin na fito daga keke na hango motar Alhaji Nafi'u. Na fito na miƙawa mai keke kuɗi ina mamakin me ya kawo wannan ɗan iskan gidanmu da rana tsaka. Yana zaune akan tabarma ya baza rumbun jikinsa yana shan lemo da Ayaba a cikin baƙin leda. Ga Baffa "Lawalli a gefe yana ta zuba masa dariya. Na ja tsaki ina faɗin ""Ɗan Maula kawai""" Ga shi dai Alhaji Nafi'u ƙanin bayansa ne amma sai wani ladabin ƙarya yake ta masa saboda kwaɗayi. "Na yi kaman ban gan su ba zan wuce na ji ya ce ""Sayyada, kin dawo?, Dama kuwa yanzu Baffanki yake" "cewa zai kiraki""" Na juyo da sauri na watsa masa harara. Tun dana blocking numbarsa bayan na tura masa kuɗinsa na manta da shi. Ya taɓa kirana da wata sabuwar number amma ina jin muryarsa na yi blocking numbar. """Ziyada ba ki ganmu zaune bane. Ba magana ake miki ba"" Baffa Lawalli ya faɗa da masifa." """Ina wuninku"" na gaishe su ina danne ɓacin ran da ya taso mini. As if ban kwaso haushi daga wajen Jalal" "ba, wannan ƙaton banzan shima zai ɓata mini rai. Ni kam ana soyayyar dole ne?." """Ki shiga gida ki ajiye jaka ki fito ku gaisa da Alhaji Nafi'u, dama ke yake jira""" Ni yake jira kamar yaya?. Miye haɗina da shi?. Na riga na sallameshi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Yo ko ni 'yar iska ce ai ba zan zaɓi yin iskanci da tujejen baƙin mutum kamar Alhaji Nafi'u ba. Allah na tuba yadda ya ke da uban jiki da tumbin nan ƙaramin aba gareshi. Ni ɗinma baƙa ce amma gaskiya baƙin Alhaji Nafi'u har da datti. Gashi da kuɗi dai-dai gwargwado amma "turare wannan ba zai saka ba kullum sai ka ji warin gumi a jikinsa. Lokacin da muke ɗan mutunci irin wai dan na ankarar da shi ɗinnan har da kyautan turare na yi masa wani lokaci amma still kamar an masa farraƙu da saka turare, baya sakawa. Maganar turare ya sa na tuno da ƙanshin turaren Jalal. Kamar ma dai ƙanshinsa biyoni ya yi har gida, dan har yanzu ina jin ƙanshin." Har na shiga gida zuciyata kamar za ta yi bindiga saboda haushin ganin Alhaji Nafi'u da Baffa Lawalli. Da gani ba abin alheri suke kitsawa ba. Wato dan na rufe masa duk wata dama da zai sameni shine ya biyo ta wajen Baffana. Ganin ƙofar ɗakinmu da kwaɗo ya sa na doka ƙatuwar tsaki na fita. Ashe ma Kaka bata dawo ba. Na fita na je na karɓo key na dawo na buɗe ɗakin. Ina shiga ɗaki na cillar da file ɗina saman gado na cire Jilbab ɗina na yar a ƙasa. Zama na yi na jingina bayana da gado ina huci. Yau dai ina ga akwai wanda ya jefeni da ɓacin rai ne. In ba haka ba ta ya zan fita daga gida na kwaso ɓacin rai a inda na je sannan na dawo gida na sake tarar da wani baƙin cikin. Zamana na yi a ɗaki na manta da batun Alhaji Nafi'u har sai da Baffa Lawalli da kansa ya shigo yana kirana sai masifa yake wai na barsu zaune. """Ki wuce ki samu Alhaji Nafi'u yana jiranki a waje""" """Ni fa Baba gaskiya, gaskiya, ka fita harkarsa dan ni babu wata alaƙa tsakaninmu yanzu. Na sallameshi" "tun da daɗewa""" """Ki ji min Ja'ira. Yanzu mutum mai arziƙi da kamala yana binki kina cewa ba kya so""" """Gaskiya Baba wannan ne na ƙarshe da zan fita saboda Alhaji Nafi'u ya zo gidan nan, bana son irin" "wannan abin""" Na yi maganar kaman zan yi kuka ina wawuran Jilbab ɗina da ke ƙasa. """ iskancin banza, mu muka kawo shi gidan nan ne. Ba ta dalilinki muka san shi ba. Za ki ce yanzu ba kya" "son shi bayan ya jima yana kashe miki kuɗi""" Na ja na tsaya idanuna suka ciko da hawaye. Ban taɓa tambayar Alhaji Nafi'u kuɗi ba. Duk abinda ya yi mini ban saka shi ba. Lokacin dana fahimci shi mutum ne da zai yi maka alkhairi kuma ya zo yana maka gori sai na dena karɓan komai a wajensa gaba ɗaya. Tun da abubuwa suka fara dai-daita mini shima karan kansa ya fahimci bana buƙatar ɗan chanji daya ke turo mini. """Baba amma..."" na buɗe baki zan yi magana sai na kasa." Da ce masa zan yi da ya san sau nawa Alhaji Nafi'u mai kamalan ke cewa na taɓa masa gabansa ko kuma na bari yai wasa dani na rage zafi a cikin mota da ba zai ce na wuce na je na same shi yanzu ba. Da ya san cewa Alhaji Nafi'u ya taɓa yunƙurin kaini hotel dan na bashi kaina da ba zai zauna da shi yana wage masa haƙora ba. "Sai dai, da wani bakin zan fara faɗa masa wannan maganar?. Ina da zafi, bana juran walaƙanci, amma" ɗan kunyar dana ke da shi ba zai bari na bayyana wa yayan Babana wannan maganar ba. "A zaure na goge hawayen da ya zubo min, na ɗan goggoge fiskata da hannun hijabina sannan na fita." Babu kowa akan tabarma dan haka sai na yi wajen da ya parking motarsa. Ina buɗe ƙofar gaba na shiga na zauna na bar ƙofar a buɗe na ɗan saka ƙafa dan kar ma ta rufu da kanta. """Sayyada kenan"" Alhaji Nafi'u ya faɗa yana wani munafukin murmushi." Allah Sarki ni. Wai mutumin da ke irƙirarin yana sona shine ba zai iya furta sunana ba. To ko sunan Chinese gareni ai dole ya koyi faɗansa. Lokacin da muke tare tun ina gyara masa har na lura iskancinsa ne kawai ba zai faɗa ɗinba wai Sayyada ya fi masa sauƙin faɗa. """To ya kike?""" """Alhaji Nafi'u me ka zo yi gidanmu?"" Na tambaya ina kallon ƙwayar idanunsa." """A'a. Da wuri haka, ai kya tsaya mu gaisa tukunna ko""" """Mu gaisa fa kace. Ka san babu wannan a tsakaninmu yanzu. Na riga na sallameka. Na tura maka kuɗin" "da Baffa Lawalli ya karɓa, ka rabu dani Dan Allah""" Dariya ya saka na yi saurin kau da fiskata gefe dan kar ya feza min yawu. """Kina tunanin dubu hamsin kawai nake bin Baffanki?. Idan ma baki sani ba to ki sani, yanzu haka abinda" "nake bin Malam Lawal da ɗayan Baffanki siririn nan zai fi dubu ɗari biyar""" Baffana siriri shine Baffa Zakari. Ya Subhanallhi! Naira Dubu ɗari biyar ta yaya? Na zaro ido. """Wannan ina nufin kuɗaɗen da suka karɓa a bashi fa kenan ba wai wanda na basu kyauta ba. Idan za a" "haɗa da lissafin kuɗin dana basu sadaka zai iya haura Miliyan guda"" yai maganar yana kallona" Na yi shiru ina Salati a zuciyata. A yaushe ɗin mutanen nan suka karɓi maƙudan kuɗi a wajensa haka?. "Tabbas ba zai yi ƙarya ba dan shi mutum ne da duk abinda zai maka sai ya saka a lissafi. Ba zan manta ba," "lokacin da ya fara kawo min kyauta, kayan Sallah ne Abaya da wata Atamfa." """Kin ga Abayar nan dubu talatin da biyu ake siyar da ita. Wannan Atamfar kuma ko ina kika shiga ba za a" "siyar miki ƙasa da dubu shatakwas ba. Ke kaɗai Sayyada na kashe miki dubu hamsin. Kar ki damu ko nawa ne zan iya kashewa dominki""" Dai dai da tsire idan ya siya sai ya faɗi na nawa ya kawo min. Irin wannan lissafin da gorin ya sa na ƙyamaci kyautarsa tun a baya. "Dan haka idan ya ce su biyun sun karɓi kuɗin da ya kai Naira dubu ɗari biyar, to ba ƙarya bane." """Kin san na jima ina sonki. Ni har yanzu ban haƙura da ke ba. Ina son ki kuma aurenki zan yi. Mutum" "yana da mace irinki a gida ai ba zai sake duba wata mace a waje ba.""" Ɗan iska dai baya ƙoshi. Ko irina goma zai samu ni na sani ba zai taɓa haƙura ba. "Ya wani lanƙwasa murya ya ce ""kin ga halittar ƙirjinkin nan, sai na kwana ina tsotsansu ban gaji ba." "Sayyada ke fa ba ki san baiwar halitta da Allah ya miki ba. Kullum na ganki sai na tafi gida da jiƙaƙƙen wando. Na jima ina marmarin taɓasu na ji laushinsu amma kin ƙi bani dama. Ke gaki 'yar Jami'a babbar yarinya amma sam kamar baki waye ba""" Dama na san kwanan zancen. Sha'awata ke cinsa ba wai sona yake ba. And duk tsawon lokacin nan "alkhairinsa gareni trap ne ya ɗana dan na dogara da shi har ya samu kaina. Sai Allah ya sa ban dogara da shi ɗin ba, nima ina da abin yi kuma ina samun rufin asiri." "Ɗaure fiskata na yi ban bari ya gane na firgita da abinda ya faɗa ba na ce ""Look Alhaji Nafi'u, ni ba ni na" "karɓi aron kuɗi a wajenka ba. Lokacin da kake basu kuɗin bana wajen dan haka sai ka je ka wanye da su," "can ku ƙarata. Idan ma Police station za ka kaisu dan su fito maka da kuɗi to Bismillah. Ni bai shafeni ba""" Wani dariyan ya sake yi wannan karan na ɗan tsorata da dariyarsa amma na dake ina addu'ar neman tsari daga sharrinsa a zuciyata. "Duk macen da matsin rayuwa ya sa ta faɗa hannun mutum irin Alhaji Nafi'u, to ta shiga uku. Ni ga shi" "daga taimako ɗaya, sai ga shi ya shigo rayuwata ya zame min jaraba." """Ki kwantar da hankalinki Sayyada, Baffanki ya yi mini alƙawarin a satin nan idan suka yi magana da" "sauran iyayenki za su bani aurenki""" """Aurena kuma? Kana Hauka ne?"" Na daka masa tsawa ko girmansa ban tuna ba. Yo dama girmansa ya" jima da zubewa tun lokacin da ya nuna mini shi ɗan iskan gari ne. """Ba hauka bane, gaskiyar magana kenan. Dan haka ki kwantar da kai mu fahimci juna tun yanzu. Ni dama" "Sayyada kin sani na jima ina son ki, ke ce dai kike nuna min ƙiyayya""" A take a lokacin na yiwa kaina alƙawarin zan auri kowaye amma banda Alhaji Nafi'u. Ko sama da ƙasa za su haɗu ba zan taɓa aurensa ba. "Kallonsa na yi cike da ƙyamarsa na ce ""sunana ZIYADA ba Sayyada ba, ɗaya kenan. Ka sa a ranka ba zan" "taɓa aurenka ba, biyu kenan. Na ƙarshe shine ka sake sawa a ranka ZIYADA ba za ta taɓa aurenka ba""" Daga haka na fito daga motar na bugo masa ƙofar bauuuu... CHAPTER FOURTEEN ZEEY Ina cikin kuka Kaka ta shigo ɗaki. Tana ganina a haka ta ajiye jakar Islamiyyarta ta rungumeni tana tambayata me ya faru. """Wa ya taɓa min ke Ziyadatu? Me ya same ki?""" Ƙanƙameta na yi na cigaba da sheshsheƙar kuka. """To yi shiru, ya isa. Faɗa mini wa ya taɓa ki? Wa ya ɓata miki rai?""" Sai dana sha kuka mai isata kafin da kaina na yi shiru ina ajiyar zuciya. A irin waɗannan moments ɗin nake jin zafin maraicina. Da Babana na da rai na tabbata Alhaji Nafi'u bai isa ya ce zai aureni ba. Kai ba lallai na haɗu da Alhaji Nafi'un bama balle na bashi dama ya shiga rayuwata. Babana Direba ne. Amma duk da haka shi mutum ne mai wadatar zuci. Ai duk wanda ya ɗauko halin "Kaka kam, dole ma ya zama mai wadatar zuci." "Kaka ta ce, Babana ya yiwa 'yan'uwansa hidima ba kaɗan ba lokacin da ya ke raye. Su kansu 'yan'uwan" "nasa idan suna faɗin halayensa, za ka ji suna ambatarsa da shi mutum ne mai yawan kyauta da tausayi." "Memories dana ke da shi na mahaifina ba su da yawa. Ya rasu a lokacin da ban yi wayo sosai ba, I think" "ina shekara bakwai ya rasu, kai! kamar takwas ne. Allah Sarki! Har na fara mantawa da lissafin. Da, na kan tuna abubuwa dayawa akansa. Yadda ya ke kawo mini tsaraba duk lokacin da ya dawo daga tafiya. Yadda ya ke ɗaukana a wuyansa yai ta jujjuyani har Kaka ta dinga faɗa wai ya dena irin wasan nan dani ni mace ce. But, a hankali ina girma, memories ɗin suna ɓacewa. Na san fiskarsa kam, saboda har yanzu akwai hoton aurensu da Ummana da kuma wani hoto da aka yi a bikin autarsu Binta. A kamanni na ɗauko yanayin fiskarsa, da baƙinsa. Amma a jiki, Ummana na biyo, dan Ummana tana da ƙiba gaskiya. Ko a hotunan bikinsu da ƙibanta balle kuma yanzu da girma ya sake buɗeta. Daga wajen Ummana na samu" dirin da mutane ke yabawa. Da na ɗauko ɓangaren Babana da abin ba zai yi kyau ba. Dan ga su nan "matansu duka shafel, babu shape." "Lokacin dana faɗawa Kaka abinda Alhaji Nafi'u ya faɗa ai tuni ta fara masifa, ta ce Baffa Lawalli bai isa ya" min auren dole ba. Ta ce min za ta kira shi ta masa magana. Wannan ya sa na ɗan ji sanyi kaɗan a raina. Da dare kuwa Baffa Lawalli ya shigo sashenmu sai huhhura hanci yake har da cewa na kawo masa abinci "kamar ya bamu kuɗin gari. Idan ba kwaɗayi bama ko bai yi magana ba Kaka za ta ce na kawo masa, dan Kaka da bawa mutane abinci 5&6 ne." Na wuce Kitchen na ɗebo masa tuwon Shinkafa da miyan busashshen kuɓewa dana mana. Da ke ina jin "haushinsa nama yanka ɗaya na saka masa a miyar, kuma sai dana zaɓo ƙarami sannan na jefa masa, duk" da kuwa akwai nama sosai a miyar dan har yanzu bamu cinye naman da aka kawo mini ba. """Ɗan bamu waje"" ya faɗa da wani gadara lokacin dana zauna can gefe ina son jin maganar da za su yi." Na ja tsaki a raina na ɗau hijabi na fita. Sashen Baffa Mamman na wuce dan ba laifi muna ɗan ɗasawa "da matarsa Anty Hafsah. Shi kaɗai ne yai gini a cikin gidan, duk sauran ginin gado ne suke zaune a ciki." Ɗakuna uku Baffa Mamman ya gina da falo da kitchen a filin da aka bashi. Da sallama na shiga falon na samu Anty Hafsah da yaranta biyu suna cin abinci suna kallo. """A'ah! Yau Chef tamu ta gargajiya ne a gidana""" """Anty Hafsah, Barka da dare""" """Barka da dare, Ziyada. Ya aka ji da hidimar biki kuma""" """Lafiya, Anty""" """Mun gode fa. Ɗazu da rana na ga saƙo""" Da rana bayan na gama kuka ne na zauna na rabawa 'yan gidan chinchin ɗin biki na aika musu. """Ki yi haƙuri ba yawa ma. Kin san jama'ar gidan namu yawa garesu. Idan ban bayar ba kuma zan shiga" "magana""" """Ashe kin sani. Na zubo miki abinci ne?""" Na girgiza mata kai na ce a ƙoshe nake. Zama na yi a kujerar one sitter na kanainaye jikina na kunna data "na shiga Instagram ina son ɗauke hankalina daga abubuwan da suka faru yau. Amma dik yadda na ke ƙoƙarin basar da maganar Alhaji Nafi'u, sai ƙara ringing yake mini a kunne. Ni yanzu abinda ya faru tsakanina da Jalal ma na ajiye shi gefe, bata shi nake ba. In Allah ya yarda ma babu abinda zai sake haɗani da shi. Tunda ya ce baya son idea ɗina, shikenan ya je ya yi duk abinda ya ke so. kuɗinsa ne, restaurant ɗinsa ne ba nawa ba. Nima idan Allah ya buɗa min zan buɗe nawa restaurant ɗin, na ɗabbakar da abinda na ke so a wajen." Za ku ga na damu da maganar buɗe restaurant. Ni kaɗai na san inda ke mini ciwo. Na farko dama ina da "sha'awar buɗe wajen cin abinci tun lokacin da Kaka ta dena sana'ar Tuwo. Na biyu kuma, ba zan taɓa dogara da food content ba, yanzu ina tashe a harkar ban san yaushe taurarona zai dishe ba, musamman saboda content ɗina na gargajiya ne ba kowa ke so ba." Na uku kuma ina son sana'ar ne saboda na san idan ta karɓi mutum akwai samu a harkar. Na yi aiki a restaurant kuma na san ya harkar ta ke idan mutum na samun ciniki. Da wannan sana'ar na ke so na cigaba da gina kaina na kuma inganta rayuwar Kakata. Ta bautu wa sana'ar siyar da abinci amma daga ƙarshe bata mori sana'ar ba. Kishiya da 'ya'yan Kishiya su suka hanata moran sana'ar. "Lokacin da Baaba Tabawa kishiyar Kaka ke raye, tun ma kafin mijinsu ya rasu. Kaka bata isa ta tara kuɗi" ta ce za ta yiwa kanta wani abun kirki da kuɗin ba. Akwai lokacin da ta tara kuɗin Hajji da sana'ar Tuwo ɗinnan amma da Baaba Tabawa ta tada fitina ƙarshe sai mijinsu ya ce Kaka ba za ta je ba. Kun san a da yardar miji shine sama da komai. Ƙarshe kuɗin da ta tara na tafiya Hajjin salwancewa ya yi. "Lokacin da Kakanmu ya fara jinya, duk da kuɗin Kaka aka yi jinyar. Bayan rasuwarsa, Baaba Tabawa da" 'ya'yanta suka kwashe kusan komai na gado. Gidan Kakana babban gidane da kuma fili amma da aka tashi sai aka bawa Kaka wani ɗan gefe inda muke yanzu kenan wai nan ne rabonta. Bata yi ƙorafi ba ta dawo wajen da zama bayan ƙurar rabon gado ya lafa. Ɓangaren Babana ma Baffa Lawalli ne ya cinye bayan rasuwarsa. Yanzu haka Amaryarsa ya saka a wajen. "Saboda wannan rikicin ya sa nake so na inganta rayuwar Kakata. Kai, barin faɗa muku. Yadda na ke ji da" "Kakata ko, ko Ummana data haifeni bana jinta kamar haka. Kafin na yiwa Ummana abu ɗaya, sai na yiwa Kaka biyunsa. Na san matsayin Uwa ya fi na Kaka, amma gaskiya saboda shaƙuwar da muka yi na fi ji da Kaka Altine sama da Ummana." Bayan rasuwar Baaba Tabawa. Kaka ta cigaba da yiwa 'yan gidan hidima kamar ita ta haifesu. Amma "jarabar aron kuɗi, da 'ya'yansu da suke mata sata, sai da suka kassara mata sana'ar." "A hakan bata dena ba, har sai da jinya ya kada ita. Lokaci guda daga faɗuwa tana tuƙa tuwo da aka kaita" "Asibiti sai ga result kala-kala na ciwukan da ta ke fama da shi. Ga matsalar ido, har yanzu ido ɗaya baya gani sosai, ɗayan ma dai gashi nan-gashi nan ne. Ga hawan jini, ga ciwon baya da ciwon ƙafa. A lokacin fa har cewa suka yi akwai Chronic typhoid da kuma ulcer a jikinta. Abin mamaki, tana sana'ar sayar da abinci amma wai tana fama da matsalar ulcer." Jinyar farko sai da Kaka ta yi wata biyu a Asibiti kafin aka sallameta. A wannan jinyar ɗan kuɗin da ta ke "tarawa ya ƙare. Nima a lokacin duk abinda na ke samu jinyar Kaka yake tafiya. Na san za ku ce ina su Baffa Lawalli suke a lokacin. Hmm! Yadda Baaba Tabawa ta nuna musu Kaka ba uwarsu bace haka suka ɗauketa har a lokacin da take cikin tsananin buƙatar tallafawarsu. Umma Hadiza dai tana zuwa duba Kaka kusan kullum har na sati biyu, kafin daga baya ta rage zuwa. Ban ji haushin ɗage ƙafarta ba saboda na san mijinta bahagon mutum ne mai baƙar aƙida, ba mamaki shi ya hanata zuwa." "Umman Fada ba komai ta ke da shi ba, itama na fama da nata Talaucin a gidanta." Baffa Mamman na bada abinda bai taka kara ya karya ba. Shima Baffan Katsina idan ya bushi iska yana turo kuɗi. Daga ƙarshe babu wani mai halin da zai iya ɗaukan nauyin jinyar Kaka. Kuɗin da ta tara shekara da shekaru da su aka ci ƙarfin jinyar har Allah ya tashi kafaɗarta. Ƙanwar Kaka da muke kira Baaba Murja ita ce ta zauna da Kaka throughout jinyar. Ni kuma kullum ina "jigilar Makaranta, ina jigilar Asibiti, ina jigilar aikace-aikace." A irin wannan yanayi na haɗu da Alhaji Nafi'u a wajen ATM har ya taimaka min lokacin da ATM ya haɗiyi "katina. Ga shi yanzu ya bijiro da wata maganar da ba zai taɓa yiwuwa ba. Alhaji Nafi'u ba mijin aure bane. Ba dan shekarunsa za su iya kaiwa hamsin ba, ba dan yana da mata ba, ba dan yana da ƙiba ba (duk da ni bana son ƙaton namiji). Ba dan kuma halinsa na gori ba. Ba zan aure shi bane saboda sha'awata yake, ba sona ba. Idan har ya aureni ya samu abinda ya ke so, to shikenan idonsa zai kauce a kaina ya fara neman wata. Wannan, ba irin auren dana ke son yi bane..." *** JAYKAY Ƙarfe tara na dare yana ɗaki yana zaune akan gado ya saka Laptop a gaba yana rubuta wani email sai wayarsa ta fara ringing. Ɗan leƙa wayar ya yi ya ga sunan C. Maria. Tsaki ya ja a fili. Sai yau ta ga daman kiransa kenan. Kusan sati guda kenan ko waya ba su yi ba. Ɗazu da yamma Junior ke masa ƙorafin ya kamata Mom ɗinsa ta zo birthday ɗinsa da za a yi ranan "Alhamis mai zuwa. Haƙuri ya bashi dan ya san ko ya faɗawa Cassy ta zo, ba zuwa za ta yi ba. Aikinta ya fi mata komai mahimmanci." """J. Lovvvvve!"" Ta faɗa da muryan maye." """Fuckkk Nigeria, I've being trying to call you for hourrrrrs""" """Cassandra are you drunk?"" Jalal ya faɗa ransa a ɓace." """No, No, No, No. It's just twoooo bottle of wine, I promise""" """Maria!"" ya daka mata tsawa. Daga ɓangarenta ta yi shiru ta ɗan nitsu dan sunanta da ya ke kira kenan" "idan ransa yana ɓace, ko kuma idan zai faɗa mata wani abu mai mahimmanci." Faɗa ya fara mata akan ba ya hanata shan giya ba. Ta yi shiru tana jinsa. Ƙarshe ta fara bashi haƙuri amma bai saurareta ba ya kashe wayar. Ransa da ya ɓaci ne ya sa shi rufe Laptop ɗinsa ya fasa aikin da ya ke yi. Fitowa ya yi daga ɗakin ya sauko ƙasa. Coffee zai haɗa wataƙila idan ya sha zai rage masa zafin da ya ke ji "a zuciyarsa. Idan ya huce sai ya koma ya ƙarisa aikin. Gobe Monday ne, kuma ya kamata a ce ya tura" email ɗin tun Friday ne bai yi ba sai da Sakatariyarsa ta tuna masa ɗazu da yamma. Yana shiga kitchen ɗin ya kunna wuta. Ko lokacin da ya ke London ya fi son haɗa Coffee da kansa. Kusan "he's addicted to coffee ne. Duk lokacin da ya ji gajiya abinda ya ke sha kenan. Ko ransa ne ya ɓaci, A cup of coffee zai iya sassauta masa ɓacin ransa." "Bai taɓa shan giya ba duk zamansa a Turai. Giya, shine babban abinda ya ke haɗa shi da Cassandra. A" "zamansu tare ta rage sha. Ba ta sha sai baya nan. Idan yana gari har ya tafi ba za ta sha ba. Ko baya nan ɗinma, bata sha a gida sai dai ta je Bar ta sha. Amma yanzu da ba sa tare, yana da yaƙinin ta koma shan giya sosai." Irin waɗannan abubuwan Hajiya ta dinga jiye masa amma ya yi kunnen ƙashi sai da ya auri Cassandra Maria. "Abun da basu sani ba shine, a lokacin da ya bijirewa Hajiya ya auri Cassy, ya yi hakan ne saboda ya" cikawa Cassy alƙawarin da ya ɗauka. """J Love, I'm Pregnant, I'm Pregnant"" ta bayyana masa sounding so excited wata biyu bayan sun yi break-" off. "A ranan da ya ji maganan baya ma London, yana Doha. Da ƙyar ya saita nitsuwarsa ya ce mata idan ya zo" London zai zo su yi magana. Two weeks bayan wayarta ya koma London. Da ya je sai ta bashi result ɗin test ɗin. Ba ta hanyar aure aka samu cikin ba dan haka dole ya karɓi sakamakon zunubinsa. Ya ce mata kar ta "damu, zai kula da ita da abinda za ta haifa." Ta dinga lallaɓashi akan ita dai so take ya aureta. Ba za ta iya kula da cikin ita ɗaya ba. Tashin farko ya ce "mata ta yi haƙuri ba zai iya aurenta ba, amma zai bawa abinda za ta haifa sunansa. Bayan ya tafi. Kwana biyu da maganarsu ta kirashi wai bata da lafiya jini na zubo mata. Lokacin da ya isa apartment ɗin da ta ke sai ya sameta cikin jini tana kuka. Tsoro ya kamashi, ya kira Ambulance. Bayan Ambulance sun zo an kaita Asibiti sai aka tabbatar musu cikin ya zube." "Babu abinda ta ke ta maimaitawa a Asibitin sai, 'shikenan yanzu zai gujeta tunda cikin ya zube'. Tsoro da" "tausayi, su suka saka shi yi mata alƙawari a gadon Asibitin cewa ba zai taɓa rabuwa da ita ba, zai aureta." Wannan alƙawari shine mafarin taurin kansa har ya ƙeƙasa ƙasa akan sai ya auri Cassandra duk da Hajiya ta nuna bata so. Bai taɓa faɗawa kowa wannan dalilin ba. Ko Jamal bai faɗa masa dalilinsa na auren Cassy ba. "Looking back, yanzu ya fahimci garin son gyara abinda ya faru, sai ga shi ya shigar da kansa wata" "sarƙaƙaƙƙiyar alaƙa da ke da wuyan yankewa. Ya auri Cassy cikin sauƙi, amma fa rabuwa da ita babu sauƙi." Yai saurin kauda tunaninsa ta hanyar ƙarewa Kitchen ɗin kallo har idanunsa suka sauka wajen deep "freezer. Nan da nan wani murmushin gefen baki ya suɓuto masa, tunowa da ya yi da yadda ya kama Ziyada ranan da ƙatuwar frozen Chicken a hannunta. Ya tuno yadda ta tsorata da ganinsa har ta fara kame-kame." Lokacin da ya kai mug bakinsa ya kurɓi coffee ɗin sai idanunsa yai masa gizau ɗin fiskarta yadda ta rinƙa masa masifa yau da safe. "Those lips. Ko a mafarki ya samu daman kama su, sai ya yi maganinsu." "Ya sake kai mug ɗin baki ya kurɓi coffee, zafin da ya taɓa harshensa ya ankarar da shi irin tunanin da ya" ke. Yai saurin kwaɓar kansa. Ta ya ƙwaƙwalwarsa za ta dinga jefo masa tunanin yarinyar nan bayan babu wata alaƙa da zai sake shiga tsakaninsu?. "A kitchen ɗin ya ƙare shan coffee, kafin ya koma ɗakinsa. Zuwa lokacin haushin Cassandra ya ragu a" "zuciyarsa. Ko kuma dai, tunanin Ziyada ya shafe haushin Cassy da ya ke ji..." CHAPTER FIFTEEN ZEEY Kiran Faty ne ya tasheni daga bacci da sassafe around 6:15AM. """Bestie, kin ga sabon exams time table da Class Rep ya tura a group?""" """An chanja time table ne?"" Na faɗa idona a rufe dan bacci bai isheni ba. Jiya ni da Kaka bamu kwanta da" "wuri ba, mun tsaya mai da magana." """Zeey, exams fa ranan Wednesday. Na shiga uku ni Faty, yaushe na gama honeymoon za a kawo mana" "exams jibi dan Allah""" Buɗe idona na yi na tashi zaune. Exams ɗinmu sai Monday mai zuwa shiyasa ma na ce ba zan fara karatu ba sai wannan satin. """Wai da gaske jibi za a fara exams ba Monday ba?""" """Ai Wallahi Bestie ki tashi ki fara karatu. Ni yanzu ban san ya zan yi ba, Baby ba zai ɗaga mini ƙafa ba." "Bani da lokaci""" """Ai kam dole ki yi karatu Faty, duka test ɗin da muka yi wannan Semestern fa babu na kirki""" """Wallahi bana son samun Spill Over Bestie. Na gaji da Boko""" Dariya na yi na cire wayar daga kunnena na shiga Group ɗin Class ɗinmu dan na duba sabon time table "ɗin da aka saka. Ai kuwa da gaske ne, an mayar da exams ɗinmu Wednesday." Allah dai ya sa damuwar da ke raina ya iya barina na yi karatu. Anjima zan kira Baffa Adamu na masa magana kamar yadda Kaka ta ce. Duk cikin Baffanuna dai shine ya ke da ɗan sauƙin kai kuma zan iya cewa ba shi da kwaɗayi. Shi yake bin Baffa Lawalli amma saboda ya fi Baffa Lawallin wadatar zuci da kuma rufin Asiri sai ya zamana Baffa Lawalli ke binsa sese-sese kamar wani ƙaninsa. Baffa Lawalli dai kwaɗayinsa ya sa girmansa da matsayinsa na Babba a gidan ya zube. Ya zamana ko magana za a yi za ka ji ana cewa bari a ji ta bakin Baffan Katsina tukunna. Ina ganin course ɗin da za mu yi ranan Laraba na tashi na fara binciko cikin shirgin handouts ɗina ina "neman handout ɗin course ɗin. Gaskiyar shine ba zan yi wasa da karatuna ba. Daga wannan exams ɗin final year za mu shiga. Ko za a hau sama a faɗo dai su Baffa Lawalli basu isa su hana ni ƙarisa karatuna ba. Iskanci! Babu ko ƙwandalarsa a ciki fa, amma ya bi ya saka mini ido. Wai na kama Boko bana son yin aure. Ko yaushe na faɗa masa haka oho." Ina fara karatun ko nisa ban yi ba da na ji ina kiran ENZYMES da ENTIME na rufe handout ɗin na fito waje dan cikina sai ƙugi ya ke dama tun tuni. Na samu Kaka a ƙofar ɗaki tana gyara waken suya wai Awara za ta mana da rana. "Da a hayyacina nake, da cewa zan yi ta dakata na zo na yi mata recording, amma sai na wuceta na shige" "banɗaki. Batun kashe maganar Alhaji Nafi'u da kuma exams ɗina nake, ba batun ɗaukan content ba. Ina da recipen Awara a channel ɗina dan haka ba sabon abu bane balle na ce zan ɗauka." Lokacin dana fito yara sun fara shigowa za su ci ɗumame. Gaba ɗayansu babu wanda uniform ɗinsa ke "wanke. Wai fa yau safiyar Monday, amma ji yaran nan da dauɗa kamar an korosu daga bola. Dole Baffa Lawalli ya yi ta zuba 'ya'ya mana, tunda ga Kaka Altine nan za ta ciyar masa da su. Ga su nan ƙananan duk safiya za su yi zuga su shigo mana sai Kaka ta basu ɗumame ko Kunu sun karya kafin su wuce Makaranta." "A baya har kuɗin tara take basu, yanzu nema ta dena. A hakan idan yaro ya yi mata kukan bashi da kuɗin" tara haka za ta shiga ɗaki ta ɗauko ta bashi. "Kar ku ce abincin safiya kawai suke zuwa ci. Da rana idan ba su ƙoshi ba, Kaka ce wajen zuwansu su yi" "mata kuka ta buɗe tukunyarta ta basu. In da a ce Kaka tana da baƙin halina ko, to da ko kukan mutuwa yaran nan za su yi sai dai su mutu amma ba zan basu abinci ba. Ubansu da ya zubo su duniya ya ciyar da su su ƙoshi. Amma Kaka akwaita da kawaici da tausayi. Yanzu za ta fara wa'azin ""wanda ka ciyar ai shine naka. Wanda ka ci a cikinka kashi ne""." "Shinkafa gwangwani biyu dan ni da ita dai zai ishemu, amma idan Kaka za ta dafa shinkafa sai ta dafa" mudu guda (gwangwani 8). Idan kayan abincinmu ya fara ƙarewa ne za ka ga ta dafa gwangwani huɗu ko shida. "Idan yara suka shigo sashenmu da rana aka ce babu abinci, to sun san ni Ziyada ce na yi girkin a ranan." "A da can baya, Maman Suwaiba ta taɓa kawo yaranta Ummiyo da Zainabu wai su riƙa kwana damu. Ai" "tuni na koresu na ce ɗakin ba zai ishemu ba. Kaka ta ce na barsu a shimfiɗa musu wata ƙaramar katifa a ƙasa su riƙa kwana, na ce Wallahi bata isa ba. Idan ta ce sai sun zauna a ɗakin zan bar gidan na koma Kaduna wajen Ummana. Daga jin haka, sai ta haƙura ta cewa Maman Suwaiba ba za ta karɓi yaran ba. A hakan sai da suka yi ta ganin baƙin Kaka. Wai mu biyu mun yi kane-kane a ƙaton ɗaki. Oho dai ba za su zo su takura mana ba." Ina ganin yadda yaran suka yanyame abincin da Kaka ta zuba musu suna ci kamar wanda suka yi 48 "hours ba su ci abinci ba, na ja tsaki na shige ɗaki yunwar da ke cina ma na ji ya koma." "Ga munafukin Ubansu ya je ya ciwo bashi a gurin Alhaji Nafi'u, yana so ya muzgunawa rayuwata ta ƙarfi." "Wallahi idan kuka tambayeni wace sana'a Baffa Lawalli yake har ya auro mata uku, ban sani ba. Gara" "Baffa Zakari gadi yake a Banki. Baffa Adamu da ke Katsina ɗan Kasuwa ne yana siyar da su Hatsi da Masara. Baffa Mamman Non Academic Staff ne a ABU. Shi kaɗai ne cikinsu ke karɓan Salary. Shi Baffa Lawalli da can muna yara na san dai yana gyaran Takalmi da Jaka a Kasuwa. Daga baya har wankin hula yana yi. Ya zo kuma wai yana dillanci. Ƙarshe dai kame-kame kawai yake ba shi da sana'a guda ɗaya da yake. Shi yasa kullum cikin cin bashi ya ke, da kuma maula." An ce Kakana Malam Haruna Manomi ne sosai. Da noma ya sayi babban fili ya gina gidan da muke ciki. A "ƙarshen rayuwarsa jinya ya hana shi yin noma. Ya yi jinya sosai, dan Kaka ta ce ya kusa shekara shida yana kwance kafin Allah ya masa rasuwa. Ya rasu ya bar gonakai da yawa, amma duka yaransa sai suka siyar suka ƙi yin noma." "An ce Manomi ba ya rasa abinda zai ci. Tunda kuwa suka ce ba za su yi noma ba, shikenan suka ƙulla" "alaƙa da bauta kafin su samu abinci. Hakan kuma akwai wahala, musamman ga mutum kamar Baffa" Lawalli da zuciyarsa ta riga ta jima da mutuwa murus. Har ɗaki Kaka ta kawo min Ɗumame ganin ban fito ba. Na karɓa na fara ci ko taste ɗinsa bana ji saboda zuciyata a jagule ta ke. Wajajen ƙarfe goma na kira Baffan Katsina na gaishe shi. Kafin ma na fara masa bayani sai ya ce mini "yana Kasuwa wai sun yi magana da Baffa Lawalli tun jiya, ƙarshen sati zai shigo Zaria a zauna a tattauna" maganar. Na sauke nannauyar ajiyar zuciya bayan na kashe wayar. Ba zai fa saɓu ba. Ba za su haɗe min kai su ce za su bayar da ni wa Alhaji Nafi'u ba. Wannan zalincin ba zai yiwu ba... *** JAYKAY """Dad!"" Junior ya kira ya nufo shi da gudu." """My Birthday Boyyy"" Jalal ya faɗa yana shafa gashin kan yaron." "Gobe ne Birthdayn ɗansa Muhammad Junior, kuma Antynsa Janan ta shirya masa Birthday Party da" yamma. Ofcourse sai da ta billing ɗinsa kuɗin party. """Mom zata zo gobe""" """Mom?, Your Mom?"" Ya tsare yaron da ido dan in dai Mom ɗinsa Cassandra ya ke nufi, to abin da" Mamaki. Tun da ya yi mata faɗa ranan ba su sake magana ba. Junior yana da waya. Ofcourse an yi customizing wayar saboda ta zama kids friendly. Kuma daga wayar Jalal akwai application da aka saka masa zai iya accessing wayar Junior ya dinga monitoring duk abinda ake da wayar. Musabbabin bashi wayar ma saboda ya samu damar magana da Cassy ne a duk lokacin da ya ke so. "Amma Hajiya ta saka masa screen time, dan haka duk dare wayar tana wajenta sannan bata barinsa ya tafi da ita school." """Cassandra, za ta zo gobe?"" Ya sake tambayar yaron, to be sure." """Yes"" yaron ya gyaɗa kai cike da farin ciki. ""She promised me she'll come for my birthday""" "Jalal ya shafa fiskar yaron ya ce ""that's good"" Cassandran da ya sani ba zata bar business ɗinta ta zo" Nigeria saboda Birthdayn ɗansu ba. Amma ba ya so ya ɓatawa yaron rai shiyasa yai shiru. Wucewa ya yi ɗakin Hajiya ya gaisheta sai kuma ta tambayeshi yana da labarin Cassandra za ta zo gobe?. "Ba ya so ya nuna mata bai sani ba, sai ya ce mata e ya sani." "Idan Cassandra bata zo goben ba, ya san ƙaryar da zai faɗa mata." "Hajiya ta ce ""Allah ya kawota lafiya""" """Amin"" ya amsa ƙasa-ƙasa." Jin bata sake cewa komai ba sai ya miƙe ya fita. "Yana shiga ɗaki suit ɗinsa kawai ya cire ya ajiye akan gado, ya zauna a gefen da ya ajiye suit ɗin ya shiga" kiran numbar Cassandra. Jin bata ɗauka ba sai ya yi tsaki ya ajiye wayar ya cire kayansa ya shiga banɗaki ya yi wanka. Bayan ya fito sai ya saka comfy black shirt da grey wando ya sake jawo wayarsa sai ya ga ashe Cassy ta tura masa saƙo ta email ɗinsa. Yana buɗewa sai ya ga ticket ɗin jirgi daga London zuwa Abuja tareda gajeran saƙo wai ya turo mata Direban da zai zo ya ɗauketa daga Abuja ya kawota Zaria. Da gaske kenan za ta zo ɗin. Gara ta zo ɗin saboda su samu damar tattauna alƙiblar aurensu. Sake duba time ɗin da flight ɗinta zai sauka ya yi saboda anjima idan zai fita sallah ya faɗawa Direbansa zai je Abuja gobe. Washegari kuwa shi ya tuƙa kansa zuwa office saboda ya aiki Direbansa Abuja. Lokacin da zai fita sai da ya yiwa Junior alƙawarin zai dawo da wuri saboda Birthday Party ɗin da aka shirya ƙarfe huɗu ne. Zuwa ƙarfe shaɗaya na safe Sakatariyarsa ta masa maganar meeting da ya ke da shi da Chef Jonah. Chef "Jonah, wanda ake kira da Chef Joxxy a social media, shine Chef ɗin da Jalal ke son ya musu aiki a restaurant." "Ba yan ya bawa Sakatariyarsa go ahead akan ta shigo da shi, sai wani ɓangare na zuciyarsa ya tuno masa" da Ziyada. He did the right thing da bai ɗauketa aiki ba. Ya sake jaddadawa ransa. Chef Jonah ne ya fi dacewa da restaurant ɗinsa in dai har yana son wajen ya bunƙasa da kyau. Chef Jonah ya fi Ziyada yawan experience. Ya yi aiki a manya-manyan hotels dake Kaduna. Ya yi aiki har a "Government house da ke Jos a matsayin Assistant Chef. Chief Financial Officer ɗinsu wato Mr Munir ne ya recommending ɗinsa, saboda ƙwarewarsa a national da international cuisine." "Chef Jonah yana kan nuna masa sample ɗin menu da za su yi amfani da shi a restaurant ɗin, amma" "ƙwaƙwalwarsa sai maimaita masa maganganun Ziyada yake. Particularly, wajen da ta ke cewa" """Da kake cewa idea ta bata dace da restaurant ɗinka ba, kada ka manta bani na kawo kaina nan ba." "Hajiya ce ta nuna tana so na yi aiki a nan saboda ta yarda dani""." "Idea ɗinta na da kyau, amma for a small scale restaurant, ba irin wanda suke son buɗewa ba." "He's right. Aiki da Chef Jonah shine dai-dai, ba wai aiki da Chef Zeey ba. Ya sake faɗawa kansa." Ganin hankalinsa ya rabu biyu sai kawai ya sallami Chef Jonah akan za su sake zama akwai inda zai je. """Ɗan'uwanka is more open to new ideas"" ya tuno kalaman Hajiya." "Tunani ya fara, idan Jamal ne, wanne zai ɗauka?..." *** Bai samu ya shigo gida da wuri ba sai ƙarfe biyar saura. Bai so haka ba. Ya so a ce da shi aka buɗe partyn. Already yara sun cika gidan. Sai wasanninsu suke yi. Hannunsa ɗauke da gift ɗin da ya siyo ya nufi wajen da Junior ke tsaye yana magana da wasu yara. """Dad!"" Ya zo wajensa da gudu Jalal ya ɗaga shi sama yana bashi haƙuri kan bai zo da wuri ba." """Look, Mom ta zo"" ya nuna masa inda Cassandra ke tsaye tana waya." Kallon wajen da ya yi sai ya yi dai-dai da juyowarta. Tana ganinsa ta fara tahowa fiskarta ɗauke da murmushi. Ajiye Junior ya yi wanda ya karɓi gift ɗin hannunsa ya yi wajen abokanansa da gudu. Kallon shigar da ta yi yayi yana girgiza kai. Yana fatan Allah ya sa Hajiya bata ga shigar nan ba. "Ba tareda ta cire wayar a kunnenta ba, ta ƙariso wajensa sannan ta kashe wayar ta faɗa jikinsa." """Come, let me kiss you"" ta tallafo kansa. Ya buɗe baki kenan zai ce mata akwai yara a wajen ta haɗe" bakinsu ta fara masa deep kiss har sai da ya breaking kiss ɗin da ƙarfi ya ɗan turata. """J Love, you know I fuckking miss you""" """Kids"" yai mata nuni da yaran da ke wasanni a wajen." Ta bi shi da kallon ko oho. Wuceta ya yi zai shiga cikin gidan ta riƙo hannunsa tana faɗin ta yi missing ɗinsa sosai. Suna shiga falo hannu sarƙe cikin na juna suka samu Hajiya da wasu mata guda biyu suna magana. Jalal yai saurin cire hannunsa daga na Cassandra amma ita sai ta ƙi sake shi. Gaishe da Hajiya ya yi da baƙin nata yayinda Cassy ta yi ko oho bata gaishe su ba. Hajiya da ranta ya ɓaci da shigar da Cassandra ta yi ta ce mata ba za ta gaishe da baƙinta bane?. "Sai a lokacin Cassy ta miƙa musu hannu tana faɗin ""Hi, I'm Cassandra, but you can call me Cassy""" Matar da Cassandra ta miƙawa hannu ta kalli hannun ta juyar da kanta gefe ta haɗe rai. Daga yanayinta ka san daga gidan Sarauta ta fito. "Ɗaya matar ce ta kalli Jalal sannan ta ce ""Hajiya Layla, na ɗauka sirikar taki daga tsatson Turawa masu" "daraja ta fito. Ashe ragowar Club ce""" Ba Hajiya Layla kaɗai ba. Shi kansa Jalal ya kaɗu da maganar da aka faɗa. """What are they saying?"" Cassandra ta tambaya saboda ta tsargu da yadda suke kallonta." Hajiya Layla ta cize leɓe tana jin wani zafi na taso mata daga can ƙasan zuciyarta. "Tun ɗazu da Cassy ta sauko daga ɗakin Jalal da shigar nan, Hajiya ta ce mata ta koma ta chanja dan bai" dace ta shiga cikin yara a haka ba. Ashe bata chanja ɗin ba. Jalal bai ce komai ba ya wuce su ya haura sama. Cassy ta bi bayanshi tana tambayarsa me matar nan ta faɗa amma bai kulata ba. """Jalol"" ta kira shi da sigar da ta ke kiran cikakken sunansa." """Hey! I'm talking to you"" ta faɗa da ɗan ƙarfi tana riƙe hannunsa ganin zai wuceta ya shiga banɗaki." """Take a look at what you're wearing, Cassy""" Kallon kanta ta yi tana ganin rashin aibun suturar da ke jikinta. Tun data shigo Nigeria ta ke ta faman shafa sunscreen saboda zafi. """What's wrong with what I'm wearing?"" Ta faɗa tana kallonsa galala dan bata ga laifin shigarta ba." """Everything's WRONG with it CASSANDRA. This is Nigeria, you have to wear DECENT clothes"" ya faɗa a" fusace. """There's so much fucking heat here, Jalol. It's not my FAULT.""" "Shiru ya yi yana kallonta, wani sabon ɓacin rai na taso mata. Crazy bum short, da rigar da bata rufe mata" ciki bane a jikinta. Shigewa banɗaki ya yi ya bugo ƙofa da ƙarfi dan babu amfanin cigaba da maganar. Lokacin da ya fito daga banɗaki sai ya samu Cassy ta cire kayan ta saka wani floral gown ja da fari da yellow da ya kai mata iya gwiwa. """Is this DECENT enough for you?""" Juyar da kansa ya yi bai kulata ba. Ya tafi wajen closet ya fara neman kayan da zai saka. Har Cassandra ta fita daga ɗakin bai sake magana ba. Saboda ya san ran Hajiya ya ɓaci sai bai sake saukowa ba har 'yan Birthday party suka gama abinsu suka watse. "A ɗaki ya yi sallar Magariba saboda wani ciwon kai da ya taso masa. Actually, gudun haɗuwa da Hajiya" "ne ya hana shi fita. Sai da aka kira Isha sannan ya daure ya yi alwala ya fito, ya haɗu da Cassandra a lobby za ta je ɗakinsa. Matsa mata ya yi ta wuce ba tareda ya mata magana ba." Bayan an yi sallar Isha purposely sai ya ƙi dawowa gida da wuri ya tsaya har kusan ƙarfe goma kafin ya taho. Lokacin da ya shiga falo sai ya ci sa'a babu kowa. Yai sauri ya haura sama ya tafi ɗakin Junior dan ya duba "shi. Yaron har ya yi bacci ko kayan jikinsa bai cire ba. Ga nan gifts kala-kala akan gadonsa, wasu a ƙasa, wasu ya buɗe, wasu bai buɗe ba. Da alama yana cikin buɗe gifts ɗinne bacci ya ɗaukeshi. Ya gyarawa yaron kwanciya ya tofa masa addu'a ya kashe wutan ɗakin ya fito." Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya shiga. """Hey"" Cassandra ta taso daga inda ta ke zaune a gaban mirror ta zo za ta rungumeshi ya dakatar da ita." """J Love, I'm sorry"" ta sake ƙoƙarin shiga jikinsa amma ya wuceta ya ce mata bacci yake ji." "Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, sannan ya fito ya saka kayan bacci ya kwanta ko kulata bai yi ba. Zuwa" lokacin ta gama shafe-shafenta ta kwanta a gado. Ta kai hannunta ta taɓa shi sai ya ture hannun ya matsa can nesa da ita. Wannan ya sa ta haƙura itama ta juya masa baya ta fara bacci. Taɓa shi da yaji ana yi ta ƙasansa ne ya sa shi buɗe ido tunma kafin alarm ɗinsa na ƙarfe huɗu ya buga. """Hey, stop, don't..."" yai yunƙurin miƙewa amma tuni Cassandra ta kifa kanta akan sandar girmansa" "hakan ya saka shi yin shirun dole. Ta riga ta san lagonsa. Sama da shekara goma, ta san ina ne weakness" ɗinsa. Lokacin da ta gama yi masa wasa da bakinta har yana ƙoƙarin kawowa sai ta yi sauri ta haye samansa ta fara tuƙashi. Tabbas idan ta wannan harkar ne. Cassandra Karuwa ce. "Kusan shekara guda rabonsa da mace, wannan ya sa ya mance da haushinta da ya ke ji. A karo na biyu" "da za su je, sai ya juyata ya haye samanta yai mata rumfa, amma me! Wannan Iskar da ke kawo masa tunaninta ne ya sake hura masa kai. Wannan karan, maimakon Cassandra, idanunsa ita suke kallo..." CHAPTER SIXTEEN JAYKAY Sai da Jalal ya makara sallar Asuba. Lokacin da ya bar jikin Cassandra ƙarfe shida na safe har da minti biyu. Yana shiga banɗaki yai wankan tsarki ya yi alwala sannan ya fito. Shimfiɗa sallaya ya yi ya tada sallah. "Bayan ya idar da sallah sai ya ɗan yi Azkar, sannan ya tashi ya zauna a kujera ya buɗe Laptop ɗinsa zai" reviewing wani Business Document da za su yi meeting a kai yau da safe. Yana cikin dubawa Cassandra ta tashi daga bacci. """Good Morning, J Lovvvve"" ta tashi daga kan gadon babu komai a jikinta, gashinta ya ɗan yi buju-buju" "har yana rufe mata gefen fiska. Ta sa hannu ta kwashe duka gashin ta naɗe shi, ta yi shi kamar bun." """Working?"" Ta tambayeshi lokacin da ta zo ta bayanshi ta rungumeshi tana kissing wuyansa." Ɗan tureta ya yi ya ce mata aiki ya ke kada ta dame shi. Cassandra ta kissing goshinsa sannan ta je ta ɗau shirt ɗinsa da ke ƙasa ta saka. """Going to get tea, wants some?""" Ba tareda ya ɗago ba ya girgiza mata kai. * A hankali take saukowa daga stairs fiskarta ɗauke da murmushin farin cikin da ta tsinci kanta a ciki bayan "gamsuwar data samu daga wajen Jalal. Ta ji jiki a hannun Jalal. Da farko ta matching ƙarfinsa ne, amma daga baya da ta ga yadda ya ke ta lailayata sai ta sadaƙar kawai, ta bar masa jagorancin. Babu wani namiji da ya taɓa zuwa close to yadda Jalal ke gamsar da ita. And to think that cewa akanta ya fara. Ita ta koya masa yadda zai jiyar da ita daɗi. And God! Ya riga ya mastering the art of giving her greatest pleasure." """Morning, Mrs Maeyerkee"" Cassandra ta gaishe da Hajiya da ta gani zaune a dining tana shan magani." Kiran Hajiya Layla da Mrs Maeyerkee da Cassandrar ke yi ba sabon abu bane a wajen Hajiyar. "Hajiya ta ɓata fuska. Ba sunan bane ya sake tuno mata da ɓacin ran da ta kwana da shi jiya, illa wucewar" da Cassy ta yi sanye da shirt ɗin Jalal a jikinta. Daga yadda take yawo a cikin rigan ka san bata sa komai a ciki ba. Janan da Junior suna ɗakinsu ba su sauko ba. Mai-aiki na kitchen tana kujuba-kujubar haɗa breakfast. "Amma duk da haka, yawo da shirt ɗin Jalal a cikin gida bai dace ba." Hajiya Layla ta ja tsaki. Ba kayan jikin Cassandran kaɗai bane ya bata haushi. Ita karan-kanta wacce ta "saka kayan ne Hajiya bata so. Tun a baya bata sonta. Balle kuma daga yammacin jiya zuwa yanzu, wani sabon tsanarta Hajiya ke ji." Daga inda ta ke zaune tana jin yadda Cassandran ke yiwa Mai-aiki bayanin yadda za ta haɗa mata tea ɗin da za ta sha. Hajiya ta miƙe ta wuce ɗakinta. * "Lokacin da Jalal ya gama shirinsa ya fito, Cassandra ta gama shan tea ta sake komawa bacci. Dan sai a" lokacin jikinta ya buƙaci hutun gajiyar jujjuyata da tanƙwarata da Jalal ya yi ta yi da Asubahin yau. Ɗakin Hajiya ya shiga zai gaisheta kafin ya wuce office. Ko breakfast ba zai iya yi ba saboda lokaci ya ƙure. Ya sameta tana zaune a kujera sanye da hijabin sallarta har da carbi a hannunta amma hankalinta ya yi wani waje. Tunani take. Ya ɗan ji jikinsa ya yi sanyi da yanayin da ya ganta. Duk sadda ka ga Hajiya a haka to tunanin Jamal ta ke yi. Lokacin da Daddynsu ya rasu. Hajiya ta kaɗu ba kaɗan ba. Amma cikin ƙanƙanin lokaci ta warware ta cigaba da kula da kasuwancinsa ita da Jamal. Kasancewar Jamal kusa da ita shi ya hanata shiga damuwa na tsawon lokaci bayan rasuwan Daddyn su. "Amma, lokacin da Jamal ya rasu. Tamkar ya tafi da wani ɓangare na rayuwarta ne da shi Jalal ba zai sake" "gani ba. Bayan rasuwan Jamal, sai Hajiya ta cire hannunta daga komai ta bar masa jagorancin kamfanin. Janan tana aiki a wajen, amma aikin da take is more of jeka na yika ne ba wani abin kirki ta ke ba. Shi yasa ma aka bata wani ƙaramin position a wajen. Idan ta Janan ne, bata ƙi kawai ta dinga kwana tana tashi bata komai ba, sai danna waya, online shopping da kuma yawon duba sabbin wajaje a ciki da wajen Zaria." "Ganin Hajiya a haka sai ya breaking ɗinsa, musamman da ya tuna cewa akwai yiwuwar abinda ya faru" jiya akan Cassandra ne ya ɓata mata rai. Amsa gaisuwarsa ta yi sannan ta kira sunansa a hankali da dasashshiyar muryar da ta fi kama da kuka ba wai mura ba. """JALAL""" """Yes, Hajiya"" ya amsa cike da tsoron abinda za ta faɗa masa" """Aure nake so ka yi Jalal"" ta faɗa ko ƙyaftawa bata yi daga kafe shi da ido da ta yi ba." AURE. Ya maimaita a ransa. """Musulma, 'yar Nigeria, kuma Bahaushiya"" ta jero masa sharuɗɗa uku." A baya ta kan ce masa zai iya auro kowacce yare ma ya kawo in dai Musulma ce kuma 'yar Nigeria. "Amma yanzu tura ta kai bango, abubuwa ukun nan take so a cikin mace ɗaya." Shiru ne ya biyo bayan abinda ta faɗa. Kowannensu da tunanin da ya ke a zuciyarsa. *** ZEEY """Hajji Jibrin, Mutanen Lagos""" Kaka ta faɗa ganin mutumin da ya shigo wajenmu. Na ɗan ɗago kaina dan a kwance nake ina karanta "handout ɗin course ɗin da za mu rubuta Friday. Jiya Laraba exams ɗin ta yi sauƙi dan elective course ne, amma ta gobe gaskiya sai a hankali. Ga shi Doctorn da ya ke ɗaukanmu course ɗin ya tara mana manya- manyan handouts guda uku har da text book biyu wai duk materials ɗinsa ne mu je mu karanta." Yaya Jibrin ne ya shigo. Sai nima na washe fiska ina gaishe shi da Hajji mutanen Lagos. "Zama ya yi a dakalin ƙofar ɗakinmu, ya fara gaishe da Kaka." """Jibrin tashi a wajen, bari Ziyadatu ta ɗauko maka kujera a ɗaki""" """Barshi kawai, Kaka Altine. Makanike ai babu inda baya zama """ Na miƙe da sauri na shiga ɗaki dan na kawo masa kujera. Wajen da ya zauna akwai ɗan rana ta gurin. Dana fito masa da kujeran sai na ajiye jikin gini kusa da Kaka na ce masa Bismillah. """Nagode, Ziya. Ya girke-girke?. Ai kafin a sace mini Andiroyid ɗina ina kallon duka bidiyon da kike" "ɗaurawa a Fezbook""" """Allah Sarki! Ai yaya Jibrin Alhamdulillahi kawai. Ɗaura girki a social media ya yi mini rana. An fara samun" "alkhairi""" "Yaya Jibrin ya ce ""Masha Allahu""" "Yaya Jibrin yana ɗaya daga cikin waɗanda suke bibiyana tun farkon fara food content ɗina, lokacin ma a" Facebook kaɗai nake yi. "Jibrin ɗan Baffa Lawalli ne. Shine babba a cikin maza. Suwaiba ita ce 'yar fari, sai Hajara, sai shi Jibrin ɗin." "Ya jima da barin gida. Tun ma kafin ya tafi Lagos ba a gida yake kwana ba saboda sun yi faɗa da Babansa. A lokacin an ce wasu kuɗi yaya Jibrin ɗin ya bashi ajiya, shi kuma Uban ya cinye." "Jibrin Makaniken mota ne. Kafin ya tafi Lagos yana ƙarƙashin wani Ubangidansa ne a nan Zaria, daga" "baya dai sai ji muka yi wai ya bi babbar mota ya tafi Lagos. Sai da ya yi shekara biyu bai dawo ba. Da ya zo gida kuwa ya taho da kuɗi masu yawa ya fara gini. Ashe dama kuɗin da Baffa Lawalli ya cinye kuɗin da ya ke tarawa zai fara gini da shi ne, dan ya jima da siyan fili." Muna chatting da shi Sama-sama ta Facebook idan ya min magana. Bayan shekara biyar a Lagos kwanaki da ya zo ya ce mana yanzu yana da garejin kansa. "Abubuwa sun bunƙasa masa gaskiya, dan the last time da ya zo an gama komai na gidansa saura fenti. 3" bedroom ne mai kyau dai dai gwargwado babu laifi. Ni da Kaka ya kaimu muka shiga gidan muka sa albarka. Har yanzu tsakaninsa da Babansa sai a hankali. Musabbabin rashin jituwarsu ɗin dai still maganar kuɗi ne. Zai turo masa kuɗi daga Lagos dan ya yiwa Maman Suwaiba da ƙannensa hidima amma sai ya cinye kuɗin Maman Suwaiba ta dinga damunsa wai baya turo musu komai. Har machine ya taɓa siyawa wani ƙaninsa akan ya riƙa hawa yana Acaɓa amma ko wata shida machine ɗin nan bata yi ba Baffa Lawalli ya je ya siyar ya biya bashi saboda an ce za a kai shi Police Station. Tun daga lokacin yaya Jibrin ya dena tura masa kuɗi ko yi masa kyauta. Duk abinda zai yiwa Mahaifiyarsa sai dai ya turo saƙo ta hannun wasu. A hakan fa wani abun sai dai ya siyo ya aiko dan idan kuɗi aka turo Baffa Lawalli ya ji labari haka zai bi gefe ya karɓe a hannun Maman Suwaiba. Idan yaya Jibrin ya tafi Lagos sai an ganshi kawai. Shi yasa muke mamakin ganinsa rana tsaka a gidan namu. Sama-sama na ke jinsu yana yiwa Kaka taɗin maganar aurensa ne ya kawo shi gida. Wai ashe har an saka "rana. Yarinyar 'yar Kano ce kuma Baffan Katsina ne ya shige masa maganar auren ba Babansa ba. Ban yi mamakin haka ba, dan har yanzu basa ga maciji da Babansa. Kuma duk inda Baffa Lawalli zai yi maganar yaya Jibrin zaginsa ya ke ya ce ya tafi bariki Lagos ba ya taimaka masa da komai. Kuma fa tsakani da Allah yana taimakawan dai-dai gwargwado. Ko lokacin da Mardiyyah za ta sake zana jarrabawar NECO, na ji an ce shi ya biya mata. Shi dai Baffa Lawalli tunda yaya Jibrin ya dena tura masa kuɗi ta hannunsa ya ke jin haushinsa." Ni da Kaka muka masa fatan alkhairi da addu'ar Allah ya sa a yi biki lafiya. Wai auren za a yi shi kwana uku bayan sallah dan haka yana nan a Zaria har sai bayan biki kafin ya koma. Sai da ya yi lissafin saura kwana nawa bikin nefa na tuna cewa ashe fa ana ta maganar Azumi saura kwana biyar ko shida. Ko jiya sai da Ummana ta tambayeni ko zan zo na yi musu Azumi na ce mata ban sani ba sai dai mun kammala exams na gani. Yaya Jibrin ya jima a sashenmu kafin ya tafi har da bawa Kaka dubu uku wai ta sayi goro. Daren ranan wuni na yi ina karatu har ɗayan dare kafin na kwanta lokacin dana ga idona ya fara ganin bibbiyu. Exams ɗinmu da safe ne dan haka da Asuba tashi ɗaya Kaka ta mini na miƙe. Ashe bacci ma waje ya samu. Wanka na yi sannan na ɗauro alwalar sallar Asuba. Ai ina idar da sallah sama-sama na yi Azkar sannan na sake jawo handouts da ɗan jotings ɗin dana yi na fara bita. Bakwai na safe har na fita daga gida. A school na haɗu da Faty Amarya idanunta sun ƙwala-ƙwala saboda rashin bacci. Hijabi ta zumɓula har "ƙasa, ta ce mun na sallarta nema tsabar sauri ta jawo ta saka. Na ce mata me ta ke yi bata tashi da wuri ba ta fara bani labarin yadda mijinta ya zo ya hanata karatu jiya da dare. Ina jin ta fara zancen Ma'aurata na dakatar da ita na ce mata Allah dai ya bamu sa'a kawai." Da aka fara shiga hall muka shiga da addu'a a bakunanmu... Na riga Faty fitowa daga exams. Ban san me ta tsaya rubutawa ba amma har sai da aka fara threatining "ɗinsu akan saura minti biyar a ƙare jarrabawa sannan ta submitting ta fito. Ni kam tunda na iya amsa questions biyu masu kyau sauran kuma na rubuta abinda zan iya, na ce ya isa haka. Allah na gani ni ban iya tambayar mutane Answer a hall ba. Ko irin ka ɗaga mini na kwafa ɗinnan bana yi. Idan muka zauna da Faty na samu dama ina ɗaga mata ta kwafa, amma bana iya magana a hall dan tsoro nake ji." Ina isa ƙofar gidanmu dana ga tsohuwar motar Baffan Katsina a ƙofar gidan sai na sawa raina ko dai na "samu Jummu'ar Alkhairi, ko kuma na samu Jummu'ar Allah Sarki!." Na shiga gidan zuciyata a sanyaye. Sashenmu na fara shiga na kuwa samu Kaka ta ce Baffa Adamu ya iso a nan garin ma ya yi sallar Jummu'ah. Ko cire kayan jikina ban yi ba jakata kawai na ajiye na yi cikin gida. Gidan Baffa Mamman na wuce bayan Yakubu ya ce min suna can. Su uku na samu a falon. Da alama Baffa Zakari yana wajen aiki. Na tsugunna har ƙasa na gaishe da Baffa Adamu sannan na gaishe da Baffa Lawalli da Baffa Mamman da ke latsa wayarsa. Baffa Adamu ya tambayeni ya karatu na ce masa Alhamdulillahi jarrabawa ma nake rubutawa. Daga "wannan, ajin ƙarshe za mu shiga." "Ya min addu'ar Allah ya bada sa'a na ce masa Amin. Lokacin dana miƙe zan tafi sai Baffa Lawalli ya ce """ "tunda kin zo, Adamu, mu yi mata maganar yanzu kawai a wuce wajen""" Sai na ji zuciyata ya buga da ƙarfi. "Baffa Adamu ya kalleni ya ce ""ZIYADATUN dawo ki zauna, akwai maganar da za mu yi da ke""." "Yau dai, Jumma'ar Allah Sarki ce..." CHAPTER SEVENTEEN ZEEY "Ina ga babu wanda bai maimaita kalmar ""mu iyayenki ne"" sau biyar ko fiye ba a cikinsu. Tunda naga sun" "dage da bayyana mini abinda na sani tun tasowata, na san cewa wani fin ƙarfin suka shirya min." Sun buɗe maganar ne da tarihin haihuwata. Yadda Babana yai ta yi mini addu'ar tsawon rai. Da yadda "mutuwarsa ya zo musu ba-zata, ya girgiza su. Suka ƙare da faɗan kyawawan halayen Babana. Baffa Lawalli har da cewa ""ai Sadiq baya faɗa da kowa. Ba shi da matsala da kowa har ya rasu""" Baffa Adamu ya kira sunana. Ya tambayeni ya ake ciki da maganar aure. Na ɗan ɗaga ido na kalli Baffa Lawalli wanda fiskarsa ya ke ɗauke da fara'ar nasara. Nasarar zuga Baffa "Adamu. Nasarar zai samu damar aurawa Alhaji Nafi'u ni. Na ɗan saci kallon Baffa Mamman na ga hankalinsa na kan waya sai na sunkuyar da kaina na ce ""Baba, dama sai na gama karatu na ke so na kawo muku shi""" """Ki kawo mana shi wa? Alhaji Nafi'u dai ko yau aka ce ya zo a ɗaura muku aure a shirye yake"" Baffa" Lawalli ya katseni tunma kafin na sauke numfashi. """Baban Suwaiba, ka bata dama ta faɗi abinda ke ranta"" Baffa Adamu ya maida dubansa gareni ya ce """ "shi waye za ki kawo mana ɗin?. Sannan a ina yake?""" "Na haɗiye wani ƙullutu, bakina ya kafe na kasa magana. Ba na son Baffa Lawalli ya ci galaba akaina" "shiyasa na ce musu akwai wanda muke tare. As far as I know, ni Ziyada bani da takamaimai saurayi. Yaya Aminu baya cikin lissafi. Bashir abokin mijin Faty da muke chatting ya faye kankanba, shiyasa har yau na ƙi bashi dama ya zo hira. Mustafa ɗan ajinmu da ya ke damuna a class yarone, nan da shekara biyar ma ban ce zai shirya aure ba. Waye kuma? Uhhmmmmm! Ko Malam Ali mai kayan miya da ke bakin layinmu zan faɗa musu?. Kai! Bani da saurayi. Amma ba zan bari su fahimci ƙaryar nan ba. Rikicin duniya da mai rai ake. In dai na kuɓuta daga tuggun Baffa Lawalli aka kashe maganar Alhaji Nafi'u shikenan zan san yadda za mu wanye da Baffa Adamu lafiya." """Ba Alhaji Nafi'u nake nufi ba. Wani ne daban. Muhammad sunansa"". Ashe ƙarya akwai daɗin faɗa." "Gashi tun dana fara bayani komai ya tafi tiryan-tiryan, har sunan saurayin da babu na ƙirƙiro, duka a" cikin abinda bai fi sakan shabiyar ba. """Ƙarya take. Babu mai zuwa wajenta zance sai Alhaji Nafi'u""" """Allah Baba akwai wanda ya ke nemana , bai cika zama a garin nan bane ya sa ba ya zuwa sosai amma" "muna magana sosai ta waya"" na katse Baffa Lawalli tun kafin ya ɓaro wani abin." """To ka ji ko. Adamu kana jinta ko. Tana nan ta maƙalewa Samarin ƙarya suna hure mata kunne sun" "hanata ta karɓi mutumin arziƙi kamar Alhaji Nafi'u""" "Baffa Adamu ya katse shi ta hanyar faɗin "" Ziyadatun, kin san bana son ƙarya ko. Tsakaninki da Allah" "akwai wanda kuke tare da shi?""" "Sai dana karanto istigfari a zuciyata kafin na ce masa ""Wallahi ina da Saurayi, dake shima akwai aikin" "daya ke so ya kammala ne, shiyasa ban gabatar muku da shi ba har sai na kammala karatu""" """Karatun Bokon ƙaryan da ya saka miki girman kai ba za ki ƙarasa shi a gidan nan ba. Adamu, ba za mu" "zuba ido ta zauna mana a gida tana soyayyar ƙarya ta waya tana ɓatawa kanta lokaci bayan akwai mutumin kirki da ke son aurenta ba. Idan ba sakashi da kuma Kakarta data zuba mata ido ba, duk cikin yaran da aka aurar a gidan nan wacece a cikinsu ta kai shekara ishirin? Amma saboda kin rantse sai kin bautawa Boko kin doshi shekara talatin kina zaune a gida babu aure, kamar baki da mafaɗi a gidan""." """Ni ban doshi talatin ba"" na faɗa ƙasa-ƙasa." """Magana kike?"" Baffa Lawalli ya sake harzuƙo mini." """Ni ban ce komai ba""'" """Ziyadatun""" """Na'am, Baba""" """Ni da sauran iyayenki mun yi magana. Amma tunda kin ce akwai wanda kuke tare da shi. Ni Adamu" "Haruna, a matsayina na wan Ubanki, ba zan miki auren dole ba. Amma maganar sai kin ƙarisa karatu kafin ki gabatar mana da wanda kuke tareda shi bai taso ba. Ke ba yarinya ba ce. Alhamdulillahi karatun naki kaɗan ya rage. Dan haka lokaci ya yi da za ki bawa maganar aure mahimmanci, koba haka ba, Mamman?""" "Baffa Mamman ya ɗago ido ya ce ""maganarka gaskiya ne, Yaya. Ai aure ba zai hanata karatu ba""" "Ya kalli gefena ya ce ""Ziyada, No Furoblem fa. Ki kwantar da hankalinki. Dan shekara ɗaya kam ai za ki" "iya ƙarisawa a gidan miji. I am Froud of you sosai Wallahi. Karatun mace yana da mahimmanci. Amma ki sani, karatu ba zai hana ki yin aure ba. So, kada ki damu, ba wani furoblem. Ki gabatar mana da saurayinki, mu kuma sai mu yi bincike akansa idan mun gamsu da shi babu wani Furoblem, sai a shirya muku aure." "Sai cewa yake babu wani Furoblem, bayan ni na san akwai babbar Problem a ƙasa." Baffa Adamu ya ƙarƙare bayaninsa da cewa sun bani wata uku na turo musu saurayina idan bai zo ya gabatar da kansa ba kuma za su bayar da aurena ga Alhaji Nafi'u tunda su Baffa Lawalli da Baffa Zakari sun yi bincike akansa sun tabbatar mutumin kirki ne. "A zuciyata na ce dole su ce mutumin kirki ne mana, tunda sun je sun ciyo uban bashi a wajensa." Lokacin dana bar falon na dawo sashenmu faɗawa kan gado na yi ina maimaita addu'ar samun sauƙi a "zuciyata. Kaka tana tambayata me su Baffa Adamu suka faɗa, amma ban kulata ba." "Wata uku na ke da shi in samawa kaina mafita, kafin a min auren biyan bashi da Alhaji Nafi'u." To kodai kawai na fito fili na faɗawa Baffa Adamu gaskiyar abinda ke faruwa ne?. To kuma idan na faɗa "masa ma ba lallai ya yarda ba, dan na san Baffa Lawalli ya riga ya gama hure masa kunne." Yanzu ni Ziyadatu ta ina zan fara nemo saurayi mai suna Muhammad?. "Yaya Aminu ne ya faɗo mini rai. Allah Sarki! Ba dan matsalar da ta katse mana soyayya ba, ai da ba za ma" a kawo wannan gaɓar ba. Gaba ɗaya yinin ranan har dare a ɗaki na wuni. Daga baya na faɗawa Kaka abinda su Baffa Adamu suka "yanke sai ta ce za ta musu magana su ƙara min lokaci, saboda ita ta san bani da Saurayi." Na ce mata ta barsu ba sai ta musu magana ba. Babu amfanin maganar. Kaka bata da zafi. Idan suka fara "kawo ƙabli da ba'adi na karatun mahimmancin aure sama da karatun Boko babu abinda za ta faɗa sai ""To! Allah ya kyauta""." Bana so ma ta ɗaga hankalinta ne akaina. Tana da hawan jini. Idan na nuna mata na damu da abinda "suka shirya mini, to abin zai tsaya mata a rai ne." Yanzu dai ina da kwana casa'in na producing musu Saurayi mai suna Muhammad da zai aureni. Tunda bani da gatan uba a raye ai Akwai Allah!. "Tun da watan Ramadan za mu shiga, zan bi dare na roƙi Ubangiji ya turo mini miji na ƙwarai kafin" wa'adin da aka bani ya cika. Ko kuma dai ya yi ikonsa har maganar Alhaji Nafi'u ta banje. "Na ɗaura aniyar zan yi tsayuwar dare, zan yi sadaka. Sannan zan kira Ummana na ce ta sakani a addu'a." Ganin na samarwa kaina mafita sai kawai na miƙe na fita na je na ɗaura ruwan zafi. Bayan na fito daga wanka na samu Kaka har ta zubo mini tuwo a kwano. """Kuma aka ce miki zan ci tuwon ne"" na faɗa ina tura baki duk da ƙanshin miyar yana bugan hancina." """To me za ki ci, 'yar lelena? Wai na ga tun da kika dawo da rana baki ci komai bane"" ta faɗa cike da" damuwa. Allah Sarki! har ta ban tausayi. """Wasa na ke, zan ci tuwon""" Bayan na saka kaya sai na zauna na jawo tuwon na fara ci. Ina fara cin abincin sai na ji komai ya dawo "mini. Hawaye ya cika mini idanu yana shirin zubowa. Na yi saurin gogewa, na tura lomar tuwon Masara da miyar kuka bakina. Cin tuwon nake ina kukan zuci. Bana so Kaka da ke can gefe tana fama da buga rediyonta da ya ƙi tashi ta gane ina kuka." Cin tuwon nake bana jin taste ɗinsa saboda ɗacin dana ke ji a zuciyata. A haka na cinye shi tas. Kaka tana tambayata ko a ƙaro mini na ce mata ya isheni. Bayan na kai kwanon kitchen sai na dawo na zauna kusa da Kaka a ƙofar ɗaki na ƙurawa Taurari idanu... *** JAYKAY "Ana meeting, amma hankalin Jalal baya wajen. Tunaninsa ya yi nisa ne wajen nemowa kansa mafita akan" "maganar Hajiya. Shi ba yaro bane. Hajiya ba za ta iya tursasa shi ya yi abinda baya so ba. Amma kalamanta na safiyar yau sun fi kama da umurni ba shawara ba. Idan a baya shawara ta ke bashi na ya ƙara aure, yanzu kam umurni ta ke masa." A baya ya bijirewa umurninta lokacin da ta ƙyamaci aurensa da Cassandra. Idan ya sake bijire mata a "karo na biyu, bai kyauta mata ba. Yanzu da babu Jamal, babu Daddynsu. Hajiya da Janan sune mutanen mafi kusa da shi. A London aka haifeshi. A nan ya taso ya yi sama da shekara talatin na rayuwarsa. Duk da suna zuwa Nigeria lokaci zuwa lokaci, amma har yanzu ba shi da wani ɗan'uwa na kusa da ya saba da shi a Familyn MAIYAƘI." "Tun asali Jalal mutum ne very private. Baya shiga harkar da ba tasa ba, kuma baya so wani ya shiga" "harkarsa. Balle tunda ya auri Baturiya sai ya zamo saniyar ware a cikin 'yan'uwa. Duk wanda zai yi kwatance da shi to da matar da ya aura zai fara. Idan za a banbance shi da Jamal, cewa ake ""wannan ɗan Hajiya Layla da ya auri Baturiya ɗinnan"". As if ba shi da wani abu bayan aurensa da Cassandra. Mantawa suke shi pilot ne, da ya kai matakin Captain ɗin jirgi. A wajen mutane, shi Jalal Kabeer Maiyaƙi, mijin Baturiya ne. Duk wani abu, sai dai ya biyo baya wannan." Ba zai so ta dalilinsa Hajiya ta sake shiga damuwa ba. Laifinsa na auren Cassandra zai iya raguwa a "zuciyarta idan ya auri wata matar. Sai dai kuma, idan ya ce zai auri wata a yanzu, tabbas zai samu matsala da Cassandra. Auren kotu suka yi, dan haka a dokar Ƙasar England da Wales ba shi da damar auren wata mace har sai idan ya rabu da Cassandra." Rabuwa da Cassandra kuma a daidai wannan gaɓar ba abu bane mai sauƙi. Sannan babu makawa Cassandra za ta yi amfani da Junior ta muzguna mishi ta hanyar ɗaukeshi daga wajensa. Wani tunanine ya faɗo masa. Idan har zai samu wacce zai aura cikin sirri ba tareda Cassandra ta ji labari "ba, to zai iya samun damar cika umurnin Hajiya." "Kotu ta ɗaura musu aure da Cassandra, wacce zai aura kuma aure za su yi na musulunci. Na bayar-Na" "karɓa, cikin sauƙi a shafa Fatiha ba tareda an yi wata hayaniya ba. Then a hankali sai ya san yadda zai samu mafita daga auren Cassandra, ta yadda za su rabu kuma a bashi custody na riƙon ɗansa." Saudah ce ta fara zuwa masa lokacin da ya keɓe a office shi kaɗai bayan sun ƙarƙare meeting ɗinsu wanda fiye da rabin abinda aka yi a wajen bai sani ba. Ya girgiza kai saboda Saudah ba za ta taɓa yarda ta yi auren da babu hidima ba. Idan kuma har ta amince "to ba lallai Mommynta da sauran 'yan'uwanta su yarda ba. Ko lokacin da aka shirya aurenta da Jamal, ba" ƙaramin biki na gani na faɗa aka shirya ba. Sai kuma Allah bai nufa ba. "Sannan, auren Saudah na nufin ba zai taɓa yunƙurin rabuwa da ita ba, saboda Hajiya." Ba shi da aboki a garin nan. Sau tari abokanan Jamal ne ya ke ɗan fita da su idan har ya buƙaci shiga mutane. Bai san ina zai samo budurwa da zai convincing ta yarda ta aure shi ba. "Haka dai ya wuni a office, rabi aiki, rabi tunani." Bai dawo gida da wuri ba. Lokacin da ya shigo gidan sai ya samu Hajiya da Junior da Janan suna cin abincin dare. Ya gaishe da Hajiya sannan ya wuce sama. Ganin Cassandra yayi ta ajiye kwalin pizza a kan gado tana aiki a Laptop ɗinta. Ya fara ƙoƙarin cire blazer ɗinsa ko magana bai mata ba. Sai ta kalleshi ta ce masa wai ya nema mata "inda ake siyar da pizza mai daɗi, wannan da Janan ta kawo mata babu daɗi da ƙyar ta ci slize ɗaya." """When are you going back?"" Ya tambaya ba tareda ya amsa ƙorafinta ba." """Missing me already, ain't ya?"" Ta faɗa tana wani faɗaɗa murmushinta." Juyawa ya yi ya cigaba da cire kayansa bai kulata ba. Ƙarfe shaɗaya da rabi na dare da ya kwanta bayan ya gama bitar schedules ɗinsa na gobe sai ya ji "hannun Cassandra tana ƙoƙarin wasa da sandar girmansa. Ta cigaba da taƙalarsa har sai da ya biye mata. Duk da ya biye mata ɗin, amma jikinsa ne kawai ke goganta amma zuciyarsa da nitsuwarsa basa tareda ita. Ita kanta ta ji banbanci tsakanin jiya da yau. Sau ɗaya da suka yi sai ya lafke with the pretense cewa a gajiye yake, amma deep down sha'awarta ce baya yi." Wani abu ne ya faɗo masa. Akwai wacce ta driving daɗewar da ya yi yana gurzan Cassandra jiya. Ba wai "saboda ya jima bai taɓa mace bane. Ba wai saboda ya missing Cassandra bane. Duk da yana hana kansa irin wannan tunanin, amma macen da ta saka shi cikin matsananciyar sha'awa jiya ,ba Cassandra bace." Da safe da ya je gaida Hajiya bata kawo masa maganar da suka yi jiya ba. Maganar rabon kayan sadaka da ake duk Azumi ta fara masa. Ya ce mata ta rubuta masa budget idan ya dawo sai ya duba. "Yau Asabat, ba zai je office ba. JK Plaza zai je ya duba da kuma wasu gidajensu da ake ginawa." Ranan Monday Cassandra za ta koma London. Idan ta tafi zai samu nitsuwar zama ya nemawa kansa masalaha ta hanyar binciko yarinyar da ta dace da sharuɗɗan Hajiya. Ƙarfe biyar na yamma ya shigo gidan bayan ya gama duba duka sites ɗin da ake yi musu aiki. Dariyar Hajiya ya fara jiyowa tun kafin ya shiga falo. A tsaye ya samesu. Hajiya na yiwa yarinyar da ke riƙe da ƙatuwar leda magana. Kamar tafiya za ta yi amma maganar Hajiya ya tsaida ita. Kallo ɗaya ya mata ya ganeta. Ba ya tunanin zai iya mantawa da cute lips ɗinta nan kusa. Jalal ya gaishe da Hajiya zai wuce ta ce masa dan Allah ya kai mata Ziyada gida Direbanta baya nan. """Hajiya da kin barshi kawai, ina fita zan tsai da keke"" yarinyar ta faɗa tana avoiding idanunsa." """Haba Ziyadah, ai ba za a yi haka dani ba. Ba zan tasoki daga gida kuma na ce ki kama hanya ke kaɗai ba," "ga Magariba ta doso""" "Hajiya ta kalli Jalal ta ce ""please, ka sauke mini ita a gidansu""" Juyawa ya yi waje ba tareda ya ce komai ba. Yarinyar ta sake yiwa Hajiya godiya sannan ta biyoshi. "Ta wutsiyar ido ya hangota ta bayansa tana tafiya a hankali, kamar tana tsoron idan ta bishi zai saceta." "Matsoraciya ce, amma sai baki." "Idan har akwai wani dalili ma da zai sa ya saceta, to abu ɗaya ne. Those damn kissable lips." Shi ya fara shiga motar yayinda ta ja ta tsaya a bakin ƙofar gaba. Jiya Direbansa ya ɗauki uzuri ya tafi gida "wai za a yi bikin ƙannensa biyu, dan haka tun jiyan shi yake driving kansa." Tana tsaye bata buɗe ƙofar ba. Ya kalleta ta cikin window sai tura baki ta ke kamar akwai abinda ta ke faɗa. Probably part 2 na masifar ranan ta ke yi. Ganin bata shigo ba sai ya danna horn wannan ya sa ta yi saurin buɗe ƙofar ta shigo. "Yana gani ta zauna can nesa kusa da window, ko kallon inda yake ta ƙi yi." Ya ja motar suka fita daga compound ɗin. Sai da suka yi nisa bata yi magana ba sai ya ɗan juyo ya "tambayeta ina ne anguwarsu ""Ghetto"" ta faɗa tana kallon cikin idanunsa." "Ta ƙara da cewa ""ka ajiyeni a titi zan hau Keke na ƙarisa gida. Na san mota irin taka bata da ce da" "anguwar ghetto irin namu ba""" "Wani ɗan faint murmushin gefen baki ya yi. Hasashensa ya yi daidai, ɗazu practicing part 2 na masifar da" za ta masa take. Wato har yanzu bata manta da abinda ya faru a restaurant ba. """ Na farko umurnin Hajiya na ke cikawa. Na biyu idan ba zaki mini kwatancen unguwarku ba, zan juyar" "da motar nan na mayar da ke wajen Hajiya""" "Shiru ta yi tana tura baki, sai can ta faɗa masa sunan unguwarsu. Ta juyar da kanta gefe tana kallon titi," "sai ya ji ƙasa-ƙasa tana faɗin ""sannu ɗan Hajiya, mijin Baturiya, Mtssw""." """Da ni kike?""" "Juyowa ta yi da sauri ta ce ""ni ba da kai nake ba""" "Ya ɗan kalleta kaɗan bai ce komai ba, sannan ya maida hankalinsa kan tuƙin da ya ke yi..." CHAPTER EIGHTEEN ZEEY Yau Asabat ina wanki da safe kusan ƙarfe goma nema sai na ji wayata na ringing a ɗaki. Na je da sauri zan ɗauka sai na ga wayar ta katse. Hajiya Layla ke kirana. Na danna mata kira amma sai ta kashe kiran ta sake kirana. """Ziyadah, yanzu na ga wani video a page ɗinki. Ai Wallahi kin tayar mini da kwaɗayi sai ki san yadda za ki" "yi dani""" Ta faɗa bayan mun gaisa. Ni dai na san ban ɗaura sabon video ba. Akwai dai wani video na tallen garin ɗanwake dana yiwa wata kwanaki shine ta ce dan Allah za ta biyani na sake reposting mata a page ɗina tunda za a fara Azumi. To shine na sake sakawa yau da safe. Ba sabon video bane. To ko kuma dai videon ɗanwaken take nufi? """Ziyadah ai ki zo ki min ɗanwaken nan a gida na ci. Ya yi min kyau a ido""" "Ashe shi ɗinne. Na sa dariya nace ""Hajiya ai kin girmi ɗanwake""" """Ziyada ai ba za ki gane ba. Ni dana shekara Arba'in a turai ina gudun abincin gida, sai gashi na dawo" "Nigeria yanzu babu abinda na fi so sama da abincinmu na nan. Kin san shiyasa fa na sallami Chef ɗin daya ke mana girki da. Na sa aka kawo mini Hassana""" Ta ƙare da cewa idan bana komai wai na zo gida na yi mata ɗanwake. Na ce mata wanki nake amma na kusa gamawa idan na gama zan zo. Daga haka ta min sallama. "Ni garin ɗanwaken dana yi amfani da shi a videon ma ya jima da ƙarewa, amma dai zan duba a Kasuwa." Lissafina na zuwa gidan Faty yau sai dai kuma gobe. Dama cewa nake idan na gama wanki zan je gidanta "na faɗa mata halin dana ke ciki, dan ta tayani jaje. In ma akwai wani tsohon saurayinta mai suna Muhammad da za ta iya haɗani da shi sai na duba na gani ko za mu dace." Bayan na gama wanki sai na shirya na fita. A hanya na tsaya na sayi garin ɗanwake. Ban samu wanda "nake nema ɗinba, amma dai na samu wani mai kyau dana taɓa amfani da shi. Na wuce gidan Hajiya Layla." Tana ganina ta fara murna kamar irin ta ga ƙawarta ɗinnan. Gaskiya matar bata da girman kai. Har kitchen ta biyoni ina kwaɓa ɗanwake tana min hira. Ta tambayeni ya shirin Azumi na ce mata "Alhamdulillahi. Ta ce akwai abincin sadaka da wata mata ke musu duk Azumi tana tunanin ko ta bani aikin wannan karan, sai na ce mata gaskiya ba zan iya ba, saboda muna exams kuma idan na gama zan je Kaduna ziyara wajen Ummana. Ta ce mini babu komai." Ina cikin jefa ɗanwake bayan Hajiya ta tafi amsa waya a ɗaki sai ga wata Baturiya ta shigo kitchen ɗin. Da farko sai dana ɗan tsorata dan motsin mutum kawai na ji. Na ɗauka ma Hassana mai aikin Hajiya ce sai na ga wata farar Baturiya kyakykyawa tana sanye da wando blue jeans da farin v neck top. """Are you the new Maid?. Where's the other one?. You know what, just make me some tea, I'll be on the" "balcony"" ta juya ta bar kitchen ɗin tun ma kafin na bata amsa." Sai da ta tafi ma na ji haushin meyasa ban ce mata ni ba Maid bane. Da Hassana ta shigo kitchen ɗin sai na ce mata wata Baturiya ta shigo tana nemanta wai ta haɗa mata tea ta kai mata. """Ke bar jarabbiyar matar nan fa. Sai shegen jarabar shan tea. Yallaɓai idan zai sha koffee ko shayi shi da" "kansa yake shigowa kitchen ya haɗa abinsa. Da wuya kiga ya saka ni aiki. Amma wannan matarsar komai sai an mata. Idan an matan ma fa ɗan Tank you ɗin nan ba zata faɗa ba sai dai ta dinga ƙorafi ba a haɗa mata shayin da kyau ba. Shegiya.""" Na buɗe baki ina kallonta. Yallaɓai?. Jalal Maiyaƙi take nufi. Shine ke auren Baturiya. Awwo! Ashe "shiyasa ya ke cewa idea ɗina bai dace da restaurant ɗin da zai buɗe ba, saboda shi ya ƙi jinin baƙin fata a rayuwarsa. Tsabar bai yadda da matan Hausawa ba, da Baturiya ya ƙare. Lallai da zafinsa mijin Baturiya." Haka dai na ƙare aikin da zan yi. Dana gama ɗanwake na zubawa Hajiya. Tana ci tana santi wai duk randa take son cin ɗanwake ni zata kira na zo na mata saboda nawa ya fi na Hassana daɗi. Na yi murmushi kawai ina jinta. Yau ma na zo ne kawai saboda ina ganin girmanta kuma dama ina son abinda zai ɗauke min hankali daga cakwakiyar dana ke ciki. "Na ɗan jima a gidan, dan bayan mun gama cin ɗanwaken sai Hajiya ta fito da wasu kaya ta min kyautarsu." Har da wani babban Swiss Lace wai in kaiwa Kaka. Na yi mata godiya. Muka tsaya kallon wani film ɗin Marigayi Ibro a tashar Daɗin Kowa. Da aka gama sai na ce mata zan tafi. "Kwatsam sai ga Jalal ya zo, ta ce masa wai ya kaini gida." "Ina ganinsa wani haushinsa ya taso mini. Wato shi komai namu baya so, matar ma bai ga wacce ta mishi" a duk faɗin Arewacin Nigeria ba. Kai ko Bayarabiya Musulma bai gani ba sai Baturiya farar fata ce ta burgeshi. To Allah ya bamu haƙuri mu baƙaƙen fatan. "A mota tunda na kira shi da Ɗan Hajiya, mijin Baturiya ya jiyo ni, sai na juyar da fiskata gefe ina kallon titi." "Da muka iso unguwarmu na ce masa ba sai ya shiga lungunmu ba, amma ya dage wai aikin da Hajiya ta saka shi shine ya kaini har gida. Na ja ƙaramar tsaki a raina sannan na nuna masa inda zai shiga. Da muka bi ta kan wani kwatami sai na ɗan juyo na kalleshi ko zai yi ƙorafi sai na ga fiskarsa normal. Haka dai na dinga nuna masa hanya har muka iso ƙofar gidanmu." "Na yi masa godiya na wawuri ledar da Hajiya ta bani zan fita sai na ji ya ce ""ina so mu yi magana""" """Magana?, wace magana kuma?"" Na faɗa ina hararansa. Har yanzu ina jin haushinsa, haushin aurensa da" "Baturiya. To wai ma miye nawa a cikin kalar matar da ya aura ne?. Still, ina jin haushinsa, dan haka ni da shi babu wata magana a tsakaninmu. Ya katse min tunani da faɗin" """I just want us to talk. Ba faɗa ba. Just, REAL talk""" "Na ɗan sake hannun ƙofar na fuskance shi da kyau na ce ""Ina jinka. Amma ka yi sauri dan ka ga ana kiran" "Sallah""" """ gobe ki zo JK Plaza, 10AM sai mu yi maganar""" Na yi seƙeƙe ina kallonsa. Wannan ɗan Hajiyar ba ƙaramin ɗan renin wayo bane. Ya ce za mu yi magana. "Na bashi dama, yanzu kuma wai in zo in sameshi a plaza gobe. Sai kace zamansa nake yi." """Ni fa idan ba za ka yi maganarka yanzu ba, shikenan na yafe""" """Zeeyadah, right?"" Ya ɗaga mini gira." "Na ɗauka Hajiya Layla ce ta iya kiran sunana. To ga wanda ya fita. Kai, ba iya faɗin sunan bane." "Munafurcin da zuciyata ke shirin yi ne ya bani mamaki. From normal bugu da take, 'yar munafuka kawai" sai ta ƙara gudu daga jin wannan Jalal ɗin ya kira sunana. Idonmu ya haɗu briefly kafin na ɗauke idona da sauri dan kada na faɗa tuggun da zuciyata ke ƙoƙarin kitsa mini. Kuma fa ban ga laifinta ba tunda Mission ɗina yanzu shine OPERATION FIND BOYFRIEND. "Idan na shiga gida zan gargaɗeta, wannan ba candidate da za a duba bane. Dan haka ABORT MISSION," ABORT MISSION. """Yana da mahimmanci mu haɗu gobe""" """10AM, Please""" Ashe fa magana yake. Na ɗan yi gyaran murya ina ƙoƙarin processing me ya faɗa. Na buge da abort mission ban ji abinda ya faɗa da kyau ba. """Zan duba, idan na samu lokaci zaka ganni"" na ƙara masa da cewa ""Dan ka ganni a Ghetto ba yana nufin" "bani da abin yi bane. Ina da abubuwan yi masu yawa""" """Alright, Miss Ghetto. Sai gobe ko"" ya faɗa yana ƙoƙarin tada motarsa." Wato har da wani Miss Ghetto. To Wallahi Ɗan Hajiya zan kira shi nima. "Na buɗe ƙofar na juyo na ce ""To, Mr Ɗan Hajiya a gaida min Hajiya""" """Za ta ji"" ya amsa irin bai ji haushi ɗinnan ba." Na fita daga motar na banko masa ƙofa na yiyo gidanmu. """Wancan motar Alhaji Nafi'u ne?"" Na waiga da sauri dan ban lura akwai mutum a wajen ba. Baffa Zakari" "ne ke Alwalar sallar Magariba. Yana sanye da uniform ɗinsa, ina ga daga wajen aiki ya ke." """Ba shi bane"" na amsa masa tun ma kafin watarana ya ga motar Jalal ya ce zai masa maula." """Shine Saurayin naki?""" """Baba ba shi bane. Idan saurayina ya shigo gari zan kawo muku shi har nan ku gaisa"" daga haka na wuce" "shi, na shiga gida." JAYKAY "Daga gidansu Ziyada, sai Jalal ya tsaya a wani Masallaci ya yi sallar Magariba kafin ya wuce gida. Wani" nishaɗi ya ke ji a zuciyarsa da ya jima bai ji irinta ba. Da ya isa gida sai ya samu Hajiya da Junior suna cin abincin dare. Zama ya yi shima ya fara serving kansa. "Hajiya ta tambayeshi ko Ziyada ta isa gida lafiya, ya ce ta isa lafiya." Janan da Cassandra basa nan. Wai Janan ɗince ta kai Cassandra wajen da za ta samu abinci mai kyau. Ya "girgiza kai kawai. Lokacin da Chef ɗinsu yake nan, idan Cassandra ta zo gidan shi yake dafa mata duk" "abinda ta buƙata, saboda Internationally train Chef ne." Amma tunda Hajiya ta sallameshi ta kawo musu Hassana sai dukkansu suka fara adopting cin abincin Nigeria. Janan ce dai babu fancy restaurant ɗin da bata sani a Zaria ba. Ta kan iya hawa mota ta tafi Kaduna dan kawai ta je ta ci abinci ta dawo. Junior shi ya fi kowa saurin adjusting. In fact ranan da Jalal ya ga tuwon Semon da yaron ya ci a gabansa sai da ya yi ta mamaki. Hajiya ta koya yaron cin abinci mai nauyi kuma yaron yana jin daɗin hakan ba kaɗan ba. Bayan ya dawo daga sallar Isha sun jima suna lissafin budget ɗin Azumi da Hajiya. Ƙarfe goma ta wuce kafin ya baro ɗakinta. Har lokacin Janan da Cassandra ba su dawo ba. Ya shiga ɗaki ya cire kayansa ya yi wanka ya saka kayan bacci. Ƙarfe shaɗaya da kwata Cassandra ta buɗe ƙofa ta shigo. Warin giyar da ya ji ne ya saka shi kiran sunanta a fusace. """Maria! Are you drunk?""" """Relaxxxx mate! I'm not drunk"" ta yi tangal-tangal ta zo ta faɗa kan gado." Janan. Sunan da ya zo masa baki kenan. Ya tashi da sauri ya fita zai je ɗakin Janan amma sai ya ja ya tsaya jin muryan Hajiya tana masifa. Ya jiyo muryan Janan tana yiwa Hajiyar bayani. """Ni fa tun ƙarfe tara muka rabu da ita. Kawai ina shirin tahowa gida ta kirani wai in zo in ɗauketa bata" "san inda take ba. Shine na kira Amir, da ƙyar muka gane kwatancen wajen muka je muka ɗaukota""" """Me yasa ba ki kira shi mijin nata ya je ya ɗaukota ba. Janan na hanaki yawon banzan nan. Wallahi ki" "kiyayeni. Ki kiyayeni, Janan""" Juyawa ya yi da baya ya koma ɗakinsa dan idan Hajiya ta ganshi faɗan zai koma kansa. Yana shiga ɗaki "sai ya kira numbar Amir. Amir cousin ɗinsu ne. Abokin faɗan Janan. Lokacin da suka dawo Zaria shi ya koyawa Janan yawo. Ga shi dai ƙaninta ne dan za ta iya bashi 3yrs ma amma tafiyarsu ta zo ɗaya. A yi daɗi, a yi faɗa." Amir ya ce masa ai yanzu Hajiya ta fatatttakeshi daga gidan bayan sun kawo Cassandra gida. Da ya bashi "labarin inda suka samu Cassandra, sai da Jalal yayi mamakin yadda aka yi ta san wajen. Koda yake za ta iya searching google ta nemi inda ake nightlife a garin Zaria." Pillow ya ɗauka ya kwanta a couch dan ba zai iya kwana gado ɗaya da Cassandra tana warin giya ba. Minti biyu da kwanciya sai ya ji ya takura. Miƙewa ya yi ya zo ya buga bayan Cassandra da ƙarfi ya ce ta "je ta wanke jikinta. Ta buɗe ido tana masa tanɓele, haushi ya kama shi ya jawota da ƙarfi ya turata cikin banɗaki ya ce ta yi wanka. Ya zo ya cire duka zanin gadon da duvet da komai ya kwashesu ya fita. Laundry room na ƙasa. A hankali ya ke takawa kar a jiyo shi duk da yanzu ya ji shiru Hajiya ta gama yiwa Janan faɗa." Yana zuwa ɗakin wanki ya jibge kayan a ƙasa ya fito ya koma ɗaki har lokacin Cassandra bata fito daga "banɗaki ba. Haushi ya cika shi kawai ya ɗau wayarsa ya fita daga ɗakin ya tafi ɗakin Junior. Idan ma bacci ta yi a banɗakin ita ta sani, wannan bai dameshi ba." Junior ya jima da bacci. Haka ya squeezing jikinsa a gadon yaron ya kwanta yana tantamar ya kwana a wajen ne ko kuma ya tafi guest room a ƙasa ya je ya kwanta. Akwai ɗakin Jamal a sama. Amma tunda aka kwashe kayan ciki Hajiya ta sa aka rufe babu wanda ya sake shiga cikin ɗakin. Haka dai Jalal ya haƙura da sake fita ya kwanta kusa da ɗansa. Da Asuba da ya tashi sai ga shi ya tashi da "ciwon jiki. Ya dropping ƙasa, ya fara push-up saboda ya ɗan warware muscles ɗinsa." Lokacin da ya shiga ɗakinsa sai ya samu Cassandra a yashe akan gado daga ita sai towel. Ya girgiza kai ya wuce banɗaki dan ya yi alwala. Bayan ya dawo daga sallar Asuba da ya shiga gaida Hajiya abinda ta fara tambayarsa shine yaushe Cassy "za ta tafi. Ya ce mata gobe Monday. Ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce ""Ina so ka yiwa ƙanwarka magana. Jiya ita da Amir ƙarfe shaɗayan dare suka shigo gidan nan. Daga yanzu na saka doka, duk inda za ta je ƙarfe takwas na dare ya mata a gida. Wani batun fita shan ice cream da dare na cancel ɗinsa daga yau. Nan ba London bane. Yanzu mutane za su fara nuna mini yatsa suna faɗin ai ga 'yar Hajiya Layla nan tana yawon" "dare. Ka ja mata kunne."" Ta ɗan yi shiru, sai kuma ta sake cewa ""Maganar matarka ta je club bai shafeni" ba. Amma ni ban yiwa Janan tarbiyyan da za ta je neman 'yan giya a Club ba. Wannan ya zamo na farko "kuma na ƙarshe a gidan nan""." "Yet again, ta sake nuna masa illar auren Cassy." Haƙuri ya bata ya ce mata zai yiwa Janan magana. Ƙarfe tara da rabi na safe yana shirin fita Cassandra ta tsare shi ta fara bashi haƙurin abinda ta yi jiya. Wai ta masa alƙawarin ba za ta sake shan giya ba har ta bar Nigeria. """Suit yourself, Cassandra"" ya faɗa yana bangajeta ya fice daga ɗakin. Akwai abu mai mahimmanci dake" "gabansa, dan haka ba zai bari ta ɓata masa rai ba." Lokacin da ya shiga mota sai ya turawa Ziyada text yana mata tuni da ƙarfe goma ne fa haɗuwarsu. "Jalal yana tuƙi, amma jin kansa yake cikin wani nishaɗi." "Idan Allah ya taimakeshi, a yau ɗinnan zai samowa kansa irin matar da Hajiya ke so." CHAPTER NINETEEN ZEEY Uban wa ya ke min kiran sassafen nan ina cikin mafarki me daɗi?. Uban waye wannan da zai kirani safiyar Sunday ina cikin bacci mai daɗi?. """Ziyadatu ba wayarki ke ƙara ba?"" muryan Kaka yasa na buɗe idanuna na fara laluben wajen pillow zan" jawo wayar ashe wayar tana ƙasa. Maybe cikin bacci na bugota ta faɗi dan na san dai gefen Pillow nake ajiyeta. Na sa hannu na ɗaukota lokacin har ta gama ringing. Ina ganin sunan wanda ya kira na ji sauran baccin dake idanuna ya washe. Jalal ne ya kirani. JALAL MAIYAƘI. Kuma ba sassafiya bane kamar yadda nake tunani. Ƙarfe goma na safe har da minti goma. Yaushe na yi bacci har haka?. Na fara tariyo abinda ya faru daga Daren jiya zuwa yau. Jiya da dare ni da yaya Aminu mun jima muna chatting akan hukuncin da su Baffa Adamu suka yanke. Ba ni na faɗa masa ba. Magulmatan gidanmu ne suka faɗa masa. Nan an yi abu ranan Jummu'ah amma sai gashi Asabat shi da ya ke Yola har ya ji labari. Na san ba zai wuce waccar Mardiyyan bane ta faɗa masa. Hassada da kishi su za su yi ajalin yarinyar nan idan bata dena ba. Babu wata matsaya da muka cimma after hours da muka kwashe muna chatting akan maganar. Wai shi "lallai dai mu dawo da maganarmu, shine Muhammad ɗin da zan gabatarwa su Baffa Lawalli. Wai idan muka dawo za mu san yadda za mu yi da maganar rashin dacewar Genotype ɗinmu. Ni dai jinsa kawai nake yi saboda na riga na haƙura da shi, na kulle soyayyarsa a cikin box na jefata can tsakiyar tekun Maliya. Key ɗin box ɗin kuma can tsaunin mount Everest na jefata. Kun ga kuwa babu yiwuwar soyayyar za ta dawo." "Akwai burbuɗin soyayyar babu ƙarya, amma tasirinsa ba kamar na da bane. Musamman a 'yan kwanaki" biyun nan da zuciyata ke daka tsalle a duk abinda ya shafi wani dogon mutum wanda sunansa ya fara da J. "Yanzu ma da nake ƙoƙarin kiran numbarsa, my heart is still daka tsalle a ƙirjina." """A Ghetto babu agogo ne?"" Abinda ya faɗa kenan yana picking call ɗin." "Sai dana samu zuciyata ta ɗan daidaita, kafin na bashi amsa." """Batirin agogon ne ya samu matsala, amma nan da minti 30 zan iso""" """20""" """Ka ce?""" """Ki iso, in 20 minutes""" Kafin na yi magana har ya kashe wayar. Ka ji gadara. """20. Ki iso in 20 minutes"" na kwaikwayi muryarsa." """Ke da wa da safen nan?""" """Kaks, wai fa ɗan Hajiyan nan ne""" """Wacce ta baki kaya jiya?""" """Ita fa. Ni ban san me yake so ba. Wai cewa ya yi in sameshi a Plazarsu yau da safe akwai maganar da za" "mu yi"" ina maganar ina brushing bakina. Dan yau babu abin da nayi bayan sallar Asuba sai bacci, kiran Jalal ne ya tasheni. Ina gama wayar kuwa na zari brush da toothpaste a jakata na haɗa na fara brush a ƙofar ɗaki." """Ko dai sonki yake?""" """Kaka Altine Mai Tuwo, sona kuma!""" """To wannan alkhairin da Hajiyarsa take miki, ga shi ya ce za ku yi magana ai zancen gizo ba zai wuce ƙoƙi" "ba. Ina ga sonki yake, Ziyadatu""" Na ma kasa magana. Kawai na je na furzar da kumfan da ke bakina na wanke bakina da ruwa na dawo bakin ɗakin. """Kaks, wa ya gaya miki sona yake. Shi fa baya harka da 'yan ƙauye da Talawaka. Matarsa fa Baturiya ce." "Baturiya, Kaka. Farar fata, gashinta har gadon baya, ga dogon hanci. Ga turanci kamar marigayiya Sarauniyar Ingila""" """To miye a ciki. Shi ba mijin mata huɗu bane""" """Kaks magana kike. Barin miki gwari-gwari ki gane. Jalal Maiyaƙi ɗan Hajiya Layla, yana da mata Baturiya." "Kuma kin san Turawa auren zobe suke, ba a musu kishiya""." "Kaka ta ɗan yi shiru, sai kuma ta ce ""To, Allah ya sa mu ji alkhairi""" """Kar ma ki kawo maganar soyayya Kaka, ni na san maganar aiki a Restaurant ɗinsa zai mini. Kuma ni na" "riga na rantse ba zan masa aiki ba sai dai idan zai tsugunna ya bani haƙuri""" Ƙarshen maganata fa ba gaskiya bane. Ban rantse ba. Kawai dai na yita cika baki akan ko Jalal ya roƙeni ya ce in dawo in masa aiki a restaurant ɗinsa ba zan yi ba. A gurguje na je na yi wanka. Abin mamaki saboda Jalal sai gashi ina wanka da ruwan sanyi. Ni tun tasowata duk min zafi sai na yi wanka da ruwan zafi koda lum-lum ne haka. Sai ga shi yau dan ina sauri zan je in yi magana da Jalal har ina wanka da ruwan Rijiya mai sanyi. Duk laifin Kaka ne da bata saka min ruwan zafi ba. Koda yake sanin cewa ba zan je makaranta ba yasa bata "ɗaura ba, akan idan na tashi sai na ɗaura da kaina." Na shiga ɗaki a gurguje na shafa mai a hannu da ƙafa. Sai gani again ina ɗan murza powder a fiskata. Ba dan Jalal na shafa ba. Na shafa ne ko zan haɗu da wani saurayi mai suna Muhammad a hanya. Shi da yake da farar Baturiya babu abinda zai sa ya kalleni har ya ji na burge shi. Dan haka ba a shi na shafawa Powder ba. Yes. Da ɗan lips gloss da yake sheƙi. Yes. Da ɗan zana baƙi a ƙasan lips ɗina. Yes. Da ɗan fesa extra body spray fiye da yadda na saba fesawa idan zan fita. Yes. Duka wannan ba dan Jalal bane. Gara ku sani. "Minti 20 ɗin da ya faɗa ma ban ko fito daga ɗaki ba, balle har na isa JK Plaza." "Da wanka, da saka kaya, da powder kaɗan dana shafa kusan 40mins ya tafi." Na fito da sauri ina yiwa Kaka sai anjima. "Sai buga sauri nake ina so na kai bakin titi na tari Keke, kai machine ma zan hau dan zai fi sauri." Horn ɗin dana ji a bayana ya sa na juyo a fusace dan kamar mai motan bina ya ke. Na hangame baki lokacin dana ga irin motar data kawoni gida jiyane. Yana sauke glass ƙasa na hango shi zaune hannunsa akan steering yana kallon hanya ko inda nake bai duba ba. Nufinsa na shiga motar. Ai bai ce na shiga ba. "What if ba shi ɗin bane wani ne mai kama da shi. No, shi ɗinne." To yaushe ya zo ƙofar gidanmu?. Was it bayan ya jira 20mins bai ganni bane. Ko kuma dai tun sanda ya kirani ina bacci yake ƙofar gidanmu?. "Juyowar da ya yi sai na ji wani bugum!. Ba dutse na taka ba, zuciyata ne ta daka tsalle. Again, saboda" idanun Jalal. Da ido ya min nuni dana shiga motar. Kafin na cewa hannuna kada ta buɗe ƙofar ai bai min magana da "baki ba, tuni ta buɗe. Sai kawai na shiga, na zauna tunda da alama duka gabban jikina munafukai ne. Daga ganin Jalal sun fara malfunctioning. Jiya zuciyata ce ta yi munafurcinta, yau kuma hannuna. Waya san mi sauran gaɓɓan nawa za su yi kafin mu kai JK Plaza." Ina cikin wannan tunanin kuwa sai cikina ya ɗau ƙugi. Subhanallahi! gaɓɓaina sun fara malfuctioning kamar wanda aka ƙerosu daga China. "Yes, ban karya ba na fito. To shine sai ta tona min asiri a cikin motar Jalal. Na sa handbag ɗina na danne" cikina ina ɗan muskutawa kaɗan dan kar ya gane. "Tunda na shiga motar bai min magana ba. Nima ban masa ba. Actually ya kamata na gaishe shi, amma" ban yi ba. Laifinsa ne ai da ya zo mini surprise babu shiri. Ina tunanin za mu je Plaza sai na ga ya ja ya tsaya a wani ƙaramin restaurant a bakin titi. Na san "restaurant ɗin. Na wata Bayarabiya ce, Anty Bose. Ta iya Amala sosai. Na taɓa zuwa neman aiki a wajenta da daɗewa ta ce bata buƙatar 'yar aiki a lokacin. Duk da dai na ji haushi amma ban ga laifinta ba. A lokacin wajen bai yi girma kaman yanzu ba. Ba zan manta ba ita da mijinta da ƙannenta biyu suke aiki a wajen. Daga baya da mutane suka gane Amalanta da daɗi sai aka fara mata tururuwa, daga nan kasuwarsu ta buɗe. Yanzu tana da ma'aikata za su yi shida." Nima idan kwaɗayin Amalan Yarabawa ya kamani ina zuwa siya a wajen dan babu nisa da unguwarmu. "Idan ban ci a wajenta ba, to zan ci a restaurant ɗin Anty Shukura. Ita kuma muna da ɗan nisa da ita shiyasa ba koyaushe nake zuwa ba." "Ganin ya yi parking bai ce mini komai ba. Sai na ce "" Amala za ka siya?""." "Na san suna siyarda wasu abincin a wajen, amma Amalarsu ce ta fi suna. Dan ba Yarabawa kaɗai ke" tururuwan cin Amala a wajen ba. Cikina ya sake wani ƙugi mai ƙarfi. Wannan karan jakar dana sa bai hana sautin ƙugin fitowa ba. "Ya ɗan kalleni ya ce ""Market survey""" """Market survey?"" Na maimaita. Na san market survey. Amma yaushe na ce masa zan yi aiki a restaurant" ɗinsa balle ya fito dani market survey. "Kafin na gama lissafina har ya buɗe ƙofa ya fita. Sai nima na buɗe na fito, dan ko ba komai ina jin yunwa" kuma sai na ci Amala kafin na tafi. Aiki a restaurant ɗin Yarabawa ya sa na koyi cin Amala. Lokacin da nake aiki a Zikks Foods sai in yita "mamakin baƙin tuwon Yarabawan nan, amma sau ɗaya dana taɓa na ji daɗinsa, ban sake mamaki ba. Zan iya cewa na fi son shi akan tuwon Semo. So, market survey or no market survey. Yau sai na ci Amalan Anty Bose." Kusa da kujerar da ya zauna nima na zauna. Staff ɗinsu tana tambayarsa mi zai ci sai ya nunani da yatsa. "Ai tuni na ce mata Amala biyu da miyar Ewedu, sai goat meat 2, Ponmo 1, da kifi 1." "Tana tafiya na saci kallon Jalal dake ɗan nazartan wajen da muke. Ƙarfe shaɗaya da wani abu ne, wajen" bai fara cika ba. Da mun zo ƙarfe biyu zuwa yamma da ya ga yadda ake turereniya a wajen nan. Aka kawo mini abincina na wanke hannu a ƙasan table na fara ci. Amalan na sauka ina jin kaina a cloud 9. Da zafi-zafinsa haka na dinga tura loma ina ci ina suɗe hannu. Shi kuwa Jalal tambayar yarinyar da ta kawo min abinci yayi menene a Menu ɗinsu dan basu da shi a rubuce irin na restaurant ɗin 'yan gayu. Yarinyar ta fara lissafo masa abubuwan da suke siyarwa. Dana gama cin abinci sai na ga ya miƙe ya je ya biya kuɗi. Nima na miƙe na bi bayansa muka fita. """Ina so muje local restaurant kamar uku haka mu yi survey, amma abincin da kika ci a wajen nan ya" "wadatar, ba sai mun je wani wajen ba""." Ya wadatar?. A malmalan Amala biyun?. Ba fa manya bane. Na san ya suke ɗaurin Amalansu shiyasa na ce a bani biyu. Koma dai yanene dai na ci na ƙoshi. Atleast yanzu hankalina ya dawo jikina zan samu damar gaya masa magana da kyau idan ya ce zai rena mini hankali. Lokacin da muka shiga ɓangaren restaurant a JK Plaza sai na ga Laptop ɗinsa a kunne a wajen. Da alama nan ya fara zuwa kafin ya zo gidanmu ɗaukana. "Dama sai dana faɗawa Kaka, maganar restaurant ya sa yake nemana ba wai wani zancen soyayya ba." "Idan ma soyayya ne, ni zan yi soyayya da shi ne?. Mutumin da ya tsallake Nigeria ya tafi England ya je ya" "auro mata, har abun sone. Yadda ya ke ƙin baƙar fata haka nima nake ƙinsa." "Duk da dai ina cikin operation neman Saurayi, wannan ba Saurayin da zan sa shi a potential candidate" "bane. Wannan mijin Baturiya ne. Wannan ɗan Hajiya Layla ne. Wannan, Jalal Maiyaƙi ne." """The last time da muka yi magana a nan, kin faɗa mini irin restaurant ɗin da za ki buɗe na abincin" "gargajiya ne""" "Ya ɗan ɗaga giransa ɗaya ya ce ""Enlighten me, miye banbancin restaurant ɗin da za ki buɗe da kuma" "wanda kika ci Amala biyu a ciki ɗazu?""" "Da farko yadda yake ɗaga gira ɗaya idan yana magana is sooooo sexy. No, ba sexy zan faɗa ba. Ina nufin" "yana ɗan masa kyau kaɗan. Na biyu, shine tun ba a je ko'ina ba har ya fara mini gorin Amala biyun da ya siya min. Eh ɗin. Na ci Amala biyun. Cikinsa ko cikina?" "Na uku, sai na yi murmushi na ce masa ""Mr Ɗan Hajiya Mijin Baturiya, nagode da abincin da ka siya min." "Amma ba sai ka faɗa masu gadi sun ji ka biya min kuɗin Amala biyun dana ci ba. Ka san dai zan iya biyawa kaina tunda kaga na ci abinci a wajen. Ni da kake gani regular customer ɗinsu ce ehe""" """Sannan, magana ka ce za mu yi shiyasa na zo nan. Ban zo nan dan na maka bayanin yadda zan buɗe" "restaurant ɗina ba. Na riga na faɗa maka ka riƙe fancy restaurant ɗinka, nima in riƙe nawa a Ghetto." "Dan haka babu sauran bayanin da zan maka yanzu""" "Ya ɗan yi shiru yana kallona, sai kuma ya ɗau wayarsa ya fara typing wani abu. Da ya ɗago sai yace ""Idan" "zan baki wannan wajen. How do you intend to run it?""" Idan zai bani wannan restaurant da muke ciki yake nufi?. Ba ya ce idea ta bata dace da wajen bane. "Kafin na bashi amsa sai ya sake cewa ""Ina da proposal, Zeeyadah. Zan baki wannan wajen, ki yi yadda" "kike so. Tuwo, Ɗanwake, whatever kike so ki girka a nan, I will allow it""" Na buɗe baki ina kallonsa da mamaki. Jalal ɗin da muka yi kaca-kaca da shi a nan akan ya kushe idea ɗina shine yanzu yake cewa zai bari na riƙe restaurant ɗinsa. To ko dai Hajiya ne ta masa magana?. """Ni fa ban ce maka ina son aiki a nan ba. Na faɗa maka na fasa. Ka riƙe kayanka ka yi yadda kake so da" "shi. Allah zai bamu kuɗi muma mu buɗe irin namu, ehe""" Ba zan bari ya tsole min ido da wani restaurant ɗinsa na 'yan ƙarya ba. """Idan kika amince da proposal ɗina. Bayan shekara ɗaya wannan wajen zai zama naki, za ki zama sole" "owner na wannan wajen"" ya wani buɗe hannayensa irin na ga girman wajen ɗinnan." """Ban gane ba?"" Na tambaya dan bayaninsa bai kama hankalina ba" """Cewa za ki yi minene proposal ɗina?"" Ya faɗa yana mini wani kallo mai ma'ana biyu." """Menene proposal ɗinka?"" Na tambaya nima ina kallonsa." Ajiye hannayensa ya yi akan table ya zuba mini idanunsa masu ƙyallin nan. A dai-dai wannan lokaci uwar munafukai ta fara munafurcinta. Zuciyar ZIYADA dai ta samu matsala. "Kafin na iya janye idanuna daga narkewan idanunsa cikin nawa sai na ji ya ce ""MARRY ME, ZEEYADAH""" "Ashe ban sani ba, kunnena ma ta bi ruɗin zuciya dan kuwa wasu kalmomi uku ta kawo min. Ni na san ba" abinda Jalal ya faɗa ba kenan. Munafurci ne kawai. Miye kuma Marry me Zeeyadah???. CHAPTER TWENTY ZEEY Mutumin nan ya sha BURKUTU. JALAL MAIYAƘI ya sha Burkutu. Irin Burkutun dana ga ana sha a Kaduna lokacin da muka je Unguwarsu ƙawata Dorcas Manzo da muka yi Culinary School da ita. "Yo idan ba Burkutu ya sha ba wani irin proposal ne wai 'Marry me, Zeeyadah' sai ka ce a film." "Tsabar mamaki sai na kasa magana ma. Yo ko Hajiyarsa ce ta ce ya aureni, kawai sai ya zo ya min tayin" aure da alƙawarin zai bani Restaurant. Restaurant ɗin a matsayin sadaki ne? ko a matsayin kyautar aure?. """Abinda na faɗa ya baki mamaki ko?. The whole Miss Ghetto ta kasa magana tun ɗazu"" ya faɗa yana ɗan" murmushin gefen baki. "Wait, ko dai wani ya faɗa masa iyayena sun bani wa'adin kawo miji ne?. To idan ba haka ba, wannan" renin hankalin daga ina. "Na gyara zamana na ce ""Mr Jalal, ni ba 'yar maula bace. Yes. Gidanmu akwai Talauci, amma mu ba" "mabarata bane. Dan haka, maganar wai in aureka saboda za ka bani kyautan restaurant ba mai yiwuwa bane. Talaucina bai kai kyautarka ya tsole min ido ba. Ina da abin yi, kuma ina samun rufin asiri, Alhamdulillah"" na miƙe tsaye na ɗau jakata na ce masa ""idan ka je gida, ka gaida min Hajiya""" "Na juya zan tafi raina a ɓace sai na ji ya ce ""your Cousin, ya faɗa mini ba ki da Saurayi""" "Na juyo da sauri ina kallonsa. Wani cousin ɗin nawa yake nufi?. Muna da yara a gidanmu dayawa, ni" kaina ban san lissafinsu ba. 'Ya'yan Baffa Mamman kawai na sani saboda su huɗu ne basu da yawa. Ganin ya samu attention ɗina sai ya taso daga inda ya ke zaune ya fara takowa a hnakali har ya iso inda "nake tsaye. Bugun ƙirjina ya ƙaru, ƙanshin turarensa ya sake shiga mini hanci na ji ilahirin jikina ya fara yin wani sanyi laƙwas. Taku ɗaya ya bari tsakaninmu. Wannan ne karo na farko da muka tsaya, kusa da kusa har haka." Na sauke idanuna saboda ba zan iya juran kallonsa ba. Akwai wani abu a idanunsa da ke barazanar narkar mini da duk wani matakan tsaron da na yiwa zuciyata. "Na yi ƙarfin hali na tattaro dukkan ƙarfina na saita nitsuwata na ce ""wa ya faɗa maka bani da Saurayi?." "Ina da Saurayi mana. Ina da Samari dayawa ma"" na ƙare da faɗin ""Ai ba duka maza bane irinka da idanunsu ya rufe da son Turawa""" "Wani slight murmushin gefen baki ya yi sannan ya ce ""an faɗa mini kina da wani Alhaji Rabi'u. Amma" "yanzu ba kya son shi, ko ya zo ba kya fita sai an saki dole""" Na ƙwalalo ido waje. Waye ya faɗa masa maganar nan?. Ko dai Yakubun Baffa Lawalli ne?. Amma idan shine yau sai na ci ubansa idan na koma gida. """Ni bani da Saurayi Alhaji Rabi'u. Ban san a ina ka ji wannan gulmar ba""" """OK. Tell me, Alhaji waye yake zuwa wajenki da?""" Zuciyata ya hasala da tambayarsa. Ni fa ko tarihin rayuwata aka ce na bayar ba zan saka sunan Alhaji "Nafi'u a matsayin Saurayina ba. A tarihin rayuwata ma kaf mutum ɗaya zan ce mun yi soyayyar da za a kira soyayya. Duk wani bayan yaya Aminu ko dai temporary ne, ko kuma waɗanda suka zo nake koransu. Alhaji Nafi'u kuma shigowarsa rayuwata ƙaddara ce da ta riga fata. Da zan iya, dana goge shi gaba ɗaya daga tarihin rayuwata." "Na gyara tsayuwata na ce ""Mr Jalal. Ina da Saurayi, bani da Saurayi, bai shafeka ba. Idan ma gulmar da" "yaran gidanmu suka maka yasa ka faɗa min maganar banza ɗazu to kuwa ba za ka ci nasara akaina ba. Idan kuma dan ka ga ina zuwa gidanku Hajiyarka tana yi min kyauta yasa kake mini kallon yarinyar da za ka yaudara to ni ba irin yarinyar da kake tunani bane. I am an adult, na san ciwon kaina. Ina da sana'a, kuma ina karatu, ni ba jahila bace"" na ɗan tsaya na ja hanci saboda kuka ne ke shirin taho mini. Ban san me yasa ba amma ban yarda da shi ba a wannan lokaci. Yana da mata Baturiya zai zo yace in aureshi saboda zai bani restaurant. Restaurant ɗin ya ci kutumarsa. 'Yan iskan maza sun yi yawa a gari. Wataƙila shima Jalal ɗin yana cikinsu ne. Haka Alhaji Nafi'u ya shigo rayuwata daga taimako ya fara min alkhairi kamar dan Allah yake. Da ya ga na sake da shi sai ya fara fito da ainihin manufarsa." Idan ma labari aka faɗa masa akan cewa 'yan Ghetto suna da son kuɗi to ni Ziyada ba kuɗin banza nake nema ba. Yanzu ma a lissafina abinda ya rage kuɗin da nake tarawa na buɗe restaurant kaɗan ya rage ya cikata dubu ɗari biyar. A hankali kuma Insha Allahu kuɗin za su haɗu. Ban san na fara hawaye ba sai da na ga ya miƙo min handkerchief yana cewa mu koma na zauna. Ban musa masa ba na koma na zauna a inda na tashi. Ba zan iya fita a haka ba. Ban san me yasa nake kuka ba. Ban san me yasa na yi kuka a gabansa ba. """Please, stop crying"" ya faɗa a hankali. Na ɗan ɗago na kalleshi, sai kuma na sunkuyar da kaina." """I, I..."" sai ya yi shiru." "Muka zauna a haka babu wanda ya yi magana. After like kamar 5 minutes da yin shirun sai ya ce ""Hajiya" "tana so na ƙara aure. Bata son aurena da Cassandra""" Na ɗan ɗago na kalleshi. Wato sunan matar tasa Cassandra. To ni ina ruwana. Dama wacce uwar arziƙi ce za ta so ya auro mata Baturiya wacce ba addininsu ɗaya ba. Irin wannan auren ai cike yake da ƙalubale dama. """Tana so na auri, Musulma, kuma Bahaushiya, 'yar Nigeria"" ya ɗan yi shiru yana kallona." Wannan karan sai da ya bari idanunmu suka haɗu sannan ya ce """She likes you. Ina ganin za ta ji daɗi sosai idan na aureki, Zeeyadah""" Na yi shiru ina tsarge kalamansa. Hajiyarsa bata son matarsa. Hajiyarsa tana so ya auri Musulma Bahaushiya. "Sannan Hajiyarsa tana sona, za ta ji daɗi idan ya aureni." "A dunƙule dai proposal ɗinsa shine, yana so ya aureni saboda Hajiyarsa. Ni kuma zai bani restaurant a" "matsayin ladan amincewa da aurensa da zan yi, kamar Business. Dama business ana yi ne dan a samu riba. Mai siye zai bada kuɗi a bashi abinda ya ke so. Shima wanda ya siyar zai karɓi kuɗi ya bayar da abunda ake buƙata dan ya ci ribar kasuwanci." GIVE and TAKE. Shi yana so ya farantawa Hajiyarsa rai. Ni kuma ya san ina son buɗe restaurant. """Ya kamata a ce na yi miki wannan bayanin ne kafin na proposing miki maganar aure da kuma restaurant." "Ofcourse auren zai iya kasancewa na lokaci kaɗan idan har ba kya son auren ya jima. Just zuwa lokacin da zan samu full custody na ɗana""" "Wannan karan kalamansa sun fi kama da alfarma ya ke so na masa, ba wai na amince da aurensa dan zai" bani kyautan restaurant ba. Maganarsa abun dubawa ne tunda nima ina danawa wa'adin da aka ɗiba mini. Amma dai ba zan bari ya sani ba balle har ya ga ai nima ina cikin matsala kuma ina buƙatarsa. Ba zan iya yanke hukunci yanzu ba har sai na yi shawara. """Ka bani lokaci, zan yi tunani akai"" na faɗa masa haka tareda miƙa masa handkerchief ɗinsa dan yanzu" kam kukan nawa ya tsaya babu sauran hawaye. Kin karɓa yayi. Hakan ya sa na saka a jaka na ce masa zan je na wanke idan muka sake haɗuwa zan bashi abinsa. Bai ce komai ba har sai dana tashi. Ya "tambayeni zuwa yaushe zan bashi amsa? Na ɗan yi shiru sai kuma na tuna za a fara Azumi gobe ko jibi," sai na ce masa bayan Azumi. Kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru. Jin bai ce komai ba sai na juya na fita daga restaurant ɗin. Na fice ma daga Plazar da sauri zuciyata cike da mix feelings na maganganun da Jalal ya faɗa mini. "Sai dana tsare Keke sai na rasa ina ma zan je, gidanmu zan koma? Ko kuma in je gidan Faty?..." JAYKAY It breaks him ganinta tana hawaye. Bai yi tunanin abinda ya faɗa zai ɓata mata rai ba. A tunaninsa tana da son kuɗi and maybe tunda tana da burin buɗe restaurant idan ya mata alƙawarin zai bata restaurant za ta yarda da buƙatansa. He was so excited ya samu yarinyar da ta dace da umurnin Hajiya da har ya manta bai zauna ya tsara ya za a yi ya convincing ɗinta ta amince da shi ba. Ya ɗauka komai zai zo masa da sauƙi. Ashe babu sauƙi. Ƙarfe goma saura ya shigo restaurant ɗin. Lokacin da ya ga goma ta wuce Ziyada bata zo ba shine ya kira numbarta bata ɗauka ba. Data sake kiransa kuma daga muryarta sai ya fahimci kamar ma daga bacci ta tashi. Bai iya jira ba shi yasa kawai ya ce gara ya je gidansu ya je ya ɗaukota and maybe su ɗan leƙa wasu restaurant su yi market survey. Lokacin da ya parking motarsa ɗan nesa da gidansu bai kirata ba. Yana so ya ga surprise fiskarta idan ta fito ta ganshi. Cikin yaran da suke wucewa suna gulmar motarsa ne wani ya zo ta wajen glass yana ƙwanƙwasa masa. Yaron ba zai wuce 11-12 ba haka dan ya ɗan fi sauran wayo. Yaron na ganin ya sauke glass sai ya zabura zai gudu shine Jalal ya kira shi. Yaron yace masa sunansa Yakubu. Wai shi ƙanin Ziyada ne. Adda Ziya kamar yadda yaron ke kiranta. Da ke Yakubu akwai surutu sai ya faɗa masa wai musu suke yi akan motar Jalal ita ce motar da ta kawowa Adda Ziyansu nama kwanaki. Ashe suna nan ranan da Direbansa ya kawowa Ziyada nama. Yakubu ya tambayi Jalal ko shi saurayin Adda Ziyan su ne?. Jalal sai ya bugi cikinsa da tambayar ko an yiwa Ziyada miji ne?. Shikenan yaron ya ɓarke bakinsa ya fara bashi labarin abinda ya tambayeshi da abinda bai tambayeshi ba. Da ya ga surutun yaron ya yi yawa kuma sauran yaran ma duka sun zo sun yanyame masa mota kawai sai "ya sallamesu, ya bawa kowannensu ɗari biyar biyar. Suka tafi sai tsalle suke suna murna. Ba su jima da tafiya bama ya hangota ta fito sai sauri take." Lokacin da suka je restaurant ya ganta tana cin Amala. He finds her cute and funny. Bata pretending masa kamar yadda wasu mata ke yi ba. And a yadda ya ga ta cinye abincin tas har da suɗe hannu kafin ta wanke hannunta ya sa. ta ji daɗin abincin sosai. "Ya yi mamakin yawan abincin da aka kawo mata, kuma sai ya ga ta cinye. Shi kam ba zai iya cinyewa ba," "ba wai dan yana dieting ko wani abu ba. Tun asali shi ba mai cin abinci sosai bane. Shi abinci a wajensa ci ake saboda kore yunwa ba wai dan wani abu ba. Shi yasa ma bashi da favourite food. Bai cika son abincin mai nauyi ba, ko zai ci sai dai kaɗan." Da Jamal na nan zai so ganin Ziyada. Shima akwai ci. Kuma yana son tuwo sosai. Hajiya a sama ta fara "son abincin gargajiya, amma shi Jamal tun tasowarsu ya fi ƙaunar abincin Nigeria akan na Turawa. Maybe saboda shi ya fi zama a Nigeria ne. Maybe kuma saboda tun suna yara idan suka zo Nigeria yana shiga cikin cousins ɗinsu su yita up and down tare. Lokacin da suke London Jamal baya cin abinci a waje idan ba na African Restaurants ba. Sau tari za ka ga ya yi tafiya me nisa wai ya ji labarin inda ake siyar da tuwo mai daɗi kamar na Nigeria." Jalal bai bar restaurant ɗin ba bayan Ziyada ta tafi. Zama ya yi ya kunna wayarsa ya shiga shafinta a Instagram ya fara kallon videos ɗinta a nitse. Ya scrolling ya je har farko-farkon videos ɗin da ta fara ɗaurawa. Wanda ya gani ranan ashe videonta na shekarun baya ne. Yanzu quality na videos ɗinta ya ƙaru duba da cewa wayar da ya lura tana riƙewa Android ce babba. Resilience ɗin yarinyar ne ya sake burgeshi bayan ya gama kallon. Ashe ta jima tana yin food content. "Perception ɗinsa akanta sai ya fara chanjawa. Yes, 'yar Ghetto ce. Amma kuma she is very hardworking and resilient. Kuma tana da wayewar da ta fi ta gidan data fito." Wani daga cikin masu gadin Plazar ne ya shigo ya ce masa ana kiran sallar Azahar. Bai san har time ya tafi "haka ba. Ya tattare laptop da sauran kayansa ya bar wajen. A cikin zuciyarsa yana fatan Ziyada ta accepting proposal ɗinsa. Yanzu da ya mata sabon fahimta, sai yake ganin ko ba dan Hajiya ba, zai so ya samu damar shiga rayuwarta. Maybe saboda business. Maybe kuma saboda wani abu mai ƙarfi. Something strong, Something more..." CHAPTER TWENTY ONE ZEEY Yau zamu rubuta exams na ƙarshe. Exam a cikin Azumi babu daɗi. Gashi dan iskanci da rana suka saka mana exam ɗin. "Na yiwa Faty alƙawarin daga school gidanta za mu wuce, wai tana gayyatana Iftar a gidanta. Actually," "cewa ta yi dole sai na je saboda tunda aka yi aurenta ban je gidanta ba. Ranan Sundayn da muka yi magana da Jalal na so na wuce gidanta dan in faɗa mata abinda su Baffa Lawalli suka yanke, da kuma tayin da Jalal ya min. Amma sai na ji ba zan iya zuwa gidanta a lokacin har sai zuciyata ta yi sanyi." Tun daga lokacin kuwa aka shiga Azumi na fara content ɗin Azumi ga kuma karatun exams. "Tare muka fito daga exam hall ɗin ni da Faty gaba ɗaya mun yi wuru-wuru dan exam ɗin bata yi daɗi ba," ga kuma Azumi. Muka tsare keke muka wuce gidanta. Ɗan watsa ruwa na yi saboda zafi na yi sallar La'asar sannan na tambayeta me za a dafa. Ta ce mini "itama bata sani ba. Wai na shiga kitchen ɗin na duba kayan miyan da take da shi sai na zaɓi abinda zan dafa mana. Ta haɗa da cewa wai wani abokin mijinta zai zo shan ruwa gidan, na mana abinci mai daɗi." Idan na biye mata ba za mu yi aikin da wuri ba sai na tashi na shiga kitchen ɗin. Na buɗe fridge ɗinta dan naga abinda ta ke da shi a ƙasa. Ƙarshe da ta ce min shinkafa da miya ta yi jiya sai na ce bari a yi doya da ƙwai da kuma jollof ɗin spaghetti. Doyar na ɗauko na fara ferewa ita kuma tana zaune a ƙasa ta baje tana danna waya. Anya ba ciki gareta "ba, wannan rakin." Ina cikin aiki na fara bata labarin abinda ya faru tsakanina da Alhaji Nafi'u da kuma abinda su Baffa Adamu suka yanke. """Wayyo! Bestie. Shine ba ki faɗa min ba tun ranan?""" """To yaushe ma muka haɗu""" """Ai ko a waya sai ki bani gist ɗinnan. Yanzu ya za ki yi?. Ko yaya Aminunki za ki gabatar musu?""" """Bestie ki ji ki fa. Yaya Aminu kamar ya. Kin san fa komai akan rabuwarmu""" """To na sani ko za ki aureshi sai ku haƙura da haihuwa""" """Hmm! Kema dai zancen kike so""" "Can ta ce ""ba akwai wani abokin Munir ɗina da ya ce yana sonki ba. Duk sanda ya zo gidan nan sai ya min" "zancenki. Ya ce wai har yanzu kin ƙi bashi dama ya zo hira gidanku""" """Yanzu ke sai ki ce na auri Bashir?""" """To miye a ciki. Ba Saurayi kike nema mai suna Muhammad ba"" ta ƙarisa maganar tana min dariya." Har ga Allah na ji haushin maganarta. Wato ma bata ɗauki maganata serious ba. Tunda ta auri wanda "take so, yake sonta, ai dole ta ce na amince da Bashir. Ko makaho ya san bamu dace ba. Balle na san Bashir bai shirya ma aure yanzu ba. Dan a surutunsa ya ce mini Masters zai fara. Kuma har yanzu a ƙarƙashin arziƙin ubansa yake. Motar da ya ke hawa ma ta gidansu ce ba tashi ba." Haushin maganar da ta mini ya sa na yi shiru ban mata maganar Jalal ba. Wani lokaci ma tsakanin "ƙawaye dole akwai sirri. Idan har aure ya haɗani da Jalal a gaba, bani da tabbacin watarana ba za ta mini gorin irin auren da na yi ba. Ko kuma garin surutu ta je ta faɗawa sisters ɗinta, ko kuma wata ƙawarta. Daga nan kuma shikenan sirrina zai fito waje. Kowa zai san ba auren soyayya muka yi da Jalal ba." Wait. Ya aka yi na fara lissafin auren Jalal?. Ban fa gama yanke shawara ba har yanzu. "Auren Jalal na nufin auren mutumin da zan zauna da shi saboda mahaifiyarsa na sona, ba wai dan shi" yana sona ba. "To ma, shin ni ɗin ina son Jalal ne?" NO. Bana son shi. Ba zan yi soyayya da shi ba. Ba mu dace da juna ba. Amma... Na girgiza kai na mayar da hankalina kan aikin dana ke tun kafin zuciyata ta fara ƙissima mini abinda ba zai yiwu ba. Kusan ni na yi girkin ma duka. Faty dai daga ɗauko kaza miƙo kaza shikenan. Na mana Jollof ɗin spaghetti "da kifi, sai na soya doya da ƙwai. Na ɗan yi sauce kaɗan a gefe. Tea za a haɗa a kai dan bata da zoɓo a gidanta, dana haɗa mana dan tana da ƙanƙara a fridge." Da aka sha ruwa sai mijinta ya zo da wani abokinsa Yusuf. Ni dai tun daga gaisuwa na koma ɗakin Faty. Ita ta kai musu abinci. Da ta gama ta shigo ɗakinta muka zuba namu muka fara ci. "Muna cikin ci tace "" Zeey, na ga kamar ranki ya ɓaci""" """Akan me?, raina bai ɓaci ba"" na yi ƙarya." """Zeey, ɗazu na kawo Bashir ne saboda mafita nake nema miki. Bashir is a nice guy, kuma...""" """Dan Allah Faty kar ki ƙara min zancen Bashir. Bai min ba, ba zan ɓata lokacina da shi ba""" """Allah ya baki haƙuri""" "Na yi shiru kaɗan ina jin haushin addu'arta, can na ce ""Amin""." Haka muka ƙarisa cin abincin babu wanda ya sake magana. "Da nayi niyyar sai bayan isha zan tafi gida, amma muna gama cin abinci na ce mata zan tafi. Itama bata" hanani ba ta saka Hijabi ta rakani bakin ƙofa. "Ban samu Keke ba sai machine. Mai machine ɗin ya dinga zuba gudu dani iska sai kaɗani yake, a haka har" muka iso gida. Bayan na shiga ɗaki dana duba wayata sai naga text ɗin Faty wai na yi haƙuri maganar da ta min. Sai na ji babu daɗi kuma. *** A goman ƙarshe na tafi Kaduna gidan Ummana. Zan mata kwana biyu sai in dawo dan ba zan iya barin tsohuwata ita kaɗai ba. "Umma ta ji daɗin kayan sallar dana mata. Atamfa ɗaya, sai wani farin dry lace ɗaya, sai hijabi da takalmi." "Ƙannena dake maza ne, suma na musu ɗinki kala bibbiyu har da hula. Aliyu shine babba, sai ƙaninsa" Tijjani. Su kenan ta haifa a gidan. "Umma, su uku ne a wajen mijinsu. Ummana ita ce ta biyu." Na kawowa sauran matan tsaraba sannan na musu kyautan dubu uku-uku kuma sun ji daɗi. Musamman "Uwargidan da suke kira Mama. Mama tana da kirki sosai. Zaman lafiyan dana ga suna yi da Ummana lokacin da na zo na zauna a gidan sanda na yi Culinary School ya sa duk sadda na yiwa Umma alkhairi bana mantawa da ita. Na so yi musu ɗinki ko kala ɗaya ne, amma abubuwa sun min yawa." "Shi kuma mijinsu Malam sai zan tafi zan bashi dubu biyar ɗin dana yi niyya. Idan da kara mijin Uwa, Uba" ne. Dan haka babu laifi shima idan na masa alkhairi. Da ke ba wani sabawa nayi sosai da Ummana ba lokacin da zan faɗa mata hukuncin da su Baffa Adamu "suka yanke, sai gaba ɗaya kunya ya cikani. Na rasa ma ta ina zan fara yi mata bayani. Sai ana gobe zan koma Zaria na yi mata maganar. Ta kama salati tana faɗin ai ta jima da sanin munafurcin Baffa Lawalli. Ko lokacin da take gidan, Baffa Lawalli ba ƙaramin munafurci yake haɗawa Babana ba. Abubuwan da ta faɗa mini gameda Baffa Lawallin sai ya sa na sake tsorata da lamarinsa. Tabbas idan wa'adin wata uku da aka yanke mini ya cika ban kawo kowa ba, to babu abinda zai hanashi aurar dani wa Alhaji Nafi'u. A yadda Umma ta sake faɗa mun, shi mutum ne mai kwaɗayi da son kai. Ta ce min har gara ma Baffa Zakari wani lokaci yana abu da hankali amma Baffa Lawalli ba shi da mutunci ko kaɗan. Kuɗi sune Ubangidansa." Daga ƙarshe ta ce in kwantar da hankalina za ta cigaba da yi mini addu'a Allah ya bani miji na gari. "Na san dai miji na garin da za ta roƙa min ba mutum kamar Jalal bane, wanda ya shirya aurena saboda" kawai ya farantawa mahaifiyarsa rai. "Wani abu kuma dana fahimta daga maganarmu da Ummana da ma Kaka tun kafin na zo Kaduna shine," dukkansu biyun suna so na yi auren. Auren dole shine abinda kawai basa so. "Suma fa na fahimci kamar kallon na tsufa a gida ban yi aure ba suke min. Ba su dai furta min ba, amma" shawarwarin da suke bani ne ya nuna hakan. Ban ma fa cika 25yrs ba fa. Sai nan da wata uku masu zuwa zan cika. Umma kam har da cewa idan akwai wanda na amince da shi to na ce ya fito ɗin kawai. Ba sai su Baffa Lawalli sun min auren fin ƙarfi ba. "Allah Sarki, Umma bata san bani da saurayi ba." "Ga shi har Sallah ta ƙarato, lokacin dana yanke zan bawa Jalal amsa ya matso amma har yanzu zuciyata" bata gama tsaida matsaya ba. Auren Jalal na nufin za mu iya rabuwa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Shin na shirya yin aure wanda ke da deadline? Mi su Baffa Lawalli za su faɗa idan Jalal ya sakeni bayan shekara ɗaya ko biyu da aure? Na sani idan na yi auren aka sakeni ba ni ce farau ɗin yin zawarci a agidan ba. Adda Suwaiban Baffa Lawalli aurenta na uku kenan. Aurenta na fari tana budurwa shekara huɗu ta yi ta fito. Aure na biyu ko shekara bai yi ba aka saketa. Wannan da ta yi na uku shine kuma Allah ya sa ta jima. Dan ina ga za ta yi shekara goma a gidan. Aishan Baffa Zakari ma saki biyu ne tsakaninta da mijin da suke tare. Yanzu ne da ya saura igiya ɗaya tsakaninsu ta nitsu ta dena yin yaji. Dan haka idan na yi aure aka sakeni ba sabon abu bane a gidan namu. Amma duk da haka. Shin na shirya ma Aure da kuma Zawarci?. Ban san ya aka yi wani ɓangare na zuciyata ya fara kwaɗaita mini auren Jalal ba. Ba dan ya min alƙawarin zai bani restaurant ba. Ba dan ina gudun auren Alhaji Nafi'u ba. Sai dan akwai wani ɗan mitsitsin lungu a zuciyata da ya ke jin wani abu akan Jalal. Irin abin da na jima ban ji irinsa ba tun bayan rabuwarmu da yaya Aminu. A ranan da zan koma Zaria Umma ta min kitso. Wata 'yar Mama kuma ta min lalle. Ban je park bama sai "ƙarfe huɗu na yamma. Na shiga mota sai Zaria, ina murna zan je na ga Kakata." *** JAYKAY "Tun daga Azumin farko har yau Azumi 29, wato jajiberin sallah Jalal Maiyaƙi bai samu kwanciyar hankali" "ba. Irga kwanaki yake yana lissafin saura kwana nawa Ziyada ta bashi amsarsa. Wani lokaci sai ya ji kamar ya kirata ya tuna mata, sai kuma ya fasa. Wani lokaci kuma kawai so yake ya ji muryarta amma sai ya basar ya hana kansa kiranta. Amma rashin kiranta bai hanashi bibiyarta a duka shafukanta ba. Duk content ɗin data ɗaura sai ya je ya kalla. Ta wannan hanyar yake jin muryanta, koda kuwa bayani take akan abincin Iftar da take dafawa." A cikin waɗannan kwanakin ya sa aka masa ƙaramin bincike akanta. Yanzu ya san cewa mahaifinta ya "rasu. Ya san sunayen Uncles ɗinta da sana'ar da suke yi. Ya san a ina ta yi karatun Primary da Secondary. Ya san sau nawa ta rubuta JAMB kafin ta samu admission a ABU. Ya san course ɗin da ta ke karantawa, ya san idan sun dawo daga hutu ajin ƙarshe za ta shiga." Jalal sai da ya piling duka information ɗinta ya zubasu a kansa ya keɓe musu waje na musamman. Hatta "ranan birthday ɗinta, ya sani." Wani abu da ya fara fahimta shine. Tun rasuwar Jamal wannan ne karo na farko da ya ji ya damu da "rayuwar wani. Wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya ke bibiyar lamarin wata mace. Ba zai iya fassara me yake ji akanta ba. Amma ya san wani abu ɗaya, ita ɗin ta kawo masa wani haske a rayuwarsa bayan duhun da ya ke fama da shi shekara uku da suke wuce tun daga rasuwar ƙaninsa da kuma ajiye aikinsa da ya yi. Ita ɗin SUNSHINE ɗinsa ce. And tabbas, zai yi duk abinda ya kamata domin ganin ta shigo rayuwarsa. Ba kuma dan Hajiya kaɗai ba, sai dan genuinely yana so ta shigo rayuwarsa ɗin..." ** Safiyar ranan Sallah Jalal ya sake tsintar kansa da bibiyar shafin Ziyada. Amma bai ga ta ɗaura komai ba. "Ya ji kamar ya kirata amma sai ya hana kansa aiwatar da hakan. It's too early, maybe tana shirye-shiryen fita idi ne." Ba a jima ba shima ya sauko ƙasa cikin shigar wata luxury white Wagambari da ta sha aikin hannu. Ɗinkin "babban riga ne amma bai saka babban rigan ba ya riƙota a hannu. Saboda yau Sallah shi yasa zai saka babbar riga, da sun dawo daga Idi zai cireta. Shi idan ka ga ya saka Jumpa ma to ranan Jummu'ah ne. Itama kuma saboda Hajiya za ta yi magana ne idan ya sa ƙananan kaya ranan Jummu'ah." "Mata da rashin shiryawa da wuri 5&6 ne. Shi da Junior sun riga sun shirya sun sauƙo ƙasa, inda yaron" "shima ke sanye da shiga irinta Jalal ɗin, har da ɗan hulansa. Uba da ɗan duka sun fito sun yi kyau." "Hajiya ce ta fara fitowa, Janan kuwa sai da aka buge da cewa za a tafi a barta tukunna ta fito da gudu ko" ɗankwali bata ɗaura ba. "Shi da Janan ne a gaba, yayinda Hajiya da Junior suke zaune a baya. Throughout tafiyar tasu zuwa" "Masallacin Idi, Janan ta yi shi ne wajen ɗaura ɗankwali da kuma recording vlog ɗinta tana bada bayanin ga su nan ita da favourite people ɗinta za su je Eid." Da aka taso daga masallaci sai suka wuce Family House dan su yi gaisuwa kafin su koma gida. In between "gaishe da Uncles da kuma cousins da suka zo sallah a Zaria daga wajaje daban-daban na ƙasar, ya samu damar sake leƙa wayarsa. This time whatsapp status ɗinta ya fara dubawa kota ɗaura wani abu. Yana neman anything daga gareta. Rubutu. Hoto. Murya. Kai anything da zai nuna masa cewa ta yi sallah lafiya. Yana ganin ta ɗaura hotuna biyu a status ya ji wani relief. At least zai ga hotonta. Hotonta ne ita da wata tsohuwa a filin idi, ta rubuta NI DA KAKS MUNA MUKU BARKA DA SALLAH❤. Ya riga ya san Kaks da ta rubuta ba typing error bane. Kwana 29 da ya ɗauka yana bibiyar videos ɗinta ya fahimci haka take kiran Kakarta. Infact zai iya mimicking yadda ta ke kiran KAKS ɗin ma. Ɗan binciken da yasa aka yi masa akanta da kuma FBI Agent ɗin da ya zama a pages ɗinta, ya fahimci cewa tana tsananin son Kakarta. An ce masa a hannun Kakarta ta taso. So, they are very close." "Hoto na gaba hotonta ne ita kaɗai, tana riƙe da Sallaya fiskarta ɗauke da murmushi, ta miƙa hannunta as" if tana so ta karɓi wayar. Daga caption da ta sa ya fahimci Kakarta ce ta ɗau hoton. Hoton a kaikaice yake saboda ba a ɗauka da kyau ba. Amma ya yi kyau. Ta yi kyau. Lokacin da suka koma gida bayan an gama gaisawa a Family House ya riga ya zaɓawa kansa zai je gidansu Ziyada ya je ya ganta. No. Zai je ya ji shawarar data yanke. Ƙarfe biyar da rabi ya shiga ɗakin Hajiya bayan ya sake wanka ya saka light blue Jumpa da ta sha aikin hannu da hula. Hajiyar ma bata jima da shiga ɗakinta ba dan tun da suka dawo gidan itama take ta karɓan baƙi. Ɗan gyara hularsa ya yi dan saka hula ba ƙaramin damunsa yake ba. A cikin ƙasa da shekara uku da dawowarsa Nigeria ya koyi sakawa dan a baya zai yi wuya ka ganshi da hula a kansa. Ko ya saka saboda wani dalili to ka bashi minti talatin za ka ga ya cire ya ajiye. Idan Jamal ya masa magana sai ya ce hula na saka masa ciwon kai. Yanzu da ya ke tsaye gaban Hajiya sai yake sake jinsa cewa shigarsa ta yi tunda Hajiya ta yaba. """Hajiya, bari mu fita hira""" """Hira?"" Hajiya ta tambaya da mamaki. Ta san dai dan zai je wajen abokansa ko 'yan'uwa ba zai ce mata" zai fita hira ba. Idan abinda ta ke tunanine to kuwa Alhamdulillahi. Bata ma ɗauka zai ɗau maganarta da mahimmanci da wuri haka ba. Amma ta ji daɗin hakan. Kuma tana masa fatan Allah ya haɗashi da mace ta gari. A dawo lafiya ta masa tareda addu'ar Allah ya shige masa gaba. Ya amsa da Amin ya fita yana jin daɗin yadda ya ga farinciki ya wanzu a fiskar Hajiya lokacin da ya tabbatar mata wajen mace zai je. "Har ya yi nisa da gida sai ya tuna bai riƙo komai ba. To mi zai riƙe mata?. Flowers?, No. Nan ba London" bane. Wani cousin ɗinsa Ibrahim ya kira wanda suka ɗan taɓa hira da shi yau da safe a Family House. Ya "tambayeshi me ake kaiwa 'yanmata ranan sallah. Sai da Ibrahim ya masa dariya yana masa shaƙiyanci wai ya gaji da Baturiyarsa kenan zai nemi baƙar fata, sannan ya faɗa masa abubuwan da zai iya kaiwa. Ibrahim ƙani yake a wajensa amma tsakaninsu bai cika shekara biyu bama. Yana cikin wanda suke ɗan ɗasawa da Jalal ɗin. Dan Jalal ba shiga cikin mutane yake ba." Lokacin da ya gama siyayyar da zai yi a wani Mall ya fito riƙe da ledoji a hannunsa sai ya fara mamakin "kansa. Wai shi Jalal ne yau yake duka wannan zirga-zirgan saboda yana neman attention ɗin yarinyar da bata kai Janan ba. No. Duk abinda yake yi saboda ya samu ta amince da tayinsa ne, and in return ya samu Hajiya ta yi farinciki da shi. Ba wani abu serious bane. Ya kwaɓi kansa." Har ya iso ƙofar gidansu Ziyada bai kirata ba. Sai da ya kashe mota sai kuma ya ga wautar yin hakan. "What if bata nan? Ko kuma ta ƙi fitowa. Ya sani, it's bad manners ka zo gidan mutum ba tareda ka nemi izinin zuwa ba. Wannan duk daga baya ne. Yanzu kam ya zo, kuma God help him tana gida dan ba zai iya komawa gida ba tareda ya ganta ba. Sannan desperately, yana so ya san position ɗinsa. Za ta aure shi ne? Ko kuma ya?..." Zaro wayarsa ya yi ya fara kiran numbarta amma ba a ɗauka ba. Ya ɗan daki steering yana fatan dai ba wai bata gidan bane. Dan a yadda yake jinsa idan bata ɗau wayar ba zai iya shiga har cikin gidan nemanta . Yana cikin dubawa ko zai ga yaro mai ɗan wayo da zai kira ya aika cikin gidan sai ya hangota ta fito ita da "wani saurayi. Ta glass ya ke ganinsu, saurayin ya buɗe mata mota. Ta ɗan tsaya tana dariya kafin ta shiga shi kuma saurayin ya zago ya shiga gefen driver." Waye shi?. Ina za su je?. Ba ƙaninta ya faɗa masa bata da saurayi ba?. Wannan ba tsoho bane balle ya yi tunanin ko Alhaji Rabi'unta ne. "Wannan saurayi ne, probably early 30s." Lokacin da motar saurayin Toyota Camry ta zo ta wuce shi sai ya ji wani nauyi a ƙirjinsa kamar an ajiye masa ƙaton dutse a wajen. Kenan gaskiya ta faɗa ranan data ce masa tana da saurayi. "Shikenan, sai ya ji duk wani hopes ɗinsa akanta ya fara rushewa." Ya zai yi idan ta ce bata amince da deal ɗinsa ba? Ya san zai iya samun wata macen da ta dace da criteria ɗin Hajiya. Infact ga su nan dayawa sai ya zaɓa ya "darje. But duk ba wannan ba. Yanzu da wani ya wuce da ita cikin ƙaramar Toyota fucking Camry, sai ya" fahimci ba wasu matan ya ke so ya aura ba. Ita ɗin ce dai ya ke son aure... CHAPTER TWENTY TWO ZEEY Vanilla ice cream da Chocolate chip cookie flavour shine favourite ice cream combo ɗina. Yaya Aminu ya sani. Bai ma tambayeni ba muna zuwa ya je ya min order. Saboda sallah wajen ya cika da mutane. Ganin babu wajen zama mai kyau ina karɓan ice cream ɗin a hannunsa na ce mu je mota kawai na sha a can. Ina zama na buɗe na fara sha. Uhmmmm! Out of this world!. Idan baku taɓa shan combo ɗinnan ba to ku gwada. Shima irin nawa combo ɗin ya siya. Amma shi scoop ɗaɗɗaya aka sa masa ni kuma double scoops aka sa min. Ina shan ice cream ɗin ina santi. Yau take Sallah. Da safe ni da Kaka mun je idi. Da muka dawo sai gidanmu ya fara cika da 'yan gaisuwa. "Ni dama ban yi girki ba, tun jiya na mana chinchin, na soya kaza, da kuma doughnut. Da safe tea muka sha da doughnut ɗin muka tafi Idi. Sashen Baffa Lawalli an yi Masa. Sashen Baffa Zakari Tuwo suka yi. Ita kuma Anty Hafsah ta yi shinkafa da miya. Idan ka cire masa guda ɗaya dana ci duka sauran ban taɓa ba." "Umman Fada da yaranta sun zo. Wasu 'yan'uwan Kaka ma sun zo daga Kano, da yamman nan suka dira." Sashen namu gaba ɗaya ya cika da hayaniyar yara. Shiyasa da yaya Aminu ya kirani ya ce in shirya mu fita yawon sallah na zari gyalena da jaka na biyoshi. Da bai zo bama gidan Faty zan je dan hayaniyar gidan namu ya yi yawa. Ko'ina ka duba yara ne sai wasa da hayaniya suke. 'Ya'ya da Jikoki ta ko'ina. """Babe, ki bari na gabatar da kaina wajen su Kawu""" "Da maganar, da riƙe min hannu ɗaya da yayi ban san wanne ya fi wani saka mini shock ba." Wani irin magana ne wannan. Mun riga mun wuce wajen nan. Mun riga mun rufe babin nan. Na yi ƙoƙarin zare hannuna daga nashi amma sai ya riƙe da ƙarfi. """Yaya Aminu...""" """Ki yi haƙuri, Ziyadah. Ba zan iya bari wancan wawan Alhajin ya aureki ba... Ba zan iya bari su Kawu su" "miki auren dole ba. I still love you. Kin sani""" "Ajiye roban ice cream ɗin dana ke sha na yi na raba hannuna da nashi sannan na kalleshi da kyau," numfashinsa sai fita yake da sauri-sauri. """Yaya Aminu, please ka dena kawo maganar nan. Mun jima da rufe zancen nan. Dan Allah kar ka sake" "ɗagoshi""" """Saboda kin dena sona?""" Na yi shiru. """Saboda kin ƙwammaci auren wancan Alhajin a kaina?""" """Ba haka bane""" """Menene Ziyadah?. Tell me kin daina sona. Look into my eyes ki faɗa min cewa kin dena sona""" "Na yi shiru. Ba dan ba zan iya faɗa masa hakan bane, sai dan wani zafi dake taso mini a can ƙasan" zuciyata. """Ni ban dena sonki ba. Kin san har yanzu ko budurwa na kasa yi. Umma kullum faɗa take min akan na ƙi" "yin aure. Amma Zeey kin san dalilin hakan. Kin san cewa har yanzu ban cire rai da ke ba""" Maganganunsa suka cigaba da hura min zafi a zuciyata. Ina jin wani ƙuna a ƙirjina. The last time da na ji "irin haka, shine lokacin da muka yi sallamar ƙarshe, inda muka sakawa soyayyarmu FULL STOP bayan" mun gano rashin dacewar genotype ɗinmu. """Ba Alhaji Nafi'u zan aura ba"" na faɗa lokacin dana samu damar sarrafa bakina da tuni ya kasa cewa" komai. """Kina da wani bayan ni ne?"" Yaya Aminu yai tambayar a tsorace. A iya sanin da ya min ya san har yanzu" bani da tsayayyen saurayi. Ya san bayan shi ban sake bawa wani ɗa namiji damar soyayya ba. """Akwai wani"" na bashi amsa sanin cewa idan ban tabbatar masa akwai wanin ba a daren nan zai iya" zuwa ya samu Babansa ya ce su zo su samu su Baffa Lawalli. """Akwai wani da muke tare"" na sake maimaitawa." Yai shiru bai ce komai ba. Wannan ya bani damar cigaba da magana. """Dama bayan sallah zan gabatar da shi wa su Baffa Lawalli. Ban faɗa maka bane saboda kafin a fara" "Azumi muka haɗu, kuma da gaske aurena zai yi""." Kallon rashin yarda ya fara bina da shi yana girgiza kai. """Kar ki min ƙarya, Ziyada. Na san har yanzu babu wani tsayayye a rayuwarki""" """Jalal sunansa. Jalal Maiyaƙi"" na katse shi tun kafin ya gano ƙaryata. Koda yake ba ƙarya bane. Ni da Jalal" "Maiyaƙi akwai maganar aure a ƙasa. Idan a da ban yanke shawara ba, to yanzu da nake cikin mota tareda yaya Aminu na riga na yankewa kaina shawara. Ni Ziyada Sadiq Haruna na amince zan auri Jalal Maiyaƙi, koda na wata shida ne, koda na shekara ɗaya ne, koda babu soyayya a tsakaninmu. In dai hakan zai sa Baffa Lawalli ya ji kunya. In dai hakan zai sa yaya Aminu ya fita a harkata gaba ɗaya, to. Na shirya aurensa." """Jalal Maiyaƙi?"" Ya maimaita sunan yana kallona yana ƙoƙarin nemo a ina ya san sunan." """Familyn Maiyaƙi dai dana sani a nan garin?""" Na gyaɗa masa kai. Still kallon rashin yarda ya ke mini. """Ba sune suke da kamfanin JK Group ba?. Akwai wani plaza ma da suka gama ginawa kwanan nan amma" "ba a buɗe ba. Shi Jalal Maiyaƙi kike faɗa?""" """Eh"" na amsa a taƙaice. Yanzu na fahimci mamakin ta inda na haɗu da shi yake ba wai tunanin ƙarya" nake masa yake ba. """Shi ɗin za ki aura?. How?""" """A gidansu muka haɗu, na je yiwa Hajiyarsa girki ya ganni muka yi exchanging contact muka fara magana." "Kuma da gaske yake aurena zai yi""" Ina ganin yadda fiskar yaya Aminu ya koma daga mamaki zuwa tsoro. Tsoron in dai Jalal Maiyaƙi ne ba "Alhaji Nafi'u ba, to ba shi da chance akan dawo da maganar soyayyarmu." Yai shiru. Can ya kwantar da kansa akan steering ya kasa magana. Na maida dubana wajen robar ice "cream sai na ga ya riga ya melting ya koma ruwa. Allah Sarki Vanilla and Chocolate chip cookie ɗina ya zama ruwa, kuma fa rabi kawai na sha. Rufe robar na yi da kyau na buɗe window na jefar da shi." Lokacin da yaya Aminu ya ja mota sai wani shiru ya sauka cikin motar kamar babu kowa dan ko sautin numfashinmu baka iya ji. Ƙarshe da na ga shirun yayi yawa sai na jawo wayata daga jaka. Ina kunnawa missed call ɗin Jalal na gani. "Allah Sarki, ashe ya kira tun kusan minti hamsin da suka wuce, ina ga sanda muka fito daga gida ne." Na riƙe wayar a ƙirjina abubuwa dayawa suna mini yawo a kwanya. Har ya kawoni gida bai ce komai ba. Sai da na zo fita ya ce mini gobe zai wuce Yola. Na ce masa Allah ya kiyaye. Ban shiga gida ba har sai da motarsa ta ƙule. Ina shiga gida na samu su Umman Fada suna shirin tafiya. Ko kulasu ban yi ba na je na haye gadon Kaka "me rumfa na rufe fiskata. Yanzu na san abu ɗaya. Na zaɓi auren JALAL. Kuma duk abinda zai biyo baya, zan karɓa da hannu bibbiyu." Kaka ta fara tambayar me ya sameni na kwanta ana kiran Magariba. Na ce mata kaina ke ciwo. Ta ce min akwai katin Paracetamol a jan Samira kusa da inda ta ke ajiye rediyonta na ɗauka na sha. Na ce mata zan sha idan na tashi. Tunanin kiran Jalal na yi. Amma sai na fasa. To idan na kira in ce masa me?. To ai shi ya fara kira. Wataƙila gaisuwar sallah zai min. Can dai ɓangaren da ke son kiransa ya rinjayi ɓangaren da ke hanani kiran. Na danna masa kira ina jin bugun zuciyata na ƙaruwa... *** JAYKAY "Bayan ya bar gidansu Ziyada, Jalal bai iya komawa gida ba. Haka yai ta yawo a gari yana neman wajen da" zai je ya ji sanyi amma ya rasa. Ƙarshe da ya gaji sai ya tsaya a wani masallaci lokacin an fara kiraye- kirayen sallar Magariba. Ya fito ya bi mutane ya je wajen da ake alwala ya ɗau buta ya cika da ruwa. Zama yai a wani dakali ya fara alwala sai ya ji wayarsa tana ringing. Bai ɗauka ba dan yana shafar kai ne. Lokacin da ya gama alwalar an shiga sallah dan haka bai bi ta kan wanda ya kira ba sai kawai ya shige masallaci. Sai bayan an idar da sallah da ya fito daga Masallaci sannan ya zaro wayarsa daga aljihu ya duba kiran da "aka masa. Missed call biyu ne. Ɗaya daga Ziyadah, ɗayan kuma daga Direbansa. Sai kuma text ɗin Ziyadar. Yai saurin buɗewa duk da har lokacin yana jin haushin ganinta ya yi da wani ɗazu da yamma." *NA AMINCE. AMMA INA DA SHARUƊƊA... CHEF ZIYADA* "Wani murmushine ya suɓuce masa ba tareda ya shirya ba. Na amince da ta rubuta shine damuwarsa," duk wani sharaɗi da za ta kawo masa wannan daga baya ne. "Ji yai ba zai iya zuwa gida ba har sai ya ganta. Ƙarfe bakwai ne da wani abu, dan haka zai iya wucewa" "gidansu. Sai kuma ya tuno yadda ta ke yiwa wancan saurayin murmushi ɗazu, sai ya ji gwiwarsa ta sace. Gara ya bari gobe su haɗu kawai. Gobe nasa ne shi kaɗai. Zai barta yau ta je ta yi sallama da duk wasu samarin da ta san tana da shi. Daga gobe ita ɗin za ta zamo tasa, shi kaɗai. As long as ta amince da deal ɗinsa, to zai saka mata cikin nasa sharaɗin, banda yiwa wasu mazan murmushi." Sai da ya shiga mota sannan ya tura mata text su haɗu gobe a inda suka saba haɗuwa. ZAN FITA KALLON HAWA GOBE ta turo masa reply. JK PLAZA. 10:00AM Bayan ya tura mata wannan sai ya ja mota ya koma gida. Da ya je gida sai ya samu yaran 'yan'uwa sun zo gidan. Suka tsare shi wai sai ya basu barka da sallah. Haka ya ciro mint ɗin ɗari biyar-biyar ya fara raba musu. Lokacin da ya gama abubuwan da zai yi ya kwanta akan gado sai bacci ya gagareshi. Da ya juya sai ya fara ganin abinda ta rubuta a idanunsa. Ya jawo wayarsa ya sake karanta saƙon 'Na amince. Amma ina da sharuɗɗa'. "Bai ɗauka za ta amince da wuri haka ba. Lokacin da ya ganta ta shiga motar wani Saurayi ɗazu, har ya" "fara tunanin cewa shikenan ba za ta amince da shi ba. Amma yanzu da ta tabbatar masa ta amince, hankalinsa ya kwanta." "Da safe kuwa niyyarsa ya wuce plaza ya jirata ne, sai kuma ya ji Junior da Janan suna maganar fita kallon" Hawa. Har Junior yana faɗin shima zai hau doki. Gidansu ana hawa. Uncle ɗinsa da ya gaji sarautar gidansu bayan rasuwar Daddy zai yi hawa. Sadda "suke yara idan suka zo Nigeria a sallah haka shi da Jamal suke marmarin fita kallon Hawan nan. Lokacin da Daddynsu ya gaji sarautar Maiyaƙi ya fara hawa Jamal yana ɗaya daga cikin waɗanda ke hawa doki ya bi bayan tawagarsa. Ko lokacin da Uncle ɗinsu ya karɓi Sarautar Jamal yana bin tawagar a yi hawan da shi. Amma shi bai taɓa hawa doki bama balle ya bi tawagar 'yan gidansu. Infact fita kallon hawan ma ba zai iya tuna yaushe rabon da ya je wajen ba. Yana dai da wasu videos da hotuna wanda Jamal ya taɓa tura masa. Wasu clips ɗin tun zamanin Daddynsu ne, wasu kuma na Jamal ɗinne akan doki yana wasa." Lokacin da Junior ya tambayeshi ko shi zai kaisu wajen kallon Hawa sai Jalal ya ce ya bi Janan kawai su tafi. Sun ma riga shi barin gidan. Dan ya ji Janan na cewa Family House za su fara zuwa tukunna. Ya yiwa Hajiya sallama ya fita. Maimakon ya tafi JK Plaza sai ya chanja aƙalar tafiyarsa ya wuce gidansu Ziyada. Sai da ya isa gidan sannan ya kirata a waya. Yana gani yara na ta fitowa daga gidan sun sha adon sallah za su tafi kallon Hawa. Minti ishirin ya jirata kafin ta fito. Bai saba jira ba. Shi mutum ne mai bin lokaci. Lokacin da ya ke tuƙa jirgi kowanni second yana da mahimmanci a aikinsu. Amma tunda ya haɗu da yarinyar nan kullum sai ta saka shi jira. Kafin su samu wajen parking sai da suka sha uban wahala. Ga shi ta dage ita lallai tana son su tsaya a wajen da za ta yi kallo da kyau. Lokacin da ya ga za ta fita daga motar sai ya ce mata akwai rana ta tsaya a cikin mota ta yi kallon kawai. Ta ce masa wai ba zai yi daɗi ba. Haka ya rufo ƙofa ya bi bayanta. Bai ga wani sabon abu a wajen Hawan ba. The same abinda ya san ake yi tun suna yara da suke zuwa kallon da Jamal shi ɗinne har yanzu. Amma da ita Ziyadar da sauran mutanen dake kusa da su kowa kallon Hawan Sallahn yake cike da wani shauƙi da farin ciki. Akwai wani abu ɗaya da ya banbanta Hawan da ya kalla a shekaru sama da ishirin baya da kuma Hawan "yau. Wannan karan ba shi da Jamal bane. Wannan karan maimakon dandazon Dawakai da mutane, da Hakimai da masu sarauta da suka sha kwalliya da ado na burgewa suna wucewa gwanin sha'awa shi Jalal Maiyaƙi wannan cute black beauty ɗin ce ta ɗauke masa hankali. Maimakon ya kalli titi kamar sauran. Ita yake kallo. And for a moment, ganinta a hakan ya fi masa kyau. Ya fi masa duk wani ado da ƙawa na wajen Hawan..." CHAPTER TWENTY THREE ZEEY Na yi mamaki da Jalal ya kirani ya ce yana ƙofar gidanmu. Shi da ya dage lallai jiya sai dai mu haɗu a Plaza sai ga shi wai yana ƙofar gidanmu. Dana fito kuwa na ce masa nifa kallon hawa zani ba wai Plazarsa "ba. Bai kulani ba ya ja motar muka tafi. Iskanci, ashe kallon Hawan zai kaini." "Na ji daɗin hakan, koba komai ya rage min wahalar neman abun hawa." "Ban san ko yana jin daɗin kallon ba. Wani lokaci idan na juyo sai na ga hankalinsa na kan wayarsa, ko" "kuma in ga yana kallona, ko in ga yana kallon wani wajen daban. Ni dai ina ruwana. Na zaƙe na yita kallo abuna. Ina ga in ba aure na yi ba ba zan dena ɗokin zuwa kallon Hawan Sallah ba. Idan na ga tawagar da ta min kyau sai na fito da wayata na ɗauki hotuna ko na yi video." Da rana ya ci ƙwal ubana ni da kaina na ce mu koma cikin mota. Ya bini da kallon I told you so ɗinnan. Dama sai da ya ce mu zauna a cikin motar mu yi kallon na ce masa a'a. Akwai ruwa a motarsa amma babu sanyi dan haka na ce barin nemo masu tallan pure water na siya. Na barshi a mota na fita ina gani yana miƙo min sabbin 'yan dubu-dubu na shareshi. A cikin dandazon mutanen nan waye za ka sayi ruwan leda a hannunsa da dubu ɗaya kuma ya baka canji. Yarinyar dana fara tsarewa ruwanta babu sanyi dan haka na sake gangarawa har na hango wasu sun fito "daga wani shago da ruwan gora mai sanyi a wajensu. Na yi sauri na ƙarisa shagon. Ina zuwa kuwa na ci sa'a wai ruwan gora mai sanyi guɗa ɗaya ya rage duk masu kallon Hawa sun kwashe. Na bashi kuɗi na karɓa. Har zan fita sai kuma na koma na siyawa Jalal coke mai sanyi. Ban san wani drink yake so ba, amma na san dai maza na son coke sosai." Kafin na kai wajen motar Jalal sai na hango wasu yara sun yanyame wani mai Fan ice. Ai sai na ji gara nima na je na siya dan na kwana biyu ban sha ba. Ina zuwa na sayi guda biyu. Sai da nasa shi ya zaɓo min wanda ya yi ƙanƙara sosai kafin na karɓa na taho. Ina zuwa na ƙwanƙwasa window Jalal ya buɗe mini ƙofa na shiga. Miƙa masa coke ɗin na yi na ce masa akwai sanyi. Ban ma bi ta kan ruwan dana siya ba na huda Fan ice ɗina na fara sha. Memories. Abin nan tun muna yara nake ganinsa kuma har yanzu yana nan. Akwai ice cream ɗin leda dayawa amma har yanzu babu wanda ya kai Fan ice daɗi. Tsayawa ya yi yana kallona kamar ya ga wata alien data fito daga duniyar Mars. """Kar ka ce na cika kwaɗayi. Dan Sallah nake sha. Yau kaɗai dan na sha wannan ai ba komai bane"" na faɗa" ina cigaba da shan abuna. Zaro farin handkerchief ɗinsa ya yi ya kai hannunsa fiskata. Na tsaya cak!. Har ya goge mun gefen bakina ban iya ƙwaƙwƙwaran motsi ba. """Stop being a Baby, Sunshine"" ya ajiye min handkerchief ɗin a cinyata. Sai a lokacin na tuna da cewa" akwai wani handkerchief ɗinsa a wajena da ban bashi ba. "Sunshine?. Sunshine?. Sunshine fa ya kirani. Ban gama fassara ma'anar Sunshine ba na ji ya ce ""mu tafi" "ko?""" Gyaɗa masa kai na yi na sake ɗaukan handkerchief ɗin ina goge bakina da kyau. Ban san me ya sa na kasa ce masa ya tsaya har sai Sarki ya wuce kafin mu tafi ba. Na tsinci kaina da gyaɗa masa kai kawai kamar wacce ya dannawa remote. Daga ledar Fan ice ɗaya ban sake shan ɗayan ba haka na haƙura har ya yi sanyi ya zama ruwa. Haka jiya "ma sauran ice cream ɗina ya zama ruwa ban sha ba. Wani ɗan mitsitsin kunyarsa ya taso mini. Ba wai dan na sha Fan ice a gabansa ba. A'a, sai dan ma'anar Sunshine ɗin da ya kirani." Haka dai ya ja motarsa muka bar wajen. Kafin mu samu fita a wajen ma sai da muka sha fama saboda mutane sun zo sun cika wajen da muka parking motar. A hanya sai na ɗan kurɓi ruwan sanyin dana siya kaɗan. Daga haka har muka isa JK Plaza ban ce komai "ba. Shima bai sake cewa komai ba. Sau ɗaya dai an kira shi ya yi waya, wanda na lura kamar staff ɗinsa ne ya kira yake masa gaisuwar Barka da Sallah." """So, kin amince za ki aureni"" Jalal ya faɗa tun ma ban zauna da kyau ba. Ya wani tsareni da ido kamar" matar da aka kama akan ƙato. """Ba cewa na yi zan aureka ba. Cewa na yi na amince da proposal ɗinka, amma ina da wasu sharuɗɗa""" """Proposal ɗina aurene, Zeeyadah. Kuma kin amince""" Na fara rarraba idanu. Yanzu da yake ta maimaita NA AMINCE ɗinnan duk sai yasa ni jin kunyar maganar. """Ina jinki, faɗi sharuɗɗanki?""" "Sai a lokacin na ɗan gyara zamana na ce "" idan muka yi aure ba za ka faɗawa kowa yarjejeniyar da ke" "tsakaninmu ba...""" """Na amince"" ya katseni" To shi ya tsaya na gama bayani mana. """Sai me?""" """Zaka bari na dinga zuwa ganin Kakata sau biyu a sati""" """Sau ɗaya a sati, next?""" """To kuma sau ɗaya a sati zan je na dinga ganinta bayan muna gari ɗaya...""" """Su kenan sharuɗɗan ko akwai wasu?""" Na ja tsaki a raina ina hararansa. Tun bamu yi aure ba har ya fara wani nuna min iko. "Na dai cigaba da lissafo masa sharuɗɗa na. Zai barni na ƙarisa karatuna, zai rubuta a rubuce cewa idan" "aka buɗe restaurant ta zauna da ƙafafunta na shekara ɗaya zai bani restaurant ɗin, ya ce min ya amince. Komai na faɗa sai ya ce ya amince. Sai na fara tsoron kar fa na zo na aureshi ya zo ya min wani abun da baya cikin yarjejeniyarmu." """Ni fa ina tsoro"" na faɗa ina binsa da kallon tuhuma." """Tsoron me kike ji?""" """Idan na aureka ka zo ka ɗirka min ciki ka sakeni fa?""" Na bi motsin bakinsa da kallo yadda ya yi wani munafukin murmushin gefen baki. Ɗan matso da fiskarsa "ya yi idanunsa cikin nawa ya ce ""Kina so na ƊIRKA miki ciki ne?""" """A'AAAAH!"" Na faɗa da ƙarfi dan wani kallon dana ga yana min kaman idan an barshi a yanzu zai haiƙe" mini ya min ciki. Ɗan ja baya ya yi ya jingina bayansa da kujera yana dariya. Wannan karan har haƙoransa na gani. And "Gosh! Dariyarsa akwai kyau. Sai yanzu na lura, ba dariyarsa kaɗai bane mai kyau. Shi ɗinne mai kyau. Shigarsa ta manyan kaya da hula na da kyau. Duk haɗuwata da shi yau ne na fara kallonsa cikin jumpa, a baya sai dai suit ko ƙananan kaya." "Jalal kyakykyawa ne. And yanzu da yake wannan dariyar sai na fara zargin kaina. Anya, na amince da" wannan auren ne saboda ina gudun hukuncin su Baffa Lawalli da kuma yaya Aminu da ya kasa haƙura "dani, ko kuma dai wani ɓangare na zuciyata mai rauni ya fara son Jalal?." Na yi saurin girgiza kaina. Ba soyayya bane. Kawai dai shi ɗin kyakykyawa ne. So what! Akwai maza kyawawa dayawa a duniya. Infact a wajen kallon Hawan nan ma ai na ga kyawawan Maza da suka fishi kyau. Ƙarya ne. Ƙarya ne. Ƙarya ne. Waƙar da zuciyata ta fara yi min kenan jin wai ina tunanin akwai wanda suka fishi kyau. "OK, Jalal yana da kyau. Faƙat! Babu ƙari, babu ragi." JAYKAY Ya jima bai ci dariya irin haka ba. Yadda ta wani yi ihu ta ce a'a da ƙarfi lokacin da ya tambayeta ko tana so ya mata cikine ba ƙaramin dariya hakan ya saka shi ba. Ya san ba lallai aurensu ya kai su fahimci juna har su samu physical intimacy ba. Amma abu ɗaya ya sani. Bayan an ɗaura musu aure he's definitely going to kiss her sexy lips. Ba zai iya haƙurin wannan ba. Ya jima yana fantasizing yadda zaƙinsu da laushinsu zai kasance. Wannan kam kota saka masa a cikin sharuɗɗanta ba amincewa zai yi ba. Saboda he's dying inside to taste those lips. """Shikenan sharuɗɗan?"" Ya tambaya bayan ya dena dariyar. Har lokacin akwai ɗan tsoro a tattare da ita." Maybe tana ganin zai iya rufeta a cikin restaurant ɗinnan har sai ya ƊIRKA mata ciki kamar yadda ta faɗa. """Waɗannan sune manyan. Akwai wasu amma ba yanzu zan faɗa ba"" ta bashi amsa." """Nima ina da sharaɗi""" """Erhmm, akwai abinda zan faɗa kafin ka faɗi sharaɗinka"" ta katse shi." """Go ahead""" Ta ɗan yi shiru tana wasa da yatsunta as if abinda za ta faɗa ɗin yana da nauyi a wajenta. Jan lallen dake yatsunta sun masa kyau. He wished zai iya riƙe hannunta ya tracing yatsun ya tickling ɗinsu. """Akwai wani yayan Babana"" sai ta sake yin shiru." Ya mata nuni da ido akan ta cigaba. """Yana da son kuɗi"" ta faɗi hakan muryanta na ɗan rawa." """Okayy"" ya faɗa jin ta yi shiru." """Zai iya roƙonka kuɗi idan ya san kai ɗin waye. Ba haka nake ba. Babana ba haka yake ba. Ka san kowa" "da halinsa ko?""" Ya gyaɗa mata kai yana binta da kallon tausayi. Daga yadda take magana ka san abinda Baffanta ke yi baya mata daɗi. """Kada ka yi amfani da halinsa ka ce gidanmu gidan kwaɗayi ne. Shi kaɗai ne halinsa haka. Idan har ka je" "wajensu kada ka ɗauki maganarsa da mahimmanci. Akwai Baffana dake Katsina da shi za ka yi duk wata magana da shi""" Ta ɗan yi shiru. """Babana ya jima da rasuwa"" ta faɗa wannan karan idanunta suka ciko da hawaye." "Yai shiru yana kallonta. Ya san Babanta ya rasu, amma yanzu da take faɗa da bakinta sai yake ganin" tsagoron zafin rashin mahaifi a idanunta. Ba zai iya kwatanta nata rashin da nasa ba. Ita mace ce. Ta rasa uba a ƙarancin shekaru. Shi kuma sadda Daddynsu ya rasu ma yanzu shekara bakwai ne ko takwas. Da rasuwan Jamal da ta Daddynsu bai kai shekara huɗu ba. Ba zai iya tuna komai na rasuwan Daddynsu ba. Rasuwar Jamal shine har yau baya iya mantawa. "Bai san ta dena taɗin Babanta ba sai da ya ji ta ce ""okay, za ka iya faɗan sharuɗɗanka yanzu"" ta yi" maganar tana goge guntun hawayen daya sauko mata. "Ya ɗan yi shiru. Sai can ya ce ""zan faɗa miki bayan an ɗaura aure""" """Ni dai ka faɗa min yanzu"" ta faɗa tana turo cute lips ɗintan nan" "Ya miƙe tsaye ya ce "" zan faɗa miki ɗaya kafin aure, sauran biyun sai bayan an ɗaura aure""" """Minene na farkon?"" Ta tambaya itama tana miƙewa tareda ɗaukan jakarta." Har suka kai bakin mota bai faɗa mata. Tun tana cewa ya faɗa har ta haƙura ta ƙyaleshi. suk "Da suka iso gida sai ya ce "" auren da za mu yi babu biki""" Ziyada ta kalleshi da ɗan mamaki. """Simple wedding za a yi. Babu taro, babu hidima...""" """Saboda ba ka so matarka ta sani ko?""" """Idan ta sani zan iya rasa Junior, Zeeyadah""" "Ziyada ta yi shiru. Can ta ce ""Auren da dama yake da iyaka ai ba sai an masa hidima ba. Na amince," "ɗaurin aure, babu hidima, babu biki"" ta faɗa tana avoiding idanunsa." """Zan bada duk abinda ake bayarwa na aure. I mean lefe and everything"" ya faɗa dan ya tabbatar mata" ba wai sadaki kawai zai biya ba. Taron biki ne kawai ba za a yi ba. Saboda hakan zai jawo hankalin mutane har Cassandra ta sani. """Na fahimta. Aurenmu is just a deal. Za ka farantawa Hajiya rai. Nima kuma zan samu kyautan restaurant." "Good, Good"" Ziyada ta faɗa har da 'yar dariyarta." "Kallonta kawai yake yi. Deep inside yana jin beyond farantawa Hajiya rai, yana son tarayya da ita. Ba zai" iya mata alƙawarin komai yanzu ba saboda shi kansa bai san me zai faru ba idan ya tuntuɓi Cassandra da batun divorce. Dan haka gara su je a deal ɗin. This way idan abubuwa basu yi kyau ba. Zai iya rabuwa da ita ba tareda ya mata alƙawarin da ba zai iya cikawa ba. And God! He wants to keep her. Ba shekara ɗaya ko biyu ba. Har iya ƙarshen rasuwarsa. "Yana gani ta masa sallama ta fita. Bai ce mata komai ba. Ya jima a wajen, har ya tada mota zai tafi sai ya" tuna abubuwan da ya siya mata tun jiya bai samu ya bata ba. Ya sauke glass ya kira wasu yara ya basu kayan ya ce su kai wa Ziyada. Sai da suka gama ɗaukan kayan sannan ya ja motarsa ya bar wajen. CHAPTER TWENTY FOUR ZEEY Yau officially Jalal Maiyaƙi zai zo hira wajena. Kwana huɗu kenan bayan na amince da deal ɗinsa. Mun yi "exchanging text sau biyu. Na farko ya ce min zai je Abuja, sai kuma jiya da ya min text akan zai zo shi" "wajena yau da ƙarfe bakwai na dare. So, kun ga hira zai zo kenan." Kafin na yi sallan Magariba sai dana yi wanka. Bayan na idar da sallah na kwanta a sallaya ina ɗan jan "carbi ina jiran lokaci. Na san baya wasa da time dan haka na saka alarm ƙarfe bakwai saura minti biyar zan tashi na saka kayana dana goge tun safe na kuma sake goge su ɗazu da yamma. Saura kuce so biyu na yi gugan. Da safe dana goge kayan a cikin akwati na saka su. To dana zo dubawa ɗazu kafin Magariba sai na ga kaman gefe-gefen ya ɗan tattare. Allah ya taimakeni ma akwai wuta, shine na sake bin kayan na goge. Dana gama sai na shimfiɗa doguwar rigar Atamfata da gyalen da zan saka a kan gado, na san babu mai taɓawa kuma ba zai yi squeezing ba tunda ba a takure yake ba kamar cikin akwati. Kaka dai in ba kwanciya za ta yi ba ba za ta hau gadon ba. Yanzu ma tana sashen Baffa Zakari, yau da safe Amaryarsa ta haihu." "Alarm ɗina na fara bugawa na yi wuff na miƙe. Kayan jikina na cire, na fesa body spray sannan na saka" doguwar rigata. Cikin ɗinkin Sallah nane wanda ban saka ba. Na sake bin rigan na fesa masa turare kaɗan. Ɗan lipgloss na saka tunda dare ne kona shafa powder ma yadda nake baƙar nan ba ganewa za a yi ba. Ina cikin jan zip ɗin rigar wayata ta fara ringing. Ai ko ban gani ba na san shine. "Da zan ɗauki kiran sai na ga ƙarfe 6:59PM ne. Na ɗau kiran da sauri ina faɗin ""gani nan fitowa""." Sai dana gama shiryawa na zari gyalena bayan na yi ɗaurin Zahra Buhari sai na ga ai bai kamata na fita da "sauri haka ba. Idan ya ga na fita bakwai da minti uku ai sai ya ɗauka dama ina ɗokin zuwansa ne. Ni fa na manta ya ake fita hira. Yaya Aminu ɗan gida ne. Yawanci hiran namu ma a ƙofar ɗaki muke. Wani lokaci kuma ina jikin machine ɗinsa a waje, ko kuma a zaure." Na ɗan zauna a bakin gado ina duba wayata hankalina na kan lokaci dan so nake sai bakwai da minti goma kafin na fita. Ai kuwa sai ga text ɗinsa bakwai da minti biyar. "*BA SAI KIN YI KWALLIYA BA, I WON'T STAY MORE THAN 10 MINUTES*" Ku ji iskanci! An gaya masa kwalliya nake. Akan me zan masa kwalliya. Mtswww!. Sabon kayan dana sa ma ai saboda duk dan ba a ƙare hidimar Sallah bane. Ba wai dan shi na saka ba. Ina tunanin zan cigaba da zama har sai 7:10PM ɗin ashe tuni ƙafata ta yi ƙofar ɗaki tunma kafin tunanin ya gama sauka mini. Na jawo ƙofa na saka key na rufe. Dana gama kullewa sai na saka key ɗin a ƙasan babbar butan Kaka dake ƙofar ɗaki. A zaure na tsaya na gyara gyalena na ɗan duba fiskata ta camerar wayata sannan na fita. Ɗan nesa da ƙofar gida yake ajiye motarsa dama dan haka na fara taku a hankali. """Ina za ki je?"" Na waiwaya da sauri dan na san mutum ɗaya ke min tambaya da faɗa-faɗa haka." """Ina wuni, Baba"" na gaisheshi ko risinawa ban yi ba." """Tambaya nake miki, ina zaki je?""" """Erhm..."" bana so Jalal ya fara haɗuwa da Baffa Lawalli, na fi so direct na kai shi wajen Baffa Adamun" Katsina. """Dama an kawo mini saƙone shine zan je na karɓa""" "Ya ɗan yi shiru yana kallona alamar bai yadda da maganata ba ɗinnan. Sai kuma ya ce ""kin kira Alhaji" "Nafi'u kin masa godiyan dana ce?""" "Na tsuke fiska nace "" Baba zan kira shi idan na dawo""" """Ki tabbatar kin kirashi. Mutumin arziƙi irin hidimar daya mini a wannan sallar abin a yaba masa ne""" """Kwaɗayayye"" na faɗa a zuciyata. Wai fa Alhaji Nafi'u ya masa ɗinki a Sallah kuma ya kawo masa" shinkafa mudu goma da kaji uku dan a yi hidimar sallah shine ya bi ya isheni tun ranan Sallan wai na kira Alhaji Nafi'u na masa godiya. Akan me zan masa godiya bayan ba ni na karɓi kyautarsa ba. """Kina sane dai lokacin da muka ɗiba miki ya kusa cika"" Baffa Lawalli ya faɗa da sigar gargaɗi." "Na ce masa ""Baba kwanan nan zan kawo muku shi"" daga haka na bar wajensa tun ma kafin ya riƙeni da" wata maganar. Ina zuwa jikin motar Jalal na ji ƙaran cire lock dan haka na buɗe na shiga. """Dan Allah ka yi haƙuri. Wani Babana ne ya tsareni da magana a ƙofar gida""" Wayarsa yake dannawa bai juyo ya kalleni ba balle ya min magana. "Farin tshirt ne a jikinsa, kamar da baƙin jeans ne ko kuma navy blue, ba zan iya tabbatarwa ba dan akwai" ɗan duhu a motar sai haske kaɗan daga wayarsa. """13 minutes. Haka kike wasa da lokaci, ko kuma ni kaɗai kike yiwa haka?"" Ƙarshen tambayar ya yi shi" yana kallon fiskata. """Ai na faɗa maka uzurina ko"" na faɗa ina ɗan tura baki." """So, 13 minutes kuka ɗauka kuna magana?""" Kai Jalal ɗinnan akwai son tada rigima. Ni kam bana bashi haƙuri bane. Ya yi haƙuri mana. """Na tsaya kulle ƙofar ɗakinmu nefa, kuma kwaɗon bai rufu da wuri ba, yayi tauri. Idan na koma ma zan" "ɗiga masa mangyaɗa"" na sake ƙaƙalo wani bayanin." """I see"" ya faɗa yana maida dubansa kan wayarsa." "Ya yi shiru. Nima na yi shiru. Can sai na ji yace ""Hajiya tana gaisheki""" """Hajiya?"" Na ɗan zaro ido. ""Har ka faɗa mata?""" """Yes""" """Shikenan ni Ziyada jikar Altine mai Tuwo. Yanzu fa cewa zata yi daga zuwa yi mata girki zan aure mata" "ɗa"" na faɗa ina kama kai." Wani dariya ya mini. Na ɗago ina faɗin mugu a zuciyata. Kuma fa ranan Sallah Hajiya da kanta ta tura "min gaisuwar Sallah ta whatsapp, dana mata reply take tambayata yaushe zan shigo ne na sake yi mata girki." "Ganin dariya ma yake mini sai na ɗago nace "" to kuma ce mata ka yi kana so ka aureni?. Ni yanzu duk ka" "sakani jin kunyar Hajiya. Ta ina zan fara haɗa ido da ita a garin nan ni Ziyada???""" """Relax""" """Ta yaya zan relax bayan ka je ka yiwa Hajiya maganata. Allah ne kaɗai ya san irin tunanin da za ta yi a" "kaina"" na sake rufe fiskata." "Ni sai yanzu ma nake ganin wautata. Da nayi saurin amincewa zan auri Jalal, da wani idon zan kalli Hajiya" Layla?. What if Hajiya tace bata amince dani ba. What if ta fara tunanin na shiga rayuwar ɗanta ne saboda suna da kuɗi?. JAYKAY Duk sadda ya haɗu da yarinyar nan sai ta saka shi dariya. The girl is just funny. Yanzuma dan ya faɗa mata cewa Hajiya tana gaisheta shine ta birkice haka tanata making funny face kamar zata yi kuka. "Bai faɗawa Hajiya wajen Ziyada zai zo ba. Ce mata yai zai je hira, shine ta ce masa ya gaisheta. Yana so" sai ya gama wasu tsare-tsaren daya shirya sannan ya gabatar da kansa wajen Uncles ɗin Ziyada. Daga nan kuma sai ya fito ya faɗawa Hajiya cewa Ziyada yake so ya aura. """Barin kira Hajiya na ce mata gashi nan kina min kuka saboda ta san zan zo wajenki""" "Saurin sake hannunta ta yi ta kalleshi tana faɗin ""ni ba kuka nake ba""" Ba zai faɗa mata gaskiya ba. Ya samu abinda zai riƙa teasing ɗinta da shi tunda ya lura tana jin kunyar Hajiya. """Now"" ya gyara zamansa dan ya mata bayanin abinda ya kawoshi ""starting tomorrow, zan haɗaki da" "Jide. Shine zai guiding ɗinki yadda za a tafi da maganar Restaurant. Already aiki yayi nisa akai dan dama a initial plan ɗinmu za a buɗe Plaza in less than two months mai zuwa ne. And the Restaurant shine muke targeting zai zama face of the Plaza. But duba da cewa idea ɗinmu na farko ya banbanta da naki dole a fara aiki daga farko. Idan muna so a buɗe Plaza tareda Restaurant ɗin dole mu fara aiki da wuri """ """Okay, ba matsala. Na fahimta"" ta bashi amsa." """Yaushe za ku koma school?"" Ya tambayeta." """Saura two weeks hutunmu ya ƙare""" "Ya ɗan yi shiru kamar mai nazarin wani abu kafin ya kalleta ya ce ""Aiki zai fara daga gobe. Gobe zaku" "haɗu da Jide ku tattauna akan Menu, Operations, Branding, and everything. Direba zai zo ya ɗaukeki 8AM gobe, please ki shirya da wuri. We have lot to cover kafin ki resuming school""" """Gaskiya ƙarfe takwas yayi wuri, ina laifin 8:30-9:00 haka""" """Saboda ki samu lokacin yin kwalliya ko?""" """Haba kwalliya. Ni bana kwalliya. Kawai dai...""" """9:00AM Zeeyadah. Banda ɓata lokaci"" ya faɗa sounding serious." "Ɗan ɓata rai ta yi ta fara faɗin "" ni fa na faɗa maka abinda ya sa na makara ɗazu. Amma sai wani cewa" "kake ina da ɓata lokaci. Ni yaushe na ɓata maka lokaci?""" Maimakon ya bata amsa sai ya fara matso da fiskarsa kusa da nata. Ja baya ta yi ta mannu da ƙofa sosai "tana rarraba idanu. Tsoro ya gani a ƙwayar idanunta. Tsoron abinda zai iya aikata mata a wannan lokaci. But he is not stupid. Duk da yana kwaɗayin kissing lips ɗinta, ba a nan zai yi ba. Ba yanzu ba. Ba gobe ba. Sai ranan da ta zama mallakinsa--- Temporarily, ya jaddadawa kansa." """Always, Sunshine. Koyaushe kina ɓata min lokaci""" Ja baya yayi ya gyara zamansa dan da ya ƙara matsawa kusa da ita ba mamaki kurma masa ihu za ta yi. Yana jin yadda ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya lokacin da ya matsa baya. "Wani abin da ya ke birkita masa zuciya shine, a duk yanayin da fiskarta yake. Tsoro. Fushi. Dariya." Murmushi. Duka burgeshi ta ke yi. This is new. Wannan sabon abune a rayuwarsa. """Zan...zan tafi"" ta faɗa da ƙyar." """Ana kiran sallan isha"" ta sake faɗa ganin bai kulata ba..." ZEEY Yau na ga bone. Saura kaɗan zuciyata yai tsalle ya fita daga ƙirjina lokacin da na ga Jalal ya matso da "fiskarsa yana kallon lips ɗina. Bakina yana shirin furta ""Wayyo!"" kenan sai na ga ya matsa baya." Allah na gani ba zan iya sake second goma a cikin motar nan tareda shi ba. Anya kuwa wannan mutumin ba yaudarata ya zo yi ba?. Idanunsa fa ɗazu da yake kallon bakina Allah kamar Kura ta ga Akuya ne. "Ni ga shi ban sani ba, tsabar ruɗewa ne ko menene. Daskarewa na yi a wajen na kasa processing komai." "Ranan da Alhaji Nafi'u ya yi ƙoƙarin kissing ɗina a motarsa hannuna ne ya fara kaiwa fiskarsa kafin ma ƙwaƙwalwata ta gama bata umurnin hakan. Shi kansa Alhaji Nafi'un bai tsammanci zan mareshi haka ba, dan riƙe fiskarsa yayi yana faɗin ""Sayyada ni kika mara?"". A lokacin sai da muka yi kusan wata biyu bama magana. Daga baya da dayake maye ne ya sake dawowa yana bani haƙuri wai ba laifinsa bane na yi haƙuri. Wai ni ɗince idan yana tare dani kamar magnet haka sha'awata ke jansa. Dama namiji ba abinda ba zai iya faɗa na daɗin baki ba dan ya yaudareka." Yanzu da nake ganin ƙwayar idanun Jalal da wannan maitar gara na fita daga motarsa. Dan da alama sheɗanin da ke zuciyata ba zai bari na kai masa mari idan yayi attempting kissing ɗina ba. Ai yana cire lock ɗin motarsa na saka ƙafata na fita ko maimaita mini lokacin da zan je restaurant gobe da yake ban saurara ba. Ina zuwa gida sashenmu na shiga straight. Na ci sa'a Kaka bata shigo ba. Na ɗau key na buɗe ƙofa na shiga ɗakin sai kuma na tsaya. Sautin da ƙirjina ke bayarwa ya sa na kai hannuna dai-dai wajen. Bugun da zuciyata ke yi tamkar na zaga stadium da gudu sau uku. Me yake shirin faruwa dani?. Me yasa nake jin wani abu akan Jalal? Auren da za mu yi DEAL ne. Babu maganar soyayya ko kuma tarayyar aure. To me yasa zuciyata ke gudu haka? Tabbas zuciyata ta haukace. Ban bata wannan umurnin ba. Duk abinda take babu sa hannuna a ciki. My HEART has gone MAD... CHAPTER TWENTY FIVE ZEEY Ƙarfe tara daidai na safe na riga na gama shiryawa ina jiran kiran Jalal. Sai na ji sallamar yaro wai na fito "ana nemana a waje. Na ɗau jakata na yiwa Kaka sallama na fita dan na san ba zai wuce Direban Jalal bane ya iso. Shi ɗinne kuwa, wanda ya kawo min nama kwanaki. Ina isa bakin motar zan shiga gaba ya ce kar na damu na shiga baya kawai. Na buɗe gidan baya na shiga sannan na gaishe shi. Ba tsoho bane, amma aƙalla zai iya kaiwa shekara arba'in haka." Maimakon mu yi hanyar Plaza sai naga mun yi wani hanyar daban. Na kasa shiru na tambayeshi ba Plaza za mu je ba?. Ya ce mini Yallaɓai ne ya ce ya kawoni Kamfani ba Plaza ba. Na yi shiru kawai ina mamakin chanjin plan ɗinsa. Wani katafaren Kamfani muka isa. Ni ban taɓa zuwa ta arean wajen bama. Dana fito daga motar na yiwa Direban godiya. Ya ce ba komai. Na shiga ciki ina mamakin girman wajen. Receptionist zaka fara tozali da su da ka shiga cikin building ɗin. Maza biyu ne a wajen dukkansu sanye da uniform. """Na zo wajen, Mr Jalal Maiyaƙi ne"" na faɗa bayan na musu good morning." """Ki hau lift, office ɗinsa yana 7th Floor""" Na kalli receptionist ɗin sannan na kalli inda yake nuna min. A duniyar nan sau ɗaya na taɓa shiga "elevator a rayuwata. Nan ma da ƙyar na yadda na shiga saboda ni da Faty ne. Har muka fito jikina ɓari yake sai da Faty ta riƙe mini hannu tana kwantar min da hankali. Ban san ya aka yi nake tsoron abun nan ba. Ƙila yana da nasaba da wani film dana taɓa kallo na ga elevator ɗin ya tsaya mutanen ciki suka kasa fita kuma babu iska, suka yita ƙaƙaren numfashi kamar za su mutu, da ƙyar aka zo aka buɗesu. Nima idan zan shiga sai na dinga ji kamar abin zai maƙale a hanya mu kasa fitowa. Duk inda na je na ga sai an" shiga elevator kafin akai wajen to kodai na bi stairs ko kuma na haƙura da zuwa wajen. Yanzunma ce musu na yi zan bi stairs suka bini da kallon mamaki. Ƙarshe ɗaya daga cikinsu ya ce zai shiga ya nuna min yadda zan yi nace masa a'a. Ya ce zai shiga mu tafi tare na ce masa ya barshi kawai ba zan iya shiga bane. Na kalli takalmina da ɗan tudunsa na ce zaka sha aiki yau. Na fara hawa stairs ɗin da ɗan sauri. Ai tun "kafin na kai hawa na biyu idona ya fara rena fata. Hawa nefa ba kaɗan ba. Dana kai hawa na uku sai ga shi na nemi waje na zauna inata hakki. Ya Subhanallahi! Dana sani na bar receptionist ɗinnan ya rakani ta elevator, da yanzu na manta da cewa ma na isa office ɗin." "Gashi ni ba 'yar firi-firi ba, daga hawa na uku har na fara jin hajijiya. Gaskiya dole na fara exercise a gida." "Da can na taɓa yin karambani na siyo igiya duk safiya sai na fito tsakar gida na fara tsalle kamar mai shirin zuwa aikin soja. Daga baya dana ga go-no-go sai na watsar da komai. 'yan gidanmu dama sun samin ido. Dana fito ina tsalle sai su kama dariya. 