*FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* *To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"* *"Littafin FARGAR JAJI goro ne zuwa ga Hajiya Zainab Inuwa Isah AUNTYSIS(My Anty) with your support na fara wannan labarin kuma da support ɗin ki na rufe shi. Thank you for always being there for me. It means the world"* *Littafin FARGAR JAJI na musamman ne zuwa Yayana JAMILU UMAR wanda ya yi aure ranar 04 ga watan April tare da Amaryansa Mariya Iman. Ina fatan Allah ya ba ku zaman lafiya tare da zuru'a masu albarka Amin.* *Tukwaicin Littafin FARGAR JAJI zuwa ga DR FADILA KABIR. Anty Fadila tana sona tana son cigaba na, yadda kike sona da kula da al'amurana Ubangiji ke ma ya so ki, ya tsare gaban ki da bayan ki ya albarkaci rayuwar su Maheer Amin* *Yabon Littafin FARGAR JAJI zuwa Aminiyata AISHA ALTO, na yaba miki Tawan Ubangiji ya yaba miki Allah ya dauwamawar da farinciki a rayuwar auren ki, Allah ya raya mana Noor da Yumna Amin* *Fatan alheri ga Ƙannena masu kula da ni tare da rubutuna. *AISHA UMAR*, *MARIYA UMAR(Hajiya)* *Allah ya taimake ku, ya ba ku sa'a akan karatun ku Amin.* *Jinjinar littafin Fargar Jaji zuwa Surayya Dee. Kawata mutuniyar kirki mai zuciyar zinare, kina da karamci da dattako Janafty ta gode miki Ubangiji ya ba ki zuru'a masu albarka Allah ya jiƙan magabata Amin* *Gaisuwar littafin Fargar jaji zuwa ga iyayen ɗakina* *Khadija Salisu Yusuf* *Haj Habiba Abubakar Imam (Yayata)* *Haj Niima Bala Rabi'u (Anty Niima)* *Haj Halima Ɗalha Shehu (Umma)* *Haj Hadiza Mahe Muhammad* *Haj Sadiya Abu.* *Haj Samira Baffa* *Haj Zainab Abdulwahab* *Haj Aisha Ahmad Iya* *Haj Lubabatu Musa(Mama)* *Barrister Salamatu Doma(Mommy)* *Haj Halima Wada Kura* *Godiya ga ƙawayena* *Halima Yusuf Gwarzo( Besty)* *Maryam Jumare* *Nana Halima(Masoyiya)* *Jamila Umar(Namesake)* *Aisha Umar Ibrahim(Tawan)* *Hafsat Mustapha(Sahiba)* *Sumayya Bashir Kugu* *"Na gode sosai Allah ya saka muku da alheri ya Allah ya bar zumunci.* *Gaisuwar sada zumunci ga Aminaina* *Maryam Aminu Musa(Kitty)* *Ummulkhairi Sani Panisau(Khairi)* *Muhammad Sani Lawal(Sayyid Amanar Janafty)* *Sadeeq Rufa'i Ɗanguguwa(Sadi namu)* *Iyalan Fam ina son ku, Ubangiji ya so ku, Allah ya ƙara haɗa kawunanmu tare da danƙon zumunci na har abada Amin.* *Fatan alheri zuwa ga Maryam Saminu Sulaiman(Anty Maryam). Wannan gaisuwar ta musamman ce daga Janafty tare da Surayya Dee. Mun gaishe da shugabar masu sharhi Allah ya yi ma rayuwa albarka Amin* *Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, Bismillah.* https://chat.whatsapp.com/IF0uPZWtcCOIczsjhdCbIZ?mode=gi_t https://www.arewapen.com/u/jamilaumarjanafty *01* *SHIMFIƊA* *NIGERIA.* *ADAMAWA:YOLA.* Jahar Adamawa(Fula: Leydi Adamawa) jaha ce da ke shiyyar Arewa maso gabashin na shiyyar Nageria. Jihar Adamawa na daga cikin Jahohin mafi girma a Nageria, kuma ta mamaye kusan faɗin 36,917sqkm. Jahar ta haɗa iyaka da Barno daga arewa maso yamma. Gombe jaha daga yamma taraba daga kudu, maso yamma a yayin da ta haɗa iyaka da ƙasar kamaru daga gabas. Jahar ta samo asalin sunanta ne daga tarihinta daga Masarautar Adamawa, tare da tsohon babban birnin Masarautar watau YOLA wanda take a matsayin babban birnin Jahar Adamawa a yau. Jahar ta kasance daga cikin mafi rabe-rabe tare da harsuna na asalin garin dabam-dabam fiye da guda 100. An kafa Jahar a shekaran 1991 a sa'anin da a ka raba tsohuwar Jahar gongola don samar da Jahar Adamawa da Taraba. A cikin jihohi guda 36 na Nigeria. Jihar Adamawa ta fi kowacce girma ta fuskar faɗin ƙasa, amma ita ce ta 13 a jerin jihohi masu ƙarancin yawan jama'a tare da kimanin mutum milayan 4.25 dangane da ƙiyasin shekaran 2016. Dangane da yanayin kasa kuma jihar ta ƙunshi tsuddai da tsaunuka(kamar su Atlantika, mandara da kuma shebshi) da kuma tsaunin Adamawa pleateu tare da kogi zagaye da tsaunika. Yanayin damshin zafi/Sanyi na Jihar Adamawa yana farawa ne, a watan nuwamba, garin na da zafi sosai musamman a lokacin zafi, sannan lokacin sanyi na farawa ne daga watan december zuwa watan fabarairu na kowacce shekara. **** *YOLA:JIMETA* *AREA:Jalingo street.* *7:20PM* JImeta birni ne, a garin Yola ta jihar Adamawa Nigeria. Yawan mutane garin ya kai 73,080 a shekaran 1991. Tsayin Jimeta yana da mita 135, kuma yana gefen kogin Benue. Ta duba agogon wayarta sau shurun masaƙi ba tare da ta gaji ba, zaune take a saman kujera mai zaman mutum biyu da suka yi ma falonta ƙwanya. Ta yi kwanciyar rigingine tana kallon rufin POP ɗin da ke falon. Ƙaramar fankar dake saman ɗakin ke gudu idanuwanta na wajen kamar tana ƙirga adadin juyawar da fankar take yi a zahiri. A baɗini kuma hankalinta ba ya wajen zuciyarta da hankalinta sun tafi tunanin me ya hana Habib dawowa gida a lokacin da ya saba dawowa? Ajiyar zuciya ta sauke lokaci ɗaya tana sake nisawa, sannan ta tashi daga kishigiɗan da ta yi ta samu nasaran zama sosai a zaman kujeran, wayar da ke gefenta ta miƙa dogon hannunta fari tas mai ɗauke da ƙunshi ja ta jawo wayar ta latsa gefe haske ya bayyana Idanuwanta na kan lokaci dai dai agogon wayarta na ƙara minti ɗaya daga cikin mintinan da ya ke ƙirgawa. 7:30Pm, iskar bakinta ta fesar kafin ta miƙe a kasalance, kasalan da ta fara jin tana muƙurƙusan jikinta a kwana biyu nan, bakin window ɗin dake falon ta isa ta yaye labulan tana mai kai duban ta zuwa haraban gidan da ba ka ji motsin komai sai ƙaran wucewar iska, sai kukan tsuntsaye, akwai haske tarwar a haraban gidan saboda akwai wutar nepa ta kai duban ta zuwa ga flat ɗin da gefen su, shima dai shuru amma akwai haske daga cikin gidan alamun masu gida suna ciki suna gudanar da rayuwar su kamar kullum, idanuwanta ya hango mata motar mai gidan a fake a bakin compoud, sai ita kaɗai ne mijinta bai dawo gida ba? Gidan su gidan haya ne, sun kai kimanin su shidda a ciki. A jere flat ɗin suke amma suna sharing filin compound ɗaya, sai ka yi sati biyu ba ka haɗu da wani na kusa da kai ba wasu ma ana yin wata, wani lokacin ma in dai ba fita za ka yi ba, wataƙila wata ma ta fito za ta fita sai ku haɗe ku gaisa amma ba mai shiga bangaren kowa musamman da yake akwai ma'aikata da masu fita makaranta a gidan. Ta yi wani luu da idanuwanta lokacin da iska ya taso sai ta kai kallon ta ga sararin samaniya, ashe haɗari ne ya haɗu sosai sannan ya ta so lokaci ɗaya da iska, suna cikin tsakiyar damuna ne, ana yawan samun ruwa musamman ma da daddare. Sanyi ne ta ji ya fara shigar ta har tsikar jikinta na tashi, saboda ƙaramar riga ce a jikinta. Sai ta yi saurin rufe window ɗin ta zuge labule ta ƙamƙame jikinta da gudu-gudu sauri-sauri ta koma kan kujeran da ta tashi ta zauna, wayarta ta sake jawowa a karo na uku ta sake kiran lambar Habib da ta yi ma Saving da NOORI, kamar sauran kiran wannan ma har ya katse bai ɗaga ba sannan bai biyo baya ba, ta fara jin ba daɗi saboda ba haka ya saba ba, duk in da ya ke yana dawowa gida kafin sallar isha'i, in kuma zai kai bayan isha'i a waje sai ya kira ta ya shaida mata. Amma yau ya makara kuma tana ta kiran shi bai ɗauka ba sai ta fara tunanin wataƙila ba lafiya ba ko wani abu ne mara daɗi ya same shi? "Aa ba abin da zai faru da Noori na" Ta faɗa a fili tana mai furzar iska daga bakinta, ƙokarin karfafa ma kanta gwiwa take yi na cewa ba abin da ya same shi, saboda ita ba ta iya shiga damuwa ba yanzu nan sai ta rasa hankalinta. Ta fi karfafa ma kanta gwiwa da cewa wata ƙila ya biya ta gidan su ne, wata ƙila can ya tsaya shi ya sa ya ɓata lokaci bai dawo ba, sannan watakila wayarsa na silent ko bata tare da shi, shi ya sa bai ji kiran ta ba. "In sha Allahu yana lafiya. Ki natsu Ummu-Salma." Ta faɗa a fili tana sake karfafa kanta, ajiyar zuciya ta riƙa saukewa a jere har sai da ta samu natsuwa sannan ta iya sauke numfashi a hankali. Jikinta ta bi da kallo a duk dare a irin wannan lokacin haka take yin ado domin tarban mijinta Habib, yau ma ɗin ba ta sauya zani ba ta yi adon ta cikin riga da wando, rigar ba ta ko rufe mata cibi ba, kuma sagalan hannayenta na vest ne shi ya sa take jin sanyi na shiga jikinta, sannan wandon jikinta iyakarsa ƙwarinta sannan ya ɗameta sosai ya bayyana suran jikinta. Kanta ba ɗankwali gashinta ta saka band ta ɗaure ta saki jelan daga tsakiya, fuskarta ba kwalliya ta yi sosai ba amma ta saka jan baki mai ƙyalli yana ɗaukan ido, daga ita har falon suna tashin ƙamshi mai sanyaya zuciyar ma'abocin son ƙamshi. Ummu-Salma Hadi BaBa farar mace doguwa, Bafullatan hausa-fulani daga tsatson fulanin Mubi, haihuwan Jimeta, ba sai an faɗa maka ba kana ganin ta za ka shai da ita ɗin jinin fulani ce daga yanayin ta da komai na ta, sannan da yanayin mganarta da ba ta da hausa sosai, kyakyawa ce ajin farko ga fari ga hanci ga zati da zubi, komai na cikar ƙimar mace ubangiji ya riga ya bata. A ƙiyasin shekarunta ba za ta gaza shekaru 24 a duniya ba. Lokaci bayan lokaci tana cigaba da duba agogon wayarta, har takwas ta kusa saura mintina goma, ga shi har an fara yayyafi. Ganin haka ya sa ta miƙe ta buɗe ƙofar tiolet ɗin dake tsakanin bedrooms ɗin ta guda biyu ta ɗauro alwala, bedroom ɗinta ta shiga mai ɗauke da makeken gado da wardrope, hijabin sallan ta na saman gado da ta yi sallar mangariba shi ta zura bayan ta shimfiɗa sallaya  ta da salla, bayan ta idar tana zaune tana ƙirga yatsunta lokaci ɗaya ta ƙura ma waje ɗaya ido tana tunani. "Wai ina Noori ya tsaya ne? Ta tambayi kanta a zucci da sarari, miƙewa ta yi da hijabin jikinta saboda ta na jin sanyi-sanyi, kwana biyun nan ta fara jin canje-canje a jikinta kamar samun kanta cikin kasala, ciwon jiki, ciwon kai ciwon mara da yanayi mara daɗi ta ji ba ta jin cin komai, ga yawan barci in za ta tashi da ƙyar jikinta ya yi ta ciwo kamar ta yi wani aikin wahala mai tsanani, tun tana jin yanayin kaɗan-kaɗan har yanzu yanayin na yin yawa, daman niyar ta yau in Habib ya dawo ta sanar da shi ba ta jin daɗi ya kamata ta je ta ga likita. Falo ta koma ta zauna a saman kujeran da ta tashi, falon babba ne yana da faɗi da tsawo, daga can ta sama akwai bangaren Dinning amma ƙarami ne mai kujerun zama guda uku, sai falon da kujeru guda huɗu suka yi masa ƙwanya sai cafet da ya malale tsakar ɗakin mai ɗauke da santer table. Daga gabas kuma ƙaton tibi ne akan tv stand, sai agogo dake sama babba yana ƙirga lokaci ɗit!ɗit. Kujerun falon black and milk ne, shi ya sa har labulayan suma colour ɗin su kenan, wayarta ta jawo saboda ta ɗauke mata hankali daga tunanin rashin dawowar Habib yau da wuri data ta buɗe ta shiga Tiktok tana ta kalle-kallen abubuwan girke-girken zamani, saboda in dai bangaren girkin ƴan gayu ne na zamanin nan za ka gan su a wajen Ummu-Salma kala-kala, tun tana gida in tana sarrafa wani abun sai ka ce in ta gama ba zai ciyu ba ne, amma in ta gama haka za a yi ta santi musamman ma Baffa da ke supporting ɗin ta a komai na rayuwarta. Amma ce sarkin faɗa ta yi ta masifa tana cewa Ummu na yi mata ɓarna da shegen iyayin nan nata, saboda ita Amma yar gargajiya ce gani take yi duk abin da Ummu ke yi wahalar da kanta ne kawai da iyayi, a cewarta abincin gargajiya shi ne sahihin abinci ba kayan ƙwalama da Ummu-Salma ta ɗauka abin birgewa ba. Amma ta sha ce mata in ta yi aure za ta gani in wannan ƙwalamar da ta fi ƙwarewa akai za ta riƙa girka ma mijin yana ci. A lokacin baki ta tura kafin ta amsa mata da cewa" Ammah ke fa ba ki gane ba, ko an yi abinci ana buƙatar irin haka saboda zamani ne ya zo mana da hakan" Baffa ya sha kashe kuɗi akan online clasess da na training akan burin Ummu na ƙwarewa a girke-girken zamani da sarrafa fulawa ta kowacce hanya kuma ta yi nasara ta koya kuma ta iya kuma har gobe tana kan koya. Yanzu haka ma tana cikin wasu guda uku, kuma a wayarta girke-girke ne sun fi guda dubu, shi ya sa ko tiktok ta shiga abin da za ka yi ta gani kenan ta kalla ta yi like in kuma tana so sai ta yi saving Vedio ɗin, sannan tana da karambani, duk abin da ta gani sai ta gwada shi, shi ya sa a wajen Ummu-Salma fulawa ba ta bata tsoro za ta iya sarrafata fiye da nau'ika goma a lokaci ɗaya. Daga Tiktok, WhatsApp ta koma charting bai wani dame ta ba tun da ba ta da yawan surutu a waya kafin ta duba chart sau goma ta lalace a wajen kallon status ɗin jama'a.  Ummu Salma sai ta yi watanni ba ta kira wayar mutum ko ta yi masa mgana ba amma kullum tana nan tana duba status ɗin ka sai dai in ba ka saka ba. Za ta duba kuma ta gani amma ba za ta yi mgana ba, ko da rashi aka yi ma mutum ko abin ƙaruwa a cewarta charting ba wajen jaje ba ne ko murna wajen nishaɗi ne, shi ya sa sau tari sai dai ta kira ka a waya ta yi maka jaje ko murna amma ba dai ta charting ba. In za ka jira ta yi maka mgana sai dai ku daumana a haka, yayyenta maza har sun saba da halinta in ka ga tana charting a waya mai tsawo da mutane uku ne. Mutum na farko Mami ce ta biyu kuma Bestie ta uku kuma Sisna, ban da mutanen nan guda uku Ummu Salma ba ta doguwar mgana da kowa, Habib ne lokacin tana gida suna yawan yin charting bayan sun yi aure suna yi amma ba sosai ba shi ya sa a saman chart ɗin ta ba ta kuskure ma waɗanan mutanen guda uku. Bestie, Mami, Sisna. Bestie da SisNa ƙawayenta ne Mami kuma wata mace ce mafi daraja a rayuwarta bayan Ammah. Yanzu haka ma tana cikin duba status ɗin Hamma Abdulrrahaman ta ga ya saka wasu hotuna shi da abokan aikin sa sun sha Suit, da alama a wajen aikin shi ne aka yi wani abun tun da lauya ne, sai ta ga saƙon Sisna ya faɗo da sauri ta fita ta je ta duba. "Sisna." Ta turo mata da emojin kuka. Wani farinciki ya kamata jiki na rawa ta ma yar mata da amsa itama. "Naam Sisna ya aka yi ne? Wa ya taɓa mini ke yau na ta da garin Jimeta da kewayan ta? Daga ƙarshen maganarta ta sirka da fullanci, ta tattara emojin wukaƙe da hannu zai kai naushi. Vioce note ta turo mata na sakwan talatin tana buɗewa ta ji muryanta cikin shagwaɓa tana faɗin. "Sisna, na gaji da karatun nan na yi matukar gajiya, ni dai kawai ki zo ki ce ma Umman ikki a yi mini aure kamar yadda aka yi miki." Ummu-Salma ta kwashe da dariya kafin itama ta danna Vn ta fara mgana. "Uhm ai ni da man na sani akwai abin da ya kai karatu wahala ne Sisna? Wallahi babu shi shi ya sa na ce na gama kuna ganin laifina. Yarinya ki zo ki yi aure a cikin aure akwai Nii'imaaa." Ta ƙarishe faɗa tana jan maa ɗin da dariya. Sannan ta tura. "Wai ke me ya sa in dai mutun ya kawo miki damuwarsa akan karatu sai ki sake ƙarya masa gwiwa? Sisna ki ƙarfafa ni tun da na saka kaina kuma na fara ki karfafa ni, ki ce Sisna ki jure keep fighting za ki iya." "SisNa Fight.!!!* Ta tura mata tare da emojin ɗaga power hannu da jinjina. "Yes Maa"!! Itama ta sake dawo mata da amsa, har da emojin kai biyu da love a saman su. "Ina Habib? "Bai dawo ba Sisna.". Ta bata amsa da gayyar emojin kuka. "Dilla ke kuma. To kin kira shi? "Ba ya ɗagawa." "Kar ki damu Sisna. Ƙila ya biya ta gidan su ne zai dawo yanzu kin ji ko? "To" "Smile my beautiful Baby." Sai ta tura mata emojin heart, da na dariya sun fi goma. "Good night. Ki yi mini addu'a kin san upper week za mu fara exams." "Ubangiji Allah ya ba ma Sisna Sa'a. Allah ya sa Aisha(Baɗɗo) ta fi kowa maki da samun nasara." "Amin Amin Sisna, sai mun yi waya." "Bye" Itama ta tura mata Bye ɗin amma bai yi marking sau biyu ba hakan ya ba ta tabbacin ta sauka daga online, numfashi ta fesar tana kallon window an fara ruwa duk da bai yi ƙarfi ba sosai, ta shi ta yi ta sake gyara labulen da kyau kar ruwan ya yi ƙarfi ya yi mata feshe duk da ta rufe window ɗin, kichen ta shiga da ya ke da ƙofa ta wajen dinning, kitchen ɗin shima Babba ne yana da space sosai ɗaya daga cikin drowers ɗin kitchen ɗin ta buɗe ta dauko wani ƙaramin mug, akwai ƙaramar buta a saman gas cike da ruwan tea da ya ji gayayyanki shi ta ɗaga ta tsiyaya bayan ta saka ƙaramar rariya ta tace, siga ta ɗan saka kaɗan sannan ta samu ƙaramin Bowl, ta buɗe wani kwali ta ɗebo doughnuts guda uku manya ta zuba a ciki sai da ta ma yar da komai a muhallin shi sannan ta ɗauki mug ɗin da Bowl ɗin ta koma falo ta jawo santer table ɗin dake tsakiyar falon ta ijiye saman ta isa gaban Tv ta kunna soket ɗin sai ta ɗauko remot ta dawo ta zauna ya kawo amma a tashar ƙwallo ne Habib ke kallo in dai yana gida sai ta ma yar da ita tashar Arewa24 suna maimacin kwana chasa'in sai ta bar shi amma ta rage sautin duk da kallo bai dame ta amma tana yi jefi-jefi. Kan kujera ta koma ta naɗe har da tankwashe kafa, ta ja mug ɗin tea din ta, tana kurɓa lokaci bayan lokaci tana gutsiran doughnuts ɗin dake saman cinyarta, har wani lumshe ido take yi saboda daɗi. "Ashe ya fi ma daɗi in ya yi kwanaki." Ta faɗa tana sake gutira a bakinta, Bowl ɗin ta sauke a saman kujera ta sake jawo wayarta chart ta shiga ta duba Habib tun 5.40pm ya sauka daga online, sai ta je ta duba Bestie itama tun safe ba ta damu ba sanin tun da suka kusa fara jarabawa Bestie za ta yi wuyar gani. Sai ta rubuta mata. "Bestie kina lafiya? Ya karatun? Da wahala ko. Ayya sannu Allah zai ba ki nasara Bestie na" Ta tura mata kuma ya tafi amma ba ta online tun da bai yi marking sau biyu ba. Sai ta koma ta duba Mami sai ta ga tana online da sauri ta tura mata. "Mami na." Ba daɗewa Mami ta dawo mata da amsa. "My first Daughter me kike yi da waya da daren nan? Ina mijin ki? "Mami bai dawo ba" "Is he Ok? Mami ta tambaya sai ta amsa mata da lafiya lau ya biya ta gida ne. "Good, nima ina duba test ɗin ɗalibai ne, gobe zan kira ki. Good night." "Good night Mami na." Ta rubuta tana tura baki kamar tana ganin ta. "Kowa sai ya ce mini wai Good night" Ta faɗa tana sake tura bakin ta gaba, ajiyar zuciya ta sauke ta fita daga nan ta koma Tiktok tana ta kalle-kalle amma tana ta duba lokaci har tara ta kusa amma Habib bai dawo ba, kuma bai kira ta ba, ta fita daga wajen da niyar sake kiran shi sai kuma ta koma cikin chart ɗin ta bangaren status, kwatsam ta ga Hamma Sadam ya saka status 4m ago. Da rawan jiki ta buɗe hotuna ne kuma hotunan ba baƙinta ba ne, duk wani ɗan Nageria dake mu'amala da social media ya san hotunan nan saboda yadda suke trending a duka kafafan sada zumunta tunda satin nan ya fara. Amma abin da ya ba ta mamaki caption ɗin Hamma Sadam a ƙasan hoton "Allah ya sanya alheri my Sis Badi'atu" Baki ta buɗe sannan ta rufe tana sakin wata dariya. "My Sis? Lalle ne ma to ko a yaushe ta zama sis ɗin ta shi ni ban sani ba? Ta faɗa a fili tana sake yin dariya hotuna ne ya saka sun fi kala biyar na Amarya Badia'tu da angon ta wato Pre-wedding pictures ne da yan zamani ƴa'ƴan masu kuɗi ke yi in za su yi aure. Hotuna ne fitattu da suke tashe a yanzu bikin sai satin sama ne amma tuni hotuna da katin shagulgula sun watsu a duniya saboda bikin na masu kumbar susa ne da masu mulki da sarauta Duk in da ka shiga hotunan Amarya da angon ne, sai katin bikin da na Program of events ke yawo a duka manya bloggers ɗin mu na arewa gabaɗaya. Kallo take yi tana taɓe baki kafin ta ce a fili. "Allah ya sa ta ma san kana yi Hamma Saddam" Ta faɗa tana sake yin mirmishin gefen baki, sau ɗaya ta taɓa ganin ta lokacin da Ammah ta matsa mata suka je naɗin sarautan Hamma Lamiɗo a matsayin Yariman Daura. Tun a lokacin ta ga jin kai da isa a wajen wannan yarinyar, ta tabbata tusa kai ne kawai irin na Hamma Saddam ba ma a san yana yi ba. Wata ƙila Hamma Lamiɗo ya yi ma kara  shima kuma tana da tabbacin bai san ma yana yi ba. Abin da ya saka na karshe a status ɗin sa katin bikin ne da shagulgulan da za a yi tun satin bikin har zuwa ranar ɗaurin aure. Ɗaurin aure ne kawai za a yi a masarautar Daura amma sauran shagulgulan duk a garin Abuja za a yi. Ba ta san ta kwashe da dariya ba sai da ta ga caption ɗin Hamma Sadam a kasan katin "Family and Friends bikin gidan mu ne fa ya zo.  Bikin gidanmu saboda haka ban ɗauke ma kowa ba." Ummu-Salma tana dariya har sai da ta shaƙe, Hamma Sadam na da abin dariya wai bikin gidan su ne.! Yaushe bikin gidan masu Sarauta da masu mulki ya zama na gidan su? Bikin ɗiyar sarkin Daura ALHAJI Dr. NASIRU MUHAMMAD DAURA ne fa za a yi, za ta auri yaron mai ba ma shugaban ƙasa shawara akan yaɗa labarai, shi ne wai Hamma Sadam ke ta rawan jiki har yana faɗin wai bikin gidan su ne, gaskiya Hamma Sadam akwai tusa kai ba ƙwarjini da gayya ta masa reply akan status ɗin sa na ƙarshe. "Ka ji Hamman nan, bikin gidanmu ma fa ka ce? Ko dai bikin gidan su Hamma Lamiɗo? Kamar yana jiran ta sai ga shi ya turo mata da sticker na an ɗaga wani an tika da ƙasa sannan tare da emojin nan na ɓacin rai. A ƙasa ya haɗo da cewa. "Bikin gidammu ne Ummu ko ke ba na gidan ku ba ne? Kai tsaye ta bashi amsa da cewa. "A'a wallahi ba na gidanmu ba ne Hamma." Emojin mamaki ya turo kafin ya ce" Ammah na gefe na nuna mata abin da kika ce? Da sauri ta ce" Rufa mini asiri Hamma bikin gidan mu ne." Ta rubuta sannan ta tura emojin heart har da na rawa. "Yauwa yarinya." Ya rubuto tare da sticker na dariya, saboda haushi ba ta amsa shi ba sai ma ta kashe data ta ajiye wayar, Hamma Sadam na so ya jawo mata masifan Ammah a daren nan ba ta shirya ba, ai tana jin yadda Amma take shirya ma wannan bikin ko ita uwar Amaryan albarka. Wanda take yin abin nan domin shi wataƙila ma ba zuwa zai yi ba, mutumin da an sha yin abubuwa na daɗi da aka sin su bai taɓa zuwa ba, shi bai ɗauki zumunci ma abakin komai ba, ba abin da ya sani sai tuƙin jirgi, kuɗi kawai alhalin ahalinsa suna da tarin dukiyar da har jokokinsa ma ba za su yi talauci ba, tana da tabbacin ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba, ba zai samu zuwa  ɗaurin auran ƙanwarsa ba shi ya sa da bai zo na ta ba, ba ta damu ba Ammah ce ta damu saboda sun yi mgana ya ce mata zai zo, a cewarsa ya ɗauka za su iso bakin gaba ne ana gobe ɗaurin aure sai kuma tafiyar ta su ta sauya tsari shi ya sa bai samu zuwa ba. Duk fa Ammah ce ke ta yawo da wannan mganar shi gogan ba wanda ya ji haka daga bakin shi. To wai wanda ko ɗaurin auran shi bai samu zuwa ba to na waye zai je? Shi ya sa ma wanda ya damu in bai gan shi a sha'aninsa ba, shi ke da kaico shi dai bai ma san kana yi ba, shi fa mutumin nan dabam yake, ɗauka yake kuɗi sune muhimmi a rayuwar nan daga naira ɗaya har miliyan goma zai iya tura maka amma kuma ba zai iya zuwa ya yi maka murna ko jaje ba shi ya sa har gobe bata taɓa saka Hamma Lamiɗo a jerin mutane masu karamci ba, ta fi saka shi a jerin mutane masu girman kai da ɗagawa.   Tana cigaba da cin doughnuts ɗin ta, tana kuma kurɓan tea a lokaci ɗaya amma sai taɓe baki take yi ita kaɗai daga gani hakan yana daga cikin ɗabi'arta. Ita fa tun wancan satin da ta je gida Ammah ta dame ta da labarin bikin nan na Daura ta ji ba za ta sake komawa ba sai bayan an gama bikin nan, domin hankalin Ammah ba a kwance yake ba yanzu sai ta ga ta je Daura an gama biki lafiya ta dawo tukunna. Baffa dai ba ruwan shi ba lalle ne ma yaje ɗaurin auran ba Ammah kuma ba wanda ya isa ya ce ba za ta je ba ai sai ranar gidan ya kwana ba lafiya. Baffa ma yasan halin kayan shi, shi ya sa ba ya ma gigin shige mata na shi addu'a ne da fatan alheri, domin in dai akan sha'anin abin da ya shafi Hamma Lamiɗo ne ko Baffa bai da ta cewa, da jikinta da zuciyarta take hidimtama wannan bawan Allah da Ubangiji ne ya haɗa wannan ƙaunar da tana tunanin ko su ƴa'ƴan cikinta ba ta nuna musu ƙauna da kula da alamuransu da muhimmanci kamar yadda take kafa-kafa da duk wani al'amarin da ya shafi Hamma Lamiɗo.   