FIRST RAMADAN WITH HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAR RAMADAN. *Manzon Allah (SAW) Yace:* *“Dukkan aikin da ɗan Adam yayi to nashi ne, Duk aikin lada yana da guda goma makamancin sa, har zuwa a ninka masa sau ɗari bakwai. Sai Allah maɗaukakin Sarki yace: Banda Azumi domin shi na wane, kuma ni ne zan saka akansa. Shi mai Azumi ya kame daga Sha’awarsa, da abinci, da abin sha saboda Ni.* LAMBA NA ƊAYA . Baccin kirki ya gagara ɗaukata saboda cike na ke da zakwaɗi da mararin shirya ma Habibina girke-girken alfarma wanda na cika wayata da su,wasu na samo su ne daga Tiktok wasu daga group ɗinmu na Whatsapp wasu kuma na cirosu ne daga shafin manyan chef da ke Facebook dan haka sam na gagara sukuni babban burina yamma ta yi in shige cikin kicin saboda wannan shine farkon azumi da zan yi a gidan HABIBI(FIRST RAMADAN WITH HABIBI). Duk na ji zaman ya isheni minti-minti nake duba agogo amma sai in ga kamar an rage ma lokacin gudu dan haka na janyo wayata na shiga cikin group ɗin mu na sababbin Amaren da suka yi aure daf da Ramadan,nan take aka goge min hadda saboda hango bidiyon da takwarorina Amaren group ɗin suke turowa na yanke-yanken da suka fara gabatarwa dan haka na zabura na miƙe na shige kicin,dankwalin turawa na ɗibo cikin faranti na fara fera wanda ya ɗaukeni fin awa ɗaya,ina kammalawa na janyo kabeji,karas,koren wake,kokumba na goge na gogewa na yanka na yankawa na sashi a freezer,wake na ɗebo rabin Mudu na hau surfe na wanke shi tsaf na sa a firinji,kafin na fara kokawar haɗa jus,ina kammalawa na ɗebo gyaɗan da Momi ta niƙa min na zuba farar shinkafa akai na yi blending na shi,kafin na dawo gurin Naman sa da kifi na ciri kaza 4 na fara aikinta,duk aikin nan da nake yi Inna kammala guda 1 ina yin video in tura group ɗin mu na FIRST RAMADAN gudun kar a yi bani ko kuma a ga gazawata dan duk  yawancinmu classmate ne mun san juna. Jin ana kiran Sallan azahar ya sa na tsagaita da aikin na je na sauke farali,ji na yi duk jikina ya yi sanyi kasala na shirin rufeni amma haka na yi ƙarfin hali na shiga cikin kicin na fara aikina,dafa wannan,sauke wancan,soya wannan sai da ya ɗauke Ni fin awa 5 ina aikin dan hatta gyaran gida sai da ana gab da ƙiran magrib sannan na kimtsa falona tare da jera kuloli bila adadin banda Flask da lemummukan da na yi ma HABIBI,turare na sa na wuta , a gaggauce na faɗa bayi na watsa ruwa na fito ban bi ta kan kicin ba dan ba zan iya gyara shi ba a wannan lokacin ga himilin wanke-wanken dana tara dan kusan rabin tukwane na na yi amfani da su bayan ribobi,blender da na yi aiki dasu ban wanke ba. Riga kawai na zura da Hijab na fara rama Sallan la'asar wanda ban samu na yi ba saboda aiki,ina idarwa na gyagygyara jikina kafin na shiga cikin Ƙayataccen Falonmu wanda abokan mijina suka yi ma ƙawanya,gaisawa muka yi cikin raha da barkwanci bakin su fal murnan yau za su kwashi ganima,na kai dubina kan HABIBI wanda yake jin kan shi a kumbure irin shima Allah ya kawo shi lokaci ya zama magidanci,murmushi na sakar mi shi mai sanyi shima ya maido min da tashi kafin na shiga Serving na su cike da son burgewa,Kunun gyaɗa mai kwakwa na fara zuba musu tare da madara wanda na kusa juye gwangwani ɗaya,sai alalen da yaji hanta da ƙwai tare da source ɗin naman rago a gefe,irish ball tare da wainan ƙwai a gefe guda,sai irian rice wacce ta ji kayan lambu tuttura musu gabansu ƙamshi duk ya cika musu ciki har wani tanɗe baki suke yi dan girkin ya sha spices,dakatawa na yi da zuba farfesun kifin jin sannu da aikin da suke min ya yi yawa sai gasashshiyar kaza da na mata gashin tukunya ganin suna ta godiya sai na sa juice ɗin karas na ajiye ma kowa a gaban shi nima na janyo kujera na zauna tare da ɗiban kunun gyaɗan ɗan kaɗan na ƙarasa juye madarar gwangwani,ƙasa-ƙasa na ga HABIBI ya kalleni tare da aiko min da saƙon harara,a cikin zuciyarsa kuwa yana jin kamar ya jawoni ya lakaɗa min dukan tsiya dan shi sai yau ya tabbatar da mahaukaciya ya auro ba mai hankali ba banda haka ina mai hankali zai aikata irin abin da(DIYAN SHi)ta aikata,ta soye rabin kiret na ƙwan da ya siyo a ƙiyasin shi,ta juye gwangwanin madarar gari a rana guda wanda yana ganin zai kai musu rabin azumi tunda yanzu kowa ya san halin da ake ciki a ƙasar nan,kifi,kaji,namomi duk ta dafe shi a lokaci guda babban takaicin shi ko mutane goma ya ƙaro za su ci abincin har ya rage wai me ta aikata haka ne?ina hankalinta ya tafi ne har ta yi wannan ɗanyen aikin? Ji ya yi abincin duk ya fice masa a rai dan HABIBI riƙaƙken Kwamared ne wanda ke da dokoki da ka'idodi a matsayin shi na cikakken ɗan boko mai degree har biyu amma har yanzu ba takamammen aiki, Ashe da sauran rina a kaba dan yana kurɓan kunu ya yi saurin fito da shi jin wani irin TSAMI da ya ziyarci harshen shi da sauri ya ɗibi Irish balls ɗin nan ya kai bakin shi sai dai jin wani irin zaƙin maggi,da gafin kori da ya baƙunce shi yasa ya miƙe a guje ya fice daga Falon da sauri DIYAN HABIBI ta mara mi shi baya sai dai tana tunkaro shi ya yi saurin hankaɗeta ya yi waje da mugun sauri gudun kar abokanan shi su ci wannan kwaɓar dan ya san ya riga da ya gama kunyata a idonsu sai dai ko kafin ya isa aikin gama ya gama,ba bu abinda ba su ɗanɗana ba dan haka marasa hakurin cikinsu har sun miƙe a gaggauce tare da shigewa cikin motocinsu dan yunwa na ƙwaƙwularsu masu hakurin ne kawai su biyu suka rage da shan lemo da abarban da suka shigo da su,takaici tare da baƙin ciki yasa ya ji kamar ya kashe DIYAN SHi  yau dan ta yi matuƙar ja masa abin kunya a cikin abokai dan haka ya tasota a gaba a kan dole sai ta cinye duk abinda ta girka bayan ya sallami sauran, ganin yanda yake huci ya sa ta ranta ana kare sai gidansu dan bai da nisa a tsakani. Regegeniyar tambayarta lafiya aka fara tsakanin Amminta da Abynta aka yi, kuka ta ke tana ƙarawa ta gagara furta uffan,ganin yanda take ƙiran sunan HABIBI a firgice ya sa Mahaifinta kama hannunta ya maidata cikin gidanta,jan hannunshi take har suka iso falonta nan ta tadda HABIBI yana kuka dafe da kumatun shi biyu, ganin asarar data tafka mi shi (Yo abin ku da kwamared iyayen tsumulmula da tsumi da tanadi),tun kafin Abynta ya ce uffan HABIBI ya miƙe yana nunota da hannu cikin rufewar ido dan ko ganin sirikin na shi ne yi ba ya ce"Ni kika kunyata DIYAH(DEAR)a gaban abokanaina?,ji yanda kika almubbazzarantar da kayan abinci dana maƙulashe fisabilillahi to na yanke hukunci ba zaki ƙara soya ko da dankwalin Hausa ba a gidannan har azumi ya ƙare,zan auno masara da kuka da kuɓewa shi ne abincin da zaki dinga ci har sai Ramadan ya wuce" Kuka ta fashe da shi tana ce wa"Dan Allah Abi ka bashi haƙuri Ni ban san mena yi ba." Nuna mata dinning Area Abyn ya yi ya ce"je ki ci abincin da kika dafa"dan tunda ya ga HABIBI na kuka a gaban manyan kololi ya san kwanan zancen, Cike da ƙarfin gwiywa ta isa ta fara kai kofin kunun bakinta ta ji tsami ya buwayi bakinta dan haka ta furzo shi,ja da baya ta fara yi cikin tsare gida Abyn ya umurce ta ta buɗe kowanne kula ta ji, cikin ɓata fuska ta ke taɓa kowanne daga wanda tsami yayi yawa,sai wanda yaji ko suga ko barkono ya yi yawa nan da nan ta fashe da kuka dan tabbas da ace ta yi koyi da mahaifiyarta bata biye ma Ramadan time table na social media ba da bata shiga cikin chakwakiyar ba dan tabbas ita ɗin gwana ce gurin girki, Ƙawayenta na group ɗin FIRST RAMADAN WITH HABIBI sun cuceta duniya da ƙiyama ko kafin ta ce uffan Abynta ya juya bayan ya jinjina ma sirikin shi akan hukuncin da ya ɗauka. Labarin gajere ne na rubuta shi ne saboda faɗakarwa akan Amare masu biye kawayen social media idan kuna buƙatar cigaba in ga comments. Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAR RAMADAN.   Manzon Allah (SAW) Ya kasance yana yin buɗa baki da ɗanyen dabino kafin yayi Sallah, idan bai sami ɗanyen dabinon ba sai ya yi da busasshe, idan kuma bai sami busasshen ba sai ya ɗan kurɓi ruwa”. [Tirmizi]. LAMBA NA BIYU. A tunzure HABIBI ya mara ma sirikin shi  baya ya fice zuwa Masallaci domin gabatar da sallan Ishsha,ana idarwa aka kabbara sallan Asham jin yanda idon shi ke rufewa tsabar yunwa ya sa ya fice daga masallacin kai tsaye ya nufi wani madaidaicin gurin sai da abinci, Layi ya bi har aka kawo kan shi sai dai yana miƙa Debit card ɗin shi domin a zari kuɗin abincin ba network, ƙoƙarin yin transfer ya yi ta cikin bankin shi na Opay da ke wayar shi nan ya nuna ya shiga amma mai gurin sam bata ga alert ba dan haka ta hana shi tafiya,abu ya haɗu ma shi goma da ishirin ganin ana niyyar karɓar abincin daga hannun shi yasa ya fizge a tsiyace ya samu gurin zama ya fara kwankwaɗar kunun tsamiyar da ya siya,sai da ya yi rabi sannan ya fara cin masan a yunwa ce ,wani irin mugun kallo ya wurga ma waiter ɗin da ke jiran alert ya ce"Matsa anan ko in barar da ke wallahi", "Ba zan matsa ba,ka bani kuɗi dan ba mu ji alert ba." "Sisi bana magani dan kin fi kowa sanin wuyar da cash yake yi kuma Bank ɗin ku ne ke da matsala dan Ni ya tafi." Da wani bank ka yi Taransifar."ce War mai gurin, "Opay"ya furta a daƙile dan ji yake yi kamar ya shaƙe su dan takaici banda shirmen da Diya ta aikata mi shi me zai sa ma har su gan shi a waje, Shikenan ba damuwa ka tafi idan bai zo ba gobe za mu haɗu."ce War Hajiyar bayan ta ga receipt na transaction ɗin, Wani dogon tsaki ya ja tare da ficewa sai dai me yana isa gida ya ƙara tadda wani kayan takaicin tun daga ƙofar falo in da ya hango throw pillows a zube a ƙofar shiga, tsallake su ya yi ya ƙarasa shiga falon in da ya tadda shi yanda ya bar shi sam Diyah bata kwashe kayan abincinta ba,tsaki ya yi ya shige cikin ɗakin shi domin ya watsa ruwa sam bai bi ta kan mashirmaciyan can ba a cewar shi.   Diyah kuwa tsabar takaicin abinda ta aikata yasa ta ji yunwar cikin nata ma kan shi ya ɗauke dan haka ta rarrafa ta shige cikin group na FRWM(First Ramadan with HABIBI)janyo wayarta ta yi ganin takwas har ta gota ta san akwai labari daɗaɗa,buɗe datar ta ke da wuya ta ga akasin haka saboda dukkanin waɗanda suka aikata kalar haukarta ko mafiyin nata ma ba su ƙarke da mazajensu lafiya ba ,matsalar da ya fi jan hankalinta shi ne na aminiyarta wacce aka saketa sanadin Ramadan time-table na social media wanda ta rubuta shi a group ɗin SIRRIN YA MACE dake Facebook in da ta ce"Ina son mijina amma ya sakeni sanadiyyar na ɗauki kuɗin shi na yi siyayyar kayan ƙwalam da maƙulashe wanda na kwafo daga shafin sada zumunta,na tambaye shi kuɗin da safe ya ce bai da shi,yana fita na ɗauki Debit card ɗin shi na je na yi siyayya dan Allah ku bani shawarar yanda zan koma hide my id sister yau aurenmu ke cika sati biyu cif da aure." Ai ban ƙara sa kai ƙarashen labarin ba na koma Facebook in da na shige SIRRIN YA MACE domin karanta comments kamar yanda na saba, Cikin manyan baƙi na ga an rubuta"FIRST RAMADAN WITH HABIBI"sannan aka ɗauro post ɗin aminiyarta Laila wanda yawancin matan sirri Allah ya ƙara suke mata,sai masu kareta da sunan ƙaddara ne ai kuma mene amfanin bude gidan idan har ba za su ba ma juna shawara ba,dan haka sai ƴan abi yarima asha kiɗa suka fara bata shawara nan da nan na ji wani gamsuwa ya riskeni yayinda na haɗu da shawarwarin masu hankalin da suka ba da shawara dan haka nima na ce bari in gwada ko Allah zai sa HABIBI ya canza shawarar shi a kaina, Ba tare da tunanin komai ba na yi post tare da tura ma mai girma admin domin ta yi hide ɗina,nan take kowa ta posta min dan na yi sara ne akan gaba tana online kuma ganin hukuncin da HABIBI ya ɗauka akaina  na cin tuwo ta san zai ja hankali dan haka ta yi min post aikuwa na sha zagi cin mutumci iri-iri kafin nagarin suka fara bani shawara, Jin yanda idona ke min nauyi yasa na ajiye wayar a gefe sai dai ina rufe ido wani irin yunwa ya tasoni gaba dan haka dole na tashi a firgice tare da shigewa cikin kicin, Haɗa shayi na yi tare da zabga Milo tunda madararmu ta ƙare,na sa sugar madaidaici tare da ɗaukan biredi da bota,sam yunwar ta rufe idona sam ban san da wanzuwar HABIBI a cikin madafar ba yana wanke kajin da na cika ma spices da yaji a gaban sink(Aikin Kwamared) Har sai da naji ya ruƙo biredi da shayin cikin haɗe fuska ya ce"To be sencere ba zaki sha shayin nan ba almubazzara." Ganin yanda ya yi maganan yasa na san he is serious dan haka cikin kuka na ce"Ni yunwa zata kasheni wayyo Ammina,ka bani ko in ƙirata Billah." Wata muguwar harara ya doka min tare da komawa kan aikin shi na dirzan kaza da soson da yake yi duk kalar da na jibga mata ta fita, Dariya ce ta so suɓuce min sai dai murɗawan da cikina ya yi yasa na fashe mi shi da kuka,cikin zafin nama ya damƙo hannuna tare da nuna min Iranian rice ɗin da na musu ya ce"Zo ki ci wannan in dai yunwa kike ji ko in maki bugun sakwara." Ɗebowa na yi na kai bakina jin yanda shinkafar ta yi zaƙo-zaƙo tare da kayan haɗin na cabbage karas,green beans,da su gurjin yasa na haɗiyeshi da ƙyar nan da nan wani tari ya turniƙeni HABIBI ya yi saurin miƙo min ruwa a cewar "Bai gama fanshe kuɗin da ya kashe ba na aurena dan haka in na mutu na cuce shi." Sai da tarin ya lafa sannan na ce"Ba zan iya cin wannan abincin ba mai kama dana ƴan fursin wallahi haba wannan wani irin gwale-gwale ne?." "Mu ɗin bayin gidanku ne da za ki bamu abincin nan ko fursunonin ki ne?" "Eh fursunonina ne"na faɗi hakan a cikin zuciyata sai dai a fili ce wa na yi"A'a HABIBI ka yi haƙuri Ni fa da niyar kyautatawa na yi maku wallahi amma ka ga alhairi na shirin zamar min sharri." Harara ya banka mata ka fin ya ce"Wa ya koya miki wannan girkin mahaukatan?"Ya mata tambayar a harzuƙe dan ya san DIYAH ɗin sa ta iya girke-girken alfarma to mai yasa a wannan karon za ta kunyata shi. A Tiktok na ga wata Chief ta ɗaura,sunan shi kawai ya ja hankalina na sauke shi a kan wayata kuma musamman na tanaje shi sai a farkon watan Ramadan dan in burgeka da shi HABIBINA. Tiktok........ More comments More Typing.. Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. *LADUBBAN HAWA KAFAR SADARWA A RAMADAN* *Mu nisanci yaɗa musu, jayayya, da zage-zage ko ƙarya musamman kan Addinin Musulunci. Da masu zama su ƙirƙiri labarin ƙarya mara amfani.*   LAMBA TA UKU. TIKTOK ki ka ce fa? cike da mantuwa na furta "Eh wallahi ka san ai manhajar akwai ababe kala-kala na amfanin rayuwa na banzan ne kawai aka fi sani." "Tabbas haka ne akwai tatattun mahaukata masu koya ma masu taɓin hankali irinki girki tunda kun raina na iyaye da kakanni da kuka gada." "No no no HABIBI wallahi ba haka ba ne kasan fa mu ƴan zamani ne kuma dole mu yi amfani da hikimomin mu na masu jini a jika domin burge mazajenmu ta kowani fanni musamman fannin girki." Harara ya banka mata cikin ƙofula ya ce"ɗauki abincin nan ki cinye, kuma This should be the last warning da zan miki magana a kan shiga TIKTOK da FACEBOOK in kunne ya ji gangan jiki ya tsira." Ɓata rai na yi ina muy-muy da baki ba a zuciyata kuma na ce"Bai isa ba." Ko duba yanayina bai yi ba ya cigaba da faɗan shi kamar zai aro baki"To banda hauka da shiririta ina naki  ni Ko a jerin girke-girken zamani da na ke haɗuwa da su a kafafen sada zumunta ban taɓa jin wani mai suna Iranian friend rice ba sai a gurinki,kuma ko da banga bidiyon ba na tabbatar da cewa daga kan green beans da duk wani abu mai tauri na tabbatar da sai sun tafasa shi sau ɗaya kafin a haɗa shi a cikin girkin amma saboda ke hauka na damunki haka kika cunkusa mana shi"jin ya yi shiru yasa na ɗago na kalle shi ganin ba alamun rahama a fuskar shi yasa na ajiye cokali gefe guda na tattara kayan lambun da suka sa shinkafar take gagara wucewa a maƙoshi na fara afawa ina yamutsa fuska,hannu baka hannu ƙwarya haka na cika cikina da fried rice ɗin mara daɗi,bayan na cire mata ingredients ɗin da yasa ta zama Irian fried rice, Ruwa na kwankwaɗa sosai na yi gyatsa ganin yanda HABIBI ya zage yana gyara duk abinda zai iya gyaruwa a cikin girke-girkena yasa na sa hannu na fara tallafa masa,mun yi nasarar soye kajin nan bayan mun sulalata da su citta,kanumfari da albasa da sinadarin ɗanɗano sannan muka komo kan source ɗin naman rago wanda maggi ya masa yawa muka ƙara masa kayan miya dan haka ya dawo daidai muka sashi a fridge,sai kunun gyaɗar da na yi wanda tsami ya mi shi yawa nan da nan na ƙara dama wani muka gauraya shi da wancan mai tsamin ya dawo daidai dan haka ya zama mun cika wani ƙaton kula da shi babba,nan da nan HABIBI ya mance da laifin da na masa ya riƙoni bayan mun kammala aikin muka shige cikin ɗakin mu, Ƙarfe huɗun asuba ya fita ya nufi masallaci mafi kusa da mu in da ya tarar da masu abinci duk sun fito dan haka ya damƙa amanar rabon abincin ga wani mai sai da rake akan a raba ma mabuƙata, ruwan addu'o'i ya sha a gurin ƴan ciranin da ke barin matansu a garuruwan su suna zuwa neman kuɗi garinmu,sun sha kunun gyaɗan nan kamar me tare da irish ball wanda na ƙara dafa wani na marmashe shi da wancan sai ƙwai dana ƙara soya shi da shi,Fried rice ɗin ma ruwa na ƙara mi shi ya dahu dan haka na zuba shi a ƙaton kula aka ba su suka hau rabo bayan sun yi layi daga ƙarshe har dambe aka kaure da shi dan wasu suna karɓar sau biyu. Kajinmu kuwa da  farfesun kifi duka mun adanasu a firiji bayan mun yi sahur muka koma ramakon baccin da ba mu samu mun yi ba, Sai guraren ɗayan rana muka farka in da muka tashi da wata sabuwar fitina daga HABIBI,neman ya sadu da Ni yake ta ƙarfi da yaji saboda yanda muka kwanta manne da juna dan haka daga farkawar sa Hajiyarsa ta fara haniniya tana wani zabura ita ala dole tana neman abincinta,a gigice na fara hankaɗe shi ina tuttura shi sanin muna cikin wata mai alfarma kuma duk jahilci na dai na san ba'a tarawa da miji in ana azumi, Amma ina ɗan talikin nan ya fututtuke ido yana son jawo min hadisan ƙarya dana gaskiya dan haka na zabura na miƙe tare da shigewa cikin bayi na danna mi shi makulli a guje ya biyo NI yana bubbuga ƙofar ya na ce wa"in buɗe ko ya ɓalla ƙofar" ko mai ya tuna kuma sai na ji ya bar bakin ƙofar yana kwafa can kuma ya rufo ƙofar ɗakin a hassale nan na fara sauke ajiyar zuwa a jajjere kamar wacce ta sha gudun tsere, wanka na yi sannan na ɗauro alwalla na fito tare da rufe ƙofata gam.   A can ɗakin Habibin Diyah kuwa istigfari ya fara tare da roƙon Allah yafiya akan abinda ya yi shirin aikatawa wanda cikin mafarki ya ga suna wasa da Amaryarsa DIYAH,farkawar sa yaji ta a jikinsa yasa ya ji sha'awar ta ƙara rufe shi sam ya manta da suna azumi kasancewar kuma tana gudun shi tunda ya amshi budurcinta yasa yake ganin kamar har yanzu tsoron ne shiyasa ya dage. Nan take yaji wani nadama da takaicin auren gaf da Ramadan ya kama shi dan kan shi har ga Allah yana cikin wani hali yanzu,kuma da ace yana da hanyar da zai ɗaga sautin shi har iyayen yara su ji tabbas da ya ɗaga tare da gargaɗin su akan yi ma zalamammun matasan yanzu aure gab da azumi dan da yawansu suna karya azumin su dan biye ma sharrin zuciya, Ya san dayawan iyaye suna aurar da ƴaƴansu ne gab da Ramadan dan su samu ladan wannan wata amma sun mance da wata ibada wanda amaren da angwayen suka mai dashi abin da yafi komai marmari a tsakaninsu tabbas ana tafka kuskure Allah dai ya kula mana da imaninmu kawai,da wannan tunanin ya shiga banɗaki ya kwara ma kan shi ruwa nan da nan sanyin ruwan ya ratsa har ƙwaƙwalwar shi,ji ya yi jikin shi ya ƙara sanyi, A daddafe ya yi wanka ya ɗauro alwalla kafin ya fito yasa jallabiyya ya tada kabbarar salla dan a yanayin da yake ciki sam ba zai iya fita ba,karatun Alkur'ani ya yi bayan idar da Sallan nan take nutsuwa ya mamaye ruhin shi,nan ya ji sanyi ya cika ƙirjin shi,a ɗikance ya fara yi ma ubangijin Annabi Muhammadu kirari da mafi daɗaɗan kalmomi har bacci ya yi awon gaba da shi mai cike da nutsuwa.   DIYAN HABIBI kuwa Data ta buɗe ta haye online,da ƙawarta Hakeema suka gaisa sama-sama dan ta tsaneta saboda ta cika yi musu karan tsaye akan shirye-shiryen su da suke gabatarwa a First Ramadan with HABIBI group,a kan komai ita bagidajiya ce kuma ana fara hiran miji zata fara sako musu Allah da Annabi dan haka suka maida ta saniyar ware tunda sam bata biye ma shirmensu,ita ɗin sam bata waye ba balle ta kile, Sai dai tana hawa Facebook ta ci karo da abin da ya kusa sata ciwon zuciya saboda ganin matsalarta da ta tura ma admin na SIRRIN YA MACE group ya zama topic of discussion a social media,har maza sanya shi suke yi ana tattauna irin shirmen da ta tafka a newsfeed, babban abin da ya karyar mata da zuciya shi ne, Yanda ta bada labarin da ta bada sam bata sakaya ba in Habibinta ya gani tabbas zai gane labarin na su ne,nan da nan na ji hancin cikina ya murɗa dan haka na yi banɗaki a guje, A wahale na fito dan duk abin da ke cikin cikinna sai da ya fita,jin numfashina na fita da ƙyar  tsabar tsoron da n ke ji hakan yasa na miƙe tare da ɗaukan wayana na koma Whatsapp in da na shiga group ɗinmu na amana,amma bisa mamakina sai na ga anan ɗin ma zancen da ake tattaunawa kenan dan haka na fice tare da shiga wani gurup,sai dai duk kanwar ja ce  duk in da na shiga labarina ake, masu screen shot sun yi sun turo ƴan copy and paste ma sun tura dan haka na fara zarya kamar zararra na rasa wani mataki yakamata in ɗauka. Hakeema ce ta faɗo mata a rai dan haka na tura mata emoji mai alamun Sannu,baiwar Allah wacce ke zaune a kan dadduma tana karatun Alkur'ani a wayarta ta ji saƙo ya shigo mata ta yi saurin kashe datan sai dai ga mamakinta bayan ta kammala karatun ta tashi da niyyar yin aiki sai ta ga numban ƙawarta Farrah ya shigo cikin wayarta, A gadarance ta ce"Ki hau Whatsapp ina son mu yi magana ƴar wulaƙanci kawai." To fah kun ji isasshshiyar taku ko? Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. *LADUBBAN HAWA KAFAR SADARWA A RAMADAN.* *Mu zamto masu yin post na faɗakarwa musamman akan abin da ya shafi Ramadan, ya zamana abin da yake shigo da mu Facebook ko Whatsapp kenan, in ma muyi posting ko kuma mu karanta rubututtukan malaman mu domin samun ƙarfin guiwa akan Ibadun mu.