'Yan iska. Yana ɗaya daga cikin abinda ya kashe min motivation ɗin exercise ɗin ma . Ga dangin Babana dama tsigarallahu da su, ni kuma na ɗauko jikin Ummana, na yi daban a gidan. Kaf 'yanmatan gidan idan wata ta ɗaga igiya tace za ta yi tsalle Wallahi iska ne zai yi wurgi da ita. Ni kam sai dai mu yi kokawa da iskar dan ba zan kai ƙasa ta daɗi ba. Sometimes ma dai sirara suna da ranarsu. Yanzu gashi tun ban yi rabin inda zan je ba har na gaji." Ina zaune ina jiran numfashina ya ɗan daidaita na cigaba da hawa sai ga kiran Jalal. """Where are you?, Abdullahi ya yi parking tun ɗazu""" Ikon Allah! Ta ya aka yi ya san Direba yayi parking tun ɗazu?. Ko dai yana waje ne?. Kai ina ga ta office ɗinsa ya hango motar. """Gani nan ƙarasowa. Na ɗan tsaya ne ƙafata ta huta""" """Staircase kika bi?"" Ya tambaya da ɗan ƙarfi." """Ni bana shiga lifter, yana bani tsoro""" """God!"" Ya faɗa ina jin sautin dukan table. Kashe kiran ya yi. Nima na cire wayar a kunnena ina ƙunƙuni." "To nina ce su gina kamfani mai hawa-hawa ne. Ina laifin a yi shi flat flat, tunda suna da enough space a wajen." Miƙewa na yi na karkaɗe jikina na cigaba da hawa stairs ɗin. Ina yanko kwana a hawa na huɗu na hango shi can tsaye ya saka hannunsa a aljihu yana kallona fiskarsa ɗauke da mix ɗin mamaki da kuma disappointment. To ni ina ruwana. Na cigaba da hawa har na zo last stair inda yake muka tsaya kallon juna. Ni ina numfashi sama-sama shi kuma yana min kallon daga wani duniyar aka tsamoni da zan ɗauki wahalar bin stairs akan na shiga lifter ta kaini inda zan je cikin sauƙi. """Ai gashi na yi rabi"" na faɗa ina ƙaƙaro murmushin ƙarya. Nan kuwa ƙafata har ta fara ciwo. Ji nake ma" "kamar na cire takalmin ƙafata na wurgar. Wa ya kaini saka 39 ni dana ke saka size 40. The thing is, 40 shine dai-dai size ɗin ƙafata amma idan takalmi ya min kyau na ganshi a size 39 sai na siya. Dan dai zai matseni kaɗan kam ba komai bane. Ko a gida idan aka duba takalmana to size 39 sun fi 40 yawa." """Ghetto girl"" ya faɗa yana juyawa. Na bi bayansa ina faɗin ""dama tun farko ai ban maka ƙarya ba""" Still dai wajen lift ɗin ya kaini. Na ce masa ba zan iya shiga ba ina tsoro. """Idan baki shiga ba zan ɗaukeki ta ƙarfi"" ya faɗa sounding serious. Hehe! Wai zai ɗaukeni ta ƙarfi. Na" "kalleshi, sannan na kalli kaina. Koda yake maza fa ƙarfi garesu. Sai ka ga yaro ƙarami yana iya ɗaukan abu mai nauyi." Saura kuce na fi buhun siminti nauyi. Ban fa kai 70kg ba. Tsakanin 65-67kg weight ɗina yake tsayawa. "Yanzu nema nake kai haka. Da can dana yi Medical exams lokacin registration a level 1, 58kg nake. Wani" "tudu wani gangare, yanzu na ci Tuwo na ƙara nauyi." A hankali na fara takawa ina ɗari-ɗarin shiga. """Get in"" ya faɗa da ɗan ƙarfi" Na yi sauri na shiga amma na tsaya kusa-kusa da shi. Ina gani ya danna 7. Na fara karanto addu'o'in tsira a zuciyata dan gaba ɗaya a tsorace nake. What if wannan lift ɗin ya tsaya aka kasa buɗewa har nimfashinmu ya ƙare muka mutu? . What if Jalal ya min wani abu da bai kamata ba a cikin lift ɗinnan?. "Babu mai ganinsa fa, daga ni sai shi a cikin wannan ɗan tsurkukun akwati mai tafiyan." "Ban san har abun ya tsaya ba. Sai dana ji ya ce ""idan baki fito ba zan barki ke kaɗai a ciki"" na yi saurin" buɗe idona ina sake hannun blazer ɗinsa dana riƙe gam. Ashe rufe idona na yi lokacin da lift ɗin ya tashi. """Ghetto girl"" ya faɗa yana yin gaba ya barni ina jin haushin kaina. Harda wani riƙe masa hannun riga," salon yace dama son taɓashi nake. Bin bayansa na yi da sauri kafin ya min nisa. Wani hall muka shiga akwai kujeru da projector da TV. Kamar dai ƙaramin conference room ne. """Sit. Jide zai zo ya sameki"" na gyaɗa masa kai ina hararan ƙeyarsa bayan ya tafi." "Minti uku sai ga wani young Saurayi ya shigo, irin ɗan early 30's haka. Daga ganinsa ka ga Bayarabe. Yana" da zanen 1-1 a fiskarsa. Bashi da gemu sai ɗan traces na gashin baki kaɗan. """So, you're the famous, Chef Zeey?"" ya faɗa lokacin da ya zauna opposite da kujerar dana ke yana ajiye" laptop ɗinsa akan table. Na gaishe shi Good morning ina faɗin ni ba famous Chef bace. """Sunana Sodiq Olajide Adeleke. Amma an fi kirana da Jide""" """Ashe kana jin Hausa"" na faɗa ina ɗan murmushi. Dan ya hutassheni ƙaƙale-ƙaƙalen turancin dana shiryo" daga gida. """Ahh! Ni haifaffen garin Zaria ne ooo""" """Duk da haka. Da an ji Hausarka an san kai yare ne""" """Abi?"" Ya faɗa yana danna laptop ɗinsa." "Sai da ya ɗan yi taɓe-taɓensa kafin ya ɗago yace ""so, Zeey. Zan iya kiranki Zeey?""" Na ce masa ba matsala. """This is JK Plaza"" ya kunna projector yan ya nuna min ginin Plazar." """Ban san ko kin taɓa shiga wajen ba?"". Na ce masa na taɓa shiga." "Jide yace ""Good. Idan kika lura Restaurant ɗin shine a farko. Shine main face na Plaza ɗin. Akwai dalilin" "daya sa aka gina shi haka. To be honest lokacin da Oga ya ce min zai chanja plan ɗin Restaurant ɗin ban ji daɗi ba. Restaurant business idan bai tafi dai-dai ba cikin ƙaramin lokaci komai zai failing. But on a brighter side dana sake tunani akan concept ɗinki, sai naga it can be a success idan har mun yi aikin daya dace""" "Ya ɗan yi shiru yana kallona sannan ya ce ""switching JK Foods daga fine dining zuwa local cuisine ba" "abune mai sauƙi ba. Ban sani ba ko kin shirya?""" """A shirye nake"" na faɗa souding business dan kar ya rena ni." """Ina nufin ba wai dan kin iya dafa Tuwo mai daɗi ba shikenan kiyi tunanin shi zai kawo kuɗi. We have a" "lot to do behind the scene""" """Ofcourse na san da wannan. Na yi aiki a restaurant ai...""" """A ina?""" """Zikks Foods"" na bashi amsa." """Ha! Zikks Foods. Kin san Mr Alade mai ƙaton kai?""" Ai sai na saka dariya. Mr Alade Managern Zikks Foods ne. Lokacin dana ke aiki a wajenma Mr Alade mai "ƙaton kai staff ɗin wajen ke kiransa a bayan idonsa. Mutumin ne gashi guntu, ga shi da ƙaton kai kamar" gwai-gwai. Haka fa muka fara taɗin aikina a Zikks Foods da masifar Mr Alade. Ashe shima Jiden wai ya taɓa aiki a wajen tun farko-farkon buɗewa. Na saki jiki dan na ga kamar ba za mu samu matsala da Jide ba. Yana da sauƙin kai. JAYKAY Dariyarta da ya ji dai dai ya karyo zai shiga hall ɗin ya saka shi banko ƙofar da ƙarfi. Dariyar kuwa ya gani a fiskarta lokacin data ɗago ta kalleshi. Me suke faɗa haka har take dariya? "Ya kirata nan ta zo ta yi hira da Jide ne, ko kuma ya kirata ta zo su haɗa kai su yi aiki tare?." Shiyasa ya ce Direba ya kawota Kamfani saboda baya so ita da Jide su keɓe a restaurant ɗin suna magana. And the nerve tana yiwa Jide dariya. Dariyar da bata taɓa yi masa ba. """Jide, aikin dana saka kenan?. Labari na ce ka zo ka bata?""" """Sorry, Sir"" Jide ya faɗa yana miƙewa." """Kun finalizing Menu?"" Ya tambaya yana kallon Ziyada" "Jide ya ce "" erm, yanzu muke maganar...""" """Tun ɗazu me kuke yi da baku gama ba?. Jide yaushe ka fara wasa da aiki haka"" Jalal yana maganar" kaman zai daki Jide. """Sorry, Sir. Yanzu za mu gama. Infact dama za mu wuce Plaza ɗin kenan saboda mu ƙarisa maganar a" "can.""" """Then me ka tsaya yi?""" "Jide ya rufe Laptop ɗinsa ya kalli Ziyada ya ce ""Zeey, let's go""" "Ziyada ta ɗau jakarta itama za ta bi bayan Jiden yace mata ""tsaya""" Cak! Ta tsaya ta juyo tana kallonsa. "Sai da Jide ya fita daga hall ɗin sannan ya fara magana babu wasa ko kaɗan a fiskarsa ""Jide is NOT your" "friend. Aiki na ce kiyi ba hira ba""" """Hira kuma. Kawai fa muna taɗin aiki a Zik...""" """Follow me"" ya katseta." Yana gani tana motsi da bakinta amma bai ji me take faɗa ba. "Akwai aikin daya kamata ya yi a office ɗinsa, amma ba zai iya barinta ita kaɗai da Jide ba. Gara su je a yi" maganar komai a gabansa. "Yana gani ta rungume jakarta tsam a ƙirji ta tamke idanunta, bakinta na motsi lokacin da suka shiga cikin" lifter. Wannan karan bata tsaya kusa da shi ba. Amma duk da haka sai ya tsinci kansa da kallon fiskarta. A can ƙasan ransa ya furta 'Matsoraciya'... CHAPTER TWENTY SIX ZEEY Idanuna a rufe a cikin lifter da muke ina addu'ar Allahumma La Sahla... dan har cikina ya fara juyawa sai "na ji mutum kusa dani. Na ɗan buɗe ido dan na san dai nesa da shi na tsaya lokacin da muka shiga lift ɗin. Ashe tsayawa muka yi wani mutum ya shigo shine ya matso kusa dani. Ina jin mutumin yana gaisheshi. Na ɗan kalleshi sai kuma na sake rufe idanuna. Haushi ya bani ɗazu, haka kawai muna cikin magana da Jide sai ya shigo ya fara mana masifa. Wallahi sai dana ji tausayin ɗan Bayaraben nan. Daga ƙarshe kuma ina ƙoƙarin yi masa bayani ya wani katseni wai na biyo shi." Lokacin da lift ɗin ya tsaya har na yi yunƙurin fita sai na ga mutumin ɗazu ne zai fita shi gogan bai ko motsa daga inda yake ba. Sai na juyar da kaina gefe nima na waske. Ko sakan 40 ina ga bamu ƙara ba lifter ɗin ta sake tsayawa. Ina ganin ya fita nima na yi wuff na bi bayansa tun kafin abun ya rufe dani na shiga uku. Ina bin bayansa ina hararansa ta ciki-ciki. Ni ban san masifaffe bane sai yau. Wai mun tsaya hira ni da "Jide. A'a ba hira ba, soyayya muke. Mtsww." Da muka fito mutane sai wani gaisheshi suke yana wani amsawa irin Boss ɗinnan. Boss my foot. Muna fitowa daga cikin building ɗin muka tsaya. Ban san tsayawar na me bane na dai tsaya a gefensa ina kallon harabar wajen. Jide ne ya fito daga building ɗin ɗauke da jakar laptop ɗinsa. Ashe mun riga shi fitowa. Ɗaga min babbar yatsarsa yayi ya min thumbs up nima sai na ɗaga masa ya wuce yana murmushi. A dai- "dai lokacin wannan Ɗan Hajiyar ya juyo yana kallona. Na sauke yatsata, na haɗe rai na juya gefe." Direbansa ne ya kawo masa mota bakin building ɗin. Ya fito yana rawar jiki ya miƙa masa key ɗin motar yana faɗin a dawo lafiya Yallaɓai. Duk sai na ji haushin hakan. Na san dai ko babu yawa Direban zai girmi Jalal amma saboda matsayinsu ba ɗaya ba sai wani rawar jiki yake masa. A rayuwata bana so na ga mutum yana haka. Shiyasa na tsani Baffa Lawalli. Idan ya ga mai kuɗi haka "yake jefar da shekarunsa ya fara ladabin ƙarya yana rusunawa yana rawar ƙafa. Allah watarana dana ga yana wani sussunne kai wa Alhaji Nafi'u ko, sai dana ji kamar na je na kifa masa mari. Mutumin nan fa ya haura sittin amma haka zaka ga yana abu kamar wani ƙaramin yaro. Shi yasa Baffa Adamu ya fi shi daraja a idon mutane. Baffa Zakari ma akwai irin wannan amma nasa da sauƙi compared to na Baffa Lawalli. Ko da yake shi dama ya saba yiwa kwastomomin Banki 'Yes Sir, Thank you, Sir'." "Sai dana ji ya cewa Direban ""Thank you, Abdullahi"" kafin na ɗan sassauta zafin dana ji a raina. Ashe dai" yana da ɗan hankali tunda ya masa godiya. Ya karɓi key ɗin motan ya je ya buɗe ya shiga. Nima na bi shi na buɗe gidan gaba na shiga. Ya ja motar muka bar cikin kamfanin. Bai min magana ba nima na tsuke fiska na manta da shi. "Sai da muka kusa kaiwa Plazar na ji ya ce ""Agnes za ta joining ɗinku daga gobe. She's part of the team""" "Ni ina ruwana. Koma mutane nawa ne za su joining ɗinmu su zo, Allah ya kawosu lafiya." Har muka ƙarisa wajen ban ce masa komai ba. Tunda masifa yake ji sai ya je can ya ƙarata. Na fito daga motar da sauri ko jiransa ban yi ba. Ɗaya daga cikin masu gadin ya taso ya zo ya buɗe mana restaurant ɗin. Na shiga na barsu suna magana. Na samu waje na zauna. Can sai gashi ya shigo shima yana wani shan ƙamshi. Da gaske fa ba zai ce na yi haƙuri ba. Na jawo wayata na fara leƙa duniyar social media. Bamu kai minti takwas da zama ba sai ga Jide ya shigo. Jide ya jawo kujera kusa dani zai zauna ina ganin wani kallo da Jalal ya masa sai na ga Jiden ya ja kujerar baya ya bada space tsakaninmu. Kai wannan Bayaraben matsoraci ne. Allah idan nine ba zan matsa ba. To ina ruwansa da inda zai zauna. Koda yake fa Ogansa ne. Mtssw! masifaffen mutum kawai. Kusan minti talatin muka ɗauka Jide yana mini bayanin abubuwan dake ƙasa da kuma yadda za mu cigaba. An riga an yi rajistar JK Foods a matsayin sunan da restaurant ɗin zai ɗauka tunda ƙarƙashin JK Group yake. Amma dama already wai Jalal ya ce za a sabunta rajistar JK Foods zai koma parent company mai zaman kansa. Shi kuma restaurant ɗin dama wasu brands ɗin da za a buɗe a gaba ƙarƙashin kamfanin JK Foods za su ɗauki sunaye daban. Wato a yadda na fahimta. Ba wai JK Foods Jalal zai bani ba. Zai bani restaurant ɗaya da zan gina ne ƙarƙashin JK Foods. Kenan a gaba JK Foods zai iya buɗe wasu restaurants ɗin ko wasu business ɗin amma wannan da za mu buɗe yanzu shine zai zama nawa idan muka yi aure. Iya shege! Ashe ya san me yake yi. Wato dama ya bar mini wannan ɗinne na yi abincin gargajiya da duk wata tsiyata. Idan ta failing ma nawa ne. Amma JK Foods za su cigaba da buɗe restaurants a wasu wajajen ko kuma su yi any food related business a gaba. To kuwa tunda na gano hakan ba zan bari wannan wajen ya yi failing ba. Wannan dama ce da zan nunawa kaina ba ma Jalal kaɗai ba cewa zan iya mallakar restaurant kuma na running ɗinsa successfully. Ni da Jide muka fara brainstorming sunan da za mu sakawa restaurant. Ni da can da nake ta lissafin zan buɗe restaurant sunaye biyu ne nake tunanin sakawa wajen. Ko CHEF ZEEY RESTAURANT ko kuma na yiwa Kakata kara in saka sunanta wato FATIMA ALTINE FOODS. Na fi jin zan saka sunan Kaka. To amma wannan wajen temporarily ne. Ba zan samu mallakarsa gabaɗaya ba har sai aurenmu da Jalal ya shekara kuma na gina wajen ya zauna da ƙafafunsa. So saka sunan Kaka a wajen ba zai yiwu ba. Balle ma yadda Jide ke ta nanata min mutanen da suke so su attracting masu kuɗi da middle class mutane ne. Dan haka na san ba za su yarda a sakawa wajen suna Fatima Altine ba. Amma Insha Allahu watarana zan buɗe ƙaramin restaurant da sunan Kaka. Jide yace tunda local cuisine za a riƙa serving mu nemi sunan da zai tafi da hakan. Shi gogan aiki da calls "kawai yake ta yi tun ɗazu. Ni ban ma san me yasa ya biyo mu ba, dan duk bayanin da muke bai sa mana baki ba. Occasionally dai za ka ga ya ɗago ya kallemu." "Sunan GIDAN ABINCI ne ya zo mini. Ina faɗa Jide yace perfect, sunan ya yi. Sai kuma ya ce ba ri ya duba" ko akwai restaurant mai irin sunan saboda kar a samu matsala. """Shit!"" Ya ɗan daki table" """Akwai irin sunan ko?""" """Wasu sun rigamu"" ya faɗa yana girgiza kai dan sunan ya masa daɗi." """What of GIDAN GIRKI?""" """Zeey, your brain is sharp ooo"" ya ɗaga min thumbs up. Na yi dariya." Dariyar dana yi ya jawo hankalin Jalal ya bar wayar da ya ke a can gefe ya taho inda muke zaune. Ya wani tambayi Jide cike da authority wai a ina muka tsaya?. Jide yace masa mun samo sunan restaurant. """So, what did you come up with?""" """GIDAN GIRKI"" na faɗa da ɗan ƙarfi dan ya san nina zaɓi sunan." """And sunan is available, Sir"" Jide ya jaddada masa." "Ya kalleni sannan ya kalli Jide ya ce ""Ku chanja""" Mu chanja?. Mu chanja a wani dalili?. """Sir, I think the name is unique, and it's suits the restaurant's core idea"" Jide ya fara masa bayani." """Gidan Girki yayi fa. Ko Jide?"" Na kalli Jide da ya fara rarraba ido tsakanin ni da Jalal." Da gangan na yi hakan. Akan me muna ta lissafi tun ɗazu bai sa mana baki ba yanzu kuma ya wani shigo wai a chanja sunan. "Jide ya ce ""I think za mu iya tsayawa zuwa Agnes ta zo gobe before we decide, hope it's okay by you" "Sir?"" Ya faɗa yana kallon Jalal." Jalal ya ɗaga masa hannu. Raina sai ya sake ɓaci. Ni fa ban gane deal ɗinnan ba. "Ta ya zai dinga yi mana katsalandan a duk abinda muke yi. Idan bai yarda da ni ba, kuma bai yarda da" "staff ɗinsa Jide ba, ai shikenan sai ya zauna yayi kayansa." Haushinsa ya sa na miƙe na cewa Jide ni zan tafi. Ma haɗu goben idan Agnes ɗin ta zo. Jide yace ba matsala. Har na fita bai yi kaman ya ji me nace ba. Ni anya ma za mu wanye lafiya da shi kuwa???. JAYKAY Jalal yana gani Ziyada ta ɗau jakarta ta fita. Me yasa take da taurin kai ne. "Why the fuck is she so comfortable with Jide, daga haɗuwar kwana ɗaya." First ta sake da shi suna taɗi a office. Then yanzu kuma sun haɗe masa kai. Shifa gani yake kaman sunan yayi local dayawa. So yake ta tsaya ta masa bayani kaman yadda ta zaƙe tana yi da Jide but sai ta ɗau jakarta ta fita. To wai mi yasa yake jin haushin sakewarta da Jide ne?. Jide dama ko a office haka yake faran-faran da mutane. Ita kuma she's just doing her job. But aiki yace ta yi ba murmushi ko dariya ba. Aiki kaɗai. Bin bayanta yayi dan ba zai bari ta tafi gida ita kaɗai ba. Da sauri ya fito ya shiga mota ya bar Plazar ya hangota tana tsaye tana jiran Keke. Dai-dai inda take ya tsaya. Yana gani tanata wani tsuke fuska irin ba zata shiga ɗinnan ba. "He waited. Patiently, ya jirata." Tun da ya haɗu da yarinyar nan take saka shi jira. Minti ɗaya ta yi tana masa jan aji kafin ta buɗe ƙofar ta shigo. Tana shiga ta fara magana. """Na shiga motan kane ne dan kawai kar mu tara jama'a, amma da ba zan shiga ba. Ehe""" Bai ce mata komai ba ta gama surutu har ta yi shiru ta juyar da fiskarta tana kallon window. So yake ta cigaba da magana dan hakan yana saka shi nishaɗi. """Gidan Girki sounds nice"" ya faɗa yana ɗan kallon gefenta." """Kan buhu. Sai yanzu ne ka san sunan is nice. Ba cewa ka yi mu chanja ba. Tun da safe sai wani masifa" "kake ta mana sai ka ce wani 'ya'yanka. Ai Wallahi Ɗan Yarabawa nan ma na ga haƙurinsa. Sai faɗa kake masa kaman wani ƙaramin yaro. Har da cewa sai wata Agnes ta zo kafin a tsayar da magana. Ba Agnes ba Agatha""." Ta yi shiru ta sake juyar da fiskarta. "Cikin ƙasan ransa murmushi yake. He loves to see her talk, koda kuwa masifa take." Those cute lips. Watarana sai ya yi maganinsu... CHAPTER TWENTY SEVEN ZEEY "Finally mai girma Yallaɓai Jalal Maiyaƙi Ɗan Hajiya Layla ya amince mu yi amfani da sunan dana zaɓa," "wato GIDAN GIRKI. Yau kwana uku kenan ni da team ɗina muna ta aiki. Agnes ta zo, kuma itama tana jin sunan da muka zaɓa ta ce ya yi." Ai dama na san son nuna mulki da iko yasa Jalal yace wai a chanja sunan. "Jide, shine aka barshi da bin procedure na registering sunan da CAC, da kuma trade marking ɗinsa. Ita" kuma Agnes ita ce take handling designing logo na restaurant ɗin da kuma setting social media pages da "sunan, saboda a nan zamu riƙa tallata restaurant ɗin idan aka buɗe." Ni kuma aka barni da creating Menu. Dukkanmu mun yarda akan Menu ɗinmu na breakfast da lunch "dama dinner ba zai yi yawa ba. Za mu fara da kaɗan, sai a gaba idan wajen ya karɓu sai mu ƙara wasu" abincin a Menu ɗin. Tunda Agnes ta fara zuwa Jalal ya dena biyo mu restaurant. Da safe dai zai aiko min Direbansa ƙarfe tara ya ɗaukeni ya kaini Plaza. A nan za mu haɗu da Jide da Agnes mu yi aiki. Kwana biyun nan ma har yamma muke kaiwa saboda aiki. Keke na ke hawa in koma gida duk da kuwa Jalal yace min idan na gama in kira shi zai saka Direbansa ya zo ya mayar dani gida. Amma ban taɓa kiransa ba. "Jide, Agnes kawai yake ɗauka a motarsa. Wai ba zai ɗaukeni a motarsa ba kar Oga Jalal ya koreshi a aiki." "Na ce masa akan me zai koreshi a aiki dan ya rage min hanya. Ya ce babu ruwansa, ai nima na san dalili." Ni kam ban san dalili ba. Har Agnes ta shiga maganar tana tambayata miye tsakanina da Jalal? Na ce mata babu. Nima ban matsawa Jiden ba wani lokaci ma ni nake rigasu tafiya. Ba yau na fara hawa Keke ba. Mu mutanen Ghetto dama ai Keke shine Jeep ɗinmu. Yau na kawo draft ɗin Menu da za mu yi amfani da shi a restaurant ɗin. Muka haɗu dukkanmu uku aka tattauna yadda komai zai kasance. "Ƙarshe aka cire wasu daga ciki, wasu kuma aka pairing ɗinsu da wasu side dishes ɗin saboda zai fi kawo" kuɗi. Next abinda za a yi shine Food testing. Zan girka duka abincin da muka selecting a Menu ɗinmu saboda su Jide da kuma anonymous tasters ɗin da aka zaɓa su yi rating abincin. "Za su rating komai, tun daga taste ɗin abincin, har zuwa plating da presentation ɗinsa. A wannan wajen" "ake so na nuna bajintata. Dan idan aka buɗe restaurant ɗin, abinci mai daɗi shi zai tafiyar da wajen." Ina da confidence akan na iya girki. Amma duk da haka sai da na ji wani ɗar da aka ce za a yi Food tasting ɗinnan. Muka rabu akan gobe za a kawo ingriedients zan dafa first batch na Menu ɗin sai na serving mutanen da za a gayyato su ci abincin. Food tasting ɗin zai ɗauki kwana uku. Dan haka kafin na tafi sai dana rubuta musu list ɗin abubuwan da nake buƙata da zai covering girkin da zan yi na kwana uku. Ina fitowa daga Plazar wayar Faty na shigowa. Ta fara ƙorafin wai gashi har an kusa resuming school amma ban kawo mata ziyara ba kuma ta ce na zo na mata ɗanwake a gidanta na ƙi zuwa. Haƙuri na bata na buge da tsokalarta Babynmu dai ke son cin ɗanwake ba ita ba. Yadda ta fara dariya tana wallewa ita bata da komai na fahimci da gasken ciki ne da ita. Na mata fatan alkhairi na ce ta yi haƙuri wani aiki ne ya riƙeni ba zan samu zuwa ba. Amma zan sa Kaka ta mata Ɗanwaken sai na sa yaro ya kai mata har gida. Ta ce ba matsala. Idan ba haka na yi ba kam bani da lokacin zuwa gidanta a yanzu da muke shirin kafa GIDAN GIRKI. "Da dare ina kwance akan gado amma bacci ya ƙaurace mini. Kaka kam ita har ta fara bacci, amma ni" gaba ɗaya tension ya sakani gaba. Sai lissafi nake. What if aka samu matsala suka ce ban iya girki ba. Tabbas idan waɗanda aka gayyato suka ci abincina suka ce bai yi ba na san Jalal sai ya yi min dariya. Cewa zai yi dama alfarma zai min amma ba zan iya running wajen ba. """Kaka"" na kira a hankali." """Kaka"" na ɗan ɗaga muryata ina taɓata" """Kaka dai""" """Na'amm"" ta faɗa da muryan bacci." "Matsowa na yi jikinta sosai na ce ""Kaka, miye sirrin sana'ar abinci?""." "Na yi tambayar ne saboda for the first time a rayuwata da nake dab da jagorantar restaurant, ina jin" tsoro. What if experience ɗina har yanzu bai kai na karɓi wannan aikin ba?. Tun farkon amincewata da deal ɗin Jalal na yiwa Kaka bayanin zan fara aiki. Ban faɗa mata deal ɗin dake "tsakanina da Jalal ba. Iya abinda ta sani shine, ɗan Hajiya Layla da nake zuwa gidanta na mata girki, ya bani aiki a restaurant ɗinsa a matsayin Head Chef. Wato kwacokam aikin abincin wajen yana ƙarƙashina." """Abinci hannu-hannu ne Ziyadatu. Ina da yaƙinin hannunki akwai albarka, duk abinda kika girka mutane" "za su ci su ji daɗinsa""" """Kaka, hannuna ba irin naki bane. Har yanzu fa idan na yi Tuwo baya daɗin naki""" """Ke kike ganin haka. Amma duk wanda ya taɓa cin Tuwon da kika yi ya san Altine Mai Tuwo ta samu" "Magajiyarta""" Na saka dariya. Yanzu data faɗi hakan sai na ji confidence ɗina ya fara dawowa. Ba zan iya tuna yaushe "na fara koyon girki ba. Idan ka taso a gidan da ake abinci tun kafin ka fara wayo zaka zama apprentice. Daga miƙo kaza, wanke kaza, daka kaza, juya kaza zaka fara, har a zo lokacin da za a fara sake maka kana yin wasu abubuwan da kanka." Ba zan taɓa manta shirme na farko dana tafkawa Kaka ba lokacin da nake tasowa. Ina JSS one lokacin. Kaka ta yi miya ta bari a wuta yana dahuwa sai ta ce na duba ko yayi lokacin zata shiga banɗaki. Dana taɓa miyar sai na ji kamar gishiri bai ji ba. Maimakon na faɗa mata sai kawai na je na ɗauko gishiri a leda na zo na kambaza a cikin miyar. Ai kuwa Kaka data zo bata taɓa ba ta sauke miya aka fara siyar da abinci. Sai gashi ba a jima ba mutane suka fara dawowa suna cewa gishiri yayi yawa a miyar. Kaka ta ɗanɗani miyar sai ta kalleni. Tun kafin ta yi magana na fara hawaye ina Wallahi Tallahi gishiri kaɗan na saka. "Kaka ta ce Allah ya kyauta. Har yau ban san me Kaka ta yiwa miyar ba, dan kuwa bayan ta gyara miyan" aka cigaba da siyar da abincin babu matsala har Tuwon nan ya ƙare tas ba a sake ƙorafin gishiri yayi yawa ba. Tabbas girki yana da sirri. Kuma sai yanzu nake ganin kamar har yanzu da saurana akwai abubuwan da ban sani ba. """Kin iya girki Ziyadatu"" Kaka ta jaddada mini." """Yau da gobe ai ba wasa ba. Gashi nan kin iya abincin zamani, har da su wannan pirayid rayis (fried rice)" "ɗinnan da kike mana""." Na fara dariya ina faɗin ai duk da haka ban kai ta iya girki ba. "Kaka ta ce ""babu wani sirri da zan baki Ziyadatu, sai abubuwa guda uku da uwata ta bani lokacin dana yi" "aure zan fara sana'ar Tuwo""" Ina jin batun sirri na buɗe kunnena da kyau. Na yi Islamiyya. Hadda ne kawai ban ƙare ba amma na yi saukan tartil kuma ba laifi kafin Boko da neman kuɗi su sakani na yaye Islamiyyar na yi nisa a karatun litattafai da dama. Haddar ma dai ba dan na dena zuwa ba da zan gamata dan na bawa izub arba'in baya. Dan haka sirrin addu'a nake tunanin zan samu a wajen Kaka ba wani abun da zai zama tsubbu ko shirka ba. Ban taɓa ganin Kaka da laya ko wani abu ba. Lokacin da nake ƙarama mutane babu abinda basa faɗa "akan Tuwon Kaka. Musamman Baaba Tabawa, Allah dai ya jiƙan rai. Har faɗawa mutane take wai Kaka ta busine layayoyi a gindin murhun da take sana'arta, shiyasa take samun sa'a." """Sirri na farko shine, ki tsaftace zuciyarki. Kada ki ce za ki dafawa mutane abinci da mummunan zuciya." "Manufarki akan mutane shine ki dafa musu abincin da za su ci, su ji daɗi. Ke kuma alkhairin da za a baki ya zamo halal ɗinki kuma silar samun rufin asirinki a duniya. Idan kika yi girki da mummunan zuciya za ki samu matsala, saboda muguntar da ke zuciyarki zai bayyana a abincinki""" Na yi shiru ina jinta. """Na biyu kuma ki tabbatar kin tsabtace muhallinki kuma ki riƙa amfani da abubuwa masu inganci. Idan" "nama zaki siya ki sayi mai kyau. Idan kayan miya ne ki tabbatar mai kyau kika siya. Amfani da kayan haɗi mai kyau da inganci wajen girki shine sirri na biyu da zan baki""" "Ta ɗan yi shiru bata sake cewa komai ba. Na ɗan leƙa fiskarta nace ""Kaka kin yi shiru baki faɗa min sirri" "na ukun ba?""" "Ta ɗan yi murmushi ta ce ""Na tuna Uwata ne. Murjanatu ikon Allah""" "Allah Sarki!. Kaka ma fa 'ya ce. Kafin ta haihu ta zama uwa. Kafin a haifeni na zama jika a gareta. Ita," Fatima Altine 'ya ce. Ɗiya ce ga Murjanatu mai Tuwo. Rayuwa kenan. """Sirri na ƙarshe shine sirrin BISMILLAH. Duk abinda aka fara shi da BISMILLAH to zai yi albarka. Dan haka," "a koda yaushe kika isa bakin murhunki za ki fara girki, to ki fara da BISMILLAH. An kawo miki kayan miya za ki gyara a kai markaɗe ne, to fara gyarawa da BISMILLAH. Abincin ne ya samu matsala kika ɗan yi dabarunki dan ki gyara shi, to ki haɗa da BISMILLAH. Wannan sirrin Uwata ta bani. Kuma shi na riƙe ake ta cewa Altine ta bisine layoyi a bakin murhunta. Ziyadatu ban san mecece laya ba. Ban gani a gidanmu ba, shima Malam dana aureshi ban ga laya a jikinsa ko a kusa da shi ba. Ban yarda da Boka ko Malamin Tsubbu ba. Sirrin BISMILLAH da kuma karatun FATIHA da aka bani shi na riƙe sama da shekara hamsin da na yi sana'ar Tuwo a gidan nan""" Na rungume Kaka da kyau ina mata godiya. "Daren ranan bamu yi bacci ba sai kusan ƙarfe biyu, dan bugewa muka yi da labari. Kaka ta yi ta bani" "labarin ƙuruciyarta, dama farkon aurensu da Kakana Malam Haruna. Har da irin matsalolin da ta rinƙa" "fiskanta a sana'arta musamman daga wajen kishiyarta, dama mahassada dake gefe." Wannan sai ya ƙara fahimtar dani duk sana'ar da za ka fara to ka riƙe Allah. Dan kuwa kana gefe kana neman kuɗinka wani can yana ta faɗi-tashi dan ganin ya ɓata maka sana'arka ko kuma ya riƙa yi maka mugunta har sai komai ya lalace. Tabbas sirrin kowanni sana'a shine yin riƙo da ADDU'A. Da safe da muka tashi sai na ji na tashi da wani sabon ƙarfi da kuma confidence. GIDAN GIRKI nawa ne. "Kuma ni Ziyada Sadiq Haruna aka Chef Zeey, zan tafiyar da shi bilhaƙƙi har a samu nasara." Lokacin dana fito daga gida sai na fara massaging goshina saboda kaina na mini wani nauyi. Har lokacin akwai ɗan bacci a idona amma mai neman Halal bai ga ta bacci ba. We move. "Na shiga mota na gaishe da Direban Jalal, muka wuce Plaza." Na yi mamaki da ban ga motar Jide ba dan kwana biyu yana rigani zuwa. Na shiga restaurant ɗin na ga "wayam babu Jide, babu Agnes, sai mutum ɗaya daya hakimce akan kujera hannunsa akan laptop yana typing da sauri." Me yake yi a nan yau da safe haka?. """Ina kwana"" na faɗa ina ɗan tsayawa. Ganin bai amsa ba, kuma bai min magana ba sai na wuce shi na yi" hanyar kitchen. To kodai yana cikin waɗanda za su judging abinci nane yau?. "Koma dai minene, ni babu ruwana da shi. Aiki zan yi da kyau na proving kaina cewa na deserving na" zama Head Chef a wannan restaurant ɗin. Ingredients ɗin dana buƙata jiya ne na gansu jibge a kitchen ɗin an kawo. Zaro wayata na yi na fara kiran "Jide dan na ji ko lafiya ba su iso ba har yanzu. Sannan kuma na tambayeshi yaushe mutanen da za su yi testing abinci za su iso, saboda na san da me zan fara." Ina kiransa kuwa ya ɗauka. Muka gaisa na ce na ji su shiru. """Oga ya moving Food testing ɗin zuwa gobe, bai faɗa miki ba?""" """Ni babu wanda ya faɗa min. Kuma ga shi ya sa an je an ɗaukoni daga gida""" Jide ya fara dariya. """Jide kana nufin ba za ka shigo ba yau kenan? Agnes fa?""" """Yau ke da Oga ne kaɗai, Zeey. Best of luck"" daga haka ya kashe wayar." Ɗan iska. Yanzu munafurcin da suka haɗa min kenan. Sun san an ɗaga abin nan suka sa na zo yau. Jakata da wayata na ɗauka zan fita daga kitchen fuuu sai cak! Na tsaya dan saura kaɗan na faɗa jikinsa. Ban san ya sako kai kitchen ɗin ba. Muka tsaya kallon juna. "Sai yanzu da ƙwayar idanunmu suka haɗu na fahimci ashe kwana biyu da ban ganshi ba, wani ɓangare" "na zuciyata yayi kewar ganinsa. A'a, ina nufin yayi kewan Bossy attitude ɗinsa." Maimakon ya matsa mini sai ya fara takowa kamar zai haɗe ɗan mitsitsin space ɗin dake tsakaninmu. "Na yi saurin ja baya kaɗan. Yana taku gaba, ina taku baya, har sai da bayana ya jingina da makeken kitchen isle dake tsakiyar kitchen ɗin." """Cook for me"" ya faɗa da wani Bossy tone" Na fara rarraba idanu. Me yake nufi?. """Kina tunanin zan bari ki yiwa wasu girki ne bayan ban taɓa tasting abincinki ba"" ya faɗa da wata" kausasashshiyar murya still idanunmu sarƙe cikin na juna. "Ina jin notinan kaina suna shirin kwancewa, zuciyata kuma tana tsananta bugu, na yi saurin girgiza kai na" matsa gefe da shi na ce """Sai ka bari gobe idan na yiwa mutanen da za su zo girki sai a fara zuba maka kai ka fara ci. Ai ba laifina" "bane. Sau biyu ina zuwa yiwa Hajiya girki har gida, me yasa ba ka ci abincin dana girka mata ba?""" """Hajiya kika yiwa girki ba ni ba"" ya faɗa yana ƙara matsowa kusa da ni." Ɗan batalikin nan fa ina ga matseni yake son yi a kitchen ɗin nan. "Na yi gyaran murya na ce ""Da Hajiya da kai duk ɗaya tunda gidanku ne. Kuma ai...""" """Shut up and cook for me, Zeeyadah""" Na sake baki ina kallonsa. He's so authoritative. """Kin cika surutu""" """Eh ɗin"" na faɗa ina murguɗa masa baki." To yanzu ni me zan dafa masa?. Mutumin da ya nuna baya son local abinci me zan dafa in burge shi ni Ziyada?. "Na ɗaga ido na kalleshi na ce ""Me kake so na dafa maka?""" """Duk abinda kika dafa zan ci""" Duk abinda na dafa zai ci. Sai na ji wani daɗi da ya faɗi hakan. """To, wani irin abinci ka fi so?""" """I mean koda ba abincin gargajiya ba. What's your favourite food?""" """Duk abinda kika dafa""" He's not helping... ta ya zan san me zan dafa masa idan bai faɗa mini irin abincin da ya ke so ba. """Kana son Tuwo?, Shinkafa?, Wake?, Spaghetti?, Yam?, Dankali?""" Inata lissafo abubuwa ya yi shiru kawai yana bina da mayataccen kallonsa. """Ni fa ban san me zan dafa maka ba. Idan ba ka yi magana ba Ɗanwake zan maka, Allah"" na faɗa ina ɗan" turo baki. """Just so you know, ban taɓa ci ba""" Na ƙwalalo idanu waje. Dama akwai Bahaushen da bai taɓa cin Ɗanwake ba?. Sai kuma na tuna ba kowa bane layin gidansu yake da kwatami. Wasu gidansu Estate ne a GRA. Dan haka "idan Jalal Maiyaƙi yace bai taɓa cin ɗanwake ba, ba abun mamaki bane. Ko Hajiyarsu ma ai ta bani labari wai sai da ta dawo Nigeria ta fara son abincin gida. Lokacin da ta yi zaman turai bata damu da cimar gida ba, amma wai mijinta na so." """Da gaske baka taɓa cin Ɗanwake ba?"" Na sake tambaya dan in san bai taɓa ci bane kwata-kwata, ko" kuma dai ya taɓa ci amma baya so?. "Ya ce ""Na san Ɗanwake. Hajiya da Jamal suna so. But I've never tried it""" """Tunda kake a rayuwarka baka taɓa ci ba?. Har lokacin da kake yaro?""" Ya girgiza kai. """Ko irin a gidan Kakanninkun nan?""" Ya sake girgiza kai. """Ikon Allah. Yanzu Dan Allah shekaranka nawa a duniya baka taɓa cin Ɗanwake ba?""" """Take a guess"" ya ɗaga mini gira." "Na ce ""35?""" Ya girgiza kai a hankali """36?""" Ya sake girgiza kai. """Da bakwai?. Da takwas?""" Nan ma ya girgiza kai. Ashe fa ba yaro bane na ke masa kallon ɗan 35. """Yanzu ka...ka...ka fi arba'in?""" Ya girgiza kai. """39?""" Slowly ya sake girgiza kai. """Yanzu shekaranka 40?"" Na faɗa ina ɗaga yatsuna huɗu." """40?... Ashe dai kai tsoho ne?"" Na fara masa dariya" """Cook, Zeeyadah. Kin cika surutu""" """A yi haƙuri Yallaɓai. Yanzu zan maka Chef Zeey's special Ɗanwake""" Na matsa da sauri na je wajen dana ga buhun 5kg Flour ɗazu. Na ɗauka na ajiye akan island ɗin. Zan haɗa garin Ɗanwaken from scratch ne dan babu ready-made garin Ɗanwake a kayan da aka kawo. Fita ya yi sai na ga ya dawo da system ɗinsa ya ajiye a saman kitchen island ɗan gefe da inda nake tsaye ina ƙoƙarin tankaɗe flour. Zama ya yi a wajen ya fara aikinsa. Nima sai na mayar da hankalina na cigaba da aikin da nake. Amma time to time ina ɗaga ido na leƙa shi. "He looked so handsome. And ba za ka taɓa cewa ya kai 40 ba. He looked barely 35 ma, shiyasa na ke" masa kallon Saurayi. Ashe babba ne. Idan na kalle shi sai na ji wani murmushi yana taho mini. Duk da dai shi masifaffe ne. Kuma wani lokaci "he's so full of himself, amma dai Jalal Maiyaƙi ya fara controlling wani ɓangare na zuciyata." "Bada shawarata hakan ya faru ba. Kuma na san idan ban bi a hankali ba, to ilahirin zuciyartawa ce za ta" "faɗa ƙarƙashin ikonsa. Kafin hakan ya faru, zan yi ƙoƙari na danne wannan sabon feelings ɗin dana ke ji a kansa. Idan ba haka ba. Duk ranan da muka yi aure muka zo rabuwa zan kasance cikin ƙunci. As much as na san cewa deal ne a tsakaninmu, ina fata wata ƙaddarar ta tabbatar da zukatanmu waje guda, har mu yi rayuwa iya ƙarshen rayuwarmu." "Ban san ina murmushi ba sai da naji ya ce ""why are you smiling?""" "Wani murmushin na sake yi kafin na girgiza masa kai, na juyar da fiskata daga kallonsa na mayar da shi" kan kwaɓin Ɗanwaken dana ke. JAYKAY Murmushi take yi. For a moment ya ɗauka ba shi ta ke kallo ba. Amma sai ya fahimci kawai ta yi nisa ne a kallon da take masa. As if abinda ke sakata murmushin yana da alaƙa da kasancewarsa a wajen. "Murmushinta looks so beautiful. Ji yake kamar ya tsayar da lokaci ya je inda take, and just hold her." "Shi yasa ba ya so ya ga tana yiwa Jide dariya. Saboda daga dariyarta har murmushinta, duk ya kamata a" "ce nasa ne, shi kaɗai." Zai iya biyanta ko nawa ne saboda kullum ta riƙa yi masa irin wannan murmushin. This killer smile da ya ke melting dukkan wani ice da ya rufe masa zuciyarsa tsawon shekaru. "With her, he feels so alive. Mantawa yake da ƙuncin rashin ɗan'uwansa. Mantawa yake da maganar" "Cassandra. Ganinsa yake a NAMIJI, da cikakken ma'anar da kalmar NAMIJI ta ƙunsa." Aiki yake amma ya raba attention ɗinsa gida biyu. Ɗaya yana drafting proposal na wani bid da yake son shiga na wani contract da Kamfaninsu ke nema. Sauran rabin hankalinsa kuma yana tracing kowanni "movement ɗin Ziyada. Yadda take sifting flour, yadda ta saka wasu abubuwa a cikin bowl ɗin har ta zo ta" fara kwaɓawa. "Akwai ɗan garin flour a saman hancinta da gefen kumatunta. Yana so ya mata magana ta goge, amma" "idan ya faɗa mata zai rasa damar ganinta a haka, messy...cute." CHAPTER TWENTY EIGHT ZEEY """Ga shi. Chef Zeey's special Ɗanwake"" na faɗa ina ajiye masa plate ɗin abincin a gabansa." "Ya kalleni sannan ya kalli abincin ya ce ""why not ki kira shi da My Jalal's Ɗanwake?""" """My Jalal's Ɗanwake kuma?"" Na faɗa ina ɗan hararansa." """Yeahhh"" ya ɗaga mini gira yana ɗaukan fork." """Sai ka yi kuma. Ni dai ka ci ka bani feed back"" na faɗa ina kallon yadda ya wani tsaya yana dibi-dibi bai" san ina zai fara ɗibawa ba. Ɗanwaken ya sha sautèd onions sai ƙanshi yake. Ga shi na dicing cucumber da tomato ƙanana. Ga boiled egg guda biyu dana raba gida biyu. Ga yaji dakan hannu dana taho da shi daga gida. Ni kaina ina ganin Ɗanwaken nan sai haɗiyar yawu nake dan ya yi ne. Na ɗauki cokali da ke gefe na ɗebi ɓangaren veggies ɗin na haɗa da ɗanwake da wajen albasan na miƙa masa cokalin dan ya karɓa ya ci. Gogan naku sai ya buɗe bakinsa yana jira in sa masa a baki. """Please, ka karɓa ka ci""" Ya girgiza min kai yana nuna mini bakinsa da yatsa. """Just this once"" ya faɗa yana wani narke min mayun idanunsan nan. Na yi saurin janye idanuna daga" "nasa na ce ""Gidan Girki baya feeding customer a baki, Mr Jalal""" "Na sake miƙa masa cokalin. Wannan karan sai ya karɓa yana faɗin ""baku da customer service mai kyau," "Chef""" Na yi masa murmushi ina kallon yadda yake taunawa. Dama idan mutum yana cin abinci yana kyau ne? ko kuma dai shi ɗinne hakan ke masa kyau?. Na girgiza kai ina adjusting tinanina kafin ya sake kamani ina masa kallon ƙurilla. """Do you like it?"" Na tambaye shi ganin ya sake ɗiban Ɗanwaken ya kai baki." Bai yi magana ba. """Dan Allah ka yi min magana. Ya yi daɗi?""" Ruwan dana ajiye masa ya ɗauka ya sha bayan yayi cokali uku. """It's very hot"" ya faɗa bayan ya ajiye ruwan." """Ba ka cin yaji kenan?""" """To ka ci nan babu yaji a wajen"" na faɗa ina juya masa plate ɗin dan ya ɗebi wajen da babu yaji." "Maimakon ya yi hakan sai ya ɗebi waje mai yajin ya sake ci. Wannan karan sai ya ce ""it's nice""" """Nice kawai?. Maybe saboda first time ɗinka ne amma Ɗan...""" """Shhhh!. Ki bar surutu""" Na yi shiru ina kallonsa har ya gama cin Ɗanwaken tas. """Ka ce it's hot gashi nan ka cinye ai""" "Ya tura plate ɗin gefe ya ce ""Idan za ku serving wannan a Menu please ku rubuta EXTRA HOT saboda" "mutanen da basa son yaji""" """Yajin fa kaɗan na sa maka"" na faɗa ina ƙoƙarin dishing Ɗanwaken dan nima na ji taste ɗin." Ina kaiwa baki na kalleshi. Tabbas yajin yana da zafi sosai. Sai yanzu ma na tuna ashe yajin ƙananun barkono masu faɗa na ɗauko. Dama na kan daka shi a gida saboda cin Ɗanwake da kuma Shinkafa da yaji. "Ga mai cin yaji wannan yajin is perfect, zai masa daɗi sosai. Amma wanda baya son yaji zai ji cewa yajin" ya masa zafi dayawa. I think maganarsa na kan hanya. Za mu sakawa wannan Extra Hot Ɗanwake a MENU ɗinmu saboda masoya cin yaji. Sai kuma a yi wani Simple Special Ɗanwake na marasa son yaji. "Na zauna na cinye ɗanwaken nan tas abuna. Ba mai yawa na yi ba, amma wanda na ci ya fi wanda na" zubawa Jalal. Na wanke abubuwan dana ɓata na goge wajen yayinda Jalal ya cigaba da aiki a Laptop ɗinsa. Time to time yana shan ruwa. Gora ɗaya da rabi ya sha kafin mu bar wajen. Na ce masa ya bari in dafa masa wani abun daban yace mini no need. The fact that ya yi complain ɗin zafin yajin sai na ji babu daɗi. Even though ya cinye abincin sai nake "ganin ya ci ne saboda kar na yi magana, ba wai dan yana so ba." "Mentally, sai na fara ticking list ɗin abubuwan da Jalal baya so." Number 1: Jalal baya cin yaji. Daga yanzu duk abinda zan bashi zai reflecting wannan. Shi ya kawo ni gida a mota dai-dai ana kiraye-kirayen sallar Azahar. Na fito daga motar ina murmushin abinda ya faɗa mini kafin na fito. Cewa fa yayi idan ya je gida zai faɗawa Hajiya na bashi one of her favourite food. Shine na ce masa sannu Ɗan Hajiya. Shi kuma ya kirani da Ghetto Girl. Cak na tsaya lokacin da Baffa Lawalli ya kira sunana. """Waye ya saukeki a mota yanzu, Ziyadatu?"" Ya tambaya yana bina da kallon tuhuma." """Dama kwana biyu an faɗa mini kullum sai wata baƙar mota ta zo ta ɗaukeki. To yau Allah ya kama ki, na" "gani da idona""" Na yi shiru ina jinsa. """Ba magana nake miki ba?. Ina kika je? kuma waye ya kawoki a mota?""" """Baba aiki fa na je yi, kuma Ogana ne ya rage min hanya"" na faɗa dan bana so Baffa Lawalli ya san Jalal" nake shirin gabatar musu. """Aiki a ina?""" """Aikin girki ne a wani restaurant"" na bashi amsa kai tsaye." """Yanzu ke da muka ce ki fitar da miji shine kika buge da aikin abinci a restaurant?""" """To Wallahi zan kira Adamu ya zo mu karɓi sadakinki a wajen Alhaji Nafi'u kawai mu huta. Tunda wasa" "da hankalinmu kike yi, ba auren kike so ba""" "Ina jin ya faɗi haka na ce ""To Baba ai wata ukun da kuka bani bai cika ba""." """Ina magana kina magana, Ziyadatu!"" Ya daka min tsawa." """Ka yi haƙuri"" na faɗa a hankali." """Ki wuce ciki. Bari na dawo daga Masallaci na kira Adamu. Ba za mu zuba miki ido ki ƙi aure ki zauna" "mana a gida ana zuwa ana ɗaukanki da mota ba""" Na wuce ciki ina faɗin ta Allah ba taka ba a zuciyata. Ina shiga gida Kaka ta tambayeni ya ta ga raina a ɓace?. Na ce mata Baffa Lawalli ne fa na haɗu da shi a ƙofar gida ya fara gaya min magana wai ana zuwa ana ɗaukata a mota. """Ki yi haƙuri. Zai wuce kin ji"" ta faɗa da sigar lallashi." "A wannan gaɓar na ga ya kamata na sanar da Kaka maganar Jalal, saboda ta bani shawaran yadda za a yi." Dan Wallahi bana so Baffa Lawalli ya shiga maganar aurena. Idan ya san Jalal yana da kuɗi Allah ne kaɗai ya san abinda zai yi. A taƙaice na faɗawa Kaka Jalal yana son aurena. 'Yar tsohuwar nan sai ta saka kabbara kamar wacce na ce mata zan je Hajji. Ta fara cewa wai tun cikin Azumi take ta min addu'ar Allah ya bani miji na yi aure bayan sallah. Har da cewa dama ta faɗa mini Ɗan Hajiya Layla yana sona. Kai! Kaka ma dai a gaisheta. """Kaka dama so kike na yi aure na barki ke kaɗai ko?"" Na faɗa ina turo baki." "Kaka ta ce "" ai tun ba yau ba na san watarana za mu rabu idan kika yi aure, Ziyadatu. Dan haka a shirye" "nake. Kin ga nan gidan mijina ne. Kema ina miki addu'ar Allah ya kaiki naki gidan mijin lafiya""" """To ni ba zan je gidan miji ba. A nan zan zauna"" Na faɗa ina shigewa jikinta." Kaka ta fara dariya tana faɗin gidan miji fa akwai daɗi. "Na ɗago na ce ""ba wani. Ke da kishiya ta hanaki jin daɗin miji""" """Wa ya faɗa miki?. Idan na kwaso gajiyar aikin Tuwo da dare idan Malam ya shigo sai ya ce mini, Fatima," "kwanta na miki tausa""" """Iyye!"" Na saka shewa." """Kice Kaka kin sha love a ɗaki""" "Kaka ta yi murmushi ta ɗan sosa kanta ta ce ""ba dan kyautatawar Malam gareni ba, da ƙunci ya kasheni" "a gidan nan. Ga mutuwar 'ya'ya ga masifar kishiya. Allah ya jiƙan Malam, ya haɗa fiskokinmu a Aljannah""." Na amsa da Amin. Ina jin hiran LOVE na manta da maganar Baffa Lawalli na buɗe kunnena da kyau ina shan labarin auren Kaka da Malam ɗinta. Ashe dai suma fa zamaninsu ana soyayya. Idan har bayan shekaru masu yawa da mutuwar miji ka ji mace na faɗin kyawawan halin mutum. To tabbas ya kyautata mata lokacin da yake raye. "Da wannan tunanin na fara tambayar kaina. Shin idan na auri Jalal, zai kyautata mini?." Ban sani ba. Lokaci ne kawai zai nuna wannan. Wajen ƙarfe tara na dare na turawa Jalal text akan Dan Allah idan baya komai ya kirani ina so mu yi magana. JAYKAY Jalal yana tareda Hajiya text ɗin Ziyada ya shigo. Yanzu ya gama faɗawa Hajiyar akan cewa sun "onboarding Ziyada ita zata zama Head Chef na restaurant da za a buɗe a cikin Plazar su. Lokacin da ya briefing ɗinta abubuwan da suka yi da kuma sunan da aka sakawa restaurant ɗin, sai Hajiya ta ce dama ta faɗa masa idea ɗin Ziyada yana da kyau. Ta ce masa Allah ya sa a buɗe a sa'a." Yana gama karanta text ɗin Ziyada ya yiwa Hajiya sallama ya baro ɗakinta ya nufi nasa ɗakin. Sai da ya gyara kwanciyarsa da kyau sannan ya kirata. Ciki-ciki ya ji sallamarta alamar itama a kwance take. """Ya aka yi Ghetto Girl. Sauro sun hanaki bacci ne?""" """Kutmelesi!"" ta faɗa daga ɓangarenta. Yana iya picturing yadda bakinta ya faɗi kalmar." """Ni ba sauro ya sa na kiraka ba. Kuma da kake maganar sauro, hala baka da labarin akwai Net. Ga" "mosquito coil. Har maganin sauro na shafawa a jiki akwai. Dan haka 'yan Ghetto suna da hanyoyin magance matsalar sauro""" Ta masa dogon bayani. Daga yanayin muryanta ya san a kufule take da shi. "Ba zai barta haka ba. He likes teasing her. Yana jin daɗi idan tana full ZIYADA mode ɗinta. Faɗa-faɗa," "sanyi-sanyi, da kuma full pride na inda ta fito." Tana burgeshi idan ta nuna masa tana alfahari da inda ta fito. Ya tsani ya ga mace ko ma namiji yana ƙyashin asalinsa. """Oh really! Duk saboda sauro kuka tanadi wannan?. Lallai mutanen Ghetto akwai su da dabara"" ya ƙarisa" maganar yana ɗan murmushi. """Sai ka yi kuma. Masu kuɗi ma suna kamuwa da Malaria. Ka ga sauro babu ruwansa da mai kuɗi ko ɗan" "Ghetto"" ta bashi amsa. Zai iya rantsewa sai da ta harareshi ta wayar." """Ni fa ba maganar sauro na ce za mu yi ba"" ta sake faɗa." """Ina jinki"" wannan karan sai ya cire wasa ya bata full attention ɗinsa." Ya riƙe wayar yana jin bayanin da take masa. So take ya kira Baffanta da ke Katsina ya gaishe shi ya kuma gabatar da kansa akan shine wanda zai aureta. A yadda ya fahimta. Ɗaya daga cikin Uncles ɗinta da ke nan Zaria ne ya sakata a gaba. """ ka ce masa Muhammad Jalal sunanka. Kada ka ce Jalal kaɗai"" ta faɗa masa." """Why?""" Ta yi shiru. """Kin musu ƙarya a kaina ko?""" """Ni ban yi ƙarya ba. Kawai dai ya fi son masu suna Muhammad ne"" bai yarda da bayaninta ba." Bayan ta gama yi masa bayani sai ya fahimci akwai pressure daga gida akan ta yi aure. That explains abinda ya sa ta amince da deal ɗinsa. Ba kawai saboda alƙawarin da yayi mata bane ya driving ɗinta ta amince da shi. Yanzu ya fahimci wani abu. Uncles ɗinta suna so ta yi aure. And luckily sai proposal ɗinsa ya zo mata a dai-dai. Koma menene. Lokaci yayi da zai ɗau next step akanta. Bayan sun gama wayar sai ya kalli numbar data turo masa. Baffa Adamun Katsina ta rubuta sai kuma numbar. "Bai kira numbar ba. Sai ya dannawa Ibrahim kira. Gobe Jummu'ah, akwai yiwuwar a garin Katsina zai yi" sallah... CHAPTER TWENTY NINE JAYKAY JALAL MAIYAƘI bai taɓa zuwa garin Katsina ba. Amma sai ga shi yau saboda mace ya shiga garin. A shekarunsa ya san cewa maganar aure ba maganar waya bane. Tunda Ziyada ta nuna masa Baffa Adamu shine Uba a gareta. To kuwa ya dace a ce ya je har gida ne ya "same shi su yi maganar face to face, ba wai ta waya ba." """Man, seriously ina taya ka murna. Kowa maganarka yake a family ka dawo ka tare gidan Hajiya kamar" "wani Gauro""" Ibrahim ya faɗawa Jalal lokacin da ya zo gida ya sameshi da safe kafin su taso. "Wato har gulmansa ake a family. Ba zai sani ba, tunda shi ba shiga cikin mutane yake ba." Da safen ya kira Baffa Adamu ya ce masa za su zo daga Zaria kan maganar Ziyada. Baffa Adamu was so happy da ya ji haka. Ya masa kwatancen gidansa tareda addu'ar Allah ya kawo su lafiya. Lokacin da suka shiga garin Katsina sai suka kira shi akan gasu nan ƙarasowa gidan. Ya ce musu yana kasuwa yanzu shima zai juyo su haɗu a can gida. Tarba na girmamawa mutumin ya musu. Da ka ganshi ka ga dattijon ƙwarai. Ibrahim ne ya jagoranci zuwan nasu inda ya gabatar da Jalal a matsayin manemin Ziyada kuma sun zo ne su yi gaisuwa sannan a basu dama za su turo magabatansu. """Kai ne Muhammad ɗin da 'yata Ziyada ta faɗa mana?""" "Jalal ya ji daɗin yadda Baffa Adamu ya referring ɗin Ziyada a matsayin 'yarsa. But, kiransa da Muhammad" tabbas akwai wani abu a ƙasa da bai gama sani ba. """Shine Muhammad Jalal ɗa ga marigayi Alhaji Kabeer Maiyaƙi"" Ibrahim ya faɗa tun kafin Jalal ya yi" yunƙurin magana. """ A'a!. Alhaji Kabiru Maiyaƙi namu na Zaria?""" """Shi ɗin dai, Baba"" Ibrahim ya sake bada amsa." """Allahu Akbar! Allah ya jiƙan rai. Alhaji Kabiru ai Yayane a garemu. Ikon Allah. Allah ya jaddada rahama a" "gareshi""" Jalal ya amsa da Amin yana murmushi. Tunda ya san mahaifinsa shikenan ba sai an yi wani dogon turanci ba. "Sai dai fa, sanin mahaifinsa bai hana Baffa Adamu yi masa tambayoyi masu zafi ba. Musamman da" "Ibrahim ya faɗa masa cewa yana da mata ɗaya Baturiya, da kuma yaro ɗaya." Bai ji haushin tambayoyinsa ba tunda duk uba na gari ya kamata ya yi bincike akan mutumin da 'yarsa za ta aura. Jalal ya tabbatar masa babu matsala. Yau kusan shekara uku kenan da dawowarsa Nigeria gaba ɗaya. "Kuma bashi da niyyar komawa London, sai dai ziyara. Matarsa kuma zuwa take sau ɗaya a shekara. Ba za a samu matsala ba." Bayan Baffa Adamu ya gamsu da bayaninsa sai ya ce masa a cikin satin da za a shiga zai je Zaria. Idan suka yi magana da sauran 'yan'uwansa zai kira shi ya bashi lokaci ya turo magabatansa. Jalal da Ibrahim suka masa godiya. Tare ma suka wuce masallacin Jummu'ah da Baffa Adamun. Da aka sauko kuma sai suka kama hanyar Zaria. "Sai da suka bar garin Katsina sannan Jalal ya fara tunanin ba dan Ibrahim ba, da ba zai iya tunkaran Baffa" "Adamu shi kaɗai ba. It feels different neman aure a Nigeria. Aurensa da Cassandra akwai banbanci sosai da wannan. Ya haɗu da Mahaifiyar Cassandra sau ɗaya kafin su yi aure. Kuma sun je ne dan su faɗa mata za su yi aure da kuma date ɗin auren, ba wai sun je neman yardarta bane." Mahaifinta Mr Morgan kuwa sai bayan an ɗaura aure ya haɗu da shi. Iyayen Cassandra sun rabu kuma a "hannun mahaifiyarta ta taso. Ba wani shiri take da mahaifinta ba shi yasa bata kai Jalal wajensa ba. Sai da Jalal ɗin ya takurata akan ta inviting Babanta zuwa ɗaurin auren sannan ta faɗawa Baban za ta yi aure. Mr Morgan bai samu halartar auren ba. Amma bayan an yi auren da suka haɗa family dinner suka gayyace shi, ya zo." "Imagine, sai bayan ka auri yarinya kake sanin waye mahaifinta." Har zuwa yanzu kuwa Jalal zai iya cewa bai fi sau biyar ya taɓa haɗuwa da Mr Morgan ba. Lokacin da "yake London yana ɗan kiransa su gaisa, amma dake shima mutumin ba wai ya damu da Cassandra bane balle shi mijin Cassandra: sai ya zamana Jalal ya ja baya da shi. Sai dai duk lokacin Christmas ko birthday ɗin Mr Morgan ya kan aika masa da gifts." "Yanzu ne Jalal ke experiencing auren macen da take da gata. Ga shi dai mahaifin Ziyada baya raye, amma" duk da haka sai da ya je ya gabatar da kansa wajen mutumin da ya ke matsayin UBA a gareta. "And despite akwai wata yarjejeniya a tsakaninsu. Ba zai iya auren Ziyada ba, sai iyayenta sun bashi ita." How beautiful... *** ZEEY A gajiye na dawo daga Restaurant. Yau na fara girka sample dake menu ɗinmu wa mutanen da aka gayyata. Na samu positive feedback daga wajen Judges ɗin da aka serving abincin. Su huɗu ne sai kuma Jide da Agnes da suma suka ci abincin. Ina zaune akan sallaya bayan na yi sallar Magariba ina ɗan scrolling social media sai na ji sallamar Baffa Lawalli. """Ina kike, Ziyadatu?"" Ya faɗa ko amsa gaisuwar Kaka dake ƙofar ɗaki bai yi ba." Na tashi da sauri zan fito ya sako kai sai na koma na zauna. """Ina wuni, Baba""" """Lafiya""" "Daga inda yake tsaye jikin ƙofa yace ""Dama ɗan gidan marigayi Alhaji Kabiru Maiyaƙi ke nemanki, shine" "kika ɓoye mana tuntuni""" Wayyo! Ba dai Baffa Adamu ne ya kira shi ya faɗa masa ba. Jalal ɗinma har yanzu bai kirani ya bani feedback na yadda suka ƙare da Baffa Adamun ba. """Shine kika tasar shi ya je har Katsina. Da kin turo shi gida ma ni da su Babanki Zakari mun yi maganar a" "nan""" Jalal ya je Katsina?. Kenan Katsina ya je ba kira yayi ba. """Yanzu abinda za a yi ki bani numbarsa mu yi magana. Nima zan sa a yi mini bincike akansa. Duk da ma" "dai ɗan Babban gida ne, amma mutumin da yayi rayuwar Turai dole a binciki halayyarsa""" Caɓ! Ni Ziyadatu in bawa Baffa Lawalli numban Jalal. Ba da ni ba. Yanzu sai ya kira shi ya fara roƙonsa kuɗi. """Baba, wayata ta mutu idan an kawo wuta zan rubuta maka numbar"" ƙaryar ta fito da kyau a bakina." Dan dai Wallahi da hannuna kam ba zan bashi numbar Jalal ba. """To babu matsala. Zan karɓa a wajen Adamun kawai""" Har ya fita ban dena Addu'ar Allah ya rabani da sharrinsa ba. "Da ke kwaɗayyaye ne, ku ji fa ko maganar Alhaji Nafi'u bai kawo ba. Saboda ya ji maganar wanda ya fi" Alhaji Nafi'un kuɗi. "Yau da Jalal ba shi da kuɗi da ya isheni da ihun Alhaji Nafi'u mutumin kirki ne, na aureshi." Yana tafiya na jawo wayata na kira numbar Jalal. Ni dana ce ya kira Baffa Adamu su yi magana a waya sai ya kwashi ƙafa ya tafi Katsina. Sai kuma na yi murmushi. Dan hakan da yayi ya burgeni. It means ya daraja Baffa Adamu. Wayarsa busy. Na ja tsaki ina tunanin ba dai da matarsa yake waya ba. Shiru-shiru har na yi sallan Isha Jalal bai kira ni ba. Na yi deliberating sake kiran numbar amma sai na ga missed call ɗayan ma ya yi. Idan na ƙara kiransa yanzu zai ce na damu da shi. Sai juyi nake akan sallaya da wayata a hannu na kasa taɓuka komai. Ko abincin dare na kasa ci. Inata kallon agogon wayar ina lissafta koma yanene dai ya ci a ce Jalal ya dawo daga sallar Isha. To ko dai yana cin abinci da su Hajiya ne?. Zai iya yiwuwa abinci suke ci. Barin sake bashi 30 minutes na ga ko zai kira. Na ɗan lafke kaɗan ko minti talatin ɗin zai cika da wuri. Amma ko minti biyar ban yi da rufe idanuna ba na sake buɗesu na jawo wayar. Still Jalal bai kirani ba. After like 20 minutes na kasa haƙuri na sake danna masa kira. Ba wai na damu da shi bane. Kawai ina so in tambayeshi ya suka yi da Baffa Adamu ne. 9:27pm amma bai ɗau wayar ba. To me yake yi?. Sai kuma na shiga Whatsapp dan in duba ko yana online. Ai kuwa gashi nan numbarsa yana reading online. Kutmelesi! Wato manna min hauka zai yi. Ashe yana kusa da wayar ya ƙi ɗaukan wayata. To ai shikenan. Dama ni ce na damu da shi. Ya je ya yi abinda ya ga dama. Afterall auren ma deal ne. It's not like soyayya muke balle na ji haushinsa dan ya ƙi kulani. Na kifar da wayar a ƙirjina ina faɗin ko ya kira ba zan ɗauka ba. Haushinsa dana fara ji sai ya sakawa zuciyata zafi. Na kasa yin komai. Ina dai kwance ko wayar na dena dubawa. Wai miye matsalata da Jalal ne?. Why does it hurt dan kawai bai ɗau wayata ba?. Jalal ne fa. Babu komai a tsakaninmu. Muna so mu yi aure ne saboda mu cimma buƙatunmu. It's just a "deal, a marriage of convenience. Nothing more." Kiransa ya shigo exactly 10pm. Ina ɗaga wayar da na ga sunansa na ce ba zan ɗau kiran ba. Ƙoƙarin ma "kashe kiran nake amma mistakenly hannuna ya ɗau kiran. Okay, ba mistake bane. Na dai ɗauka ne dan na ji me zai faɗa." """Miss me?""" """Miss you how?"" Na turo baki kamar yana gabana ""ni fa na kira ne saboda in ce maka an ce ka je" "Katsina...""" """Ance na je Katsina, ko kuma na je Katsina?""" """Ni ina zan sani. Ba cewa na yi ka kira numbarsa ba. Ni nace ka je ne?. Ni ban ce ka je har Katsina ba""" """Sunshine, kina da rigima""" "Ya Ilahi, ya sake kirana SUNSHINE. Why???." """Okay, na je Katsina""" Na yi shiru ina jiran ƙarin bayani. "Jin yayi shiru kuma na ƙosa na san how far, sai na ce ""me Baffa Adamun ya faɗa maka?""" """Ce mini ya yi an miki miji da wani Alhaji Muhammad. Dan haka na yi haƙuri kawai""" "A ɗan tsorace na ce ""Dan Allah abinda ya faɗa maka kenan?""" """Ba ke kika ce musu za ki turo wani Muhammad ba. To ai Muhammad ɗin ya rigani zuwa""" Na shiga uku. Ba dai Yaya Aminu bane ya je Katsina wajen Baffa Adamu. "Kai, da ya je ai Baffan zai kirani." "Kai, Yaya Aminu ba zai min haka ba tunda na faɗa masa maganar Jalal." """Ya kika yi shiru?. Tunda an miki miji, our deal is off""" """Dan Allah ka dena wasa. Da gaske Baffa Adamu ne yace maka an min miji?"" Na yi maganar hankalina a" tashe. """Bayan ni akwai wanda kika tura ne?""" """Ni ban tura kowa ba"" na faɗa da ƙarfi har da tashi zaune." """To faɗa min, waye Muhammad?""" Ya Ilahi! Yanzu shikenan zai san sirrina. Na yi shiru ban bashi amsa ba. """Ina jin ki""" """Sai ka fara faɗa min yadda kuka yi da Baffana kafin na faɗa maka""" "Ɗan murmushi ya yi sannan yace ""kin san shekara nawa na baki kuwa? To na fiki wayo""" Tsoho kawai. na faɗa a zuciyata. """Faɗa min. Who is Muhammad?""" Tunda an kamani dai gara na fayyace masa komai. Idan magana ta yi magana ma zai iya gano komai da kansa. Bayan na faɗa masa yadda su Baffa Lawalli suka tsareni har na yi musu ƙaryar ina da saurayi Muhammad. "Sai yace ""ba ƙarya kika yi ba""." """Actually, Registered name ɗina, Muhammad Jalal Kabeer Maiyaƙi ne""" """Aww!""" """Barin turo miki wani abu." Yana faɗin haka sai na fara jin muryarsa a background yana tambayar ina ya saka folder ɗinnan ne. Har kusan minti biyar yana dibi-dibin neman wani abu. Sai chan ya ce na shiga whatsapp ɗina. Ina dubawa sai na ga hoto ya turo min. Na buɗe hoton. Hoton jariri ne kwance a gadon Asibiti. A jikin gadon yaron an rubuta suna MUHAMMAD J.K. MAIYAƘI sai kuma date ɗin da aka haifeshi. Allah Sarki! Ashe a Azumin da ta wuce nema ya cika shekara 40. Da gangan na tura masa chat. 'Wannan ɗin waye?' 'Muhammad ɗinki' ya turo min reply. Wani dariya na saka. Jalal ɗan duniya ne. Allah. Kan kace me haushinsa dana ke ji ya ɓace ɓat. A maimakon haushi sai na fara jin wani abu yana motsi a ƙasan zuciyata. No. It cannot be. Ba dai... CHAPTER THIRTY JAYKAY Ƙwanƙwasa ƙofar Jalal aka yi da sassafe ne ya saka shi farkawa daga baccin da ya ɗan fara bayan ya dawo daga sallar Asuba. """It's me, Janan""" Yaye duvet ya yi ya sauko daga kan gadonsa yana mamakin me ya faru Janan take ƙwanƙwasa masa ƙofa da sassafe haka. It's 6:11AM. Yau Saturday. Shima ba zai fita site ba sai 9 koma 10 haka. Bai kwanta da wuri jiya ba so yana so ya ɗan samu baccin safe kaɗan kafin ya fita. Yana buɗe ƙofar ta tura shi ta shiga ɗakin """Me ya faru? Kin yiwa Hajiya laifi ko?"" Jalal ya tambaya bayan ya rufo ƙofar ya dawo cikin ɗakin." "Janan ta zauna a bakin gado ta ce ""'ban yi faɗa da Hajiya ba. Magana nake so mu yi""" """Shine kike buga mini ƙofa this early morning. It better be good. Me ya faru?""" "Sai da ya zauna kusa da ita sannan itama ta gyara zamanta ta juyo ta fuskance shi ta ce ""What's" "happening tsakaninka da local Chef ɗinnan?""" """What do you mean?"" Jalal ya yi tambayan kaman be san me take nufi ba." """Bro, da idona na ganku kun shiga mota tare. Shekaranjiya na je in duba aikin da ake a Plaza na ga kun" "fito daga cikin Restaurant, Driver ya baka key ka driving motar""" """Oh! Dama abinda ya hanaki shigowa kenan?. I saw your car. Ban miki magana bane kawai""" """It's not what I'm thinking, right?"" Ta faɗa tana waro idanunta waje." Ganin Jalal ya yi shiru bai kulata ba. Ta sa hannu a baki tana faɗin """Don't tell me... yanzu nemanta kake?. Like, gwara maka wata lowlife daga God knows where da" "Saudah?. Our Saudah fa""" """Abinda ya sa kika katse min baccina kenan?""" """Yaya you mean da gaske ne?. Hajiya ta sani?""" """Yau zata sani""" """Yaya J please don't do this. Yarinyar nan tun sau ɗaya dana ganta na san Gold digger ce. She wants your" "money. Ban san a ina Hajiya ta jajuɓota ba but Zaria girls are not nice""" """Ba ajinka bane, yaya. Ni i'm not happy da kai da Hajiya kuka bata restaurant. But this, this relationship" "ba zan...""" """Ba za ki amince da shi ba?"" Jalal ya katseta." """Yaayaa!"" Ta kira shi kaman za ta yi kuka." """I appreciate your concern little Sis"" ya patting ƙafaɗarta." """But, kar ki manta cewa I am entitled to date any girl I want""" Girgiza kai ta fara yi. Dan kwata-kwata Ziyada bata kwanta mata ba. Tun ranan da ta ganta a Kitchen tana aiki ta ji yarinyar ta mata local dayawa. """Yaya Jalal ba zaka gane ba...""" """I knowww. I appreciate it""" """This feels wrong. I won't be a party to this gaskiya."" Ta janye hannunsa daga jikinta ta juya masa baya" tana ɓata fuska. Kuka biyu ke cinta. Ga shi Jalal ya dumping best cousin ɗinta kuma ƙawarta ƙut da ƙut. Ga kuma maimakon ya zaɓo wacce ta fi Saudah ko kuma wacce take dai-dai da ita sai ya je ya zaɓo wata wadda bata kai class ɗin gidansu ba. For God sake. Mi Jalal ya gani a wajen yarinyar nan. """Sorry, little Sis"" Jalal ya kai hannu zai riƙeta." """Don't little Sis me"" ta buge hannunsa." The moment ta yo kwana da motarta ta ga Jalal yana yiwa yarinyar nan murmushi. Har kuma ya karɓi key ɗin mota ya ɗauketa a motarsa ta san abinda ke tsakaninsu ya wuce maganar aikin Restaurant. Jalal ɗin da ta sani wanda baya sakewa da mutane tun a da can ma balle yanzu shine ya sake da yarinyar nan. Dole akwai wani abu a ƙasa. Tun jiya ta ke so ta tambayeshi sai aka ce mata ya yi tafiya. Shi yasa yau tace bari ta titsiyeshi a ɗaki da safen nan kafin ma yace zai fita. """Yaushe Khalifah zai dawo?""" "Jin bata amsa ba sai ya ce ""ko dai mu ɗaga date ɗin aurenku sai nan da shekara biyu ne?""" """You dare not, Allah. """ Dariya ya saka mata. Ta fara shagwaɓa tana faɗin ya dena mata dariya. Sai da ta tashi za ta tafi sai ya kira sunanta. Cewa yayi ta dawo ta zauna. """Promise me, Cassandra ba za ta san maganar nan ba. Not now, not later""" """Hoho! So you're cheating behind her back kenan. Allah ya kamaka""" """Technically I'm not cheating, tunda ni mijin mata huɗu ne""" """Tell that to the Court idan Cassy ta sueing ɗinka for bigamy"" Janan ta faɗa tana dariya." """I'm serious, Jan""" Ta yi shiru tana riƙe chin ɗinta. """Ka bribing ɗina sai na yi shiru?""" """Janaaan""" """Ka bribing ɗina fa. Idan ba haka ba yanzu zan kirata""" """Me kike so?""" """A new car and...""" """Babu AND, Janan. I'll get you a new car. Shikenan""" """Hmm!""" """Je ki kwanta. Just keep this a secret, Please"" ya yi maganar yana turata." Ta fita tana faɗin idan bata ga sabuwar mota ba zuwa ƙarshen wata zata fallasa sirrinsa wa Cassy. Lokacin da Janan ta fita sai ya ji baccin dake idanunsa ma ya washe. "The more maganarsa da Ziyada yake matsowa kusa, the more yake tsoron yadda za a yi yayi wannan" auren low key ba tareda Cassy ta sani ba. The only two people da za su iya kiran Cassy direct su faɗa mata sune Janan da kuma ɗansa Junior. Idan "magana ta tabbata zai kira Junior ya faɗa masa komai sannan ya roƙe shi kada ya faɗawa Mamansa auren da zai yi. Junior is a good kid, ya san zai fahimce shi." Bayan waɗannan biyun baya tunanin akwai wani a cikin familynsu da yake da direct access da Cassy. Hajiya dai ba za ta kirata ba. Cassy bata cikin any of the Maiyaƙi family groups da suke da shi. Ita yaushe ma ta damu da 'yan'uwansa balle ta yi mu'amala da extended family ɗinsa. Tunda take zuwa Nigeria ma ko family house bai taɓa kaita ba. Iya kacinta wannan gidan. Baya son ƙananan maganganu shi yasa ya avoiding introducing ɗinta ga sauran 'yan'uwansa. Yawan zuwan da Junior ke yi family house ɗinne ma yake tunasar musu da cewa Jalal fa Baturiya ya aura. Fatansa dai komai ya tafi dai-dai kada a samu matsala. Idan ya samu ya auri Ziyada zai maida hankalinsa wajen neman yadda za a yi ya saki Cassy ba tareda ya rasa custody ɗin ɗansa ba. Idan har yana son zaman lafiya dole ya saki Cassy ya mayar da hankalinsa kan wata macen daban. Touching a woman once or twice a year is not good for his health and mental wellbeing. He's 40 not 60. Har yanzu da ƙarfinsa. Infact yanzu ma yake jin sabon ƙarfi yana zuwan masa. And yadda waccar yarinyar take terrorizing mafarkinsa he can't help but feel attracted to her. Ba zai ce "so bane, dan bai san so ba. But, in a longest time ita ce mace ta farko da yake jin yana son tarayya da ita." Kullum ya ganta sai yayi fantasizing kissing ɗinta. That's how badly attracted to her yake. "Infact, attraction ɗin da ya ke ji akanta ya fi wanda ya ji a lokacin da ya haɗu da Cassy shekaru kusan" "shabiyu da suka wuce. Cassy kuskuren ƙuruciyarsa ce. Over the years ya ɗauke hankalinsa akan mata especially saboda yana tsoron kada abinda ya faru da Cassy ya maimaita kansa. He was faithful to Cassy. Akwai temptation da suke zuwa dayawa, amma ya discipline ɗin kansa ta yadda bai sake biyewa son zuciyarsa ba. Ko kuma ya faɗa tarkon matan da suke kawo masa hari." Amma yanzu akwai macen da take chaza masa kai. Tana ƙoƙarin yin fatali da duk wani wall da ya ginawa kansa akan mu'amala da mata. *** Shiru ne ya mamaye ɗakin. Ba za ka ce akwai mutane biyu a zaune a ɗakin ba saboda sun ja sun yi shiru. Babu wani cikinsu da ya sake magana tun bayan da Jalal ya faɗawa Hajiya yana neman auren Ziyada. "At first bata gane Ziyadar data sani yake nufi ba. She innocently asked. "" 'yar gidan waye?""" Sai da ya mata ƙarin bayani ya ce Chef Zeey. New Head Chef na Gidan Girki Restaurant. Sai ta yi shiru. Shirun ne har yanzu. He thought Hajiya liked Ziyada. Me yasa ta yi shiru?. Infact idan ka cire nasa sirrin da yasa ya approaching Ziyada da deal ɗinsa. Kasancewar Hajiya na son Ziyada shine dalili na biyu da yasa ya nemi aurenta. "But, why is she quite?" Ko dai itama tunani irin na Janan take. Na cewa Ziyada ba class ɗinsa bace. """Ka bata aiki ne saboda ka fara sonta?""" Hajiya ta yi tambaya bayan dogon shiru. """No"" ya amsa a taƙaice." A gaban Hajiya baya iya dogon bayani. Musamman ma da yake gaba ɗaya maganar aurenma saboda Hajiyar ne. """Da kanta ta amince da kai, ko dai takura ka yi?"" Hajiya ta sake jefo wata tambayar." """Da yardarta"" ya bata amsa a taƙaice." """To. Allah ya shige mana gaba ya tabbatar da alkhairi""" Jalal ya amsa da Amin. """Zan je Abuja gobe. Idan na dawo cikin satin nan sai ka kawota mu gaisa""" """It's Alright. Za a yi hakan""" Daga haka ya miƙe ya bar ɗakin Hajiya da take ta faman adjusting ɗin reading glass ɗinta tana karanta wani abu a wayarta. *** ZEEY Yau Monday na gama aikin food testing. Feedback ɗin dana samu ya sa muka zauna da su Jide aka gyara Menu ɗin. Yanzu final approval muke jira daga wajen Jalal sai Agnes ta designing Menu card ɗin a yi printing. Ga shi Monday mai zuwa za a resuming school ga kuma staff training za mu fara ranan Laraba. Shikenan fa aiki kan aiki. At this rate na san za a buɗe wajen a exact lokacin da Jalal ya saka. Ina zuwa gida tun ma ban shiga sashenmu ba nake jin wai Baffa Adamu ya zo. Sai na ji gaba ɗaya kunya ya rufeni. Yanzu fa wai 'yar ni ɗinnan ce na tura namiji wajensa. Na shigo ina tambayar Kaka tun yaushe Baffa Adamun ya zo ta ce min kafin la'asar ya shigo. Na san bada jimawa ba zai nemeni dan haka a gurguje na yi wanka na yi alwala na yi sallar la'asar na zauna a Sallaya ina jiran Magriba ta yi na tada ita. Wajen ƙarfe takwas da rabi na dare sai ga kiran Baffa Adamu ya ce in zo in samesu a gidan Baffa Mamman. Dama da hijabi a jikina kawai na ɗau wayata na yiwa Kaka magana na fita. "Wannan karan su huɗu ne, har da Baffa Zakari. Ina ga yana off ne a aikinsa." Na zauna a kan carpet na jingina da jikin kujera one seater dake falon. Shi kaɗai ne babu mutum akai. Na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsuna. Yau fa ake yinta. Iyayena huɗu sun sakani a gaba ana maganar aurena. Ni ZIYADA wai zan yi aure. Ikon Allah!. Tunda muka rabu da yaya Aminu na dena kawo wannan lokaci a raina musamman a kusa haka. Abinda ke gabana dama shine na kammala karatuna na nemi kuɗi. Soyayya. Aure duk zai zo daga baya. Baffa Lawalli da Baffa Adamu sune yayun Babana. Baffa Zakari da Baffa Mamman ƙannen Babana ne. Amma tsakanin Babana da Baffa Zakari ance bai fi shekara ɗaya da rabi ba. Bayan an buɗe zaman da addu'a sai Baffa Adamu ya fara gabatar da jawabi akan Jalal Maiyaƙi ya je gida ya sameshi da maganar aurena. Kuma ya faɗa masa ya dakata idan ya yi magana da sauran iyayen Ziyada zai kirashi ya bashi lokacin da zai turo magabatansa. Ya kalleni ya tambayeni ko nina turo Jalal Maiyaƙi wajensa?. Wait! Dama haka ake yi?. Sai a tambayeka ko kai ka turo mutum. Na yi shiru ina neman amsar data dace na bayar da ba za a ce na yi rashin kunya ba. """Ba tambayarki ake miki ba?"". Baffa Lawalli ya faɗa ." Ashe dai na daɗe ban bada amsar ba. Dukkansu huɗu suka zubo min idanunsu. Har Baffa Mamman sarkin taɓa waya ma ni yake kallo yanzu. """E, nine"" na faɗa da wata siririyar murya." "Baffa Adamu ya ce ""Masha Allahu""." Sai kuma ya kira sunana da sigar da ya fi kirana musamman lokacin da nake yarinya. """Ziyadatun""" """Na'am"" na amsa idona na kallon ƙasa." """Kin amince mu bawa Jalal Maiyaƙi aurenki?""" Tashi ɗaya sai na fara jin dif-dif-dif. Ashe zuciyata ke bugu. I thought it will be simple. Ni da bakina nace na amince da deal ɗin Jalal. Amma yanzu da abin ya fara zama serious. Yanzu da maganar ta tashi daga tsakanina da Jalal ta koma gaban iyayena sai ma'anar aure ya fara zuwan mini. "Shin, ni Ziyada na amince zan auri Jalal Maiyaƙi, knowing cewa babu soyayya a tsakaninmu?" "Shin, ni Ziyada Sadiq Haruna na amince zan auri Jalal Maiyaƙi da sanin cewa zai iya rabuwa dani bayan" "shekara ɗaya, highest biyu?." Ya Ilahi! Wani irin tunani nake na amince da deal ɗin Jalal?. What was I thinking?. No. It's too late to back out. Yanzu da waɗannan iyayen nawa suka zura mini idanu suna jiran amsata ba zan iya cewa a'a ba. "Idan na ce A'a tabbas maganar Alhaji Nafi'u ce za ta sake dawowa. Ni kuma dana auri Alhaji Nafi'u, gara" na auri Jalal koda na wata shida ne. """Na amince""" Two simple words kenan da za su tying ɗina da Jalal Maiyaƙi. Na san bayan wannan zaman duk wani zama ba za a sake kirana ba. Na san duk wani shiri ba za a sake jin ra'ayina akai ba. Sune za su shirya komai. Sai dai kawai a faɗa mini abinda aka shirya. Sallamata suka yi. Suka cigaba da tattaunawarsu. Na san daga baya zasu faɗa mini ranan da iyayen Jalal za su zo. NA AMINCE dana faɗa a karo na biyu ya sake tabbatar da deal ɗina da Jalal. Abinda zai sealing komai shine idan aka ɗaura aure. Which na san su Baffa ba za su saka da nisa ba. Ya Allah!... CHAPTER THIRTY ONE JAYKAY Ƙarfe tara ne na safe. Tun ƙarfe takwas da rabi suka shiga meeting. Basu fito ba sai ƙarfe goma da rabi. Jalal yana fitowa daga meeting room ɗin kenan Jide ya tsareshi yana tuna masa maganar Menu. Har yanzu bai basu final go ahead ba. Sai da Jide ya yi maganar ne ya tuna ashe fa bai buɗe file ɗin da Jiden ya bashi ba tun ranan Monday. """I'll get back to you kafin a tashi""" """Yes, Sir"" Jide ya faɗa yana sara masa." Lifter Jalal ya shiga ya wuce 7th floor inda office ɗinsa yake. Dan a ƙasa aka yi meeting ɗin. Yana shiga office ɗinsa da ya zauna sai ya fara ɗaɗɗaga files ɗin dake wajen har ya kai wanda aka rubuta JK Foods a jiki. Ya buɗe Menu template da kuma samples ɗin design ɗin da Agnes ta yi. Sunayen abinci da kuma price ɗin da aka saka ya fara dubawa. "Jide ne ke da alhakin setting price point ɗin ba Ziyada ba, dan haka ya ga an capturing standard mai kyau." Gidan Girki zai riƙa serving luxury Abincin Gargajiya ne ba wai irin price point ɗin roadside Bukka restaurant ba. Sama-sama yake dubawa saboda akwai tarin ayyuka a gabansa. Wani suna ne ya ɗauke masa ido. Ya karanta sunan abincin a fili *MJ's Hot Ɗanwake*. Murmushi ya suɓuce masa. Sunan da ya ce ta sakawa Ɗanwaken data bashi ranan ne. MY JALAL's ƊANWAKE. Shi wasa yake mata. But ga shi ta ɗau abin serious. Abinda bai tabbatar ba shine. Ta saka ne saboda ta ɗauka da gaske yake maganar sunan. Ko kuma ta saka sunan ne saboda ta yarda shi ɗin JALAL ɗinta ne?. Ya rufe file ɗin yana murmushi. Jiya Talata Malam Adamu ya kira shi ya faɗa masa an bashi dama ya turo magabatansa ranan 27 ga "watan da suke ciki, wanda ya kama saura kwana 16 kenan." In 16 days Uncles ɗinsa za su je su kai sadaki. That's the plan. "Ba ya so auren ya ɗau lokaci. Tunda ba wani celebration za a yi ba, zai fi so a saka komai nan kusa." Bayan ya tura file ɗin JK Foods gefe sai ya buɗe system ɗinsa ya fara karanta wani report da Sakatariyarsa ta turo masa. Yana cikin dubawa aka kira Telephone ɗin office ɗinsa. "Ya ɗau kiran. ""Yes?""" Daga ɓangaren Sakatariya ta ce masa ga wani tsoho ya dage yana son ganinsa wai sirikinsa ne. Siriki kuma? Sun gama magana da Malam Adamu tun jiya ai. Who could it be? "Sakatariyar ta ce ""Ya ce sunansa Lawan Haruna""" """Ki ce ya shigo"" ya bata umurni yana tunanin ɗaya daga cikin sauran Uncles ɗin Ziyada ne." Wani ƙyamusashshen Tsoho ne ya shigo office ɗin. Kallo ɗaya ya masa ya ga kamanni tsakaninsa da Malam Adamu. Sai dai wannan ya fi Malam Adamun tsufa da ƙyamushewa. Miƙewa ya yi dan baya karɓan baƙi a office desk ɗinsa idan ba business ya kawo su ba. """Bismillah"" ya nunawa Baffa Lawalli wajen da kujerun zama suke. Jalal ya zauna a seater ɗaya ya ɗaura" "ƙafa ɗaya akan ɗaya. Baffa Lawalli kuma ya zauna a two seater dake kallon kujerar Jalal. Sai wani zazzare idanu yake yana ƙarewa office ɗin kallo, yana buɗe haƙura yana faɗin Masha Allahu. Haƙoransa duk sun ɓaci da cin goro." """Ranka shi daɗe, Alhaji Jalal. Na san baka sanni ba""" Jalal ya bishi da ido. Ko ba a faɗa masa ba ya san wannan ne Uncle ɗin Ziyada da take yawan magana akansa. """Sunana Malam Lawal Haruna. Ni wan Malam Adamu Haruna dake Katsina ne. Mune iyayen Ziyadatu""" yai maganar yana wage haƙura. """Sannu da zuwa, Malam. Me zan sa a kawo maka?""" """Lah! Babu komai. Ai gaisuwa ce ta kawoni""" Jalal ya ciro wayarsa ya kira Sakatariya ya ce a kawowa baƙonsa ruwa. Baffa Lawalli ya yi shiru yana kalle-kalle har sai da aka kawo masa ruwa da drinks mai sanyi sannan ya fara bayani. """Dama na ce tunda baka samu zuwa can gidana ba barin kawo maka ziyara mu gaisa kafin Magabatanka" "su iso""" """Nagode, Malam. Allah ya ƙara lafiya"" Jalal ya faɗa dan bai san me zai faɗawa wannan mutumin da ya zo" masa office babu notice ba. Ganin Baffa Lawalli ya buɗe Maltina ya fara sha sai Jalal ya buɗe tab ɗinsa ya cigaba da aiki dan tab ɗinsa is connected to his laptop. Yana iya yi aiki da kowanne. """Na ce idan babu damuwa akwai 'yar matsalar data kawoni wajenka""" "Jalal ya ɗan raising idonsa ya kalle shi. Sai kuma ya ce ""Bismillah""" "Baffa Lawalli ya gyara tsohuwar hularsa ya fara bayani. ""Dama akwai wani manemin Ziyadatu da suka" "jima tare. To a baya-bayan nan sai ta ce ta dena ra'ayinsa, ta ce mana kai take so""." """Yes?""" """To gaskiyar magana dai akwai wasu kuɗaɗe da Alhaji Nafi'u yake bina. Ba ni kaɗai ba shima Zakari ya" "karɓi aron wasu kuɗi a wajensa""" Ya ɗan kalli Jalal ya ga ya bar taɓa tab ɗin hannunsa yana sauraron bayaninsa. Sai ya cigaba. """A halin da ake ciki dai kuɗin nan ba za su samu ba dan suna da yawa. Idan kuma ya ji labarin mun baka" "'yarmu na san dole zai bibiyi labarin kuɗinsa. Shine na ce bari na zo ko akwai wani taimako da za a yi mana saboda kada magana ta fito a ji kunya""" Jalal ya yi shiru yana processing maganganun Baffa Lawalli. Mutumin fa yadda Ziyada ta faɗa haka yake. Bai taɓa ganinsa ba. Bai taɓa magana da shi ba. Amma sai ga shi daga haɗuwar farko maganar kuɗi ce ta kawo shi. "Ganin shirun yayi yawa sai Baffa Lawalli ya ce ""na ji labarin ka bawa Ziyadatu aikin abinci a rastarant" "ɗinka. Ai Ziyadatu tana da ƙoƙari sosai. Tunda Allah ya yiwa mahaifinta rasuwa duk wani faɗi-tashi na Makarantarta duka a hannunmu yake. Riƙon marainiya akwai wahala. Ga naka 'ya'yan haka zaka rufe ido ka riƙe maraya da hannu bibbiyu. Ka san yanzu haka ta kusa kammala karatun Digiri ko?""" "Jalal ya shiga mamakin ƙaryar mutumin nan. A ɗan binciken da ya yi, makarantar da Ziyada take self-" sponsored ne. Ita take biyawa kanta kuɗin makaranta. Amma sai ga shi wannan tsohon yana claiming shi yake faɗi-tashi akan karatunta. """Haka ne, Malam. Allah ya saka muku da Alkhairi""" "Jin ya yarda da bayaninsa sai Baffa Lawalli ya gyara zamansa yana faɗin ""ya za a yi. Ai yiwa kaine. Abinda" "ya yi Sadiqu ai shi yayi ni. Dan haka 'yarsa 'yata ce""" """Nawa ne kuɗin da shi Alhaji Rabi'un ke binka?""" """Alhaji Nafi'u sunansa, Ranka shi daɗe""" """Okayyy""" """Kuɗin da ɗan yawansu. Dama na karɓi aron kuɗin ne na sa a gona bara. To kuma sai gona ba ta yi kyau" "ba""" Jalal dai kallonsa yake. Wannan mutumin expert ne wajen roƙo. Ya san manipulation tactics da zai "blackmailing mutum emotionally. Ba dan ya san labarin mutumin ba, da babu abinda zai hana shi yarda da duk waɗannan ƙaryan da ya shirga masa." """Kuɗin ya kai dubu ɗari takwas da hamsin. Idan aka haɗa da wanda Zakari ke binsa zai cikata Miliyan" "ɗaya babu dubu arba'in""" """In short dai Miliyan ɗaya, right?""" Baffa Lawalli ya gyaɗa masa kai. """Sunansa ka ce Alhaji Naa...""" """Alhaji Nafi'u Badamasi. Yana da gidan Fiya water mai suna NAFI'U TABIL WATER""" """It's alright"" Jalal ya miƙe tsaye ya kai hannunsa wa Baffa Lawalli daya sake baki, saboda a tunaninsa Jalal" zai ce ya bashi account numbarsa ya tura masa kuɗin ne. """Ka yi haƙuri akwai baƙin dake jirana. Insha Allahu za a yi wani abu a kai""" Baffa Lawalli dai ba haka ya so ba. Ya dai miƙe ya yi musabaha da Jalal yana murmushin yaƙe. Jalal komawa desk ɗinsa ya yi amma sai Baffa Lawalli ya tsaya yana sosa kai. """Na ce, ko zan jiraka a waje zuwa baƙin naka su tafi?""" "Jalal ya washe fiska ya ce ""Baba ai aikine a gabana dayawa. Abinda za a yi ga katina, idan an kwana biyu" "ka kirani ka tuna mini. Insha Allahu za a yi wani abu a kai. Wannan ba zai gagara ba""" Ya ciro complementary card ɗinsa tareda saka hannu ya ɗau wallet ɗinsa ya ciro sabbin 'yan dubu-dubu. "Bai cika riƙe cash ba, amma kaman akwai cash ɗin dubu goma a wallet ɗin. Ya ciresu duka ya haɗa da card ɗinsa ya bawa Baffa Lawalli. Baffa Lawalli harda ɗan risinawa ya karɓa yana masa godiya." Har ya fita Jalal bai dena mamakin mutumin ba. Zai yi bincike akan maganar kuɗin. Idan ya tabbatar Alhaji Nafi'u na binsa kuɗi kamar yadda ya faɗa kawai zai sa a biya direct ta account ɗin Alhaji Nafi'un ne. Idan ya fara bashi kuɗi haka tun daga yanzu. A gaba ma duk wata matsala wajensa zai taho. Not that baya son taimaka masa. Amma baya son mutane masu maula. Saboda duk taimakon da za ka masu ba zai taɓa isarsu ba. Zai yi iya taimakon da zai iya. Amma ba zai yi abinda zai jawo a riƙa yi masa sintiri zuwa office ɗinsa kamar yana running charity organization ba. He's glad cewa Baffa Lawalli ba shine mahaifin Ziyada na asali ba. Da bai san da wani ido zai riƙa kallon future sirikinsa ba. ZEEY """Wayyo na shiga uku!""" """Ni Ziyada ina zan sa kaina."" Yanzu fa Jalal ya kirani wai in shirya zai zo ya ɗaukeni muje na gaishe da" Hajiyarsa. Jama'a da wani ido zan kalli Hajiya Layla?. Daga haɗani da ɗanta akan maganar aiki sai ga shi na bi gefe mun shirya wani deal ɗin aure a tsakaninmu. Koda yake ita bata ma san auren yana kan wani yarjejeniya bane. A tunaninta Jalal sona yake kuma zai aureni. Kuma fa za ta iya tunanin cewa ni nake son Jalal har na convincing ɗinsa yace zai aureni. Wallahi kunyarta nake. To me zan ce mata idan na je?. Wait! What if ta ce masa bata yarda ya aureni ba. Kuma fa za ta iya faɗan haka. """Wayyo Allah na!"" Na zauna a bakin gado na rasa me yake min daɗi." """Ba za ki shirya ba"" Kaka ta min magana." Na yi wanka tun ɗazu. Zani nema a jikina. Na shafa mai amma ban saka kaya ba. 5PM Jalal ya ce zai zo. Yanzu kuma huɗu da rabi ma ta wuce. Dana gama dibi-dibi sai na tashi na fara neman kayan da zan saka. Na san wannan Discipline Master "ɗinnan tunda ya ce ƙarfe biyar zai zo, to biyar ɗin zai iso." """Kaka in saka Abaya ko Hijabi?"" Na ɗaga mata su duka biyu." """Ki sa Abayar zai fi miki kyau""" """Kaka, kuma sai na saka Abaya na je gaban sarkuwa""" """Ikon Allah. Akwai wanda ya hana sakawa ne?""" """Kaka, wai irin ta ganni da shigar mutunci ɗinnan""" """To ki sa wando ki tafi""" """Kaka ke ko!""" """To me zan ce miki tunda na yi magana kin ce ba haka ba""" Sai da wayata ta fara ringing ina cikin tunanin Abaya ko Hijab sannan na yi sauri na fara saka bra ɗina. Koda ban kalli wayar ba na san mai kiran. Abayar dai na saka. Last year na siya mana ni da Faty muka yi Anko. To ina ga ma sau uku na taɓa sakata tunda na sayeta. "A gurguje na ƙarisa shiri na fito bayan na yi rolling gyalen. Navy blue Abaya ce, akwai stones a wuya da" kuma hannun rigar. "Ina shiga motarsa ya ɗan kalleni ya ce ""zan fara cin taranki idan kika sake ɓata min lokaci""" "Na duba wayata na ce ""minti shaɗaya ne kawai fa""" """Komai zai iya faruwa a minti shaɗaya, kin sani""" """Me zai faru?. Saceka za a yi?"" Na faɗa ina ɗan sake gyara rolling ɗina dan ya matse min wuya sosai." """Na ga wata doguwar yarinya ta shiga gidanku yanzu. Next time idan kika ɓata min lokaci ita zan kira""" Doguwar yarinya?. Mardiyya?. Itane ta shigo dai-dai zan fito muka haɗu a zaure. """To sai me. Ai akwai 'yanmata a gidan namu dayawa"" na faɗa ina tura baki. Wato ma doguwar yarinya." Thank God ni ba guntuwa bace. Balle ya min gorin tsayi. Ina nan dai-dai. Average height irin wanda maza suke so. """Are you jealous?""" """Huh!. Ni Jealous. Allah ya kiyaye"" na faɗa ina dariya. Amma can ciki na ji zafin maganar fa." Doguwa my foot. "Da ya ganta doguwa, tana da shape ne?. Eh. Tana da shape ne?." Relax Ziyada ba wannan ne a gabanki ba. Abinda ke gabanki shine haɗuwarki da Hajiya Layla. Sai da muka iso gidan zuciyata ta fara bugawa da ƙarfi. Na ji kamar na ce masa ya komar dani gida ba zan iya kallon Hajiya ba. Na dai daure muka shiga gidan ya yi parking muka fito. Na jira shi har ya yi gaba sannan na bi bayansa muka shiga gidan. Tsabar a tsorace nake gidan ma chanja mini ya yi. Babu kowa a falon sai TV dake aiki. Na zauna ina ɗaura hannuna a ƙirji ina karanto addu'ar samun sauƙi. Jalal ya haura sama ya barni ni ɗaya a ƙaton falon kamar wata mayya. Janan ce ta fara fitowa. Ta ci kwalliya alamun fita za ta yi. """Ina wuni"" na gaisheta a ɗan tsorace dan tun daga stairs take hararata." Bata kulani ba ta wuce bayan ta ja doguwar tsaki. A zuciyata na ce an fara. """Lale marhaban"" muryan Hajiya Layla ya katseni daga tunanin dana ke." Fiskarta ɗauke da murmushi ta ƙariso falon. Na miƙe tsaye ina gaisheta. """Zauna mana. Ziyadah ai ke ba baƙuwa bace a gidan nan""" Na zauna inata murmushi kamar wadda aka bani contract ɗin tallen Close-Up. Har kumatuna sun fara ciwo tsabar murmushi. "Bata kawo maganar Jalal ba. Ta tambayeni labarin Kaks, daga nan muka shiga taɗin content ta ce yanzu" bata ganin post ɗina. Na ce mata Aikin restaurant da muke ne kwana biyu ya sa ban samu daman yin content a gida na ɗaura ba. Ta ce Allah ya taimaka na amsa da Amin. Muka ɗan yi shiru. Har lokacin ban sake jikina ba. Dan a lissafina tana tunanin yadda za a yi ta sallameni "daga rayuwar ɗanta ne. Sai kuma ta ce ""Ziyadah, Jalal ya same ni da maganarki. Kuma gaskiya na ji daɗin maganar dan Wallahi tun kafin na ganki ido-da ido kike burgeni""" Alhamdulillah. Alamu sun nuna ba korata za a yi ba. Na sunkuyar da kaina ƙasa ina murmushi. "Ta ɗan yi shiru kafin ta ce ""Ziyadah, ina so ki saurareni da kyau""" Wayyo Jama'a!. Korata za ta yi... CHAPTER THIRTY TWO "Ta ɗan yi shiru kafin ta ce ""Ziyadah, ina so ki saurareni da kyau""" Wayyo Jama'a!. Korata za ta yi... "Hajiya Layla ta ce ""A wajena yanzu ne Jalal zai yi aure. Na san ya faɗa miki wacece matarsa?""" Na gyaɗa mata kai ina jin wani sanyi a raina dan har ga Allah na ɗauka cewa za ta yi ban dace da ɗanta ba. """To, ina so ki nuna masa banbancin auren waccar kucakar da kuma aurenki. Ina so ki nuna masa daɗin" "auren mace Bahaushiya data ke da tarbiyya. Kin ji?""" Hmm! Ta ya zan nuna masa daɗin auren Bahaushiya while gaba ɗaya auren namu deal ne. "Jin ban yi magana ba sai ta ce "" zan takuraki ko?""" """A'a, Hajiya"" na yi saurin furtawa." """ Ni fa idan bai rabu da shegiyar nan ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba. Na jima ina son Jalal ya auri" "wata a Nigeria, amma sai yanzu ne burina zai cika. Dan haka ki yi duk dabarar da za ki yi dan ganin ya rabu da Cassandra. Wallahi albarkacin Junior ta ke ci, da ba zan yarda ko kusa dani Jalal ya kawota ba""" """Nagode, Hajiya. Insha Allahu zan yi iya ƙoƙarina"" na faɗa ina tantamar hakan a raina. Wani ƙoƙari zan yi" "in raba shi da Baturiya?. Ga ta fara, doguwa, gashinta har gadon baya. Gata ta shape mai kyau ba irin shafaffun matan Turawa dana saba gani a film ba." Mi zan nuna masa da ya fi na matarsa? """Thank you, Ziyadah. Na san ba za ki bani kunya ba. And I suspect Jalal really likes you, so ba za ki sha" "wahalar shawo kansa ba""" Lallai! Wai Jalal likes me. "Hajiya, Jalal acting kawai yake dan ya faranta miki rai. Amma ba maganar LIKE a tsakaninmu." """Ya ba a kawo miki komai ba. Ina yarinyar nan Hassana?""" """Hassanah!"" Hajiya ta ƙwalawa mai aikinta kira." Jin shiru sai ta miƙe tana faɗin bari ta dubata ko tana ta baya. Sai da Hajiya ta miƙe na ɗaga fuskata da kyau ina sake ƙarewa falon kallo. Wataƙila fa nan za a kawoni idan muka yi aure. Gaskiya I feel comfortable da Hajiya tun ban auri ɗanta ba. Matar genuinely Lovee me ne kawai. Sai dai ba zaman Hajiya zan yi ba. Shi Ɗan Hajiyan yana sona ne? Ga wani Assignment da Hajiya ta bani wai na saka shi ya rabu da Baturiyar matarsa. Ta ya zan iya hakan ni da ban san matsayina a wajensa ba. Dawowar Hajiya falon ya sa na sunkuyar da kaina na cigaba da murmushi. """Ashe tana ta baya ne""" Minti biyu sai ga Hassanar ta shigo ɗauke da tray. """Hassana sannu da aiki"" na yi ƙoƙarin karɓan tray ɗin a hannunta ta ce na bari." Ta ajiye min juice da ruwa da kuma chinchin da soyayyen nama. Na buɗe ruwan na sha kaɗan. Sama-sama muka cigaba da taɗi da Hajiya. Yawanci akan maganar Restaurant ne inda ta ke ce min idan ta samu lokaci za ta zo ta ga wajen kafin a buɗe. After like one hour Jalal ya sauko ya ce zamu tafi saboda Magariba ta kusa. Muka yi sallama da Hajiya na tafi bayan ta bani kyautar wani abu a cikin wata ƙaramar paper bag mai kyau. Sai dana ɗan yi pulaku irin na Fulani kafin da ta miƙawa Jalal jakar bayan na ƙi karɓa sai na risina na mata godiya. """So, maganar me ku ka yi da Hajiya?"" Jalal ya tambaya lokacin da muka fara tafiya." """Ina ruwanka. Tsakanina da Hajiya ne babu ruwanka a ciki""" """Ta baki tarihin rayuwata ko?""" "Na sa dariya na ce ""ai ta faɗa min duk wani sirrinka""" """Oh really!""" """Yanzu na san komai naka, ciki da bai"" ɗan juyowa ya yi yana mini wani kallo yace ""Kina nufin kin san" "komai nawa? Har da nan...?""" """Na shiga uku. Ban san komai ba. Wasa nake. Bata faɗa min komai ba. Hiran Restaurant kawai muka yi""" Na faɗa da ƙarfi ina ɗaga hannuna dan sai yanzu na fahimci fassarar da ya yiwa maganata. Wato ma yana so ya mayar dani 'yar iska. Ta ya ma za a yi na san komai na shi in ba nima da shegen bakina ba. """I was thinking abinda baki sani ba sai na nuna miki yanzu...""" """Wayyo!. Dan Allah ka dena"" na katse shi ina rufe kunnena." Dariya ya fara min. Na kauda kaina gefe ina kallon window still hannuna a kunnena bana son sake jin maganarsa. Sai da muka kusa isowa gidanmu sannan na buɗe kunnena. "Munafuki kawai. Abinda na faɗa daban, fassarar da ya yiwa maganata daban." "Da zan fita sai ya miƙa min kyautar da Hajiya ta bani ya ce ""sai yaushe zan sake ganinki?. Ina so nima na" "san duk wani sirri naki""" """Allah ka dena. Na ce maka fa wasa nake""" """Don't worry. Za ki san komai nawa idan aka kawoki gidana""" Ai tuni na buɗe ƙofa na fita. Ina jin dariyarsa. Mugu kawai. Ni fa sai in ce na fasa auren. Zai wani zo yana min maganar bariki. Ni na hana shi zama da matarsa ne. Ko ni na ce ya auro Baturiya ta ƙi zama da shi a ƙasarsa. Sai kuma kalaman Hajiya suka dawo mini. Ni yanzu dai maganar auren nan ya fara ƙwace mini. Ga Hajiya da buƙatarta. Ga zuciyata da ban gane mata ba. Ga kuma Jalal da ya fara kawo min wani zance. Wai zan san komai nasa idan aka kaini gidansa. Mtssw! As if na damu na san komai nasa . Ni ina ruwana da shi. Sai kuma wani tunani ya fara zuwa min kwanya. """I'm not dirty"" na faɗa da sauri ganin na fara hasaso Jalal babu komai..." I'm not dirty. Okay. Just adult thoughts... JAYKAY Har ya bar ƙofar gidansu bai dena dariyanta ba. Wani tunani ya faɗo masa. Duk ranan da aka kawo masa ita he's going to shock her. Wannan komai nasa da ta ce ta sani ɗin sai ya nuna mata na gaskiya. He can't wait to see her reaction idan ya nuna mata kansa in his full form. Ya san ihu za ta masa ta rufe idanunta. And he'll tickle her har sai ta kalleshi a dukkansa. Ganin dirty thoughts da ke zuwa masa na shirin saka shi tsarkin dole sai ya tattare tunaninta ya watsar. At least for now tunda Masallaci zai je. Da ya fito daga Masallacin sai ya koma gida. Kwana biyu baya samun zuwa Masallaci da Junior. Dan haka da ya je gidan bayan ya leƙa yaron nasa a ɗaki sai ya ce masa ya fito su tafi Masallaci in 10 minutes. Ɗakinsa ya koma ya ɗan watsa ruwa ya yi alwala ya fito ya saka Jallabiyarsa. Yana ƙoƙarin fitowa ya ji knocking ɗin Junior. Fitowa ya yi yana shafa kan yaron sannan ya kama hannunsa suka fita. Lokacin da suka dawo daga sallar Isha Hajiya da Janan suna zaune a dinning suna cin abinci. Junior ya je ya joining ɗinsu yayinda shi kuma ya wuce sama. Jallabiyarsa ya cire ya saka comfy Tshirt blue da baƙin gajeran wando wanda bai kai gwiwa ba. """Hajiya, wai da gaske kin approving local girl ɗinnan?"" Janan ta faɗa tana riƙe da cokali." """Yana da International woman, ba kya ganin it's high time ya san daɗin zama da Local woman?""" """Hajiya, kin san ba haka nake nufi bafa. I mean ba zai nemi dai-dai class ɗinsa ba. Someone more...""" """Ci