Shi ma kuma ba ya iya tsallake umarninta komai tsaurin shi a gare shi. Da Amma kaɗai yake iya doguwar hira cikin nishaɗi, ita ce kawai take iya ganin dariyan shi har da haƙora a waje. In ba za ta manta ba lokacin tana aji biyu a matakin babban sakandiri aka yi bikin Hamma Lamiɗo, auran da a farko cewa ya yi ba ya so tunda haɗin daga kakarsa ce Fulanin Daura, Mai martaba kuma ya ce ba zai matsa masa ba, Mami kuma ta ce ina ruwanta da sha'anin Lamiɗo? A nemi uwar sa Ammah ita ce za ta iya saka baki akan mganar, Hamma Lamiɗo da bayan gaisuwa magana ta mintina biyar ba ta taɓa haɗa shi da Mami a matsayinta na mahaifiyarsa ba, ko da za su yini waje ɗaya su kwana. Ba ma ita ba, Hamma Lamiɗo zai yi rayuwa da mutum na tsawon kwanaki amma ban da gaisuwa magana ta fatar baki ba zai yarda ta haɗa su ba. In ko ka matsa ka yi hira da shi kai ne da haushi, domin a ginshiƙe zai din ga tafiyar da kai da har sai ka yi zuciya ka ƙyale shi. Haka ko aka yi  tawagar Fulanin Daura har cikin falon Ammah, ta zauna ta roƙe ta da ta sanya baki Lamiɗo ya karɓi auran nan, da suka je suka karɓo masa ƙafa da ƙafa har wajen Mai martaba Sarkin Kano a lokacin Balkisu ba ta daɗe da dawowa daga ƙasar Spain ba, a can ta yi duka karatun ta na likitan ci. Ammah ta yi ma Fulanin Daura alƙawarin za'a yi auran nan kuma maganarta ya tabbata. Tana cema Hamma Lamiɗo in har ya ɗauke ta a matsayin uwa to ya karɓi wannan auran da cewarta da auran ko wata biyu ba a yi ba. Abin mamaki sun rufe shekara da wattani ne da aure matar Hamma Lamiɗo ta haihu,  har yau Ummu-Salma na mamakin wannan abu, ka ce ba ka son aure amma kuma ana yi sai shuru, kuma ko zuwa suka yi tare ba mai gane yanayin shi. Ba za ka ce yana son ta ba, ba kuma za ka ce baya son ta ko da wani lokaci yana nan a ginshiƙen sa. Shi fa ba ka iya gane ma yanayinsa kwata-kwata, fuskarsa ba ta bayyana farincikinsa ko bakincikinsa. Ammah kuma al'amarin ƴa'yanta kuwa sai dai Ummi ikki ta yi gaba ita tana baya, amma in dai lamarin Hamma Lamiɗo ne ba ta jira ba ta kuma sakawa a yi mata, ita ce da kanta take yi masa komai, tun tana ƙarama ta shaida Ammah ta fi hidimtama Hamma Lamiɗo fiye da su ƴa'ƴanta na cikinta tun tana damuwa har ta saduda ta sare. Ta taɓa tambayan Baffa me ya sa Ammah ta fi son Hamma Lamiɗo akan kowa a gidan nan? "Sabo da shima ɗan ta ne Ummu Salma. Nima ba ki ga ta fi son shi a kaina ba? A lokacin dariya ta yi, kuma gaskiya ya faɗa ko Baffa bai isa ya ce wani abu akan Hamma Lamiɗo ba, ko yana nan ko baya nan Ammah mai tsaya ma yau ɗin sa ne har da jiyansa ma sannan za ta tsaya ma gobensa ma. Ba ta san Habib ya dawo ba domin ba ta ji motsin ko shigowar motarsa haraban gidan ba hankalin ta na kan Tv tana hakaito soyayyar Ammah ga Hamma Lamiɗo gefe ɗaya tana kallon drama ɗin Rayya da Avm Adnan, haka kurum take son film ɗin sabo da su, soyayyarsu na matukar birge ta Kamar ita da Noorin ta. Su suka sanya ta mantawa da Komai ta ma yar da hankalinta kan kallon gabaɗaya. Kamar daga sama ta ji ana murza ƙofa alamun an saka key za a buɗe, ƙurama ƙofar ido ta yi ba ta yi ko motsi ba. Ya saba ina tana dirin shigowar motarsa ta ke kamewa a tsakiyar falo yana shigowa za ta tafi da gudu ta naɗe a jikin shi, shi kuma kamar ko yaushe ya fara juyi da ita a tsakiyar falon cikin soyayya da muradi. Amma yau sai ta ji kasala ya rufe ta ta kasa tashi, ko mararin ganin shi a lokacin ba ta ji ba wataƙila da ba ta gan shi ba ne ya sake ta ba ta dai sani ba. Tana nan zaune ya shigo falon ɗauke da karamar jakarsa ya ɗan jiƙe domin ga alamun yayyafi nan a jikin baƙaken suit ɗin da ke jikinsa. Wataƙila ya ɗauka ba ta falon ne, shi ya sa ya tuɓe takalmansa ya ƙariso ciki sai dai me! Sai ya gan ta zaune tana mai kallon shi da manyan idanuwan ta. Waro ido ya yi kafin ya ce. "Baby da man kina jina? Ya faɗa yana mai sauke jakar hannunsa a saman kujera mai zaman mutum ukun dake kusa da shi, ware ma ta hannuwa ya yi lokaci ɗaya yana sake faɗin. "Baby na i miss you." Ya faɗa yana yi mata murmishi, wannan murmishin na shi mai tsada da ya kan narkar ma ta da zuciya a lokuta da dama in ya kalle ta ya yi mata. Maƙe kafaɗa ta yi, lokaci ɗaya tana tura baki , sannan ta kauda kanta alamun ta yi fushi, yana ganin haka ya yi saurin isowa kujeran da takwle zaune yana faɗin. "Baby am sorry, kin ji ni shuru ko? Ta ƙi yarda ta kalle shi, ganin haka yasa ya ɗauke Bowl ɗin dakw gaban ta da mug ɗin tea ya ɗora bisa table ɗin gaban su da karfin sa ya saka hannu yana ƙokarin juyo da fuskarta ta ki ba shi damar haka. "Baby ni ne fa? Noori ɗin ki ne yau ba ki son kallon fuskar shi? Ya faɗa yana kawo mata hannu zai taɓa fuskarta da sauri ta bige hannun shi, cikin shagwaɓa ta ce. "Noori ka san zan damu ko? Ta faɗa tana mai kallonsa lokaci ɗaya hawaye suna cika kwarmin idanuwanta  ba ta da wuyar kuka abu kaɗan sai ya saka ta kuka ko kallo ta ke yi ɗan emotion kaɗan sai ta fara hawaye, yanzu ɗin ma ji kawai ta yi tana so ta yi kuka. Jin muryar ta na rawa ga shi idanuwanta da jwalla ya sa ya ruɗe ya tarairayo ta da hijabin jikinta ya ɗora ta bisa cinyarsa yana tallabe da fuskarta da tafukan hannayensa duka biyu "Ni ne ko? Sorry Baby Gwaggo ce t kira ni kuma na manta waya ta a mota na saka ta chaji, lokacin da na fito na ga kiran ki sai ban kira ba, tun da lokacin ina kan hanyar dawowa ne" Ya faɗa yana mai kallon ta itama shi ta ƙura masa ido, tana sake runtse ido sai kawai hawaye suka zubo mata sharr a saman kumatun ta. "Baby ki daina kuka mana. Bana so kin sani." Ya sake faɗa bayan ya saka tafin hannunsa yana share mata hawaye. Buɗe idanuwanta  ta yi  tana kallon shi, gashin idanuwan ta duka biyu ya sumbata kafin ya ɗago yana faɗin. "Gudu na yi ta yi a mota fa Baby." "Ba na hana ka ba." Ta faɗa cikin wata irin shagwaɓaɓbiyar murya. "Kin hana ni Baby." Ya ba ta amsa shima cikin ƙaramar murya, lokaci ɗaya yana kwantar da kan shi a saman kirjin ta hannayensa kuma ya tusa su ta ƙasa hijabinta yana shafa mararta zuwa ƙirjin ta banƙarewa ta yi shi kuma sai ya ji daɗin haka zare mata hijabin jikin ta ya yi ya tsaya yana kallon kirjin ta. Ganin haka ya sa kunya ya kamata sai ta faɗa kan kirjinsa tana masa kukan shagwaɓa. "Noori ka bari." "Me zan bari Baby? "Uhm" Ya faɗa yana shinshinar wuyanta cikin lokaci ya fara birkicewa, yana bin sasaan jikinta da wasanni ta kasa mgana sannan ta kasa hana shi, duk da yau ɗin tana jin gajiya a jikinta amma Habib ya sabar mata da komai, ƙa'ida ne in ya dawo kafin ya yi wanka ya ci abinci sai ya riban ce ta, kuma a daran ma ba zai bar ta ba kafin asuba ya yi sau uku ko sui huɗu, haka ma bayan asuba, tun Ummu-Salma na ɗaukan hakan a matsayin amarci a farkon auran su har yanzu ta daina ɗauka haka. Sai ta bar shi a matsayin mijinta Habib na daga cikin mabukatan maza ma su yawan buƙata. A farko-farkon auran su ta sha tambayan ta kanta da man wanne ne daɗin auran? Ba hutu sam, lokacin ba ta yi kiban amarci ba sai rama saboda kwazzaban Habib saboda ba ta cikin jinsin mata fitannanu, amma saboda Habib ta koya, har in bai neme ta ba sai ta ji ta a takure, da farko ta ɗauka illa ne hakan sai da ta ga wani rubutu a faceebook wanda ke nuni da cewa yawan mu'amalar aure ga mace nuna soyayya ce makura daga mijinta shike nan ta daina fargaba ta saki jikinta duk lokacin da Habib ya marabanceta za ta ba shi cikakken goyon baya, amma tunda ta yi ɓarin cikinta wattani biyu baya da suka wuce ta daina jin shauƙin abin, kwana biyu kamar lamarin ya yi sauƙi yanzu kuma ya dawo mata, sai ta rika jin ta gaji sannan ba ta son a sakar mata wata gajiyan bayan wacce take muƙurƙusan kashin ta a lokacin, sai dai ta kasa mgana ta na ji tana gani Habib ya ɗaga ta sama yana nishi zuwa bedroom ɗin su, kan gado suka faɗa ya cigaba da abin da ya fara. Ta yi ƙokarin ta bashi dukkan haɗin kai har ya samu natsuwa, bayan ya shiga wanka ko ɗan yatsan ta ba ta iya motsawa tsabar yadda take jin jikinta a mace. Tana kwance ta rufe rabin jikinta da blanket saboda Habib ya yi fatali da kayan jikinta tun a farkon yaƙin. Tana kwance ya fito ɗaure da towel a ƙugun shi karamin kuma yana goge ruwan da ke gashin kansa. Tana daga kwance take ƙare ma Habib kallo, in dai ana neman cikar zati da mazantaka Habib ya kai a namiji, fari ne tas shima sannan dogo amma ba shi da tsaho sosai yana da faɗin jiki daga sama kaɗan kyakyawa asalin bafullatanin Yola ne na uwa da na uba, hancinsa har baka sumar kansa tana nannaɗe irin ta fulani, ko ta ko'ina Habib ya kai za kuma a nuna shi daga nan har Saudiya a matsayin namijin da ya ƙera sa'a ga ilmi ga martaba ga sanin ya kamata ga iya soyayya, a kalla a shekarunsa ba zai gaza talatin da biyu ba 32. Shi ya sa yana cikin jerin layin matasa masu jini a jika, ma'aikacin banki ne shi ya sa ya zama ɗan gayu na karshe da kwatance. Habib Idris Mai imani ya kai  ya haɗu ya gaji da haɗuwa da duk macen da ta mallake shi zai zama abin alfarinta. "Baby ki tashi mana." Ya faɗa bayan ya yarfa mata ruwan dake gashin kansa. Mirmshi ta yi masa shima ya mayar mata da martanin mirmishin nata. "Tashi ki yi wanka ki ba ni abinci yunwa na ke ji Baby." Ya sake faɗa cikin yar shagwaɓa, hannunta guda ɗaya ta mika masa lokaci ɗaya tana faɗin" Noori ka ɗaga ni." Ta faɗa tana mele masa baki. "Baby me ke damun ki yau? Kin gaji ne da yawa? Ya faɗa yana rike hannunta da taimakon shi ta miƙe zaune. "Baby are you sick? Ya faɗa yana kallonta ganin ta lamgwaɓe kai. "Ban sani ba Noori amma jikina ya yi weak" Da sauri ya matso gabanta ya dafa goshinta kafin ya ce" Kuma tempereture ɗin ki is Normal." Shagwaɓa fuska ta yi kafin ta ce" Ni ma ban san meke damuna ba Noor." Kallonta ya yi kafin ya kashe mata ido ɗaya yana sake faɗin. "Ko ni ne Baby? Ture shi na yi ina faɗin" Yau ne farkon mu? "Baby to amma ai yau na kai farmaki na da kyau ko? Sake ture shi ta yi sannan ta miƙe ya taimaka mata yana tura ta bakin tiolet. "Baby yunwa." Ya sake faɗa da karfi gwiwa ta tura ƙofar toilet ɗin ta shiga tana faɗin" 5 minutes." Ta faɗa tana mai rufe ƙofar, da kallo ya bita kafin ya yi mirmishi. Wardrope ya buɗe ya ɗauko saukaƙkun kayan barci ya saka riga mai gajeren wando falo ya fita ya sauya tasha zuwa tashar ƙwallo mintina goma tsakani Ummu Salma ta fito itama cikin rigar barci mai shara-shara wacce ba ta wuce gwiwarta ba. Abinci ta jera bisa dinning, yana daga can a falo ta kira shi. "Noori Dinner is ready" Da sauri ya taso, ita ta ja masa kujeran ya zauna yana faɗin" Thank you Baby." "You are always welcome Noori na." Mirmishi ya yi mata lokaci ɗaya yana kashe mata ido ɗaya, kau da kai ta yi tana yar dariya. White rice ne da miyar allayahu, sai zoɓo da tea, tare suka ci abinci suna yi suna hiran su ta masoya. Bayan sum gama suka shiga tiolet suka wanke bakin su, Ummu-Salma ta kwashe abin da suka ɓata zuwa kitchen sannan ta koma falo wajen Habib da ya rage hasken falon ta naɗe a jikin shi, suna kallo suna hira suna kuma soyayyar su. **** Duk da yanayin Ummu-Salma da Habib ya gani bai saka ya ɗaga mata kafa ba, kafin su kwanta sai da ya maimaita. Can cikin dare ma sai da ya tashe ta tana so ta ce ya ƙyaleta ba ta jin daɗin jikinta amma ta kasa, yana dawowa daga sallar asuba ma sai da ya yi duk yadda ya ga jikin Ummu-Salma ya yi laushi a cewarsa jarumatarsa ce ta ƙaru, shi ya sa ta makara sai wajen bakwai saura ta iya ƙarfin halin tashi ta shiga kitchen, da ya ke girki Hobby ɗin ta ne garin fulawa ta iya sarrafa wa, cikin lokaci ta kwaɓa fulawa ta sarrafa shi zuwa Naan Bread. Tun da tana da kayan lambu, nama ne babu sai ta yi amfani da ƙwai. Ko kafin takwas ta yi ta jera komai a saman dinning. Ta koma bedroom ta tashi ta Habib ta taimaka masa ya yi wanka, ya tsuke cikin suit masu ruwan  baƙi da ruwan toka. Tare suka zauna zaman ƙaryawan Naan bread ɗin suke ci haɗe da tea Habib na gutsira yana yi mata santi. "Baby ina son wannan abin. Ya ma sunan shi? Tana dariya ta ce" Naan Bread Noori, amma wannan mai ƙwai ne ba nama ba." Sai ya jinjina kai kafin ya ce" A online clases ɗin ku aka koya miki? Bayansa ta dafa kafin ta ce" Noori na santi." Sai da ya kurɓi tea kafin ya ce" Ba santi ba ne, Allah Baby yana da daɗi, in dai kika yi shi ai ina cewa yana da daɗi ko? "Yes My Noori." Hira suke yi, jefi-jefi ita tea ɗin ma kawai ta ke kurɓa saboda zuciyarta ta ji tana tashi tun da safe, shi ya sa ma ba ta ci ba naan bread ɗin ba. Habib wayarsa ce a hannunsa yana ta dubawa. Lokaci ɗaya kuma yana cin abinci. "Baby." "Naam" "Ashe kuna da biki ban sani ba? Sai ta kalle shi cikin mamaki. "Noori Biki kuma? "Yes" Ya faɗa yana karkata mata wayar ta leƙo da kanta sai ta yi arba da zafafan hotunan Badia'tu yar sarkin Daura. "Ba bikin gidanku ba ne? Ya faɗa  yana sake tura abin da ke hannunsa a baki lokaci ɗaya yana korawa da ruwan tea. "Oh ai fa." Ummu-Salma ta faɗa tana kauda kanta. "Ammah za ta je? "Za ta je mana. Kai ma ka sani" "Mami fa? Itama za ta je? Sai ta kalle shi kafin ta ce. "Kai ma ka san Mami ba za ta je ba." Sai ya jinjina kai yana cigaba da kallon wayarsa kafin ya ce" Baby da kin tambayeni da na bar ki, kin raka Ammah dagaa ganin bikin nan za a sha shagali." "Uhm" Ta faɗa ba tare da ta sake mgana ba. Dariya Habib ya yi kafin ya ce" Am just joking. In kika tafi ni kuma ya za ki yi da ni? Hararan shi ta yi, yana sake yin wata dariyan ya ce. "I love you Baby." Juya masa ido ta yi sannan ta yi masa fari, jinjina kai ya yi kafin ya ce" Ki bari kafin na ce mu shiga daga ciki." Tana jin haka ta yi saurin gyara zama tana faɗin. "Za ka makara fa Noori?. "Ina sane da time fa Baby." Sai ta jinjina kai, ba ta yi mgana saboda cikinta ne ta ji yana juya mata. "Baby." "Noori." Sai da ya kalleta kafin ya ce. "Hamma Lamiɗon to zai je can Daura ɗin ne? "Ban sani ba Noori." "Serous fa? "Allah fa ban sani ba." Ta faɗa tana mai kallon shi. "Ko Ammah ba ta faɗa miki ba.? "Ba ta faɗa mini ba Noori." Ta faɗa cikin gajiya da tambayoyin. "Noori yau kuma Hamma Lamiɗon kake son gani? Ta  faɗa tana kallon shi mirmishi ya yi kafin ya ce" Ba laifi ba ne, kin manta sau ɗaya na taɓa ganin shi, shima daga nesa kafin na karisa ya shige cikin mota." Baki ta taɓe kafin ta ce. "Uhm" "Baby ke dai kawai ki ce jininku bai haɗu ba, kuma saboda kin ƙi karatu ne " Wani kallo ta yi masa da ya sa ya fara dariya kafin ya ce. "Baby gaskiya na faɗa, nima fa ta shafe ni kamar baya sona saboda ke." Kai Ummu-Salma ta girgiza kafin ta ce" Shi wannan yana neman dalilin tsanar mutum ne? in dai haka ne kowa ya tsana kenan." "Me ya sa kika ce haka? "To ban da Ammah wa ke ganin dariyan mutumin nan! Ko Baffa a ginshiƙe yake masa mgana. To bari ka ji ko su Hamma Jibril a takamance yake yi musu mgana, ballanta irin mu ƙananun ƙwari." Habib ya kwashe da dariya ganin yadda matar tashi ta haɗe rai, tissue ya ɗauka yana goge bakin shi kafin ya ce. "Kuma Ammah tafi son shi da ke ba Baby." "Ta fi son shi da kowa ma Noori. Ni ai na bar masa ita na kama Mami na da Umman ikki." Ta faɗa tana juya masa baki, miƙewa ya yi yana faɗin" Baby is time." Itama sai ta mike, bedroom ta koma ta ɗauko masa briefcase ɗin sa ta dawo falon suka rumgume juna sai da ya sumbaci bakin ta kafin ya ce. "Baby take care kin ji ko." "In sha Allahu" Ya hana ta masa rakiya a haraba shi ya sa iyakarta kofar falo ya fita tana ɗaga masa hannu har ta za ta rufe ƙofar sai ga shi ya dawo da sauri yana faɗin. "Baby key ɗin mota ko a kafa kike son na je wajen aikin yau? Sai ta juya da sarssarfa ta koma ciki ta ɗauko masa, bayan ta kawo masa sai da ya sumbaci hannun sannan ya wuce yana faɗin "I love you Baby." "Love you too Noori na." Hannu ya ɗaga mata, itama ta daga masa sannan ta rufe ƙofar. Dinning ɗin ta koma ta zauna domin ba ta ƙoshi ba sauran Naan bread ɗin da Habib ya rage ta ɗauka ta ci guda ɗaya ta hada da ruwan tea, Allah ne ya sota da ta yi amai saboda zuciyarta ta yi ta tashi sai da ta sha ruwa sai ta ji zuciyarta ta kwanta Tunani take yi ko dai ciki gare ta? Sai ta fara tunanin yaushen da rabon da ta ga al'adanta? Tun bayan ɗaukewar jinin nan na ɓarin da ta yi ba ta sake wani jini ba, tsalle ta buga ita kaɗai a falo da gudu ta ruga ɗaki ta dauko wayarta Habib ta so kira sai kuma ta fasa kar ta ɗaga masa hankali. Sai ta mai da alkalan kiran ga Sisna amma ba ta ɗauki wayar ba wata kila ta shiga cikin makaranta ne Sai ta bar mata saƙo. "Albishirin ki. Ina tunanin ina da wani cikin SisNa." Ita kaɗai a gaban madubi tana shafa cikinta tana kallo, farincikinta ya kasa ɓoyuwa wani irin murna Habib zai yi in ya san tana da ciki? Ba ta da tabbaci amma alamominta na kwana biyun nan ya fi kama da na masu juna biyu, sai a lokacin ta kula da nonuwanta sun tasa, kuma da man cikinta na farko kafin ta yi ɓarin shi a Nono ya fara nuna kansa kenan wannan ma anan zai fara bayyana kan shi? Wata zuciyar na faɗa mata kar ta faɗa ma Habib sai ta je asibiti an tabbatar mata sannan sai ta faɗa masa cikin mamakin da tasan murnan da zai yi ba ƙarama ba ce, saboda lokacin da ta yi ɓari ya shiga damuwa sosai har ta dinga mamakin haka yake son haihuwa? Ko da yake in ta yi duba da gidan da ya fito gidan yawa ne shi ya sa zai so shima ya tara yara kamar mahaifinsa. *littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗannan lambobin kamar haka.* 09069067488. 08032773332. *Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.* *Janafty* *Sat, 05. June 2025.* 5:53pm. *Posting on 17/04/2026* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/IF0uPZWtcCOIczsjhdCbIZ?mode=gi_t https://www.arewapen.com/u/jamilaumarjanafty *02* _JIMETA: Zone 3_ *10:30pm.* Alhaji Hadi Baba na zaune a gefen gadon dake cikin turakan shi, wasu takardu ne a hannun shi yake dubawa sanye yake da jallabiya mai ruwan madara, kansa da tsilintsilin furfura wani siririn farin gilashin ne a idanuwansa wanda in zai karanta wani abu yake amfani da shi saboda raunin ganin sa. Sallaman matarsa ne ya katse masa nazarin takardun dake hannunsa, ya ɗago kansa lokaci ɗaya yana mai amsa mata cikakkiyar sallaman kamar yadda ta yi. Dattijo ne mai cikar kamala da haiba, fari ne amma ba shi da haske sosai wataƙila ya yi sirki shekarunsa na haihuwa za su kai 66 amma hutu da jin daɗi sun saka fatarsa da yanayin jikinsa suna ƙaryata shekarunsa mai ɗakin sa yake kallo dai-dai lokacin da ta ƙariso gaban shi. "Baffa ba ka kwanta ba? Ta faɗa da muryanta da ta cakuɗe irin na fulani lokaci ɗaya kuma tana nufar can ƙurar ɗakin in da ta ijiye mganin sauron da ta kunno a hannunta a saman wata kwalba lokaci ɗaya tana sake faɗin" Na manta yau ban yi maka feshin magani ba Baffa." "Sannu da ƙoƙari. Na gode." Ya faɗa da cikin harshen fillanci, dawowa ta yi zuwa gefen shi ta zauna tana kallon shi, itama ita ya kalla amma bai yi mgana ba sai ta fara dariya tana faɗin" Baffa me kuma na yi ni Jamila? Kai ya girgiza kafin ya ce" Ba ki yi komai ba." Agogon da ke sama ta ɗaga kai tana kallo sha ɗaya saura daga nan ta gano laifinta. "Baffa ka san ina da tafiya a gaba na ina can ina ta ƴ'an kimtse-kimtse ne " Ta sake faɗa tana yi masa mirmishi, takardun hannun shi ya adana a cikin dirowan gefen sa, sannan ya mai da hankalin shi a kanta, ba ta damu da jiran amsar shi ba har ta miƙe, farantin kwanukan abincin da ta kawo masa tun bayan dawowarsa ta sumguma tana faɗin" Bari na kai wannan kitchen na dawo Baffa." Daga haka ta sake ficewa shi dai kawai ya bita da kallo yana mai girgiza kai, lokaci ɗaya yana sakin mirmishi. Mintina huɗu sai ga ta ta sake shigowa da sallama wannan karon har sai da ta tura ƙofar daƙin lokaci ɗaya tana cewa" Baffa ko za ka sake fita ne? Sai da ya amsa mata da kai kafin ya amsa mata da baki. "A'a" Ta fara tahowa zuwa gare shi, shi kuma yana kallonta, Jamila (Ammah) ko da shekaru suka tura kyanta da dirin ta bai samu wani tawaya ba, ko yanzu da yake kallonta yana ganin kyawunta na shekaru sama da talatin da auran su, ita ce dai Jamilar da ya aura yarinya yar shekaru sha shidda a lokacin, ita ce wacce Gwaggo ta yi masa auran gata da ita(Allah ya gafarta mata) ita ce kuma a yau uwar zaratan maza ginannu har guda bakwai, uwa kuma ga Muhammad Lamiɗo, kuma uwar Auta Ummu-Salma, har yau hasken fatarta ba ta dishe ba, da ya ke fara ce sosai mahaifiyarta kafin rasuwarta Nenne tsada ake kiranta saboda tsabar jan ta, sannnan kaf ya'yan su jan fatan ta suka ɗauko a kammani ma ta rinjaye shi, duk da mutane da dama sun sha cewa shi da Jamila suna ɗiban kama, tun da su ɗin jini ɗaya ne, wani lokacin Amma ba uwa ce kaɗai a wajen ƴa'ƴan shi ba hatta shi kan shi uwa ce gare shi, in ta rufe shi da faɗa kamar Gwaggo, shi ya sa ya sha cewa Ammah mata ce, ƙawa ce Aminiya ce sannan uwa ce a gare shi da ƴa'ƴan su gabaɗaya. Da yake kuma ya aure ta da ƙananun shekarun a wancan lokaci yanzu ma take cikin shekarunta na hamsin da shidda, babban yaron su Jibo ya zo duniya tana da shekaru goma sha bakwai, sau tari in suka jera da Jibril kamar ƙaninta yake ba ɗanta ba, yadda tserensu yake kamar a jere da juna. Sannan ta mori jikinta ba da ta kiba kuma ba ta da tsawo, gajera ce tsawon da yaran suke ɗaukowa tsawon uban su ne shi Alhaji Hadi Baaba. Sai da ta zauna kusa da shi sannan ya sauke ajiyar zuciya. Ya juyo yana kallonta ita kuma sai ta saka hannu ta zare masa gilashin fuskar shi lokaci ɗaya tana faɗin" Baffa a cire gilashin hakan nan, ko nima sai da shi kake iya ganina tarwai? Dariya ya yi har sai da haƙoran shi suka bayyana a waje. "Ahto Baffa ba amana a ce ba ka gane ni sai ka sanya gilashin ƙara karfin gani." "Ammah ba ki da dama." Ya faɗa da sautin muryan shi ya saba da kiranta Ammah kamar yadda yaran su, suke kiran ta ba ma shi ba kowa yanzu Ammah ne yara da manya. Shi kuma da man ita ce take ce masa Baffa kafin yaran su su tashi da sunan a bakinta. Akwai wata rana da ya shuɗe Saddam na zolayanta da cewa. "Amma wai kema Baffa Baffan ki ne? Dakuwa ta yi masa kafin ta ce. "A'a naka ne mai uba, to ni ce mai Baffan gabaɗaya ku duk yan cikon banci ne." Suna falo ne suna karyawa a wata safiya shi kan shi sai da ya yi dariya da kalamanta Ammah ce, ba ta da dama mace ce mai jajircewa kan mijinta da ƴa'ƴanta mai son zumunci da yaƙana ce, amma kuma ba ta da haƙuri Amma mace ce da ba ta ɗaukan Nonsense  tana da faɗa da zafi, zafin namanta har a jikinta da kazar-kazar ita ce mata ɗaya cal da Alhaji Hadi Baba ya mallaka a matsayin mata anan duniya amma ko yanzu da shekaru suka tura ba ta taɓa jin ta gaza daga hidimta masa ba. Yanzu ɗin ma cewa ta yi ya kwantar da kansa saman filo, ta jawo kafafunsa a saman cinyarta tana matsa masa a hankali cikin kulawa tana faɗin. " Baffa ya kamata ka huta. Kwana biyun nan ba ka samun zama sosai." Sai da ya dan muskuta kafin ya ce" In na zauna gida na huta sauran harkokin nawa wa zai yi mini? "Ka bar ma Baba" "Ban da abin ki ai ko a yanzu shi ke yin harkokin, shima abin a tausaya masa ne ba ya cikakken sati tare da iyalansa." Amma ta jinjina kai kafin ta ce" To shi yanzu jininsa yake Baffa kai kuma jiya ba yau ba, ni dai ka dinga hutawa kar wata rana aga tsoho na ya faɗi." Ta ƙarishe faɗa tana masa dariya da man in tana jin nishaɗi ɗan tsohona take kiran shi, kai ya jinjina kafin ya ce. "Tun da haka kike bukata ai haka za a yi uwar Lamiɗo " Ta sake faɗaɗa mirmishinta ba ta dai ce komai ba tana cigaba da matsa masa kafafuwansa. Idanuwan Baffa na lumshewa domin akwai gajiya a jikinsa Ammah dai sai dai Allah ya yi mata albarka ta san shi fiye da yadda shi ya karance ta. Mubi ya je shi da Abdullahi duk da ba shi ya yi driving ba doguwar tafiya yanzu na bashi wahala ko don shekaru sun tura ne? Shi da a shekaran baya a jihohin Nageria ba in da kafarsa ba ta ka da sunan kasuwanci ba. Kasuwanci ma irin na shi na siyan injinan manyan motoci ƙananu da manya da kuma wasu part-part na jikin mota ya daɗe yana wannan harkan kafin daga baya ya fara sirkawa da harkokin siyar da motoci sanadin haɗuwar shi da Alhaji Isa Ɗanmarke. amma yanzu saboda girma da shekaru in ya yi doguwar tafiya a mota sai ya ji duk ya gaji sauƙi sauƙin ta ma in a jirgi ne. "Saddam ya dawo gidan nan kuwa? Ya tambaya cikin sanyin murya. "Tun ɗazu fa ya dawo muna tare da shi, ya so ma ya jira ka har ka shigo sai ya ce mini kansa na ciwo zai shiga ya sha mgani, wataƙila lokacin da ka shigo ya kwanta ne." "Me ya sa yake jira na? Ya tambaya har lokacin idanuwansa na lumshe. "Gobe ya ce yake so ya koma makaranta." Sai a lokacin ya buɗe idanuwansa kafin ya ce" Gobe kuma? Ya fasa raka ki Dauran ne kuma?. "Aa bai fasa ba ya ce akwai abin da zai yi ne a can, satin da za mu tafi zai dawo." Ɗan miƙar da kansa ya yi yana gyara kwanciyarsa kafin ya ce" Allah ya ba da sa'a." Ta amsa masa da Amin Amin. "Bayan Umman ikki, sai kuma suwa kika shirya tafiyar da su? Ya tambayeta yana kallonta, kai tsaye ta ce" Umma A'i tunda na fara yi ma mgana sai ta ce ba ta nan ɗiyar mijinta ta haihu a kano za su tafi, Umma salamatu kuma kasan ba ta son doguwar tafiya. Yanzu daga ni sai Umma Balki, sai Saddam da Ummin ikki." Kai ya jinjina kafin ya ce"Kun isa ma, Allah ya nuna mana ya sa a yi biki lafiya a gama lafiya." Ta amsa masa da Amin tana cigaba da faɗa masa sun yi waya da Lamiɗo ya ce Abdulrahaman zai siya musu tiket jirgi za su bi zuwa katsina daga nan motocin gidan Mai martaba sarkin Daura suna jiran su za su ɗauke su zuwa masarauta. "Allah ya sa albarka." Ta amsa da Amin kafin ta ce" Baffa ba za ka je ko ɗaurin auran ba? Kai tsaye ya ce" Zai yi wahala. Ban dai sani ba, bari mu gani." Tana jin ya ce haka ta san bai yi niyyar zuwa ba. "Kai Baffa ban san ka da riƙo ba fa. Ai komai ya wuce yanzu mun zama ɗaya silan Lamiɗon mu." Shuru ya yi na wani lokaci ba tare da ya yi mgana ba. Ya manta sannan ya yafe, kara yake yi ma Fatima, shi ya sa bai cika tusa kansa a wannan bangaren ba. Janye kafafunsa ya yi daga cinyar Amma ya sauke a ƙasan cafet ɗin da ke ɗakin. Sannan lokaci ɗaya ya yunƙura ya miƙe zaune yana mai kallon Amma. "Na san zuwan ba zai gagare ka ba, sai dai in Fatima ce ta ce maka kar ka je ko? Baffa Mai martaba fa da kansa ya kira ka ya sanar da kai bikin ɗiyarsa me ya sa ba zaka yi masa kara ba! Sannan Gimbiya Shahida ba ka ga yadda ta ke yawan kirana tana tambayana yaushe za mu taho ba, a ƙalla dai sun nuna mana ƙauna hatta Fulani ta kira ni, ta ce ba ta ɗauke mini zuwa wannan bikin ba." Mirmishin gefen baki ya yi, a cikin ran shi yana faɗin sai yanzu? Da ma ace za su iya mayar da hannun agogo baya wataƙila da sun gyara kuskuren su na baya da Fargar jaji bai kama su a yanzu ba amma a sarari sai ya kalli Amma kafin ya ce" Ni wallahi ban taɓa rike su a raina ba Ammah kin sanni kin san halina. Kawai dai." "Kawai dai me? Ta katse shi tana kallon shi sai ya kasa amsa mata, domin ai ta san amsar tambayar nata. "Fatima ce! Saboda Fatima ce ya sa kake yin wannan baya bayan ko Baffa? Tafaɗa tana sake matsawa gare shi lokaci ɗaya ta tsare shi da kaifaffun idanuwanta masu sanya shi ya yi laushi bai shirya ba. "Baffa don Allah kar ka biye ma wannan ƙanwar taka mai zuciyar rashin yafiya, yadda na sanka mai yi ma zumumci hidima ne. Ko saboda Lamiɗon mu ko sabo da shi, kar ka manta har abada Lamiɗo ɗan mu ne." Ta gama faɗa tana mai riƙo duka hannayensa a cikin nata, ta kuma kafe shi da idanuwanta da ba ya iya mata gaddama in dai ta kafe shi da su. "Za ka je ko Baffa? Ta faɗa har tana kasa-ƙasa da murya. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Za mu je, zan yi ma Abdullahi(Baba) mgana." "Baffa ka yi ma Abdurrahaman mgana ku zo tare da shi." Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce" Shike nan. Da ma kin sani kin yi ma Abdullahi(Baba) mgana ko da matarsa sai ku tafi." Baki ta riƙe bakin ta ce" Na sha'afa wallahi bari zan yi masa mgana na ji." "To Amman Lamiɗo." Tana dariya ta ce"Kai kuma Baffan Lamiɗo ba." Yana y'ar dariya ya ce" Na bar miki, duka matsayin tuntuni. Wannan Lamiɗon naki ai sai ke. Ni fa cikin satin nan da ya doka mini kira cikin dare sai da ya sa jinina ya hau na ɗauka ba lafiya ba ina ɗaukan kiran cikin damuwa na ce" Lamiɗo lafiya cikin daren nan? Buɗar bakinsa sai ce mini ya yi" Baffa me ya sa kake tambaya? Ai da man wannan ne lokacin da na ke kiran ku a waya" Ja'irin yaron nan ko a jikinsa bai ma damu da ɗaga mini hankalin da ya yi ba, muna gama gaisawa ya kashe wayarsa shi ya sa ma ko zan je ba saboda Lamiɗo ba ne sai saboda zumunci da girman mahaifinsa , amma shi Lamiɗo da na samu zuwa da kar na samu zuwa duka ɗaya ne a wajen sa." Amma na dariya Baffa na taya ta, ya ci gaba da faɗin" Ta bakin Fatima ta ce ba zan iya da ɗan Ammah ba shegen faɗin rai. Ta manta jinin dake gudana a jikinshi." Amma na gimtse dariyanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ni fa bana ganin duk abin da ake faɗa akan Lamiɗo, a wajena yafi kowa sauƙin kai." "Uhm da yake ɗan gaban goshin ki ne ai ba kya ganin laifinsa. Gaskiya Fatima ne ke kika bata Lamiɗo ya saba da komai ya yi dai-dai ne a wajen ki." Amma ta dariya ta ce" to ba ta bar mini ɗan ba, babu kuma ruwanta da ni balle rayuwar ɗa na." "Allah ya ba da sa'a." Baffa ya faɗa Amma ta amsa da Amin.. "To iyalan na Lamiɗon za su taho bikin dai ko? Domin shi gogan na san ba zai samu zuwa ba." Amma ta ce" Gaskiya ya ce mini da wuya ya zo suna can ko wata ƙasa ne ma, sunan da wuyar faɗa Baffa, amma ita Balkisu ya ce za su taho tare da yaran gabaɗaya tun da sun samu hutun makaranta." Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Hakan ma ya wadatar. Allah ya nuna mana lokacin." Ta amsa da Amin suna cigaba da tattaunawa har sha biyu saura na dare sannnan suka yi shirin kwanciya sai bayan sun kwanta ne Amma ta ce. "Baffa ka yi mgana da Ummu ne a kwanaki nan? Baffa na daga kwance ya ce" Jiya ta kira ni da safe mun gaisa. Tana lafiya ita da mijinta, shima yau da safe sai da ya kira ni muka gaisa." Amma ta yi kyafci kafin ta ce" Habibu dai ya kira ni da safe amma Ummu ba ta kira ni ba." "To ai kin yi mata faɗa zuwan ta na karshe shi ya sa ba ta kira ki ba." Baffa ya faɗa yana dariya Amma ta kalle shi tana cigaba da faɗin" Au har ta faɗa maka? Munasiran yarinya." "Ki rage yi ma uwata faɗa, kar ki manta ta girma yanzu matar aure ce." "Ai ko duniya ta haifa sai na ci mata in ta yi mini ba dai-dai ba." '"To me ta yi miki kuma? Ammah ta miƙe daga kwancen da take tana faɗin" Zuwa fa ta yi ina mata hiran bikin nan na Daura ta yi banza da ni, shi ne na danƙwashe ta yarinyar nan ta fara mini kukan shagwaɓa wai ita ina ruwanta da bikin da zan ce sai ta saka baki a hiran? Ka ji fa shi ne na fattatake ta na ce kar ta dawo mini gida ta ce wai gidan ai na Baffa ne, na ce ta ci ubanta Baffan ma a ƙarƙashina yake ballanta ita " Kafin ta gama bashi labarin ya fara dariya, Ammah dai ba za ta sauya ba, in tana faɗa da yara sai ka ce ba ita ta haife su ba musamman ma ita da Autar ta Ummi, ba sa zama a inuwa ɗaya yanzu nan lafiya anjuma za a ji su suna tafka tsiya ta fattateketa a gidan tun kafin ta yi aure gidan Ummin ikki take zuwa ta yi ma Amman ya ji sai in ta gaji da kanta take dawowa, ita fa Ammah ba ga ya'yanta ba ko na yan'uwa ne ba ta da sauƙi, jikoki kan sun san sauran in ƴa'yan su Jibo suka zo hutu sun ma san hali ba ruwanta da wasan jika da kaka yanzu sai ta ji ƙaniyar mutum, ba a yi mata wargi in aka dame ta ta kira uban ko uwar ta ce su zo su tattara ƴayan su ta gaji, ita da gidan Baffa ba za a bar ta sake ba. Babar ɗiyar Jibo Sauda wancan hutun da suka zo kafin su koma ta ci dundun Ammah, saboda ba ta jin mgana ga son jiki ita kuma Ammah ba ta shiri da yaro mara kunya da son jiki yanzu za ku samu matsala,  ba su gama cinye hutun ba ta kira Jibo ta ce ya zo ɗauki sangartatun ya'yan shi ba za ta iya ba sun dame ta. Da yake shi ne babba kuma yana aiki ne Airport na Abuja can yake zaune da iyalansa. Baffa ne mai wasa da jikokinsa da ƴa'ƴan sa amma ban da Ammah kana yi mata wasan za ta ma yar da shi na faɗa, ƴaƴan lamido ne kawai jokokin gata a wajenta in suka zo ta rasa ina za ta saka su kamar yadda take yi ma ubansu hidima suma haka take yi musu. Hatta matar Lamiɗo hidima Ammah ke yi mata, ita kuma sanin Amma ce komai na mijin nata sai ta riƙe ta gam, domin yadda take yi ma Amma hidima da kuɗinta ko Mami da ta kawo Hamma Lamiɗo duniya ba ta yi mata haka, to ina ma ta ga fuska Mami ko a fili ko a sarari ba ta taɓa nuna Lamiɗo ɗan ta ba ne, Islam da Faruk sune duniya ta shaida ƴa'ƴanta. Shima bai taɓa nuna wata a matsayin uwa ba bayan Ammah ba Sannan matar Hamma Lamiɗo  ita ɗin yar masu kuɗi ce ɗiyar sarauta ce domin babanta shi ne Sarkin Kano na yanzu, ita kuma likitar mata ne mai zaman kanta, shi ya sa ko su matan Yaya Jibo ba su isa su haɗa kan su da Balkisu ba,  ita ɗin ta musamman ce a wajen Ammah kamar yadda mijin nata yake gangariyan na musamman a wajen Amma. "Ummu ta raina ni Baffa." "Ba ruwana ina shiga zan ji kunya ke da Autar ki." Da sauri Amma ta ce" Ba Auta ta ba ce, Autar Umman ikki ne." Baffa ya sake yin wata dariyan kafin ya ce" Har da ke me, ni na ɗauka har da ita za ki tafi bikin. Na tabbata Habibu ba zai hana ta zuwa ba." Da sauri Amma ta ce" Wallahi ba zan je da ita ba, kawai ta kunya ta ni, ka manta zuwan da na yi da  ita naɗin Sarautan Lamiɗo nan fa na faɗa maka abin da ta yi mini sai da na yi nadamar zuwa da ita, tana ta taɓe taben fuska suna jan ta da mgana sai ta ga dama take amsawa, sannan ta maƙale mini  ta ƙi zuwa ko'ina sai na yi mgana sai ta tura baki ta ce ba ta san kowa ba, wallahi ban ji daɗin zuwan da na yi da ita da man na ce har abada sai dai in ita ta kai kanta ba dai ni ba." Baffa dai na ta dariya bai yi mgana ba. "Ka san ta da shegen iyayin tsiya, ba ta da wayewa a wajen shiga mutane. In da Baɗɗo ta fita kenan da ba domin makarantar ta ba da tare da Baɗɗo zan tafi" Baffa ya gyaɗa kai amma bai yi mgana ba. "Ka dinga yi mata faɗa Baffa in kana so mu shirya da Auta nan ta ka." "Zan yi mata" Ya faɗa yana riƙo hannun Ammah, sai ta kalle shi, shima ita yake kallo waiwayi ya fara mata sai ta fara dariya tana  kiran sunan shi. "Baffa..!!! ***** Jalingo Street. Taa ƙasa faɗa ma Habib canje-canjen da ta ke ji a jikin ta. Tsoron ta kar ta sanya masa rai akan cikin kuma su je a yi gwaji a ga ba shi ba ne, kuma sun yi mgana da Sisna da ta nemi shawaranta sai ta ce kar ta faɗa masa amma ga shawara mai zai hana ta yi gwajin da PT ta fara gani in tabbas akwai cikin? Sai ta aminta da shawaran Baɗɗo, ita ta bar ma alhakin siyo mata PT ɗin da alƙawarin in za ta zo gidan sai ta taho mata da shi, haka kuma aka yi ranar wata Jumma'a daga makarantar da take karatu wato State polytechnic Yola(SPY JIMETA)  ta hayo abin hawa zuwa gidan Ummu. Tare suka yi gwajin har tsinke biyu amma sai ya nuna babu cikin shike nan murnan Ummu ya koma ciki. "SisNa kar ki wani damu, soon in sha Allahu za mu samu wani Baby kin ji ko? Baɗɗo ta faɗa cikin sigan lallashi ganin Ummu ta ɗaga hankalinta. "To amma yanayin da na ke ji a jikina fa SisNa? Baɗɗo ta ce" Wata ƙila gajiya ce kawai ba wani abu ba." Ummu dai duk da ba haka ta so ba amma hakan nan ta haƙura ta cigaba da karɓan lallashi daga wajen yaruwata Aisha(Baɗɗo) wata ƙawarta kwara ɗaya da dangatakar jini bai haɗa su ba amma amincin Amma da Ummi ikki shi ya haifar da wannan kyakyawan dangantar dake tsakaninta da Baɗɗo a yau. Ba sa iya ɓoye ma juna komai, tun suna yara tare suka taso, duk da Ummu ta ɗan girme ma Baɗɗon da shekara ɗaya, amma yadda suka taso suka ga aminci mai ƙarfi a tsakanin iyayensu suma haka suka samar da na su misalin aminci a tsakanin su, duk da ita Ummu tana da wata ƙawar da suke kusanci sosai Shamsiya(Bestie) ita makaranta ce ta haɗa su tun da ga primary har gama babban sakandiri, a yayin da ita Baɗɗo ba ta da wata ƙawa Aminiya kamar Ummu Salma Tare suka yi girkin dare, don Ummu ta hana Baɗɗo tafiya da ta matsa ma sai ta kira Habib a waya ta kai masa ƙaran ta shi kuma ya ce a ba ma Baɗɗo wayar ya yi mata magana da cewa ta tsaya har ya dawo su ci abiinci sai ya ma yar da ita gida tun da itama duk suna cikin garin Jimeta ne a wata anguwa mai suna Nasarawo. Baɗɗo ba ta da yadda za ta yi dole ta zauna da man in dai ta zo gidan Habib da Ummu ke ma yar da ita gida wata rana kuma shi kaɗai, ta daɗe tana yi ma Ummu murna da farincikin samun gwarzo irin Habib, ta daɗe tana sha'awar irama ta yi aure ta tafiyar da mijinta da gidanta kamar da Ummu ke tafiyar da na ta gidan abin sha'awa abin birgewa, sannan abin da ke ƙara sa take ganin girman Habib girmama duk wani ahalin Ummu, son duk wanda take so shi ya sa ita da Shamsiya Habib ke yi musu hidima da jikinsa da aljihunsa saboda kawai sune makusantan Ummu na sosai ɗin da ba wanda ya san tsakanin su. Bayan sun gama girkin Baɗɗo ta gyara gidan tas ta goge ta saka turaren wuta yana tashin ƙamshi, Ummu ta matsa mata sai da ta yi wanka kaya ma ta dage sai ta saka nata taƙi, a cewarta na ta ba su yi datti ba tun da ta ƙwabe su da za su fara girki ta saka wata doguwar rigar Ummu sauƙaƙƙa ta zaman gida. Bayan sun yi sallar mangriba ne Ummu ta yi wanka ta ci ado suka zauna a falo suna kallo suna hira a cikin hiran ne Baɗɗo ke faɗa ma Ummu ranar litini su Ummin ikki da Amma za su wuce Daura. "Au da man  tare da Ummin ikki Ammah za ta tafi? Ummu ta tambaya Baɗɗo ta gyaɗa kai mata kafin ta ce" Ke ma ai kin sani, suna nan suna shiri." Baɗɗo da Ummu suka kwashe da dariya har suna tafawa. "To su Daura za su je ko Abuja? Tun da na ga duka events ɗin na su a Abuja za su yi ɗaurin aure ne kawai a garin Daura fa." Ummu ta tambaya tana  kallon Baɗɗo da dariya a bakin ta. "To ni ina zan sani, kullum dai dai sai Ammah ta kira Ummi a shige ciki a daɗe ana tattaunawa." A tare ma wannan karon suka kwashe da dariya kafin Ummu ta ce" Wa ya ga su Ammah a tawagan uwar Amarya." "Sai ki iya ganin su." Suka sake yin dariya nan Ummu ta fara ba ma Baɗɗo labarin karon su da Amma zuwanta gida na karshe. "Sisna haka fa Ammah ta fitike ta in da take shiga ba ta nan take fita ba wai kawai saboda tana labarin bikin Daura ban tanka ba, shike nan fa ta fara faɗa daga ƙarshe  ta ce na bar mata gida tun da ba gidana ba ne, ki ji ƙarfin hali." Ummu ta ƙarishe faɗa tana, riƙe haba da sigar mamaki. "Amma hoo. Ammah drama Queen." Baɗɗo ta faɗa tana dariya. "Ba wanda Amma ta ƙyale. Hamma Lamiɗo ne kawai ban taɓa ganin ta yi ma faɗa ba." "Ke ko wannan ai ɗan gaban goshi ne." Ummu ta taɓe baki kafin ta ce" Ai ni tun da gabda bikina ya taɓa kiran wayar Amma na ɗauka ya ji ni ce, ina fa mgana ya yi banza da ni daga karshe sai ce mini ya yi wai shi ba ya mgana da mara son makaranta . Ummu ta karishe faɗa hawaye na cika ƙwarmin idanuwanta in ta tuna da cin mutumcin da Hamma Lamiɗo ya yi mata sai ta yi hawaye. "To ke me ya kai ki ɗaga kiran sa? Mutumin da sai ya gan ka ya nuna bai san ka ba, ka gaishe shi yana ji sai ya ga dama zai amsa sai ka ce jinin sarauta hauka ne." Baɗɗo ta faɗa cikin jin takaici domin itama ya taɓa yi mata wulakanci zuwan farko da ya kawo ma Amma matarsa, sai ya kawo ta wajen Ummin ikki, ta shigo falon tana gaishe shi ya yi kamar bai ji ba sai da Ummi ta ce Baɗɗo na gaishe ka sannan hankalinsa na kan wayarsa ya amsa a ɗakune kamar mai ciwon baki da " lafiya" Wannan abin ya yi mata ciwo tana uwar ɗakin Ummin ta ji yana cewa bai gane ta ba lamarin Hamma Lamiɗo bayan jinin sarauta har da wulakanci da ɗagawa ma a cikin shi. "Ban san shi ba ne, saboda lambar ba suna, kuma ni na san sai dare ko asuba yake kiran Amma, in da na san shi ne ai ba zan ɗauka ba, ni da lokacin da maganar aurena da Habib ya taso ya kira Amma a waya yana faɗa wai ya za su biye mini na ƙi karatu na ce aure zan yi ina yarinya da ni ban san komai ba? Da shi da Hamma Kabiru da yake shima irin halin su ɗaya ya zo yana ma Baffa kumfar bakin cewa na yi ƙankanta da aure." Baɗɗo ta kalli Ummu ganin har ta fara hawaye. "Ni yaushe na ce aure na ke so? Ni dai ba na ce ba ne a ƙyale ni bana son cigaba da karatu abin da na san kawai na ce kenan." Sai kawai Ummu ta fashe kuka Baɗɗo da ya ke ta san hali sai ta dafa kafaɗanta tana faɗin" To ke ma ban da abin ki duk wanda ya ji ba ki son karatu ai zai fassara ki da cewa aure kike so ne SisNa" Kafaɗan Baɗɗo ta kai ma duka ita kuma sai ta goje tana dariya . "In kowa bai fahimci halin da na ke ciki ai ke na san za ki fahimce ni. Karatu na daga cikin abin da ke wahalar da ni, tun da ya ke ba ni wahala na yi kuma iya yina na riƙa ganewa na kasa ba gwara na hakura ba, domin ina tsoron na shiga jami'a domin faranta ma su Hamma Kabiru rai kafin na yi nisa a kore ni." Baɗɗo ta kwashe da dariya Ummi na ta ya ta da guntun hawayenta. "Hamma Saddam ya ce sai ya ga wanda zai aure ni ina low class ban ji turanci mai zurfi, sai ko ga shi ya sha mamaki. Ya ga Noori na, wanda kyau dai na fuska da zati bai isa ya nuna masa ba." "Bai isa ba." Baɗɗo ta faɗa tana dariya. "Bestie ta ce tana roƙon Allah ya ba ta miji kamar Habib. Ya so ta kamar yadda yake sona." "Amin." Baɗɗo ta amsa kafin ta ce" Ai Habib miji goma ne, kin gama dacewa SisNa muma Allah ya sa mu da ce irin na ki." "In sha Allahu za ku samu fiye da wanda ya fi Habib ma." "Allah ya sa hakan." Baɗɗo ta sake amsa mata, sannan suka cigaba da hiran su, ana haka sai ga Shamsiya ta kira wayar Ummu sai ta saka ta speaker suna fara mgana Baɗɗo ta kira sunanta. "Bestien SisNa." Tana jin haka ta san Baɗɗo ce domin haka take kiran ta, ita kuma sai ta ce mata Sisna Bestie na. "Wayau kika yi mini Sisna bestie na? Kika taho duba Bestie ba tare da ni ba? Shamsiya ta faɗa daga cikin wayar, Baɗɗo ta ce mata itama fa ta kwana biyu ban leƙo ta ba sai yau fa kin san saboda makaranta mun kusa fara jarabawa. Shamsiya ta ce suma sun kusa farawa shi ya sa amfani da wayar ma sai a hankali. Shamsiya irin yaran nan ne masu ƙoƙari da nacin karatu, kaf gidansu yan boko ne sai kin gama jami'a ko kin kusa gamawa kike da damar fidda mijin aure, ko ba ka son karatu su a gidan su wajibi ne sun ɗauki boko kamar wani zunubi ne in ba ka yi ba. Ita kanta Shamsiyar ɗaliba ce a jami'ar Modibbo Adama University Yola a garin girai can ta ke zama a hostel sai sun samu hutu take zuwa ganin gida. Sun daɗe suna waya suna ta hira, har sai da dawowar Habib ya katse su. Baɗɗo sai da ta kauda idanuwanta, saboda rumgumar da ta gudana tsakanin Habib da Ummu in da a ce ana sabo da tuni ta saba da ganin haka tun bayan auran Ummun da Habib. "Baɗɗon mu." Habib ya faɗa yana yi mata murmishi bayan sun gama oyoyon shi da Ummu. "Noorin mu." Dariya ya yi, domin Habib akwai harka ko yau kuka taɓa haɗuwa da shi sai ka ji kamar ka yi shekara da sanin shi, yana da magana da harka sosai. "Na sa ka ki jirana ko? Bari na yi wanka mu ci abinci sai mu je mu kai Baɗɗon mu gida ko Baby? Ummu ta gyaɗa masa kanta lokaci ɗaya tana mai saukar da kanta a saman kafaɗan sa. A falo suka bar Baɗɗo suka shiga ciki mintina talatin sai ga su sun fito Habib ya yi wanka ya sanya kaya zuwa jallabiya baƙa a dinning suka zauna Ummu ta yi serving ɗin su jalop rice mai salat, sai zoɓo sauran na jiya ne da ta saka a frizer suna ci jefi-jefi suna hira, hiran kuma tsakanin Habib da Baɗɗo ne yawanci kuma akan karatun ta ne. Sai can ne Ummu ta kan sako musu baki ko kuma in ya juya ya sako ta a ciki. Sai wajen tara na dare Habib da Ummu suka tafi kai Baɗɗo gida, da suka isa ƙofar gidan Habib ya ce su shiga ciki su gaisa da Ummu ikki, Ummu ta ce aa suna shiga za ta yi musu faɗa ne. "Mu shiga Baby, ba fa Ammah ba ce." Ya faɗa yana dariya Ummu ta girgiza kai kafin ta ce" Ba ka san su ba ne, daga ita har Amma halin su ɗaya." Ya dage sai da suka shiga cikin gida, matan baban su Baɗɗo Biyu Ummin ikki ce uwargida sai Anty Saratu, suna tsakar gida ne suna hira lokacin da suka shigo Baɗɗo da Ummu Habib kuma ya tsaya a sauro kafin su yi masa iso. "Ke yanzu Ummu kin kyauta ma kan ki kenan? Da tsohon daren nan? Ummin ikki ta fara faɗan ta, itama kamar Amma ne ba su gani su ƙyale. "Ummi Baɗɗo ce ta yi dare Habib ya ce ta jira mu kawo ta gida." "Habib ya ce ko ku kuka ce? Umma ikki ta faɗa tana hararan su, Baɗdo ta kwaso rantsuwa tana faɗin" Wallahi Ummi shi ya ce na jira shi." Wata uwar harara ta maka musu, atare  Ummu da Baɗɗo suka saka dariya  suna kumshe bakin su. "Ja'iran yara kawai, to ina shi Habibun? Waje ku ka baro shi? Jin haka yasa Ummu ta miƙe tana faɗin" Bari na ce ya shigo." Ummin Ikki ta yi ƙaramin tsaki kafin ta ce" Ba ni hijabi na" Hijabin Baɗɗo ta ɗauko mata a cikin ɗaki ta saka ita kuma Anty Saratu da man ta shiga ciki tun bayan da suka gaisa da Ummu da farko. Habib har ƙasa ya duka ya gaishe da Ummin ikki kamar yadda ya saba ta amsa mishi cikin sakewa, ba su daɗe ba suka yi musu Baɗɗo ta raka su har bakin gida nan suka ci karo da Baban su Baɗɗo ya dawo shima faɗan ya fara yi da ya gan su. "Kai Habibu ba za ka daina biye ma shirmanmun yaran nan kuna yawan dare ba ko? Ya faɗa ba wasa a muryan shi Habib a ka bari da kare su Ummu. "To ku yi sauri ku isa gida garin da kamar hadari. Allah ya yi muku albarka." Suka amsa da Amin ya shiga gida, su kuma suka shige motar Habib ta kamfanin Toyata, Baɗɗo na ɗaga musu hannu har suka ɓace daga layin. ***** Ammah da tawagarta ranar litini da safe jirginsu ya ɗaga zuwa katsina. Ummu ma ba ta san tafiyarsu ba sai da ta ga Hamma Sadam na posting ɗin hotunan shi a status a cikin jirgi a first class, shi ne ta tambaye shi ya ce tun safe suna Daura. "Eyye Baffa ne ya biya muku kuɗin jirgin? "Wani Baffa, ai wani kaya sai amale Hamma Lamiɗo ne, na ke faɗa miki a rukunin masu kuɗi muka je katsina. A VIP muka kame, muna sauka kuma ga motocin masarauta da dogarai da yan sanda suna jiran saukan mu, suka kwashe mu da jerin convoy motoci hadaɗɗu, sai ga mu dai a cikin Masarautan Daura." Duk Hamma Saddam ne ya zayyano mata wannan labarin, da man shi nan ya fi ƙwarewa. "Ba shakka. To ina su Ammah yanzu? "Suna can cikin gida ni ina bangaren Hamma Lamiɗo ne nan ake sauke ni, Ummu kin ga masarautar Daura? Kin ga shashen Hamma Lamiɗo? Na rantse da girman Allah ban taɓa ganin tsaruwa da kyau na masarauta kamar yadda na ga tsaruwa irin ta masarautar Daura ba" "Uhm. Na gani." Ta tura masa ganin yana neman ya manta itama fa ta je ta ga komai ba sai ya sake zayyana mata ba. "Yanzu muna tare da Saleem ne ƙanin Hamma Lamiɗo, anjuma za mu je gaida Mai mairtaba Sarki" Ba ta tambaye shi ba amma sai zuba mata labarai yake yi, gajiya ta yi ta katse shi da cewa." kai ma har can Abuja za ka je? Ya dawo mata da amsa da cewa sosai ma a gobe za su tafi tare da tawagar matayen Sarki amarya da tawaganta suna can tun shekaranjiya. "Allah ya ba da sa'a." Ta rubuta mai daga nan ta kashe data, amma bayan awa ɗaya da ta sake kunnawa sai da ta ga saƙon sa "Kin san Mai martaba Sarki na da wani ƙaton gida a garin Abuja acan za mu sauka. Har sai an gama shagulgula sai ranar ɗaurin daure da safe za mu koma Daura." Emojin mirmishi kawai Ummu ta tura masa, ita fa shi yasa ba ta yi mamaki da ta ga Hamma Saddam ya je Jamia yana karantar aikin jarida daman ya fi dacewa da shi, shi fa duk in da ya je sai kowa ya sani posting ne kan posting har da karin bayanai, ranar ya saka status sun fi goma na ƙarshe shi ne wanda ya ɗauka tare da Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Nasiru Muhammad Daura a cikin fadar shi yana zaune kan ƙaraga idanuwansa ne kawai ake iya gani saboda yana cikin naɗi. Caption ɗin da ya saka ne ya sa Ummu kwashewa da dariya. "Allah ya ja zamanin ka ubanmu uban ƙasa, Allah ya ƙara maka lafiya Mai mairtaba Sarkin Daura." Hamma Saddam na da abin ban mamaki, sawa yake yi har bargar dawakai da ya shiga sai da ya yi hoto ya saka, Ummu ta tabbatar da ba za ta yi missing komai na shagalin bikin nan ba, tun da dai Hamma Saddam ya na can ai kamar suna can ne suma.   