[8/26, 11:21 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* _(LOVE IS BLIND)_ 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 Assalamualaikum warahmatullah, ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. My first novel, ina fatan zaya nishaɗantar da ku haɗi da ilimantarwa, short an romantic novel. _Written by_✍️✍️✍️✍️ *Qwinn minerhly* Part 1-5 Noor !noor!! nasir ne yake ƙwala mata ƙira da misalin karfe 6:30pm a wani katafaran babban hotel wanda ya haɗe, da duk wani abu na more rayuwa aciki wato A N N palace hotel (ASHMIR NASIR NOOR) PALACE HOTEL. nan ya hangota akan wani resting cheer tana lilo haɗe da hot coffee a hannunta tana sha, tana hangoshi tace “yaya nasir what happened?" Yace “bansaniba, tun ɗazu naketa neman ki”. shagwab’e fuska tayi tace “to yaya nasir meye laifi na dan nazo nan, nifa hutawa ta na keyi“, yace “gud ba laifi, dama tambayarki zanyi ina babban yaya yake?” taɓe baki tayi, sannan tace “maybe yana chan gefen sweeming pool yana wanka kasan babban yaya akwai son wanka kamar shark” ta karasa fada ta na dariya," Nasir yace “wlh ba ruwana, ke kika sani idan yaji ki” riƙe baki tayi tace “ni na isa ma nafada har yajini hmm babban yaya ba sauki”. Juyawa Naseer yayi yace “Noor am coming” tace “ina zaka je” yace “zan danga managers ɗin gurin nan ne” ya faɗa haɗe da juyawa," tace “alright sai ka dawo. Kwance yake akan resting chair by the pool side, ya ɗaura hannun sa a karkashin Kansa, staring at the cloudy sky, iska ne mai cike da ni'ima da saka zuciya natsuwa ke kaɗawa hakan yasa flowers da tall trees din da ke gurin kadawa. His eyes are closed, amma ba barci yake ba idan kayi ma sa kallon tsaf zaga gane yana da sihirtaccen kyau,his thick eyelashes zara zara, eyebrow ɗinsa kuma so thick and black kamar Wanda yayi caving, his pointed nose and cute pink lips kamar wadan da aka shafa ma lipstick, he is a body builder dan jikin sa a murde yake, sanye yake da all black armless shirt sai 3/4 trouser shima black. Haɗaddiyar sweeming pool ne, wanda ke zagaye a gun, mai cike da kayan alatu, na more rayuwa, wato VIP ɗin gurin, guri ne aka ta nade shi na musamman, domin manyan mutane irinsu ashmir, Shi kaɗai ne agun, ko masu gadin shi ya kore su, a cewar shi baya son hayaniya, hmm babban yaya kenan. Tsaki yayi jin wayar sa na ringing for the 5th time kafin ya dauka amma bai ce komai ba sai dai yana sauraron abunda ake fada daga daya side din, after like 3 minutes “ok” kawai yace cike da yanga kafin yayi hanging off. *Sanye* take da kayan sarauta a jikin ta red nd black wow abunka da farar mace sai kayan suka amshi jikin ta tayi wani mugun kyau sai sheki take ga kamshi yana tashi ajikinta, sai shan kamshi take ko magana bata son yi sbd sarauta amma fa akwae tsiwa gimbiya kenan yar sarki wato PRINCESS NEEHAL. se kuma tawagarta da suka rakota gurun shakatawar kasancewar yau weekend ne, niko nace yayan masu dashi dai akwae son hutu, Juyowa tayi ta kalli bayinta cike da isa da izzar mulki “tace ku dakata daga nan” sukayi cirko cirko kuwa ita kuma ta nufi VIP SWEEMING POOL CENTER ga sign board a gurun, tana zuwa ta iske masu gadin gurun sai ko kallonsu batayi ba tace masu zan shiga vip ne, sai babban ya durkusa har kasa yace “mata ranki ya daɗe ahm kiyi hakuri wlh babban yaya ne aciki wato yallabai” sakin baki tayi tana kallonsa, waye kuma babban yaya? To ko ma waye shi wlh sai ta shiga, sabida itama tasaba idan tazo gurun nan take zuwa, kuma itama bata son hayaniya ita kaɗai take kama gurun. sai tace masa “dallah malan matsa kabani guri na wuce dan wlh babu wanda ya isa ya hanani shiga gurin nan yau” shidai da yake duk suna tsoranta sai ya matsa mata yabata hanya ta wuce, tana shiga gurun ta samu wani resting cheer ta zauna tana shan wani hadaddan ice cream wanda aka ajiyewa babban yaya wato ashmir, kuma hankalinta kwance batada damuwa kona sile daya, shikuma gogan duk wainar da ake toyawa yana gani a wani karamin system din dake gabansa hhmm ashmir knan, Sukuma masu gadin gurun suna chan sunata gulma sun rasa yanda zasuyi yau sun shiga ukunsu, ga dan governor ga yar sarki kuma sun haɗe a guri daya, sai dayan yace “yau zamuga abinda zai faru agurun nan izzah ta hadu da izzah” woow masu karatu ku hasko min abunda zai faru a next page.... ✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Taku Qwinn minerhly Mrs Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:21 PM] Qwinn Minerhly: SO MAKAWO NE (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 My first novel, ina fatan zaya nishadantar daku fans, very short nd romantic novel. Writer✍️✍️✍️✍️ Na Qwinn minerhly Part 5-10 Nan take ashmir ya soma fito wa ahankali daga cikin pool din yana taka matattakalan gurun, yana fitowa ya samu wani hadad'iyar coat baki me ratsin fari ya ɗaura akan kananun kayan dake jikin shi inda yakara wani sihirtaccen kyau, ga ruwa yanata sauka ajikinshi gashin jikinshi yadad'a kwanciya gwanin sha'awa. Nan fa ya dirfafi inda gimbiya take, Yana tafiya yana wani shan kamshi yana basarwa yana ta wani yauki kamar mace, hmm tofah! Ita ko gimbiya yar sarki sai shan ice cream ɗinta take tana lumshe ido, dan tunda take bata taɓa shan ice cream din daya gamsar daita ba irin na yau, Yana isowa gurin ya tsaya chakk yana kallonta kallo irin na mamaki gata dai yarinya ƙarama bata wuce age ɗin little sist dinsa ba wato noor, gata kuma kyakyawa gata daga gani hutu ya zauna mata sosai, saida yayi dogon nazari akan ta sannan ya samu kujera wanda yake facing ɗinta ya zauna akai, in a slowly voice murya me dadin gaske, yace ke! Da sauri gimbiya ta dago kanta jin sautin murya akanta, yaci gaba: "ke wacece ke da zaki shigo gurin, nan ehe nace who are you? Yafada da tsawa, daga ganinki ke karamar mara kunya ce ko? to bari kiji wlh saina yi maganinki stupid girl", take gimbiya ta ɗago kanta da sauri ganin ana ci mata mutunci abinda ba'a taɓa yima ta ba a tarihin rayuwarta ba sai yau, aikuwa ta ɗago fuskarta tayi masa wani irin kallon raini, tasaka yatsanta a daidai saitin bakin shi tace "shshshh" alamar yayi shiru, ai sabida mamaki baisan lokacin daya saki baki ba yana kallonta. "Hmm har kaisa kaci min mutunci wlh baka isaba, okay! tambaya ta kake ko ni wace ce ko to zaka san ko ni wacece kuwa yanzu, amma saika fara faɗa min kaima ɗin wanene kai"? Ai ta ke ran maza ya ɓaci, ya ɗaga hannu zai sharara mata mari knan, phone ɗinsa yayi ringing, sai ya fasa marin ta, ya ɗauko phone ɗin sa yana dubawa yaga sunan little sistern sa ce, tayi masa kusan five misscalled, bai ma san ta ƙira ba, ai kuwa ya ɗaga cikin slowly voice ɗin sa kamar ba shi ba ne ransa yayi mugun ɓaci yanzu, yace "baby luv ya akayi"? nan fa noor ta shagwaɓe fuska tace "sweet brother wlh tun ɗazu muke neman ka, nida yaya nasir", yace "to ya akayi ne baby luv"? tace "wlh yaya mun gaji ne gida muke so mu koma", yace "okay babu damuwa gani nan zuwa 5 mnts bari na shirya saina fito mutafi ko"? tace "yauwa my sweet brother sai ka fito" nan take ya ajiye wayar sa a gefe, Ya matso inda gimbiya take azaune, sai cika take tana batsewa yace mata "ke be careful bcause ni ba tsaran ki bane da zakizo kina min misbehave anan, wlh kinci sa'a yarinya sauri nake zan tafi, yau da saikin yaba wa aya zaƙin ta nonsense girl", itako gimbiya da ranta ya gama ɓaci saboda ta ɗauka da budurwar sa yake waya ya kyaleta tana jiran sa, ga shi basu gama faɗan nasu ba sabida ita taso yau tayi maganin shi saiya bata hakuri, tayi masa wulakanci tukun saita hakura amma wai dan rainin hankali saida ya gama wayar sa wai kuma zai tafi sauri yake wlh yau yaci sa'a sosai. Nan fa gimbiya tace "ai ban san kai matsoraci ba ne sai yanzu, da ka tsaya mana kaga aikin karamar yarinya wlh", Shiko ashmir ya juyo sai tin ta yasa ɗan yatsarsa ya buge mata baƙi sannan yace "banda lokacin ki karamar yarinya, amma nayi alkawarin ko ba yau ba sainayi maganinki small rat kawaii", nan fa ashmir ya sa kai yayi tafiyar sa ya bar gimbiya agun riƙe da d'an karamin leben ta, wanda har ya tashi sabida abunda yayi mata yayi mata zafi sosae hawayen bakin ciki ne kawa yake kwarara a fuskanta, nan gimbiya ta durkushe agun tana hawayen bakin ciki bata ankara ba kawai saita ga duhu yafara yi alamun anyi magriba ma, sai kawai ta miƙe ta fita da gudu. Su kuma masu gadin gun tunda sukaga D.ashmir ya fito ransa matuƙar bace suka san an tabka tsiya knan gashi suna so su kulle gurin sabida gurin yanada tsaro sosai amma suna tsoron gimbiya da take gun, ai kuwa tana fitowa suka samu suka kulle gurin. Shiko ashmir yana fito wa yaga nasir da noor da bodyguards dinsu sunyi cirko cirko shi kawai ake jira agun, aikuwa ba ɓata lokaci ya shige mota, lil sist ma ta shiga nashi motan, shikuma nasir ya shiga wani daga cikin motocin nan da nan aka tashi motocin aka hau kan kwalta dasu ana basu wuta. A hanya kuwa duk surutun lil sist yau ba tayi surutu ba sbd taga ran babban yaya aɓace yake shiyasa tayi shiru. Shi kuma ashmir ran sa ne a matuƙar ɓa ce, wai yau shi karamar yarinya tayiwa rashin kunya, hmm wlh daya san ko yar wace ce da yau sai ya sa an dauko mai ita yayi maganinta amma bari ya san me zaiyi akai ai! Ita kuma gimbiya tana fitowa tayi ta waige waige ko zata ga ashmir ta rama abinda yayi mata dan wlh taso ta ganshi da saita mare shi taga abinda ya isa yayi, mugu kawai babba dashi amma sai mugunta, ai wlh sai ta nemo shi tayi maganinshi duk da ran daɗe wa mugu kawae. Nanda nanda bayinta suka nufo ta suka duƙa suna kwasar gaisuwa itako bata ma san sunayi ba ko kallo basu ishe taba balle ta amsa musu. Su kace "ran gimbiya ya daɗe tafiya zamuyi ne"? to anan ne ma ta daga musu kai alamar yes, su kuma ko ajikin su daman sun saba da hakan, wulaƙanta su takeyi dama, ita ala dole yar sarki jikan sarki yar na gada. To nan fa itama gimbiya aka buɗe mata mota suka shiga bodyguard ɗinta suka rufa mata baya suka hau kwalta sai gida. Doctor ashmir kuwa suna isa gida wato government house ya nufi part ɗinsa, wanda haɗuwar wajan ya isa, Kai tsaye shiga ciki yayi, ya shiga wata hadadd'iyar bathroom ɗin sa zai yi wanka, nan fa yayi wankan sa ya fito ya saka wasu kayan shan iska ya tafi dressing mirror ya taje gashinsa da sajensa, yatashi ya dauko sallahya ya shimfiɗa ya tada sallah yayi sallolin sa yayi nafila yayi azkar ɗinsa na dare, take anan yaji ya dai na jin bacin ran dayake ji zuciyarsa tayi masa wasai. ya tashi ya tafi main parlor na gidan yana zuwa ya tafi gun mum, yayi hugging ɗinta yace "sweet mum am back, sannu da gida", Mum tace "wlcm my luv" yace "mum so sorry mun barki ke ka dai a gida ko"? mum tace "no ba komai son ai dadyn ku yana gida kasan yau weekend ne," Ashmir ya shafa kan sa yace "ohh mum ina dad yake?" tace "yana sama amma yanxu zai sauko, sai ayi lunch" Sai ga noor ta sauko da gudu tana zuwa tayi hugging ɗinn mum tace "mum sannu da gida" mum tace "yauwa sannu my princess, ya gajiya?" noor ta shagwaɓe fuska tace "wlh mum yau nagaji sosai," mum tace "sorry tunda kinyi wanka za kiji warware ko." nan fa noor ta kalli ashmir tace "sweet bro yau kamar kana fushi ko?" yace mata "no ba ba fushi nake ba," sai tace "okay, to yayi kyau bros, shi kuma yayi pecking dinta a kumatu yace lil sis kiriniya ko? tace "aa yaya," yace "okay ba damuwa ai," sai ga nasir ya sakko shima yana zuwa yaje kusa da mum yace "mum sannu da hutawa" tace "yauwa my son ya kuka dawo?" nasir yace "lafiya lau mum," yatafi yayi hugging ɗin babban yaya yace "sannu bros" ashmir yace "yauwa my luv sannu kaima ya gajiyan mu?" Nasir yace "alhmdlh bros." nan suka zauna a dinning cheers ɗin suna jiran dad, sai ga dad ɗin juwa nan ya sauko, aikuwa nan duk suka miƙe amma banda mum, sai da dad ya zauna tukun suma suka zauna, duk suka gaishe da dad ya amsa yana ta doka murmushi afuskar sa nan fa dad yace "bismillan ku" kowa yafara cin abinci, sai da aka gama cin abinci sai dad yace "ahm kun dawo lafiya? sukace "lafiya lau dad" yace "to Masha Allah," yace wa ashmir "amma dai gurin babu matsalan komai ko? suka ce "eh dad babu matsala," noor tace "dad kasan yaya nasir ne ya gana da managers din fa, dad yace "alright yayi kyau, "shi sarkin miskilancin mai yayi acan? noor tace "dad yana chan wajan sweeming pool, sai dad "yace ai na sani sarkin wanka ko agwagwa albarka," nan fa akai ta dariya, shi ko gogan murmusawa kawai yayi bai ce komai ba, to nan fa dad yayi gyarar murya, kowa yayi shiru sannan yace "yanzu dare yayi kowa yaje ya kwanta, gobe da safe inada magana daku. Kawai ashmir yaji gaban sa ya fadi, amma sai ya dake, to nan dai kowa ya watse yatafi ɓangaren sa inda noor tabi bayan mum, domin ita dakin ta yana kusa dana mum bata yarda tayi nisa da mum ba. To wannan knan A can part ɗin babban yaya kuwa yana Chan yana ta juyi yara sa mai ke yimasa dadi a duniya, da ya rufe ido sai yaga wannan fitsarariyar yarinyar, to shi wai me hakan yake nufi ne? Shi dai yasan bawani k'are mata kallo yayi ba amma dai ya ɗanga fuskar ta lokacin da take yimasa tsiwa da wani ɗan ƙaramin bakin ta daya gwabje mata shi,sai kuma kyau tabbas kyakyawa ce ba laifi amma kuma ai daga gani yarinya ce baza ta wuce 18 ba sa'ar noor ce ai, To fah nan dai ashmir ya dinga tunanin gimbiya kuma shi dai yasan ba son ta yake ji ba to amma kuma me hakan yake nufi??? "Hhhh niko nace babban yaya ka tambayi kanka zamu fi samun amsa." To masu karatu mai ya ƙare anan, amma kuma kada ku gaji kuci gaba da bin mu a sannu a hankali domin jin ita kuma gimbiya awani hali take ciki yanzu... More comments more typing✍️✍️✍️✍️✍️ Taku Qwinn minerhly Mrs Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO* *MAKAWO* *NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 My first novel,ina fatan zaya nishadantar daku Fan's very short and romantic novel. *Writer* ✍️✍️✍️✍️ *Na* *Qwinn* *minerhly* *ELEGANT* *ONLINE* *WRITERS*📖 Part 10-15 ....... itako gimbiya a hanyar su ta komawa gida sai cika take tana batsewa ita ala dole ran ta abace yake. To suna ƙara sowa gida, ana bude mata mota "fuhhh" kamar iska tayi part ɗinta dan bata son ganin kowa balle ayita mata questions akan abunda ke damunta, ita kuma bata son too much of questions. To gimbiya tana shiga part ɗinta sai ta nufi bathroom ɗinta tayi wanka ta fito ta tsaya a dressing mirror ɗin dake cikin bathroom ɗinta tayi handryer ɗin gashinta, tayi oiling ɗinshi ta samu peach color ɗin ribbon tayi parking ɗin gashin. Wow har gadon bayanta gashi sai sheki yake gashi baki ga santsi kamar na Indians. Tana fito wa daga bathroom ɗinta sai ta nufi dressing room ɗinta ta buɗe wardrobe ta ɗauko wani peach color ɗin sleeping dress dogo har kasa me siririn hannu ta saka shi, wow tayi masifar kyau kamar asace ta. Ta ɗauko hijab har kasa da pray mat ta shimfiɗa ta tada sallah. Ko da gimbiya ta kammala sallolinta da nafilfilinta saitayi addu'ointa ta shafa. "Domin duk abun gimbiya bata wasa da ibadah sosae ta rike ibadah" Tana kammalawa ta miƙe ta naɗe pray mat ɗin ta cire hijab ta samu small vail ɗinta ta yafa tanufi part ɗin *FULANI* wato mum ɗinta. Tana shiga ta tarar da mum ta idar da sallah Isha'i tana addu'a, mum tana shafa adduar, gimbiya ta taso tafaɗa jikin mum ta rungumi mum sosai, sannan ta gaishe ta, *cikin* *harshan* *Arab* mum ta amsa mata da fara'a sosai akan fuskar ta, gimbiya tace "I really miss u my mummah," mum ma tace "I miss u too my princess," nan fa gimbiya takara shige wa jikin mum tanata zuba shagwaɓa. Chan gimbiya tace mum ina dad? "Sai mum tace "*MAI* *MARTABA* yana part ɗin sa, bai daɗe da barin *FADA*" ba, Sai gimbiya tace "okay mum gobe ma haɗu da shi bcoz yau nagaji wlh. Mum ta ɗago tana kallon yar tata, sai taga leɓen yar ta kamar a kumbura yake, sai mum tace "my princess meya samu lips dinki?" Duhmm!!! Taji gabanta ya faɗi, domin batayi tunanin mum zata gane ba, sai ta tsaya tana kallon mum wanda azuciyar ta kuma ba haka bane tunanin me zata faɗawa mum take, Ita dai ta san baza ta iya faɗa wa mum gaskiyar abinda yafaru ba, don tasan wlh sai mum tayi mata faɗa sabida mum tana yawan yimata nasiha akan yawan nuna izzah da gadara sabida ita mace ce, Nan fa gimbiya ta shagwaɓe fuska tace mum " santsin tyles ne ya kwashe ni nayi tuntuɓe ɗazu, na bugu da kofa," sai mum tace "sorry my princess kinsha magani?ko kuma akira maki D. Usman ne?" Nan fa gimbiya tayi saurin girgiza kanta tace wa mum, "no! Mum just leave nasha magani kuma naji sauƙi", sai mum tace "alright! yanzu tashi kije kiyi dinner sai ki je ki kwanta ko my baby?" Sai gimbiya ta ɗaga mata kai alamar "eh' To nan fa ta nufi dinning area ta zauna ta buɗe womers ɗin ta zuba farfesun kayan ciki ta dan ci kaɗan ta kora da hot coffee ta miƙe taje tayiwa mum sallama ta tafi part ɗinta. To kafin gimbiya ta kwanta sai ta nufi dressing mirror ɗinta dake cikin bedroom ɗin ɗakinta, ta zauna tana duba leɓenta daya mata nauyi ya ku mayi jah sosai, kawai sai naga murmushi akan fuskar ta wanda ita kaɗai ta san manufar sa. To bayan gimbiya ta kwanta sai bacci ya gagara, sai kalaman wannan kyakyawan mutumin me siffar aljanu ne yake tayi mata yawo a kunnuwan ta. "" Ke!!! Ke wacece ke dazaki shigo gurin nan? Ehe nace who are u? Daga gani ke ƙaramar mara kunya ce , to bari kiji wlh sainayi maganinki stupid girl"' Gimbiya ta dada yin wani juyi a katon haɗaɗɗan royal bed ɗinta . ""'' ke becareful danni ba tsaran ki bane da zakizo kina min misbehave anan wlh kinci sa'a yarinya sauri nake yi yau da saikin yabawa aya zaƙinta nonsense girl""' Firgigit gimbiya ta miƙe zaune ta mari kumatun ta tace cikin tsawa, "Wai what's going up with me!!! Wlh ba zai yuba, Ka zageni Ka buge ni Kaci min mutunci, Kuma sannan na dawo gida ka hana ni bacci, toh wlh saina rama. Ke zuciyata bazaki cuce ni ba, wlh imporsible don baka daƙi banza ehe. To anan fa ta kwanta barci, da ƙyar wani bacci me nauyi ya kwashe ta inda tayi ta mafarke mafarke kuma duk akan D.Ashmir. ""Hmm niko nace tofah"" *GIDAN* *DARAUTA* comments and I will type more for you my fans ✍️✍️✍️✍️ _Taku_ _Qwinn_ _minrerhly_ _Mrs_ _Yusuf_ ❤️❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 __My_ _first_ _novel_ , _inafatan_ _zaya_ _nishadantar_ _daku_ ya ilimantar _da_ _ku_ , _Short_ _and_ _romantic__. *_Writer* ✍️✍️✍️✍️ *Na* *Qwinn* *minerhly* _Masoyan_ _novel_ _ɗina_ _ina_ _godiya_ _da_ _nuna_ _kaunaku_ _ga_ _wannan_ _book_ _din_ _da_ _kuma_ _addu'oin_ _ku_ , _Allah_ _yabar kauna_ . Part 15_20 *GIDAN* *SARAUTA* MAI MARTABA Sarki *BELLO MUHAMMAD ll Sarki ne agarin Kano wanda ya gada a gun mahaifin shi, asalin su *FULANI* ne. sarauta ce tun na iyaye da kakanni. Mahaifin sa wato *SARKI* *MUHAMMAD* *YUNUS* ya mutu ne shekaru kusan ashirin, wanda bayan mutuwar sa da sati uku aka naɗa ɗansa kuma magajin sa wato Sarki Bello Muhammad ll, Wanda alokacin yanada mata ɗaya, wato *Hajiya* *Kilishi* da kuma ɗa guda ɗaya, wato *Adnan* wanda alokacin bai fi 8yrs ba. Hajiya Maryam wato (Kilishi) dai ƙanwa ce agun *Sarkin* *Karaye* , bafulatana ce ta usuli, kyakkyawa ce ba laifi. Tunda akayi auran, ta samu cikin yarima wato (Adnan) bayan ta haife shi, bata ƙara samun wani cikin ba. Sai da tayi shekara biyar da haihuwar yarima tukun ta samu wani cikin, Inda ta haifi ya mace saide ta fito babu rai, to tun daga nan bata ƙara samun wani cikin ba. Wanda alokacin ne aka fara bawa yarima wani irin gata wanda har ya so yayi yawa musamman agun mahaifiyar sa, wanda take ganin babu ya ita tunda ta haifi ɗa namiji kuma Magaji, wanda haka ne yayi sanadiyar tasowar yarima cikin rashin tarbiyya da ɗaha. Wannan kenan... Bayan shekara kamar huɗu mai martaba ya kara aure inda ya auro yar *Sarkin* *Borno* Hajiya Turai wato (Fulani). Asalin ta shuwa'arab ne, ( "Kar ku ji na kirata da fulani kuma tana shuwa, to kunsan gidan sarauta yana da tsari, saboda suna da al'ada, musamman matan sarki akwai sunayen da a ke kiran su dashi wanda bana yanka ba indai a gidan sarauta suke aure, to a taƙaice dai sunayen matan