abincinki, Jamila""" """Hajiya!"" Janan ta saki ƙara tana bubbuga ƙafa." """Ni kar ki sake kirana da sunan nan, bana so""" Hajiya ta saka dariya dan dama da gangan ta kirata da hakan. Jamila Kabeer Maiyaƙi shine formal name ɗinta duk da kuwa a gida Janan ake kiranta saboda Hajiya ce ta "bata inkiyar. Tana shiga High School ta je ta chanja zuwa Janan Kabeer Maiyaƙi, ta dena amfani da Jamila." Hajiya bata ce mata komai ba tunda itama ba son sunan take ba. Allah Sarki! Daddynsu ne yai ta kwarwa wai Uwa da 'yar duka suna ƙin suna mai daɗi. Wai da sun san ma'anar suna JAMILA da ba za su ƙi sunan ba. Shi yasa ya dage yake kiran Hajiya Layla da sunan. Itama Janan ɗin ya fi kiranta da Auta ko yace mata little Jamila. Bayan Daddy babu wanda yake kiran Janan da Jamila ta ƙyaleshi. Yanzu zata fara faɗa tan cewa ba sunanta bane. Yanzu ma miƙewa ta yi a dining ɗin tana faɗin Hajiya ta hanata cin abinci. "Hajiya ta ce ta dawo ta ci abincinta, Janan ta ƙi. Ta haura sama da sauri." Jalal ya ce Hajiya ta ƙyaleta dama ba ci za ta yi ba gashi tun ɗazu ai wasa kawai take da wayarta. Da suka gama cin abinci sai suka zauna a falon suna ɗan kallo. Can Hajiya ta sakowa Jalal maganar gyaran gidansa Jalal ya yi shiru. """Ai za ku fi sakewa a can. Kuma ba daɗi gidan yana nan shekara da shekaru babu kowa""" "Shima ya yi tunanin hakan, amma tsarin gidan ne idan ya tuno yake kashe masa jiki." Duplex ne guda biyu iri ɗaya suka gina. Ga gidan nan katanga ɗaya ne da gidan Hajiya. Lokacin da Daddynsu ya gina wannan gidan already ya sayi filin da ke gefensa akan a nan yake so 'ya'yansa maza su zauna. Tun kafin su dawo Nigeria shi da Jamal suka haɗa kai aka tada ginin. Jamal ɗinne ya ke supervising komai. Sau biyu ya taɓa zuwa ya duba gidan. Ɗaya lokacin da aka gama gidan wani lokaci da ya zo Nigeria. Ɗayan kuma lokacin da Jamal yake shirye-shiryen aure. Haɗuwarsu ta ƙarshe da Jamal ɗin kenan. """Dan Allah ka zaɓa"" Jamal ya pleading ɗinsa." """It's the same design. Ka shiga duk wanda ya yi maka.""" A ranan Jamal bai barshi ba. Ya dinga binsa har sai da ya tursasa shi ya nuna ɗaya daga cikin duplex ɗin ya ce ya zaɓa. Ashe Jamal ba zai yi auren bama balle har ya zauna a gidan. Yanzu da Hajiya ta ce ya gyara gidan sai ya ji wani deep sadness a ransa. Bai san yaushe zai dena jin raɗaɗin mutuwar Jamal ba. Therapist ɗinsa ya ce he's living in denial. Wai ya kamata ya yarda a ransa cewa Jamal ya tafi kenan ba zai taɓa dawowa ba. Ba mutuwar ba. It was the unfinish plans. The unfinish discussions. Abubuwan da ya ke so ya faɗa da bai faɗa ba. Abubuwan da ya ke son tambayarsa da ba zai taɓa samun damar tambayar ba. Jamal yana daga cikin babban dalilin da yasa shi kasa hoɓɓasa akan rabuwa da Cassy. """Bayan aurena zan zo mu yi maganar. Komai zai zo da sauƙi. Kar ka damu""" "Jamal kaɗai ya yiwa zancen yana son rabuwa da Cassy, amma yana tsoron rasa custody na ɗansa" Muhammad. Jalal da kansa yayi tunanin rabuwa da Cassandra saboda auren nasu ya fara gundurarsa. Babu wani nitsuwar aure da ya ke samu. And then ga maganar shan giyanta. Sannan lokacin da ya ke tuƙa Jirgi duk lokacin da ya samu damar zuwa gida a lokacin ne ita kuma Cassandra za ta tsiri tafiye-tafiye akan business ɗinta. """Bayan aurena"" da Jamal ya bashi yake tunowa duk lokacin da yayi tunanin rabuwa da Cassy. Gani yake" kamar Jamal zai zo ya same shi su tattauna maganar su samu mafita. Bai san ya yi nisa a tunani ba sai da Hajiya ta ce masa za ta je ta kwanta. Ita da Junior suka haura sama aka barshi shi kaɗai a falon. Maybe it's time to let go. Ya dena jiran Jamal ɗin da ba zai dawo ba. Ya dena jiran shawaran Jamal ya fara amfani da nasa shawaran. Ƙaran kira ne ya dawo da shi daga tunanin da ya ke. Lazily ya jawo wayar dake gefensa ya ga sunan da ke yawo a screen ɗin. """JLove"" ta kira sounding excited." """I miss you""" Ya yi shiru. Wai so take su yi video call za ta nuna masa recent collection na fashion brand ɗinta. Ɗaga wayar ya yi yana kallonta dan gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake. Wani red tight dress ta saka. Ta fara juya jikinta tana tattaɓa ƙirjinta. Ya san me take ƙoƙarin yi. He's not in the mood for wannan shirmen. Ta tambayeshi ya yaga kayan?. Ya mata shiru fiskarsa blank. Sai ta fara wani moaning tana kwatanta masa yadda zai saka mata hannu a cleavage ɗinta ya jawo boobs ɗinta ya fara mata... Shirmenta kawai take. Idan akwai wacce zai so ganinta cikin kayan har ya ji marmarin sa hannu a cleavage ɗinta to Ziyada ce. Yana gani Cassandra ta zuge rigan ƙasa ta fara masa wasa ta waya ya kifa wayar akan kujera ya mayar da hankalinsa kan TV. A yanzu mace ɗaya yake son ganin komai nata. And very soon zai gani ɗin. Yana jin muryan Cassy ta wayar tana tambayar ya take ganin duhu bai kulata ba. Idan ta gaji zata kashe call ɗin da kanta... CHAPTER THIRTY THREE JAYKAY """Ranka shi daɗe, na ce, ko ka manta na jika shiru. Inata kiran wayarka baka ɗauka"" yai maganar yana" wage baki. "Ba dan alaƙar da yake shirin ƙullawa da Ziyada ba, da sai ya gayawa mutumin nan magana." Zuwa masa gida da sassafe haka sai kace wanda ya sace masa 'ya. Baffa Lawalli ne ya yiwa Jalal sammako. Dake masu gadi ba su yarda da bayaninsa na cewa shi sirikin Yallaɓai Jalal bane sai suka ƙi yiwa Jalal ɗin magana suka ce ya jira har sai ya fito. Haka Baffa Lawalli ya zauna tareda masu gadi har sai da Jalal ya fito zai fita office shine ya taso yana masa magana. Jalal ya amsa gaisuwarsa sama-sama. """Baba, ka ga ina sauri"" ya fara magana yana danne ɓacin ransa." """Ban manta maganarmu ba. Zan kiraka da kaina idan na shirya""" """Ko kuma na baka akawun nambana ka tura kawai. Ina da babban akawun har biyu da Fez Bank da...""" """Baba ka yi haƙuri zan kiraka zuwa gobe Insha Allah""" Kuɗi ya sake fitarwa ya bashi ya ce yai haƙuri yai kuɗin mota. Baffa Lawalli ya karɓi kuɗin fiskarsa babu fara'a. Shi fa bai zo dan Jalal ya dinga bashi dubu goma dubu biyar ba. So yake ya tura masa Miliyan ɗayan nan ya cirewa Alhaji Nafi'u nasa shima ya samu kusan rabin Miliyan a ciki. Aure zai ƙara. Akwai wata Bazawararsa da ya ke son aura zuwa ƙarshen shekarar nan. Ya dai saka dubu biyar ɗin da Jalal ya bashi a aljihu ya nufi gate zai fita yayin da masu gadi suka buɗewa Jalal gate ya fice da motarsa. *** ZEEY """1,2,3, Action"" Jide dake gefen Camera Man ya faɗa." Content ake shooting wanda za a riƙa ɗaura tallace-tallace a gidan TV da kuma wanda za a riƙa ɗaurawa a social media. Yanzu haka daga Makaranta nake. Ina zuwa na chanja kaya na saka baƙin Chef Coat da aka rubuta Chef Zeey's GIDAN GIRKI a jiki. Yana daga cikin branded uniforms da Agnes ta sa aka min. Hatta Apron ɗina shima sunan da ke jiki kenan. Kwanaki gudu suke. Mun gama staff training last week yanzu kuma ana creating content wanda za a riƙa tallata Restaurants ɗin. Ga shi kuma wannan Asabat ɗin Magabatan Jalal za su zo gidanmu. Nan da kwana biyu fa kenan. Idan na ce muku tun daga ranan da Jalal ya kaini ganin Hajiya ban sake samun sukuni ba to ba ƙarya na yi ba. Yanzu da komai ya fara matsowa. Aure. Restaurant. Sai na ke ganin ashe fa ba ƙaramin risk na ɗauka ba. "Idan ba karambani irin nawa ba. Ta ya zan joggling aikin Restaurant, final year a makaranta, da kuma maganar aure?. Koda yake aure kam wahalar a yi shi ne. Tunda ba auren soyayya bane I don't think akwai wata hidima da zan yiwa mijina. I mean mijin da zan aura." Koda yake idan aka yi auren fa a wajen mutane Jalal MIJINA ne. Kuma nima idan zan yi maganarsa hakan zan faɗa. Wa ya ga MIJINA. Na ɗan sake murmushi. "Amma fa. Ai ba zan zauna a gidan Jalal kamar kayan wanki ba ko?. Dole zan kula da gidan, and probably" ni zan riƙa yi masa girki. Idan ma tare za mu zauna da Hajiya na san ni za ta ce na riƙa dafa mata abinci. Wohoho!. Ni Ziyada na ɗaukowa kaina Dala babu gammo. Na maida hankalina kan abinda nake yayinda Camera Man ɗin ya matso kusa da hannuna inda na ke zuba daddawa a cikin miyar kukan da nake girkawa saboda ya samu close up shot. Ɗazu a Makaranta daga practical na taho nan. Yanzu ma kuma na fi awa biyu ina tsaye ina girki ana ɗauka. Tuwo miyar kuka shine abinci na uku da muke ɗauka a yau kaɗai. Bayan nan zan sake yin miyar taushe shima a ɗauka. Ya Ilahi! Neman Halal akwai wahala. Musamman mu mata da muka ɗaura ɗamara muka ce muna so mu samu nakanmu. Yanzu da aka yi nisa da shooting ɗin sai na fara jin cramps kaɗan-kaɗan. Subhanallahi! This cannot happen. Sai gobe za mu ƙarisa shoot ɗinnan fa. Idan period ɗina ya zo yau ba zan iya yin komai gobe ba. Silently na fara addu'ar Allah ya sa ba yau ko gobe abin nan zai zo mini ba. Kuma fa busy dana shiga ne ya sa ban duba Period app ɗina na ga prediction na ranan da zai zo ba. Na san dai ba zai wuce tsakanin daren yau ɗin ko gobe ba. Tun shekaranjiya nake jin cramps ɗin kaɗan- "kaɗan na shareshi, yanzu ne da na sha aiki cramps ɗin ya fara yawa. Idan kuma ya fara yawa hakan nan" to Anty Red tana nan tafe kenan in 24hrs ko ƙasa da haka. Thank God shooting ɗin da ake ba wai fiskata ake nunawa ba. Da yanzu fiskata ya nuna discomfort ɗin da nake ciki. A videos ɗin da aka yi jiya an ɗauki fiskata inda na yi short Intro sannan ni da sauran staffs muka welcoming mutane zuwa GIDAN GIRKI Restaurant. Amma bayan nan hannuna da kuma voice ɗina kawai ake naɗa. Mun riga min ɗauki ƙarshen part ɗin inda na sake faɗin scripted lines na call to action da zai ja hankalin mutane ya saka su anticipating ranan da za a buɗe Restaurant ɗin. Agnes ce incharge of Creatives and Marketing na Restaurant ɗin. Idan aka buɗe wajen Jide ne zai zama temporary Manager. Idan wajen ya zauna da ƙafafunsa sai a hiring wani Managern a training ɗinsa. Lokacin da Jide ya ce CUT! Kwantar da kaina na yi kan kitchen island ɗin ina numfashi sama-sama. Na "saba a baya ni kaɗai nake recording videos ɗina da 'yar wayata, tripod da kuma Kaka da take taimakawa wani lokaci. Ni ce Director, Producer, Creator da komai. Yanzu kuma ina girki ne ana ɗauka a gaban mutane. It's overwhelming. Ga Director Jide da ya dage sai komai ya tafi dai-dai." """Zeey, are you okay?"" Jide ya tambayeni lokacin da ya matso kusa da inda nake." """Kawai na gaji ne""" """Sorry, gaskiya kin yi aiki. Ki je office ki ɗan huta before you go. Shoot ɗin gobe babu yawa""" Na gyaɗa masa kai. Office ɗin Manager na shiga na cire Rigar Chef na mayar da Abayar dana saka na je class da safe na zauna a kujera. Ina jin surutun su Jide sunata faɗa akan abincin dana girka. "Wayata na jawo na duba lokaci. Ashe har biyar ta wuce. Sallar Azahar kawai na yi, dan haka ban ga ta" "zama ba. Na fara contemplating in yi sallar la'asar a nan ne, ko kuma na bari sai na je gida kawai sai na yi?." Ƙarshe kawai na yanke shawaran in je gida kawai dan ba zan iya sallah a haka ba. Jikina gaba ɗaya warin gumi da kayan miya da spices yake. "Barin tafi gidan kawai in yi wanka, in yi sallah." Dole na nemawa kaina mafita incase abin nan ya zo mini daren yau ko gobe da safe. "Kai mata ma sun ga takansu. Ga fama da matsalar rayuwa, ga matsalar period duk wata. Wasu ma suna" business ɗin suna fama da laulayin ciki ko kuma shayarwa. Kai duk macen da period yake zuwa mata da sauƙi to ta godewa Allah kawai. Ga shi an ce yawanci sai Mace ta haihu za ta dena. To ni yaushe na san zan haihu?. What if ban haihun ba?. Lissafin haihuwa ya sa tunanina ya koma kan mutumin da zan aura. JALAL. "Da ace auren soyayya za mu yi, da shikenan fa daga aure Jalal zai fara hawa kaina." Ya Allah! Ni da Jalal a gado ɗaya!. Manne da juna!. Probably kissing!. And maybe naked... Na shiga uku ni Ziyada! Me yasa nake irin wannan tunanin. Cikina ya juya a dai-dai lokacin da marata ta sokeni. Cramps. Na fara haɗa jakana dan na gudu gida. Shi gogan ma ko sau ɗaya bai zo Restaurant ɗin ba tunda muka fara shooting content. "Ni na kawo kaina, dan haka ni zan komar da kaina gida." Na tattara kayana har da practical report book da ban san yaushe zan yi ba. Idan ba department ɗinmu "bama daga resuming first semester final year sai su fara bombarding ɗinmu da practicals. Kai, Allah!." "Da maganar project za mu ji, ko kuma practicals?. Thank God ma classes ɗinmu ba yawa yanzu. Yawanci" lectures biyu ne a rana. "Dana fito daga office sai na wuce kitchen, na samu mutanen wajen kowa abinci yake ci. Har Agnes itama" ta samu waje ta ajiye gashin wig ɗinta a gefe tana cin Tuwon shinkafa da miyar taushe. """Our Chef, har za ki tafi?"" Jide ya tambaya yana faman gwagwuyan wani ƙashi. Da ƙashin miya na yi" Taushen. """Zan wuce. Na ga kaman akwai hadari a garin""" """I still need to round up things a nan dana kai ki""" """Yau kuma? Jide ka dena tsoron ne?"" Na faɗa ina masa dariya." """Ewoooo! Na manta. Ofcourse zan tambayi permission daga Oga kafin na kai ki""" """Kar ka damu, ina fita zan hau Keke""" """Bisola, akwai sauran Tuwon nan?"" Na tambaya ina kallon ɗaya daga cikin staffs ɗin da aka hiring a" kitchen. Su uku aka ɗauka a kitchen ɗin. Bisola da Zainab sai namijin mai suna Tanimu amma Tee yake kiransa "dan ɗan gaye ne. Ya iya abinci dan yana da experience sosai. Infact da muka yi musu interview da training ya ma fi sauran matan iya aiki. A da, duka mata nake so a ɗauka. Amma sai na ga Tee zai iya supervising kitchen ɗin idan bana nan fiye da matan." Bisola Bayarabiya ce. Allah ya sa dai kar ta haɗa kai da Jide su mayar da wajen nan Gidan Amala. Okay. Wasa nake. "Ta ce mana a Jos aka haifeta, amma yanzu tana zama a gidan Antynta a nan Zaria. Tana da kwalin" Diploma kuma ta taɓa aiki a restaurant. Zainab 'yar Maiduguri ce amma tashin Zaria ta dai gama Secondary School shekara biyu kenan bata cigaba ba. """Kamar fa Tuwon ya ƙare"" Bisola ta bani amsa. Caɓɗi!. Yanzu duk cikin abincin dana girka basu rage mini" komai ba? "Jiya dana zo ban ci abincin dana yi ba, amma na ɗauki take-away na kaiwa Kaka ai. Yau kuma saboda na" bar wajen shikenan sai su cinye komai. Dake saboda promo content ne abincin kaɗan-kaɗan na ke yi. Duk da haka sai su cinye komai. Tuwo kala biyu fa na yi!. Na fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya. Shareni ma suka yi suna ta cin abincinsu. Camera Man ɗinma ya "rataya Camerarsa a wuya yana cin Tuwon Masara miyar Kuka, har da suɗe hannu." Na haɗiye maganar da ya taho mini dan bani da ƙarfin masifa. Gobe za su ga me zan musu ai. Na juya ina dragging jakata da kuma ledar dake hannuna na yi hanyar fita ina jin cramps ɗina yana ƙaruwa. A tsakiyar hall ɗin Restaurant ɗin Jide ya ƙwala min kira. "Leda ya miƙo min. ""Kin ɗauka zan bari a cinye babu naki ne. Ba ki ji inata masifa ɗazu ba. On a serious" "note. You're a great cook, Zeey""" Na karɓi ledar a hannunsa ina faɗin an gode Manajan Gidan Girki. Jide ya sa dariya. "Lokacin dana fito waje kuwa, sai na ga ashe fa hadari ya turnuƙe sama. Ruwa ne yake haɗuwa. Idan ya" sauko kafin na kai gida zan sha wahala. Allah dai ya sa na samu Keke da wuri. Na yiwa masu gadin Plazar Sallama na fita. Ai ko taku goma ban yi ba na ji horn a bayana. Ban juya ba dan a tunanina irin masu tsare mata a hanya ɗinnan ne. Ban gama tunanin hakan ba Motar "Jalal ta zo ta wuce ni, sai kuma ta tsaya a gabana." "Alhamdulillahi! Na ji wani sanyi a raina duk da ban san ko Jalal ɗinne da kansa ya zo ɗaukata ba, ko kuma" dai Direbansa ya aiko mini. Kafin na ƙaraso aka buɗe min gidan gaba. Jalal ne. Na shiga motar da sauri dan har an fara yayyafi kaɗan. CHAPTER THIRTY FOUR JAYKAY 4 days kenan bai ganta ba. 4 days kenan yana son ganinta amma ayyuka sun riƙe shi. Yau da safe ya je Abuja ya gana da Uncle Idris akan maganar kai sadaki da za a yi. Direba na ajiye shi a gida wanka kawai ya yi ya chanja kaya ya fito ya karɓi key ɗin mota ya taho Plaza. Sai da ya kusa isowa ma ya kira Jide ya tambayeshi ko Ziyadah tana nan dan ya kira numbarta ba ta ɗauka ba. Jide ya ce masa yanzu ta fita. """Ya hanya?"" Ta tambaye shi dan ya faɗa mata zai yi tafiya jiya." """Lafiya. How's school?""" """School kam an dawo kenan ai. Mun fara final battle""" "Kallonta ya tsaya yi. She looks tired. Da da hali, yana so ya bata warm hug ya comforting ɗinta. Ya san ta" sha aiki sosai. "Shinshina kayanta ta yi sannan ta ce ""Tuwo muka yi yau. Miyan kuka da miyan Taushe...""" """Are you okay?"" Ya katseta. Dan idan ya barta za ta cikashi da surutunta." """Yes. Me ka gani?""" """You look weak. Kin ci abinci kuwa? ko aiki kika tsaya yi tun safe?""" """Aww!"" Ta ɗan gyara zamanta. ""Na ɗauka cewa za ka yi ina warin spices""" """Kina warin spices ne?"" Ya faɗa yana ɗaga mata girarsa" """A'ah!"" Ta faɗa da ƙarfi." """I mean. Ka san miyan Kuka idan babu daddawa, da su citta...""" """Ba wai...Ka san na fi awa huɗu ina kitchen kuma...""" """So nake a riƙa siyar da abincin gargajiya"" ya faɗa yana mimicking muryarta." Ziyada ta haɗe fiska. """Eh ɗin. Ai ban gayyaceka ba ka zo. Ni ka tsai da motarka ma na fita"" ta ɓata fuska ta juya tana kallon" window. """Miye laifina a nan?. Ke fa kika fara kawo maganar""" """Ai abinda ke ranka kenan, shi yasa kake ta wani kallona tun dana shiga motarka""" """Dama wani na iya sanin abinda ke ran wani ne?""" """To miyasa kake kallona idan ba cewa za ka yi ina warin Daddawa ba?. Kuma da kake cewa na ce zan" "siyar da abincin gargajiya, dama ban ce kai zan siyarwa abincin ba ai. Ai kwana biyu da baka zuwa Gidan Girki hankalin kowa a kwance yake, yanzu ka dawo kenan za ka fara..."" ta yi shiru" Juyawa ya yi ganin ta tsayar da surutun nata. """Are you okay?"" Ya tambaya ganin tana ɗan matsa cikinta." """Hey, what's wrong? Mu je Asibiti ne?"" Ya jero tambayoyin rabin hankalinsa na kanta sauran kuma yana" tuƙin da ya ke. """Dan Allah idan ka ga pharmacy kusa ka tsaya zan sayi magani"" ta faɗa muryarta ƙasa-ƙasa." Me yake damunta?. Tashi ɗaya ta switching daga surutu ta koma abar tausayi. """Me ya same ki?"" Ya sake tambaya dan gaskiya she looks sick. Tunda ta shigo motar ya lura da hakan." """Ba komai""" """Ba komai kuma?""" Kwantar da kanta ta yi still tana matsa cikinta. """Sunshine, please me yake damunki ne?"" Wannan karan muryarsa cike take da damuwa." "Ta ɗago ta ce "" ba komai. Idan na sha pain reliever zan ji sauƙi""" """Bari mu je Asibiti, please.""" """Kayya! Wai sai na fito maka da komai fili ne. Idan ka ga mace tana haka ai ka san me take nufi. Ni ka" "kaini pharmacy zan sayi magani"" ta ƙarisa maganar kamar za ta yi kuka." Ta ya zai san me yake damunta idan bata faɗa masa ba. Lokacin da ya parking a dai-dai wani pharmacy dake bakin titi ruwa ya riga ya ɓarke sosai. Yana gani tana yunƙurin fita ya dakatar da ita. """Wani magani za a siya miki?""" """Diclofenac""" """Shi kaɗai?""" """Eh""" Ko tunanin ɗaukan Lema bai yi ba ya fita ya sa kansa cikin ruwa ya shiga pharmacy ɗin. Minti huɗu sai gashi ya shigo motar kayansa ya ɗan jiƙe kaɗan. Ya miƙa mata ledar har da ruwan gora. """Ki sha yanzu""" Yana kallo ta ɓalli maganin guda biyu ta sha ta kora da ruwa. """Sorry ko. Are you sure wannan maganin kaɗai zai miki?""" "Ta gyaɗa masa kai ta ce ""shi na ke sha""" Sai da ya tada motar suka fara tafiya sannan ya sake tambayarta me yake damunta. Shiru ta yi bata amsa ba. """I'm worried, Zeeyadah. Please, ki faɗa min abinda ke damunki""" "Ƙasa-ƙasa ta ce ""cramps""" """Cramps"" ya maimaita" Abinda ta faɗa left him more confused. Me ya jawo haka? """Dama yana miki haka ne?""" Ta gyaɗa masa kai. """Sorry"" ya furta dan baya so ya takurata." Saboda ruwan da ake daf ƙofar gida ya parking motarsa. Ya ce ta tsaya ya ɗau Lema a baya ta shiga da shi ta ce masa kar ya damu za ta shiga gidan a haka """NO. Ba za ki fita a haka ruwa ya taɓaki ba""" Ya fita ya ɗau Lema a bayan mota ya buɗeta. Shi da kansa ya buɗe mata ƙofar motar ta fito ya riƙe mata Lemar saboda akwai kaya a hannunta. Rakata ya yi har bakin zauren gidansu sannan ya juya ya koma ya shiga mota. Yana shiga ya jawo wayarsa ya fara browsing me yake jawo cramps na ciwon ciki ga mata?. Daga kalmar MENSTURATION da ya fara gani ya fahimci abinda ke damunta. Dariyan kansa ya fara. Na rashin sanin duk waɗannan abubuwan. Ya san mata na period. But bai taɓa sanin suna shiga pain har haka ba. Cassandra ba ta ciwon mara. Janan ma dai as far as he knows bata irin haka. Mutane biyu kenan da ta dalilinsu ya kamata a ce ya san mata na fama da matsanancin ciwon mara idan suna period. Maimakon ya koma gida sai ya sake komawa Pharmacy. Da ya fito sai ya shiga wani babban provision store dake gefen wajen ya yi siyayya. Gidansu Ziyada ya dawo. Zuwa lokacin ruwa ya tsagaita sai yayyafi. Kiran numbar Ziyada ya yi. Daga yanayin yadda ta ɗau kiran ya san a kwance take. Ce mata ya yi ta turo yaro waje ya zo ya karɓa mata saƙo. Ya jira kusan minti biyar kafin wasu yara su biyu suka zo wajen motarsa. ZEEY Lokacin da Amir da Mu'azu suka kawo mini saƙon Jalal ina kwance akan gado na yi rub da ciki na sa pillow a ta cikina. """Kaka, miye a ciki?"" Na tambaya dan ita ta karɓi ledan." Ita ta kira min yaran ma dan ruwa ya hanasu shigowa sashenmu su ci tuwon dare. "Na ɗan matso da kaina bakin gado ina kallon abinda Kaka ke fitarwa. Ta fito da gwangwanin Milo," Madara... Subhanallahi!. Na tashi da sauri na sauka a gadon na ɗau pack ɗin Always da Kaka ta fitar na mayar cikin ledar. """Kaka a gaban yaran nan fa""" """Ku wuce ku tafi"" na fatattakesu. Wato so suke su ga abinda aka kawo su kai wa Iyayensu gulmata." Sai da yaran suka fita sannan na ɗau ledar na hau gado da shi. Da wayar hannuna na dinga haska ledar ina duba kayan ciki. Kaka tana min tsiya wai idan akwai Kaza in fito da shi za ta ci. Wai Ango ya iya dubiya. Ni dai ban kulata ba. Uban wa ya ce masa ya siyo min pad har kala uku?. Uban wa ma yace masa ya siya min pad?. Haba dan Allah. "Sauran kayan shayi ne a ciki. Madara, Bournvita da Milo. Manyan slize bread guda biyu. Sai wani packet" na dabino. Uban wa ya faɗa masa idan ina period ina iya cin abinci. Sai kuma wata zuciyar ta ce mini. But Ziyada it means he cares... He cares about me... sai na ji na yafe masa laifin siyo mini Pad da ya yi. Yau Jalal ya nuna damuwa a kaina. Tun a cikin mota da ciwon mara ya sani a gaba na ga ya rikice da halin da nake ciki. Har da shiga cikin ruwa ya siyo min pain reliever. He cares... Amma kuma da farko ya bani haushi. Nufinsa bai san me mace take nufi ba idan tana ciwon ciki ta buƙaci shan pain reliever? Wata zuciyar ta ce ƙila Baturiyar matarsa bata yi. And Maybe Janan ma baya mata haka. Amma duk da haka. Ya kamata a ce ya sani tunda shi ba yaro bane. Sai wajajen goma saura na dare da aka gama ruwa sannan na saka ruwan zafi a gas na je na yi wanka. "Anty Red bata iso ba, amma ba mamaki ta min saukar tsakar dare ko Asuba." Bayan na yi wanka sai na yi Alwala na zo na gabatar da sallolin da suka wuce ni. Abincin dana zo da shima ba iya ci na yi ba. Kaka ce ta ci. Sauran kuma ta adana sai da safe. Kiran Jalal ne ya tasheni da sassafe bayan Asuba. Na yi mamaki da na ga period ɗina bai zo cikin dare ba. "Lokacin dana ɗauka sai ya min ya jiki, na ce masa da sauƙi." """Ki zauna a gida ki huta. Zan kira Jide na faɗa masa sai next week za ki cigaba da aikin""" """Amma fa yau ne ƙarshe. Kuma ba jimawa za a yi ba""" """Zeeyaadah"" ya kira sunana da serious voice." """Iya abinda kuka ɗauka ya isa. Daga baya idan akwai buƙatan hakan sai ku cigaba""" """To, na ji"" na faɗa a hankali." """Kin ga abinda na tura miki jiya?""" """Ni Dan Allah ka dena sakani jin kunyar ka. Kuma kawai sai ka je ka siyo abinda ba a sakaka ba. Ce maka" "aka yi bani da shi""" "Sautin murmushinsa na ji kafin ya ce""ki duba Whatsapp ɗinki""" """Aww! Ashe..."" na cire wayar a kunnena na kunna data na shiga Whatsapp." """Ki duba videos ɗinnan da kyau. And please take care of yourself, kin ji""" Rufe bakina na yi ina girgiza kai. Na fara scrolling videos da articles da Jalal ya tura mini duk akan abubuwan da mace za ta yi idan tana ciwon cikin period. Har da tutorial na yadda za ka riƙa compressing cikinka da ruwan zafi. Lallai kam! To an gaya masa ban san duka waɗannan bane. Ya wani kama ya cika min waya da tarin videos da rubutu. Inama na ke da lokacin karanta wani article akan period cramps. Abun da tun sama da shekara goma ake fama da shi kam ai na san ya nake managing kaina. Na tashi daga inda nake kwance. Muna da class guda ɗaya yau da safe. Tunda an ce ba zan ƙarisa aikin "shooting content ba, zan je class ɗin kawai. Sannan dama ina so na je na ga project Supervisor na dan har yanzu bai approving min topic ba." Cikin kayan tea da Jalal ya aiko jiya na haɗa tea mai kauri babu sugar na sha. Na sha pain reliever guda "biyu na saka sauran a jaka. Da shirina na fito in case Anty Red ta kawo mini ziyara ina cikin school. Na sake saka extra pad, a jaka just incase. Kun san dai wannan abun shegen abu ne. Yana iya baka mamaki a koda yaushe." Na yi sallama da Kaka na fito zan wuce school. Ina cikin tafiya na ji muryan yaro na kirana. """Adda Ziya, Adda Ziya"" na juya na ga Faruƙ ne ɗan Baffa Zakari." """Wai ki je Baba Babba yana kiranki""" "Baba Babba, Baffa Lawalli kenan. Haka yawanci 'yan yara-yaran gidan ke kiransa." Na ja ƙaramar tsaki dan na san sai ya ɓata min lokaci. Na wuce sashensu. Ɗan waken siyarwa na ga ɗaya daga cikin matansa tana yi. Ko yaushe ma aka fara a gidan ni ban sani ba. """Ina Ziyadatun take ne?"" Baffa Lawalli ya faɗa yana leƙo kai daga ƙofar ɗakinsa." """Gata nan zuwa"" 'yarsa Ummiyo ta faɗa." """Ina kwana, Baba"" na gaishe shi lokacin dana shiga ɗakinsa." """Lafiya"" ya amsa fiskarsa babu fara'a." """Gobe Wakilan yaron nan Jalal za su zo. A yadda muka tsara za su kawo sadaki ne da abubuwan da ake" "buƙata na al'ada sai a saka rana.""" "Ya ɗaga murya ya ce ""Amma ni ban gane alƙiblar mutumin da kika kawo mana ba""" Didish! Wani irin magana ne wannan? Ana gobe Asabat wakilan Jalal za su zo Dan Allah. """Yaron nan har office ɗinsa na je na yi masa wata magana mai mahimmanci amma duk sadda na kira shi" "baya ɗaukar wayata. Haka yake so mu bashi ke. Bayan bai san darajar Iyayenki ba""" Ya Subhanallahi! Ba dai kuɗi ya je roƙan Jalal ba. Shi ya sa na yi mamaki da ranan Jalal ya tambayeni ko "akwai kuɗin da Alhaji Rabi'u kamar yadda yake kiran Alhaji Nafi'u yake bina. Na faɗa masa babu. Amma kaman ya ce yana bin su Baffa Lawalli kuɗi masu yawa, kusan dubu ɗari biyar. Bai ce komai ba bayan na masa bayanin." Nima kuma ban kawo komai akai ba. """Alhaji Nafi'u mutumin nan hannunsa a buɗe yake. Alkhairi kan Alkhairi idan ya zo gidan nan. Amma shi" "wannan sai dai ya barka da dubu biyar kuɗin mota. Uban me dubu biyar zata mini. Ga shi zai zo gidan nan yana cikin mota ba zai sauko ya zo ya gaishe da mutane ba. Amma ya iya kiran yara ya saka su kwaso mishi leda su kai miki cikin gida""" "To, to, to. Wato har an masa gulman abinda ya faru jiya. To ma wai Fisabilillahi ana cikin ruwan zai ce a" kira masa mutanen gidan zai gaishesu ne?. Babu kowa fa a waje sanda ya kawoni gida jiya saboda ruwa. """Ko ce masa aka yi ke kaɗai ce a gidan. Ba ki faɗa masa kina da ƙanne bane?. Duka yaran gidan nan" "ƙannenki ne fa. Ke ce babba a cikin yara mata a gidan nan""" Na yi shiru ina danne maganar dake taho mini. """Ko ba ke bace babba?""" """Ni ce"" na faɗa a hankali." "Ya ɗan yi shiru ya sosa kansa sannan ya ce ""yanzu dai nawa kuka yi da shi zai kawo sadaki?""" Nawa muka yi da shi zai kawo Sadaki kuma?. Abin ciniki ne? """Baba, na barshi ne ya kawo abinda ya sawwaƙa"" na faɗa ina kallon fiskarsa." Mutumin nan dai ya rantse sai ya kunyata gidanmu a wajen Jalal. Allah ya sa kar ya yi abin kunya a gaban mutanen da za su zo gobe. Ga shi 'yan'uwan Jalal manyan mutane ne. """Abinda ya sawwaƙa kuma?. Ke ba ki san kina da damar da za ki faɗi adadin kuɗi ko dukiyar da kike so a" "matsayin Sadaki bane. Idan ma baki sani ba shi mai arziƙi ne. Dan haka tun yau ki faɗa masa gobe fa Sadakinki kada ya gaza Miliyan ɗaya. Kina jina?""" Dariya ne ya taho min. Yo maganarsa ai abar dariya ce. "Haka kawai sai na kira Jalal na ce ""Hello, Jalal. Wai in ji yayan Babana kada ku kawo Sadaki ƙasa da Naira" "Miliyan ɗaya""." """Kina jina dai?"" Ya sake maimaitawa." """Na ji Baba. Zan wuce Makaranta"" na miƙe tun ma kafin ya sake ɓaro wata maganar da zai sa na ɗura" masa ashar. Na ga alama idan ban masa hakan ba ba zai fita a harkata ba. Dama na san saboda ya ga Jalal ya fi Alhaji Nafi'u kuɗi ya saka shi haƙura da batun Alhaji Nafi'un. To yanzu kuma ya je ya yiwa Jalal maula bai kulashi ba. Shine yake cewa Alhaji Nafi'u ya fi Jalal alkhairi. Na fito daga sashensu raina a ɓace. Da ɓacin rai na isa school. Ban san wace tsiyar Baffa Lawalli zai kawo ba idan Wakilan Jalal suka zo gobe. Duk da dai Baffa Adamu ne zai jagoranci zaman amma ina tsoron abinda kwaɗayayyen tsohon nan zai iya yi. "Ku ji fa. Wai na ce kada a kawo sadaki ƙasa da Miliyan ɗaya. A'a, su siyar dani kawai na san cewa aurena" da Jalal shi zai kawo masa ƙarshen Talauci. Mtssw! A da na yi niyyar yau zan faɗawa Faty za a kawo Sadakina. Sai kawai na fasa. Gara na bari idan an kawo ɗin komai ya tafi lafiya sai na faɗa mata. "Kai ciki bai karɓi Faty ba. Gaba ɗaya sai wasu ƙuraje fiskarta yake, ga wani baƙi da ta yi. Duk wani gayun" "Faty babu shi yanzu. Tunda muka resuming school ma manyan hijabi da jilbab take sakawa ta shigo school. Fiskarta fayau wani lokacin ko mai babu. Dama an ce ciki yana saka wasu matan ƙazanta. Har ji nake ana cewa wasu matan idan suna laulayin ciki basa son wanka. Sai su yi kwanaki ba su yi wanka ba. To, Allah dai ya sauketa lafiya." Muna gama class za mu fita mu je wajen supervisor ɗinmu Faty ta tambayeni aron kuɗi dubu biyar. Na ce mata bani da cash na ciro wayata na mata transfer. Da muka je Department sai muka samu nata supervisor ɗin baya nan. Ta jirani na shiga wajen nawa. Ba mu ɗau lokaci ba dan shima Supervisorn nawa fita zai yi wai suna da meeting. Ni dai tunda ya approving min topic ya ce in je in kawo Chapter One na masa godiya na fita. """Yanzu gida za ki wuce?"" Faty ta tambayeni." """Gida zan wuce""" """Yau ba za ki je Restaurant ɗin bane?"" Na faɗa mata ina zuwa aiki a restaurant amma bata san full" details ɗin ba. """Bestie bana jin daɗi ne. Kin san idan abun nan ya zo yadda nake komawa. Yanzuma daurewa kawai" "nake""" """Ni kuma da nake fama da Baby a ciki fa?""" """Sannu Maman Baby. Allah ya baki lafiya"" na faɗa ina dariya. Maganar kawo Sadakin nan yanata" "mintsinina na faɗa mata, amma na danne. Idan komai ya tabbata zan faɗa mata." "Anguwarmu akwai nisa da nata dan haka ita ta fara shiga Keke na biya mata kuɗin ta wuce, kafin nima" na tsare wani na wuce gida. Tabbas akwai wani abu a ƙasa gameda auren Faty. Ba kawai laulayin ciki bane. Na dai ja bakina na yi shiru. Idan bata faɗa ba nima ba zan tambaya ba. Ai dama cewa aka yi AURE SIRRI NE. Tun ina cikin Keke na ke jin alamar Anty Red ta iso. Ina zuwa gida ko kaya ban cire ba ita na fara dubawa. "Ga shi nan ta faso da muƙarrabenta baƙi-baƙi, fatsi-fatsi, ja-ja-ja-ja. Dama su suke fara isowa. Yau ake yinta..." CHAPTER THIRTY FIVE JAYKAY 4 days kenan bai ganta ba. 4 days kenan yana son ganinta amma ayyuka sun riƙe shi. Yau da safe ya je Abuja ya gana da Uncle Idris akan maganar kai sadaki da za a yi. Direba na ajiye shi a gida wanka kawai ya yi ya chanja kaya ya fito ya karɓi key ɗin mota ya taho Plaza. Sai da ya kusa isowa ma ya kira Jide ya tambayeshi ko Ziyadah tana nan dan ya kira numbarta ba ta ɗauka ba. Jide ya ce masa yanzu ta fita. """Ya hanya?"" Ta tambaye shi dan ya faɗa mata zai yi tafiya jiya." """Lafiya. How's school?""" """School kam an dawo kenan ai. Mun fara final battle""" "Kallonta ya tsaya yi. She looks tired. Da da hali, yana so ya bata warm hug ya comforting ɗinta. Ya san ta" sha aiki sosai. "Shinshina kayanta ta yi sannan ta ce ""Tuwo muka yi yau. Miyan kuka da miyan Taushe...""" """Are you okay?"" Ya katseta. Dan idan ya barta za ta cikashi da surutunta." """Yes. Me ka gani?""" """You look weak. Kin ci abinci kuwa? ko aiki kika tsaya yi tun safe?""" """Aww!"" Ta ɗan gyara zamanta. ""Na ɗauka cewa za ka yi ina warin spices""" """Kina warin spices ne?"" Ya faɗa yana ɗaga mata girarsa" """A'ah!"" Ta faɗa da ƙarfi." """I mean. Ka san miyan Kuka idan babu daddawa, da su citta...""" """Ba wai...Ka san na fi awa huɗu ina kitchen kuma...""" """So nake a riƙa siyar da abincin gargajiya"" ya faɗa yana mimicking muryarta." Ziyada ta haɗe fiska. """Eh ɗin. Ai ban gayyaceka ba ka zo. Ni ka tsai da motarka ma na fita"" ta ɓata fuska ta juya tana kallon" window. """Miye laifina a nan?. Ke fa kika fara kawo maganar""" """Ai abinda ke ranka kenan, shi yasa kake ta wani kallona tun dana shiga motarka""" """Dama wani na iya sanin abinda ke ran wani ne?""" """To miyasa kake kallona idan ba cewa za ka yi ina warin Daddawa ba?. Kuma da kake cewa na ce zan" "siyar da abincin gargajiya, dama ban ce kai zan siyarwa abincin ba ai. Ai kwana biyu da baka zuwa Gidan Girki hankalin kowa a kwance yake, yanzu ka dawo kenan za ka fara..."" ta yi shiru" Juyawa ya yi ganin ta tsayar da surutun nata. """Are you okay?"" Ya tambaya ganin tana ɗan matsa cikinta." """Hey, what's wrong? Mu je Asibiti ne?"" Ya jero tambayoyin rabin hankalinsa na kanta sauran kuma yana" tuƙin da ya ke. """Dan Allah idan ka ga pharmacy kusa ka tsaya zan sayi magani"" ta faɗa muryarta ƙasa-ƙasa." Me yake damunta?. Tashi ɗaya ta switching daga surutu ta koma abar tausayi. """Me ya same ki?"" Ya sake tambaya dan gaskiya she looks sick. Tunda ta shigo motar ya lura da hakan." """Ba komai""" """Ba komai kuma?""" Kwantar da kanta ta yi still tana matsa cikinta. """Sunshine, please me yake damunki ne?"" Wannan karan muryarsa cike take da damuwa." "Ta ɗago ta ce "" ba komai. Idan na sha pain reliever zan ji sauƙi""" """Bari mu je Asibiti, please.""" """Kayya! Wai sai na fito maka da komai fili ne. Idan ka ga mace tana haka ai ka san me take nufi. Ni ka" "kaini pharmacy zan sayi magani"" ta ƙarisa maganar kamar za ta yi kuka." Ta ya zai san me yake damunta idan bata faɗa masa ba. Lokacin da ya parking a dai-dai wani pharmacy dake bakin titi ruwa ya riga ya ɓarke sosai. Yana gani tana yunƙurin fita ya dakatar da ita. """Wani magani za a siya miki?""" """Diclofenac""" """Shi kaɗai?""" """Eh""" Ko tunanin ɗaukan Lema bai yi ba ya fita ya sa kansa cikin ruwa ya shiga pharmacy ɗin. Minti huɗu sai gashi ya shigo motar kayansa ya ɗan jiƙe kaɗan. Ya miƙa mata ledar har da ruwan gora. """Ki sha yanzu""" Yana kallo ta ɓalli maganin guda biyu ta sha ta kora da ruwa. """Sorry ko. Are you sure wannan maganin kaɗai zai miki?""" "Ta gyaɗa masa kai ta ce ""shi na ke sha""" Sai da ya tada motar suka fara tafiya sannan ya sake tambayarta me yake damunta. Shiru ta yi bata amsa ba. """I'm worried, Zeeyadah. Please, ki faɗa min abinda ke damunki""" "Ƙasa-ƙasa ta ce ""cramps""" """Cramps"" ya maimaita" Abinda ta faɗa left him more confused. Me ya jawo haka? """Dama yana miki haka ne?""" Ta gyaɗa masa kai. """Sorry"" ya furta dan baya so ya takurata." Saboda ruwan da ake daf ƙofar gida ya parking motarsa. Ya ce ta tsaya ya ɗau Lema a baya ta shiga da shi ta ce masa kar ya damu za ta shiga gidan a haka """NO. Ba za ki fita a haka ruwa ya taɓaki ba""" Ya fita ya ɗau Lema a bayan mota ya buɗeta. Shi da kansa ya buɗe mata ƙofar motar ta fito ya riƙe mata Lemar saboda akwai kaya a hannunta. Rakata ya yi har bakin zauren gidansu sannan ya juya ya koma ya shiga mota. Yana shiga ya jawo wayarsa ya fara browsing me yake jawo cramps na ciwon ciki ga mata?. Daga kalmar MENSTURATION da ya fara gani ya fahimci abinda ke damunta. Dariyan kansa ya fara. Na rashin sanin duk waɗannan abubuwan. Ya san mata na period. But bai taɓa sanin suna shiga pain har haka ba. Cassandra ba ta ciwon mara. Janan ma dai as far as he knows bata irin haka. Mutane biyu kenan da ta dalilinsu ya kamata a ce ya san mata na fama da matsanancin ciwon mara idan suna period. Maimakon ya koma gida sai ya sake komawa Pharmacy. Da ya fito sai ya shiga wani babban provision store dake gefen wajen ya yi siyayya. Gidansu Ziyada ya dawo. Zuwa lokacin ruwa ya tsagaita sai yayyafi. Kiran numbar Ziyada ya yi. Daga yanayin yadda ta ɗau kiran ya san a kwance take. Ce mata ya yi ta turo yaro waje ya zo ya karɓa mata saƙo. Ya jira kusan minti biyar kafin wasu yara su biyu suka zo wajen motarsa. ZEEY Lokacin da Amir da Mu'azu suka kawo mini saƙon Jalal ina kwance akan gado na yi rub da ciki na sa pillow a ta cikina. """Kaka, miye a ciki?"" Na tambaya dan ita ta karɓi ledan." Ita ta kira min yaran ma dan ruwa ya hanasu shigowa sashenmu su ci tuwon dare. "Na ɗan matso da kaina bakin gado ina kallon abinda Kaka ke fitarwa. Ta fito da gwangwanin Milo," Madara... Subhanallahi!. Na tashi da sauri na sauka a gadon na ɗau pack ɗin Always da Kaka ta fitar na mayar cikin ledar. """Kaka a gaban yaran nan fa""" """Ku wuce ku tafi"" na fatattakesu. Wato so suke su ga abinda aka kawo su kai wa Iyayensu gulmata." Sai da yaran suka fita sannan na ɗau ledar na hau gado da shi. Da wayar hannuna na dinga haska ledar ina duba kayan ciki. Kaka tana min tsiya wai idan akwai Kaza in fito da shi za ta ci. Wai Ango ya iya dubiya. Ni dai ban kulata ba. Uban wa ya ce masa ya siyo min pad har kala uku?. Uban wa ma yace masa ya siya min pad?. Haba dan Allah. "Sauran kayan shayi ne a ciki. Madara, Bournvita da Milo. Manyan slize bread guda biyu. Sai wani packet" na dabino. Uban wa ya faɗa masa idan ina period ina iya cin abinci. Sai kuma wata zuciyar ta ce mini. But Ziyada it means he cares... He cares about me... sai na ji na yafe masa laifin siyo mini Pad da ya yi. Yau Jalal ya nuna damuwa a kaina. Tun a cikin mota da ciwon mara ya sani a gaba na ga ya rikice da halin da nake ciki. Har da shiga cikin ruwa ya siyo min pain reliever. He cares... Amma kuma da farko ya bani haushi. Nufinsa bai san me mace take nufi ba idan tana ciwon ciki ta buƙaci shan pain reliever? Wata zuciyar ta ce ƙila Baturiyar matarsa bata yi. And Maybe Janan ma baya mata haka. Amma duk da haka. Ya kamata a ce ya sani tunda shi ba yaro bane. Sai wajajen goma saura na dare da aka gama ruwa sannan na saka ruwan zafi a gas na je na yi wanka. "Anty Red bata iso ba, amma ba mamaki ta min saukar tsakar dare ko Asuba." Bayan na yi wanka sai na yi Alwala na zo na gabatar da sallolin da suka wuce ni. Abincin dana zo da shima ba iya ci na yi ba. Kaka ce ta ci. Sauran kuma ta adana sai da safe. Kiran Jalal ne ya tasheni da sassafe bayan Asuba. Na yi mamaki da na ga period ɗina bai zo cikin dare ba. "Lokacin dana ɗauka sai ya min ya jiki, na ce masa da sauƙi." """Ki zauna a gida ki huta. Zan kira Jide na faɗa masa sai next week za ki cigaba da aikin""" """Amma fa yau ne ƙarshe. Kuma ba jimawa za a yi ba""" """Zeeyaadah"" ya kira sunana da serious voice." """Iya abinda kuka ɗauka ya isa. Daga baya idan akwai buƙatan hakan sai ku cigaba""" """To, na ji"" na faɗa a hankali." """Kin ga abinda na tura miki jiya?""" """Ni Dan Allah ka dena sakani jin kunyar ka. Kuma kawai sai ka je ka siyo abinda ba a sakaka ba. Ce maka" "aka yi bani da shi""" "Sautin murmushinsa na ji kafin ya ce""ki duba Whatsapp ɗinki""" """Aww! Ashe..."" na cire wayar a kunnena na kunna data na shiga Whatsapp." """Ki duba videos ɗinnan da kyau. And please take care of yourself, kin ji""" Rufe bakina na yi ina girgiza kai. Na fara scrolling videos da articles da Jalal ya tura mini duk akan abubuwan da mace za ta yi idan tana ciwon cikin period. Har da tutorial na yadda za ka riƙa compressing cikinka da ruwan zafi. Lallai kam! To an gaya masa ban san duka waɗannan bane. Ya wani kama ya cika min waya da tarin videos da rubutu. Inama na ke da lokacin karanta wani article akan period cramps. Abun da tun sama da shekara goma ake fama da shi kam ai na san ya nake managing kaina. Na tashi daga inda nake kwance. Muna da class guda ɗaya yau da safe. Tunda an ce ba zan ƙarisa aikin "shooting content ba, zan je class ɗin kawai. Sannan dama ina so na je na ga project Supervisor na dan har yanzu bai approving min topic ba." Cikin kayan tea da Jalal ya aiko jiya na haɗa tea mai kauri babu sugar na sha. Na sha pain reliever guda "biyu na saka sauran a jaka. Da shirina na fito in case Anty Red ta kawo mini ziyara ina cikin school. Na sake saka extra pad, a jaka just incase. Kun san dai wannan abun shegen abu ne. Yana iya baka mamaki a koda yaushe." Na yi sallama da Kaka na fito zan wuce school. Ina cikin tafiya na ji muryan yaro na kirana. """Adda Ziya, Adda Ziya"" na juya na ga Faruƙ ne ɗan Baffa Zakari." """Wai ki je Baba Babba yana kiranki""" "Baba Babba, Baffa Lawalli kenan. Haka yawanci 'yan yara-yaran gidan ke kiransa." Na ja ƙaramar tsaki dan na san sai ya ɓata min lokaci. Na wuce sashensu. Ɗan waken siyarwa na ga ɗaya daga cikin matansa tana yi. Ko yaushe ma aka fara a gidan ni ban sani ba. """Ina Ziyadatun take ne?"" Baffa Lawalli ya faɗa yana leƙo kai daga ƙofar ɗakinsa." """Gata nan zuwa"" 'yarsa Ummiyo ta faɗa." """Ina kwana, Baba"" na gaishe shi lokacin dana shiga ɗakinsa." """Lafiya"" ya amsa fiskarsa babu fara'a." """Gobe Wakilan yaron nan Jalal za su zo. A yadda muka tsara za su kawo sadaki ne da abubuwan da ake" "buƙata na al'ada sai a saka rana.""" "Ya ɗaga murya ya ce ""Amma ni ban gane alƙiblar mutumin da kika kawo mana ba""" Didish! Wani irin magana ne wannan? Ana gobe Asabat wakilan Jalal za su zo Dan Allah. """Yaron nan har office ɗinsa na je na yi masa wata magana mai mahimmanci amma duk sadda na kira shi" "baya ɗaukar wayata. Haka yake so mu bashi ke. Bayan bai san darajar Iyayenki ba""" Ya Subhanallahi! Ba dai kuɗi ya je roƙan Jalal ba. Shi ya sa na yi mamaki da ranan Jalal ya tambayeni ko "akwai kuɗin da Alhaji Rabi'u kamar yadda yake kiran Alhaji Nafi'u yake bina. Na faɗa masa babu. Amma kaman ya ce yana bin su Baffa Lawalli kuɗi masu yawa, kusan dubu ɗari biyar. Bai ce komai ba bayan na masa bayanin." Nima kuma ban kawo komai akai ba. """Alhaji Nafi'u mutumin nan hannunsa a buɗe yake. Alkhairi kan Alkhairi idan ya zo gidan nan. Amma shi" "wannan sai dai ya barka da dubu biyar kuɗin mota. Uban me dubu biyar zata mini. Ga shi zai zo gidan nan yana cikin mota ba zai sauko ya zo ya gaishe da mutane ba. Amma ya iya kiran yara ya saka su kwaso mishi leda su kai miki cikin gida""" "To, to, to. Wato har an masa gulman abinda ya faru jiya. To ma wai Fisabilillahi ana cikin ruwan zai ce a" kira masa mutanen gidan zai gaishesu ne?. Babu kowa fa a waje sanda ya kawoni gida jiya saboda ruwa. """Ko ce masa aka yi ke kaɗai ce a gidan. Ba ki faɗa masa kina da ƙanne bane?. Duka yaran gidan nan" "ƙannenki ne fa. Ke ce babba a cikin yara mata a gidan nan""" Na yi shiru ina danne maganar dake taho mini. """Ko ba ke bace babba?""" """Ni ce"" na faɗa a hankali." "Ya ɗan yi shiru ya sosa kansa sannan ya ce ""yanzu dai nawa kuka yi da shi zai kawo sadaki?""" Nawa muka yi da shi zai kawo Sadaki kuma?. Abin ciniki ne? """Baba, na barshi ne ya kawo abinda ya sawwaƙa"" na faɗa ina kallon fiskarsa." Mutumin nan dai ya rantse sai ya kunyata gidanmu a wajen Jalal. Allah ya sa kar ya yi abin kunya a gaban mutanen da za su zo gobe. Ga shi 'yan'uwan Jalal manyan mutane ne. """Abinda ya sawwaƙa kuma?. Ke ba ki san kina da damar da za ki faɗi adadin kuɗi ko dukiyar da kike so a" "matsayin Sadaki bane. Idan ma baki sani ba shi mai arziƙi ne. Dan haka tun yau ki faɗa masa gobe fa Sadakinki kada ya gaza Miliyan ɗaya. Kina jina?""" Dariya ne ya taho min. Yo maganarsa ai abar dariya ce. "Haka kawai sai na kira Jalal na ce ""Hello, Jalal. Wai in ji yayan Babana kada ku kawo Sadaki ƙasa da Naira" "Miliyan ɗaya""." """Kina jina dai?"" Ya sake maimaitawa." """Na ji Baba. Zan wuce Makaranta"" na miƙe tun ma kafin ya sake ɓaro wata maganar da zai sa na ɗura" masa ashar. Na ga alama idan ban masa hakan ba ba zai fita a harkata ba. Dama na san saboda ya ga Jalal ya fi Alhaji Nafi'u kuɗi ya saka shi haƙura da batun Alhaji Nafi'un. To yanzu kuma ya je ya yiwa Jalal maula bai kulashi ba. Shine yake cewa Alhaji Nafi'u ya fi Jalal alkhairi. Na fito daga sashensu raina a ɓace. Da ɓacin rai na isa school. Ban san wace tsiyar Baffa Lawalli zai kawo ba idan Wakilan Jalal suka zo gobe. Duk da dai Baffa Adamu ne zai jagoranci zaman amma ina tsoron abinda kwaɗayayyen tsohon nan zai iya yi. "Ku ji fa. Wai na ce kada a kawo sadaki ƙasa da Miliyan ɗaya. A'a, su siyar dani kawai na san cewa aurena" da Jalal shi zai kawo masa ƙarshen Talauci. Mtssw! A da na yi niyyar yau zan faɗawa Faty za a kawo Sadakina. Sai kawai na fasa. Gara na bari idan an kawo ɗin komai ya tafi lafiya sai na faɗa mata. "Kai ciki bai karɓi Faty ba. Gaba ɗaya sai wasu ƙuraje fiskarta yake, ga wani baƙi da ta yi. Duk wani gayun" "Faty babu shi yanzu. Tunda muka resuming school ma manyan hijabi da jilbab take sakawa ta shigo school. Fiskarta fayau wani lokacin ko mai babu. Dama an ce ciki yana saka wasu matan ƙazanta. Har ji nake ana cewa wasu matan idan suna laulayin ciki basa son wanka. Sai su yi kwanaki ba su yi wanka ba. To, Allah dai ya sauketa lafiya." Muna gama class za mu fita mu je wajen supervisor ɗinmu Faty ta tambayeni aron kuɗi dubu biyar. Na ce mata bani da cash na ciro wayata na mata transfer. Da muka je Department sai muka samu nata supervisor ɗin baya nan. Ta jirani na shiga wajen nawa. Ba mu ɗau lokaci ba dan shima Supervisorn nawa fita zai yi wai suna da meeting. Ni dai tunda ya approving min topic ya ce in je in kawo Chapter One na masa godiya na fita. """Yanzu gida za ki wuce?"" Faty ta tambayeni." """Gida zan wuce""" """Yau ba za ki je Restaurant ɗin bane?"" Na faɗa mata ina zuwa aiki a restaurant amma bata san full" details ɗin ba. """Bestie bana jin daɗi ne. Kin san idan abun nan ya zo yadda nake komawa. Yanzuma daurewa kawai" "nake""" """Ni kuma da nake fama da Baby a ciki fa?""" """Sannu Maman Baby. Allah ya baki lafiya"" na faɗa ina dariya. Maganar kawo Sadakin nan yanata" "mintsinina na faɗa mata, amma na danne. Idan komai ya tabbata zan faɗa mata." "Anguwarmu akwai nisa da nata dan haka ita ta fara shiga Keke na biya mata kuɗin ta wuce, kafin nima" na tsare wani na wuce gida. Tabbas akwai wani abu a ƙasa gameda auren Faty. Ba kawai laulayin ciki bane. Na dai ja bakina na yi shiru. Idan bata faɗa ba nima ba zan tambaya ba. Ai dama cewa aka yi AURE SIRRI NE. Tun ina cikin Keke na ke jin alamar Anty Red ta iso. Ina zuwa gida ko kaya ban cire ba ita na fara dubawa. "Ga shi nan ta faso da muƙarrabenta baƙi-baƙi, fatsi-fatsi, ja-ja-ja-ja. Dama su suke fara isowa. Yau ake yinta..." CHAPTER THIRTY SIX JAYKAY Jalal yana zaune a ɗakinsa yana duba wasu takardu sai ya ji ana buga masa ƙofa. """Dad, it's me"" ya jiyo muryan Junior" """Come in"" Jalal ya faɗa dan ɗakin nasa a buɗe yake." Junior ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo. Sanye yake da Blue Pyjamas mai zanen space ships. """Ba ka yi bacci ba?"" Jalal ya tambaya hankalinsa na kan takardar da yake dubawa" """Dad, a nan zan yi bacci yau""" "Sai a lokacin Jalal ya ɗago idanunsa ya cire reading glass ɗinsa sannan ya ce wa yaron ""come here""" Junior ya zo ya zauna a cinyarsa. """Are you okay?"" Ya tambayeshi yana taɓa goshinsa. Junior ya ce ""I'm fine, Dad""" """You sure?, babu zazzaɓi?""" """Babu""" """Good""" Gyara masa zama ya yi a cinyar nasa sannan ya cigaba da duba takardun da ke gabansa. Wani sabon gini ne da suke son fara aikinsa cikin satin nan shine Engineer ɗin ya tura masa final plan ɗin da aka sake adjusting bayan Architect ya zana wajen. """Dad, wai za ka yi aure?"" Junior ya faɗa yana kallon Dad ɗinsa." Jalal ya juyo da ɗan sauri. """Who told you that?""" """Na ji Aunt Janan da Hajiya suna magana yau da safe """ Ajiye takardar hannunsa ya yi ya rungumeshi da kyau. Ashe gabaɗaya ya manta bai zaunar da ɗan nasa ya masa maganar auren da zai yi ba. "Lokacin da ya sake shi, sai ya kissing goshinsa ya fara masa bayani da sigar da zai fahimci abinda yake" faruwa. Ya masa bayani akan halarcin auren mace sama da ɗaya a Musulunci da kuma yadda hakan ya banbanta da al'adun wasu addinan. Ya nuna masa idan aka yi auren Mom ɗinsa ta sani za ta zo ta ɗauke shi daga Nigeria dan haka kar ya faɗa mata. Wannan ya zama little secret ɗinsu. "Ya tambayi yaron ko ya fi son zama da Mom ɗinsa a London?. Junior ya ce a'a, shi ya fi son zaman" Nigeria. A nan Nigeria yana da friends sosai kuma Hajiya ta fi kula da shi akan Mom ɗinsa da bata zama a gida. Ashe shima yaron ba jin daɗin rashin samun kulawar Mom ɗinsa yake ba. Lokacin da Jalal ya gamsu cewa Junior ya fahimce shi sai ya ce ya je ya kwanta a gado. Junior ya miƙe ya je ya hau gadon Jalal ya kwanta. """Recite your Azkar kafin ka kwanta ka ji?""" """Yes, Dad""" Yana jin yaron ya fara karanto Azkar ɗin da ɗan ƙarfi. Hakan sai ya faranta masa rai. Gaskiya Hajiya tana ƙoƙari sosai akan tarbiyan ɗan nasa. Bai gama aikin da ya ke ba har kusan ƙarfe ɗaya na dare kafin ya tattara komai ya miƙe ya shiga banɗaki. Da ya fito sai ya kwanta gefen Junior ya kashe wutan ɗakin. Yaron tuni har ya yi bacci. "Tunanin matar da zai aura ɗinne ya faɗo masa. Nan da kwanaki kaɗan za ta zama matarsa, amma har" yanzu fushi take da shi saboda ya turawa Alhaji Nafi'u kuɗi. Jiya ya so ya je ya ganta ta ce masa wai za ta je Kaduna gidan Mamanta. Bayan ta isa daga baya sai ya kira ya ce ta bawa Ummanta su gaisa. Jiya ta ce masa za ta dawo amma bata dawo a jiyan ba sai ƙarfe takwas na dare ta tura masa saƙo wai ta dawo. Gobe kam dole ya je ya ganta. Sannan ya tambayeta ko akwai abinda ta ke buƙata. Da safe da ya shirya ya fito zai wuce office sai Hajiya ke ce masa ya kira ƙanwarta Hajiya Amina dake "Lagos su yi magana, wai akwai cikon kuɗin da zai bayar na lefe. Ya ce mata zai kira." Bai yi mamaki ba da Hajiya ta ƙi ɗaukan kwangilar haɗa kayan Lefe da sauran abubuwan da ya shafi auren nasa. Ya san yin hakan zai tuno mata da shirye-shiryen bikin Jamal ne. Yadda ta yi ta up and down akan shirye-shiryen bikin abu kuma ya zo da ƙarar kwana bikin bai yiwu ba. Da ya ce mata ba za a yi biki ba simple wedding ne daga ɗaurin aure shikenan bata ce komai ba sai addu'ar alkhairi da ta yi masa dan kamar ma ta fi son hakan. A ranan yana ji Janan tana faɗin ita fa gara Hajiya ta shirya dan Wallahi sai an yi hidima sosai a bikinta. Hajiya ta ce mata Allah ya nuna mana lokacin tukunna. Yana cikin mota ya kira Hajiya Aminan. Tana fara masa bayanin ƙabli da ba'adi na abubuwan da suka rage ya tambayeta nawa zai tura ta faɗa masa. Ya ce idan ya isa office zai tura mata kuɗin. "Haɗa lefe, kai sadaki, everything was new to him. Shekaru goma baya bai yi duka wannan ba. Lokacin da" aka kai sadaki bayan an dawo sai da Jalal ya tsare Ibrahim saboda da shi aka je ya ce ya bashi labarin yadda abun ya kasance. Ibrahim yai ta masa tsiya kafin daga baya ya faɗa masa irin tarbar da aka musu a gidansu Ziyada. ZEEY Dama haka Mata ke jigila idan za su yi aure?. Like na san ni da Faty mun yi ta jigilar shiga kasuwa kafin bikinta amma ni nawa jigilar ta ziyarar 'yan'uwa ne. Jiya da dare na dawo daga Kaduna wajen Ummana. Daga dawowata kuma yau da safe na sake wucewa gidansu Ummana a nan Zaria. Wai suma sai na je na faɗa musu an saka rana. Haka na dinga yawon raba goro da drinks ina zuwa gidan 'yan'uwan Ummana da ke Zaria ina faɗa musu an sa bikina. Kakannina na wajen uwa duka sun rasu. Baban Mamana nema na ɗan san shi lokacin da nake yarinya muna zuwa gidan. Ina ga ya rasu ina Primary 5 ko 6 haka. Ban san Kakata mace ba. Ta rasu tun kafin Ummana ta auri Babana. Duk inda na je sai su fara ƙorafin wai an saka auren da wuri. Wai yanzu da suka zuba kuɗi a gona da "wani kuɗin za a min kayan ɗaki?. Ni dai na dinga maimaita musu abu ɗaya, kada su damu daga baya za a yi taron biki dan haka sai su shirya su min duk abinda suke so." Duk yadda na so in je gidan Umma Hadiza a ranan ban samu zuwa ba dan kafin na baro gidansu wani Kawuna ma Magariba ta kusa ga shi Jalal ya kirani wai yana hanya. Haka na tarkata na koma gida. Kaman haɗin baki ina komawa gida sai na tarar Umman Fada ta zo wai sun yi waya da Anty Binta ta ce ta zo ta sameni. Ga Anty Hafsah da Maman Asma'u Amaryar Baffa Zakari sun shigo wai ni suke jira dama. Haka suka sakani a gaba akan batun Waliman Aure. Wai duk da an ce babu biki dole fa za a yi Walima. """Yanzu dai ki kira Ango ki karɓi kuɗin Walima a wajensa. Duk waɗanda aka aurar a gidan nan ai sai da" "aka musu Walima ko?"" Umman Fada ta faɗa tana kallon Kaka." """Ga maganar Lefe ma mun ji shiru. Ko dan ya kawo Daloli shikenan sai a yafe masa lefe"" Maman Asma'u" ce ke magana. """To ke Ziyada kun yi maganar an yafe masa lefe ne?"" Maman Suwaiba da ban san yaushe ta shigo ɗakin" ba ta tambaya. Yau na shiga uku. Ni wai mi suke nufi da nine da suka sakani a gaba kowa na faɗin son ransa. Su za su yi auren ne da suke ta damuwa akan an kawo lefe ko ba a kawo lefe ba. Na yi shiru ban musu magana ba. "Anty Hafsah ce ta ari bakina ta ce ""Jama'a, kuɗin Walima dai za a karɓa a wajen Ango. Maganar Lefe" "kuma ina so yake ta je ta gani a gidansa""" """Shikenan kuma sai ba za a kawo Lefe gida 'yan'uwa su gani a sa Albarka ba""" """Hafsah ku a Gombe ba har akwatin iyayen Amarya kuke ba?"" Maman Suwaiba ta faɗa bayan Maman" Asma'u ta yi magana. """Ai na ga yanzu wasu basa kawo Lefe saboda sata da kuma gudun bakin mutane. Varin Lefen ake a gidan" "Amarya idan ta je sai ta ga kayanta a can""" Miƙewa na yi na zari Hijabi na fita dan idan na cigaba da sauraron maganganunsu raina ne zai yi ta ɓaci. Ina jin Umman Fada tana ƙwala min kira na yi ficewata. Allah ya taimakeni ko zaure ban kai ba sai ga kiran Jalal. Ina ɗauka ya ce mini ya iso. Duk da dai na so a ce na yi wanka na shirya kafin in fita amma mutanen da suka zo suka ritseni a ɗaki sun hana hakan. "Ina shiga motar Jalal ya ce ""Masha Allah""." """Me ya faru?""" """Ke ce kuwa? Barin ga fiskarki da kyau ko wata ce ba ke ba""" Na juyar da fiskata gefe dan ƙoƙarin haska fiskata yake da wayarsa. """I'm actually happy kin fara respecting lokaci""" """Dama ina respecting lokaci kai ne dai baka da haƙuri""" """Oh really!""" """Yes""" """To ya aka yi Amaryar Jalal. Ya kika baro su Mama a Kaduna?""" Na riƙe goshina dake sarawa na ce masa suna nan lafiya ta ce na gaishe shi. """Are you okay?""" """I'm okay, kawai gajiya ne""" """Sorry, idan an kawo ki gidana, zan miki massage za ki warware""" """Wa ɗin?"" Na faɗa ina zaro ido." """Ke mana"" ya faɗa yana ɗaga mini gira" """Ni bana buƙata""" """Are you sure?. Na iya fa""" """Still bana buƙata""" Kiran wayarsa aka yi. Ina ji yana maganar yanzu zai tambayeni sizes ɗin na ce to an zo wajen. "Bayan ya gama wayar sai ya juyo ya kalleni ya ce ""kin ji wata Aunt ɗina ta ce na tambayeki sizes ɗinki""" Har zan ce masa sizes ɗin me sai na tuna yanzu sai ya twisting maganata ya fara min maganan 'yan Bariki. """Ka bani numbanta zan tura mata""" """Ba kya so na san sizes ɗinki ne?""" """Babu ruwanka a ciki""" """Kar ki damu zan gwada su da kaina idan kika zo""" Na yi saurin tare ƙirjina duk da hijabi na saka. Zai gwada me?. Wani munafukin murmushi ya saka. Na ce a raina yau na ɗebo ruwan dafa kaina da wannan mutumin. Sai da ya gama min iya shege kafin ya tambayeni ko akwai abinda nake buƙata for the wedding na ce masa babu. Ya ce na tura masa account details ɗina zai bani kuɗin salon Janan ta ce ana bawa Amare kuɗin salon. A raina na ce da Janan bata faɗa masa ba ba zai bayar ba kenan. Kaman na yi masa maganar Walima sai kuma na fasa. Kada ya ga ina tambayarsa kuɗi tun ba a yi aure ba. Akwai wasu kuɗaɗena dana ke tarawa na Restaurant idan har ta kama sai an yi Walimar sai na cire wani abu a ciki na basu. Ina cikin motar alert ya shigo bayan na masa text ɗin account number na. Na zaro ido ganin amount ɗin. """Kuɗin dayawa""" """Dayawa sosai ko?. To rage kaɗan ki bawa doguwar Sisternki dana gani ranan""" Na haɗe rai. Wato bai manta da Mardiyyah ba. """Ya da ɓata rai. Cewa fa kika yi ya yi yawa""" """To an gode""" """Zeeyadah"" jin yadda ya kirani sounding serious sai na fuskance shi da kyau na ce na'am." """Aurenmu is in 6 days. Kin shirya?""" Na yi shiru. Nauyin tambayar na sauka mini. NA SHIRYA? Tabbas ban shirya ba "Ban shirya amsa sunan matarsa ba. Ban shirya barin wajen Kakata ba. Yanzu idan na bar gidan nan, Kaka" will be lonely. Ban shirya ma komai ba. Ko Faty Bestie ban faɗawa zan yi aure ba har yanzu. "And most importantly," Ban shirya yaƙi da feelings ɗin dana ke ji akan Jalal ba. And wataƙila saboda denying ɗinsa da nake shi ya sa kullum ƙaruwa yake a zuciyata. """Ai babu shirin da zan yi. It's just a deal ko?"" Na faɗa ina hiding wani ɗacin da ya taho mini." """It's just a deal"" ya maimaita abinda na faɗa." Ni da shi ɗin duk sai muka yi shiru... "Lokacin dana shiga gida 'yan gulma sun tafi. Umman Fada ce kawai, itama kuma tafiyar take shirin yi." "Ban kulata ba tana ta tambayata ko Ango ne ya zo, ko na masa maganar Walima. Na shareta." Sai da ta tafi Kaka ta fara lallashina. """Ki yi hakuri. Komai zai zo da sauƙi. Da yardar Allah wannan auren zai zame miki alkhairi duniya da" "lahira""" Na ɗan kalleta ina tuno yadda muka gama maimaitawa junanmu cewa auren nan bana soyayya bane. DEAL ne Kaka dai ta dage tana ta min addu'ar Allah ya zaunar dani lafiya a gidan Jalal har ƙarshen rayuwata. Ko Amin ban iya faɗa ba saboda ina tsoron auren. Washegari cikin 1.5 Million da Jalal ya tura mini na turawa Anty Hafsah 500k na ce kuɗin Walima. Ita ce na yarda da ita za ta tsaya akan komai tsakani da Allah. Dana bar gidanta sai na wuce gidan Faty. Itama yau nake so na faɗa mata komai. Ba wasu ƙawaye nake da su ba dama. Wanda muka taso a Anguwarmu yawanci sun yi aure. Sai tsirarun 'yan class ɗinmu da muke mutunci sai kuma kaɗan daga cikin ƙawayen Faty da muke tare. Ni gaskiya ba zan yi gayya ba. Idan Faty ta zo shikenan. Inada cousins mata dayawa da za su maye gurbin "ƙawaye. Akwai wata ƙawata Aishatu da muka yi Secondary School tare, ta gama Diploma a KadPoly" "kwanaki yanzu tana teaching a wani private School. Itama har yanzu bata yi aure ba, so zan gayyaceta." Hakan ya wadatar tunda komai lowkey ne. *** """Zeey, wasa kike amma?"" Faty ta faɗa bayan na faɗa mata aurena nan da 5 days." """Ki yi haƙuri komai ya zo a ƙurarren lokaci ne na san ban kyauta miki ba"" na yi ƙoƙarin depending kaina." """Wait, Wait, Wait. Ziyada kina nufin ina garin nan kika yi sabon Saurayi. Kika bashi dama ya turo gidanku." "Har ya kawo sadaki aka sa rana amma baki faɗa min ba sai yanzu. Bestie I'm confused. Na san dai ba mu yi faɗa ba. Me yake faruwa?. Ko kina da wata Bestie ɗinne bayan ni?""" """Na san ban kyauta ba. Allah nima ban san za a saka ranan da wurwuri haka ba. Ki yi haƙuri...""" """Tukunna ma waye Angon? A ina kuka haɗu da ban sani ba. Ko Alhaji Nafi'u ne?""" """Allah ya sawwaƙa na auri Alhaji Nafi'u"" na yi saurin faɗa." """To waye mysterious Angon namu?""" Na ɗan yi shiru ina lissafin ta ina ma zan fara faɗa mata. """Jalal Maiyaƙi. Ɗan Hajiya Layla dana ce miki ina zuwa gidanta kwanaki""" Faty ta waro ido tana kallona cikin rashin gamsuwa. """Hajiya Laylan da kika ce min za ki fara aiki a Restaurant ɗinta. Wait Jalal Maiyaƙi?... yayan Janan" "Maiyaƙi?. Ina Following Janan a Instagram""" """Shi"" na faɗa a hankali." """As in Jalal Maiyaƙi za ki aura nan da kwana biyar?""" Na gyaɗa mata kai. """Ikon Allah. Like ya kuka haɗu?. Yaushe kuka fara soyayya?. Ko Hajiyarsa ce ta haɗa ku?""" """Kawai Allah ne ya haɗamu. Ranan na je gidansu sai ya rage min hanya. We exchange contact and here" "we are"" na yi mata bayanin da zai fi kama hankalinta." """Shegiya ƙawata. Ashe kin samu big fish shine kika yi ta ɓoye shi sai yanzu ki ce wai komai ya zo a" "ƙurarren lokaci""" """Ni dai ki yi haƙuri""" """Gaskiya na yi mamaki wai Jalal Maiyaƙi za ki aura. Like gidansu fa Babban Family ne. Zeey, gaskiya you" "are so lucky""" """Thank you Bestie""" """To, Allah ya bada zaman lafiya"" Faty ta faɗa fiskarta na nuni da addu'ar da ta yi bai kai zuci ba." CHAPTER THIRTY SEVEN ZEEY Jummu'ah Babbar rana. Jummu'ar yau Babban rana ce a gareni. Yau za a yi Walimar aurena. Jiya Kaka ta sakani kukan da ban taɓa yi ba tun da muke tare. 'Yar tsohuwar nan ashe tana da kuɗi a "ɓoye bata taɓa faɗa mini ba. Baffa Adamu ne ya kirani a waya jiya yake ce mini wai Kaka ta bada Dubu ɗari bakwai a yi min kayan ɗaki da hidimar biki. Lokacin dana comfronting ɗinta sai ta ce wai ta jima tana tara mini kuɗin kayan ɗaki. Dama so take ya kai Miliyan ɗaya kafin bikina to kuma sai auren ya zo a kusa- kusa. Like, Why?. Bana tunanin duk kuɗin da aka ce su Baffa sun tara na hidimar bikina ya kai rabin abinda Kaka ta bayar." Haka na riƙe Kaka na dinga yi mata kuka. Yanzu muna tare kullum da tsohuwar nan amma taru take ban sani ba. Wani Ƙaninta dake Kano ne ya turawa Baffa Adamu kuɗin ina ga shine yake tara mata a account ɗinsa. Jiya saboda yadda Kaka ta sakani emotional ko iya zuwa Salon wanke kai ban yi ba. Da yamma nema wata yarinyar maƙotanmu da take Lalle da kitso ta zo ta mini Lalle a hannu da ƙafa ja da ɗan baƙi kaɗan. Lallen kuwa ya yi kyau ba kaɗan ba. Da ace shagon Faty a buɗe yake da nan zan je a min gyaran jiki da Lalle. Ni yanzu ma na bar maganar gyaran jiki idan na je salon na wanke kai na yi kitso shikenan. Babu lokacin yin wani tsarabe-tsarabe. Gidanmu ya fara cika. Dan mutanen Katsina ma jiya suka shigo. Anty Binta autarsu Baffa Lawalli da ke aure a Bauchi itama ta iso. Ni da Mardiyyah da Walidah 'yar Baffa Adamu muka tafi shagon Salon ɗin. Shekaranjiya na tattara kayana na rabawa 'yan gidan kayayyakina da ba zan tafi da su ba. Kusan takalma da bags ɗina da wasu kayan duka a Mardiyyah na bawa. Na haɗa mata har da ring light ɗina da nake content da shi. Da dare sai ta shigo yi min godiya. Bata taɓa tsammani zan mata kyauta irin haka ba. Ni dama ba gaba "nake da ita ba. Munafurcin Mamanta da kuma yadda take competition da ni ya sa bana shiga harkarta. Na bata shawaran ta dena content da take na girki. Tunda ɗinki ta ke yi yanzu ta riƙa yi content na ɗinki, ai babu teloli masu content ɗin ɗinki sosai da Hausa ba kaman food content da mutane suka yi yawa ba." "Sai da na yi maganar nema ta ce mini ashe ta watsar da shi saboda babu followers, wai har yanzu a" Instagram ko Followers ɗari bata kai ba. A tiktok nema take da Followers 500. Wannan magana da muka yi ya sa ta sake jiki da ni ta fara bina munata up and down na maganar Walima. Ummana ma ta zo daga Kaduna jiya da safe. A gidanmu ta wuni sai yamma lis ta koma gidansu. Itama da "ta ji kuɗin da Kaka ta bayar sai da ta yiwa Kaka godiya na musamman. Har cewa ta yi ""Baaba Altine ai ke ce uwar Ziyada ba ni ba""" "Muka je Salon aka fara wanke min kai. Bayan an gama min wanki an yi blow drying, sai aka yi stretching" ɗinsa ya sake miƙewa ya sauka a kafaɗana. Dama ina da cikar gashi wanda sai an yi stretching ake ganin tsayinsa. Suka fara zuba min ƙananun kitso. Ana cikin kitson Faty ta kirani wai ta iso gidanmu an ce mata bana nan. Na mata kwatancen shagon da muke dan babu nisa da Unguwarmu na ce ta zo ta sameni. Ƙarshe da bata gane wajen bama Mardiyyah na saka ta je ta taho da ita. Da ta zo muka zauna muna taɓa hiran bikin. Sai tsiya take min wai Amaryar Jalal. Ni dai nawa murmushi. Muna shagon sai ga alert ɗin dubu ɗari daga yaya Aminu. Ina gani na ce Allah Sarki. Yanzu haka yana da uzuri da kuɗin amma ya tura min gudummawa. Na kira shi bai ɗauka ba sai bayan minti biyu ya kira ni. Ina ɗaukan wayar na fara masa godiya na ce masa kuɗin sun yi yawa. Yace idan yana da fiye da haka ma zai yiwa Favourite Sister ɗinsa. Ya ce min Insha Allahu yau yana hanya. Ya nemi excuse a wajen aiki zai tashi ƙarfe ɗaya ana sallan Jummu'ah zai kamo hanyar Zaria. Na ce masa Allah ya kawo shi lafiya. Na sake yi masa godiya sannan na kashe wayar. Ba mu muka bar salon ba sai wajen ƙarfe ɗaya har ta wuce. Da ƙyar muka samu Keke saboda ana tafiya sallar Jummu'ah. Muka dawo gida na samu ana ta masifar wai wasu sun kwashe naman da aka soya jiya. Sa guda aka aiko "daga gidansu Jalal na hidiman Biki. Kuma a jiyan da aka kawo aka yanka aka gyarata. Cewa Anty Hafsah na yi dan Allah ta tsaya akai. Ƙarshe da suka fara masifarsu tun a wajen suyan shine Kaka ta ce a raba kashi huɗu. Ɗaya za a ajiye a wajen Kaka. Kashi biyu Anty Hafsah ta ajiye wanda za a yi abincin ranan ɗaurin aure da shi ɗaya kashin kuma Maman Suwaiba ta ajiye wanda za a yi abincin Walima da shi. To shine wai ana saka abinci a takeaway ba a je ko'ina ba nama ya ƙare. Kuma fa harda Kaji guda goma da aka ce Baffa Adamu ya aiko. Ita Maman Suwaiba sai masifar wai ai naman da ke wajenta dama babu yawa take, wai Anty Hafsah ta fito mata da naman wajenta a ƙara. Ita kuma Anty Hafsah na maganar ai naman dake wajenta na abincin gobe ne. Wai naman da aka bawa Maman Suwaiba yana da yawa me yasa ya kasa idan ba ɓoyewa ta yi ba." Kai! Ni da ban dawo gidan bama. Wani irin abu ne gida ya cika da mutane amma ana faɗa akan nama. Ƙarshe dai Kaka ce ta sa aka fito da naman wajenta a cikin Kwalla ta ɗebi rabi ta bawa Maman Suwaiba. "Ni ko magana ban yi ba dan raina a ɓace yake, idan na ce zan yi magana ma wani ƙarin ɓacin ran zan" sakawa kaina. "Da aka watse sai Faty ke faɗa mini a kowanni Biki sai an samu irin haka, wai itama haka aka yi ta faɗa a" lokacin bikinta. Na ce mata nata da sauƙi. Ni nawa da gangan dama so suke su ɓata Bikin nan. Tun jiya da safe dana fita na karɓo wasu ɗinkakkun kaya da Jalal ya aiko mini wanda zan saka a biki suke ta gulmar wai ba a kawo Lefe ba. Ku ji gulma fa. Lokacin da na yi wanka na yi sallar la'asar sai na saka ɗaya da cikin kayan da Jalal ya aiko mini. Har da wata haɗaɗɗiyar Alkyabba amma ban sakata ba sai zamu fita wajen Walima. Faty ce ta min light makeup a fiskata na yi kyau sosai. Ƙarfe huɗu da minti goma aka zo aka kiramu wai Malama ta iso. "Na saka Alkyabbata muka yi hotuna da su Faty, Mardiyya, Aishatu, da wasu cousins ɗina kafin muka fita." A ƙofar gidanmu aka kafa tanti guda biyu aka saka kujeru. A nan za a yi Walimar. Na zauna a kujera Faty da Aishatu suka sakani a tsakiya. Malamar da ta zo na santa. Matar Babban Malamin Islamiyyarmu ne lokacin da nake Hadda. Ta zage ta "yi nasiha mai ratsa jiki. Duk da rabin hankalina baya wajen amma akwai abu biyu da ta riƙa maimaitawa har sai da suka tsaya min a rai, BIYAYYA da kuma HAƘURI." Gobe za a ɗaura aurena da Jalal. Daga gobe zan fara amsa sunan matarsa. Daga gobe zan koyawa kaina yi masa biyayya da kuma haƙurin zama da shi. Ga shi dai it's sound easy a baki. Amma ni na san abune mai matuƙar wahala. "Sai dai, na ɗau alƙawarin zan yi iya ƙoƙarina a kan wannan auren. Idan kuma na gaza to duk abinda ya" "biyo baya zan rungumeshi da hannu bibbiyu na ɗaukeshi a matsayin ƙaddarata. Afterall, Allah shi ya haɗamu tun farko. Kuma shi na barwa ragaman wannan auren. Idan akwai yiwuwar Jalal zai soni a gaba har ya riƙeni a matsayin matarsa ta gaskiya, to Alhamdulillahi. Idan kuma akwai ƙaddarar rabuwa da shi a gaba, to Allah ya sa ya zo min da sauƙi." Tsirarun 'yan Makarantarmu sun zo. Na ga kaman mutane huɗu a wajen Walimar. Da aka tashi daga Walima na saka Faty ta musu magana muka koma cikin gida Mardiyyah ta basu ledar dana sa ta haɗawa ƙawayen da za su zo. Har dare ban samu kaina ba. Daga wannan su shigo gaisheni. Sai masu kirana su bani shawara. Sai waɗanda suka zo suka ɗan kawo mini Gift. Zuwa waɗanda suke kirana suna lissafin mutane nawa za su kai Amarya da kuma maganar kayan gara. Har ƙarfe ɗayan dare ban kwanta ba. Ƙarshe ma yunwa ya sakani a gaba. Na tashi na nemo kayan tea na haɗa da daren na fara sha na ɗau soyayyen nama guda huɗu ina ci. Ina ga tun safe rabona da abincin kirki dana sha kunu da Alalen da aka yi da safe. Kai hidimar aure akwai wahala. Ina shan shayin ina kallon mutanen da ke kwance a ɗakin namu. Mutane huɗu ne a ƙasa. Kaka tana kwance a gado. Allah Sarki Kaks tawa. Daga gobe shikenan ita kaɗai zata riƙa kwana a wannan ɗakin. Dana gama shan shayin sai na zo na hau gadon nima na kwanta na jawo wayata dan na kalli hotunan da muka yi ɗazu da yamma. """Ki kwanta ki huta, Ziyadatu"" Kaka ta faɗa da muryan bacci." """Zan kwanta Kaka"" na faɗa ina ajiye wayar a gefen pillow. Kaina kamar zai fashe saboda ciwo. Ga zafin" "kitso, hannun matar data min kitson akwai zafi." Na matsa jikin Kaka sosai sannan na rufe idanuna. Allah ya nuna mana gobe da rai da lafiya. Allah kuma ya kaɗe fitina ya sa a yi komai lafiya a gama lafiya. *** """Yaushe ne ɗaurin auren?"" Anty Ruƙayya ƙanwar Ummana ta tambaya lokacin da ta shigo ɗakin Kaka ta" ajiye jakarta. """Ƙarfe shaɗaya za a ɗaura a Masallaci"" Walida ta amsa mata." """Ni dana ga ba a ɗauke tantin jiya ba na ɗauka a ƙofar gida za a ɗaura ai""" "Kaka da ke shan Kunun gyaɗa ta ce ""za su kwashe ai. A Masallacin Malam Shamsu nan kusa za a ɗaura" "auren""" Fiskar Kaka ɗauke da farin ciki. Ta sha farin dry lace ɗinkin doguwar riga ta ci ɗauri. Yau ake aurena kam ai dole ta sha kyau. "Nima wankan na yi amma ban sa kaya ba tukun, ina jiran Faty ta iso ta min makeup. Cikin kayan da aka" kawo min zan sa ɗaya da safe. Ɗaya da rana. Sai kuma farin lafayyar da ke ciki sai zan saka idan za a kaini. """Amarya wai ki zo in ji Maman Suwaiba"" wata mata da ban gama gane alaƙar dake tsakaninmu da ita ba" ta leƙo ɗakin ta faɗa. """Kai ni kam ku barni dan Allah. Ɗazu ma fa kafin na yi wanka na je wajenta. Ni kam ku rabani da maganar" "abincin nan"" na faɗa ina jan tsaki. Tun jiya ake abu ɗaya sai kace a kaina za a fara Biki a gidan." "Ummana da suka shigo tareda Anty Ruƙayya ta ce ""ki yi haƙuri ki je ki sameta. Tun shekaranjiya take" "hidima a gidan nan saboda ke""" Na zari gyalen Abayar da ke jikina na fita. Ina shiga wajensu aka fara kirana Amarya-Amarya. Ina zuwa na samu Maman Suwaiba. Wai abincin da za a kai gidansu Ummana take tambayar ya za a yi. Like seriously! Ni na san ya ake yi ne. Na ce mata su yi duk yadda suka ga dama. Na san neman magana ne ya sa ta nemeni saboda in ce ta yi abun kai za ta aika abincin Biki gidansu Ummana. Ina dawowa ɗakinmu sai na kira Faty na tambayeta yaushe za ta iso ga shi har ƙarfe tara ta wuce. Ta ce min yanzu za ta fito daga gida. """Amarya kin ci abinci kuwa?"" Anty Binta ta tambayeni lokacin da ta sa aka karɓo mata Masa a cikin gida." Na girgiza mata kai. """Ina Walida. Ko karɓo wa Amarya abinci ta ci""" "Mardiyyah da ke ɗakin ta miƙe ta ce ""me za a karɓo miki?""" Wai!. Ni bata abinci ma nake ba. Kunu zan sha ko Masa zan ci ko kuma Shinkafa?. """Akwai Tuwo. Mardiyyah ku kawo mata Tuwo jiya haka ta wuni bata ci abinci ba"" Kaka ta faɗawa" Mardiyyah. Allah Sarki. Kaka ta fini sanin abinda ya dace na ci. "Ummana da ke cin Masa ta ce itama a karɓo mata Tuwon, da ta san akwai Tuwo da bata fara cin Masar" ba. Lokacin da Mardiyyah ta kawo min tuwon sai na ɗauki cokalin dana gani a wani plate da aka ci abinci aka ajiye na fara ci. Tuwon Shinkafa ne da miyar Taushe. Ina cikin ci sai ga yara sun shigo sashenmu da gudu suna faɗin wai ana rikici a ƙofar gida. """Rikici kuma?"" Anty Binta ta faɗa ta fita wajensu." Addu'a na fara karantowa a raina dan har ga Allah bana son abinda zai kawo rikici a yau ɗinnan. "Duk sai suka fita suka barni a ɗakin, har Kaka ta fita ana tambayar yaran mi yake faruwa." Sunan da na ji Yakubu ya faɗa ya sa na furta Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un. Alhaji Nafi'u. Me Alhaji Nafi'u ya zo yi?. "Ina zaune cikina ya murɗa, jikina ya fara rawa." """Ya Allah ka rabani da sharrin wannan mutumin"" na furta a fili hawaye na ciko mini." Ina jin surutu da hayaniyar na ƙaruwa amma ban tashi daga inda nake ba. Addu'a kawai nake maimaitawa. Can na jiyo muryan Baffa Mamman yana tambayar ina nake. Aka ce masa ina cikin ɗakin Kaka. "Ɗago labulen aka yi Baffa Mamman ya ce ""saka hijabinki ki fito""." Ƙulululu cikina yai ƙara. Ban san hijabin wa na zara ba a hannun kujera na saka na bi bayansa. Sai dana fito daga ɗakin na ga ashe fa an cika ƙofar ɗakin ne maƙil. Me ya ke shirin faruwa? Mi ya kawo Alhaji Nafi'u da safen nan ana saura awa ɗaya da rabi a ɗaura aurena?. Na shiga uku ni ZIYADA. Allah ka taimakeni... CHAPTER THIRTY EIGHT JAYKAY """Ango"" sunan da ake kiransa kenan tun da aka shiga satin aurensa." Funny enough sai ya ji sunan yana masa daɗi idan aka faɗa. "Jalal ya sake duba fiskarsa a jikin mirror. Ba ƙarya ya yi kyau. Sabon aski, gyaran fuska, clean shave. Ba" ƙaramin kyau ya yi ba cikin farar Getzner Wagambari da ya sha ɗinki mai kyau da aikin hannu. Aurensa na farko suit ya sa. Yana iya tuno lokacin vividly a idanunsa. Jamal da ya masa Best Man ne ya saka blue Jumfa har da hula. Hoton da suka ɗauka yana nan a cikin Album ɗin hotunansa. Wannan auren daban yake da wancan. Wannan auren cike yake da tsari da ƙa'idoji. Dan haka yau zai bi "dukkan tsari ya kuma cika duka ƙa'idojin da aka shar'anta ya auri ZIYADA, 'yar Nigeria, kuma Bahaushiya." Ranan Laraba da yamma ya je ya ɗauketa suka je gwaji. Abin ma ya escaping ɗinsa sai da Hajiya ta tambayeshi ko sun yi pre-marital screening ya tuna ba su yi ba. Da ya je ɗaukanta bai faɗa mata inda za su je ba sai da ta fito ya ce mata Clinic za su je su yi screening sai ta fara kame-kame wai ita tana tsoron Allura. Ƙarshe ta ce masa ya bari ta kira wata ƙanwarta su tafi tare. Bai musa ba ya jira ta shiga gida ta "sake fitowa ita da wata teenage girl, da ba za ta fi 13-14yrs ba." Kafin su isa Asibitin sai ta tambayeshi miye genotype ɗinsa? Ya ce mata AA. Da ya faɗi haka sai ya ga "fiskarta ya washe ta furta wani abu ƙasa-ƙasa amma bai ji me ta faɗa ba. Da ya tambayeta sai ta ce masa babu komai. Har suka isa Asibitin fiskarta a sake yake, as if maganar genotype shine kaɗai matsalarta." Already ya riga ya yi magana da mutumin da Ibrahim ya haɗasu a Lab ɗin dan haka suna zuwa aka fara ɗaukan sample ɗinsu. Nasa aka fara ɗauka kafin nata. Ya riga ya san genotype da blood group ɗinsa. Dama baya wasa da check up duk bayan wata shida saboda ya saba da haka tun yana Pilot. Awa biyu aka ce su jira result ɗin ya fito wannan ya sa ya ɗaukesu suka je JK Plaza bayan ya siya musu shawarma da ice cream a hanya. Da suka shiga Restaurant Ziyada ta yi mamakin yadda aka sake gyara decorating Gidan Girki aka saka "abubuwan gargajiya a wajen, hatta paintings ɗin wajen an chanja zuwa painting ɗin riga da ƙauyuka." Wajen ya sake bada classic gargajiya vibe haka. Aiki Jalal ya yi a Laptop ɗinsa occasionally yana ɗan ɗagowa ya kalli Ziyada da ƙanwarta da suke cin shawarma. Da suka gama cin Shawarma da ice cream sai yace su koma Asibitin time ɗin da aka basu ya kusa cika. Dukkansu lafiyarsu ƙalau. Blood group ɗinsu babu matsala saboda duka rhesus factor ɗin positive ne. Sai kuma genotype wanda kasancewarsa AA yasa suka zama compatible da ita mai AS genotype. It was the last time da ya sakata a idanunsa. Tun daga ranan ba su sake haɗuwa ba sai yau idan Allah ya sa an kawo masa ita. Zai ganta. Zai taɓata. Yau kam bata isa ta ce masa ai sadaki ya biya ba a ɗaura aure ba. Yau za a bashi lasisin taɓata. And "taɓata, he will." """Dad, su Uncle Ibrahim na jiranka a ƙasa"" Junior ya leƙo ɗakinsa ya faɗa. Shima sanye yake da shiga irin" "ta Jalal har da Babban riga, da hula, da takalmi." Miƙawa Yaron Babban rigansa dake naɗe yayi ya ce ya sauka masa da shi yanzu zai fito. Kallon ƙarshe ya yiwa kansa a mirror sannan ya sake fesa turare ya fito. Yes. Jalal Maiyaƙi ya fito sak Ango. Babu wanda zai ganshi da ba zai ga ƙwarjinin Angwaye a tattare da "shi ba. He looks so handsome, sai wani ƙanshi mai sanyi yake zubawa." "Yana saukowa ƙasa matan da ke wajen ke ta kiransa 'Ango, Ango'." Hajiya bata ɗakinta. Bai san ina ta shiga ba. Ya so ya gaisheta kafin su wuce. Da ya fito waje inda Ibrahim da wani cousin ɗinsu AbdulSamad ke jiransa sai ya ga Janan a wajen. """Make some noise for the Groommmmm"" ta faɗa tana saka ihu da tafi" """Jan, ina Hajiya?""" """Bata ɗaki?. Ban san ina ta shiga ba to""" """Ango za mu makara fa. Ka san sai mun fara biyawa gidan Uncle Idris kafin mu wuce"" Ibrahim ya faɗa" yana gyara zaman hularsa. """Ku tsaya mu yi hoto"" Janan ta faɗa tana fito da wayarta." """Janan we are going to be late. Ki bari idan muka dawo za a yi hotuna""" """Guys ina zuwa"" Jalal ya excusing kansa zai koma cikin gidan." """Ina kuma za ka je?. Mutumina ƙarfe goma ta cika fa. Please ka yi sauri""" Bai tsaya sauraron Ibrahim ba ya yi cikin gida. Wani tunani ne ya zo masa. Idan Hajiya bata ɗakinta kuma bata falon ƙasa cikin mutane tabbas wajen da yake tunani ta shiga. Lokacin da ya murɗa ƙofar ɗakin Jamal bai yi mamakin jin ƙofar a buɗe ba. Hajiya ya gani zaune a bakin gado riƙe da rigan Jamal tana kuka. Tsayawa ya yi a bakin ƙofar yana kallonta yana jin zuciyarsa na masa zafi. """Lah! Har ka shirya. Za ku tafi ko?"" Hajiya ta faɗa tana ɓoye rigan a bayanta tareda saurin goge idanunta." Yadda ɗakin yake so neat babu ƙura babu komai ya tabbatar masa ba wannan ne karon farko da Hajiya ke zuwa ɗakin ba. Kenan nan ta ke zuwa ta sha kukanta idan ciwon rashin Jamal ya taso mata. Ya ɗauka shi kaɗai ne ya kasa mantawa da mutuwar ɗan'uwansa. Ya ɗauka Hajiya ta manta da komai shi yasa bata son maganarsa. Sai yanzu ya fahimci Hajiya ta fi shi jin zafin rashin Jamal. Sai yanzu ya fahimci uwa ba za ta taɓa mantawa da ɗanta da ya rasu ba. """Hajiya, ki yi haƙuri"" ya samo kalmomin da ƙyar ya furta su lokacin da ya tako tsakiyar ɗakin inda Hajiya" ke tsaye. """Babu komai Jalal. Wannan ai ranan farin ciki ne. Kawai..."" sai ta yi shiru ta fara sheshsheƙar kuka." "Kawai dai ta tuna cewa da Jamal bai yi accident ba, da shima ya yi aure kamar yadda Jalal yake shirin yin" sabon aure a yau. Sa hannu ya yi ya rungumeta yana bata haƙuri. Tabbas tana buƙatar wannan comfort ɗin. Ba zai iya tuna yaushe rabon da ya yiwa Hajiya comfort hug irin haka ba. Wataƙila tun ranan da suka zo graduation ɗinsa lokacin da ya gama Aviation Academy ta ce masa 'I'm Proud of You'. "Sai dai yanzu, da shi da ita ɗin duka suna buƙatar wannan Mother-Son bonding ɗin." Shima Jalal hawayen ne yake ƙoƙarin taho masa amma sai yai ta maza ya shanye saboda idan ya nuna weakness ɗinsa a gaban Hajiya to wa zai rarrashi Hajiyar a yanzu da take buƙatar lallashi. Ita ce ta fara janye jikinta. Ta goge fiskarta ta ce ya wuce wajen ɗaurin aure kada ya makara. Ta yi masa addu'ar da bai taɓa ji a bakinta ba tun daga ranan da ya auri Cassy har zuwa yau. Wannan "addu'ar ya sake tabbatar masa auren Ziyada, yana da mahimmanci sosai a wajen Hajiya." """Muhammad Jalal, Allah ya sa Albarka a wannan aure da zaka yi. Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe" "fitina""" Jalal ya amsa da Amin yana jin wani sanyi a zuciyarsa. Sai da suka fito daga ɗakin ya ga Hajiya ta sa key ta rufe ɗakin Jamal sannan ya mata sallama ya tafi. Ta "ce masa a dawo lafiya, Ango. Jalal ya yi murmushin jin daɗi..." ZEEY "Dokawar da zuciyata yayi a ƙirjina lokacin da muka fito waje na ga cincirindon mutane, na ɗauka daga" nan numfashina ɗaukewa zai yi na jini gaban Malaiku ina amsa Man Rabbuka. "Ban san ya aka yi na dinga takawa ba har na ratsa mutane na kawo wajen da Baffa Adamu, Baffa Lawalli," Baffa Zakari da kuma Alhaji Nafi'u suke tsaye cirko-cirko """Yaya Adamu, ga Ziyadatun"" Baffa Mamman ya faɗa yana nuna ni. Idanun kowa sai ya yo kaina, na ji" wani juyi ya kamani. Riƙe hannuna da Baffa Adamu ya yi ya sa ban faɗi a wajen ba. """Alhaji Nafi'u, ka ganta nan. To Nine Ubanta. Ka faɗa mana dalilin zuwanka wajen nan yau""." 