Sai ranar Jumma'a Habib ya sauke ta gida da safe kafin ya tafi wajen aiki, duk da Ammah ba ta nan amma Baffa na gida bai je ko'ina ba tare suka yi ta hira sai da ya fita zuwa sallar jumma'a, yana fita ba daɗewa matar Hamma Abdurrahaman ta zo ita da yara, Adda Ummu Sulain tare suka yini a gidan har dare, Ummu ta yi ma Baffa tuwo miyar yauƙi, da man da Amma ba ta nan daga gidajen su Hamma Abdullahi ake kawo masa abinci sai misalin tara na dare Habib ya zo ya ɗauki Ummu suka koma gida bayan ta yi guzirin tuwo saboda ɗumamen safe. Lalle ko an sha shagali a garin Abuja, ashe su Ammah duk uwar Amarya ta yi musu anko da man shi ya sa take ta tambayan mutanen da za su zo daga bangaren Ammah. An yi mothers Day su Amma an sha kamfala da mayafi ita da Ummin ikki, Hamma Saddam ya ɗora su a status a ƙasa ya saka "Hamma Lamiɗo mai uwaye biyu." Hoton ya yi kyau, sai da Ummi ta ɗauka itama ta yi status, da wanda aka yi ma Ammah ita kaɗai ta yi shar da ita, ita da ta tashi saka hoton sai ta yi zolaya. "Amman Baffa" Ta saka emojin love da rawa. Baffa kuma ya gani dariya kawai ya yi bai yi mgana ba. Da man Hamman Saddam ya faɗa ma Ummu Amma na ta masa faɗan wai ya yi ya tura ma tsohon ta hotunan ta. Ummu ta yi dariya sosai rayuwar auran Ammah da Baffa rayuwa ce abar burgewa da tsari, ita tana da zafi shi kuma Baffa mai sanyi ne da haƙuri shi ya sa aka zauna lafiya. An yi Dinner na gani na faɗa abu ne masu mulki da sarauta, matan sarakuna sun zo ma uwar Amarya biki, a matsayinta na uwargidan Mai mairtaba Sarkin Daura Gimbiya Shahida, itama ɗiya take ga tsohon wazirin na garin Daura. Sai ga su Ammah a tawagan uwar Amarya suna jera kafaɗa da matan gwamnoni da  sarakuna da matan ƴ'an majilisu har da matar mataimakin shugaban ƙasa, ga matar Gwamnan Jihar Katsina  sannan ga bangaren uwar ango itama da na ta tawagan, matan ministoci da masu faɗa aji a fadar gwammatin tarayya. Ammah sun yi hotuna da uwar Amarya sannan ta yi da Amaryan da ango sai kuma wanda ta yi ita da matar Hamma Lamiɗo Dr. Balkisu Usman Bayero" Su Hamma Saddam an saje cikin ƴaƴan sarakuna da ƴaƴan ministoci shima cikin ɗanyar gezner irin ta masu bikin, sai da Ummu ta yi da gaske ta iya ma gane shi, lalle su Hamma Saddam an samu duniya. Matar Hamma Lamiɗo Ummu ta shagala da kallo, matar nan akwai gayu, yar gayu ce ta bugawa a jarida ga kyau ga ilimi ga gayu, ƴa'ƴan su Biyu mai sunan Maimartaba Nasiru(Sultan) sai mai sunan Amma, Jamila(Beena) wani arnen leshi ne a jikinta da ga gan shi ka ga kuɗi, ankon Dinner ɗin ne amma na ta kalan peach ne na su Amma kuma maroon ne kalan ya yi kyau sannan da mayafin su kalan head ɗin su, Amma da Ummin ikki fa har da makeup aka sha irin light ɗin nan sun fa ba za kafacity. Baɗɗo ta saka su a status ta rubuta. "Capacity iya capacity Amma da Ummin ikki." Babu wanda bai saka su a status ba, har Hamma Jibo, Hamma Kabiru ne ya saka hoton Amma ita kaɗai ya yi caption da cewa. "Ammah uwar Amini Lamiɗo" Ummu na gani sai da ta taɓe baki, duk wannan bidirin da ake yi shi gogan bai san ma ana yi ba. Ba ta da lambarsa , yadda bai taɓa nuna damuwarsa akan rayuwarta ba, itama ba ta damu  dashi ba duk da ko uwa ɗaya ce ta yi musu tarbiya. Har Adda Nauwara matar Hamma Jibo ta je Dinner ɗin ita da su Saudat, tun da suna garin suma sun yi kyau da ya ke Hamma Jibo shima ba daga nan ba ɗan gayu ne sosai, matarsa ma yar gayu ce haka ma ƴaƴan su. In suka zo hutu Jimeta ba sa yin hausa wa junan su yaran su yi ta turanci wata rana da Saudat ta yi ma Ammah mgana da turanci yini ta yi faɗa tana cewa ita za a nuna ma iskanci to ko uban ta nan ya girma ita da Baffa hausa da fillanci suka koya masa ba ta son tsirfa da iyayi, kar a sake yi mata turanci a gida gargaɗi aka yi ma Hamma Jibo da Adda Nauwara, da cewa ba su ko ya ma yara fillanci ba sai wani turanci yaren da ba na su ba. Ammah fa  Ƴa'ƴan Hamma Lamiɗo ba su jin hausa daga uwar har uban da turanci suke yi musu mgana gwara ma Hamma Lamiɗo shi yana yi musu hausa da fillanci wani lokacin amma uwar sai turanci amma har yau ba a ji Amma ta yi faɗa akan haka ba tun da Hamma Lamiɗo ne, shi kuma Hamma Lamiɗo shalele ne a wajen Ammaj ba ya laifi. Ranar da aka yi Dinner sai wajen ɗaya na dare Ummu ta kwanta Habib ya gaji da jiranta ya kwanta ta kafa ta tsare tana kallon abin da ke kwana a garin Abuja a wani ƙayattacen hall, an sha Dinner sai wanda ya je ya gani su ɗin ma dake gida sun gamsu da Dinner ɗin ta masu mulki da sarauta ne. Maƙawan arewa sun hallarta kowanne mawaƙi ya baje na shi kolin, irin su Ali jita, Naziru sarkin waƙa, Nazifi Asnanic, Auta MgBoy, Auta waziri, Salim smart, Ɗan musa da sauran su ko wanne da irin karin waƙar shi ga amarya da ango sun kuma sha kuɗi, domin miliyoyi ne ke tashi da dollars, wannan daren dai Dinner ɗin ce ta dinga trending a kafafen sada zumunta ita dai ko alama bata nuna ma tana da alaqa da masu bikin ba. Sai washegarin ranar asabar aka ɗaura aure a masarautar Daura, Hamma Kabiru ya saka hoton Hamma Lamiɗo. Sai da Ummu ta kau  da wayar daga fuskarta saboda tsoratar da ta yi, sanye yake da uniform ɗin su na matuƙan jirgin ruwa Farar riga da baƙin wando fuskar shi ce ta ba ta tsoro, ta yi gargasa gemunsa ya yi kamu uku, kansa gashi ya cika ya yi yawa babu kyan gani. "Amini a bakin aiki." Haka Hamma Kabiru ya saka, sai da ta je hoton gaba sai ta ga ya saka wanda ya yi gyaran fuska ya rage gashin fuskar da na sumar kan amma ba sosai ba. "Amini ya yi gyaran fuska." Wataƙila Hamma Kabiru ne ke wahalar posting ɗin Hamma lamiɗo, shi ko ba ta da tabbacin yana saka shi, duk dai kowa ya shaida akwai aminci a tsakaninsu fiye da kowa ma, Hamma Lamiɗo mutum ne da bai cika bayyana ƙarfin alaqar sa da ko ma waye a zahiri ba, fuskar shi ba ta fallasa sirrin zuciyarsa. Kullum a ginshiƙe za ka gan shi,  fuskar nan kamar yana cikin wani damuwa a kame in ma ka samu ganin shi kenan, mutumin da a shekara bai wuce sau ɗaya yake zuwa ganin gida ba. Duk da yana da tamƙamemen gida anan garin Jimeta, sai ya yi rabin shekara a rufe wani lokacin a shekara sau ɗaya yake zuwa in an yi wani abu ne sau biyu sai dai yana yin sama da wata a Jimeta in ya samu hutun karshen shekara wani lokacin shi kaɗai ya ke tahowa matar tashi sai aiki ya yi mata sauƙi sai ta biyo shi ita da yara, daga nan ne suka wucewa Daura can ma wani alkarya guda ne da sunan bangaren Hamma Lamiɗo. Aikin su na yana da tsauri, Captain ne shi ma'ana matuƙin jirgin ruwa ne. CAPTAIN M.N. MUHAMMAD. Yana aiki da kamfanin Nigerian port Authority jiragen dake jigilan mutane da kayan masarufi shi ya sa suke daɗewa a saman ruwa Babu ƙasar da ba sa zuwa ta kogi sai su yi wattani sama da shidda a saman ruwa ba su shigo gari ba, sun fi ma saurin dawowa gida in sun ɗauko kayan masarufi. Shi ya sa suma kan cika fuskar shi wani lokacin sai sun zo bakin gabar wani garin ne suke samun damar yin wani abu, hutu ko bai wuce na awanni huɗu ba ka ci abinci ka kwanta kana tashi ka koma bakin aiki, sau tari shi ya sa ba ya kiran waya da rana sai cikin dare ko asuba, wani lokacin ma sai a yi kwanaki ba a samu wayar sa ba. *littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗannan lambobin kamar haka.* 09069067488. 08032773332. *Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.* *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/BxcTrVcz7GoIDzbqZTpIxF?mode=gi_t *03* Daga Daura bayan an gama ɗaura aure Abuja aka sake dawo da Amarya tunda anan ne ƙayattace gidanta yake a cikin jerin gidajen masu kumbar susa da faɗa a aji a ƙasar gabaɗaya. A ranar aka yi buɗar kan Amarya a gidan iyayen ango, tab an yi ɓarin miloyoyi wajen buɗan kan Amarya kamar kuɗi ba matsala ba ne a wajen su,  shi kan shi Ango dangin Amarya sun fanshe shi da miloyoyi, Matar Hamma Lamiɗo miliyan biyu ta fanshi kan Ango a madadin ita da Mijinta Yariman Daura, Muhammad Nasiru Muhammad Daura(Lamiɗo). MC da aka gayyato domin gabatar da program ɗin ta kacame da guɗa tana yi ma Balkisu kirari. "Takawarki lafiya Uwargida kuma Amarya a gidan Yariman Daura. Muhammad Lamiɗo ke ya zaɓa ke ma shi kika zaɓa, ɗiyar masu sarauta kike kuma Yariman daura ne mijin ki, sannu ƴar sarki matar ɗan sarki, uban ki sarki mijin ki ma zai yi sarki in sha Allahu, kuma za ki haifi Sarki da ikon Allah Sannu likita bokan turai, uwar Sultan kike sannan ke ce kika haifi Beena. Na gaishe da sarauniya Balkisu, na gaishe da Matar Yariman Daura takwarki lafiya Gimbiya Balkisu Zinariya." Sai dai kawai aka ga ta saƙa ma MC ɗin kuɗi a hannunta waje ya ɗau tafi Ummu ranar ba abin da ta yi sai faman bin shagulgulan bikin nan, matar nan ta Hamma Lamiɗo hadaɗɗiya ce ranar ma shigar lafaya ta yi, ta saka wani material gangariya daga ganin shi ya ba ma wasu nairori baya. Tabbas ta cancanta domin zinariya ce. Duk da Hamma Lamiɗo ba gwanin ta ba ne, ita ma matar tashi wata doguwar mu'amala ba ta taɓa haɗa su ba, amma dai ita a karan kanta tana yin matar saboda yar gayu ce mai kyau ce mai kama da model ce, ga ƴaƴan su farare gwanin ban shawa'a in ka ga rayuwar wasu sai ka yi tunanin wataƙila su suka zaɓa ma kansu, to komai na rayuwa na duniya sun same shi a hannu, suna yadda suka ga dama da shi. Ita kanta irin mijinta ne ba ta samun zama, a ƙiyasin kirgin Ummu Salma sau biyu Dr Balkisu ta taɓa zuwa gidan su zuwa na musamman da ta kwana fiye da ɗaya. Akwai zuwan da ta yi bayan auran su da Hamma Lamiɗo, to bayan shi ta yi biyu haihuwan matar Hamma Kabiru da yake wannan Aminin shi ne ta zo, sai wani zazzaɓi da Ammah ta yi mai zafi har ta fara sambatu hankula sun tashi, kowa ya ɗauka Ammah lokaci ya yi ashe zafin ciwo ne, suna Abuja lokacin kafin ta koma Lagos da zama ta zo duba Ammah, a lokacin Sultan na ƙarami to bayan shi Yanzu daga baya tana biyo shi in ya zo hutun karshen shekara, tunda sai ya fara sauka a Jimeta ya gama kwanakin sa a nan suke wucewa Daura. Daga ita har mijin nata suna yin wuyar gani, hutun na shi kuma a shekara sau ɗaya ne, in salla ne ma baya daɗewa za su fara sauka nan Jimeta su yi kwana biyu daga nan su wuce Daura saboda wasan hawan salla akwai ma sallolin da aka yi yana can bakin aiki bai ma samu zuwa ba. Duk da itama tana da halin ɗagawa da ji da kai bai damu Ummu ba, ita dai bata ba ta haushi sannan tana burgeta ,hankalin ta bai kwanta ba sai da aka gama shagulgulan bikin nan sannan ta bari waya ta huta daga hannunta ta samu ta kira Ammah a waya ta gaisheta sama sama ma suka yi mgana tana cikin hayaniya ta ce za ta kirata ba kuma ba ta kira tan ba. Sai ta kudirta cewa in Ammah suka dawo za ta je har gida ta yi mata sannu da zuwa. **** *NO. 224 NDC QUATERS. KADUNA NAGERIA.* *9:47AM* Da sassarfa take sauko wa daga kafar bene lokaci ɗaya hankalinta na kan agogon I.wacth ɗin dake maƙale a tsitsiyan hannun ta na hagu,  lokaci take dubawa domin tana da aji ƙarfe goma da rabi na safiya yau ɗin nan Falon ƙasa ta sauƙo da yake shuru ba ka jin motsin kowa, farar mace ce doguwa mai ɗan kaurin jiki, tana sanye da wata gold ɗin atamfa mai ruwan ganye shi yasa mayafin jikinta ma da takalminta haɗe da jakan dake hannunta masu kalan ruwan ganye ne. Hannayenta da zobban gold guda biyu da a warwaro suna ƙyalli, haka wuyan ta wani ɗan kunnen gold ne da sarƙan shi mai kyau da yarari. A ƙiyasin shekarunta ba za ta wuce 52 ba sannan ba za ta gaza ba, amma a kallon farko za ka fahimci mace ce mai ilimi da gayu. Sake duba lokaci ta yi, kafin ta ɗago kanta tana sake nazarin ƙayattacen falon mai kama da aljanar duniya. Falon babba ne domin saitin kujeru ne sama da guda huɗu saboda tsabar girman falon. Zama ta yi kan ɗaya daga cikin kujerun falon lokaci ɗaya tana sauke jakar hannunta daga gefenta. "Baraka." "Baraka." Ta shiga kiran ta wacce aka kira da Baraka, da fito da sauri daga wani koridon dake yamma, matashiya ce domin ba za ta wuce 20's ba har gabanta ta ƙariso ta durkusa lokaci ɗaya tana faɗin. "Barka da fitowa Mami." "Kin tashi lafiya Baraka? Ta amsa mata, muryanta da ɗan asset na fillanci, lokaci ɗaya tana ciro wayarta daga cikin jakar dake gefenta. "Lafiya lau Mami." Jinjina kai ta yi kafin ta ce" Kin gama gyara ko'ina ko? "Na gama Mami, saura na kitchen ne kawai." "Da kyau Baraka shi ya sa nake son ki saboda zafin naman ki." Dariya ta yi kanta na ƙasa itama Mamin murmusawa ta yi kafin ta ce" Yau na ga mutumin naki bai yi rigiman tafiya makaranta ba" "Bai yi ba Mami, na lallashe shi da cewa zan goya sa in ya dawo." Mami ta yi dariya har haƙoranta suka bayyana farare, da haƙoran makka a bakinta. "Baraka ina ta ya Faruk kewa ranar da Iya tace a maida ke gida." Baraka sai ta dukar da kai ba ta yi mgana ba Mami na ta dariya kunya take ji domin an saka ranar auranta karshen shekara nan za su ma yar da ita gida, daga can garin megidanta suka ɗauko ta Ɗan marke, ta fi shekaru biyar tare tasu tun ba ta kai haka girma ba. Miƙewa ta yi, kafin ta ɗau jakarta Baraka ta yi saurin riga ta ɗauka lokaci ɗaya tana faɗin" Mami ba ki karya ba za ki fita? "Sai na dawo Baraka." Sai ta jinjina mata kai, suna tafe har habaran gidan makeke mai cike da motoci ga su nan kala kala sun kai guda biyar,  duka na kamfanin Toyota ita ma wata fara ta nufa camry da ita za ta fita yau, jakarta ta karɓa lokaci ɗaya tana cewa. "Baraka ki kula da gidan sai na dawo." Sai ta jinjina kai kafin ta ce" To Mami Allah ya dawo dake lafiya." Lokaci ɗaya tana mai ɗan ramƙwafawa alamun ladabi, tana ƙoƙarin buɗe mota wani matashi ya rugo da gudu ya zo ya buɗe mata. "Barka da Safiya Mami." Sai da ta shiga cikin motar ta zauna sannan ta amsa masa. "Ka tashi lafiya Hamisu? Ya amsa cikin ladabi kafin ya ce" Lafiya lau Mami.. za a fita ne? Allah ya tsare ki ya sa ki dawo lafiya." Mami na mirmishi ta amsa kafin ta ce" Ba wata matsala ko Hamisu? Yana sosa kai ya ce"Hajiya Baraka ba ta ba ni abin karyawa ba goma ta kusa ta san ni mutumin kauye ne da wuri na ke karyawa amma Baraka sai sha biyu na rana take kawo mini abin karyawa fisabillahi fa Mami." Kafin ya dire maganarsa ya fara sha harara wajen Baraka, Mami tana ta dariya diraman Hamisu da Baraka. Kuma duka daga gari ɗaya suke Abban islam ne ya ɗauko Hamisu yana kai yara makaranta sai ɗan aike-aike da kula da fulawoyin gida. "In ka matsu sai ka shiga ka dafa." Baraka ta faɗa sannan ta yi tsaki ta kama hanyar komawa cikin gida. "Mami kina dai jin ta dai ko? Mami na dariya haƙoranta a waje kafin ta ce" Na ji ta Hamisu ƙyale ta." Jakarta dake kan kujeran mai zaman banza ta buɗe ta ɗauko masa 5k yan dubu dubu ta miƙa masa ya rankwafa ya karɓa. "Ka siya wani abu ka ci, ka rabu da ita lokacin da ta kawo maka sai ka ƙara" Washe baki ya yi kafin ya ce" Na gode Mami, Allah ya tsare gaban ki da bayan ki. Allah ya raya miki yaran ki cikin aminci, yadda kika ɗauke mu da mutumci kina saka mana da dukkan alheri ke ma Allah ya saka miki da alheri." Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" To sai na dawo Hamisu." "A dawo lafiya Mami Allah ya tsare." Ya rufe mata ƙofar motar ya ruga da gudu wajen Sunusi maigadi, itama sai ta kunna motar ta yi riverse ta dumfari get tana zuwa da man Sunusu ya buɗe mata sai ta tsaya ta ɗan sauke gilashi bangarenta suka gaisa cike da mumtatawa. "Sunusi ina sane da mganar mu. Jibi Abban islam zai dawo za mu yi mgana da shi in sha Allahu." Ya jinjina kai kafin ya amsa" Allah ya dawo da shi lafiya Hajiya. Na gode sosai da karamcin ki." Kai ta gyaɗa masa kafin ta ce" Ba komai, sai na dawo" "Allah ya tsare ki Hajiya." Ta zuge gilashin sannan ta taka mota ta fice shi kuma ya rufe get ɗin ya koma saman farar kujeran da ya tashi kusa da Hamisu suka cigaba da hiran su, kuma duk na yabon kyawawan hallayan Mami ne na kirki. Sannu sannu tana ta tafiya har zuwa cikin garin kaduna, daga nan ta ɗauke hanyar jami'ar ta Kaduna, Kaduna state University KASU.  In da anan take koyarwa a Department ɗin Biology. Har cikin department ɗin su ta shiga da motar ta, ta yi parking ɗin ta in da aka tanada domin parking ɗin motoci, tana ƙoƙarin fitowa daga motar ne ta ji wayarta dake jikin jaka ta ɗan yi ƙara alamun an tura mata saƙo da kamar ba za ta duba ba, saboda ita saƙonni ma sun isheta a waya ba ta dubawa gwara mutum ya kirata da ya yi mata saƙo. Jakarta ta jawo ta ɗauko wayar na ta iphone 14 ce, tana dannawa haske ya kawo sai ta ga saƙo ne daga My First Daughter, sai da ta murmusa ta manta yau Jumma'a da man ƙa'ida ne duk ranar irin ta yau Ummu Salma tana tura mata saƙon barka da Jumma'a kuma tana jin daɗi sosai. "Barka da Jumma'a Mami na. Allah ya tsare ki da tsarewarsa. Allah ya ba ki abin da kike nema duniya da lahira. Ubangiji ya yi ma rayuwarki albarka. Happy Jumma'at mubarak."    Har ta gama karantawa da mirmishi a saman fuskarta, latsa lambar Ummu ta yi, jiya da daddare ta so kiranta sai ta sha'afa gwara ta kira ta yanzu kar ta sake mantawa. Ringing ɗaya zuwa biyu Ummu-Salma daga can garin Jemeta ta ɗaga kiran. "Mami na" Ta faɗa daga can bangaren cikin murna da bayyana har a muryanta. "Naam Daughter kuna lafiya? Ummu ta amsa mata, suka gaisa daga can bangaren Ummu ta ce" Mami na ina su Islam? "Suna makaranta." "Yaushe za su zo? "Sai sun samu hutu za mu taho gabaɗaya Daughter." Daga can bangaren Ummu ta yi tsalle kafin ta ce" Mami na da man na yi kewar ki." "Nima na yi kewar ɗiya ta." Habib ta tambaye ta sai ta amsa mata da cewa ya tafi wajen aiki. "Ki gaishe mini da shi." "In sha Allahu Mami na." "Daughter na siya miki kayan measurement ɗin fulawa, har spicess na kayan girki suna nan in zan taho zan taho miki da su in sha Allahu." "Na gode Mami na. Allah ya saka miki da alheri." Ta faɗa muryanta cike da murna, Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" Take care na shigo cikin makaranta ne "To Mami Allah ya ba ki sa'a." Daga nan suka yi sallama. Tana shirin mai da wayar cikin jaka ne, sai kuma ta fasa saboda wajen messages ɗin ta 99 ta gani alamun tana da saƙonni da yawa nufinta ta shiga ta yi delete all, duk MTN ne sai na bankun nan ta, amma sai me tana shiga sai ta bige da ɗan dubawa, tana ɗan jan ƙasa ta ga wata lamba ta turo mata saƙo, yanayin lambar ne ya sa dole ta shiga saƙon domin special number ce. "Za a yi auran ɗiyarki Batula. Ko ba ki zo dan ni ba ki zo don Lamiɗo, in shi ma ba za ki zo domin shi ba to ki zo domin gudan jinin da Allah ya haɗa a tsakanina da ke. " Na farko kenan na biyu kuma cewa aka yi. "Tun da ba za ki samu zuwa ba Batula ba, ko yaran mu ki bar su su zo don Allah Batula." Ko bai saka sunan shi ba,  ko bai ambaci wata magana da za ta nuna shi ɗin ba ne, to shi ne domin nan duniya mutum ɗaya ne ke kiranta Batula ko Baffa Fatima ya ke kiranta, tuni fara'an dake saman fuskarta ya gushe cikin lokaci ƙalilan fuskarta ta sauya ta yi wani ja saboda bacin rai. Hannunta na rawa ta goge saƙon gabaɗaya daga wayarta. Tana mamakin yadda aka yi ya same ta? Ita dai ta san ta rufe duka layukan da ya ke kiran ta da su, sai daga baya ta duba sai ta fahimci ya sauya wata lambar ne me ya rage tsakanin su? Ɗan shi ne kuma ba ya tare da ita, yana tare da shi me ya sa ita ba zai ƙyale ta ba? Ta ce ta yafe masa amma ba za ta bari mu'amalan wai Uba da uwa ta haɗa su ba.  Tana da miji shima yana da matan shi, ɗan shi kuma ya san in da yake ba to bini-binin na mene ne? Ita fa har abada ba za ta yi wani aminci da su ba, babu sauran wani aminci har abada atsakanin su.   Sai yanzu ne ya san da gudun jinin da ya haɗa su? Sai yanzu?  Ai lokaci ya kure musu, kurewan da ba za su iya gyara abin da suka lalata shi sama da shekaru talatin ba. Sai yanzu ne Fargar jaji ya kama su? Ba su da sauran abin da za su iya yi a yanzu, gabɗaya ta rasa natsuwarta in ta fita a haka ma ta je aji  ɗalibai za su fahimci yanayin ta ba daɗi shi ya sa ta yi zamanta cikin mota tana faman sauke ajiyar zuciya. Wai saboda Lamiɗo! Waye wani Lamiɗo! A lokacin da ya ke zanin goyo da jinin haihuwa a jikinshi da ba a samu damar wanke shi ba, mahaifiyar shi ba ta duba Lamiɗon a lokacin ba, ba ta duba shi ba ta saka ya yi ma rayuwarta mummuman taɓon da har ta koma ga Allah ba za ta taɓa mantawa ba. Shi kuma ya aiwatar da Umarnin mahaifiyarsa saboda kare martaban masarautar su me ta aika ta? Wani laifi ta aikata da za a sake ta a lokacin da zufan naguda bai gama safka daga jikinta ba? Saboda ita ba yar masu kuɗi ba ce, saboda ita ubanta ba sarki ba ne, tuna haka kawai in ta yi sai ta ji yanayin ta cikin kuka, yanzu ma hawaye ne suka kece mata, shi ya sa har abada ta tsani duk wani abu da ya shafi Sarauta daga kowani bangare ne, abin da ta sani su ɗin masu son kan su ne marasa adalci abin da suka yi mata ya munin da har abada ba ta fatan kafarta ta sake takawa Daura, tun bayan fitar ta ɗauke da jinin haihuwar dake jikinta ta yi alƙawarin ita da wannan garin har abada. Duk da ko da har gobe akwai dangin mahaifiyarsu a garin ba ta taɓa jin marmarin sake saka kafarta a cikin sa ba, domin a cikin sa ta samu farinciki amma kuma ya gurɓata da baƙincikin rayuwarta duk farincikin da rayuwarta da ta ke ciki yanzu da ta tuna da rayuwarta ta baya sai ta ji komai na duniya ya yi mata ƙunci. In tana tuna wahalar da ta sha, deperession ne ya nemi kama ta, Allah ya saka ma Baffa da Ammah da alheri sune suka zama silar da ta zama Fatima a yau, in ta kalli rayuwarta yanzu sai ta ji ba za ta iya saka ma Baffa da Ammah ba domin sun yi mata komai anan duniya. Ammah kuma ita ce ta sakar ma ɗan ta, ita ce ta yi wahala da shi, shi ya sa nan duniya kowa ya shaida Lamiɗo ba shi da wata uwa sama da Ammah itama ta shaida haka, yadda ta wahala da Kabiru haka ta wahala da Lamiɗo, kawai ita mahaifiyarsa ce a haihuwa, Ammah kuma uwa ce a gare shi da ta sadaukar da duka rayuwanta wajen kula da shi. Hawayenta take sharewa, tana jin sanyi a cikin ranta tunda tun a duniya Fulani ta ga sakamakon ta, domin sai da ta zo ta roƙe ta gafara akan abin da ta yi mata sannan ɗan da ta guda tun yana cikin jinin haihuwa shine Sanyin idaniyar masauratar Dauran da suke taƙama da shi, ko a haka aka tsaya sun ga sakamako mai kyau, su ƴa'ƴan sarakunan da ta aura masa ba su iya ba ta abin da take so ba, dole dai sai ita ita ɗin da ba ƴar kowa ba ita ce ta sama mata abin da take muradi, to a haka aka tsaya ita Fatima ta yi nasara. Tissue ta zaro daga cikin motarta ta goge fuskarta a fili ta furta" Allah ya jiƙan ka da Rahama Abba. Marigayi tsohon Sarkin Daura Muhammad Shitu Daura." Tana tuna yadda ya ƙauna ce ta wata ƙila da yana raye da an yi mata adalci. Shi ne ya ce in ta haifi namiji sunan yaro Muhammad Lamiɗo in mace ce kuma Ummu-Kursum shi ya sa lokacin da ta iso Jimeta ta ce ma Baffa ya yi ma jaririn huɗuba da Muhammad Lamiɗo, ko ba ya raye za ta saka masa da ƙaunar da ya nuna mata wajen cika wasiyyarsa. Ita ce za ta ba da labarin mutuwa mai tonon asiri domin mutuwa ce ta yi sanadiyar tonuwar asirinta, ta yi sillar gurbata rayuwar farincikinta zuwa baƙin ciki, ta wani bangaren kuma hakan ya yi sillar sauya rayuwarta daga wannan Fatimar yar mubi bafullatan ƙauye mara ilimi zuwa wata Fatima ta dabam da ta samu cigaban rayuwa ta ƙo'ina. Tabbas ta wannan bangaren za ta gode musu domin sun ma yar da rayuwarta yadda ba taɓa tunanin komawa ba. Kimtsa kanta ta yi, gilashinta ta fiddo a cikin jaka ta saka saboda kauda idanuwan mutane a kanta bayan ta duba madubin motar ta ga idanuwanta sun yi jajir, sannan ta ɗau jakarta ta fito daga cikin motar ta yi amfani da key ɗin ta rufe motar. Tana fara takawa zuwa office ɗin ta daliɓan da take ɗauka yan level 1 suna ta gaishe ta ita kuma tana amsawa cikin sakewa daliɓai suna son ta saboda tana da sauƙin kai da taimako har malaman ma sun san Dr Fatima Baba wajen karamci da kyautatama duk wanda take tare da shi. **** Su Ammah sai da suka yi kwana goma sha ɗaya sannan suka dawo, washegari Ummu-Salma ta je yi mata sannu da dawowa. Ta iske kayan biki niƙi-niƙi ga su nan a ɗakin Ammah har da bag da aka raba mai ƙaton hoton Amarya a ciki ake saka atamfa mai kyau da mayafi har da turaruka, ga kayan su fulawa tun da ta zo Ammah ke ba ta labarin abin da ya faru a wajen bikin nan, Hamma Sadam ma ba a bar shi a baya ba shima yana ɗorawa da na shi, su Ammah fa kaya suka dawo da shi niƙi niƙi ita da Ummin ikki, bayan kala ukun da aka yi musu Fulani ta ba su turame goma da dubu 200k Maimartaba Sarki ya ba su naira dubu 500k tukwaici Gimbiya Shahida ma da turamen zannuwa 20 da kuɗi har shaddodi aka ba da aka wo ma Baffa sun je ɗaurin auran amma tare da Hamma Abdullahi, Hamma Abdulrahaman bai samu zuwa ba, shi kan shi Hamma Sadam shaddoji sun fi kala biyar sabbi gezner masu tsada da takalma haɗe da hulana da ya dawo da su, cikin jin daɗi suke ba da labarin zuwan su Daura da man haka ne in dai Ammah ta je to haka za a rako ta da kayan arziƙi niƙi-niki Ammah kuma ta shiga rabo gidajen yan'uwa da Dangi, har can Mubi saƙon na iske musu. Ta ciccire ma su Umma Balki na su kason, da matan su Baffa Umaru. Duk da ba ta samu zuwa ba tare da na Umma Salamatu da Umman A'i, Hamma Sadam ne zai je ya kai musu gobe, jibi zai koma makaranta. Sannan ta ɗibar ma matan su Hamma Abdullahi, ita dai Adda Nauwara an ba ta na ta acan, amma na su Hamma