sarki ne kilishi da fulani"). Hajiya Turai dai Arab ce wanda take da wani irin kyan gaske harta doke uwar gida, wanda hakan ne yayi sanadin haddasa wata iriyar tsana, tsakanin ta da hajiya kilishi. A gaskiya kilishi ta tsani fulani, a cewar ta wai "gata da kyau kuma mai martaba yana mugun son ta" to wannan ne silar rashin jituwar su. To bayan auran mai martaba da fulani ne da shekara biyu ta haifi kyakkyawar yarta mai kama daita wato *Gimbiya* *Nihal* Wacce ta taso cikin gatan uwa da uba domin mai martaba yana son ya mace sosai, ga kuma soyayyar mahaifiyar ta. To princess nihal dai yarinya ce wacce ta taso cikin gata da kuma kulawa, shi yasa ta taso bata fiya son jama'a ba, sai iyayenta, To tunda tayi primary, tagama tayi secondary a Abuja na yayan shuwa'gabanni zallah, me suna (INTERNATIONAL DAILY CARE). wanda a yanzu tana University ne, a kasar Wow Russia under American. To tunda gimbiya ta taso bata da wasu ƙawaye wanda har tayi primary nd secondary School, ƙawaye suna ta binta har gidansu wai suna son suyi ƙawance amma gimbiya taƙi basu fuska, kuma suma ya'yan manya ne fa, but ita kawai bata son hayaniya ne da disturbance, Aduniyar nan ƙawar gimbiya ɗaya ce wacce suka haɗu daita a achan wow Russian, school ɗinsu ɗaya amma course kowa da nashi, sun haɗu daita ne dalilin anfito a makaranta zasu shiga wani restaurant me suna (Special Gift Restaurant) Wanda gimbiya bata taɓa zuwa gun cin abinci ba, wani take zuwa me suna (Small Chops) to sai take jin wasu daga cikin course mate ɗinta suna labarin special gift restaurant, to shine fa a yau ta ce bari taje chan taji ya abincin gun yake. Shi ne fa yau taje chan har tayi ƙawa achan, me suna *Noor* Wanda saida suka fara faɗa kafin ƙawancen inda gimbiya ce ta fara zuwa gun sai Peter ɗin yazo ya tambaye ta me take so? cikin harshen turanci ta bashi list ya tafi, to sai ga noor ta shigo ciki, to Kasan cewar ta saba da masu gurin kuma sun san abinda take so kawai tana shigowa zasu miƙo mata, to yau ma haka akayi, tana zuwa saita nemi kujera ta zauna kawai sai Peter ya kawo wa noor abinda tafiso a gurin, karaf sai akan idon gimbiya aikam ta miƙe ta taho wajan tana zuwa tafara bala'i da harshen turanci cewar "kai kaisa ni na fara zuwa gun amma sai wata tazo a bata itaɗin wace ce?wlh baku isa ba", nan fa noor ta tanka mata tace "ke din wace ce kema? da baza aji dani ba dan kina gurin"? nan fa faɗa ya ɓarke tsakanin su, Inda gimbiya tace oh! tambaya ta kike wace ce ni?"to "sunana Princess Nihal, ya ce ga SARKIN KANO MAI MARTABA BELLO MUHAMMAD ll". Nan taga noor ko gizau ba tayi ba saima kwafa da tayi tace to nima kina son sanin wacece ni? "sunana Noor ya ce agun GOVERNOR ABDULKARIM NASIR GAYA". Tofah! Kowa yana da iko kenan? Nan fa guri yayi tsit kamar ba mutane dama peters ɗin suna ta basu hakuri tun ɗazu, to amma yanzu kowanne su yayi shock da jin abinda junan su suka faɗa musamman gimbiya, sai fa kallon kallo sukewa juna,inda noor take mamakin irin kyaun da gimbiya take dashi to sai dai a ɓangaran gimbiya kuma sai da tafi noor shock sabida bata taba ganin me irin kyan noor ba. Niko nace " tofah ya'yan masu kyau an haɗu gu ɗaya" to nan dai kowa ya watse sai gimbiya da noor kaɗai suka ragu inda gimbiya ta fasa cin abincin tayi tafiyar ta, ita kuma noor tayi zaman ta taci abinci, tukun tayi tafiyar ta. To washe gari ma hakan ce ta faru sun kuma haɗuwa a gunrin cin abincin, To anan ne gimbiya ta zo har inda noor take tayi mata sallama itama noor ta amsa da fara'a, dama noor ba baƙuwar zafi bace ita, nan suka zauna fira ta ɓarke tsakanin su dama noor gwanace a surutu, To silar ƙawancen gimbiya da noor kenan. Inda sukayi wata irin shaƙuwa a tsakaninsu idan ɗaya bai ga ɗaya ba, ba sukuni. To yanzu ma hutu suka yi, suka dawo Nigeria shi ne har gimbiya ta haɗu da ashmir a palace. Wannan kenan To anan muka kawo karshen labarin gidan mai martaba wato gidansu nihal. *GOVERNMENT* *HOUSE* ..... To zamuje muji a wani hali ashmir yake ciki...... More comments more typing✍️✍️✍️✍️ _Taku_ _Qwinn_ _minerhly_ _Mrs_ _Yusuf_ ❤️❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* Masoyan so makaho ne, jinjina gareku fans Allah ya bar kauna❤️❤️❤️ Page 25_30 ______ to bayan mahaifiyar hajiya nuhaira ta amince da zancen auran su, sai Alh Abdulkarim ya dawo Nigeria ya sanar da iyayensa cewar, "shifa ya samu mata a Sudan don haka aure zai yi," ba tare da ɓata lokaci ba akaje aka tambayo masa auran ta, iyayen ta suka amince aka ɗauro aure aka taho da amarya. To bayan haka... Abdulkarim da nuhaira soyayyar su suke zubawa son ransu, domin kuwa suna matuƙar son junan su, tana masa biyayya sosai, yayin da shi kuma yake kyautata mata. To ana cikin haka Hajiya nuhaira ta samu ciki, farin ciki agurun su babu magana, aikuwa ta haifo ɗanta kyakkyawan gaske me kama da ita kamar tayi kaƙi, aka saka mishi sunan mahaifinta daya rasu wato (Ashmir) Aikuwa ɗan nan yaga gata, gurin iyaye da kakanni, kowa kamar ya lashe shi don so, to bayan shekaru biyar da haihuwar ashmir, sai nuhaira ta samu wani cikin, shima sunyi murna sosai, don ta samu jinkiri sosai, aikuwa after 9months ta haifo kyakyawan ɗan ta me kama da ubansa wato Abdulkarim, yaci sunan Alh Nasir me naira, wato mahaifin Abdulkarim, aikuwa shima ya samu gata, saide kunsan gatan da ɗan fari yake samu, babu ya shi, domin ashmir ya samu gata sosai, kuma both ta kowane fanni, don mahaifiyar hajiya nuhaira lokacin da aka haifi ashmir sai da tazo taga ɗan jikanta, a cewar ta wai "dama su bata shi, ta tafi da shi Sudan ɗin ya rayu a chan gurin ta. To ana haka kwatsam wata ranar Alhamis aka tashi da wata rasuwa, wato mahaifin Abdulkarim ya rasu bayan gajeran jinyar da yayi ta kwana biyu, Allah sarki Alh Nasir me Naira, (kulli nafsin zaikatul maut) mutum na gari me taimakon al'ummar sa ga hakuri da kawaici, To saide muce Allah yaji kansa da rahama, Ameen, sunji mutuwar sa sosai, don kuwa Abdulkarim har zazzaɓi saida yayi, to bayan arba'in, sai al'amura suka ɗan daidaitu, aka fara sabawa da rashin Alh Nasir, inda Alh Abdulkarim yayi yayi mahaifiyar sa ta dawo cikin gidan sa ita kuma taƙi, a cewar ta yabarta achan gidan tafi sabawa da shi. To wannan kenan Alokacin shekaran Nasir goma sha ɗaya, kawai Hajiya nuhaira tafara laulayi, ita wlh harta hakura da haihuwar, sun cira rai gaba ɗaya da haihuwar, sai ga shi ta samu cikin noor, bayan wata tara, ta haifi yarta me kama daita sak, kamar su ɗaya da ashmir. Wow abunka da ya mace nan kuwa aka dinga nan nan da ita, haka ta taso cikin shagwaɓa, To kasan cewar Mum tafi ji da ashmir acikin ƴaƴanta, wai acewar ta, "me sunan mahaifin ta ne, kuma gashi me kama da ita sosai, shi yasa take mugun son sa, shi kuma dad yace to ayi raba dai-dai, shima yafi ji da Nasir wai acewar sa me sunan baban sa ne, kuma gashi yana mugun kama da shi, niko nace"tofah! Ita kuma noor waya fi son ta? ... Ita kuma noor gaba ɗayan su suka haɗu suke nuna mata soyayya a cewar su wai basu da y'a mace sai ita, shiyasa ta taso cikin soyayyar iyaye da yan'uwa da kuma kakanni ta. Shi kuma Alh kabeer wato kanin Alh Abdulkarim yazama babban ɗan kasuwa, ya gaji mahaifin su, yanada mata biyu, Hajiya Hafsah, da Hajiya Binta, wato dai Hajiya Hafsah itace uwar gida, kuma tanada ya, me suna (Amira), ita kuma Hajiya Binta itace amarya, sannan itama tanada ya, me suna (Islam). basa zaman lafiya kwata kwata ga kishin tsiya, kowacce yarta ɗaya, ya'ya mata suke da shi, kuma kowacce na son ta haifi ɗa namiji amma bata samu ba, shi kuma yafi ji da amaryar sa, shiyasa uwar gidan ta tsani amaryar, kuma gashi da Amira da Islam, kowacce tana masifar son ashmir. To fah! Wannan kenan To alokacin ashmir ya kammala karatunsa na likitoci a jermany inda ya karanci, DERMARTOLOGIST and CARDIOLOGIST, To ayanzu dai, D. Ashmir dai kwararre kuma shahararren babban likita ne a ɓangaren, FATA(DERMARTOLOGIST) ZUCIYA (CARDIOLOGIST). Inda suka rike shi achan, cewar su wai shi ɗin na daban ne, gashi da baiwa kuma ya san aikin shi sosai, shi yasa ba sa son ya ƙubce masu. To shi kuma D. Ashmir, anasa ɓangaren, cewa yayi " zai yi masu aiki na ɗan wani lokaci ne, bayan ya kammala zai dawo ya bautawa ƙasar sa, domin shi ɗin me kishin ƙasar sa ne. To bayan haka, shi kuma Nasir ya kammala karatunsa a ƙasar Sudan, wato ƙasar mahaifiyarsa, inda shi ɗinma kwararran likita ne Yanzu me matsayin, MEDICAL OFFICER DOCTOR. To ayanzu dai nasir yana aiki ne a Nigeria acikin tangamemen asibitin da Alh Abdulkarim ya bude masu shida ashmir, me suna ANN MEDICAL HOSPITAL (ASHMIR NASIR NOOR MEDICAL HOSPITAL), acikin babban unguwar nan me suna Nassarawa GRA. Ita kuma noor tana chan ƙasar Wow Russian, tana karanta (Mass communication ) ita burinta ace yau tazama babbar yar jarida wato (Journalist) noor kenan. To abubuwa da dama sun shuɗe a wannan lokacin. Bayan Alh Abdulkarim ya taka manyan matakai na mulki a ɓangaren siyasa, har ta kai iyanzu yana takarar gwamna, inda kuwa Allah ya bashi nasara ya lashe wannan zaɓen, domin jama'ar gari suna son shi sosai, a cewar su wai ya cika kuma shi ɗin ɗan halak ne. Shi ne yanzu fa ya zama governor Abdulkarim Nasir Gaya. (namanta ban faɗa maku asalin ƙauyan su abaya ba, gaya ne.) To mundawo daga labarin su ashmir, yanzu labari zai ɗora... ____________________ to bayan Mum ta tafi part ɗin His Excelency, sai ta same shi ya zauna a resting chair ɗin ɗakin, yana kallon tashar zeeworld, inda suke hasko wannan Film ɗin me suna, Jodha Akbar, aikuwa dad ya natsu yana kallo domin Film ɗin ya tafi da shi, mum ta shigo da sallama, dad ya ɗago ya amsa mata sallama, ta ƙaraso haɗe da cewa Barka da hutawa ranka ya dade, dad yace yauwa firstlady sannun ki da shigowa, Mum ta matso kusa da dad, ta dafa shi tace "zaujih! Dad ya amsa mata da "na'am, mum tace "pls ur Excellency inason mu natsu gaba ɗayan mu, bcaus bana so ɗan mu yaje yayi zaɓen tumun dare, garin nemen gira a rasa ido, kaga wa gari ya waya"? Dad ya ɗago kanshi yace "kamar ya kenan Hajiya"? Mum tace "abunda nake nufi shi ne idan muka matsa masa ya nemo matar aure yanzu, kaga zai iya zaɓo mana ɓata gari, wacce bata da halaiya me kyau, kuma kasan duk nagartar ɗa namiji, to idan fa bai samu mace ta gari ba, to dole zata sauya shi kota halin ƙaƙa, to shi yasa nake so mubi abun a sannu, so that mu samu results me kyau, bana son a gurɓata min tarbiyyar ɗana, duk shekarun da muka ɗiba muna bashi tarbiyya kawai rana ɗaya mace ta ruguza mana shi, ka gane ko zaujih"? Nan fa jikin dad yayi sanyi, sosai, sabida duk Abinda Hajiya tafaɗa gaskiya ne, to amma yasan da cewa ya'yan kanin shi wato kabeer suna son ashmir ɗin, to ashmir ya zaɓi ɗaya mana acikin su, sabida kada kanin sa yayi zargin wani abu. To ganin ganin his excelency ya tafi tunani ne, shi yasa Mum ta dafa shi, tace "meya faru ne zaujih ko dai da matsala ne"? Nan dad ya ɗago kanshi, yace "ahm Hajiya na gamsu da kalaman ki, but amma wani hanzari ba gudu ba, bakya ganin cewa Alh kabeer zai yi zargin wani abu, musamman idan ashmir bai amshi tayin soyayyar yar sa ɗaya ba? Kinsan da cewa kabeer ya taɓa tuntuɓa ta akan wannan zancen cewa, ashmir yaje gidan sa ya zaɓi ɗaya cikin ya'yan sa ko Amira ko islam, ya zaɓi duk wacce tayi masa, kinsan da haka ko? To bana son wannan zancen ya shafi zumuncin mu, domin na fahimci Yaron nan baya ra'ayin yaran nan, shi kuma kabeer yana ganin kamar mune ba ma son abun, domin shi a tunanin sa zamu iya tursasa ashmir akan hakan". Itako mum ta tafi tunani domin ita a gaskiya bata son ɗan ta ya auri ɗaya daga cikin su amira, Dalili kuwa gidan Alh kabeer babu isasshen tarbiyya, daga iyayen mata har ya'yan, sabida idan iyayen mata suna faɗa har ya'yan shiga suke, kowacce ta shigar wa uwarta, to saboda haka ita bata so gaskiya, amma matsalar shine ba zata iya fitowa ƙiri ƙiri ta faɗa wa his Excellency ba sabida ko ba komai ya'yan ɗan uwansa ne, ba zaiji daɗi ba idan ta kushe abun, to amma tasan yanda zata biyo wa lamarin, sabida bazai yuba, ai itama akwai wata yarinya a Sudan me suna LIARAH, yar kanin baban ta ne kuma yarinya tun da taga ashmir, take mugun son shi, amma shi yace baya so, kuma gata balarabiya sak, amma ashmir yace ba yaso, ita kuma mum a tsarinta babu dole idan ɗanta yace bayaso to shike nan. Nan his Excellency yayi gyaran murya yace, "ya dai Hajiya nuhaira", Mum tayi firgigit tace "no ba komai, amma inaso kasani Alh, yanzu ba'a auran dole, kai da kanka kasan irin illar da hakan ke haifar wa ko? Kuma kasan muddin ashmir ya zaɓi ɗaya daga cikin su Amira to babu zaman lafiya saboda kasan bawani jituwa tsakanin su ko, to ya lafiyar kura dama? kuma ina so kasan cewa ɗan ka me tsatsauran ra'ayi ne, baya son dole, kasan da cewa liarah yar kanin babana tana son sa amma fafir yaƙi, kuma bazan masa dole ba tunda namiji ne shi, kawai mu hakura har nanda 3months ɗin muga abinda Allah zai yi", Nan dad ya numfasa Domin shi bai taɓa sanin cewar ma iyalan kabeer basa zaman lafiya ba, yace, "to shikenan Hajiya mujira nanda 3months ɗin muga abinda Allah zai yi, amma lallai ashmir nan da 3months yayi ƙoƙarin samun matar aure", mum ta numfasa tace insha Allahu zaujih. GIDAN ALHAJI KABEER Amira ce sanye da abaya red tayi rolling da ɗan gyalen abayar, ta fito sai wani yauƙi take, tana fitowa daidai corridor ɗin su, sai ta ji wayarta na ringing, ta ɗaga tace, "hello sady babe, lfya lau ƙawata wlh, eh zanje government house ne gurin masoyi na ance yazo hutu, kuma tunda yazo bamu haɗu ba, okay to karki damu zan biyo ta gidanku kinji? Okay bye. Ashe Islam tana tsaye itama ta fito taci make up tasaka wani maroon ɗin atamfa da wani karamin mayafi agefen kafaɗar ta, ɗinkin riga da skirt, kayan ya masifar kamata , aikuwa amira tace "ke!!! Ina zaki?" Islam ta watsa mata harara tace "ban sani ba ai ke ba uwata bace ba, da zakizo kina tambaya ta, aikuwa nan faɗa ya ɓarke tsakanin su, Islam tace kuma gurin masoyi na zanje idan kin isa ki hanani, nan kuwa amira tace "kam bala'i wlh baki isa ba, naje kema kije, to billahillazi saide ki fasa zuwa domin Ni ce zanje yau ehe", aikuwa Islam tace "wlh baki isa ba saide ke kifasa zuwa, ehe", aikuwa nan suka dinga fada, kwatsam sai ga Alh kabeer nan ya dawo daga kasuwa, tun daga bakin get yake jiyo hayaniya, aikuwa me gadi na buɗe masa get, drivern sa yayi parking yafito ya buɗe masa marfin mota, ya fito, ya tarar ya'yan sa ne ke faɗan ashe, nan kuwa ya hausu da faɗa yana tambayar me ya faru? Amira ce ta mayar masa da abinda ya faru, aikuwa nan ya hausu da faɗa, yana cewa "sabida ku baku da hankali ko? Yan iska marasa jin magana, a haka ashmir ɗin zai so ku? shiyasa ma baya ta ku ai, to wlh bari kuji na faɗa maku tun wuri ku natsu ku daina wannan haukan naku, domin dole ɗaya ce zata auri ashmir, ku zauna kuyi wa kanku sulhu ɗaya ta hakura, ko kuma Ni na zaɓar masa da kaina, kuma wlh duk wacce na zaba daita za'ayi, kuma babu wacce zata fita acikin ku yau." Nan kuwa kowacce tayi tsuru tsuru, sai kallon kallon akewa juna, shi ko dad yayi tafiyar sa yabar su wajan, Amira ta matso kusa da islam tace "sister pls kibar min ashmir wlh nayi maki alkawarin komai kikeso zaki samu pls", islam tayi wani uban ashar tace "wlh baki isa ba saide ke kici girma kibar min shi ehe, nan kuwa Islam ta juya fuuh ta koma cikin gida, itama amira ta koma cikin gidan, Islam na shiga part din su taje ta zube ajikin mummy tana kuka tace "mum wlh ba zaiyu ba, wai dad saide ya azaɓi guda ɗaya cikin nida Amira, mum kar fa dad ya zaɓe ta, pls mum kiyi wani abu", Hajiya Binta kuwa wani murmushi tayi, tace "haba dai yarinya an isa ma? To bari kiji gobe zanje gun malam na tudu akan zancen nan kuma dole kece zaki auri ashmir", nan kuwa Islam tayi murmushin mugun ta, tayi hugging ɗin mummy tace that's my luvly mum shiyasa nake ƙara sonki. Itama amira tana shiga ɗaki taje ta rungume mum tana kuka, ta kwashe duk abinda sukayi da Islam da abinda dad ya faɗa, ta haɗa da cewa "wlh mum tsorona kar dad ya ce Islam ce zata auri yaya ashmir, nan kuwa Hajiya Hafsah tayi wata ashar tace' wlh bazata saɓu ba wanka kuturu da sabulu, to bari kiji, zan ɗau mataki yau yau, bari na kira kawata hajiya salamatu naji ta bakin ta tukun. Nan kuwa amira ta dinga murna wai ita ce zata auri ashmir. GIDAN SARAUTA✍️✍️✍️✍️ Mu haɗu a next page... Taku Qwinn minerhly Mrs Yusuf ❤️❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📖 My first novel, ina fatan zaya nishaɗantar da ku haɗi da ilimantarwa, Short and romantic novel. *Writer* ✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* Party 20_25 *GOVERNMENT HOUSE* Bayan Ashmir ya samu bacci ya ɗauke shi da kyar. Baby luv!!! Baby luv!!!, Yes!!! "my durling sweety!, Gani nan dama naga hadari ya haɗo ne, shi ne na ɗan shiga kitchen na haɗa maka abu me ɗan galmi galmi, ka gani my luv, farfesun hanta da ƙoda na hada maka me dan yaji yaji, saboda nasan idan hadarin nan ya fashe ba ƙaramin ruwa za'ayi ba, kuma za'a sha sanyi yau sosai, ga kuma ginger juice nan sai a haɗa da shi, ai komai zanyi domin ka, my heart indai zakayi farin ciki", ai kafin ta karasa maganan ya caɓe baƙin ta yana ta tsotsa kamar ya samu lollipop. Daidai nan tsadaddan agogon dake jikin bangon ɗakin ya fara ringing kie kie kie!!! Alama ce ta lokacin sallah yayi wato 4:30am Take ashmir ya farka daga nauyayyan baccin daya kwashe shi, yayi addu'an tashi daga bacci yayi miƙa, yace "ohh my God wai meke faruwa da ashmir ne? I said what is going up with me? Ohh! dreaming with dat stupid girl? "To dole ma na ɗauki mataki akanki yarinya, taya ina cikin tafiyar da rayuwa na cikin jin daɗi da kwanciyar hankali zakizo ki tarwatsa min farin ciki na, to wlh baki isa ba, na rasa da wacce zanyi soyayya sai ke mara kunya". Nan dai ashmir yayi ta surutai kamar mara hankali, duk yarinya karama ta haukata shi. To bai ankara ba sai ji yayi ana kiran sallah, acikin masallacin dake gidan na su. Yayi tsaki yace a ransa yarinya karama ta hanani tashi da wuri gashi banyi nafilfili na ba, nan ya miƙe a gurguje ya tafi bayi ya ɗauro alwala ya tafi masallaci. WAYEWAR GARI Misalin ƙarfe 9:30am a yau litinin wato monday suna kan dinning table gaba dayansu har *His Excellence*. waiter! ne a tsaye a kansu yana tambayar kowa abinda zai ci ya zuba masa. Ana haka sai wayar dad yayi ringing, aka miƙo masa wayar, dad ya duba yaga waye me Kiran? Yana duba wa yaga sunan Mai Martaba ajiki, ya ɗaga. Daga dayan ɓangaren kuma mai martaba ne ya kira His Excellence yana ganin ya ɗaga yayi masa sallama, shima his excellency ya amsa cikin natsuwa, bayan sun gama gaisawa ne, sai mai martaba "yace dama na kira ne danga ne da zancen buɗe wannan sabbin company's ɗin, kasan nan da 3months za'a kammala shi gaba ɗaya". To anan fah his excellency yace "Yes! "Kasan nima akwai breech's, da kuma hanyar da'aka kammala, so inason a buɗe su nan da 2months amma bari na hakura har nan da 3months ɗin sai mu haɗe bikin buɗewa gaba ɗaya domin nima zanyi tafiya nanda jibi, kuma sai nayi 1month zan dawo". To a nan fah mai martaba ya gyaɗa kai yace "to masha Allahu naji daɗin hakan sosai, Allah ya nuna mana", his excelency yace "Ameen ngd," mai martaba yace "yayi kyau ina y'ayaa na suke"? His Excellency yace "gasu nan wlh yanzu ma break muka gama," mai martaba yace yayi kyau "ina babban ɗana ashmir"? His ecxelency yace "tuzuru dai zakace," mai martaba yace "No no! Ni ɗana ba tuzuru bane duk gaba ɗaya guda nawa yake 36yrs ne fa gaba ɗayan sa". His Excellency "yace kana dai ƙare masa ne sabida ɗan ka ne ko"? Mai martaba yace "to ai komai lokaci ne, shima zai yi auren ai with time insha Allah." To nan dai suka ƙarƙare wayar su cikin nishaɗi bayan dad ya ajiye wayar sa ne, sai yaga duk ya'yan na sa sun zuba mashi ido suna kallon sa amma banda ashmir, domin shi ashmir ma wayar sa kawai yake operating. Nan dad yayi gyaran murya, kowa hankalin shi ya dawo kanshi, harda mum wato Hajiya Nuhaira, dad yace "ahm inada magana daku yau ko?" Suka