* LAMBA TA HUƊU. A gadarance ta ce"Ki hau Whatsapp ina son mu yi magana ƴar wulaƙanci kawai." "To fah! mai kuma na yi miki DIYAN HABIBI?" "Kina ganin magana na a online kika ba banza ajiyata daga ƙarshe ma kika sauka tsabar banda muhimmanci." "Bana Online Datar ce a kunne."ta furta hakan a taƙaice, Kwafa ta yi kamar tana Kallonta ta ce"Ina cikin matsala ne gaggaruma Billah,and i am totally confused That is the reason da yasa na ke nemanki" "Turƙashi!Mai kuma ya faru?"ta furta hakan a kiɗime. "Zan faɗa miki dan ina neman mafita ne kawai kuma kar ki min dariya dan Allah." Murmushi ne ya suɓuce mata jin abinda ta ce amma tuno da tana cikin matsala ya sa ta ce"kai tsaye ki faɗi matsalarki ba zan miki dariya ba matsalarki ai tawa ce." "Promise." "Yeah i mean it, straight forward Please zan fara aikin girki." I Don't now from where to start na furta hakan cikin zuciyata amma sai na kwantar da kai na fara shiryi mata yanda lamarin ya faru tun daga farko har ƙarshen shi, Shiru ta yi na wasu sakanni saboda yanda ta ji wani shock ya kamata har sai da DIYAN HABIBI ta ce"Kina tare da Ni?" "Sosai ina jinki,kawai na yi suman zaune ne wallahi Farrah,Haba ina hankalinki da tunanin suka tafi da har zaki kwashe sirrin gidan aurenki ki kai shi Facebook ko da yake rayuwar da mata suka ɗauka kenan na yayata sirrinsu a social media abu ne dake ce min tuwo a ƙwarya,ba ga ƴanmata ba wanda su nake musu uzuri da ƙuruciya ce,sai dai matan aure nasu abin ya fi munana a ganina." Hararar fuskar wayar tawa na yi na ce"Ji wani baƙin iyeyi a gurinki dan Allah, yanzu mene ne illa dan matan aure ta je group ɗin mata zalla ta kai damuwarta dan ta samu mafita?" "Babban matsalar ita ce dubannin gardawan da ke buɗe akawut da sunan mace suna shiga suna leƙan mana sirrikanmu har ma su yi copy and paste su yaɗa ma duniya,shin wai mun rasa mafaɗa ne ko kuwa ba mu da iyaye,kanne,yayu,ƙawaye da za mu yi shawara da sune muke yaɗa ma duniya?" "Ɓatan basira mana yanzu da ta kwaɓe min ba ga shi ke na nema ba." "Allah ya mana magani to amma dai ya kamata mu yi ma kanmu faɗa wallahi dan wasu dayawa sun rasa mutuncinsu a idon mazajensu sanadin wannan shirmen." "Ke ni fa ba dan kin hango matsalar ba wallahi Ni normal ce a gurina dan dai ke ɗin akwai zurfafa tunani ne Ƙawata." "Dan dai ba ki san yanda wannan matsalar na rashin riƙe sirrikan gidajen mu na aure ya ke taka muhimmiyar rawa wajen janyo ma mata n matsala ba ne." "Kan aje da nisa ma ai gani nan ma Hakeema,ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka sannan na tabbatar da in wani ya taka rawa aka masa liƙi to wani ɗan karan duka zai sa dan in HABIBI ya ga labarin da nasa ake yamaɗiɗi da shi wallahi na kaɗe,dan Allah ki bani mafita ba dan halina ba ƙawata." Voice ta min na minti biyar nan take ta sauka ganin har ƙarfe huɗu ya yi ta san mijinta ya kusa shigowa kawo mata abin da za su sarrafa dan buɗa baki, addu'a ta shiga yi akan Allah ya sa ya samu abinda suka je nema dan ba su da ko ƙwallin shinkafa balle ƙwayar gero jiya haka ta yi buɗa baki da ruwa zalla shi kuwa Angonta na can yana bibiyar gidajen abokai kwaɗayi,ya gagara tsayuwa da ƙafarsa ya nemi sana'a domin dogaro da Kai,dan tunda garar bikinsu ya ƙare wanda rabi ya kwashe ya sayar suka yi cefane shikenan ta fara zama da yunwa har gara ma da take azumin ta san azumi take. DIYAN HABIBI. Bayan na gama sauraran voice ɗin Hakeema nan da nan na ji hankalina ya kwanta dan haka na fice zuwa kicin ɗina wanda himilin wanke-wanken jiya ke jirana kamar mai ƴaƴa goma,ji na yi sam ba zan iya tsayuwar ba tsabar yawansu dan haka na ɗau kujera ƴar tsugunno na fito da kayan harabar kicin na fara wankewa,na shafe awa ɗaya da rabi ina wanke-wanken ƙarshe dana ga yaƙi ƙarawa na ji kamar in rusa kuka(Shawara kyauta ga mata a cikin wannan aikin Ramadan ɗin,sam bai kamata kina aiki ko mai kika ɓata ki bar shi ba,kamata ya yi kina ƙoƙari kina wankewa hakan zai sa gobe ki tashi da wanke-wanken kaɗan.) Ƙarin minti talatin na ƙara wanda ya zama awa biyu cut kenan sannan na kammala,na shige Falo na gyara,uwarɗakana sannan na shiga ɗakin HABIBI na tadda shi tsaye yana shirin fita,dakatawa na yi ganin ba alamun rahama har yanzu akan fuskar shi na ce"Mai zamu girka yau." Zuro jikin shi ya yi ya idasa fitowa daga ɗakin kafin ya ce"White rice da Coslow tunda muna da source na naman ragon nan,sai kunun tsamiya da ƙosai." Gwalalo ido na yi na ce"Duba agogo fa HABIBI." "Shida ne dai-dai Farrah,dafa farar shinkafa da dama kunun ne abu mai wahala kome?" "Na surfa wake da hannuna tun kafin Ramadan na sa shi a rana ya bushe na sheƙe tare da ɗura shi a bokiti jiƙawan ne ki markaɗa ki soya min ne zai gagareki ko me?" Shiru na yi ina zare ido danni har ga Allah na gaji haba FIRST RAMADAN WITH HABIBI ko first Ramadan with cin uban aiki da wahala, Jiki a sanyaye haka na juya na nufi madafar har na kusa isa  cikin ɗaga murya na ji yace" Kuma ki haɗa min juice na ƴaƴan itatuwa kar ki kuskura ki sa min kayan zaƙi a ciki." "Ka kasheni kawai ka huta HABIBI."na furta hakan ina shigewa cikin madafar a guje, Tausayinta ya ji ya kama shi amma sai ya danne tare da biyota madafar cikin son tura mata haushi ya ce"Bar ganin yau ban niƙo miki garin dawa dana masara ba tare da daddawa da kuka da kuɓewa ki min iskanci,wallahi in aka samu akasi akan aikin dana baki zan tsaurara matakai wannan ma ba haƙura na yi ba."Ficewa ya yi yana cewa"Jiya da kika so yin haukarki ai bakiji zan kashe ki ba sai yau dana baki umurni. Uffan ban ce mishi ba dan matuƙar na buɗe baki ba alhairi ne zai fito daga bakina ba dan haka na sa ruwan shinkafa akan electric tare da kunna gas tare da jiƙa waken, Tamkar ƙiftawar gira da bismillah na dafa shinkafar ,na ɗumama source ɗin haɗe da haɗa Coslow,na jere su akan dinning tare da kunun tsamiyan da cups,ina suyan ƙosan gefe guda ina haɗa mi shi fruit salad, kammala aikina ya yi daidai da kiran sallan magrib nan take na faɗa ɗaki na sillo wanka na shirya cikin doguwar Armenian gown, feshe jikina na yi da turare kafin na zura Hijab na kabbara sallah, Lokacin na ji shigowar HABIBI tare da abokan shi ƴan amana su biyu,mijin Hakeema Lukman da Sayyid Ali nan take na ji farinciki ya mamaye ruhina dan haka na ƙara so cike da ƙarfin gwiywa muka gaisa kafin na zuzzuba musu abinci da abin sha, Lumshe ido HABIBI ya yi cikin jindaɗi ya bini da wani sansanyar murmushi mai nuna alamun albarka yake sa min a cikin zuciyar shi, Sosai suka duƙufa suna cin abincinsu a nutse sai ƙarar cokula da filet tare da cups kake ji sai da suka ci suka yi nak sannan aka fara yi min santi"To ko ke fa Amarsu,ai abincin gargajiya dabanne a gurin mu." "Musamman ma mu ƴan gargajiya mun fi son namu,mu ba irin su Kwamared ba ne turawan Ingila"Cewar Sayyid Ali suka fashe da dariya dukkanin su. "Ni kaina bar ni a mutunta turanci amma nafi girmama cimar mu fiye da tasu gaskiya haba mai ake da abincin da ba kayan ƙamshi sai kala Kore shar." Miƙewa na yi na fara tattare wajen sai dai tun kafin in kai ficewa falon na tsinkayo muryan Lukman mijin Hakeema yana ce wa"A min take away na shinkafa da source da Coslow ɗin  nan dan gaskiya raina ya biya." Murmushi na yi kawai tare da shigewa ina ƙunƙuni a zuciyata haka na haɗo mi shi su a cikin wani madaidaicin basket albarkacin ƙawata Hakeema ya ci Allah,sai dai me ina shiga cikin Falon na tsinkayo muryan Sayyid Ali yana ce wa"Kalli wani shirme dake yawo a Facebook yau." Dararam! haka na ji zuciyata ya buga....... To fa ko ya zata ƙarke a tsakanin HABIBI da DIYANSA? *Bakwa comments Readers kar in maida littafina na kuɗi ku ga rashin kirkina,Fatan kun sha ruwa lafiya, Allah ya karɓi ibadumu ya yafe mana zunabanmu yasa muna daga cikin ƴantattun bayi." Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. *Nana Aisha (R.A) tana cewa* كان اجود الناس وكان اجود ما يكون في رمضان فلرسول الله صلى الله عليه وسلم اجود باالخير من الريح المرسلة Manzon Allah (SAW) yafi kowa karamci, kuma yafi karamci a cikin Watan Ramadan, kuma lallai Manzon Allah (SAW) yafi karamci da Alkhairi sama da iska mai ratsa jiki. *[Bukhari da Musulim].* LAMBA NA BIYAR. Dararam! haka na ji zuciyata ya buga ganin ya juyo da hankalinshi kacokan a kan allon wayar yasa na ƙara sauri burina dai in cimmasa sai dai ina aikin gaba ya gaba ko kafin in iso har ya karanta, Fizge wayar da ke hannun shi na yi ina hakin uban saurin dana sha na ce"Bani in gani" Yanayina kaɗai ya kalla ya tabbatar mi shi da zargin shi dan haka ya kauda kai daga gareni Ni kuma na miƙa ma Lukman mijin Hakeema basket na abincin na juya, Wayar Aliyu ne fa Farrah"muryan HABIBI ta tsayar da ni juyawar da na yi ina tafiya zan tafi ɗaki da wayar, A kiɗime na dawo cikin son basarwa hannuna na rawa na miƙa ma HABIBI wayar amsa ya yi yana bina da wani mugun kallo ganin ya karɓa yasa na juya da sauri na shige ɗaki jikina sai rawa yake yi,key na sa ma ɗakin na sulale a wajen hawaye na kwarara a idona, Ina jin HABIBI ya dawo daga rakiyar abokan shi na ji cikina ya murɗa dan na san tunda muka yi aure ya hanani shiga TIKTOK da FACEBOOK Whatsapp ɗin ma daya yarda dan yaga sabon layi ne, Banɗaki na faɗa na je na zazzage cikina da ya ruɗe sai dai ina fitowa na fara jin ƙara tsakanin kicin da Falo,nan na ji tsoro ya kamani dan ji nayi ana jan abu kamar a buhu haka dan haka a hanzarce na buɗe ƙofar sai dai bisa ga mamaki HABIBI na hango yana jan buhun shinkafa ɗayar hannun shi riƙe dana Semonvita ya nufi hanyar ɗakin shi,hangangan haka na yi da baki a buɗe na rasa mai ma zance mi shi tsabar mamaki, Ko kallon gefen da nake bai yi ba ya shige da su ya ƙara fitowa da Taliya,macaroni da jarkan mai ya kai ɗaki ya dawo ya ƙara komawa cikin ɗakin, Kaf kayan cikin freezern mu dake kicin ya kwashe tare da gurguro da freezern ya nufi hanyar ɗakin shi da shi,dan da man cikin ɗakin na shi apartment ne guda har store akwai a ciki da kicin, Mutuwar tsaye na yi ina kallon ikon Allah haka ya shigar da shi ciki ya dawo ya fara kinkimar su robobi da tukwane yana shiga da su kai a sannan ne naji zuciya ta kawo min wuya na ji wani ƙululu ya tattaru min a wuya dan haka na ce"Kwamared Mashkur wannan tattara kayan na meye wai." Shiru ya min yana niyyar shan gabana na yi saurin yin birki a gaban shi na ce"Kaf kayan da ka ke yunƙurin shiga da su apartment ɗinka garata ne wanda Ubana ya min na ga ba kai ka siya ba amma sai kwasarsu kake kana shigar da su cikin ɗaki sai ka ce wani ɗan ƙauy............" Ai bai bari na kai ƙarshe ba ya falla min mari dama da hauni,nan take na ga wasu taurari masu hasken gaske sun haske min idona tare da tafiya da jina da ganina lokaci guda, Dafe kuncina na yi ina ƙoƙarin buɗe idona na ji ya ce"Ni za ki kunyata a gaban abokai in kyaleki tare da yi miki uziri akan yarinta ke damunki sannan ki kwashi sirrina ki kai kafar sada zumunta na Facebook?" Giyar wake kika sha ko ta burkutu da za ki maida rayuwar mu topic of discussion na wannan week ɗin? Nayin Mashkur(yau ba HABIBI ba Kwamared)ka kasheni. Saukar belt na fara ji a jikina amma saboda kafiya da naci irin nawa ko gezau ban yi ba sai faɗi yake yana maimaitawa"Ko ban kasheki ba tabbas zan koya miki darasin da duk wacce ta ji labari makamancin naki ba zata yi yunƙurin maimaitawa ba,dan in ma bata fara biye ma Ramadan time-table na social media kar ta soma tunanin farawa." Duka yake shauɗo min a haukace Ni kuma ina danno mi shi ashar ganin yana shirin sauya min kamani ya sa na riƙe belt ɗin tare da rantawa ana kare,ban dire ko'ina ba sai ɗakina na danna key, Biyoni ya yi a fusace ya ce"ashe ke a marasa kunyar ƙarama ce ai da kin barni ki ga in ban kashekin ba doluwa kawai wacce bata iya riƙe sirrin gidanta ba,zan ga kuma wanda ya isa ya sa ni in canza ƙudirina na tuwon dawa da koriyar miya a social media tunda ke har kin rasa mafaɗi." Eh na rasan kuma ka rabu da Ni tare da dawo min da kayan garata azzalumi macuci kawai,ashe da man haka ka ke bansani ba"na furta hakan duk da raɗaɗin da jikina yake min na dukan da na sha, Ba zan rabu da ke ba har abada,Gara kuma tawa ce dan lefen da na yi muku na al'ada shiyasa aka biyoki da kayan waɗannan ƙananan kuɗin dan haka na ci halas,ki kuma kai ƙarata duk in da kike tunanin zaki kai ko da kuwa Kotun jemage ne"yana gama faɗin haka ya shige ɗakin shi yana haki tsabar ɓacin rai ya barni da dudduba jikina ganin yanda duk ya yi ruɗu-rudu wayata na janyo tare da danna ma Ammina ƙira,bugu ɗaya ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama sai dai jin na fashe mata da kuka yasa ta ce"My Farrah what is wrong with You." "Mashkur Ammi zai kasheni ya.............."ai bata bari na ƙarashe zancen ba ta katse kiran nan take ta fara ƙwalama ƴar aikinta kira domin ta ɗakko mata mayafi, Gudu-gudu sauri-sauri haka take tafiya har ta baro cikin layinmu ta shigo layin su HABIBI in da nan ta yi kiciɓis da Abbiy ya dawo daga masallaci, "Lafiya Ammin Farrah?."ya tambayeta a kiɗime dan har ga Allah ya tsorata da ganin yanayinta, Ina fa lafiya Mashkur na can yana shirin kashe min........." Katseta ya yi bar barta ta ƙarasa ba ya ce"Kuma shine za ki je ku daku da sirikin naki?"ta mi shi shiru ganin yanda take cika take tumbatsa ya ce"To shige muje gida in har na isa dake." Mugun kallo ta jefe shi da shi ta ce"Gaskiya Alhaji sai dai ka yi hakuri ba zan iya ƙyale ɗiyata a cikin irin halin dana jita ba"dan haka ta wuce shi fuuuu jikinta har wani mazari yake yi, Sumar tsaye ya yi yana mamakin iyayen yanzu da suka maida bayyana soyayyar ƴaƴa a wannan zamani tare da yanda wasu matan suka raina mazajensu musamman idan sun ga mazajen ba su kai su ƙarfi ba dan Mahaifiyata babban likita ce dan haka ita ke jan ragamar duk wata ɗawainiya ta mu data raina wanda mahaifinmu ke ba mu duk da mutum ne mai zuciya malamin jami'a ne kuma yana iya ƙoƙarin shi wajen ganin ya hidimta mana amma bata gani. Shiru ya yi na wasu ƴan mintoci kafin ya tsaida shawarar abinda ya ke ganin ya kamata ya yi dan haka ya zaro waya daga cikin aljihun shi. HAKEEMA. Hakeema wacce tun bayan gama chat ɗin su da Farrah take tsimayen ganin mijinta ya dawo shiru har aka soma ƙiraye-ƙirayen Sallan magrib,Iya wacce ke daf da ɗakinta ne ta leƙo ta ce"Ke kowa yau lafiya baki fito ba yarinya?" "Kaina ke ciwo."ta furta hakan a taƙaice dan tun zuwanta gidan ta karanci halin duka halayyar matan gidan na son tsegumi da shiga abinda ba ruwansu,ga kuma kwaɗayin tsiya su dai burinsu ta girka ta basu kamar wasu mayunwata, Kasancewar tunda gas ɗin ta ya ƙare Lukman bai siyo mata wani ba yasa take aiki a ƙofar ɗakinta a gawayi sai dai in akwai wuta ta yi a electric cooker,kuma matuƙar ta girka a waje to zata zuba ma kowa zuwa anjima kaɗan kuwa in sha Allahu duk wanda ya girka zai sa mata idan taƙi karɓa Lukman ya yita faɗa wai hana alhairi ne dan dole take amsa yana lashewa, ganin ta yi zurfi cikin tunani ya sa iyan ta ce"ku ci me kenan to?" Zai shigo da shi"ta bata amsa ranta a ɓace ganin hakan yasa ta juya cikin sigar munafukan asali ta ce"Oho ki ce yau amarcin ne ya tashi,kaji da burodi da ƙwai zai siyo muku a sokaway(Take-away)." Shiru ta yi mata tare da raɓawa gefenta ta isa gaban fanfo ta fara alwalla tana yi zuciyarta na mata suya tare da nadamar auren Uztaz Lukman da tayi tun ba'aje ko'ina ba. To fah Fans ga fa uwar DIYAN HABIBI ta je tare ma ƴarta faɗa ko ya zata ƙarke ku biyoni a sannu. Share Like Comments Fisabilillahi. Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. *Daga cikin Sunnonin da aka shar’anta ga Azumi.* *Shine cin abincin Sahur da kuma jinkirta shi saboda taimakawa mai Azumi don kar ya sha wuya.* LAMBA NA SHIDA. Zuciyarta na mata suya tare da nadamar auren Uztaz Lukman da tayi tun ba'aje ko'ina ba. Tabbas duk wanda ya ƙi jin bari ba zai ƙi gani ba da ace ta yi amfani da nasihar da Mahaifinta ke mata na zaɓen miji na gari bata biye ma banbancin ra'ayi da aƙida ba da bata dawo tana danasani ba dan ya sha faɗa ce War"Ɗiyata Hakeema na tabbatar da ke mai ilimi ce da riƙo da addini nasani amma yanda ki ke fifita aƙida fiye da komai abin yana bani tsoro." Murmushi na ke yi mai sanyi sannan in kalli fuskar kyakykyawan farin dattijo(Mahaifina)in ce"Abba kenan,babban burina a duniya shi ne auren miji mai tarin ilimi,mai ruƙo da sunnar ma'aiki sam bana son ɗan bidi'a a zuciyata wallahi dalilin hakan ya sa ka ga sam bana kula kowa sai uztazan da muke haɗuwa da su a islamiyya ko wajen tarukanmu na addini,shigarsu,ɗabi'unsu kaɗai na ke buƙata domin raya sunnar ma'aiki." Murmushi irin ta su ta manya yake min sannan ya ce"Allah ta'ala ya baki nagari,Ni dai abinda nake son nutsar da ke shi ne duk wanda ya furta kalmar shahada musulmi ne a gurin Allah kuma Annabi ya faɗa mana musulmi ɗan'uwan musulmi ne dan haka nake son duk wanda kika ga ya karkace ki bi shi da addu'ar shiriya,ba wayonki ko dabarar ki ba ce ta sanya ki ka zama kamila mace mai ruƙo da addini, sannan a zaɓen mijin aure Annabi ya umurce mu da yi muku zaɓi amma saboda hani da ya yi da auren dole ya sa muka damƙa muku ragamar zaɓar mijin aure,idan kin zaɓo mai addini da tarin ilimi ki duba halayya dan da halin shi zaku zauna kin ji ɗiyar albarka." "In sha Allah Abba." "Allah ya muku albarka." Sai in amsa da "Amin." sai dai a inda ya min wannan nasihar a gurin nake bari Ni dai babban burina in auri Uztaz mai gemo,ya goyo Ni a bayan mashin ɗinsa tsuntsun soyayya mu je islamiyya da taron addini aikuwa na samu Uztaz lukman in da Allah ya haɗa ni da shi a wata musabaƙa da muka yi na zama ta ɗaya a jaharmu,nan muka fara shimfiɗa nagartacciyar soyayya ya shigo gida na gabatar da shi ma Abbana,ko da aka yi bincike ba'a same shi da wani mugun hali ba kuma babban Malami ne a wata makarantar islamiyya dan haka yana karɓar salaryn dubu ishirin,zaunar da Ni Mahaifina ya yi ya gwada min muhimmancin sana'a a rayuwar aure ko da na sami Uztaz lukman da zancen sai ya ce min ai yana tsare wani shagon litattafai a kasuwa a na bashi albashi ashe duk  kanzon kurege Ni dan Daga yin auranmu na tabbatar da dubu ishirin din albashinsa kaɗai ya dogara kuma ko kafin watan ya ƙare mashin ɗin mu(tsuntsun soyayya)ya cinye rabin kuɗin, Haka aka ɗaura aurenmu zuciyar mahaifina sam bai natsu da shi ba amma ganin na kafe ina ganin Lukman shi ne zai bani farinci tare da shimfiɗa nagartacciyar zuriya a ban ƙasa yasa ya haƙura ashe ba anan gizo ke saƙar ba zan fuskanci rayuwar yunwa tun auren bai yi nisa ba, Da wannan tunanin na miƙe na gabatar da Sallah a daddafe saboda jirin da nake gani na kwanta samɓal a wajen ina ambaton Allah. Sai bayan ishsha Uztaz Lukman ya shigo gidan da basket a hannunsa,sai dai yana hango yanda na zama ya fara muzurai dan shi har ga Allah ya ɗauka matan gidan da muke haya sun sammana abincin da suka sa a  bani idan na basu bai san duniya na tafiya akan karin maganar"Yi in yi maka"ba ne yanzu, Duk a tanajin shi sahoor zai yi da abincin DIYAN HABIBI dan haka ya ɓata rai,Ni kuwa da murna na na tarbe shi sannu da zuwa ɗauke a bakina, Ciki-ciki ya amsa min sannan ya ce"Da fatan kin sha ruwa lafiya?" "Alhamdulillah amma ban ci komai ba bayan ruwa." Wani irin mugun kallo..........    (Assalamu alaikum, wannan labarin na Hakeema jan hankali ne ga ƴanmata masu zurfafawa a kan aƙida ban yi shi dan cin fuskar wani ko wata ba,hasalima abinda idona ne ya gani na rubuta saboda haka idan ya yi daidai da rayuwar ki ko na wani ku min afuwa,A kowace aƙida da muke da su a addinin musulunci akwai nagari akwai na banza shi ne abinda nake son yin jan hankali a kai tare da nuna muhimmancin sana'a a cikin rayuwar aure Na gode.) HABIBI. Kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye sabo da ran shi in ya yi dubu ya ɓaci,sai maimaita Headline ɗin da yaga abokanan shi wanda suka yi fushi akan gayyato su buɗa baki da ya yi yake yi"MUN GA GIRKI GANIN IDON MU GURIN AMARYAR HABIBI."   A akwatin gurin aje bayanai(Comments)kuma shaguɓe ne kala-kala ake yi ana tagging ɗin sa,ayayin da kuma posting ɗin Farrah ya karaɗe sosai media sai Yaga sun sa daga gani wannan hukuncin Kwamared ne ga Amaryarsa,nan take ya ji fushin shi na ƙara hauhawa tabbas ya ɗebo ruwan dafa kan sa ji ya yi zuciyarsa na zafi ga zagin da Farrah ta dinga aiko masa yana masa amsa kuwwa a cikin kunnen shi,jin kan shi na niyyar tarwatsewa yasa ya fara ambaton Allah sai dai tun kafin nutsuwa ya game da jikin shi yaji muryan sirikar shi tana ƙwala mi shi kira tamkar maƙoshinta zai fita MASHAKURU! Ya yi saurin dafe kunnuwan shi tare da afkawa a cikin dogon tunani wato hukuncin da ya yanke akan Farrah shi ne har ta ƙira mara mutuncin mahaifiyarta gidan shi har ta mance ɗauki ba daɗin da aka yi tsakanin shi da ita kafin auren su dan ita sam bata so auren ba ta so Farrah ta auri mai dukiya ne ba Kwamared kamar shi ba wanda da ke riƙe da kwali ba fus tunda  ingantaccen aiki ya gagara, Wani ƙara ƙiran sunan na shi ta yi a hassale ta ce"Mashakuru ka fito dan na san kana jina,Ka fito in rama ma ɗiyata dukan da kamata mugu azzalumi kawai,ina dalili ina mafari daga baka yarinya ka mata wannan mummunan aikin,wannan ai rashin sanin haƙƙin mace ne dan haka ka fito ka bata takardan sakinta ko kuma mu dangana lamarin da police station, kai wallahi idan ya gagara ma har Human right sai na kaika dan Ni na san mutuncin ƴata." "Yo banda sanin darajar mace ta ya ya gandamemen kamar ka zaka zage ƙwanji ka zane min ɗiya kamar wata dabba........"bai kai ga jin ƙarashen zancen ta ba ya fara Kokawada zuciyar shi akan ya fito ko kar ya fito sai dai ɗayan ɓarin zuciyar tafi ƙarfi a kansa na ya fita ayi duk wacce ma za'ayi dan haka ya nufi bakin ƙofar ɗakin wanda Farrah ke bubbugata kamar zata karyata, Wayar shi ce ta yi ƙara dan haka ya juya ya ɗakko shi ganin mai ƙiran yasa ya ɗaga da gaggawa a hanzarce ya ce"Abbiy ka zo ka fitar Ammin Farrah daga gidana dan Allah." Da "To"ya amsa nan take ya ci burki ya yi baya ya dumfari gidan sirikin na shi da matuƙar sauri, Ihun Farrah da masifar Amminta kaɗai yake jiyowa tun daga ƙofar get ɗin gidan,dan haka jikin shi na rawa har baya ganin gaban shi ya afka cikin falon kamar zai kifu, tamkar mahaukaci haka ya isa gurin Ammin Farrah ya janyo ta tare da sauke mata yatsu biyar akan ƙonanniyar fuskarta da man bilicin duk ya gama siɗewa,A firgice Farrah ta dakata daga bugun ƙofar da take yi falon ya yi tsit tamkar ruwa ya cinye ma'abota cikin shi, Jin shirun yasa Mashkur (HABIBI)ya buɗe ƙofan ɗakin jikin shi duk a sanyaye dan tabbas ya ji ƙarar marin da sirikin shi ya sauke ma matar shi wacce takaici, mamaki da ta'ajjubin marinta da mijin da ta raina yasa tayi mutuwar tsaye sai dai ganin shigowar Mashkur ya sa...... Tabbas na ga ruwan comments da madaran ƙauna gareku masoya wannan littafin,ina roƙon mai kowa mai komai ya sa littafin ya amfanar da ni daku gaba-daya,ya sa Amaren FIRST RAMADAN WITH HABIBI su ɗau darasi,wacce bata yi haukar da farrah ta yi ba dan Allah kar ta jaraba irin kalan girke-girken banza da wofin nan ta yi na masu hankali, wacce kuma ta yi oga ya yaba sai ta ƙara ɗamara, dangane da illar zaɓen mace ko miji nagari kuma ga shi duk muna gani a cikin wannan littafi Mai albarka. Mu je zuwa shin Ammin Farrah shaƙe HABIBI za ta yi? Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. Manzon *Allah* (SAW) yana cewa: (تسحروا فان في السحور بركة) *“Lallai ku yi sahur saboda acikin yin sahur akwai albarka”.