Kabiru da Mustapha Amma ta ajiye musu abin biki, ita kanta Ummu da ta je an ba ta jaka da kayan fulawa sai turare. Sannan ta karɓan ma Baɗɗo itama. "Amma na Bestie fa? Amma ta ce za ta ijiye mata in ta zo da kanta sai ta ba ta. Ummu tura baki ta yi kafin ta ce" Amma ni zan ci ne? Zan ajiye mata ne tana can makaranta sun kusa farawa jarabawa." Amma ta ce Allah ya sa a yi cikin sa'a amma ba za ta ba yar ba. "To na Noori na Ammah." Ummu ta faɗa, Amma ta yi mata wani kallo kafin ta ce" Waye kuma haka? Ummu na dariya ta ce" Kai Amma Habib ɗin ne ba ki san sunan shi Noori ba? Ammah ta aika mata da daƙuwa kafin ta ce" ƙaniyar ki Ummu Salma." Sai ta fara dariya ƙarshen ta dai sai da Amma ta ba da nashi shima tana cewa" Ya kira ni ina can ya gaishe ni, ya cancanci ya samu tsaraban Daura." Saboda tana so ta tsokani Ammah ya sa ta sake cewa " Amma to ina na Mami na? Na ga ba ki cire mata ba ne" Wannan karon sai da aka wurgeta da mafici sannan aka ce" Mamiyo, in tana son tsaraban me ya hana ta je da kanta? Uwar nan taki zuciyarta ba ta da kyau ko a waya ba ta kira ni ba, nima ko na ce ba zan kira ta ba ina nan za ta zo ta same ni." Ummu ta gyara zama tana faɗin" Ammah to suma sauran da kika ba su ai ba su je ba." Ta gama faɗa tana tura baki. Amma ta miƙe ta fice tana faɗin" Ba zan ba yar ba, na ƙarfi ne ki ƙwatan mata mai uwa." Ta fita ta bar Ummu na dariya da man ta san ba za ta ajiye mata ba amma ta yi son kai za ta aika da shi Mubi, ita Mami ko oho. Ummu har dare tana gidan, labari kam sai da ta gaji da shi, Hamma Lamiɗo dai bai zo ba wai yana cikin aiki, matar shi ce dai ta samu zuwa da yaran shi itama Ammah ta ce ana gama biki daga Abuja ta hau jirgi ta koma Lagos saboda aikinta. Da man Baffa baya nan ko da Ammah ta dawo ya je kwatano Habib ya zo ya ɗauki Ummu da yamma, daga nan suka ƙarisa gidan iyayen shi dake anguwar Doubeli, Baban Habib ya tsufa yana zaune ma ba ya iya tafiya mahaifiyar Habib ce ta rasu, amma akwai sauran mata uku a cikin gida. Suna da yawa wasu duk sun yi aure mata da mazan wasu kuma yanzu suke tasowa. Da ya ke lokacin da aka yi ma Ummu buɗar kai(Fansa) akwai sunan da suka sanya mata bisa al'ada Tafisu da shi duka ahalin Habib suke kiranta da shi, shi ya sa in dai ta shiga cikin su ba sunan ta Ummu Salma ba, sunan ta Tafisu nan suka yi dare sai wajen tara na dare suka koma gida. Duk kuma gajiyar nan da Ummu Salma ta kwaso bai saka Habib ya ɗaga mata ƙafa ba, har mamakin shi take yi ba ya gajiya, in har Habib bai kusanceta ba sai dai in tana jinin haila ne, shima ɗin saboda ba shi da yadda zai yi ne ammaa kafin ta samu tsarki duka gabban jikinta sai sun koma suna raɗaɗi saboda yadda suke shan yamutsa ba ya barin ta sukuni ko kaɗan shi ya sa har yau ta saka kumarin nan na masu aure ga shi sun kwarari wattani takwas da yin aure, ko lokacin da ta samu ciki da ga samanta ne kawai ta yi kiɓa amma ban da jikinta, irin yadda Habib ke matsa mata lamba ba lalle ta yi  kumari ba, abu kamar cin tuwo ba ya gajiya. Kuma har lokacin tana jin wannan sauye-sauyen a jikinta amma tun da ta yi gwaji ta ga ba haka ba ne sai ba ta saka ma kanta tunanin komai ba. Ta fi danganta hakan da rashin hutun da Habib ba ya bari gangar jikinta ya samu shi ne dalili. Abin da ba ta sani ba shi ne tana da shigar ciki. Dalilin wannan cikin rayuwarta za ta juye daga farinciki zuwa aƙasin hakan. **** Jalingo street. Tun jiya da daddare take fama da tashin zuciya amma ba ta damu ba, ta fi danganta hakan da soyayyen ƙwan da ta ci da safiyar ranar ne, can kuma da rana da ta sha zoɓo sai tashin zuciyar ya kwanta har dare da Habib ya dawo ba ta sake ji ba, da safe kuma da tashi sai kasala duk ya rufeta miyau na taruwa a bakinta sannan da zafin jiki ta kwana, Habib bai sani ba kuma bai hana da asuban ya sake nemanta ba, wani abu ke ba ta mamaki a group ɗin makarantan su na sakandiri mai suna Ahmadu ribaɗu Collage wanda suka buɗe na mata zalla akwai matan aure kuma tana gani suna hira, wata Aisha Iro ta taɓa tambayan cewa mijinta sai su yi kwana biyu bai neme ta ba, hakan ba matsala ba ce, nan fa aka yi ma tambayar caa, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Mafi rinjaye sun ce ba wani abu ba ne, domin rayuwar aure ba domin saduwa ba ne, zamantakewar aure ibada ne. Wasu ma suna ta cewa sai su yi sati kuma ana zaune lafiya, sai dai a yi romance kawai a kwanta tun lokacin da ta ga maganganun su abin ya tsaya mata arai, ba ta taɓa tattauna wannan matsalan da kowa ba sai Baɗɗo ita kuma ba aure ta yi ba sai ta nuna mata wataƙila Habib na cikin maza mabuƙata, ko Bestie ba su taɓa maganar da ita ba amma lamarin na damun ta, ba ta nemi komai ta rasa ba, ba abin da Habib ba ya yi mata matsalanta da shi kawai wannan bangaren ne, kamar wata machine haka ya ɗauke ta kwata-kwata ba ya barin ta samu hutu, tana haɗa musu abin karyawa tana ta tunane-tunane a cikin ranta, ta taɓa yi masa mgana tun farkon auren su ya ce ta shirya mijinta mai yawan buƙata ne amma ita a ganin ta buƙatar ta shi ta yi yawa ne. Indomie da ƙwai ta dafa ma Habib ba ta jin daɗin jikinta shi yasa ba ta yi dogon breakfast ɗin da zai ba ta wahala ba, sai ruwan tea da ta dafa masa sai da ta jera komai saman dinning sannan ta koma ciki ta tashe shi, wajen taimaka masa ya yi wanka ma sai da ya maimaita a tiolet, in Ummu ba ta furta ta gaji a baki ba gangar jikinta ya nuna gajiya da jarabar Habib, shi ya fara tsarkake jikinsa ya fito ya bar ta a cikin tiolet tana jin kirjinta da kanta sun yi mata nauyi. Ko da ta fito har ya shirya kan shi cikin suit, ko yadda ya ganta ta yi wani suku-suku ba fara'a bai damu da ya tambayi dalili ba, faɗa mata yake yi ta yi sauri kar ya makara. Wata riga mai gajeren hannu doguwa ta saka  sai hula ta rufe gashin kanta dake jiƙe sai ta sallame shi ko za ta dawo ta busar da shi. Tun da suka zauna saman Dinning karnin Dafaffen ƙwan nan ya dame ta, ba ta ma saka ma kanta shi ba, indomie ɗin kawai ta zuba wacce ta dafa tare da su carrot da greenbeans, tana kai cokali na ɗaya biyu, na ukun ne ya gagare ta haɗiyewa tuni ta ji kayan cikinta sun fara yamutsawa da gudu ta tashi ta faɗa tiolet kafin Habib ya samu damar mgana ya ji Ummu na ta sheƙa amai kamar  za ta amayar da kayan cikinta. Da sauri ya tashi daga zaman karyan da yake yi cikin mamaki ya bita tiolet ɗin amma daga baƙin kofa ya tsaya. "Baby me ke faruwa? Wani abu kika ci? Ya faɗa cikin bayyana damuwa a muryansa. Kuma damuwar har ya bayyana a saman fuskar shi. Ba ta ma san yana yi ba, tana duƙe tana sheka amai sai da ta amayar da duk abin da ke cikinta sannan ta samu sukuni, ruwa ta buɗe a famfon sink ɗin ta wanke bakinta sannan ta kora Aman ta ɗago tana haki ta nufo hanyar fitowa jiri ya ɗebe ta za ta faɗi Habib ya yi saurin riƙo ta. "Baby me ke damun ki ne? Are you sick? Ummu da saurin kuka tuni ta lafe a jikin shi ta fashe masa da kuka. "Ni ma ban sani ba Noori amma ina jin jikina duk ba daɗi." Ta faɗa cikin shagwaɓa, tarairayota ya yi suka dawo falo ya zaunar da ita akan kujera ya zauna a gefenta yana mai ƙura mata ido. Gabansa ya faɗi kar dai a ce Ummu Salma wani cikin ta samu? Da ko ya shiga uku. Da sauri ya tallabo fuskarta da duka tafukan hannayensa kafin ya ce" Baby yaushe rabon ki da ganin al'adan ki? "Tun bayan ɓarin da na yi sau ɗaya na yi Noori." Ta faɗa tana wani lumshe idanuwa har ga Allah jikinta ba ya yi mata daɗi so take yi ta kwanta. "Ummu-Salma ko ciki ne da ke? Ya faɗa cikin wata murya mai cike da fargaba. "Ban sani ba, nima kwanaki na yi tunanin haka sai da na siyo PT na yi gwaji sai na ga babu komai." Ta faɗa cikin sanyin murya tana mai ɗora kanta a saman kafaɗanta. Duk da haka bai gamsu ba, sake ɗagota ya yi yana sake ƙare mata kallo. "Noori ka bar ni na kwanta jiri nake gani." Ta faɗa cikin shagwaɓa shi ba ma ta ita yake yi ba kirjinta yake kallo sai a lokacin ya lura kirjinta sun tasa bai taɓa lura da hakan ba. "Wani yanayi kika ce kina ji a jikin ki? Ya tambaya agaggauce. Ita ko Ummu Salma ta ɗauka duk murna ce ya sa cikin sanyin murya ta amsa shin "Noori ina ji fa ba ciki ba ne, na faɗa  maka na gwada ba komai." "Ki amsa mini tambaya ta." Ya katse ta da sauri, numfashi ta fesar kafin ta shiga faɗa masa yanayin da take ciki ai tun kafin ta ƙarisa ya miƙe da sauri ya koma cikin bedroom  ɗin su, da mamaki ta bi shi da kallo ganin ya fito da Hijabin ta a hannun shi da key ɗin motarsa lokaci ɗaya yana faɗin. "Tashi mu je asibiti a yi gwaji." Cikin mamaki take bin sa da kallo ba ta samu damar mgana ba har ya zura mata hijabi ya koma ciki ya ɗauko mata takalmi jikinsa sai rawa yake yi kamar mazari. Tausayin shi ya kamata lokacin da ya duka yana zura mata takalmi kansa ta shafa lokaci ɗaya tana faɗin" Ka kwantar da hankalin ka Noori." Miƙewa ya yi lokaci ɗaya yana kama hannunta ta miƙe tsaye ba tare da ya amsa mganar ta ba. "Ka ji ? Ta sake faɗa bayan ta riƙo hannunsa guda ɗaya kallonta ya yi duk ya firgice a cikin ƙanƙanin lokaci. "Hankalina ba zai kwanta ba sai an yi gwajin nan." Ya faɗa da sauri lokaci ɗaya ya ja jakarsa dake gefenta ya rataya, riƙe da key ɗin mota a ɗayan hannun na shi, ɗayan kuma ya jawo hannunta. Ita ce ma ta ce ya tsaya ta kashe kayan wuta sannan ta ɗauko key ɗin gidan suka fita tare ta rufe suka rankaya motarsa ƙirar Benz har suka ɗauki hanya bai sake yi mata mgana ba hankalinsa duk ya tashi sai faman gudu yake yi a titi Ganin haka ya sa Ummu ta kama hannun shi dake saman sintari sai ya juyo yana mai kallon ta. "Noori." Da sauri ya katse ta da faɗin. "Boshon clinic za mu je ko? Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta ce" E. Ai can na ke da fayel." Daga nan bai sake magana ba hankalinsa na wajen tuƙi amma daga ganin shi ba ya cikin natsuwarsa. "Noori ka kwantar da hankalin ka, in ba cikin ba ne ma in sha Allahu na kusa samu." Wani irin kallo ya yi mata kallon da ba ta taɓa ganin ya yi mata irin shi ba za ta sake mgana ya ɗaga murya yana faɗin. "Ki bar ni, ba ki ga ina driving ba ne." Sai da ta kalle shi cikin mamaki shi kuma ba ya ma cikin natsuwarsa ballanta ya ji ba daɗi kan ɗaga mata muryan da ya yi. Idanuwanta suka cika da kwalla, tausayin Habib ya kamata yanzu in suka je asibitin suka ce ba ciki ba ne fa? Wani hali zai shiga sai ta koma addu'an Allah ya sa ciki gare ta, ko domin hankalin Habib ya kwanta daga gani ya ƙwallafa rai akan samun cikin ta. Abin da ba ta sani ba, tunanin da ke zuciyar Habib kishiyar tunanin da ke zuciyarta ne. **** BOSHON CLINIC. Suna isa asibitin sai da suka sake siyan kati saboda sauri sun manta da shi a gida. Bayan Ummu ta ga likita ta yi mishi bayanin duk abubuwan da ta ke ji a jikinta nan take ya saka aka ɗibi jininta zuwa lap, ya ce su ɗan jira sakamakon ya fita. Da yake asbitin na kuɗi ne ba wani ɓata lokaci, suna waiting area suna jira  Habib ya kasa zaune ya kasa tsaye, tana shirin ta ce masa ko zai bar ta ne ya tafi wajen aiki in ta karɓi result ɗin sai ta nemi Napep ɗin da zai kaita gida kafin ma ta yi mgana ta ji yana waya yana cewa ba zai shigo office da wuri ba shi ya sa sai ta yi shuru da bakinta.   Ita dai tana zaune saboda ba za ta iya tsayuwa ba, Habib kuma ko ya zauna sai ya tashi ya kasa zama a waje ɗaya tuni farar fuskan shi ta bayyana halin damuwar da yake ciki. Ummu na zaune tana bin shi da kallo tausayin shi take ji ta cikin hijabin ta, tana ta shafa cikinta a cikin zuciyarta take faɗin. "Allah ya tabbatar da cikin nan." Da ace Ummu-Salma ta san gaibu, da ace ta san fargan jajin da ke jiranta da ba ta yi ma kanta wannan addu'ar ba, da ta yi  addu'an in ma cikin ne Allah ya sa ya bi rariya. Zaman jiran mintina arba'in suka karɓi sakamakon gwajin. Bakin Ummu ya ƙi rufuwa tun bayan da likita ya ce tana da ciki na wata ɗaya da kwanaki, an rubuta mata magungunar karin jini da cin abinci, sai vitamin e, amma murnanta sai ya koma ciki na ganin fuskar Habib ta yi baƙiƙirin kamar an faɗa masa saƙon mutuwa, ita da ta yi tunanin yana jin tabbacin tana da ciki sai ya ɗaga ta sama ya yi juyi da ita, amma sai ta ga saɓanin tunanin ta, amma sai ta ƙarfafi kanta da cewa haka ya yi a cikin ta na farko lokacin da ya ji labari bai nuna murnansa ba amma lokacin da ya tabbatar da ta yi ɓarin shi ya fi kowa damuwa, ya yi jinyar ta har sai da ta warke da jikinsa da aljihunsa tunda ta kwanta asibiti wajen kwana uku aka ƙara mata jini, tun a lokacin likitan ya ce ta rasa jini da yawa. A lokacin ma jinin Hamma Kabiru aka saka mata tunda sun gwada na su Hamma Abdullahi bai yi mata ba, ita jininta O Negative. Na sauran kuma duk AB Negative ne. Suna cikin mota a hanyar komawar su gida, kamar Habib zai ta shi sama. Ummu ta kasa yi masa mganar siyan mgani ganin fuskar shi tumu tumu ba annuri daga gani ba ya cikin natsuwarsa. A ƙofar get ɗin su ya sauke ta bai shiga ba tana kuma sauka bai ce mata komai ba ya fizgi mota a guje ya wuce ba domin ta yi saurin matsawa ba da ya take mata ƙafa. Har ya ɓace ma ganinta bakin ta bai rufu ba saboda mamaki. "Me ya samu Noori kuma? Ta faɗa a fili saboda tunda suka yi aure bata taɓaa ganin shi cikin firgici da zafi haka ba. Jiki a sanyaye ta shiga compound ɗin su har ta buɗe ɗakin ta shiga jikinta bai dawo daidai ba, mamakin yanayin yadda Habib ya yi mata yafi ba ta mamaki ta ɗauka cikin tattali da murna zai dawo da ita gida amma sai ta ga akasin abin da ta yi tunani, sai dai ta yi masa uziri da cewa watakila wani abu ne ke damun shi. Takardan cikin ta ɗauko duk da ba gane yaren na likitoci take yi ba amma kallo kawai na saka ta farinciki, tana shafa cikinta tana jin murna da farinciki nan da watanni takwas za ta zama uwa. **** Habib tun da ya fizgi motar nan a guje bai ci burki a ko'ina ba sai da ya isa haraban bankin su, a parking space ya faka motar shi amma bai fito ba kansa ya dafe da hannu biyu yana jujjuyawa. Kafin lokaci ɗaya ya zaro wayarsa cikin aljihun wandon sa ya lalubo wata lamba da ya yi ma saving da M.S. wajen saƙo ya shiga ya fara rubuta mai lambar saƙo. "An sake samun matsala Ummu-Salma ma da ciki a karo na biyu." Ya tura da mintina huɗu yana zaman jira riƙe da waya a hannun shi sannan mai lambar ya dawo masa da amsa. "Again kuma? Habib wasa da hankalina kake yi? Da man ai ka san za ta iya samun ciki tun da mahaifarta lafiya lau. Sai da na ce ka yi mata planning ko a ɓoye ne amma ka ƙi amincewa. To na rantse da Allah ba zan amince ba, in farko ya zama kuskure wannan ganganci ne." Jikinsa na rawa ya sake rubutawa ya tura. "Ki yi haƙuri ki bar wannan mganar yanzu dai mene ne mafita? Yana turawa da mintina biyu aka dawo masa da amsa. "Ka fi ni sanin mafita. Ni dai ina so ka sani bayan ni babu wata macen  da ta isa ta haihu da kai Habib. Ni ce uwar ƴa'yan ka nan duniya. Ka tuna da hakan" Sai da ya share zufa duk da A.C ɗin dake cikin motar, daga ganin shi yana cikin tashin hankali. Yana shirin sake rubuta wani sakon ne wani ya sake shigowa. "Ka tuna da alƙawarin mu shekara ɗaya ka ce na baka za ka cire Ummu Salma daga rayuwarka na har abada. Yanzu kuna da wattani takwas da aure. Wattani huɗu suka rage maka Habib." Sai ya dakata yana mai kallon saƙon zuciyarsa na bugawa da gudu fat! fat. Ajiyar zuciya ya sauke a jere kafin ya ba da amsa. "Ina sane da komai. Zan kuma ɗau matakin da ya dace." Yana gama turawa, ya rufe wayar ya mai da ta cikin aljihun wandon shi, sai da ya ɗan natsa sannan ya ɗauki brief case ɗin sa ya fito daga motar bayan ya kulleta cikin Sassarfa ya nufi katafaren ginin ma'aikatan su na First bank. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/BxcTrVcz7GoIDzbqZTpIxF?mode=gi_t *04* *9:43pm* Har zuwa lokacin Habib bai dawo ba, Ummu ta kira shi sau uku bai ɗaga wayarta ba daga karshe ma sai ta ji ta daina samun shi kwata-kwata. Zaune take a falo saman ɗaya daga cikin kujerun da suka yi ma falon ƙwanya, tun ɗazu ta gama girki ta yi wanka tana jiran dawowar Habib amma har zuwa wannan lokacin bai shigo ba, kuma bai saba yin dare a waje ba sai da dalili mai karfi. Tunaninta da hasashenta bai taɓa kawo mata matsalan daga ita ba ne, tagumi ta yi ta ƙura ma talabijin ido a tashar tauraruwa an saka wakar Salin smart na Labarina. Amma hankalinta da nazarin ta ba ya wajen, idanuwanta na juyawa akan allon talabijin ɗin amma tunanin ta da dukkan zuciyarta yana kan Habib. "Me aka yi masa? Ta tambayi kanta sau shurun masaki a cikin zuciyarta ko daga ɗazu bayan dawowarsu daga asibiti ta yi ma Habib wani laifi ne? Ya iya hangen ta da tunanin ba ta hango wani laifin da ta yi masa ba, fuskar sa da ayyukansa sun sauya ne daga lokacin da ya samu tabbacin tana da shigar ciki, daga lokacin Habib ya sauya sauyawar da ta kasa gano dalilin shi, kuma zuciyarta ta aminta da shi, shi ya sa ba ta yarda ta kintsa mata wani mugun tunani a game da shi. Ƙarfafa kanta take yi da cewa watakila wani ne ya ɓata masa rai, amma Habib sai ya fi kowa murna da samun cikinta anan duniya. Tun da ya sauketa a bakin get ta shigo gida take nazarin abin da ya faru amma ta kasa gano bakin zaren. Ko da daddaren nan sai da ta yi Amai bayan ta yini kwanciya saboda kasalan da ta rufe ta amma ba ta biye ma yanayin jikinta ba yamma na yi ta miƙe ta yi ma Habib girki, soyayyan taliya da Nama mai kayan lambu da ya ke ana gobe su Amma za su dawo ya ɗauke ta sun je kasuwa sun yo cefane mai yawa tana da komai na buƙata kayan miya ta ñika shi ta tafasa shi yana cikin Frezer ɗiɓa kawai take yi in ta tashi amfani da shi. Wayarta ta sake jawowa yanzu kam har goma ta wuce amma babu alamun Habib, tunanin ta ya sake karkata kan ko dai yana fushi da ita ne ya ɗauka ta san tana da ciki ba ta faɗa masa ba? Tuna haka ya sa ta yi mirmishi ita kaɗai ta san ma saboda haka ne ya ke fushi yaƙi dawowa gida da wuri, in ya dawo za ta bashi haƙuri in dai Habib ne ba ya  iya dogon fushi a kanta saboda yadda yake tsananin sonta da gudun duk wani abu da zai ɓata mata rai. Gajiya ta yi ta zaman shuru sai ta yi tunanin bari ta kira Bestie sai dai wayar na ta ringing ba ta ɗaga ba, sai ta ma yar da akalan kiran ga Baɗɗo ita dai ta ɗauka sun yi mgana ga shi tana so ta sanar da ita tana da ciki amma kamar an matse bakinta ta kasa faɗa mata, ba su daɗe suna waya ba saboda ta ce mata tana karatu sun fara jarabawa a satin nan da ya shiga. Ta tambayi Habib sai Ummu ta yi mata ƙaryan ya biya ta gidan su bai riga ya ƙariso ba. "Allah ya ba ki sa'a da nasara SisNa." Ummu ta faɗa cikin mirmishi lokaci ɗaya tana shafa cikinta. Domin in ta tuna nan da wattani takwas ita ɗin uwa ce kuma mai uba irin Habib sai ta ji kamar ba macen da ta kai ta farinciki anan duniya. Daga can bangaren Baɗɗo ta amsa ma ta da Amin,  sannan suka yi sallama bayan Ummu ta ce a gaishe mata da Ummin ikki. Bayan sun gama wayar Data ta buɗe ta shiga tiktok tana kallon girke-girke akan account ɗin Maryama Kitchen. Duk yadda ta ke son abin da ya shafi girki, in tana kallo ma wani nishaɗi take ji amma yau kwata-kwata ba wannan nishaɗin sai ta ji ma komai ya fita daga kanta kawai sai ta kashe datan, saboda kar ta zauna shuru ya sa ta fara duba contact ɗin ta. Lambobin da ba su da amfani take bi tana faman gogewa domin wasu lambobin ma sai su shekara ba su yi waya ba. Wasu ma duk sun daina amfani da layukan. Lokacin da ta iso jerin sunayen Yayyenta da ko wanne ta yi masa saving da Hamma sannan da sunan mutum a gaba. Tsayawa ta yi tana kallo Hamma Mustapha ne suka ɗan jima ba su yi mgana ba. Kuma yana da ƙoƙarin kiranta lokaci bayan lokaci, ba za ta iya tuna last da suka yi waya da shi ba. Ita kuma ta sha'afa ganin bai kira ta ba, kuma ita ba ta kira shi ta gaishe shi. An ce ka gaida mai gaishe ka duk cikin yayyenta ta fi son Hamma Mustapha yana da sauƙin kai da sanyin hali ga haƙuri da kawaici hallayan Baffa kaɗan ne bai deɓo ba.   Yana da son ƴan'uwan shi sosai, saɓanin irin su Hamma Kabiru da bashi da kula kwata-kwata, duk a cikin su Hamma Mustpaha ne da Hamma Jibo suke ji da ita, to sai gwara ma Hamma Abdulrrahaman, shi Hamma Abdullahi in ya gan ka dai zai yi murnan ganin ka amma don bai gan ka baa zai damu da neman ka ba. Kar su Hamma Kabiru su ji labari, shi a motor ɗin shi cewa yake yi in ka ji shuru lafiya ne. Baya neman mutane in kuma ya gan ka ba zai yi murna ba in ma bai gan ka ba zai damu ba kuma ba zai tambaya ba. Shi ya sa Ummu ta sha faɗin cewa suna da kamanceceniyar halayya da Hamma Lamiɗo, wataƙila saboda tare suka yi wasan ƙasa suka kuma girma tare shi ya sa wasu hallayan na su marasa kyau suke kamanceceniya da juna.   