'Nine Ubanta' dana ji ya faɗa sai ya saka hawayen da nake ta ɓoyewa suka zubo. Na yi saurin saka hannuna ɗaya na goge. """Kamar yadda na faɗa. Na zo ne na mayar da kuɗin da Saurayinta ya aiko mini. Ni ba za a sayi bakina da" "Miliyan ɗaya ba. Na fi ƙarfin Naira Miliyan ɗaya tunda ba yau na fara kasuwanci ba. Ko ba haka ba?"" ya faɗa da ƙarfi yana kallon wani mutumi da ke gefensa da alama tare suka zo. Mutumin ya amsa da hakane yana gyaɗa kai kamar wani ƙwajen Ƙadangare." """Wannan dai check ɗin Miliyan ɗaya ne ga shi nan, ga sunan Saurayin da Sayyada za ta aura nan a kai." "Jalal Maiyaƙi"" yai maganar yana ɗaga check ɗin kuɗin sama yana so mutanen da ke wajen su masa shaida." Wato dama abinda ya shirya mun kenan. Ya zo gidanmu safiyar ɗaurin aurena ya walaƙantani gaban "iyayena, gaban mutane. Ya nuna musu na ƙi aurensa ne saboda Jalal ya fi shi kuɗi." """Dakata, Alhaji Nafi'u"" Baffa Adamu ya katse shi. ""Baban Suwaiba kar ka karɓi check ɗin nan"" ya dakatar" da Baffa Lawalli dake shirin karɓan check a hannun Alhaji Nafi'u. """Kana ji dai na ce maka nine Uban Ziyadatu ko?""" "Alhaji Nafi'u ya ce ""ina jinka"". Yadda ya yi maganar irin ko oho ɗinnan ya riga ya samu abinda yake so" tunda mutane sun shaida ya kawo check ɗin kuɗin da aka bashi. """Alhaji Nafi'u, miye haɗinka da 'yata?""" Rarraba idanu ya fara dan bai zata Baffa Adamu zai masa wannan tambayar ba. """Ni manemin Sayyadah ne. Na yi shekara biyu ina nemanta"" ya faɗa yana wani gyara babban rigansa." """Sunan 'yata Ziyada, ba Sayyada ba""" """Na'am"" Baffa Lawalli ya faɗa da ka ganshi ka san a tsorace yake. Saboda shine silar wannan case ɗin." """Sunan nata ne ke da wuyar faɗa. Amma ita ta san haka nake kiranta tun da muka haɗu"" Alhaji Nafi'u ya" faɗa yana washe baki. """Da kake nemanta ta amince za ta aureka ne?""" Kallon Alhaji Nafi'u na ke da rinannun idanuna ina jira yai min ƙaryar na taɓa amincewa zan aure shi. """Farko-farko ta amince da ni, daga baya sai ta zo ta ce ta fasa. Amma ni na san hure mata kunne aka yi" "saboda ta samu wanda ya fini kuɗi"" yai maganar yana ɗaga murya dan mutane su ji maganarsa da ƙyau." "Allah ya isa!. Allah ya isa na, Alhaji Nafi'u. Ba zan taɓa yafe maka ba har abada." """Alhaji Nafi'u ba zan yarda da ƙazafin da kake yiwa 'yata ba. Dukkanmun nan dattawa ne dan haka ka iya" "bakinka. Ina Malam Liman?""" """Gani, Malam Adamu"" Liman ya faɗa bayan Baffa Mamman ya nemo shi." """Ina Alhaji MaiUnguwa?"" Ya waiwaya ya kalli Baffa Mamman ya ce "" Mamman a kori kowa a wajen nan" dan Allah. Baffa Mamman da Baffa Zakari da wani da ban ga fiskarsa da kyau ba suka fara koran mutane a wajen. "Aka barmu daga mu sai Limamin Masallacin da za a ɗaura mini aure, sai MaiUnguwa, sai kuma Abokin Alhaji Nafi'u da suka zo tare." """Ina so ku yi mini shaidah. Wannan mutumi yana so ya yiwa 'yata ƙazafi kuma Wallahi idan bai janye" "maganarsa ba sai na yi ƙaransa""" """Malam Adamu, a bi komai a sannu"" inji Liman." "Baffa Adamu ya kalleni ya ce ""Ziyadatun, kin san wannan?"" Ya nuna Alhaji Nafi'u. Na gyaɗa kai." """Miye tsakaninki da shi?""" Ta ina zan fara? Ta ya zan bada labarin alaƙar da bata da suna dana bari ta jima tsakanina da wannan mugun mutumin. Muryata na rawa na fara bayani a taƙaice. Na faɗa musu yadda muka haɗu da yadda ya ce yana sona ni kuma na ce ban amince masa ba. Na kuma faɗa musu rabuwarmu ta ƙarshe da shi ma ya fi wata shida. """Kin taɓa amincewa za ki aure shi?"" Baffa Adamu ya jefo min tambaya." """Wallahi, Baba. Na rantse da wanda raina ke hannunsa ban taɓa amincewa da soyayyarsa ba balle kuma" "na amince da aurensa""" """Ya isa"" ya juya ya kalli Alhaji Nafi'u da ke zazzare idanu ya ce "" ka ji abinda ta faɗa. An yi haka ko ba a yi" "haka ba?""" "Alhaji Nafi'u sai ya fara kame-kame. Shi ai bai ce yanzu bane, yana nufin tun farkon haɗuwarmu ne na" nuna ina ra'ayinsa daga baya kuma sai na chanja masa. """Baban Suwaiba""" """Na'am""" """Lokacin da ka min maganar Alhaji Nafi'u ban dakatar da kai ba bayan Ziyadatu ta nuna mana akwai" "wanda take so?""" "Baffa Lawalli ya ce ""an yi haka""" "Ya kalli Alhaji Nafi'u ya ce "" kuɗin da ka kawo yanzu kuɗin miye ne?""" """Jalal Maiyaƙi ne ya aiko min"" ya faɗa yana huhhura hanci." """Shin ya baka kuɗin ne saboda ka rabu da Ziyadatu?""" Alhaji Nafi'u ya yi shiru. """Magana nake Alhaji Nafi'u""" """Wanda ya kawo check ɗin ya ce bashin da nake bin su Malam Lawal ne aka biya musu""." """Kuna ji ko?"" Baffa Adamu ya faɗawa su Liman." """Ƙarya kake kuɗin da kake bina da wanda kake bin Zakari bai kai dubu ɗari biyar bama. Kawo check ɗin" "za mu mayar maka kuɗinka"" Baffa Lawalli ya yi maganar ko kunya babu." Alhaji Nafi'u ganin abinda ya ƙulla ya fara warwarewa sai ya fara kame-kame yana masifar wai ai shi Baffa Lawalli yake bi kuɗi me yasa Jalal Maiyaƙi zai aika masa da kuɗi. Baffa Lawalli ya buɗe murya shima ya fara faɗa wai ai shi ya je ya roƙi Jalal alfarma ya biya musu bashin shine ya biya over dan haka ya kawo Miliyan ɗayan zai cashing kuɗin ya bashi iya abinda yake binsu. Magana sai ta rikice ta koma Alhaji Nafi'u da Baffa Lawalli suna yaɓawa juna magana shi Alhaji Nafi'un na "yiwa Baffa Lawalli gorin abinda ya masa yana kiransa da kwaɗayayye, butulu." Sai da Baffa Adamu da Liman suka tsawatar kafin suka yi shiru. """Mamman nemo mana takarda da Biro"" Baffa Adamu ya umurci Baffa Mamman." Muna tsaye aka kawo biro da littafin 80 leaves aka cire fulls cap ɗaya. """Alhaji Nafi'u, Check ɗin da ka kawo zaka mayarwa wanda ya aiko maka. Ba mu za ka kawowa ba saboda" ba mu muka baka kuɗi ba. Kuɗin da su Zakari ke binka kuma wannan tsakaninka da su ne. Yanzu so nake "a gaban shaidu ka warware ƙazafin da ka yiwa 'yata""" Tunda Baffa Adamu ya fara maganar fiskar Alhaji Nafi'u yake a ɗaure. Ga shi Abokinsa da suke tare shima ya dena goya masa baya. Takardar da aka cire aka bawa Alhaji Nafi'u. Baffa Adamu ya fara karanto masa abinda zai rubuta. Ya tsaya ya ƙi rubutun. """Idan ba ka warware maganar da ka zo da ita ba yanzu sai mu wuce gaban 'yan Sanda a ƙarisa shari'ar a" "chan""" MaiUnguwa ya ce zai ma rubuta. Ai da girmansa ba zai bari a je gaban 'yan Sanda akan magana irin wannan ba. "Baffa Adamu ya ce masa ya rubuta cewa ni ban yaudare shi ba, ban taɓa amincewa zan aure shi ba. Ya" ce ya rubuta duk wata hidima da ya yi mini a baya ya yine a karan kansa ba roƙonsa na yi ba. Sannan baya bina bashin komai. Maganar kuɗin da Baffa Lawalli da Baffa Zakari suka karɓa bai shafeni ba. Dogon rubutu dai har sai da ya cika shafi biyu da rabi kafin bayan Baffa Mamman ya karanta abinda Alhaji Nafi'un ya rubuta kowa ya ji sai aka ce ya saka hannu. Ya sa hannu sai ɓata fuska yake. Liman da Maiunguwa suka sa hannu. Baffa Adamu da Baffa Mamman suka sa hannu sai aka miƙo min Biro wai nima na sa hannu. Hannuna na rawa na karɓi Biron na yi signing hawaye na ɗiga a takardar. Lokacin dana ɗago sai na yi ido huɗu da yaya Aminu. Ashe yana wajen ban ganshi ba tun ɗazu. Na ji kamar na nitse cikin ƙasa. Sai da ya ce min na rabu da Alhaji Nafi'u tun da jimawa tun farkon haɗuwata da shi. Yace min mutumin bai masa ba. Yau gashi na ƙi jin maganarsa na bari alaƙarmu ta yi nisa kafin na rabu da shi yanzu ya zo ya zamo min fitina a ranan Aurena. Motocine suka fara isowa wajen wannan ya sa Baffa Adamu ya ce Baffa Mamman ya shiga da ni gida tawagar Ango ne suka fara isowa. Rufe fiskata na yi da hijabi na bi bayan Baffa Mamman da ya ke bani haƙuri yana faɗin kar in damu komai ya wuce babu abinda zai faru. Aurena da Jalal kamar an ɗaura. Ina ma ina da halin da zan erasing haɗuwata da Alhaji Nafi'u daga rayuwata. Ina ma zan iya goge abinda ya faru a yau. Ina ma na fahimci cewa idan NAMIJI ya ce yana son mace amsar E ko A'A ne. Duk wani abu bayan wannan ruɗu ne da ka iya jawo matsala daga baya. Muna shigowa sashinmu mutane suka fara tambayar Baffa Mamman me yake faruwa?. Yace musu babu komai a cigaba da Biki tawagar Ango sun fara isowa nan da mintuna kaɗan za a ɗaura aure. Ina shiga ɗaki na jawo ƙofa na rufe na saka sakata. Ban lura da Ummana dake zaune a kujera ba balle Kaka dake tambayata me yake faruwa. Faɗawa gado na yi na fashe da kuka da dukkan ƙarfina... CHAPTER THIRTY NINE ZEEY Mata biyu da suka fi kowa daraja a rayuwata ne suka sakani a gaba suna bani haƙuri. Kaka ce ma ta ke ta "lallashina ita Umma cewa ta yi komai mai wucewa ne, kuka ba zai min maganin matsalata ba." "Gaskiya ne, kuka ba zai min maganin komai ba. Alhaji Nafi'u ya riga ya zo ya yi tsiyarsa, sauran kuma zai" gani tunda ni kam na ja masa Allah ya isa. Idan na cigaba da kuka zan bawa 'yan gulma damar gulmata kenan. Wataƙila su ce da gaske saboda kuɗin Jalal na rabu da Alhaji Nafi'u. Muna cikin ɗaki mu uku sai 'yar Anty Binta da ke bacci muka fara jiyo guɗa daga waje. Yara na ihun An ɗaura. An ɗaura. Sai na ji wani dif. Komai ya tsaya mini. "Like, I'm not feeling anything. For a split second sai na tambayi kaina, dama ɗaurin Auren kenan?." Shikenan yanzu na zama mallakin Jalal Maiyaƙi?. Yes. Maganar Aurenmu ya fara ne saboda wani manufa da muke son cimmawa. Amma a yadda abubuwa "suke tafiya bana tunanin wannan manufar ne kaɗai dalilin wannan aure. Ban san a ɓangaren shi Jalal ba. Amma a ɓangarena, ina jin feelings akan Jalal and zan so aurenmu ya zama more than just a deal. Sannan a yadda abubuwa suka faru yau, idan aurena da Jalal ya ƙare nan kusa, tabbas zan zamo abin kwatance a cikin Unguwarmu. Tabbas mutane za su yarda da maganar Alhaji Nafi'u, sannan za su yi min madallah da na je na auri mai kuɗi saboda kwaɗayi." Cikin zuciyata na yiwa kaina alƙawarin zan riƙe aurena beyond deal dake tsakaninmu. Idan Allah ya "taimakeni Jalal ya buɗe mini zuciyarsa, just maybe aurenmu ba zai ƙare ba balle na ji kunya a wajen" mutane. """Ku buɗe ƙofa. Adda Ladidi. Amarya kina jina? Ki kwantar da hankalinki an riga an ɗaura aure. Aure ya" "ɗauru, duk abinda ya faru ɗazu da safe ya wuce"" Anty Ruƙayya ƙanwar Umma kenan take buga mana ƙofar ɗaki." "Umma ce ta miƙe za ta buɗe ƙofar ta juyo ta ce ""Dan Allah kukan ya isa haka. Kin dai ji an ɗaura aure." "Bana so ki bawa mutane dama su yi ta maganan ki. Kina jina?""" Na gyaɗa mata kai. Tabbas ba zan bari su ga ɓacin rai a tattare da ni ba. Lokacin da Umma ta buɗe ƙofar kamar dama jira ake a buɗe. Anty Ruƙayya na shigowa zugan mata suka "biyota, sai zolayata suke wai Amarya mai Daloli. Na san yawancinsu gulma ne ya kawo su. Tunda dai na san by now kowa ya san Alhaji Nafi'u ya zo ya tada rikici." Ina zaune akan gado na hango Faty tana tsaye jikin ƙofa. Ɗaga mata hannu na yi na ce ta ƙariso. """Bestie, me ya faru ne?. Na zo sai na samu wani mummunan labari wai ana rikici a waje da Alhaji Nafi'u." "Ke kuma kina shigowa kika kulle ƙofa kika barmu tsaye. What is happening?""." """Faty, ki bar maganan nan kawai. Ni dai na riga na yiwa Alhaji Nafi'u Allah ya isa. Ya je shi zai gani"" na" faɗa ƙasa-ƙasa dan na ga mutanen ɗakin sai kallona suke suna so su ji gulmar abinda ya faru ta bakina. """To Allah ya kyauta. Yanzu kin yi wanka ne in miki makeup ɗin?. Kar a shigo ganin Amarya a ganta da" "jajayen idanu""" Na ɗan yi murmushin yaƙe na ce barin sake wankan kawai. Miƙewa na yi zan bar ɗakin Umma ta tambayeni ina zan je na ce mata wanka zan yi. Sai Kaka ta ce in kira Mardiyyah ko wata ta karɓo min ruwan zafi a cikin gida. Allah ya sa Ummiyo na kusa sai na faɗa mata. Na dawo na zauna kusa da Faty. Da aka karɓo min ruwan sai na fita na je na yi wanka. Ina cikin banɗakin ma sai da hawaye ya taho min dana tuno dramar da aka yi ɗazu. Na dai daure na shanye kukan na watsa ruwa na fito. "Ina fitowa na samu na chanja kaya. Wani farin bridal lace gown na saka, ɗinkin ya yi kyau. Gaskiya" "Hajiyar Lagos da Jalal ya ce na turawa sizes ɗina ta san fashion. Bayan na karɓo kayan cewa ta yi na gwada ko akwai matsala dan zata ci uban fashion designer data ɗinka a Lagos idan aka samu matsala. Sakawar farko ma gidan Anty Hafsa na je na gwada duka kayan, kuma ina saka gown ɗin na ji dole shi zan saka safiyar aurena. Kowanni curve ɗina ya fito Masha Allah. Ga bridal veil ɗinshi har ƙasa. Nima na yi kamar Amaren Instagram. Wato kaya mai kyau yana ɗaga mace. Na fi ma ranan Walima kyau. Faty ta tsantsara min kwalliya, simple yet elegant da ya tafi da softness na kayan. Danne zuciyata nake ta yi saboda kar hawaye su zubo min na ɓata make up ɗina. And Allah ya taimakeni duk yadda ake ta yi mini guɗa anata Amarya mai Daloli ban bari hakan ya stirring emotions ɗina ba. Idan na biye ta tasu zan fara kuka ne har gobe ban gama ba." "Babu professional photographer da muka kira saboda ni duk ban saka wannan a lissafina ba, tunda" "auren ma gashi komai a ƙure ya zo mini. Sai dai muna cikin yin hotuna da wayoyinmu aka yi Sallama wai mai hoto yana so ya shigo. Da alama dai shi ya kawo kansa. Sai da aka ce ya shigo ɗinma na ji wasu na kiran sunansa ashe ɗan unguwarmu ne. Da ya ƙariso inda muke tsaye a ƙofar ɗakin Kaka sai na tuna ashe ma na san shi. Wani abokin yaya Aminu ne. Kaman Hussaini ko Hassan sunansa, na dai manta wanne ne. Na san ba zai wuce yaya Aminun bane ya kira shi, ko kuma dai saboda ya ji bikina za a yi shiyasa ya taho. Koma wanne ne dai ni dai muka tsaya aka fara mana hoto da professional Camera." Ƙarshe saboda yadda wajen yake babu background mai kyau kuma mutane nata shigowa sashen namu "ya cika, sai ya ce mu fita waje za a fi samun haske." "Na ce masa to, dan ina so ma mu yi hoto da iyayena a waje. Musamman mutumin da ya nunani a gaban" "mutane ya ce shine Ubana. Ba zan taɓa mantawa da wannan rana ba a rayuwata. Na san ko Ubana dake kwance a kabari idan a ce Mala'ikun Rahama za su bashi labarin abinda ya faru, na san zai ji daɗi sosai. Zai ce yaya Adamu ɗan'uwane na ƙwarai." "Har muka fito daga gidan, mata da yara sai guɗa suke ayyiririyiriri..." Na ɗauka idan muka fito zan samu Ango da tawagarsa basu tafi ba. Maybe ma na ɗan glimpsing fiskar Ango na ga irin kyaun da yayi har ma mu yi hoto. Amma sai na ji ana cewa gashi su Ango sun wuce. Koda yake dama yace ɗaurin Aure kawai za a yi. Tsayawa hoto da Amarya zai iya jawo matsala idan hoton ya leak a social media Baturiyar matarsa ta gani. Amma duk da haka sai na ji babu daɗi. I wish ya tsaya ya shigo wajenmu dan ya gaishe da Kaka da Ummana. Na san za su ji daɗi idan suka ga Mijina tunda waya kawai suka taɓa yi. Na cire tunanin a raina lokacin da Mai Hoto ya ce na yi murmushi. Iyayena maza suma suka fara zuwa aka fara ɗaukan family pictures. Sai dana tabbatar an ɗaukeni ni da "Baffa Adamu mu biyu, ni da Kaka mu biyu, sai kuma ni da Ummana. Waɗannan ukun zan sa a enlarging" ɗinsu ne in ajiye a gidana. Domin waɗannan mutane uku su suka taka rawar gani a rayuwata. Ina ganin Baffa Lawalli yana matsowa kusa da ni da za a ɗaukemu hoto yana wage haƙora na haɗe fiskata. Wannan ne mutumin da ya so rusa min Aure. Saboda kwaɗayinsa ya sa wani banza wai Alhaji Nafi'u ya zo da niyyar ɓata min suna. Lokacin da muka gama hoto da su Baffa Lawalli da Baffa Mamman sai yaya Aminu ya shigo hoton. """Congratulations! favourite Sis"" ya furta a hankali dai-dai kunnena. Na ce masa Thank you. Ƙila wannan" "shine hoto na ƙarshe da za mu ɗauka tare. Na ɗan yi murmushi aka ɗau hoton sannan na ga ya matsa ya fara tafiya zai bar wajen da muke, as if dama hoton ne kawai ya tsayar da shi." """Allah ya baka mata ta gari, yaya Aminu"" na masa addu'a a zuciyata." Matan gida ma da suke aiki suka fara fitowa ana hoto. Yaran gidanmu kowa kokawan hoto yake da Adda Ziya. "Ƙarshe sai da tsayuwa ya fara gagarata. Ga zafin da ƙafana ke yi a cikin heel, ga kuma yunwar da ke cina" tun safe ban ci komai ba. Tuwon dana fara ci maganar Alhaji Nafi'u ya sa na ajiye shi. Da naga dai mun gama hotuna da muhimman mutanen da ya kamata har da su Kawunnai na da suka zo "daga ɓangaren Ummana, sai kawai na ce ya isa haka zan shiga gida. Sauran matan gida da yara da kuma 'yan unguwarmu dake son hoto dani su biyoni za a yi da waya idan na huta." Ina shiga gida kaman dama ruwan ni yake jira aka ɓarke da ruwa. Ruwa sosai fa. Thank God babu "hidimar da aka yi. Dama an ce da an ɗaura aure za a raba abinci a takeaway kuma na tabbata inma ba a gama rabon ba to dai 'yan gida ne suka rage saboda waɗanda suka zo ɗaurin aure daga nesa kam duk sun tafi kafin ma mu fara hotuna a waje, balle yanzu da aka fara ruwa." Na ji daɗi da ruwan bai zo ba sai da aka gama hotuna. Dana cire kayan jikina sai na saka wani doguwar "rigar material ɗina, ba sabuwa bace dan a gida nake sakata. Tunda ruwa ake babu amfanin saka wani kayan. And ina so na jini cikin comfortable kaya dan gown ɗin dana saka ya takurani. Wasu suna cewa fashion is pain. Amma ni a wajena fashion is comfort. Ga shi dai matsatstsen bridal gown ɗin dana saka ya min kyau, picture-perfect. Amma ina cire shi dana saka comfortable gown ɗina na ji na dawo dai-dai. Na ji ni saƙayau babu takuri." Faty aka kawowa abinci tana ci. Aishatu data zo muka yi hoto ɗazu ta tafi wai sai da yamma idan za a kaini zata dawo. Faty kam za ta tsaya min har sai za a wuce dani kafin ta tafi saboda mijinta bai barta ta yi rakiyar Amarya ba. Ganin abincin da ta ke ci sai nima cikina ya ɗau ƙugi. Na ce ta matso mu ci tare. Tace bata san wannan ba na sa a karɓo mini nawa. Ruwan da ake ya ɗan tsagaita sai yayyafi. Na leƙa bakin ɗakinmu ina kiran sunan Walida da Ummiyo. Ni kam dama haka ake yi ne?. Ni ce Amarya amma babu wanda yake ta batun abincina sai ta baƙi kawai ake yi. Ba dan ma Kaka ta tattare kayan tea ɗinmu ta ɓoye ba ai da tea zan haɗa in sha kawai a wuce wajen. Ƙanina Aliyu na gani zai shigo nace masa ya je wajen Maman Suwaiba yace mata ta zuba min abinci. """Ka ce mata ni zan ci fa"" na jaddada masa. Dan yanzu sai Maman Suwaiba ta ɗan ɗokano mini a" takeaway da ɗan mitsitsin nama. Gara ta san Amarya ce za ta ci. Kafin ya kawo abincin sai ga Baffa Zakari ya shigo wai Kaka ta zo za a yi magana. Kaka har lokacin bata cire kayan biki ba ta ɗaura hijabi akai ta bi shi suka fita. Daga inda nake tsaye ina jin ɗan hayaniya ana magana sama-sama. Ya Allah ka sa ba wata fitinar bace ta kunno kai. Gaba ɗaya ma sai na ji na loosing appetite ɗina. Na jawo buta a ƙofar ɗaki kawai na fara alwalar sallar Azahar. Ina cikin sallah Aliyu ya kawo min abinci ya ajiye ya yi tafiyarsa. Dana idar da sallah Faty ta ce wai ta ɗau naman kan abincin. Na duba jollof rice ɗin da aka cika a plate da nama ɗaya da Faty ta bari akai na ji ni bama ta abinci nake ba. Me yake faruwa su Baffa Zakari suka ce Kaka ta zo a yi magana?. "Ce mata na yi ta cinye abincin idan za ta ci. Ko cikinta ne ya saka mata kwaɗayi, oho, haka ta jawo plate" ɗin ta fara ci wai Jollof ɗin ya mata daɗi. Ina zaune a sallaya ina Azkar tareda addu'ar Allah ya kaɗe fitina sai ga su Kaka sun dawo har da Baffa Adamu da Baffa Mamman. Cewa aka yi kowa ya fita a ɗakin. Faty ta ɗau plate ɗin abinci ta fita. "A take zuciyata ta fara zafi da na ji Baffa Adamu na cewa a kira masa Ladidi, wato Ummana dan bata" ɗakin. Na sunkuyar da kaina ina kiran sunan Allah. Allah dai ya sa wannan zama ya zo min da sauƙi. Har Ummana ta shigo ɗakin aka kulle ƙofa ban ɗago kaina ba. Baffa Adamu ne ya buɗe zaman da addu'a. "Sai ya kira sunana ""Ziyadatu""" "Na amsa da ""na'am, Baba""." """Alhamdulillahi yau da safe an ɗaura aurenki da Muhammad Jalal. Daga yanzu kin tashi daga budurwa" "zuwa matar aure""" Jakar da ya shigo da ita ya ɗauka ya ciro Qur'ani da sallaya ya miƙa min. Na sa hannu biyu na karɓa. As if turaren Jalal aka fesa a jiki sai ƙanshinsa nake ji. """Ga wannan naki ne da wakilin Ango ya bayar a wajen ɗaurin aure""" Ya sa hannu cikin babban rigarsa yana lalumo abu. Kuɗi ya ciro. Sabbin Dollars 'yan $100 notes dukkansu. "Ya miƙa min kuɗin ya ce ""Ziyadatu, ga sadakinki nan Dollar dubu biyu aka bayar""" "Ya kalli Baffa Mamman ya ce ""kana min shaida ko?""" """Yaya ai babu komai. Allah ya saka da alkhairi""" Kaka da Umma suka amsa da Amin. "Na karɓi kuɗin a hannunsa ina faɗin ""Baba, Allah ya saka da alkhairi""" "Bayan ya amsa da Amin sai ya ce ""To ni dai sauran aikina a nan shine na tabbatar an miƙa ki gidan mijinki" "lafiya, Ziyadatu. Na faɗawa shi Jalal a zo da wuri ba sai dare yayi gari ya yi duhu ba""." """Ziyadatun"" ya kira sunana da sigar jan hankali." """Na'am"" na amsa already hawaye ya fara cika a idona tunda na ji ya fara batun aikinsa na ƙarshe shine ya" miƙa ni gidan Mijina. """To, Allah ya kawomu aurenki. Ni dai a wajena 'yata kike. Dan na san ko Sadiq yana raye ni ɗin dai zai" "bawa waliccin aurenki. Dan haka, a matsayina na uba a gareki ina yi miki nasiha da ki bi Mijinki sau da ƙafa. Ki yi masa biyayya, sannan ki riƙe gidansa da 'yan'uwansa da Amana. Aure da kike gani zo-mu- zauna, zo-mu-saɓa ne. Idan wata matsala ta faru a tsakaninku ba kawai sai ki tattaro ki dawo gida ba, ba a haka. Ku zauna tsakaninku ku riƙa magance matsalolinku. Ba fata ba, idan wata matsalar ta shigo wanda ta fi ƙarfinki kika ga kina buƙatan shawaran manya. To Bismillah ƙofata a buɗe take, idan bana nan ga Muhammadu, na san zai baki shawaran da ta dace da ke""" """ Babban abinda zan faɗa miki a yau shine ki riƙe sirrin Mijinki. Mijinki yana da dukiya Alhamdulillahi," "wannan ba shi zai sa ki zo gida ki riƙa faɗin sirrin arziƙinsa ba. Bamu bashi ke saboda ki riƙa ɗebo dukiyarsa kina kawo mana ba. Idan ya baki ya ce ki yi alkhairi da shi Alhamdulillahi. Idan bai baki ba kuma banda maula, banda kuma sata. Wannan kenan. Abu na ƙarshe kuma addu'a. Komai yai zafi maganinsa Allah. Ina yi miki nasiha da ki yawaita addu'a""" At this point na fara kuka sosai. Nasihar Baffa Adamu ya shiga jikina sosai. Ji nake anya na shirya ma aure kuwa duba da nauyinsa dana fara hangowa tun daga yanzu. Baffa Adamu ya tambayi Baffa Mamman ko yana da magana ya ce ai ya riga ya faɗi komai da ya matsa "masa sai shima ya min nasa nasihar a tsanake, tareda emphasizing maganar riƙe dukiyar Jalal bisa" Amana. Su basa neman komai daga wajen Jalal. Da ya gama nasa aka ce Umma ta yi min nasiha. Itama dai kalmar haƙuri ta dinga nanatawa da kuma addu'a. "Kaka kam da aka ce ta yi magana addu'a kawai take mini, can kuma ta fashe da kuka. Nima kukan nake." Na matsa jikinta na rungumeta muna kukan tare. Baffa Adamu ya ce ya dai?. Ya ce Kaka ta dena kuka abin Alheri ne ya sameni dan haka farin ciki za ta yi ba kuka ba. Bayan fitansu Baffa Adamu daga ɗakin a hankali fa sai mutane suka fara shigowa kowa na tofa albarkacin bakinsa. Wasu na bani shawaran yadda zan yi a gidan miji. Wasu na faɗin kada na yadda a samu matsala a auren nan duba da yadda aka riga aka saka min ido. Wasu kuma na faɗin idan na tafi na riƙa zuwa ina duba Kaka akai-akai tunda a Zaria zan zauna. Gaba ɗaya sai aka birkitani. Na yi kuka kaman babu gobe. Ni gaba ɗaya sun tsorata mini auren ma. Sai bayan la'asar na ke jin wai ashe ɗazun dana ji hayaniya har aka kira Kaka Baffa Lawalli ne ya tuɓure wai a bashi daga kuɗin sadakina wai zai biya Alhaji Nafi'u tunda Baffa Adamu ya hana shi karɓan Check ɗin da Alhaji Nafi'un ya kawo da safe. Shi kuma Baffa Adamu ya ce masa ƙwandala ba zai bashi ba. Sadaki nawa ne. Shine fa suke ta magana har sai da aka kira Kaka ta zo ta saka baki. Ni kam na ce Allah kawai ya kyauta. Da ana iya chanja Baffa dana je an chanja min Baffa Lawalli da wani Baffan mai hankali irin Baffa Adamu. Abincin dana ke son ci ma ban samu daman ci ba. Bayan na yi sallar la'asar sai aka ce na sake wanka na shirya saboda ƙarfe biyar aka ce masu ɗaukan "Amarya za su zo. Haka na sake tashi na je na yi wanka na fito. Idanuna duk sun kumbura saboda kuka, ga wani uban ciwon kai dana ke ji." Dana zo zan saka kaya sai Kaka ta ce in dakata in ci abinci tukunna. Mutanen ɗakin sai cewa suke ya aka yi ban ci abinci ba. Tea mai zafi Kaka ta fara haɗa min. Daga ƙasan gado ta jawo kwallar data ɓoye kayan tea ɗin ta haɗa min shi da kauri. Dama garin ya ɗan yi sanyi saboda ruwan da aka sha da rana. Na karɓi kofin na fara sha ina jan hanci saboda muran dole da ya kamani. Shinkafa da miya aka kawo mini yana tiriri. Daga gidan Anty Hafsah aka karɓo. Na karɓi plate ɗin ina ɗan ci a hankali amma gaba ɗaya bana jin taste ɗinsa saboda yanayin dana ke ciki. Ina cikin ci na ji ana maganar motocin ɗaukan Amarya fa sun iso. Sai na ji cikina ya yi wani ƙara ƙulululululu. """Ki ci abincinki a hankali. Ai ba daga zuwansu za ki fita ba"" in ji Anty Binta." Rabin abincin na ci ko naman kai ban ci ba na tura plate ɗin gefe na ƙarisa shan shayin. Ina miƙewa zan saka kaya na ji ana ga Baffa Lawalli zai shigo. "Na kira sunan Allah, dan the last thing dana ke son ji shine Baffa Lawalli ya yi wani abu da zai birkita" wannan ɗaukan Amaryan. Wai nasiha ya shigo min. Yana magana yana maimaita saura na je na zauna a gidan Mijina ina cin arziƙi "na manta gidan dana fito. Har da cewa wai ""ko za ki manta damu ai ba za ki manta da Kakar ki data riƙe" "ki ba ko. Dan haka yanzu ne lokacin da za ki saka mata duk ɗawainiyar data yi da ke""." Ai dama na san labarin gizo ba zai wuce na ƙoƙi ba. Shi dai maganar kuɗi ce a gabansa ba wai ya min nasihar yadda zan samu zaman lafiya da Mijina ba. Bayan ya fita sai aka rufe ɗakin saboda na shirya. Laffaya na saka fari mai pattern design ɗinsa golden color. Faty ce ta tayani ɗaurawa ta gyagygyara mini na fito na yi kyau. Ni na ce mata kar ta min make-up ta bar fiskata plain haka. Sai da aka zo aka ce a fito da Amarya sai na fara kuka. Like na riga na.ce ba zan sake kuka ba fa tun wanda muka yi ɗazu ni da Kaka amma da na ji an zo tafiyar sai hawaye ya fara zubo mini da kansa. Na je na rungume Kaka ina kuka. Anata lallashina ana faɗin Allah Sarki dama dole watarana za mu rabu. Lokacin da aka fito dani sai na ji hayaniya ya kaure ana ta masifar wa za su yi rakiyar Amarya. Ya Allah!. Wannan aure nawa ya shiga uku a wajen 'yan gidanmu. A haka dai aka fito dani anata guɗa. Da muka fito ƙofar gida sai muka tarar Baffa Adamu ya ja ya tsaya. Ashe da aka ce masa matan gida na ta faɗa dan su suka tsayar da tafiyar ma sai yace ya san me zai yi. """Ina Muhammadu?""" """Gani nan""" Ya kamo hannuna ya haɗa dana Bafffa Mamman. """Ina Halima take?""" """Gani nan"" Umman Fada ta fito da sauri." """Muhammadu, ku shiga motar nan"" ya nuna motar da za a saka Amarya a ciki." Na shiga uku!. Ba dai su biyu za su rakani ba?. Ina ji su Maman Suwaiba na masifar Baffa Adamu bai kyauta ba tunda ga motoci nan available. Wasu na cewa ai ko Kaka sai a bari ta je. Ƙarshe na ji yana cewa ƙawata guda ɗaya ta zo sai kuma Anty Ruƙayya. Ina ga itama ya kirata ne saboda a samu ɓangaren Ummana da za su je. Ban san wa aka sake kira ba har motarmu ta tashi. Ni Ziyada yau na ga bala'i a wannan aure. Ga ni dai a tsakiyar ƙanin Babana da ƙanwar Babana. Su aka ce su yi mini rakiyar. Lokacin da motarmu ta tashi sai na ji tausayin kaina ya fara kamani. Auren nan dole na riƙe shi da kyau idan ba so nake munafukai su ji daɗi ba... CHAPTER FORTY ZEEY Lokacin da muka iso gidansu Jalal kai tsaye gaban Hajiya Layla aka kai ni. Tana zaune da wasu mata itama ta zuba kwalliya ta yi kyau sosai. Baffa Mamman daga wajen mota ya juya Umman Fada da Anty Ruƙayya ne suka damƙani wa Hajiya Layla. Hajiya Layla ta dinga koro mana addu'a har da cewa wai shekara mai zuwa taron suna za a yi. A raina na ce lallai kam. Daga nan ta haɗamu da wata Hajiya za ta mana jagora zuwa ɗakin da za a kaini. Wai ba a gama gyaran "gidan da zamu zauna ba, hopefully nan da sati ɗaya za mu koma gidan." Duk zuwa gidan Hajiya Layla iyakata falo da kitchen ɗinsu da dinning area. Wannan ne karo na farko "dana hau sama. Wani babban ɗaki aka shiga dani. Muna shiga ƙanshin Jalal ya bugeni. Komai tsaf-tsaf a ɗakin. Kuma ɗakin na da girma sosai babu wani tarkace. Akwai seater guda biyu a ɗakin ta wajen window wanda files dake wajen da reading glasses da kuma laptop da aka ajiye a saman ƙaramin stool dake wajen ne kaɗai zai tabbatar maka akwai mai zama a ɗakin, amma everything else looks clean and cozy." "Sai da aka zaunar dani a bakin gado sannan na lura da mutanen da suka rako ni. Ashe har da Mardiyyah," "ƙawata Aishatu, da kuma Maman Asma'u matar Baffa Zakari. Sai da aka zazzauna ne na ji suna mata dariyar ai ƙin fitowa daga motar ta yi da Baffa Adamu ya ce ta fito mutanen da za su yi rakiyar sun isa haka." """Haka kawai ga motoci abailable amma Yaya ya ce ba za mu kai Amarya ba. Inaaa!"" ta faɗa tana riƙe" ƙugu. Sauran suka sa dariya. """Wai! ga ɗaki har ɗaki fa. Yanzu ko a nan aka barki ai kin more, Ziyada"" still Maman Asma'u ke magana." Ai na san yanzu haka Maman Suwaiba tana can tana kumfar baki ba a bari ta taho ba. Kuma duk abinda suka gani a nan sai sun kwashe sun kai mata. Anty Ruƙayya ne ta tambayi Umman Fada yaushe za a kawo gara. Sai ta ce mata bata sani ba. Amma ƙila gobe a kawo. Matar da ta kawo mu ɗakin Jalal ne da Hassana mai aikin Hajiya suka shigo da abinci ɗakin. """Yanzu sai mu tsaya mu ci abinci a nan?. Ana haka ne dama? Komai na gidan masu kuɗi daban yake""" """Maman Asma'u ki yi shiru da bakinki da Allah. Haba!"" Anty Ruƙayya ta faɗa tana jan tsaki." "Zama Anty Ruƙayya ta yi gefena ta ce ""Amarya ga Magariba ta yi mu za mu wuce. Ki yi haƙuri, zaman" "aure ɗan haƙuri ne. Allah ya bada zaman lafiya""" "Ta kalli sauran ta ce ""Jama'a, mun sauke nauyin da yake kanmu dan haka mu ƙara gaba kowa ta je ta riƙe" "nata mijin ku bar Amarya ta huta kafin Ango ya zo ya samu ladan Sadakinsa""" Dukkansu dariya suka saka mini. Mugaye kawai. Abinda suke tunanin ma baya gabana. Ni ta yadda zan samu ciwon kan dana ke ji ya tsaya nake. Ga yunwar data jima a jikina ban samu nitsuwar cin abinci ba. "Ina ganin Mardiyyah da Aishatu suna maganar za su tafi suma na ce ""kuma tafiya za ku yi?. Mardiyyah ki" "tsaya min mana""" """Ta tsaya ta yi miki me?. Da Ango ya iso ke da kanki za ki fatattaketa ki ce ta bar miki ɗaki za ki karɓi" "soyayya""" Haɗewa Maman Asma'u rai na yi dan tun ɗazu take ta ɓarin magana bakinta babu control. "Na riƙo hannun Mardiyyah ɗaya na ce ""akwai Akwatina dana ce a taho min da shi kun zo da shi kuwa?""" Ta ce ai Wallahi ta manta bata ɗauka ba. Dake maganar kawo Amarya duk a ruɗe aka yi shi. Ita ta ɗauka ma Baffa Adamu ba zai barta ta zo ba shi yasa ta manta akwatin. Na shiga uku!. Idan babu akwatin nan fa bani da kayan da zan saka sai kayan jikina. Ga shi ni ba Lefe aka kawo mini ba. """Gobe zan kawo miki akwatin"" Mardiyyah ta faɗa ganin na damu." Wayata ta miƙo min dan ita na bawa alhaƙin riƙe min purse da waya. Na karɓa na fara yiwa Aishatu "godiya dan ta min mutunci duk da mu ba wai ƙawaye bane can-can. An dai tashi tare an yi Secondary, sai occasional chatting ta whatsapp amma ta min mutunci." Sai da maganar Aurena ya tashi nema na je har gidansu na inviting ɗinta na ce tana cikin friends dan "bani da ƙawaye. Ta yi ta min dariya wai ai ni ɗinne tun dana zama celebrity a Instagram na dena kula 'yan unguwarmu. Na ce mata ba haka bane. Ni tun asalina dama ba wai ina shiga harkar mutane bane. Na san ta san hakan, magana ce kawai." "Mardiyyah na yiwa magana na ce akwai kayan biki dana haɗa mata a leda, na bawa Faty nata na" Aishatun kuma ta karɓa a wajen Kaka ta bata idan suka je gida. Haka dai ina gani suka fita daga ɗakin suka barni ni kaɗai. Na dafe kaina dake wani sara min. Can ina zaune ni kaɗai a bakin gado na ji an murɗa ƙofar cikina sai ya ɗuri ruwa na ɗauka Ango ne ya shigo. """Amarya, Amarya"" ina jin haka na sauke ƙaton ajiyar zuciya. Hassana ce ta dawo kwashe abincin da aka" kawo ɗazu. """Amarya barka da zuwa. Mun yi murna da wannan aure. Allah ya sa ki haihowa Yallaɓai Jalal 'yan uku""" "Maganarta sai ya sakani dariya. Wato bama 'yan biyu ba, 'yan uku." Ce mata na yi ba a ci abincin ba. Ta ce mini kada na damu Hajiya ta basu kyautar data fi abinci kafin su tafi. Daga jin haka na san kuɗi ta basu ko wani abu mai daraja dan Hajiya Layla tana da sake hannu. """Ke kam ai Kazar Amarci za a kawo miki. Ki jira Yallaɓai Jalal yana nan shigowa"" ta yi min wani shegen" dariya ta fita. Iskanci! ba Kazar Amarci ba Giwar Amarci. Mtssw!. Ni sun ɗauka wannan ke gabana. Bana tunanin shi "uban gayyar ma zai saka wannan abin cikin lissafinsa. But then, you never know." Na shiga uku! Yanzu idan Jalal ya ce na bashi haƙƙinsa ya zan yi?. Ofcourse ina son aurenmu ya ɗaure! Amma... What if jikina kawai ya ke so?. What if bayan ya samu abinda ya ke so idan deal ɗinmu ya ƙare ya ga na dena burgeshi ya ce in tafi fa?. Subhanallahi!. I'm in for a big mess. Na fara hurzar da iska saboda tunanin zawarci da ya zo mini. Sai yanzu na fahimci lokacin da na ce na amince da deal ɗin Jalal ban gama sanin ma'anar aure ba. Yanzu da na fara analyzing komai daki-daki sai na fara ganin akwai cakwakwiya a gaba. "Ni yanzu wai a tunanina, a 40 year old lafiyayyen namiji zai aureni sannan ya zauna dani haka kawai yana" kallona ba tareda ya taɓani ba. Deal or No Deal?. "Hasbunallahu! I'm an adult, na san me marital intimacy yake nufi. Amma ban taɓa kawo wannan rana a" "raina ba. Tun da muka fara maganar aure da Jalal ban hasaso first night ɗinmu ba. Technicallly, wannan ne first night ɗinmu. Ya Allah!." Gumi ne ya fara karyo mini har tafin hannuna. Na fara rubbing hannun nawa ina ƙoƙarin dai-daita numfashina. Sake buɗe ƙofar aka yi na yi saurin jawo Lifayata zan rufe fiska kamar yadda aka min da farko sai na ga ashe ba Jalal bane. Janan ce da wata. Kaman na taɓa ganinta a gidan. """So, finally sai da kika auri Big bro ɗina"" ta faɗa tana min kallon sama da ƙasa." """Amarya, sannunki da zuwa. Allah ya bada zaman lafiya"" ɗayar da suke tare ta faɗa." """Seriously Saudah ban san me yaya Jalal ya gani a wajen wannan local girl ɗinnan ba. Like among all the" "classy women da ya kamata a ce ya zaɓa he choosed wannan low budget Chef ɗin. Urghh!"" Ta wani yarfe hannunta." "Saudah ta ja hannunta ta ce ""fatan alkhairi muka zo mata Janan, let's go""" "Har sun juya za su tafi sai Janan ta sake juyowa ta ce ""I don't like you. But tunda kin shigo just make my" "Brother happy. Idan ba haka ba, I WILL DESTROY YOU""" Daga haka suka fita daga ɗakin. Sai na ji ɗan guntun confidence ɗina ya yi ƙasa. Kenan dai bayan Jalal zan sha fama da ƙanwarsa. Thank God Hajiya na sona da ni kam ban san ta ina zan samu sauƙi ba. Can na duba wayata na ga ashe time ya tafi sosai. Ina so na tashi na yi sallar Magariba da Isha ma amma ina tsoron tashi daga inda nake na shiga banɗakin mutumin da ban san irin zaman da za mu yi da shi ba. Na cigaba da zama inata dibi-dibin tunanin yadda rayuwata zai kasance a haka har na fara gyangyaɗi. Ƙarshe na ɗan kwantar da kaina a bakin gadon ina jiran Ango... JAYKAY """God!"" Ya furta da ƙarfi lokacin da ya samu damar kaucewa hayaniyar mutane. Finally zai je ya ga" Amaryarsa. From ɗaurin aure zuwa yanzu bai samu zama ba. Up and down kawai yake ta yi. Auren nan was supposed to be short and simple babu hayaniya amma trust Maiyaƙi Family sai da suka yi reception a cikin gida. Dole sai da ya fitowa Ibrahim gaskiyarsa cewa baya son hayaniya saboda kar Cassandra ta ji labari dan bata san ya yi aure ba. Sannan ɗan'uwan nasa ya fara tsaya masa ya taya shi avoiding cousins masu son yin hotuna and specifically ya tura a Family Group cewa Jalal yana so a respecting privacy ɗinsa. Duk da haka bai samu zama ba. Making sure su Uncles ɗinsa da suka masa jagora akan auren sun isa gida lafiya. A yadda ya tsara kafin auren. Iya mutane kaɗan ne za su zo a ɗaura aure kowa ya yi tafiyarsa shi yasa auren ko Invitation Card babu. Amma few days to auren da magana ta fito a Family sai aka yi ta tsare- tsare a bayan idanunsa. Alhamdulillah! Tunda yanzu dai Ibrahim da sauran cousins ɗinsa da suka riƙe shi a waje sun bashi go ahead ya je ya ga Amaryarsa. Bayan ya yi sallar Isha da ya rabu da su sai da ya je ya karɓo wani order da ya placing sannan ya taho gidan. Da ya shigo akwai 'yan biki a gidan amma ba sosai ba duk yawanci an watse. Box ne a hannunsa sai paper bag da ya sayi Kaza. It was weird lokacin da Ibrahim ya tuna masa kada ya manta fa ya shiga da Kaza. Ba ya so ya looking stupid shi yasa bai tambayeshi Kazar me ba?. "Sai yai sauri ya chatting Mr Munir yana tambayarsa ina zai samu Kaza mai kyau a daren nan, and stylishly" ya tambayeshi ko Kazar is necessary. CFO ɗinsa Mr Munir ya masa dariya kafin ya masa bayani akan muhimmancin riƙewa Amarya Kaza ranan farko. Ba wai bai shirya mata special treat bane. Amma bai taɓa sanin haka ake yi ba. Ɗaya daga cikin disadvantage na auren Baturiya kenan. Da farko sai ya yi tunanin ai ba za a rasa Kaza a gida ba idan babu ma zai iya sawa a sarrafa a kawo masa. "But then idan ya fahimci bayanin Mr Munir da kyau, to dai is not proper ya je gida ya fara cewa a grilling masa Kaza. Shine kawai ya biya wani waje da suka yi suna wajen iya grilling Kaza ya siya." Lokacin da ya tura ƙofar ɗakin sai ya hangota kwance a bakin gado. She looks exhausted duk da baya iya ganin fuskarta sosai dan ta rufe da Lafayarta. Ajiye kayan hannunsa ya yi ya tako wajen da take kwance. Tsayawa ya yi yana kallon yadda take bacci. FINALLY ta zama tasa. Finally zai iya riƙeta. Hannu ya kai zai yaye mata fuska sai ta yi firgigit ta tashi. """Relax"" ya faɗa kamar mai raɗa." Fiskarta da take ta cukwikwuye lafayarta tana ƙoƙarin ɓoye masa yake son gani. Hannunsa biyu ya ɗaura akan nata ya haɗa da hannuntan ya yi baya da lafayar har sai da gaba ɗaya fiskarta ya bayyana. Ya tura farin kwalin ciki gashinta da ya sha ƙananun ƙitson chuku ya bayyana. She looks BEAUTIFUL. Ƙura mata idanunsa ya yi yana kallom ƙwayar kumburarrun idanunta. Da ta kasa ɗaukan nauyin idanunsa sai ta sauke nata idanun. Riƙo hannunta ya yi ya ɗagata tsaye. Bai yi wata-wata ba ya haɗata da ƙirjinsa. """Alhamdulillah"" ya furta a hankali yana mai sauke numfashi." ZEEY Ban san ya shigo ɗakin ba sai da na ji ana ƙoƙarin buɗe min fiska. Ɗakin dama tar yake da haske dan haka ina buɗe idanuna na ci karo da fiskar Jalal. Fiskar Ango. Fiskar Mijina. Lokacin da ya buɗe min fiska ya tuge min ɗankwali sai ƙirjina ya shiga dukan tara-tara. Amma yana ɗagani da ya haɗani da jikinsa sai na ji wani sanyi. Na kwantar da kaina a ƙirjinsa. Lokacin da ya kissing saman kaina sai na ji wani tingling a duka jikina. Kai auren namijin da ya fika tsayi ma akwai alfanu. Yadda Jalal ya enveloping ɗina a faffaɗan ƙirjinsa I feel like babu laushin katifar da ta kai ƙirjinsa daɗin kwanciya. Sau ɗaya namijin da ba muharramina ba ya rungumeni. It was stupid bakwanar da muka yi da yaya "Aminu farkon datse soyayyarmu. A ɗakin Kaka ne da muka yi ɗan kukanmu muka ce za mu haƙura da juna. Saboda a tsorace nake kar Kaka ta shigo ɗakin dan ta shiga cikin gida ne. Saboda bai dace ba, gaba ɗaya good bye hug ɗin bai kai minti ɗaya ba. Ba shi da wani meaning shi yasa na manta da komai." "But, This feels different. This feel home, kaman na samu gidana." "Ashe Amaren Instagram da suke cewa first Halal hug ba su yi ƙarya ba. Yanzu da na ke rungume jikin Jalal," yanzu da na samu first Halal hug ɗina sai na ke jin ina ma mu tsaya a haka har tashin duniya. I feel relief daga ciwon kan dana ke ji tun safe. Kaman duk abubuwan da suka faru na baƙin ciki a yau ɗinnan sun washe. I feel kaman in yi bacci a haka and never wake up. Rufe idanuna na yi. I hate to admit amma I'm enjoying this moment da muke tare haka. Kamar bani da wata damuwa a duniya. Ban san mintuna nawa muka yi a tsaye ba. Sama-sama na tsinkayi muryarsa yana raɗa min magana a kunne... CHAPTER FORTY ONE ZEEY """Are you ready for me?"" Na grasping abinda ya faɗa bayan na ɗago kaina daga ƙirjinshi." Ƙura masa ido na yi dan ban gama fahimtar me yake nufi ba. Ready for what? "Sa hannunsa ya yi duka biyu ya ja kumatuna kaɗan ya ce ""da na san haka kike son kwanciya a jikina da na" "ce a ɗaura aurenmu tun ranan da aka kai Sadaki""" "Tab! Na yi baya kaɗan zan bar jikinsa ya dawo dani jikinsa ya ce ""kar ki damu, you can hug me as much" "as you like""" Ƙoƙarin zillewa nake dan sai yanzu na fara jin kunyar kaina. Daga kawoni har na maƙale masa sai kace auren soyayya muka yi. """Come"" ya ja hannuna bayan na bar jikinsa, ya min jagora zuwa wajen kujeran ɗakin inda ya ajiye wani" "cake box da wani paper bag dake ta ƙanshin gasashshiyar Kaza, sai wata leda da nake tunanin drinks ne" a ciki. """Sit"" ya zaunar dani. Ni kam binsa kawai nake da idanu." """Ban san ko kin tuna ma'anar date ɗin yau ba?""" """Date ɗin yau...?. Yau aka ɗaura mana aure...What else?... Ha!"" Na waro idanuna tunowa da na yi yau" date ɗin Birthday ɗina ne. Yau officially na cika 25yrs a duniya. """Ya aka yi ka san...?""" """Surprised, right?"" Ya ɗaga min gira. ""Kar ki yi mamaki, na san kusan komai naki. Kuma yau zan ga" "sauran""" """Me zaka gani?"" Na yi saurin kare ƙirjina. Ga shi Lafayata ya yi sako-sako saboda tunda Jalal ya yaye min" fiska ya koma kaman Sari. """Komai naki"" ya faɗa yana lakutan hancina. Ƙanƙame jikina na yi ina tsoron abinda zai wakana a wannan" dare. Sai da na ga ya buɗe cake box ɗin sannan na ɗan sake jikina ina murmushi. Ƙaramin cake ne da aka rubuta HAPPY BIRTHDAY ZIYADAH a kai. Ban taɓa celebrating Birthday ba. Wanda ma ya damu da Birthday ɗina a baya Yaya Aminu ne. Shine yake ƙoƙarin aiko min gifts duk ranan Birthday ɗina. Hana ƙarya ya taɓa kawo min cake sau biyu. Amma ni a karan kaina ban taɓa wani tsayawa na yi wani abu na celebration a ranan Birthday ɗina ba. Wataƙila shi yasa ma na manta. Tun ina yanka cake ɗin cikina yake ƙogi. Na ajiye slize ɗin dana yanka a saucer plate da ke wajen sannan na sake yanka slize ɗin kashi uku. Ina ƙoƙarin ɗauka na kai bakina ya riƙe min hannu. """Allow me""" Ɗaukan cake ɗin yayi da hannunsa ya sa min a baki. Na fara taunawa a hankali. """Kai ma ka ci"" na faɗa ganin ya bani har sau biyu." """Kema ki bani dai"" ya kwaikwayi maganata." Murmushi na saka kafin na ɗauki last piece ɗin zan sa masa a baki. "Ɗan batalikin nan maimakon ya ci cake ya bar min hannu, sai ya riƙe hannun nawa ya fara lashe min" saman yatsu yana min wani kallo kaman wani maye. Ji na yi wani sanyi na zirya a duka jikina. Ni kam yau sai ta Allah a hannun Jalal. Ban sake gigin bashi cake ɗin ba. Ganin kallon da yake min sai na yi saurin ɗaukan goran ruwa mai sanyi na buɗe na ɗan kurɓa. "Miƙewa ya yi yace ""I have a gift for you""" Sa hannu yayi a Aljihunsa ya fito da wani ƙaramin box. Ya buɗe ya fito da wani customize gold ring mai kyau a ciki. Ya saka min a yatsa na. Ƙurawa zoben ido na yi na fara ƙoƙarin karanta abinda aka rubuta a jiki. JAY. Na ɗago ina kallonsa. Shima kallon nawa yake bai yi magana ba. """You don't like it?"" Ya tambaya ganin ban yi magana ba." """Thank You... JAY"" na furta a hankali." "Kai hannuna yayi dai-dai bakinsa ya kissing sannan ya ce ""don't ever take it off""" Na gyaɗa masa kai duk da kuwa ko bai faɗa ba bani da intention ɗin cirewa. Gift ɗin first Birthday a gidan miji ne dan haka I have to cherish it. Sunansa dake maƙale a jikin zoben zai riƙa tuna min cewa ni ɗin matar Jalal Maiyaƙi ce. Zama ya yi ya tambayeni ko na ci abinci. Na girgiza masa kai. Ya turo min Kazar da ya kawo ya ce na duba idan bai min ba zai je ya siyo wani. Na ce masa ya yi. Ina buɗe paper bag ɗin ƙanshin Grilled Chicken ɗin ya buge min hanci. Take na tuno maganar Hassana na ɗazu da take ce min wai Jalal zai kawo mini Kazar Amarci. "Sai kawai na ji tsoron taɓawa. Na tsaya ina kallon Kaza, Kaza na kallona. Ga shi dai gashin yayi so juicy" har yawuna yana tsinkewa amma ina tsoron taɓawa. """Ban sa poison a ciki ba, Sunshine. Eat. Saboda ke na siya""" Heck! yunwa nake ji. Kazar nan dai nawa ne kuma ba zai ci kansa ba idan ba a ci shi ba. Koma mi Jalal ya zuba a ciki kafin ya kawo min dai cin abuna zan yi. Wai me ma yasa ake tsorata mata da Kazan Amarci ne?. Kuma laifin masu Hausa novels ne dan nima a nan na san batun Kazar Amarci. "Barina ya yi ya ce zai watsa ruwa, ganin na ɗan sa hannu na yagi tsoka kaɗan na fara ci." Ina ganin ya nufi wani kwana inda nake tunanin nan closet ɗinsa yake da bathroom sai na zage na fara cin Kazar sosai. Na sake yanka cake na ci abuna. To ai duka nawa ne. Time to time ina ɗaga yatsuna in kalli zoben da aka bani. JAY. Ina jin kamar ya fito daga banɗakin na yi saurin rufe cake ɗin da box ɗinsa dan kar ya ga na sake yankawa. Na kora ruwa na zauna na matse. "Fitsari nema ya dameni, marata ta cika. Shi yasa ma na sha ruwa kawai ban taɓa drinks ɗin da ya kawo" ba. Matsalar yanzu idan na ce zan yi wanka wani kaya zan saka?. Gashi ina so na yi sallah ma. Kai na yi ragon azanci ma da ban sa Mardiyyah ta je gida ta kawo min akwatina ba. "Lokacin daya fito already ya saka Pyjamas ɗinsa baƙi mai tsantsi, ta wajen wuyan rigan da hannun akwai" ɗan layin fari-fari a wajen. """Kin gama?""" Na ce masa eh. """Za ki yi wanka da kanki ko na zo na miki?""" """A'a!"" Tuni na tashi daga inda nake zaune. Ya wani sa dariya. Mugu kawai." "Hanyar banɗaki na yi sai na tsaya cak ganin walk in closet ɗinsa. Wajen shirts daban, wajen suits daban," wajen tie ɗinsa gasu nan a jere different designs and color. Ga takalma. Ga wajen huluna. Wani pink Akwati babba na gani har da ribbon a jiki kaman irin Akwatin lefe ɗinnan. To kodai Akwatin kaya na ne? "Kar na yi karambani sai na leƙo na ce ""erhm, please zan iya buɗe pink box ɗinnan na duba ko akwai" "kayan da zan iya sawa a ciki?"" Na tambayeshi duk da akwatin ya fi kama da dan ni aka ajiye a wajen. Yadda wajen closet ɗinsa yake cike da kaloli masu sanyi ba zai ajiye pink akwati a wajen haka kawai ba." """It's yours, Sunshine. Hajiya ta sa aka ajiye a wajen. Sauran kayanki suna sabon gida""" Ai kafin ma ya gama bayani tuni na yi wajen akwatin na fara ƙoƙarin buɗewa. Alhamdulillahi!. Kayan bacci ne a ciki da underwears sai kuma wasu ɗikakkun kaya kala huɗu da takalmi da veils da hijabin Sallah. Dai kayan da zai isheni kwana biyu haka. "But babu kayan baccin Arziƙi a ciki. Pyjamas ɗin da aka saka mai guntun wando ne, shorts, na san iya" rabin cinyata ma zai tsaya. Eh! Lallai Hajiya Layla. Wato in sawa ɗanta shorts ko!. Cire Kayan jikina na yi na shiga banɗaki na fara wanka bayan na ɗan yi ƙauyancin kyan banɗakin kaɗan. Da Alwalata na fito. Amma no way zan saka guntu-guntun kayan baccin da aka tara min a akwatin nan har huɗu. Pyjamas ɗaya nema a ciki sauran sexy lingerie ne. Maimakon na ɗau kayan cikin akwatin sai na tafi ɓangaren da kayan baccin Jalal suke a jere na fara neman wanda zan saka. Ina zumɓula riga da wandonsa na jini bururum rigan ya min tsayi wandon ma haka. Na fara ƙoƙarin naɗe "hannun rigan na ji ance ""daga zuwa kin fara min sata ko"" na juyo da sauri ina faɗin ""ni ba sata na yi ba, aro na ɗauka""" """Really!. Me ya samu wancan?"" Ya nuna akwatin dana bari a buɗe. Kayan baccin ne kuma a sama. Sexy" red nightwear dana gama jujjuyawa ina faɗin no way zan saka irin kayan nan Jalal ya ganni a cikinsu. Takowa ya yi inda na ke tsaye. """Allah, sanyi nake ji shiyasa na ɗauki aron naka"" na faɗa da sauri." """I see""" """Da gaske nake""" """Zan iya rabaki da su in 2 seconds, Sunshine"" ya faɗa yana min wani mayetaccen kallo" """Da gaske ni bance...kawai... barin yi Sallah"" na yi saurin barin wajensa na je na ɗau hijabin dana samu a" cikin Akwatin na fito ɗakin. Already ya ajiye Sallaya a wajen kaman ma shima sallar ya gama yi dan na ga har da carbi a wajen. Tada Sallah na yi ƙirjina na ƙara gudu saboda tunanin abinda ka iya wakana a wannan daren farko namu. Bayan na gabatar da Sallar Magariba da Isha sai na ƙara da nafila dan Mai Girma Ango yana can gado da Laptop ɗinsa a cinyarsa yana aiki. Ban ga alamar zai ce zai jagorancemu Sallah ba. Na jima zaune ina koro addu'o'i. Na roƙi Allah ya tabbar da Alkhairinsa a wannan auren. Bayan na gama sai na miƙe na naɗe sallayar na je na ajiye tareda hijabina. Ina dawowa sai na zo na hau gadon zuciyata na dukan tara-tara. Da gaske dai a gado ɗaya za mu kwana. Ni dana saba da kwana kusa da 'yar tsohuwata tana ƙanshin Lalle da Robb da Aɗaral Bakur sai gani gefen mutumin dake saka zuciyata fluttering Can ƙarshen gadon na takure jikina ina Allah-Allah bacci ya ɗaukeni dan gaskiya ban shirya ma komai ba. JAYKAY Lokacin da Jalal ya gama duba ayyukansa miƙewa ya yi ya je ya ajiye Laptop ɗinsa ya dawo ya tsaya yana kallon yadda Ziyada take bacci a bakin gado. Musabbabin fara aikin nasa ma saboda ita ne. Lokacin da ya ganta cikin Pyjamas ɗinsa da ƙyar ya iya "controlling kansa. Dan a yadda wani sha'awarta ya taso masa all he wants to do shine ya yi fatali da kayan jikinta ya nuna mata yadda yake buƙatarta. But, NO. Dole ya controlling kansa. YES, ya sani ita ɗin mallakinsa ce yanzu, yana da damar yin yadda yake so da ita. Kuma bisa yadda ta ɗan sake da shi ba za ta hana shi hakan ba idan ya buƙata. But, that's not abinda ya shirya musu. Yana so ne ya fara da bata kulawarsa, yana so ya koya mata sonsa. Yana so a lokacin da zai yi tarayya da ita to ya zamto a shirye take da buƙatarsa as much as yake buƙatarta. He wants to make LOVE to her ba wai have SEX with her ba. A yanzu idan ya nemeta, zata submitting masa ne bisa cewa shi Mijinta ne. Not because itama wutar sonsa da sha'awarsa na cinta. Yana son ganin duka wannan idan yana tarayya da ita. Wannan ɗin shi ya rasa a tattare da Cassandra. Shi yake kwaɗayin samu a wajen Ziyada." From day one har wa yau. Shi da Cassandra suna gogar juna ne don biyan buƙatan gangan jikinsu. Amma da zaran an gama kuma shikenan sai wani haɗuwar. "With Ziyada, so yake jikinsu, haɗe da zuciya da kuma ruhinsu su yi tarayya da juna duka a lokaci guda." Ba kawai jikinta yake so ba. So yake ya sameta. ALL of her. Zuwa lokacin da ya gama duba wasu reports a Laptop ɗinsa. Ya riga ya daidaita kansa. Sai da ya gama ƙare mata kallo sannan ya hau gadon. Matsowa ya yi kusa da ita ya raɗa mata magana a kunne. A yadda ta gaji baccinta har ya fara nisa. Lokacin da ya jawota jikinsa ya cuddling ɗinta ne ta ɗan farka tana ƙoƙarin zillewa. """Relax, Bacci za mu yi"" yana raɗa mata a kunne." Yana jin yadda heart ɗinta ke bugawa da ƙarfi. She's tense. A hankali kuma sai bugun zuciyarta ya fara raguwa. Ta relaxing jikinta sosai. Daga baya kuma bacci ya tafi da ita. "Shima Jalal ɗin bai jima ba, baccin ya sace shi. Afterall dukkansu a gajiye suke..." CHAPTER FORTY TWO ZEEY Wani kanshi mai daɗi ne ya tashe ni. Soft and homy. Na sake rungume pillown da ke kusa dani mai laushi "mai daɗi. But, wait! Pillown nan dogo ne, kuma ya kanannanɗe mini duka jikina. Yadda ya wrapping ɗina sai na ji bana son tashi. Na cigaba da shafa ƙaton pillowna ina tsoron idan na buɗe idanuna daɗin zai ƙare." A hankali kuma sai abubuwa suka fara dawo mini. Ba a gadon Kaka nake ba. Pillown gadon Kaka ƙaramine kuma bashi da daɗin wannan. Sannan babu wani tsini mai motsi dake zungurina idan na kwanta a gadon Kaka. Subhanallahi! Ba a gadon Kaka nake ba. Jiya aka yi aurena. Akan gadon Mijina nake. Kuma wannan "pillow dana runguma ba pillow bane, mutum ne. Jalal. Mijina." Na yi saurin tashi a zabure ina jin kaman wani abu marar kyau muke yi. "Wait, ni da Jalal a haka muka kwana?" It feels wrong. Sai kuma realisation na cewar ƙarƙashin inuwar aure muke ya sauka mini. Duk da haka sai na ji kunyar kaina musamman da idanuna suka yi tozali da abinda yake ta zungurina tun ɗazu. Na yi saurin ɗauke idanuna na yi gefe da su ina tunanin duk abinda Jalal ya packing a wajen nan ba na wasa bane. Na taɓa karanta cewa wai duk safiya Alhaji Dogon duk wani lafiyayyen namiji yana tashi. To gashi yau kam na tabbatar da hakan. Ba zan iya tuna yadda aka yi na yi bacci jiya ba. Na dai san na yi sallah. Na zo na hau gado lokacin Jalal "yana aiki a Laptop ɗinsa. Amma ban tuna dawowa tsakiyar gadon ba, ko kuma manne ma jikin Jalal." "Sake jawoni ya yi na faɗa jikinsa ya wrapping ɗina yana faɗin ""Good Morning, Sunshine. Wa ya faɗa miki" "ana gudun Miji idan an tashi da safe""" """Ni ba gudunka nake ba"" na faɗa still ina jin hardness ɗinsa yana taɓa ni. Sharewa na yi kamar ban san" dawar garin ba dan kar ya gane na san abarsa na motsi ya ce zai min abinda bai min daren jiya ba. """Zan yi fitsari"" na faɗa ganin bashi da niyyar sakeni kuma da alama time ya tafi." Soft kiss ya min a wuyana kafin ya sakeni. Na ji tsikar jikina ya tashi. Akwai wani spark dake tashi duk lokacin da Jalal ya taɓani ko ya kissing ɗina. Tun jiya na lura da hakan. Lokacin dana bar gadon sai na ɗau wayata na duba time ashe har shida saura na safe. Bana tunanin shima ya yi sallar Asuba. Dan haka a gurguje na shiga banɗakin na yi fitsari na yi Alwala na fito. Lokacin dana fito daga banɗakin yana tsaye wajen closet ya cire rigarsa sai wando kawai a jikinsa. Na yi saurin wuce shi ina tsoron ganin abinda ban shirya ma ba. But Damn! Ganin fafaɗan ƙirjinsa babu ya tuna min da yadda na ji daɗin rungumar da ya mini jiya. Subhanallahi! Sallah fa zan yi. Na shimfiɗa sallaya a inda na ga ya saka jiya na tada Sallah. Bayan na idar da Sallah sai ga shi ya fito sanye da Jallabiya. Wata sallayar ya shimfiɗa shima ya fara sallah. "Ƙarfe shida ta riga ta wuce, dukkanmu mun makara Sallar Asuba." Yanzu fa ƙila mutanen gidan nan su yi tunanin ko wani abun muka yi daren jiya har ya sa muka makara. Da yatsuna na fara irgen Azkar dan ban ɗauko Carbina daga gida ba. Jefo mini nasa ya yi daga inda ya kalmashe ƙafarsa yana Addu'a. Lokacin da ya ke Sallar na ji karatun da ya yi. Kuma na ji daɗi da zamansa a Turai bai hana shi iya karatun "Qur'ani ba. Suratul Qiyama ya karanta, ya rabata biyu. Ɗaya a raka'ar farko, ya ƙarisa sauran a raka'a ta" biyu. Shi ya fara miƙewa ni ina zaune ina cigaba da Istigfari. Yawanci in dai ina da lokaci duk bayan Asuba Istigfari dubu ɗaya nake yi. Addu'a shine sirrina. Lokacin dana gama sai nima na naɗe sallayar. Yana zaune a kujera ya saka earpiece yana kallon Laptop ɗinsa. Kaman video call yake yi. Tunanin shiga banɗaki na yi wanka na shirya na yi. Sai na ga gara na koma na kwanta na sake ɗan hutawa. Dana koma kan gadon kuma sai na fara lissafin anya haka ake yi kuwa? Ranan farko na auren mutum tashi ake da sassafe a yi wanka a ci kwalliya ko ya ake yi?. Ya kamata a ce akwai Manual da za a riƙa baiwa kowacce Amarya saboda ta san yadda za ta yi musamman a first weeks na aurenta kafin ta saba. To kuma fa zai iya yiwuwa kowacce Amaryar da ta yi auren soyayya ta san ya ake yi. Da an yi daren first night an raya sunna da safe dai dole a tashi a yi wankan tsarki. To ni kuma da nake clean babu wani saƙon dana amsa balle na yi wanka ya ya kamata na yi?. Na ɗaga wayata na duba time na ga 6:49AM. Zan bari kawai sai bakwai da rabi sai na tashi na yi wanka. Na gyara kwanciyata dan na sake huta gajiyar biki. Ina rufe idanuna kuma sai zuciyata ta fara hasaso min tudun dana gani ɗazu. NO. Na girgiza kaina ina ƙoƙarin kore duk wani dirty tunani da yake zuwa mani. Amma sheɗanin da ke zuciyata sai ya cigaba da hasaso mini abubuwan da ka iya faruwa idan Jalal ya ce zai sake mini ajiyar dake tsakiyar cinyoyinsa... * Ban san yaushe na yi bacci ba. Lokacin dana farka Jalal baya ɗakin. Na jawo wayata na duba sai na ga ƙarfe takwas har da minti Arba'in. Ya Ilahi! Ashe na jima da bacci. Na miƙe na fara gyara gado. Dana gama sai na je na cire pyjamas ɗin Jalal sannan na shiga banɗaki na yi wanka. Dana fito sai na buɗe Akwatina na fara neman kayan da zan sa. Wata doguwar rigar Atamfa blue da fari na zaɓa na saka. Na ɗau gyalensa da takalmi flat da zai shiga da shi na sa. Na tsaya a gaban mirror ina gyara ɗaurin ɗankwalina. Ɗaurin Zahra Buhari na yi mai kyau na fito a Amarya sak duk da babu kwalliya a fiskata. Ina cikin shiri wayata ta fara ringing. Na je na ɗauketa akan gado sai na ga Agnes ke kirana. Na saka wayar a handsfree "Agnes: ""Amarya, Amarya. Tun jiya kike trending fa. Account ɗinki is blowing up. Na san an yi haka dan a" "ɓata miki suna ne but this is free visibility, ki using wannan lokaci ki pushing Gidan Girki saboda ya boosting engagement a page ɗinmu""" Sarƙar da nake ƙoƙarin sakawa na tsayar na tambayi Agnes ban gane ina trending ba. Ni ban posting komai akan aurena a shafina ba. Dama niyyata idan an gama kujuba-kujubar biki na samu time sai na ɗan posting few pictures haka saboda mutane su san na tashi daga Single Pringle na koma Matar Aure. "Agnes ta ce ""wait, ba ki ga hotunanki da ke ta flying a blogs ba?. Account ɗinki ya blowing fa, tsakanin" "jiya da yau kin samu ƙarin 3k followers a Instagram. Mutane nata shiga page ɗinki dan suga ko za ki posting wedding pictures ɗinki""" """Agnes ban sa komai a page ɗina ba. Ni ko a whatsapp status ban saka komai da zai hinting na yi aure ba." "What is happening?""" Ina maganar na ɗau wayar na buɗe data na shiga Instagram account ɗina. Scrolling na fara yi ina neman shafin bloggers ɗin Arewa dana ke following sai na ci karo da post ɗin da Faty ta yi jiya da dare ta tagging ɗina. Hotona ne cikin farin Lafayar dana sa jiya da yamma. A ɗakin Kaka aka yi hoton kafin a zo ɗaukana. Babu "make-up a fiskata, ga idanuna da suke kumbura saboda kukan dana sha." "Yes, kayana ya yi kyau sak classy Amarya. Ni ɗinma make-up free face ɗina ba laifi ba wai na yi muni" "bane saboda camerar iphone ɗin ya fitar da hoton sosai. Amma haɗa hoton tareda hoton Jalal yana cikin mota ƙafarsa ɗaya a waje an ɗau hoton kamar bai san an ɗauka ba, looking handsome cikin kayan daya saka ya je ɗaurin aure sai na yi kamar wata 'yar Maula a gefensa." Ina ma Faty ta samu hoton Jalal ne?. Dan Jalal baya Instagram. At least babu official account da sunansa a IG. "Tukunna ma, ba na faɗa mata sai bayan biki zan ɗaura pictures a page ɗina ba idan aka turo min wanda" mai hoto ya ɗauka. Me yasa bata saka hotona da ita ba sai ta nemo hoton mijina ta haɗa da nawa ta nunawa mutane shi tun ni mai mijin ban fito na nuna musu ba?. Wani dogon turanci ta zuba da ya ƙare da CONGRATULATIONS! HAPPY MARRIED LIFE BESTIE❤. A Account ɗinta na Tyma Glams ta posting dan shine yake da followers sosai. Yanzu tsakani da Allah duk cikin pictures da muka ɗauka da make up a fiskata bata ɗaura ba sai wannan da nake looking tired and stressed saboda abubuwan da suka yita faruwa. "Comments ɗin post ɗin na shiga, na fara karantawa. Over one thousand comment a ƙasan hoton. Abun" mamaki ga kowanni comment na Congratulations guda ɗaya sai ka ga negative comments biyu ko uku kafin ka sake ganin wani Congratulations ɗin. Hawaye ne ya taru a idanuna lokacin dana ga abinda mutanen da ba su sanni ba suke ta faɗa a kaina. Mijin ya fita kyau. Chef ɗin Talakawa ta samu ɗan Abuja. Kutumai! Yanzu Jalal Maiyaƙi take aure?. An ce uwarsa ta maƙalewa sai da ya aureta. Mismatched. Wannan daga gani daɗin abinci ya ji ya aureta. Tsakani da Allah idan ba ƙarya mutum zai yi ba Angon ya fita kyau. Babu mai son Auren a familyn. Janan Maiyaƙi ta ƙi posting ɗin hoton Amaryar. Wait! Yayan Janan Maiyaƙi ta aura???. Kaɗan kenan daga abubuwan da suke ta faɗa. Shiga shafin Janan ɗin na yi dan na ga ko da gaske bata yi posting hotona ba. Hoton da Faty ta ɗauko daga page ɗin Janan na gani a ƙasan hoton ta rubuta A NEW BEGINNING❤. Na san me yasa Janan ba ta posting hotunan bikinmu ba. Na san me yasa bata nunawa followers ɗinta cewa yayanta ya yi aure ba. Saboda matar Jalal ne. Cassandra. Na san komai amma duk da haka sai na ji wani zafi a raina. Wani ɓangare na zuciyata na jaddada mini comments ɗin mutane akaina gaskiya ne. Ban gama shiga tashin hankali ba sai da na ga wata babbar blogger ta saka hoton da Faty ta haɗa ta yi dogon rubutu. Na zauna a bakin gado ina karantawa hawaye na zubo mini. Ashe har part 1-3 aka yi labari a kaina. A part one aka zage aka rubuta yadda Chef Zeey mai abincin gargajiya ta shiga jikin wata Hajiya har sai da ta auri ɗanta. A part two kuma aka rubuta yadda Chef Zeey mai abincin gargajiya ta ci kuɗin wani Alhaji sannan ta rabu da shi ta auri wani Millionaire. "A part three kuma suka rubuta yadda Chef Zeey mai abincin gargajiya ta auri kanta, babu Lefe, babu" kayan aure. Family basa son aure komai a ɓoye aka yi. Wa ye ya harhaɗo ƙarya da gaskiyan nan ya rubuta a kaina?. Wannan labarinma a wajen Fatyn suka ji ko dai wani ne daban ya je ya kitsa min ƙarya saboda ya ɓata min suna?. Kai Faty ba za ta min haka ba. Ba za ta bada labarin Alhaji Nafi'u ko kuma ta ce ta dalilin Hajiya Layla na "haɗu da Jalal ba. Amma the more nake tunanin ba za ta min haka ba, the more na ke jin babu wanda yake da information ɗin abubuwan da suka faru a aurena sai ita." Wato comments ɗin shafin Faty nafila ne akan na wannan blog ɗin. A shafin blog ɗinnan cin mutucina ake ta yi yadda ban taɓa tsammani ba. Sun jefe ni da yin asiri. Sun jefe ni da bin masu kuɗi. Sun jefe ni da siyar da mutuncina saboda kuɗi. Agnes tanata kirana amma na kasa ɗauka. Numbar Faty na danna saboda ban taɓa tunanin zata min haka ba. Da ace Janan ce ta posting ba zan damu ba. Da a ce wani daban ne ya posting. Kai ko 'yan gidanmu ne "suka yi posting ba zan damu ba. Amma Faty, Bestie na!." """Amarsu manya. Hope dai kin gasa jikinki da kyau dan na san Jalal ba zai miki da sauƙi ba"" Faty ta faɗa" tana min dariya. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya taso mani na ji kamar na ɗura mata ashar amma sai na danne na ce mata """Faty, yanzu Fisabilillahi abinda kika min ya dace?. Kin je kin ɗaura pics ɗina dana mijina bayan da bakina na ce miki sai bayan biki zan ɗaura""" """Subhanallahi! Bestie kawai na ga hoton Ango a shafin Janan Maiyaƙi ne shine na haɗa na ce na posting" "tunda baku ɗau hoto tare ba""" """Amma, kin ga abinda mutane ke ta faɗa a kan hoton kika yi shiru ba ki ce komai ba?""" """Me ake faɗa?. Ni Wallahi daga jiya dana ɗaura post ɗin har yanzu ban hau Instagram ba. Amma tunda" "ba kya so ba rin je na sauke post ɗin""" Kashe wayar na yi tun ma kafin ɓacin rai ya ɗebeni na faɗa mata maganar da har abada ba zata manta da ni ba... CHAPTER FORTY THREE JAYKAY Lokacin da ya bar ɗakinsa bayan ya gama waya da Cassandra Ziyada ta riga ta yi bacci. Bai tasheta ba saboda ya san tana buƙatar hutu. For a second da ya ga message ɗin Cassandra ya ɗauka ta ji labarin aurensa ne. Lokacin da yake magana da ita kuwa sai ta buge da jaddada masa irin soyayyar da take masa da kuma irin missing ɗinsa da ta yi. Biye mata ya yi ya bata lokacinsa suka yi magana. Har da tambayarsa ko shi kaɗai ne a ɗakin. "Sai da ya leƙa fiskar Ziyada da ke bacci sannan ya jaddada mata shi kaɗai ne a ɗakin, aiki ma yake." Da suka gama wayar sai ya je ya shirya ya fita. Ɗakin Hajiya ya shiga. Bayan sun gaisa ta tambayeshi ya kwanan Amarya ya ce mata lafiya. "Da zai fita ta ce masa zuwa yamma sai ya shirya ya kai Ziyada family house ta gaishe da Inna, wato" mahaifiyar Daddynsu. Har yanzu tana raye sai dai tsufa da ciwon ƙafa. Bayan ya bar ɗakin Hajiya fita ya yi ya sa Direbansa ya kaishi gidan Uncle Idris ya masa gaisuwar ban gajiya dan a safiyar zai wuce Abuja. Uncle Idris ya ce masa idan an kwana biyu ya kawo musu Amarya Abuja su gaisa. Ya ce zai yi hakan Insha Allah. Lokacin da ya dawo gidan ya shiga ɗakinsa sai ya samu Ziyada kwance tana kuka. Me ya sameta?. Lafiya lafiya fa ya fita ya barta tana bacci. "Da sauri ya ƙariso inda take kwance ya kira sunanta a hankali ""Zeeyadah""" Ta ɗago kanta fiskarta a kumbure idanunta sun yi ja tana jan hanci. """What happened?"" Ya tambaya hankalinsa a tashe." """Come here"" ya buɗe mata hannunsa. Kwantar da kanta ta yi a ƙirjinsa tana sheshsheƙar kuka." """Faɗa min me ya faru?""" """Kin yi missing ɗina ne?""" """Shhh! Sorry, ya isa. Ya isa""" Ya cigaba da lallashinta har sai da ta yi shiru. Wayarta ta jawo ta kunna masa wani video. Wani mutumi da bai san ko waye bane yake masifa. Malam Adamu da ya gani gefensa kuna Ziyada tsaye ne ya sa shi karɓan wayar a hannunta yana ƙoƙarin fahimtar abinda ake faɗa. Videon gaba ɗaya bai kai minti ɗaya ba. """Waye wannan?""" """Who is he?"" Ya tambaya da kakkausar murya har sai da Ziyada ta ɗan ja baya a tsorace." """Alhaji Nafi'u ne. Wani ne ya uploading videon abinda ya faru jiya da safe kafin a ɗaura aure"" ta faɗa" tana sheshsheƙar kuka. Yadda jijiyoyin kansa suka firfito lokaci guda ka san ransa a mugun ɓace yake. Instantly ya ji ba zai yarda da wannan cin fuskar ba. Duk abinda zai taɓata. Duk abinda zai sakata kuka sai ya daƙile. Wayarsa ya ɗaga ya danna numbar Lawyansa. """Zan tura maka wani video yanzu, ka duba ka drafting defamation case akai""" Yana gama faɗin haka sai ya sake kiran wani number. """JK Maiyaƙi speaking. Akwai wani video da nake so a tracing min wanda ya fara ɗaurawa. And all copies" "should be taken down. Yes. Thank you""" Zuba masa ido Ziyada ta yi jin abinda ya faɗa. "Tashi ɗaya kuma sai ya sake fiskarsa yace ""Ke da kike da Miji me ya sa za ki yi kuka?"" Ya sa babbar" yatsarsa ya fara share wani ƙwalla guda da ya gani a saman kumatunta. """I'm here for you. Duk abinda zai sameki ni za ki kira kin ji?"" ta gyaɗa masa kai wasu hawayen na" saukowa. """Wannan ba komai bane. Za a yi maganinsa according to the Law""" """Ba shi ya ɗaura videon ba""" """Shhhh! Manta da shi"" ya faɗa yana ɗan murza tsakanin girarta." """Ni dana ɗauka zan dawo na samu Amarya ta min shiri na musamman6 sai ga shi kin ɓata kwalliyarki da" "hawaye""" """Ni ban yi kwalliya ba"" ta faɗa muryarta a dashe." """Wannan fa?"" Ya nuna idanunta. Ko bata kalli fiskarta a madubi ba ta san kwallinta da ya zazzago saboda" kuka yake nufi. """Kwalli ne kawai""" Ƙwanƙwasa musu ƙofar da aka fara yi ne ya katse maganar da ya ke son yi. """Yallaɓai, Hajiya ta ce a kawo muku abinci yanzu ne ko sai anjima?""" "Jalal ya kalli Ziyada ya ce ""ba ki ci abinci ba?"" Ta gyaɗa masa kai." """Why?"" Sai kuma ya ɗaga muryarsa ya ce ""Ki kawo"" ." Shi ba ma'abocin karyawa da wuri bane. Infact a mafiya yawan lokuta ma yana skipping breakfast sai da rana ya ci abinci. Yana hakan ne saboda baya son ajiye tumbi. Kusan minti uku sai aka sake ƙwanƙwasa ƙofar. Jalal ya miƙe ya je ya buɗi ƙofar ya karɓi tray ɗin abinci daga hannun Hassana da take ta rarraba ido tana son ganin cikin ɗakin. Ajiye tray ɗin ya yi a saman ƙaramin stool ya ce Ziyada ta taso ta zo ta karya. Har ƙarfe goma na safe ta wuce bata karya ba saboda ta tsayawa yiwa wani banza kuka. Idan ya gama da Alhaji Nafi'u sai zaman garin Zaria ya gagare shi. """Eat"" ya commanding ganin ta tsaya kallon abincin." """Idan kika sake tunanin wancan mutumin sai na yi maganinki""" """Kalleni"" ya tallafo fiskarta." """I'm the ONLY MAN you should think about. Idan kin gaji da tunanina then you can start thinking about" "yadda za ki running Gidan Girki. Za a buɗe JK Plaza nan da kwana bakwai""" """Kwana bakwai ?"" Ta maimaita da ƙarfi." """YES""" Sai da ta fara cin abinci sannan shima ya ɗau mug ya fara shan coffee. Ga shi dai yana jin zafin coffee ɗin "a harshensa, amma zafin da ya ke ji a zuciyarsa ya fi ƙona shi. Bai taɓa jin zai iya illata wani a rayuwarsa ba, sai yau da ya ga Ziyada ta yi kuka saboda wani banza." A yadda ya ji zafin hakan idan Alhaji Nafi'u bai kwana a prison ba sunansa ba Jalal Kabeer Maiyaƙi ba... ZEEY Wanka na sake yi na chanja kaya bayan Jalal ya fita jim kaɗan bayan mun gama yin breakfast. Tunda ya ce min kada na sake kuka akan Alhaji Nafi'u na ji wani sanyi a raina. "Na tuno maganarsa ""Ke da kike da Miji me ya sa za ki yi kuka?""" Kwana ɗaya da aure amma har na fara ganin amfanin Miji a rayuwata. Duk kukan da na sha saboda ɓata min suna da ake son yi a social media amma one hug da kuma assurance daya bani har na ji kamar duka damuwata sun zo ƙarshe. "Sai yanzu na gane ɗaya daga cikin definition ɗin MIJI shine, mutumin da ya ke ɗaukewa matarsa ko kuma" ya rage mata duk wani damuwarta. "Duk namijin da bai faɗa wannan definition ɗin ba, to bai cika a kira shi MIJI ba." "Da a ce bani da aure aka saki wannan videon a social media, da ni kaɗai zan tunkari abin na fara ƙoƙarin" "kare kaina. Amma yanzu, auren Jalal ya saka mini wani blanket na kariya. Duk abinda ya sameni to ya shafeshi, kuma zai handling ɗin abin ba tareda na sha wahala ba." A kunyace na fito daga ɗakinmu kusan ƙarfe shabiyu na rana ɗauke da tray ɗin abincin da muka ci. Ina saukowa zan kai kitchen na haɗu da Hassana sai ta karɓa a hannuna tana min wani munafukin dariya "wai ""Amarya sannu da fitowa""" Yadda na ga tana kallon fiskata da ya kumbura saboda kukan da na yi na san gulmar wani abun ne a ranta. "To ba abun da take tunanin bane ya sakani kuka, ko kuma ya hana ni fitowa tun safe." Tambayarta na yi ina Hajiya ta ce min Hajiya tana ɗakinta. Na tambayeta wani ɗaki ne ta min kwatance. Ƙwanƙwasa ɗakin Hajiya na yi tareda sallama. Buɗe min ƙofar aka yi. Ɗan Jalal ne. "Kallona yake bai yi magana ba. Na masa murmushi na ce ""Junior ya kake""." """I'm fine"" ya faɗa kaman wanda yake ƙoƙarin karanto wani abu a fiskata." """Muhammad, ba za ka gaishe da Antynka da kyau ba"" Hajiya ta masa magana." """Ziyadah ki ƙariso ciki mana""" "Yaron bai gaisheni ba, sai ma ya fice daga ɗakin da gudu." Ban ga laifinsa ba. Wa zai so a yiwa mahaifiyarsa kishiya. Tsugunnawa na yi na fara gaishe da Hajiya ta ce sam na tashi na zauna a kujera. """Ya aka ji da gajiyar biki"" na ce mata lafiya." """Masha Allahu. Anjima da yamma za ku je can Family House ki gaishe da Inna""" Na ce mata to. "Sai kuma ta sake kallon fiskata ta ce ""idan ba za ki iya fita ba ki faɗa masa a bar gaisuwar sai gobe""" "Na yi saurin cewa "" za mu je yau ɗin""" Ina zaune a ɗakin Hajiya muna hira sama-sama Mardiyyah ta kira wayata wai sun zo suna gate. Ce mata na yi su buga za a barsu su shigo. Rayuwa kenan. Na taso a gidan zaure ga shi yanzu ina gida mai Gate. """Hajiya, ƙannena ne suka zo""" """Bismillah, ki je ku gaisa""" Na mata godiya na miƙe na bar ɗakin na sauko ƙasa. Lokacin dana sauko suna shigowa kenan. Ashe ita da Ummiyo da Walida ne. """Amarya, Amarya""" """Kai bana son iskanci""." """Adda Ziya da muka ce mu ƙannen Amarya ne sai aka buɗe mana gate aka ce mu shigo-mu shigo muma" "'yan gida ne"" Ummiyo ta faɗa tana dariya." Akwatin kayana dana haɗa daga gida Mardiyyah ta kawo mini. Na mata godiya na ce mata ya ta baro su Kaka. Ni gashi ɓacin rai ya sa ko tsohuwata ban kira na ji muryarta ba. Ta ce mini ai Kaka bayan an wuce dani jiya sai da ta sha kuka sosai sai da su Baffa Adamu suka yi ta bata haƙuri. Allah Sarki Kaks ɗina. Idan na koma ɗaki zan kirata na ji muryarta na san hankalinta zai kwanta sosai. Mardiyyah ta ce wai an ce su tambayeni yaushe nake so a kawo mini kayan Gara? Sanin cewa za mu fita da Jalal da yamma kuma ban yiwa Hajiya maganar ba sai na ce a bari sai gobe da yamma zan yiwa Hajiya magana. "Sun jima min. Dan sai da muka ci abincin rana, suka yi sallar Azahar a ɗakin baƙi dake ƙasa kafin suka ce" za su tafi. Na raka su har bakin ƙofa na dawo. Dana shiga ɗaki sai na jawo wayata. Tunda Jalal yace na cire komai a raina na ajiye wayar ma saboda "bana so na sake ganin wani abun takaicin. Tunda yau dai sheɗanun social media ne suka dira akan sunana, daga wannan sai wannan." Missed call ɗin Faty na gani har guda uku da kuma wasu nambobi guda biyu. Goge missed calls ɗin na yi sannan na kira numbar Kaka. Bata ɗauka ba sai a kira na biyu. """Kaka shine kika yi ta kuka ko""" """Ba kuka na yi ba Ziyadatu. Farin ciki nake Allah ya bani aron rai har na ga aurenki. Allah ya miki albarka""" """Amin Kaka. Dan Allah banda kuka. Kuma ki riƙa cin abinci sosai""" """Ya mijin naki?""" """Yana nan lafiya""" Ta ce na gaishe shi. Na ce mata zai ji. Bayan na gama waya da Kaka sai na shiga banɗaki na yi wanka na ɗauro Alwala na gabatar da sallar la'asar. Dana idar na ɗan yi addu'o'i sannan na tashi na naɗe sallayar na shirya na wuce ɗakin Hajiya. Na haɗu da Janan a falon sama ita da wata suna magana babu wanda ya kulani a cikinsu. Dana shiga ɗakin Hajiya sai na tarar itama ta idar da sallan kenan. A kunyace na faɗa mata wai ana so a kawo kayan Gara daga gida. Ta ce babu komai dama akwai sauran gyaran da ba a yi bane a kitchen ɗin gidan da za mu zauna. Amma babu matsala za su iya zuwa goben. Na yi mata godiya. Na zauna a ɗakinta ina jiran Jalal ya dawo mu wuce gaisuwan da za mu je. Can kusan ƙarfe biyar da rabi saura sai ga shi ya shigo. Hajiya ta fara masa masifar ina ya je bai dawo da wuri ba bayan ya san ana jiransa. Haƙuri ya bata ya ce wani abu ne ya riƙe shi. Ya ce yanzu zai shirya mu wuce. Bayan ya bar ɗakin da kamar minti biyu sai Hajiya ta ce in tashi in bishi ko akwai abinda ya ke buƙata. Hajiya ma dai. To me zai buƙata bayan na san wanka zai yi kawai ya sa kaya ya fito. Na dai miƙe na fita. Kar ta ce daga kwana ɗaya na fara mata gardama. Na shigo ɗakin ashe yana wajen closet. Zuwa na yi in tambayeshi ko zai ci abinci in sa a kawo masa kafin mu fita sai na ganshi tsaye ɗaure da towel a ƙugunsa. Da sauri na yi baya """Ina za ki je?. Come back""." Ban kula shi ba na yi hanyar ƙofa. """Where are you running to?""" Ashe biyoni ya yi. """Ni ba guduwa zan yi ba"" na faɗa ina waskewa tareda barin kusa da ƙofar." Ƙarasowa ya yi inda na ke tsaye ya closing gap dake tsakaninmu. """Look at me"" ya commanding ɗina." Ɗagowa na yi ina kallon bare chest ɗinsa ƙirjina yana dukan uku-uku. Lokacin da ya ɗaga hannunsa sai na yi saurin rintse idanuna dan ban shirya ganin sirrinsa dake ɓoye cikin towel ba. """Kin yi kuka bayan na fita ko?""" """Allah ban yi ba"" na faɗa da sauri ina buɗe idanuna." """Kin ci abinci?""" "Na gyaɗa kaina ina faɗin ""tareda ƙannena da suka zo ma muka ci""" """Good. Ki jira na shirya sai mu fita"" ya ɗan shafa kumatuna." """Ko za ki min wankan?"" Na yi saurin girgiza kaina." Wani murmushi ya min sannan ya wuce banɗaki. Sai a lokacin na sa hannu a ƙirjina da ke ta rawan disco tun ɗazu. Zama na yi a bakin gado na jira shi har yai wanka ya shirya ya fito. Tare muka fito muka nufi ɗakin Hajiya ashe bata nan. A ƙasa muka sameta wasu mata sun zo mata gaisuwa. Sallama muka mata muka fita. Family House ɗinsu Jalal tsohon gida ne irin ginin gidan Sarautan gargajiya ɗinnan. Amma kuma ƙato ne kuma akwai ɓangare-ɓangare da yawa. Wajen Kakarsa Hajiya Inna ya fara kaini. Tsohuwar da surutu. Tana ganinmu ta fara cewa wai yanzu kam za ta karɓi gaisuwan Jalalu tunda ya auro mace mai Sallah. Jalal ya haɗe rai. Ina ga baya son Jalalu da take kiransa ne. A wajen Inna ya barni. Dake ni renon Kaka ce tuni na sake jiki da Inna muka ɓalle da hira. Ta dinga bani "labarin ɗanta, wato marigayi Babansu Jalal. Da kuma ƙanin Jalal da ya rasu. Ta ce ai Jamal ya fi Jalal sakewa da mutane. Wai da shi ne da ba zai kawoni ya tafi haka ba. Tsayawa zai yi a sha hira. Na ce Allah Sarki." Wata mata aka haɗani da ita ta kaini sashe biyu a gidan na gaisa da mutanen wajen. Daga nan kuma muka dawo wajen Inna. Jalal bai dawo ba sai bayan Isha. Ni kam har na ci Tuwo a wajen Inna. Da dai na so in yi pulaku amma yadda Inna ta ja ni a jiki sai na ga gara kawai na ci ko kaɗan ne dan tsofi babu abinda suke so irin su ga ka sake kana walwala kusa da su. Ai kuwa ta ji daɗin hakan. Muka buge da taɗin abinci na ce mata Kakata ta jima tana Tuwo a Zaria kafin tsufa da ciwo ya sa ta dena sana'ar. Ta ce mini tana da labarin Altine mai Tuwo. Shekaru kusan arba'in da suka wuce ta kan sa a siyo mata Tuwo a wajen Kaka. Na ce ikon Allah. Ina ga lokacin da Kaka ta yi tashe sosai kenan. Lokacin da Jalal ya zo sai na mata sallama muka tafi bayan ta bani kyautan turmin zani da ruwan ZamZam. Na ji daɗin haɗuwa da tsohuwar. Har da cewa in riƙa zuwa ina dubata fa. Ciwon ƙafa ya hanata yawo shi kuma Jalalu ba ya zuwa gidan sai ya ga dama. Na ce mata zan riƙa zuwa. A hanyar mu ta dawowa Faty ta sake kirana. Wannan karan sai na ɗauka dan in ji wace tsiyar kuma za ta faɗa min. Ina ɗagawa ta fara bani haƙuri wai ta ga videon Alhaji Nafi'u yana trending kuma ita ta riga ta goge post "ɗin da ta yi na yi haƙuri dama so take ta yi celebrating aurena, ba da wata manufa ta yi ba." Ta tambayeni yanzu ya zan yi da batun Alhaji Nafi'u?. Kallon Jalal da ke tuƙi na yi sannan na ce mata """Mijina ya ce kar na damu zai ɗau mataki a kai""." Ƙatuwar ajiyar zuciya ta yi ta ɗan yi shiru kafin ta ce mini wai gaskiya abinda Jalal ya yi ya burgeta. Har da "mayar da maganar wasa wai ""su Ziyada manya, jiya-jiya fa aka yi aurenki har kin fara baza capacity. Wai Mijina zai ɗau mataki. Kina wuta fa Bestie, Allah ya barku tare daga nan har tsayuwar ƙiyama""" "Ko addu'ar ya kai zuciyarta ko bai kai ba, ni dai na amsa mata da Amin na kashe wayata." Na ji daɗi da Jalal bai tambayeni da wa nake magana ba. Dan idan ya ji maganar Alhaji Nafi'u muka yi ransa zai iya ɓaci. Da safe da yake mini kashedi akan na cire maganar a raina ba da wasa yake ba. "Na ji wani chills a jikina dana tuno furucinsa na safe ""I'm the only MAN you should think about...""