gyada kai gaba dayansu, dad yace "to akwai companies na gwamnati da za'a buɗe nan da 3mounths sannan kuma da wasu breeche's da kuma hanyoyin da gwamnati tayi to shi ne nake son buɗe su by that time wato nan da 3months kenan, so sannan kuma zanyi tafiya jibi zanje japan, sai nayi 1mounth zan dawo, bayan na dawo sai mu fara shirin buɗe abubuwan da za'a buɗe ɗin. So kafin nan kai ashmir ka karbi hutu acan ƙasar da kake aiki, ke kuma baby noor zanyi wa director na makarantar waya sai a bamu hutu na 3days sabida ana bukatar ku gaba ɗaya agun, Right?". Suka ce "Yes Dad." To kai kuma ashmir yaushe zaka koma chan garin? Nan fa ashmir ya ɗago kanshi yana kallon dad sannan yace "sai nan da 1 week dad". Nan dad yace "to ina son kafin ka koma chan, dole saika fito da matar aure," dudum! Kirjin ashmir ya buga to shi ina yaga budurwa? Shi dai yasan yanada masoya wato mata masu son shi amma shi ko kallo basu ishe shi ba, abun takaicin ma harda turawa wai faɗa suke a kanshi, kwanakin baya harda zuwa police station wai daya ta chizke gashin ɗaya, shi ko yace bai ma san sunayi ba. Nan fa dad yace "uhm da kai nake fa so nake kafito da matar aure next idan ka dawo nan da 3months sai a ɗaura maku aure ko Hajiya"? Ya kalli mum, mum tace "hakane kam ur excellence nima nagaji da zaman shi a haka." Nan fa ashmir ya marairai ce kamar ƙaramin yaro yace "pls mum nd dad kar ku min haka pls, wlh I have no idea about this, pls ku bani time har yanzu ban samu wacce nakeso ba ne," dad yace "kamar ya ashmir mai kake so ka mai damu ne? Ƙananan yara ko mai? To bari kaji, na baka daga yau zuwa gobe kafito da wacce ka ke so, idan ba haka ba duk hukuncin dana zartar haka zakabi." Tofah! Wayyo Allah ashimir duniyar tayi masa zafi, dady ba zai gane ba ne amma shi wlh yanada tsari akan matar da zai aura, yafison mace me aji da kamun kai baya son masu bibiyar sa, sabida basu da aji, shi fa idan mace ta fara cewa tana son sa shikenan ya raina ta sabida ba mutunci da kamala, alamarin gaba ɗaya. Da mum taga abun yayi wa lovely son ɗin ta yawa ne, sai ta ɗanyi gyaran murya tace, "pls ur Excellency kayi hakuri har nan da jibi kan kayi tafiya zan shawo kan problem ɗin kaji?" Dad yace "ai nasani sai kin ƙare shi wato antaɓa ɗan lelenki ko?" Mum tayi murmushi irin nasu na manya tace" no! Zaujih, kawai dai nason halin son, baya kula mata, suke son sa but amma shi baya son su kana gani har biyo shi gida suke, amma shi yace baya son mace mara kamun kai, so pls zaujih muɗanyi masa hakuri, insha Allahu Rabbi zai fito da matar aure soon kaji"? dad dai gyaɗa kai kawai yayi sannan yace " nidai na gaya masa nan da gobe ko jibi ina sauraran sa. Nan fa dad ya miƙe ya nufi part ɗinsa, nan kuwa ashmir ya miƙe yaje ya kwantar da kansa a kan cinyar mum yanata mayar da numfashi, saida ya natsu tukun yace wa mum "pls mum ki taimaki rayuwa ta kar dad ya min auran dole pls mum ki shaho kanshi kinji mum pls," ya marairaice sosai nan fa mum ta shafa kansa, tace "kaima son da naka kullum maganar kenan, kaƙi fito da matar aure, to yanzu dai shikenan naji zanje na shaho kan shi kaji, but amma ka kiyaye gaba." Itako noor tayi caraf ta cafke zancen da cewa "yaya ashmir wlh kazo na baka wata frnd ɗita me suna princess nihal, wlh Yaya she is very nice and beautiful, wlh kana ganin ta zakaji kana son ta, pls Yaya ashmir ka amince kuma wlh gata da class da kamun kai ga aji, wlh bata bawa maza fuska kwatakwata, kuma yar Sarau... Shut up!!! Noor bana son zancen banza da harkan yarinta mai zanyi da sa'ar ki gayyar ƙuruciya, Allah ya kiyaye min. Itako noor ta turo ɗan ƙaramin bakinta, tace a ranta "ai nasani dama yaya ba ayi maka gwaninta ko tsaya wa ma bai yiba na gama faɗa mishi wacece ita ba, kuma gata jinin sarauta ce ma". Nan ashmir ya rungume mum yana ta godiya haɗe da cewa "dama nasani ai mum u luvs me more." Mum ta miƙe itama noor ta miƙe tabi bayan mum yaya nasir kuwa yaje gaban ɗan uwansa ya dafa sa yace"pls bro karka damu da abinda dad ya faɗa kaji? Kuma insha Allahu ba zai maka auran dole ba". nan fa ashmir ya rungume ɗan uwansa yace "thanks my love." To wannan kenan... *ASALIN* *SU* *ASHMIR* *HIS* *EXCELLENCY* wato (dad) asalin sa shima ba kano ne kuma Bahaushe ne na usul, su biyu mahaifiyar su ta haifa, wato dai yana da ɗan'uwa, mahaifin su babban ɗan kasuwa ne wanda ya shahara, Mai suna Alh Nasir Mai Naira, inda ya auri mahaifiyar su a wata riga bayan yaje rigan domin siyan shanayen sallah domin a lokacin babban sallah ya matso, saida ya sayi tirke guda domin yana bada sadakan su. Sunan ta midilli mahaifin ta ne babban mai kuɗi a rigan sabida shi ne mai bada sarin shanaye, aikuwa Alh Nasir yana ganin midilli yace inba ita ba sai rijiya domin tana da kyau sosai ga hankali, saide rashin wayewa, to nan fa Alh Nasir ya magantu kuma shi bada wasa yake ba, nan dai har aka ba shi auren ta, Bayan anyi biki ne ya kaita birni cikin babban gidan sa kuma ya ɗauko malami ana koya mata karatu a cewar sa "wai ko bata je makaranta ba brain ɗin ta ya ɗan washe, ace dai she can read an write, hakan ma is enough. To haka dai sukayi ta zaman su har ta haifi babban ɗanta me suna, Abdulkarim (his excellence) sai kuma kabeer wato kanin sa kenan. Inda haka dai suka yi ta girma,shi Abdulkarim ya fi son yayi karatun boko sosai shi kuma kabeer yafi son harkan kasuwanci, shiyasa yana gama NCE ya fada harkan kasuwan ci, shi kuma Abdulkarim sai da yayi degree ɗinsa na farko a jamihar bayero, bayan nan ya tafi ABU Zaria yayi masters ɗinshi, kawai yana kammala masters ɗin shi ya faɗa harkan siyasa, to ana haka ya tafi ƙasar Uganda yin wani course akan harkan siyasa, saida yayi 8mounths achan tukunna ya kamma ya biya yayi ummarah, to shi ne ya biya ta Kasar Sudan ya gaisa da wani abokin sa daya ke zaman chan, tunda shi friend ɗin nasa lecturer ne a jami'an Sudan ɗin, ya shiga makarantar kenan yaga wata ɗaliba me suna nuhaira, asalin ta balarabiyar chan ce tana zaune da iyayenta amma mahaifinta ya rasu, tana zaune da mahaifiyar ta ne, tana karatu ta gama 1s degree ɗin ta yanzu masters takeyi a wannan jami'ar, shi ne ta haɗu da Abdulkarim, Ba tare da ɓata time ba Abdulkarim yaji ya yaba daita gata kyakkyawa ce ajin karshe gatada ilimi da kuma hankali ga kuma asali, to shi ne yafaɗa wa abokin sa, shi kuma yayi mashi hanya har suka je gidansu. Nan kuwa nuhaira ta karɓi soyayyar Abdulkarim ba tare da ɓata lokaci ba sabida shima ɗin kyakkyawa ne Kasan cewar ya ɗauko mahaifiyarsa, kuma gashi da natsuwa sosai ga kuma uwa uba ilimi, to bayan nan, sai ta kai shi gun mahaifiyar ta, ya nemi auran ta, da farko mahaifiyar ta taso ta ƙi sabida ba k'abilan su bane, gashi zai rabata da tilon yarta, zata yi nisa da ita, to amma da yake nuhaira na son sa, sai ta lallaɓa mahaifiyar ta harta yarda da auran. To wannan kenan.. Pls more comments✍️✍️✍️✍️ _Taku_ _Qwinn_ _minerhly_ _Mrs_ _Yusuf_ ❤️❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _ina_ _fatan_ _xaya_ _nishaɗantar_ , _daku_ _haɗi_ _da_ _ilmantarwa_ , _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 30_35 GIDAN SARAUTA mum!!! mum!!!, Wai meye ne kike ta wani kwala min kira my princess? Wlh mum, yanzu mukayi waya da noor, tace min "tana so tazo guna, but Mum u no wannan brodern nata ya dawo, kuma mum kinsan shi da takura yake, baya barinta fita idan yana nan, mum pls kibar ni naje gidan su yau, pls mum?" Mum ta ce "naji, zaki je but ku daina yi da ɗana ashmir sabida, ashmir akwai hankali da sanin ya kamata, yaron na birgrni sosai". nihal tace "hmm mum kenan kinaji da wannan ɗan naki, wanda Ni ban sanki da wani ɗa ba, bayan yaya adnan", Mum tace " eh ai bazaki san shi ba tunda baki da zumunci. nan dai noor ta katse zancen domin ita ta gaji da maganan ma wlh, ita banda mum, abba, yaya adnan, sai kuma ƙawarta noor, ai bata dogon zance, kuma shima yaya adnan ɗin shine yake janta da zance, amma da bazata iya da shi ba, aikuwa gimbiya tacewa mum " alright mum bari naje fada, zan gaida dad after then, sai nazo na shirya, okay"? Mum tace "to shikenan my princess ashirya lfya", nihal tace " yauwa godiya nake mum." To bayan fitar gimbiya nihal ne, ta durfafi part ɗin mai martaba, nan kuwa barori suka dinga mika gaisuwa gurin gimbiya, itako ta murtuke fuska, tana gyada kai ahankali kamar hawainiya, aikuwa tana shiga part ɗin mai martaba ta nemi guri a kusa da shi ta zauna, ta gaishe shi, mai martaba ya amsa da fara'ar sa ganin princess ɗin nasa, sai a time ɗin gimbiya ta lura da Hajiya kilishi wato uwargidan mai martaba mahaifiyar adnan, aikuwa gimbiya ta gaishe ta, ta amsa mata ba yabo ba fallasa, shi kuma adnan wanda sai a lokacin yayi magana yace "ahm my lil sis dama kina nan, kwana biyu bamu haɗu ba." gimbiya tace "eh wlh yaya adnan dafatan an tashi lafiya?" Yace "lafiya lau ƙanwata ya kike? Tace "lafiya brother." aikuwa hajiya kilishi tayi ta wurga masa harara , amma fa a ɓoye saboda tana tsoron kar mai martaba ya ganta, nan ta miƙe tace wa Mai martaba "ranka shi daɗe a yini lafiya na barka lafiya", mai martaba yace "yauwa kilishi a sauka lafiya," tace "Amin nagode", tana miƙe wa ta cewa adnan, "idan ka fito ina jiran ka yarima," yace mata "yauwa umma angama", tafi ce ta barsu a zaune, shi ko mai martaba ya kalli ya'yan nasa yayi murmushi yace "Allah ya maku albarka," su kace "Amen ranka ya daɗe", ya ɗaura da cewa "yauwa akwai wani companies da zamu buɗe nan da 3months, kuma muna so ku ma ku halarci gun, don haka ke gimbiya zanwa director na school ɗinku waya akan karban excuse, kuma ina so ki fara shirya shiryan komawa school daga yau because nan da 4 days zaku koma , really"? Nihal ta girgiza kai tace " haka ne abba kuma insha Allahu zan fara shirye-shiryen." yace "yauwa my princess take care of yourself," tace "insha Allahu dad." Nan ya dawo da duban sa ga adnan yace "yarima da fatan ka fahimci abinda nake nufi," adnan yace "am sorry dad, but pls kayi hakuri at that time inada wani schedules da freinds ɗina so pls dad am sorry ba lallai na samu daman halarta ba.. shutup my friend!!! Mai martaba ya faɗa cikin tsawa, ya cigaba, adnan wlh ka kiyaye bacin raina, sakarai kawai, kai kullum sai shashanci da abokai, to wlh na kusan ɗaukar mataki akan ka stupid, mara hankali, na kawo magana mai mahimmanci kai ka kawo min shiririta, to bari muga nawa za'a ɗauka, to baka isa ba. nan fa adnan yayi ta sosa kai alamar mara gaskiya yace "don Allah abba kayi min gafara na tuba kayi hakuri wlh bazan sake ba," aikuwa nan dad yace "yimin shiru, ko dan uwarka tana goya maka baya shiyasa kake iskancin da kaga dama ko?" Yarima yace "am so sorry dad," gimbiya tace "pls dad kayi masa afuwa tunda ya tuba kaji dad? Sai anan mai martaba ya gyada kai yace alright shikenan amma a kiyaye gaba, suka ce insha Allahu, nan suka miƙe suka fice suna wa mai martaba sallama. Bayan sun fito yarima yace wa gimbiya "lil sis sai ina kuma"? Tace "wlh brother zan ɗan fita ne yau," yarima yace mata "alright sai kin dawo lil sis," tace masa "to shikenan bro bye". tayi wucewar ta. Tana isa part ɗin ta, ta ɗauki wayar ta, ta kira noor, achan ɓangaren noor ta ɗaga waya haɗe da cewa "wow besty kamar kinsan ke nake tunani yanzu", nihal tace wlh kuwa besty gani nan yau zan cika alkawarin da na daɗe ina ɗauka, noor tayi charaf tace "ba dai gidan mu zakizo ba? Gimbiya tace "yeah besty am coming right now. nan kuwa noor ta kurma wani uban ihu tace "kai amma naji daɗi wlh, gimbiya da tayi saurin kawar wayar daga kunnen ta sabida kar noor ta toshe mata kunnuwa ta daina ji dasu, tayi maza ta mayar tace "kai noor meye na ihu kuma? Noor tace "bari kawai sis ko nayi maki bayani ba zaki gane ba", gimbiya tayi murmushi tace "eh ai ganuwa sai ku, iyalan Elizabeth", dariya noor tayi tace "lah abun harda su zagi to wlh karki bari yan elegant su ji ki," nan kuwa gimbiya tayi murmushi tace "hmm wlh ko sunji Ni babu abinda zasu iya min," noor tace hhhh to ai shikenan, sai kinzo ɗin dai, gimbiya tace "alright saikin ganni, ta kashe wayar ta, ta fada bathroom tayi wanka, ta fito ta tsaya, ta shafa cream, ta gyara gashin ta, ta feshe jikin ta da turare, ta nufi dressing room ɗin ta, ta je ta ɗauko wani tsadaddan less red nd black, tayi simple ɗaurin ɗwankwali, ta ɗauki wani alkyabba baƙi mai santsi bugun Dubai ta ɗaura akai, wow tayi matuƙar kyau wlh gimbiya kenan, an iya ɗaukan wanka, ta ɗauki wani heel red color ta saka, faɗar irin kyan da tayi ma ɓata lokaci ne, domin har wani haska gun takeyi. Nan ta fito bayin ta na biye da ita, tana takun ƙasaita kamar hawainiya, ta nufi part ɗin mum ta mata sallama, mum tace ga wannan ki kaiwa yata noor, gimbiya ta duba taga wani haɗaddan alkyabba ne, shigen irin na jikin ta amma shi wannan yafi stones, da kyau, kuma shi peach ne zallah sai sheƙi yake, aikuwa gimbiya tace wow mum yaushe kikayi ordern irin wannan?, yayi kyau sosai, mum kuma wlh jiya Anty fanan, (ƙanwar maman nihal ce, tana zaune ne a dubai,ita da mijinta da ƴaƴanta). Jiya ta turo min da irin su sak wai a satin nan aka sake su a Dubai, shi ne nace zamu yi ordern sa da yawa, aikuwa mum tace "eh nima shekaran jiya nasaka order, yau kuma ya iso, ku biyu dama na saka wa order keda noor, kuma kalan ɗaya ne, babu bambanci," nan nihal ta rungume mum tana murna tace "mun gode mum sosai," mum tace "ki gaishe min da hajiya nuhaira, noor tace "zataji kuwa insha Allah, to shikenan saina dawo mum, mum tace a dawo lafiya, tace "Allah yasa Amin. Tana fitowa bayin ta suka yafa mata baya, suna isa haraban gidan, wajan parking space aikuwa motoci ne a parke agun sunfi a ƙirga, nan kuwa gimbiya ta ɗaga masu hannu, tace "dawa za kuje ? common get out of my side!!! Ba daku zani ba, da kaina zanyi drive yau ku koma, har ku tayi poiting bodyguard ɗin ta aikuwa suka zube suna mata kirari, ɗaya yace to ran gimbiya ya daɗe wani mota zaki hau a buɗe miki marfin ta? Batare da tace komai ba, tayi poiting ɗin wata haɗaddiyar mota (AUDI RS5) nan kuwa aka buɗe mata shi, ta shiga ta bashi wuta tayi ficewar ta, ta ɗau hanya, sai government house, aikuwa tana zuwa get aka buɗe mata, kasancewar akwai number gidan sarauta ajikin motar, aikuwa gimbiya tana shiga ta nufi main parlour taga babu kowa, Kasan cewar yanzu mum suka bar parlon, ita da ashmir, don ashmir ne ma yayi mata sallama ya tafi, a cewar sa yayi baƙo, wani freind ɗinsa ne yazo ziyartar sa, aikuwa yana miƙewa, mum ma ta miƙe. nan kuwa gimbiya ta nufi part ɗin mum ta gaishe da mum, tayi murna da ganin ta, tace "welcome to U mu daughter, I miss u a lot, nan gimbiya taje tayi hugging ɗin mum, sannan ta duƙa ta gaishe ta mum ta amsa da fara'a tace "yasu hajiya Fulani da sauran mutan gidan? Gimbiya tace kowa lfya mum, "mum tace a gaishe ki, aikuwa tace ina amsa wa, nan noor ta shigo a guje ta rungemi gimbiya tace ur highly welcome my lovely friend, gimbiya tace thanks my luv, mum tayi murmushi tace "to uwar surutu zaki rakata can part ɗin, ta warware gajiya ko kuwa? Noor tayi dariya tace "mum yanzu zamu tafi ai, don naga nihal bata saki jikin ta anan ba, sai ka ce wacce ta je gaishe da surukarta, nan gimbiya ta daɗa sunkuyar da kanta domin wani kunyar mum taji ya sake shiganta, aikuwa mum ta wurgi noor da thow pillows ɗin da suke jere a akusa da gadon ɗakin, nan kuwa noor ta ja hannun nihal suka tafi, mum tace "jaira da kin tsaya ai, parrot kawaii." Nan fa mum ta fara tunanin ilham a matsayin surukar ta, aikuwa da taji ɗaɗin hakan sabida tana matuƙar son yarinyar, dama tunanin noor ya zama gaske. Noor suna shigowa part ɗin ta, gimbiya ta zuba mata duka a baya, noor ta zuba ihu tace "shi ne zaki na kasa min baya ki cuci mijina ko? Gimbiya ta rike baki tace oh sweet luv am sorry but kinsan baki kyauta min ba ko? Kin san ai zanji kunyar mum, kika faɗi wannan maganar, kuma kinsan da kunya ko", noor tace "to meye? Ai babu komai, mum ai social mum ce karki damu", ta ɗaga mata gira ɗaya, nan gimbiya tayi murmushi tace "daɗi na da yan jarida, iya zance da zaƙin baki, noor tayi dariya, tace, "am coming few minutes," nihal ta gyada mata kai, noor na fita ta je tayiwa Peter bayanin abubuwan da zai kawo masu ita da bakuwar ta, aikuwa ta taho kenan ta hango yaya ashmir da abokin sa suna tahowa, aikuwa ta ƙarasa ta gaishe da su, abokinsa me suna fayal yace "wow lil sis amma fa kin girma sosai, so beautiful, ashmir yayi murmushi yace "to aku is okay don naga alama idan kuka haɗu da noor sai ku yini kuna surutu domin ita ma gwanace, noor ta turo baki tace "yaya fayal ka ganshi ko? Kullum sai yace min parot, fayal yace rabu da shi, kin san ai shi kurma ne baya magana, ga shegen miskilanci, ai kan yakarasa ashmir ya doka masa wata uban harara, yace nayi gaba idan ka gama zuban ina ciki, yayi tafiyar sa, kasancewar fayal yasan hali, shi yasa yayi murmushi ya dafa lil sis yace "don't mind ashmir, haka yake kullum, shi baya son yawan magana, but lil sis sai anijima bari naje na samu mutumin nawa ko"? Nan noor ta gyaɗa mishi kanta haɗe da murmushi, tace "yauwa yaya fayal bye", ta miƙe ta dawo cikin part ɗinta ta samu ilham na kallon laptor ɗin ta, ta ƙaraso tace "sorry my luv na barki ko? Gimbiya tace no ba komai ai ina kallon pics dinki ne a gallary, tace ki ce kinga brothers ɗina guda biyu? Nihal ta girgiza kai tace "no ban kai nan ba but ai zan gani ko ba yanzu ba, aushsh nayi mantuwa, noor tace "me kika manta? Nihal tace "no ba damuwa yana cikin mota mum ce tabani saƙo na kawo miki, noor tayi murmushi tace "Allah sarki luvly mum ɗina, aikuwa naji daɗi wlh, ilham tace "eh idan na tashi tafiya sai ki karba yana mota, noor tace "okay ba damuwa," to daman tun ɗazu Peter ya zo ya ajiye tire tire na kayan kwalam da makulashe, Noor ta matso masu da kayan lasawa, tacewa ilham "pls ki matso kici abinci", gimbiya tace "wlh bana jin yunwa," noor tace "wlh baki isa ba kawai ki matso ko dambun nama kici, pls my luv" ilham ta matso tace "kai! ni wlh kin takura min" noor tace "eh naji ɗin amma sai kin ci, ke bari ma ki gani da kaina zan baki a baki," ta ɗebi dambun nama a ƙaramin spoon ta kai saitin bakin gimbiya tace ahm, to sanin halin noor da kafiya shi yasa bata musa ba, ta buɗa baki, aikuwa noor ta zuba mata a baki, suna cikin haka ilham tace "yaisa na koshi" noor tace "saura yurghourt ta tsiyaya mata shi a cup ta bata shima ta sha. Can noor tace "wai besty lafiya kuwa kike"? Gimbiya tace "mai kika gani"? Noor tace "wlh da ganinki akwai abinda yake damunki", ilham tace "wlh babu komai sist", noor tace "lallai ma yaushe muka fara ɓoye wa junan mu abu"? Nihal tayi murmushi sannan tace "ai bamu taɓa ba, kuma ba zamu taɓa ba, insha Allahu." Tace "sister kinsan dai bana soyayya ko"? Noor ta girgiza kai alamar eh, Ta cigaba da bata labarin wannan haɗaddan gayan da ta haɗu da shi a palace, har izuwa mafarkin shi da tayi da kuma yawan tunanin shi da take yi. Ta ɗaura da cewa "ni abinda nake tunani shi ne, maybe sabida ina so na rama abinda yayi min ne shi yasa nake yawan tunanin shi ko besty?" Noor ta ɗan yi ajiyar zuciya da jin labarin ilham sannan tace "a gaskiya besty Abinda na lura da shi a cikin story ɗinki kamar kin kamu da soyayya ne". What wlh ba gaskiya tunanin ki ya baki ba, taya zan so wannan mugun mutumin, wlh bazan so shi ba, kina nufin ya bugu banza? Ko kina nufin ya zagi banza, kuma ya sha? To ki buɗe kunnan ki kiji ni, wlh sai na rama abinda yayi min ko waye shi. Noor tayi murmushi tace "Besty baza ki gane ba ne, but amma na barki shike nan, idan tayi tsami ma ji. "Kai nifa wlh ka fara bani haushi, a ce mutum ba dama a fara zancen budurwa ko aure sai ya ɓata fuska wai shi baya so, sai ka ce wani dutse." "Cewar fayal" Tsaki ashmir ya ja sannan yace "kanka ake ji." Fayal yace "kai ma ɗin kanka a keji." Ashmir yace "comm'on pls mu bar wannan zancen, ni tambaya ce ma dani." Fayal yace "ina jin ka freind". Saida ya ɗanyi jimm sannan yace "pls wai meke sa mutum ya paya tunanin abu, ko kuma ka faya mafarkin