* [Bukhari]. LAMBA NA BAKWAI. HAKEEMA. Wani irin mugun kallo Uztazuna ya bini da shi sai dai ganin yanda na langwaɓar da wuya ya sa yaji wani tausayina ya kama shi amma sai ya dake ya ce"Ittaƙillaha ya Uztaziyya ko dai dan kin ganni da Gara." Ji na yi raina ya ɓaci amma sai na danne cikin muryan shagwaɓa na ce"To mai ka bar min da zan ci Fisabilillahi ya Uztaz ummm, har kana wani in ji tsoron Allah." Dage kafaɗa ya yi cikin nuna halin ko in kula ya ce"Allah dai ya so ba gidana ne kaɗai ake rasa abincin ci ba har gidan Annabi an sha yin kwana da kwanaki ba'a ɗaura sanwa ba haka ma gidan Sahabbai na san baki manta da ayar da ta sauka akan Imam Ali Bin Abi Thalib ba da matar shi." "Ban mance ba tabbas amma misalin da ka kawo na gidan ma'aiki ba sam ba haka abin yake ba,Annabin rahama mai neman na kan sa ne kuma  ayar Haƙuri da jarawabawa take nunawa wanda hatta a gidan ma'aiki an rasa abin ci amma ba dan bai je nemowa ba,na gidan Imam Ali kuwa ayar koyar da sadaukarwa da falalar ciyar da miskinai take  amma kai naka ya banbanta dan baka fita ka nema ba ma balle ka ce ka rasa kai dai kawai ka kama sana'a ya  Uztaz."ina dire maganata ban ko kalli gefen da yake ba na raɓa ta kusa da shi na shige na ɗakko faranti da cokali na duƙa na fara zuba abincin da ke cikin basket ɗin,shaƙe farantin na yi taf tare da sa Coslow ɗin a gefe kafin na buɗe kular source ɗin,anan ya yi wani irin tsalle sai ga shi a gabana ya dafe kulan,abin dariya ya so bani amma takaicin shi ya hanani darawar, "Kawo in sa miki da kaina." sake mi shi kular na yi yasa min yankan nama ɗaya  tare da tarfo min source ɗin akai,miƙo min filet ɗin ya yi yana janyo min hadisin raba ciki gida uku dan shi a haukar shi na yi zari(sam bai tunano yanda ya je ya take nashi cikin ba hadda riƙo extra.) Gyara zama na yi ina cin abincin ina tuno makomar rayuwata sai dai samun matsaya akan wata shawara da zuciyata ta bani yasa na ji na gamsu dan haka murmushi ya suɓuce min, Cin abinci nake yi ina murmushi, Uztazuna kuwa sai suɗe kwanon da ya zuba source ɗin nan yake yana zare ido,jin yanda ƙamshin miyar duk ta cika masa ciki ya sa ya miƙa hannu domin ɗakko kula,nan take wata farar takarda ta faɗo ƙasa ya yi saurin buɗeta ya ga an ya fara karantata. "Matar Uztazu Barka da shan ruwa,ga ɗaya daga cikin girkin ƴan group ɗin first Ramadan with HABIBI nan ki ci ki ji,santi sosai mijinki yake yi hadda yin Take-away,to ya ci albarkacin ki na zubo dan ki ci,muma sai mun zo cin girkin matar Uztazu."    Farrah Diyan Habibi. Gumi ne ya ji yana tsatstsafo mi shi tsabar ruɗewa,karatun yake a cikin zuciyar shi amma ya fito fili dan haka ina kammala cin nawa abincin na ce"ka ji dai saƙon Farrah ko ashe ma abincin nawa ne har ka ke min rowa." Kame-kame ya fara na sa ɗan yatsana akan bakina alamun ya yi shiru cikin murya mai sanyi na ce"Kayan Allah ai na Annabi ne Noor fatana dai zaka koma shagon da kake tsare musu littafan nan dan kar abinda zamu ci ya dinga gagarar mu dan Allah." Tsam ya tashi ya shige ɗaki Ni kuwa na buɗe data na hau online dan fara gabatar da shirina. GIDAN HABIBI. Mamaki da ta'ajjubin marinta da mijin da ta raina yasa tayi mutuwar tsaye sai dai ganin shigowar Mashkur ya fito yasa ta ji ta wartsake,amma hango yanda ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya sa ta ji ya mata kwarjini dan haka ta juyo bangaren mijina ya ce"Ka mareni a kan gaskiyata?" Shiru ya mata tare da jan hannun Farrah dana Mashkur ya ja su zuwa cikin falon,yana isa tsakiyar falon ya sake hannun na su tare da yi musu nuni da hannu akan su zauna, Ba musu suka zauna akan maidaidaicin carpet ɗin da ke shimfiɗe a tsakiyar falon sai dai sun bama juna matuƙar tazara saboda haushin juna da suke ji, Me ya faru tsakaninki da mijinki Farrah har kika yi ƙiran mahaifiyarki?" Dukan tsiya ya lakaɗa ma........." Dakata Malama sunan ki ne Farrah"ce War Abbiy wanda ya yi saurin dakatar da Ammi wanda ta karaso cikin falon tana cika tana batsewa, Tsit ta yi saboda ganin yanayin shi, Ina jinki Farrah."kuka ta fashe da shi sannan ta fara shiryo ƙarya da gaskiya ta faɗa ma Mahaifinnata, Mamanta sai gyada kai take tana ce wa"Ka ji baƙin zaluncin na shi ko"sai ta yi kwafa tana jin kamar ta tashi ta shaƙo wuyar shi ya mutu kowa ma ya huta dan takaici, Uffan Mashkur bai ce ma har sai da Abbiy ya jeho masa tambaya da ce wa"Haka aka yi Mashkur?"bayan Farrah ta gama shimfiɗo zancenta kenan, "A'a Abbiy kai shaida ne akan abinda ta aikata min a ranar farko na watan Ramadan idonka ya ga komai kuma ka ji hukuncin da na ce zan ɗauka." Cike da gamsuwa ya ce"Eh hakane tabbas." To ban ɗau hukuncin ba gata nan ka tambayeta sai........nan HABIBI ya feɗe biri har wutsiyar shi,ya faɗi sanadiyyar da yasa ya duketa Abbiy banda faɗin"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"da yake yi yana maimaitawa ba abin da yake ce wa, Jin Mashkur ya yi shiru alamun ya gama yasa ya ce"Tabbas ka yi hakuri ma da baka turo min ita gida ba duk kalar rashin tarbiyyar nan da ta nuna maka ka yi hakuri dan Allah,ina baka haƙuri a matsayina na mahaifinta da matsayina na uba a gareka ka yi hakuri ka ji." Na yi Abbiy nima a yi haƙuri da ni ga hukuncin da na yanke a kanta duk a cikin fushi ne sharrin shaiɗan ne, Ba wani sharrin shaidan Malam dan kaine babban shaiɗanin,shaiɗanu ai a ɗaure suke tunda muka shigo cikin watan Ramadana, kawai dai ka yi abinda kake so ka zalunci yarinyata,so what dan ta kai magananka social media an tattauna matsalar ku baka gode ba ma kun zama cele,ko ka san shekaru nawa Farrah ta ɗauka tana cin burin ganin ta nuna bajintar ta ga mijinta a cikin watan Ramadan? Ita ce ta fara buɗe group a Whatsapp na FIRST RAMADAN WITH HABIBI tana kawo ma classic ladies zafafan girke-girke na gida dana ƙetare kawai dan ta gwada akan mijinta shikenan an samu mishkila shine zaka tasa min ita a gaba ka duka kamar ka samu jaka? To ahir ɗin ka This should be the last warning da zan maka akan taɓa lafiyar ɗiyata in ka ki ji wallahi hukuma ce zata rabani da kai." Kin ji kunya, matuƙar kunya A'isha(Ammin Farrah)saboda matuƙar haka za ki ci gaba da yi ma yaƴanki mata to tabbas baki so zaman su a gidan miji ba kuma a irin al'ada irin tamu ta bahaushe zaki bar musu abin gori ƴaƴa da jikoki,tir da irin wannan halayyar naki ta rashin kara da sanin ya kamata ke ga ƴar boko mai kokawa da ilimin addini, So what dan ka ce haka"Ni dai na faɗa maka aure ne kuma tsakanin Farrah da Mashkur ya ƙare dukan da ya mata ya daki auren shi Billahi dan haka tashi mu je." Ba tare da tunanin komai ba Farrah ta ce"Ina son mijina Ammi."jin haka ya sa ta fara masifa kamar zata ari baki ganin ba wanda ya kulata ya sa ta fice tana bin Farrah da mugun kallo. "Allah ya miki albarka" shi ne kalmar da ta fito daga bakin Abbiy,HABIBI ma wani sassanyar kallo ya bini da shi wanda duk ɓacin ran da yake ciki ya ji ya wanku Ni kuwa na ce tsakanin mata da miji ai da man sai Allah, Nasiha mai ratsa jiki ne Abbiy ya fara yi min kafin ya dawo kan HABIBI ya mi shi tashi nan take aka rufe taron da addu'a sai dai Abbiy na wucewa na shige ɗaki a guje na rufe tare da cin alwashin sai na gasa ma HABIBI aya a hannu matuƙar ina raye,bai daki banza ba. To fah Fans kun ji wata sabuwa fa a ɗaukata mutuniyar taku ta yi hankali. Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. *Kuskuren Musulmi Game da Azumi*   *Shi ne yin buɗa baki da abin da Allah ya haramta kamar abin da ke sa maye, wiwi, hodar iblis, sigari, ko kuma shi sha, da sauran su.* LAMBA NA TAKWAS. Nasiha mai ratsa jiki ne Abbiy ya fara yi min kafin ya dawo kan HABIBI ya mi shi tashi nan take aka rufe taron da addu'a sai dai Abbiy na wucewa na shige ɗaki a guje na rufe tare da cin alwashin sai na gasa ma HABIBI aya a hannu matuƙar ina raye,bai daki banza ba. Wayata na ɗaga na dinga jera ma Ammina ƙira amma sam bata ɗaga ba sanin na yi matuƙar ɓata mata rai tare da kunyata ta a idon su Abbiy da HABIBI ya sa na rubuta mata text message kamar haka"Ba umurninki naƙi bi ba ya Ammi face son in koyar da Mashkur darasin da bai taɓa riska ba a rayuwar shi,mace mai aji bata yaji haka kika sha faɗa min a kullu-yaumin, ƙasaitacciyar mace ita ce mai zama cikin gidanta har sai ta hora mijinta akan laifin da ya mata,tabbas Mashkur zai fuskanci hukuncin da ya fi dukan da ya mini da wanda Abbiy ya maki a kan shi,na rantse da Ubangiji sai na gwada ma shi nononki na tsotsa,Sai na gasa ma shi gyaɗa a hannu tabbas sai ya gwammace kiɗa da karatu trust me ny First love." Tura saƙon na yi ina addu'ar Allah ya sa ta buɗe ta karanta aikuwa yana shiga ta duba,wani murmushin kashe Boss ta yi cikin zuciyarta ta ce"Tabbas ƴar halak na haifa" Dan haka ta ji kaso cassa'in na ɓacin ran da take ciki ya tafi dan ta san Farrah will make it,she will make sure ta mi shi discipline ɗin da sai ya gwammace kiɗa da karatu dan haka ta tuɓe kayanta ta shige cikin bayi ranta fess dan ta san wacece Farrah. HABIBI kuwa ji ya yi ƙafafun shi sun yi sanyi da buga ƙofar da DIYAN SHi ta yi dan da lalurar buƙatar matar shi ya yini ɓacin ran da ta sanya shi a ciki ya sa ya mance da damuwar shi ma, sai dai yaji wani irin soyayyarta ya mamaye jiki da ruhinshi yayinda ta ƙi bin umurnin da mahaifiyarta ta bata,ya ji ta cancanci yafiya dangane da duk wani laifi da ta aikata a gareshi,ya fahimci tarbiyyar mahaifiyarta ne a haka,ita ke ɗaurata a kan keken ɓera na koyi da rayuwar yahudawa tunda ya ga har alfahari take da yanda Diyah ta iya handling case ɗin ta ba sai da ta kai mata ƙara ba,aiki ne tuƙuru a gareshi na koyar da Diyah yanda zasu rayu cikin aure bisa ga turban addinin musulunci ya shimfiɗa dan haka kai tsaye ya koma ɗakin shi ya yi wanka tare da sa farin singelet da sabon boxer,sabuwar jallabiyya mai ruwan zuma ya ɗauro tare da zura shi a jiki a murɗaɗɗen surar shi,ya fesa turaren shi mai sanyin ƙamshi na Black oud,spare key ya ɗauka tare da dosar ƙofar ɗakin da Diyan shi take,a daidai wannan lokacin na fito daga wanka jikina duk ya yi tsami saboda bugun da nasha, sosai na gaggasa jikina tare da zura rigar bacci na ɗale kan gado ina jin zazzaɓi na niyyar kamani,ko minti biyar ban 0 yi da kwanciya ba na ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar da nake ciki tare da tattaɓa shi,wani munafikin murmushi ne ya suɓuce min dan na san na bar key a jikin ƙofar so duk ƙoƙarin HABIBI na son ya buɗe ƙofar sam  keyn ba zai shiga ba tunda da wani a ciki dan haka ya fara ƙwala min kira cikin murya mai sanyi, Jin shiru ban amsa ba yasa ya ɗauka ko bacci na yi dan haka ya fara bubbuga ƙofar yanda na ke tunanin zai ji amma sai yaji ɗiff,shiru ba ko alamun mai rai na kwance a ƙarƙashin rufin ɗakin,ji ya yi ya fara gajiya dan a bukace yake da DIYANSA dan haka cikin sauri ya hau bubbuga ƙofar irin bugun haukar nan,ban san lokacin da wani munafikin murmushi ya suɓuce min ba dan haka cikin farin ciki na sakko da ƙafafuwana ƙasa dan tsabar farinciki ji na yi zazzaɓin ma ya sauka na nufi bakin ƙofar cikin azama, Cikin kasalalliyar murya da sigar janyo hankalin shi gareni na ce"HA....BI....BI....." "Na'am, Please open the door Diya,i need youuuuu"ya ƙara sa maganan yana jan kalmar ƙarshen cikin sigar da ke nuna a buƙace ya ke dani, Dariyar shaƙiyanci na fashe da shi yanda nake da tabbacin zai jini ka fin na ce"Bakaji mai Ammi ta ce bane HABIBI?." "A'ahhhh Diya dan Allah kar ki hukunta ni ta wannan fuskar zaki janyo ma kan ki fushin Allah dana Mala'iku." Bravo!Kwamared Habibi,tabbas ka yi kyan kai daka gane hakan kai kuma dukan da kayi min kana tunanin lada Angels ɗin suka rubuta maka ne?, wannan shine ladan dukan da kayi min ai baka daki banza ba Billah." Ji ya yi kamar ya fashe da kuka sai dai ya daure ya ce"Ok ki dafa kayanki ki ci Farrah,ba dai Ni zaki wulaƙanta a cikin wannan wata mai alfarma ba? Na ba banza ajiyarsa dan haka na jingina da jikin ƙofar ɗakin yanda har ina iya juyo nishin wahalar da yake fesar wa amma ko a jikina dan yanda bai tausaya min a matsayina na mace ba ya dukeni she deserved such punishment daga gareni, Zufa ce ya gama wanke mi shi jiki har yana ɗiga muryan shi yana kyarma ya ce"da man soyayyar da kika ce kina min ashe ta ƙarya ce to zan fita kuma duk in da naje na kai kaina ke kika janyo."Dan haka cikin azama na ji takun shi yana ciccira ya fita, Komawa kan gadona na yi na lulluɓa farinciki kwance a fuskata, sai jin tashin motarsa na yi daga harabar cikin gidan ya sa na ji wani irin tashin hankali ya ziyarce ni,zumbur na miƙe jin wani irin tashin hankali ya ziyarce ni lokaci guda nan da nan na fara kaikawo tsakanin gaban gado da ƙofar ɗakin,tunanin gurin da zai je na fara yi tsabar tashin hankalin da na shiga, Zuciya da saka kuwa ta raɗamin gurin ƴan good evening(Ƙaruwai)domin su biya mi shi buƙatar shi. HAKEEMA. Tsam ya tashi ya shige ɗaki Ni kuwa na buɗe data na hau online dan fara gabatar da shirina. Group ɗin mu na FIRST RAMADAN WITH HABIBI na shiga,group ɗin da na san ya tara classic ladies masu ji da kan su na fara tallata hajata ta ɗinki,tela ce ni ta mata kuma babu wani ɗinki da za'a kawo min wanda zai iya gagarata dan haka na kwaso zafafan style daga instgram na watso shi cikin group,nan take suka ruɗe dan duk yawancin su ƴaƴan manya ne kuma mata ne masu son kece raini sam basa son aga gazawar su dan haka suka fara selecting kowacce burinta ta zaɓi daidai da kalar jikinta wanda zai fiddata,duk da ba wani faɗa aji nake da shi a group ɗin ba amma tallata musu hajata da na yi akan su kawo ɗinkin Sallah zan musu kuma duk wacce na ɓata ma kaya zan biyata tabbacin su san na san kai aikina sai duka hankalinsu ya dawo kaina take yanke na samu kostoma guda 2 suka karɓi address ɗina akan za su kawo min ɗinki in fara gwada wa a kan su kafin sauran su kawo na sallarsu, Da man inada keken ɗinkina wanda Abba ya siya min kuma tun ina budurwa sana'ata kenan har ma inada yara yan koyon aiki,dalilin da yasa ƴan First Ramadan with HABIBI ba su Sanni da shi ba shine bayan gama candyn mu na ƙware har na fara yin na kuɗi,su kuma tun a Sakandire muka rabu suka cigaba da karatu tunda ƴaƴan masu ƙumba da susa ne Ni ce kaɗai ƴar gidan malam Shehu, Samun waɗannan kostoma ya faranta raina matuƙa gaya kuma shawarar da zuciyata ta bani tabbas ta min aiki dan haka na fita  a group su kuwa suka ci gaba da tattauna zancen girke-girken da za su yi gobe dan su nan suka fi auki tare da bada labarin yanda mijin ke ɗoki wanda yawancin su ƙarya ne kawai suke sharara ma junansu dan a cikin su akwai wacce ko tukunya bata iya ɗaurawa ba ƴar aikinta ne ke mata komai,Ni kuwa status na koma na yi posting tare da tura ma duk group ɗin da nake ciki a Whatsapp sannan na koma Facebook na sa hotunan ɗinki tare da nuna sana'ata ma duniya cike da alfahari,nasa sunan gari da sunana,numban waya ce kawai na ɓoye gudun janyo ma kaina matsala. Sauka na yi farinciki ɗauke a fuskata dan haka na shiga cikin ɗaki gurin Uztazuna sai dai me samun shi na yi ya cika ya yi fam kamar gasashshiyar buredin da ya ƙone, Yana ganina ya ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa nan da nan na ji gwiywowina sun yi sanyi akan daddaɗan albishir da na zo mi shi da shi cikin sanyi na ce"Allah ya huci ran Maigidana na barka kai kaɗai ko?" Taɓe baki ya yi cikin son cusa min haushi ya ce......... To fah ta Uztazu ya dai lamarin naku ne yake tafiya a baibai ko dai da sa hannun ƴan group ɗin First Ramadan with HABIBI ne ba mu sani ba?dan na ga kafi kowa baƙin jini lolz. Ina masu goyon bayan HABIBI akan hukuncin da ya yanke i mean (Team HABIBI)Da masu goyon bayan Farrah (Team Farrah) su waye da nasara ne a wannan page ɗin? Mu je zuwa. Ummu-jidda ce. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. *Kuskuren Musulmi Game da Azumi.* Ƙirƙiro tafiya zuwa wani gari ba tare da wata buƙata ba ko wani dalili, kawai don an halartawa matafiya ajiye Azumi a halin tafiya, har ma ya kafa hujja cewa ai shi matafiyi ne, wannan kuma baya halatta. *Allah ya karɓi Ibadunmu* LAMBA NA TARA. Zuciya da saka kuwa ta raɗamin gurin ƴan good evening(Ƙaruwai)ya tafi domin su biya mi shi buƙatar shi tamkar mahaukaciya haka na dawo nan take na fara kokawa da ƙofa a niyyata in buɗe in fita amma tsabar kyarma da hannuna yake yi ƙofar taƙi buɗuwa sai jujjuya mabuɗin na ke yi tamkar ƙaramar yarinya, Can dai Allah ya bani ikon buɗe ƙofar ɗakin na fita a guje zuwa sashinshi,lalleƙa lungu da saƙon sassan na yi ban hangi ko ƙurar shi ba nan take na gasgata zancen da zuciyata ke yi na ya tafi zuwa ga biyan buƙatar shi a gurin wata mace ba Ni ba, Kuka na fashe da shi ina jin wani irin kishi na sukata a ƙarƙashin zuciyata,nan take na fice a cikin hayyacina dan da gaske ina son HABIBI da zuciya da gangan jiki kai har ma da ruhina kuma ba na jin baƙin kishi zai iya barina in zauna da kishiya ma balle wata a waje,danasi na fara mara amfani dan da na san wannan hukuncin dana yanke zai janyo min shiga wannan halin tabbas da ban ɗauki shawarar zuciyata ba,nan na shiga tufka da warwara idona kafe a kan agogon dake manne a jikin bangon ɗakin ina bin kowani sakan da kallo har zuwa minti,a tare da bugun zuciyata kowanni minti ke ƙaruwa har na shafe awa ɗaya ba amo ba labarin shi,sai kai komo nake yi tsakanin ɗakin, Tsabar ruɗun da nake ciki yasa ko tuna ana ƙira a waya ban yi ba sai dana jiyo sautin kira daga wayar shi dake yashe akan gado sannan na tunota, Private numba ne dan ba suna kuma an ɓoye numban hannuna na karkarwa na latsa koren da ke nuna alamun kira na manna wayar a kunnena, Muryan mace na ji cikin siririyar murya tana kiran Mashkur cikin sanyi,gashin jikina mimmiƙewa ya yi lokaci guda na ji zufa ta karyo min"Mashkur masu gari tunda ka yi aure ka gujeni,sai dai Ni zuciyata ta gagara mancewa da kai kuma har kwanan gobe ina sonka ina fatan shigowa ata biyu in ka bani dama." Leɓena rawa ya dinga yi na gagara ce wa uffan tsabar rudanin da nake ciki har ta gama zubarta kamar kanya ban yi ko tari ba jin tana ta "Hello,Hello."ya sa na tattaro dukkanin wani ƙarfi da ya rage min na ce"Sai dai ko a lahira idan ana aure ki aure shi amma ba a wannan duniyar da muke ciki ba sakarai shashasha kawai." Ƙit ta kashe wayar jin muryata ina kwararo mata na maguzawa,nan take na miƙe a fusace na fita zuwa falo ina dakon jiran Mashkur ya dawo,awa biyu ya ɗauka sannan ya shigo cikin gidan hannun shi ɗauke da kaya niƙi-niƙi,ko kallo ban isheshi ba ya wuce kai tsaye zuwa madafa ya dire su,ƙara dawowa ya yi ya giftani yana niyyar wucewa zuwa waje na yi karaf na cafke ƙafafuwan shi,cike da rauni na ce"Ba in da zaka ƙara fita  HABIBI har sai ka faɗa min gurin wa ce ƴar iskan ka je,sannan wata haihuwar haram ɗin ce ta kiraka a waya tana burin mallakar ka." Ci kanki bai ce mata ba hasalima fizge ƙafar shi ya yi ya fita yaje ya kwaso sauran kayayyakin da ke cikin Boot ɗin sa yaje ya kai su kicin ya dawo sai a sannan ya fuskance ni tare buɗe min hannayen shi biyu alamun in taho gare shi na bi shi da wani mugun kallo zuciyata na zugani akan haka kawai ya je ya gama harka da matan banza sannan ya zo ya taɓa Ni, Kamar ya san mai nake saƙawa a cikin zuciyata  ya ce"Bana son shaiɗan ya ci gaba da samun gurbin zama a zamantakewar mu Diyah ki yaƙi zuciyarki mu shimfiɗa nagartacciyar soyayya a gidan mu dan Allah." Maƙe kafada na yi alamun naƙi ɗin sanin shegen kafiyata ya min yawa yasa ya ƙaraso gareni tare da kama hannuna ya janyo ni har zuwa ɗakina ya kwantar da Ni kan gado tare da lulluɓa min bargo cikin raɗa ya ce min"Ki kwanta gobe za mu yi magana in sha Allah."har na yunƙura zan miƙe ya haɗa hannayen shi biyu alamun roƙo na koma na kwanta,fita ya yi ya je ya ɓallo min Paracetamol jin alamun zazzaɓi a jikina ya sa ya bani maganin dana rage raɗaɗi bacci ne ke fizgata bayan fitar shi sai dai zuciyata cike take da son jin ina Mashkur ya je bayan fitar shi sannan wata shaiɗaniyar ce jikan Mayu ke bibiyar min miji haka na yi baccin rabi-rabi tsabar ruɗun dana shiga ganin na gagara baccin yasa na hau online (Madadin tashi ta gabatar da nafilfilu,karatun Alkur'ani da addo'o'i.), sosai na shagala da duba saƙonni har na ji an fara ƙiran salla,dirowa na yi daga gadon a hankali na tafi kai tsaye zuwa banɗaki,fitowata ke da wuya na hango HABIBI tsaye ya goya hannayen shi biyu a baya yana jiran fitowata,fuskar shi a sake dan daga gani ya shirya sulhu da ni amma Ni ta bangarena sam ba sauƙi dan haka ko kallon in da yake ban yi ba na nufi closet na zaro jallabiyya na sa tare da ɗaura ɗankwalin a kaina,na zauna a bakin gado na cigaba da jujjuya wayata ina duba saƙonnina dan har yanzu zuciyata tafasa take, Ƙarasowa ya yi daf da ƙafata ya zauna,ya fara yi min tafiyar tsutsa a saman ƙafata har zuwa kan sharaɓata,da sauri na janye ƙafar tare da matsawa gefe cikin salon shi mai narkan da zuciya ya ce"Duk fa wayon amarya sai an sha manta yarinya." "Haka kuma duk soyayyarka da namiji sai ya ci amanar ka,kamar Ni HABIBI dan na maka laifi har ka ɗauki hannu ka dukeni hakan bai isheka ba ka kwashi ƙafa ka tafi gurin matan banza shaiɗanu haihuwar titi,ashe da man kana da su tunda ga wata la'ananniyar na kiranka har tana tambayar tunda ka yi aure shi......." Enough dear wallahi tallahi Ni ban je gurin kowace mace ba idan kin yarda,duka dai na ɗau laifina amma ke ma matsayinki na mace bai kamata in kin ga na yi fushi ba ki dinga ɗaga muryarki a saman tawa ba saboda kin fi kowa sanin halina bana iya controlling temper na,secondly bana son zagi dan Ni a gurina cin mutunci ne na yankar ƙauna and wace ce wacce kuka yi waya da ita? Oho maka daman can yawa ne ma da su HABIBI har da kake tambayata wacce daga ciki? "O'o Farrah rigima." ya furta hakan cikin wasa yana Kallona ƙasa-ƙasa yana dariya,dariyar ta shi kuwa ƙara tunzurani ya yi gani nake ya raina min wayo shiyasa ya ke faɗa min haka fuskar shi ɗauke da murmushi tsabar na kira mi shi sunan masoyiyar shi shiyasa yake annashuwa, "Inajinka na ce wacece ita?" Ban sani ba Diyah hasalima bi ban san ina waya da kowacce mace ba tunda muke waje dake balle yanzu da na kawo ki gidana shiyasa na ke tambayar ki." Shine kuwa ƙaryan da zaka min wanda ba zan taɓa yafewa ba Billah,kuma matuƙar baka faɗa min wacece ita ba da alaƙar dake tsakanin ku masifa da bala'i ba zai taɓa ƙarewa a tsakanin mu ba." Haka kika ce? Ta ɗaga mi shi kai cikin fushi ya ce"To yanzu aka fara wasan wallahi mu zuba Ni da ke mugani shege ka ka fasa." Fuuu haka ya fice zuciyar shi na tururi sai dai kuma ko mai ya tuna sai ya dawo tare da hangame ƙofar ɗakin cikin ɗaga murya ya ce"Ta shi muje ki tuƙa min tuwo da shi zan yi sahoor." "Billahillazi ba uban da ya isa ya sani aikin tuwo yanzu ai ba baiwa aka kawo maka na"Ce War Farrah wacce ke cika tana batsewa har wani karkaɗa ƙafa take tsabar fitina. To fah Fans masoyan Farrah wannan mutuniyar taku an ya ta san menene aure? Sorry For late update Fans, ayyuka sun riƙe Ni jiya da yau amma daga gobe na zama free in sha Allah,idan na ga ruwan comments zan biya bashin pages ɗin da kuke bina lolz. Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). TSARABAN RAMADAN. *Ka zamo mai soyayya don Allah kuma kada ka cutar da wanda yake sonka don Allah.* LAMBA NA GOMA. DIYAN HABIBI. "Billahillazi ba uban da ya isa ya sani aikin tuwo yanzu ai ba baiwa aka kawo maka ba"na faɗi hakan ina cika ina batsewa har wani karkaɗa ƙafa na ke yi tsabar fitinar da ke cikin zuciyata." "Wannan ne kuma baki isa ba Farrah sai dai in aurena ne kika gaji da shi." "Eh na gajin ka sakeni in huta." "Kin yi kaɗan wallahi dan aurena da ke ba saki ba yaji mutu ka raba takalmin kaza sai dai in auro wacce zata koya miki yi min biyayya sau da ƙafa wataƙil......"ai ban bari ya dasa aya ba na miƙe tare da hayyaƙo mi shi ba tare da ya saurareni ba ya shiga cikin ɗakin kai tsaye ya ɗauki wayata zai fice. Da sauri na yi kan shi zan rarume shi da  kokawa ya bini da kallon kar ki kuskura ki taɓa ni haka ina ji ina gani  ya wuce min da wayata wanda nake jin Kamar da raina ya tafi,mara mi shi baya na yi har ina haɗawa da gudu, Kai tsaye kicin ya nufa ya tafasa ruwan shayi ya juye a flask ya haɗa duk abinda ya san yana da buƙata a kan babban tray ya fice zuwa ɗakin shi jin yunwa na murɗa min ciki ya sa ban bi ta kan wayar ba dan haka na ƙarasa shiga cikin kicin ɗin domin dafa Noodles, nema na shiga yi na ga wayam,sam na mance da kayan abincinmu na side ɗin shi, dudduba cikin buhunhunan da ya shigo da su na yi nan na ga garin masara ne dana dawa,sai gero wanda ba'a surfa ba da suga sai da daddawa da kuka da kuɓewa busasshe. "Kuturun uban nan kayyasa lallai HABIBI bai shirya zaman aure da ni ba aradun Allah,ko ba azumi yaushe zan iya cin wannan abincin gidadawan?"sanin ba bai bani amsa yasa na fice Fuuu ina ƙwala mi shi kira. Ko tari bai yi ba duk uban kiran da na ke ƙwala mi shi kuwa har sai da na yi  tattaki na isa ɗakin shi na tsaya akan shi na ce"Wani salon wulaƙanci ne hakan da zaka ajiye min gingima gingiman buhu sai ka ce wacce ka auro daga karkara?" Shiru ya min ya cigaba da shan shayin shi cikin kwanciyar hankali sai tura bread yake yi yana haɗiya da ƙyar dan da abu mai laushi mai kama ciki ya so  ya yi sahur da shi tunda mun tashi tun ukun da shabiyar a ganin shi har zan iya girka mi shi naƙi, "Noodles zan ci HABIBI ina jin yunwa"na furta hakan cikin muryan sangarta,idan kun tunka ya ɓara, jin agogon dáke ɗakin shi ya buga alamun huɗu da rabi yasa na fara hawaye dan da gaske yunwa nake ji na fitar hankali dan rabona da sa wani abu mai nauyi a cikina tun jiya da magrib, Ganin ya miƙe yana shirin kabbara salla tamkar bai ganni ba yasa na ce"HABIBI fa magana na ke maka ka yi banza da ni dan wulaƙanci yanzu abinda zan ci a sahur  ma shirin hanani ka ke? Sam! Sai dai ke baki isa ki ƙi bin umurnina ba ne kiyi tunanin samun farinciki daga gareni wai Farrah mai kika ɗauki aure ne? "Rayuwar jindaɗi da samun cikakkiyar ƴancin yin duk abinda raina ke so." "Tabbas kin yi kuskure aure bautar Allah ce kuma a cikin kowani bautar Allah dole sai ka lanƙwasa zuciyarka domin samun rabauta,ni mijinki ne wanda ya zamto shugaba a gareki ya kuma zamto dole ki yi min biyayya ga duk abinda na umurce ki matuƙar ba saɓon Allah ba ne." "Matsalata da kai daga mun fara magana sai ka so nuna Ni ban san Allah ba to Ni dai ko meye ka bani abinci." Nuna min trayn da kayan da yayi sahur ya yi ya kabbara sallah nan na haɗa kakkauran shayi tare da juye rabin madara na zuba Milo tare da ɗiban biredi na fara  ci a yunwa ce,sosai naci sai da naji ya kai min karo sannan na ture bayan na yi wata irin gyatsa ina mai neman kwanciya akan lallausa carpet ɗin dake Malale a ɗakin shi dan ba shan wasa na ma tean ba, "Tashi ki ɗauro alwalla tare da kuskure baki mu yi nafila."ce war HABIBI wanda idar da sallar shi kenan, "A'a Ni bacci nake ji." "Ok to tashi ki zauna ba kyau daga mutum ya ci abinci ya kwanta dan yana kashe zuciya sannan kuma ya kamata ki san muhimmancin wannan watan dan haka nake son ki dage da ibada." "A'a fa gaskiya na gaji ka barni kawai laisal matsi wala takura a addini komai sai da niyya." Shiru ya yi kamar ba zai ɓara ba can dai ya ce"Kowani musulmi murna ya ke da shigan wannan wata domin ya nemi yafiya,shin ke bakya yi ma kanki wani tanadi ne domin samun gafarar Allah tare da roƙon alhairai ma rayuwarki ta duniya da ta lahira?" "Ya wuce tanajin da na yi maka shekara da shekaru ina koyon girki a zahiri da online saboda kawai in ɓarje gumina a First Ramadan ɗin da zamu yi shi tare?,ko shi ba ibadan bane?" "Wannan fannin shi daban amma mai muhimmanci ai shine raya wannan watan da ambaton Allah,zikiri,karatun Alkur'ani,yin Bacci da sunna ta tanadar ba mai sa shagala ba tare da saurare ko kallon malamai magabata domin samun kusanci da Allah." "To ai ka gode ma Allah ma da yanzu nake cika Farillan Ni fa kaga Sallan safe Allah ko a gidanmu sai na tumu na tumulmule nake tashi in yi, sallar ishsha kuwa ba kullum nake yi ba amma darajar wannan watan ka ga ina ƙoƙarin ramakon shi da asuba." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Farrah Sallar ki ke wasa da ita? "To meye kuma da jan wani dogon salati  dan na faɗa maka gaskiya daga duniyar fa sai Kaduna....... (Jan hankali gareku mata dangane da zage damtse cikin wannan wata mai alfarma da addu'a, yawancinmu hankalinmu ya fi karkata akan harkar girke-girke ba su damu da tsayuwar dare ba wata ma ko farillan bata cikawa,azumin kawai ake ba sallah,mu dage mu jajirce dan samu mu rabauta, Allah ya karɓi ibadunmu.) To fah Fans an ya wannan DIYAN TAKU TA JE ISLAMIYYA kuwa? ***** **** **** HAKEEMA. Uztazuna taɓe baki ya yi cikin son tura min haushi ya ce "Sai ka ce wani ɗan ki? Shanye ɓacin ran da yake shirin cusa min na yi nace"My Noor ala Noor sannan daddaɗan albishir na taho maka da shi wanda na tabbatar da in ka ji shi yau har goyani sai ka yi." "Kuɗi muka samu?"ya tambayeni a hanzarce har yana niyyar hantsilowa daga gado, "Eh,A'a" "Wace irin amsa ce haka Hakeema?" "Idan ka bada izini tare da yardanka za'a samu kuɗin da yardan Allah amma da sharaɗi ɗaya." "Tun kafin in jima  nina amince ai Annabi da kan shi ya ce mu nemi tsari da talauci,dan me shi talaucin zai mana kaka-gida ya hanamu morar amarcin mu yanda ya kamata." "Saboda mun ƙi tashi mu nema yanzu kuma na samu mafita ta hanyar amfani da wayata domin tallata irin sana'ar da nake yi har ma na samu kostomomi biyu gobe za su kawo min ɗinki." Tuni ya washe baki sai Murmushin farinciki yake kamoni ya yi ya zaunar akan cinyar shi ya ce"Ma sha Allah,barakallahu fiki." "Amin Uztazuna." "Da man kina da wannan hikimar kika bar mu a gantale haba Uztaziyya matar Uztazu mai halin matar Sahabbai." Dariya ce ta ƙwace min har ina tuntsirawa dan sai yau na yarda Uztazuna mayen son kuɗi ne to amma me yasa  baya son ya nema? "Son jiki da mutuwar zuciya"na ba kaina amsa ganin yanda ya biyoni ƙasan yana niyyar tumurmusheni yasa na ce"Sai dai wani hanzari ba gudu ba." "Eh ina jinki Hakimar zuciyata." Nan ma dariyar ya bani ganin naƙi tsagaitawa yasa ya haɗe fuska,da kyar na tsaida dariyar na ce"Wanda zai haɗa mana keken ɗinkin alhalin ko ficika Bama magani." "Ba zai gagara ba gobe da sassafe zan je in yi buga-buga in samu mai haɗa mana keken nan,tabbas kin kasance Furen zuciyata,Allah ya saka miki da alhairin sa shikenan wahala taƙare mana da yardan Allah." Take yanke na haɗa fuska na ce"Wahalar mu bata ƙare ba matuƙar ba zaka tashi ka nemi sana'a ba wallahi dan dubu 20 ba zai riƙe mu a wata ba ko ba tsuntsun soyyyarmu(Mashin)balle kuma akwai ta tana iya ƙoƙarinta wajen shanye man da kake shawagi da shi a gari." "Haaakimar zuciyata kenan"ya kawar da wannan zancen gefe dan baya son yawan ƙorafin da nake mi shi akan sana'a. "Ai Allah dai ya zambaɗa miki albarka, Allah kuma yasa ki fara a sa'a,yasa zamu huta  da nemanki ko har kin mance alƙawarin da kika min ne kafin Allah yasa mu mallaki juna?" "Alƙawarin me?"na tambaye shi, "Alƙawarin sama min sana'ar da zan dogara da kaina idan har Allah yana sa miki albarka a naki kasuwancin......" *Saƙonninku ya ƙayatar da ni Fans, ina godiya ga ɗaukacin masoyana waɗanda suka bani goyon baya domin ci gaba da rubuta wannan littafin sannan ina mai farincikin sanar da ku zan cigaba da rubuta shi sai dai salon zai canza.* Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. *Khalid bin Walid* (RA) Ya kan ɗauki *Al-Qur-ani* ya sa kuka yana mai cewa: "Jihadi da yaƙe-yaƙe ya shagaltar damu ga barin karanta ka". *A yau kuma ko me yake shagaltar damu ga barin karanta shi.....?* LAMBA NA SHA ƊAYA. HAKEEMA. "Alƙawarin sama min sana'ar da zan dogara da kaina tunda Allah yana sa miki albarka a naki kasuwancin." "Zan cika da yardan Allah amma sai ka koma shagon da kake saida musu littafan nan kai ma kana samo na cefane nima ina nema har mu haɗa mu tadaka." "In sha Allah,ke dai ki ja ɗamara tare da sa himma,ki hana kan ki baccin banza mu samu kuɗin da zamu mori amarcinmu." Murmushi kawai na yi ƙasan zuciyata kwance da takaicin halin Uztazu dan ina sane da samarin Sunna maza ne masu ƙoƙari gurin kiyaye dukkanin abinda Allah ya yi umurni da shi da Manzon shi, musamman ɓangaren neman ilimi da sana'a tabbas na san basa zaman banza, Uztazu ne kawai Allah ya jarabce ni da shi,hakan muka kwanta cikin farinciki sai wani lallaɓani yake yi abin har abin dariya da takaici saboda halin shi ne zafin rai da faɗa kuma komai kayi baka iyan masa ashe banda lamarin Naira. DIYAN HABIBI. "To meye kuma daga duniyar fa sai Kaduna, ka ga ka isheni da surutu alhalin Ni bacci nake ji tunda kai na lura duk training da Ammina ta bani na zama good wife bakaso tunda ga kayan girke-girken duk ka sa musu kwaɗo." Magana yake da niyyar yi amma tsabar shiga ruɗani ya kasa ganin yanda ya zama kamar dolo ya sa na ce"Tunda baka da ta cewa ni ka ga tafiyata dan bazaka hanani gudanar da abinda na yi niyya ba ato." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un." shine kalmar da HABIBI ya ke maimaitawa har DIYAH ta wuce shi ji ya yi jikin shi ya yi sanyi ƙalau tabbas shi ya janyo ma kan shi wannan gaggarumar matsalan da yake ciki da na ce"Sai cikakkiyar ƴar boko zan aura saboda ita ce kaɗai  macen da zata iya jiyar dani daɗi a zamantakewarmu na aure,a tunanina duk sauran mata fanko ne matuƙar baka goge a rayuwa irin ta turawa ba,sai dai sam ban taɓa tunanin bokon ne kaɗai a kan Farrah ba ko karatun Fatiha da ƙyar take karantashi daidai, Dalili kuwa ta taso ne a hannun mahaifiyar data fifita boko akan komai na rayuwarta dan daidai da karatun Sallan data iya ta koya ne da Alkur'ani mai  translation ɗin larabcin zuwa Turanci,kamar yanda ta sha faɗa min yayinda nake zuwa hira,A wata tattaunawar da muka yi da ita bayan na mata tambayoyin da suka shafi addini ce wa ta yi"Sam Mahaifiyata ne duk ta jawo min wannan matsalar saboda ta ƙi bani damar zuwa islamiyya in zauna gaban malami ya koya min karatu saboda in na yi laifi takakkiya take yi ta je har islamiyar ta masife malamin a ce warta"Bata haifa ma mai dattin hula ɗiyar da zai yi ta jibga ba." "Dan haka ta cireni tun ina da ƙuruciya, ta sanyani a makarantar boko mai tsada wanda inna tafi tun bakwai na  safe sai huɗun yamma nake dawowa,ina dawowa kuwa na cire kaya wanka zan yi in ci abinci in hau yin assignment tare da lesson ticana,Asabar da Lahadi kuwa ranar kitso ne da bacci sam Mahaifiyata bata taɓa koya min sallah ba,na dai tashi naga Abbiy na zuwa massallaci,Ammina kuwa sam ibadar ba damunta ya yi ba sai jifa-jifa idan ma tana yin to sai dai ko a Office,a makarantar boko na koyi sallah ganin sauran ƙawayenaa musulmai da muke zuwa Salla massallacin makaranta,ina bin su muje in tsaya ƙiƙam duk abinda naga sun yi nima in yi  har dai na gaji na faɗa ma ɗaya daga cikinmu ni fa ban iya karatun Sallan  ba,jin haka sai ta yi mamaki dan ko su  basa zuwa Islamiyyar amma malami na zuwa har gida ya musu karatu, washegari ƙawart tawa ta min kyautan Alkur'ani mai fassara,idan mun yi break ta koya min Ni kuma da dare in yi bita ta hanyar amfani da karatun turancin da aka rubuta,haka na tashi in kaga a gidanmu wani wani ya yi sallah bayan Abbiy to kuwa Kulu ce mai aikinmu ita kam ina ganinta tana yi sau biyar a rana ranan weekend,da ke Ni kuma gwanar tambaya ce sai na yi ta jero mata tambaya tana faɗa min iya abinda tasani,Abbiy kuwa matuƙar yana gida yana ƙoƙarin sanyani  na yi alwala ya ce in yi sallah ya fice massallaci sam bai san ban san ya ake ibadar ba ma,kuma yanayin aikin shi yasa sam bai san bana  zuwa islamiyya ba saboda yawanci sai dare yake shigowa gida.   (Wannan babban ƙalubale ne gareku iyaye maza damƙa ma mace ragamar gida dan kawai ta Fika hali Babban ɓaraka yake kawowa a rayuwar iyali,yana da gayen muhimmanci uba ya yi iya ƙoƙarin shi ba ya bar ragamar ma mace ita kaɗai, dangane da koyar da yara ibada shi ma iyaye suna sakaci yawanci ba ma ƙoƙarin zaunar da yaranmu mu koyar da su yanda ake karatun Salla mun bar ma malaman islamiyya wannan ragamar shiyasa ga irin su Farrah wanda mahaifiyarta ta hanata karatun addinin aka samu mishkila,ina shawartan iyaye da su rage sa soyayyar ƴaƴa a rai wanda yake hana ba ma ƴaƴa ilimi, wannan matsalar yana faruwa ne ga ƴawancin yaran masu ƙumban susa kaɗan ne daga cikin yaran Malam Shehu ke kokawa da malamai idan an daki ƴaƴansu, Allah yasa mu fi ƙarfin zuciyarmu Amin.) Ammina wacce ta hanani  zuwa Islamiyyar kullum ta shigo cikin gida tambayarta na farko"Kin yi Assignment?na amsa da "Eh"wanda kuma ya gagareni in lesson ticana ya zo kuma ya ɗaura min a  inda na tsaya,a haka ta taso tun ƙuruciyata."Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke bayan tuno wannan labarin sannan ya fara hasko yanda haɗuwarsu da Farrah ya kasance"Mun haɗu ne a wani taron ƙarawa juna sani a wata jami'a,Farrah ta fito gaban stage ta fara zubo speech cikin ƙwarewa da har sai da maɗaukacin mazauna gurin suka tafa mata nan take ta siye zuciyata dan haka ana tashi a gurin taron  tsareta sai dai ko saurarona bata yi ba saboda jan aji,wani daɗi ne ya tsirga zuciyata dan komai nata birgeni yake ,ganin ta nufi motarta yasa nima na yi sauri na rufa mata baya,anan na san gidansu tun bata kulani inna zo har na ƙulla alaƙa da ita mai ƙarfin gaske, kasancewar bata taɓa soyáyyá ba yasa na saye zuciyarta lokaci guda, ranar da ta gabatar dani a gurin mahaifiyarta sam ban samu karɓuwaba dan a gaban idona ta ce"In gama ɗaura burin duniya a kanki amma ki rasa wanda zaki ɗakko a matsayin miji sai mai 206(Mota)."nan take Farrah ta bijire mata tare da kafewa akan tana sona kuma har aka mana maure mahaifiyarta bata taɓa so naba." Ban fahimci zaɓen tumun dare na yi ba sai yanzu da wannan matsalar ta shiga tsakaninmu da Farrah in da ta gwada min Jahilci ne ke mata jagora a zamantakewarmu na aure amma da yardan Allah zan yi ƙoƙarin gyarata da ƙarfin soyayyar da take min,miƙewa na yi cikin sanyin jiki na fara gabatar da nafilfilu a sujjadata na ƙarshe na koka ma ubangiji akan sauyin halin matar shi. Jin ana kiran sallah yasa na fice zuwa ɗakinta na tasheta dan ni masallaci zan wuce sai dai na sami ƙofar a garƙame in da bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita a daidai lokacin da muminai ke neman rahamar Allah ba ita ta farka ba sai 9 na safe,duk nacina HABIBI dole na haƙura har sai da ta tashi dan kanta sannan na samu na shigo sai a sannan take Sallan asuban in da naji gabaɗaya rayuwata  ya ɓaci amma tuno da duk wanda ya kauce akwai buƙatar a janyo shi a jiki yasa na sassauta. "Bani wayata Habibi."ce wa ta ina nufar in da yake zaune a bakin gado, "A haka ake gaida miji dear?"yanayin yanda ya yi maganan yasa na ji wani kunya ya kamani dan haka cikin kawar da kai na ce"Good morning Habibi,fatan ka tashi lafiya?" "Bana lafiya?" "Meya sameka?"na furta haka ina kallon shi. "Damuwa dear,ina jin ciwo a cikin ƙirjina,damuwa na shirin yi min illa Diyah kuma duka ke ce silah" "Ni kuma?" na furta hakan idanuna na bisa kan shi ganin idanun  shi na sheƙi ya yi ruwa-ruwa alamun hawaye ne kwance a cikinsu ya sa na ji na karaya, "Eh ke." "Mai na yi maka dan Allah." "Hana zuciyata sukuni da nuna min Ni ba kowan kowa ba ne face faƙirin da kika nace sai kin aura, tabbas na san naci darajar so shiyasa har kika aure ni amma ban cancanci wannan kalar horon daga gareki ba."ya ɓullo mata ta hakanne dan ya san shine hanya mafi sauƙi da zai iya koya mata komai a sauƙaƙe dan tana son shi. "Ban yi komai ba Ni dear,a sanin dana maka kai mutum ne wayayye mai iya tarairaya amma daga yi maka laifi sau ɗaya shikenan sai ka dinga wahalar da Ni?" "Kin bani haƙuri da kika yi min laifin?" "No...no...no saboda the way You treat me,make me crazy and i AM disappointent." "Duka laifin ki ne tunda kin fi kowa sanin halina sannan mun kuma tsara yanda zamu gudanar da rayuwar mu a sauƙake so now tell me sorry." "So so sorry Habibin Diya."na furta hakan ina tale baki, Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Habibi har ya kamota ya sumbaci goshinta jin tana mi shi kuka ƙasa-kasa ya ce"Mene ne?" "Kaine ka ƙi appreciating ɗin abinda nake mama Habibi You know i love You and spend my time gurin koyan girke-girke duk saboda kaine amma ka dinga masife Ni Meyasa? Ajizanci"ya furta hakan a taƙaice, Amma kafi kowa sanin ina maka wani irin so mai wuyar fassara Meyasa komai na yi baka yi min uzuri har kake waya da wasu matan a waje bayan Ni har wata ke faɗa min zata aure ka ohhhhh! "Na daina kuma wacce kike tuhumata a kanta yarinyar nan ce fa jawahir ke ma kin san ai ba ajina ba ce mai zan yi da ita wacce ko Hausa bata iya karantawa ba gani da Queen Elizabet a gidana."Ya fasa min kai, Murmushin farinciki ne ya suɓuce min sai na ji rabi daga cikin damuwata ya kau saboda girman kishi a zuciyata kuma ga HABIBI yana gwada min matsayina a gurin shi nan da nan na yi laushi na sauke nauyina akan ƙafan shi ina bin shi da wani shu'umin murmushi, Murmushi ya yi wanda ya ƙara fito da ainihin kyawun shi sannan ya ce"Dear inasonki." "Me yasa kake sona Habibi?" "Saboda kin cancanci in so ki dan kin sadaukar da rayuwar ki ma Ni  shiyasa nima na miki kyautar rai,ruhi da gangan jiki." "Zuciyar fa?"na tambaye shi ina turo baki, "Da man taki ce matata sai dai kin san meye?" Na girgiza kai" I have a special gift For You amma sai kin ɗaukar min alƙawarin Inna umurce ki ba zaki ƙara yi min musu ba, promise?" "Yeaah HABIBI."nan take ya miƙo min wani ɗan akwati na ga zoben azurfa na walwali tare da sheƙi ai nan take na miƙe na rumgume shi sai da ƙyar ya ɓanɓareni daga jikin shi saboda azumin da muke yi murnan bai gama sakina ba na ji yace "Another suprise for You Dear,close Your eyes." Da sauri na runtse idona  nan ya zaunar dani tare da ajiye min wasu manyan littattafai akan cinyata kafin ya ce in buɗe ido da sauri na buɗe idon na fara bin littafan nake da kallo ina jujjuya su,ganin sai rarraba ido nake yi yasa ya ce"Ki duba su ɗaya bayan ɗaya sai kiji ƙarin bayani." Dudduba su na shiga yi duka na ga littafai ne na addini,wasu hukunce-hukuncen azumi da Sallah ne,wasu akan tsarki nan take naji wani sanyi ya mamaye ruhina dan har ga Allah inason karatu dan Ni ma'abociyar son karance-karance ce, yawanci labarai nake karantawa wannan da ya kasance na addini sai naji ina muradin karanta shi dan jin meya ƙunsa, Dan haka a hankali na fara zubo mi shi godiya har sai da ya rufe min baki cikin raɗa ya ce min"Zan fita in je in dawo kafin na dawo ki fara duba wannan duba na tsanaki kuma duk in da baki gane ba ina dawowa ki tambaye ni." "Toh HABIBI gaskiya You really make my day today Allah ya saka, amma wayata fa inason kiran Ammi ne." "Wasu karatuttuka zan turo miki na saurare dana  karantawa wanda suka shafi addini musamman na wannan watan da muke ciki mai albarka,dan so nake a cikin wannan watan mu yi gamda Katar da ganin daren lailatul ƙadri. "Lailatul ƙadri wani dare ne kuwa wannan Habibi?" "Darene da Allah ya ambace shi a cikin Alkur'ani mai girma......" *Maƙasudin rubuta wannan littafin da man janyo hankalin mata akan girman wannan wata mai alfarma ne masu hisabi suka fara yi min kwarwa,da yawan mata sam basu damu da yin bincike akan addini ba da wayoyin su na hannu ko neman littafin da suka shafi tsarki, Salla,azumi alhalin kuma da yawanmu muna buƙatar sani dangane da addininmu musamman manyan mata da basu da lokacin kan su sai na aikinsu,dalilin hakan na zaɓi yin rubutu dan mata mu ƙara ƙaimi mu tashi tsaye mu sa Ni Ramadan ba kawai girke-girke yake buƙata ba hadda shiri na musamman dan neman kusanci da Allah, Allah ya karɓi ibadunmu.* Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. *Alƙur'ani* Duk yadda mutum zai samu magani mai gusar da damuwa ba zai samu kamar *Alƙur'ani* ba. LAMBA NA SHA BIYU. HABIBIN DIYAH. "Lailatul ƙadri darene da Allah ya ambace shi a cikin Alkur'ani mai girma saboda girman shi,a cikin shine ake ƙaddara abubuwan da zai faru da mutum a cikin wannan shekaran wa lau na alhairi ko sharri,shiyasa ya ke da gayen muhimmanci mutum ya hana idanuwan shi barci domin roƙar ma kan shi alhairi ta yiwu ƙarfin addu'a yasa masifun da za su sami mutum a cikin shekarar ta ragu tare da maye gurbin sa da alhairi. "Kudus Habibi, gaskiya na ji daɗin wannan taƙaitaccen bayanin amma Ni fa a labarin da Kulu take bani a wata tatsuniya ta ce"Idan mutum ya yi katari da ganin wannan daren mafarki zai yi ya gan shi cikin koren ciyawu bishiyoyi na rangaji suna ambaton Allah." "Allah masani amma gaskiya wannan shaci faɗi ne kawai Ni dai kamar yanda Malamaina suka sanarmin dangane da dacewa da riskar wannan daren shi ne"Zaka tsinci kanka a cikin wani irin walwala mara misaltuwa sannan ni'ima zata yalwaci washegarin ranar ta yanda rana kan shi ba zai yi fitowar da zai dami mutum ba, za'a samu lullumi ta yanda ni'ima zata riski ma'abota bautar Allah." "Very good Habibi,to yaushe ne daren lailatul ƙadrin kenan?" Annabi ya faɗa mana ce wa"Ana riskan daren a goman  ƙarshe na watan Ramadan." "Ba tsayayyen rana?"ta tambaye shi. "Ba bu saboda malamai sun sassaɓa a kan shi wasu sun ce ana riskan daren a daren ishirin da ɗaya,wasu sun ce daren ishirin da uku wasu kuma sun ce daren ishirin da bakwai so abu dai mai gayen muhimmanci ana  son a waɗannan dararen sam kar mutum ya shagalta da bacci ko yin wani aiki har sai ya yi bauta cike da ikhlasi." "Da yardar Allah nima zan dage Habibi ko zan yi gamdakatar da wannan daren, tabbas kai haske ne ga rayuwata fitila mai haskaka min duhun da rayuwata ta shiga."Murmushi ya bini dashi mayalwaci kafin na jefo mi shi tambaya, "Shin an keɓe daren da yin wata addu'a ta musamman ne ko kuma duk wanda ka iya zaka yi?" "Ba zance ba kin san nima ba malami ba ne sai dai zan bincika miki kamar yanda ke ma nakeso ki bincika da kanki. "Ta ya ya Habibi?" "A duniyar yanar gizo Diyah." "Da yardan Allah zan dage  amma ada kai wanne kake yi idan goman ƙarshe ta riskeka?" "Karatun Alkur'ani da yi ma Allah kirari sannan in roƙi Allah da irin sigar da annabawa suka roƙe shi da shi ina mai zubda hawaye tare da neman gafarar shi akan laifin dana aikata da wanda ma nake shirin aikata shi a gaba sannan ina kamun ƙafa da Annabi da iyalan gidansa in fara addu'ar da salatin Annabi in rufe da salatin shi wannan ma wata hikima ce na amsar addu'a." Lumshe ido na yi wani irin daɗi na ratsani tabbas sai yanzu na san ina addini mai daɗi adah can sunan Musulma kawai nake,jin ya tsareni da ido yasa na yi saurin buɗe ido na ce"Ka yi haƙuri na san na cika tambaya." Murmushi ya yi kafin ya ce"Yi tambayarki farinciki nakeji mara misaltuwa in har nasani ina amsa su." "Toh,wani irin siga ne Annabawa suke roƙon Allah da shi." "Ayoyin suna cikin Alkur'ani mai girma har ma an yi littafi na musamman domin saukaƙa ma bayin Allah su dinga karantashi a saukaƙe, sunan littafin 40 rabbana." "Zan nema in sha Allahu Habibi dan daga yau ina son in ji na iya komai wallahi." Murmushi mai ƙayatarwa ya yi mata dan shi kam har ga Allah yana son Diya musamman halinta na son bincike akan duk wani baƙon ilimi da ta ji shi,godiya ya yi ma Allah kafin yasa kai ya fice domin zuwa tura mata karatu na musamman wanda ya shafi tsarki, Salla,Azumi har ma da Ahlaƙ da sauran ilmummukan da ya kamata ace ta sani a matsayinta Na Musulma. Wucewar shi ke da wuya na duƙufa akan duba littafin da ke hannuna wanda aka rubuta shi musamman akan tsarki da Sallah,ɗumi-ɗumin hawaye na ji yana bin kumatuttukana dan na kasance mace mai wasa da Sallah kuma ba ko yaushe nake damuwa da yin shi ba musamman in azumi ya wahalar da ni ranar,auren da nayi nema har nake ramakonta in ban yi shi akan lokaci ba ashe shi kan shi yin sallar an fi so a yi shi a farkon lokaci tabbas rayuwata tana cikin duhu mabayyana kuma da izinin Allah zan bi Habibi sau da ƙafa dan in kori wannan jahilcin da yake damuna. Ina cikin wannan tunanin Hakeema ce kawai ta faɗo mun a rai ashe-ashe kallon da muke mata na wacce bata waye ba mune manyan gidadawan ba ita ba? Ashe keɓance kanta da take yi ita ce wacce ta san kanta mu kawai duniya ce a gabanmu ba muma san lahirar mu ba? Tabbas lokaci ya yi da zan yaƙi duhun(Jahilci)da ke bibiye da rayuwata da ikon Allah. Nan na duƙufa da karatu har sai da naji ƙiran sallar azahar na yi wuff na miƙe dan ina kwaɗayin samun ladan da ke cikin yin Salla a farkon lokaci kamar yanda na ji wani hadisi ya yi magana akai. (Wasu ba'adin mata suna sakaci da yin Sallah a cikin wannan wata mai alfarma wasu ta hanyar jinkirtata wasu kuma sam yinta ne basa yi sai jefa-jefa dan haka wannan shafin ke jan hankali dangane da masu irin wannan hali da su ji tsoron Allah su daina dan Salla ita ce Farkon aikin da za'a fara dubawa na ɗan adam idan ta cika to komai zai zo mi shi da sauƙi dan haka a kula,a rage yawan girke-girken da zasu shagaltar da mu ga yin ibada a wannan watan,yin girki ba laifi ba ne amma a samar da lokacin ambaton Allah ta yanda ruhi zai tsaftata, Allah ya karɓi tubanmu ba dan halinmu ba." HAKEEMA. Washegari ko baccin asarar da Uztazuna ya saba komawa duk bayan Sallan asuba bai koma ba,sa kai ya yi ya fita, ya barni zaune akan dadduma ina karanta Alkur'ani ban kai ga tashi ba na ji sallamar shi shi da wani mutum wanda bansani ba ,amsa sallamar na yi ina mai kai dubana kan agogon dake sagale a bango na ga ya nuna ƙarfe 7 daidai,mamaki ne kawai ya kasheni ganin Uztazuna yana shirin fita da keken zuwa ƴar barandar mu domin a haɗa min shi tare da yi mi shi service,ɗayar zuciyar kuma yana mamakin meyasa baya kwatanta kwatankwacin wannan himmar a fita nema tunda har yana da ita ban samu mai bani amsa ba dan haka zuciya ta cigaba da min saƙa,ganin tunanin ba amfanin komai zai min ba yasa na ci gaba da karatun Alkur'anina har suka kammala ya sallame shi,ban san in da ya samu kuɗin biyan mai gyaran ba Ni dai koda ya gama naga ya sallame shi da wasu kuɗaɗe bayan shafe awa biyu yana aikin cike da ƙwarewa,taimaka ma Uztazuna na yi muka shigo da keken ɗaki gudun kar ya yaga min ledar dake Malale a tsakar ɗakin,nan na shiga  lallaɓashi ya yi wanka mu yi bacci amma fir yaƙi kwanciya ce wa yake" Ba yau kika ce za su zo ba?" "Su wa kenan?" "Baƙinki mana." "Eh in sha Allah amma ka san su fa masu kuɗi basa fitan sassafe suna bacci su more ma ran su." "Au nine talaka ko dan haka bana bacci in more ma rayuwata, to daɗin abin dai duniya da kayanta aro ce ga mai hankali kuma suma ba rawa suka taka Allah ya basu arzikin ba." "Ni fa ban ce ba Noor haba mene na min mummunan fassara." "Ni kuma na san kin ce su masu kuɗi Ni talaka." Dariya ce taso suɓuce min na yi saurin rufe bakina saboda yanda ya yi kicin-kicin da fuska na ce"Talaka bawan Allah ba." Ya yi murmushi yana jifata da kallon zan rama cikin hanzari na haɗa hannayena biyu alamun roƙo na ce"Afwan Noor, ƙarfe 12 suka ce zasu iso kuma da yardan Allah za su zo ɗin, ka san Classic ladies na First Ramadan with HABIBI group masu koyi da turawa ne dan haka suna kiyaye lokaci kuma suna ƙoƙarin cika alƙawari." "Kyakkyawan halayya ta Annabinmu dai ai turawa kwaikwayo suka yi tare da yi mana wayo suka ɗauki cika alƙawari abu muhim suka bar wasunmu da wasa da lokaci da rashin sanin muhimmancinsa,uwa uba alƙawari wanda sosai Annabi ya yi jan kunne a kan shi har ma ya siffanta rashin cika alƙawari da alamu ne na munafurci." "Hakane tabbas to Ubangiji ya yi mana muwafaƙa." "Amin ya hayyu ya ƙayyum,to ni zan fita na ga 10 ya kusa yau Ni zan ja ma Malam aya a gurin tafsir." "Ma sha Allah,Ubangiji ya sa a mizani ya kuma kai min kai lafiya ya dawo da kai lafiya." "Amin."ya sa kai ya fice wani irin daɗi naji jin gurin yaɗa alhairi zai je na tsani jin ya ɗauki mashin yana shawagi da shi a gari,tashi na yi na kimtsa wajena tare da feshe shi da turare(Airfeshner),sannan na bi lafiyar kujera nan da nan wani bacci mai daɗin gaske ya yi awon gaba dani. Ƙarar wayata ne ya farkar da Ni ganin numban dake kirana yasa naji wani daɗi ya kamani na kai dubana kan agogo naga shabiyu dai-dai na yi saurin amsa kiran ina musu kwatance har suka gane gidan,jin ce war sun iso yasa na sa hijabina tare da ficewa waje na musu iso, Ba yabo ba fassala haka suke amsa min komai dan basu ƙarajin sun rainani ba ma sai da suka ga tsakurkurin muhallin da nake rayuwa a ciki wanda suka tabbatar da na hayane,ko a jikina wai an mari kakkausa sai ma washe musu baki da nake yi Ni dai babban burina su bani ɗinki, ganin yanda na musu yasa kowacce daga cikin su ta bani kala bibbiyu akan in fara yi musu a matsayin gwaji bayan sun tabbatar min da Inna ɓata musu zannuwansu ba sa Ni ba sabo nan take na ji sun wanke min ido dan haka na gwada kowacce tare da cajar kowaccensu dubu goma -goma kowani kala ɗaya yana matsayin dubu biyar na yi musu hakan ne dan su san na san kan aikina dan haka a take suka bani dubu biyar biyar kafin muka yi sallama suka fice da sauri da man kamar a ƙaya suke jin kansu. Kiciɓus......... *Da fatan munsha ruwa lafiya Fans a min afuwa abubuwa sun sha kaina jiya zuwa yau ga double page nan,ina yinku fisabilillah* Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. *Duk abinda ka rasa, matuƙar imanin ka na tare da kai wallahi ba ka yi hasara ba, haka duk abinda za ka samu kuma, matuƙar ka rabu da imanin ka wallahi ka yi hasarar duniya da lahira.* LAMBA NA SHA UKU. ABBIYN DIYAH. Mahaifin Farrah kuwa tunda yake a Rayuwar shi da matar shi(Ammi)bai taɓa jin ya yi danasanin yanda ya sake mata jan ragamar rayuwar gidan shi ba sai da faɗan da taje ta yi da sirinkinta(HABIBI)ya ji zuciyar shi ta shiga ƙunci mara misaltuwa dan haka a karon farko na tsawon rayuwar su da shi da ita ya ɗauke mata wuta,ko kallo bata ishe shi ba,ya daina cin abincinta ya ƙaurace mata a shimfiɗa ko gaishe shi tayi irin na su na ƴan boko ciki-ciki yake amsawa,nan fa ta shiga cikin ruɗani kamar yanda ta kirani a waya take sanar da ni halin da suke ciki da mahaifina bayan an sha ruwa, Haƙuri na bata tare da bata shawarwari dan Ni kaɗai ke gareta babbar ƴa dan haka sam Bama ɓoye ma junanmu sirrinmu, Tashi ta yi bayan mun gama wayar ta je ta fara aiwatar da ƙudurinta sai dai hango katin ɗaurin aure zube a gaban Abbiy bayan shigarta cikin ɗakin tana gwalangwatso yasa ta ji ƙafafunta sun yi sanyi, Ƙara sawa ta yi cikin son jan magana ta ce"Auren wa za'a yi kuma ba labari Abban Farrah duk cikin fushin........"sauran maganan ya maƙale a bakinta hango sunan mijinta ɓaro-ɓaro a jikin katin tare da wata mace da sauri ta zabura ta yo kan shi ta ce"Aure Mansur! "Ni zaka tozarta ka cima mutunci bayan shekara arba'in da aurenmu sannan ka ce zaka yi min kishiya?"ɓanɓare hannunta ya yi daga jikin shi ka fin ya ce"Ai an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa Fatsuma saboda haƙurina ya yi yawa,sai dai ban san ashe haƙurin nawa lalata tarbiyyar ƴaƴana zai yi ba,rashin tarbiyyar ya bibiye su har cikin gidan aurensu su da mazajenmu in sun hayayyafa ya bi jikoki hadda tattaɓa kunne duk tsawon shekarun nan ban fuskanci hakan ba sai da kika bi ƴarki har cikin gidan mijinta kina shirin faɗa da sirikinki saboda kin saba yi min faɗa da tsawa daga ƙarshe kuma in dawo ina baki haƙuri saboda sanyin halina,ina hakan kawai dan son zaman lafiya ne ba wai dan abin baya damuna ba ashe-ashe babban kuskure na tafka na rashin taka miki birki da banyi ba ga shi ya wuce kaina da mutanen gari da ƴan'uwana ya komq kan mijin ƴar........"ta katse shi cikin zafin rai, Duk wannan dogon jawabin na son ka gamsar da ni ce wa faɗan da baka bari munyi da Mashkur ba shine dalilin da yasa zaka ƙara aure? Ko mai kake son fahimtar da nine dan Allah bana fahimtar ka sam." Abin da na ke nufi zan yi aure dan in raya sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama tare da gyara kuskuren da na yi na zaɓenki a matsayin mata kuma uwar ƴaƴana. Buɗe baki na yi zan yi magana ya yi saurin dakatar da Ni"Ba shawara nake nema ba na riga da na aiwatar da ƙudirina kuma a shirye nake da duk wani mataki da kike ganin zaki ɗauka ko min muninshi,ba kuma sai mun je kotu ba kamar yanda kike iƙirarin kai sirikinki kina iya faɗa min a yanzu in baki takardar ki.! Daramdam!haka zuciyarta ta yi wani irin bugu dan jin Abbiy na nuna mata ita yanzu bata gaban shi ko rabuwa ce ta shirya zai rabu da ita lallai abin babba ne bata dawo daga vibration ɗin da yasa ta ba ya ƙara ce wa"Sai dai ki sani ke kaɗai kika shigo gidana ba tare da ƴaƴana ba dan haka ki tafi ke kaɗai Matana zata riƙe kuma ta basu tarbiyyar da duk Yakamata uwa tagari ta ba ƴaƴanta."durƙushewa ta yi a wajen ta rasa ma a wata duniyar take ciki nan take jikinta ya fara rawa ƙirjinta na sama na ƙasa take yanke ta fara kokawa da numfashinta sam yaƙi daidaita take yanke ta faɗi a wajen sumammiya, Ko a jikin Abbiy hasalima tashi ya yi ya fice ya kira Kulu akan ta zo ta zuba mata ruwa ko zata farfaɗo sai dai ina ta yi nisan zango dole sai da ya figi mota zuwa babban asibitin da take aiki a ciki nan take likitoci suka rufu a kanta domin ceto rayuwarta sai dai ko ta farfaɗo tana tuno Abban Farrah zai yi aure take fara jijjiga kafin ta kara komawa gidan jiya, Abbiy kuwa addu'a kawai yake mata na samun sauƙi dan alƙawari ya ɗauka koda Ammin Farrah mutuwa zatayi to wallahi sai ya yi aure dan ya zamto ma mata darasi a rayuwar su musamman irin matan da ke maida mazajen su tamkar ƴaƴan da suka haifa kawai saboda Allah ya yi zuciyar mazan na su da haƙuri.   Kwananmu biyu a asibiti da Ammina alhamdulillah jikin da sauƙi sai dai tana zaune zakaga ta firgita tsigar jikinta ya miƙe a ranar kuma aka ɗaura auren Abbiy da tsohuwar budurwansa wacce iyayensa suka mashi zaɓi ya tubure shi bai son baƙauyiya ƴar boko zallah yake so,ta yi aure hadda ƴaƴanta Allah ya karɓi rayuwar mijinta Abbiy na shiga cikin ruɗanin halin matar shi yasa ya ji ya kamata ya mata kishiya wataƙil hakan zai sa ta dawo cikin hayyacinta ta gyara halayyarta. A daren ranar suka zo shi da matar ta shi asibitin domin duba Ammina da jiki in da ta...... HAKEEMA. Kiciɓus suka yi da Uztaz wanda yake shirin shigowa sai dai irin kallon ƙasƙancin da suke mi shi yasa ya haɗiye sauran kalmar gaisuwar da yake musu cike da fadanci, Sai shegen kallo kamar mutum zai haɗiye mu."ce War ɗaya daga cikin ta furta hakan tana tsaki suka raɓa ta gefen shi suna fice,ƙara gyara tsayuwar ya yi har sai da ya ji dirin tashin motocin su sun tafi sannan ya shigo ɗakinmu sallama ɗauke a bakin shi, Matse fuska na yi dan har ga ina jin haushin yanda Uztazuna ya iya ƙare ma mata kallo wannan halin shi ne koda kina cikin Hijab da liƙabi ne balle kuma waɗannan da ke yafe da gyale iya kafaɗa. "Baƙin Alhairi sun zo har sun tafi."ya furta hakan ko damuwa da yanayin fuskata bai yi ba, "Eh sun zo."na amsa mi shi a taƙaice, "To ma sha Allah,ki ce yau a kwai mu da cin ƙwalam da maƙulashe?" Da kuɗin kayan aikin ko kuma kuɗi ka samo mana? Da ribar ki na ɗinkin dai za ki bani in sayo mana irish da ƙwai,mangyada sai mu yi stew na kwana biyu kin ga kin samu damar hutu kina tashi sai dai ki ɗora mana shinkafa ko taliya." "Hakane gaskiya Noory,lallai yau kayo mana samuwa tunda har dage-dage za mu ci."na furta mi shi haka cike da gatse cikin wasa ya ce"Tabbas yau na samu kyautar kuɗi har dubu goma amma...." Me?na yi saurin katse shi, Na canza ma tsuntsun soyayyarmu robar gaba dana baya dan haka dubu 1 ne kacal a tare da Ni." Ya yi kyau Allah ya ƙara arziki. Ya amsa da "Amin." Shigewa ciki na yi saboda takaici da baƙin cikin da Uztazuna ya ƙunsa min wato Mashin ɗin shi yafini muhimmanci tunda ko ƙwayar shinkafa ba mu da shi amma zai iya kashe ma Mashin dubu tara kawai dan ya cigaba da bagu to Allah kuwa zai sa Ni. Biyoni ya yi cikin raha ya ce"Ai in faɗa miki alhajin nan namu(Mai makarantar su) miliyan goma ya cire a cikin dukiyar sa ya ce a raba ma mabuƙata musamman mu da muke aiki a ƙarƙashin shi amma saboda mugunta irin na ɗan Arewa ƴan'uwan shi suka rabe kuɗin a tsakanin su,wani ya ɗau miliyan 5,wani 3 wani biyu sauran miliyan ɗayan shine aka kakkasa mana hadda gero da su suga." Ina suke to." Na sadakar mana to Ni dake da ke Hajjaju mai zamuyi da wani gero ai sai dai kiyi mana kunun gadara da madara ya ji kwakwa a ciki, "Zaka sha kuwa."na furta hakan a cikin zuciyata tare da raɓawa gefen shi zan fice ya riƙoni yana ce wa"ina zaki je?" "Banɗaki kuma a uzurce nake." Sakina ya yi tare da samun bakin gado ya zauna yana jirana in dawo in ba shi kuɗin cefane mu ci irish da ƙwai ,da  miyan dage-dage har mu kora da Kunun gadara da madara mai kwakwa. To fah bari muga ko tare zasu sha kunun nan tare da ku Fans idan Hakeema ta ba shi kuɗin ribar ɗinki. *Kun rage comments shiyasa jikina ya yi sanyi da typing ɗin fatan za ku gyara in ci gaba da typing sau biyu a rana Na gode." Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. Haƙiƙa shi ilmin addini shine ado da kwalliya a garemu, dukkanin wanda bashi da ilmin addininsa, to haƙiƙa yana cikin duhun jahilci wanda shaiɗan ya dilmiya shi cikinsa,dan haka wannan littafin ki zaburantar da mata ƴan boko zalla da su miƙe su nemi ilimin addini saboda sai min san Allah kafin za mu bauta mi shi,kuma bai yiwa ka san ubangijinka batare da ka nemi ilimi ba. LAMBA NA SHA HUƊU. AMMIN FARRAH. A daren ranar suka zo shi da matar ta shi asibitin domin duba Ammina da jiki in da ta fara kokawar miƙewa zaune sai dai kash ta kasa saboda yanda jikinnata ke mata matuƙar nauyi cike da nadama ta ce"Mansur amaryan taka kenan?" Abbiy ya ɗaga mata kai alamun "Eh." To Ubangiji ya baku zaman lafiya mai ɗorewa. Suka amsa da "Amin."Fashewa ta yi da kuka Zuciyarta na mata ƙona tsabar kishin da ke azalzalarta amma ciwon da Allah ya jarabeta da shi sam bata da wani kuzarin gabatar da dukkanin ƙudurin da ta yi niyyar aiwatarwa idan mijinta ya mata kishiya, Lallai ɗan adam ba a bakin komai yake ba kuma ba zaka san da hakan ba sai Allah ya baka komai na duniya ya hanaka lafiya hawayen tausayin kanta take yi har Abbiy ya ƙaraso gaban gadon ya kama hannayenta biyu cikin son kwantar mata da hankali ganin yanda ta yi laushi yasa ya ce"Ki yi haƙuri Fatima, wannan auren ƙaddara ce da rabo dan rabon shi ya kashe mijinta dan in aureta, babban abinda nake sonki da shi ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya alfarman Annabi da Alkur'ani zan kwatanta adalci a tsakaninku Ni dai babban burina ki canza halayya kin ji." Da yardan Allah zan canza dan inaji a jikina ba zan ƙara rayuwa ba a duniya tunda har wata ta mallakeka,Gara in kyautata tsakanina da Allahko zan dace da aljanna. To ai aljannar sai ya ɗaga ƙafa sannan zaki shiga ƴar'uwata ki yi hakuri sannan ki rungumi ƙaddarar ki in sha Allahu Ni ɗin alhairi ce a gareku ba zan taɓa shiga tsakanin soyayyarku da mijinki ba."Ce War Amaryan Abbiy wacce ta tattako ta ƙara so gaban gadon da Ammie ke zaune ta ja kujera ta zauna tana fuskantar Ammina fuskarta ɗauke da murmushi, Wani sanyin daɗi ne ya shiga ratsa kowani lungu da saƙo na jikina har ban san lokacin da na furta Alhamdulillahi ba a zuciyata ashe a fili na furta hakan har yasa hankalin Abbiy da amaryan ya dawo kaina dan sam basu san ina cikin ɗakin ba saboda sun shigo ina salla idarwata kenan, "Farrah mai kike yi anan baki koma gida kin ma mijinki abin buɗa baki ba?" "Na je dawowa na yi Abbiy na kawo ma Ammina abincin dare shi ne Mashkur ya ce in kwana tare da ita." "Sam ba za'a yi haka ba maza kira shi a waya ni aikin me nake yi da ɗiyata amarya zata kwana a asibiti ta bar mijinta."Ce War Amaryan Abbiy. Ganin duk mun zura mata na mujiya mamaki shimfiɗe a fuskarmu ya sa ta ce"Maza kira min sirikin nawa ki koma gida Ni anan zan kwana da mamanki ai kin yi ƙankanta da jinya irin wannan." Tuni asirin zuciyata ya fallasu akan fuskata dan haka na fara murmushi cikin jin kunya na fara ƙoƙarin gaisheta, Buɗe min hannayenta biyu ta yi alamun in iso gareta da man na santa tunda daɗewa mutuniyar kirki ce ta bugawa a jarida muna haɗuwa da ita a duk wani sha'anin ahalin gidan su Abbiy,Ammi ce ta gargade Ni da daina gaisheta ko ta cire min kwankwaso tunda ta san  an so haɗata da Abbiy dan haka take kishi da ita ala dole in muna tare da ita nake kauda kai sai dai in mata sansanyar murmushi itama ta maida min da nata sansanya dan mace ce da bata son matsala,ko da naji hukuncin da Abbiy ya yanke akan Ammina jinjina mi shi na yi dan hauka ɗaya ma HABIBI na karɓi bulala to ina ga shi daya ɗauki tsawon shekaru arba'in tare da Ammi mace mai shegen mitan tsiya da faɗa,gwaliya,ƙyaliya da raina duk wanda bai kaita ba shine halayyarta,kamar yaron aikinta haka ta ɗauki Abbiy yana zaune zata aike shi ya ɗakko mata abu kuskure kaɗan zai yi mata ta balbale shi da faɗa kamar zata duke shi,ita kaɗai ce gwana a duniya duk wanda ya aikata saɓanin abinda take so ya shiga uku ai ma ya yi matuƙar ƙoƙari wallahi dan kullum cikin nasiha da faɗa mata matsayin shi a gareta yake amma ta gagara ganewa  ina da tabbacin ba dan ya mata hakan ba ba zata taɓa nadama ba (Ni kuwa na ce Allah dai ya so ta da shiriya ai ba dan yasota ba da akan kishiyar sai ta ƙara zarmewa, Allah ya shiryi mata masu irin halin Ammi ya sa kuma su yi nadama tun kafin lokacin da nadamar bata da amfani zata riske su.) Ganin na zurfafa a cikin tunani yasa Hajiya Amina tasowa ta iso gurina ta ɗago Ni duba na kai kan Ammina wacce jikinta ya mata nauyi ta gagara miƙewa naga hawaye na zuba a idonta da sauri na ƙarasa gurinta cikin gunjin kuka na ce"Dan Allah dan Annabin shi Ammina ki cire damuwa ki rayu ko dan mu da  ƴan'uwana kin san daga Allah da Annabin shi bamu da kowa sai ke,ke ce sanyin idaniyarmu kar ki tsawwala ma kanki damuwa akan Abbiy ya ƙara aure Sunna ce ta Annabinmu,wanda ya fi kowa ma a duniya da lahira matan shi sun zauna da kishiyoyi to ina gamu?. Still hawayen take yi bakinta sai rawa yake yi yana ɓari amma ta gagara motsa shi ta yi magana,hannun Hajiya Amina na kama na haɗa shi dana Ammina cikin kuka na ce"Ammina ga amanar abokiyar zamanki na baki haƙika na yarda da halayyarta da kyakkyawan ɗabi'unta ke ce kawai zuciyata ke taraddadin yanda zaki karɓeta Ni kam zuciyata ya natsu da ita." Bisa ga mamaki sai na ji Ammina ta ce"Nima na karbi ƙaddarata hannu bibbiyu tabbas idan har Allah ya ƙaddara zan miƙe akan dugadugaina sabuwar Fatima ce wannan mai koyi da halayyar ɗiyar Manzon Allah da yardan Allah." Take Abbiy ya durƙushe akan gwiywowin shi biyu ya sa fuskar shi a ƙasa ya yi ma Allah sujjuda ta godiya da farincikin ganin wannan rana na shiryuwar masoyiyar shi kuma uwar ya'yan shi, Koda ya ɗago rungume su ya yi dukkanin su biyu yana shi musu albarka kafin aka dawo kaina Hajiya Amina tasa na kira Habibi ya zo ya ɗauke ni ,tare muka fito da Abbiy ango wanda ya bar Hajiya Amina a gurin Ammina dan su kwana a tare, Hira mai daɗi ta dinga mata tare da bata kissoshi na manyan bayin Allah mata waɗanda suka hidimtawa addini musamman Sayyida Fatima da Mahaifiyarta Nana  Khadijah wacce dukiyarta gabaɗaya ta ba ma addinin musulunci amma hakan bai sa taƙi yi ma manzon Allah biyayya ba nan Ammina ta ji tana da burin ta ƙara rayuwa ko dan ta aikata ayyukan alhairi tare da gyara tsakaninta da mutane har bacci ya yi awon gaba da ita, A sannan Hajiya Amina ta amsa kiran Abbiy a waya tana ɗauka ya fara yi mata ƙorafi akan yanda ta zaɓi yin daren farkonta a asibiti gurin jinyar kishiyarta ita ta bar shi shi kaɗai, Dariya ma abin ya so bata tsofai-tsofai da su ai ita bata tunanin zasu ƙara yin wani soyayya a cikin auren su amma dai ko mene ne ta ji daɗin kulawar da ya bata dan haka ta bi shi da daɗaɗan kalamai da yasa ya ji tamkar yana rumgume da ita a hakarƙarin shi. Habibi kuwa............ HAKEEMA. Sakina ya yi tare da samun bakin gado ya zauna yana jirana in dawo in ba shi kuɗin cefane mu ci irish da ƙwai ,da  miyan dage-dage har mu kora da Kunun gadara da madara mai kwakwag a ciki, Wayata na fiddota daga cikin aljihun rigar dake jikina na da7nna ma ƙanina kira,jin na ce zan bashi kuɗin mashin yasa y f jin an admin suka fara da Uztazu Ni kuwa na shige cikin daki na kwaso kayayyakin da suka kawo na zube su a tsakiyar ɗakin na fara yi ma ƙanina lissafi, Tun daga landing har kan man keke almakashi,allura,zare stone da duk na bashi kuɗin su wanda suka kama dubu tara daidai,ɗari biyar na cira a sauran dubu ɗayan na bashi ya fice bayan na gama yi mishi bayanin kalolin da duk nakeso ƙarshe ma ya ɗauki zannuwan ya tafi da su dan kar a samu failure, Jiyowa na yi gurin Uztazuna murmushi  akan fuskata na ce"Ka ga mun cika Sunna Noor mun karɓi amanan kayan mutane da kuɗinsu mun je za mu kashe kudin yanda ya kamata." "Me kike nufi?",ya tambaye Ni a fusace dan ina lura da shi tun shigar mu ɗakin da ƙanina ya ke bina da kallo ƙasa-ƙasa, Cikin sanyin murya na ce"Ina nufin na bada kuɗin kaf an je siyo min kayan aiki  Inna gama suka ciko kuɗin sai muyi amfani da shi." "Saboda kin fi kowa rashin wayo ko saboda ke ce muguwa ta bugawa a jarida Haba Hakeema wato ainufin tun ina karatu na ke haɗiyar yawu saboda na san ke ɗin gwana ce gurin sarrafa nama,kin san duk wani hukunce-hukuncen da ake masa ya kama maggi ya yi zauyy." Dariya na fashe da shi hadda ina ƙyakyatawa ganin yanda yake kumburi kamar zai fashe yasa na fara daidaita nutsuwata ganin hakan yasa ya ce"Ki yi ma Allah ki shiga ki fito da kuɗaɗen nan in je kasuwa da wuri dan da kunun gadaran nan nake son yin buɗa baki." Babu su kuma ba dalilin su Noori sabo da idan kiɗa ya sauya to rawar ma canza shi a ke yi yanzu a matsayin matarka nake ba budurwan dana saba hana kaina bacci in nemi kuɗina ka zo ka cinye min su ba kullum da kayan buɗa baki,ko tausayin maraicina baka yi da yanda nake tsaye akan ƙannena dan rufa ma juna asiri kai dai kullum burinka in haɗa maka kayan daɗi ka zo ka take ciki ko ƙwandala baka bani balle in ɗan rage daga an yi magana ka ce bidi'a ne yin Ramadan basket amma Sunna ce zuwa gidanmu ka ci abincin dana siya da kuɗina ka kakkaɓe jiki ka yi gaba. Tun muna waje baka taɓa yi min kayan sallah ba amma fa kana jiran abincin sallah na sati guda a jere batare da ko goron Sallah ka bani ba Shin ba Allah ne ya halasta kyautatawa ba a tsakanin mutane? "Shi ne tabbas." "Ni da ke kyautata maka shin bakajin daɗi?" "Ina ji sosaima har ma ina alfahari da ke." Ka san dalilin da yasa na ɗaga maka ƙafa san da muke waje?ya girgiza kai alamun A'a To na yi hakan ne saboda a lokacin Allah bai kallafa maka ɗaukar ɗawainiyata ba kuma Ni dan na kyautata maka ba laifi ba ne sai dai kuma yanzu na tabbatar da ce wa"Na tafka babban kuskuren sabar maka da yin  komai tunda ka gagara ciyar da Ni da ɗaukar ɗawainiya........." Na ji kuma ba gode da gori ai Bama sai kin kai da nisa ba Hakima ki ce kawai ba zaki bada kuɗin ba zan yarda sai dai ki sani bafa ki isa ki hanani bin gidajen abokai ba ina kwasar Gara fahimtum?. Na'ammm ya Uztazul Karim....... *Wannan shafin na rubuta shi ne ga ƴan mata masu shagwaɓa mazaje ta hanyar bugun ƙirji tun suna waje su ƙi saba ma namiji da yi musu komai sai dai su suyita hidima da saurayin kwatankwacin hakan ne ya faru da Hakima na cikin wannan labarin kuma kun ga yanda zuciyar shi ta mace sam burin shi Ita dai ta mi shi hidima da dukiyar ta,dan haka ku yi takatsantsan Allah ne ya kawo mu wani lokaci da maza ke son mace ta musu sam ban hanaku kyautatawa ba ban kuma ce mace ta zubda kimarta ta roƙa ba sai dai kar a wuce gona da iri gudun matsalar da ka iya zuwa ya dawo, Allah ya sa mu dace* *Ban yi 2 page ba amma na yi double page a tafa min🤩💃, Allah ya karɓi ibadunmu,Barka da shan ruwa* Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. Misalin ƴan uwantaka saboda Allah, kamar misalin hannu da idanu ne, idan ido ya zubar da hawaye sai hannu ya share masa, idan kuma hannu ya ji ciwo sai idon ya zub da hawaye sabo da zafin da hannu ya ke ji. Allah ya bamu ikon soyayya domin shi. LAMBA NA SHA BIYAR. DIYAN HABIBI. Habibi kuwa tun a motar yake kwantar min da hankali dan ya san inada kyakkyawan alaka da Mahaifiyata ba matsayin uwa kawai take a gareni ba ƙawata ce wacce sam ba ma rabuwa dan haka duk abinda zai shafeta dole ya taɓani dan haka ya dinga rarrashina cikin tattausan kalamai masu sanya nutsuwa har na ji na samu ƙarfin gwiywar yi mata addu'ar samun lafiya nagartacciya. Muna isa gida ya hanani taka ƙasa tsabar gata ya sunkuce ni zuwa ɗakin shi kamar wata ƴar baby kasancewar ba wani nauyi ke gareni ba, Sakina ya yi a daidai saitin katifa in dana faɗa kai,nannauyan ajiyar zuciya na sauke dan sam ban yi tunanin akan abu mai laushi zan sauka ba,hararar wasa na mi shi ina ciccije leɓena alamun na ɗan ji zafi ya bini da murmushi tare da zaro harshen shi waje alamun gwalo, Ƙoƙarin raba jikin shi da kayan da yake yi ne yasa na yi saurin runtse ido dan wani irin zafi da ake yi ga kuma rashin wadatacciyar iska a gari shiyasa daga shigowar mu yayi tunanin yin wanka,dariya ma na ba shi sosai hadda ƙyakyatawa dan haka ya dawo saitin fuskata ya fasa ƙara tare da rarumo Ni,a gigice na miƙe na yi kan shi sanin ni matsoraciya ce lamba ta ɗaya yasa ya ce"Ƙarshen runtse ido gaki gani sai in ga na jin kunya." Murmushi kawai na yi tare da sunne kaina a jikin ƙirjin shi nan take na haifar mana da baƙon yanayi wanda muka dulmiya a cikin har sai bayan awanni biyu muka dawo hayyacinmu, Wanka muka yi a tare,ina fitowa na shimfiɗe akan gadon tsabar gajiyar da na yi da taimakon shi da komai ya sa min kayan bacci sannan ya kunna mana kira'a nan take wani bacci mai daɗin gaske ya yi awon gaba da mu.   Washegari a asibiti na wuni in da na samu ana samun ci gaba sosai dangane da ciwon Ammina dan a jingine da gadon na sameta tana shan kankana Hajiya Amina zaune kusa da ita tana riƙe da filet ɗin, Sai hira suke abin gwanin ban sha'awa suna ganina Hajiya ta fara yi min oyoyo fuskarta ɗauke da murmushi a haka muka gaisa kafin na isa gurin Ammina na mata ya jiki, Amsa min ta yi cike da kulawa sannan na samu guri na zauna ina bitar littafin addu'o'i wanda Habibi ya koya min da asuban nan,ko da muka samu keɓewa da Ammina tambayata ta yi dangane da zamana da mijina wanda na faɗa mata duk yanda muka yi a taƙaice,tabbas ta ji daɗin wannan al'amarin kuma ta yi min nasiha mai ratsa jiki wanda yasa har hawaye sai da nayi dan ina ganin kamar wasiyya take bar min tsabar yanda ta yi laushi ta ɗauki duniya ba koman komai ba da haka muka rabu zuciyata ƙunshe da farinciki canjin halayyar uwatawashegari kuwa aka sallameta muka ɗugunzuma zuwa gida in da har ɗaki na bi Hajiya Amina na yi mata godiyan karamcin da ta gwada mana yanda daga zuwanta ta yi jinyar Mahaifiyata,faɗa ta dinga yi min akan godiyan kan shi in da ta ce"Ai yi ma kaine." Na daɗe a shashinta sannan na shiga gurin Ammina na fara tausarta,tare da nuna mata girman ƙaddara da yarda da ƙaddara mai kyau da mummuna,hawaye kawai take yi sai naji  jikina ya yi sanyi dan haka na cigaba da kwantar mata da hankali ina kuma mamakin irin wannan shiriyar da ya zo mata a lokaci guda dan da ada ne wane mutum in ji mutuwa har yaushe na isa in tunkareta da ce War su zauna lafiya da kishiya,kishiyar da taci alwashin matuƙar aka yi mata ita sai ta ƙonata da ranta in yaso duk ma abinda zai faru ya faru,tabbas da na san zata aika dan nafi kowa sanin halinta na rashin tsoro da tsayuwa akan ra'ayinta amma yanzu sau nake hango sassauci a cikin ƙwayar idonta da gangan jikinta wanda ya yi laƙwas, godiya na yi ma Allah da ya nuna min wannan rana Sannan na yabi Manzonsa ɗan daɗin Allah. Sai dare sannan Habibi ya zo  ɗaukata bayan ya shiga gurin Ammina ya mata ya jiki, cikin sanyin murya a karon farko na rayuwarta da shi ta dinga mi shi godiya tare da damƙa amanata a gare shi tana kuma mai neman yafiyar shi akan duk kuskuren data aikata a gareshi, Murmushi kawai yake yi cike da farinciki sannan ya ce"Uwa ai bata yi ma ɗan ta laifi Ammi, Ubangiji ya baki lafiya nagartacciya." Ta amsa da "Amin, Allah ya muku albarka."muka haɗa baki wajen amsawa,da taga ina ta kai komo wajen shiryawa da kanta ta ƙira Kulu ta haɗa mana abinci cikin basket tunda an sha ruwa lokacin har an sauke abincin dare wanda Hajiya Amina ta aiko min da nawa na musamman,sallamarta na yi ina kallon fuskarta wacce ta yi fayau sai kallona take itama har na fita na ƙara dawowa na zo na rumgumeta a tare muka fashe da kuka kafin ta yi jarumtar ɓanɓareni daga jikinta ta yi min rakiya har gaban motar Habibi,lallaɓawa ta yi ta koma dan jikinta sam ba ƙarfi nan ta fara yin istigfari a cikin zuciyarta dan sam bata son wani mugun tunani ya zo ranta,kishingidar da ta yi anan wani nannauyan bácci ya yi awon gaba da ita. Tun a cikin mota Habibi ya lura da yanayina da ya yi matuƙar canzawa dan haka ya sake mana ƙira'a cikin muryan Sheikh Abdullahi Abba sai bi yake yi cike da nishaɗi nan nima tawa zuciyar ta sanyaya dan haka koda muka koma gida na ware ganin haka ya  ɗaukeni  a hannu ya dinga zagaye falon da ni tamkar ya samu jaririya sai da ya gaji dan kan shi kafin ya sauke Ni yana godiya ga Allah da ya nuna mi shi wannan ranar cikin farin ciki ya ce"Tabbas mahaƙurci mawadaci sannan mai haƙuri shi zai dafa dutse har ya sha romon sa." "Da mai ya faru?" Da Ammina ta amshi auren mu mana,tabbas rayuwar aurenmu zai inganta tunda mun samu albarkan uwa Diyah, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai." Hakane alhmdulillah mun gode ma Allah da ya sa muka tama silar shiryuwan Ammi zuwa ga hanya madaidaiciya, Allah ya cigaba da zama jagoranmu a cikin kowani al'amarurruka na rayuwar mu. Ya amsa da "Amin."ka fin y nuna min hanyar kicin alamun in yi gaba,tafiya na fara cikin saiɓi da yanga wacce ta kasance halittana,ya  dinga bina da kallo cike da sha'awa har na kai bakin ƙofa sannan na juyo cike da mamaki nake kallon shi na ce"Ya da kallona?" "My property nake kallo Diyah."dariya ya bani amma na kanne tare da ɗaga mi shi gira ɗaya da sauri ya fara tattakowa ganin zai cimmini yasa na shige da sauri ya biyo ni da sauri, Kyakkyawan runguma ya min ta baya kafin ya ce"Close Your eyes Dear." Rufe idon na yi da gaske kafin ya juyar dani saitin store ɗin mu sannan ya ce"in buɗe." Wal!haka na yi tozali da...........tamkar a mafarki 🤪💃. HAKEEMA. Na'ammm ya Uztazul Karim." Ganin yanda ya wuce ni fuu kamar guguwa yasa na ce"Allah ya huci ran maigida."in kun tanka ya tanka haka ya saka kai ya fice yana cika yana batsewa ko a jikina wai an mari kakkausa hasalima miƙewa na yi a gurin har ƙanina ya kawo min kayan ɗinkin nan take na yi yanka na mamman gum a jikin kayan kafin na faka su gefe,ban ko tuna Uztazuna na fushi da Ni ba sai da lokacin shan ruwa ya yi,jin shiru bai dawo ba yasa na aika taliya yar murji ta ɗari biyu na watsa shi a tukunya,ana kiran sallah na gabatar da salla sannan na yi buɗa baki da taliyata da sansanyar ruwa na hamsin a gefe,ci na yi na ji nayi nak kafin na adana sauran wanda zan yi sahur da shi,da 3 in 1 ɗina wanda na siye shi saboda tsaro,ko da Uztazuna ya zo na wanke komai na maida shi mazaunin shi tamkar ban girka komai ba,sai bai bi takaina ba samun guri guda ya yi yana sakace da tooth pick sai gyasa yake jerowa a jajjere,daurewa na yi na je na same shi na mi shi sannu da zuwa amma ci kan ki bai ce min ba Ganin haka yasa na kama kaina na bi lafiyar gado Dan matuƙar mutun na son ƴanci to fa dole yaga vadaidai ba. Cikin kwana biyu na hana kaina sukuni har sai da na tabbatar na musu aiki na bajinta wanda duk wanda ya gani zai yaba ina kammalawa na goge sannan na hau Whatsapp na sanar musu aikuwa a ranar suka rankayo dan sun matsu su ga kayan su babban tsoron su kar in ɓata musu zani, Sai dai bisa ga mamakina sun yaba fiye da tunanin mai tunani nan na dinga hamdala a cikin zuciyata har suka biyani cikon kuɗina tare da min alƙawarin kawo wasu gobe idan mai duka ya kaimu. Suna ficewa na danna ma ƙanina kira in da na bashi dubu goman cancat domin ya sayo ma kan shi yadi da sauran ƙannena mata turmin atamfa biyu domin rufa ma kanmu asiri, Sauran kuɗin na mishi lissafin roll ɗin Milo guda dana madara milky domin in raba biyu ya kaima mahaifina sauran canjin kuma ya dawo min da shi dan in riƙe a hannuna. Fitar shi ke da wuya sai ga Uztazu ya faɗo cikin ɗakin yana haki"Ina kuɗin ɗinkin?" Na yi shiru saboda yanayin shi kaɗai na kalla na san ina buɗe baki ba alhairi ne zai fito daga bakina ba, Ina miki magana kin min banza dan kin maisheni ɗan iska"ya furta hakan a fusace, Ka yi hakuri gani na yi baka bani ajiyar kuɗi ba shiyasa ka ji na maka shiru, kuɗin ɗinki kuma tuni na aika kasuwa a sayo ma marayun ƙannena kayan zuwa idi." Nan kika fi ƙauri wajen iya zance amma ki taimaka ma mijinki da bashi da shi kin kasa bayan kin fi kowa sanin da arzikin Nana Khadijah addinin Allah ya kafu a Makka." Dariya kalaman shi ya bani sannan na ce"Tabbas haka ne amma ya ka ji kissar farin jakada ɗan Aminatu ɗan Abdullahi Muhammadur-rasulullahi?" Shiru ya min dan ya san ya ɓallo ma kan shi ruwa jin ya yi shiru yasa na ce"Ba ka ji sanadin tafiya fatauci da Manzon tsira ke zuwa ma Nana Khadijah ba suka haɗu da shi ba saboda yaba ma ƙwazon shi?" Tabbas rayuwar ma'aiki ya ishe mu yin gadara saboda ya zo mana da komai dan haka Noor ka ƙara zage dantse sam kar ka yarda Sunna ta wannan ɓangaren(Sana'a)ka samu tawaya,ko ba ka ji yanda abin koyinmu yafi kowa kula da matan shi ba ne duk da yafi kowa yafi komai?" Na ji kuma tun kafin ki je islamiyya na san da hakan kawai ki bani kuɗi mu kwashi girki yau kamar yanda kika alƙawaranta mana." Ban yi alƙawari ba in ma na yi na fasa dan haka ka fita ka nemo mana abin da zamuci tun kafin in ɗauki kwaƙwaran mataki a kanka. Ki ɗauka kawai ina ganin hakan zai fi dan Ni kaina na gaji da zama dake. Haka ka ce? Eh nan take na fara kakkauda kayana dake waje na kintsa su tsaf a ɗaki,zumbulelen hijabina na janyo sai ........ *I AM so sorry masu jiran page ɗin safe,rashin wuta ya mana katutu wannan ma a inji na samu na sa fatan kun sha ruwa lafiya, Allah ya karɓi ibadunmu* Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. *"Kowacce rana da Allah ya halitta tana cewa:" Ya ɗan adam kayi amfani dani watakila bazaka rayu zuwa wani yinin ba, kowane dare da Allah ya halitta yana cewa: "Ya ɗan adam kayi amfani dani watakila bazaka ƙara kaiwa wani daren ba".* LAMBA NA SHA SHIDA. DIYAN HABIBI. Wal!haka na yi tozali da kayan abinci tamkar a mafarki hadda buhun irish a ciki ga kiret ɗin ƙwai,cabbage, karas, green pearls da kayan marmari nan take na ruƙunƙune shi ina tsallen farinciki, Hannuna ya kama muka taho falo na kwantar da kaina a jikin kafaɗar shi na ce"Habibi na rasa da wace irin kalma zan maka godiya ma Billah, because kana sani farinciki ta kowani fanni,fatana dai Allah ya cigaba da wanzar da soyayya da ƙauna a rayuwarmu." Ƙayataccen murmushi ya yi kafin ya ce"Amin Diya amma fa kin cancanci fiye da haka saboda samun mace kamar ki mai ƙanƙan da kai da yarda da cewa bata sani ba tare da rumgumar sabon ilimin da aka zo mata da shi abu ne mai matuƙar wahala,ina sonki zan kuma ci gaba da sonki har ƙarshen rayuwata,Allah ya albarkaci rayuwarki da zuriya ta gari." "Amin Habibina kuma in sha Allahu zan yi dukkanin iyawata dan ganin na zama maka mar'atus saliha dangane da fannin girki kuma zan sa nutsuwa da lura wajen ganin na girka mana abinci mai lafiya ba tare da na yi almubbaranci da shi ba." "Ma sha Allah,haka nake son ji daga gareki Diya,koyon girki a kafafen sada zumunta sam ba laifi bane matuƙar zaka sa hankali da lura tare da ɗakko irin abincin da muka saba ci kuma daidai da aljihun maigida idan kika yi hakan faffaɗan fada zaki samu a cikin zuciyata, sannan Ni Masoyin abincin gargajiya ne,inason tuwo daga na masara har kan na dawa ya dahu ya ji wuta ta yanda da asuba zaki min ɗumame in yi sahur da shi." Murmushi mayalwaci na yi na ce"Shiyasa ka ke kato ashe  Habibi ka ce tuwo ke gina ka." "Sosai ma ba ki ga ku ƴan indomie generation sam baku da ƙarkon mu ba." Murmushi na yi kafin na ce" Tabbas amma fa ni gaskiya ban iya miyan gargajiyan nan ba sai dai in koma gida a koya min." "Shameless to You Dear kin ji kunya da baki iya Mulka tuwo da miyan kuka mai daddawa da naman rago ba Billah,ki samu man shanu ki zuba a gefe wayaga daɗi kan daɗi." Dariya nake hadda ƙyakyatawa sai dana sahirta sannan ya ce"gobe gidanmu zan kaiki wajen maman Kwamared ta koya miki miyan gargajiya,kin ga in kika yi sai mu zo mu sa a firiza na tabbata idan kika ga yanda ake sau ɗaya shikenan zaki iya i trust You." Turo baki na yi gaba kafin na ce"Gurin Maman Farrah za'a je Billah ba wani maman Kwamared haka kawai kana shirin yi min ƙwace." "To na ji gurin Mamanki ina shikenan."Ya furta hakan yan yi min kallon ƙasa-ƙasa. Kwaɓe fuska na yi alamun shirin yin kuka ya rarrashe Ni ta cikin ƙwayar idon shi na ce"Ummm abinci ko karatun za mu yi dan na fara jin bacci." "Karatun dear kin san muna gab da shiga halwa remain few days mu shiga goman ƙarshe dole mu tsage dantse dan ke ma ki shiga sahu kar ban kai wata shekarar ba ki zo kina kuka kina Allah sarki HABIBI."muryata ya kwaikwaya ta ƙarshen amma jin ya ambato mutuwa yasa na ce"No,No....dan Allah ka daina ambatar min mutuwa Habibi haba!" "Aikuwa ta zama dole ba ki ji mai Allah ya ce ba ne a cikin Alkur'ani mai girma"Duba na kai kan shi cikin alamun tambaya da neman sani. "Ce wa ya yi Kullu nafsin za'ikatul maut summa ilaina turja'un(dukkanin rai sai ta ɗanɗani zafin mutuwa kuma gare shi zamu koma.)." "Haka ne tabbas Allah ya ba mu ikon cikawa da imani Amma na fi yi mana addu'ar samun tsawon rai mai amfani dan mu mori rayuwar aurenmu da muke burin ginata da tubali mai kyau sannan ina mana ƙwaɗayin samun Waladus-saleh ɗan da ko ba ma raye zai tuna da mu ya mana addu'a" "To Allah ya ba mu tsawon rai mai albarka tare da ƴaƴaye na gari." "Amin ya rabbi."miƙewa na yi cikin sanyi naje na ɗakko littattafaina na dawo muka ɗaura daga in da muka tsaya duk jikina a sanyaye haka muka tashi har muka yi bacci sam zuciyata ba daɗi duk in na tuno da ummata sai in ji gabana ya yanke ya faɗi Ras. ABBIYN FARRAH. Ango an shiga sabon rayuwa yayinda matsanancin kishi da kaɗaici ke tare da zuciyar Ammi na rashin shi a kusa da ita,duk da daman ita ba mai yawan ciwo ba ce amma in ya kamata ya kan yi kamar zai kasheta,to duk lokacin da ta tsinci kanta a cikin irin wannan tashin hankalin tana samun wani kulawa na musamman daga gareshi sai ga shi tana ji tana gani wata ta ƙwace mata shi ta rasa shi a gefenta yana can tare da wata  suna raya sunnar ma'aiki,gado ɗaya shimfiɗa ɗaya jikin shi tare da nata kai Subhanallahi! Firgirgit ta farka daga cikin nannauyan  báccin da ya yi awon gaba da ita sai dai ta tashi a firgice gumi  duk ya gama jiƙa mata jiki tsabar m Kiɗima ga uban zufan da ta haɗa wanda sam bata damu da share shi ba,  nan take ta fara ambaton Allah da neman taimakon shi saboda mummunan mafarki take akan ƙarin auren da mijinta ya yi ,Kulu ce ta faɗo cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama,turus ta yi dan ganin uwargiyarta a cikin wannan halin har zata juya kuma ta tsaya tuno da roƙonta da ta yi  gafara a safiyar yau akan duk abinda ta aikata a gareta na rashin kirki ta yafe mata da yardan Allah yanzu rayuwarta ba irin ta da ba ce ta canza hali,ta santa sarai a dah wanda ba ƙaramin aikinta ba ne  yanda ta shigo ta balbaleta da masifa, "Allah ka ɗau raina in huta da ganin wannan mummunan rana"karaf sai a kunnen Kulu ta yi daurin ƙarasowa kusa da ita ta  zauna a ƙasan ƙafarta durƙushewa ta yi kafin  ta ce"Hajiya ki yi hakuri dan Allah sannan ki rungumi ƙaddarar ki da hannu bibbiyu duk da na san kishiya ko ta bubuzu ce akwai ta da zafi amma idan kika ɗakko abinda ke gabanki wanda ya fi zama da ita ɗin muhimmanci shikenan kin rabu da damuwa." "Duniyata ba zata ƙara daɗi ba Kulu,alƙiyamata ce ta tsaya dan Mansur shine fitilar dake haskaka rayuwata kuma ya samu makwafina to me ce ce amfanin rayuwata ki faɗa min?" "Rayuwar ki kuwa ita ke da matuƙar amfani tunda har kike neman canzata daga mummuna zuwa kyakykyawa, shin idan kika sa damuwa har hawanjini ya ƙara bigeki irin na wancan karon zuciyarki ta buga kika mutu ta ya ya zaki nemi gafarar mutanen da kika ƙuntata ma na gurin aiki da dangin mijinki?" Shin kin san Allah ba ya laifin da ke tsakanin bawa da bawa kuwa?" Ta girgiza kai cike da tsoron haɗuwa da Ubangijinta  cikin rashin kuzari ta kai duba kan  Kulu wacce ta cigaba"To tun wuri ki farka dan Allah baya yafewa kuma wallahi Hajiya ko akan haƙƙin Maigidan nan kadai aka kyaleki ba zaki zauna cikin kabarinki da daɗi ba dan haka ki saki ranki ki yi kishin birni ki riƙe mijinki gam-gam sai ki samu aljanna cikin sauƙi." "Hakane Kulu na gane yanzu mai zanyi?" Nan ta fara jero mata duk abinda ta sa Ni dangane da tarairayan miji da ba shi kulawa sannan ta yi mata hannunka mai sanda dangane da ƙarancin ilmin addinin da take fama da shi, sosai ta yi mata godiya kafin ta sallameta,tana ficewa ta fara nazarin kalaman da Kulun ta faɗa mata tare da tariyo su tamkar mai bita,dake maca ce gogaggiya wacce ta saba mu'amala da jama'a ta samo mafita in da ta ɗauki remote ta fara bibiyan tashoshi wanda ke gabatar da shirye shirye akan addini musamman cikin wannan wata na Ramadana,Afrika Tv 3 ta tsaya in da ta yi dace da wani Farin dattijo yana tafsirin Alkur'ani mai girma nan da nan ta maida hankali tana jin fassarar ayoyin Allah masu tsuma zuciya,lema-lema ta ji a saman kuncinta wanda ta tabbatar da hawaye ne ke kwarara tsabar yanda take jin wa'azin tamkar da ita ake,jiyo rahama tare da ni'imomin da Allah ya tanadar ma bayin shi masu tuba yasa ta ji wani irin ƙarfin gwiywa ya zo mata nan take ta fara hamdala,sai da aka kammala tafsirin tsaf sannan ta miƙe jin an sanya karatun Alkur'ani yasa ta ƙara volume ta shige banɗaki domin gabatar da wanka. HAKEEMA. Nan take na fara kakkauda kayana dake waje na kintsa su tsaf a ɗaki,zumbulelen hijabina na janyo sai jiyo hannun shi na yi cikin nawa ya riƙe hijabina gam tare da rumgumo Ni. Kin ci jarabawar tabbas kin cinyeta duka Hakeema." Ƙoƙarin ƙwace jikina daga nasa nake yi yaƙi bani damar hakan cikin fushi na ce"Ka cikani dan Allah Malam in wuce ba kaima ka gaji da zama da Ni ba?"na ƙarashe maganan hawaye Malale akan fuskata dan rikenin da ya yi shine abinda ya fi komai ɓata min rai, "Ki yi hakuri kamar yanda na ce kin ci jarabawa to wallahi jarabawa ce na yi miki domin in samu mace mai sona dan Allah."Shiru na yi ina sauraron shi jin wata sabuwar maganar da ya ɓullo da ita. Nine tilon ɗa a gidan Alhaji Bisallah,shararren