." * Da dare da za mu kwanta na so yin gardama lokacin da ya yi ƙoƙarin cuddling ɗina. Shine ya tsokaleni wai jiya da ya rungumeni da safe kasa tashi na yi saboda na ji daɗin jikinsa. Ku ji min fa!. Lokacin da ya manna min soft kiss a wuyana ai sai na tafi factory reset. Mantawa na yi da duk abubuwan "da suka faru. Zagina da ake yi a social media da ma videon Alhaji Nafi'u yana masifa a gidanmu da aka fitar. Mantawa na yi da komai, sai mutum ɗaya. Mutumin da cikin kwana biyu kacal da muka yi tare, har na amince a raina ina son zama na har abada da shi..." CHAPTER FORTY FOUR CASSANDRA Baturiyar matar da ke zaune a wani ƙayataccen office cikin wani tsantsararren building dake tsakiyar "birnin London ba za ta gaza shekara 37 zuwa 38 ba. Cikin shekaru takwas da buɗe fashion brand ɗinta mai suna CASSYMARÌA ta samu lambar yabo a matsayinta na ɗaya daga cikin Luxury fashion brand masu tashe da manyan Celebrities suke sakawa. Lokacin da kamfanin ta ya designing kayan da wata fitacciyar 'yar film ɗin Hollywood ta saka a taron MET GALA da aka yi shekara huɗu da suka wuce, sai darajar kamfanin nata ya ƙaru. Dan kuwa tun daga lokacin zuwa yanzu revenue ɗin kamfanin ya ƙaru sosai har ya ninka target ɗin da suke tunanin za su cimma nan da shekara goma. Sai ga shi sun cimma target ɗin nasu a shekara huɗu." "CEO na kamfanin CASSYMARÌA ita ce Cassandra Maria Morgan. Cikakken sunanta na haihuwa kenan," amma tun daga lokacin da ta auri Jalal Kabeer Maiyaƙi sai sunanta ya koma Cassandra Maria Morgan Maiyaƙi. "Zaune Cassy take a ofishinta, hankalinta kwacokam yana ga wani hoto da aka turo mata." A ranan da ta ga DM daga wani account da ke ɗauke da family name irin na mijinta ba ta buɗe DM ɗin "ba. Daga baya sai ga email nan an sake turo mata da wani bayani da ya ruɗar da ita lokaci guda. A take ta kira ƙanwar mijinta Janan Maiyaƙi dan ta ji gaskiyar abinda aka turo mata, amma sai Janan ɗin ta ƙaryata hakan. Ta kira Jalal amma sai ta kasa tambayarsa gameda abinda aka turo mata saboda abin ma bai kama hankali ba. Ta ya ma za a ce wai Jalal ya yi wani auren bayan basu rabu ba." Bibiyar DM ɗin da aka mata ta yi ta kalli hotunan da aka turo mata da dogon bayani wai mijinta Jalal ya auri wata baƙar fata 'yar Nigeria. Hotunan da aka turo na Jalal ne ya sha manyan kaya yana cikin wasu 'yan'uwansa da suma suka yi shiga ta alfarma. Sai kuma hoton wata budurwa da ake iƙirarin ita ce matar da Mijinta ya aura. Hotunan da aka turo mata ba su nuna komai ba domin hoton Jalal cikin 'yan'uwansa ya sha native attire ba shi ke nuni da cewa aure ya yi ba. And hoton yarinyar da aka tura mata bai yi kama da irin macen da zata ja hankalin Jalal bama balle har ya ce zai aureta. Kwana biyu ta share abin a ranta amma sai zuciyarta ya riƙa kawo mata tambayar idan kuma gaskiya ne Jalal ya auri wata fa?. "Ta san uwar mijinta bata sonta, amma kuma ai matar ta san illar Jalal ya yi aure ba tareda sun rabu ba." It's bigamy. "A zamanta da Jalal ta ɗan yi bincike akan musulunci, ta san musulmai suna da damar auren mace sama" da ɗaya amma kuma auren kotu suka yi. Kotu kuma abinda ta sani shine Cassandra Maria Morgan ita kaɗai ce legal wife ɗin Jalal Kabeer Maiyaƙi. Wannan ya sa bata taɓa damuwa da cewa watarana Jalal zai ce zai yi aure ba. It's not possible nema. They are still legally married duk da basa zama tare. Saboda ta samu nitsuwa har ɗanta Junior ta tambaya da suka yi waya aka ko ubansa ya yi aure amma yaron ya nuna mata bai san maganar ba. Wannan ya sake sawa Cassandra ruɗu. Idan ɗanta ya ce Jalal bai yi aure ba. Sannan Janan ta tabbatar mata maganar da aka turo ƙarya ne. To wacece wannan S. Maiyaƙi da ta turo mata hotuna da bayanan ƙarya wai mijinta Jalal ya auri wata a Nigeria?. Blocking ɗin yarinyar ta yi. Amma yanzu da take sake kallon hoton Jalal sai ta ji dole ne ta samu lokaci ta je Nigeria ta gani da idanunta cewa Jalal bai ci amanarta ba. Hakan zai fi mata kwanciyar hankali. Daga haka ta ajiye wayarta ta mayar da hankali kan wasu files dake gabanta tana dubawa... ZEEY Yau Alhamis muka koma sabon gida. Gidan Jalal. Gidana ba gidan Hajiya Layla ba. "Gidan ba ƙaramin kyau yake da shi ba. Hawa biyu ne da ɗakuna shida. A ƙasan akwai falo, dining area," "kitchen da store sai guest room ɗaya da spare room ɗaya. Akwai kuma guest bathroom separate shima. A saman kuma akwai ƙaramin falo kaman lounge haka, sai Master bedroom na Jalal dake haɗe da banɗaki da kuma ƙofar da zai fitar da ke balcony. Balcony ɗinma akwai kujeru biyu na zaman shaƙatawa ana duba farfajiyan gidan daga wajen. Wajen zai yi kyau idan aka saka plants. Nawa ɗakin bai kai master bedroom girma ba amma shima babba ne kuma akwai walk in closet da banɗaki. An jera min kayana a closet sauran da ba a ɗinka ba aka barsu cikin akwatunan Lefe na." Sai ɗakuna biyu wanda nake tunanin na yara ne amma dai babu wani decoration da aka masa akwai dai gado a ɗakin. Abinda ya fi tafiya dani a gidan shine mini-kitchen dake sama. Like irin wajen da za a iya warming abinci ko a haɗa tea ko a dafa fast abu haka a wajen ba sai an je babban kitchen dake ƙasa ba. "Wajen ya burgeni. Abunka da Chef, Mentally sai na fara calculating yadda zan gyara wajen. Idan na yi" girki a ƙasa sai na kai mini-kitchen ɗin na ajiye zuwa lokacin da za a ci sai na fito da shi. Idan ma yunwar dare ya taso mutum za a iya soya ƙwai a haɗa shayi a wajen. Lissafi dai iri-iri na dinga yi na yadda zan gyara space ɗin. Bayan mun gama duba duka gidan da su Hajiya da suka rakoni sai aka zauna aka yi addu'ar Allah ya kaɗe fitinar dake gidan ya kuma bamu zaman lafiya a gidan. Na yiwa su Hajiya godiya na raka su har bakin gate kafin na koma. Gidana da Gidan Hajiya katanga ne ya rabamu. Na ji Hajiyar ma na cewa za a fasa ƙofa ta baya da zai connecting ɗinmu ta yadda zan iya zuwa cikin gidan Hajiya ba tareda na bi ta gate ba. Dana dawo falona sai na ji gidan ya min faɗi. Ni kaɗai a wannan babban gidan sai kuma Maigadi dake bakin gate. Ance akwai Boys quarter a baya da Maigadi zai ajiye iyalinsa amma kuma babu kowa a wajen for now. Maigadin ma Hajiya ta ce ba shi da mata. Ɗayan duplex ɗin kuma babu kowa. A yadda na ji labari dama gidan an gina ne saboda Jalal da ƙaninsa "Jamal su zauna a waje ɗaya, to ƙaddara bai sa Jamal ɗin ya yi Aure bama balle ya zauna a gidan." Babu daɗi a bar gidan empty. Ko 'yan haya aka saka a ciki zan samu maƙota kusa da ni. A cikin kwanakin da muka yi ni da Jalal mun fara shaƙuwa. Duk dare za mu kwanta manne da juna. Wani lokaci har ya kissing wuyana ko goshina. Babban abinda ya sa na ƙara jin son Jalal a raina shine maganar ƙarar Alhaji Nafi'u da ya yi. Bai min maganar ba dan tunda ya ce faɗan nasa ne yake ta faɗi-tashi akai shi kaɗai. Baffa Adamu ne ya kirani ya sanar dani wai an kama Alhaji Nafi'u kuma lallai Jalal ya dage sai ya yi shari'a da shi. Ashe da aka bincika shi ɗinne ya je ya posting video ɗin dai-dai wajen da yake iƙirarin ba zai yarda ba an cuce shi ya sa a fake account ɗinsa na Facebook. Daga nan ne video ya kai har shafin bloggers. Wato bayan an rufe magana har Baffa Adamu ya saka shi rubuta undertaken da kansa ya sa hannu ashe bai haƙura ba. Shi kawai so yake ya ga ya fentani da baƙin fenti cewa na ci kuɗinsa na je na auri wanda ya fishi kuɗi. "Baffa Adamu ya ce mini Alhaji Nafi'un ya turo wani dattijo har Katsina ya same shi wai a janye ƙara," amma Jalal ya ce ba zai haƙura ba. Ya ce mini shi ba zai tursasani na yafewa Alhaji Nafi'u ba. Amma kuma tunda ya yi nadama na yi haƙuri a wuce wajen na fuskanci aurena na manta da komai. Na yi masa godiya na ce zan roƙi Jalal a janye ƙaran. A ranan Talata da dare da muka zo kwanciya dana kawo maganar wa Jalal sai ce mini ya yi kada na sake kawo masa maganar. Ashe ma har da wata blogger aka haɗa da shari'ar amma ita ta bada haƙuri a pages ɗinta publicly na yaɗa videos ɗina da ta yi. Duk da videon daga Alhaji Nafi'u ya fito itama tana da hannu wajen yaɗawa. Ni duk ban san an yi haka ba. Sai yau da safe kafin mu taho sabon gida na duba shafin Instagram ɗina. Dan tun ranan da abin ya faru ban sake shiga Instagram ba. Ashe dai Alhaji Nafi'u matsoracin banza ne. Duk cika bakinsa sai gashi cikin kwana uku kaɗai da fara case da shi har ya fara neman sulhu. Wannan abin da Jalal ya min ya sa ni jin a raina zan zauna da Jalal koda baya sona. Balle ma idan wannan abin da yake min ba so bane to tabbas akwai ƙanshin soyayya a ciki. Kuma ni Ziyada Sadiq Haruna sai na koyawa Jalal Maiyaƙi sona... Jalal baya nan ya tafi office. Bayan na raka su Hajiya sai na haura sama dan na ƙarisa arranging ɗakina. Yanzu da muka dawo wannan gidan ban san ya baccinmu zai kasance ba. Ni zan je ɗakinsa ko shi zai zo nawa?. Ko kuma dai shikenan ba zamu sake kwana a ɗaki ɗaya ba?. Idan muka koma kwana daban na san zan missing Jalal dan har na fara sabawa da kwantawa a jikinsa ina jin hardness ɗinsa yana gogan jikina. Bayan na gama gyaran ɗaki which gaskiya ba wani aiki sosai bane dan waɗanda Hajiya ta sa suka zo suka yi jere sun yi aiki mai kyau. Kitchen na dawo ko zan iya dafa abinci kafin Jalal ya dawo sai na ga ai girki ba zai yiwu a Kitchen ɗin ba. Beside ma babu komai a fridge ɗin na kayan miya. Akwai dai kayan abinci a store har ma da kayan Gara na da aka min amma babu kayan miyan da zan yi abinci da shi. Ina ga sun bar fridge ɗin empty ne akan idan na zo sai na stocking ɗinsa da abubuwan da nake buƙata. Yawanci kayan amfanin kitchen ɗinma cikin kwali suke ba a buɗe su ba. Haka na naɗe hannun doguwar rigana na fara gyara kitchen ɗin. Ina so na saita komai ya zamo dai daga gobe idan na sa aka kawo kayan miya zan iya fara girki a kitchen ɗina. Ban ankara ba ina arranging kayan abinci a cikin manyan containers ashe time ya tafi. Abunka da sabon gida Maigadi na buɗe gate na bar abinda na ke na zo na leƙa. Ganin motar Jalal ne sai na koma kitchen. Sai kuma na fara kallon kayan jikina dana wuni da su tun da rana inata aiki. Duk ga shi na yi gumi da ƙura dana ɗauka daga kwalayen da na yita buɗewa. Yanzu a haka zai ganni? Ban gama tunanin abinda zan yi ba na ji ƙaran shigowarsa gidan. To ko na bari idan ya haura sama sai na yi siɗak-siɗak na je ɗakina na yi wanka na chanja kaya ne? Ina cikin lissafin ya zan yi kada Jalal ya ganni cikin datti na ji an yi gyaran murya a bayana. A tsorace na juya da sauri dan ban san har ya shigo kitchen ɗin ba. Na sha sama zai hau ya je ɗakinsa. """Sannu da aiki, Amarya""" """Sannu da dawowa. Ya aiki?"" na faɗa ina avoiding idanunsa. Yanzu sai ya ce tun safe ban gama aiki na" kimtsa kaina ba. An ce wai a satin Amarci kada Amarya ta bari Ango ya ganta cikin datti. To gani a gaban Ango jikina babu kanta. "Ganin yana mini wani kallo sai na fara magana ""Kitchen ɗin ba a gama arranging ɗinsa ba shine na ce" "barin rage aiki. Na so na yi girki ma amma babu komai a fridge. Amma zan haɗa mana shayi sai mu ci da chinchin ɗin kayan Gara""" Still dai kallona ya ke yi. Da alama dai kallon dattin da na yi yake. """Ahm! Yanzu zan kammala na je na yi wanka. Dama sabo...""" """Shhh!"" ya matso kusa da ni." """Kin cika surutu, Zeeyadah"" ya haɗe space ɗin dake tsakaninmu." "Ganin yana shirin matseni sai na fara magana. ""Na cika surutun. Kaima sai ka yita yiwa mutum kallo...""" Ya rufe min baki da nasa. """Ni ka barni, warin gumi nake"" na faɗa ina turashi. Amma ilahirin jikina yana craving jikinsa. I mean" bakinsa. Ƙanshinsa da wani calm dake tattare da shi ne ya kashe min jiki. Ga softness na lips ɗinsa da sai yanzu daya ɗaura su akan nawa na san hakan. Fiskata ya tallafo da hannunsa ya sa babbar yatsarsa ya fara grazing saman lips ɗina. Ƙwayar idanunsa nake kallo bugun ƙirjina na ƙaruwa. I'm craving him. Gaskiyar kenan. Wai me Jalal ya min ne daga kiss ɗaya ina shirin narke masa. Rankwafowa ya yi ya sake claiming lips ɗina. Wannan karan ban yi gigin tura shi ba ko kuma na ce ya barni. At this point ma idan ya barni ni zan cutu saboda I want the kiss more than I can admit. "Ban taɓa hasaso wannan lokacin ba. No. Na taɓa imagining Jalal yana min irin wannan abin, amma ban" "taɓa hasasowa hakan zai iya faruwa nan kusa ba. Ko sati fa ba mu cika da aure ba, amma sai gashi yana kissing ɗina ba tareda ya duba ƙura da dattin da jikina ya yi ba." """Na jima ina son tasting lips ɗinki, Zeeyadah"" ya faɗa a saman lips ɗina muryarsa sarƙe da wani nishi." Abinda ya faɗa sai ya fara ringing a ƙwaƙwalwata. Ya jima yana son kissing ɗina?. Tun yaushe?. Tun kafin mu yi aure ko kuma daga lokacin da muka yi aure muka fara sharing gado ɗaya?. Kissing ɗina ya sake yi. """What did you do to me?"" Ya tambaya yana kallon ƙwayar idanuna." Me na masa? ko me ya min?. A yadda zuciyata ke bugawa dominsa babu abinda ba zan iya yi dan mu kasance tare ba. Not just a kiss. Idan ya ce na tuɓe na bashi kaina a wannan kitchen ɗin ba zan musa ba. That's how bad nake jin "buƙatarsa, na ke jin sonsa." Kai! Wasa nake ba zan so mu yi wani abu a nan ba. Zan so ya kasance a ɗaya daga cikin ɗakunan sama ko "na shi, ko nawa." Amma ban faɗa masa haka ba. Sai kawai na saukar da idanuna ina mamakin wannan sabon al'amari da ya shiga tsakaninmu wanda ya saka wani motsi da damshi a tsakiyar cinyoyina. Ganin ban bashi amsa ba sai ya sake haɗe bakinmu. Wannan karan da wani yunwar da nake tunanin zamu iya yin more than a kiss a kitchen ɗin. Ban san na iya kiss ba sai yanzu. Na sa hannuna a bayan kansa na dinga yi masa irin abinda yake min. Ƙaran waya ne ya fargar da mu. "Ya breaking kiss ɗin ya zaro waya daga aljihunsa ba tareda ya sakeni ba ya ce ""Hello""" A hankali kuma sai ya sakeni ya fara ja da baya. Turancin da na ji yana yi ya sa na fahimci kamar Baturiyar matarsa ce ta kira shi. Barin kitchen ɗin da ya yi da sauri ya gaskatar da hasashena. Na yi shiru ni kaɗai a kichen ɗin ina kokonton kiss ɗin da ya faru da gaske ne ko dai imagination ɗina ne?. Amma dana ɗan lashe lip ɗina na ƙasa sai na sake jin taste ɗin bakin Jalal a wajen. Wannan yana nufin duk abinda ya faru gaskiya ne. Ban yi gigin barin kitchen ɗin ba balle na jiyo hirarsa da MATARSA. Na cigaba da ƙarisa aikin da nake yi. In between ina jin taste ɗin Jalal da ya ƙi barin bakina. Sai dana gama gyara komai kafin na rufo ƙofar kitchen ɗin na wuce ɗakina. CHAPTER FORTY FIVE ZEEY "Yau dai baccin sabon gida zan yi. Lokacin da na gama wanka, na yi sallar Magariba da Isha har ƙarfe" goma ta yi. Har lokacin ban sake jin ɗuriyar Jalal ba. Kamar ma fita ya yi daga gidan. Ba zan iya bacci babu komai a cikina ba dan haka sai na sauko ƙasa dan in haɗa tea ko da chin chin ne sai na ci da ɗan soyayyen nama haka. Da na shiga kitchen ɗin sai na ga ba zan iya tsayawa haɗa tea ba sai kawai na ɗauki Maltina guda ɗaya cikin wanda na arranging ɗazu a fridge. Ina fitowa falo na ji ƙaran shigowar motar Jalal. Maimakon na koma ɗaki sai na samu kujera na zauna a falon. So nake na ga ko zai kulani. Daga kawai matarsa ta kirashi sai ya yi ghosting ɗina ya yi tafiyarsa. Kunna smart TV ɗin falon na yi na fara kallo ina cin chin-chin. Gaskiya sun yi ƙoƙari dan chinchin ɗin bai sha mai ba. A gajiye ya shigo falon ɗauke da ledar take-out dai dai ina kora Maltina. "Ganin abinda na ke ci sai ya ce ""Sorry, Sunshine. Na tsaya wajen Hajiya ne shi yasa na jima""" "Ɗaga masa plate ɗin chinchin na yi sai ya ce ""Wannan ba abinci bane. Ki tashi ki ci wannan""." Karɓan ledar abincin na yi na ga jollof and fried rice ne da chicken. Take away ɗaya ne a ciki. """Ba za ka ci bane?"" Na tambaye shi" """Bana cin abinci mai nauyi idan dare ya yi sosai""" """Shikenan sai ba za ka ci abinci ba"" na faɗa ina tura baki" """I'm 40, Sunshine. Dole na kula da lafiyata""" """Lafiya ai shine mutum ya ci abinci ya samu ƙarfi"" na faɗa ina fara cin jollof ɗin. Tsabar ganda ko plate" ban ɗauko a kitchen ba. A robar na ke ci da ƙaramin cokalin da suka saka a ciki. """An ce Healthy lifestyle yana saka namiji ya yi lasting. Ba kya so na miki lasting ne?"" Ya ɗaga mini gira." Innalillahi. Lasting a me?. Ni ban ji wannan ba. Share shi na yi na matse kaman ban san me yake nufi ba. Idan na bashi amsa cigaba zai yi da ɓare-ɓare. "Miƙewa ya yi ya lakuci hancina ya ce ""Matsoraciya. Barin je na yi wanka. Idan kin gama ina son ganinki""" Dididish! Yana son ganina?. Me zai min?. Me zan masa?. Kazar da nake taunawa na haɗiye da ƙyar. Da alama fa yau zan shiga hannun maza. Ya Allah!. Ban san me yasa tsoro ya shigeni ba. An ce first time da zafi. Ni kuma har yanzu ina tsoron allura ma balle babbar sanda ta shigeni. Ban ma gama cinye abincin ba na ji ya fita a kaina. Tattarawa na yi na kai kitchen. Ƙirjina na dukan tara- tara na wuce ɗakin Jalal. Riga da wandon pyjamas dogo ne a jikina. Thank God dana duba cikin closet ashe akwai kayan bacci masu hankali saɓanin wanda aka sako min a akwati sadda muke kwana a gidan Hajiya. Lokacin dana shiga ɗakin bai fito a banɗaki ba. Zama na yi a kujera kar ya fito ya ganni a bakin gado. Irin ga nama ta kawo kanta bakin Kura ɗinnan. Ina zaune sai na fara tunanin ko na koma ɗakina na chanja kayan jikina ne?. Ko na je na sake wanka ne?. Ina ta dibi-dibin ko in tashi ko kar na tashi har Jalal ya fito. Daga shi sai towel dan haka na yi saurin kawar "da kaina na fara danna waya. Ina son sake kallonsa a inda yake tsaye gaban mirror yana shafa mai. Na dai resisting hakan kar ya kamani, na cigaba da scrolling social media." """Zo ki shafa min mai a bayana"" sai dana kusa ƙwarewa dan mamakin kalamansa." Daga shi sai towel fa. """Taso mana, Zeeyadah"" ya juyo yana miƙo min cream ɗin dake hannunsa." Rarraba idanu na fara ina tunanin kar na je taɓa mishi baya ya sake towel ɗin da ya ɗaura. Ga shi ya yiwa towel ɗin ma ɗaurin sako-sako. Ni gaskiya ban shirya ganin komai ba. I'm innocent. """Please"" ya faɗa da sigar magiya." Bani da choice haka na miƙe na bar wayata akan kujera na taho wajen da yake tsaye. Karɓan cream ɗin na yi a hannunsa sai na ɗaga kaina ina kallon faffaɗan bayansa. Har yanzu akwai sauran ruwa a bayansa da bai gama bushewa ba. """Ai...kkk kamin tsayi"" na faɗa da ƙyar. Tunanin kiss ɗin da muka yi ɗazu ne ya dawo mini. Ji nake kamar" "na nitse a bayansa, na yi ta absorbing ƙanshinsa." Tun farkon ganin Jalal ƙanshinsa ne ya fara burgeni. Duk da haɗuwarmu na farko bai zo ta daɗi ba amma har na je gida daɗin ƙanshinsa bai barni ba. Har yanzu kuwa ina da handkerchief ɗinsa guda biyu dana kasa mayar masa. Suna cikin akwatin kayana dana haɗo daga gida. Lakutar hancina ya yi sannan ya zauna a bakin gado sai nima na zauna a bayansa. Ɗan taɓani da ya yi har ya igniting wani wuta a jikina. I think...at this point I AM READY. Na shirya ma buƙatarsa. Ban taɓa sanin ina buƙatar samun nitsuwar namiji a rayuwata ba sai yanzu da nake jin gaba ɗaya gaɓɓan "jikina suna yearning ma jikin Jalal, dukkansa." I want him. Lakuto cream ɗin na yi ɗan kaɗan na fara mulmulawa a tafin hannuna. Ni ban san ana shafa mai a baya ba sai yanzu. Iya rayuwata ban taɓa shafa mai a bayana ba. Maybe lokacin da nake ƙarama Umma tana shafa mini. Amma da girmana dai ban taɓa ko kwatanta shafa mai a bayana ba. A tunanina baya ba ya buƙatar a shafa masa komai tunda ba ganinsa ake ba. Da ka saka riga shikenan. In dai ba bayan mutum ke zafi ba ya ce a shafa masa Robb ko Aboniki saboda ya samu relief me zai sa a shafa mai a baya? Kuma da dare fa. To yau dai ga shi Aure ya sa na samu wani sabon ilimi. "To wai, da ɗin ta ya yake shafawa ne? ko haka yake zura hannu a bayan nasa iya inda hannun ya kai, iya" nan za a shafa?. To wannan ma ya shiga list ɗin amfanin Miji. Kun ga nima watarana sai na ce ya shafa min mai a bayana na ji yadda ake ji. "A hankali na fara shafa masa saman bayansa ina working hannuna zuwa tsakiyar bayansa, all the while" "ina jin tsoro da kuma shauƙinsa. Da ba dan tsoron da nake ji ba, da kwantawa kawai zan yi a bayansa mu jima a haka. Ko kuma na kissing wuyansa da wajen kunnensa inda na ke ganin wani tsillin ruwa yana daf da ɗiga wuyansa." Ziyada focus. Na yi saurin ƙwaɓar kaina tun kafin ya gane irin dirty tunanin da nake akansa. Sake lakato cream ɗin na yi dan ƙasan bayansa bai samu ba. A hankali na fara shafa ƙasan ina ƙoƙarin avoiding kaiwa ƙugunsa dai-dai ɗaurin towel ɗinsa. """A bit down, Sunshine"" ya faɗa kamar ya san da gangan na ke avoiding wajen." Ina shirin janye hannuna daga wajen bayan na kai ƙarshen bayansa sai ya sa hannunsa akan nawa ya sake yin ƙasa da shi sai da yatsata ta tsakiya ta ɗan shiga matse-matsin mazaunansa. """Ki cika ladarki"". Kasa magana na yi saboda gaba ɗaya na birkice. Wannan shine as far as taɓa jikinsa da" na yi tun da muka yi aure. Lokacin da ya miƙe daga gadon rintse idanuna na yi dan a tunanina kwance towel ɗin zai yi. Sai da na ji iskar tafiyarsa sannan na buɗe idanuna. Lokacin da ya fito daga closet har ya saka kayan bacci. Wani short ne da matching comfy night tshirt ya "saka kalar grey, ko ash ne ma. Kai! kalar tokar da ta yi baƙi dai." """Zzzan wuce ɗakina"" na faɗa da kyar tunda na gama aikin da ya sakani." """Sunshine, a nan za ki riƙa kwana"" ya faɗa babu ƙofar yin musu." Ganin shima shirin bacci yake sai na ce barin shiga banɗaki. Mamaki ya kamani ganin yauƙi a ƙasana. Na shiga uku! Ba dai ina cikin jarababbun mata ba. Daga shafa masa baya sai gashi na jiƙe. "An ce ba ka sanin ƙarfin sha'awarka har sai ka gwada. To, Allah kada yasa na kasance cikin jarabbabun" Mata. Bayan na tsaftace jikina sai na dawo na kwanta ɗan nesa da shi. Tab ɗinsa yake dannawa a lokacin. Kwanciyata na yi ina jin zuciyata na pounding kamar zai fasa ƙirjina ya fito. Ban san fate ɗina ba a daren nan. Koma yanene dai a wannan dare na shirya sallamawa Jay zuciyata da gangar jikina. "Koda ba zai karɓi zuciyata ba, ni dai na riga na sallama masa ita. He owns My Heart. Babu kowa a zuciyar" sai shi kaɗai. Ina cikin wannan tunanin na ji shi a bayana. Ya saka kanshi a wuyana. Numfashinsa na sauka a wajen na ji wani tsut jikina ya amsa. """I want to kiss you again, Sunshine"" ya faɗa yana juyar da fiskata." Saman lips ɗinsa na sauka akan nawa na amshe nashi. I want to kiss him too. """I'll make you Happy this night, Sunshine"" ya faɗa bayan ya ɓalle button ɗin rigar baccina guda ɗaya." "Sake kissing ɗina ya yi gently sannan ya ce ""tafiyar gaggawa ta kamani zuwa Lagos gobe""." Lokacin da ya gama ɓalle buttons ɗin rigana sai ya ƙurawa boobs ɗina idanu. Shegu nipples ɗina har sun wani mimmiƙe kamar dama jiran Jalal ɗin suke. Hannunsa ɗaya ya sa ya fara shafa ƙasan wajen kafin ya kai yatsarsa kansu yana ɗan lailayawa. Wani daɗi ne ya ziyarceni da ya fara hakan. Ashe ba nan ne ƙololuwar daɗin ba sai da ya sa bakinsa a wajen ya fara sha na gane hakan. Lokacin da ya ɗago kansa yana kallona sai na ji kunyar haɗa ido da shi. Na rufe idanuna ina jin nauyin abunda muke. Wutar ɗakin a kashe yake sai ɗan dim light da ke kunne. """Idan na dawo daga Lagos, I want to have you, Zeeyadah...ALL of YOU""." Wani yawu na haɗiya ina jin ma'anar maganar na sauka mini. Ga shi gobe zai tafi Lagos ya barni ni kaɗai a ƙaton gida da kewarsa. "Sake kafa kansa ya yi a wajen, ya saka hannunsa ɗaya cikin wandon pyjamas ɗina. Sai dana kusa shiɗewa" "da hannunsa ya gogi clit ɗina. Thank God dama bana barin gashi a wajen. Shaving nake yi, amma ana saura kwana biyu aurenmu na siyo Veet na kwashe komai. Dake na ɗan kwana biyu da yi ya ɗan fara tohowa kaɗan. Which makes me ticklish lokacin da hannunsa ya fara shafa saman wajen." """Zan dawo Wednesday da dare, ko Thursday Morning""" "Ya ɗago kansa ya kissing goshina, then saman hancina." "Sai ya sake cewa ""Until then, think of me every night, Sunshine""" """And imagine all the pleasure I'll make you feel idan na dawo"" ya haɗe bakinmu." Har ya zare min komai ban musa masa ba. For the first time sai ga shi wani ya ga sirrina. No. For the first time Mijina ya ga sirrina. Kasa kallonsa na yi a haka. It feels strange kamar bai dace ya ganni a haka ba. At the same time kuma it "feels beautiful sanin cewa a ƙarƙashin inuwar Aure muke. Duk da kunyarsa da nake ji, hakan bai hanani jin tsananin buƙatarsa ba." Ya fara yi min wasu abubuwan da a da ban san suna iya susutar da lissafin mace ba sai yanzu. Yatsarsa ya ɗan saka kaɗan ya fara fingering ɗina amma ko dan ina tsoron shigar wani abu wajen ne sai na fara jin zafi maimakon daɗi. Can ya lura da reaction ɗin fiskata. Sadda yake goga saman clit ɗina fiskata bai ɓoye jin daɗin hakan da nake ba. Yanzu kuma fiskata neutral ne. Wannan ya sa shi yin ƙasa da kansa wajen. """No"" na riƙe kansa lokacin dana farga da abin da yake shirin yi." """NO"" na sake faɗa da ƙarfi." """Relax, you'll like it. I promise""" Girgiza kaina na fara yi saboda it feels weird and wrong. Bai saurareni ba. Ya saukar da kansa a wajen ya fara wasa da clit ɗina. It feels WRONG. Ta ya zai sa kansa a wajen. To amma ban gama auna dacewar hakan ko rashinsa ba sai na ji ina ƙoƙarin fasa ihu saboda daɗin da ya ziyarceni. Ta ya wasan da bakinsa ke mini a clit ɗina zai sakani zaucewa cikin ƙanƙanin lokaci haka?. Ina so na hana shi wasan da yake min a wajen. But at the same time kuma ina jin daɗin hakan. Ji nake kamar a wata duniyar nake. Kamar a sabuwar duniyar tamu babu kowa. Daga ni sai shi. Bai barni ba sai dana fitar da wani ruwa a dai-dai lokacin da ƙafana ya fara shaking tsabar ɗimaucewar dana yi. Ƙanƙameni ya yi bayan haka. Wannan daren nawa ne. Shi babu abinda na masa sai kiss. Infact rigarsa kawai ya cire. Wannan Mijin Baturiyar ya iya sarrafa Mace. A take kuma sai na fara jin wani kishinsa da haushinsa. Kenan haka yake kafawa Baturiyar matarsa kai. Wayyo! Take it easy Ziyada. Wannan bai shafeki ba. Duk abinda ya yi da Baturiyarsa babu ruwanki a ciki. Na kwaɓi kaina. A Yanzu da muke tare shi nawa ne. Ni kaɗai. Ranan Laraba ko Alhamis idan ya dawo zan masa shiri na musamman. Zan bashi nitsuwar da bai taɓa samu a wajen wata Baturiya Cassandra ba. Na kwanta a jikinsa cike da kunyarsa da kuma wani sanyin daɗi da ya fara shigata. Ɗaukan remote ɗin AC ya yi ya rage saboda ya lura sanyi nake ji. Abinda Jalal ya min ya sauke min duk wani gajiya dake tattare da ni. Na ji wani relief ya sauka min. Na rufe idanuna ina shaƙar ƙanshin mutumin dana ke matuƙar SO. CHAPTER FORTY SIX ZEEY Jummu'ar da za ta yi kyau daga Laraba ake ganeta. Akwai alamun aurena da Jalal zai zame mini Alkhairi. "Mutumin da ya daraja ni, yake faɗa da wani banza da ya yi ƙoƙarin ɓata mini suna." Mutumin da ya min abinda ban taɓa tunanin za a min na ji daɗi ba. Mutumin da nake fata a ce kullum na kasance tare da shi. Wannan mutumi shine silar farin cikina. Shine silar samun nitsuwata jiya da dare. A yanzu duk da Jalal "bai furta yana sona ba, ni Ziyada na fahimci hakan." Da Asuba tuni na fice daga ɗakin Jalal na koma ɗakina bayan na ji shigarsa banɗaki. Bayan abubuwan da ya min jiya ba zan iya haɗa ido da shi ba. Balle da wani idon zan fara wankan tsarki a banɗakinsa. Ina shiga ɗakina na saka key. Bayan na yi wanka na fito sai na fara neman hand dryer a ɓangaren kayan kwalliyana. Kaman jiya na gani da nake gyara ɗakin. Ina gani na ɗauko na jona na fara busar da gashina. Dama haka matan Aure ke fama. Kullum kana cikin zuba ruwa a kai. Da na yi sallar Asuba sai na zauna ina Azkar. Can wajen 6 sai aka fara ƙwanƙwasa ƙofata. Na miƙe na ɗan kalli fiskata a mirror kafin na je na buɗe masa. """Shine kika gudu ko"" ya faɗa yana lakutar hancina. Na sunkuyar da kaina ina murmushi." """Amarya zan wuce""" Na ɗago na kalleshi. Ya shirya cikin ƙanan kaya da wani baƙin blazer a sama. He looks so Handsome. """Ba za ka tsaya ka karya ba?. Jiya ma baka ci abincin dare ba fa""" """Ban cika son karyawa da sassafe ba. Zan yi breakfast a Abuja kafin mu wuce""." Na ɗan yi shiru. Still dai ban ji daɗi ba. Ko da yake ko nima in ba yunwar dare ne ya tasheni ba bana iya karyawan ƙarfe shida gaskiya. Karɓan jakarsa na yi na bi bayansa muka sauko ƙasa. Direbansa zai wuce da shi Abuja daga nan zai hau jirgi ya tafi Lagos. A bakin ƙofa ya haɗeni da jikinsa bayan na miƙa masa jakarsa. Sai na ji kamar in masa kuka kar ya tafi. Ya kissing ɗina briefly kafin ya juya ya fita. Daga ƙofa na tsaya ina kallonsa har ya je ya shiga mota Direba ya ja motar suka fita. Sai da motar ta fita daga gidan sannan na rufo ƙofar falo na zo na zauna a kujera na naɗe ƙafafuna na rungume jikina. Har na fara missing ɗinsa. Na tuno darenmu na jiya. Yadda ya bani kulawarsa. I am missing him already. A wajen na ƙarisa Azkar ɗina. Sai daga baya na koma sama na cire hijab na kwanta. Ban tashi da wuri ba sai wajajen goma saura ma. Kitchen na wuce dan na nemi abinda zan ci. Tea na haɗa na dawo falo na fara sha da chinchin. Ina cikin ci sai na ji ƙaran doorbell. Na je na buɗe ƙofar ina tunanin wa zai zo mini da safe haka. Hassana ce. Na buɗe mata ta shigo. """Amaryanmu. Barka da safiya""" Muka gaisa sosai na tambayeta Hajiya ta ce lafiyarta ƙalau. Tace mun wai Yallaɓai ne ya ce na yi mata list ɗin abubuwan da nake so za a kawo anjima. Na je na ɗauko biro da joter a sama na dawo na fara rubuta mata abubuwan da nake buƙata. Ta karɓi list ɗin ta tafi. Bayan fitarta sai na ga text ɗin Jalal wai yanzu jirginsu zai tashi. Na masa reply da addu'ar Allah ya saukesu lafiya. Dana hau sama sai na shiga ɗakin Jalal na fara gyarawa. Da Azahar sai ga kiran Faty. Na ɗauka muka gaisa sama-sama. Ta ce wai yaushe zan fara shiga Makaranta an bada Assignment har biyu kuma wai ta ji Supervisor ɗina yana neman 'yan group ɗinmu ranan Monday. Na mata godiya na ce ina nan shigowa school ɗin in Allah ya yarda. "Daga maganar Makaranta kowa ya ja ya yi shiru, ƙarshe ta min sai anjima na ajiye wayata." Ban taɓa hasaso wai za a kawo lokacin da ni da Faty za mu fara taka-tsantsan da juna ba. In ji 'yan Kudu suka ce 'Na so life be'. Bayan na yi Sallar Azahar sai na sauko ƙasa. Kamar haɗin baki ina saukowa Hassana ta danna doorbell. "Dana buɗe mata sai ta ce min da Direban Hajiya ta ke. Na ce mata ba matsala ya shigo, dan Jilbab ne a jikina dama." Haka suka fara shigo da manyan ledoji da kwalaye. Da suka gama shigo da su na yi musu godiya. Na ja Hassana gefe na ce ta jirani. Na shiga kitchen na haɗo musu ChinChin da Diblan da nama a leda na ce ta bawa Direban Hajiya da ya kawota nasa ta ɗau ɗayan. Ta min godiya ta fita. Bayan fitarsu dana koma kitchen ɗin sai riƙe ƙugu ina tunanin ta ina zan fara da tulin kayan da suka kawo mini. Dake ina jin yunwa sai na ce barin yi ta cikina tukunna. Ba abinda zai min sauƙin dafawa sharp-sharp sai noodles. Na ɗau Attaruhu da Albasa cikin kayan miyan da aka kawo na yanka na fara haɗa noodles ɗina. Har da fasa Sardine guda ɗaya dan ba zan iya tsayawa soya ƙwai ba. Dana gama haɗawa zama na yi na fara ci a cikin tukunyar. Ni dai gani a babban gida amma ɗabi'ar 'yan "Ghetto bai bar jikina ba. Ina ci, ina lissafin yadda zan yi da kayayyakin da aka kawo." Dana gama cin abincin sai na wanke tukunyar na mayar inda na ɗauko. "Wai wai wai! Yanzu ni nama zan fara gyarawa ko Kifi? Ko kuma kayan miya, ko fruits da aka lodo mini?." Haka dai na fara cire kayan daga ledojinsu. Wanda za a saka a ziploc a sa a Freezer na sa. Wanda za a kaisu store na kaisu. Koda yake 'yan IG Pantry suke cewa ba store ba. Dake Jalal baya nan sai na yi stew 'yar kaɗan da miyar egusi na ajiye wanda zai min iya kwana biyu kafin Jalal ya dawo. Sai ranan Laraba zan zage na yiwa Jalal girki na musamman. Ban gama aikin ba sai kusan Magariba. Hajiya ta kirani da Magariba muka gaisa. Ta ce min ya kwanan sabon gida na ce mata Alhamdulillah amma na yi missing ɗinta. Karya! Mutum ɗaya nake missing. JALAL. Bayan na gama Sallar Isha kuwa ko saukowa ƙasa ban yi ba. Na je ɗakin Jalal na kwanta a gadonsa na rungume Pillow ina tuno moments ɗinmu na daren jiya. "Kamar yadda ya ce na riƙa tunaninsa har ya dawo, to tunanin nasa ne ya cika mini kai." Ƙarfe tara da rabi na fara kiran numbarsa. Ba zan iya bacci ba tareda na ji muryarsa ba. Na masa kira har biyu bai ɗauka ba. Na rungume pillow ina kallon ceiling. After like 15 minutes sai ga kiransa. Ƙafin na ce zan ja masa aji tuni hannuna ya danna ACCEPT. """Sorry Amaryata. Yanzu na shigo hotel ɗin da zan sauka"" ya faɗa tun ma kafin na masa ƙorafin rashin" kirana da kuma ɗaukar wayata da bai yi ba. """Ya hanya. Fatan ka isa lafiya"" na faɗa ciki-ciki ina wasa da button ɗin rigana. Ba rigar jiya bace amma" yanzu da nake taɓa button ɗin sai nake imagining yadda Jalal ya cire buttons ɗin jiya ɗaya bayan ɗaya. Ya tambayeni ko an kawo min abubuwan da nake buƙata na ce masa eh an kawo har da abubuwan da ban lissafta ba. Godiya na fara masa ya basar ya fara tambayata ko na yi missing ɗinsa. Ofcourse na yi missing ɗinsa. Da tunaninsa fa na wuni yau. Yanzu ma saboda kewarsa na ƙi kwana a ɗakina na dawo ɗakinsa. Na tambayeshi ina so gobe na je na gaishe da Hajiya sai ya fara min dariya wai dan zan je gidan Hajiya ai ba sai na tambayeshi ba. To ma idan Baturiyarsa haka take masa duk inda za ta je gatsau take tafiya ba tareda ta tambayeshi ba. Ni dai na san darajar tambayar miji kafin a fita. """To ai sai da izininka zan fita"" na faɗa dan ya san addini ne ya halarta hakan." "Ya ɗan yi shiru sai kuma na ji ya ce ""in dai wajen Hajiya ne na yarje miki, za ki iya zuwa duk sadda kika ga" "dama""" """Nagode"" na furta a hankali." Sai kuma na tuno maganar Makaranta na ce masa Monday ina son shiga school na kai Assignment sannan na ga Supervisor na. """School. Asibiti. Your Restaurant. And any emergency za ki iya fita. I am not caging you, Sunshine""" """To ai addini ne ya ce a tambayi Miji kafin a fita. Ko ba haka ba?""" Murmushi ya fara. Sautin murmushinsa ya fara evoking wani sabon feelings a jikina. I wish yana kusa da ni. """Na san ba za ki je inda bai kamata ki je ba. And I know duk inda kika je, za ki mutunta ni ki mutunta" "kanki. Wannan kaɗai ya wadatar""" """U'um fa! Kada na ce maka zan je gidanmu na yi sati ɗaya ka ce baka yarda ba""" """Idan tare za mu je ai ba matsala"" dariya na fara shima ya yi dariyar." Kai! Ina son Jalal. I am so inlove with him. Mun ɗan yi hira kaɗan kafin muka yi sallama dan ya ce zai yi wanka. Har da cewa da ina nan sai in masa. Ai tuni na ce masa sai anjima bacci nake ji.Ah to... *** Washegari da safe na kira Class Rep ɗinmu na ce dan Allah ya turo min questions ɗin Assignment ɗin da aka bayar ya ce min akwai a group na ce ban gani ba. Yace zai turo min. Idan na ga zan iya Assignment ɗin da kaina sai na yi. Idan na ga kuma zai bani wahala to sai na kira wani Faisal ɗan ajinmu da yake da Cafe in tura masa kuɗi ya min kawai. Wajan ƙarfe shaɗaya na safe sai na kulle gida na wuce gidan Hajiya. Ai tunda maƙota muke ta dinga ganina kenan duk sadda Jalal ya yi tafiya. Ai kuwa ta ji daɗin ganina. Ta tisani a gaba wai in mata ɗanwake sha'awar ɗanwake ta ke. Na shiga kitchen na haɗa mata na kawo. Tare ma muka ci a dinning. Da Junior ya dawo daga Islamiyyar safe saboda weekend ne sai na yi ƙoƙarin jan yaron a jiki amma sai na ga kamar yaron baya sona. Sama-sama yake amsa dik maganar da nake masa. Hajiya ta ce kar in damu a hankali zai sake dani. Wai lokacin da aka dawo da shi Nigeria haka yake baya "son magana da kowa, baya son shiga mutane. Daga Babansa da Hajiya sai Janan, su kaɗai yake yiwa magana. A hankali kuma ya fara sakewa har ya yi abokai a Family house da kuma school." Banga Hajiya Janan a gidan ba wai ta tafi Abuja. Na ce a dawo lafiya. Haka na wuni a gidan Hajiya har bayan la'asar. Da muka idar da sallar la'asar a ɗakinta sai ta tambayeni maganar Restaurant. Na ce mata dama da an buɗe Plaza za a buɗe wajen na fara aiki. """Za ki iya haɗa aiki da karatunki da kuma kula da gida?""" Na sunkuyar da kaina ƙasa na ce mata zan iya. """It's not easy Ziyadah. Ba zan ɓoye miki ba, haɗa duka ukun zai baki wahala. Lokacin da muke London da" "marigayi duk da ina da mai aiki, duk da ina da manyan yara riƙon gidana ya bani wahala sosai. Allah dai ya zubawa marigayi haƙuri ne da tuni ya hanani fita aiki""" Ta fara bani shawarar shi business ko wani iri ne dole ka gina shi yadda ko ba ka wajen zai cigaba da tafiya. Ta ce idan Gidan Girki ya zama stable ya fara tafiya sosai na tabbatar na training kitchen staffs ɗina ta yadda ba sai na je Restaurant ɗin ba za su iya girka komai exactly kamar yadda nake. Na ce mata Insha Allah zan yi hakan. """To Allah ya taimaka ya kuma bada nasara"" na amsa da Amin." Ƙarfe biyar na mata sallama na wuce gidana. Da na je sai na kira Kaka muka gaisa. Ina missing ɗinta sosai. "Idan na cika wata ɗaya da aure zan tambayi Jalal ya bar ni na je gida gaisuwa. Na je na ga 'yar Tsohuwata. Na san ba ƙaramin kaɗaici bane zai dameta. Akwai mutane a gidan. Akwai yara dayawa a gidan, amma ni Ziyada ni ce komai nata. Because we've got each other shi yasa kullum daga Islamiyya sai ɓangarenta. Sai da dalili ta ke shiga ɓangaren sauran matan gidan." "I miss Kaka, Allah." "Ni ga shi missing ɗin har ya min yawa. Ga kewar Jalal, ga kewar Kaka..." *** Ranan Sunday ma sai dana shiga wajen Hajiya. Ina wajen ma Agnes ta kirani wai ita da Jide za su zo mini Barka. Na ce musu sai sun zo. A gidan Hajiyar suka sameni dan babu amfanin kaisu gidana tunda duk ɗaya ne. Free nake a gidan Hajiya babu takuri. Mun ɗan jima da su muna ta hiran Grand Opening da za a yi na Plaza da kuma Restaurant ɗina Gidan Girki. Sai a lokacin nake ji wai ashe saboda tallen da suka fara ɗaurawa na content ɗin da muka ɗauka kwanaki Pages ɗin Gidan Girki a social media ya tafi viral. Nima account ɗina na Chef Zeey kullum ƙaruwa yake. Mutane suna shigowa page ɗina ne saboda gulma. Ni kuma har yanzu na ƙi ɗaura komai akan Aurena ko Gidan Girki. Aurena dai ban shirya nunawa duniya ba. Amma Gidan Girki kam zan fara tallata shi da zaran an buɗe shi. Bayan su Agnes sun tafi sai nima na yiwa Hajiya sallama na ce zan wuce gida. Monday da safe na shiga school. Muka yi Lectures biyu. Around ƙarfe shabiyu muka haɗa kai da sauran waɗanda muke ƙarƙashin Supervisor ɗaya muka tafi office ɗinsa. Tun dana shigo class ɗin da Faty ta ganni sai ta fara wani nan nan da ni. Har da cewa Leshin dana saka ya mata kyau. Ga shi ita ciki ya mayar da ita ƙazama kamar ma idan zata zo aji Hijab kawai take zurawa ta taho. "'Yan ajinmu da ba su zo bikina ba sai wani cewa suke aure ya karɓeni na yi kyau. Munafukai, na tura" musu IV ɗin Walima a group amma bai fi su uku na gani a wajen Waliman ba. A maza ne ma mutane kusan biyar suka ce min sun halarci ɗaurin auren. Wani Kawuwa har da nuna min hotonsa tareda Mijina Jalal. Wai yana kamun ƙafa dani yana so ya yi Service ɗinsa a JK Group. Matan ajin namu da suke ta wani Awwn! ɗin banza. Dramar da aka yi a social media akan aurena ya sa "suke neman gulma a bakina. Ai na yi hankali da mutane. Ko Faty da muke Bestie-Bestie a da ba zan bata labarin aurena ba balle kuma su da dama haɗuwar aji ne, rabuwar gate." Ban bar school ba sai 3PM da Direban Jalal ya zo ɗaukata. Supervisor ɗinmu wai suna meeting sai ƙarfe biyu ya samu ganinmu. Da ke ni ce latest Amarya ni ya fara gani. Alfarmar Aure sai bai min faɗa ba dan Chapter one ɗin dana kai masa bai yi kyau ba. A hankali ya min bayanin yadda zan gyara. Na masa godiya na fita. Kai! Aure Rahama ne. CHAPTER FORTY SEVEN JAYKAY Ranan Laraba Jalal su ka yi meeting na ƙarshe a Lagos. Ba su fito da wuri ba sai wajen ƙarfe biyar na "yamma. Yana confirming akwai Jirgin Lagos to Abuja ƙarfe bakwai na yamma ya wuce masaukinsa ya ɗau jakarsa ya kira Uber ya kai shi Airport. Ba dan za su shiga Abuja da dare ba, da a daren zai wuce Zaria ya je ya ga Sunshine ɗinsa. Ya san idan ya yi hakan Hajiya za ta yi masa faɗa. Tun accident ɗin Jamal, duk lokacin da zai yi tafiya za ka ga hankalinta ya tashi, bata taɓa samun nitsuwa har sai ya isa inda zai je. Watarana da ya shigo Zaria kusan ƙarfe ɗayan dare haka ta dinga masifa wai me yasa zai yi tafiyar dare ita bata so." A gidan Uncle Idris ya sauka. Da ya isa kuwa sai ya tarar da Janan a gidan satinta guda ma a wajen. "Lokacin da ta biyo shi ɗakin da ya sauka sai yake mata masifar wasa da aikinta da take yi. Ko a jikinta, wai ta zo sun yi Celebrating Birthdayn Saudah ne, sai kuma ta tsaya hutawa." Sallar Magariba da Isha ya ke son yi Janan ta tsare shi da maganar Cassandra. Wannan ya sa shi fasa shiga banɗaki yin alwala. """Yaya, I have a feeling Cassandra ta san ka yi aure. Ka san na faɗa maka ta kira ni wai she suspects you're" "cheating on her""" """Me kika ce mata?""" """Ce mata na yi ƙarya ne. You're not cheating on her, ba wata mace a rayuwarka. But gaskiya kamar bata" "yarda dani ba. I don't know ko wani ya faɗa mata ka yi aure ne or something""" """Kar ki damu, Cassandra dana sani idan ta ji labarin na yi aure ba za ta zauna a London ba. She'll book" "the fastest flight to Nigeria""" "Janan ta ce ""Okay. Tunda ka ce haka shikenan. Dama shi yasa na ce idan ka dawo zan maka maganar""" "Juyawa ya yi ya ce ""barin yi sallah""" """Yawwa!. Yaya gobe kai zaka kaimu Zaria ko?""" """Ni kuma. Tare muka zo ne?""" """I mean ka ga tunda da motata na zo sai ka sa Direba ya kai mun ita Zaria, kai kuma sai ka tuƙa mu a" "naka""" """Get out. Ni Direbanki ne"" ya wuce banɗaki ya bar Janan tana dariya." *** ZEEY "Idan na ce muku daren ranan Laraba ban yi bacci ba na san za ku ce saboda me?. Well, it's obvious ai. Ina" "ɗokin dawowar Jalal, My JAY, Mijina." Tunda muka yi waya jiya da dare ya ce min yana gidan Uncle ɗinsu a Abuja sai na ji na ƙagu ya dawo. Da na zo kwanciya haka na rinƙa juyi ni kaɗai a gado. Da na rufe ido kaɗan sai tunani kala-kala su cika min "kai. Kwakwalwata ya ƙi yin shut down, sai aikin ayyano min abubuwa masu daɗi yake." Yau da sassafe da na kira shi dan na ji yaushe za su taso hanya sai yake ce mini wai yana jiran Janan ne wai tare za su taho tana ɓata masa lokaci. Na ce Allah Sarki! Na masa addu'ar Allah ya kawo su lafiya. "Jiya Laraba wuni na yi ina prepping abinci. Na yi miyar egusi, miyar sauce, da base ɗin miyar ganye" "saboda duk sadda zan yi miyar ganyen kawai zan zuba a cikin sauce base ɗin. Stew ɗin da na yi ma kala biyu ne, akwai mai kifi akwai mai nama. Mai naman da manja na yi shi. Sai kuma na prepping dankali na fere su na saka a freezer idan na tashi amfani da shi kawai soyawa zan yi." "A yammacin ranan na tafi salon, dama na booking appointment a wani salon da Hajiya ta recommending" mini wai nan Janan ke zuwa. Na je aka min gyaran kai da ƙananun kitso. "Ba zan juri barin gashina babu kitso ba, I mean obviously kun san idan muka fara honeymoon zan fara" "jigilar zuba ruwa a kaina. Kuma kun san mu masu natural gashi da cika ɗinnan daka zuba masa ruwa sai ya danƙare ya dawo Afro. One moment gashinka a cike gwanin sha'awa, the next moment gashinka ya zama wani abu daban." "Kitson ya yi kyau sosai, kuma ruwa zai shiga ciki easily. Sannan ba zai yi wahalar bushewa ba ko da ba" sau ɗaya zan yi wankan ba. I mean an ce akwai masu wanka biyu-uku a rana. Ban sani ba ko gaskiya ne. Yanzu dai zan lura na ga iya gudun ruwan Jalal kafin na san sau ɗaya a rana ruwa zai taɓa kaina ko kuma har da ƙari. Ƙarfe bakwai na safe bayan na gama waya da Jalal sai na wuce kitchen dan na shirya wa MIJINA abinci mai daɗi. Shekaranjiya dana leƙa gidan Hajiya na tambayi Hassana wani abinci Jalal ya fi so ?. Ta lissafo mini abubuwan da ta lura yana ci sosai idan aka yi. A hankali na san idan zama ya yi zama ni da kaina zan gano abubuwan da ya fi so. Da ke na riga na harhaɗa komai tun jiya aikin zai min sauƙi. Dama zan masa jollof rice da coconut rice ne. Mijin nawa an ce ya fi son Rice dishes ko Pasta akan Tuwo. Wai yana cin Tuwon Semo da Tuwon Shinkafa amma bai dame shi ba. Dana gama da shinkafa sai na soya chips da plantain. Na grilling kifi. Akwai pepper chicken da na yi jiya duka idan na tashi serving zan haɗa masa da shi. Anything for My Husband. Tunda aurenmu ya tashi daga deal kun ga ai sai na nuna masa amfanin auren Chef da ta iya girki. Har pepper soup ɗin kayan ciki na yi jiya yana freezer idan yana buƙata. Ƙarfe tara na safe ina kitchen ina girki wayata ta fara ringing. Sunan da na gani ya sa ni ɗaukan kiran da murmushi a fiskata. Ni da na ke jira in ji ya ce min sun kusa shigowa Zaria sai ya ce min wai yanzu suka hau hanya Janan ta dage wai shi zai driving. Na tambayeshi Direbansa fa? Wai ya wuce da motar Janan tun ɗazu. Ni dai ban ji daɗin hakan ba. Wannan Janan ɗin za ta sa Mijina ya sha wahalar tuƙi bayan ya kwaso gajiya daga tafiyar da ya yi. Na yi musu addu'ar a dawo lafiya. Burina su iso gida lafiya ba wai isowarsu da wuri ba. At least ma zan samu enough time na kammala aikin da nake kafin su iso. A yadda na ke girkin sai na ji kwaɗayin fara content a kitchen ɗin. Ni Ziyada da karambani. Yaushe-yaushe aka gama dragging ɗina wai na yi auren jari. Idan aka ga sati biyu da aure na fara food content a sabon kitchen ai sai su samu abun gulma. Zan koma Food Content amma ba yanzu ba. Akwai buɗe Gidan Girki a gabana and most importantly akwai kula da Mijina. Idan muka gama honeymoon kuma Restaurant ya fara tafiya normal then sai na fara content a gida ina sakawa a pages ɗina. Da wannan tunanin na cigaba da aiki. *** Ƙarfe shabiyu na rana ina wanke-wanke saboda na gama duk abinda zan yi sai na ji ƙaran doorbell. Da sauri na goge hannuna da kitchen towel na yi hanyar falo ƙila Jalal ne ya zo duk da ban ji ƙaran shigowar mota gidan ba. Idan ba shi bane ma ba zai wuce Hassana mai aikin Hajiya ba. Na buɗe ƙofar da tunanin ɗayan biyun zan gani amma sai na ga saɓanin haka. Na taɓa ganinta sau ɗaya watarana da na je yiwa Hajiya girki kafin ma na san zan auri Jalal. Sannan na je Instagram ɗinta na yi gulma. Kar ku tambayeni mi ya kaini bibiyar kishiya a Instagram. Na "san kuma za ku iya yin hakan. Amma fa ban bar page ɗinta da daɗin rai ba, dan wuni na yi a ranan ina ta jin haushinta da ma Jalal ɗin. Abu kaɗan sai na fara comparing curves ɗinta da nawa. Duk dama nawa ya fi nata fitowa. And boobs ɗinta manya ne ba laifi. Kun san Spanish da Mexicans suma babu laifi akwai su da diri mai kyau. To itama matar ta ɗauko ɓangaren mahaifiyarta da aka ce asalinta 'yar Spain ce." Sai dana ga hotunan ma na fahimci dalilin da ya sa Jalal ya yiwa boobs ɗina shan hauka ranan. Ashe su ya fi so tunda ga Baturiyarsa ma tana da su babu laifi. CASSANDRA ce a gabana. Cassandra matar Jalal. """Hello, who are you?"" Ta tambayeni ganin na zuba mata idanu na kasa ko ƙyaftawa." Maimakon na bata amsa sai na matsa mata dan ta shigo dan ban san me zan ce mata ba. Ta jawo Box ɗinta tana bin falon da kallo. Ba san me ya kawota ba. Ban san ko da sanin Jalal ta zo gidan ba. Ban kuma san ko ta san Jalal ya aureni ba. It's best na bari Jalal ya zo ya clearing abinda ke ƙasa da kansa kar na yi ƙaurin baki na faɗi abinda ba a sakani ba. Ina ji tana tambayata ko bana jin Turanci ne na ƙi kulata. Kujerar zama na nuna mata na yi hanyar kitchen. Ina shiga kitchen ɗin sai na rasa abinda zan yi. Shin in kira Jalal ne na faɗa masa babbar baƙuwar da ta zo ko kuma Hajiya zan kira?. What if kuma daga gidan Hajiyar ta taho nan?. Na dai ɗau wayata na fara kiran Jalal sai kuma wayar bata shiga ba. Subhanallahi! Na sake danna kiran "still not reachable, ganin haka sai na tura masa text." Na ja dogon numfashi sannan na sauke ƙatuwar ajiyar zuciya. Jikina yana bani akwai matsala. "Cigaba da wanke-wanke na yi. Lokaci zuwa lokaci ina sauke ajiyar zuciya. The truth is, gwiwata ya fara" sacewa. Zuwan Cassandra ba alkhairi bane. Bai saketa ba. Kuma tun farko ya ce min baya so ta san da auren saboda zai iya rasa ɗansa. To ko kuma dai ya faɗa mata ne sadda yake Lagos shi yasa ta zo dan ta tabbatar da auren?. Kai! Ba haka bane. Jiki a sanyaye na ƙarisa gyara kitchen ɗin na fito har lokacin Cassandra tana zaune a falo tana danna waya har ta kunna TV ma. Da zan wuce ta tambayeni ina ne ɗakin Jalal. Ban kulata ba na wuce sama abuna. Ina zuwa ɗaki sai na cire kaya na shiga banɗaki na yi wanka na fito da Alwalata. Lokacin da nake neman kayan da zan saka idan na yi sallah ne na hango wani jan nightie da na saƙala a "hanger wanda nake shirin sakawa daren yau. Duk da akwai wanda za su fi shi jan hankali na zaɓi wannan ne saboda ja yana min kyau kuma rigar ya kai gwiwa. Har yanzu ina jin kunyar Jalal, dan haka ba zan iya saka wasu daga cikin sexy night dress da aka sa a lefena ba." Yanzu kam zuwan Cassandra gidan ya rusa duk wani shiri da na yi. Bayan na yi sallar Azahar sai na saka wani simple BouBou gown na ɗaura ɗankwalinsa na fito. Ashe na baro wayata a kitchen. Ina saukowa sai na ji ƙaran buɗe gate. Dam! ƙirjina ya buga. Cassandra tana nan a inda na barta sai dai ta cire heels ɗinta ta ɗaura ƙafafunta akan kujera """Is that Jalol?"" Ta faɗa da British accent ɗinta." Ban amsa mata ba na wuce kitchen na je na ɗauko wayata. Amma ban fito ba jin kamar ana ƙoƙarin buɗe ƙofar falon. Jalal yana da password ɗin ƙofar dan haka ba sai ya danna doorbell ba. Daga inda na ke tsaye sai na ji babu amfanin tsayawata a Kitchen gara na fito falo a yi ta ta ƙare. "Janan ce ta fara shigowa. ""Cassy!"" ta kira da ɗan ƙarfi ganin Cassandra a falon. Yadda ta yi ya nuna bata" san da zuwan Cassandran ba. """What are you doing here?"" Janan ta tambaya a kiɗime. Jalal da ya shigo ne ya sa Cassy miƙewa da sauri" ta je ta faɗa jikinsa tana kiransa da J love. Ɗagowa ya yi idanunsa suka sauka cikin nawa. """Maria, what are you doing here?"" Ya yi tambayar yana ɓanɓareta daga jikinsa." Kasa haɗa ido da ni ya yi a karo na biyu. Ni kuma sai na kafa masa nawa idanun ina ganin dramar da ake yi. Ina jin Cassandra tana masa bayanin ta zo ne saboda ta yi missing ɗinsa sannan tana so su celebrating 10yrs Anniversary ɗinsu. Sai shi kuma ya ce mata Anniversary date ɗinsu ya wuce. Wato ma ya damu da ita har ya riƙe date ɗin Anniversary ɗin aurensu. Ta kissing ɗinsa lightly a baki ta ce wai su yi pre-celebrating Anniversary ɗinsu na cika shekara shaɗaya da aure. Janan ce ta katse maganar ta hanyar tambayar Cassy yaushe ta shigo Nigeria?. Cassandra ta ce mata yau ta shigo. Janan ta ce ta yi mamaki ne saboda bata faɗa mata za ta shigo ba. "Nuna ni Cassandra ta yi sannan ta tambayi Jalal wacece ni. ""Who is she?""" Sai a lokacin Jalal ya sake haɗa ido dani. Ina ganin yadda yake ƙoƙarin aika min saƙon ban haƙuri da idanunsa. To haƙurin me zai bani?. Tambayarsa fa a ka yi wacece ni?. Miye matsayina a gurinsa?. Shi yasa ban yi magana da Cassandra ba tunda ta zo dan bana son faɗa mata abinda ba dai dai ba. "Ban san sadda Janan ta iso wajen da nake tsaye har ta kama hannuna ba sai ji na yi ta ce ""She's a Chef," "Cassy. She works here""" """Ohh!"" Cassandra ta faɗa tana kallon Jalal ta ce ""Jalol, is she JUST a Chef?"" Ta yi tambayar dan ta samu" tabbacin abinda Janan ta faɗa. Akwai zargi a tattare da tambayarta kuma mutum ɗaya ne zai warware wannan sarƙaƙiyar. """Yes, She's MY Chef"" Jalal ya bata amsa yana kallona still idanunsa na ban haƙuri. Gwiwowina ne suka" "sace, lokaci guda na ji ƙafafuna na shirin kada ni." "Ba wannan bama, wani abu ne mai tsini ya sokeni a ƙirji." Sama-sama na ke jin Cassandra tana faɗa masa wai tunda ta zo gidan take tambayata amma ban kulata "ba, wai ko ni kurma ce?." Ku ji fa. Janan ta jani muka yi kitchen. Har lokacin idanuna sai tara hawaye yake amma sun ƙi zubowa. """Ban san me ya kawo Cassy gidan nan ba. I think wani ne ya kirata ya ce Yaya Jalal ya yi aure""" "Sa tafin hannuna na yi a idona na mayar da hawayena ciki. Na kalli Janan na ce ""Ba komai. Dama ya ce" "min baya son MATARSA ta san dani so kamar yadda yace zan tsaya a matsayin Chef kawai"" ina maganar ina danne hawayen da ke taho min. Babu abin da ke ringing a kwanyata sai amsar Jalal ""Yes, She's my Chef"". It hurts. Tsoron matarsa ya sa ba zai iya acknowledging aurenmu ba." "Ban san hawaye sun fara zubo min ba sai da Janan ta ce ""kuka ki ke yi?""" "Na yi saurin kai hannu na fara goge hawayena, amma ina yi wasu na saukowa." """Ni fa shi yasa tun farko ba ki min ba kwata-kwata. You don't have CLASS. Daga ganin Cassandra" "shikenan sai ki fara kuka""" Abinda bata sani ba shine ba zuwan Cassandra bane ya sakani kuka. Amsar MIJIN Cassandra ne ya saka "ni kuka. Domin a yanzu matsayin Chef gareni a gidan nan, bani da ikon kiran Jalal da Mijina." """Look Ziyada, I don't like you. Amma gaskiyar da na sani shine my brother loves you. Ban san" "yarjejeniyar dake tsakaninku ba. Ban kuma san me yasa bai jira ya rabu da Cassy legally ba kafin ya aureki""" Laifina ne ai. Ni ne da bakina na furta masa na amince da deal ɗinsa. Ai ban cancanci kuka ba tunda na san haka zata iya faruwa. I got carried away ne saboda romantic night ɗinmu da kuma alƙawarin da ya yi a daren. "I want to have you, Zeeyadah. All of You..." """See, kuka ba zai chanja cewa Cassandra matar yaya Jalal bace. But ki arawa kanki class ki nemawa kanki" "'yanci""" "Ta riƙo hannuna ɗaya ta ce ""Cassandra ba za ta taɓa yarda ya zauna da ke ba idan ta san ya aureki""" "Ta ɗan matse yatsuna ta ce ""kema ki ce masa ya zaɓi ɗaya, ko ke ko Cassandra. Idan ya ji haka lallai zai yi" "abinda ya dace""" "Sake hannuna ta yi ta ce ""akwai abinci a gidan nan, I'm starving""" """Akwai abinci"" na faɗa muryata shaƙe da kuka." Lokacin da muka fito falon sai muka tarar Cassy da Jalal ba sa nan sai akwatin Cassy kaɗai a falon. "Janan ta zauna a dining na ce barin serving ɗinta, sai ta fara min iyayi wai Allah ya sa ba local food dana" saba yiwa Hajiya zan bata ba. Na ce mata a'a. Ina serving abincin ina jin kamar zuciyata zai bulluƙo ya faɗo plate ɗin. Dana gama serving ɗinta sai na ce zan je ɗakina in yi sallah. Ina haurawa sama sai na ga Cassandra da Jalal tsaye suna musayar yawu. Wuce su na yi na shige ɗakina. Ina shiga na saka key. Rufe bakina na yi na fashe da kuka... CHAPTER FORTY EIGHT ZEEY Bayan na sha kuka na gaji sai na kwanta akan gado na rufe gabaɗaya jikina da bargo kamar mai zazzaɓi. "Can sai wayata ta fara ringing. Da ƙyar na jawo wayar saboda a tunanina Jalal ne ya sake kira. Ɗazu ya yita kiran wayata na ƙi ɗaukan wayar. Har knocking ƙofar ɗakina ya yi ina jinsa yana kiran Sunshine na yi banza da shi. Ku ji munafurcin NAMIJI fa, wai har yana da bakin kirana 'Sunshine' bayan a gaban Baturiyar matarsa ya gama cewa ni CHEF ɗinsa ce ba matarsa ba." Hajiya ce ke kirana. Na tashi zaune sannan na ɗau wayar bayan na yi gyaran murya saboda muryata dake shaƙe da kuka. Sama-sama muka gaisa ta ce maza in zo gida tana nemana. Na ce mata gani nan zuwa. Bayan na ajiye wayar sai na miƙe na je na kalli kaina a madubi fiskata da idanuna duk sun kumbura saboda kuka. Bani da ko ƙarfin yin wanka kawai na shiga banɗaki na wanke fiskata na fito. Jilbab na nema na saka har zan fita sai na tuna ai ban faɗawa Jalal zan je gidan Hajiya ba. To ai ya bani izinin zuwa gidan Hajiyarsa duk sadda na ga dama. Na dai tura masa text na ce Hajiya tana nemana na tafi gidanta. Wayata kawai na riƙo da keys ɗin gidan na fito. Babu kowa a falon ƙasa sai TV dake aiki. Akwatunan Cassandra dake falon babu su yanzu. Kenan ɗakin Jalal ta kai su. Na yi ficewata daga gidan ina jin wani ɗaci a raina. Ganin motar Jalal a gidan ya sa na yi tunanin ko dai yana ɗakinsa shi da Cassandra ko kuma ya fita daga gidan ba tareda mota ba. Hassana ce ta buɗe min ƙofa muka gaisa ta ce min Hajiya na ɗakinta. Na wuce ɗakin ina tunanin me Hajiya za ta faɗa min. Da sallama na shiga ɗakin Hajiya tana zaune akan sallaya tana karanta wani littafi. Da fara'a a fiskarta ta mini barka da zuwa. Muka gaisa sannan na samu kujera na zauna. Sai dana jirata "kusan minti goma sannan ta rufe littafin da take karantawa ta cire reading glass ɗinta ta ce ""'yata, zo nan""" "Tasowa na yi na zo na zauna a gabanta. Riƙe min hannu ta yi ta ce ""Janan ta faɗa mini Cassandra ta zo." "Ina so ki sani ke matar Jalal ce, babu abinda Cassandra ta fiki, yadda take matarsa haka kike matarsa. Infact ke da aka ɗaura aurenki ƙarƙashin sunnar ma'aiki ai kin fita matsayi. Ki kwantar da hankalinki kin ji zuwanta ba zai chanza matsayinki ba""" """Idan ita ko Jalal ɗin suka takura miki ki zo ki faɗa mini kin ji""" Na gyaɗa mata kai. """Shima tun tuni ya rabu da ita ya ƙi"" Hajiya ta faɗa fiskarta na nuna ɗacin auren Jalal da Cassandra." Da alama Janan bata faɗa mata yadda Jalal ya yi denying ɗina a gaban shalelen Baturiyarsa ba. Dan na san yanzu sai ta kira Cassandrar ta faɗa mata da kanta. Ba zan so haka ba. Idan akwai wanda ya kamata Cassandra ta ji maganar a bakinsa to Jalal ne. Haka dai hajiya ta yi ta min nasiha ta ce kada na ɗaga hankalina da zuwan Cassandra gidan. Gidan Jalal gidana ne na ma fita iko da gidan tunda itama Cassandrar tana da gidan da Jalal ya siya mata a London. Ni dai jinta kawai nake amma ba Cassandra bace damuwata. Mijin Cassandra da ban gama gane matsayina a wajensa ba shine damuwata. Ƙarshe muka koma hiran Restaurant da za a buɗe ranan Asabat da Plaza duka na ce mata a shirye nake da komai. Su Jide da Agnes suna bani feedback na yadda komai ke tafiya. "Can na tambayi Hajiya ko an yi saukar buɗe Plazan?. Ta ce mini gaskiya Jalal bai ce mata an yi ba, tunda" kuma bai faɗa ba ba a yin ba kenan. A gabana ta kira shi ta tambayeshi ya ce mata ba a yi ba. Ta ce maza gobe Jummu'ah ya sa a kirawo Alarammomi su zo su yi saukar Qur'ani a wajen ya bayar da abun sadaka. "Sai daf Magariba na bar gidan Hajiya na koma gidana, ko in ce gidan Jalal. A yadda abubuwa suka tafiya" bani da confidence ɗin kiran wajen da gidana. Ina shigowa gidan abincin da ke dining na fara duba dan kar ya ɓaci. Da alama bayan Janan akwai wanda ya taɓa abincin. Na kai abincin kitchen na sake warming ɗinsu sannan na kira Maigadi na bashi. Ni kam tea kawai zan sha na kwanta idan na yi sallar Isha dan wani mugun ciwon kai ke damuna. Shayi nake dafawa Cassandra ta shigo kitchen ɗin. Kallo ɗaya na mata na kau da kaina ina ƙoƙarin ture duk wani kishi da haushinta da ke taho mini. Rigar Jalal ne a jikinta. Baƙin Tshirt ɗinsa da ya tsaya mata iya cinya. Babu komai a ciki tana yawo da sangala-sangalan cinyoyinta a waje. """You're Jalol's live-in Chef, correct?""" Na yi banza da ita. Ganin ban kulata ba sai ta tambayeni ko bana jin turanci ne. Nan ma ban kulata ba. """I want fish and chips for dinner... and some tea""" Sai a sannan na ɗago na kalleta. Wato fa da gaske mai girkin gidan ta ɗaukeni. """That's Jalol's favourite you know""." Na san da gayya ta faɗi hakan. Saboda ta tabbatar mini a matsayinta na matar Jalal ta san abincin da yake so. Kaman ba zan yi abinda ta ce ba bayan ta fita daga kitchen ɗin sai kuma wata zuciyar ta ce na yi ɗin kawai. Ai daga yanzu zaman Chef zan yi a gidan har sai Jalal ya fayyace mata matsayina a gidan. Dama akwai dankalin dana fere a freezer na ciro zan soya. Duk da Hajiya ta jaddada mini matsayina hakan bai sa na ji sassauci a zuciyata ba duba da cewa shi mutumin da ake ta magana a kansa har yanzu bai janye maganarsa ba. Ina cikin soya marinated Tilafia Fish bayan na gama soya chips sai na ji kamar ana buɗe ƙofar falo. Duk da ƙanshin chips da kifin da nake soyawa ya cika kitchen ɗin hakan bai hanani jin ƙanshinsa ba lokacin da ya shigo kitchen ɗin. With every step ɗinsa ji nake kamar zuciyata zai yi tsalle ya faɗo. Damn it! Har yanzu Jalal yana da tasiri akaina. """Sannu da aiki"" ya faɗa da muryarsa da ke tattare da gajiyar da ke jikinsa." Maimakon na ji tausayinsa sai na ji zafin abinda ya faɗa. Wato matarsa ta saka ni aiki har yana da bakin ce mini sannu. Hannunsa ne ya gogi nawa lokacin da ya tsaya a gefena. Wani spark ya wuce tsakaninmu. Ban sani ba ko shima ya ji abinda na ji. Zuciyata ya ƙara gudu saboda kusancinmu da yai yawa. Ba zuciyata kaɗai ke kewarsa ba. Ilahirin jikina ke buƙatarsa. Ta ya soyayya da sha'awarsa za su cikani alhalin shi bai damu dani ba. Ni da na yi alƙawarin yaƙice shi a zuciyata me yasa jikina ke adawa da hakan. "Hannuna ɗaya da ya riƙo ya jefa ilahirin jikina kakkarwa, tsikar jikina suka tashi." """I'M SORRY, Zeeyadah. Wallahi ban san da zuwan Cassandra ba. I will fix this. Zan lallaɓata ta koma" "London ranan Monday""" Kutmelesi!. Zai lallaɓata ta koma London ranan Monday. Kenan ba shi da niyyar rabuwa da ita?. Gaskiyar Janan da ta ce dole na nemawa kaina 'yanci. Zan fara samarwa kaina 'yanci ne idan na nuna masa ban damu da abinda ya ke ba. "Ba zan bari ya fahimci tasirinsa akaina ba. Yaƙice hannuna na yi daga riƙonsa na matsa gefe na ce ""ni ban" "ce ka kori MATARKA ba. Wajen MIJINTA fa ta zo saboda ta yi missing ɗinsa. Haka kawai sai ka ce mata ta koma. Ta yi zamanta, duk lokacin data ga damar komawa sai ta koma. Ni Chef Ziyada zan yi ƙoƙari na cigaba da girka muku favourite food ɗinku""" Ina maganar ne ina juya kifin dake wuta ina avoiding idanunsa. """Zeeyadah, ba abinda kike tunani bane. Idan Cassandra ta san abinda ke tsakaninmu za ta ɗauke" "Muhammad""" "A fusace na juyo na ce ""Minene a tsakaninmu, Mr Jalal?""." """Oh! Ka ɗauka zan ji haushi dan ka kirani da Chef ɗinka ne. Ai ba ƙarya ka mata ba. Babu wani abu" "tsakanina da kai. Deal ɗin da ke tsakaninmu shine, za ka bani Restaurant idan na aureka. Aurena kuma zai farantawa Hajiyarka rai. Win-Win. Ranan Asabat za a buɗe Restaurant ɗina Gidan Girki ko ka fasa buɗewar?""" """Zeeyadah, please ki fahimceni...""" """Na fa fahimceka Mr Jalal. Na fahimceka sosai""" "Zai yi magana muka ji muryar Cassandra tana kiran ""Jalol""" Ɗan matsawar da ya yi daga gefena bayan ta kira sunansa ya sa dukkan wani hope da nake tunanin samu idan na tunzura Jalal ya tarwatse. Jalal bai shirya faɗawa Cassandra gaskiya ba. Idan kuma ba zai faɗa mata gaskiya ba to ni ba zan taɓa bashi dama akaina ba. Mu tafi a auren deal ɗin. Ranan da ya shirya buɗe baki ya faɗawa Baturiyarsa gaskiya ma ɗaura daga nan. Ƙarisowa ta yi ta rungumeshi tana ƙoƙarin kissing ɗinsa tana faɗin ya shigo bai zo ya sameta a ɗaki ba. """I asked the Chef to make your favourite. Let's have dinner together""" """I'm not hungry, Cassy"" ya faɗa yana ƙoƙarin cireta daga jikinsa." Fita ya yi daga kitchen ɗin ta bi shi da sauri tana tambayarsa me ya ke damunsa. Na ja doguwar tsaki. A dining na ajiye musu 'Favourite Dinner' ɗinsu na wuce ɗakina da kofin shayi. "Shine ni bai taɓa faɗa mini favourite ɗinsa ba, har da ce mini wai shi bai cika son cin abinci mai nauyi da" dare ba. Ina shiga ɗakina na saka key na kulle... *** JAYKAY Daga Massalaci Jalal ya wuce gidan Hajiya inda ya sha faɗa sosai a wajenta. Ta kuma gargaɗeshi da cewa kada ya yarda ko da wasa ya ce zai walaƙanta Ziyada saboda Cassandra ta zo. "Lokacin da ya ga Cassy a gidan he was confused. Ba dan Janan ta yi saurin magana ba, a lokacin ya shirya" faɗawa Cassandra gaskiya ne. Da Janan ta yi magana kuma sai ya ga gara a tafi a hakan zuwa lokacin da zai zaunar da ita ya faɗa mata a nitse. Bai san hakan ya yiwa Ziyada zafi ba sai yanzu da ta gama faɗa masa baƙaƙen maganganu. Kafin ya bar gidan ya yi ƙoƙarin samunta ya bata haƙuri amma ta ƙi ɗaukan kiransa sannan ta rufe ɗakinta da key. Abubuwan da Ziyada ta faɗa masa a kitchen suka sake jefa Jalal cikin tashin hankali. Me ya sa za ta kawo "maganar deal ɗinsu bayan sun riga sun wuce wajen. Idan ba zuwan Cassy da ya ɓata komai ba, a yadda ya tsara wannan dare was supposed to be a romantic night. Ya shirya buɗe musu sabon babi ne a rayuwarsu. Ya shirya cikata da soyayyarsa, da kuma kulawarsa." A Yanzu dai ba zai iya fayyacewa Cassandra gaskiyar magana ba har sai sun yi magana da Lawyansa. Zai kira Lawyansa dake London gobe ya ji ta yadda za a yi ya filing divorce ba tareda Kotu ta bawa Cassandra custody na ɗansa ba idan ta ƙi bar masa yaron. Yadda Cassy ta saka shi a gaba da tambayar me yake faruwa? Wani magana yake da Ziyada kafin ta zo kitchen ɗin ya sa shi sake mata fiskarsa ya ce kawai gajiya ne. Afterall tun safe ko hutawa bai yi ba. Tun breakfast da ya yi sama-sama a Abuja kafin su taho ma har yanzu ko ruwa ya kasa sakawa a bakinsa. Ɗazu bayan ya bar gidan Masallaci ya wuce saboda ya samu nitsuwar tashin hankalin da ya shiga. Fakewa Jalal ya yi da aiki ya ɗau Laptop ɗinsa ya ce ba zai ci abinci ba a ƙoshe yake. Lokacin da Cassandra ta bar ɗakin wayarsa ya jawo ya sake kiran numbar Ziyada dan su yi magana sai ya ji numbar a kashe. Hakan ya sake ɗaga masa hankali. Kenan da gaske so take ta ɓata masa rai ta hanyar dawo da maganar deal ɗinsu na baya. Fuck! Deal. Yana sonta. Yana buƙatarta. kuma idan abinda ya gani a ƙwayar idanunta kwanakin da suka "yi tare kafin ya tafi Lagos gaskiya ne, to tabbas itama tana son shi." Bai san time ya tafi ba sai da ya ga Cassy ta shigo bayan ta je ta ci abinci ta dawo. Ƙoƙarin shiga jikinsa ta yi za ta fara taƙalarsa ya dakatar da ita. Babu abinda ya ke ji a kanta yanzu. Idan akwai macen da yake buƙata a yanzu to Ziyada ne. Ba zai iya tarayya da kowacce mace ba idan ba Matarsa Ziyada ba. Aurensa da Cassandra ya ƙare. Abinda ya saura shine Kotu ta tabbatar da rabuwan. Masifa Cassandra ta fara yi wai ta zo Nigeria ne saboda ta yi missing ɗinsa mi ya sa zai shareta. """Are you cheating on me, Jalol?"" Ta jefa masa tambaya tana binsa da kallon tuhuma." Miƙewa ya yi ya ɗau laptop ɗinsa ya bar mata ɗakin. Gara ya occupying kansa da aiki kawai dan ba zai iya biyewa masifar Cassandra ba. Yana zama a kujera tunanin Ziyada ya sake faɗo masa. "So yake ya ganta, ya jita a jikinsa." So yake ya sake bata haƙuri. Ya nemi alfarma a wajenta ta bashi wata ɗaya ya je har London ya filing divorce. CASSANDRA Ƙarfe shabiyu na dare Cassandra ta fito daga ɗakin Jalal. So take ta je ta kama Jalal a ɗakin Chef ɗinnan red-handed. Ɗazu da rana da ya mata ƙaryar yarinyar Chef ɗinsa ce bata gama yarda ba. There's more. Especially yadda ta lura Jalal yana yiwa yarinyar wani irin kallo da bai taɓa yi mata ba. Tsayawa ta yi chak ganin Jalal kwance a falo Laptop ɗinsa a kunne yana bacci. He looks so tired. Maybe da gaske yarinyar Chef ɗinsa ce kawai babu komai a tsakaninsu. But wacce ta turo mata hoton Ziyada ta tabbatar mata ita ce yarinyar da Jalal ya aura kuma tare suke zama a gida ɗaya. Wannan ya sa ta taho Nigeria babu shiri dan ta tabbatar da gaskiyar. Komawa ɗaki ta yi tana ayyanawa a ranta cewa idan ma ƙarya Jalal ya mata to za ta gano gaskiyar komai kafin ta bar Nigeria. Wardrobe ɗin ɗakin ta fara buɗewa tana neman passport ɗin Junior. Dole ta riƙe makamin da zai illata Jalal idan gaskiyar da take tsoro ya fito. Passport ɗin yaron a wajen Jalal yake. Duk yadda za a yi passport ɗin yana cikin ɗakin nan. Ta fi minti "talatin tana birkita ɗakin tana neman Passport ɗin kafin Allah ya sa ta gani a wani briefcase ɗin Jalal. Canka biyu ta yi ta dace da code ɗin da ya buɗe jakar. Da farko Birthday ɗin Junior ta saka bai buɗe ba. Sai ta gwada date ɗin mutuwar ƙanin Jalal sai ya buɗe. Over the years, ta san wani irin mutum ne Jalal. Ko password ɗin Gidansu na London wedding anniversary date na iyayensa ne." Tana ganin Passport ɗin yaron ta yi hamdala ta ciro ta rufe jakar ta mayar inda ta same shi. Da wannan "duk sadda ta samu evidence na cin amanar Jalal za ta ɗauki ɗanta ne ta mayar da shi London, kuma ba za ta taɓa bari Jalal ya sake ganinsa ba har sai ya bata haƙuri ya yi nadamar abinda ya mata. Sannan dole ne ya riƙa raba zamansa tsakanin London da Nigeria dai-dai. Da wannan ta samu damar yin bacci." CHAPTER FORTY NINE ZEEY Ban yi tunanin ganin Jalal a kitchen ba lokacin dana sauko. Na fito da wuri ne saboda in gyara kitchen ɗin "dan haushin jiya ina gama girkawa mai girma Cassandra matar Jalal abinda ta ke son ci na bar kichen ɗin ba tareda na gyara ba. Ga kuma yunwar da ta isheni tun dare. Ba yunwar kaɗai ba, bacci ne ya gagare ni. Tunanin abinda Jalal ya ke yiwa farar Baturiyarsa a ɗaki ya hanani sukuni." Ƙila yana can yana wasa da ita. Ƙila yana can ya kafa kansa yana wasa da matattarar ma'adananta kamar yadda ya mini ranan. Tunanin hakan shi ya hanani bacci. Ba zan iya cewa na yi baccin awa biyu ba a gabaɗaya daren. Yanzu dana fito na ga Jalal a kitchen yana wanke Apple sai na ji raina ya sake ɓaci. Wato ya je ya bi dare yana servicing matarsa yanzu kuma zai fito da sassafe yana cin Apple saboda ƙarfinsa ya ƙare akanta ko?. """Barka da safiya"" na faɗa ciki-ciki ina ɗaukan kitchen towel da nake goge counter top da shi." """Ina so mu yi magana, Zeeyadah. Please ki bani dama""" """Ina jinka"" na faɗa ko haɗa ido na ƙi yi da shi." "Zuwa ya yi ya riƙe hannun da nake goge-gogen da shi ya ce ""zan sa Abdullahi ya kawo ki Plaza ƙarfe" "goma. We have to talk. Ba abinda kike tunani bane""" """Idan maganarka yana da alaƙa da abinda ya faru jiya ba sai ka ɓata lokacinka wajen yi mini bayani ba""" """Just come"" ya faɗa tareda sake mini hannu ya juya zai bar kitchen ɗin." Ba zan bashi dama ya dinga bossing ɗina yana min abinda ya ga dama saboda bani da kima a wajensa ba. """Idan ba za ka iya min magana a gidan nan ba duk maganar da ta wuce ta Restaurant ba zan saurareka a" "waje ba. Personal magana a gida. Maganar Business a waje""" Ya juyo ya kalleni sannan ya fita. Yana fita kuma sai na ji dama ban faɗa masa haka ba. Sai kuma na tuna cewa idan ban faɗa masa haka ba ba zai fahimci ƙuncin da ya jefa ni ciki tun jiya da rana ba. Bayan na gama gyara kitchen ɗin sai na haɗawa kaina noodles da ƙwai. Na toasting slize bread uku na "haɗa shayi na jera a ƙaramin tray na haura da shi sama. Yunwa nake ji sosai. Ina shiga ɗakina na saka key. Bajewa na yi a ƙasa na fara cin abinci. Ina ci ina ayyana abubuwan da zan faɗawa Jalal idan muka haɗu a plaza yau. Da nace ba zan je ba, amma yanzu dole na je na ji wace tsiyar zai faɗa mini. Duk abinda ya kawo ina dai-dai da shi." JAYKAY Har ya shiga banɗaki ya yi wanka ya yi shirin office Cassandra tana bacci bata tashi ba. Ba dan zuwanta ba da yanzu yana can yana lallaɓa Babynsa cikin bargo ba ma zai je office ba sai Monday. Amma yanzu babu amfanin zama a gidan saboda ba zai iya minti biyar kusa da Cassy ba. Ita kuma wacce yake son tarayya da itan ta ƙi bashi haɗin kai. Fatansa shine idan suka haɗu a Plaza yau zai roƙeta ta yi haƙuri ta bashi wata ɗaya ya samu damar zuwa London ya fara prrocessing sakin Cassandra. Ba ya so ya yiwa Cassy maganar a nan ne saboda kada ta tafi masa da ɗansa. Amma idan ya lallaɓata suka tafi London tare zai samu damar shigar da maganar saki ba tareda ta yi amfani da ɗansa ta blackmailing ɗinsa ba. Ya san idan ya yiwa Ziyada wannan bayanin za ta sassauta masa ta dena jin haushinsa. Cikinsa ne ya yi ƙugi lokacin da yake saka belt ɗinsa. Yunwa ya ke ji. "Ba zai iya cewa Ziyada ta bashi abinci ba, saboda zata iya fassara hakan da wata manufa. Zai kira Janan" ya ce ta sa a haɗa masa breakfast ta kawo masa office. Lokacin da ya fito daga ɗakinsa zai wuce ta gaban ɗakin Ziyada sai ya ji ba zai iya fita ba tareda ya sakata a idanunsa ba. Ƙwanƙwasa ƙofarta ya yi har sau biyu amma ya ji shiru. A karo na uku da ya ƙwanƙwasa sai ya kira sunanta a hankali yana roƙon ta buɗe. Bai yi tunanin za ta buɗe da wuri ba sai ya ji ƙaran cire key. Buɗewa ta yi ta riƙe ƙofar saboda kar ma ya ce zai shigo. Kallonta ya tsaya yi yadda bakinta ya yi nasha-nasha da mai. """Zan wuce office"" ya faɗa yana kallon fiskarta." """A dawo lafiya""" Motsin bakinta ne ya ƙarisa birkita shi. Kasa haƙuri ya yi ya yi taku ɗaya ya tallafo fiskarta tun ma kafin ta yi resisting ɗinsa. Bai bata damar da za ta yi jayayya da shi ba ya haɗe bakinsu ZEEY Ban ankara ba Jalal ya haɗe bakinmu. A take na ji komai ya ɗauke min ɗif. Abinci na gama ci na ji ana ƙwanƙwasa min ƙofa. Na san Jalal ne amma ban buɗe ba sai dana ji yana kiran sunana. So nake na ji wace tsiyar zai faɗa min. Amma kafin na ankara tuni ya fara fara kissing ɗina. Lokacin da ya raba bakinmu kallon juna muka fara yi. Kallonsa na ke ina jin duk wani katangar dana gina tsakanin jiya da yau yana shirin rushewa. Kallona Jalal ya ke da yunwar namijin da ya jima bai samu nitsuwar mace ba. Kallona ya ke da buƙatata da ta bayyana a ilahirin fuskarsa. Sake haɗe bakinmu ya yi tareda turani cikin ɗaki ya kaini bango. Pinning hannuna ɗaya ya yi jikin bango "ya cigaba da kissing ɗina da yunwar sha'awata da ke cinsa. Na yi ƙoƙarin raba kiss ɗin a karo na biyu, amma Jay ya mini kane-kanen da ba zan iya taɓuka komai ba." "And, I don't want the kiss to stop." "Ban san lokacin da ya yi cilli da rigata ba, sai jin sanyin bakinsa na yi a kan nipples ɗina." Shansu kawai ya ke kamar yaro ya samu alawa. Na rintse idanuna saboda daɗin da hakan yake mini. A take kuma na tuno da abinda ya ke faruwa. Bai kamata na bari ya taɓani ba. Ba zai yiwu ya sato jiki daga wajen Baturiyarsa ya zo mini kuma na bashi kaina a ɓagas ba. A yadda ya faɗa ni CHEF ɗinsa ce ba matarsa ba. JUST A CHEF. "Matuƙar bai rabu da Cassandra ba kuwa, ba zan taɓa bashi damar taɓa jikina ta daɗi ba. Idan haƙƙinsa" yake so Bismillah. Amma idan yardata yake nema to fa ba zai samu ba har sai ya shaidawa Cassandra cewa ni Ziyada Sadiq Haruna legal matarsa ce ta sunna. "Jikinsa rawa yake lokacin da ya ɗago kansa ya sake kaiwa bakina zai kissing, na yi saurin saka hannu na" rufe bakina. Yai ƙasa zai sake kai kansa ƙirjina na sa hannu na tare. """Please..."" ya faɗa da muryar da ke narke da tsantsan sha'awata dake cinsa." "Ba maganar please bane. Idan yana son tarayya dani, to dole sai ya yi abinda ya dace. Ba zai cewa" Baturiyarsa ni Chef ɗinsa ba ce sannan ya sato ƙafa ya zo min ɗaki ya ce zai taɓani ba. Ba zai saɓu ba. Ba zan bashi wannan damar ba. Zuciyata bata mace har haka ba. Gara na ɗau shawarar Janan. Nima ina da CLASS. """Please..."" ya sake faɗa cike da tsantsan buƙatata. Na girgiza masa kai." """We...You should stop. Matarka za ta iya zuwa""" "Shiru ya yi yana kallona, daga fiskata zuwa ƙirjina. Har lokacin nipples ɗina a jiƙe suke da shaidar jimawar" bakinsa a wajen. """Yes, you're right"" ya faɗa yana matsawa baya. Na san haushin abinda na faɗa ya ji." To ai gaskiya ne. Kafin Matarsa Cassandra ta zo ta ganmu ya fara mata ƙaryar ni ce na cusa masa kaina. Hana shi jikina da na yi ya sa shi dragging ƙafafuwansa ya bar mini ɗaki. Sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya. The weight of abinda muka aikata ya sauka mini. It's not that bana son shi. Ko kuma bana son tarayya da shi. Infact ɗan wasan da yayi da ni yanzu ya sa na fahimci rantse-rantsen da na yi ta yi daren jiya fa akan ko shekara za mu yi ba zan sake bari wani abu ya shiga tsakaninmu ba ƙarya ne. I want him just as much as he wants me. Sai dai dole na siyawa kaina daraja. Idan har ina son tafiya mai ɗorewa dole na jure na share Jalal na lokaci kaɗan har ya gyara kuskurensa. Koda ba zai rabu da Cassandra ba saboda wani dalili nasa. To dole ne ya sanar da ita akwai aure a tsakaninmu saboda mu yi zaman kishiyoyi ba zaman mata da mai girkin gidan ba. Tura ƙofar ɗakina na yi har lokacin ina jin minty taste ɗin bakinshi a bakina... JAYKAY Jiki a sanyaye ya baro ɗakin Ziyada. A hankali yake takowa daga stairs yana ƙoƙarin saita nitsuwarsa. Ba zai iya jurewa har wata ɗaya ba. Gobe za a buɗe Plaza. Tun kafin aikin Restaurant ya ɗauke mata hankali dole ya warware wannan matsalar saboda ya samu nitsuwar da yake nema daga wajenta. A mota ya kira Janan ya ce ta taho masa da breakfast. Tana kwance ma kiransa ne ya tasheta ta fara ƙorafin ita fa bata shirya zuwa office ba sai Monday. Ya kashe wayar ba tareda ya ce mata komai ba wanda hakan ke nuni da ba wasa yake mata ba. Sai ƙarfe tara saura 'yan mintuna Janan ta iso office ɗinsa. """Kana da mata biyu kana cin abincin Hajiya"" Janan ta faɗa lokacin da ta ajiye basket ɗin abinci a table ɗin" office ɗin Jalal. """Wannan fa ba aikina bane aikin matanka ne""" Shiru bai kulata ba sai ma duba wasu takardu da yake yi. "Ƙarisowa wajensa ta yi ta ce ""Na serving ɗinka yanzu ne?""." """Yes"" ya faɗa a taƙaice." Zuwa ta yi ta ɗau plate ta fara zuba masa abincin. Jalal ya taso daga office chair ɗinsa ya dawo wajen kujerun da yake ganawa da baƙinsa ya zauna. """Kana auren Chef guda ba za ta maka breakfast kafin ka fito ba"" Janan ta tsokaneshi." """Ko har yanzu ba ta huce takaicin zuwan Cassandra bane""" Mug ɗin data miƙa masa ya karɓa ya fara shan tea. """On a serious note yaya Jalal, dole fa ka zaɓi ɗaya a cikinsu. Idan baka son Cassandra to ka saketa ka" "huta""" """Bana son surutu""" "Riƙe bakinta ta yi ta miƙe tana faɗin ""na yi shiru. Babu ruwana da duk wani yaƙin da zai taso a gidanka""" Wani kallo ya mata ta ɗau jakarta tana dariya ta ce gida za ta wuce dan ba aiki ta fito ba. Dan yunwa kawai Jalal ya ke cin abinci ba dan taste ɗin abincin na masa daɗi ba. Babu abinda yake so irin kasancewa da Ziyada. Bai ji daɗin yadda ta koreshi daga ɗakinta ɗazu ba. Me yasa za ta ce masa Cassandra za ta iya zuwa ta same su. Laifi ya ke ne?. Matarsa ce. Sai kuma ya fara blaming kansa. Da a ce ya faɗawa Cassandra gaskiya tun farko da ba zai riƙa jin tsoron kasancewa da Ziyada ba. Sati ɗaya ya bawa kansa yanzu. Ba zai iya jure wata ɗaya ba. Lokacin da ya isa Plaza. Cikowar da ke wajen saboda ana ta shirye-shiryen gudananr da bikin buɗewa da "za ayi gobe Asabat ya sa shi tunanin ba zai samu damar magana da Ziyada a nitse a wajen ba. Lokacin da ya shiga Restaurant ɗinma su Jide ya samu sunata aiki. Babu halin ya ce su fita, wannan ya sa ya kira Direbansa da ya je ɗauko Ziyada a gida ya ce masa ya kawota office ɗinsa ba Plaza ba." CHAPTER FIFTY CASSANDRA Zaune take a Balcony ɗin ɗakin Jalal tana kallon Ziyada da ta fito daga cikin gida ta shiga mota Driver ya fita da ita. Ganin motar ta fita daga cikin gidan sai ta miƙe ta wuce ɗakin Ziyada. Tana buɗewa ta ji ƙofar "a rufe ""Shit!"" Ta faɗa da ƙarfi." Komawa ɗakin Jalal ta yi ta fara neman spare keys ɗin gidan. Jalal mutum ne mai tsari. Yadda yake organising abubuwansa a gidansu na London haka yake yi a gidansa na Nigeria. Tana ganin spare keys na gidan ta yi murmushi. Har yanzu Jalal ɗinta bai chanza ba. Cikin keys ɗin da ta ke gwadawa aka dace ɗaya ya buɗe mata ɗakin Ziyada. Tsayawa ta yi a bakin ƙofa tana ƙarewa ɗakin kallo. Babu yadda za a yi Jalal ya bawa Chef ɗinsa ƙaton "ɗaki haka. Idan ita Chef ce akwai guest room a ƙasa, nan ya kamata ta zauna ba wannan ƙaton ɗakin ba." Ƙanshin turaren wuta mai daɗi da Ziyada ta sa kafin ta fita ne ya bugi hancinta. Ta ƙarisa gaban vanity table ta tsaya tana kallon turaruka da kayan kwalliyar dake wajen. Da wani mahaukacin ƙarfi ta sa hannu ta turasu suka zube gaba ɗaya. Ta kalli kanta ta jikin madubi fiskarta na bayyana tsananin ɓacin ran dake taso mata tun daga ƙasan zuciyarta. Ta ya Jalal zai ci amanarta haka?. Ba zai yiwu ba. Ba za ta bari wata ta shiga tsakaninta da Jalal ɗinta ba. "Wajen closet ta wuce ta ga gurin jimgim da kaya. Ta tsaya tana kallon nighties ɗin Ziyada, a take kuma" tana ayyana sau nawa Jalal ya taɓa yarinyar nan. Ciro su daga jikin hanger ta fara yi tana zubarwa a ƙasa. Ƙarshe kuma ta shiga tattakasu. Cassandra bata bar ɗakin Ziyada ba sai data mata kaca-kaca da kayanta. """Jalol is MINE. I won't let you have him""" ta furta da ƙarfi. Fita ta yi daga ɗakin ko ƙofar bata rufe ba. Ta koma ɗakin Jalal ta chanja kaya sannan ta fita daga gidan. "Ɗauko Junior za ta yi ta kawo shi kusa da su. Wannan zai tunawa Jalal cewa su ukun Happy Family ne," "wata can ƙaramar Karuwa, a tunaninta, ba za ta zo ta shiga tsakaninsu ba." Gidan Hajiya ta wuce. Ta tambayi Hassana mai aiki ina Junior?. Hassana ta ce mata yana Makaranta. Ta ce mata ta kawo shi gidan Jalal idan ya dawo. Ɗakin yaron ta wuce ta fara tattara wasu daga cikin kayansa. Lokacin da ta fito daga ɗakin sai ta haɗu da Janan. """Cassy, What are you doing?"" Janan ta tambaya ganin Cassy ta fito daga ɗakin Junior da akwati." """Nothing...Janon"" Cassy ta faɗa ta wuce ba tareda ta mata bayanin komai ba. Janan ta bi bayanta da" kallo cike da mamaki. Duk yadda aka yi Cassy ta gano gaskiyar komai. Koma yanene dai Jalal ne ke da haƙƙin warware wannan matsalar ba ita ba. Ta girgiza kai tareda wucewa ɗakinta. ZEEY Yau ne karo na farko dana shiga office ɗin Jalal. Office ɗin na da girma sosai. Na zauna a kujera na kunna TV ina danna wayata. Ganin yau Jummu'ah sai na ce barin kira Baffa Adamu na masa Barka da Jummu'ah. "A take ya ɗau wayar ina kiransa. Muka gaisa, ya tambayeni ya muke da Mijina na ce masa muna lafiya." "Ya ce na yiwa mijina godiya ya yi mishi wani alkhairi, dama yana so ya kirani bayan sallar Jummu'ah ne sai kuma na riga shi kira. Na ce masa babu komai." Maganar Alhaji Nafi'u ya kawo mini. Ya ce jiya da rana aka sake shi bayan ya yi kwana biyar a rufe. Lawyan Jalal ne ya tsaya akan komai. "Ya ce mini wai, Jalal ya so a tsaurara case ɗin har sai Alhaji Nafi'u ya yi shekara biyu a prison saboda ɓata" "mini suna da ya yi, amma Baffa Adamun ne ya ce a rufe case ɗin haka tunda ya riga ya amsa laifinsa" kuma ya bada haƙuri shikenan babu amfanin jan case ɗin. Da ya gama yi mini bayanin yadda aka ƙare case ɗin sai ya ce nima na cire maganar a raina. Na manta da komai tunda an kashe maganar. Ko a yanzu girman Alhaji Nafi'u ya faɗi. "Na ce masa babu komai, Insha Allahu maganar ta wuce a wajena. Har za mu yi sallama sai na tambayeshi" maganar kuɗin da Alhaji Nafi'u ya ce yana bin su Baffa Lawalli fa?. Baffa Adamu ya ce min an biya shi. Da ya ce ba zai karɓa ba wai ya yafe amma dai daga baya ya karɓi kuɗin. Na ce Alhamdulillahi. Finally dai na rabu da masifar Alhaji Nafi'u. "Baffa Adamu ya sake jaddada mini cewa in dai ina da wata matsala, to ƙofarsa a buɗe take na kira shi na" faɗa masa. Na yi masa godiya sannan na ce masa gobe za a buɗe Restaurant ɗina. "Ya yi mini addu'ar samun sa'a, sannan ya ce idan ya shigo Zaria zai zo ya ga gurin. Daga haka muka yi" sallama. Bayan mun yi sallama sai na kira Kaka itama na faɗa mata. Allah Sarki! ashe ma mura ta ke yi. Na yi mata addu'ar samun lafiya. Na tambayeta ko tana cin abinci ta ce min tana ci. Ji na yi kamar na je na je gida yanzu na ganta. Amma ba zan iya zuwa gida a yanayin dana ke ciki ba. Idan na je gida Kaka za ta fahimci ina cikin matsala ni kuma bana son haka. Bayan mun gama wayar sai na kira Ummana dan itama ta min addu'a. Wasa-wasa fa haka Jalal ya shuka ni a office ɗinsa har sama da awa biyu ina zaman jiransa. Ni da wannan zaman ma ai da Gidan Girki na wuce dan na ga shirin da su Jide suke yi. Sai dana tura masa text akan zan wuce gida sannan ya kirani yana bani haƙuri wai wata 'yar matsala ce ta riƙe shi a Plaza amma yana hanya ya kusa isowa. Bayan kusan minti ishirin sai gashi ya shigo. Yana shigowa ko kulashi ban yi ba. Yo bayan abubuwan da ya min sai na bashi fiska. Caɓɗi!. """Please, ki yi haƙuri na ajiye ki""." "Cire blazer ɗinsa ya yi sannan ya wuce banɗakin dake office ɗin. Can sai ga shi ya fito, ya zo ya zauna a" gefena. "Basket ɗin abinci dana gani tun zuwana na nuna na ce ""Ashe har Breakfast MATARKA ta haɗoka da shi""" "Murmushin mai sauti ya yi ya kamo hannuna ya ce ""tun jiya kike min horon yunwa, shi yasa na ce Janan" "ta kawo min abinci""" Na yi gefe da fuskata. Ku ji munafurci wai na masa horon yunwa. Jiya fa abinda Matarsa ta ce na dafa na "musu, amma tsabar rainin hankali wai ina horonsa da yunwa." """Zeeyadah"" ya kira sunana a hankali" """Na san na yi miki laifi. Na cancanci fushin da kike da ni. Amma please, ina so ki sani abinda ya faru jiya" "was not intentional. Bana so a tada rigima shi yasa na yi shiru. But I promise you zan gyara komai""" """Ki yi haƙuri ki bani sati ɗaya zuwa biyu, I promise, zan fixing komai, Sunshine""" "Maganar da ya yi sai ya kashe mini jiki. Tunda ya bani haƙuri kuma ya nemi na bashi lokaci, zan bashi. To" amma fa ina da sharaɗi. "Na kalleshi na ce ""Allah ya kaimu sati biyun. Amma, nima ina da sharaɗi""" "Ganin ya yi shiru sai na cigaba ""Gidan Girki da Makaranta ne a gabana ba yiwa matarka abinci ba. Ka" "nemo mata wacce za ta riƙa yi mata girki dan bani da lokacinta""" """Har nima ba zan samu girkin ba?""" Wata harara na watsa masa. Dana zage na yi masa girkin jiya ya yaba abinda na masa ne???. "Ya ɗaga hannunsa biyu yai surrender ya ce ""shikenan, za a kawo House Help""" """Da zai fi kam""" Saƙala hannunsa ya yi a bayana ya jawoni jikinsa. Numfashinsa a ta kunnena ya saka ni jin wani zirrrr a jikina. """please, ki min Tuwo mai daɗi idan kika koma gida""" """Aka ce Chips and Fish ne favourite ɗinka""" """Shhhh! Favourite ɗina duk abinda kika dafa ne"" ya faɗa yana nutsar da kansa a wuyana." "Ina so na tureshi daga jikina na nuna masa fa haƙurinsa bai chanja komai ba, amma sai na kasa motsa" hannuna. Gaskiya akwai abinda Jalal ya min. Ba haka kawai nake narke masa da ya taɓani kaɗan ba. Akwai abin da "ya min, akwai sirri a tattare da hakan." "Light kiss ya manna min a kumatu ya ce ""lokacin sallah ya kusa, kada ki hanani fita masallaci""" """In haka fita Masallaci kuma?"" Na faɗa ina haɗa tura baki. Lakutar hancina ya yi sannan ya miƙe ya ce zai" kira Direba ya kaini Plaza dan na ga preparations ɗin da su Jide suke yi. *** "Ina zuwa JK Plaza na ga an yiwa wajen decorations sosai, sun haɗa wajen game da kuma booth ɗin" promo da za a saka DJ ya zo ya entertaining mutane. "Gidan Girki ma ya yi kyau. Gaskiya Jide da Agnes sun yi ƙoƙari. Ina zuwa suka fara tsokalata wai Amarya," Amarya. Bayan na shiga kitchen ɗin na ga kayayyakin da ke ƙasa sai Jide ya kira Staff meeting muka haɗu ya briefing ɗinmu yadda Opening Day na gobe zai kasance. Ashe ma sun yi nisa a komai. Na san ko ban zo wajen ba za su iya handling komai. Ƙarfe biyu ta wuce Jide da Tee da kuma waiters da aka ɗauka suka wuce Masallacin Jummu'ah. Ban bar Restaurant ba sai ƙarfe huɗu da Jalal ya turo min Direbansa ya zo ya mayar dani gida. Ina shiga falo na ga Junior a gidan yana Assignment ya baza books ɗinsa a ƙasa. """Junior, yaushe ka zo?"" Na faɗa ina ƙarisawa wajensa. Na ɗauki ɗaya daga cikin books ɗinsa ina dubawa," sunan dake jiki na karanta a fili Muhammad Jalal Maiyaƙi. "Na ɗaga kai ina kallon yaron, kamannin Jalal gareshi amma ya ɗauko farin Mamansa da irin gashinta." """Ka ci abinci?"" Na tambaye shi. ""Yes"" Ya gyaɗa min kai." Wajen Mamansa ya zo ai dole ta bashi abinci ya ci. Ina haurawa sama na ga pack ɗin Pizza an ci an bari a falon wajen yayi kaca-kaca. Wato Pizza ta siya musu. Na girgiza kai na wuce ɗakina. Ina ƙoƙarin saka key sai na ga ƙofar a buɗe take. Na rufe ɗakin kafin na fita fa. To wa ya buɗe min ɗaki?. Na dai tura ƙofar na shiga. Sai dana sake rufe idona na buɗe dan na tabbatar da cewa ɗakin dana bari tsaf-tsaf na shiga. Tsayawa na yi ina kallon ɗakin na ma rasa me zan yi. Ni dana dawo gida dan na yi sallah na shiga kitchen na yiwa Jalal Tuwon Semo tunda ina da miyar egusi a freezer sai ga shi an jiƙa mini aiki an mayar mini ɗaki kamar bola. """Allah ya kyauta"" na faɗa tareda cire gyalena. Ina son fara sallah amma yadda ɗakin yake ya sa ba zan iya" "sallah a ciki ba sai na gyara, wa ya san me ta zuba min a ciki. Haka na sauka ƙasa na je na ɗauko vacuum cleaner na zo na fara share ɗakin. Allah ya isa turaruka na data fasa mini." Kayayyakina da suke ƙasa kuma duk na tarasu waje guda na kai laundry room a ƙasa dan ban yarda da "tsaftarsu ba, wa ya san me ta yi a kansu." Dana gama gyara ɗakin sai na koma ƙasa na fara wanke kayan a washing machine. Ba dan washing machine ba ina ga sai na kai tsakar dare ban gama ba. "Ina wanki na ji muryar Mahaukaciyar da ta ɓata min ɗaki tana yiwa Junior magana, daga baya kuma na ji" kamar fita ma suka yi daga gidan. "Sai ƙarfe takwas na dare na gama tuƙa tuwo, na ɗumama miyar Egushi na saka a food warmer na kai" dinning table na ajiye. "Sai a sannan na samu damar yin wanka, dana fito sai na fara haɗa Salloli. Allah dai ya yafe ni." JAYKAY Lokacin da Jalal ya shigo gidan kai tsaye ɗakin Ziyada ya wuce. Ya tura ƙofar a hankali ya shigo. Sallah ta ke yi. "Ya ɗan tsaya yana kallonta, she looks so peaceful." Alhamdulillahi tunda ta fahimce shi. Idan aka ƙare hidimar buɗe Plaza gobe Asabat to ranan Monday zai je office akwai meeting da za su yi "daga nan zai booking flight Talata ko Laraba sai ya wuce London. Sun yi magana briefly da Lawyansa ta waya, amma dole ne ya je London saboda su tattauna maganar Custody na yaronsa kafin ma ya shigar da maganar saki." He's going to make everything right. Ba ya son wannan ɓoye-ɓoyen. Ga shi yana matuƙar kewar Ziyada zuwan Cassandra ya ɓata masa komai. Yana shiga ɗakinsa banɗaki ya wuce ya sakewa kansa ruwan ɗumi. "Akwai gajiya sosai a tattare da shi, ga shi tunda ya dawo daga Lagos har yanzu bai samu nitsuwa mai" kyau ba. Fishin Ziyada ya fi komai birkita masa lissafi. Buɗe ƙofar banɗakin aka yi. Kallonta ya yi babu komai a jikinta. Ya san me take son yi wannan ya sa shi "kashe shower ɗin dan ya bar mata banɗakin, abunda take shirin yi baya gabansa. Buɗe glass door na shower space ɗin ta yi tana masa wani kallo. Shima babu komai a jikinsa. Matsawa ya yi zai fita ta riƙe shi." Ya ture hannunta zai bar mata wajen amma ta hana shi hakan ta hanyar rungumarsa da ta yi tana kai hannunta ƙasansa. "Wani nishi ta sake tana faɗin ""I miss you""" """I'm tired, Cassandra"" ya faɗa yana turata amma ta ƙi barin jikinsa. Ganin idan ya barta salonta zai iya" sawa ya biye mata sai ya turata da ɗan ƙarfi ya fita daga wajen. Towel ya ciro ya ɗaura a ƙugunsa ya fito ruwan jikinsa na bin floor ɗin wajen. Cassandra ta biyo bayansa dan ba zata bari ya zille mata ba saboda ta ga alama ya fara hawa layi. """Don't you miss me""" """I'm busy, Maria"" ya faɗa yana matsawa daga inda take. Binsa ta dinga yi har sai da ya iso tsakiyar ɗakin." Da ƙarfi ya daka mata tsawa