abu?" "Cewar ashmir" Fayal yace "amma kafin na baka amsar tambayar ka, zan so naji akan me kake yawan mafarki da tunani?" Ashmir yace "na tambaye ka, kai ma ka tambaye ni, so pls bana son haka, babu ruwan ka da sanin wannan, idan zaka bani amsar tambaya ta to, idan kuma baza ka bani amsar ba to shike nan." Fayal yayi murmushi idan da sabo ya saba da halin ashmir. Sannan yace "okay! Pls ka maida wukar, sannan kuma ga amsar tambayar ka." A gaskiya abinda yake jawo yawan mafarke mafarke da kuma yawan tunanin abu, ba komai bane illa kasa ka abun a ranka,domin idan ka saka abu a ranka, za kaji ka faya tunanin wannan abin har ma da mafarkin sa. Pls freind ka faɗa min meke faruwa ne?pls ashmir. Ashmir ya kwashe komai daya faru tsakanin shi da wannan yarinyar ya faɗa wa fayal, sannan yace nifa freind na kasa gane komai,brain ɗina ya toshe. Fayal yace "frend akwai mafita but saika bani haɗin kai tukun, sannan sai ka yarda da cewar ka kamu da soyayyar wannan yarinyar ne, sai kuma mu samu mafita." Is okay pls, bana son yawan comments, ni babu wani soyyaya, na rasa da wacce zanyi soyayya sai da fitsararriya, to bazan iya ba, kasan me kake faɗa." Murmushi fayal yayi sannan yace "gud, wlh wannan kafiyar taka yana birgeni muje zuwa, amma kar a sake azo nemen shawarata wata rana, kuma ka tashi ka raka ni zan tafi. Fayal ya mike, ashmir ma ya mike haɗe da cewa "naga alamar kayi fushi ko to sai kayita yi bazan baka hakuri. Besty yaushe zamu je saloon gyaran gashi? "Cewar noor" Gobe sai mu je saloon ɗin, sabida kinsan nanda 4days zamu koma ko? "Cewar gimbiya" To shike nan besty Allah ya kaimu goben, "Ameen" Besty tashi ki rakani zan tafi, "cewar nihal" Nihal tun yanzu zaki tafi ? To ai noor magriba yana daf dayi kuma kinga na yini maki da wuri nazo fa. To shike nan muje ki sallami mum saimu tafi. Nan suka miƙe gaba ɗayan su, suka nufi part ɗin mum, nihal tace "mum zan tafi," Mum tace "my princess har zaki tafi?" Nihal taji daɗin sunan sabida haka mum ɗin ta ke ƙiran ta. Tace "Yes Mum zan tafi magrib ya kusa". Mum ta miƙo wa nihal wata ƙatuwar leda haɗe da cewa "ga wannan my princess, ki gaishe min da Hajiya Fulani." Nihal ta noke tace mum harda ɗawainiya? Mum tace ke noor gashi rike mata rakata har mota, noor ta karba tayi wa Mum godiya, nihal ma tayi godiya haɗe da cewa mum zataji inshallah, nan suka fice sai parking space. "A hankali ta dinga hango bayan shi, domin suna da nisa a tsakanin su, sabida sune a gaba, kawai taji gaban ta ya faɗi." Bayan wa aka hango? Wai shin ashmir da nihal suna haɗuwa kuwa? Idan sun haɗu me zai faru? Ku biyo ni a next page domin jin ya zata kasance. Taku Qwinn minerhl Mr Yusuf ❤️❤️❤️ More comment more typing✍️✍️✍️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _ina_ _fatan_ _xaya_ _nishaɗantar_ , _daku_ _haɗi_ _da_ _ilmantarwa_ , _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 40_45 Shi ko yaya fayal tunda ya ga princess nihal gaba daya ya rasa sukunin sa,duk ya rikice a kan ta, yana kwance a kan 3 sitter din dake parlon sa, sai ya dauki wayar sa ya kira noor, tana daga wa suka gaisa, yace mata "pls noor ki bani num din kawar ki pls lil sis," Itako noor tace "to shikenan yaya fayal bari na kirata na fada mata ko, sai na turo maka shi true sms. Fayal yace "yauwa lil sis Nagode kwarai da gaske." Tace masa "ba komi yaya". A can ɓangaren yaya ashmir kuwa yana can cikin daki yana ta wani aiki da aka kira sa a waya yanzu a can jarmany wai suna buƙatar taimakon sa na gaggawa ko ta laptop ne, to shi ne ya dukufa yana ta aikin shi cikin natsuwa. Gidan Alhaji kabeer Hajiya binta ce ta kira yar ta wato islam, ta zaunar daita ta bata wani turare tace "ungo wannan Malam na tudu ne jiya da naje ya bani yace "ki shafa a jikin ki yanzu kitafi government house yanzu kije ku gana da ashmir, kuma ki tabbatar ya shafi koda mayafin ki ne kinji na gaya miki," Islam tayi wani ihu ta rungume mamin tace "nagode mami ai dama nasani ke ta daban ce, sai na auri yaya ashmir." Nan ta tashi ta shirya cikin riga da wando damammu ta daura afterdress a kai ta yi wa mami sallama ta tafi. A dayan part din ne ita kuma Hajiya Hafsah yanzu ta gama waya da aminiyar ta me suna hajiya salame, ta gama zugata akan wai Amira ta tafi government house, ta je tayi kwana biyu sabida zasu fi shakuwa da ashmir, wai ta dinga shishige masa a jiki a sosai, wannan ne mafitan su. Inda Amira ta ce a bari ita sai gobe ta tafi wai yau zata je saloon tayi gyaran gashi da kuma na jiki. GOVERNMENT HOUSE suna kan dinning suna breakfast gaba dayan su amma banda daddy shi baya nan wai suna da meeting a nan government house din shida ministry of education na jahar. Bayan sun kammala ne sai suka ji ana nocking hade da sallama inda Islam ta shigo cikin parlon ta durkusa ta gaishe da mummy, ta kuma gaishe yaya ashmir da kuma yaya nasir, ashmir a yatsine fuska yace lfya. Shi kuma yaya nasir cewa yayi " ahh Islam ce yau a gidan na mu? Tace wlh kuwa yaya nasir Ni ce", sai cewa yayi very gud kin kyauta kwarai wlh. Shiko gogan karamin tsaki yayi ya tashi yace "mummy zan dan shiga ciki" mumy tace "to son a fito lafiya." Mummy ta ce "Islam ina yan gidan naku da Amira?" Islam tace wlh mummy duk suna nan sunce na gaishe ku gaba daya. "Muna amsa wa cewa mummy". Islam tace "noor ko magana babu yau kin wani share ni" Noor tace "sorry my sist naga kuna ta hira da yaya Nasir ne shi yasa na kyale ku kar na takura maku ko?" Chan noor ta ce "mummy bari nazo na tafi kinsan yau ne zamuje saloon da besty ko?" Mummy tace "alright sai kun dawo" Noor tayi hugging din islam tace "kina nan dai ko har na dawo koma dai ya kamata ki kwana mana a nan", Islam tace "wlh anjima da yamma zan koma ba kwana zanyi ba." Nan noor tasa kai tana cewa "alright sai na dawo mummy da yaya nasir" Suka amsa da a dawo lafya. Can mummy ta tashi tace "bari na shiga ciki islam," Islam tace "to mummy sai na shigo bangaren naki." Islam ta dubi yaya nasir tace "babban yaya yana ina?" Yace mata "yana part din shi', Tace to bari na leka sa Tana zuwa part din babban yaya ta hau nocking.... Ita kuma noor ta tafi sun hade da neehal a can wani katafaren saloon me suna PRINCESS GLAMOUR'S SALOON mallakin neehal ne, babban saloon ne babu abinda ba sayi anan akwai bangaren maza akwai na mata. Sun hadu anan parking space din gurin suka shiga gun tare suna hiran yaushe gamo. Sunje anyi musu gyaran gashi, gyaran fuska, da kuma wankin kafa. Bayan sun fito ne zasu tafi boutique sun nufi parking space din gurin sai wani hadaddan guy ya fito daga cikin saloon din bangaren maza, sai hango su, aikuwa yayi maza ya nufe su yace da su "hy guys ya kuke?" Dukan su suka kauda fuska wai a cewar basu ma san yana yi ba. Aikuwa yace "pls yan mata ku taimaka wa rayuwa na ku saurare ni," Nan ya shiga rattafo zance shi wai yana son gimbiya kuma don Allah ta bashi number ta. Noor tace "kayi hakuri an bada ita" Neehal da tuni ta bude murfin mota zata shiga ya maza ya riko murfin, ya durkusa har kasa, kuma gashi haddaden gaye, gashi da ga gani yana ji da kansa. Kawai sai gimbiya tace "mike ya zaka duka kasa a kan wannan abun?" Aikuwa gayan yace "wlh ko cewa kikayi na yi tsallan kwado yi zanyi?" Gimbiya tace "zan baka number ta amma da sharadi" Yace eh "na yarda ko mene ne sharadin" Tace "bana son yawan kira, zaka ga ka kira ba lallai na daga ba kuma bana son dogon zance a waya kaji ni"? Da gudu yace mata "eh eh naji Madam wlh haka za'a yi" Ta sa masa number ta, ta cewa noor "ki shiga naki motar mu tafi" Aikuwa nan kowa yaja motor sa suka bar gun. Bayan sun shiga boutique sun gama siyyaya sai suka tafi gun biyan kudi, suna zuwa aka ce wai an biya masu kudin su, neehal tace "wane ne shi din?" Ai suma suna da kudin biya ko sunyi masu kama da wadan da baza su iya biya bane," shidai accountant sai basu hakuri yake, yana cewa wlh me girma chirman ne yazo yanzu da ya ganku kuna siyyaya sai yace "kada a bari ku biya kudi shi zai biya maku, kuma dama shi ne me boutique din." Noor tace "shut up malan ai bamu tambaye ka ka fada mana ko shi waye ba". Da kyar ya samu ya basu hakuri suka hakura. Suna fito wa, suka hange shi a wani dan table a kusa da wani office. Yana hango su ya taso da sauri sauri. Assalamu alaikum Barkan ku da wannan lokacin yan mata, Aciki ciki suka amsa sallama. Yace "suna na Alh Adamu, dan Allah ko zaku bani dama na gabatar maku da kaina?" Neehal ta kawar da kai, Noor tace "malam dan Allah kayi hakuri wlh sauri muke mu koma gida." Yace "dama da ke nake son nagana dan Allah ko zaki bani dama?" Noor ta juyar da kanta can gefe. Ita kuma nihal tace "to Alh adam kayi hakuri ba zaka samu shiga ba," Yace haba dan Allah kuyi hakuri mana yan mata kuyi min alfarma, ai nasa ni, daga ganin ku, ku ba irin wadan nan yan matan bane mara sa kamun kai." Nihal tace "to shikenan tunda kace Allah ai angama magana, kawo wayar ka nasa maka number ta." Da sauri ya bata wayar, tasa ka mashi number, ita kuma noor sai wurgo wa nihal harara take. Nihal tayi kamar bata ganta ba, shi ko Alh Adamu sai godiya yake zabgawa nihal. Kowa ya nufi tashi motar, nihal tace wa noor "pls besty karki wulakanta shi, ki saurare shi pls kinji kawata?" Noor tace "alright naji, kuma kema ki shirya domin yau zan bawa yaya fayal number ki, domin ya dame ni, dama cewa nayi sai mun hadu zan maki bayani kinji kawata? ki kular min da kanki pls n pls ki gaida mummy kinji?" Nihal tayi murmushi sannan tace "to ya zan dake tunda haka kika yi besty, kar ki damu zan kula da kaina kuma zan isar da sakon ki, sai anijima, my regard to mum." Nan dai kowa ya tada motar shi yaja, suka bar gurin gaba daya. Duk wannan abun Alh Adamu yana kallon su cike da birgewa domin wlh sun birgeshi sosai gasu kyawawa da su, bai san lokacin da wani murmushi ya subuce masa ba. Mrs Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _ina_ _fatan_ _xaya_ _nishaɗantar_ , _daku_ _haɗi_ _da_ _ilmantarwa_ , _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 35_40 "A hankali ta dinga hango bayan shi,domin suna da nisa a tsakanin su, sabida sune a gaba, kawai sai taji gaban ta ya faɗi." Oh my God, "cewar fayal" What happened? "Cewar ashmir." Ashmir am coming rights now, na manta waya na beside bed. "Cewar fayal" Okay, saika dawo kuma kayi sauri. "Cewar ashmir" Tafiya yake, kawai ya hango wata kyakkyawar yarinya tana tahowa, "innallilahi wace ce wannan? Gaskia ina son ta wlh I love her, kawai sai ya doshe su domin ya ganta da noor, kuma ya tabbatar ƙawar ta ce. Nan fa fayal ya nufu su, yana zuwa noor tace "lahhh yaya fayal kaine?" Fayal yayi wani murnushi me sauti haɗi da cewa "yeah lil sis ni ne." Noor tace "yaya fayal ina yaya ash... Ai kafin ta ƙarasa fayal yace "lil sis is she ur friend? Haɗe da pointing ɗin nihal. Noor tace "eh yaya fayal nihal ce, ƙawa ta ce kuma aminiya ta ce." Sai a sannan nihal ta ɗago ta kalli fayal, eh lallai dai kam ba laifi yana da kyau, amma ko kadan bai birge ta ba. Sai taga kamar bai dace ba ace bata gaishe shi ba, sabida ita a tunanin ta ma shi ne babban yaya da taji noor na yawan faɗa. Saida ta ɗan yi jim sannan tace "ina wuni" Fayal daya daskare a gun tun lokacin da gimbiya ta ɗago tana kallon shi, sabida bai gama ganin kyan ta ba saida ta ɗago. Yace "lafiya lau gimbiyar mata, da fatan kina lafiya? Gimbiya tace "lafiya a gajarce". Fayal yace "very nice" Gimbiya tace "ahm besty nayi gaba zan je na tada motor kafin ki ƙara so." Noor tace "okay besty" Ai kanfin ta ƙarasa gimbiya tayi gaba, sabida ta gaji da kallon da fayal yake mata. Noor tace "yaya fayal ina yaya ashmir? Fayal yace "yana can cikin motar zamu fita ne da shi, sai kuma nayi mantuwa, shi ne na dawo zan je na ɗauko sai na hango ki keda ƙawar ki, pls noor help me wlh I fall in love with her, wlh ta haɗu sosai, she is very nice." noor tayi haɗiyar zuciya haɗi da cewa "yaya fayal gimbiya tana da tsari amma nayi maka alƙawarin shawo maka kanta, dama a da naso ta da yaya ashmir, shi kuma yaƙi saurara ta, kasan halin shi, to amma tunda kana son ta inshallah I will try my best yaya fayal." Nan ya riƙo hannun noor yana cewa "thanks my sister idan kika yi min haka kin gama min komai, nagode." Noor ta yi murmushi tace "babu komai yaya fayal, let me go to her tana jirana." Fayal yace "is okay sai an jima lil sis thanks." Noor tayi gaba tana saƙe saƙe a cikin ranta. Shi kuma fayal har ya nufi part din ashmir sai ya shafa aljihun shi yaji wayar tasa a ciki, murmushi yayi yace "awesome dama ina tare da waya na shi ne na dawo ɗaukar ta, wow to rabon na haɗu da baby luv ɗita ce, i love that. Acan ɓangaren ashmir ya gaji da jiran sa, ya shige mota yana zaune yana researching wani abu a wayar sa, to shi ne ya dauke masa hankali har bai damu ba sosai. Sai ga fayal ya dawo, ya buɗe motar ya shiga, ashmir ya haɗe rai sosai haɗe da cewa "aina ka tsaya? Kuma sai ka barni a mota ina jiran ka sai kace wani drivern ka?" Murmushi fayal yayi sabida ya san za'a rina, sannan yace "sorry friend baza'a kuma, kasan me ya faru kuwa a wannan fitar ta wa? Ashmir yace "ina zan sani nida ka barni a anan, sai ka faɗa." Fayal yayi murmushi yace "freind yau nayi wani babban kamo wlh a gidan nan, wata ƙawar noor ce tazo, ashmir ta haɗu to the extent, wlh bayan yan gidan nan ban taba ganin kyakkyawa irin ta ba, aboki na kasan ku ɗin na daban ne sabida idan akace maka Balarabe an gama Magana, but ina matukar son ta wlh yana faɗa yana murnushi." Ɗan ƙaramin tsaki ashmir yaja sannan yace "kullum kai a haka kake, yau kaga wannnan gobe kaga wancan, pls freind kar ka zubar min da girma a idon su noor, sabida kaje yau kuma ka jajiɓo mana wata ƙaramar yarinya, wai ita ƙawar noor, banda yarinta mai za'ayi anan? Pls cool down mana aboki na, suwa da suwa kake magana akai? Daga maryam da raiha sai kuma zee to har wani yawa ne dasu kuma su ɗin ma duk sune suke bi na, zee ce kawai na san ina sonta, kuma itama yau na haɗu da wacce nafi so a duniya sai dai tayi hakuri." Taɓe baki ashmir yayi yace "nidai na faɗa maka kar je ka rage mana ƙima a idon yara." Murmushi fayal yayi, bai yi magana ba, drivern ashmir ne ya jasu suka tafi. Noor tana ƙara sawa taga nihal jingeni da motar ta, noor tace "sory habbibty na barki na tsaya na ɗan sallami yaya fayal ne shi yasa na ɗan jima." Hararar ta nihal tayi, noor ta matso kusa da ita tace "sorry ko habibty." Nihal tace "shike nan ya wuce zan tafi besty, ga saƙon da mum tace a baki, ta faɗa haɗe da miƙa mata jakar. Noor ta ƙarba ta buɗe jakar taga wani haɗaddan alkyabba, tayi hugging ɗin nihal tace wow ina godiya kiyiwa mum godiya, wlh yayi kyau sosai." Nihal tace "yayi kyau, haɗe da shige wa cikin motar sannan tace gobe ki shirya around 12:00pm sai mu tafi saloon ɗin okay?" Noor tace babu danuwa, Allah ya kaimu, kema ga saƙon da mum ta baki nan, ta ajiye mata a sit ɗin baya. Nihal tace "godiya nake sosai freind I will miss u." Me too I will miss u alot, take care of ur self, drive safe. "Cewar Noor haɗe da ɗaga mata hannu tana mata bye." Nihal ta fice da gudu haɗe da murmushi a kan fukarta. Wannan kenan Taku Qwinn minerhly Mr Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* Assalamu alaikum, masoyan book din nan ina godiya, Allah ya bar zumunci Amin, sannan ina barar addu'ar ku, ga yayata, Allah Ubangiji yayi mata rahama, Allah ya kai haske kabarin ta, Amin thumma Amin👏👏👏👏👏👏 _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 55_60 Sai nanata Innalillahi waiinna ilaihi rajiun yake..... Amma duk wannan maganar acikin zuciyarsa yake yi, Fayal yace "ya dai naga kamar ka tafi tunani ko ka santa ne?" Da sauri ashmir ya gyada kansa yana cewa "no ban santa ba, kawai dai tayi min kama da wata ce." Ajiyar zuciya fayal yayi "yana cewa Alhmdlhi kar ka ballo min ruwa." Nan suka ci gaba da hiran su, inda gaba daya hankalin ashmir yayi can wani gurin. Alh adamu ne a cikin office dinsa yana kallon hotunan su noor da ta saka a status dinta na gefen sweeming pool a school dinsu, sai doka murmushi yake tayi yana cewa "kinyi kyau my princess u look so cute, kamar a sace ki, inda yayi mata comments da kinyi kyau my noor, ya school din?" Dukan su na hango a gefen pool suna ta nishadi abin su, suna hira, noor ce taga anyi mata message, ta duba sai taga Alh adam ne, tayi mashi reply, suka ci-gaba da hiran su, sai ga wani Baturen saurayi kyakkyawa da shi ya zo gun, Yana yi musu magana, hi guy's, suka ansa mashi da hi, nan ya fara rattafo zance wai shi noor yake so waya mutu waya tashi, aikuwa Minal tace mashi "idan kana so mu ba ka ita sai kayi mana Yaren mu wato hausa, nan fa ya dinga bin bakin su yana jin me suke fada shima yana jagwalgwalawa, su kuma suka dinga kwasan dariya abinsu, tun daga ranar ya zama freind din su, ko'ina yana bin su. Government house Bayan rabuwar fayal da ashmir, yaya ashmir ya shiga matsanancin damuwa domin bai san yana son wannan yarinyar ba sai ranan, yanzu ya kara zama so silent, baya son yawan magana da shiga mutane, wai dama haka soyayya take? Shi dai Allah ya sani yana son ta, gashi abokin sa na son ta, kuma ya riga shi furta wa, ya zama dole ya bar masa ita, shi dai ya shiga ukun sa, a haka ya keta tunanin ta kullum. Amira ta gama kwanakin ta har ta tafi, an hada mata goma ta arziki, ta tafi da shi, don daddy ma sai da ya bata babban kyauta ita da yar uwar ta. Ta koma gida cike da farin ciki da annashuwa. Bayan kwana biyu Mummy ce a cikin dakin ta, tana tasbihi, amma hankalinta yana can gun son, ta daina ganin sa, ya daina zuwa ayi breakfast dashi, ya daina zuwa lunch, ya daina zuwa dinner, ya daina zuwa hira daita a part dinta, to bari ita ta je ta gano shi ko lfya, gashi ya kusa koma wa jermany aikin sa. Mum ce a dakin yaya ashmir a kusa da gadon sa, tana cewa "son meya same ka, baka da lafiya ne shi ne baka fada wa kowa ba, ta taɓa jikin sa taji da zafi rau, son me kake so ka fada min, pls son tell me, what's going on son?" Ashmir ne ya samu da kyar ya buɗe bakin sa, yana cewa mummy, "mummy bani da lafiya ne, sannan kuma akwai wata yarinya da nake yawan dreaming dinta, wlh mummy son ta nake yi, ban taba tunanin zan so wata y'a a duniya ba sai yau, mummy sai de kash da matsala." Cikin ruɗe wa mummy take tambayar shi mece ce matsalar? Jimm yayi yana tunani, kawai gwara kar ya cewa mummy itace kawar noor, gwara yace mata bai san inda take ba, sabida itace zabin abokin sa, mum matsalar itace, ban san inda take ba, so daya na taba ganin ta, kuma ban sake ganin ta ba sai a mafarki." Nauyayyan ajiyar zuciya Mum ta sauke tana cewa "son soyayya ce ta mai da kai haka, son tunda nake da kai baka taɓa ce min kana son wata ba sai yau, lallai dole nasan abun yi, dole na nemo maka ita son insha Allahu." Nan tayi wa family doctor su waya take sanar da shi yazo ya duba ashmir. Doctor suraj, ne akan ashmir yana duba sa, inda ya gano cewa damuwa da tunani ce kawai ta haifar masa da ciwo, kuma idan bai rage ba zai iya haddasa masa ciwon zuciya. To bayan doctor Suraj ya gama masa treatment, har ya samu bacci, bayan nan doctor ya tafi. Bayan kwana biyu ashmir ne da doctor suraj, yana ɗan dada masa wasu gwaje gwaje, inda ya gano ashmir ya warware sosai sai abinda baza a rasa ba. Doctor ne yake cewa ashmir "haba dr ashmir sai kace ba CARDIOLOGIST BA (LIKITAN ZUCIYA) gaba daya ka sawa zuciyar ka damuwa to dan Allah a bi a hankali, kune fa masu taimakawa mutane, to kuma idan kuma kuka rafke wa zai duba su, so pls doctor take it easy, nd ko da ban san abinda kake so ba nasan insha Allahu bazai fi karfin ka." Nan ashmir ya shiga masa godiya yana masa sallama. Yau ne hutun ashmir ya ƙare, zai koma jermany, jiki yayi kyau sosai, yana yi wa mutan gidan sallama, nasir kuma zai raka sa har airport. Nihal ce take waya da fayal, yana ta ce mata shi yayi missing din ta wlh zai biyo ta america har school, nihal ta rike baki tana cewa "rufa min asiri, ka dai yi hakuri mun kusa karɓar excuse, zamu dawo sai ka ganni." Noor kuma