ɗan kasuwar nan wanda ya shahara da arziki a garin nan namu mai albarka, sanadin arzikin mahaifina ya sa na auri mata har guda 3 suna niyyar hallakani saboda su gaji arzikin dana gada,na rabu da su bayan Allah ya tuna musu asiri dan auren gata mahaifina ya min in da aura min mata 2 rana 1,Mahaifiyata ta aura min zaɓinta itama,duka a cikin shekara guda na auri waɗannan matan kuma a cikin shekarar muka rabu sanadiyyar CCTV camerar dake maƙale a kowani lungu da saƙo na gidan saboda tsaron lafiyata. Kallonshi nake cike da mamaki bakina sam ya gagara rufuwa sai bin lallausan fatar jikin shi nake da kallo wanda sai a lokacin ma na ankara da yanda take sheƙi ga wani lallausan gashi ya musu rumfa(gargasa),shaƙar daddaɗan turaren shi na yi wanda na sha jin ƙamshin shi a jikin ƴaƴan masu hannu da shuni na lumshe ido cikin murya sansanya na ce"Mahaifinka ya maka auren gata har mata biyu su kuma matan sun so kasheka saboda su gaji arzikin da ka Gada shin daman ana gado kafin mutuwa ne ko Mahaifin naka ya rasu ne." Murmushi ya yi mai sanyi kafin ya zaunar da Ni a daya daga cikin kujerun dake ɗakin namu ya ce"Mahaifina tun yana raye ya raba dukiyar shi saboda sanin yanda zamu fuskanci barazana Ni da Mahaifiyata idan har ya faɗi ya mutu saboda Ni kaɗai ya haifa yana kuma da sauran mata guda uku." "Na'am na fahimce ka." Wannan barazana dana samu daga matayena yasa na ji na tsani mata da auren kan shi,in da iyayena suka kaɗa suka raya akan in zo da zaɓina tunda sun min nasu na nuna a bari sai na huta,sun yi matuƙar gajiya da hutun nawa in da suka bani nan da sati biyu akan in fito da mata ko kuma su min auren dole." Meyasa suka matsu da auren naka." Dan su ga jikokin su, wannan shi ne babban burin mahaifina a duniya saboda tarin arzikin da yake da shi amma ba shi da yawan ƴaƴa dan haka ya ɗaura burin duniya a kaina." Na'am."Na furta hakan ina bin gemun shi da kallo wanda ya Kusan zuwa ƙirjin shi saboda yalwar shi ga shi sai sheƙi yake tabbacin yana samun gyara mai kyau dan haka ya kusa kamu 3. "Damuwar da nake ciki na takurar Mahaifina da yanda aure ya fice min a rai yasa na samu Abokina mijin Farrah da wannan mas'alar in da ya bani shawarar yin basaja har in samo wacce ke sona domin Allah da hannu bibbiyu na karɓi shawarar shi amma sai nake tunanin ta yaya zan samu kalar wannan matar tunda ayyukan da ke gabana sun min yawa, Kwatsam sai aka gayyaci Mahaifina taro domin zuwa musabakar da kika zo na ɗaya,ranar sai ya kasance yana da mitin da wani babban kamfani dan haka yasa na wakilce shi,anan na yi gamo da ke Hakima wanda tun daga yanayin takun tafiyarki na ji kin tafi da imanina kina samun guri kika zauna kuma na ji zazzaƙar muryanki na ji ina neman ɗimaucewa,tun daga wannan ranar na jingine dukkanin wani abu mai muhimmanci wanda ya danganci kasuwancinmu na fara bibiyarki har sai da na samu duk wani bayanai da ya dangance ki,hatta kalar mijin da kike so,irin shigar sa da komai kwaikwayo na yi, sabbin ɗinki na yadi nasa aka min dan na ji labarin kina son miji mai tawadu'u da gudun duniya,ganin duk abin buƙata ya samu hakan yasa na tunkare ki,sai na sameki da sauƙin kai da iya kulawa,sam baki da kwaɗayi ke macace mai neman na kanta,na so miki a matsayin namiji mai son banza ne da hannun kutare (a dunkule)sam bana miki kyauta sai kika nuna min koda kyauta ko ba bu kina sona. Ban ƙara sakankancewa da lamarinki ba sai da aka kawo kuɗin aure da komai na ce"ban da halin yin lefe kuma a ɗaki ɗaya za mu zauna kika bani saitin akwati da zannuwan da kike tarawa idan auren ƙaninki ya tashi ki bashi kika bani na kawo gidanku." Tun daga nan na sallama na san ce Wa ke ɗin ta musamman ce kuma kyauta ce ke wanda Allah ya min bayan an yi aurenmu a daddafe sai na tsiro da sabon iya shege kawai dan in jaraba ki shin dan kina sana'a kina kama kuɗi ne yasa ba ki damu da babuna ba ko kuma halinki ne haka? Nan ma sai naga kin zarce tunanin duk mai tunani dan ke ɗin samfarin matan aljanna ne a gidan duniya ke a yanda na lura da ke ba babuna kike gudu ba zamana ba sana'a shi ne babban abinda kika fi tsana. Fagen Amana da cika alƙawari,sanin ya kamata kula da Mahaifinki da marayun kannenki tabbas kin kasance mace abin koyi ga mata uwa uba zuciya da yarda da sana'a shi ne mutuncin duk wata mace a rayuwa tabbas ina godiya ma Allah da samunki Haaakimar zuciyata,ba sai gobe ba yanzu-yanzu zan kai ki  gurin iyayena dan sun matsu su ganki. Waya ya ɗakko daga aljihun wandonsa Iphone 15 ya kara a kunnen shi cikin ƙasaitacciyar murya ya yi magana da wanda nake zaton direbansa akan ya zo ya ɗauke mu. Miƙewa yake da shirin yi na yi saurin janyo shi dan inada tarin tambayoyin dake ƙunshe a ƙirjina dangane da shammatata da ya yi. Uztaz Fans how market today🤪ya kuka ga kafcen shin wani darasi kuka ɗauka daga rayuwar gidan Hakima dana uztanta,kowa dai ya san akwai kalan mazan nan masu yi ma matansu wayo musamman idan sun kasance tailoli,ko masu sana'a,sake musu komai suke yi su dogara da ɗan samuwar da suke yi dan su yi ma yaransu kayan sallah shin idan hakan ya faru dake jan wuya zaki zama kamar Hakima ko kuma zama zakiyi kiyi ta masa bauta kamar Allah ne ya aiko ki?   Ina buƙatar ganin tarin comments ɗinku ƙarƙashin wannan post ɗin dan littafin First Ramadan with HABIBI yana gab da ƙarewa saboda gabatowar goman ƙarshe na watan Ramadan, fatan ba zaku manta da   sa Ummu jidda a cikin addu'o'inku ba Fans na gode. *Masu kiran waya,saƙon text message both whatsapp and Facebook ina godiya sosai,jiki alhmdulillah na gode sosai Allah ya bar zumunci inayinku irin sosai ɗin nan,yanzu rashin wuta ne ke kawo min tsaiko ku jama ƴan Nefa carmandudu cikin carbi lolz* Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. *Mai Azumi* Yana da Farin ciki guda biyu: Farin ciki a lokacin da zai sha ruwa, da farin ciki lokacin gamuwa da Ubangijin sa, kuma tabbas warin bakin me Azumi shi yafi daɗi a wurin Allah akan ƙamshin turaren Almiski.” LAMBA NA SHA BAKWAI. DIYAN HABIBI. Bayan na kammala ayyukana na gida na samu nutsuwa a ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujeruna na alfarma na zauna hannuna riƙe da Zubdatul Ahkam domin yin bita,wayana ne yayi ƙara cikin hanzari na ɗauka ganin Ammina ne yasa na kara shi a kunnena bakina ɗauke da sallama,lumshe ido na yi jin yanda ta amsa min sallamar i cikin walwala alamun ta Rungumi ƙaddararta,gaisawa muka yi sannan muka ɗan taɓa hira kaɗan wanda ya shafi lafiyarta,jin zata kashe yasa ni ƙara rarrashinta akan zamantá da kishiyarta amma bisa ga mamakina sai na ji ta ce"Farrah magana akan auren ABBIYnki daga yau a rufe shi dan Allah saboda umurnin Allah ya aikata,Ni kuma ba zan yita jayayya dangane da halal ba babban addu'a dai shi ne Allah Ya ba shi ikon yin adalci a tsakaninmu." "Amin ya rabbi Ammi amma gaskiya kin sakko da wuri a ce Habibi ne ya yi wata mata ai sai dai ya zaɓa tsakanin Ni Ko ita Allah,Ni fa i cannot share Habibi with any Woman Billah." Dariya sosai na bata har sai da ta tsagaita sannan ta ce"Eh lallai yaro yaro ne,to idan ya zaɓe ta kuma fa." "Sai ya rabu da Ni amma i will make sure na kashe shi itama na zama ajalinta." "This is the great mistake da yawancin matan wannan zamanin suke aikatawa kowacce mace burinta ta mallaki mijinta ita kaɗai alhalin Ubangiji ya fi mu sanin hikimar da yasa ya ce maza su auri mata 4 saboda maza ba su kaimu yawa ba,koma sun kaimu to duk tashin tashina na yaƙi in ana yi su ake kashewa,to shin idan ke kin samu miji asirinki ya rufu bakya yi ma ƴar'uwarki kwaɗayin samun kwatankwacin ni'imar da kike ciki." Ina mata amma ina jin tsoro yawanci ƴanmatan yanzu babban burinsu su shiga su fitar da na gida ko a wulaƙanta wacce suka samu. Thats is Your beleive dear ,hakan kike ma kanki fata shiyasa zai faru dake amma da'ace zaki tsarkake zuciyarki wallahi ko da wani mugun abu kishiya ta zo Allah ba zai bata nasara akan ki matuƙar kin riƙe addu'a,idan kuma har ta yi nasaran to na lokaci kaɗan ne Allah sai ya warware shi tare da baki ladan hakurin da kika aikata." Hakane Ammi haka na ji wani malami na faɗin irin wahalar da mahaifiyar shi tasha a hannun kishiyoyinta ƙarshe Allah ya ɗaukaka ƴaƴanta,ga shi malami,a cikinsu akwai attajiri,mai muƙamin gwamnati da babban ɗan kasuwa hakan ya faru ne bayan mahaifin na su baya raye." To kin gani dan haka ki tsarkake zuciyarki ki daina kambama kishi a cikin zuciyar ki duk da halal ne amma in ya yi yawa yana jawo bushewar zuciya da ƙeƙeshewarta daga ƙarshe ka aikata mummunan abu danasani mara amfani ya biyo baya bayan sunanka ya karaɗe duniya da hotonka liƙe a shafin kowace jarida." Hakane Ammi Allah ya bamu ikon yaƙar zuciyarmu." Ta amsa da "Amin,ga wani sirri na musamman da aka bani." All ears Ammina."na furta hakan ina baza fatun kunnuwa, "Kowani sallah idan zaki yi ki dinga roƙon Allah akan baƙin kishi da zuciyarki ke da kinji Dear and ki roƙi Allah ya mallaka miki zuciyar mijinki idan kuma ya ƙaddara miki zama da kishiya ya ba ki hakuri da juriyar danne duk abinda zai kawo miki danasani." "In sha Allah amma Ammi na ƙarshen nan Ni........." Common ki yi na ce kuma ki daina kambama kishin hakan ke sa mata shiga uku,ke ko miji ne kika sa a gaba da fitina da shegen dube-duben waya ai baki da sukuni balle kuma wacce zama da ita ya zama miki dole." "To na ji."na furta hakan ina turo bakina gaba sam banda wadatacciyar walwala tunda ta ambato min kishiya tana datse kiran wata ta ƙara shigowa ganin Sarauniyar jijjida kan First Ramadan with HABIBI group ce ke ƙirana(Shamzee), "Egiyar gari ina kika shige ne 2days." Na koma ga Allah stop calling me with that stupid name." Shegiya na ce do what You can banziya kawai." Dariya na fashe da shi na ce"Allah ya shirya min ke Shamzee(Zainab ta Shamsuddeen.),Hope dai bakya azumi tunda na ji kina zagi." Ina yi sai dai in ke zaki min breaking na shi with Your shegen iyeyen tsiya." Annabi ne ya faɗa not Farrah so mind Your tongue. "SAW to na ji Astagfirullah wallahi ban taɓa sa nin zagi na karya azumi ba." Zan turo miki audio clif ɗin ta Whatsapp Habibi ya tutturo min." Zan kuwa saurara na gode,Kin san mai yasa na kiraki? No Shamzee Gidan wancan ƙawar taki Uztaziyyar muka je what that her name i even forget ma Billah." Hakeema. Yeahhh ita,shi ne kika sa mana ita a group ga shi kina shirin janyo mana asarar manyan classic ladies dan labarin ghetto Area da muka je muka sameta da muka bayar ya janyo cecekuce a group amma fa ta iya ɗinki gaskiya,kira na yi akan ki je ki cireta if not group ya tarwatse dan we can stay with Fakiriya gaskiyan magana a group." So what idan group ɗin ya tarwatse,talaka ba mutum ba ne da har zaku fita dan kuna amsa sunan Classic ladies,a matsayinku dana iyayenku me yasa ba zaku yi ƙoƙarin tallafa mata dan ganin kun cireta a halin da take ciki ba, Haka ne kuma fa wallahi balle in da ta birgeni ba maula take ba hajarta ta tallata amma duk da haka bata cancanci zama a cikinmu ba maganar Allah kawai ki cireta Ni dai. "Ba zan cireta ba because tama fiku cancanta da ta zauna a wannan group ɗin." Hujja Tana auren Social Uztaz the must richest guy a wannan town ɗin . You mean da gaske ne shi muka gani zai shiga wannan ƙazantaccen gidan rannan har yana gaishe mu muna wucewa,sai da muka shiga cikin mota muka yi ribas sannan Juwairiyya ke ce min Kamar"Social Uztaz." Na ce mai zai kawo shi wannan jujin amma Meyasa shi yin wannan basajar da matsayin shi da komai na shi. Neman mai son shi dan Allah. Aikuwa ya samu am happy For her yanzu kuwa zan je musu da sabon gist." Alright mu haɗu a group zuwa dare akwai shawarar dana yanke a matsayinku na ƴaƴan masu akwai ya kamata mu kafa gidauniya domin tallafar marayu da kayan sallah,start yours now. Me ɗin Investigation Akan me Akan gidajen masu ƙaramin ƙarfi a Unguwarku dan ki tallafa musu. Ba bu ai kin san a GRA nake. Ok zan je unguwar su Hakeema na da zan binciko the only thing da zan roƙe ku shine ku daure ku tallafa ku bada ƙalilan Allah zai baku kasiran. To malaman Ramadan."Kit ta kashe wayarta raina ya so sosuwa amma tuno da ɗimbin ladan da zan samu yasa na ji dole zan yi kuma insha Allahu sai marayu sun sa kayan sallah kamar yanda kowane ƴaƴa ke sawa.   (Dan Allah makaranta littafin nan ku taimaka ma marayu da kayan abinci,kayan Sallah gwargwadon iyawarku,ku tuna kuma watarana ƴaƴanku zasu zama tamkar su kar ku yi tunanin kun bar musu dukiya mai yawa idan wata musiba ta faɗa ma dukiyar fa,idan kuma sun rayu cikin daula ba lallai ne ma su tuna da ku ba tunda baku horesu da tausayi da jinƙan na ƙasa da su ba,talakawa na cikin wani hali a ƙasar nan ku taimake su da abinci da dukkanin abin buƙata kuma Allah zai yalwata muku a sanda babu mai taimakon ku idan bashi ba,ga masu buƙatar tallafawa kuma babu hanyar taimakon ma'ana unguwannin da suke rayuwa ba mabuƙata kuna iya tuntuɓata,kar dai ku manta da har yanzu Yusuf na littafin SUN GUJE NI yana nan yana rayuwa akan keken guragu duk da yana sa ran zai miƙe in kun tallafa, Allah ya bamu abin tallafama na ƙasa da mu alfarman Annabi.) HAKEEMA. Miƙewa yake da shirin yi na yi saurin janyo shi dan ina da tarin tambayoyin dake ƙunshe a ƙirjina dangane da shammatata da ya yi,sai dai yanda ya ruƙunƙune Ni ya hanani furta komai dan dole na gumtse bakina tare da rumgumar shi ina shaƙar daddaɗan turaren da ke fita a jikin shi har na ji ana horn a waje, Kafin ƙiftawar gira da bismillah zarata majiya ƙarfi suka bayyana a ƙofar ɗakin namu wanda alamu sun nuna masu tsaron lafiyar shi ne,gyara min zaman hijabin dake jikina ya yi tare da gyara min nikabin da ke jikin shi kafin ya saƙalo hannuna a cikin nasa muka fito,muna fitowa suka rufa mana baya, Motoci ne na alfarma guda uku reras a bakin ƙofar gidan yara sun kewaye su tare da yi musu daɓa-daɓa har muka fito, Umurtan ɗaya daga cikin masu rakiyar na shi yayi da yaga yaran nan kuɗi,dan haka ya fara yi musu rabon ƴan dubu-dubu before You know har manya sun shiga cikin sahu ganin abun bana ƙare ba ne yasa Social Uztaz ya umurce su da su shigo mu je gobe zai zo ya yi rabon kayan abinci,kayan sallah da gyara hanyar ruwa da samar da rijiyar burtsatsi da yin kwalta duk zasu biyo baya da yardan Allah dan a dan zaman da ya yi a wannan unguwar har kamuwa ya yi da zazzabin cizon sauro saboda yawan kwatoci da suka buwayi unguwar tabbas zasu ga aikin Social Uztaz soon. Iya na hango ta fito ba ko ɗankwali alamun labari ya risketa akan ana rabon kuɗi sai dai ƙurar motocin mu ta hango dan haka aka barta da cizon yatsa ta jikin madubi na hango ta na yi murmushi jin Uztaz ya matse min gefen ciki yasa na yi ƙara da sauri ya rufe min baki tare da ce wa"Idan kika kuskura kika karya min azumi Hajiya will make sure ta rama min."Sororo na tsaya kallon shi ganin yanda yake magana cike da shagwaɓa da sangarta tuni zuciyata ta ƙara dulmiya a cikin ƙaunar shi, Sannan na yi mamakin yanda ya iya yin basajar dawowa mafaɗacin ƙarfi da yaji,ban gama mamakin wannan ba sai da naga motocin sun tsaya suna horn a wani makeken Estate wanda ya yi gari guda,buɗe mana get ɗin suka yi sannan suka cilla motocin saman kwaltar da ke shimfiɗe,a daidai wani tamfatsetsen gida wanda na yi ma laƙani da aljanar duniya Suka yi parking nan take suka fiffito suna jiran namu fitowar,Uztazuna kuwa sai kallona yake yi ganin yanda na sake baki da hanci ta cikin nikabin ina kallo,lakuce min hanci ya yi kafin ya ce"Mu je ko Qalbee and kar ki badani wajen kallon nan naki Please a cikin Family kin ji You Are my choice forever and ever." Sunne kaina na yi alamun jin kunya sannan ya kama hannuna muka shige bayan ya dakatar da masu tsaron lafiyarsa,wani tamfatsetsen ƙofa muka dumfara bayan ya danna wasu lambobi gilashin ƙofar ya bude muka shige. Tun daga bakin ƙofa yake ƙwala ma Ummiee ƙira bayan mun yi sallama,jin bata amsa ba yasa ya ajiyeni a falo ya shige in da nake da tabbacin uwarɗakanta ne,buɗe manyan idona na yi ina kallon Royal chairs ɗin dake cikin ƙasaitaccen wannan falon,na yi saurin kai dubana kan katifa-katifar da ƙafata ke nutse a ciki na ga ashe kafet ne,ƙare ma ko'ina kallo nake dan har ga Allah Ni tunda nake a duniyata ban taɓa ganin gida mai kyan nasu Uztazuna ba sai dai a irin fina-finan ƙetare,jin motsi daga gefena yasa na yi saurin daidaita nutsuwata sai dai jin Muryar wata hamshaƙiyar mace da ƙamshinta yasa na ji kawai na raina zamtowata sirika a wannan gida ya kamani. Tuni na tsantsani kaina na takure waje ɗaya,yayinda take dumfaro Ni haka duk takun nata ke tafiya da bugun da zuciyata ke yi da sauri-sauri har ta iso gareni tana yi ma ni wani irin kallo....... To fah Fans ana wata ga wata mu je zuwa,ya dai kamata a samu wata ƴar aljannar ta haɗa mana document na littafin nan dan sama min sauƙi na gode. Ummu-jidda. FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z TSARABAN RAMADAN. Ka zamo mai kyauta, Amma kar kyautar ta janyo maka riya. LAMBA NA SHA TAKWAS. Har ta iso gareni tana yi ma ni wani irin kallo mai cike da tsantsan soyayya da sauri ta ɗagoni tare da rungumeni a cikin jikinta,Muryar Uztaz na ji yana ce ma Ummiensa"Wayyo Ummiee kar ki karya min ita bata da ƙarfi." Daƙuwa ta yi masa ya yi saurin ƙarasowa yana niyyar zuwa gurina na yi saurin hararar sa ƙasa-ƙasa ina yi masa gargaɗi da idona cikin sanyi Ummien ta fara yi min sannu da zuwa na yi saurin duƙawa na gaisheta cike da girmamawa,amsa min ta yi cikin sakin fuska da soyayya kafin ta umurci Uztazuna ya kaini sashenshi mu shirya muna da hadaɗaɗen buɗa baki wanda aka shirya na musamman domin taryata a cikin wannan zuriya mai albarka, Kama hannuna yake shirin yi ta yi saurin bige hannunsa tare da kama hannuna muka yi cikin ɗakinta ya yi saurin mara mana baya, "Ni dai naƙi wayon Ummiee ki bani matata kawai,ke fa kika ce in je mu shirya kuma kina shirin yi min ƙwalele." "Anƙi ɗin je ka faɗa ma Abbanka in yaso ya zo ya ƙwatar maka matar mara kunyan yaro kawai,ƙiri-kiri ka maidani kakarka ta ƙarfi da yaji." Ficewa ya yi fuuu ya barni da baki hangame cike da mamakin gidansu da tsarinsu mai cike da gamsarwa,ji na yi ina kewar nawa Mahaifiyar na ji hawaye ya taru a idona jin an dafani na yi fara ƙoƙarin maida shi,zaunar da ni Ummiee ta yi tana min hirar Social Uztaz, murmushi kawai nake zabgawa har ta kama hannuna zuwa banɗaki,sake hannuna ta yi  bayan ta nunnuna min yanda zan yi amfani da komai a taƙaice,saurin kai hannuna kan famfon na yi naga ya zubo ina cirewa na ga ya ɗauke a zuciyata na ce lallai duniya ta cigaba Allah ya azurta duk wani bawa da arzikin duniya dana lahira amma tabbas masu akwai suna walawa,gani dai a banɗaki amma kamar a wani ƙayataccen ɗaki nake,jin alamun motsi yasa na miƙa bayan na gama ƙare ma shahararren banɗakin kallo mai kama da wata daula, Shafe kusan minti talatin na yi ina cuccuɗa jikina da  sabulai masu ƙamshin gaske kafin na ɗaura tawul a kirjina na zuro hijabina na fito zuwa ɗakin bakina ɗauke da sallama,ba kowa sai kayan da zan sa a kan gadon dan haka na cire hijabin na fara shafa mai wanda rabona da shafa mai ai tun kafin azumi amma tunda na shigo gidan nan sanyin Ac yasa na mance da ana zafi ma hadda zama ina ƙalailaye jikina,ina cikin shafa na ji an turo ƙofar an shigo dan haka na dirirece sai dai ganin Uztazuna ta jikin standing mirror yasa na turo baki, Rungume hannun shi ya yi a kirji yana ƙare min kallo ta jikin madubi jin wani kasala na niyyar rufe shi ganin lafiyayyen fatata da rabin ƙirjina a waje yasa ya juya cikin muryan tsokana na ce"Ina zuwa rasa kunya." "Azumina zaki karya min Allah matuƙar na tsaya ina kallon wannan lallausan fatar naki."ban ce mi shi komai ba har ya fice nima na cigaba da shirina na gama sa kaya kenan wata matsashiyar budurwa ta shigo ta gaisheni kafin ta sauke jakarta ta fara tsamtsara min light makeup wanda ya yi matuƙar dacewa da round face ɗina, Warware ɗankwalin kaina ta yi ta min ɗaurin manyan mata kafin ta ciro wata alkyabba a kwali ta warwareta ta samun bayan ta umurce Ni da ,miƙewa,baƙace adon dake gabanta golden ne,dan haka sarƙar da ta sa min da ɗan kunne ya kasance golden takalmi ma haka, turarurruka masu sanyin ƙamshi ta feffesa min tare da gyara min zamar hular alkyabbar a kaina. Fatubarakkallahu ahsanu khalikin!Gaskiya matan Social Uztaz ke kyakykyawa kuma kin yi dace da samun miji nagari. Murmushi na mata bayan na ɗago fuskata na kalli kaina a madubi,gani na yi kamar bani ba dan Ni kaina bansan haka nake da kyau ba sai yau,da man Ni fara ce dan haka adon baƙin kaya da brown na leshin ya fito da Ni. Chanchaɗi!Muryar Uztazuna ya daki kunnena na yi saurin ɗagowa ina ƙare mi shi kallo dan shigar shi mai kama dana Yarima ya yi matuƙar tafiya da imanina,baƙin yadi ne kofta aka mi shi ado irin na sarakuna a ƙasan wandon da hannun sai gaban rigar sai farin gariyar da yasa wanda tasha aiki kamar daga Mali(Daga Zaria ne kun san nan ma muna da ƙwararrun masu aikin hannu da designers)Hular shi mu haɗu a banki ya kafa mai ruwan fari da baƙi sai ɗigon ruwan kunkumadi a jiki,sai half Cover daya sanya baƙi mai design ɗin aikin da ke jikin shi,nan take na ji haiba da kwarjinin shi ya cika ruhina dan haka na yi saurin yin ƙasa da idona ina gode ma Ubangijin sammai da ƙassai, Ɗagoni ya yi yana shaƙar daddaɗan turarena duk da tun daga shigowar shi ƙamshim shi ya buwaye mu,hoto ya fara yi mana ganin yanda muka zamto zara a cikin taurarin da ke sama, Ban san lokacin da mai min kwalliya ta zurare ba dan zuciyoyinmu ya yi nisa Ni da Uztazuna sai jin muryan Ummiee na yi na fara kiciniyar ya cikani yaƙi, Murmushi Ummiee ta yi irin nasu na manya kafin ta ce"Sai hakuri ba ɗiyata dan wannan da kike gani ba kunya ce da shi ba sai du'a'i." Zumburo baki ya yi zai yi magana ta yi saurin nuna mi shi agogon dake ɗaure a jikin hannun shi(Rollex)ganin lokaci ya tafi yasa ta yi gaba muka rufa mata baya. Faffaɗan falo wanda zai iya cin mutum ɗari hadda ɗoriya muka shiga,nan muka tarad da mutane zaune akan daddumomi na alfarma suna jiran isowar mu,tada salla aka yi muka bi sahu dan lokacin shan ruwa ya gabato,ana idarwa Uztazuna ya ja hannuna zuwa gaban Alhaji Bisallah muka durƙushe muka yi gaisuwa, addo'o'i ya dinga sharara mana kafin aka fara shigowa da abin buɗa baki kamar mutum dubu ne zasu ci,ɗaukacin ilahirin Ahalin su ne a wannan Estate ɗin kuma alhamdulillah duk sun hallara an gabatar musu da Ni a matsayin matar Uztaz wasu sun karɓeni hannu bibbiyu wasu kuma ta ciki na ciki musamman kishiyoyin maman shi dake jin kamar su shaƙeni in mutu,an ci an sha kuma an mana nasiha mai gamsarwa nan take aka dinga bina da kyaututtuka na alfarma. Ganin na gaji yasa Ummiee