akan ta bar shi Sallah zai yi. """What's happening, Jalol?. Are you cheating on me?""" """No, Cassy"" ya brushing ɗinta ya wuce wajen dresser ya fara ƙoƙarin shafa mai ta riƙe man ta ce ""allow" "me"" ." Baya son doguwar magana sai ya sake mata. "Gabansa ta dawo ta fara shafa masa mai a ƙirjinsa, bai ankara ba ta haɗe bakinsu a dai-dai sadda ta lura" da ya sake mata jikinsa. Bai san ya aka yi ya biye mata da kiss ɗin ba. Few seconds ya raba bakinsu amma Cassandra ta taɓa masa inda yake masa ƙaiƙayi nan da nan ya ɗauke wuta. Bai resisting kiss ɗinta ba har sai da ƙaran buɗe ƙofar da aka yi ya sa dukkansu biyu suka juya suna kallon ƙofar. Tsoro da firgici ya gani a fiskarta. Ture Cassandra daga jikinsa ya yi wanda ya yi dai dai da fitarta daga ɗakin da gudu... CHAPTER FIFTY ONE ZEEY """Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un""" Aka ce idan masifa ta tunkaroka ka riƙa maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un. Wannan addu'ar nake ta maimaitawa tunda na shigo ɗakina saboda zafin da ƙirjina yake yana dokawa da ƙarfi kamar zai tarwatse. Jalal maƙaryaci ne. Na shiga uku! Jalal mugun maƙaryaci ne. Ashe yaudarata yake. Ashe yadarar kaina nake. Jalal ba ya sona. Na ɗauka a cikin sati biyun daya ce na bashi zai rabu da Cassandra ne rabuwa na har abada. "Ashe yaudarata yake, yana son matarsa. Yana son Baturiyarsa." Dake na ji shigowarsa lokacin da nake Sallah shine na ce na je na duba shi. A tunanina Cassandra bata dawo ba. A tunanin zan kawo masa Tuwon da ya ce na masa. A tunanina zai ƙarfafa mini gwiwa akan Gidan Girki da za a buɗe gobe. Ashe ni kaɗai nake tunanin wannan. Ashe shi ba ta tawa yake ba. Ashe tunda Cassandra ta zo yake manne da ita. Kuka nake jikina na rawa. Ban taɓa jin tsanar kaina irin na yau ba. Na miƙawa Jalal zuciyata duk da bai buƙaci na bashi ita ba. Shi yasa na rasa kima da daraja a idanunsa. Shi yasa zai cewa shalelen matarsa ni Chef ce. Shi ya sa ya ce na bashi sati biyu saboda ya farantawa matarsa rai daga nan kuma sai ya juyo kaina ya bani ragowar abinda zai bani. Tabbas bani da daraja ko wani kima a wajen Jalal. Kallon kwaɗayyiyar mace yake min. Kallon matar da bata da 'yanci yake mini. Kallon matar da ta aureshi saboda Restaurant yake min. Shi yasa yake mugun rena mini hankali. Ina jin bugun ƙofar da ake na ji na tsani mutumin da ke bakin ƙofar. Na tsane shi. """Sunshine, please ki buɗe ƙofa""" """Please...""" Hawaye ya cigaba da zubo mini ina kuka ina danne ƙirjina dake min zafi. Na yi dana sanin wannan auren. Na yi dana sanin amincewa da kalaman Jalal. Sannan na yi dana sanin sakaci da na yi har na faɗa soyayyar Jalal. Ya san ina sonsa. Ya san irin auren da muka yi ba zan taɓa cewa zan rabu da shi ba saboda 'yan gidanmu. Ya aureni ne saboda ya samu matar da zai riƙa latsawa duk sadda ASALIN Matarsa ta koma London. "Baya son ɓacin ran MATARSA Cassandra, amma ni zai cusa min baƙin ciki ya bini da ƙaryar SORRY." """Jalal bai damu da ke ba Ziyada""." """Jalal bai damu da ke ba Ziyada"". Abin da nake ta maimaitawa kenan da ƙarfi." Kuka na ke yi kaman idanuna za su makance. Buɗe ƙofar ɗakin aka yi. Ya shigo da sauri ya ɗagani daga kwancen da nake a ƙasa ina kuka. """Please, ba abinda kike tunani bane. Please, it was... Ki dena kuka. Na yi alƙawari a daren nan zan" "faɗawa Cassandra alaƙar dake tsakaninmu. Zan faɗa mata gaskiya, I am sorry. Dan Allah ki dena kuka""" "Dariya ne ya taho mini, ina dariyar hawaye na saukowa. Ku ji renin hankali. Wai zai faɗa mata gaskiya." Gaskiyan me kuma ya rage da zai faɗa mata. """Ba sai ka..."" ya rungumeni jikinsa ya ƙanƙameni kamar zan gudu yana faɗin ""Please...I'm sorry"" duk ya" rikice. Yana bani haƙuri ina jin wutar tsanarsa na ruruwa a zuciyata. Ya san yana son matarsa me ya sa ya aureni. Me ya sa zai yaudareni da cewa yana son rabuwa da ita?. Duk yadda na so ƙwacewa sai ya ƙi sakeni. Na haƙura na cigaba da kuka a jikinsa. Kusan minti biyar muna haka a hankali sai na dena kukan. Ganin na dena kuka sai ya sakeni. Na ɗago na kalleshi idanunsa sun rikiɗa sun koma ja. "Muryata a dashe na ce ""Zan koma gidan Hajiya gobe da safe. Idan aka buɗe Gidan Girki gobe zan cigaba" "da riƙe wajen har zuwa ƙarshen shekara. Bayan nan, please ka sallameni ka zauna da MATARKA""" """Please, don't do this, Zeeyadah. Na yi kuskure, ba ni da uzurin da zan baki akan abinda ya faru. It was" "just a kiss, ba abinda kike tunani bane. Kuskure ne, Wallahi kuskure ne. Zan faɗawa Cassandra komai a daren nan. Monday zan wuce London na filing divorce""" Girgiza kai na fara yi. Dama ana kuskuren kiss ne? Shi Makaho ne da bakin Cassandra zai taɓa nasa bai sani ba?. "Koda yake Cassandra matarsa ce, ba wani abu bane idan ma sun yi fiye da kiss ɗin. Ni dai na gaji da" wannan renin hankalin. Gara na basu waje su yi abinda suka ga dama da junansu. """Idan ka hanani zama a gidan Hajiya, to zan kirata a daren nan na faɗa mata auren deal muka yi, kuma" "na fasa deal ɗin gidanmu zan koma""" "Tallafo fiskata ya yi da hannunsa biyu ya ce "" Dan Allah ki bar maganar deal, Zeeyadah""" """I want you, Sunshine. I've always wanted YOU""" Na ga gaskiyar hakan a ƙwayar idanunsa. Amma ba zan sake amincewa da maganar bakinsa ba. Na gaji da maganar baki babu Action. """Na gama zaman gidan nan, Mr Jalal. Iya adalcin da zan maka shine na koma gidan Hajiya""" """Please ki bani dama na gyara komai""" Miƙewa na yi shima ya miƙe yana kallona idanunsa cike da tsoro. """Dan Allah ki bani dama na gyara kuskure na""" """Ka san me?"" Na faɗa ina goge fiskata. Sai dana tabbatar babu hawaye ko ɗaya a idanuna sannan na" "kalleshi na ce ""Na gaji da alƙawarin ƙarya. Na haƙura da kai, na haƙura da aurenka...""" """Alƙawarin ƙarya?""" """YES. Alƙawarin ƙarya""" JAYKAY Babu sauran bayanin da zai mata tunda maƙaryaci ta ɗauke shi. Duk wani bayani da zai mata ba za ta yarda da shi ba. Zai je ya samu Cassandra ya faɗa mata komai. Duk abinda zai faru ya faru amma ba zai iya rasa Ziyada ba. Dukkansu biyu suka kalli juna kowa da irin ciwon da yake ji a zuciyarsa. Bai ce komai ba ya juya ya fita. Ɗakinsa ya koma. Zuwa lokacin Cassandra ta gama cika ta yi fam saboda tunda Ziyada ta bar ɗakin da "gudu da Jalal ya jawo Jallabiya ya saka a baibai ya bi bayanta take tambayarsa ina zai je me yake faruwa," ya ƙi kulata. Har ya sake dawowa ya ɗau keys ya fita bai amsa tambayoyinta ba. Gwiwa a sace Jalal ya shigo ɗakin. Cassy ta taso daga inda take zaune wani oversized red Tshirt ne a jikinta yanzu. """Cassandra"" ya kira sunanta." """I want to tell you something"" ya faɗa zuciyarsa na ƙuna saboda haushin kansa da ya ji na ɗaukan lokaci" "da ya yi bai faɗi gaskiyar ba, har sai da Ziyada ta yi masa kallon maƙaryaci." "Ta san me yake shirin faɗa shi yasa ta ƙwalalo idanunta waje ta ce ""She's not JUST a Chef, is she?""" "Jalal ya ɗaga murya ya ce ""YES""" """Oh Fuck!"" Cassy ta yi tugging gashinta baya da hannunta duka biyu har sai da jijiyoyin goshinta suka" bayyana. For a brief moment sai ta kasa magana. A baya tana da yaƙinin duk da basa tare Jalal ba zai taɓa cin amanarta ba. Jalal ba zai taɓa kwana da wata mace ba. Jalal ɗinta ba zai taɓa son wata mace ba. "Duk da ita ɗin ta sha cin amanarsa, musamman a cikin shekaru ukun da basa tare. Amma tana da yaƙinin" Jalal ba zai iya neman wata mace a bayanta ba. Irin yardar data masa kenan saboda ta jima da karantar halayensa. """You are cheating on me with her, right?"" Ta faɗa da ƙarfi" """She's MY WIFE, Maria"" ya katseta." Takowa ya yi kusa da ita yana sake tsanar kansa bisa walaƙanta Ziyada da yayi har ta kai ga ta ganshi yana kissing Cassandra. Da gaske har zuciyarsa ya gama auren Cassandra. Kuskure ne da ya faru saboda sakacinsa. Yanzu kam ko mai zai faru sai dai ya faru amma yana son kasancewa da Ziyada. """She's my wife"" ya sake maimaitawa" """I married her... Islamically""" """Fuck you! Jalol"" ta faɗa da ƙarfi har yawun data furzo yana taɓa fiskar Jalal." "Ta nuna shi da yatsa ta ce ""Fuck your ass!"" Sintiri ta fara yi a ɗakin. Chan ta tsaya ta juyo ta kalle shi ta" "ce ""I am your ONLY LEGAL WIFE, Jalol. And I will sue you for bigamy if you don't...""" """We are getting a divorce, Cassy"" ya katseta." "Maganar saki da ta ji ya sata faɗin ""What do you mean?"". Ta zaro idanu waje saboda ko a mafarki bata" taɓa zaton Jalal zai kawo maganar saki ba. "Aurensu ya jima da ƙarewa, rabuwar ne kawai ba su yi. Infact ba tun da ya dawo Nigeria bane auren" "nasu ya ƙare, daga lokacin da ya shalleka shawaran Hajiya ya auri Cassandra daga lokacin ne ya rasa farin cikin da ake samu na aure. Bai gama sanin cewa babu farin ciki a zamansa da Cassandra ba sai da ya auri Ziyada." "Yes, ta ɓangaren kwanciya Cassy tana bashi gamsuwa saboda ta san sirrin sarrafa namiji." "Akwai masu cewa akwai banbanci tsakanin HAVING SEX da mace da kuma MAKING LOVE. With Cassy, it" was just sex. Amma Ziyada... Ziyada ita ce komai. Ba jikinta kawai yake so ba. Gangan jikinsa da ruhinsa ne yake jin daɗin kasancewa da ita. Yanzu da ya fitar wa Cassandra gaskiya sai ya ke jin wani ɗaci yana taruwa masa a maƙoƙoro. Maimakon ya ji relief sai yake jin ɗacin abinda ya yiwa Ziyada. Yadda idanunta suka cika da shock da kuma nadama ranan da ya kirata da JUST A CHEF. Da kuma yanzu da ta tabbatar masa da ta haƙura da aurensa. "Da dai zai iya mayar da hannun agogo baya, da zai kirata da Matarsa. Zai tabbatarwa Cassandra cewa" Ziyada Matarsa ce. Da ya yi hakan da ba za a zo gandun da Ziyada za ta kalleshi yana kissing Cassandra ba. Kallon Cassandra ya yi ya ce mata ta riga ta san aurensu ya ƙare tun da jimawa. """What about your promise to me, Jalol?"" Ta katse shi tsoro bayyane a fuskarta." """I kept my promise, Cassy. "" ya bata amsa. Ya mata alƙawarin zai aureta a lokacin da yake tunanin shi ya" yi sanadiyar zubewar cikinta. "Ya cika alƙawarinsa tunda alƙawarin aure ya mata, kuma ya aureta yau aure shekara goma da watanni." Dan haka ba za ta tuhumeshi da rashin cika alƙawari ba ai. """You promised to never leave me, Jalol. That was your promise"" ta ƙarisa maganar hawaye na zubo mata." So take ta guilt tripping ɗinsa kamar yadda ta yi farkon haɗuwarsu. Cikin da ya zube ba nasa bane. Amma ta manna masa ta saka shi tsanar kansa har ya mata alƙawarin zai aureta saboda ya kula da ita. Shi yasa da ta ga ya damu da cikin ta ƙi yin planning a farkon aurensu. Allah ya taimaketa a wata huɗu da auren nasu ta samu cikin Junior. Bai ce mata komai ba kawai ya tsaya kallonta. Hakan ya sake kashe mata jiki. Mutumin da ta ke kallo ba "Jalal ɗin da ta sani da bane. Jalal ɗin baya yana da rauni. Yana tsoron ɓatawa mace rayuwa. Wannan da ke gabanta namijin da ya ke da zaɓi ne, kuma a yanzu ya zaɓi wata mace daban ba ita ba." Ganin fa emotional blackmail ba zai yi mata amfani kamar da ba sai ta fara masifar cewa ita kaɗai ce legal wife ɗinsa kuma ta san haƙƙinta. Idan bai fitar da Ziyada daga rayuwarsa ba to zata tafi da ɗansu. Ta ce idan ta tafi da shi kuwa ba zai sake ganin ɗansa ba har abada. """You dare not, Cassandra"" Jalal ya faɗa da muryar mutumin da ya shirya bawa ɗansa da kuma matarsa" ta sunna kariya. "Ficewa ya yi daga ɗakin. Cassandra ta bi bayansa tana kiran sunansa ""Jalol, Jalol"" amma bai kulata ba." Tsayawa ta yi jikin stairs tana huci. Ba za ta yarda da divorce ba. Divorce a yanzu zai ɓata mata suna ne ya kuma saka brand ɗinta cikin matsala. Bai jima da aka kamata da laifin tuƙi cikin maye ba wanda sai da ta biya tara sannan aka saketa. Duk Lawyanta da kuma PR team ɗinta sun yi ƙoƙarin ganin maganar bata fito ba idan Jalal ya ji labari zai iya amfani da hakan wajen samun hujjar gabatarwa a kotu dan a raba aurensu. "Bayan maganar tabbatar da auren Jalal da ta zo yi Nigeria, babban dalilinta na zuwa Nigeria saboda case" ɗin da aka yi da ita ya lafa ne kafin ta dawo. Ta san abinda za ta yi. Ɗauke Junior za ta yi. Idan ta tafi da shi Jalal zai dawo hayyacinsa ya dena maganar zai saketa. *** CHAPTER FIFTY TWO ZEEY Fiskata na kalla a madubi. Fiskata ne shaidar abinda na gani jiya da dare ba mafarki bane. Ba zan iya tuna "yaushe bacci ya ɗaukeni ba. A daren na haɗa kayana a cikin akwati. Daga nan kuma sai na yi sallah na kaiwa Allah kukana. Tabbas na tafka kuskure, na yi wasa da sunnar Ma'aiki (SAW). Tun a wajen neman aure na tafka kuskure. Ta ya zan amince na ƙulla yarjejeniyar aure saboda wata manufa daban ta neman duniya. Wataƙila wannan dalili yasa abubuwa suka yita kwaɓe mini daga sadda aka saka auren har zuwa yanzu." Na fita daga sharrin Alhaji Nafi'u da ƙyar yanzu kuma na shiga wata jarrabawar ta yaudara dana gani ƙarara a gurin Jalal. "Shi ga shi mai wayo, yana son Baturiyarsa, amma yana mini ƙaryar zai rabu da ita. A halin dana ke ciki" "yanzu Aurena ba shi da Guarantee a wajen Jalal. Idan kuwa haka ne gara na koma wajen Allah na nefi yafiyarsa sannan na riƙe sana'ata da mahimmanci, wannan shine mafita a gareni koda Jalal ya nemi rabuwa da ni." "Na jima ina yiwa Gidan Girki Restaurant addu'a, dan business sai da roƙon Allah." Ɗan baccin dana samu yi kaɗan ne kafin alarm ɗina na ƙarfe huɗu da rabi ya tasheni. Daga nan kuma na sake shiga banɗaki na iho wata alwalar na yi sallah raka'a biyu na kama salati. Yanzu da nake kallon kaina a madubi sai na ke ganin anya idan na je gidan Hajiya a haka ba zan ɗaga mata hankali ba?. Na kalli akwatuna biyu manya dana cika da kaya sannan na sake kallon kaina ta madubi. Tabbas da an kalli fiskata an san babu lafiya. Ban gama tsaida shawarar in tafi ko kar in tafi ba aka fara buga mini ƙofa da ƙarfi. Bugun matar gidan ne bana Yallaɓai Jalal ba. Har zan share sai kuma na ce gara dai na fuskanceta na ji da wata tsiyar ta sake zuwa mini. Miji dai na bar mata ta je ta ji da shi. "Ina buɗe ƙofar na ganta sanye da wani shegen guntu riga iya gwiwa, rigar babu hannu, gashinta ya yi" "buju-buju, make-up ɗin fiskarta duk ya zazzago. Warin giya ne ya bugo ni." Ta nuna ni da yatsa tana gyara tsayuwarta da alama giyan da ta sha bai saketa ba. """HE'S MINE"" ta faɗa da ƙarfi." """Jalol is MINE""" Ta fara karanto mini tarihin soyayyarta da Jalal. Yadda Jalal yake matuƙar sonta har ya bijirewa "mahaifiyarsa ya aureta. Ta kira ni da kalmar Karuwa, ta ce ban isa na rabata da mijinta Jalol ba." Daga ƙarshe ta fara yi mini kashedin wai na tattara kayana na bar gidan sannan na fita daga rayuwar "Jalal idan ba haka ba zan yi sanadiyyar da Jalal zai rasa ɗansa, kuma na san yadda Jalal ya ke son yaronsa." Ban ce mata uffan ba. Babu amfanin tanka ma 'yar giyar da giya bai gama sakinta ba. Rufe ƙofar na yi tana cikin magana. Ta cigaba da buga ƙofar da ƙarfi tana kirana da 'Bitch'. Ƙarshe sai na ji ta koma kiran sunan Jalal da ƙarfi. "Bayan abinda na gani jiya, babu wani sabon abu da za a yi da zai sake ɓata mini rai, dan haka haukar" Cassandra ko kaɗan bai ɗaga mini hankali ba. Gida ne dai ko bata faɗa ba zan bar musu gidan su je can su ƙarata tsakaninsu. Lokacin dana fito da Akwatunana sai na ga ba zan iya jansu zuwa ƙasa ta daɗi ba wannan ya sa na ɗaga ɗaya na fara saukowa da shi ina tafiya a hankali saboda takalmin dana saka yana da tudu sosai. Ban kai ƙasa ba na ganshi yana kawowa saman. Yana zuwa ya karɓi Akwatin daga hannuna. Maimakon ya yi ƙasa sai na ga ya koma sama. """Gidan Hajiya zan wuce"" na faɗa ina bin bayansa. Da gaske fa ba zan cigaba da zama da shi a gidan nan" ba. A ƙofar ɗakina ya ajiye Akwatin. Ya sa hannu zai buɗe ɗakin ya jita a rufe. """Na faɗa maka gidan Hajiya zan koma""" Sai a lokacin ya ɗago ya kalleni. Jajayen idanunwansa da suka ƙanƙance kamar na 'yan China ne suka nuna shaidar rashin bacci a fiskarsa. """Ki buɗe"" ya faɗa yana kallona da wani sanyin da yake roƙon in tausaya masa. Na kawar da kaina gefe." Na gama jin tausayinsa. Fiska biyu gareshi. """Key"" ya faɗa yana miƙa min faffaɗan hannunsa." """Please"" ya marairaice ganin na ƙi bashi key ɗin. Sai a lokacin na fito da key ɗin daga purse ɗina na buɗe" ɗakin muka shiga. """Ba zan hanaki tafiya ba"" ya faɗa bayan ya kai min Akwatunan wajen closet." """Hajiya tana da baƙi a gidanta. Idan kika je a haka hankalinta zai tashi"" ya faɗa yana kallona." Jallabiyar jiya ne a jikinsa sai dai yanzu ya sakata da kyau ba kamar jiya da ya saka a juye ba. Sai dai yadda take a cakuɗe ma ya nuna tun jiyan bai cireta ba. Na ɗauke idanuna daga fiskarsa dan haushinsa nake ji. Ban ankara ba ya kamo hannuna. Wani shock na ji amma sai na danne tasirin hakan na kafe shi da idanuna. """Ina so ki sani Gidan Girki Restaurant naki ne""" Ya sa hannunsa ɗaya ya tallafo fiskata. """I'm wishing you best of luck, Sunshine""" "Ya shafa kumatuna da babbar yatsarsa ya ce ""Allah ya sa miki Albarka a wajen""" Amin ɗin dana faɗa ya yi dai dai da cire hannunsa da na yi daga fiskata. Idanunsa suka wani marairaice alamar in tausaya masa. """Zan wuce"" na faɗa bayan na matsa daga gefensa" Ya buɗe baki kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru. Muka tsaya kallon juna. "Can sai ya ce ""Idan kin shirya, Abdullahi zai kai ki""" "Daga haka sai ya fita, na bi bayansa da kallo ina jin zuciyata na min wani zafi..." *** "Ƙarfe tara na safe aka buɗe JK Plaza, muma a lokacin ne muka buɗewa ɗimbin Jama'ar da suke shigowa" Plazar ƙofar Gidan Girki. Duk da halin da na ke ciki cikowar da Restaurant ɗin ya yi da yadda ake shige da fice a wajen sai ya ɗauke min damuwar dake zuciyata. Na mayar da hankalina kan kula da yadda staff ɗina suke tafiyar da komai. Kafin ƙarfe shaɗaya ma breakfast menu ɗinmu ya ƙare. Har an kusa fara serving lunch. Wajen ƙarfe shabiyun ne kuma Hajiya ta shigo Restaurant ɗin. Office ɗina Janan da ke ta up-and-down "tun safe ta kawota. Ta yi mini Addu'ar Allah ya sawa wajen Albarka. Ita da wasu ƙawayenta guda biyu da wata da ta ce matar ƙaninta ne suka kama table suka bada order abinci. Abinka da uwar miji ni da kaina na karɓi order na zo na serving ɗinsu. Hajiya tana faɗin ya haka na ce mata babu komai, Special Customer Service nake bata. Mutanen dake tare da ita suka sa dariya." Lokacin dana koma office ɗina ne wasu 'yanmata guda biyu suka shigo. Ɗayar kaman na taɓa ganinta a "lokacin bikina, ina ga 'yar uwarsu Janan ce" """Madam Chef Chef"" ta faɗa tana wani kwashewa da dariya. Itama yarinyar da suka shigo taren dariyar ta" saka. Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina na cigaba da danna Laptop dake ƙaramin desk ɗina. Na ɗan iya Computer tun a hutun JSCE da muka yi da nake karɓan Laptop ɗin yaya Aminu nake kallo. Lokacin dana ke ta fafutukar karatun JAMB kuma yaya Aminu ya sake koya min saboda CBT ne Jamb ɗin. Jiya dana shigo Jide ya nuna min yadda zan yi amfani da Software ɗin da aka saka dan na riƙa tracking "duk abinda yake faruwa a restaurant ɗin, tun daga shigowar kuɗi da fitarsa. Yanzun ma ina ƙara bibiyar Software ɗinne saboda ban gama ganewa ba waɗannan ƙananan yaran suka shigo. Duk su biyun babu wacce za ta yi shekara ishirin a cikinsu. Shi yasa wani falli da suke bai dameni ba." """Idan babu abinda ya kawoku please ku fita min daga office aiki nake yi""" Yarinyar dana ke tunanin 'yar uwarsu Janan ce ta kwashe da dariya har da tafawa. """Ku jita fa. Har ke za ki ce mu fita daga office. Kin san alaƙar dake tsakanina da yaya Jalal?""" """To barin gaya miki ni ƙanwarsa ce. Kuma na san ya aureki ne dan ki kula masa da wannan Restaurant" "ɗin, baki da wani matsayi a wajensa""" "Ta kalli ƙawarta ta ce ""In faɗa miki a gaban Matarsa Cassandra ya kirata da JUST a Chef"" suka ƙyalƙyale" da dariya. """Sharifa!"" Janan ta shigo office ɗin ranta a ɓace." """Sharifa, dama ke kika faɗawa Cassy yaya Jalal ya yi aure?""" Rarraba idanu ta fara yi ganin babu wasa a fiskar Janan. """Answer me!"" Janan ta daka mata tsawa." """Sai me dan na faɗa. Ai dama na san ɓoye mata aka yi saboda munafurci""" """Saudah ce ta saki?""" """Babu ruwan Anty Saudah da wannan""" Na baza ido kawai ina ganin dramar su. Ƙarshe dai Sharifa da ƙawarta suka fita suna ɓaɓɓata fuska bayan Janan ta ce za ta kai ƙaranta wajen Uncle Idris. "A yadda na fahimta, Sharifar ƙanwar Saudah ce." """Don't mind them please"" Janan ta faɗa bayan fitarsu. ""Sharifa bata da hankali Wallahi, ƙanwar Saudah" "ce. Kin san Cousin ɗina Saudah ai?""" Na gyaɗa mata kai. A wajen Hassana mai aikin Hajiya na samu gulmar Saudah. Ita ce ƙanin Jalal zai aura Allah ya masa rasuwa sati biyu kafin auren. Daga baya kuma Hajiya ta ce Jalal ya aureta amma sai ya ƙi. I guess saboda baya son auren Saudah shi yasa ya zo mini da maganar auren deal. Ni sai yanzu ma nake "ganin wautata, tun farko ni ɗin ban dace da Jalal ba. Ya zaɓe ni ne saboda ya samu damar cimma burinsa ba tareda ya sha wahala ba. Ai da 'yar uwarsa Saudah ya aura da ba zai mata walaƙancin da yake mini ba. Ai ba za ma ta yarda ya walaƙantata a gaban Baturiyarsa ba. Ni ɗin ce dai ya renawa hankali, saboda bani da gata." Na yi mamakin yadda Janan ta ke ta bani haƙuri duba da cewa baki da baki ta ce min bata sona. Koda "yake ta faɗa mini dalilin da ya sa ta ce bata sona ɗin. Da gaskiyarta, ni ɗin Local ce. Wataƙila hakan na daga cikin dalilin da ya sa Jalal yake rena mini hankali. Yana tunanin idan ya shirya mini zance ya mini daɗin baki zan yarda da shi har ya samu kaina." Wataƙila ma nufinsa idan ya samu kaina ya gama marmarina ya ga na gundureshi mayar da ni Ghetton da ya ɗaukoni zai yi. """Wata Aunt ɗin Khalifah ce ta zo siyayya a plaza shine na ce ta shigo Gidan Girki ta ci abinci"" Janan ta" katse ni. """Please ki sa a kawo musu best abincin dake Menu ɗinku, ita da yaranta suka zo""" Tashi na yi ta bi bayana. Na lura dai ba ƙaramin so take yiwa Mi Amor ɗinta Khalifa ba. Kitchen na wuce na yiwa Bisola magana na ce a serving ɗinsu White rice da Classic Jajjage Sauce. "Lokacin dana leƙa hall ɗin Restaurant ɗin sai na ji wani daɗi ya mamayeni, ta ko'ina mutane ne. Addu'ata" shine kamar yadda mutane suka mana tururuwa a ranan farko Allah ya sa kasuwa ta cigaba da ɗorewa a haka. Wajen ƙarfe shida saura na yamma Jide ya shigo office ɗina. Maganar cinikin da muka yi a yau ya mini. Ya ce idan muka cigaba da samun irin numbers ɗinnan kafin "shekara zai tara kuɗin aure. Na yi dariya na ce shi burinsa kuɗin aure, ni kuma burina idan Gidan Girki ya haɓaka za mu buɗe branch ne a Abuja da Kano, har Lagos." Jide ya ce very soon kuwa za mu kai haka. For now dai aiki za mu cigaba da yi muna haɗawa da addu'a saboda wannan sabon waje da ya tara ɗimbin Jama'a yau ya cigaba da cika kullum. Hakan shi zai sa mu cimma dogon burinmu na buɗe rassan Gidan Girki a wasu garuruwan. Bayan mun gama reviewing cinikin yau sai na tattara kayana na yi musu sallama. Na shiga Kitchen na musu jinjinar ban gajiya saboda da ni da su ɗin duka mun sha aiki. "Lokacin dana fito mutane sun ragu a Plazar, ba kaman cikowar da aka yi daga safe zuwa ƙarfe huɗu na" yamma ba. "Lokacin dana iso gida ko'ina shiru. Da ƙyar nake taka stairs saboda gajiya, dukkan jikina ke mini ciwo, ga" uwa uba kaina dake sarawa kamar zai rabe biyu. Wanka na yi da ruwa mai zafi na yi Alwala na fito. Ina idar da Sallar Magariba na kwanta akan Sallaya jikina na ɓari. A daddafe na miƙe lokacin da Isha ta yi na tada Sallah. Da ƙyar na dragging jikina na hau gado na lulluɓu da bargo saboda wani sanyi dana ke ji. Ina kwanciya zazzaɓi ya rufeni ni kaɗai sai rawar sanyi nake a cikin bargo. Akwai First Aid Box a banɗakin Jalal amma ba zan iya tashi bama balle na je ɗakin na dubo magani. Ba "ma zan sake shiga ɗakinsa ba, kar na ci karo da abinda zai ɗaga mini hankali." JAYKAY A gajiye Jalal ya shigo gidansa ƙarfe tara na dare. Da safe yana shirin fita wajen buɗe Plaza Cassandra ta tsare shi da maganar ba ta yarda da maganar saki ba. Ba za ta bashi saki ba saboda har yanzu tana sonsa. Har da cewa za ta yafe mishi cin amanarta da ya yi amma dole ne ya kori Ziyada daga gidan ya kuma cireta daga rayuwarsa. Sake jaddada mata rushewar aurensu ya yi tareda faɗa mata hukuncin da ya yanke shine dai-dai. Idan ta bashi haɗin kai divorce proceeding ɗinsu zai tafi da sauƙi. Ai kuwa Cassandra ta haukace masa akan bata san zance ba. Ta cigaba da iƙirarin ba za ta taɓa rabuwa da shi ba. A haka ya fita daga gidan ya barta tana ta hauka ita kaɗai. Ɗakin Ziyada ya buɗe a hankali ya hangota lulluɓe cikin bargo tana bacci. Ƙarisawa ya yi bakin gadon ya "ƙura mata idanu. Ɗan gyara mata bargo ya yi saboda ya ga kamar tana zufa. Ta kashe AC ɗin ɗakin, sai ya yi tunanin ko sanyi take ji ya sa ta kashe. Manna mata kiss ya yi a kumatu da goshi sannan ya fita daga ɗakin. Yana son kwanciya kusa da ita, amma ya san idan ta buɗe ido ta ganshi ranta zai iya ɓaci tunda fushi take da shi." Zai bata space ne zuwa lokacin da za ta sassauta fushinta. Spare room dake sama da ya ajiye wasu daga cikin kayansa yau da safe ya shiga. Wanka ya shiga ya sakewa kansa ruwan zafi. Lokacin da ya fito sai ya ga missed call ɗin Hajiya har guda biyu. Zama ya yi a bakin gado ɗaure da towel a ƙugunsa ya dannawa Hajiya kira. """Muhammad zai kwana a wajenku ne?"" Ta tambaya bayan ya amsa sallamarta." """Muhammad ya zo nan ne?"" Ya tambaya cikin rashin fahimta" """Kai zan tambaya ai. Tunda muka dawo daga Plaza da ya ce zai je gidanka ban sake saka shi a idona ba." "Na ce ko wajen Mamansa zai je shi yasa ban hana shi ba""" Miƙewa Jalal ya yi bugun ƙirjinsa na ƙaruwa ya nufi hanyar ɗakinsa. """Hello, kana jina?. Hello, Hello""" Kasa motsawa ya yi daga inda yake tsaye ganin babu Akwatunan Cassandra a ɗakin. Da ƙyar ya ƙarisa wajen da ya ke ajiye mahimman takardunsa da passport ɗinsa ya buɗe ya ga wayam babu Passport ɗin ɗansa Muhammad. Subhanallahi! Cassandra ta gudu masa da yaro... CHAPTER FIFTY THREE *** Nambar Cassandra Jalal ya shiga kira amma numbar bata tafiya. A haukace ya fito daga gidan bayan ya saka Jallabiyarsa. Wajen Maigadi ya nufa yana tambayarsa yaushe Cassandra ta fita daga gidan?. Maigadi ya ce masa wajen ƙarfe uku na rana ne. """Ita da Muhammad suka fita?"" Ya tambaya da ƙarfi." """Eh, Yallaɓai"" Maigadi ya amsa a tsorace." """Shit!""" """Yallaɓai, lafiya?""" """Ina Abdullahi?""" """Ya tafi gida, Yallaɓai""" Jalal ya koma ciki a rikice. Key ɗin mota ya ɗauko ya fita daga gidan da gudu. Yana tuƙi yana sake gwada numbar Cassandra. Sai da ya yi nisa ne ma ya fara tunanin ai bai san takamaimai inda zai nemeta ba tunda numbarta ba shiga yake ba. Kiran Hajiya ne ya shigo wayarsa. Hankalinta ya tashi. Jiki a sanyaye ya ɗau kiran. """Jalal ina ta magana ka kashe wayar. Ina Muhammad yake?""" "Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce ""Cassandra bata nan. Na duba babu Passport ɗinsa""" """Subhanallahi!. Garin yaya ka bari ta ɗauke Passport ɗinsa?""" Ya yi shiru bai yi magana ba. """Tunda ta ɗau Passport ɗinsa kam kaima ka san London za ta kai shi. Ai shikenan... Mu kwana lafiya""" Yadda ta kashe wayar cikin fushi ba ƙaramin ɗaga masa hankali hakan ya yi ba. Ganin babu amfanin fitarsa sai ya dawo gida. A falon ƙasa ya zauna ya kira wani IT Staff ɗin office ɗinsa "ya ce ya bincika masa ko Jirgi ya tashi daga Abuja zuwa London a daren yau, sannan ya duba masa" sunayen Passengers ko akwai sunan Cassandra da kuma yaronsa. Cikakken sunansu ya tura masa ya zauna yana jiran bayani daga wajensa. Bayan kusan minti arba'in sannan aka kira shi aka tabbatar masa da cewa Cassandra da ɗansa suna "hanyar London a yanzu haka, dan Jirgin ƙarfe bakwai na yamma suka shiga daga Abuja..." Bai iya bacci a daren ba. Tunani ne kala-kala suka cika masa kai. Washegari da sassafe ya wuce gidan Hajiya bayan ya leƙa ɗakin Ziyada ya ga tana bacci. A ɗaki ya sameta tana Azkar. Ya gaisheta jikinsa a sanyaye. """Hajiya, a yi mana addu'a zan wuce Abuja, na booking flight zuwa London ƙarfe uku""" "Hajiya ta tsaida carbin da take ja ta ce ""yanzu idan ka je can ɗin kana ga za ta yarda ka dawo da yaron" "cikin sauƙi ne?. Tun yaushe ya kamata a ce ka nemi sole custody ɗin Muhammad. Da yanzu kai ne da Custody ɗinsa ai da ba za ta samu damar kidnapping ɗinsa haka ba""." """Dama abinda nake jiye maka kenan ga shi an zo wajen. Kai komai naka babu tsari. Da tuni ka rabu da" "shegiyar yarinyar nan da an riga an wuce wajen. Ni dai ka saurareni da kyau. Ba zan sa baki a aurenka da Cassandra ba, amma zaman Muhammad a wajenta ba zai yiwu ba. Ka dawo min da jikana gidan nan""" Zuciyarsa ne ya karye da maganganun Hajiya. Tabbas ta ji zafin abinda ya faru. Ita ce ke kula da Muhammad tunda ya kawo shi Nigeria. Zaman yaron kaɗai a gidan ya cirewa Hajiya yawan tunani. """Is bad enough ka aurota"" Hajiya ta cigaba da faɗa. ""Yanzu yaron da nake Alfahari da ƙoƙarinsa a" "Islamiyya shine za a mayar da shi London inda ko Sallah ba kwa bari ya yi""" """Sanda ka kawo yaron nan ko Alwala bai iya ba balle ya san menene Sallah. Idan ba dan Jamal bama da" "ina ga..."" sai ta yi shiru." Once again ta sake nuna gazawarsa. Wani lokaci idan ta nuna masa hakan sai ya yi tunanin da za a bata zaɓi a ce mata wa za a ɗauke wa za a bar mata a cikin shi da Jamal. Babu makawa ya san da yanzu shine a cikin ƙasa ba Jamal ba. """Insha Allahu zan karɓo Muhammad"" ya faɗa a raunace." """Ba maganan karɓo shi bane. Idan ka ce ba zaka raba alaƙarka da Cassandra ba to ko ka karɓo" "Muhammad ka riƙe shi a wajenka""" Miƙewa ya yi jiki a sanyaye ya fito daga ɗakin Hajiya bayan ya mata sallama. Ji ya yi ya tsani kansa. Ji yayi tarin shekaru kawai gareshi amma ba shi da basirar yadda zai tafiyar da rayuwarsa bisa tsarin da zai farantawa mutanen da ke kusa da shi rai. Ga Ziyada tana fushi da shi. Ga Hajiya da ta sake tabbatar masa da abinda ya jima da sani. Tun ranan da ya auri Cassandra ta ke jin haushin aurensa har yanzu abin na damunta. Ga shi saboda sakacinsa Cassandra ta samu damar tafiya da Junior. Tambayar kansa ya fara yi. Me ya sa tun farko da ya ajiye aikinsa ya dawo Nigeria bai nemi rabuwa da Cassandra ba sai yanzu da abubuwa suka kwaɓe masa?. Dalilin hakan kuwa TSORO ne. Shi ɗin MATSORACI ne. TSORO ne ya banbanta shi da Jamal. A yayinda ya bari tsoro ya saka shi auren Cassandra. Tsoron ne kuma ya hana shi rabuwa da ita har yanzu. Yana tsoron mai zai faru idan ya rabu da ita ba tareda ya shirya komai na rabuwar ba. "Ya sani da Jamal ne da tuni ya jima da rabuwa da Cassandra, kuma ya cigaba da riƙon ɗansa ba tareda" tsoron komai ba. "A halin yanzu ba zai iya rasa mutane uku da suke da mahimmanci a rayuwarsa ba. Ziyada, Junior da" kuma Hajiya. Zai fara da Ziyada. Zai sake roƙonta ta bashi dama ko zai samu sassaucin ƙuncin da zuciyarsa ke ciki. *** Tea take sha tana duba wayarta lokacin da ya shigo ɗakin. Tsayawa ya yi bai yi magana ba. Ta ɗago ta kalleshi. Da alama tafiya zai yi dan har da ɗan jakarsa a hannu. Idanunsa ta kalla ta ga yadda suka yi rami. Cikin ɗan sakannin da ta yi tana kallon fiskarsa kafin ta kauda kai har wani tsufa ta ga ya mata. Yanayin Idanunsa kaɗai manuni ne na irin damuwar da ke cinsa. """Zan wuce Abuja"" ya furta mata a hankali. Yadda ta yi halin ko in kula da shi ya nuna masa bata san" abinda yake faruwa ba. """Cassandra ta tafi da Muhammad"" ya mata ƙarin bayani." Sai a lokacin ta ɗaga ido ta kalleshi. Tiririn shayin da ta gama kurɓa ya saka mata zufa a saman bakinta. """Allah ya kiyaye hanya"" ta faɗa a hankali sannan ta sake kurɓan tea ɗin." """Idan na je zan iya jimawa saboda zan shigar da ƙara a bani full custody ɗinsa""" """Allah ya bada sa'a""" Yadda take masa magana ɗaɗɗaya-ɗaɗɗaya cikin halin ko in kula ne ya breaking ɗinsa. Already maganganun Hajiya sun riga sun karya masa zuciya. "Ba zai iya tafiya a haka tana ɗaure masa fiska ba. Koda ba zata yafe masa a yanzu ba, gara ya warware" mata iya gaskiyarsa Ajiye jakarsa ya yi ya ƙaraso inda ta ke. Ta yi saurin juyawa tana kurɓan shayin da sauri har yana ƙona mata harshe. "Kamo hannunta ɗaya ya yi ya ɗaura akan ƙirjinsa ya ce ""ban san yaushe kika shiga nan ba""." Ta ƙura masa idanunta yayinda bugun ƙirjinta yake ƙaruwa. """Kin jima da samun masauki a zuciyata, Zeeyadah. Barin faɗa miki wani abu yau, da baki amince da deal" "ɗina ba, da zan sake nemo wata hanyar da zan samu damar aurenki...kin san saboda me???""" Shiru ta yi masa hawaye na taruwa a idanunta. """Saboda INA SON KI, Zeeyadah. I Love You so much, Sunshine""" Ɗago fiskarta ya yi yana so ta kalli ƙwayar idanunsa ta ga gaskiyar da yake faɗa mata. "Hawaye ne suka fara zubo mata, ta kai hannu za ta share ya rigata yin hakan." """Zan baki lokaci. Nima kuma zan yi abinda ya dace. Wannan karan ba alƙawarin ƙarya zan miki ba." "Wannan karan na shirya rabuwa da Cassandra...""" """Sai da ta gudu maka da ɗanka shine zaka ɗau mataki?... ai baka burgeni ba tunda ba komawa zaka yi" "London ɗin da zama ku tare a can ba. Afterall cewa ta yi soyayyar da kake mata ya sa ka aureta duk da Hajiya bata so. Nima kuma na gani da idanuna tunda...""" Hannu ya sa ya rufe mata baki da yatsarsa. """Please..."" bai bata damar magana ba ya rungumeta jikinsa sosai yana fitar da numfashi da ƙarfi." Ƙoƙarin janye jikinta take da ƙarfi amma ta kasa. """Kada ki sa na tafi da ɓacin rai, Zeeyadah. I'm in too much pain already"" ya raɗa mata a kunne." Shirun da ta yi ya saka shi rankwafo kansa zai kissing ɗinta ta yi saurin rufe bakinta. """Please...""" Kuka ta saka masa lokacin da ya fara kissing wuyanta. """Ka je ka samu matarka. Ka je ka samu Baturiyarka, farar fata wacce ta iya soyayya"" ta faɗa cikin kuka." """I want you, Sunshine... ke nake so ba Cassy ba, only YOU"" bai bari ta yi magana ba ya shiga kissing ɗinta" "sosai, duk yadda take ƙoƙarin zille masa ya yi mata kane-kane." Lokaci guda ya birkice mata ya fara ƙoƙarin rabata da kayan jikinta. Ƙoƙarin kare ƙirjinta ta ke amma bai bata damar hakan ba har ya kai bakinsa wajen. "Har ya ɗauketa daga ƙasa, har ya kaita kan gado har ya fara cire nasa rigan hawaye ne a idanunta." "Babu abinda yake faɗa mata a duk lokacin da ya raba bakinsa daga jikinta sai ""I'm Sorry"" da ""I love you""." Tun tana resisting ɗinsa har ta sake masa jikinta ta sadaƙar Jalal ba ya cikin hayyacinsa balle ya sarara mata. """Please, kar ki ce a'a"" ya faɗa idanunsa cike da tsananin buƙatarta da kuma tsoron cewa idan ta hana shi" a wannan lokacin bai san ko zai iya haƙura ya barta ba. He wants her. And he wants her NOW! "Yanzu yake buƙatarta, saboda nitsuwar da zai samu a wajenta ya sassauta masa tashin hankali da kuma" ƙuncin da yake ciki. """Zee...ya...dah?"" Ya kira sunanta da sigar magiya. Har yanzun yana tsakiyar cinyoyinta ne sandarsa na" harbawa da ƙarfin bugawar da zuciyarsa ke yi a ƙirjinsa. Izininta ya ke jira ya shiga ko kuma ya hana kansa abunda ilahirin jikinsa ke so. Ganin ta yi shiru ta rufe idanunta sai zuciyarsa ya karaya. Hawaye suka taru a idanunsa. Ya ja dogon numfashi zai sauka daga kanta sai ya ga ta ɗan ware masa cinyoyinta. Hakan da ta yi ya saka shi ɗan tallafo kanta ya manna mata kiss yayinda yai Bismillah a zuciyarsa... """Let me know if you're feeling Pain in any way, kin ji?""" """should I...should I go slower? Ya faɗa amma movements ɗinsa bai nuna alamun zai sassauta mata ba." Ruɗewa ya yi. Yana so ya bita a hankali amma baƙon yanayin da ya tsinci kansa ya hanashi sarrafa kansa cikin sauƙi. Cassandra ce farkonsa. Bayan ita bai sake taɓa wata mace ba sai yanzu. Yadda take cize leɓenta ya nuna masa tana jin zafin abinda yake mata. Amma ba zai iya hana kansa "abinda yake mata ba, wannan ya saka shi ja mata wuridin 'Sorry da I'm Sorry"" wanda ko ɗaya kalmomin da ya ke faɗa bai rage mata zafin da take ji ba..." ZEEY "Shikenan, yau Jalal ya raba shamakin dake tsakaninmu." Kalmar 'Thank you' da ya dinga faɗa mini kafin bacci ya ɗauke shi bayan abinda ya wakana ne ya tsaya "mini a rai. Tambayar kaina na fara yi, minene makoman aurenmu?" Mi zai faru idan ya je London Matarsa ta ce ba za ta bari ya ga ɗansa ba har sai ya sakeni?. Ni na san da Cassandra bata tafi da Junior ba da ba zai ce zai rabu da ita ba. Mutumin da yake son rabuwa da mace zai yarda ya sake zama gida ɗaya da ita ne balle har ya kissing ɗinta?. Zame jikina na yi daga riƙon da ya mini na wuce banɗaki dan na tsarkake jikina. Yanzu kam ya samu abinda yake so shikenan zai je London ya samu Cassandra su cigaba da soyayyarsu. "Haka ya min ranan ai, daga neman alfarman sati biyu zai rabu da Cassandra sai ga shi yana kissing ɗinta kamar ma'auratan da ke tsakiyar HoneyMoon. Yanzu ma wa ya san me za su yi idan ya je can." Waɗannan tunanin ne suka cika min zuciya a lokacin da nake gasa jikina da ruwan zafi. Na sha baƙar wahala a hannun Jalal. Sai dai ba haka na so ba. Ba haka na so farkonmu ya kasance ba. Har yanzu ina jin haushinsa a raina. Na kasa goge abinda na gani. Na amince masa ne saboda ni matarsa ce. Idan na ce masa a'a a lokacin da ya nemi yardata na san Allah zai kamani da haƙƙinsa. Hawaye ne suka zubo mini. Idan na ce zan manta da komai na rungumi Jalal a duk yadda ya zo min zuciyata za ta takura. Ni yanzu ban san gaskiyarsa ba. Ban san wannene gaskiya ko yaudara a cikin kalamansa ba. Wataƙila kuma na san gaskiyar amma kishin dana ke ji ne ya hanani yarda da gaskiyar ta sa. Kuka na fara yi a banɗakin. Jin ana taɓa ƙofar sai na share hawayena na cigaba da wanka. Lokacin dana fito daga banɗakin Boxers ne kawai a jikinsa. Na yi saurin kau da kaina. Zuwa ya yi ya rungumeni ta baya. Ya sa kansa a wuyana yana shaƙar ƙanshin Coconut body wash dana yi amfani da shi. """Shine ba ki tashe ni na zo na yi miki wanka ba"" ya faɗa yana manna min soft kissess a bayana." """Thank you"" ya faɗa yana rungumeni tsam a jikinsa." """Zan bar tafiyata sai gobe. Ki yi haƙuri zan tafi na barki da jinya. I'll make things right and come back for" "you, kin ji""" Barin jikinsa na yi na juyo ina kallonsa. Saka hannu ya yi a kafaɗata fiskarsa ɗauke da wani nitsuwa da fara'ar da babu ita awa biyu da suka wuce da ya fara shigowa ɗakina. """Tunda ka samu abinda kake so, ina ga ba sai ka takura kanka ba, idan ka ga zamanka a London zai" "faranta mata rai kawai ka yi zamanka a can""" Idanunsa ne suka tsaya cak akan fiskata. Mamakin kalamaina ne suka bayyana a fiskarsa. Annurin dake fiskarsa ya fara gushewa. Ganin ya kasa magana sai na cigaba da magana ina hawaye. Na sani hawayen da ban yi ɗazu da yake gurzana bane suka samu daman zubowa yanzu. """Dan ka ce kana sona ba shi zai goge son da kake yiwa ɗaya matarka ba. Na san dai yanzu kam" "hankalinka ya kwanta ka samu abinda kake nema ba wani abin da zai sa ka dawo Nigeria idan ka tafi London. Wa ya sani ma ko wani shiri ne ka yi kai da matar taka saboda ku tattara ku koma can London ɗin da zama. Tana can, ɗanka na can ai babu abinda zai zaunar da kai a Nigeria""" Buɗe baki ya yi zai min magana sai numfashinsa ya tsaya cak ya kasa magana. Muryarsa a karye ya kira "sunana ""Zee...ya..dah!!!""." """Amma..."" sai ya kasa magana." Na sani iya gaskiyarsa ya faɗa mini ɗazu. Amma ba zan iya yarda da dukkan gaskiyarsa ba. Na sani kishi "ke cina. Kishinsa, kishin Matarsa wacce yake gudun ɓacin ranta sama da nawa." Wataƙila hawayen da na ke yi ne ya sa shi ɗaukan kalamaina a matsayin gaskiyar dake zuciyata. "Maimakon ya sake rungumeni ya bani haƙuri. Maimakon ya sake faɗa mini cewa yana sona. Ya sake cewa ""INA SON KI, Zeeyadah"" saboda na ji sassaucin abinda na ke ji a raina sai ya ja baya." """Ban san me zan yi ki yarda dani ba, Zeeyadah"" ya faɗa muryasa a karye." Ka ce kana sona. Ka ce na yafe maka. Ka ce na yi haƙuri. "Ka ce ba ka son Cassandra, ni kake so." Bai faɗi ko ɗaya daga cikin abinda nake tunanin zai faɗa ba. Bai ce komai ba. Sai ya juya ya je ya fara saka kayansa. So nake na je na rungumeshi na bashi haƙuri. Amma sai gaɓɓaina suka ƙi motsawa. Ba ni ce zan bashi haƙuri ba. Shi ya kamata ya bani haƙuri. Shi ya kamata ya lallaɓani. Ko juyowa bai yi ya kalleni ba ya saka kayansa ya fita daga ɗakin. A karon farko sai na sake jin so da ƙaunarsa yana shigata. "Ina son Jalal, har yanzu ina son Jalal." Kwanciya na yi a bakin gado ina jinyar zuciyata da kuma tsakiyar cinyoyina dake mini zogi... JAYKAY Iya gaskiyarta ya gani lokacin da take zarginsa da cewa zai tafi ya barta saboda Cassandra. Bai san da wani yare zai bayyana mata irin soyayyar da yake mata da za ta fahimce shi ba. He's madly in love with her. Wataƙila soyayyar ce bai iya ba. Wataƙila kuma ya gaza ne wajen nuna soyayyar ta sa a fili. Ba ya so ya cigaba da sauraron maganganunta masu ɗaci shi ya sa ya yi shiru ya bar mata ɗakin. Ta ya za ta zarge shi da kawai son jikinta yake?. A shekarunsa ya fi ƙarfin ya yi mata ƙaryar abunda ba shine a zuciyarsa ba. Bai faɗa mata kalmar SO ba har sai da ya gama tabbatarwa kansa cewa soyayyar da yake mata ba ta sha'awa bace. Shi yasa tun da aka ɗaura musu aure ya ke binta a sannu saboda ta nitsu da shi ta san cewa ba jikinta ne ya saka shi aurota ba. Bai san yaushe ya fara sonta ba. Wataƙila ta samu shiga zuciyarsa ne a ranan da ta masa masifar ita 'yar Ghetto ce kuma tana alfahari da inda ta fito. Wataƙila kuma a ranan da ya kaita kallon Hawan Sallah ne. Wataƙila ma a ranan da ya fara ganinta ne. Riƙe kansa ya yi da ke mugun sara masa. Mummunan fahimtar da ta masa ya fi komai ɗaga masa hankali yanzu. Wataƙila lokaci take buƙata da za ta huce. Zai bata lokaci. Shima kuma zai je London ya yi maganin matsalar Cassandra once and for all. Ya sani idan har Kotu ta tabbatar da SAKI tsakaninsa da Cassandra to tabbas Ziyada za ta yarda da gaskiyarsa. "Duk da yana son komawa ɗakinta ya rungumeta ya bata haƙuri, ya cuddling ɗinta ta ji sauƙin wahalar da" ya bata ɗazu sai ya hana kansa hakan saboda kada komawarsa ɗakin ya sake sakata hawaye. Hawayenta kuma yana mugun ƙona masa rai. *** "Ƙarfe shabiyu na rana bayan ya gama shiryawa sai ya wuce ɗakin Ziyadah, bacci ta ke yi. Dama ya samu" kira daga Jide akan ta kira ta ce ba za ta samu fitowa ba su yi handling Gidan Girki da kansu. Ajiye mata wani envelope ya yi a gefen wardrobe dake gefen gadonta ya manna mata light kiss ya fita daga ɗakin. Direbansa ne ya wuce da shi Abuja inda daga nan zai hau Jirgi ya tafi London. A halin yanzu ba zai iya fuskantar Hajiya ba tareda ya dawo da Muhammad ba. Sannan ba zai iya fuskantar Ziyada ba tareda ya saki Cassandra ba. Lokacin da jirginsu ya tashi gangan jikinsa ne ke cikin jirgin amma zuciyarsa tana Nigeria. Tunaninsa yana "Zaria, sannan farincikinsa yana gurin Ziyadah..." CHAPTER FIFTY FOUR ZEEY Ƙaran waya ne ya tasheni daga baccin da na yi bayan na sha kukan tafiyar Jalal. Hajiya ke kirana. Yanayin muryata da ta ji a dashe ya sa ta tambayeni ko lafiya? Na ce mata kaina ke ciwo. Ta min sannu sannan ta ce za ta shigo ta duba ni. Jama'a in sauƙo da ƙafata in miƙe sai fa tashi ya gagareni. Ƙafafuwana ne suka yi tsami. Sai yanzu aikin Jalal ya fara tasiri a kaina. Ɗazu da safe ban ji wahalar tashi sosai ba. Da ɗan ƙarfina na shiga banɗaki na yi wanka. Ikon Allah! Na miƙe da ƙyar ina tafiya ina ɗan buɗe ƙafafuna kamar wacce aka yiwa kaciya. In zauna in yi fitsari sai na ji wani zogi ta ƙasana. Innalillahi! Da ƙyar na yi tsarki ina ɗan rintse idanuna saboda zafi. Na yi Alwala na fito. Sallaya na shimfiɗa na yi sallar Azahar a tsaye da ƙyar. Na zauna ina Istigfari. Ƙarfe biyar saura na sauko ƙasa lokacin da Hajiya ta kirani wai ta iso. Sai dana sauko ƙasa sannan na gyara tafiyata saboda kar Hajiya ta gane akwai matsala. Na ajiye murmushi a fiskata na buɗe ƙofar. """Ya jikin naki?"" Ta tambaya lokacin da muka zauna." """Da sauƙi, Hajiya"" na amsa ina murmushi amma ni kaɗai na san ciwon da nake ji a jikina." Na tambayeta me zan kawo mata ta ce ba sai na yi wahala ba. Anjima kaɗan ma Hassana za ta kawo min abinci. Na yi mata godiya. """A can Restaurant dai babu wata matsala ko?""" "Na ce mata lokacin dana kira Jide dai yace babu matsala. Ta ce mini Alhamdulillah, Allah ya ƙaro kasuwa." """Jalal, ya wuce ko?""" Na yi shiru dan ban san ko yana nan ko ya tafi ba. Sadda na tashi daga barci ta kaina na yi ba ta tasa ba. """Na san tafiyarsa ba zai miki daɗi ba. Amma dole ne ya je ya karɓo Muhammad kuma ya warware" "aurensa da Cassandra. Idan ba rashin hankali irin nasa ba, wani irin zaman aure ne yana zaune a Nigeria tana can London sai ta ga dama ta zo. Allah kaɗai ya san me ta ke yi a bayan idonsa dan yarinyar kwata- kwata bata da kamun kai""" Jin Hajiya na ƙorafi akan Cassandra sai na ji daɗi a raina. Ashe dai ina da tudun dafawa. Haka dai ta yi ta kwantar min da Hankali ta ce mini idan ba zan iya zama ni ɗaya ba in tattaro in dawo gidanta. Na yi shiru dan gaskiya bana so in je gidanta a halin da nake ciki. Tunda Jalal baya gidan gara na zauna na yi jinyar kaina ba tareda takura ba. Da ta ga kamar bana so sai ta ce babu matsala in zauna ɗin dama Jalal ya mata magana za ta sa a kawo "min 'yar aiki da za ta riƙa tayani kwana. Na yi mata godiya amma na ce ba sai an kawo 'yar aiki ba, tunda a Gidan Girki zan riƙa wuni ma." Gabanin Magariba Hajiya ta tafi. Da za ta wuce na tambayeta ina Janan ta ce tana can tana ta shirye- shirye Mijin da za ta aura zai shigo Nigeria a satin nan. Na ce mata ta gaisheta. Bayan tafiyarta ban bar falon bama na zauna ina ɗan kallo sai can ga Hassana ta iso. Ta gaisheni sannan ta kai min kwandon abincin kan dining. Bata wani tsaya ba ta tafi. Daga nan na je dining na buɗe kulolin abincin na ɗan ɗebi abinda zan iya ci na zauna a wajen ina ci ina tunanin Jalal. Ko ya isa London ɗin?. Ko sun haɗu da Cassandra?. Ko da gaske rabuwa zai yi da itan? Allah ne kaɗai masani... JAYKAY """JLove"" Cassandra ta faɗa lokacin da ta buɗewa Jalal ƙofa. Wani kallon tsana ya mata." """Where's my Son?"" Ya tambaya da ƙarfi." Juyawa ta yi ta barshi a bakin ƙofa tana faɗin idan Junior ya zo nema to baya nan. Sake tambayarta ina yaron yake ya yi amma ta shareshi. Ya wuce upstairs da sauri ko bin bayansa ba ta yi ba. Jalal ya buɗe ɗakin Junior ya ga wayam babu yaron. Ya je ɗakinsa da suke kwana da Cassandra nan ma babu kowa. """Where is he?"" Ya faɗa da ƙarfi lokacin da ya sauƙo ƙasa ya samu Cassandra tana zaune a kujera ta ɗaura" ƙafa ɗaya akan ɗaya. Ka shirya magana kenan? Ta faɗa ko a jikinta da yadda ya haukace da bai ga Junior a gidan ba. Ta ce masa ai ba zai taɓa ganin yaron ba har sai ya dawo hayyacinsa. """Stop playing games with me, Cassandra. Where's my Son?"". Ya daka mata tsawa. Ɗan ja da baya ta yi a" tsorace. Ganin haka sai ya damƙe hannunsa yana furzar da iska. Tunzura shi Cassandra ke son yi saboda ya yi abinda zai ɓata komai. Ba a Nigeria suke ba. Kira ɗaya za ta yi Police su zo gidan. Haƙura ya yi da tambayarta ina Junior ya fita ya bar mata gidan. Gidansu na London ya wuce wanda a yanzu ya koma Masauki ga duk wani ɗan Familyn Maiyaƙi da zai zo London. Wani lokaci ko ba a cikin Family ba idan aka nemi alfarma suna bada aron gidan wa baƙi 'yan Nigeria. House keeper ɗinsu kaɗai ya samu a gidan. Dake tsohuwar tana aikinta yadda ya kamata duk da bai faɗa mata zai shigo ba tsaf-tsaf ya samu gidan. Gidan yana da dogon tarihi a gareshi. A gidan suka taso shi da Jamal. Daddynsu ya sayi gidan ne lokacin yana shekara 7 a Duniya shi kuma Jamal yana shekara 4. Haka za su yita wasa shi da Jamal a gidan suna rigimarsu. Idan ka ga suna wasa sai kace 'yanbiyu ne ba wa da ƙani ba. Kwatsam bayan sun gama tunanin su biyu ne kaɗai a wajen iyayensu sai Hajiya ta haifo musu Janan. Ba zai taɓa manta ranan da Daddynsu ya faɗa musu Hajiya tana da ciki ba. Ya dawo daga Makaranta ne ya samu Hajiya bata da lafiya sun je Asibiti. Da suka dawo kuma Daddy ya musu Albishir da cikin Hajiya. A lokacin Hajiya sai ɓaɓɓata fuska take har tana cewa me yasa zai faɗawa yaran daga zuwansu. Shi da Jamal suka dinga murna za su samu Baby sister dan sun riga sun sawa ransu mace Hajiya za ta haifo musu. "Shekaransa 15, Jamal kuma 12 aka haifi Janan. Pretty little Sister ɗinsu. Haka suka ɗauki soyayya suka" ɗaurawa Janan. Tun kafin a haifeta ma suka gyara mata ɗaki da pink decorations suna jiran zuwan ƙanwarsu. Wani abin ma idan suka yi sai Hajiya ta fara faɗa amma Daddynsu ba ruwansa. Shine ma yake biye musu a komai saboda shima yana son Baby Janan sosai. Ba Hajiya kaɗai ke reno ba. Su biyun duka suka zage suna yiwa ƙanwarsu hidima. In dai suna gida kowa rige-rigen chanjawa Janan Napkin yake ko kuma a ce su bata Madara saboda Hajiya bata shayar da ita ba ance ruwan Nononta ya tsaya. Lokacin da Jalal ya fara Jami'a sai renon Janan ya koma hannun Jamal. Wannan ya sa ta fi shaƙuwa da shi. Shi Jalal idan ya zo sai ya yita tsokalarta wai Adopting ɗinta Hajiya ta yi ba 'yar gidan bace. Janan ta yi ta kuka har sai Jamal ya lallaɓata ya nuna mata hotunan haihuwarta a Asibiti da hotunan Suna. "Good old days kenan, kafin komai ya lalace." "Jalal ya sa key ya buɗe Master Bedroom ɗin gidan, shi kaɗai ne ɗakin da ba a bawa baƙi saboda a nan" Hajiya ke sauka idan ta shigo London. Komai na ɗakin na nan yadda ya san shi a da. """Jamila, kin kuwa san me Manajan nan yake faɗa. I think gara na je Nigeria na duba me yake faruwa""" Jalal ya jiyo muryan Daddynsu a kunnensa. Irin hiran da yake yiwa Hajiya kenan idan suka zauna cin abinci a dinning. Back then ba Hajiya suke kiranta ba Mom suke ce mata. Wani zuwansu Nigeria ne da Janan ta ji 'yan'uwa "da ma'aikatan gidansu na Zaria kowa na kiran Mom da Hajiya sai ta kama sunan a bakinta, da suka dawo London sai ta cigaba da kiran Mom da Hajiya. Shikenan kuma Daddynsu ya ce ai kuwa Hajiya ya fi dacewa da ita ba Mom ba. A hankali shi da Jamal suka switching suma suka fara kiran Mom da Hajiya." Rayuwarsu mai daɗi ne musamman idan suka je Nigeria. Hajiya ita ce mai faɗa a cikin iyayensa. "Daddynsu mutum ne mai sauƙi ga shi da raha da barkwanci, halinsa Jamal ya ɗauko shi yasa duk Family aka fi sonsa." Lokacin da Daddynsu ya kafa Business ɗinsa a Nigeria haka yake sintiri tsakanin London da Nigeria. Daga baya sai ya ga rashin zamansa a Nigeria yana jawowa Kamfanin nasa koma baya saboda mutanen da ya barwa dukiyar tasa ba su da Amana. Daga ƙarshe sai ya haƙura da zaman London ya dawo Nigeria da zama gaba ɗaya. Ƙaramar jinya ce ta yi ajalin Daddynsu. Ya yi fama da jinya wata da watanni ana ɗan sintirin Asibiti har ya samu lafiya. Daga nan kuma sai da ya shekara guda check-up kaɗai ke kai shi Asibiti. Kai ko ciwon kai bai taɓa ce musu yana ji ba. Kwatsam safiyar wata Laraba ya tashi da zazzaɓi. Daga barin ɗan kwanta bayan ya sha magani sai Mutuwa ta ɗauke shi... Wani hoto da aka kifa ƙasa a saman Drawer Jalal ya ɗaga. Hoton da ɗan ƙura ya sa hannu ya goge shi. "Hawaye suka taru a idanunsa. Shine hoto na ƙarshe da ya ɗauka da Daddynsa. A ranan sunan Junior ne, Daddyn nema ke ɗauke da jaririn yana murmushi. Ga Hajiya a gefensa fiskarta babu yabo babu fallasa. Jamal na gefen Hajiya, shi kuma na gefen Janan da take jikin Daddy." "Babu Cassandra a hoton, iya su 6 ne ahalin Alhaji Kabeer Maiyaƙi." """Idan na kira shi Muhammad Jamilu yanzu sai ki ɓata rai"" Daddy ya faɗa yana kallon Hajiya. ""Barin bar" "shi da babban sunansa, ina tawassuli da girman sunan da ya ci Allah ya sa wannan jikana na farko dana bashi suna MUHAMMAD ya rayu a Musulmi na ƙwarai har zuwa mutuwarsa. Ina addu'ar ya zamo ɗa na gari ga iyayensa da ma duk Al'ummar Musulmi"" ya tuno kalaman Daddynsu a ranan sunan Junior." Sai gashi yanzu yana daf da tura yaron inda za a nesanta shi da Musulunci. Gaskiyar Hajiya da ta ce shi baya komai akan lokaci sai komai ya ƙure masa. Ga shi yanzu abubuwa sun zo su kwaɓe masa. Ziyada ce ta faɗo masa rai. Idan ya ce zai bata lokaci har sai ta huce za ta iya fassara shi da cewa ya shareta. Idan ya nesanta kansa da ita zai iya rasata gaba ɗaya. Wannan kuma ba "abu ne da zai iya ɗauka ba. Ba zai barta ba. Yanzu ne ya kamata ya ƙara nuna mata kulawarsa, ya nuna" mata cewa yana sonta kuma ya damu da ita koda ba zata yarda da shi ba. Da wannan ya kira numbarta amma bata ɗauka ba. Sai ya tura mata text akan ya isa London lafiya. A ƙarshen sai ya rubuta I MISS YOU. *** Washegari da sassafe ya wuce gidansa amma sai ya samu Cassandra bata nan kuma ta chanja password "ɗin gidan. Wannan ya sa ya shiga Taxi ya je office ɗinta. Da ya je aka ce masa bata shigo ba. Ya dinga kiran numbarta amma yana tafiya voice mail. Cike da ɓacin rai ya tafi office ɗin Lawyansa. Sun jima suna tattauna yadda za a gabatar da ƙaran. Lawyan ya ce masa ya riga ya turawa Kotu application na Divorce kamar yadda suka yi magana a waya, dan haka jiran reply suke daga Cassandra da Lawyanta." Shi Jalal babban damuwarsa ma maganar Custody ne ba na Divorce ba tukunna. Lawyan ya ce masa kar ya damu zai pushing a gama da case ɗin Junior tukunna kafin a finalizing Divorce ɗinsu tunda Divorce yana ɗaukan lokaci. Abinda yake gabansu shine dole su nemo shaidar da za su gabatarwa Alƙali da zai bayyana cewa Jalal ne ya fi dacewa ya riƙe Junior ba Cassandra ba. Jalal ya ce su yi amfani da shan giyar Cassandra. Lawyan ya ce masa dole sai sun nemo hujjar da zai nuna Cassandra 'yar giya ce kuma hakan zai hanata kula da Junior. Sai Jalal ya tuno akwai wani lokaci da Cassandra ta mari Sakatariyarta a wajen wani Company Party da suka yi wanda har sai da aka yi ƙaranta daga baya ta biya Sakatariyar tata taran kuɗi aka rufe case ɗin. Lawyan ya ce zai biya wani Investigator ya duba musu ko akwai wani case ɗin irin wannan wanda aka rufe bai fito ba saboda au samu hujjoji masu ƙarfi akanta. Da yammaci Jalal ya sake turawa Ziyada text ganin bata masa reply ɗin text ɗinsa na jiya ba. Amma still har dare babu reply. Sai washegari da safe Cassandra ta kira shi da kanta wai ta ga takardar ƙara daga Kotu. Ta ce ba za ta yarda da saki ba sannan ba zai taɓa samun Custody ɗin Junior ba. Idan yana son ganin ɗansa to dole ne ya rabu da Ziyada sannan ya bata haƙurin cin amanarta da ya yi. Sai a sannan za ta bar shi ya ga Junior sannan ta yafe masa su koma Happy Family kamar da. Ganin ba za ta saurareshi ta waya ba sai ya ce mata yana so su haɗu. Ta ce masa ya zo gida ƙarfe shida na yamma. Tun biyar da rabi yake ƙofar gidan. Abin mamaki shi ya sayi gidan amma a yanzu ba shi da ikon shiga gidan nasa tunda Cassandra ta chanja key. Cassandra ba ta dawo ba sai takwas na dare. Haka Jalal ya sha zaman jiranta har ta iso. Ta fito daga motarta tana wani catwalking da high heel ɗinta ta zo ta buɗe gidan. "Tambaya dai ɗaya ce ta kawo shi, ina ɗansa Muhammad Junior?." Dan ta bashi haushi sai ta ce masa ya jirata har sai ta je ta yi wanka kafin su yi magana yanzu a gajiye take. Haka ya sake jiranta kusan awa ɗaya sannan ta sauƙo ƙasa ta sha wani sexy night wear babu takalmi a ƙafarta. Yunƙurin shiga jikinsa ta yi ya tureta ya ce idan ba za ta tsaya su yi magana ba zai tafi. Ta ce masa in dai ba haƙuri ya zo bata ba to tabbas ya sani ko an je gaban Alƙali ita za ta winning Custody "ɗin Junior, saboda ita ta haife shi." """Let's just get a Divorce peacefully, Cassy"" ya faɗa a hankali. Ya ce idan suka rabu zai riƙa barin Junior" yana zuwa mata hutu. Nan fa ta fara ihu tana cewa ba za ta yarda ba. Kuma idan ya ce zai nemi saki ta ƙarfi to sai ta ƙwace Junior sannan ta ƙwace duk abinda ya mallaka daga London har Nigeria. Jin haka sai Jalal ya ciro wasu takardu daga jakarsa ya ajiye a gabanta ya ce ta karanta. "A wani daƙile ta ɗau takardan ta fara karantawa. Takardar Prenuptial Agreement ɗinsu ne, wato" yarjejeniyar da suka rubuta kafin aure. Zaro idanu Cassandra ta yi ganin abinda aka rubuta a takardar. Jalal yai murmushin mugunta yana ƙara godewa Allah da Jamal ya saka shi rubuta wannan yarjejeniyar kafin aurensa da Cassy. """Ɗan'uwa ba mu san gobe ba. Idan a gaba Cassy ta ce za ta rabu da kai ko kuma kai a karan kanka ka" "shirya rabuwa da ita za ta iya rabaka da duk abunda ka mallaka. Wannan yarjejeniyar zai covering ɗinka"" kalaman Jamal kenan a gare shi." """How is this possible?"" Cassy ta faɗa tana cillar da takardar dan ta manta da cewa ta sa hannu a wannan" yarjejeniyar kafin aurensu. Jalal ya ce mata idan ta ƙi su rabu ta sauƙi shi zai nemi Kotu ta raba su kuma daga ƙarshe zai samu rabin dukiyarta tunda shi ya bata rabin jarin da ta kafa kamfaninta da shi. "Nan fa Cassandra ta fara zazzare idanu. A yarjejeniyar da suka ƙulla, duk wani abu da Jalal ya mallaka ta" dalilin gadon iyayensa baya cikin lissafin dukiyar da ke aurensu. Dan haka duk kuɗin da take gani yanzu har ta ke cewa zata raba shi da shi to baya cikin lissafin kuɗin da Kotu za ta ce su raba idan suka rabu tunda kuɗin gado ne. A yanzu ba shi da kuɗin da za ta ci nasa tunda ya jima da ajiye aikinsa baya cin Pension ma balle ta yi tsammanin Gratuity. """WHERE IS MY SON?"" Ya faɗa a nitse ganin ta tsorata da abinda ya faɗa mata." "Shiru ta yi, can kuma sai ta ɗau waya ta kira Lawyanta ta fara yi masa bayani. Can sai ta tsugunna ta" tattare takardun daga ƙasa ta kai wajen dinning tana ɗaukan hotonsu. Da alama turawa Lawyanta za ta yi. Ko ɗar bai ji ba dan ba original copies ɗin bane. Yana ji tana masifa alamar bata yarda da bayanin da Lawyan ke mata ba. Ta ƙare da cewa za ta je office ɗinsa gobe su yi magana. Lokacin da ta dawo wajen da Jalal ke zaune yana jiranta sai ta ce masa ta ji bayaninsa amma still ba zata bashi Junior ba. """Is he with your Mom?"" Yana wajen Mamanki? Ya tambayeta da ƙarfi." Ba za ka samu Custody ɗinsa ba. Ta amsa masa da ƙarfi itama. """You're not his father"" ta faɗa a taƙaice tana kallon gefe." Dariya ya fara mata saboda ko makaho ya shafa fiskar Junior ya san ɗansa ne. Sai dai dariyar da yake mata ne ya tsaya lokacin da ta faɗa masa abinda ya datse masa numfashinsa na 'yan wasu daƙiƙu. Cikin da ta ce ya zube shekara shabiyu da suka wuce ba nasa bane. Ƙarya ta masa dan ya aureta. Dan haka Junior ma ba ɗansa bane. "Bata tsaya iya wajen ba, sai da ta faɗa masa cewa cikin na Ex ɗinta ne, da ya ce baya so shine ta manna" masa. Kuma zubewar cikin ma saboda ta sha giya ta bugu ne ta zame a banɗaki shine cikin ya fita. Tana faɗa masa hakan ne saboda ta san idan ta yi ƙaryar Junior ba ɗansa bane zai fasa maganar saki su yi "sulhu. Ta shirya tsaf dan nemo DNA result na ƙarya dan ta tabbatar da cewa Junior ba ɗansa bane. Nemo wani baƙin fatar za ta yi ta gabatar da shi a matsayin Baban Junior. Idan Jalal ya ga zai rasa Junior gaba ɗaya to zai yi haƙuri ya bar maganan saki ko kuma ya compensating ɗinta da kuɗi masu yawa. Ba zata rasa Jalal, ta rasa ɗanta, sannan ta tashi babu kuɗi ba." Kasa magana Jalal ya yi ya ɗau jakarsa a hankali ya fara tafiya. Ta zo da gudu ta rungumeshi ta baya tana faɗin zata bari ya ga Junior idan har zai janye maganar saki. Bangajeta ya yi ya fice daga gidan jikinsa a sanyaye. Har ya tsai da Taxi ya shiga har aka wuce da shi gidan Daddynsu bai daina jinjina wannan sabon labarin da ya ji ba. Ashe shi wawa ne. Ashe shi ɗin matsoraci ne. All this years yana riƙe da laifin saboda shi Cassandra ta samu Miscarriage ashe cikin ma ba nashi bane. Me yasa ya yi saurin amincewa da ƙaryar kalaman Cassandra ba tareda ya nitsu ya gane shiri ta mishi ba. "Wataƙila da ya faɗawa Jamal gaskiyar dalilin da ya yasa ya dage sai ya auri Cassandra, da zai fahimtar da" shi tuggun da ta shirya tunda shi bai iya gane komai ba. Kodayake a lokacin kunyar faɗawa ɗan'uwansa babban zunubin da ya aikata yake. Ta ya zai fara faɗawa Jamal da yake ganin girmansa cewa ya kwana da Cassandra ba tareda aure ba kuma har ta samu cikinsa cikin kuma ya zube. Da dai bai ɓoyewa ɗan'uwansa ba da babu makawa bai auri Cassandra ba balle a kawo wannan gaɓar. Koda yake ƙaddararsa ce ta zo a haka. Yanzu ya shirya gyara kura-kurensa ba zai bari ta ɗauke masa ɗansa ba. Ba shi da wani kokonto cewa Junior ɗansa ne. Kuma zai karɓi yaronsa daga wajen wannan mayaudariyar. Lokacin da ya isa gida mai kula da gidan ta tambayeshi ko a kawo masa abinci ya ce baya buƙata. Yana zuwa ya gabatar da sallolin da ya rasa saboda ya zauna jiran Cassandra. A karo na biyu bayan shekaru masu yawa ya sake ɗaga hannunsa yana roƙon Allah ya yafe masa laifin da ya aikata... CHAPTER FIFTY FIVE ZEEY Kwana uku kenan da tafiyar Jalal London. Kusan kullum sai na ga text ɗinsa amma bana yi masa reply. Jiya da dare ya turo min text dake ɗauke da kalmomi uku rak dake ƙunshe da amon nadamar da ya yi. I AM SORRY!. Ga shi dai text ne amma dana karanta sai da tausayinsa ya kamani. Na ji kamar na rubuta masa reply ko kuma na kira shi amma sai na hana kaina saboda matuƙar ban ga "takardar shaidar an raba aurensa da Cassandra ba, to babu yadda za a yi na sake yarda da soyayyarsa." Hutun sati ɗaya na so yi kafin na fara fita Gidan Girki saboda in lallaɓa kaina na ƙarisa jinyar da Jalal ya barni da shi amma kwatsam jiya da dare Jide ya kirani wai dole in fita yau dan akwai matsala a kitchen. Bayan na yi sallar Asuba na yi Azkar sai na fara shiri. Akwai matsala a Restaurant ɗina ai ban ga ta zama ba. Yaushe-yaushe aka buɗe har an fara samun matsala. "Ƙafafuwana sun dena ciwo, amma har yanzu idan zan yi tsarki sai na ji raɗaɗin shaidar shigan Jalal wajen." Lokacin da Direban Jalal ya saukeni a bakin Restaurant ɗin a dai dai lokacin shima Jide ya iso cikin Plazar da motarsa. Office ɗina muka shiga ya tambayeni ya jiki na ce masa da sauƙi. """Jide, mi yake faruwa ne?"" Na tambaya a ɗan tsorace." """Sincerely, bana so na ɗaga miki hankali amma na san yadda kika damu da wannan wajen so tun kafin" "mu bari matsalar nan ta yi ƙarfi gara mu tackling ɗinsa""" """Wace irin matsala ni Ziyada""" """I think ya kamata ki sake training ɗin staff ɗin Kitchen. Na samu complain na Customers guda uku da" "suka ce abincin da suka ci ranan da aka buɗe Gidan Girki da kuma wanda suka siya daga baya akwai banbanci. Specically miyan Kuka da kuma Alalen gwangwani. Even Ɗumame da mutane ke siya everyday jiya an yi complain ɗinsa""" Na yi shiru ina nazarin bayanin Jide. To ko dai basa amfani da recipe dana koya musu ne?. """Chef, ni kaina moimoi dana ci jiya was not good. Ya yi so soft kaman ruwa. Jiya a office gudawa ne ya" "kamani sai dana sha magani""" """Subhanallahi!. Sannu. Gaskiya akwai matsala kam. Abinda za a yi, zan saka musu ido na ga yadda suke" "yi""" """That will be good""" Kafin staff su fara zuwa tuni na shiga kitchen na fara shirya abubuwan da za mu yi serving a menu ɗinmu na safe. Na fito da tuwo daga Freezer na fara yayyankawa kafin a zo a fara ɗumamawa. Duka staff ɗin a Kitchen suka sameni ina cikin aiki Dumu-dumu. Ban tambayesu ya suke aikinsu ba na ce bari kawai na saka musu ido na ga yadda suke aiki. Lokacin da za a haɗa Alale sai na lura da measurement ɗin abubuwan da Zainab ke sakawa. """Wannan daga ina?"" Na tambayeta ganin tana shirin juye sachet ɗin Ajino a cikin ƙullin Alale." Ta yi shiru bata amsa mini ba. """Ina Tanimu?"" Na faɗa babu wasa a muryata." """Chef, ga ni""" """Ba kai ne Kitchen Supervisor ba?"". Kana ganin ina take saka mana abubuwan da ban ce a saka ba a cikin" "abinci?""" """Wallahi Boss ban lura bane"" ya faɗa yana ɗaga hannunsa sama." """Me yasa kike sakamin abinda baya cikin list of Ingredients da muke amfani da shi a wannan Restaurant" "ɗin?"" na kalleta ina jiran ƙarin bayani dan ban san wani irin ƙarfin hali gareta ba, wannan ai iskanci ne." Na musu training na yi komai amma ko sati ɗaya ba a yi da buɗe Restaurant ba har tana da confidence ɗin chanja mini recipe. """Wai na ga Alale babu Ajino baya daɗi ne, kuma kin ce kar a sa shine nake saka kaɗan dan ya saka shi" "laushi""" Ya saka shi laushi? """Zainab, mun ɗaukeki a nan dan ki riƙa saka mana abinda kika ga dama a abinci ne, ko kuma dan ki bi" "tsarin Gidan Girki wajen dafa abinci?""" """Akwai tsarin da na ce ku bi wajen girka kowanni Menu da muke da shi a wannan Restaurant ɗin""" """Bisola na muku training ko ban yi ba?""" """You did, Ma"" Bisola ta faɗa ɗan tsorace." """To, Chef Zainab ko ke ce CHEF ZEEY ne kam na sallama miki komai ki riƙe Gidan Girki da kanki?""" Shiru ta yi bata ce komai ba. Na cigaba da masifa har sai da Jide ya shigo. Sai a lokacin ta ce na yi haƙuri tana wani hahhaɗa rai kamar babu abinda ta yi. """Kar wanda ya sake saka mini abinda ban ce a saka ba. Kuna jina?"" suka amsa da EH." Tanimu Tee ne ya karɓi aikin Alalen muka fita daga kitchen ɗin ni da Jide. """Dole mu updating policy ɗinmu"" Jide ya faɗa lokacin dana zauna." """Ni fa ban karanta Policy ɗin da ka turo min kwanaki ba""" """Ha! Madam ki karanta da kyau fa saboda shi zai protecting wajen nan. Ke kin san yadda aiki a" "Restaurant yake, matsalar Staff ke kashe most Restaurants. Kin yi aiki a Zikks Foods ai, kin san wajen nan basa ɗaukan nonsense, kana yin abu kaɗan za a koreka""" """Seriously raina ya ɓaci. Ka ji fa wai Alale babu Ajino ba ya daɗi. Mtssw!""" Bayan mun gama jimamin abinda ya faru sai Jide ya tambayeni wani hukunci za a yiwa Zainab na ce "shine Manager ya mata hukuncin da ya ga ya dace tunda ba a rubuta hakan a Policy ɗinmu ba. Ya ce tunda ko sati bamu yi da buɗe wajen ba bai kamata mu koreta ba, zai kirata office ɗinsa ya mata warning." Kusan ƙarfe uku na rana sai ga kiran Faty wai gata a Plaza ta zo ganin Restaurant. Wani Waiter ɗinmu ne ya shigo da ita wajena. """Hajiya Zeey, Ashe za a iya ganinki"" ta taɓe baki tana kallona." """Faty kenan. Ke dana gayyaceki buɗe wajen nan kika ƙi zuwa""" """Wallahi ba wai na ƙi zuwa bane na tashi da rashin lafiya ne ko tashi bana iya yi""" """Allah Sarki, ya jikin?""" """Da sauƙi, Bestie. Ashe haka wajen nan ya haɗu, gaskiya Yallaɓai ya yi ƙoƙari a wajen nan kuma na ga" "wajen a cike akwai mutane""" "Na ɗan yi murmushi na ce ""ai kin san sabon wuri ne mutane na ta rububin zuwa saboda har yanzu ana" "tallen wajen a gidan Rediyo""" """Ai har a Instagram na ga ads ɗinku. Waje yayi kyau, Allah ya sa Albarka""" Na amsa mata da Amin. Na sa aka kawo mata abinci wai daga School take gobe muna da test shine ta ce bari ta zo ta faɗa mini. "Na yi mata godiya, ban ce mata ma na ga update ɗin test ɗin a group ba." ClassRep ɗinma da kansa ya chatting ɗina ya faɗa min. Da ke mun ɗan yi yarjejeniya da shi na tura masa "kuɗi bani da matsalar Assignment ko Attendance, kuma duk wani abu da ya taso idan ban shigo School" ɗin ba zai min magana. Tana gama cin abinci ta ce za ta tafi wai za ta je ta ɗaura abincin dare dan Mijinta yana dawowa da wuri. Muka yi sallama na ɗan rakata har bakin Plaza. Sai dana dawo office na je banɗaki na yi Alwala na dawo office ɗina na shimfiɗa sallaya na tada sallar la'asar. Dana idar da Sallah na ga Zainab bata shigo office ɗina sallah ba sai na ce barin leƙa Kitchen na mata magana. """Ai Wallahi da ta ce za ta koreni da ta ga bura'uba a wajen nan. Ƙaramar yarinya da ita tana wani yiwa" "mutane tsawa ita a dole ta auri mai Kuɗi. Kamar bamu san ya aka yi ta auri Alhaji Jalal ɗin ba...""" Bisola da take yiwa gulmar ta ganni sai ta sha jinin jikinta ta kau da fiska ta cigaba da aikin da ta ke. """Miye ne?"" Zainab ta faɗa tareda juyowa ta kalli hanyar ƙofa. Ganina tsaye a wajen sai ta fara kame-" kame ƙarshe ta je wajen Freezer ta buɗe tana dube-dube. Ban yi magana ba. Na koma office ɗina na zauna. Da dane ba zan yi mata shiru ba amma yanzu na fara fahimtar cewa ba komai ake gyarawa da ihu ko masifa ba. Wani abin shiru ma amsa ne. Lokacin dana tashi tafiya gida sai na leƙa office ɗin Jide na ce masa idan aka kai ƙarshen wata aka biya ma'aikata Albashi ya haɗawa Zainab har da Sack Letter. Shi ya ɗauka ma saboda laifinta na safe ne na ce masa ko ɗaya na ga ba zan iya aiki da ita bane. Bai tambayi dalili ba ya ce zai yi hakan. A gajiye na koma gida. Bayan na yi wanka na chanja kaya sai na kira Kaka saboda lokacin da nake cikin "mota ta kirani, dana kashe kiran dan na kirata kuma sai numbarta ya ƙi shiga. Yanzun ma numbarta Switched off ya ce dan haka sai na kira numbar Mardiyyah na ce dan Allah ta kaiwa Kaka wayarta zan yi magana da ita." Bayan kaman minti biyar sai ta mini flashing na kirata. """Ashe wai wayarta ce ta mutu ba chaji. Ga Kakar"" ta miƙawa Kaka waya." "Allah Sarki Kaks ɗina, na yi missing ɗinta overrrr." """Ziyadatu, kina nan lafiya. Ya Maigidan naki. Da fatan dai kuna lafiya duka""" """Duk muna lafiya, Kaka""" """Allah ya yi muku Albarka duka"" na amsa da Amin. Yanayin muryarta ya sa na fahimci kaman tana ɗan jin" jiki. Na tambayeta me yake damunta wai zazzaɓi ne kuma ta ji sauƙi. Na ce Insha Allahu zan shigo na gaisheta gobe. Ta ce ai ba sai na zo ba ta warke ma. Ni dai jinta kawai nake amma tabbas sai na je na dubata. Bayan mun gama gaisawa na ce ta miƙawa Mardiyyah wayar. Na ce Dan Allah idan ta samu dama ta riƙa leƙa sashen Kaka tana saka mata wayarta a Chaji dan ko ina nan ma Kaka sai ta manta da batun saka "wayarta a Chaji, sai wayar ta mutu ka ga ta fara neman yadda za ta saka Chaji." "Mardiyyah ta ce wai ashe Chager wayar ce aka ɗauke, har extension wire dana saka a ɗakin ma yanzu" babu. Ikon Allah! Yaushe na bar gida har sun fara lallɓowa suna yiwa Kaka sata. Dama saboda ni ne basa "samun damar yiwa Kaka 'yan ɗauke-ɗauken da suka saba, yanzu dana bar gidan kuma shikenan liyafa ta cigaba." Na ce zan turawa Mardiyyah kuɗi ta siyawa Kaka Charger gobe. Bayan na kashe wayar sai na koma kan texts ɗin Jalal na fara bitarsu. Ɓangaren da yake missing ɗinsa ne ya fara rinjayar ɓangaren da yake fushi da shi. Ko me yake yanzu? Allah ne masani. "Ina son yi masa reply amma ina ganin ya yi wuri, kar ya ɗauka na damu da shi." "Na riga na yiwa kaina faɗa, duk sadda Jalal ya dawo garin nan matuƙar bai rabu da Baturiyarsa ba to ba" zan kulashi ba. Duk da na san ya bani damar fita idan buƙatar hakan ta taso sai na ga babu daɗi na je gidanmu duba jikin Kaka ba tareda na faɗa masa ba. Haka na tsinci kaina da fara rubuta masa text. Sai na yi typing sai na goge. Ƙarshe na rubuta masa gajeren text kamar haka: "KAKA BATA DA LAFIYA, ZAN JE GIDANMU GOBE." Na karanta ya yi sau biyar kafin na tura. Bai yi min reply a lokacin ba. Na sauƙa ƙasa na je na ɗumama sauran abincin da Hassana ta kawo min. Sai dana hawo sama na zauna a falo na fara cin abinci sannan na ga reply ɗinsa. Text uku ya min a jere: """So sorry, Sunshine. Allah ya bata lafiya""" """Ki isar min da gaisuwa""" """ I MISS YOU""" Sai kuma alert ɗin kuɗi dana gani wanda nake tsammanin ya turo ne dan na siyawa Kaka kayan dubiya. Na zauna shiru a falo ga TV yana aiki amma bana fahimtar abinda a ke yi a ciki. Hankalina gaba ɗaya yana ga maganganun da na ji Zainab ta faɗa. Wato ta san ya aka yi na auri Jalal. Na san a social media ta ɗauki wannan karatun a lokacin da Alhaji Nafi'u ya min ƙazafi. Ko mutane nawa irinta ne suke da wannan tunanin a kaina sai Allah. To wai ma miye laifina ne?. Idan ma cusa kaina na yi wajen Jalal har ya aureni ai hakan ma iyawa ne. Wasu ko za su mutu idan suka cusa kansu wajen namiji ko kallonsu ba zai yi ba balle ya kula su. Tunowa na yi da kalaman Jalal kafin ya tafi London. """Kin jima da samun masauki a zuciyata, Zeeyadah. Barin faɗa miki wani abu yau, da baki amince da deal" "ɗina ba, da zan sake nemo wata hanyar da zan samu damar aurenki...kin san saboda me?...Saboda INA SON KI, Zeeyadah. I Love You so much, Sunshine""" Wani yirrr na ji a jikina. Gaskiya ya faɗa min ranan. Subhanallahi! JALAL YANA SONA. Ba sai da muka yi aure ya fara sona ba. Ya jima yana sona kuma idanunsa sun jima da fallasa hakan. Ni ce dai nake ganin kamar kallon sha'awa yake mini ba kallon soyayya ba. Jalal kallon SO yake mini tun farkon haɗuwarmu. Wayyo ni! Ashe tun kafin mu yi aure yake sona. "Dariya na fara ina tuno farkon haɗuwarmu, faɗanmu, hiranmu da duka moments ɗinmu." Haka na fara bin ranaku daki-daki ina tuno labarinmu. Na shiga chats ɗinmu na scrolling sama har farkon fara maganarmu ta Whatsapp. Thank God ma ina "backing messages ɗina, da na loosing komai sadda na chanja waya." Ni kaina ba zan ce ga takamaimai yaushe na fara son Jalal ba. Amma a yau na sake tabbatarwa kaina abu "ɗaya, ni Ziyada Sadiq Haruna na fara son Jalal Maiyaƙi ne tun kafin mu yi aure." I HAVE ALWAYS LOVED HIM. Har yanzu ina son Jalal. Ba zan iya rayuwa mai daɗi ba tareda shi ba. "Idan kuma haka ne, bai kamata na bawa wata Baturiya dama ta shiga tsakaninmu ba." Jalal Mijinane. Auren Sunna muka yi. "Na miƙe a hankali na je na kashe TV. Ina taka stairs ina murmushi, for the first time bayan tafiyarsa sai na" ji na dena jin haushinsa. Na wuce ɗakina na je na ɗauko file ɗin da ya bar mini kafin ya tafi. Takardu ne dake ɗauke da shaidar Gidan Girki Restaurant mallakin Ziyada Sadiq Haruna ne wanda ke ƙarƙashin Kamfanin JK Foods. Na manna file ɗin a ƙirjina ina shaƙar ƙanshin Jalal dake jiki. Ba zan sake bari maganar mutane ya karya mini zuciya ba. Zan nunawa duniya cewa Gidan Girki Restaurant business ɗina ne kuma ina alfahari da hakan. "Saboda gudun bakin mutane ba zan taɓa sako labarin aurenmu a social media ba, amma gidan girki kam" tabbas zan fara tallata shi with my full strength. "Mijina Jalal kuma zan sassauta masa, amma dai ba zan sake masa gaba ɗaya ba har sai ya cika alƙawarin" da ya ɗauka na rabuwa da Cassandra. *** "Washegari da safe briefly na leƙa Gidan Girki daga nan na wuce School, ƙarfe goma na safe muka rubuta" Test. Da aka gama na karɓi project ɗina a hannun wanda yake tayani yi na wuce office ɗin Supervisor na kai masa. Ni kaɗai na je dan Faty kam muna gama test ta tafi gida wai bata jin daɗi. "Dana gama da School sai na kira Direban Jalal ya zo ya wuce da ni gidanmu, dama na bashi list ɗin" abubuwan da zai siyo mini na tsarabar da zan kai musu. Ina fitowa daga mota yaran da ke ƙofar gida suna ganina sai suka saka ihu suka nufoni. Kowa sai ƙoƙarin "shiga jikina yake suna ""Oyoyo Adda Ziya"" saura kaɗan su kada ni." Haka na shiga gida da zugar yara suna ta bina. """Ziyadatu. Shine kika taho bayan na ce miki na warware..."" ai kafin ta ƙarisa magana sai na faɗa jikinta na" rungumeta sosai. Allah Sarki har ta rame. """I miss you, Kaka""" """Masha Allahu. Sannu da zuwa""" Kan kace me matan gidanmu sun fara shigowa sashen Kaka suna gaishe ni sai cewa suke Amaryar GRA ne yau a gidan. Maman Suwaiba har da miƙo min sauran Faten da ta yi da rana. Sai cewa suke wai sunata waƙar za su zo gidana amma basu samu zuwa ba. Na ce Allah Sarki. Anty Hafsah ta zo min Barka ranan da aka buɗe Gidan Girki amma sauran ba su zo ba. Bayan na yi sallah na sa aka miƙa musu tsarabarsu. Can da yamma lis bayan la'asar da aka ce min Baffa Lawalli ya shigo gida sai na je sashensa dan na gaishe shi. Yana ganina ya fara haɗa fuska. Na tsugunna na gaishe shi maimakon ya amsa ta daɗi sai ya fara faɗa wai ya ɗauka na tafi kenan ba zan sake zuwa duba su ba. Har da cewa Mijina ya buɗe min gidan abinci ban zo na faɗa masa ba. Wai shi ya hana Matansa zuwa ranan da aka buɗe da suka ce za su je ganin waje. "Wai, tsabar mugun hali irin nawa ko yaro ɗaya ban ɗauka a gidan na bashi aiki ba." Yadda ya tisani a gaba yana ta masifa sai da na yi ƙwalla. Wani irin mummunan shaida ya mini haka. Ban ce masa uffan ba da ya gama masifar kuma sai ya fara cewa haka ya sha jinya babu kuɗin magani da ni da mijina babu wanda ya zo ya gaishe shi. Fisabilillahi ta ya zan san bashi da lafiya idan ba a faɗa mini ba?. Na tabbata da ace jinyar da yayi mai tsanani ce da Kaka za ta faɗa mini ko kuma Baffa Adamu. """Tunda Mijin naki da hukuma ya ke taƙama shi baya taimakon kowa ai sai ki je ki ƙarata da shi. Saboda" "Mijin ki dai Ziyadatu sai gani a gaban hukuma ina bada bahasi. Tunda na ke ban taɓa zuwa Chaji Ofis ba sai akan mijinki. Daga ƙarshe me ya tsinana min?. Ƙwandala bai ce ungo Baba ka sa kati a waya ba kuma na san yana turawa Adamu kuɗi. Ba laifinsa bane, ke kika nuna masa cewa Adamu ne Ubanki ba ni ba""" "Ya nuna kansa ya ce ""Ni ne nan Lawallin Baba Haruna na ke kula da tarbiyyanki har shi Alhaji Jalal ɗin ya" "ganki ya ce yana so. Ko ba haka ba?""" "Na goge hancina na ce ""haka ne""." "'To kin gani. Ni na miki tarbiyya"" ya faɗa yana bugan ƙirjinsa." """Shi Adamun yaushe yake zama a gari. Zakari ko idan ya tafi wajen gadinsa yana saka ido a lamarinki ne?." "Ni ne nan na saka ido a tarbiyyanki, ba dan na saka miki ido ba sadda kika fara Jami'a Allah ne kaɗai ya san abinda za ki zama""" """ Iyi!"" Ya wani zaro ido" """ 'Yanmata nawa ne suke zuwa Jami'a su lalace. Amma na tsaya tsayin daka akanki saboda na riƙe" "Amanar da Sadiqu ya bar mini.""" """Ga ki nan"" ya nuna ni. ""Da me kika saka min?. Ke da Mijinki sai dai ku hau mota ku yita yawo a gari ba" "za ku zo ku sada zumunci ba. Yara nawa ne a gidan nan suka gama Sakandare suna zaune ba Makaranta ba aiki amma ki gagara ɗaukansu aiki, Ziyadatu. Eh?""" Na yi shiru dan na san duk faɗan da yake kuɗi yake nema. Wannan tarihin da yake ta karantowa duk dan na bashi kuɗi ne. Na san za su ga baƙina saboda ban ɗau kowa a gidanmu na bashi aiki ba. Bana son haɗa business da "aurena ne. Idan aka samu matsala ba zai mana daɗi ba da ni da su duka. Kuma in dai yaran gidanmu dana sani ne to babu wanda zan iya bada shaida akansa, gara ma matan, amma mazan sai a hankali, akwai dai dama-dama a cikinsu su kuma basa buƙatan aiki suna da buga-bugar da suke yi." Bayan na fito Maman Suwaiba ta jani ɗakinta ta ce kada na ɗaga hankalina akan abinda Baffa Lawalli ya "faɗa, wai Jalal ya cewa su Baffa Zakari da Baffa Lawallin su kawo masa sana'ar da suke son yi zai basu jari. Wai Baffa Zakari ma na shirin barin aiki ƙarshen watan nan, amma shi Baffa Lawalli sai ya ɗau abin da zafi wai Jalal ya rena masa wayo. Ni dai ban ce mata komai ba." Lokacin dana dawo gida bayan Magariba kwantawa na yi akan gado ina tunanin 'yan'uwana. Baffa "Lawalli ganin wacce za ta fitar dashi daga Talauci yake mini. Dukiya kuma ba tawa bace, ko shi Jalal" ɗinma ba nasa shi kaɗai bane balle ya riƙa kashewa 'yan'uwana kuɗi. Ni kuma Restaurant ɗina yanzu aka "buɗeta, bamu ma san ko za mu ɗaure da ciniki ba balle mu yi maganar riba. Kafin na baro gidan dai na" yiwa Baffa Lawalli transfer ɗin dubu ishirin. Da dubu goma cash na yi niyyar bashi amma yadda ya buge da yi mini faɗa yana mini karatun shi yayi mini tarbiyya sai na ga idan na bashi dubu goma ma renawa zai yi. Kai! Allah dai ya sa na wanye da kowa lafiya. Gobe zan yiwa Jide magana ko za a samu space da za a ɗauki staff ko biyu ne na ɗauki yaron Baffa Lawalli ɗaya na Baffa Zakari ɗaya. Ba a jima ba na fara juyi ni kaɗai bacci ya ƙi zuwa mini. Kewan Jalal nake. Tun safe da ya mini text bai "sake yi mini wani ba, da kuwa sai na ga text ɗinsa biyu ko uku a rana." Wayata na jawo na shiga Whatsapp ɗina sai na ga yana online na tura masa sallama. Bai buɗe ba sai wajen minti uku kafin ya min reply wai na yi haƙuri yana video call da Junior ne. Na tambayeshi video call kuma. Dama ba a gida ɗaya suke bane?. Ya ce min wai tunda ya tafi bai samu ganin Junior ba sai ɗazu ne bayan ya yi waya da Kakar yaron ta haɗasu a waya. Ashe Matar tasa ɓoye Junior ta yi a wajen Mamanta. Na ce Allah ya kyauta. Ya tambayeni ya jikin Kaka na ce masa da sauƙi tana gaishe shi. Haka kawai sai na tsinci kaina da jan hirar tamu. Na faɗa masa abinda kitchen staff ɗina Zainab ta yi a Gidan Girki. Na ce masa zan sacking ɗinta ƙarshen wata ya ce hakan ya yi dai-dai saboda chanja mana ingriedients na nufin za ta iya saka wani abun a gaba da zai lalata mana abinci. Na ce masa ina so na ɗauki yara biyu a gidanmu na basu aiki a Restaurant ɗin. Ya ce zai tambayi Manager Plaza ɗin ya ji ko akwai vacancy a wajensu koda na mutum ɗaya ne. Kan kace me mun share awa ɗaya muna chatting muna tattauna abubuwan da suka shafi business. "Shi da kansa ya ce na kwanta tunda zan yi fitar sassafe. Na yi masa sallama, ina shirin sauka ya turo last" "message ɗinsa: I LOVE YOU, Sunshine." Na manna wayar a ƙirjina ina murmushi... CHAPTER FIFTY SIX ZEEY "Ƙarfe shaɗaya na safiyar ranan Alhamis kenan na gama shiri zan je gidan Hajiya, ta kirani wai na zo na" mata miyan kukan wai Saurayin Janan zai zo ta sa an yi masa girke-girke ita kuma ba za ta iya ci ba. Dama ban je Gidan Girki ba. Da safe na je School mun yi wani test ƙarfe takwas na safe daga nan na tattaro na dawo gida saboda kaina dake ciwo. Sati guda kenan back-to-back idan na fita Restaurant bana dawowa gida sai ƙarfe biyar ko shida na yamma. Allah ya buɗa mana a satin mun samu order daga gidan Sarki. An yi wani bikin naɗin Sarauta shine aka bamu order yin abinci na kwana biyu. Mun sake samun wani order daga wani babban ɗan Kasuwa ana bikin 'yarsa muka musu abincin ranan Kamu. Wannan ya sa na ja ragamar girkin da kaina saboda kar a samu matsala su ɓata mana suna. Lokacin dana ke kulle ɗakina sai na ji ƙaran shigowar text a wayata. Ko ban duba wayar ba na san Jalal ne. Cikin sati ɗaya wani sabon shiri muka ƙulla har mamakin kaina nake ni da na yi ta cika bakin ba zan kula shi ba har sai ya saki Cassandra. SO wani wawan abu ne. "Ba fa wai na dena jin haushin Jalal gabaɗaya bane, har yanzu ina jin haushin abinda ya mini amma kuma" wani mugun sonsa da nake ji sai ya danne fushin dana ke mishi ya mayar da shi kewa. I MISS HIM SO MUCH. "Ni dama ban iya soyayya ba, idan na fara son mutum to da dukkan zuciyata nake yi. Lokacin da muka yi" soyayya da yaya Aminu har bayan mun rabu ban dena son shi ba sai a hankali soyayyar ta fara raguwa har kuma na rufe komai. Bana tunanin na yiwa yaya Aminu irin son da na ke yiwa Jalal yanzu. Ni kaina ina mamakin yadda nake wani mahaukacin sonsa. Shi yasa duk da ina fushi da shi hakan bai hana ni jin daɗin hiran da muke idan muna chatting ba. Mun jingine maganar Cassandra a gefe. Ba ya mun maganarta nima bana tambayarsa labarinta. Idan abinda ya faɗa kafin ya tafi gaskiya ne to duk rintsi zai tsinke alaƙar dake tsakaninsu kafin ya dawo gareni. Ko maganar Junior bana yi masa. Tunda ya ce min yaron yana wajen Maman Cassandra kuma suna waya "sai na ja bakina na tsuke. Tunda yaron na nan lafiya, shikenan babu abinda zan iya masa sai addu'ar samun nasara, which ina yi kullum." Hirarmu da shi ta fi karkata kan business ɗina. Kuma sosai nake jin daɗin yi masa taɗin Gidan Girki. "Gidan Girki, ko gidan Drama." "I LOVE YOU AGAIN, SUNSHINE." Na karanta abinda ya turo. Ina ga dai kafin ya tafi sai da ya sha laƙanin kalaman soyayya. Murmushi ne "ya suɓuce min dana sake karanta text ɗin. A kullum sai na samu saƙon I Love You sau uku a rana. Ban taɓa nuna masa abinda ya ke turowa yana tasiri a zuciyata ba, amma kuma ni kaɗai na san sau nawa nake maimaita saƙonnin nasa a rana. Tilawarsu nake duk dare kafin na kwanta idan muka gama chatting da shi. Kuma hakan ba shi zai hana na tisasu bayan sallar Asuba ba." Wataƙila da ya buɗa mini zuciyarsa tun farkon aurenmu da ba zan yi kokonton soyayyarsa gareni ba. Lokacin dana isa gidan Hajiya sai na samu an cika dining da abinci kala-kala ko ina sai ƙanshi yake. "Hassana data buɗe min ƙofa ta fara min gulmar wai yanzu Saurayin da ya yi girkin ya tafi, ashe ma namiji" ne Chef ɗin. Na ce ina Hajiya wai tana falon sama na wuce saman dan na gaishe da Hajiya kafin na koma kitchen na yi mata girki. """Lale Marhaban! Ai yanzu nake cewa zan sake kiranki ashe kina tafe""" "Na yi murmushi na risina na ce ""Hajiya, Ina kwana""" """Lafiya, Ziyada. Daga can Plaza kike ne?""" """A'a"" na ajiye jakata a gefe na gyara zamana." """Ban ma leƙasu ba yau. Na dai je School da safe mun yi test. Sadda kika kirani ma ban jima da dawowa" "ba""" """Allah Sarki. Ya test ɗin?. Kina dai samun lokaci kina karatu ko?""" """Ina karatu sosai Hajiya""" """Allah ya sa a gama lafiya"" na amsa da Amin." """Hajiya, ina Janan ne?""" """Yanzu ta shiga ɗakinta ina ga shiryawa za ta yi. Khalifa ya shigo gari yana gidan yayarsa daga can zai" "taho nan""" """Ayya! Allah ya kawo shi lafiya"" Hajiya ta ce Amin." Lokacin dana miƙe zan tafi sai Hajiya ta tambayeni fatan babu matsala na ce mata babu. Na sauka ƙasa na samu Hassana mai aiki na tambayeta me suke da shi a ƙasa. Lokacin da nake tuƙa tuwon shinkafa tsinin takalmin Janan da gudunta ya tabbatar mini Saurayinta ya iso dan na ji ƙaran shigowar mota gidan. Yau dai zan ga Mi Amor da Janan ke ta waƙarsa tun zuwana gidan. Bayan na gama kwashe tuwon ban fito ba na ce Hassana ta je ta ɗauko min gyalena dana bari a falon sama. Matar aure nake babu mutunci na wuce ta gabansu babu mayafi. Da ta kawo min na gyara mayafina da kyau sannan na fito. Suna zaune a falo. Hajiya na kujerar mutum ɗaya ita kuma Janan da baƙon namu suna zaune a two seater. Yadda ta Janan ke yi ka ce za ta shiga jikinsa ne. """Zo, zo, 'yata ku gaisa da Khalifa"" na ƙarisa wajensu na gaishe shi bayan Hajiya ta ce masa ni ce matar" Jalal. "Sai wani shan ƙamshi yake yana wani amsawa a daƙile, na ce kan buuu ya jima bai buɗe baki yayi" "magana ba. Ko lokacin da Jalal yake jin kansa kafin mu yi aure ba zai min haka na ƙyaleshi ba balle wannan guntun. Khalifa kyakyawa ne kam, sai dai guntu ne. Ga masu son farin namiji zai musu kyau overrrr amma irinmu da muke son baƙin mutum,to a kai kasuwa." Na tabbata yadda Janan ta saka takalmi mai shegen tsinin nan idan ta tashi sai ta fi shi tsayi. Na yi "mamakin wannan ne Khalifan da take ta rawar jiki a kansa. Koda yake abincin wani, guban wani." """Ashe kai ne KHALIFAN?"" na kausasa ƙarshen dan ya tabbatar jinsa ya fi ganinsa a wajena. Daga yanayin" "yadda ya wani haɗe gira na san ya ji zafin hakan. Aikin ɓur in ji tusa!. Ni da nake da miji dogo santalele zai tsaya yana wani ja min aji, mtswww!." Wucewa sama na yi na barsu a falon. Ɗakin Jalal dake gidan na shiga dan na yi sallar Azahar. Dana idar na fito daga ɗakin dan na ɗebi abinci dan yunwa nake ji. Tuwon zan ci nima dama na ce Hassana ta kawo abincin sama tunda dining ɗin ƙasa kam Mai girma Janan ta cike shi da abinda Chef ɗinta ya girkawa Khalifanta. Ai ina fitowa na samu Hajiyar ma abincin take ci. Sai na ji babu daɗi na ɗebi nawa na koma ɗaki sai kawai na zauna nima a wajen na fara ci. """Wallahi miyar kukan ki daban ce. Sau dubu idan Hassana ta yi miyar Kuka idan na taɓa naki sai na ji" "banbanci, kuma ba Hassana kaɗai bafa. Na rasa ya aka yi duk sadda nake cin miyanki sai na riƙa tunowa da Kakata, Allah ya jiƙan Hajiya. It's like kamar ita ta yi miyan""" Na yi murmushi. Nima ban san sirrin ba. Yau har tsayawa Hassana ta yi wai ta ga yadda nake yi saboda "itama Hajiya ta dinga yaba nata. Ban ɓoye mata yadda nake yi ba. Wataƙila banbancin yana daga haƙurin jiran ruwan kukan ya tafasa da kyau ne kamar yadda Kaka ta koya min kafin a kaɗa, ko kuma dai hannuna ne tunda akan ce girki hannu-hannu ne. Allah ne masani." Muna cikin cin abinci Hassana ta zo wai idan akwai sauran tuwon za a kaiwa Khalifah ya ce Tuwo zai ci. """Sai dana cewa Janan a mishi Tuwo ta ce wai Tuwo bai dame shi ba, ai gashi nan. Abubuwan da ta sa aka" "masa dai shi ya saba shi a chan UK ɗin""." "Ina ganin Hassana tana ɓoye dariyarta, da alama akwai gulma a bakinta kenan." Ta ɗauki ragowan Tuwon ta wuce da shi ƙasa. Bayan na ci abinci ɗakin Jalal na wuce dan na ɗan kwanta na huta kafin la'asar sai na wuce gida ko kuma na leƙa Gidan Girki. Ban jima da fara bacci ba na ji ana ƙwanƙwasa min ƙofa. Na miƙe da ƙyar dan bacci ya fara min daɗi na je na buɗe ƙofar...Janan ce. "Ta wani shigo fuuu ta ce ""Na zo ki bani maganin da kike sakawa a abincinki""" Na haɗe gira dan ban fahimci me take nufi ba. """Tell me why Khalifah zai cinye ƙaton Tuwon da Hassana ta kawo mishi. Me kike sa a ciki?. Shi yasa" "tunda kika yiwa Hajiya girki sau ɗaya Hajiya bata dena yabon abincinki ba har yau. Yanzu kuma, Khalifana" "da ba ya son cin Tuwo shine yake tambayar wai idan da ƙari yana so miyar ya masa daɗi...""" """Ki ce ya je Gidan Girki ya siya a chan"" na faɗa ina dariya." """Allah ba wasa nake ba""" """Maza ai suna da munafurci. Dama dai yana son cin Tuwon ke ce dai ba ki gano hakan ba"" na faɗa ina" dariya. """It's not funny, Ziyadah. Allah ban taɓa ganin Khalifah ya cinye ƙaramin Tuwo bama balle babban Tuwo" "haka""" """Ba mamaki dan bai taɓa cin mai daɗin nawa bane. Amma ki biya ni Miliyan goma na koya miki sai ki" "dinga yi masa idan kuka yi aure""" "Ta watsa min harara tana faɗin ""Allah ya kiyaye in zama Cook. Zan dai nema masa wacce ta iya Local" "Dishes ta dinga masa duk sadda yake so""" """Uhumn!"" Na faɗa ina jijjiga kai. Janan bata san karatun aure ba. A yadda nake ganin Khalifan nan ba" mamaki idan suka yi aure yace ba ya son 'yar aiki a gidansa. Na san idan muka samu zama da Hassana za ta min gulmar abinda ya faru har ya ce Tuwo zai ci. Da yamma lis na koma gida dan ban tashi daga baccin dana yi da wuri ba. "Da dare da Jalal ya chatting ɗina sai nake faɗa masa Khalifah ya zo, na tambayeshi ya aka yi suka fara" soyayya da Janan. Ya ce min Uncle ɗin Khalifah abokin Daddynsu ne ƙut da ƙut. Sadda Khalifah ya zo London karatu shine "Uncle ɗinsa ya ce ya zauna a gidansu. To a wannan zaman ne suka saba sosai da Janan daga baya kuma suka fara soyayya. Dake yana son boko sosai wai ba zai yi aure ba sai ya ƙare Phd ɗinsa shine fa aka ɗaga auren har sai yanzu daya gama degree ɗinsa na uku. Na ce ikon Allah! Na tambayeshi yaushe auren ya ce min sai ƙarshen February. Yanzu muna November, da ɗan sauran lokaci." Ban faɗa masa yadda Khalifan ya wani sha min ƙamshi ba lokacin dana gaishe shi. Amma daga yadda ya ɗan bani labarinsa sai na fahimci mugun girman kai gare shi. Yadda Janan ke ta rawar ƙafa a kansa. Allah dai ya sa yana sonta. *** Bayan sati ɗaya da zuwan Khalifa wata ranan Asabat ina Gidan Girki sai ga Janan ta zo office ɗina wai tana so na koya mata yadda ake yin Tuwo da miyar Kuka mai daɗi irin nawa. """Shi kaɗai zan koya tunda Mi Amor yana so"" ta faɗa tana wani haɗe fiska dan kar na mata dariya." Ni ce dai nan CHEF ZEEY data kira da Local Chef. """An gama ranki shi daɗe"" na faɗa nima ina haɗe rai." """Nawa za ki biya?""" """Sai na biya?. Kina matar Yayana ɗin""" """Matar Yayanki nake ai ba Malamarki ba""" """Whatever, nawa zan tura miki?"" Ta faɗa tana ɗaga wayarta irin dana faɗa za ta min transfer ɗinnan." """10 Million""" """10 Million! You're not serious. Dan za ki koya min abu ɗayan shine zan baki 10 Million. 