suna can gefe ita da minal da wannan baturan mai suna lucky, suna ta hira suna shan ice cream abin su. After 1 months da dawowarsa jermany, yana hakince a kan wani hadaddan kujera, yana ta lilo da shi, da wani soft drink a hannun sa, idon sa alumshe kamar mai bacci, amma ba bacci yake ba, kawai dai yana enjoying moment din ne. Wayar sa ce tayi ruri, sai da ta kusan katsewa tukun ya ɗauka, yana duba sunan ya maza ya daga. Muryar sa a sarke yake cewa "hlo lil sis, y school? Sai da noor ta shagwabe fuska tukun tace "wlh brother baka so na, ka manta dani kwakwata, baka nema na, sai idan ni ce na neme ka." Sai da ta gama tukun ya shiga rarrashin ta, yana cewa sorry lil sis, wlh kina rai na, kawai dai aiki ne ya min yawa shiya sa ba kya jina amma yanzu zan dinga neman ki kinji ko?" Nan ta gyada kai tana cewa "to yaya, yanzu yaushe zaka kawo min visiting? Sai da yayi jimm sannan yace "on Sunday insha Allah zaki ganni kinji ko? Nan ta shiga murna tana cewa "Allah ya kawo ka lafiya big bross." Yayi hanging din wayar yana jinjina rigimar lil sis, mumushi yayi da shi kadai ya baiwa kan shi sani. Bayan 2 days, ashmir ne a school din su noor, yanzu yayi parking, da ya ke ya hana mabiyan sa bin sa, suma anan sun bashi masu tsaro sabida kasancewar sa babban ma'aikaci a wannan babban asibiti, to amma yau shi kadai ya fito. Da gudun ta ta fito tana ihun yaya ashmir!!! Oyo yo, ta yi hugging dinsa, da gudun ta, tana cewa "nayi missing dinka yaya ashmir," Lil sis zaki kada ni fa, ke ba kya girma ko, kullum kamar karamar yarinya kike ko, to sake ni ya isa haka let's have a sit." Nan ta ja shi suka zauna a wasu chairs da suke jera a gun, suna zama yayi pecking din ta a goshi yana ce mata "i miss u too my lil sis." Nan suka shiga hiran yaushe gamo, tana ta bashi labarin su nihal da minal. Yaya ashmir me ya same ka naga duk ka rame amma ka ƙara fari sosai? Hmm lil sis wata damuwa ce dani wlh amma barshi kawai nan gaba zaki ji. Ina kawayen naki, mu gaisa sabida ni tafiya zanyi. Yaya ashmir bari na je na kira maka su, sai ku gaisa kasan ban fada masu yau zaka zo ba, so nake na yi musu surprising, yaya baka ci komai ba, muje kaci abinci a restaurant din can, wlh yaya sun iya abinci." No lil sis bar abincin nan, ba sai na ci ba, a koshe nake wlh, yi sauri kije ki kirawo su mu gaisa kinga sai kira na ake a waya. Yauwa yaya am coming. Da gudun ta, ta tafi kiran su nihal da minal. Sai de tana cikin tafiya suka ci karo da minal amma ba nihal, minal ina besty take? Wlh noor banga ta ba, tun dazu nake neman ta nima. Kema ina ta neman ki wlh ban gan ki ba. Wlh kinga yaya ashmir ne ya kawo min visiting, dama surprising din ku zan yi, shi ya sa ban fada maku ba, kinga kawai muje ke ki gaisa da shi dan wlh sauri yake yi, amma naji ba dadi dan na so, su gaisa da yaya ashmir yau wlh, tunda suke basu taba gaisawa ba,kuma itama nihal ɗin tana so su gaisa da shi. To ya za'ayi kawai muje mu gaisa a isar mata da saƙon ta, cewar minal. Suna ƙara so wa, gurin suka zauna a chairs din, noor tace "yaya ashmir ga minal nan ku gaisa, banga besty ta ba." Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo dan ya so ya ganta wlh ko sau daya ne. Minal kuwa daskare wa tayi a gun sabida ashmir ya mata mugun kyau ga kwarjini, da kyar ta iya cewa "ina wuni yaya ashmir" Lafiya lau kawar lil sis ya kuke, ya school din? Wlh school alhmdlh To masha Allah sannun ku, Lil sis zan tafi take care, yayi hugging dinta hade da pecking dinta a goshi, sannan ya mika mata wata ƙatuwar leda yace "take it, ke da friend's dinki." Noor ta ce mun gode yaya ashmir, u too take care of ur self, ka kular min da kanka yaya, mun gode," Minal ma tace mun gode yaya ashmir, take care" Nan ya shige motar sa ya tada ita. Sai ga nihal ta taho tana ihun besty minal where are you guys? Mr Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 50_55 ________can dai ta nusa tace da shi, "Alh adam, ina so pls kabi komai a hankali, kuma ka fahimce ni da kyau, a gaskiya ni yanzu ko zance bana yi, sabida yanayin tsarin gidan mu, kuma wlh bani da ra'ayin auran mai mata, amma kuma kayi hakuri, kabi komai a hankali kuma kasan ance matar mutum kabarin sa." Nan Alh adamu ya ji wani abu ya doki zuciyar sa, amma abinka da babban mutum, sai yayi murmushi haɗe da sauke ajiyar zuciya, sannan yace "ba komai baby noor am waiting for the day, dat u will accept my request, Keep waiting. Kin san dama haka abin yake kuma kowa da ra'ayinsa, amma pls ki bani dama na dinga waya da ke, kin ji ni baby Noor?" Nan dai noor ta amince da hakan, suka ci gaba da hiran su. Islam ce ta faɗa dakin mamin ta da gudu, tana murna, mami tace "yata lafiya naga kin dawo kina murna?" Nan islam ta kwashe duk yacce aka yi a government house, ta fadawa mami, sannan ta daura da cewa, "wlh mami yaya ashmir ya fara so na, dan baki ga, yanda ya dinga jana da hira ba, kuma kamar kar mu rabu." Murmushi mami tayi irin nasu na shu'umai sannan tace "ai na fada miki Islam, sai ashmir ya so ki, kuma mu aure shi mu juya shi, kuma ni nasan malam na tudu, bazai taba bani kunya ba." Nan suka ci gaba da kulle kullen su. Washe gari A ɗayan part din gidan kuwa, amira na hango sai kwalliya ake ɗauka, tayi kyau a cikin wani doguwar riga na less, ta sha ɗaurin ɗan kwali. Umma ce ta kalli ɗiyar tata sannan tace "wannan kwalliya haka ai ko gasar kyau zaki je sai haka, kuma kya lashe sabida kinyi kyau." Amira tace "umma ai gwara nayi kwalliya, ko na sace masa zuciya, kin san Yaya ashmir din nawa akwai son ado da kwalliya." Umma tace eeh kwarai kuwa,amma gwara ki maza ki tashi ki tafi sabida kar ya fita, kije baki same shi ba." Government house Suna babban parlon gidan gaba dayan su, har daddy, suna kallon wani indian series film a zeeworld mai suna *Khushi Dreams* film din yana da dadi da ma'ana sosai, ashmir kuwa bai taba zama ya kalli irin wannan film din ba sai yau, amma sai yaji da dadi. Yarinyar Film din akwai tsiwa, kuma gata kyakkyawa, sai shima ya dinga tunato wannan yar aljanar yarinyar mai shegen tsiwa, ko meye sunan ta ma, oho. Ita kuma noor kasancewar gobe da safe ne tafiyar su, tana can cikin kitchen tana lissafa wa cook din su abinda zata mata na tafiya school, irin su dambun kaza Kilishi Soyyayan nama etc. Ita a cewar ta wai tafi son yin gida, yafi dadi. Sallaman amira ce ta dawo da ashmir daga tunanin daya tafi, nan ta zauna ta shiga gaishe da da Daddy, daddy yace "zo nan yata, saukar yaushe? Amira tace "yanzu na iso daddy" Ina su baban ku da iyayen ku, da kanwar ki? Amira tace "wlh daddy suna nan klau kuma suna gaishe ku" Daddy yace"madallah" Nan ta gaishe da mummy, mummy ta amsa da fara'ar ta, tana mai tambayian amira ya mutan gidan. Sannan ta gaishe da yaya ashmir da kuma yaya nasir. Ashmir kuwa ganin ga mum ga daddy, shiyasa ya amsa mata da fara'ar sa. Shi kuwa nasir sai da suka dan taba hira da shi ma, kunsan shi akwai barkwanci. Nan ta tambayi noor taga bata ganta ba Mummy tace mata "noor tana can cikin kitchen kinsan gobe zata koma school. Amira da gudun ta, ta tafi inda noor take, tana zuwa ta rungumo ta ta baya, haɗe da rufe mata ido. Sannan ta ce "ki canki ko waye? Nan noor tace mata "sist amira ce" Amira ta sake ra tana dariya sannan tace "gud, ai na ɗauka bazaki gane Ni ba ne. Noor tace "haba dai ai dana ji kunya kuwa." Nan suka shiga hiran yaushe gamo, inda anan amira take jin cewar wai islam tazo jiya, nan ta cika da mamaki. Can na hango gimbiya da noor sun jero a tare suna ta farinci ki, zasu shiga wani katafaren restaurant, mai suna (special gift restaurant) nan na hango gimbiya da noor, ana jere masu abinci kala kala, sai wanda suka ci. Suna tsaka da cin abincin su, sai ga wata yar school dinsu ta tunkaro su, tana zuwa kuwa ta nemi kujera ta zauna tare da cewa, "hlo guys, suna na Amina Salis Daura, amma anfi sani na da minal asalin mu yan daura ne amma yanzu muna zaune a garin Abuja, babana wato salis Aminu daura shi ne ministry of health, na garin Abuja, na dade ina ganin ku a school din nan, wlh kuna birgeni, gaku kyakkyawa, gaku da aji, pls ko zan iya zama friend din ku, wato na cike ta ukun ku?" Nihal ce ta dago kanta tana kallon minal, ita kuma noor dama tun dazu da minal ta fara bayani take kallon ta, inda suka ganta da kyau, itama kyakkyawa ce, black beauty ce, gata da hanci, ga karamin baki, gata doguwa. Noor ce ta fara magana kamar haka "ur welcome mhiz minal, nice to meet u, kuma babu komai zamu iya zama freind." Sai a sannan nihal ma tayi magana kamar haka "nice to meet u dear, muna maki Barka da zuwa cikin mu." Nan minal tace masu "thanks dearest friends, na gabatar maku da kaina kuma ku gabatar min da kanku" Noor ce ta fara gabatar mata da kanta, itama nihal ta gabatar. Minal tace "WOW kuce daga princess sai his excellent, nan suka kwashe da dariya suka ce kedai baki da dama wlh. Bayan sun kammala cin abincin. Kasancewar kowa da department dinsa, nan kowa ya watse, ya shiga ya daukar lecture. nihal ta shiga part dinta wato bangaren, low department. Ita kuma noor, mass communication department. Ita kuma minal, science health department. Skyline University kenan da ke Wow Russian Under American Government house Amira ce a part din ashmir, sai fira take mashi, shi kuma ya ɗan sake mata fuska, sabida fadan da mummy ta mishi a kansu, cewar ko baya son su, bai kamata ya dinga wulakanta ta su ba. To shiyasa ya ɗan sakar wa amira fuska kadan, ita kuma sai farinci ki take, nocking suka ji anayi, aikuwa amira ta je bakin door din tana cewa "waye? Yace Ni ne fayal, kasan cewar ta san shi abokin yaya ashmir ne, shiya sa ta maza ta bude masa kofar. Aikuwa yana shigo wa, amira ta gaishe shi, fayal ya ansa da fara'ar sa, yana cewa "yau mutan Zooroad ne a gidan na mu," amira tace"eh wlh yaya fayal, ai ku ba kwa neman mu, saide mu neme ku mu, ta fada tana satan kallon yaya ashmir, shi kuwa yana jinsu, amma sai yayi kamar baya jinsu, ya ci-gaba da latsa wayar sa. Nan fayal yace "mun isa mu watsar da mutan Zooroad, ai wlh bamu isa ba, kawai dai bamu leko ta nan bane." Ko mutumina? Ya fada yana kallon ashmir. Ashmir kuwa taɓe bakin sa yayi bai ce komai ba. Fayal yace "ai matsala ta da kai kenan, wulakanci, dan tunda na shigo yi kayi kamar baka ganni ba, kai wlh kana da matsala, ace mutum sai shegen miskilanci kamar mai aljanu. Shi dai ashmir yana jinsa yayi masa banza, wayar sa ce ta hau ruri, yana du bawa yaga daga kasar Sudan ake kiran sa, yana duba wa ko yaga sunan liara ce me kiran, wato yar kanin baban mummy, Wanda suke kira da Uncle sauban ko kuma ammih sauban a larabce. Nan ya daga wayar hade da juya harshen sa, ya koma balaraben sa sak, nan su kayi ta zancen su da liara, tana ba shi labarin tayi wani saurayi tsoho zai yi sa'an baban ta, wato suger daddy, shiko ashmir mai zaiyi banda dariya, harda rike cikin sa yana cewa cikin harshen larabci, kawai ki so shi, tunda yana sonki, kuma zai kula da ke sosai, kinsan irinsu akwai showing caring." Nan liarah ta shiga cewa "lallai dan uwa yanzu na tabbatar da cewar baka so na, shikenan na gode." Ashimir ko da kyar ya tsagaita dariyar sa yana cewa "no, ni ba haka nake nufi ba, but kiyi hakuri, yana fada yana gintse dariyar sa, Ita kuwa liara sabida takaici har hawaye tayi, amma saita dake ta kashe wayar ta kawai. Shi ko ashmir kashe wayar sa yayi yana dariyar ƙeta, nan amira ta cika tayi fam ita ala dole kishin sa take, wai ai ta gano da mace yake wayar sa, har yake ta babbaka dariyar sa, wanda tunda take da shi bata taba ganin yayi irin wannan dariyar ba. Nan ta tashi fuhhh ta fice a parlon gaba daya. Shi ko ashmir wani dariyar ya kuma yi yana cewa "dama kin ishe ni wlh, duk kin hanani sakewa nida gidana." Shi ko fayal zugum yayi yana kallon abokin sa. Ashimir yace meye haka zaka wani zuba min ido kana kallo na sai kace wani maye." Fayal yace "eh ka kira ni da maye mana, tunda ka gama miskilancin naka, ace anyi mutum kana magana da shi yayi maka banza kuma har a gaban sister din mu." Ashmir cewa yayi "come down my freind, to kayi hakuri, tunda kai dole so kake sai na baka hakuri sai kace wani yaro." Murmushi fayal yayi yana cewa "ya zan da kai, ai dole na hakura." Nan suka shiga hiran su na abokai. Fayal ne yake operating wayar sa, kawai sai yaga gimbiya nihal tayi opdate din status dinta, ta rubuta chills at de school with my besties, ta saka pics din su ita da noor da minal suna gefen sweeming pool, da yake school din akwai swimming pool aciki. Nan fa fayal ya gigice yana cewa "wow my luv kinyi kyau sosai wlh, kamar na zo nayi hugging dinki nake ji, kaga ashmir wannan lover tawa Dana ke fada maka ne kawar noor, ka ganta wlh she is gergurse she look so beautiful. Ashmir yace "ni fa ka kyale ni, bana ciki da yarintar ku," Fayal yace "ai kawai ganin ta nake so kayi, kasan cewa yarinyar akwai rikita mutum." Ashmir ko cewa yayi "pls ka kyale ni mana nifa ka isheni wlh, kuma naga idan na ganta ma so what?...ai bai karasa maganar ba bakin sa ya ƙame ƙamas, what my dream girl, wannan mara kunyar yarinyar ne dama, wacce yake yawan tunani da mafarki, ita fayal ya gani yake so, ai bai san sanda yaji kirjinsa ya wani buga ba, sai nanata innalilahi wainna ilaihi raijiun yake.... Mr yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 45_50 Shiko babban yaya ji yayi a nata masa nock. Can dai ya nusa ya mike da kyar ya karasa jikin door din yace "wane ne yake ta min nocking tun dazu?" Islam cikin sanyin murya tace "Ni ce Islam yaya ashmir". Sai da ya ɗan dada bata rai tukun ya bude mata kofa, ya maza ya koma ciki. Islam tace "yaya ashmir ina kwana ya aiki?" Yace mata "lfya alhmdlh," Islam tace yaya ashe ka jima da dawo wa hutu Ni wlh ban sani ba, ai da tuni na zo." Ashmir ko cewa yayi "ai yanzun ma is okay". Nan fa Islam aka fara zuba kamar parrot. "Yaya wlh nayi missing dinka sosai, wai yaya pls yaushe zamu sha bikin ka ne? Yaya kaza, yaya kaza. Shiko ashmir ma wlh ta ishe shi da surutu gashi ta hana shi aikin sa. Aikuwa sai tashi yayi zai nufi bedroom din shi, sabida ya gaji da surutun ta, nan kuwa Islam ta bi shi zata riko hannun sa, ashmir yaji duk ransa ya ɓaci kawai sai juyo ya wanka wa Islam mari, yace "ke ashe baki da tarbiyya, har kina kokarin riko min hannu, to ke ba kida hankali ne, shasha kawai, out of my house yanzu ba sai an jima ba. Islam da fuskar ta yayi jazir kawai saita fashe da kuka, ta fice da gudu sabida ta san halin sa zai iya kara mata wani marin. Tana fito wa kuwa ta durkushe tayi ta kuka, sai da tayi ta gaji sannan ta share fuskar ta, ta nufi part din mummy. Mummy na zaune taji sallamar islam, ta ce mata "maza shigo yata, zo ki zauna anan." Mummy ta lura da fuskar Islam kwarai kamar tayi kuka, sai tace mata Islam lafiya? kuwa naga fuskar ki kamar kinyi kuka, sai Islam tace "wlh mummy yaya ashmir ne ya ci min mutunci wai sabida kawai naje part din shi". Mummy da ta san za'a rina sai tace mata "lallai son bai kyauta ba amma kiyi hakuri kinji doughter ta, zan mashi magana karya kara, kin ci abinci kuwa?" Islam ta gyada kai "mummy ba yanzu ba sai an jima zanci" Mummy ta murmusa tace alright dear to jeki wancan dakin, ki huta, bari na kira miki peter yazo ya kawo miki kayan kwalam da makulashe kinji". Islam tayi murmushi tace "yauwa mummy na gode sosai." GIDAN SARAUTA Gimbiya ce a part din mummy wato fulani, suna ta hira na tsakanin ɗa da uwa, mummy take cewa gimbiya, "doughter yaushe zaki fito mana da siriki, kinga kuna gama school sai ayi bikin, ko?" Gimbiya ta wani ɓata rai tace cike da shagwaba "ni fa wlh mummy ba wani auran da zan yi yanzu, kuma ma mummy bazan iya barin ki ba na tafi." Mummy tace "aa ni wlh ki daina fake wa dani, kuma aure ai ya zama dole doughter." Gimbiya dai murmusa wa mummy tayi bata kuma cewa komai ba. Can dai wayar gimbiya tayi ta ruri tana ringing, tayi banza da wayar kamar bata ji ba, sai da mummy tayi mata magana tukun ta tashi ta tafi dayan parlon mummy tayi receiving din kiran. Ta daga wayar a yangan ce tace "hello" Da sauri ya ce "hello gimbiyar zuciya ta, ya kike ya kuma kika je gida, da fatan kina cikin koshin lafiya?" Gimbiya tace "who is on de line?" Yace mata "suna na Abubakar sadiq amma an fi sani na da bubby boy, kuma ni dan gidan duputy governor ne, wato mataimakin gomna,Ni din ɗan gata ne both uwa da uba suna so na, amma wlh gimbiya daga ganin ki naji gaba daya na rufta, wlh am in luv with u, pls gimbiya ki so ni dan Allah, kuma muyi aure. Kina ji na kuwa gimbiya?" Ajiyar zuciya tayi sannan tace "hmmm naji ka mana amma kuma gaskiya sai dai kayi hakuri domin ina da wanda nake so, sai an jima zan kashe waya ta, saboda na gaji zanje na kwanta." Kafin yayi magana yaji kitt, an kashe wayar. Dafe kai yayi yana cewa "oh my God, na shiga ukuna ni sadiq, yau na hadu da gamo na, Ni da nake yaudarar yan mata yau gashi na hadu da wacce na fi so kuma taki saurarata, Nan dai bubby boy ya dinga saka da warwara duk shika dai ya saka waccen ya warware wancan. Gimbiya kuma part dinta ta koma ta kwanta a gado, tana kallon saman dakin, tana ta tunanin wannan me siffan aljanu, Ita dai ta rasa me yake sata yawan tunanin sa, to ko dan yayi mata rashin mutunci ne shiyasa, aikuwa tana cikin tunani kawai taji wayar ta na ringing. Dubawa tayi saita ga sabon number, amma Truecaller ya nuna mata sunan wanda ya kira ta. Sai da wayar tayi ringing kusan 5times tukun ta dauka a yangance. "Hello nihal, bestyn besty ykk,dafatan kin gane me magana, suna na Dr. fayal Muhammad,abokin Dr.ashmir, yayan su noor. Nihal pls ki saurare ni wlh am in luv, pls koda baza ki so ni ba, to pls mu cigaba da zumunci ko kuma na zama freind dinki, sabida bana san na takura Miki, kuma gaggawa ba shida kyau, pls nihal zaki saurare ni?" Saida gimbiya ta dan nusa sannan kuma ta ɗan zurfafa tunanin ta, sannan kuma ko ba komai fayal ya iya kalamai na kwantar da hankali da kuma saukar da kai, sannan can kuma tace "ahm shikenan yayan noor babu damuwa, zamu cigaba da zumunci kafin muga abinda Allah zai yi." Nan fayal ya shiga zuba mata godiya yana mata daɗaɗan kalamai, har sai da suka yi sallama, suka kashe wayar. Nihal dai tana ajiye wayar ta, ta gyara kwanciyar tana ta tunanin rayuwar duniya, can kuma ta koma tunanin me siffar aljanu, wai ita Meya ke damun ta ne, kullum tunanin wanda bai damu daita ba, to meya ke damun ta? Ita da ta dauki alwashin saita rama abinda yayi mata, shine take nema ta kamu da son shi, kai Allah ma ya kiyaye na so wannan mugun me kama da aljanu, to ko dai mummy zan fada wa ayi min saukar Alkur'ani, ko gamo nayi da aljani watakil. Gimbiya dai tana ta tunanin yaya ashmir har sai da bacci yayi awon gaba da ita, kuma shima a bacci ma mafarki sa take tayi. Government house Islam ce a dakin mummy tana wa mummy sallama, zata tafi sabida magrib yayi, mummy sai hada mata sha tara ta arziki take, kuma tace driver ya kaita, Islam tace "mummy wlh da mota ta nazo." Sai mummy tace "to shikenan doughter drive safe, ki kula da kanki, ki gaida min da mutan gidan, sannan ga wannan ki saka a gaban motar ki, sabida tsaro kuma idan kika saka babu wanda zai tare ki ko da kuwa yan road safety ne. Islam kuwa zuba godiya take yi. Noor ce ta shigo cikin dakin mummy, da gudu tayi hugging islam tace "eyya sister kin ki kwana mana, amma ba komai ki gaida su umma da mami." Islam tace "bazan fada ba, bayan ba kya san zuwa gidan mu." Noor ta ce "wlh zanzo, amma next time bayan dawo wa daga school sabida yanzu jibi zamu koma." Islam tace "to babu komai sister sai kin dawo ɗin." Nan dai Islam tayi musu sallama tana tambayan yaya nasir, noor tace mata "yaya nasir baya nan wlh, bai dawo daga office ba, dazu da mu kayi waya, yake ce min "wlh wasu patient aka kawo mashi su uku, sunyi accident." Islam tace"Allah sarki yaya Nasir Allah ya taimaka." Duka suka ce "Amin" Nan Islam tayi musu sallama sannan suka fito ita da noor, islam tace wa noor "noor raka ni part din yaya ashmir, pls zan yi