janyeni muka shige ciki kamar jira yake mu shiga ɗakinta ya biyo mu cike da gajiya ya ce"Ya kamata mu kwanta, Allah na gaji."ya furta hakan yana cire babban rigar dake jikin shi da hular yana mai kwanciya akan gadon Ummiee . Oh ni ƴar nan me haka kuma goɗoɗo da kai a gadona dan Allah,na ga abinda ya isheni bai ishi Allah ba." Dariya ya shiga yi ya ce"Nima yau anan zan kwana a gadon Ummieena." "Saboda matarka ko?"ta tambaye shi ya fara sosa ƙeya yana dariya ƙasa-kasa sunne kai na yi ina jin tamkar ƙasa ta buɗe in shiga dan kunya dan sam Uztazuna bai da ta ido ina cikin tunanin hakan na ji Ummiee ta ce"Ƴar albárka tashi kije ku kwanta kin ji." Ya daka tsalle ya miƙe tare da ɗaura min babban rigar shi a jikina ya riƙe ƙugu alamun in miƙe,bin shi da throw pillows Ummiee ta yi da sauri ya yi waje yana dariya,ganin naƙi motsawa yasa Ummiee ta ce"Tashi ki bi mijinki kinji ina jin motsin shi a falo." Ni a nan zan kwana." Kul ɗinki yanda mijinki ke son ki da mararinki sam kar kiyi wasa da damarki na riƙe shi gam-gam dan maza tsada suke a wannan lokacin ko so kike ya miki kishiya." Na girgiza kai tare da rufe idona da tafukan hannuna guda biyu,nan take ta shiga yi min nasiha da yanda zan kula da mijina tare da faɗa min duk wani abinda ta san Uztazuna na so tun daga girman shi har yarintar shi,hannuna ta kama ta fitar dani daga shashinta tafiya mai tsawo muka yi har muka riski sashin shi wanda tun daga ƙofar shiga na ga alaman yafi na Ammi haɗuwa har cikin falon mai kama da aljannar duniya ta shigar dani jin alamun motsi daga cikin banɗakin falon yasa ta zarce da Ni uwarɗaka,anan na saki baki da hanci ina ƙarema gadon shi mai siffar mota kallo jin na lumtsuma akan katifar dake ɗaure akan yasa na jini a wata duniyar na daban nasiha sosai ta yi min kafin ta fice bakinta ɗauke da albarkar da take ta sanya min dan tun data ɗaura ido akaina ta ji na kwanta mata arai ta ji tana min kwatankwacin ƙaunar da take yi ma ƴaƴan cikinta,shiru na yi ina nazari can dai na ɗakko wayata na buɗe data dan ganin wainar da ƴan group ɗin First Ramadan with HABIBI ke toyawa. Hirar su na dinga bi ɗaya bayan ɗaya har na ƙara so kan hirata da yanayin gidan hayar da nake ciki bayyanar social Uztaz a matsayin mijina ya yi matuƙar ɗaga musu hankali,dan basa sona sam tunda Ni talaka ce sai ga shi Allah ya azurtani da samun miji wanda ya wuce tunaninsu,ƙalilan ne daga cikin su suka tayani murna Farrah ita ce kan gaba kafin aka dawo tattaunawa dangane da tallafin marayu da Farrah ke son wakilta, ya samu karɓuwa ba laifi sai dai an samu masu kushe tsarin, Tun ina zaune har na kai ga kwanciya dan saƙonnin sun yi yawa,duk wanda ya kamata in mi shi reply na mi shi sannan na fita a group ɗin,duba Farrah na yi naga bata online dan haka na ajiye mata saƙo zuciyata cike da tunanin meya hana Uztaz shigowa wajena,rage kayan jikina na yi na faɗa banɗaki na shirya a gaggauce kiciɓus muka yi da shi yana shirin shigowa gurina ya yi saurin cafkoni ya min ɗaukar jarirai bai direni a ko'ina ba sai a kan gadon shi nan muka fara mulmula ganin ina shirin faduwa yasa ya yi saurin kamoni ya rungume. Godiya ga Allah ya fara yi min sannan ya bidi da in faɗa mi shi komai nake so ya min a wannan duniyar matuƙar bai fi ƙarfin shi ba zai min. Shiru na yi ina nazari cikin sanyin murya na ce"Fashion House nake son ka buɗe min,a zuba min industrial machine tare da ɗaukan kwararrun teloli wanda sun iya ɗinkin amma ba su da halin buɗe shago,za mu dinga sayar da yadi,in ka saya mu ɗinka maka sannan zamu dinga saida ready made da kayan ɗinki." An gama Hakimar Zuciyata Your wish Is my command Biliyan uku ya isa?" Biliyan?ya ɗaga min kai ganin ina mamaki yasa ya ɓata fuska cikin sanyi na ce"Idan Allah ya sama wannan sana'ar albarka gidan marayu zan buɗe wanda da ribar da muke samu zamu dinga ɗaukar ɗawainiyarsu tare da inganta rayuwarsu. Sakin baki ya yi yana kallona cikin murya mai sanyi ya ce"Fara mai farar Aniya,zuciyarki fari burinki aikata alhairi,kin goya ƙannenki yayinda kike hana idaniyarki bacci domin ganin rayuwarsu ta inganta yayinda mata ke burin mallakar gidaje da motoci na alfarma tare da suturu ke kuma burinki ki share hawayen marasa gata,tabbas rayuwarki abin koyi ce ga duk wanda ke da dama irin taki Allah ya albarkaci rayuwarki." "Amin ya rabbi,mallakar abin duniya bashi ne abu mai muhimmanci ba saboda duk abinda ka tara anan duniyar zaka barta,babban guzuri a ranar lahira shine sadakatul jariya ." DIYAN HABIBI. Ummu-jidda FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.   💔Heart touching story.💔 FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA). *ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION* https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z ƘARSHEN LAMBA. DIYAN HABIBI. Yanzu gabaki ɗaya haske ya baibaye rayuwata tunda na fara neman ilimin addinin musulunci hakan  yasa ko zama a  online ya daina damuna,yanzu haka ina zaune ne ina kallon wata tasha in da ake bayani akan wafatin Nana A'isha matar Manzon Allah wanda lamarin ya faru ne a cikin wannan wata da muke ciki na Ramadan wayata ta yi tsuwwa,ɗaukarta na yi sai dai ta katse dan haka nabi numban da kira amma bata shiga sai dai guntun saƙon da ya biyo baya daga Hakeema kamar haka"Na ajiye maki saƙo a Whatsapp and Habibinki zai baki wadataccen kuɗi da zaki iya wadata marayu dubu da kayan sallah sai dai ki sa lura gurin rabon kin san wasu da haɗama,yanzu haka muna Airport za mu Umura da Uztazuna ki yafe min in na taɓa miki laifi."Kabbara mai ƙarfi na yi tare da durƙushewa na yi  sujiudar godiya ga Allah mahalicci sannan na miƙe na zauna, farinciki biyu zuwa 3 ne ya zo min lokaci guda na farko samun ni'imar da Hakeema ƙawata ta yi duk da ba wani ɗasawa muke yi ba dan ta cika iyeyi komai ta ce Allah sai kace Allah nata ne ita kaɗai, lokacin haka nake cewa saboda rashin fahimtana da addini,na biyu shawarar Habibina Uztazu ya bi har ya kai wannan matakin na samun Hakeema a matsayin matar shi duk da Habibi bai taɓa faɗa min plan ɗin Uztaz ba sai da abu ya bayyana sannan yake sanar da ni,na uku cikar burina na zamtowa bango majinginar marasa gata,baya mai goya marayu ya tabbata dan haka tuni na buɗe data na hau domin duba sakon Hakima,godiya ce ga Allah tare da ƙarfa min gwiywa akan aikin Allah dana assasata, sai biyo yi min babban albishir da ta yi akan Uztazu ya naɗa Mijina matsayin Manaja na babban kamfanin su dake Jahar Kano ta dabo babban birni yaro koda mai ka zo an Fika sannan an ba shi kwangilar gina Fashion House da samar da duk abinda ake bukata tare da gina gidan marayu,Ni kuma ta naɗani matsayin mataimakiyarta wanda tun daga Rana Mai kamar ta yau in fara tattara marayun da na  tabbatar sun rasa iyayensu dan a shirye take ta tallafa musu da dukkanin wani ƙarfi wanda Allah ya bata, dan wata 3 kacal aka ba Habibi ya kammala gina wannan shararren Fashion House ɗin tare da gidan marayu,albishir ɗin salaryn mai tsoka ta yi  min nan take na ƙara jinjina lamarin Allah tabbas kowani mutum da baiwar da Allah ya mi shi ga shi dai Hakeema dana raina yau ita ce ta ɗaga likafata gaba tunda ta samar ma mijina babban aikin da zai riƙeni ya riƙe Ahalin shi gabaɗaya,ita da bata yi zurfin ilimi ba na boko ita ce mai ba mai degree aiki(Ni kenan.)Tabbas na jinjina lamarin Allah zuciyata ta ƙara sakankancewa da Allah buwayi ne gagara misali. Koda Ammina ta ji madarar albishir ɗin dana yi mata take yanke ta fashe da kuka jin dare ɗaya Allah ya yi Bature ma'ana Habibi ya tashi daga talakan da take ƙi ya dawo babban mutum dan kwangilar da aka bashi kaɗai ya isa ya tabbatar da yanzu ya shiga cikin manyan mutane tunda ya zama na hannun daman Social Uztaz ɗan Alhaji Bisallah bata ƙara shiga cikin farin ciki ba sai da taji irin aikin alhairin dana assasa da karɓuwan da ya samu nan take ta ce"Ita ma zata bada Tata gudummawar ta hanyar duba lafiyar marayun kyauta sai dai a siyo magunguna ."tunda likita ce ita,nan fa wani daɗin ya ƙara rufeni na ƙira Hajiya Amina itama na sanar mata da Abbiynmu,nan take Hajiya Amina ta lissafo min matan da mazajensu suka mutu wanda ta sani aka bar mata da yara sun kusa ishirin jin ita ɗin mai jama'a ne yasa na ce dole mu haɗa hannu da ita da  yin wannan aiki na alhairi,koda Habibi ya shigo sosai muka taya juna murna,nan take muka zauna muka tsara jadawalin yanda abubuwan zasu kasance,harkar yadi abokin shi Sayyadi Ali ya ba wannan kwangilar sai nemo teloli masu amana wanda cikin sati guda kacal zasu ɗinka ma yaran kayansu takalma,hijabai, ɗan kunne duka ya sayo su dan haka washegari za mu shiga gari dan fara wannan aikin alhairin,ban yi ƙasa a gwiywa ba gurin sanar ma ƴan First Ramadan with HABIBI nan take wasu suka amsa kira dan haka washegari muka shiga cikin unguwan marasa ƙarfi muka fara zaƙulo marayun da ke a galabaice Ammie ta fara basu kulawa tare da kayan abinci masu gina jiki, Ƙauyen dake arewa da garinmu muka shiga nan fa muka tarar dá babban tashin hankali wanda yawanci mutanen ƙauyen sun yi Ridda saboda Malamai basa bin ƙauyuka yin da'awa kiristoci kuwa suna kai musu tallafi na abinci da suturu kai har ma da kuɗi tare da tallata musu addininsu nan take suka koma faɗin"Yesu Almasihu."su fara bautar wanin Allah. Dawowa gida muka yi jiki duk ya yi tsami koda na sanar ma HABIBI halin da ake ciki nan take ya fara buge-bugen waya,abinka da lamari na ƴaƴan canji tuni ya samu matasan yara malamai aka haɗa mu dasu washegari muka je muka musuluntar da  dayawa daga cikinsu,dake cikin ƴan group ɗin First Ramadan with HABIBI akwai matan manyan ƴan siyasa har alƙawarin samar musu da tituna da magudanan ruwa da tsaftataccen ruwan sha suka yi kuma cikin ikon Allah ya tabbatu dan da muka koma rabon kayan sallah ma marayu da gajiyayyu da mabuƙata tuni muka ga an fara aiki. Komai muke yi muna da mai ɗaukar mu video coverage ganin zirga-zirgan ya mana yawa yasa Habibi ya bude mana temporary Office a shagon dake ƙofar gidana na karɓan record ɗin duk wani Maraya dake Unguwar mu da unguwar dake nesa da mu ma,al'umma sun tuttuɗo ciki kuwa hadda waɗanda ba marayun ba duk an taimaka daga ƙarshe har sai da muka fara neman taimako Uztaz na ji ya ƙara ƙaro mana wasu dalolin, Cikin ikon Allah haka muka gudanar da goman ƙarshe na wannan wata cike da ayyukan alhairi masu gamsarwa dan tabbas marayu sun dara kuma sun samu aikin yi ƙarƙashin wannan cibiya,masu dayes da kitso da ɗinki duka mun samu daga cikin marayun suna yi ma takwarorinsu ƴan yuyuyu kuma mun biyasu,Hajiya Hakeema da kullum nake tura mata Video ta Whatsapp tana ganin ayyukan alhairin da mijinta yake yi da sunanta kuka take fashewa da shi a mafiya yawan lokaci tare da gode ma Allah da gode min da wannan kyakykyawan tunanin da yazo min ita kuma ta ƙaddamar,Ni kuma Habibina nake rumgumewa kuma duk sujjadata da addu'o'ina rabi na nema mi shi yardan Allah ne shi da iyayena tare da addu'ar Allah ya sanya shi a aljanna da ya zama Silar shiryuwata,ta bangaren shi kuwa ittaƙafi ya shiga Ni da ganin shi sai ranar Sallah a ganina tunda Allah ya bamu duniya ai da ita zamu nemi lahirar dan haka sam ban so ya yi nisa da Ni ba,kalmar dai da ya faɗa min ita ce"Wata duniyar abin gudu ne Gara mu nemi lahirar dan ita ce abin nema tunda can ne gidanmu na asali,Dukiya da ƴaƴa duka musiba ce a garemu matuƙar zasu hanamu ambaton Allah."jin haka yasa na bi shi da fatan alhairi nima kuma na zage dantse ina ta addu'a gwargwadon wanda na iya sam bana bacci da dare dan in samu in riski wannan dare na lailatul kadri. A SAUDIYYA. Ni Hakeema Ni ce rumgume da kaba'a ina kuka tare da nema ma Mahaifiyata gafara,Abbana wanda tare da shi muka zo dan tunda labari ya riske shi akan basajar da Uztazuna ya yi ya nemi ya dawo masa da ni gida,sam bai Mu sa ba ya ɗauke ni ya kaini Sannan ya mi shi gamsasshen bayani dangane da lamarin da yasa ya yi haka, ya gamsu tare da bin mu da kyakykyawan addu'a tare da fatan alhairi,a ranar aka mana cuku-cukun samun passport tare da biza cikin kwana biyu muka ɗage bayan Uztazuna ya aura ma Abbana wata matan dake kula damu mijinta ya daɗe da rasuwa maƙwafciyarmu  ce kuma aminiyar mamanmu dan tunda Mamanmu ta rasu Abbana yaƙi aure shekara goma sha kenan, dan haka tare da ita aka bar ƙannena mu kuma muka shillo cikin wannan alƙarya ta ni'ima da rahama. Sosai na zage ina addu'a ba dare ba rana dan haka wata irin nutsuwa ke shigata surfa-surfa ji nayi a jikina tabbas wannan dare ta kaddara alhairi da sharri na risketa saboda yanda na gudanar da ibadar cike da sakankancewa nan take ƴanuwana Teloli suka faɗo min a rai ganin Ni ce yau ke ɗawafi a gaban ka'aba bayan na saba duk goman ƙarshe ina nan kan keke Sallah ma ta farilla fizgar jiki nake in yi  shi da ƙyar saboda aikin da yake min yawa, sam bana raya wannan dare da wata ibada babban burina in kammala kayan mutane dana kakkarɓa da wannan kuɗin nake samun inyima marayun ƙannena ɗinki da sauran hidimomin dana wajabta ma kaina yi musu dan Mahaifinmu miskini ne duk da sam baida mutuwar zuciya amma samun shi ya yi ƙaranci Ni ce babban ƴar shi dake tallafa mi shi, Hawaye na ji yana bin fuskata nan take na fara suburbuɗo ma Teloli addu'ar fita daga ƙangin talauci wanda duk shi ke sanya su ƙuƙewa su yi dan wannan lokacin shine lokacin samuwarsu,ta baya na ji an taɓani ina juyowa na ga Abbana ne zaune akan keken guragu Askarawa na tuƙa shi ,hawaye na ji ya zubo min saboda irin addo'in dana ji yana fita daga bakin shi mai albarka akaina da mijina,ganin hakan yasa Uztazuna ya taho gurina dan lokacin komawar mu gida ya yi dan haka muka tari taxi muka shige sai masauki tare da Ummiee da Abban Uztaz muka yi buɗa baki cikin farinciki da walwala. Duk tarin gajiyar da muke ciki sai da Uztazuna ya ƙara tsumani da soyayyar shi mai tsayawa a rai dan ya ce"Babban burin shi mu samu ciki a garin Madina."aikuwa anan ɗin Allah ya azurtani da samun Madaniyya (Fatima)idan namiji ne kuma za mu ƙura shi da suna Shakur(Muhammad)kenan. A haka har muka kammala ibadarmu cikin ɗimbin nasara muka dawo ƙasar mu ta gado bayan Sallah,na yi ƙiba na yi mul-mul dan sam cikin ba mai laulayi ba ne sai ma wani haske da cika daya sani,a sabon gidan mu mai kama da wata masarauta a Dubai tsabar tsaruwa muka tare in da Farrah ta fara kawo min ziyara, rumgumar juna muka yi Ni da ita hawaye kwance akan fuskar mu dukkaninmu rayuwar mu ta baya muke tunawa, Uztaz da Habibi da suka shigo hannayensu cikin na juna dariya suke mana,sai dai Hakima hawaye yaƙi barin fuskarta har sai da Uztazu ya fara yi mata nasiha cikin daddaɗan murya sannan ta shagwaɓe fuska ta ce"Naƙi yin shirun har sai ka fadamin."ta fashe da wani irin kukan tabara take jikin shi ya fara rawa a diririce ya ce"me kike son in faɗa maki?", "Wanda ya koya maka basajar zama Uztaz." Dukkanin mu dariya muka fashe da shi dan Ni har ga Allah na ɗauka wani abin ne na daban ta ruɗa ɗan talikin nan a gaban idonmu ko kunyar Habibi bata ji ba, Ganin tana niyyar fashe mi shi da wani kukan ya sa ya ce"Wait my lady Please kar ki  koya ma yarona rigima Ni kam,zan faɗa miki."Murmushi ta yi bayan ta bamu guri mun zazzauna haɗe da abin sha ya ce"Daman dai sunana ne Social Uztaz kamar yanda ki ka ji abokaina na ƙirana da shi saboda na tsani duk wata saɓon Allah duk da kasancewata shahararren ɗan boko dake na ƙoshi da ilimin addini yasa duk wata wayewa ta Bature na san koma bayan namu ne dan haka a komai nawa Addinin Musulunci a gaba sam ban damu da akida ba,Ni dai kowace Aƙida kake a gurina in dai kai Musulmi ne zan yi aiki da kai dan haka sunan ya samo asali ne tun daga rayuwar mu ta jami'a, dangane da basajar da na miki kuwa na Uztazanci shiga cikin su na yi na gabatar ma babban Malaminku buƙatana nan take ya yi maraba da Ni ya rungume ni hannu bibbiyu,cikin kwana uku kacal na dawo yanda zaki so Ni larabci kuwa shine course ɗin da na fara karanta a jami'a dan haka ina jin shi fiye da tunaninki." Ma sha Allah yanzu na ji magana amma da kullum Inna tambayeka sai dai ka yita kame-kame."dariya kawai muka yi nan muka fara sabon gaisuwa bayan mun nitsa muka gabatar da ayyukan da muka gudanar da basa nan suka gani,sun yaba da ƙwazonmu da Himmarmu dan haka bizar mu na tafiya China yana fitowa na yi ma HABIBI rakiya ya je ya yi odar kekuna,kujeru da duk abinda Fashion House da gidajen marayu zai buƙata acan cikin dake maƙale a marata ya bayyana in da tashin zuciya ya hanani zaune da tsaye,murna a wajen Habibi ba'a magana bayan mun zaga gari mun gagga wajaje muka biyo jirgi muka dawo ƙasar mu ta gado.   Alhamdulillah cikin watanni ukun aka kammala ginin har gashi yau ana bikin buɗe Fashion House da gidan marayu,taro ya yi taro in da hadda mai girma gwamna sai da ya samu halartar bikin buɗe gidan Marayu mai suna"HAMSAL ORPHANAGE AND FARRAH FOUNDATION",Sarkin garinmu shine ya zama babban baƙo,manyan attajiri da masu hannu da shuni duk sun samu halartar bude Gidan marayu da GIDAUNIYAR da Farrah ta buɗe na tallafa ma gajiyayyu,an ci an sha zuciyoyin ilahirin Ahalin mu duk sun sanyaya,masu hannu da shuni da manyan yan kasuwa sun zuba hannun jari a HAMSAL(Hakima Bisallah) FASHION HOUSE dan kara mata karfin gwiywa akan ayyukan alhairin da ta yi,mai girma gwamna ya samar da nagartattun ma'aikata ma marayu na gidan dan akwai katafaren makarantar boko tun daga matakin Nursery har zuwa Sakandire da babban makarantar addini wanda ya tara manyan malamai,sai asibiti da Ammi ta zama babban likita Hajiya Amina kuma ta zama uwar Raino mai ba yara tarbiyya saboda sanyin halinta,tabbas labarin wannan taro wanda gidajen rediyo dana jaridu har ma dana talabijin ya ja hankalin mutanen arewacin ƙasar nan musamman yanda ƴan group ɗin first Ramadan with HABIBI suka gayyato manyan jaridun online aka watsa shi a media,Hajiya Farrah da Habibinta sun zamto abin kwatance a cikin al'umma yayinda HAMSAL da mijinta suka fi ƴan siyasa farinjini. Tammat bi hamdillahi wa husni aunihi wassalatu wassalamu ala Mustapha Abul ƙasim Muhammadur-rasullullah, Muhammadur-rasullullah wa ala Alihi wa sahbihi wajma'in.   Ina mai godiya ga Allah da ya bani ikon kammala rubuta wannan littafi Mai albarka, JINJINA. *Jinjina ga ɗaukacin marubuta na hannun damana Musamman Malamaina waɗanda idan sun ga kuskurena basa sanya gurin gyara min Oga Bamai dabuwa,Malam Mubarak Saulawa,MALAM JIBRIN RANO,Sarauniyar tsokana(Hajara Oum Nass)ina godiya a gareku Allah ya ƙara muku ɗaukaka da tarin nasarori.* *Kakata Hadiza D Auta gaisuwarki ta musamman ce saboda kin tsaya tsayin daka hadda tare min faɗa akan rubutun wannan littafin Allah ya saka miki da alhairi ya kuma bar soyáyyá a tsakanin mu tabbas kina da kishin marubuta ƴan'uwank*i. *Jarumar jarumai.* *Sarauniyar jarumai writers wato Maman Amatullahi tabbas kin ciri tuta kin kasance abokiya mai ƙoƙarin ƙarfafa min gwiywa a duk inda na ji rauni,ina godiya da muhimman shawarwarinki wanda tabbas ba dan ke ba da tuni na ajiye rubutun wannan littafin Allah ya raya min yarana ya kuma sa musu albarka,fagen rubutu kuwa Allah ya kara basira da ɗaukaka* USMAN IlIYASU MAJIDAƊI. Ka kasance ƙashin bayana mai kara min karsashi a duk lokacin da na yi niyyar kwantawa tabbas kana ɗaya daga cikin sirrin nasarata Kandenmu,Ubangiji ya azurtaka da samun mata ta gari ya jiƙan Abba da Hajiyata ya kuma yalwata maka samunka ya shirya mana kai shirin addinin musulunci alfarman wannan wata mai albarka. Kungiyata Abar alfahari na. Jinjina gareku gabaɗayanku,shugaba Pinky Cutie,Dotana Jidda washa,Jikalle Hilfat,sirikata Matar Sayyadi, Shalelen....,FATIMA,Laurat da saurann duk waɗanda ban ambata ba ina godiya. MARUBUTA. Gareku Marubuta ina godiya da karfafa gwiywarku da juriya da bibiyata duk da raunina musamman S Fulani daddyn dota,Hajara,Rukayya Ibrahim Gazawa,Qamshi and co Allah ya saka da khairan ya kuma karbi ibadanmu. Masu share. Musamman Hajiya Maryam da babban admin na hairan and teddys palace ina godiya ɗan'uwana,Fatima Abubakar Saje da ma wadanda ban ambata ba jazakumullah. *First Ramadan with HABIBI group 1 and 2*   Kun ji jarumaina,masoyana,ƙawayena masu ƙara min ƙarfin gwiywa,tabbas yawanku ya yi yawan da ba zan iya ambatar sunayenku ba dan kar ku ce na yi son kai,kun dai san kanku dotas ɗina,ƙawayena,ƴan'uwana marubuta da sauran Fans ɗin a masu hana wayata motsi saboda hira,dukka ina yinku Fisabilillah, Allah ya barku da mazajenku har a aljanna ƴanmatan dake cikin gidan kuma Allah ya baku mazaje na gari. HADIZA AUTA PALACE. ƁARIN ZANCE...... TAWA SOYÁYYÁ... JARUMAI.......da dukkanin group ɗin da littafin nan ke zagayawa ina sonku fisabilillahi,ƴar garinmu ina godiya, Amarya kuma Uwargidan Abban hydar (Malama Zeenatuddeen Musa)ban mance da ke ba da addu'arku nake taƙama,Muhd Sabi'u (Jauro)ina godiya da karamcinka tare da ɗan'uwsnka Fulani Abdul Faskari Allah ya bar zumuncin dake tsakanin mu har gaban abada. KUNE A ƘARSHE. Masu zagina saboda na yi typing a watan Ramadan,na yafe muku dan kune tushen nasarata Allah ya shirye Ni daku gabaɗaya. Littafin First Ramadan with HABIBI sadaukarwa ne ga ruhin mahaifina da ruhin da ke kwance a ƙasa, Mahaifiyata dake rayuwa Aban ƙasa,Allah ya ƙara mata tsawon rai da lafiya mai albarka,Mahaifina kuma Allah ya jiƙan shi ya gafarta mishi. A dalilin AUREN JARI matata wacce na aura saboda yi ma mahaifiyata biyayya Ita da abokaina SUN GUJE NI saboda cutar lakka dana kamu da ita sai dai kuma SANADIN FACEBOOK na haɗu na dubun dubatar masoya, ITA CE SILAH(WAYAR ANDROID) da ta zamto min fitila har na yi SOYAYYA LOKACIN KULLE(SOYAYYA A LOCKDOWN)sai dai na gagara gane LAIFIN SU WAYE tsakanin BESTYN MIJINA da danginsa,duk da dana yarda da MUTUNCINA YANCINA ne da ban watsa sirrina a social Media ba da ban zama shugaba a cikin  group ɗin Amaren First Ramadan with HABIBI ba har na zamto fitilar data haska rayuwar HAMSAL,danasi ya riskeni dana yi YAWON TA ZUBAR a ƙasa mai alfarma(Saudiyya)a cikin wata mai alfarma kuma a goman ƙarshe da sunan zuwa Tahajjud duk da na san  babban zunubi ne da ba zan yafe ma kaina ba. To masoya gani gareku ɗauke da sabon salo cikin littafina mai suna YAWON TA ZUBAR  littafi ne da ya taɓo rayuwar yara mata ƴan talle da wadanda ake safarar su  zuwa Saudiyya aikatau domin samun abin duniya.shin kin shirya mallakar naki/naka akan yan'kudi ƙalilan? To ku tsumayeni Ranar sallah zai zo muku a matsayin Barka da Sallah masoyana, dangane da BESTYN MIJINA Book 2 shima yana nan zuwar muku da yardan Allah sai dai book 2 paid book ne,maza garzayo ka nemi na farko in baka karantaba ba domin cigaban shi na nan tafe,taku ce har kullum Ummu-jidda. Ummu-jidda.