10 Million fa" "budget ɗin kayan kitchen ɗina ne""" """Iyi. Idan kika yi siyayyar kayan kitchen ɗin ai sai kin iya amfani da su kafin su ci kuɗinsu ko"" na faɗa ina" dariya """Dariya ma kike min ko. To na fasa ma ba sai kin koya min ba. Kuma zan kira yaya Jalal na faɗa masa""" """Ki roƙe ni ki ce 'Anty Chef Zeey, dan Allah ki koya min yadda ake Local Dishes wanda zai ja hankalin" "Mijina, yanzu na gane cewa Maza sun fi son abincin gida' kin ga sai na koya miki ko sisinki ba zan karɓa ba""" """Sai na baki haƙuri?. You know what, manta kawai"" ta tashi fuuu ta fita tana faɗin ta fasa ma ba zata" koya a wajena ba. Maza kenan! Janan dai dana sani data ƙwammaci ta riƙa cin pizza da shawarma kullum da ta ci Tuwo ita ce wai ke son na koya mata girki. Daga sanin Hajiya Layla har zuwa yau bana tunanin Janan ta taɓa shiga Kitchen ta dafa ruwan shayi ma balle wai ace Shinkafa ko Tuwo. Sai ga shi son namiji ya chanjata rana ɗaya? Ikon Allah!. Fushin Janan ko kwana biyu bai kai ba. Hajiya ta kirani wai Dan Allah na zo zan fara koyawa Janan girki. "Ai kuwa dana je gidan na zage na dinga yi mata dariya, wai ashe Hajiyar ce ta ce idan bata tsaya ta koyi girki ba ba za ta barta ta je Dubai da China siyayyar kayan kitchen da kayan ɗaki ba." Kai Jama'a! da gaske fa Janan bata iya komai ba. Ko lokacin dana ke koyawa Hayfa girki 'yar Hajiya Maryam ban ga irin wannan kwaɓar da Janan ke yi ba. Ai Hayfa ma nata da sauƙi ta ɗan iya dafa su Indomie da su soya ƙwai. Har Jollof Rice ta ɗan iya kafin mu fara class da ita amma wannan yadda ka san 'yar shekara takwas nake koyawa girki haka muke da ita. Komai bata iya ba. Idan ta yi wata tambayar ma idan na kalleta sai na rasa abin faɗa. Hassana ce 'yar dariya idan ta ji muna drama da ita. Ni kam abin ma ya dena bani dariya sai mamaki. Like na san a gidan kuɗi da jin daɗi ta taso amma koyon girki ai bana ɗan talaka kaɗai bane. Abu ne da duk min kuɗinka dai za ka kowa ko dan sha'awa ko kuma dan ɓacin rana. Maza dayawa sun iya girki balle Mace. To ko matar jikan Queen Elizabeth an ce tana girki. Na taɓa ganin video a YouTube an nuna tana girki. Kuma ta ce lokaci zuwa lokaci tana yiwa Mijinta da 'ya'yanta girki dan tana jin daɗin hakan. Koda yake itama an ce 'yar Talaka ce kafin ta auri Prince William ɗin. To ko kuma dai Talaka kaɗai ya kamata ya iya girki ne?... "A haka dai muka yita gurgurawa, a yi faɗa a shirya. Tun tana yi dan Hajiya har ta zo ta saduda fa ta gane" koda za ta ɗauki mai yi mata girki akwai ranan fa da Khalifah zai buƙaci ta yi masa da kanta. Kuma da alama Khalifan na ta ɗan packaging ne. A waje zai nuna baya son gargajiya a gefe kuma yana so. Ranan da ya sake zuwa dake da safe ne Masa muka yi masa da Danderu. Ni dai dan Hajiya na yiwa ba dan shi ba. Janan har da maƙale masa tana nuna masa hannunta wai har ƙonewa ta yi wajen juya Masa. Ku ji fa!. A hankali sanyin December ya shigo wanda ya ƙara mini kaɗaici da kewar Mijina. Yanzu kam na saduda ko da ba zai rabu da Cassandra ba in dai zai dawo gareni ya bani kaɗan daga kulawarsa zan zauna da shi a hakan. Zuciyata da gangan jikina suna kewarsa. Duk lokacin dana kwanta na tuno da ranan dana sha kashi a hannunsa sai na ji ina tsirtar da ruwa. Ina ga har da laifin sanyi a yadda nake missing ɗinsa sosai. A January za mu yi Jarrabawar First Semester. Bana son samun Spill Over dan haka na sakawa kaina karatun dole. Ko na fita aiki idan ina zaune a office babu abinda nake handout ɗina nake ɗaukowa na ɗan lelleƙa sama-sama. "Ni ba guruwa bace a Makaranta, na san kaina, in dai na yi tisin karatu a ƙalla sau biyar kafin exams to da" wuya ka ga na manta abubuwan dana karanta. Allah na gani idan na karɓi BSc Certificate ɗina to ni da Karatu mun yi hannun riga kenan. "Kafin mu shiga January Janan da wata ƙanwar Hajiya dake Lagos suka tafi Dubai siyayya, wai har India da" China za su je. "Har yanzu dai bata iya abubuwa dayawa ba, amma dai babu laifi ta ɗan fara iya wasu." "Gidan Girki kuwa har yanzu Masha Allah, muna samun mutane musamman masu order daga gida. Sai" dai fama da matsalar Staff. Mun sallami Zainab Jide ya kawo mana wasu guda biyu mace da namiji. Namijin sunansa Sanusi sai macen sunanta Majida. Da aka fara exams sai na maida hankalina gaba ɗaya kan karatu. EDD ɗin Faty ya faɗa cikin Exams dan "haka sai addu'ar kada ta haifu take sai bayan mun gama Exams. Kai ciki bai karɓeta ba, ta yi wani ƙiba ne ta kumbura ta yi baƙi ga Pimples da ya cika mata Fiska. Ba ƙaramin tausayinta nake ji ba musamman idan na tuna halin da take ciki. Ta auri maƙaryaci. Ya mata alƙawarin zai barta ta cigaba da sana'arta idan sun yi aure ta zo ta aureshi ya ƙi fir ta cigaba da sana'ar Make up ɗinta kuma ba wai yana da halin ciyar da ita da kyau bane. Gaskiya lamarin aure sai da addu'a da Istigfari. Ba za ka taɓa sanin gaskiyar namiji ba sai ka aure shi." A yadda ta faɗa mini dai wai idan ta haihu zata koma sana'arta ko yana so ko baya so wai ta gaji da bani- bani da take yiwa mutane. Ni dai ce mata na yi Allah ya taimaka. Ah to! Yanzu na ce mata ta yiwa Mijinta bore ta zo gobe su shirya da mijinta ta ce ai yiwa Miji biyayya sunna ne shi yasa ta watsar da sana'ar Make up ta riƙe Miji. To ba da ni ba. A hankali idan ta nitsu za ta nemawa kanta mafita. Ko Make up ɗinne ko wata sana'ar daban ne dai dole ta yi idan tana so ta siyawa kanta mutunci ta kuma samu kwanciyar hankali. Dan BABU mugun ciwo ne. Allah ya rabamu da BABU. Saura Exams biyu mu gama Faty ta haihu. Ana gobe zamu rubuta Paper ta haihu da dare ta samu ɗanta namiji. Bata samu zuwa Exams ɗin ba wanda ta sani Automatic Spill Over biyu kenan. Ban samu na je na dubata bama sai bayan kwana huɗu da haihuwar. "Dama cikin ya sakata ƙazanta to haihuwar ma dai bai chanja komai ba, Matar dana samu da ita kuma" itama wata ƙazamar ce tunda ta ƙi tsaftace gidan. Dana shiga ɗakinta kaman zan yi amai saboda ƙarni. Subhanallahi!. Faty ta ce Dan Allah na zo mata Suna. Wai na yi haƙuri na manta da abubuwan da suka faru mu koma "kamar da. Wai yadda na yi ta shige da fice a bikinta na daure na zo a yi hidimar suna da ni. A take na ce mata ta yi haƙuri Jalal ya ce ba zan zo Suna ba, daga Barka shikenan. ASTAGHFIRULLAH nima na shiga sahun masu ƙarya da sunan Miji. Jalal bai hanani zuwa Suna ba, dana ce masa zan zo mata barka ne na ce ina ji ba zan je Suna ba, sai bayan Sunan zan nemi lokaci in sake zuwa ya ce mini ba komai. Dubu talatin ya tura min in bata na haɗa da nawa dubu goman na kawo mata Cash dan na lura kamar Mijinta na da access da account ɗinta. Na haɗo da rigan yara guda biyu dana siya a Plaza da kuma Pampers mai guda hamsin. Ai na mata. Lokacin aurenta ma dana yi ta up and down na kashe kuɗi na yi ta zirga-zirga da me ta saka min. Ta roƙeni kuma na yafe, amma maganar BESTIE BESTIE ya ƙare kenan kuma sai a wata duniyar idan ana yi..." JAYKAY A ɓangaren Jalal cikin wata biyu da ya yi a London sun yi zama a Kotu sau biyu akan maganar riƙon ɗansa "Junior. Abinda Cassandra ta faɗawa Kotu shine wai zaman Junior a Nigeria akwai hatsari. Tana tsoron saboda rashin tsaro a Arewacin Nigeria ɗanta zai iya faɗawa hannun Kidnappers ko kuma 'yan Ta'adda, ko kuma ma rikicin rashin tsaro ya jawo masa mummunan Trauma a rayuwarsa. Sannan ta sake gabatar da cewa Jalal ya auri wata matar a Nigeria dan haka baya kula da yaron yadda ya kamata wai baya ma zama da shi a gidan Kakarsa yake zama kuma Kakar yaron bata kula da shi saboda bata son Cassandra. Ta cakuɗa ƙarya da gaskiya ta faɗa. Sai dai Kotu ta yi watsi da maganar auren Jalal saboda baya cikin abinda za su duba tunda case ɗin Divorce da ake daban da wannan na neman Custodyn Muhammad Junior." Shi kuma Jalal ya gabatar da cewa yana neman full Custody na ɗansa ne saboda Cassandra tana shan giya (Alcohol abuse). Saboda haka zamansa tare da Cassandra zai iya jawo masa hatsari sannan ya gurɓata tarbiyyansa. Da aka ce ko suna da shaidar cewa tana shan giya ta bugu har ta fita hayyacinta sai Lawyan Jalal ya fito da wasu takardu ya miƙawa Alƙali. """He's my son. Why would I do anything to hurt him?"" Cassandra ta faɗa da ƙarfi." Alƙali ya ɗaga kansa ya tambayeta ko ita ce aka kamata da laifin tuƙi cikin maye watanni biyu da suka wuce. Cassandra ta zaro ido. Alƙalin ya sake ɗaga wani takarda ya ce shekara huɗu da suka wuce an kamaki da laifin cin zarafin Sakatariyarki mai suna Jessica Edwards inda Kotu ta sa kika biyata taran kuɗi Euro dubu goma shabiyar. """It was a mistake, your Honour"" Cassandra ta faɗa a ƙoƙarinta na son kare kanta." Alƙali ya cigaba da kallon takardun da aka bashi daga baya ya tambayi ina yaron yake aka ce yaron yana waje tareda Kakarsa. Ya ce a kawo masa yaron Chamber sa zai gana da shi... CHAPTER FIFTY SEVEN """Darling, you have to choose me, okay?"" Cassandra ta faɗa da ƙarfi lokacin da aka wuce da Junior ta" gabansu. Jalal ko ɗar bai ji ba da yadda Cassandra ke roƙon Junior ya zaɓeta ba shi ba. Ya riga ya san yadda yaron ke son Hajiya ba zai amince ya cigaba da zama wajen Mamansa ba. Amma duk da haka sai ya fara addu'ar samun nasara a ransa. Allah ya tabbatar masa da burinsa. Ita kuwa Cassandra sai sintiri take a wajen. Ba zai yiwu ta rasa ɗanta sannan ta rasa Jalal ba. Divorce petition ɗinsu yana gaban Alƙali kuma yadda Jalal ya ɗaɗɗaureta da cewa idan ta ƙi amincewa da sakin zai nemi rabin dukiyar data samu bayan aurensu sai ta fara saduda da lamarin. Duk abinda ta samu ta same shi ne bayan aurensu da Jalal dan haka idan Lawyansa ya buƙaci a raba dukiyartata biyu a bashi rabi a matsayin compensation ko Alimony babu yadda za ta yi. "Idan har babu wanda ya janye Sakin tsakaninsu ya tabbata kenan wata shida bayan shigar da ƙaran," aurensu zai warware. Yanzu saura watanni uku da kwana goma shaɗaya aurensu ya ƙare. Bayan minti talatin da shigar Junior chamber Alƙali sai aka kirasu. Suna shiga Cassandra ta yi kan Junior za ta rungumeshi yaron ya yi sauri ya faɗa jikin jalal ya ƙanƙameshi. Tunda Cassy ta ɗaukeshi daga Nigeria sai yau ya ga Babansa ido-da-ido. Lokacin da Jalal ya gano yaron na wajen Maman Cassandra Lawyansa ne ya ce ya barshi a can saboda su samu hujja a gaban Alƙali na cewa Cassandra ta hana shi ganin yaron. Abinda yaron ya yi sai ya sake tabbatar wa mutanen da ke wajen cewa Jalal ne zaɓinsa. Dukkansu suka kasa kunne lokacin da Alƙali ya fara karanto hukuncin da Kotu ta yanke. """The Court awards full custody of MUHAMMAD JALAL MAIYAƘI, age nine, to his father, Mr. Jalal Kabeer" "Maiyaƙi""" """NO...Nooo"" Cassandra ta yi ihu tana miƙewa." Lawyanta ne ya zaunar da ita yana cewa ta kwantar da hankalinta a gama karanto hukuncin Kotun. Shi kam Jalal tunda Alƙali ya ce ya damƙa masa gabaɗaya riƙon ɗansa sai ya fara Hamdala a zuciyarsa. "Alƙali ya cigaba da bayani, inda ya bawa Cassandra damar zata iya zuwa ganin Junior a Nigeria a duk" lokacin da ta ke so amma sai da izinin Jalal. Sannan sau biyu a shekara dole ne Jalal ya tura yaron hutu wajen Cassandra har zuwa lokacin da yaron zai cika shekara 18 ya zaɓi inda zai zauna da kansa. Jalal kam ba shi da matsala da wannan tsarin. Dan dai sau biyu a shekara ya tura mata Junior hutu ai ba komai bane. Dama riƙon yaron ya dawo hannunsa shine cikar burinsa. Shi da Lawyansa suka tsaya cika takardu yayin da Cassandra ta tsugunna gaban Junior tana masa masifar "me ya faɗawa Alkali lokacin da ya tambayeshi da wa zai zauna. Yaron ya yi shiru bai amsa ba. Da ta ga ya tsorata da yadda take masifa sai ta kwantar da murya ta fara cewa ""I'm going to be a good mother from now on. I won't yell at you again, I promise. Please stay with me, okay"" sai kissing ɗinsa take tana jaddada cewa za ta ɗaukaka ƙara ta karɓe shi, ba za ta bari ya koma Nigeria ba." Lokacin da Jalal ya fito daga office ɗin Alkali ya zo zai tafi da Junior sai Cassandra ta rike yaron tana masifar ba zata bari ya tafi da shi ba. """He's my son"" ta faɗa da ƙarfi kamar za ta yi kuka." Sai da Lawyanta ya jata gefe ya mata magana sannan ta haƙura ta sakewa Jalal Junior. Maman Cassandra ta ce za ta aikowa Jalal kayan yaron gidansa. Ya ce mata Passport ɗin yaron kawai yake buƙata. """Dad, ka kaini wajen Hajiya"" Junior ya faɗa lokacin da suka shiga mota." """Zan kaika wajen Hajiya, da Janan, da Zeeyadah, da kowa ka ji"" ya faɗa yana kissing goshinsa." "Matseshi ya yi a jikinsa kamar za a ƙwace masa shi a cikin motar, a haka har Lawyansa ya sauke su a" Family house ɗinsu na London... *** ZEEY "Wallahi idan kana business ko, idan Staff ba su sa maka hawan jini ba za su iya haukatar da kai." Jiya-jiya aka yi case ɗin wani Waiter ɗinmu da yake karɓan kuɗi a personal account ɗinsa a VIP section ɗinmu. Wai ashe idan za su biya kuɗi sai ya ce musu POS ɗinmu na Gidan Girki yana da matsala zai bada account "su tura kafin a gyara. A irin haka a irin haka sai da ya rafke kuɗi ya kai dubu ɗari biyu da talatin ba a gane ba sai jiya da wani ya kira Manager ya ke ƙorafin ta ya zai biya kuɗi a account ɗin waiter ba Account ɗin Restaurant ba. Shine fa Jide ya ankara ya riƙe yaron ko sunansa ban sani ba sai jiyan, wai Kelvin." Yau kuma na shigo na samu ana case wai an kama Kitchen Staff ɗina Majida tana satan kayan abinci da Ingriedients ɗin Kitchen. Kaina ya ɗau zafi da aka faɗa mini. Lokacin da aka ɗauketa na ganta shiru-shiru da ita har nake cewa Jide yarinyar tana da hankali ashe-ashe. Da Jide ya tsareta da tambayoyi me yasa ta ke satan mana ingriedients da spices bata bamu amsar "gaskiya ba sai da ta ji zancen za a kira mata Police, Waiter da aka kama jiya ma yana hannun 'yan Sanda har yanzu." Farko ta ce mana gida take kaiwa saboda gidansu akwai matsalar abinci da ta ji an fara karanto Hadisan 'yan Sanda sai ta ce wai content ta ke yi da shi tana da TikTok da Instagram page. Ai kuwa da aka duba Majida's Meals a TikTok sai ga ta nan har da followers dubu biyu. Ikon Allah!. Ba ka da gashin wance ka ce kitson wance za ka yi. Ni sadda na fara food content ɗina da iya abinda Allah ya hore mini nake yi. Da murhun itace na fara na koma gawayi kafin na fara amfani da gas cylinder dana siya mana. Da naga ma an fi samun engagement idan na yi girki a murhu sai na fi yi da shi. Rasa ma me zan faɗa mata na yi. Na barta da Jide su je can su ƙarata. Ba za su samin hawan jini ba ana zaune ƙalau. "Washegari ina zaune a office ɗina sai ga Jide, ya ƙwanƙwasa min ƙofa ya tsaya daga bakin ƙofar ya ce" """Big Madam, ana son ganin ki""." """Dan Allah Jide kar ka ce wani rikicin ne ya sake ɓullowa. Na gaji"". Na faɗa ina murza goshina." "Dariya ya saka yana faɗin ""barin turo miki shi""" Maida hankalina kan ƙofar na yi ko sakan biyar ba a yi da fitan Jide ba sai ga shi an buɗe ƙofar. Wa zan gani face mutumin dana ke mafarkin ganinsa a kullum JALAL. JAY ɗina. Ban san sadda na miƙe tsaye ba ina tunanin shi ɗinne ko ba shi bane. Na ƙurawa fiskarsa ido ban ko ƙyafta ba. Takowa ya fara yi a hankali yana nufoni bugun ƙirjina yana ƙaruwa. Har yanzu kallonsa nake na kasa magana. Na kafe shi da idanuna wanda ya sakani lura da wrinkles ɗin daya taru masa a gefen idanunsa. Matsowa ya yi kusa da ni idanunsa suka sauka akan lips ɗina. Na san me yake shirin yi kuma ina maraba "da hakan, ilahirin jikina yana maraba da taste ɗin lips ɗinsa akan nawa, yaushe rabon?." Na ɗan buɗe bakina and kafin na gama bashi access tuni ya haɗe bakinmu ya shiga kissing. "Na faɗa jikinsa na saka kuka bayan ya raba kiss ɗin. Dukan ƙirjinsa na fara yi ina faɗin ""shine ka tafi ka" "barni ko waiwayowa baka yi ba. Shine ka tafi ka barni saboda saboda..."" ya rufe min baki da nasa na yi shiru ina mayar masa da zazzafan kiss har da tallafo kansa sosai." Jiya da dare fa mun yi chatting kuma bai ce min zai shigo Nigeria ba. Sake narkewa na yi a jikinsa ina shaƙar daddaɗan ƙamshinsa. I Love Him. "I Love JALAL so much. Na faɗa a zuciyata a dai dai lokacin ya furta min ""I MISS YOU SO MUCH, Sunshine""" na ji wasu ƙwalla sun zubo mini. Mantawa na yi a ƙaramin office ɗina muke. Mantawa na yi da muryoyin mutanen da ke shige da fice cikin Restaurant ɗin. Mantawa na yi da cewa watanni kusan uku baya na yi iƙirarin dena son shi. All that matters shine ya dawo gareni. Ban san me ya dawo da shi ba. Ko ya samu abinda ya je nema ko bai samu ba. Kai koda a ce idan na je gida yanzu zan samu Cassandra da gaba ɗaya danginta a gidan ba zai chanja "cewa ina son Mijina ba, kuma na shirya nuna masa soyayyar Aure." Ya tattaro fiskata ya riƙe zuwa lokacin hawaye ya gama ɓata mini fuska. """Please ki dena kuka. Bana son ganin hawayenki""" Ya kissing tsakiyar goshina da kuma karan hancina sannan ya fara goge min hawayen. ** """Shine ba ka ce min za ka dawo yau ba"" na faɗa a shagwaɓe lokacin da muka shiga mota zai kai mu gida." Yo! Me zan tsaya na yi a Restaurant bacin Mijina ya shigo gari. """Saboda na ga soyayyar dana gani a ƙwayar idanunki ɗazu""" """Ni babu abinda ka gani a idanuna""" """Aka ce ido dai baya ƙarya kuma sun fallasa sirrin dake cikin zuciyarki""" """Babu wani sirri a zuciyata. Kai dai ka sake binciƙe"" na faɗa ina juyar da fiskata." "Kamo hannuna ɗaya ya yi ya haɗe yatsunmu ya ce ""abinda na ke ji gameda ke ya fi abinda na gani a" "idanunki, Zeeyadah"" ban juyo ba amma murmushin da ya suɓuce min ya fallasa tasirin kalamansa a zuciyata." Gaskiya tafiyarsa London akwai alkairi tunda yanzu ya koyi bayyana abinda ke ransa. Muna shiga falon gidanmu ya sake rungumata sosai kamar an ce masa zan gudu. Kafin na ankara mun "fara kissing junanmu kaman wanda an ce daga yau ba za mu sake haɗuwa ba. Lokacin da ya ɗaukeni ya yi sama dani already na manta da batun jan aji na sallama masa kaina, ya yi duk abinda ya ga dama da ni." Kash! Bai yi abinda nake tunanin ba duk da na ga tsananin kwaɗayin hakan a idanunsa. Kwanciya muka yi a gadona muna mayar da numfashi bayan ya birkitani da rikitattun kisses ɗinsa. Sai dana fara dawowa hayyacina sannan na tambaye shi ina Junior?. Ya ce min yana wajen Hajiya. """Alhamdulillahi"" na furta a fili." Can ya tashi ya ce min yana zuwa. Ina ga ɗakinsa ya je bayan kamar minti uku sai ga shi ya dawo. Copy ne na takardar yarjejeniyar Custody ɗin Junior da aka bashi. "Ban tsaya karanta dogon turancin da ke jiki ba nace ""yanzu shikenan kai zaka riƙe Junior?"" Ya gyaɗa min" kansa. """Masha Allahu. Allah ya kaɗe fitina ya baka ikon riƙe shi da Amana"" ya amsa min da Amin." Divorce Petition na gani ɓaro-ɓaro a takarda na biyu da ya bani. Na ɗaga ido ina kallonsa dan ban san me hakan ke nufi ba. """Maganar rabuwata da Cassandra yana Kotu. Ina da sauran wata uku kafin auren ya warware gabaɗaya""" ya yi min bayani. Ikon Allah. Allah ɗaya gari banban. Yanzu dai saboda auren Kotu suka yi dole dai sai kotun ce za ta raba su. Wai yanzu a 'waiting period' suke. Idan waiting period ya ƙare shikenan Kotu za ta bada Final Order wanda shine lasisin raba aurensu. Daga nan Jalal Maiyaƙi da Cassandra Morgan za su kasance ba mata da miji ba. "Yayinda mu a nan Aure ke rabuwa da kalmomi uku rak! NA SAKE KI. Shi Bature, ko in ce Auren Kotu yana" da na shi tsarabe-tsaraben. Bayan Maghriba muka je gidan Hajiya dan na yi mata Barka. Dake Janan bata nan ita ɗaya muka samu da shalelen jikanta Muhammad. Mun samu yana kwance a jikinta wai ashe wai tunda Jalal ya kawo shi ya ƙi barin jikinta. Itama Hajiyar har fara'arta ya dawo sosai. Allah Sarki sai dana ga rama a jikin yaron. Ashe ba ubansa kaɗai ne ya rame ba har da yaron. """Haka kawai kun ɗagawa yaro hankali yana zaman-zamansa. Jibi fa yadda yaron nan ya koma daga ɗan" "wata uku da ya yi baya nan. Kun katse masa Makaranta, kun birkita shi""" "Haka Hajiya ta yi ta yiwa Jalal faɗa, har nima sai da faɗan ta shafeni. Jalal dai haƙuri ya yi ta bata yace" daga yanzu zai riƙa kula da lamarin yaron sosai. Sannan zai riƙa zuwa mana weekend gidanmu tunda dai Hajiya ba zata sake mana shi gaba ɗaya ba musamman yanzu da ake gab da auren Janan. Bamu bar gidan ba sai bayan Isha. Lokacin da muka koma gida bayan mun yi shirin kwanciya ina jikin Jalal ya kanainayeni sai ya fara bani labarin haɗuwarsa da Cassandra. Dana fahimci bai shirya taɓani ba sai nima na sake jiki da shi babu wancan tunanin a raina na buɗe kunne ina jin tarihin rayuwarsa dan ya faro ne daga kusanci da kuma soyayyar dake tsakaninsa da ƙaninsa JAMAL. """Ban taɓa faɗawa kowa wannan ba sai ke"" ya faɗa sadda ya karanto mini yadda ya biyema Cassandra" "har ya kwana da ita da yadda ta ce masa tana da ciki da yadda ta saka shi ɗaukan alƙawarin aurenta bayan cikin ya zube. Har zuwa yadda aka kira shi watarana yana shirin tuƙa jirgi aka ce masa Jamal ya rasu. Yadda hakan ya jawo ya tafka kuskure lokacin da Jirgi ya zo sauka, da yadda hukumar kamfanin jirgi na British Airways suka bashi suspension suka saka shi yin Therapy na dole. Bayan ya dawo kuma suka ce ba shi da nitsuwar da zai sake tuƙa jirgi sai dai ya yi aiki a ƙasa shi kuma ya ajiye aikin saboda babu abinda yake so sama da tuƙin Jirgi." Lokacin da ya faɗa mini Cassandra ta faɗa mishi cikin farko ba nashi bane sai na ji tausayinsa. Koda yake "ƙaddararsa ce ta zo da hakan, sannan shima har da laifinsa. Da bai kusanceta ba da ba za ta yi masa" ƙaryar ya mata ciki ba. "Kamo hannuna ya yi ya sarƙe da nasa ina jin nauyin da numfashinsa ya yi, abubuwan da ya faɗa sun taso" masa da ciwon da yake fama da shi shekara da shekaru. """Na san ban kyauta miki ba, Zeeyadah"" ya yi shiru." """ Ni da kike gani MATSORACI ne"" ya faɗi kalmar matsoraci da ɗacin abin a muryarsa." Na fara girgiza masa kai. """Shi yasa Hajiya ta ke cewa Jamal ya fini a komai""" """Ba haka bane"" na faɗa da sauri." "Ya yi dariyar takaici ya ce ""sai dana kai shekara 40 tukunna na fahimci a rayuwar nan idan kana tsoro ba" "za ka iya cimma komai ba. Da bani da tsoro da ban yiwa Cassandra alƙawarin aurenta ba. Da bani da tsoro dana rabu da Cassandra a lokacin dana shirya zama a Nigeria. Da bani da tsoro, da ban aureki ba sai dana warware Aurena da Cassandra""" "Ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""kin san yaushe na fara rage tsoro?""" Na girgiza kai. """Lokacin dana tinkareki da maganar deal ɗinnan""" Na waro idanuna waje. """Yes, Sunshine. Ke kika chanjani. Kuma har a yanzu ma fushinki da tsoron rasaki shi ya bani ƙwarin" "gwiwar rabuwa da Cassandra""" Ya yi shiru ina jin fitar numfashinsa da bugun ƙirjinsa yana ƙaruwa. Wani nitsuwa ne yake sauka mini a yanayin da muke ciki. A yanzu ko shakka babu ya cire min duk wani trace na kokonto da nake da shi akan son da yake mini. JALAL YANA SONA. TUN KAFIN NA FARA SON SHI. """I Love You, Zeeyadah""" """Wannan Tsohon kuma matsoracin yana matuƙar ƙaunarki""" """I LOVE YOU TOO"" na furta a hankali. ""Wannan 'yar Ghetton dai tana sonka sosai""" Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke wanda hawaye suka biyo bayan hakan. Na juyo na fuskance shi na sa hannu na fara goge masa hawayen. Na sani abubuwa dayawa ne suka saka shi zubar da ƙwalla. Nadama. Kewa. Soyayya. Da kuma Godiya. An ce Maza basa kuka. An ce bai kamata Namiji ya yi kuka ba. An ce kuka alama ce ta rauni. "Ni babu ruwana da 'an ce', abinda na sani shine Allah ya halicci ƊAN ADAM da rauni. Kuma babu laifi" "idan NAMIJI ya zubar da ƙwalla, a mafi aksari Jarumta ke saka hakan ba gazawa ba." """Thank you"" ya furta yana kissing hannuna lokacin dana gama goge hawayensa." Ban iya bacci da wuri ba. Na buɗe idanuna tar bayan Jalal ya jima da bacci. Labarinsa ne ya tsaya mini a rai. Na dinga jinjina lamarin Allah da yadda yake tsara ƙaddarar mutane daki-daki har watarana ka ga ƙaddarar wasu mabanbanta mutane sun haɗu waje ɗaya. "Wataƙila da baƙar fata, 'yar Nigeria Jalal ya aura ba Cassandra ba, da ni da shi ba za mu taɓa kasancewa" tare ba. Ƙila shigar Cassandra rayuwarsa ita ce sababin jawo zaren ƙaddararmu ta haɗu waje guda. "Babu abinda zan ce sai dai na ƙara yiwa Allah Godiya, domin shine Ubangijin da ya halicci Ƙaddara yake" kuma jujjuyata cikin ilimin Ghaibunsa wanda babu wani Mahalukin da ya san ya yake abinsa sai shi ɗin dai JALLA JALALUHU... CHAPTER FIFTY EIGHT JAYKAY Washegari da Asuba Jalal ya tashi zuciyarsa cike da farinciki. Ya ƙurawa Ziyadah dake bacci idanu yana jin so da ƙaunarta na ƙara shigarsa. "Faɗa mata labarinsa da kuma sirrin da yake ta ɓoyewa shekara da shekaru alkhairi ne, gashi ya taimaka" masa wajen ƙara samun fahimtar juna. Wani sanyi yake ji yana jinsa kamar wani sabon mutum. Alƙawari ya ɗaukanma kansa cewa daga yanzu ba zai sake ɓoye mata komai ba. Kuma zai riƙa jaddada mata irin soyayyar da yake mata. Ziyada Alkhairi ce a rayuwarsa. Tun yana London ya kira Janan ya ce mata za a haɗa bikinta da Reception ɗin aurensa da Ziyada. Ai kuwa sai da ta yi ta ƙuƙƙuni wai zai ɓata mata shiri kafin daga baya tace masa babu matsala. Duk da yana son sake kasancewa da ita amma sai ya baiwa kansa haƙuri zuwa lokaci kaɗan da zai bayyanawa duniya cewa Ziyada matarsa ce. Miƙewa ya yi ya shiga banɗaki ya ɗauro Alwala. Yana shirin fita Masallaci bayan ya yi Nafila Raka'a biyu a ɗakin sai Ziyada ta tashi. "Da ya dawo daga Masallaci kuwa sai ya samu bacci ya ɗauketa akan sallaya, da alama ba ta yi bacci da" wuri ba jiya. Shi kam rabonsa da bacci mai daɗi irin na jiya tun kafin Cassandra ta zo Nigeria. Ƙoƙarin ɗaukanta yake ya kaita kan gado ta buɗe ido. """Ki yi baccin ki"" ta rufe idanunta amma da ya gama shimfiɗata akan gadon sai ta tashi zaune ta ce ""Zan" "fita aiki. In haɗa maka breakfast? Me za ka ci?""" """Koma ki kwanta. You need to rest""" """Ina na ga ta rest. Staff ɗina dukka basu da hankali, daga masu satan kuɗin customers sai masu sace" "mana kayan abinci a kitchen. Ni Wallahi har na fara gajiya da business ɗinnan""" Ya yi shiru yana kallonta har ta gama bashi labarin abinda ya faru. Ba maganar sata bane ma matsalar Gidan Girki. Jiya kafin ya je office ɗinta sai da ya zauna kamar customer a VIP space ɗinsu ya bada order dan yaga ya kyawun service ɗin wajen yake. Yadda Waiter ɗin "ya treating ɗinsa ko haɗi babu da yadda ya kamata a yiwa VIP customer. Cewa ya yi a kira masa Manager," da Jide ya zo ya ganshi sai ya fara sara masa yana dariya. Sun ɗan jima suna magana da Jiden ma kafin ya kai shi wajen Ziyada. Hanata fita Restaurant ɗin ya yi ya ce ta kwanta ta huta. Sai ƙarfe tara na safe ta sauko za ta haɗa musu Breakfast. Biyota ya yi kitchen ɗin yana ganin yadda ta ke ta dibi-dibi tana neman abinda za ta haɗa musu. """Me za ka ci?. Ko in maka chips da Kifi tunda an ce kana so?"" Ta faɗa tana ɗan dariya." "Girgiza kansa ya yi ya tako inda take tsaye ya rungumeta ta baya ya ce ""Ki yi abinda kika saba yi duk" "safiya""" """To...ni fa ɗumame na fi ci da safe""" """Nima shi zan ci""" """Anya zai ishemu mu biyu. Tuwon fa babu yawa"" ta faɗa tana buɗe fridge." Bayan minti talatin suka zauna su biyu a dinning. Ɗumamen tuwo da shayi mai kauri da kuma toasted bread ta haɗa musu. Yaushe rabon su zauna su ci abinci tare. Har zuciyarsa yana jin zafin yadda abubuwa suka kwaɓe bayan "ya dawo daga Lagos, amma Alhamdulillahi komai zai dawo dai-dai." "Daga yanzu matarsa ɗaya ce, ita yake so, kuma ita yake son gina rayuwa da ita har ƙarshen rayuwarsa." Duk da dai sai nan da wata uku masu zuwa sannan Kotu ta bada Final Order da zai raba Aurensa da Cassandra hakan ba zai hana Wedding Reception ɗin Aurensu da ya shirya ba. "A shirye tsaf yake a yi biki a yi bidiri. A yi hotuna, a yi video a watsa ko'ina." So yake Duniya ta taya su murnan aurensu. So yake kowa ya san da cewa JALAL KABEER MAIYAƘI ya auri "kyakykyawar matarsa ZIYADA SADIQ HARUNA. Babu maganar ɓoye-ɓoye, kamar yadda aka yi lokacin da aka ɗaura aurensu." Yana son Ziyada kuma yana so Duniya ta shaida hakan. Bayan sun gama Karyawa Ziyada ta tattara plates ta kai kitchen. Biyota ya yi yana tambayarta da me zai "taimaka mata ta ce babu. Amma sai ya karɓe soson wanke-wanken daga hannunta ya fara wankewa. Dariya ta fara yi masa. Ta ce ""ka san na fara koyawa Janan girki""" """Ta faɗa mini ai. Chatting ɗina ma ta yi ranan ta tura min hoton hannunta wai kin sata ta ƙone a Kitchen""" """Lallai a gaishe da Janan. Mangyaɗa ne fa ya ɗiga mata a hannu ɗan kaɗan""" """Kin san sakalcin Janan kuwa...""" """Ga yayan Janan ma uban girman kai yana min wanke-wanke"" ta faɗa tana murmushi." "Sai da ya ɗauraye kofi a faucet sannan ya juyo ya ce ""wani yayan Janan ɗin kike nufi?""" """CAPTAIN JAY, Yayan Janan Maiyaƙi"" ta faɗa tana murmushi." """Ban san wa kike nufi ba. Amma Captain Jay ɗin dana sani ba shi da girman kai""" """Hu'umh! Da fa farkon haɗuwarmu da ƙyar kake mini magana""" """Anya ni ɗin kike faɗa ba wani ba""" """Kai ɗin dai, Mr Jalal""" "Ajiye plates ɗin ya yi a rack ɗinsu sannan ya juyo ya fuskanceta ya ce ""da gaske kallon mai girman kai" "kike mini?""" """Iyi. Sai ka yi ta wani shan ƙamshi kana yiwa mutane magana da gadara""" "Jawota ya yi ta faɗa jikinsa ya fara shafa gefen fuskarta da hannunsa ya ce "" bani da girman kai, Sunshine." "Ke ce dai baki fahimceni ba"" ya manna mata kiss a wuyanta. Suna cikin haka aka danna doorbell wannan ya sa Ziyada ta ja baya da sauri." Jalal ne ya je ya buɗe ƙofan. Hassana ce riƙe da hannun Junior. Ta gaishe shi ta ce Hajiya ta ce a kawo shi za ta Kano da safen nan. """Kano kuma?""" Wayarsa ya je ya ɗauko akan dinning ashe Hajiya ta masa missed call biyu ma bai sani ba. Kiranta ya yi yana tambayar lafiya za ta je Kano? ta ce masa an yiwa su Khalifa rasuwa za ta je gaisuwa tunda Janan "tana China bata dawo ba. Ya tambayi wa ya rasu, wai wani ƙanin Maman Khalifa ne." """Kaima ko zuwa gobe sai ka zo ka musu ta'aziyya tunda an zama ɗaya"" ya ce zai yi hakan." Bayan sun gama waya da Hajiya sai ya kira Khalifan a waya ya masa ta'aziyya... A gidan Junior ya kwana. Yaron dai bai sake da Ziyada ba amma yana maƙale da Ubansa har sai da ya yi bacci. Da suka zo kwanciya Ziyada ta cewa Jalal kaman yaron baya sonta. """Kar ki damu haka yake zai sake dake a hankali""" """Kana ji fa Hajiya ta ce nima har da laifina da Cassandra ta sace Junior ba tareda na sani ba""" """Kwantar da hankalinki fushi kawai take saboda ta yi 3 Months bata ga Grandson ɗinta ba""" """Me zan yi dan ya sake dani. Shi ba ɗan yaye ba balle na yaudare shi da Bobo""" Dariya ya saka ya tambayeta ko Bobo shine abinda ta sha ranan a wajen Hawar Sallah. Ta ce masa ba shi bane. Ta jawo wayarta ta browsing kamfanin Bobo ta nuna masa. Lallaɓata ya yi ya ce idan ya dawo daga Kano zai fita da su duka shan ice cream wataƙila a samu chanji "tunda Junior yana son ice cream sosai. A haka suka kwanta, wannan karan ma suna manne da junansu amma Jalal bai yi wani motsi ba har safiya..." ZEEY Bayan mun yi Breakfast sai Jalal ya wuce Kano zai je Ta'aziyya. Dake na ga babu abinda zan yi a gida tunda baya nan sai na samu Junior da ke kallon Cartoon a falo na tambayeshi ko zai bini mu je Plaza sai ya ce eh. Bayan na shirya sai muka fito tare. """Hajiya ga shi Yallaɓai ya fita da motar"" Maigadi ya faɗa." Ce masa na yi ya nemo mana Keke. Wani kallo ya mini irin zan hau Keke kuma. Akwai wata motar a can parking lot amma ni ban iya Mota ba. Ina tsaye a compound ɗin gidan Junior yana harba bindigar wasansa sai ga Maigadin ya shigo. """Hajiya, mai Keken yana waje""" Muka fito ya biyo mu yana yiwa mai Keken kashedin ya tafi damu a hankali. JK Plaza na ce ya kaimu ya ce 1500 na bishi da kallon baka da hankali. Dan kawai ya ga na fito daga gida mai Gate. """Dubu ɗaya Malam, za ka je ko ya?""" Dubu ɗayan ma na faɗa ne dan kar ya rena ni amma ai ɗari biyar ake zuwa. """Ai kin fi ƙarfin haka Hajiya. Ki biya 1500 ɗin dai""" Tuni Junior ya shige Keken tun ma kafin na gama ciniki da mai Keken. Na shiga nima ina ce masa idan na bashi 1500 ba zai ɗau kowa a hanya ba. Sai wani magana yake yana cewa gani kalar kuɗi bai kamata in yi jayyaya ba ko nawa ya faɗa sai dai "kawai na ciro kuɗi a jaka na bashi. Ban kula shi ba, da ya ga na share shi sai ya yi shiru. Ah to! Ina matar" aure ina zan tsaya dogon magana da wani ƙato. Abinda ya sa na ce zan hau Keke ma saboda Junior ne. Bana tunanin ya taɓa shiga Keke. Ai kuwa dana ga yadda yake ta kallon ƙauyanci sai na tambayeshi ko ya taɓa shiga Keke ya ce min a'a. To yau dai ya shiga. Da muka sauka a cikin Plaza sai na tambayeshi ko ya ji daɗin tafiyar ya ce min ya ji daɗi sosai zai faɗawa Dad ɗinsa a dinga kai shi Makaranta a Keke. A zuciyata na ce kana so ubanka ya maidani Ghetton dana fito kenan. Office ɗina muka fara zuwa dana fito zan shiga kitchen sai shima ya biyoni. A kitchen yake har sai da Jide ya zo ya ɗaukeshi suka fita. Ban sake ganinsa bama sai da aka yi Azahar. Captain Jay ɗina ya kira wai suna hanyar dawowa na ce masa muma muna Gidan Girki amma yanzu zan tashi ma. "Captain Jay, sunan dana ke kiransa yanzu kenan tun ranan da ya bani tarihin rayuwarsa. Na san ba zai" "sake tuƙa Jirgi ba, amma ni a wajena har yanzu Captain ne. Baya tuƙa jirgi amma yana tuƙa zuciyata, shi" yasa nake jinsa har raina. Lokacin da za mu dawo ma Keken muka hau aka kawo mu har bakin gate. Da muka shigo sai na shiga kitchen na fara tunanin me zan dafa mana. """Aunty"" na juya da sauri. For the first time Junior ya kirani da Aunty." """Yes, kana son wani abu ne?""" Miƙo min wayata ya yi ashe na bari a falo. """Nagode, Junior"" maimakon ya bar Kitchen ɗin sai ya tsaya yana kallon yadda nake fito da kayan miya" daga freezer ina sarrafawa. Jifa-jifa idan na tambayeshi wani abu yana bani amsa. Na tambayeshi ko yana cin Tuwo ya ce Hajiya ta koya masa. Na ce wani irin Tuwo yake so ya ce bai sani ba amma wanda yake fari da miya mai yauƙi. Ina ga dai Tuwon Semo da miyar kuɓewa yake nufi. Zan kira Hassana na tambayeta. Daf Magariba Jalal ya dawo. Ai kan ma ya shaƙi iskar gidan har Junior ya faɗa jikinsa yana bashi labarin wai yau mun je Plaza a Keke. Jalal ya ɗago ya kalleni na yi murmushi. Lokacin da muka keɓe sai ya ke ce mini zai fara koya mini mota baya son shiga Keken nan na ce masa an gama Captain... *** Ban san abinda Jalal yake shirya mana ba sai da Janan ta shigo gari. """Wallahi ni fa Dinner za a yi ba Reception ba. Gara ma ki faɗawa Hajiya ta fasa shirin da ta ke yi. Dan" "yaya yana son haɗa muku Reception ba shi zai hana a yi Dinner ba"" ta tsareni da masifa lokacin dana shigo ɗakinta dan yi mata ta'aziyyar rasuwan da aka yiwa Saurayinta." Ɗinner? Reception? Ban gane ba?. """Janan ki yi mini dalla-dalla ban gane ba""" """Ba mijinki bane ya ce zai haɗa muku Reception Hajiya kuma tace a cancel ɗin Dinner da aka shirya." "Fisabilillahi an yi min adalci. Har final fitting ɗin Dinner gown ɗina fa na yi a zo a ce Reception kaɗai za a yi babu Dinner""" To wai ma menene banbancin Dinner da Reception? Ni Ziyada 'yar Ghetto ina zan sani. Ƙarshe fa ƙaramar magana sai ta zamo babba. Ni da ban san maganar Reception ba an sakani cikin rikici tsakanin Hajiya da Autarta Janan. Na samu Jalal na ce masa dan Allah ya fasa dik abinda ya shirya a bar Janan ta yi Dinner ɗinta. Ya ce kar na damu Janan za ta sauko. Yaushe muka fara shiri da Janan har maganar Reception ko Dinner zai sake haɗamu faɗa. Dududu saura sati biyu bikin suna so su ɗagawa Amarya Janan hankali. Da na ga faɗan ba nawa bane sai na barsu. Ai dama uban gayyar bai nemi shawarata ba ya shirya maganar Reception ɗin aurenmu. Reception bayan mun baiwa wata shida da aure baya. Ƙarshe dai Janan da kanta ta sauko za a yi Wedding Reception nawa da nata a rana ɗaya maimakon Dinner. Sai a lokacin ta fara yi mini magana har da cewa na bata size ɗina za ta sa Designer ɗinta ta min Dinner gown mai kyau kafin ranan Reception ɗin. Na ce mata bana son abunda zai ja ido tunda ita ce Amarya ba ni ba. A yi shi simple kawai. Na tura mata sample ɗin gown ɗin da na gani a Pinterest. """Wannan ai Jallabiya ce Ziyada. What is this?"" ta turo min reply. Haka muka dinga musayar pictures" daga ƙarshe na tsaya a wani simple gown daya baje sosai sai wasu stones masu kyau a saman. Ni dama bana son matsatsten gown. "Da ƙyar Janan ta yarda a yi mini shi, har da cewa ko ciki ne da ni da ba zan saka corset gown ba. Allah na" tuba Amaren dana ke gani a irin matsatstun corset gown ɗinnan duk a takure suke. Kawai dan a yi hotuna ne amma ko kaffara babu ba sa sakewa a cikin kayan. Saura sati ɗaya bikin Janan ni da Jalal muka je gida gaishe da Kaka. Har ɗakin Kaka na shigo da shi sai addu'a take zubo mana. Baffa Lawalli baya gari wai ya tafi wani ƙauye ina ji suna maganar wata Bazawara yake nema na ce mai hali baya fasa halinsa. Mardiyyah na sa ta yiwa Kaka ɗinki dan hidimar da za a yi. Na kira Ummana na sake tuna mata amma ta ce na yi haƙuri ba za ta samu zuwa ba Malam ya ce ai an gama hidimar biki idan na haihu za ta zo. Ban ji daɗi ba na ce to Dan Allah ta aiko ƙannena su zo ta ce za ta yiwa Babansu magana. Ƙarshe dai su ɗinma cewa aka yi ba za su samu zuwa ba sai na ji babu daɗi. Har gida na kaiwa Faty katin bikin Janan dana Reception ɗinmu da za a haɗa. Karo na biyu kenan dana je bayan haihuwarta dan ban je Suna ba. Ta ce min Insha Allahu za ta zo. Allah dai ya sa Mijinta ya barta. Mutumin da ya hanata sana'ar Makeup ban ce zai barta ta zo hidimar Reception ba musamman yanzu da take shayarwa... *** A satin biki dai sai dana cirewa Janan tutar Amaryar da ta fi kowacce Amarya rawar kai. Innalillahi!. Ɗaukan content ɗin hidimar ta ke duk inda ta gifta ana binta da Ringlight. Ni dai fatana Allah ya bata zaman lafiya a gidanta. Dan yadda take fallin nan ban ga alama Khalifah zai barta ta cigaba da hakan ba idan suka yi aure. A ranan bridal shower ɗin Janan ne Saudah ta sameni a gefe wai na yi haƙuri Janan ta faɗa mata abinda ƙanwarta ta yi. Na ce mata babu komai ya wuce. Idan ba neman magana ba tun da aka yi abin bata neme ni ta bani haƙuri ba sai yanzu take wani bada haƙurin munafurci da gulma. Irin an kira Cassandra dan a wargaza tsakanina da Jalal ga shi kuma har yanzu muna nan tare. Allah na tuba ni dai zuciyata na bani da saninta ƙanwarta ta yi abinda ta yi. Ana gobe ɗaurin aure tun daga safe har yamma haka muka wuni ana doka tambura a gidan Hajiya. *** A ranan Asabat da misalin ƙarfe goma shaɗaya na safe aka ɗaura auren JANAN KABEER MAIYAƘI da Angonta ABUBAKAR (Khalifah) SAIDU GALADIMA. Auren ya samu halartar mutane da dama. Muna ciki wajen Amarya wasu mata suka shigo da guɗa wai an ɗaura aure. Sai hakan ya tuno mini da ranan da aka ɗaura nawa auren. """Da gaske an ɗaura?"" Janan ta faɗa duk ta ruɗe." Sai aka saka mata dariya. A gabanmu ta shiga updating social media handle ɗinta tana rubuta MARRIED❤. Wasu Cousins ɗinta mata sai tsokalarta suke. Ta ce musu su barta yau rananta ne. Tabbas yau rananta ne. Shi yasa ma da Jalal ya ce mu yi photo shoot bayan Janan ta yi nata da Khalifah na ce ba sai mun yi ba. Kafin ƙarfe biyu na rana ni da Janan an gama mana make up ɗinmu. Ni dai simple make up na ce a min "kuma na yi kyau sosai. Sai dana saka gown ɗina ma kyau na ya fito, kuma kayan ya bala'in yin kyau. Janan har da cewa anya ba zan fita kyau a bikinta ba. Ina ji Sharifa da wasu ƙawayen Janan suna dariya ƙasa-ƙasa na ce ohon su." Kafin mu fita na kira Mardiyyah ko sun isa venue ɗin da za a yi reception ɗin ta ce ai har sun shiga ma. Na ce dan Allah ta kula min da Kaka. A motar Jalal muka taho. Ina shiga motar na ga shima ya sha farar Babban riga ya yi kyau. Ya jawoni jikinsa ya manna mini kiss a goshina da kumatuna. """Za ka goge min kwalliya"" na janye fiskata dan kar ya fahimci tasirin kissess ɗinsa ne ke ƙoƙarin birkitani." "Ya riƙo hannuna ya kissing sannan ya ce ""you look beautiful, Zeeyadah""." Na saka murmushi. Bayan mun isa. Bayan MC ya announcing shigowarmu. Bayan Janan da Mijinta sun fara zama. Bayan dogon surutu daga MC da sauran activities. Bayan na hango Kaka a high table na ɗaga mata hannu ina murmushi. Bayan MC ya kiramu mun fito fili dan mu yi rawa sai ni da Jalal ɗin muka tsaya kallon juna. Yadda ba zan iya rawa dan na ceci rayuwata ba na tabbata shima a wajensa hakan ne. "Kallon juna muke yi, fuskar Captain Jay ɗina sai sheƙi ta ke cike da so da ƙauna." Yanzu kam na yarda 100/100 yana sona. Yanzu kam na amince da soyayyar da yake mini har cikin zuciyata. "Yanzu kam soyayyata a bayyane take a fiskarsa, da kalamansa da ayyukansa." Takawa mu ke yi a hankali. Mantawa na yi akwai Janan da Angonta Khalifah a gefenmu balle taron "jama'ar dake hall ɗin, 'yan'uwa da abokan Arziƙi." Jay kawai nake kallo. Na shagala da kallon kyakykyawar fiskarsa. Yadda ya sha gyaran fiska ji nake kamar na sa hannu na shafa fiskar na yi wasa da saje da gemunsa. """Da na san haka 'yan Ghetto suka iya murmushi dana dawo Nigeria a lokacin da su Hajiya suka dawo""" "Dariya na saka na ce masa ""da ka dawo Nigeria a lokacin da wata 'yar Ghetton daban za ka samu ba ni" "ba""." A hankali ya ɗaga hannuna sama ya fara juyani. Sai murmushi nake yi fiskata na ƙyalli. Ba ƙyallin make up "bane, ƙyalli ne dake tabbatar da kwanciyar hankali da nitsuwar dana ke samu a wajen Mijina." I am so happy da wannan dogon mutumin da ya sakani zubar da hawaye a baya amma a yanzu ya musanya kukana da dariya. Ina fata wannan farinciki dana ke ciki ya zamo mai ɗaurewa har abada. "Haɗa bayana da ƙirjinsa ya yi ya rankwafo kansa dai-dai wuyana ya ce ""I love you, Sunshine""" Murmushi na yi hawaye suka taru a idanuna. Juyo dani ya yi muna fuskantar juna. Lokacin da muka haɗa ido sai ƙwalla ya zubo mini. "Tattaro fiskata ya yi da hannunsa ya ce ""Hey, hey, banda kuka, Sunshine. Yau ranan farinciki ne"" ya saka" babbar yatsarsa ya fara goge ƙwallar da ya sauko a fiskata. """Idan kika ɓata make-up ɗinki, Janan za ta ce kin ɓata mata Party saboda ba ki da Class"" Dariya na saka" hakan ya saka shi manna mini kiss a goshina. Ina jin yadda hall ɗin ya ɗau ihu. Hasken flashes ɗin Camerorin mutane ya fara wawal-wawal a wajen. Faɗawa jikinsa na yi ina ƙoƙarin danne hawayen da ke taho mini. Hawayen farinciki ne da godiya bisa "ni'imar da Allah ya mini, ni Ziyada jikar Altine mai Tuwo. A haka muka cigaba da takawa har MC ya ce Amarya da Ango su je su zauna." Lokacin da aka kiramu yanka cake Janan da Khalifa ne suka fara yanka nasu. Wani ƙaton cake mai shegen tsayi. Namu ƙaramin vanilla cake ne single layer aka rubuta JAY&ZEEY a samansa. Ni na ce bana son babban cake. Muka yanka cake ɗin a tare. Shi ya fara saka min a baki sannan nima na ɗan risina kaɗan na saka masa a baki sai tafi ake mana. "Lokacin da aka sake kiranmu wani rawan ni dai cewa Jalal na yi ba zan iya fita ba, na gaji. Ya ce na yi" zamana. Haka dai muka ƙare Reception lafiya. Amma zuwa lokacin ba ƙaramin gajiya na yi ba. Da ke za a wuce da Janan Kano ƙarfe shida na yamma saura 'yan mintuna aka tashi. Kan kace me anata hayaniyar kai Amarya Kano. Ni dai gogan nawa ne ya sace ni daga cikin hayaniyar "mutane muka yi gidanmu. Dama Janan ce Amarya, ni kam ai na haura wata shida da aure ma. Sai dai bisa take-taken Captain Jay ɗina, yau fa da alama shi zai kasance first night ɗin aurenmu." "Bayan mun yi sallar Maghriba sai muka zauna a wajen, shi yana karatun Qur'ani ni kuma ina jan carbi ina" yiwa Annabi Salati. Can ƙasan raina kuma ina tuno baƙar wahalar dana sha a hannun Jalal watanni huɗu da suka wuce. Da muka gabatar da Sallar Isha sai ya ce mu tashi mu yi sallan godiya. Na miƙe na bi bayansa. Jimawar da muka yi a Sujudi ya tabbatar mini ba ni kaɗai na jerawa Allah addu'o'in samun Albarka a wannan sabon babi na rayuwar aurenmu ba. Bayan mun idar da Sallan. Sai na ga ya miƙe ya fita. Da ya dawo sai ga shi da Kaza. Dariya na saka ina tuno ranan da aka fara kawoni gidansa yadda na zage na ci kazar da ya kawo mini. Dukkanmu biyu muka ci Kazar time to time yana yagar Kazar ya sa mini a baki. Bayan mun gama ci still shi ya tattara wajen. Ni kuma na wuce banɗaki dan na yi brush. Baccin wuri zan yi dan a gajiye nake. Ina cikin Alwalar bacci a banɗakin bayan na gama brush ya shigo. Brush ɗinsa ya ɗauko ya fara goge bakinsa ni kuma na ƙarisa Alwalata na fito. Gado na haye dan na kwanta kar ma ya yi tunanin na shirya masa. Shi yasa ma na saka doguwar rigar bacci. Fitowa ya yi daga banɗaki ya shigo ɗakin daga shi sai wandon Pyjamas ɗinsa fari mai layi-layin navy blue. """Wa ya gaya miki yau ranan bacci ne""" Na ɗan ɗago da fiskata ina kallonsa sosai. Janye wandon ya yi ta faɗo ƙasa. Ina kallon haka na fara wiki- "wiki da idanu ganin sandar da ke tsaye tana pointing ɗina. Ya kicking wandon pyjamas ɗin daga ƙafarsa sannan ya ɗan yi taku ɗaya biyu sai ya tsaya, daga shi sai shi. Ware hannayensa ya yi yana banƙara ƙirjinsa. So yake na gan shi, na ga komai nasa." Wannan shine sirrin Miji ga Matarsa. This is the first time dana ga girmansa. Maimakon na ɗauke idanuna daga kansa sai na tsinci kaina da ƙurawa halittarsa ido. Gaskiya shi ɗin ta kowanni ɓangare NAMIJI ne. Ashe shi yasa na sha baƙar wahala ranan farkonmu. Ashe da wannan ƙatuwar abar ya zungureni ya sakani jinyar sati guda. Har yanzu ban manta zogin da na yi ta fama da shi ba bayan tafiyarsa London. Ƙwalalo ido na yi ganin yana nufoni yana wani munafukin murmushi. Yanzu dana ga sirrinsa. Yanzu da na ga komai nasa sai na ji wani sabon kunyarsa ya kamani. Na yi saurin rufe fiskata da tafin hannuna. Yana zuwa kuwa ya cire hannuna daga fiskata ya ɗaura akan sandarsa. """Touch it, Sunshine... Feel it. Naki ne dukkansa""" Fara tracing saman na yi ina bin jijiyoyin wajen yadda suka mimmiƙe suna motsar da sandar. Yadda nake wasa da ita yana jin daɗin hakan. Ban ankara ba ya hawo gadon ya fara kissing ɗina yana zare mini riga da kuma dogon wandon dana saka da sunan kariya. Lokacin da yake ƙoƙarin shigata sai na ɗame saboda tsoron da nake ji. """Zan biki a hankali. I'll be gentle with you like the first time. Ki sake jikinki kin ji""" Ba wani. First time ɗinmu baƙar wahala na sha. Ganin dai har lokacin a tsorace na ke sai ya dakata da shiga ya fara massaging saman marana yana faɗa min kalamai masu daɗi yana kwantar min da hankali. Da kaina na sake jikina saboda nima wasannin nasa sun motsoni. Ya haɗe hannayenmu yana bina a hankali. Wannan karan ban rufe idanuna ba ina kallon yadda yake mini murmushi. "Da ya zo ta ƙarshen sai ya ƙara gudunsa, bai saurara min ba har sai da ya sauke. Ya kwanta akaina Ina jin" nishinsa. Daga baya sai ya mirgina gefe ya kwantar dani a ƙirjinsa. """Allah ya miki Albarka"" ya raɗa mini a kunnena. Na sunne kaina jikinsa ina murmushi." Dukkanmu baccin gajiya muka yi ba mu tashi ba sai ƙarfe shida na safe. CHAPTER FIFTY NINE ZEEY Aure akwai daɗi. Yanzu kam ina jin daɗin aurena da Jalal. Har sati ɗaya bayan auren Janan muna shan Amarci. Shi dai ya fita Office sau biyu amma ni kam rabona da Gidan Girki tun kan satin bikin Janan. A cikin satin nan na ji jiki a hannun Captain ɗina. Bai sarara mini ba ko kaɗan. Ina ga haƙurin da ya mini bayan ya dawo ne yake fanshewa. Amarya Janan tana Kano abinta min yi waya sau ɗaya bayan auren. Yau da safe Jalal ke cewa wai Janan "da Mijinta za su je London sati biyu. Na ce Allah ya kaisu lafiya. Shine ya ce min za mu je namu HoneyMoon ɗin idan wa'adin aurensa da Cassandra ya ƙare wanda a lissafina bai ma kai wata biyu ba. Amma wai za a min International Passport, sannan a fara processing Visa na." A sati na biyu da fara shimfiɗa sabuwar rayuwarmu ƙwatsam sai ga kira daga Plaza da sassafe. Ni har yanzu ban leƙa su bama ina gida ina shan soyayya. Nemana a ke emergency hankalina ya tashi. Na tambaya ko gobara ne ta tashi wanda ya kiranin ya ce wai wata 'yar matsala ce ake so na zo a warwareta. A ɗan rikice na fita daga gidan bayan na yiwa Jalal text cewa na tafi plaza. Jiya ya tafi Abuja wai Uncle ɗinsa ya kira shi. Ina zuwa Plaza da naga motar Polisawa sai na kama Innalillahi. Mutane huɗu da aka kama ɗaya daga cikinsu jinina ne. Rabi'u ne ɗan Baffa Lawalli wanda Jalal ya samawa aiki a Plaza. Shi Kawuwa ɗan Baffa Zakari a cikin "Restaurant ɗina ya ke aiki. Shima wani ciwon kan ne, saboda ba ya son zuwa aiki sai ya ga dama, kuma ko ya zo ɗinma sai ya tafi yawonsa ko ya yita shirme a Restaurant ɗin. Duka ina ɗauke masa ido, to yanzu ga ɗan'uwansa nan sun yi sata a Plaza an kama su." Na kalli Rabi'un cike da takaici. Da ya ke ta yi musu kukan shi ƙanin matar Oga ne uban me zan yi masa a nan ɗin?. Na kau da kai na cewa Jide babu abinda zan yi a nan idan Jalal ya dawo sa yi magana. Ko awa biyu ban yi da shiga gida ba sai ga Maman Rabi'un da Maman Suwaiba da ta rako ta gidana suna kuka wai an zo gida an faɗa musu an kama Rabi'u. """Dan Allah ki sa a sake shi, Ziyadatu. Wallahi sharri aka masa banda shi a cikin masu sata. Rabi'una ba zai" "taɓa sata ba""" Na kalli idanun Maman Suwaiba wanda ya ƙaryata abinda Maman Rabi'un ta faɗa. Ko ni da ba sanin yaran na yi sosai ba daga yanayin yaron akwai alamu zai iya yin abinda aka ce ya yi. Ni da take ta bani haƙuri me zan sa a yi mata. Ba ni aka yiwa satar ba. Wajen da suka yi satan ba nawa bane. Ko a Gidan Girki aka kama shi da laifin sata babu abinda zan iya yi masa. Na dai bata haƙuri akan mijina baya gari da ya dawo zan faɗa masa amma taƙi yarda da ni tana cewa wai na ɗaga waya na kira Station ɗin na ce a sake shi. Da ƙyar Maman Suwaiba ta lallaɓata suka bar mini gida. Na san yanzu haka zuwa za su yi su ce na ƙi na sake musu yaro. Su ba za su ga laifin ɗansu ba. Ba za su yarda a hukunta shi ba saboda gaba kar ya sake sai dai a sake musu shi su cigaba da faɗawa kansu ƙaryar sharri aka masa yaronsu ba ɓarawo bane. Ai kuwa kafin yamma sai da suka sakani kuka saboda kira akan kirar da aka yi ta mini wai na sa an kulle Rabi'u. Baffa Lawalli ma da ya kira da ashar ya amsa sallamata. Kuma Wallahi na san dukkansu sun san yaron zai iya aikata abinda aka ce ya yi ba wai wannan karan bane farko. Kaka ma ta kirani ta ce wai ta san Rabi'u yana 'yan sace-sace kuma ta yarda cewa sun yi satan amma dan "Allah na sa a sake shi saboda a zauna lafiya. Na ce mata Wallahi bani da halin cewa a sake shi koda ina so, Kamfani ya yiwa sata ba ni ba." Da Maghariba Jalal ya dawo zuwa lokacin ko abincin dare ban yi masa ba duk raina a ɓace yake na kasa taɓuka komai. """Me ya samu Sunshine ɗina?"" Ya faɗa bayan ya sakeni daga rungumar da ya mini." """Ba dai maganar yaran da aka kama bane ya sa miki wannan damuwar""" """My Captain ya zan yi? Kowa a gidanmu ya sakani a gaba wai na hana a sake musu yaro""" """Kwantar da hankalinki. Babu abinda zai faru kin ji"" ya share mini hawayena." Abu dai har sati guda ba a sake yaran ba. Cikin Baffanuna Baffa Mamman ne kawai ya goyi bayan kar a "sake Rabi'u, ko dan shi ya ɗan yi karatu ne oho. Amma Baffa Adamu ma cewa ya yi zai fi a sake yaron idan ya so a kore shi a aiki ya riƙa biyan abinda suka sace a hankali. Yaya Aminu ma ya kirani ya bani full support cewa kada a sake yaron saboda idan aka sake shi ba zai horu ba." "Ba fa satan kawai bane, an kama su har da makami. Da a ce shi ɗaya ne ma sai na ce a sake shi amma su" huɗu ne kuma wai ashe shine ya basu information na yadda za su shigo Plazar su yi sata. Ba dan Allah ya taƙaita ba da a ce masu gadi ba su ci ƙarfinsu ba ai da ba wannan maganar ake ba. "Bayan sati uku aka sake Rabi'u da sauran yaran zuwa lokacin Baffa Lawalli gaba yake dani, har Gidan" Girki ya zo ya ci min mutunci wai yana Allah wadai da auren dana yi. Ni da mijina mun haɗa baki muna so mu kashe masa ɗa. Na ji duk na tsani kaina. Ni kam a auren Jalal ina ganin jarabawa kala-kala. Wani abin da ya ɗan kwantar mini da hankali shine Kamfanin Ajinomoto da suka tuntuɓeni ta email wai suna so na musu aiki na tallata musu Daddawar da suke mai suna Deli Dawa. Dake na taɓa amfani da shi yana da daɗi sai na yiwa Jalal magana. Shi ya tayani duba Email ɗin ya tabbatar daga Marketing Agent ɗin Kamfanin Ajino ɗinne sannan ya ce na karɓi aikin amma na faɗa musu kuɗi masu yawa. "Tare da shi muka rubuta musu reply, 'yan renin hankali wai kuɗin dana ke buƙata ya yi yawa ga abinda za" "su biyani har zan amince tunda still kuɗin dayawa amma Jalal ya ce kul, kada na karɓi haka za su rena ni." "Ai su suke buƙatata suka neme ni, ba ni na neme su ba." A satin ya sa Agnes ta mini Registar sunan Food Content business ɗina. Dake sunan CHEF ZEEY's KITCHEN an riga an ɗauke sai na registering Business name ɗina da CHEF ZEEY's MENU AND MORE. "Bayan sati ɗaya sai ga shi sun sake yi mini email wai sun amince da kuɗim dana faɗa, suka turo mini" Contract ɗinsu. Waɗanda na saba yiwa talle a Instagram ƙananun Vendors ne babu maganar Contract wannan ne karon farko da zan yi aiki da babban Kamfani. Lawyan kamfanin Jalal na turawa Contract ɗin dan ya yi mini bayani dalla-dalla dan Jalal baya gari kuma bai san ya Kamfani suke amfani da Influencers wajen talle ba. Barin faɗa muku wani abin mamaki. Bayan an turo min Contract ɗin sai na yiwa wata babbar Food "Influencer na Arewa magana ta DM ina neman shawara. Ashe, Ashe mu masu food content kanmu ba a haɗe yake ba kowa ta kansa yake. Sai daga baya ma bayan na signing Contract ɗin nake jin wai ai an so ma a hanani samun Contract ɗin amma dake ina cikin manyan Food Content Creators da suke Content ɗin gargajiya zalla shi yasa aka neme ni. Kuma a lokacin nima social media followers ɗina sun ƙaru sosai musamman a lokacin farkon aurena da na yi trending aka yi ta yawo da maganata." Bayan an cire abinda za a cire a Contract ɗin an yi mata kwaskwarima sai suka biyani 70% na kuɗin kafin na fara musu aiki. Lokacin da alert ɗin kuɗin ya shigo wayata sai dana yi ƙwalla. Wai yau ni Ziyada jikar Altine mai Tuwo ne na samu kuɗi masu yawa haka. Ashe zan iya samun sama da Miliyan ɗaya akan aikin talla kawai. Gaskiya Alhamdulillah da ban cire rai ba a harkar food content a lokacin da wasu tsirarun mutane ke kirana da Chef ɗin Talakawa. Yau gashi saboda girkin Talakawan dai wannan kamfanin suka neme ni. Idan na waiwaya baya ma to ai haɗuwata da Jalal ma ta dalilin shafin CHEF ZEEY ne. Ba dan Hajiya Layla tana ganin abincin da nake a Instagram ba da babu yadda za a yi na haɗu da ita saboda akwai tazara mai yawa a tsakaninmu. "Kamar sihiri daga fara yiwa mutanen nan Content ɗin tallata DeliDawa sai na fara ciwo, kasala da amai" "ya sakani a gaba. Ranan dai Jalal ya ce mu je Asibiti. Da muka je sai suka gwadani. Da gaske mantawa na yi da lissafin kwanakina, sai da aka ce mana ina ɗauke da ƙaramin ciki sannan na tuna ashe fa sati biyu kenan ban ga period ɗina ba." Lokacin da muka iso gida Jalal ya ɗagani sama ya fara juyi dani sai dariya yake. """Ka sauke ni, Hajijiya...""" """Oh sorry, sorry"" ya saukeni sai Hamdala ya ke yi." Ciki fa kaman jira yake a san da shi sai laulayi ya ɓarke mini. Amai daga safe har dare. Ranan Hajiya ta zo dubani ta ga yadda na dawo ta ce za ta samo mini 'yar aiki na ce mata to. Nima a lokacin kam ina buƙatar taimako. "Kwana biyu Jalal bai fita aiki ba, haka ya taimaka mini har muka gama shooting content ɗin tallen da aka" bani. Bayan na tura musu sun yi approving sannan na fara ɗaurawa a shafukana. Ranan da Jalal ya dawo ya ga 'yar aikin da Hajiya ta kawo mini sai ya ce me zai hana in kawo wata "ƙanwata daga gidanmu, yarinyar da Hajiya ta kawo ta yi ƙarama sosai." """Wallahi Captain yanzu sai su fassarani idan na ce zan ɗauko yarinya na kawo gidan nan. Tun maganar" "Rabi'u Baffa Lawalli baya kulani""" """Idan Kaka ta dawo gidan nan fa"" ya faɗa yana kallona." Na ɗan tashi zaune daga kwancen da nake. Kuma fa da gaskiyarsa. Zai yi kyau Kaka ta dawo gidana da zama dan tunda na yi aure sai lalacewa take mutanen gidanmu ba kula da ita suke yadda ya kamata ba. """Zan yiwa Kaka magana amma ba lallai ta yarda ba, za ta iya cewa ba za ta bar gidan Mijinta ba""" "Jalal ya kalleni ya ce ""what if muka ce mata jinyar ki za ta zo ta yi na kwana biyu kafin ki warke. Idan ta zo" "kin ga sai mu hanata tafiya""" """Hakan zai fi kam. Dan Kaka za ta iya cewa mutane za su yi magana""" "Magana kam tabbas na san sai an yi, shi yasa na toshe kunnena lokacin da muka ɗauko Kaka. Itama" wayo muka mata muka ce mata kwana biyu za ta yi ta koma. Da ta zo ta ga yadda na rame nake wahala sai ta manta da batun kwana biyu ta ce sai na warke kafin ta tafi. A ƙasa muka gyara mata ɗaki saboda ba za ta ji daɗin hawa da saukan stairs ba. Ranan Hajiya ta shigo dubani sai ta ke cewa an kawo kuɗin auren Saudah. Haka kawai sai na ji zuciyata ya buga. Ba dai Abujan da Jalal ke ta sintiri kwana biyun nan auren Saudah yake shirin yi ba. Hajiya ta ce Saudah ta ce bata son hidima dan haka aure kawai za a ɗaura ta tare. Na ce Allah ya bata zaman lafiya. Dama Jalal ya ce mini washegari zai je Abuja. Da dare sai na haɗe masa fuska na ƙi sakewa da shi. Shi ya ɗauka saboda ya ce zai yi tafiya ne nake fushi. """Me nene?"" Ya rungumoni lokacin dana ce masa zan sauka ƙasa wajen Kaka mu yi hira." """Na san fushi kike. Faɗa min laifin me Ɗan Hajiya ya miki?""" """Ni fa babu komai. A gaishe da Amarya Saudah idan ka je"" na faɗa ina kau da kaina gefe." "Murmushi ya yi mai sauti ya sake matseni da jikinsa ya ce "" Zeeyaaadaahhh""" """Ni ka sake ni"" na yi ƙoƙarin barin jikinsa." """Ina jin daɗi idan na ga kina kishi na""" """Ni ba kishinka nake ba""" """To me kike?""" """Kawai dan na ce a gaishe da Amarya Saudah sai ka ce wai kishi nake. Kai da kake ta sintirin zuwa Abuja" "ai ka san me yake kaika can""" "Ya saƙalo kansa wuyana ya ce ""kishin dai kike 'yanmata. To Albishirinki"" na yi shiru." """Da gaske ne Saudah za ta yi aure. Amma ki kwantar da hankalinki ba ni ne Angon ba""" """Dama ni na ce kaine Angon ne"" na faɗa ina sake fuskata" """Ga shi nan har kin yi dariya. To wani abokin Jamal ne yake sonta tuntuni tana ƙinsa, amma yanzu Allah" "ya haɗa kansu ƙarshen watan nan za a ɗaura auren""" """Allah Sarki. Allah ya basu zaman lafiya"" ya amsa da Amin." Kwana uku da tafiyarsa sai ga shi ya dawo. Bai ce min zai dawo bama ina kwance ina jin jiki ban jima da amayar da duka abinda na ci ba sai ga shi ya shigo ɗakina. """Ka ce min sati ɗaya za ka yi"" na faɗa ina kallonsa ko miƙewa na kasa yi. Ƙarasowa ya yi idan nake ya ce" ko zamu je Asibiti na ce ba sai mun je ba. """Seriously ki shirya na kaiki Asibiti""" """Magani za su ƙara min ko suce za su saka min ruwa, na gaji da komai""" """Ko na kira Likita ya zo gida ya duba ki?"" na girgiza masa kai." Sai bayan Isha dana sha tea na ɗan samu ƙarfin jikina. Tea ɗin kaɗai ya zauna a cikina. Miƙo min wani babban envelope ya yi ya ce na buɗe. """Takardar miye?""" """Ke dai ki buɗe""" Takardar Final Order ɗinsu ne dake nuna shaidar Kotu ta raba aurensa da Cassandra. Na ɗago na kalle "shi na ce ""dama London ka je ba Abuja ba""" """Na je Abuja mana... amma na ɗan karɓo saƙo a London briefly""" """Allah ya shiryeka"" na faɗa ina mayar da takardar cikin envelope." "Dawowa ya yi bayana ya rungumeni ya ce ""daga yanzu ke ɗaya ce babu ƙari""" """Kama ƙara mana""" """Ki ɗan yi murmushi mana kar Princess ɗina ta yi gadon fushi""" Na ɗan ture shi sai ya kamo ni. Na shiga jikinsa sai na sa masa kuka. Ni kaina ban san kukan me nake ba. Kukan finally ya rabu da Cassandra ne ko kuma kukan laulayin dana ke fama da shi. Duka biyu ma dai laifinsa ne. """Sorry, 'yanmata"" ya fara shafa mini baya..." *** A ƙarshen Second trimester ɗina muka fara Jarrabawar ƙarshe a Makaranta. Har zuwa lokacin sai dai "abinda ya ragu amma ina jin jiki. Allah na tuba ko dan na yi gulman Faty ne lokacin da take da ciki nima Allah ya jarrabceni da laulayi mai tsanani, sai Allah." Ahamdulillahi ina da supportive Husband. Abinda Faty ta rasa na support ɗin Miji lokacin da take da ciki ni kuma Allah ya bani. Na sani ba iyawata bane shi yasa babu abinda zan ce sai dai na cigaba da yi masa godiya bisa wannan ni'imar. Ta ɓangaren Business ɗina duk da bana zuwa sai time to time komai na tafiya dai dai. An chanja "Manager, Jide ya koma JK Group. Shi kan ma sabon Managern ya fi Jide tsauri." Sannan sabon training da aka yiwa staff akan customer service da kuma updating policy ɗinmu da muka "yi ya saka abubuwa suna tafiya normal fiye da da, sai ɗan abinda ba za ka rasa ba dan ko last week an kori wani Waiter." Food content ɗina kuma tunda na yi Contract ɗin tallen DeliDawa na kamfanin Ajinomoto sai ƙofar talle ya buɗe mini. A yanzu ma dai Contract ɗin kamfanin Mr Chef ne a ƙasa na ke yiwa aiki. Ba dan Kaka da Jalal ba dana watsar da harkar tuntuni dan wani lokaci idan laulayi ya sani a gaba sai na ji na tsani komai. Zaman Kaka a gidana ba ƙaramin rahama bane. Ga shi itama har ta warware saboda hankalinta a kwance take kullum tana ganina. "Mutanen gidanmu kuwa ina yi musu iya abinda zan iya yi, na dena tsawwalawa kaina. A yanzu haka wai" jira suke na haihu Kaka ta dawo gida. Ai Insha Allahu abinda zai fitar da Kaka daga gidana mutuwa ne. Soyayyar da Jalal ke min ba a baki kaɗai bane dan na gan shi a zahiri a lokacin dana ke buƙatan soyayyar. Yana supporting ɗina har tausayinsa nake ji wani lokacin. Ga shi tunda na fara laulayin nan na tsani ya taɓani. Zan iya cewa mun fi wata biyu babu abinda ya shiga tsakaninmu. Bawan Allah nan akwai shi da haƙuri. Shi kuma Junior tunda aka ce masa zan haifa masa baby mace sai ya sake jiki da ni fiye da da. Idan ya ga na wuni a ɗaki ban fito bama sai ya ƙwanƙwasa mini ƙofa ya ce ya zo gaisheni. A hankali nima sai na ke sake masa mu yi taɗi sosai. Har wani gift Box ya kawo mini wai a ajiyewa Baby. A dole nake karatun exams saboda Jalal ya ce baya so na faɗi ko ɗaya. Wani lokaci shi zai karanta handout ɗin ya zo yana karanta mini summary ɗin. Ko kuma ya ɗauko past "question ya ce na duba na kama wasu, za a iya samun wanda zai dawo." Cikin ikon Allah dai haka na gama rubuta exams lafiya. Na san ba zan samu A ko B ba kam amma dai na yi ƙoƙarin da babu paper da za ta dawo mini Insha Allahu. Ranan da muka yi Project Defence ma da "tulelen ciki na tafi, kuma na yi Defence ɗina successfully." "Tunda na shiga wata takwas sai na fara wani kumburi, har mamakin yadda na koma nake. Haka Jalal zai" sako ni gaba da dare ko da sassafe mu fita motsa jiki. "Kai ba zan sake gulmar wata mai ciki ba tunda nima ga shi na ɗanɗana na ji abun fa ba shi da Manual, ko" ya zo maka da wahala ne ko ya zo maka da ɗan sauƙi. Alhamdulillah dai ina samun taimako daga Mijina. Ina fata duk wata mai ciki ta samu irin taimako da kulawar dana ke samu... CHAPTER SIXTY ZEEY """Sannu kin ji. Sannu, Ziyadah""" Hajiya ke mini sannu. Dole ta mini sannu mana tunda ɗanta ne ya sakani laulayin wata tara na zo kuma na yi wahalar naƙuda. """Masha Allahu, ga ta nan sak Janan tana jaririya"" ta faɗa tana kallon kyakykyawan yarinyar da Allah ya" bamu. "Jiya da dare na haihu a Asibiti. Alhamdulillahi haihuwan ya zo min da sauƙi, duk da haka fa na ɗanɗani" kuɗena. Sai dai babu matsalar tear ko wani abu. Da safe ma suka sallamemu muka dawo gida. Shi uban yarinyar fiskarsa kamar gonar auduga. Junior ma haka ya tsaya gefen Hajiya yana ta kallon jaririyar. Sai can dare bayan mutane sun watse sannan muka samu keɓewa ni da Jalal. """Thank you, kin bani kyautar FATIMA ZAHRA"" na yi murmushi dan nima sunan ya min." "A rana ta uku Janan ta zo daga Kano tana zuwa ta fara ihun wai ta zo ganin mai kama da ita, wai kowa na" cewa yarinyar kamarta ta ɗauko. "Ta riƙe Zahra tana faɗin ""Cutie, cutie""" Ni dai nawa ido. Dana ga ta ɗauko waya za ta fara mata video sai na ce Dan Allah ban da ɗaurawa a "social media, ko za ta ɗaura ta rufe fiskar. Ah to! Ni na san sharrin Social Media." """Sannu Maman Baby""" Duk da dai na ga tunda ta yi aure ta rage abubuwan da take posting ba kamar da ba amma dai gara na ja mata kunne kafin a fara yawo da hoton 'yata ana ce mata tana da ƙaton hanci. Hidima sosai aka yi a sunan Fatima Zahra. Jalal da Hajiya sun kashe kuɗi ba kaɗan ba. 'Yan gidanmu da suka zo suna ma na san da gulma a bakinsu suka tafi gida. Wai a gabana fa suke tambayar Kaka wai yaushe zata koma gida tunda na haihu. Ku ji min fa. Kaman akwai abinda za ta musu idan ta koma gidan. Ummana ma ta zo suna da ƙannena. Kwana uku ta yi min "suka koma, na ji daɗin hakan sosai." Na sha baƙar wahala a renon ciki amma da ikon Allah sai shayarwa ya zo min da sauƙi. Ga ni da masu reno ta ko'ina. Ga Kaka a kusa da ni. Ga Hajiya da ka ji sallamarta a gidan to wajen Zahra ta zo. Haka kawai ma a weekend sai Jalal ya ɗauki yarinyar ya kai mata. Shima Junior yanzu saboda Zahra idan ya dawo daga Makaranta ko Islamiyya a gidanmu yake wuni. A haka har wata uku ni da 'yata sai lafiya muke ƙarawa. Kwatsam sai ga Kaka ta tada rikici wai zata koma gida tunda dai Zahra ta fara wayo kuma ina da mai aiki wata Bazawara dake zuwa mini aiki daga safe zuwa yamma ta tafi. Dana ga fa da gaske gida take son tafiya sai na fashe mata da kuka. """Yanzu fisabilillahi Kaka mun miki laifi ne da zaki ce za ki tafi. Idan kika je gidan me za ki musu. Akwai" "wanda ya damu dake a can ne?"" Haka na cigaba da masifa ina hawaye. Wallahi har ƙiba ta yi saboda kwanciyar hankali amma wai zata koma can inda za a riƙa ɗosana abinci a kwano ana miƙo mata." Fita na yi daga ɗakinta na haura sama. Jalal baya gida na zauna ina share hawaye. Daga baya na kira Jalal a waya na ce masa ga Kaka wai tana shiri za ta koma gida. Babu shiri ya dawo gidan ya samu Kaka a ɗaki ya fara bata haƙuri. Abu fa sai da muka haɗa da Umman Fada. Ai kuwa da ta zo ta dinga masifa wai Kaka zata bar gidan hutu ta koma gidan wahala. """To yanzu Halimatu sai na yita zama a gidan Jikata, ai sai mutane su zageni""" """Sun ci kutumarsu masu zagin. Kina ga nima da Allah ya hore mini zan barki ki cigaba da zama a can" "gidan ne. To Wallahi ki yi zamanki a nan""" Da ta ga babu wanda ya goya mata baya sai ta haƙura. Amma fa da ni da ita Kakan mun sha magana da "gori. Sai dai ko kaɗan hakan bai dameni ba. Na riga na dawo daga rakiyarsu, babu abinda zan yi na burgesu." Shekarar Zahra ɗaya da wata uku Jalal ya biya mana Umura ni da Kaka. Ina tunanin ya za a yi da yarinyar kawai sai na yanke shawaran in yayeta. A haka na damƙata wajen Hajiya lokacin da za mu tafi. Yarinyar ko a jikinta dama 'yar gaban goshin Hajiyar ce. Ni da Kaka sai ga mu muna kuka shaɓe-shaɓe lokacin da muka zo Ka'aba. Alhamdulillahi bisa wannan ni'imar. Lokacin da muka dawo kowa na zuwa yiwa Hajiya Kaka Barka har Baffan Katsina ya zo amma Baffa Lawalli fir ya ƙi zuwa. Shi kaɗai ne har yanzu yake jin zafin ɗauke Kaka da na yi daga wajensu. Ko ina ya zauna idan za a yi maganata sai dai ya yita zagina yana cewa na auri mai kuɗi na manta da Asalina. "Ban manta da asalina ba, kuma ina ƙoƙari dai-dai gwargwado duk da su basa gani." Sadda aka saka auren Mardiyyah ma ni na ɗau nauyin kayan ɗakinta har sabon Keken ɗinki na siya mata saboda tunda na mata faɗa ta sa himma a ɗinki kuma tana ɗan samu. A haka da aka yi bikin Baffa Lawalli ko Sannu bai ce min ba balle ya min godiya. Maman Suwaiba kam har gida ta zo bayan bikin tana mini godiya tana kwararo addu'o'i saboda na fitar da ita kunya. Na ce mata babu komai Mardiyyah ai ƙanwata ce... BAYAN SHEKARA BIYU """A nan... A nan za mu yi?"" Na faɗa lokacin da Jalal ya banƙareni da bango ya ɗan ɗaga ƙafata ɗaya." """An hana yi a nan ɗinne?""" """To ai...""" """Shhhh! Kin cika surutu. Just relax and enjoy""" Na kuwa rufe idanuna na wrapping hannuna a wuyansa sai nishi nake. Ciki ne dani da ya saka mini shegen jaraba. A cikin Zahra tsanar abun na yi gaba ɗaya. Amma wannan "cikin sai ya sakani masifar jarabar son abun. Har mamakin kaina nake yi. Shi kuwa ɗan Batalikin nan back to back yake bani, different styles. Wani lokaci har kishi nake ji idan na tuno yadda yake min fa haka ya yita yiwa Cassandra." Lokacin da na samu nitsuwa ne muka shiga banɗaki muka yi wanka tare. """Wato ka sha wahala a cikin Zarah shine ka min addu'a wannan ya zo da jaraba ko""" "Murmushi ya yi mai sauti yana shafa fuskata ya ce ""Cikin Zarah ai sai da kika mai dani Waliyyin dole. Kin" "ga yanzu double episode nake samu a rana""" """Ba wani double episode ɗinnan dan dai ba mu yi jiya bane""" """Wanda muka yi da Asuba fa""" """Ni ba ruwana"" na tashi zan bar jikinsa ya mayar dani """ """Ni ai fatana kullum na saka ki farin ciki ne, Sunshine. I don't mind ko sau nawa ne""" Wayata ce ta shiga ƙara. Jalal ya jawo wayar ya miƙa mini. Ina ga sunan da ya gani ne ya saka shi miƙewa ya je ya fara saka kaya. Yaya Aminu ne ya kirani. Wai matarsa ta sauka jiya da dare. Na yiwa uwa da yaron addu'a. Dana ajiye wayar sai na taso na zo wajen Jalal. """Yallaɓai ya da tashi?""" """Matarsa ce ta haihu ita ba za ta kira ba sai shi""" Hmm! Kishi. """A yi haƙuri Captain, saƙon haihuwar kawai ya bayar""" """Ke kuma kika dinga jero masa addu'o'i saboda ya ji daɗin muryanki ko""" Na shiga uku. """A yi haƙuri, Yallaɓai"" ya juya ya fita bai ce komai ba. Yana fita na sauke ajiyar zuciya. Dana sani da ban" "bashi labarin soyayyata da yaya Aminu ba. Ga shi dai yaya Aminun ya yi aure last year, ya auri wata farar Bafulatana a Yola amma duk sadda wani abu ya sa muka yi waya sai ransa ya ɓaci. Gaskiya kishin maza babu kyau." "Bai dawo gidan ba sai dare. Allah ya taimakeni da ya shigo sai na ga ya ɗan sauko, dan haka sai na buge" "da yi masa taɗin Zahra, ai kuwa sai gashi har da dariya. Yana son Zahra so bana wasa ba. Bana jin yana yiwa Junior son da yake mata. Itama yarinyar 'yar gaban goshin Daddy ce, komai Daddynta." Da muka kwanta ban taƙalo shi bama shi ya taƙaloni na kuwa saki jiki na fara karɓan sunnar Aure. *** Captain yana tsaye jikin madubi yana saka links ɗin rigarsa na zuba masa idanu ina kallon yadda yake "komai cikin nitsuwa. Wani murmushi ne ya ƙwace mini ba tareda na shirya ba. Mijina kenan fa, farincikina, uban 'ya'yana, Abokina, Business Partner ɗina. Saboda ina tare da shi babu wata matsala da zata tunkaroni a rayuwata ko business ɗina da ba zan iya warwarewa ba." """Ka yi kyau"" na furta lokacin dana miƙe na tako inda ya ke. Juyowa ya yi yana kallona hannunsa ɗauke da" hula. """Na yi kyau ko?"" Ya faɗa zai saka hular na karɓe hular daga hannunsa na ɗan yi ɗagel na saka masa na ce" """ka yi kyau sosai""" "Ya zagayeni da hannunsa ya ce ""wannan dana ke samun Compliment da safen nan so ake a hanani" "tafiyar nan ko""" """Kaima ka san idan son raina ne ba za ka yi tafiyar nan ba""" Hutu aka yi Jalal zai raka Muhammad London wajen Mamanshi. Yaron ba son zuwa yake ba amma saboda yana cikin tsarin da Kotu ta saka musu dole ne Jalal ya tura shi hutu wajen ta. Tsarin zai ƙare ne idan Muhammad ɗin ya kai shekara shatakwas. A lokacin ne zai zaɓi ya je ko kar ya je wajen Mamansa. Idan ya je London ɗin ya ce akwai abinda zai tsaya yi dan haka sai ya yi sati guda kafin ya dawo. Sati gudan nan yawa ne garesu a wajena. Idan son samu ne duk tafiyar da zai yi kada ya tsallake kwana biyu ya dawo gareni. Kissing goshina ya yi sannan ya kwantar dani a ƙirjinsa. Wani sanyi ne ya ratsa ni. Bani da wani waje da ya fi mini daɗi a duniya sama da kwanciya a jikin Mijina. Ina fata na ɗau shekaru masu yawa nan gaba ina kwanciya a jikinsa irin haka. """Ka san me?""" """Sai kin faɗa""" """Ina sonka, Mr Jalal Maiyaƙi""" "Murmushi ya yi sannan ya ce""Nima ina sonki, MY SUNSHINE"" manna mini kiss ya sake yi a goshi." """Dad na shirya"" muka jiyo muryar Muhammad a bakin ƙofa." """Gani saukowa""" Ina jin ƙaran gudun yaron a stairs na ɗauko wayata na ce barin mana Selfie. A yadda nake kwance a ƙirjinsa na yi mana hoton. Bayan na yi guda uku sannan na ajiye wayar na raka shi waje. """Ɗan duba mana Hajiya Kaka idan bata yi bacci ba sai na mata sallama"" na shiga ɗakin Kaka na sameta" tana sharɓan bacci. Na fito na ce masa tana bacci. A bakin ƙofa na tsaya ina gani ya wuce ya je ya shiga motar wanda tuni Muhammad ya shiga. Bayan motar ta fita daga gidan sai na koma ciki. Kayan wasan Zahra dana gani a falon na tattare na yi sama da su na kai ɗakinta na mayar da su cikin sauran kayan wasanta. Tana can wajen Hajiya tana rigimarta. Komawa na yi ɗakina na kalli kaina a madubi. Wata Madam na gani tana kallona. Gaskiya ban ga ta zama "ba, idan na haihu dole na mayar da hankali kan diet ɗina da exercise Gym ɗinnan dai dana watsar shi zan koma." Na shafa cikin ina addu'ar Allah ya sa na saukeshi lafiya. Haka kawai dana zauna sai na ji ina son posting hoton dana ɗauka. Hoton ya fito sosai mun yi bala'in kyau ga shi dukkanmu murmushi muke yi. "Tunda na auri Jalal da aka riƙa cecekuce akan aurena ana zagina wai ya fini kyau, a'a ba auren soyayya" "muka yi ba, a'a dan kuɗinsa na aureshi bayan na walaƙanta Alhaji Nafi'u, ban taɓa ɗaura wani abu gameda mijina a social media ba." Ko lokacin bikin Janan da muka yi Reception ban ɗaura hoto ko ɗaya a shafukana ba. Janan ce ma ta "ɗaura hotonmu a Instagram page ɗinta amma ni ban ɗaura ba. Na yi hakan ne saboda in ɗan kiyaye Aurena daga bakin 'yan social media saboda bakinsu guba ne a gareni. Ina yin food content, ina saka business ɗina a social media, amma aurena kam sai dai su yi ta hasashe." Ban sani ba ko daɗi ne ya min yawa ko kuma dai hormones ɗin ciki ne suke ingizani ban sani ba. Na dai ɗaura hotonmu a duka social media pages ɗina bayan na rufe fiskar Jalal da emoji ɗin zuciya❤. Na rubuta MY HOME a ƙasan hoton. "Daga 2 likes ɗin dana fara gani a Instagram daga ɗaurawa haka likes ɗin suka fara ƙaruwa. 10 likes, 74" "likes, 1050 likes, 3k likes sai ƙara yawa suke, kan kace me cikin ƙasa da awa ɗaya har hoton ya kai 17k likes, ga comments ɗin mutane rututu. Da gangan na ƙi karanta comments ɗin saboda na san raina zai iya ɓaci. Ban damu da comments ɗinsu ba, ko su faɗi alkhairi ko su faɗi sharri." Abinda na ke so su shaida shine MIJINA shine GIDANA. JALAL is my HOME Ba a babin makwanci ko ciyarwa ko shayarwa ba. Ina nufin idan za a yi yaƙin duniya na uku. Idan za mu tashi bamu da komai gobe. "Idan wata rigima ko matsala za ta tunkaromu, ina da tabbacin idan ina tare da shi, to ina GIDA!" Jalal is HOME. NOW and FOREVER. Alhamdulillahi bisa wannan ni'imar... THE END Thank you for loving Jay and Zeey Thank you for buying CHEF ZEEY. "Allah Ubangiji ya saka muku Albarka a naku kasuwancin, Amin." Whatsapp: 08137311900 AudioBooks on YouTube @ Marubuciya Azizat Hamza Channel ©AzizatHamza2025