masa sallama ne." Noor tace "okay muje" Nocking suka shiga yi suna sallama, can dai ya fito yace "waye?" Noor tace "yaya ashmir mune." Nan ya bude musu kofa ya maza ya shige ciki, ya nemi kujera ya zauna. Noor ce ta fara gaishe shi, ya amsa yana murnushi, sannan Islam ta gaishe shi, to Kasan cewar mummy tayi masa fada akan abinda ya mata dazu, shi yasa ya ɗan sakar mata fuska kadan yanzu, ya amsa cikin lowly voice din sa, noor tace "yaya wai tafiya zata yi shi ne zata maka sallama, bari ni na tafi, da sauri ashmir yace "no yi zaman ki lil sis" Ita ko Islam dama tsoran sa take shi yasa tayi saurin riko hannun noor, ta marairaice fuska, tace "no sist ki zauna pls" Noor tace to shikenan bari na kunna mana tv mu kalla, ita so take ta ɗan matsa ta ba su guri. Aikuwa Yaya ashmir yace wa Islam "tafiya zakiyi , baza ki kwana ba kenan, Ko sabida school ne? Islam ta fadada murmushin ta, tace "yaya wlh dama bada shirin kwana nazo ba, kuma gobe ina da lecture na safe. Ashmir yace "alright ba damuwa ga wannan sannan ki gaida mutan gidan, ya bude wata yar drawer ya dauko sabbin yan raffers na dubu dubu ya ajiye mata, sannan ya mike ya nufi bedroom ya na cewa noor da take ta kallon wani American series a tashar mbcmax yace "lilsist idan kun fita ki kulle min kofa kinji?" Noor ta ɗago kai tace "alright broder". Nan dai ashmir ya shige dakin sa. Ita ko islam suman zaune tayi dan wlh ashmir ya tafi daita, kuma wlh komai nasa birgeta yake yi, ga kyau. Noor dai sai da ta ɗan tabo ta sannan tace sist Islam ta shi muje pls, dare yana yi. Bayan fitowar su a dakin yaya ashmir saida noor ta raka islam, har parking space din gidan sannan, ta bata kudin da yaya ashmir ya bata, suka yi sallama taja motar ta tafi. Noor ce acikin dakin ta, tana kwance a kan haddan royal bed dinta, tana lullube da bargo. Kawai sai wayar ta ya hau rigging. Sai da yayi ringing kusan so uku, zai yi na hudu shi ne ta ɗaga, acan ɓangaren kuwa taji yana cewa "Assalamu alaikum dafatan kina cikin koshin lafiya sarauniya ta, kuma hasken zuciya ta, kina magana da Alh adamu rano, wanda kuka hadu dazu da rana, a wani special guy's boutique. Dan Allah sunan ki nake son sani don naman ta dazu ban tambaya ba, wlh saving ma da nayi sai my love na saka." Noor tace "sunana noor" a gajarce. Yace "masha Allah nice name" Ya shiga mata bayanin kanshi da kuma sana'a sa "Sunana Alh Adamu Rano, Ni dan Asalin garin rano ne, amma ina zaune a cikin kano, a unguwar hotoro GRA, amma iyaye na suna can rano da zama, ni dan kasuwa ne, ina kasuwanci kayan na maza da na mata, babu abinda bana siyar wa, kama daga less, shadda, atamfa, material, gizna, yadi, kamfala, takalma, mayafai, jakukuna, da dai rauransu. Sannan ina da mata ɗaya da yaya biyu, sunan mata ta fauziyya, yaya kuma inada, ayman shine babba sai kanwar sa me suna amany. Fatan zan samu karɓuwa a gurin ki hajiya noor, kuma wlh auren ki nake so nayi?" Ajiyar zuciya noor tayi sannan ta nusa a tunanin ta, tabbas ta san sunan Alh Adamu Rano sananne ne kuma ya shahara a harkan kasuwanci, dan akwai wasu yaran shi da suka taba kawo masu kaya suka siya har gida wato dai ordern kayan suka yi. Amma ita Allah ma yasa ni, baza ta iya auren me mata ba wlh." Can dai ta nusa tace .... Made by Qwinn minerhly Mr. Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 65_70 Noor ce ta taho a guje, tana kiran sunan nihal... kawai taji ta bangaje wani bata sani ba. Ke!!! Makauniyar ina ce ke? Ba kya gani ne da zaki bangaje ni? Ban sani ba, waya ce ka tsaya a kan hanya, Ni wlh babu abinda ya min zafi, ko yanzu ka kuma tsaya wa a hanya, sai na bangaje ka, ehe. Duk wannan maganar, bata san da wa take ba, shima bai sani ba. Aikuwa kamar ance su juyo, suka juyo at desame time. Sai lokacin kowan nan su yaga ɗan uwan sa. Shi dai yarima adnan bai san lokacin da ya zaro ido ba, ita kuma sai taji ba dadi domin taga babba ne, zai yi age ɗin big bross. Nan fa adnan ya fara sausauta murya yana cewa "ahm ƙanwata idan baza ki damu ba, ina son magana da ke pls." Noor ta cuno baki tana cewa "ina jin ka," Adnan ya ce "no ba a nan ba, mu samu guri mana mu zauna pls" Ba tayi masa musu ba, suka samu guri suka zauna, nan dai yarima ya fara rattabo zance, shi wlh son noor yake da gaske. Noor dai ta gano shi ne yayan nihal shiyasa taji duk kunyar sa ta kama ta, da sauri ta rufe fuska. Shi kuma ya tsaya yana kallon ta, yana murmushi. Shi ko yaya nasir yace dawa Allah ya haɗa sa idan bada minal ba, ƙawar su noor. Nan ya je ta same ta yayi mata sallama, har suka fara ɗan taba zance, ita ko ta saki jiki da shi, domin yana mata yanayi da yaya ashmir. Nan suka yi ta hira har da kyalkyala dariya. Shima yaya fayal yace tunda ashmir ya naka sa da ƙasa to gwara ya koma a yi yar gida, domin shi kar ya tashi a zero, wai shi kuma amira yake so, nan ya lallaba ya tafi gurin ta. Nan ya je ya samu amira suna ɗan taba hira, amma ita fuskar nan ba yabo ba fallasa, wai ita ala dole ashmir ya shaka mata bakin ciki. Tuni ashmir ya sake nihal yana cewa "servant ɗin ki ne ni da zaki wani lafe a jiki na, ko kuwa dan aikin ki ne ni? taji faɗadd'an kirji harda wani lumshe ido, to kwalelen ki, yafi karfin ki, sai my dream girl, ita kadai zata more wannan faɗadd'ar kirjin." Nihal kuwa tuni wani tuƙuƙi ya turnike ta, aikuwa ta ɓata rai, sannan ta murguɗa masa baƙi, tace "eh ai daya ke ba ni nace ka riko ni ba ehe, me yasa baka barni na faɗi ba, ai ba jikin ka bane nawa ne, ta kuma murguda masa baƙi." Ashmir kuwa wannan ɗan bakin ya so cafke yayi ta tsotsa kamar lolly pop sai de babu dama, nan ya ci-gaba da kallon yadda take motsa bakin, yana murmushi. Sannan yace "kedai faɗi gaskiya yarinya, kishi ne ke damun ki, domin kinji nace kirjina na wata ne. Ya fada yana kashe mata ido ɗaya. Nihal kuwa kasa cewa komai tayi sabida takaici. Yarima adnan ana can ana ta zuba wa noor hira, ita kuma sai dariya take yi, nan taji ya kwanta mata sosai, amma bata nuna masa ba, sai de ta saki jiki da shi sosai. Yaya nasir ma tuni ya zaiyana wa minal sirrin zuciyar shi, ta ko yi na'am da shi, domin ita a tunanin ta, nasir zai maye mata gurbin ashmir, domin ashmir yayi mata nisa, nan suka yi sharing contact. Shi kuwa fayal yana can yana tausan amira, sabida so yake ya fara tausan ta, ta hakura da ashmir, kafin ya fallasa mata sirrin zuciyar sa. Ita kuwa islam ƙanwar amira, tun ɗazu aka tafi daita gida, yau sun shiga tashin hankali ita da mamin ta, yau sun tabbatar da yarda da boka aikin banza ne, yau mami ta fara istigifari a rayuwar ta, tana wa yar ta fatan Allah ya kawo mata wani mafi Alkhairi. Tuni mutane suka fara watsewa a sannu a hankali, inda ashmir yace shi da kanshi zai kai amaryar sa gida. Ita kuma minal kasancewar a gidan su noor zata kwana, shi yasa nasir ya dauke ta suka yi gida wato government house. Itama noor adnan yace "shi zai kaita gida da kansa." Inda fayal ma ya dauki Amira ya kaita gidan su wato Zooroad. Nan kowa ya watse Ashmir ne a harabar gidan sarauta, ya sauke gimbiya nihal sannan ya duƙa saitin kunnun ta, ya raɗa mata "ki kular min da kan ki, kar ki bari komai ya taba min ke, kiyi mafarkina, ki kwana da bege na, masoyi ya ta." Nihal ce ta ce "yaya ashmir meye haka zaka wani kusanto ni, fuskar ka gab da ni kuma kai ba wani abu zaka ce min ba." Nan ashmir ya sosa kansa yana jin wani takaicin kansa, au dama duk wannan maganar ba a fili yake yi ba, a she acikin zuciyarsa yake maganar. Hmmm yarinya ni kike wa tsiwa ko, wlh zan kama ki, za kiyi bayani. Oya wuce gida, take care, ki gaidar min da mum. Nan ta wuce jiki a sanyaye, ita wlh ta dauka ko wani magana mai dadi zai gaya mata, ashe wai babu abinda zai ce mata. Sai da yaga wucewar ta, sannna ya shima ya shige motar sa, ya tafi. Government house Ashmir ne a kusa da Mum, yana mata tausa, yana daddanna wa mum kafar ta. Sannan mum tace "son yau ka bani mamaki fa, to dama kana son nihal ne, ko kuwa? Hmm mum, ai itace wacce nake so, itace wacce kwanaki ta hargitsa ni, mum wai ya akayi su dad suka yanke wannan shawarar ne, kai amma dai daddy ya gama min komai mum. Mum tace "ni dai a tunani na, ranar da suka haɗu akan maganar bikin buɗe companies, to a ranar suka yanke wannan shawarar." Kai amma naji dadi mummy, ance biki nan da 3 months, kin ga kafin nan nayi closeup na aiki na a jamany sai na dawo nan kasa ta. Mum tace "yayi kyau, son na taya ka murnar samun wacce kake so. Dadai nan noor ta fado dakin tana cewa "yaya ashmir dama kana son nihal ban sani ba, kai amma naji dadi, yaya congrat. Smilling yayi mata, sannan yace thanks lil sis. Nihal ce tayi wanka ta sa ka wani light sleeping dress, ta daure gashin ta, ta feshe jikin ta da turare, sai ta nufi part din mummy, tana zuwa tayi hugging din mummy sannan tace "mum sannu da hutawa" Mum tace "yauwa nihal sannu, ya gajiya, dafatan kin karbi zabin daddyn ki, hannu bibiyu, dan ɗana ashmir ba duk kai ba, wlh doughter kinyi dace da samun miji nagari, ina taya ki murna daughter. Nihal kuwa sadda kai kasa tayi bata ce komai ba. Amma mummy ta gane ta karbi zaɓin daddyn ta. Bayan ta dawo daga part ɗin ta ne ta kwanta, domin yin bacci, amma sai tunanin yaya ashmir take yi, da abinda ya wakana a tsakanin su, Ita dai tasan tana son ashmir, idan tace bata son shi tayi ƙarya, hmm to kodai shima yana so na ne, naji harda wani cewa take care. Cike da tunanin sa bacci yayi awon gaba daita. Haka kowanne su, ya kasance a wannan daren. Bayan komawar kowanne su bakin aikin sa, su noor kuma sun koma school. Can na hango noor sai waya take da adnan ɗin ta, anata soyewa, kasancewar yarima adnan, ba karamin so yake wa noor ba. Nihal ma kuwa waya suke da yaya ashmir, sai tsokanan ta yake, ita wlh idan yayi wani abin ma har mamaki yake bata, kamar ba shi ba. Minal kuwa chat suke da yaya nasir ɗin ta, suma yanzu soyayya suke sosai. Alh kabeer ne ya zaunar da iyalin sa yana masu magana...... Mrs Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 70_75 Alh kabeer ne ya zaunar da iyalin sa. suna tattaunawa tsakaninsu, inda yake cewa "kuyi hakuri yaya na, babu komai rayuwar duniya ce, idan banda son kai irin na yaya, taya za'a yi gida bata koshi ba, ka kwasa ka kaiwa na waje, amma babu komai, kuma Abinda nake so da ku shine kuyi hakuri ku dangana, Allah zai baku mafi alkhairi." Nan kuwa suka sunkuyar da kansu, Islam sai hawaye take, umma kuwa cewa tayi "ai babu komai Alh kasan ance matar mutum kabarin sa, dan ga dukkan alamu, ni dai naga kamar amira ta, ta samu mijin aure, don naga akwai wanda yake yawan kiran ta, kuma na tambaye ta, tace min abokin ashmir ne, kaga kuwa mu Allah ya musanya mana da mafi Alkhairi sai dai ko su wance. Ta fada tana kallon mamin islam." Aikuwa bata ce mata komai ba, don yanzu ba kamar da ba, ta rage zafin kishi, sabida ita yanzu damuwar ta, Allah ya fito wa yar ta da mijin aure, duniya ta koya mata hankali. Nan kuwa ya ƙara yi musu nasiha, yana cewa Islam ma kar ta damu, insha Allahu, Allah zai kawo mata mijin aure. Ita kuwa amira yanzu ta saduda ta karbi zaɓin Allah, ta amince da yaya fayal, yanzu soyayya ake zuba wa. GIDAN SARAUTA yarima adnan na hango a fada, shi da mai martaba, kansa a sunkuye, yana ta magiya yana cewa "dan Allah daddy ka shige min gaba, akan maganar yarinyar nan, wlh ina son ta, kuma yanzu na shiryu na daina shan komai, bana bin abokan banza yanzu, pls ranka shi dade ka gafarce ni." Cikin fushi mai martaba yake cewa "yi min shiru, kai ne babban ɗana kuma kai kaɗai ne namiji, kuma kaine magajina, amma sai dai baka da hankalin da zaka iya daukar al'ummar mu, ka gaza, kayi rauni, kuma yanzu kazo ka ce min, wani kana son yar gidan manya, wato kaje ka tozarta ni ko, ko kuma kaje ka kunya ta ni, domin muddin kaje ka watsar da amanar yarinya ai kaga ka kunya ta ni, sabida tsakanin mu da waɗannan mutanen sai dai addu'a sabida nagartattun mutane ne, dan haka ko zan shige maka gaba akan wannan maganar to sai na kafa maka sharudai da kashedi. Cikin sauri yarima yace "wlh na yarda daddy, komai kace na amince zan yi. Nan Mai martaba ya dinga jero masa da shuruɗan sa, shi kuma yana gyada kai, yana cewa "na amince daddy." After three months Nihal na hango, sanye take da wata atamfa pink nd black, wow abinka da farar mace sai tayi wani irin kyau, dama gashi amarya ce, an fara karbar gyaran jiki, sai sheki take ga wani kamshi da ke tashi a sassan jikin ta. Waya take yi, sai wani zumburo baƙi take, tana yatsine fuska, ni fa wlh ka dame ni, taya zaka wani ce in dinga yawo da mayafi a cikin gida don kawai mun fara baƙin biƙi. Okay, to ba zaki yi ba kenan, hmmm yarinya ki bini a sannu fa, zanyi maganin ki. Nasan yanzu ma a haka kike babu mayafi ko? To ki jira ki ga abinda zan yi. Kittt taga ya kashe wayar. Ɗan karamin tsaki taja sannan tace "kayi ka gama, an fada maka ni baiwar kace. Anty fanan ce (kanwar maman nihal) ta shigo part din gimbiya, tana cewa "ke nihal meye haka kike yi, tun dazu mijin ki yazo, amma ko shirin zuwa baki yi ba ko, to wlh ki shiga hankalin ki, domin kiris ya rage ya zama mijin ki yarinya, tashi na shirya ki, ki je gun sa." Nan ta shi tana ta wani zumburo baki, ita ala dole an takura mata, wai to ya akayi ma yazo gidan su, dama ashe dagaske yake, daya ce mata zata ga abinda zai faru, ashe zuwan zai yi, kai yaya ashmir halin ka, sai kai. Hangota yayi a cikin garden din gidan tana tahowa, tuni ya shagaltu da kallon ta, sanye take da wani hadadd'an material, kirar dubai, baki da orange color, yayi mata matukar kyau. Har ta iso gun bai sani ba, turaran dake tashi a jikin ta ne, ya dawo da shi daga duniyar tunani. Ina wuni, ta fada a gajarce. Lafiya ya fada, sannan yace dai ita, "baby luv, meyasa kike da taurin kai ne, ke baki san kishin ki nake ba, ko kuwa kin dauka takura ki nake yi, to wlh ki kiyaye ni." Baki sake nihal ta bi ashmir da kallo, don jin sunan daya ƙira ta da shi, wai baby luv, idan bata manta ba, ta sha mafarkin sa yana kiran ta da wannan sunan, ikon Allah ashe shima yana son ta, yake wani noƙe wa. Ta manta duk wannan tunanin da take wai ashe kuresa tayi da ido, ita zata iya cewa ma, tunda take da shi bata taɓa ƙare masa kallo irin na yau ba, a gaskiya Yaya ashmir Yana da kyau matuƙa. Iska taji ana hure mata a fuskar ta, tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data tafi. Ya dai yan mata, kina ta ƙare min kallo ko, kinga balaraben saurayi, to karki damu an kusa ai, daddy ya taimaki rayuwar ki, tunda kin same ni. Turo baki tayi sannan tace cikin shagwaɓa, "bawa ni nan, ni ce dai na taimaki rayuwar ka, amma ni ai maneji zanyi da kai, ga shi ka zama tuzur.... Ai kasa ƙarasawa tayi sakamakon ƙure ta da yayi da idon sa mai kama da gajimari tsananin kyau, ga shi yau yayi mata wani kyau, kuma sai ya ƙara mata kwarjini. Hmm baby luv Kenan ba dai tsiwa ba, to zan tashi na tafi sai after 4 din, kinsan dai yaune mother's day. Pecking ɗin ta yayi a goshi sannan yace mata gud day, ki kular min da kanki. Nan ya tafi ya shiga motar sa, ya tada ita ya tafi. Nihal kuwa wani farin ciki ta tsinta kan ta da shi kasancewar yau ce rana ta musamman a rayuwar su, yaune ranar da za'a fara gudanar da hidiman bikin su, gashi yau ashmir yayi mata wani irin kyau, ko meyasa. Yau ce ranar Laraba, ranar da aka fara gudanar da taron mother's day, taro yayi taro a wajan mother's day din su nihal da noor, guri yayi kyau masha Allahu, kowa yayi kyau, nan na hango amare sun sha kyau cikin wani kayataccen, Gown me wani tattara a kasa, ya sha stones masu kyau, wow abin dai ba'a cewa komai, kayan su iri daya komai babu bambanci, nan aka cigaba da gudanar da bikin. Washe gari kuma ranar Alhamis, ranar kamun amare kenan, inda aka gudanar da kamu, shima yayi matukar kyau abinka da bikin manya, amare sun sha kyau barakallah, sunyi ado da wani arnen less me kyau da tsada, kalar sky blue, da ratsin silver. Shima anyi an gama cikin tsari. Yau ne ranar juma'a ranar da ake gudanar da wani kayattaccen dinner a wani katafaren hall mai suna DIAMOND LADIES EVENT CENTER, wow hall din ya hadu, mai karatu ka hasko haduwar shi a cikin zuciyar ka, amare sunsha wani irin white wedding gown mai Jan ƙasa, ƙirar turkiyya, sunyi wani irin kyau, anan na hango amaren ashe su uku ne, kasancewar kawar su minal, tare aka hada bikin da na su, to itama a can abuja suke ta nasu hidimar, amma kasancewar yau kayataccen dinner ne shiyasa aka dauko ta, ayi shi a haɗe lokaci ɗaya, angwaye kuma sun sha wani Black suite amma kowa da yanayin nasa, dinner yayi dinner, an gayyato mawaƙa irin su, Umar m Sharif, Hamisu breaker, nura m inuwa, ado gwanja, auta mg boy, da dai sauransu, kowa yazo ya baje kolinsa a gun, sai watsa kudi ake, ashmir kuwa tuni ya riko hannun nihal yana kissing, bayan komawar su kujera, yana ce mata masha Allah amarya ta, kinyi kyau sosai kamar na sace ki mu gudu. Ita kuwa nihal cewa tayi ba sai ka sace ni ba, nan da jibi na zama taka, amma a fili cewa tayi "yaya ashmir ka sake min hannu na, ka ga mutane su mommy's da kowa ma yana gun pls leave my hand, ta fada cike da shagwaɓa." Ashmir kuwa ji yayi jikin sa yayi wani yarrr, tsigan jikin sa, sai tashi yake, ji yake kamar ya kamo ɗan bakin nan nata mai tsiwa ya tsotse shi tas, amma ba hali sai hakuri. Nan aka zo bada cake, su ashmir ne suka fara bada na su, inda yaya ashmir ya ɗauki cake din ya saka a bakin sa, sai da ya tauna sosai sannan ya ɗago kan amaryar sa, ta buɗe baƙi yayi maza ya tura mata rabin cake ɗin bakin sa daya tauna, itama nihal haka tayi sai da ta tauna tukun ta ba sa, haba wa sunyi wani matukar kyau da birgewa, nan guri ya ɗauki tafi ana ta masu vidios. Sauran ma kowa ya bawa kowa. Nan aka ci aka sha taro ya watse. Washe gari ranar asabar, her excellency ce matar gwamna wato maman su ashmir tayi wa dangin ta ƙara aka gudanar da Arabian nights a ranar. Da yake dama da larabawa a bikin sai taron ya ƙayatar sosai, amare sun sha shigar larabawa, kalar black suma angwaye sun sha white din pakistan, kai abin yayi kyau yanda kuka san a can ake yi, shima an gayyato mawakan hipop irin su, dezell, dj ab, morell, nomis gee, classic, g fresh da dai sauran su. Nan aka ci aka sha aka watse kowa yayi gida Lafiya. Ranar Lahadi, rana ce mai cike da dimbin tarihi a rayuwar su nihal domin...... Mr Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Page 75_80 Ranar lahadi, rana ce mai cike da dimbin tarihi a rayuwar su nihal, domin yau ne ake ɗaurin auren su, wannan ɗaurin auren ya haɗa manyan mutane kamar su, manyan yan kasuwa da manyan yan siyasa, da kuma sarakai, gwamnoni kuwa sai da ya haɗa na kusan state biyar ko shida, wasu kuma wakilan su, suka turo, Abin dai sai masha Allahu, nan naji ana sanarwan cewa, an ɗaura auren, DR.ASHMIR ABDULKARIM NASIR GAYA, DA NIHAL BELLO MUHAMMAD SARKI II, NASIR ABDULKARIM NASIR GAYA, tare da AMINA SALIS DAURA (minal), YARIMA ADNAN BELLO MUHAMMAD SARKU II, tare da NOOR ABDULKARIM NASIR GAYA, Bayan idar da ɗaurin auran ne, nan na hango Dr. Ashmir sai murmushi yake dokawa kamar gonar auduga, yana ta gaisawa da mutane, shima yarima mai jiran gado haka sai gaisawa da mutane suke, shima nasir haka, to abin dai sai wanda ya gani, nan aka ƙarasa da baƙi wajan taron walimar maza, hhmm wannan walimar sai wanda ya gani, nan aka fara serving mutane, abinci kala kala, gashassun kaji, dana naman rago, ga pepper chicken da dai sauransu. Islam ce anci ado sai sheƙi take, tana ta sauri zata ƙara sa gidan biƙin, Alh adam rano tsohon saurayin noor, shine yayi kiciɓus da Islam, kasancewar yazo ɗaurin auren su noor ɗin, a gaskiya yaji ciwon rasa noor da yayi, amma ba zai riƙe ta ba, dan ba zai taba manta wani furuci da noor ta taɓa yi masa ba, cewar "matar mutum kabarin sa," don haka yana mata fatan Alhkhairi shima Allah ya musanya masa da kamar ta, aikuwa sai ga shi yayi farin duba inda yayi kiciɓus da Islam, nan yaji kaunar yarinya, aikuwa ba ɓata lokaci yayi mata magana, suka ɗan koma gefe suna zanta wa, to ita Islam dama ita duniya ta koya mata hankali, yanzu ma mijin aure take nema tayi auran ta, domin rufin asirin duk wata ya mace shine aure, nan da nan tayi na'am da Alh adam. Can na hango amare sun sha ado da wani shadda mai kyau da tsada ɗinkin Senegal, ta sha stones da ado, sunyi matukar kyau abun su, noor da nihal baƙi ya mutu murus, an fara zama abin tausayi, gashi wasu freind ɗin su sai tsokanar su suke, kasancewar minal an mayar da ita abuja, sai an jima za'a kawo ta gidan mijin ta. Bayan la'asar sai da aka gudanar da wani ɗan ƙayataccen walima na mata mai kyau da birgewa acikin government house, inda aka gayyato malamai maza da mata sabida su faɗakar da amare da angwaye, da kuma masu sauraro, bayan an kammala, aka fara shirye shiryen kai amare gidan su. Ashmir da nasir, na hango kansu a duke, a gaban daddy da mommy, daddy yana masu nasiha akan zaman aure da kiyaye hakk'in mace, bayan haka ya ɗora da cewa "kai ashmir dan Allah ka rike amana, dan ni kai nake ji, bana jin baba na, wato (nasir) ka ga dai a gidan kunya muka nemi aure, to dan Allah ka rike amana kaji," nan suka gyada kai sannan ashmir yace "insha Allahu daddy sai kayi alfahari da wannan auren kuma zan rike amana, shi ko nasir kasa cewa komai yayi sabida kunya. Nan daddy ya shafa kansu duka yana shi masu albarka, itama mommy ɗora wa tayi da shi masu albarka, sannan daddy ya sallami su, ya koma kan noor a dan gaggauce sabida yanzu za'a kai su dakin su, noor sai kuka take tana rungume da mommy, mommy na lallashin ta, shi kuma daddy yana nasiha mai ratsa jikin mai sauraro. Can na hango nihal bayan daddy ya gama mata nasihar zaman aure mai ratsa jiki, sai sharban kuka take tana cewa "dan Allah mommy kice kar a kaini yau, wlh bazan iya barin ki na tafi ba," mommy kuma sai lallabata take, tana ƙara yi mata nasiha akan zaman aure, shima adnan ya sha nasiha musamman a gun daddy, har hawaye sai da yayi sannan yayi wa mai martaba godiya sosai. Bayan wasu lokuta an kai kowacce amarya ɗakin ta, inda na hango gidajen su a jere suke, a SHARADA GRA gidaje ne tsararru kuma kowanne da zubin sa, shi dama ashmir a can out side ya ƙira masu aiki domin a ƙera masa nasa gidan. Nihal ce a zaune a gefen gadon ta, sai kuka take, bayan angwaye sun tafi, sai ga ashmir ya shigo cikin ɗakin nata, da sallama, sai da kirjin nihal ya buga sabida fargaba, amma bata daina kukan ba, nan taci gaba da rera kukan ta, ta ɗauka ko ashmir zai zo ya rarrashe ta, amma sai taga ya wuce ta, ya nufi toilet, a ranta kuwa sai jinjina hali irin na yaya ashmir take, tana cewa, "yanzu sabida Allah, ina amaryar ka, amma ka shigo ɗaki ka tarar dani ina kuka a ranar farkon mu, amma baza ka lallashe ni ba, ai dama na sani baya so na, gashi da fadin rai." Nihal tana ta zancen ta, kasa kasa tana sharɓan hawaye, sai dai duk wannan zancen ashmir yana jiyo ta, sabida shi mutum ne mai ji kamar maciji, murmushi yayi wanda shi ya baiwa kanshi sani, sai da ya ɗauki ƙimanin rabin awa a cikin bathroom din sannan ya fito da wani ƙaramin towel a kukunsa daidai rabin cinyar sa. Taku taji yana kusan to ta, aikuwa cike da tsoro haɗe da fargaba tayi firgigit ta mike tsaye, mai zata gani? Tun daga dunduniyar kafar sa ta fara kallon sa, waiyyazubillah, wani gashi ne mai tsananin kyau tun daga silin kafar sa, a kwance kamar an shafa masa oil na jarirai, sai da ta dire idon ta, har kansa, wai wannan mutumin anya mutum ne kuwa, wlh ba dan ta san gidan su ba, da tace ya haɗa iri da aljanu, sabida tsananin kyan sa. Hmm ya dai yan mata, kar fa ki cinye ni pls, hmm ya fada yana murmushin gefen fuska. Kunya nihal taji sabida dama da taga cinyar sa sai da tsigar jikin ta ya tashi, sabida wani yarr taji a jikin ta, ai kuwa tayi maza ta sunkuyar da kan ta, ran nihal ya daɗa baci, ga lefin daya mata amma yazo kuma yana tsokanar ta, lallai ma wannan mutumin. My wife ta shi ki je kiyi wanka, ya faɗa yana kallon ta, nihal ta masa banza, sai da ya gama shiryawar sa tsab cikin wani sleeping dress mai kyau riga da wando, mai santsi, wandon dogo har kasa, kalar sky blue, yayi kyau sosai, duk da tana fushi da shi amma ta kasa ɓoye kan ta, domin sai satan kallon sa take yi. takowa yayi kuwa yazo ya zauna dab da ita, sannan ya dafa ta da hannu bibbiyu yana cewa "pls baby luv kukan ya isa haka mana, bana son kanki yayi ciwo, oya tashi kije kiyi wanka, sannan kiyi alwala, kizo muyi sallah." Nifa nayi sallah tun a gida ta faɗa tana mai turo baki, murmushi yayi sannan yace "eh na sani baby luv, wannan sallan ta daban ce, kowane ango da amarya suna fatan yin sa a rayuwar su, dan haka tashi kije kiyi. Cike da jin kunya ta tashi, tana layi kamar mai jin bacci, ta nufi bathroom din. Bayan wasu yan mintina nihal ta kammala wankar ta, sannan ta ɗauro alwala ta fito. Ba'ki ya sake yana kallon halittar Ubangiji, domin nihal ce ta fito sanye da wani ɗan ƙaramin towel, daidai cinya, ruwa sai sauka yake a jikin ta, gashin ƙafan ta sun kwanta luf luf, gashin kanta kuwa, ta wanke shi tas, yanzu ma tsane shi take son yi da hand dryer. Ruwan da yake sauka a jikin ta, shi ya haɗe da santsin tiles din su, aikuwa nan da nan nihal ta suɓale zata yi ƙasa, ihun tane yasa shi yin firgigit daga shagalan kallon ta daya tafi, aikuwa cike da zafin nama ashmir ya riƙo ta, Ita kuwa nihal ta riga ta sadakar ta gama faduwa, domin har ta rufe idon ta ma, amma sai taji wani abu mai taushi ya riƙo ta gam ya tokare ta gaba ɗaya, a hankali take buɗe idon ta har ta sauke su a kan fuskar ashmir, shima ita yake kallo, sunfi minti biyar a haka, suna kallon junan su, nihal ce tayi maza tayi firgigit ta zabura ta kwace daga riƙon da ashimr yayi mata, nan ta nemi guri ta zauna, tana haki, sai da ta ɗan huta sannan ta fara drying gashin ta, ta gama ta shafa mishi oil mai kamshi, sannan ta tufke gashin da ribom. Nan ta hangi wasu kayan bacci kalar sky blue ɗin itama, ta ɗauka ta nufi dressing room, ta saka su, wow zo kuga madarar kyau a wajan, nan ta ɗauki wani hijab har kasa ta saka, sannan ta nufo bedroom ɗin ta, hasken ta ya fara hango wa, aikuwa nan ya kafe ta da ido, tana karaso wa kuwa ya miƙe, ya shimfida ma su pray mat, sannan ya ta da sallah tana bin shi, bayan sun idar ne ya dafa kan ta yana kwararo ma su addu'a, ya jima yana masu addu'ar fatan zaman lafiya sannan suka shafa. Miƙe wa yayi ya nufi wani ɗan frizer ya ɗauko masu wani lafiyayyan yougout da five alive, da swan, sannan ya tafi ya ɗauko masu gashashan kaji dana nama sannan ya ɗauko ma su plate da cups da spoon da fork. Duk wannan hidimar da yake yi, nihal tana zaune a kan pray mat tana kallon shi, ita mamaki ma yake bata wlh, wai kamar Yaya ashmir mutum mai ji da kansa amma yau ya sauke sai lallaba ta yake. Gyaran muryan sane ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, yan mata matso nan mana, ko na zo na ɗauke ki, dan bana so ki fiya motsawa, ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya. Jiki a sanyaye ta tashi tana sarssarfa ta ƙarasa gun da ya ke, ta zauna kusa da shi, nan ya zubo mata youghurt mai sanyi ya mika mata, ta karɓa tana kallon youghurt ɗin, yace ki sha mana baby luv ko sai na miki ɗure ne, aikuwa tasan ba karamin aikin sa bane ya mata ɗuren shi yasa ta maza ta kai cup din baƙin ta, shi kuma five alive ɗin ya sha, sannan ya yago chicken pepper ya ce mata "ahm" alamar ta buɗe baki ya sa mata kazar, ita kuwa ta noke, sai da ya ce mata "oya open ur mouth" sannan ta ɗan buɗe ɗan bakin ta mai kyau, shi kuwa ji yayi kamar yayi ta tsotse wannan baƙin nata mai kyau, haka dai ya daure yayi feeding nata, har sai daya tabbatar ta koshi sannan ya bar ta, shima kaɗan ya ɗan ci ya ture. Ta shi yayi ya kwashe wannan kayan da suka ci abinci, sannan ya dawo ya ɗauke ta cak kamar baby, nihal kuwa kunyar sa ce ta kama ta, bai dire ta ko'ina ba sai kan gadon su, nan ya koma yayi switch ɗin komai sannan ya dawo kusa da nihal yace mata "baby luv, zan tafi daki na, amma dai zaki iya kwana ke kaɗai ko?" Cike da tsoro ta kallo sa, sannan tace cike da shagwaba "ni wlh bazan iya kwana ni ɗaya ba anan, kaga ai ban saba da wajan ba, wlh tsoro nake ji, ta karashe maganar tana gunjin kuka." Wani murmushi mai sauti ashmir ya sauke ganin haƙan shi ya cimma ruwa, sannan yace da ita, "no stop crying my baby, i promise u i will stay here with u." Nan ya rungumo ta, yana shafa gadon bayan ta, ajiyar zuciya take saukewa a hankali, daga nan kida ya fara canzawa............. Ba karamin more amaryar ta sa yayi ba yau, sai de ita duk ta galaɓai ta, da asuba da kanshi ya haɗa mata ruwan wanka, sannan ya kaita bayi, ya taimaka mata ta gaza jikin ta, sannan tayi wanka, sannan shima yayi nasa wankan suka fito. Bayan sunyi sallar asuba, ashmir ne ya ga jikin nihal yayi zafi, ya ƙauko magani ya bata, Allah da ikon sa kuwa sai zazzaɓin ya fara sauka, daga nan suka koma gado, nihal tana shirin komawa bacci, kawai taga ashmir ya fara wasa da dukiyar fulanin ta, yana yi yana kissing din bakin ta, nan ya fara fita hayyacin sa, yunkurin yin part two yake, aikuwa nihal da sauri ta fara kuka tana cewa, "dan Allah ka barni haka yaya ashmir, wlh na sha wahala jiya, pls ka barni na warke, da kyar ya iya buɗe bakin sa yana cewa "baby luv pls kiyi hakuri just romance ne, bazan je can kasa ba kin ji my wife, a hankali ta gyada masa kanta.... Bayan sati biyu da bikin su ashmir, nihal ce a gefen swimming pool ɗin gidan tana zaune a bakin ruwa ƙafafuwan ta suna cikin ruwan, waya ce rike a hannun ta, ta kai shi kunnen ta, tana cewa "besty ykk ya yaya na, a can ɓangaren kuma noor ce take ce mata "wlh komai Alhmdlh, yayan ki ya na nan, yanzu ya shiga wanka, nihal tace "to dai a kular min da brother na, komai yace yana so a ba shi pls" noor tace "hmm abinda zan fada shi kika rigani faɗa, to dai nima a kular min da yaya na pls, a tarairaye shi kamar kwai a cikin miya," nihal tace "kaji ta to sannu mai yaya, yayan naki da duk ya bi ya takura min, kullum abu ɗaya, ko office ya kasa zuwa wlh kullum yana gida" Hmm to nima fa hakan take "wannan yayan naki ya fiya naci, kamar cingum, ni duk na ƙosa ya fara fita ma. Cewar noor Oh abin harda su cin mutunci, to ai shike nan, cewar nihal Ga minal na ƙira na, bari na haɗa conference mu sha hiran mu na yaushe gamo, cewar nihal Nan suka haɗa junansu a waya suna ta hira harda kyakyatawa. Washe gari Nihal ce take ta shiri, wani haɗadd'en less ta sa kalar purple mai ratsin peach, ta sha kyau ta yafa peach din mayafi da jaka da takalmi ma duk peach ne, tasa wani diamond dankuni da sarka da abin hannu, wow tayi matuƙar kyau gaskiya, hugging ɗin ta taji anyi ta baya ana lashe mata wuyan ta, wow kinyi kyau mata ta, duban shi tayi tun daga sama har kasa sai taga yayi mata wani kyau, ya sha wani yadi mai tsada peach color, kai ma kayi kyau miji na ta fada tana lumshe idon ta. Nihal na hango a palon mummy, sai jan ta take da hira ita kuma nihal kunya ya hana ta sake wa, mummy ce ta juya gefen ta tana cewa "son fita ka bamu guri da ɗiya ta, duk ka hana ta sake wa, yaya ashmir kuwa sosa kan yake yana cewa "yanzu mum ƙora ta kike yi, naga alamar kin ma daina ji da ni mum, yanzu ba kya tani" eh ɗin bana ta kai ta ɗiya ta nake, murmushi ashmir yayi sannan ya fice yana sosa ƙeya, sosai nihal ta saki jiki da mum suna ta hira. Sai da suka yini a gidan sannan suka koma gidan su. Washe gari Noor ce ta buga sammako a gidan yaya ashmir, aikuwa nihal tayi murna, nan suka ƙaraso ita da mijin ta, wato yarima adnan, dama shi ya kawo ta, nan nihal tayi masu iso sannan tace "bari taje ta ƙira wo yaya ashmir su gaisa, nan kuwa ta tafi ɗaki, tana zuwa ta shige cikin bargon sa, nan ya cakumo ta, yana cewa "wa na kama? Wato dan kin yi baƙi, shine kika tafi kika kyaleni ko? To yanzu wa na kama, kuma sai na rama." Lah wlh yaya ashmir baƙi ne damu kuma yanzu ma suna parlon kasa suna jiran mu... Ai kan ta ƙarasa ya caɓe baƙin ta yana kissing kamar ya samu lollipop....... Mr Yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . I dedicated this page to my besty, Allah ya bar mu tare, much luv. Page 60_65 Ɗa gowan da zai yi, sai ya hango bayan wata, a gaban su noor, kawai sai ya ja motar sa ya fice da gudu, yana tunanin ta a zuciyar sa, ya so ya gan ta ko so ɗaya ne. Noor kuwa har ta buɗe bakin ta, zata kira shi, kawai sai ta ga ya fice da gudu. Nihal kuwa motar sa na tashi ta kalli gurin a guje, sai de kash bayan motar kawai ta iya hango wa. Minal kuwa tana ganin yaya ashmir ya tafi ta fara zuba wai "wow noor dama haka yayan ki ya ke da kyau, wlh ya hadu, wlh duk kyan ki, ya fi ki kyau yarinya." Noor ta taɓe baki sannan tace "bawa ni nan, bai fini kyau ba, kai amma dai wlh besty yau kin ban haushi, ina ta neman ki, ku gaisa da yaya na, shi ne zaki wani tafi wani gun. Ta kare maganar tana ɓata fuska." Nihal kuwa cewa tayi "oh sorry my dear friend, wlh bansan zai zo ba, da ban je ko'ina ba, ai kece da lefi baki gaya mana ba, why?" Noor tace "wlh I just want to surprise you guy's ne kawai amma ba komai wataran a hadu, ga tsara bar mu nan daya kawo mana." Nan nihal ta shiga duba wa sosai yayi masu tsara ba irin su chocolate, cake, ice cream, snacks, sweet, cingum, da abubuwan kwamulashe, kala kala, don sai da ya ciko masu manyan ledoji biyu. Nihal tace "wow amma Allah ya shi ma yaya ashmir din nan Albarka, kuce yau ni babu ruwa na da abinci." Nan suka fara cin wannan kayan kwalam din, nihal tana ba su labarin abinda yasa basu ganta ba, wai wani lecturer su ne, ya kira ta wai yana son ta, kuma da wai da aure, ga shi ba musulmi ba ne, kuma bature ne. Aikuwa suka kwashe da dariya, harda tafa wa, noor tace "sayi su gama wlh ai nan da 6months zamu yi graduate, naga ta tsiya" Ashmir ne a katon gadon sa, bayan dawowarsa gida, da yake direct gida ya wuce, idon sa alumshe yana tunano zancen sa da mummy a kan yarinyar da yace yana so. Bayan wata biyu da sati uku Gidan sarauta Mai martaba ne ake ta hada hada a cikin masarautar sa, dalilin yau suna da Babban bako wato His Excellent, governor Abdulkarim Nasir Gaya, shi ne yau zai zo gun mai martaba sabida bikin buɗe companies din da suka yi haɗa ka, wajan gina su, ya kammala, kuma ga wata muhimmiyar magana da ke tafe da shi. Fada yau a cike take da dimbin al'umma, sabida baƙi na musamman da aka yi, nan na hango mai martaba da his excellent, suna tattaunawa, a tsakanin su, inda bayan sun kammala tattaunawar su ne, na bikin bude companies din, sai his excellent yace da mai martaba, "ni kuwa akwai wani abin ya ke damu na, game da yaron nan, ashmir, yaki ya kawo mana wacce yake so, sannan akwai ya'yan kani na, Alh kabeer nace masa yaje ya zaɓa a can, nan ma yaƙi, to amma nan ɗin ban ji rashin dadi ba, dalili kuwa ance duk yaran biyu suna son shi, to kaga idan har ya zaɓi ɗaya acikin su, zai yi san kai, to gwara a hakura, Allah ya fito masu da mafi Alkhairi, to shi ne nace bari na kawo zancen nan ko zamu samu mafita." Mai martabar sai da yayi ajiyar zuciya sannan yace "to ai ur excellent wannan ba wani abun damuwa bane, kawai ayi tuwo na mai na." Sai da his excellent ya kuma tambaya yana cewa "ban fahimce ka ba." Mai martaba yace "Abinda na ke nufi shi ne, mu hada su aure da yata nihal." Nan fa his excellent ya washe baki yana cewa "kai masha Allah, wannan abu yayi dadi, sosai, Allah ya saka da Alkhairi. Nan suka amsa da Amin Sai mai martaba yace "sai a bari ranar bikin buɗe companies, kawai sai a sanar a ranar, ayi walimar saka ranar aure." His excellent yace hakan ma yayi kyau sosai, nan aka bawa malamai dama suka rufe taro da addu'a. Bayan nan a kaje aka yi lunch kowa ya watse. After 1 week Wani katafaren babban wajan taron manya na hango, cike da al'umma. Wajan zama daki daki kowa da wajan sa Kowa da inda aka tanadar masa ya zauna Akwai kujerun masu taron, Akwai na masu gabatar da taro, Akwai na yayan masu taron, da matan su, Akwai na yan gayyyata, Akwai na masu tsara taron yadda ya kamata. Can na hango kujera ta musamman Ga his excellent, ga mai martaba, ga gwamnan bauchi ma ya zo, gana jigawa ma yazo dana kaduna. Ga hadimai da wazirai da turakai. Can na hango wasu kujeru na musamman na matan gwamnoni da matan sarakai. Can na hango wasu high tables kujeru, dana maza dana mata. Anan na hango ɓangaren yayan gwamnoni, da ya'yan sarakai, dana wasu manyan, iya maza. Ana can ma haka na hango na ya'yan gwamnoni da yayan sarakai, da dai sauran su. Taro yayi taro ya hadu iya haduwa, da kyar na samu na hango doctor ashmir ya sha wani suit silver color, fuskarsa ta sha gyara, gashin kansa ya sha gyara ya kwanta luf luf, yayi matuƙar kyau a kayan, kamar balarabe ko daya ke dama balaraben ne. Gasu yaya nasir shima an sha kyau a cikin wani bakin suit, yayi kyau sosai. Ga adnan, wato yarima mai jiran gado, shima yayi kyau matuka, ya sha wani White nd black suit, dama shima kyakkyawa ne, kasan cewar shi black beauty, ga shi dogo, ga hanci ga zara zaran idanuwa ga karamin baki, gashin kansa shima ya sha gyara luf luf. Ga sauran ya'yan manya a gun kowa naji da kansa. Nan na hango nihal ta sha kwalliya a cikin wata haddan wedding gown, silver nd white color, ta sha kyau, gashin kanta ya sha gyara an rufe sa da wata yar mayafi shara shara silver. Itama noor irin shigar su ɗaya da nihal, sai de nata calon Black nd white ne itama ta sha kyau. Minal ma wata hadaddiyar less ta saka maroon color, Kasancewar dad dinta da yan gidan su sun zo taron, itama tayi matukar kyau abin ta. Amira kuwa ta sha kwalliya da wani atamfa super wax red nd yellow, tayi kyau sosai itama. Islam kuwa wata hadadd'iyar abaya ta saka, black nd orange color, tayi kyau sosai itama. Taro yayi taro ana ta gabatar da abinda ya haɗa mutane, komai cikin tsari a keyi, ga lafiyayyun abinci kala kala, irin su fried rice, jellof rice, fried supagetti, fried cous cous, chips nd kaji, tsire, snaks, drinks, dambun kaza dana nama etc. Sai drinks kala kala. Nan aka gama gabatar da abinda ake yi, sannan a kazo ana sanar da an haɗa dr ashmir aure da gimbiya nihal, inda aka umarce su da su fito a gan su da kyau, domin a shaida su. Kirjin nihal da na ashmir a tare suka buga lokaci guda. Da taimakon Noor nihal ta samu ta fito, shi ko ashmir ya dade da fito wa. Nan masu camera da video suka dinga watsa masu camera, amm sun dace kowa yake cewa, dama an bawa, ashmir zobe kafin ya fito wanda iyayen ne suka tana da, domin ya sawa nihal itama an bawa noor ta bawa nihal, ita kuwa nihal sai da noor ta ja mata kunne akan dan Allah kar ta bada su, domin akwai yan jarida a gun. Nan nihal ta taho, tana tafiya a hankali, rigar ta sai jan kasa yake yi, duk ta firgice wai wannan mutumin ne za'a hada su aure, Ita dai kashin ta ya bushe. Nan ashmir ya taho shima da karfin sa, domin Allah ne kadai yasan irin farin cikin daya ke ciki, amma abinka da miskili daya matso kusa da ita sai ya sha mur. Nan ashmir ya duka har kasa ya riko hannun ta yana daukar alkwaririka, cikin harshen turanci yake maganar, ana ta tafi domin sun ƙayata gurin kamar a indian film, sannan ya saka mata zoben, itama ta saka ma shi, nan aka din ga watsa masu kudi ana tafi ana video da camera. Wayyo ku hasko kuga irin burgewar da suka yi a gun. Bayan nan kowa yaje ya zauna a gun zaman sa, inda wani babba ya tashi ya na sanar da mutane cewa an tsayar da biki nan da 3 months. Fatan Alkhairi. Nan fa a kaci aka sha, taro ya fara watsewa. Islam ce ta fashe da kuka ganin yaya ashmir ba ita zai aura ba, sai lallashin ta ake. Amira kuwa gigicewa tayi ganin wai yaya ashmir wata zai aura, su ko oho. Minal kuwa itama kamar tayi kuka, don Allah ya sani tun ranar da ta fara ganin ashmir taji ta fara san sa, amma ya zata yi, kuma ko ba komai ai nihal ƙawar ta ce, sai de tayi masu fatan Alkhairi. Fayal kuwa ruɗewa yayi ganin abinda ya faru amma kuma ya san cewa, abokin sa bashi da lefi ko kaɗan. Dan haka yana masu fatan Alkhairi. To daya ke manyan taron sun watse saura matasan, su gwamnoni da su manyan yan siyasa da sarakai da hadimai an tafi da su government house, wai za'a danyi wani meeting daga nan kowa ya watse ya tafi gida. Ashmir ne a zaune kusa da nihal wacce noor ta kawo masa ita, ya sha mur kamar ba shi ba, itama nihal sai wani harare harare ta ke yi. Ke ba ki iya gaisuwa bane, kin wani zauna kamar an jefo ki. Eh ban iya ba, ka koya min mana, to cewa nayi ina son ka da zaka yi min wulakanci. Ashmir baki sake yake kallon ta, hmm yarinya zaki shigo hannu ne, za kiyi bayani, nima ai ba cewa nayi ina son ki ba, karamar mara kunya. Murguɗa masa baƙi tayi, ta tashi zata bar gurin ai kawai rigar ta ya naɗe a takalmin ta, tayi kasa gaba ɗaya zata fadi. Ashmir ne ya riko ta, ya rike ta gam, shi yasa bata karasa faɗuwar ba, tuni ya tallabo ta, ta fado kirjinsa, ya rungume ta, yana sauke nauyayyan ajiyar zuciya. Tuni gurin ya ɗau tafi ana ta masu hotuna. Noor ce ta taho a guje, tana kiran sunan nihal.... Mrs yusuf ❤️❤️❤️ [8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE* (LOVE IS BLIND) 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤 *ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖 *Writer*✍️✍️✍️✍️ *Na Qwinn minerhly* _Short_ _and_ _romantic_ _story_ . Ina kuke masoyan book ɗina, to gani na tawo maku da sabon littafi na mai suna RAYUWAR SALEEMA, wannan littafin yana tattare da abun mamaki, ban al'ajab, ban tausayi tare da ɗaukan darasi, don haka kada ku bari a barku a baya. Wannan littafin sadaukarwa ne, ga miji na domin da bazar ka nake taka rawa.much love End End End Page 80_85 Ai kan ta ƙarasa ya caɓe baƙin ta yana kissing kamar ya samu lollipop..... Da kyar ta samu ta lallaɓa yaya ashmir suka miƙe suna shirya wa, English wears suka sa, iri ɗaya, jan top, a nata an rubuta "my king", a nashi an rubuta "my qween" sai kuma ashe ɗin wando, sai de nata yana da kwalliyar mata, sun yi matuƙar kyau abin su, sai dai nihal ta ɗaura after dress a nata, suka feshe jikin su da turare, tafe suke suna zancen soyayya, hannun ta saƙale a kan kafaɗar shi. Takun su ne yayi wa noor iso a kunnuwan ta, aikuwa tana ɗago fuskar ta, ta hange su saman step suna takowa a hankali cikin kwanciyar hankali abin su. Harara kawai noor take wurgawa nihal sabida ta ƙulu da ita, dan gani take ta shanya su, sai de bata san yaya ashmir ya gan ta ba, suna ƙarasowa kuwa noor ta kuma wurgawa nihal wata harara, nihal kuwa murmushi tayi sannan taje tayi hug ɗin noor tana cewa "wlcm my sister, amma fa ki maida wukar, dan wlh bani na kar zoman ba, nima rataya aka bani," ta faɗa tana kallon yaya ashmir, shi kuma ya wani haɗe rai, kamar bai taɓa dariya ba, kamar ba shine suka gama wasa da shi ba yanzu a sama. Nan ashmir suka gaisa da adnan sannan nihal ma ta gaishe da yaya adnan, sannan noor ma ta gaishe da yaya ashmir, ya amsa mata ba yabo ba fallasa, sannan yaya ashmir yace wa noor " wai meya faru ne kike ta hararar min mata?" Iah yaya ashmir wlh ni fa ba hararar ta nayi ba, "cewar noor" to nayi miki ƙarya, kin bugo mana sammako duk bai ishe ki ba, amma sai kin zo kina hararar ta dan baki da kunya ko? To kar na sake gani, baƙi san ta zama yayar ki ba ko? oya bata haƙuri, "cewar yaya ashmir" da ya faɗa yana wani cin magani, adnan ne ya maza ya ƙarɓi zancen da cewa "yau nake ganin faɗan rashin gaskiya, to dan ta harare ta ai itace da lefi, sannan kuma sai ta wani bata hakuri, aikuwa kina bata hakuri itama zata baƙi hakuri a matsayin ta na ƙanwa ta, sabida har yanzu ban gane wace yaya, wace ƙanwa ba? ya faɗa tare da murmushi akan fuskar shi. Nan kuwa kowa ya sa dariya ban da yaya ashmir da ya murmusa sabida shi kaf ya sha'afa ma wlh, ashe fa su ɗin a da ƙawaye ne, kuma kowacce da ta tashi aure sai ta auri wan yar uwar ta, kaga kuwa kowa ya zama boss. Ana cikin haka sai ga su minal da yaya nasir sun shigo cikin gidan, nan kuwa nihal da noor suka yi farin cikin ganin su, nan hira ta barƙe a tsakanin su nan ashmir ya ja su, suka koma ɗayan part ɗin, itama nihal ta ja su suka shiga kitchen su ukun suna girki, minal tana jin ƙamshin tafarnuwa ta fita a guje tana amai, inda suka bita hankali a tashe suna tambayar ta "me ya same ta?" Nan take ce masu tana da 2wks pregnant, aikuwa sun mata murna sosai nan suka ce ta zauna ta huta, su sa shiga su ƙarasa aikin. After 8wks Nihal ce an sha wanka, da wata exclusive atamfa kalar maroon da ratsin butter color, ɗinƙin riga da skirt, kayan sun amshe ta, tayi matuƙar kyau, nan shima yaya ashmir ya shirya suka fita, hanyar gidan sarauta suka shiga, bayan isar su ne suka fara zuwa fadar mai martaba da suka gaishe shi, yayi matuƙar farin ciki da ganin su, sannan suka ƙarasa part ɗin hajiya kilishi wato mahaifiyar yarima adnan, itama tayi matuƙar farin ciki da zuwan su, tunda yanzu ta gane ta daina kishi da mum, har part ɗin ta take zuwa, itama mum tana zuwa nata part ɗin, bayan sun ɗan zauna kaɗan sai suka tashi suka tafi part ɗin mummy, nan barori suka dinga kawo masu gaisuwa, suna kawo abubuwa, su kawo wannan su kawo wancan, mum tayi matuƙar farin ciki da ganin su a tare, gashi yar ta, ta ƙara wani kyau, skin ɗin ta, ya dada haske da kyau, a gaskiya ta yaba da kiwon ɗan ta ashmir, sai shi masu albarka take, nan yaya ashmir ya miƙe yana masu sallama, sannan yace wa nihal ta zauna ta yini zai dawo sannan su tafi, aikuwa nihal sun sha hira da mum, dan har part ɗin hajiya kilishi ta koma, itama ta haɗa wa nihal kayan gyara iri daban daban, sai bayan magriba yaya ashmir ya dawo suka tafi gida, a hanyar su ta komawa ma sai da yaya ashmir ya kai su shopping mall. Bayan sun isa gida ne, kowanne su ya shiga wanka, suka yi sallan ishai sannan suka ci abincin da suka siyo sannan suka fara shirin kwanciya. After 9months Yaya ashmir ne da nihal a cikin garden ɗin gidan su, babban garden ne mai tattare da komai na more rayuwa, yaya ashmirr ne zaune a kan wani ɗan ƙaramin godo dake cikin gurin, ita kuma nihal tana kwance, kanta akan cinyar sa, mix fruit ne a cikin wani jug mai kyau, ga kuma milkshake a kusa da su, hira suke mai ban sha'awa a tsakanin su, nihal ce ta ga yaya ashmir yana zubar da hawaye, tace da shi "yaya na, me ya faru, wani abu ne yake damun ka?" A'a baby luv, babu abinda yake damuna sai son ki, wlh na rainu da soyayyar ki, wlh kece mace ta farko dana fara so a rayuwata, hakikanin gaskiya SO MAKAHO NE domin ya maƙantar dani da soyayyar ki, ya zame min abinci na da ruwan sha na, ke nake gani a mafarki na, ke nake yawan tunani, wlh nihal tun ranar da na fara ganin ki naji na fara son ki, amma nauyin baƙi ya hanani faɗa, sai ranar da na ji abokina fayal yana zancen ki, har ta kai ya nuna min hoton ki to a ranar ne na ƙasa boye abinda yake raina, na shiga cikin damuwa har sai da ta kai ta kwantar dani, wlh ina sonki my baby, I luv u, I need u, I can't do without you my luv," ya ƙarasa maganar yana yi mata wani hot kiss a baƙin ta. Hmmm yaya na, ashe duk abu ɗaya muka ji, ashe a rana ɗaya muka fara son junan mu, wlh nima tun ranar da muka fara haɗuwa naji na fara son ka, lallai SO MAKAHO NE domin nima shi ya maƙantar dani, bana ganin kowane ɗa namiji sai kai, na kasa miƙa soyayya ta ga kowa sabida ruhina yana tattare da naka, i luv u more my love, I can't stay without u, I love u more, ta fada tana rungumo shi haɗe da rikunkume shi kamar za'a sace Mata shi, suna cikin haka sai ga wayar ta yana ringing, nan ta ɗaga da sauri sabida taga sunan noor ce mai ƙiran, bayan sun gaisa ne take ce mata wai minal ta haihu, baby boy ɗazu, nan nihal ta shiga murna sosai tana cewa lallai kice mun yi ɗa, bayan tayi hang-up, take gayawa yaya ashmir zancen haihuwar minal, shima yayi matuƙar murna sosai, sannan shima ya shafo cikin ta yana cewa "nima na ƙosa naga ɗana, kai insha Allahu ma yan biyu ne a cikin nan," kasancewar sun je sunyi gwaji sun tabbatar tana da ciki. ita dai nihal murmushi kawai take dokawa sabida zumuɗin shi akan wannan cikin yayi yawa, sannan tace "nifa wlh yaya ashmir tausayin noor nake, kaga ita kaɗai ce har yanzu bata samu ba, sannan ga shi duk tare muka yi aure." Hannu ya maza ya sa mata a baƙi alamar tayi shiru kar ta ƙarasa, sannan ya ɗaura da "kul karna ƙara ji kin yi wannan zancen baby luv, shi haihuwa ai na Allah ne, muma daya bamu ba dabarar mu bane, kuma ita ma ɗin ai Allah bai manta da ita ba, kuma ma duk gaba ɗaya yaushe aka yi auren ɓalle ki damu, don haka kar na ƙara ji kinyi wannan zancen kinji my baby?" Girgiza mashi kanta tayi tana hawaye, sannan yace "baby luv meyasa kike kuka, ko dan nayi miki nasiha ne?" A'a wlh yaya ashmir ko ɗaya, kawai dai nasihar ka ce ta ratsa ni, kuma na gode da tunatar war ka, ita kuma Allah ya bata mai Albarka, suka amsa da "Amin" Washe gari da safe Suna kwance a kan gado a cikin ɗakin yaya ashmir, nihal tana kwance a kusa da shi tana wasa da gashin kansa, wai ita kitso zata mishi, sai jagwalgwala masa kan take, shi kuma dadin hakan yake ji shi yasa yayi lamo a kwance, can dai nihal ta tashi tace da shi "yaya na ina zuwa" miƙe wa tayi ta nufi kitchen ɗin sama ta fara masu aikin breakfast wai yau sai tayi mishi surprise, don kuwa abincin gargajiya take ta haɗa wa, tayi masu awara mai kwai, ta soya masu wainar fulawa, tayi masu ɗan wake, ta soya masu kosai, da alala, sannan ta dama masu kunun gyaɗa, sannan ta haɗa masu soɓo, ta kuma haɗa da ruwan tea. Kan dinning table ɗin sama ta nufa, ta shirya masu komai anan, kasancewar komai da yake asama a kwai a ƙasa, wanka taje tayi sannan ta shirya tsaf cikin wata shadda ɗinkin stone work, doguwar riga, kalar blue, ta kashe ɗaurin ɗankwali, sannan ta nufi ɗaki taje ta tashe shi, ya shiga yayi wanka shima ya shirya sannan suka nufi dinning, nihal ce take ce mashi "yaya ashmir guest what?" Nan ya ɗan juya idon sa, sannan yace "hmm I can't guest anything but u." Nidai don Allah a bani naci, tun da na fito nake jin kanshi ya baɗa ko'ina, pls a taimaka wa wannan bawan Allah, wlh ana shiga hakkin sa sosai." Murmushi nihal tayi sannan tace "hmm to gaskiya kayi failing ace ka kasa gane me nayi hmm amma dai bari kawai dai mu ci." Ta faɗa tana kashe masa ido ɗaya, sannan ta fara ɗiban kowanne tana zuba wa a cikin plate, ta zuba masu kunun gyada da zoɓo, a cups sannan tace da shi "Bismillah" to yanzu banda abin ki a'ina zan gane duk waɗannan abincin, abu ba ɗaya ba, ba biyu ba, amma fa gaskiya sunyi kyau, sannan dan Allah wai dama duk kin iya irin waɗannan abincin ne dama, a gaskiya sai dai Allah ya biya su mum, amma wlh ni na ɗauka ma ko ba ki iya girki ba sai dai a miki, wai ashe kina shiga kitchen a gida, to ai dama wannnan shine gatan ya mace, amma ace kaga yarinya kawai sabida tana cikin daula amma sai ta ƙi shiga kitchen sai anyi aure a yi ta fama da miji, yanzu gashi mun huta da ɗaukan kuku, tunda kince zaki iya mana abinci da kan ki, masu share share da wanke wanke, da goge gogen gida kawai kika ce a kawo, sai mai gadi, kinga ai kin samu tarbiyya, amma ban da haka kina yar gidan sarauta ga kuɗi ga mulki amma kina wa mijin ki hidima, baby Allah ya biya ki da gidan Aljanna, Allah ya sakawa iyayen mu da gidan aljanna, a tare suka ce "Amin" bayan sun kammala cin abincin ne yaya ashmir sai santi yake zubawa yana cewa dan Allah ta ringa yi mishi ire iren kalar abincin nan, dan shi wlh dama ya gaji da cin na zamani, nan tace da shi "insha Allahu zata dinga yi" yau ma da rana dambun shinkafa zata yi, da source ɗin ƙoda, da lemun kankana, aikuwa yayi matuƙar farin ciki da jin haka. Bayan anyi sunan ɗan su minal yaro yaci sunan mahaifin su yaya nasir, ana ƙiran shi da, "abid" suna yayi dad'i domin kuwa an yi lafiya an tashi lafiya. After 9months Nihal ce kwance a ɗakin labour sai kuka take yi, yaya ashmir kuwa yana riƙe da hannun ta, yana bata baƙi, sai cewa take "na shiga uku yaya ashmir wlh mutuwa zan yi, ni kaɗai na san abinda nake ji, yaya ashmir kataimake ni kada na mutu wayyo Allah na" yaya ashmir kuwa duk ta ruɗa sa ya rasa mai zai mata, kawai sai hawaye yake yana cewa "ba zaki mutu ba baby insha Allahu, zaki haihu lafiya, kinji baby na, ki yawaita cewa innalillahi wainna ilaihi rajiun. Nan kuwa nihal ta ɗin ga faɗan haka, can sai ta fara wani nishi, tana ƙiran sunan ashmir, kawai sai faya ta fashe, sai ga ɗa ya faɗo, aikuwa ashmir ya taro ɗan sa, yana kwalawa doctor's mata kira, dama can shi ya ƙore su, yace su zo su gyara masa matar sa da babyn sa, aikuwa sai ga su sun shigo da sauri suna yes sir, nan da nan suka fara gyara su, kawai sai su ka ga nihal tana wani yunkurin ashe yaya biyu ne acikin, na da nan suka karbi ɗayan haihuwar, da gudun su suka fito suna yiwa dr ashmir albishir, aikuwa sun sha tukuici don kuwa kyautar mota yayi wa kowaccen su, ƙirar kia K5 babbar mota ce aikuwa sunyi farin ciki sosai, kan kace me asibiti ya cika fal da yan uwa. Bayan kwana biyu da haihuwar nihal, bayan an sallame ta daga asibiti, mum tace gidan ta za'a kawo nihal, wato government house, nan suka kwashi nihal da twins ɗin ta, duk mata ne, kuma sun ci sunan mummy's, sunan maman su ashmir, da maman su nihal, ana kiran su da suna "af'reen, da jasmin, nan kuwa aka cika gidan tab, rana bata ƙarya sai de uwar ɗiya taji kunya, domin kuwa yaune ranar suna, sunan daya tara dumbban mutane, rabo kuwa an sha rabo kala kala, har da su atamfofi chiganvi, da dai sauransu an sha shagali ba kaɗan ba, an ci an sha an watse lafiya. Sai da nihal tayi arba'in sannnan mum ta bari aka maida ita, amma fa sai da ta sha gyara, domin tun daga sudan mum tayi waya aka zo aka aka gyara ta na musamman sannan ta koma, a ranar da ta koma ashmir ji yayi kamar aranar aka ɗaura masu aure don farin ciki. Bayan kwana biyu twins ne, a hannun baban su, sai wasa yake ma su, nihal ce ta miƙo masa wayar sa da yake ta ringing amma sabida ya shagala da wasa yaran shi bai ji ba, ya ɗaga cikin girmamawa, ya gaishe da daddy, bayan sun gama gaisawa ne, ya tambayi nihal da yara, sannan yace "dafatan kuna cikin koshin lafiya?" Ashmir ya amsa da "kowa lafiya daddy, sannan daddy ya fara yi mishi nasiha akan rashin zuwan sa aiki tun bayan da yayi aure, ya ɗaura da cewa "idan ma yanzu kana ganin ga yara, to ba mummyn ka ta samo maku me kula da su ba?" ashmir yace "eh daddy ta kawo wata dattijuwa" to ka gani pls son ka koma baƙin aikin ka, kasan cewa aikin ka na taimakon al'umma ne, yanzu nan da monday u should go back to ur duty right? Da sauri ashmir ya cewa daddy "yes dad, insha Allahu Rabbi I will do so, kuma nagode da tuna min abinda na manta, dama daɗin iyaye kenan, nagode Allah ya ƙara girma dad, daddy ya amsa da "Amin son, ka gaishe min da doughter ta, tare da yamma ta na," murmushi ashmir yayi sannan yace "zasu ji insha Allahu" To bayan dad ya gama waya da ashmir ne sai mom take tambayar dad "wai da son kake ta waya ne?" Murmushi dad yayi sannan yace "eh wlh wannan lover boy ɗin ɗan naki ne wai dan anyi aure shikenan kuma sai a daina fita nema, ko dan yaga ya tara dukiya ne, to kuma duk yawan su, idan ba'a nema ai sai su ƙare ko?" Ya ƙarasa maganar yana kashe wa mum ido ɗaya, murmushi tayi sannan tace "hmm ina ruwan son, kasan shi bai iya son abu ba, tun yana yaro haka yake, amma kuma idan baya son abu an shiga uku, ko kallon arziki baya wa abun, to shi yasa ma nake masa uzuri." Dad ne yace "eh ai nasani dama kece ke ɗaure masa gindi ko?" murmushi mum tayi kawai bata ce komai ba, kamo ta dad yayi yana cewa zo nan wa na kama? Naga kwana biyun nan sai wani share ni kike ko? Ko dan kinga mun fara jikoki, to aikuwa kina azabtar dani dan ba haka kika sabar min ba, kuma yau sai nayi maganin ki, ya faɗa yana rungumo ta, ita dai mum kawai dariya take, to anan dai na jawo masu kofa, dan naga abun harda tsofaffi, lol. Bayan shekara ɗaya da haihuwar nihal, afreen da jasmin sun yi matukar wayau, ga girma kamar ya'yan turawa, ga kyau, ɗaya tana kama da nihal, ɗaya tana kama da ashmir, kunga kuwa an haɗa kyau kam masha Allah, rayuwa suke yi mai cike da ban sha'awa da birgewa, ba'a taɓa jin kan su ba, suna kula da hakkin junan su, basa son bacin ran juna, shi yasa suke burge kowa a family, kowa sha'awar su yake, ana alfahari da wannan auren, ga arziki kam masha Allah sai abin da ya karu a gidan ashmir, domin itama nihal yanzu tana da kanfaninnuka, ta zama wata shahararriya mai kuɗi gata babbar lauyer mai zaman kanta, don yanzu ma bata zuwa office sai dai idan taga dama zata je tayi hanging wani case, shima talakawa take wa sabida taimakon su, ita da ashmir sun zama tamkar wasu taurari, abin sha'awa, daddyn su ashmir ya sauka a kujerar gwamna, yanzu na shugaban ƙasa yake nema, don haka shima doctor ashmir ya faɗa harkan siyasa, yanzu haka kujerar gwamna yake nema, kuma alhamdulillah anyi zaɓe an gama kowa ya samu abinda yake so, ashimir an zama his excellence doctor ashmir abdulkareem nasir gaya, fannin su noor da minal abun sai dai ace masha Allah, dan yanzu haka itama noor tana ɗauke da ƙaramin ciki, kuma yanzu haka mai martaba ya kusan mubaya'a, sabida karfi ya fara ja, ana shirye shiryen naɗa yarima adnan sarauta, gimbiya noor za'a koma sarauniya noor, shi kuwa doctor nasir, ya zama babban Kwamishina of healthcare na ƙasa baki ɗaya, hajiya minal an zama babban hajiya. Amira da fayal ɗin ta suna zaman lafiya abin su, suna da ɗa ɗaya, itama islam suna zaune lafiya da Alh adam ɗin ta, ya haɗa su guri ɗaya, da matar sa, amma suna zaman lafiya abin su, sai dai ita Islam har yanzu bata samu rabo ba. Ashmir ne ya riƙo hannun nihal da gudu yana cewa " shikenan sai a dinga wani share ni idan an yi baƙi, kina ganin baƙi ne dani, suna can office suna jira na, amma nace sai na gama da iyalina, dan haka ki saurare ni da kyau kinji ni ko," abi wlh ba wani gu zani ba, abin sha nake so na kawo maka," a'a na yafe zo nan, nan suka shige cikin bargo suna nishaɗantar da junan su, sai a nan nihal take ce mashi tana da wani ƙaramin cikin, aikuwa yayi matukar murna da samun wannan ƙaruwar, bayan sun kammala ne, nihal tayi firgigit zata mike kawai sai taga ya kuma riƙo ta, sannan yace "ina zaki ai bamu gama ba, second round zamu yi ko sai gurin ya warke, dariya suka kwashe da shi da tuna first night ɗin su, sannan ya kuma janyo ta suka lulluba da blanket, ashmir har an fara romancing kawai suka jiyo ihun su jasmin, nan kuwa suka sakko a ɗari, suka fito da gudu, suna fitowa suka gan su a parlon su na yara sunyi kaca kaca da parlon, tambayar su, suka shiga yi suna cewa "Meya faru kuka zabga uban ihu haka, "cewar nihal" aikuwa banza suka yi mata kamar basu ji ta ba, nan nihal ta fusa ta tana cewa "bada ku nake ba, kunyi mana shiru, shi ko ashmir tagumi yayi yana kallon su cike da so, sabida yasan yaran sun biyo su a miskilanci, musamman ma shi yaji labari, nan nihal ta fara shirin dukan su, ai da gudu suka buɗe baƙi suna cewa "daddy wai wannan ne teddyn ta, nata ba red bane cewar afreen" itama jasmin cewa tayi "ni wlh yanzu bana son red ɗin daddy, nafi son black ɗin, dariya ashmir yayi sannan yace wa nihal "kul kar na ƙara gani, wai zaki dake waɗannan yan tayin, To wlh kul." Sannan ya kallo su yana cewa "my kids kuje mummy ta daɗa shirya min ku na kai ku shopping mall ku ƙara kayan wasa, ko mummy ya fada yana kallon nihal" murmushi tayi mai sauti sannan tace "hmm baban kids a rage son yara fa, wata rana sai sun hana ka shiga lambun maman su, ko ka manta me ya faru ɗazu? Ta faɗa tana rungume afreen sannan shima ya haɗa su har jasmin ya rungumo haɗe da saka wani sabon dariya dukan su ma dariyar suke, yace "My beautiful families, Allah ya bar mu tare" ALHMDULILLAHI BI NI'IMAT Allah shine abun godiya daya bani ikon sauke wannan book ɗin lafiya, Allah yasa mu amfana da abun daya ƙunsa, kuskeren da nayi aciki, Allah ka yafe mana baki ɗaya, Allah ya bani ikon faɗakar da ku masoya na. Ina godiya ga daukakin lovers ɗin wannan book ɗin, Allah ya bar kauna. Kasancewar wannan book din na SOYAYYA ne, na sadaukar da shi ga mijina abin alfahari na. Sai kun jini acikin sabon book ɗina mai suna RAYUWAR SALEEMA. mr yusuf ❤️❤️❤️