Hamma Mustapha ta latsa ma kira, ringing ɗaya ana biyu ya danna mata busy, ta sani da man ba ya ɗaga kiranta. Shi zai kashe sannan ya kira ta. Cikin minti ɗaya sai ga shi ya biyo bayan kiran da sauri ta ɗauka cikin zumuɗi. "Hamma ka manta da ni " Ta faɗa cikin yar shagwaɓa kamar za ta yi masa kuka. Daga can bangaren ya yi dariya har tana fidda sauti. "Wane Hamma ya manta da Autan Ammah. Kina raina ayyuka ne suka yi mini waya a kwanaki nan. Kina lafiya? Ya faɗa daga ƙarshe yana sirka mganar shi da yaren fillanci. Ta amsa mishi itama cikin harshen fillancin, sun gaisa cikin fara'a da tambayan iyalan shi, da ya ke shi Gombe yake aiki can ya ke zaune da iyalansa. "Ina Adda Aisha? Ina su Mahma da Baffan mu? Duk ya ce sun yi barci saboda makaranta gobe Adda Aisha yanzu ta bar ɗakin sa. "Ka gaishe mini da ita sosai." "Zan faɗa mata Autan Ammah. Ya wajen megidan na ki? Tana shafa cikinta cikin mirmishi ta ce" Duk muna nan lafiya Hamma. Yaushe za ka zo? Sai da ya yi tunani kafin ya ce. "Kin san ga aiki sannan yara suna makaranta itama Aisha tana makaranta ko? "E na sani Hamma." "To sai mun samu hutu za mu zo mu yi ko sati ɗaya ne in sha Allahu." Cikin murna ta ce" Allah ya kawo ku lafiya Hamma." Ya amsa da Amin. "Ba dai wata matsala ko? Ya tambaya sai ta amsa mishi da babu wata matsala ya ɗauka za ta yi masa sallama ne tun da dare ya yi sai ya ga ta fara zaro wata hiran. "Auta dare ya yi, kar ki bar megidan na ki shi kaɗai." Sai ta kasa mgana, jiki a sanyaye suka yi sallama in ta ce Habib bai dawo ba zai saka ayar tambaya, ko ba ma haka bai kamata ta faɗa mishi wani abu ba, yau dai zumumci take jin yi wayar Hamma Jibo ta kira shi, shi dai ba ta same shi ba Adda Nauwara ta ɗauka ta ce ya shiga wanka. "Ummu yanzu da daren nan? Ko kewar mu kike ji ne? Nauwara ta faɗa tana dariya, sai Ummu ta rufe fuska kamar tana ganinta itama tana dariyan, yara ta tambaya itama ta ce duk sun kwanta dare ya yi, suna ta hira da Nauwara har Hamma Jibon ya fito ya karɓa shima suna gaisawa sai da ya ce. "Autan Baffa ko akwai damuwa ne? "Ba komai Hamma kawai na kira ka ne na gaishe ka." "To na gode. Ki kwanta kin ga dare ya yi, da safe za mu yi waya." Da haka shima ya sallame ta, sai bayan sun gama wayar ne ta ga Hamma Mustapha ya tura mata 10k,  duk da ya san ba ta buƙatar komai amma shi mai kyauta ne da alheri shi kafin ta yi kukan wani abu ya ba ta saƙon godiya ta tura masa da addu'an Allah ya sa ya gama da duniya lafiya. lambar Hamma Abdulrahim ta gani shi da ya ke ba ya ƙasar sai dai in shi ya kira ka ko da yaushe wayarsa ba ta shiga. Amma suna mgana a chart sosai har Vadeo call suna yi wani lokaci in karatu ya yi musu sauƙi tana kewar shi ko bikinta bai samu zuwa ba ya fi shekara rabon shi da zuwa gida amman ya ce ya kusa kamallawa gabaɗaya shi ya sa zai jima a can kafin ya dawo gida. Da har ta wuce lambar Hamma Kabiru, sai ta dawo bari dai ta kira shi, ko ba komai ɗan'uwanta ne kuma ba za ta biye ma halin shi ba, in ta duba ma ai akwai jininsa roba biyu a cikin jikinta. Sai ta latsa masa kira har ta katse bai ɗauka ba taɓe baki ta yi a cikin ranta ta ce ka huta. Agogon wayarta ta sake kallo sha ɗaya har da mintina ta gota. Tagumi ta sake yi cikin bugawar zuciya sake kiran lambar Habib ta yi amma ba ta shiga ba. Niyyarta ta kira ko ƙaninsa Maharazu acan gida ta ji ko yana gida ne tana cikin neman lambar ne kiran Hamma Kabiru ya shigo mata sai ta ɗauka. A ginshiƙe ya yi mata sallama da muryan nan ta shi a cunkushe kamar mara lafiya ta amsa ita ta fara gaishe shi ya amsa da lafiya jin ya yi shuru itama sai ta yi shuru sai ta rasa ma abin da za ta ce masa, ba wani shaƙuwa sosai a tsakanin ta da shi ba kamar sauran yayyen nata. "Mene ne haka, na zo na ga kiran ki ba na kusa. Na zo na gani na kira kuma kin yi shuru." Tana so ta yi magana kamar an ɗinke mata baki ta kasa. "Ke in ba ki da abin cewa zan kashe wayata. Kin san aikin da na katse ne na kira ki? Ya faɗa cikin faɗa shi da man ko mganar arziƙi ce ta faɗa ce a wajen shi. "Hamma." Ta faɗa a sanyaye tana jin hawaye suna cika kwarmin idanuwanta. "Me ya faru? Ya faɗa a hankali jin muryanta ta yi sanyi alamun kamar za ta yi kuka, duk da ya san Ummu da shagwaɓan tsiya sai dai ganin dare ya yi yasa ya yi tunanin ba lafiya. "Ki yi mgana mana." Ya faɗa da karfi. "Hamma." Ta sake kiran shi a raunane lokaci ɗaya hawaye na zubo mata muryansa kawai da ta ji sai ta ji wani irin abu ya sauko mata mai kama da rauni, sai ta ke jin kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gaban shi kawai shi take son gani domin ta fi wata uku ba ta saka shi a idanuwanta ba, tunda shima a Jalingo ya ke aiki can ya ke zaune da iyalansa yana zuwa amma ita tana gidan ta in dai ba hutu suka zo shi da iyalansa ba ba ta samun ganin shi. "Lafiya wai kike ta kiran sunana kuma ƙin ki mgana." Hawayenta ta yi saurin sharewa. "Mijin naki ne ya yi miki wani abu? Ya faɗa kai tsaye domin shi abin da zuciyarshi ta kitsa masa kenan. "Aa Hamma." "To A'a me ye? Ke ba na son fa shanshanci in ba ki da abin faɗa zan kashe waya ta ina da abun yi." Jin abin da ya ce ne ya sa cikin yar shagwaɓa ta ce" Hamma na kira ne fa na gaishe ka " "Ƙarya ne" Ya faɗa kai tsaye. "Wallahi Hamma." "Gaisuwan ne sai da daddare za ki kira ni Ummu? Kanta ta sosa kafin ta ce" Ni ban ma lura da dare ya yi haka ba Hamma." Kai ya jinjina kamar tana ganin shi kafin ya ce" Ko dai ba ki da kuɗi ne? Kin talauce ne? "Kai Hamma." Ta faɗa tana rufe bakinta. "To ni dai ba saba kira na ki gaishe ni kika yi ba Ummu Salma." Ya faɗa kai tsaye saboda haka ɗin ne suna daɗewa ba su yi mgana ta waya ba. "Ina kiran ka mana Hamma." "Ba na son ƙarya kina dai kiran su Mustapha amma  ba ni ba. Ko da ya ke kin ce kin fi son su ni ina da mugun hali irin na Lamiɗo ko? Ummu ta rasa in da za ta saka kanta saboda kunya da nauyi. Ashe ya ji wannan mganar? Amma abin mamaki wa ya faɗa masa?. "Kin yi shuru ko ba haka na ji kina faɗa ma Baɗɗo ba." Tabbas an yi haka tun kafin ta yi aure ne. Suka taɓa hiran a ɗakin Ammah ne su ba su taɓa sanin ya ji ba in ba za ta manta ba yana garin lokacin wataƙila ya zo shigowa ɗakin Ammah ne ya ji suna hiran "Duk mugun hali na ina da kirki Ummu. Lamiɗo ma don ba ki zauna da shi ba ne he is a nice person." Ta aminta da kirkin shi tun da shi uwa ɗaya ce ta haife su amma gwara shi akan wancan, ita dai ba ta yarda da cewa wai Hamma Lamiɗo is nice person ba. "Ka yi haƙuri Hamma. Ba.." Ya katse ta da sauri yana cigaba da faɗin" Hallaya ce Ummu. Wani haka Allah ya hallice shi ba ya son shiga rayuwar kowa. Kamar ni nan na fi son shuru fiye da komai, kamar Lamiɗo ya fi son rayuwa kamar yadda kika ga yana rayuwa, amma duka muna da kirki ba mugaye ba ne kamar yadda kika ɗauka ba." Tana danne bakinta kar ta yi dariya ta ce" Na fahimta Hamma." "So ko gobe ki daina yanke hukunci kan mutumin da zama mai tsawo bai haɗa ku ba." Ta amsa masa da toh, suna ma cikin wayar ne ta ji ana taɓa kofa. "Sai da Safe Hamma a gaida Adda Safina da su Yusra." "Za su ji, da safe zan saka miki ko na kati ne domin na san dalilin kiran kenan." Tana so ta ce ba haka ba ne sai har ya kashe wayarsa dai-dai lokacin da Habib ya shigo falon da sauri ta miƙe tana kallon shi cikin mirmishi, shi ko gogan kallo ɗaya ya yi mata bai sake ba, yana rataye da jakarsa ya fara takawa zai wuceta zuwa bedroom. "Sannu da zuwa Noori." Ta faɗa tana nufarsa, bai tsaya ba amma ya amsa da yauwa a ɗakune yadda ta bar fuskar shi a cunkushe ɗazu to a yanzu ma haka ya shigo Tana ƙoƙarin karɓan jakar hannun shi ya wuce ta da sauri zuwa cikin bedroom tana jin ƙaran yadda ya rufe ƙofar da ƙarfi. Ummu salma ta yi sansarairai a tsaye ta kasa motsi saboda mamaki da al'ajabi a wattani takwas ɗin da suka yi da aure ita da Habib ba su taɓa riskan wannan matakin ba sai yau. Ajiyar zuciya ta sauke, komawa ta yi ta zauna tana sake karfafa ma kanta gwiwan ba komai yana fushi ne ya ɗauka ta san tana da ciki ne ba ta faɗa masa ba. Tana nan zaune sama da mintina talatin sha biyu saura na dare sannan Habib ya fito daga cikin Bedroom, ya sauya kaya zuwa wani gajeron wando da farar singlete da alamu wanka ya yi ko kallon ta bai yi ba ya wuce kitchen ya ɗauko ruwan gora ya fito da shi a hannu ita kuma ganin haka ya sa ta miƙe jikinta har yana rawa. "Noori."   Ta faɗa cikin sanyi da karyewan murya. Sai da ya sha ruwan rabin goran  sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin kallo da ya sanyaya mata jiki. "Ga abinci." Ta faɗa tana nuna masa Dinner ɗin da ta gama shirya masa komai tun ɗazu. "Na ƙoshi." Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya yana sauke goran hannun shi  a saman dinning ɗin ya wuce ta ya koma ciki, da sauri ta bi bayan shi ta ci sa'a bai rufe ƙofar ba. Yana zaune a gefen gado yana duba wayarsa ta shigo gefensa ta zauna tana neman kwanciya  a saman kafaɗan shi ya yi saurin matsawa gefe, Ummu ta saki baki tana kallon shi. "Noori." Ta kira shi da mamaki a muryanta bai amsa ba ya dai kalleta a tsaye da idanuwansa fuskar nan ba fara'a. "Me ya faru ne? Banza ya yi da ita sai ma ya cigaba da duba wayarsa. Sai ta yi mirmishi kafin ta ce. "Wai akan mganar ciki ne? Ga mamakin ta  sai ya amsa mata da cewa. "E." Ta ɗauka tunanin ta gaskiya ne yana fushi ne akan yana tunanin ta sani ba ta faɗa masa ba, ba ta san tunanin Habib a lokacin ba. "To ka yi haƙuri Noori na, wallahi da gaske na ke yi nima ban san ina da ciki ba." Har ta gama mgana bai ɗago ba, yana cigaba da latsa wayarsa. "Ka ji Allah ban sani ba ka yarda da ni." Matsowa ta sake yi kusa da shi tana mai riƙe hannun shi guda ɗaya tana sake marairaicewa da muryan tare da shagwaɓan da ta san yana kunna shi. "Am sorry Noori na. Baby ce fa? Za ka iya fushi da ni? Ta faɗa tana mai kwantar da kanta a saman kafaɗan shi. Sai ya sake matsawa da mamaki ta sake ɗagowa tana kallon shi kafin ta samu damar mgana ya miƙe tsaye. "Ummu-Salma ina son na yi mgana da ke." Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai kallonta a mganar shi da yanayin shi babu wasa ko kaɗan. "Magana kuma? Wata mgana? Ta faɗa cikin mamaki gabanta na faɗi kaɗan-kaɗan. Bai amsa mata ba sai ya koma can farko gado ya zauna sannan ya juyo yana kallon Ummu-Salma da ta daskare a zaune saboda ita fa ba ta gane ma yanayin Habib ba gaskiya "Ki natsu ki fahimci umarnin da zan ba ki." Kallonsa kawai take yi amma ta kasa mgana sai dai ta kasa haɗiye miyau a bakinta saboda faragaba da tarardadi "Ina sauraran ka." Ta faɗa dakyar cikin rauni har idanuwanta sun fara cikowa da ƙwallah tun kafin ma ya faɗi mganar. "Ummu-Salma." Ya kira sunan ta a kausashe, sunan da ba taɓa jin ya kira ta ba tun tana gida da Baby yake kiranta har bayan auran su bai sauya mata suna ba shi ya sa jin yau yana kiran ta da sunan ta cikin kaushi ba tausasawa jikinta ya fara rawa cikin tsoro ta amsa. "Na'am. " A muryan ta kamar saura ƙiris ta fashe da kuka. "Umarni na ke so na ba ki, ta wani fanni kuma ba Umarni ba ne." Ita dai ta ƙura masa ido, ta kasa cewa komai amma ta matsu ya faɗi abin da zai faɗa kafin  zullumi ya ɗauke mata numfashinta. "Ina son a zubar da cikin jikin ki Ummu-Salma." Ya faɗa yana mai kallonta domin ganin yanayin ta. Ita ta ko sai ta ji kamar ba ta ji da kyau ba ya sa ta sake tambaya. "Naam me ka ce? Ta faɗa tana mai ƙura masa ido, kamar ta ji Habib na maganar ciki, me ya ke cewa ne? "Na ce ina so a zubar da cikin nan." Ido ta zaro kafin ta ce" Wa ni  ci ki.? Ta faɗa a rarrabe cikin tashin hankali. "Wanda ke jikin ki." Ya faɗa ba tare da ɗar ba, kuma babu nadama a mganarsa. Sai Ummu ta fara mirmishi kafin ta ce. " Haba Noori ka bar irin wannan wasan don Allah ba na so." Ta faɗa lokaci ɗaya tana girgiza kanta. Domin a tunanin ta wasa ya ke yi, ita kuma ba ta son irin wannan wasan, duk duniya a yanzu ba wanda ya isa ya raba ta da cikin jikinta sai wanda ya ba ta, amma ba dai wani mutum ba.  "Wasa ka ke yi ko Noori? Ta sake faɗa tana kallon shi. Amma sai Habib ya miƙe a fusace har yana nuna ta da hannu. "Kin ga wasa a mgana ta! Ko kin ga fuskata da alamun wasa? Ya faɗa a fusace, jikin Ummu na rawa ta miƙe, cikin mamaki da aljabi ta ce" Cikina zan zubar Noori? "E haka na ce" "To saboda mene? Cikin yana da wata matsala ne? "Ba shi da wata matsala, amma ni ne zai iya kawo ma matsala a rayuwata nan gaba." Ummu cikin rawan baki da na murya ta ce "Ban ga ne ba? "Ai ba za ki gane ba. Malama ni dai ga abin da na ce. Ciki za a zubar da shi." "Aa" Ummu ta faɗa hawaye na zubo mata cikin kuka ta ce" Me ya sa zan zubar da cikina? Cikin sunna ne ba na shege ba." Ta faɗa cikin zubar hawaye "Ni haka na ce za a zubar da shi." "Ba zan iya ba. Ba zan iya zubar da cikin nan ba,  haka kawai sai ka ce na zubar da ciki kuma ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba" Ta faɗa tana share ƙwalla kafin ta matsa kusa da shi tana cewa" Noori ni ce fa, ka tuna lokacin da ka shiga damuwa da na rasa cikina na farko me ya sa ba za ka yi murna da samun cikina a karo na biyu? Me ya sa ka canza? Ciki fa ka ce na zubar? Zunubi fa kake so mu aikata." Ta ƙarishe faɗa tana ƙoƙarin riko shi da sauri ya kauce yana faɗin "Ni ba damuwa na shiga don cikin ki ya zuɓe ba, ko bai zube ba za ki zubar da shi. Murna na yi lokacin da ya fita ba baƙin ciki ba.". Ya faɗa yana kallon ta, cikin ɗimuwa da firgici Ummu ta zare ido, kafin ta kifta idanuwanta amma ta kasa mgana domin sai ta ji wani abu ya tokare mata maƙogwaro "Kin ji da kyau, saboda haka na ba ki  kwana uku ki yi shawara. Duk da Umarni ne ba zan miki dole ba amma ki sani zubar da cikin nan kamar makullin auran ki ne, taurin kai kuma na ƙin zubarwa dai dai ya ke da rasa komai na ki, in na ce komai ina nufin komai. Kuma wallahi sai  kin yi nadaman saɓa ma umarnina." Yana gama faɗin haka ya fice ya bar mata bedroom ɗin. Ummu ta rasa wani tunani za ta yi, sai take ganin kamar a mafarki gaskiya ne abin da ke faruwa ko ƙarya, amma kuma kamar da gaske, ganin ta kawai ta yi tana tafiya a falo ta iske Habib zaune a saman kansa ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki, so take yi ta ga shin Habib ɗin ta ne ko sauya mata shi aka yi amma ba ta gano wani abu da zai saka Habib ɗin ta ya sha bambam da wannan dake zaune a gabanta ba. Tashi ya yi zai bar mata falon da sauri ta sha gaban shi tana faɗin" Noori an ya kasan me kake faɗa kuwa? Ta faɗa muryanta na rawa kaɗan ya rage  ta fashe da kuka "Kwana uku na ba ki , ki yanke ma rayuwarki hukunci. Kwana uku kacal." Ya faɗi haka sannan ya raɓa ta gefen ta ya bar falon, nan ƙasan cafet Ummu ta durƙushe tana mai fashewa da kuka, ji take yi kamar ba ita ba zuciyarta na zafi kirjinta wani abu ya tokare mata da ya kasa wucewa kuka  ya sake kece mata, tunani take yi ko Habib ya fara shaye-shaye ne yau wata ƙila ya sha wacce ta fi karfin ƙwakwalwarshi shi ne ta faɗa masa ba daidai ba, amma ta ya ya zai ce ta zubar da cikin jikinta cikin sunna ba ta taɓa jin maganar da ta ruguza zuciyarta kamar wannan mganar ba, me mganganunsa suke nuna mata! Me ya sa ta ji zuciyarta na yi mata rawa akan Habib? Me ya sa yau ya sauya mata? Me ya sa zai yi haka? Kuka take yi kamar ranta zai fita, tana kuma dafe cikinta da ta ji wani kaunar shi na ratsa jinin jikinta, tun tana gida ita mai sha'awar yara ce duk in da ta ga yaro sai ta ji da man na ta ne, ɓarin ta na farko kuka ta dinga yi sai da Ummin ikki ta yi ta lallashin ta. Ammah kuma faɗa ta dinga mata da cewa ba Allah ne ya ba ta ba, sai ta yi haƙuri shi zai sake ba ta wani, to ga Habib na faɗin da man ko cikin bai bare ba za a zubar da shi, an ya yana cikin hayyacinsa kuwa ita ce fa Ummu-Salma da ya ke so kamar ransa, ita ce matarsa da ya ke burin ta zama uwar ƴaƴan shi, me ya sa yanzu zai zo yana wasu mganganu? Ta kasa gano dalili, ta fi tunanin wani abu Habib ya sha da ya birkita masa tunani amma a cikin hayyacinsa ba zai ce ta zubar da gudan jininsu ba. Wataƙila zuwa da safe zai dawo hayyacinsa ya ba ta haƙuri ya fahimci kuskuren da ya yi, ita kuma za ta yafe masa ta rufe mganar nan har duniya ta naɗe ba wanda zai ji "Habib na shaye-shaye ne? Wata zuciyar ta tamabaye ta, ko ba ya yi wataƙila dai jiya ya fara haka ta ba ma kanta amsam yunwa ta ke ji, amma ta kasa iya saka ma cikinta komai anan saman cafet ɗin ta kwana sai gabda asuba ta koma ɗaki, ta iske Habib na ta barci sai ta lallaɓa ta kwanta a gefen shi tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta sun kumbura saboda kuka da man ita mai saurin kuka balle ta samu dalili, cikin lokaci barci ya kwashe ta duk da kanta na ciwo ba ta tashi ba sai da ta ji ƙaran ruwa a banɗaki sannan ta san asuba ta yi. Habib ne ya fito sanye da jallabiya ko kallonta bai yi ba ya saka hula ya fita zuwa masallaci. Ita kuma daƙyar ta lallaɓa itama ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta ta da salla. Ta idar kenan Habib ya shigo jallabiyan jikinsa ya cire daga shi sai ƙaramin wando ya koma ya kwanta. Ita kuma sai da ta gama addu'o'in ta sannan na nannaɗe darduman ta ijiye ta tare da hijabin nan saman side drower na gadon. Habib idanuwansa biyu yana latsa wayarsa yau asabar ba fita aiki. "Ina kwana Noori." Kamar bai ji ba sai da ta sake maimaitawa sannan ya amsa da lafiya kamar ba ya so har yana juya mata baya. Ajiyar zuciya ta sauke ko a cikin Sujjadan ta sai da ta roƙi Allah ya dawo da hankalin Habib jikinsa ita fa a tunanin Habib ba ya cikin hayyacinsa ne. Gefen sa ta koma ta kwanta tana cigaba da saƙe-saƙe. Saboda rashin barcin da ba ta yi ba ya sa ta ji barci na shirin fizgan ta sai dai me? Kamar a mafarki ta ji Habib ya matso kusa da ita, yana shafa ta sai da ta yi mirmishi a fili a tunanin ta Habib ya dawo hayyacinsa ne tuni ta zage ta bashi dukkan halin kai, da a ce Ummu ta san manufar Habib a kanta da ko sama da ƙasa za su haɗe ba za ta sake ba shi jikinta ba. Da safiyar ma da ta ɗumama musu taliyar ya ci sai ta dafa musu ruwan tea suka haɗa da shi, kuma a gida ya yini bai fita ba duk da bai sakar mata fuska ba amma in ta yi masa mgana zai amsa sai dai ba cikin walwala ba, sai dai yinin nan da ya yi a gida Ummu-Salma ta gane ba ta da wayau ita ya yi ta moruwa ita kuma jin daɗi take yi a tunanin ta ya bar wancan mganar ganin bai sake yi mata ba, har wani zumuɗin ba shi haɗin kai ta ke yi yana ta murzanta ko tausayi ba shi da shi a kanta alhalin a daran ranar ma ta ci abinci kenan ta amayar da shi duka kuma bai saka ya ɗaga mata ƙafa ba. Haka ma washegari a gida ya yini sai da yamma ya samu fita shima bayan duk ya gana sakar mata gajiya, Ummu ba ta damu ba tuni ta manta da mganar Habib a tunaninta ya dawo cikin hayyacin sa ya bar mganar, tun da kuma ta ga yana cin abincinta sannan yana neman ta a shimfiɗa sai ta yi tunanin addua'nta ce ta karɓu Habib ya dawo cikin hayyacinsa. Shi ya sa ma ba ta yi mganar da kowa ba hatta Bestie ko da ta kira ta a ranar lahadi suka daɗe suna magana tana ta tambayanta. "Bestie kina dai lafiya ko? Ita kuma ta ba ta tabbacin lafiyan ta ƙalau, a tunaninta ta rufe mganar ba wanda zai ji. Sai dai abin da ba ta sani ba Habib zai yi silan tarihin auren ta da shi zai zama abin tunawa gare ta da ahalinta na har abada. Abin da ba ta sani ba game Habib, ko ta manta ya ce lokaci ya ba ta. Wataƙila yana jiran cikar wa'adin kwanakin da ya ɗiba mata ne" **** Monday. Tun a daren jiya da zazzaɓi ta kwana da asuba ma sai da ta yi amai amma a haka Habib ya neme ta, ta fara jan jikinta da wannan rashin tausayin da Habib ke nuna mata. Za ta gama yin Amai amma sannu Habib ba zai ce mata ba. Yadda ya ke son ta ta ɗauka tare za su yi wannan laulayin amma sai ta ga aka sin haka. Ya ganta kwance cikin bargo tana rawan sanyi amma ya ce ta tashi ta sama masa abin karyawa, haka nan ta tashi tana makyarkyata ta fita zuwa kitchen buredi ta gasa masa a ovean ta dafa ruwan zafi ta so ko ƙwai ta soya masa amma ta kasa sai ta haɗa masa da sauran cake ɗin ta yi bai ida ƙarewa ba.  Ba ta ma tsaya ba ta koma ta kwanta shi kuma sai da ya ci ya yi nak sannan ya fita ba tare da ma ya yi mata sallama ba. Haka Ummu ta yini kwance da zazzaɓi sai can zuwa yamma ne ta ji sauƙi tun da ta sha paracetamol komai babu a cikinta ruwan lipton ta dafa ta sha sannan ta yi wanka ta ji ta ɗan samu sauƙi. Shi ne ta rarrafa ta yi ma Habib friederice mai nama tunda ba ta da hanta, abin ya ba ta mamaki ganin da wuri yau ya dawo tun kafin isha'i Sai da ya ci abinci sannan ya fita sallar isha'i kafin ya dawo Ummu ta sake yin wanka duk da ta na jin kamar zazzaɓin zai dawo mata tana jin sanyi-sanyi. Sai ta saka wata doguwar riga ta haɗa da rigan sanyi saboda ta fara rawan sanyi. Komawa ta yi ta kwanta ta rufa da bargo saboda har kanta sara mata yake yi, Habib na dawowa ya biyo ta har cikin ɗakin ganin ta a kwance bai sa ya yi tunanin ba ta da lafiya ba kawai sai ya saka hannu ya yaye bargon da ta rufa da shii. A kasalance Ummu ta ɗago tana kallon shi. "Ta shi mu yi mgana." Ya faɗa a kausashe. "Noori ba ni da lafiya zazzaɓi na ke ji." Ta faɗa cikin rawan sanyi tana ƙoƙarin sake jan bargon ta rufa ya fizge cikin mamaki ta kalle shi kafin ta samu damar magana ya tare ta da cewa. "Kin manta da maganar mu ne? Gaban Ummu-Salma ya faɗi ras!. Cikin rawan baki da na jiki ta ce. "Wa ta maga na."? Ta faɗa cikin mutuwar jiki, maganar cikin ne! Kar dai a ce Habib bai manta da mganar nan ba, kar dai a ce yana kan bakan shi. "Kin manta ne? Mganar da muka yi da ke ranar. Da man kwana uku na ba ki ki yi tunani ki yanke shawara, yau kuma cikon kwana uku shi ya sa na ce ki ta shi ki faɗa mini matsayar ki " Ummu ta ji kanta ya sake sarawa da ƙarfi da man kaɗan kaɗan yake ɗan sara mata. Maganar Habib ya sa ta ji kamar gefen kanta zai cire kallon Habib take yi cikin mamaki da gaske ya ke yi? "Me kika yanke? Za ki zubar ko a'a? Ya faɗa yana mai kallonta. Ummu ta runtse ido kafin ta buɗe tana mai dafe kanta. "Habib wai da man da gaske kake yi? "Wasa na ke yi miki? Ya katse ta a fusace. "Na ɗauka ba ka cikin hayyacinka ne." Ummu ta faɗa masa ido cikin ido saboda tana so ta samu tabbacin lafiyan Habib ƙalau. "Au kin ɗauka na fara shaye-shaye ne? Ya faɗa cikin riƙe haɓa, ita kuma Ummu sai ta ma yar da kanta a saman fito ta ma kasa magana mamaki take yi wai da gaske wannan abin da ke faruwa da gaske yake faruwa! "Ummu-Salma." Ya kira sunanta ta amsa ta na mai sake ɗagowa a lokacin ita gani take yi wasa ne ba gaskiya ba ne abin da ke faruwa. "Kin ga wasa a magana ta ne? Shuru ta yi masa ba ta yi mgana kawai sai ta ji ya daka mata wani matsanacin tsawa har sai da ta firgita "Na ce kin ga wasa a magana ta ne Ummu-Salma." Ya faɗa cikin ta da jijiyan wuya, Ummu ta firgita domin ba ta taɓa jin Habib ya yi mata tsawa irin na yau ba har ta fara hawaye. "Ba wasa na ke yi ba. Mene ne matsayar ki? Kanta dake girgizawa tana kwance amma ta kasa mgana saboda kuka ne ya taho mata zuciyarta na wani rawa rawa na ganin ko jin abin da ba ta taba tunanin gani ko ji daga bakin Habib ba. "Amsa za ki ba ni da bakin ki ba kai za ki dinga kaɗa mini ba malama." Ya sake faɗa lokaci ɗaya yana mai ɗora kafarsa a jikin gado ya ɗan duƙo yana mai kallon Ummu da ta fara rawan sanyi haƙoranta  na haɗuwa gap! gap!. Mirmishi ya yi, mirmishin da iyakarsa fatar bakinsa kafin ya ce" Ko mutuwa za ki yi sai kin faɗa mini matsayar ki." Da ƙyar Ummu ta iya miƙewa zaune tana mai kallon Habib tana hawaye. "Me kika yanke? Ya sake tambayanta wannan karon ya ɗan ɗaga murya. "Me ya sa kake son sai na zubar da ciki Habib? Me ya sa? Lafiyata kalau, ba ni da wata damuwa cikin nan kuma na sunna ne to me zai saka ka ce sai na zubar da shi? Kallonta yake yi amma bai yi mgana ba, ita kuma tana kallon shi hawaye na gudu bisa kumatun ta mamaki take yi? Mamakin Habib? Mamakin me ya sauya shi cikin lokaci ƙanƙani haka. "Kawai ina so ki zubar da shi ne." "Saboda mene? Ummu ta katse shi da sauri cikin kuka. Sai ya yi shuru bai yi mgana ba amma yana ta kaɗa kafa. "Ba zan zubar da cikin ba, sai ka ba ni ƙwaƙwaran dalilin da zan gamsu da ya cancanta da na zubar ɗin sai na bi abin da kake so." Kallonta ya ke yi cikin mamaki, bai ɗauka  Ummu za ta ba shi matsala ba ya yi tunanin yadda take son shi komai ya ce ta yi, za ta yi ba tare da ta yi masa gaddama ba amma ya ga alamun sai ya fito mata a Habib ɗin sa sannan za ta fahimci ba da wasa yake yi ba. "In kuma ban faɗa miki dalilin ba fa?? Ummu tana mai kallon shi hawaye na zuba ta ce" Ba zan bi Umarninka na saɓa ma Allah ba Habib. Ina son cikina kuma zan rene shi har ya fito Duniya. Ba zan yi ma Ubangiji butulci da kyautar da ya yi mini ba, ya tsamo ni a cikin dubu ya ba ni sai na yi masa butulci a wajen kashe rai? "Ai bai za ma rai ba malama. Babu zunubi in  an zubar da shi yanzu." Ya katse ta a fusace, Ummu ba ta san tana da ƙarfi ba sai da ta gan ta a tsaye a kan kafafunta. "Ai daga gudan jinin ne ake busa masa rai. Ka ga ko shima zunubi ne." Ummu ta faɗa kai tsaye tana mai share hawayenta. "Ban san dalilin ka ba, ko ma mene ne dalilin ka na tsayar da shawaran cewa ba zan zubar da cikin nan ba Habib." "Ko da na ce ba yanzu na shirya zama uba ba.? Habib ya katse Ummu lokaci ɗaya yana yi mata wani kallo. Cikin mamaki ta ke kallon shi, amma ta kasa mgana saboda bakinta ya yi mata nauyi. "Ko da na ce miki ba ke nake so ki zama uwar ƴa'ƴana ba?" Ya faɗa yana mai kafe ta da idanuwansa sannan lokaci ɗaya yana takawa zuwa gaban Ummu-Salma da ta kasa mgana sai kallon Habib ta ke yi, domin sai ta ke ganin kamar a mafarki komai ke faruwa. "Ko da na ce miki ban taɓa son ki ba, ba ke ba ce matar da na shirya ki zamo uwar ƴa'yana ba, a hakan za ki yarda ki haifi cikin da ni ba zan amsa sunan uban shi ba? Ummu ta ji wani jiri ya kwashe ta, ba domin ta yi saurin jingina da wardrope ɗin da ke gefenta ba da sai ta faɗi saboda yadda kalaman Habib suka ruguza duka saurin kuzarinta. Kan ta ta ji ya sake sara mata har wani duhu-duhu take gani, jikinta na rawa kamar ana mata kiɗan mazari, kallon Habib ta ke yi kamar tana tunanin in ta buɗe ido za ta ga komai da ya ke faruwa ba gaskiya ba ne. Sai dai ta runtse ido ta sake budewa still Habib ta ke gani a gabanta yana sake jadadda mata bai taɓa son ta ba. "Kin shirya ma hakan!? Ta kasa mgana hawaye ne kawai ke yi mata ambaliya, duhu duhu ma take iya ganin Habib tsabar yadda ta ji kamar ba a duniya take ba. "To ki sani in dai kin ƙi bin umarni na , kin yi taurin kai to ina so ki san wasu abubuwa guda uku." Har wajen fuskarta ya kawo kansa sannan ya nuna ta yatsa kafin ya cigaba da faɗin. "Ki sani wannan cikin ba ni da danganta da shi, tun da kika ƙi bin mganata to ki je na bar miki. Na biyu kuma da man na faɗa miki sai kin yi nadaman jayayya da ni Ummu-Salma. Na uku kuma ba zan ce miki komai ba amma zan sanar da ke daga yau kin fara bankwana da farinciki, kin ƙulla ƙawance da baƙin ciki da tashin hankali a rayuwarki, sannan kin fara rasa komai tun daga yau ɗin nan, kin rasa ni Ummu Salma. Watakila da kin bi umarnina da kin tsira da wani abun tun da kuma kika zaɓi taurin kai mu zuba mu gani." Yana gama faɗin haka ya juya zai bar ɗakin cikin ƙaraji da ihu Ummu ta ce. "To ka san ba ka sona me ya sa ka aure ni Habib?. Ta faɗa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita. Kuka take yi da dukkan muryanta da iya ƙarfinta. Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya ɗan cije baki kafin ya yi mgana Ummu ta zuɓe a kasa a kan gwiwoyinta tana sake faɗin. "Me ya sa Habib? Me ya sa haka? Me ya sa ka je ka nemi aurena a hannun iyayena in dai har ka san ba ka taɓa sona ba? Sannan ka san ba ka san haihuwa da ni me ya sa ka yi mini cikin? Kuka take kamar ranta zai fita amma bai sa Habib ya ji tausayin Ummu ba, bala'in jin haushin ta ya ke ji, domin taurin kanta adadin ɓacin ran masoyiyar shi, shi kuma duk abin da zai ɓata mata rai yana gudun shi. "Za ki san dalilin anan kusa." Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin har yana bango ƙofa yana jin ƙaran Ummu da sanda ta sake fashewa da kuka mai cike da sauti. Falo ya fito ya kasa zaune ya kasa tsaye me ya sa Ummu za ta yi masa haka? Bai taɓa tunanin za ta ba shi matsala haka ba, ƙaran shigowan saƙo daga wayarsa ne ya dakatar da shi daga tunanin mafitan da ya ke yi. "Ya ake ciki? Ta amince? Wannan lambar dai da ya yi ma saving da M.S ita ne aka sake turo masa saƙo da ita. Jikinsa na rawa shima ya ma yar da amsa. "Ba ta amince ba." Ya tura ba daɗewa sai ga shi an dawo masa da amsa. "Duk da ka faɗa mata cewa ba ka taɓa son ta ba? Shi ya sa ba za ka so haɗa zuru'a da ita ba? "Na faɗa mata." "Me ya kamata ka yi a yanzu? "Na kasa samun mafita." "Ka sake ta Habib." Shuru ya yi kafin ya rubuta amsa. "Zan sake ta. Amma sai na nuna mata kuskurenta sai na saka ta yi nadaman sanina a rayuwarta. Sai na saka ta ji dama ba ta yi mini gaddama ba tun fari. Sannan daga karshe na yi mata sakin wulaƙanci da ƙasƙancin da ba ma ita ba dangin ta ma  ba za su taɓa mantawa da ni ba" "Good Job.. Cikin jikin ta fa? "Zai fita ko tana so ko ba ta so." "Ka aiwatar da hakan da gaggawa domin ka san ba mu da lokaci" "Ki yarda da ni." "Na daɗe da Aminta da kai Masoyi na" Saƙon ƙarshe ya saka shi farinciki har sai da ya murmusa, wayarsa ya ma yar cikin aljihun wandon jikin shi, ya fara safa da marwa yana tunanin yadda zai yi sanadiyar zubar cikin jikin Ummu Salma ko ta karfin tsiya, yana jiyo kukanta a cikin ɗaki amma ko a jikinsa tunanimsa kawai ta ina zai samar masa da kansa mafitar zubar da cikin nan? Domin bai shirya ba, kuma ba akan Ummu Salma ba. Abin da bai sani ba, wannan gudun jinin sai an busa masa rai kuma sai ya shaƙi iskar duniya, duk abin da zai yi Ubangiji ya riga da ya gama na shi. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *05* Ummu-Salma ta sha jin wata hausa a bakin hausawa. Da sukan ce wai yadda na ga rana haka na dare,  ta ɗauka wata mgana ce kawai ta shaɗi faɗi, wacce ba ta da tushe ballanta makama, ita a da in aka ce mutum ya kwana bai yi barci sai ta yi ta mamakin me zai hana shi barci? ta ɗauka sai in an yi maka mutuwa ta uwa ko ta uba, ko ciwo ita bai hana ta barci. Sannan Ammah da Baffa duk suna raye kuma duka yayyenta ba wanda ta taɓa rasawa. Sannan tun tasowarta take cikin farinciki da gata. Har haɗuwarta da Habib da yadda ya shafe wattani takwas ya na nuna mata fassaran so da ƙauna a baki da aikace. Ba ta taɓa riskan kanta a yanayin da ta kwana a ciki ba ranar. Har aka kira sallar asuba idanuwanta biyu suna kuma masu zubar da ƙwalla ko sun gaji sun haƙura da zubar ƙwalla ba a ɗaukan lokaci za su dawo suna kwarara kamar an buɗe famfo. Tunanin ta guda ɗaya ne, yanzu duk wannan soyayya da ƙaunar da Habib ya nuna mata duk na ƙarya ce? In tana so ta aminta da mganar shi sai ta ji ta kasa ta fi gasgata da gaske Habib na son ta ɓacin rai ne ya sa ya faɗi wannan mganar, amma in yana son ta me ya sa ba ya son haɗa zuru'a da ita? Ta kwana a ƙasan cafet jingine da wardrope ba ta damu da komai ba, ita kawai fatan ta, ta buɗe ido ta ga komai a mafarki ne in kuma da gaske ne to ya kasance Habib ya zo ya ɗuka yana ba ta haƙuri ya ce duka mganganun da ya faɗa ba gaskiya ba ne, sai hakan bai faru ba har garin Allah ya waye ba ta sake ganin Habib ba, ba a ɗakin barcin su ya kwana ba sannan ko da ta rarrafa ta fita da safe ta iske shi ya bar gidan. Kukan da ta kwana yi ya taimaka wajen sake sakar mata zazzaɓi mai zafi, tana kwance tana hawaye in ta gaji ta yi kuka salla ne kawai ke ta yar da ita tun jiya ta kasa saka komai a cikin ta sai dare da ta ga za ta mutu ta sulala indomie da ruwan tea ta ci shima ɗin bai zauna ba ta amayar da shi, ruwan zafin ta sake sha shi ne ya samu zama a cikinta. Yadda ya bar ta da ajiyan da daddare haka ya sake dawowa ya iske ta kwance a falo tana rawan sanyi. Yadda bai ce mata sannu ba itama ta yi alƙawarin ba za ta sake yi masa mgana ba sai shi da kan shi ya gano ya yi mata laifi ya ba ta haƙuri, tunanin Ummu-Salma Habib na son ta kuma zai dawo gare ta domin ya ba ta hakuri su daidaita kansu har a wannan lokacin yardan da ta yi ma Habib bai samu nakasu ba. Tsayin kwana biyu ba ta da lafiya sannan ta warware tun da ta na shan pracetamol amai kuma da man laulayi ne ba shi da magani, a kuma kwanakin nan magana ta fatar baki ba ta sake haɗa Ummu da Habib ba, ya sauya akalan zaman su gabaɗaya. Ba ta sanin fitan shi ba ta sanin dawowar shi, sannan ya daina kwana ɗaki ɗaya da ita, ya koma yana kwana a ɗayan bedroom ɗin da daman na shi yawancin ma kayan sa suna ciki ne, kawai shi ya ce ya fi son na ta ne saboda yana da tiolet a cikin ɗakin saɓanin ɗayan sai an fito yana tsakiya shi ya raba bedrooms ɗin su guda biyu. Da ta ji sauƙi ta fara yin abinci ta jera a saman dinning da beakfast kamar yadda ta saba sai dai yadda ta ijiye haka take ɗauka, sun kwashe sama da sati a haka tun Ummu na tunanin nadamar Habib har ta fara sarewa, ta dawo tana gaishe shi in sun haɗu da safe amma bai taɓa amsata ba, yadda ya ke yi ma a cikin gidan kamar bai taɓa sanin ta ba. Saboda in ya dawo ba ya neman ta ballanta ya san a wani hali take ciki, abin da ya faɗa ne yake aiwatar wa da man  ya ce sai ta yi nadaman ƙin bin umarninsa tun kuma tafiya ba ta yi nisa ba Ummu ta fara nadama sai dai ba ta jin za ta iya zubar da cikin jikinta, abin da ke damunta ta kasa jin haushi Habib a cikin zuciyarta da duk da irin yadda zaman auran su ya sauya. Ta kwana kuka ta yini kuka duk ta rame ta lalace ta kuma ta kasa tattauna mganar da kowa, tunanin ta da hangen ta Habib zai dawo ya ba ta hakuri ba za ta yi saurin fallasa sirrin auran ta ba, sannan tana son shi har gobe Habib na nan da wannan matsayin a cikin zuciyarta ta kasa jin haushin shi ko kaɗan a cikin zuciyarta. Da a ce wani ɗan'uwanta zai gan ta a yanayin da ta ke ciki sai ya yi gaggawan tambayan ta ko wani abu na damun ta ne, saboda yadda Ummu-Salma ta koma, ta sake yin fari ta ɗashe ga shi tana laulayi mai zafi ba ta iya cin komai sai ruwan lipton in dai ta ci abinci sai ta amayar da shi, yini take yi a kwance kamar ruwa amma babu ruwan Habib, tana jin shi zai shigo da daddare sosai tun da zaman su ya sauya sai ya kai sha ɗaya na dare a waje bai dawo ba in ko ya dawo yana ɗayan ɗakin sai dai ta ji shi yana ta waya ba kuma za ta iya gane da wanda yake yin wayar ba. Wani lokacin sai in ta ji zai fita ne da sassafe sai ta rarrafa ta fita falo in ya fito ta gaishe shi amma bai taɓa amsawa ba har ya saka kai ya fita ba zai sake kallon ta ba. Duniyar duk ta yi mata ƙunci ba abin da ke yi mata daɗi, kowa sai ya ji ta ɗif kamar ba ta nan Ammah duk rashin nuna kulawanta ga Ummu sai da ta kira ta, an ci sa'a ma ranar wayar na kusa da ita domin kwana biyu nan sai a hankali ko iya amfani da wayar ba ta yi saboda kasala da zazzaɓin da ta ke fama da shi. "Ummu kwana biyu daga ke har megidan na ki mun ji ku shuru ina fatan dai kuna lafiya? Haka Ammah ta faɗa bayan Ummu ta ɗaga wayar. Lokacin da ta amsa mata da lafiya sai da ta danne bakin ta saboda kuka take yi hawaye sun kece mata amma ta kasa iya faɗa ma Ammah wani abu. Tunanin ta Habib zai dawo zai yi nadama sannan zaman auren su zai gyaru bai kamata ta yi gaggawan fallasa sirrin gidan auran ta ba shi ya sa ta daure ta ce ma Ammah zazzaɓi suka yi ta yi ita da Habib kwana biyu shi ya sa a ka ji su shuru amma duk sun samu sauƙi. Ammah ta yi fatan ƙara samun sauƙin su sannan suka yi sallama to shi ma Baffa haka ya kira ta yana tambayan ko tana lafiya. "Lafiya ta ƙalau Baffa." Ta ba shi amsa da fillanci, shima ba ta faɗa masa komai ba sannan ba ta bar shi ya fahimci wani abu ba. Mami ma da ta ji ta shuru sai da ta kira ta, itama ce ma ta ta yi zazzaɓi suka yi ta fama da shi a kwana biyu nan. Baɗɗo ma sai da ta kira ta, ta ce a online kwana biyu ba ta ga ta hau ba itama dai ƙaryan ta yi mata na zazzaɓin sai ta ce satin nan za su gama jarabawa za ta zo ta duba ta daga haka suka rabu. Abin da ya ba ta mamaki yadda Bestie ba ta kira ta ba sai da ta kunna Data sai ta ga ta yi mata mgana ta faɗa mata za ta kashe wayarta sai dai lokaci bayan lokaci za ta dinga kunnawa har su gama jarabawa, shi ya sa ba ta san ta yi kwana biyu ba ta online ba. Sannan dalilin da ya sa ba ta kira ta ba kenan. Sun shafe wajen sati uku a haka ita da Habib ba abin da ya canza, ba ta sake tsinkewa da lamarin Habib ba sai da ta kama shi yana saka mata wani abu a cikin zoɓon da ke cikin frezer ɗin ta. Abin da bai sani ba ita yanzu ko ruwa ba ta sha ya zauna mata ballanta wani zoɓo tun wanda ta haɗa ne kafin zaman su ya lalace ta ma manta da shi. Da daddare cikin ta na ta juya mata saboda yunwa domin yini ta yi ba ta ci abinci ba, ba ta san shigowar Habib gidan ba tun da ta samu barci ya ɗauke ta sai a lokacin ta farka da agogon wayarta ta yi amfani ta duba lokaci. Ƙarfe 2:43am na dare, tana fitowa sai ta ga kitchen da ɗan hasken fitila ita da farko ma ta tsorata shi ya sa ta yi tsam, ta fara takawa salaf-salaf ta leƙa kitchen ɗin tun da ƙofar a buɗe ne daidai ya na saka wani abu a cikin zoɓon da ba za ta iya tantance mene ne ba, amma koma mene ne ba abu ba ne mai kyau tana da tabbacin haka, ba abin da zai ta da mutum cikin dare yana zuba wani abu a cikin abin sha kuma ace alheri ne. Ba ta bari ya lura da ita ba bakin ta alaikum ta koma ɗakinta ta faɗa kan gado ta na mai fashewa da kuka matsananci, kuka take yi kamar ranta zai fita ta yi ta tunanin mene ne dalilin Habib na aikata haka? Sai wata zuciyar ta bata amsa da cikin jikin ki, tabbas ko ta amince ko kar ta amince cikin jikin ta ne Habib ya yi alwashin sai ya fidda shi ko ta ƙarfin tsiya. Ita kuma yanzu ta ji ma tana sake ƙaunar cikin ta, ta yi alƙawarin komai zai same ta sai ta kare shi ta zame masa garkuwan yadda Habib bai isa ya matso kusa da shi ba. washegari Habib na fita ta je ta kwarara wannan zoɓon a tiolet ta zuba masa ruwa ya wuce. In da ta sake tabbatar da zargin ta a daran da ya dawo har ɗakin sai da ya leƙa ta ya ɗauka zai gan ta a galabai ce wata ƙila cikin ya zube amma bai fahimci komai ba a fusace ya buga mata ƙofa ya fice ya bar Ummu da hawaye a fili tana tambayan kanta. "Me ya sa Habib? Me ya sa haka? Tana mai ƙara kecewa da kuka da ƙarfi har yana fidda Sauti a cikin zuciyarta ta ke jin wani zafi da radaɗi, gani ta ke yi kamar ba rayuwarta ba ce, ita fa ce Ummu-Salma wacce Habib ya nuna duk duniya ba shi da kamarta amma kalle ta a cikin gidansa kashi ma ya fita daraja, duk da ya ce bai shirya zama uba ba, sannan ba ya son ta shi ya sa ba zai iya haɗa zuru'a da ita ba. Ita tana son shi har kuma gobe ba ta ji ta cikin nadaman auren shi ba wallahi tana son Habib kuma za ta yi komai domin ta ga ta tsira da mijinta da auran ta. ** *3:45am* Habib ne a cikin ɗakin sa ya kasa zaune ya kasa tsaye,  kansa har sara masa yake yi saboda damuwa da tunanin mafita? Wani amsa zai ba ma Masoyiyar shi in ta tambaye shi labarin cikin da ke jikin Umma-Salma? Ya faɗa mata cikin na nan bai zube ba, ya saɓa alƙawari domin ba haka suka yi ba, shi kuma duk wata hanya da zai bi domin Ummu ta saduda ya bi amma taurin kanta ya wuce tunanin shi, ya ɗauka matakin da ya fara ɗauka akanta zai yi tasirin da za ta neme shi ta bashi hakuri, salim alim a zubar da cikin nan ya gama more sadakin sa sannan ya kaɗa ta amma ta nuna masa ita ɗin mai taurin kai ne, saboda rasa mafita ya sa ya je ya siyo mganin barci sleeping pills ya saka mata da yawa a cikin zoɓon da ya san tana so sosai amma ya fahimci kamar ko ta sha bai yi mata komai ba. Sannan ya duba bai ga roban zoɓan ba in da a ce tasha yana da tabbacin ba a gida zai gan ta  ba sai dai a kira shi a ce tana asibiti amma yanayin da ya ganta ya ba shi tabbacin wannan karon bai samu mafita ba. Hannun shi guda ɗaya ya buga a ɗayan, lokaci ɗaya yana mai dafe kan shi cikin matsanancin damuwa na rashin mafita,  me ya sa Ummu-Salma ta kasa gane wa ne?  Ita duk maganganun da ya faɗa mata ba ta yarda ba ya son ta ba? Ba ta yarda ba ita ce zaɓin sa ba, ko kuwa sai ya zauna ya yi mata gwari-gwari ne sannan za ta  gane manufar auran shi da ita, yana cikin wannan tunanin wayarsa dake yashe saman gado ta fara vibration yana kai idanuwan shi wajen sai da gaban shi ya faɗi. "M.S..! Ita ce ke kira, a kuma yanzu ba shi da amsar da zai ba ta, ya na ta falling ɗin ta yana ta gazawa. Me ya sa ya yi wannan wawancin tun farko bai kai Ummu Salma an cire mata cikin nan ba tare da ta sani ba? Ba ya bukatar barin wani abu na shi a rayuwar Ummu Salma, bukatar shi in ya gama biyan buƙatar shi da ita ya sake ta shike nan babu wani sauran alaqa, sannan ba haka suka yi da Masoyiyar shi ba ya riga ya yi mata alƙawarin ba wata macen da za ta fara haifa masa zuru'a sai ita, kuma ba ya son saɓa wannan alƙawarin a matsayin shi na namiji, kwata-kwata ya rasa mafita duk yadda ya ɗau lamarin kamar wasa ba wasa ba ne, lamarin na bukatar ya yi aiki tukari akan haka in ba haka ba daga baya zai zo ya yi fargar jaji alhalin lokaci ya riga ya ƙure masa. Ganin ba za'a daina kiran ba ne, ya san halin mai kiran da saka damuwa , kuma so ta ke ta ji yadda labarin cikin jikin Umma ya tsaya shi kuma ba shi da wata amsa mai daɗin da zai iya sanar da ita. Kiran na ƙarshe da ya katse ba a sake kira ba sai can ba daɗewa sai ya ji ƙaran shigowan saƙo hannunsa na rawa ya jawo wayar ya buɗe saƙon "Habib ko ka ɗaga kirana ko gobe na zo gidan ka, koma me zai faru sai da ya faru. Ka amsa kirana." Haka aka rubuta a jikin saƙon, jikinsa na rawa yana ƙokarin kiran lambar sai ga shi an sake kira a sanyaye ya ɗaga amma bai yi mgana ba. "Habib me ya faru ne? Aka tambaye shi, daga can cikin sanyin murya kuma muryan ta mace ce. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"  Ina tunanin cikin yana nan" Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai shafa kansa cikin damuwa. "Kana ma tunani ne ba ka da tabbaci Habib? Aka sake faɗa wannan karon cikin ɗaga murya. "Walahi na saka mata kamar yadda na faɗa miki. Sai dai..." "Sai dai me? Ta katse shi a fusace. "Ina tunanin ba ta sha ba." Wani ɗan ihu aka saki acikin wayar daga can bangaren. "Ki yi hakuri zan samo wata mafitar." "Wata mafitar! Ai ka daɗe da rasa damar ka Habib. Tun farko kai ka jawo mana wannan matsalan tun farkon auran ku na ce ka sa a yi mata planning yadda wanzuwar ciki a jikinta ba zai ba mu matsala ba, ba ka aminta da shawarana ba ka zauna a tunanin shekara ɗaya ya yi kaɗan ɗin da za ta samu ciki, ka manta da yanzu aure ma ba a shekara ake haihuwa, cikin ta na farko ba domin Allah ya yi zubewar shi da shi ma ya bamu matsala wannan ma Habib ka kasa yin wani tunani? Sai da na ce maka kar ka sanar da ita komai ka ɗauke ta ka kai ta asibiti a zubar da cikin ka kuma sake ta daga can amma ka ce ba haka ba na ka tsarin za a bi yanzu ga in da na ka tsarin ya kai mu. Haba Habib ina jin kamar na haukace in na tuna jakar yarinyar ce ta riga ni aje ƙwan haihuwarka a mahaifarta ji na ke yi kamar zan suma saboda baƙin ciki." Ta karishe faɗa cikin ƙaraji, jikinsa har rawa yake yi wajen zayyano mata kalaman ban haƙuri da rarrashi. "My love kin ga kwantar da hankalin ki, ni na yi miki alƙawarin bayan ke babu wata macen da ita isa ta fara haɗa zuru'a da ni. Ki kwantar da hankalin ki dole cikin nan ya zube a goben nan in sha Allahu." Ya faɗa cikin sigan lallashi, daƙyar har yana ɗan ɗaga hannu kamar tana ganin shi. Shuru na wani lokaci daga can bangaren kafin ta sauke numfashi ta ce" Habib ka san ina son ka shi ya sa na ba ka damar yin abin da kake so ko? "Na sani." "To kar ka ba ni kunya. Kar ka saka na cire yaƙini na a kan ka." "In sha Allahu, gobe zan ɗauke ta mu je asibiti a cire cikin nan ko tana so ba ta so." Dariya aka yi daga can bangaren kafin ta ce" Habib kar ma ka fara, in ka yi haka za ka yi nadama. Yadda Ummu ta san manufarka akan cikin jikinta ko Saudiya ne ba za ta sake aminta da kai ba balle har ta haɗa tafiya da kai. Ka samo wata mafitar dai." Sai da ta faɗa kuma ya fahimci haka yadda ya bayyana munafarsa ba lalle Ummu ta sake aminta da shi ba amma duk da haka ba zai sare ba zai sake jaraba sa'ar shi sun daɗe suna waya yana faɗa mata kalaman soyayya cikin lallashi har sai da ya tabbatar da hankalinta ya kwanta sun rabu da cewa duk yadda zai yi zai yi na ganin cikin nan ya zube a gobe in sha Allahu. Su sun gama na su tsarin, abin da kuma ba su sani ba Ubangiji shi ya riga ya gama nashi. A cikin zanen kaddaran su Ubangiji ya rubuta cewa Habib da Ummu za su samar da gudan jini, daga gudan jini zuwa rai. *** Wani abu ya ba ma Ummu mamaki da ya sa kuma ta fara shakku, lamarin Habib yanzu ya zama abin tsoro da taka tsan-tsan a wajen ta. Shigowa fa ɗakin ta ya yi da safe kafin ya wuce wajen aiki yana tambayan ta ya jikin ta yana fatan ba ta da wata matsala. Tsabar mamaki sai ta kasa mgana, tana kallon shi yana yi mata mirmishi, mirmishin da har cikin zuciyarta ba ta yarda da shi ba. "Sannu, Baby zan tafi wajen aiki, amma ina so ki yi mini girki da kwalliya yau in na dawo za mu yi mgana." Har ya fice daga ɗakin tana bin shi da kallo bakin ta sake ta kasa mgana wata zuciyar na faɗa mata Ko dai ya saduda ne, wata ƙila ya gane kuskuren shi ne zai ba ta haƙuri, da ya ke tana son Habib ta kuma aminta dashi shi ya sa wata zuciyarta ta rinjaye ta da cewa hakuri zai ba ta, ayayin da wata zuciyar a can gefe tana ɗan ɗari-ɗari alamun ba ta aminta da saukowan Habib lokaci ɗaya ba. Sai dai duk da haka ba ta fasa yin abin da ya ce ba, yamma na yi ba ta ko jin daɗin jikinta ta miƙe ta fara aiki Baɗɗo ma ta kira ta a waya ta ce tana tunanin za ta shigo sai ta ce mata ta bari sai gobe, acikin ranta tana murna da farinciki na daidatawar ta da Habib ko da Baɗɗo za ta zo gobe ba za ta fahimci komai ba. Farar shinkafa ta dafa da miya sai salat. Har da kunun aya ta yi duk da tana yi tana faman hutawa domin sai ta ke jin numfashin ta na yin sama sama kamar zai ɗauke. Ko kafin mangariba ta gama komai sai da ta idar da salla sannan ta rarrafa ta yi wanka tana jin jikinta ya yi zafi zazzaɓin jikinta ya dawo, ammma haka nan ta yi masa kwalliya cikin wata doguwar riga baka mai kwalliyan ja a jikinta shi ya sa ma mayafin rigar ja ne, ta yi kyau duk da ba kwalliya ta yi ba amma fuskarta ta yi mata fayau kamar wacce ta shekara tana jinya. Da wuri Habib ya dawo tun kafin ma a kira sallar isha'i ya shigo  gidan da niƙi-niƙin ledoji ya siyo balangu da su lemon exotic. Yana ganin ta ya buɗe mata hannuwana ya ce ta taho ita dai ba ta saki jiki ba, ta tafi gare shi ya rumgume ta yana wani shinshina wuyanta cikin sanyaya murya ya ce. "Na yi kewar ki Baby." Hawaye suka kece ma Ummu, amma Habib bai bar ta haka ba sai da ya ɗago ta ya saka harshen shi yana lashe mata hawayen fuskarta, daga nan ya fara yamutsa ta, duk da zuciyarta na son ta hana shi amma ta kasa cewa ta ke yi Habib ne, Habib ne fa mijinta masoyinta. Tun a falo ya raba ta da rigan jikinta sanyi take ji shi ya sa duk tsigan jikinta ya tashi ga shi jikin na ta ya ɗau zafi amma Habib bai lura da wannan ba. Haka ya iza ta zuwa cikin bedroom ɗin su ya mora jikin Ummu fiye da yadda ya saba mora tana ji ana ta sallar isha'i a masallatan kusa da su amma Habib bai saurara mata ba, ta gaji ba za ta iya ba amma bai fahimta ba, lamarin na shi babu tausayi da ya kawo kamar zai sauka sai ya koma tun Ummu na kuka a ɓoye har ta dawo tana yi a sarari babu in da jikinta ba ya rawa, sai ta ji kamar ba Habib ba sai ta ji yau ba ta ji daɗin abin ba kwata kwata ta ji wani haushi na sukan zuciyarta amma bai saurara mata ba sai da ya gaji domin kan shi ya kuma tsallake ta ya shiga tiolet domin tsarkake kan shi. Kanta ta tusa cikin bargo tana kuka amma  ta rufe bakin ta kar ya yi sauti, tana jin shi ya fito yana ce mata ta tashi ta yi wanka su ci abinci yana jin yunwa, ko tsayawa bi ta kanta bai yi ba ya fice ya bar ta nan kwance tana kuka. Da kyar ta iya rarrafawa ta shiga tiolet mene ne ya sa Habib ya yi mata haka! Ko yana so da karfin tsiya sai ya yi ajalin cikin jikin ta ne, Allah ya fi shi domin tun da ta gano manufarsa ta ke saka shi cikin addu'o'in ta na Allah ya tsare ta ita da cikin ta daga sharrin Habib, amma me ya sa har yanzu ba ta daina jin ta daina son Habib ba, tana son shi tana son cikin jikinta sannan tana son auransu shi ya sa yau ɗin ma ta kasa yi masa gaddama. Jikinta zazzaɓi ne rau haka ta rarrafa ta fito ta sauya kaya ga shi kanta ya jike kuma ciwo yake yi mata ba ta ko samu damar busar da shi ba Habib ya zo ya dame ta da cewa yana jin yunwa haka ta fita daga ita sai wata riga doguwa ta wani yadin material ita ce a farkon wardrope shi ya sa ta saka ta. saman dinning suka zauna ta yi serving ɗin shi ganin ita ba ta saka ma kanta ba ya sa ya tambayeta a sanyaye ta ce ba ta ci ko ta ci sai ta yi amai. Sai ya ɗauko mata balangun da ya siyo ya ce ta ci ko kaɗan ne. "Ba zan iya ci ba." Ta faɗa a sanyaye ajiye spoon ɗin hannun shi ya yi yana kallon ta hannunta guda ɗaya ya kama yana faɗin" Sannu Sorry ki ci ko kaɗan ne sai ki sha wannan lemun in sha Allahu ba zaki yi Amai ba" Tana cewa ba za ta ci ba yana ɗaukowa ya nufi bakinta da shi tana kauda kai amma sai da ya saka mata shi a cikin bakin ta da ta tauna sai ta ji daɗin shi, shi ya sa sai ta sake ɗauka ta kai bakinta tana taunawa lokaci ɗaya tana kallon shi. "Kin gani, ba za ki yi amai ba" Ya faɗa yana yi mata mirmishi, yake ta yi masa ba ta yi mgana ba, abin da ya ba ta mamaki da ya sa ta sake jin a ran ta cewa Habib ba shi da gaskiya, lemun exotic guda biyu ya siyo da zai tsiyaya mata na ta dabam ne, na shi ma na dabam sai ta fara tunanin tunda sha za su yi me ya sa sai ya buɗe har guda biyu, kawai sai ta ji ba ta aminta da cewa Habib ba yana wannan abin don Allah ba ne. Yana yi ne ba domin komai ba sai domin cimma manufar da ya so ta biye mishi ya aiwatar. Ita kuma ta shirya masa da sanin ta ba za ta taɓa bari ya yi galaba akan ta ba. Guda huɗu ta ci balangun sai ta cire hannunta da sauri ya kalle ta." Kin ƙoshi kenan? Sai ta jinjina masa kai, da sauri ya miƙo mata lemun da ya saka kofin tangaran yana faɗin" Sha wannan sai naman ya kwanta miki yadda ba za ki yi amai ba." Kallon shi ta ke yi kafin ta ce ta ƙoshi. "Sha mana." Ya sake faɗa yana tura mata kofin a bakinta da sauri ta kauda kai, maimakon Habib ya bar ta haka sai ga shi har yana miƙewa ƙoƙarin sa ya tura mata wannan lemun na dole sai ta sha ganin haka kawai ya ba ta tabbacin koma mene ne yana cikin wannan lemun na hannun Habib. Ganin ta yi Habib na neman yi mata ɗure, tunda ya tashi daga zaune ya matso kusa da ita, ya rike kanta yana tura mata kofin zuwa bakin ta yana faɗin ta sha. "Ki sha mana." Ya faɗa yana kallonta. "Na ƙoshi, zan yi amai in na sha." Ran shi ya fara ɓaci ko ta fahimci akwai wani abu a cikin lemun ne " Ki sha na ce miki ba za ki yi Amai ba." "Ba na so na sha." Ummu ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙokarin miƙewa zaune shi kuma bai sani ba ya kawo hannun shi sai ta kaɓe kofin da lemun suka tarwatse a saman dinning ɗin. Jikin Ummu na rawa take kallon shi, shi kuma lemun da fashasshan kofin ya ke bi da kallo ran shi na ɓaci. "Ka yi haƙuri." Bai ce mata komai ba ya wuce kitchen ya sake ɗauko wani kofin ya zuba mata yana faɗin" Wannan ki sha, ki sha na ce Ummu Salma kafin ki ɓata mini rai." Ai kafin ya nufota ta bar wajen Dinning ɗin zuwa falo sai ya yi tsaye da lemu a hannun shi yana kallon ta. "Ke me ye haka? Ya faɗa ganin Ummu ta nufi bakin ƙofa ta tsaya. "Dawo nan malama." Ya faɗa yana takowa tsakiyar falon. Ummu ta sake matsawa jikin kofa ta saka hannu ta murza key ɗin ta buɗe ƙofar lokaci ɗaya tana faɗin" Na ce ba zan sha ba dole ne." "Dole ne, dole ki sha wannan lemun domin cikin jikin ki ya zube." Ya faɗa cikin tsawa har yana zare mata idanuwansa Da man ta san za a rina hawaye suka kece mata cikin rauni ta ce" Me ya sa Habib? Wai me ya sa kake son raba ni da gudun jinina ne? "Saboda bana so ki haihu. Ban shirya hakan tare da ke ba." "To me ya sa? Ummu ta katse shi a tsawa ce da karfi sai kawai ya tsaya yana kallonta ga ƙofa a buɗe kar saboda hayaniyarta ta tara musu jama'a da ya shiga uku. "Ki dawo cikin falo mu yi mgana." Ya faɗa yana ɗan kwantar da murya har lokacin kuma lemun na hanmun shi dama yake so ya samu ya yi mata ɗuren shi chemist ɗin da ya siya mganin mai wajen ya ba shi tabbacin in ya saka mata guda biyu a cikin lemu ya tabbatar ta sha ko kaɗan ne cikin nan ba zai kwana ba zai zube, hankalin shi da natsuwar kawai yanzu ya ga cikin nan ya zube, idanuwansa sun rufe kawai cikar burin sa ya ke nema ko ta halin ƙaƙa ne. "Ummu-Salma ki rufe ƙofar nan ki dawo nan ki zauna ki karɓi lemun nan ki sha tun kafin raina ya ɓaci." Ya faɗa yana kallonta ita ko sai ta sake matsawa kamar za ta fita tana faɗin" Wallahi ba zan sha ba, kuma kana cewa za ka matso ni zan fita na yi maka ihu." Ta faɗa cikin kuka yadda ta yi ɗin ya san za ta aikata haka, shi kuma ba zai so mutane su taru akan sa ba, kowa ya ji ga abin da ke faruwa za a ba ma rashin gaskiya. Kansa ya dafe da hannu ɗaya da yake jin yana sara masa lemun ya koma ya ajiye a saman dinning sannan ya dawo tsakiyar falon yana faɗin. "Ki dawo nan mu yi mgana " "Ba zan dawo ba," Ummu ta mayar masa da amsa  da iya gaskiyan ta domin tana da tabbacin in har ta bari Habib ya kama ta to ba cikin jikinta ba har ita zai iya yi ma lahani tun da alamomin sa sun nuna duka abin da ya faɗa gaskiya ne. Ba ya son ta sannan ba ya son haɗa zuru'a da ita, ya faɗa ya kuma nuna shi a aikace kamar yadda yake nunawa yanzu. Habib ya fara rasa control ɗin shi, ya nufi Ummu da sauri ita kuma ta fita waje ya fito sai ga megidan flat ɗin gefen su, yadda ya gan su kamar zakaru ne ya sa ya ɗan tsaya ganin shi ya sa Habib ya yi saurin wayancewa da cewa" Baby mu yi wasan a ɗaki mana kin ga nan saboda dare" Jin haka yasa magidanci ya yi mirmishi ya wuce yana shigewa shashen shi Habib ya kalli Ummu cikin tsana da baƙin ciki ya ce. "Ke wata irin daƙiƙiya ce, komai sai an yi miki bayani ne za ki gane? Ya faɗa a fusace har jijiyon kansa sun miƙe saboda yanayin da ya ke ciki. "Sau nawa zan faɗa bana son ki, ba kuma don ki haihu na auro ki ba." Ya faɗa yana yarfa hannnuwansa yarinyar nan tana so ta bashi matsala tana so ta rusa duka shirin sa. "To in ba ka sona ba ka son ka haihu da ni me ya sa ka aure ni.? Sannan me ya sa ka yi mini ciki? Ai ka san ba ni na ba ma kaina cikin ba." Ummu ta sake tambayan shi cikin kuka hawaye na kece mata Kallon ta ya yi, tabbas ya yarda ita daƙiƙiiya ce sai ya yi mata bayani? Sai ya furta mata dalilin da ya sa ya aureta sannan za ta gane lalle ya yarda dakikiya ce Ummu ba ta da lissafi. Tsaki ya ja kafin ya ce" Lalle na yarda rashin ilimin boko mai zurfi ya cuce ki, tunda har yanzu tunanin ki bai faɗa miki dalilin da ya sa na aure ki ba." Yana gama faɗin haka ya juya ya koma cikin ɗaki, ya bar Ummu na tsiyayan hawaye. Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahaman sun sha nuna mata akwai ranar da za a iya goran ta mata rashin karatun ta mai zurfi a bangaren boko, ɗauka ta ke yi suna faɗa ne saboda ta yi zuciya ta ce za ta yi, sai yau da Habib ya goran ta mata ta sake aminta da maganar su, sai dai har a lokacin ba ta yi nadamar haka ba, ba ta son karatu har kuma gobe ba ta so iya sakandirin da ta gama ya ishe ta zaman duniya tunda tana da na muhammadiyan fiye da yadda ta samu na bokon, Hamma Saddam ya taɓa faɗa mata wata rana tana ji tana gani za a yi mata gorin ilimi sai ga shi yau Habib ya yi mata, hawaye ke kwaranyo mata ga jikinta ya sake ɗaukan zafi saboda sanyin da ta sha, tana son komawa ciki amma tana tsoron ka da Habib ya shirya mata wani gadan zaren, ba ta koma ciki ba sai da ta tabbatar da ba shi a falon sannan ta lallaɓa ta shige ɗakin ta ta rufe ta kwanta a saman gado ta fashe da kuka. "Wayyo ni Ummu-Salma Ubangiji ka kawo mini agaji" Ta faɗa a fili tana mai dafe kanta da ta ji yana sara mata, me ya kamata ta yi? Zama tare da Habib yana neman yi mata illa da karfin cin tuwo ba nata ba ne, ya kamata ta sanar da wani abin da ke faruwa. Ta daɗe kwance tana kuka amma ta rasa mafita, kunya ta ke ji da nauyi yadda kowa a dangi da ƙawaye suke yi mata kallon wacce ta yi dacen miji yanzu kuma ta je da wannan mganar? Amma in ba ta faɗa ba akwai yuyuwar ko ta ƙarfin tsiya sai Habib ya cimma burin sa na raba ta da cikin nan ita kuma ba za ta bar shi ya cika wannan burin ba, har ta rarrafa ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ba ta samu mafita ba tana salla tana kuka bayan ta idar ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah ya tsare ta daga sharrin Habib ya kuma tsare cikin jikin ta. Haushin kanta take ji da har a lokacin ba ta ji ko da son Habib ya ragu daga cikin zuciyarta ba, sai ma ta ji kamar ana ƙara hura wutar ƙaunar sa ne a cikin zuciyanta. A saman darduman da ta yi sallan ta kwana cikin matsanan cin ciwon jiki da kai, sanna ga zazzaɓi mai zafi sallar asuba ma sai da safe lokacin akwai hasken rana sannan ta samu damar yi,  shima a zaune saboda jiri take gani in da ta idar nan ta sake sulalewa ta kwanta numfashinta na sarƙewa ga zafin zazzaɓi kamar za ta mutu, ganin ta yi in ta cigaba da zama a cikin ɗaki za ta iya mutuwa Habib ba shi da asara ya sa ta rarrafa zuwa saman drowers ɗin gefen gadon ta lalubo wayarta Ummin ikki take da niyar kira amma dishi dishi ta ke gani tsabar zafin zazzaɓi. Wayar na hannunta kira ya shigo ba ta iya gane sunan saboda yanayin da ta ke ciki ta samu dai ta yi ƙarfin halin ɗaga kiran sai ta ji muryan Baɗɗo. "Sisna gani a ƙofar bangaren ki, ina ta knooking shuru ko bakwa nan ne? Jin muryan Baɗɗo da abin da ta ce ne ya sa ta ji kamar an buɗe mata idanuwanta wani karfi ta ji ya zo mata da ya sa muryatan a dishe ta ce. "Ga ni nan zuwa." Sai ta sauke wayar a saman gado da taimakon gadon ta iya miƙewa tsaye tana dafa bango har ta buɗe kofar Bedroom ɗin ta fita falo tana dafe da bango, ƙofar ma a buɗe take Habib ya fita ita kuma ba ta san ma fitan shi ba, ballatana ta taso ta rufe. Ita kuma Baɗɗo ba ta murɗa handel ɗin ba a tunanin ta ƙofar na rufe ne kamar yadda Ummu ta saba rufewa sai an yi knooking take zuwa ta buɗe ma wanda ya zo. Tana buɗe ƙofar suka yi arba da Baɗɗo wacce sai da ta tsorata da ganin yadda Ummu Salma ta koma. "Ummu lafiya.? Ta faɗa cikin fizgo mganar, ita kuma Ummu jiri ya kwashe ta sai kawai ta faɗa ma Baɗɗo a jiki, da sai da ta saka ƙarfi ta iya riƙe ta suka shiga cikin falon da kafa ta rufe ƙofar lokaci ɗaya tana sake faɗin. "Innalillahi Ummu lafiya? Ba ta amsa mata saboda shaƙan turaran Baɗɗo da ta yi ya ta yar mata da zuciya Amai ta ji yana taso mata shi ya sa ta sake ta, da dafe bango ta isa tiolet ɗin falon nan ta fara kwara Amai, a su kwane Baɗɗo ta bita har ciki ta riƙe ta, tana yi mata sannu aman ba komai sai ruwa ruwa sai naman da ta ci jiya da daddare, a galabai ce ta gama aman Baɗɗo ce ma ta taimaka mata ta wanke bakin sannan ta kama ta suka dawo falo. Ummu a kan kujera ta zube ta na mayar da numfashi Baɗɗo ta zauna gefen ta tana faɗin. "Subhanalla  jikin ki ya yi zafi ne haka ne Ummu? Habib ya fita ne? Shuru ta yi ba ta yi mgana ba tana ma yar da numfashi kawai sai Baɗɗo ta jawo jakarta ta fiddo wayarta lokaci ɗaya tana faɗin. "Bari na kira shi ko asibiti sai mu je amma barin ki a gida ke kaɗai a yanayin ki ai akwai matsala Sisna." Da sauri Ummu ta riƙe hannun Baɗɗo cikin mamaki ta kalle ta sai ta hau girgiza mata kai. "Wai kar na kira Habib ɗin? Baɗɗo ta tambaya cikin mamaki. Sai Ummu ta gyaɗa mata kai tana mai lumshe idanuwanta sai ga hawaye ta gefe da gefen kumatun ta. "Sabo da mene ne! Ko ba ya garin ne? Baɗɗo ta sake tambaya cikin mamaki. "Baɗɗo." Ummu ta kira ta a raunane ta amsa da sauri. " Naam." "Ina da ciki." Ta faɗa tana numfashi da sauri da sauri. Sai Baɗɗo ta washe baki kafin ta ce" Da man a yadda na gan ki na yi tunanin cikin ne. Congratulations Sisna" Ta faɗa da duka haƙoran ta a waje. "Amma Habib." Sai ta kasa ƙarisawa Baɗɗo ta kalle ta kafin ta ce. "Amma Habib me ne? Me ya faru da shi? Ummu ta miƙa ma Baɗdo hannu ita ta taimaka mata ta tashi zaune ta jingina da jikin kujera jin yadda jikinta ya yi zafi ne ya sa Baɗɗo ta ce. "Sannu Zazzaɓi ne ma a jikin ki Ummu." Shuru ta yi mata ba ta yi mgana ba. "Kun je asibiti? Sai Ummu ta girgiza mata kai cikin mamaki Baɗɗo ta ce. "To saboda mene ne, Habib bai san ba ki da lafiya ba ne? Ummu ta runtse idanuwanta sai hawaye suka kece mata. Ganin haka ya sa sai jikin Baɗɗo ya yi sanyi. "Sisna wani abu ne ya faru da Habib ɗin ne? Ta sake faɗa tana riƙe hannayenta ganin yadda take hawaye wasu na ganganrowa wasu na sake kwaranya. "Me ke faruwa ne Ummu Salma? Ta sake tambayan ta cikin damuwa da ya bayyana har a muryan ta. "Baɗɗo." Ummu ta sake kiran sunan ta wannan karon bata ba ta damar amsawa bq ta cigaba da faɗin. "Habib ya ce ba ya sona sannan kuma ba ya son haɗa zuru'a da ni." Baɗɗo ta zaro ido, tana kallon Ummu da ta fashe da kuka har yana fidda sauti. "Me ne kika ce? Baɗɗo ta faɗa da sauri lokaci ɗaya tana zaro idanuwanta waje. "Haka ya ce Baɗɗo. Yanzu ma ƙoƙarinsa na zubar da cikin dake jikina." Ummu ta sake faɗa cikin kuka, lokaci ɗaya tana ma yar da kanta saman cinyar Baɗɗo. "Baɗɗo Habib ya canza ya tsane ni  bai da mu da ni ba. burin shi kawai cikin dake jikina ya fita. Burin shi kawai na rasa cikin da ke jikina, ya faɗa mini bai aure ni domin ya haihu da ni ba." Ta ƙarishe faɗa cikin kuka,har da shessheƙa. Baɗɗo da itama har ta fara hawaayen tausayin yar'uwanta nata ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un" "Me na ke ji haka Ummu? Shi Habib ɗin? Ummu ta kasa mgana ban da kuka ba abin da take yi, kukan baƙinciki da takaici kanta kukan ciwo da zafin zazzaɓin jikinta kukan samun salama tunda ta samu ta iya faɗa ma Baɗɗo damuwarta. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *06* Cikin kuka mai tsanani da shessheƙa Ummu ta sanar ma da Baɗɗo abin da ke faruwa. Lamarin da ya girgiza duniyar Baɗɗo kafin Ummu ta gama ba ta labarin halin da ta ke ciki hawaye sun gama jiƙa ma Baɗɗo gaban doguwar rigar atamfar dake jikinta. Tana kuka Ummu na kuka suka haɗu suka rumgume juna suna ta kuka a tare, ita Ummu kukan halin da ta tsinci kanta a ciki take yi da tausayin kanta sannan tana kukan takaici na har a yanzu tana yi ma Habib uziri, har yanzu tana tunanin cewa zai dawo gare ta, har a lokacin tana tunanin wasa yake yi yana son ta sannan kuma yana son haɗa zuru'a da ita. Ga gaskiya ƙiri-ƙiri amma soyayyar Habib ta rufe mata ido daga ganin wannan gaskiyn.   Baɗɗo kuma kukan tausayin Ummu take yi. Tausayi mai yawa ganin irin halin da take ciki, gani ta ke yi kamar a mafarki ba domin Ummu ce da kanta ta e faɗa mata wannan labarin ba sai ta ƙarya ta ko ma waye, Habib ne fa? Ba ta taɓa tunanin zai iya aikata haka ba, ba ta taɓa tunanin Habib jahili ba ne mara ilimi sai da Ummu ke ba ta labarin shi. "Ya zan yi? Na rasa yadda zan yi Baɗɗo gani na ke yi kamar a mafarki, gani na ke yi kamar ba Habib ba ne." Ummu Ta sake faɗa tana gunjin kuka kanta a saman cinyar Baɗɗo ya yin da ita kuma take shafa kitson da ke kanta alamun lallashi amma ita ma kukan take yi, hawaye sun kasa tsaya mata saboda tausayin halin da Ummu take ciki? Lalle ta ƙara sarewa da lamarin mazan wannan zamanin masu sauya launi a duk lokacin da suka ga dama, za su kuma iya juya rayuwar wanda ya yarda da su daga sama zuwa ƙasa. "Ya ce ba ya sona sannan ba ya son haɗa zuru'a da ni. Ƙarya yake yi ko? Ke ma ai kin shaida irin son da ya ke yi mini ko Baɗɗo? Ta sake faɗa cikin kuka tana mai riƙo hannayen Baɗdo a cikin nata. Baɗɗo ta kalli Ummu kafin ta share hawayenta duk da ta fahimci Ummu na son Habib ba za ta fasa faɗa mata gaskiyan da soyayyarsa ta rufe mata idon da ta kasa fahimtar manufarsa ba. "Ummu-Salma ta so nan ki saurare ni ki ji." Ta faɗa lokaci ɗaya tana taimaka mata ta tashi zaune suna fuskantar juna hannayenta Baɗɗo ta riƙe duka biyun kafin ta sake kiran sunan ta. "Ummu-Salma." Ta amsa mata cikin shaƙewar murya saboda kuka. "Ki kalli gaskiyan dake gaban ki. Da gaske ne duk abin da Habib ya faɗa, domin wanda ke son ka shi ke ƙaunar haɗa zuru'a da kai, kin ce ya faɗa miki da bakin shi sannan ya yi ƙokarin aikata hakan a aikace, kin ga kenan zaman ki tare da shi ma hatsari ne, tun da ya sha alwashi zai iya miki lahani domin ya ga ya cimma burin shi." Ta ƙarishe faɗa cikin ƙura ma Ummu ido tana so ta ga yadda ta ƙarɓi mganar, tun da ta ce mata tana cikin halin wannan laulayin amma bai damu da ita ba, shi dai burin sa ta zubar da cikin jikinta da kuma  yadda ta faɗa mata matakan da ya bi domin ganin ya cimma manufarsa ta tsoraci Habib da lamarinsa ta kuma tabbatar da yadda yake son cimma burinsa zai iya komai in ta ce komai tana nufin komai domin ya ga cikin jikin Ummu ya fita ko da ita za ta shiga haɗari ne. "Ya zan yi.! Ina son cikina Baɗɗo sannan ina son Habib." Baɗɗo ta taɗe tana  kallon ta kafin ta ce" Ni ma ban ba ki goyon bayan ki zubar da cikin nan ba domin ba ki sani ba ko shi ne kaɗai ƙwan ki a duniya ba. Shi ma jahilci ne da rashin tunani sannan da manufarsa ta auran ki, mganar kina son shi duk ki cire shi Ummu tunda da bakin ki kika faɗa mini ya ce shi bai taɓa son ki ba, sannan bai aure ki domin haihuwa ba." "Habib ne fa Baɗɗo. Habib na sona ke ma kin sani? Ummu ta katse ta cikin kuka hawaye sun kece mata da ƙarfi kuma tana yin kukan mai fidda sauti. Baɗɗo ta yi mata uziri domin ko ita tantaman Habib ta ke yi, in ta yi nazari duba da tun daga lokacin da suka haɗu da Ummu da irin soyayya da ƙauna da tattali da ya nuna mata suma saboda ita duk ya ƙaunace su, ita kanta ba domin Ummu ce da kanta ta ga zahirin Habib ba za ta iya ƙaryata wannan labarin, Ummu na cikin damuwa ta kasa gasgasta Habib ne zai yi mata haka? Tunani ta ke yi kamar ba zai iya nuna haka ba saboda ya gurɓata rayuwarta cikin so da ƙaunarsa tare da kuma Aminta da shi. "Mun sani a baya yana son ki ayadda ya nuna mana a aikace Ummu. Yanzu kuma ya fito da zahirin manufarsa a kan ki." Baɗɗo ta sake faɗa tana jijjiga hannayen Ummu dake cikin na ta. "To ya san ba ya sona me ya sa ya zo ya nuna mini so da ƙauna har ya aure ni? "To wannan kuma manufarsa ce tun da bai faɗa ba, ba za mu iya yanke masa hukunci ba. Amma duk namijin da ya ce ya aure ka ba domin  yana son ka ba sannan ya nuna ba zai iya haɗa zuru'a da kai ba to dalili biyu ne, na farko ko ya yi auran fansa dake domin rama wani abu da kika yi masa na biyu kuma ko ya yi auren sha'awa da ke Ummu." Ummu ta ƙura ma Baɗɗo ido  tana mai tsiyayan hawaye. Ta fi amin ta da auran sha'awan da Baɗɗo ta ce in ta yi duba da yadda Habib ya tsara zamantakewar su ta aure, yadda ya mai da abin cin tuwo ba dare ba rana ko ba ta da lafiya bai damu ba sai ya aikata abin da yake so da ita. "Ni na fi tunanin auren sha'awa ya yi dake Ummu." Baɗɗo ta faɗa hawaye na sake kece mata Ummu ma ta sake fashewa da kuka suka sake curewa waje ɗaya suna kuka kamar wasu ƙananun yara. Baɗɗo ce ta fara haƙura da kukan ta koma tana mai lallashin Ummu da kalaman ban haƙuri da cewa ta yi hakuri Allah na sama kuma yana sane da ita zai saka mata. "Ya zan yi Baɗɗo? Zuciyata zafi take yi ji na ke yi kamar na rasa komai a duniya" Ummu ta faɗa muryanta ma ba ta fita saboda dishewar da ta yi. Baɗɗo ta sake share hawayen ta kafin ta ce" Kina da yadda za ki yi ko Ummu, kuma ke ce kike da kowa. Wannan mganar ba shuru za ki yi ba dole ne su Baffa sun san abin da ke faruwa" Da sauri Ummu ta waro jajayen idanuwanta tana kallon Baɗɗo jin ta ambaci su Baffa in mgana ta kai wajen su Baffa ai shike nan kuma. "E dole su sani saboda mgana ce da ta wuce tsakanin ku. Neman fa cikar burin sa ya ke yi saboda haka zai iya yin komai saboda haka. A dalilin haka ma zai iya yi miki illa Ummu." Kai Ummu ta ke girgizawa lokaci ɗaya tana faɗin" Habib ba zai iya cutar da ni ba. Ba zai iya ba." Baɗɗo ta yi kasaƙe tana kallon ta kafin ta ce" Nima na yi tunanin haka a baya. Amma yanzu kam ban yarda da shi ba. Ke da kan ki kika ce ya saka miki mganin da zai lalata cikin jikin ki har sau biyu a lemu bai yi nasara ba, na ƙarshen ma kin ce da karfin tsiya ya so ya yi miki ɗure, kina da tabbacin maganin ba zai yi miki lahani ba ke a karan kanki bayan cikin dake jikin ki? Ko kina da tabbacin ke ɗin za ki tsira? Sai jikin Ummu ya yi sanyi ta koma ta yi lakwas tana tsiyayan hawaye. "To kin gani dole iyaye su shiga ciki Sisna, in sha Allahu komai zai daidai ta." Ta faɗa tana mai share mata hawaye da hannayenta duka biyu. "Ina tsoro, ina tsoron kar su Baffa su ji wannan abun su raba ni da Habib." Ummu ta sake faɗa da har sai da Baɗdo ta ji kamar ta sake fashewa da kuka saboda tausayin Ummu, wata kila ya yi kusa zuciyarta ta aminta da cewa Habib ba masoyin ƙwarai ba ne a gare ta, ba yanzu za ta tantance girman yaudaran da ya yi mata ba wataƙila sai anan gaba. "Ba raba ki da shi za su yi ba. A matsayin su na iyaye za su shiga su gyara ta in da aka samu ɓaraka ne" Ummu ta jinjina kai kafin ta ce" Ba yanzu zan sanar da su ba Baɗɗo " "To sai yaushe? Ta tambaaye ta cikin mamaki." "Mu sake ba ma Habib lokaci. Wataƙila wasa ya ke yi, wataƙila yana gwada ni ne ya gani." Kallon ba ki da hankali Baɗɗo ke yi mata ta ma kasa mgana saboda mamaki, mutumin da a cikin idanuwan ki ya ce ba ya son ki ba domin ki haihu ya aure ki ba, sannan ya yi ƙokarin lalata cikin jikin ki da karfin tsiya amma har a yanzu kare shi Ummu ke yi! Tana tunanin wai wasa Habib ya ke yi? "Kin ga kar mu yi gaggawan sanar ma gida, in ya zo muka daidaita fa ? Baɗɗo ta kasa mgana saboda ta rasa ma abin cewa saboda tausayin Ummu da mamakin ta. "Kin ji? Mu sake ba shi lokaci na yi miki alƙawarin in bai sauya ba da kaina zan je gida na faɗa ma Baffa duk abin da ke faruwa." Baɗɗo ba ta da cewa tun da Ummu na ta mata magiyan kar ta faɗa ma kowa, ita da kanta za ta je ta faɗa ma su Baffa in har Habib bai sauka daga kan gudirin shi ba. "Na ji ba zan faɗa ma kowa ba. Sai dai ina tunanin yadda za ki cigaba da rayuwa a haka da shi, ina tsoron kar ya sake yunƙurin cimma burin sa ya yi miki lahani wata rana." "Allah ba zai ba shi sa'a ba" Tunda ta ce Allah sai jikin Baɗɗo ya yi sanyi amma jikinta da zuciyarta suna cike da tausayin Ummu ne, ganin yadda ta koma duk ta lalace sannan daga ganin ta, tana bukatar ma ganin likita. Ummu ta faɗa mata magungunar da aka rubuta mata a asibiti Habib bai siya ba sannan ga yanayin da take kwana tana ta shi a ciki. "Gaskiya ya kama ta mu je asibiti." Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa. Ummu ta kalle ta a sanyaye kafin ta ce" Nima ina son na je asibiti ba ni da lafiya sosai." "Yanzu za ki tashi mu je." Ummu ta sake kallonta kafin ta ce" Habib bai sani ba." Baɗɗo ta ji kamar ta rufe Ummu da duka saboda baƙin ciki da takaici. "Kina ganin in na fita bai sani ba, ba matsala.? Ta sake tambayan ta a sanyaye. Sai da Baɗɗo ta ya fa mayafin ta sannan ta kalli Ummu tana faɗin" Yana gidan kike fama da ciwo amma bai damu da ke ba, kin ga kenan in kin fita domin neman lafiyarki hakan ba matsala ba ne." Ummu ta girgiza kai kafin ta ce" A'a bari dai na kira shi na sanar da shi." Kasa ma mgana Baɗɗo ta yi sai ma ta koma ta zauna tana kallo Ummu ta tashi tana dafe dafen bango ta koma bedroom ɗin ta sai ga shi ta fito da wayarta a hannu tana ta kiran wayar Habib amma sai a saka kiran na ta a forwording. "Ba na samun shi." Ta faɗa a sanyaye Baɗɗo ta yi kamar ba ta ji ta ba haushi duk ya ishe ta. "Ya zan yi yanzu? "Ki zauna sai lokacin da kika same shi a waya, in ya ce ma kar ki je ki zauna ki mutu" Ta faɗa cikin haushi jin haka  Ya sa jikin Ummu ya sake yin sanyi ta zauna kusa da Baɗɗo tana mai marairaicewa. "Ya zan yi to? Na rasa tunanin da zan yi? Ta faɗa hawaye suna taruwa a ƙwarmin idanuwanta. "Ki ta shi na raka ki asibiti a duba lafiyarki Ummu-Salma." Baɗɗo ta faɗa tana mai sake miƙewa tsaye wannan karon har tana rataya jakar da ta zo da ita ba yadda Ummu ta iya haka ta ɗauko hijabi ta da ƙaramar jakarta da Atm ɗin ta ke ciki ba ta da kuɗi a hannunta, kulle ɗakin suka yi suka fita zuwa bakin titi sannan suka hau Keke Napep zuwa asibitin da Ummu ta ke da fayel, boshon clinic da taimakon Baɗɗo dake  riƙe da ita. Suna zuwa suka ga likita da ya ke ta je da katin ta, likitan na ta faɗa cewa babu wadattacen ruwa a jikinta sannan akwai maleria mai zafi a tare da ita. Riƙe ta suka yi bayan sun saka mata drip sun yi mata allurai har da na barci ta samu barci sannan likita ya ce Ummu ba ta cin abinci sannan ga jinin ta ya ɗan hau shi ya sa za su rike ta zuwa yamma su gani. Baɗɗo ce ta zauna da ita a asibiti nan tun kafin azahar sai gabda mangariba kuma ba ta kira kowa ba, Ummin ikki dai ta kira ta ganin duhu ya shiga ba ta dawo ba sai ta ce mata ta samu Ummu na fama da zazzaɓi ta ɗan taya ta ayyuka ne amma in dare ya yi sosai ba ta dawo ba to za ta  kwana tare da ita, ta yi ma Ummin ƙaryan cewa Habib ba ya nan ya yi tafiya. An sallami Ummu tare da magunguna da dokokin likita bayan ta sha leda uku na ruwa sai kuma ta ji daɗin jikinta ta daina jin jirin nan da ciwon kai, ya ce ta samu hutu sosai ma'ana sun ba ta bedrest sannan ta riƙa cin abincin domin inganta jaririn dake cikin ta. Ba su suka shigo gida ba sai ana kiran sallar isha'i kuma har a lokacin Habib bai dawo ba, Ummu wanka ta yi ta shiga  rama salollin da ke kanta ita kuma Baɗɗo bayan ta yi sallar isha'i ta zage tana gyara gidan duk ya yi ƙura tun da Ummu tana ta kanta ba ta gyaran gida ba, har fashasshen kwalban da ke saman dinning Baɗɗo ce ta kwashe shi ta gyara wajen lemun da Habib ya saka ma mganin ita ta kwarara shi a tiolet ta saka kwalayen exotic ɗin a dusbin sannan ta yi ma Ummu faten wake ta so ta saka allayahu amma babu, kuma  in da ake siyarwa sai kasuwa. An ci sa'a kuma Ummu ta ci faten waken bai dawo mata ba sai ta ɗora da ruwan lipton mai zafi ya samu ya warware mata ciki sannan Baɗɗo ta ba ta magungunar ta tasha, ta ji daɗi da Baɗɗon ta ce mata sai gobe da safe za ta tafi in ta ga jikin na ta da sauƙi. Suna zaune a falo Ummu na kwance kanta na saman cinyar Baɗɗo suna kallo gefe ɗaya kuma suna hira sama sama sai aka kira Baɗɗo a waya wata class mate ɗin ta ce, ganin suna mgana ne ya sa Ummu ta shiga tunani mai zurfi tsoron ta in mganar nan ta je kunnen Baffa har yayyenta suka ji labari sai Habib ya gane ba shi da wayau sannan tana da tabbacin sai sun raba auran nan da nan a cikin su akwai waɗanda ba su so auren nata ba, ba wai don ba su son Habib ba, a cewar su karatu ya kamata ta cigaba da yi ba aure ba ita kuma ba saboda haɗuwarta da Habib ba. Tun tana ƙarama da ta fahimci ba ta da ƙwaƙwalwar karatu ta ce ita daga sakandiri ba ta son ta cigaba da karatu. A lokacin ba tasa aure a lissafin ta ba domin ba ta ɗauka za ta haɗu da Habib a gabar ba, shi ya sa son auren ma baya cikin lissafin ta, ba ta taɓa tunanin za ta haɗu da Habib a lokacin ba ballanta har aure ya shiga tsakanin su ba. Abu ne da ya faru lokaci kaɗan haɗuwarsu da auren su wattani biyar ne a wancan lokacin Hamma Kabiru ya yi ta faɗa da cewa an yi gaggawa ya kamata a ɗan sake jira, shi kuma Baffa ya ce tunda dai Ummu tana so kuma shima Habib ɗin ya shirya bai ga amfanin ɓata lokaci ba. Tsoron ta ɗaya in suka ji mganar ba ta san yadda lamarin zai ƙare ba, wataƙila ya yi lalacewar da kafin lamarin ya gyaru za a ɗau lokaci. Ta yi nisa cikin tunaninta ba ta san shigowar Habib ba, sai da ta ji ƙamshin turaran shi sannan ta farga, tana ɗagowa suka haɗa ido huɗu da shi yana tsaye yana kallon su. Da sauri ta miƙe zaune tana kallon shi, jikinta har rawa ya ke yi saboda ganin Habib ba ta san ta yi kewarsa ba sai da ta gan  shi, ta ji wani irin sanyi a cikin ranta. "Sannu da zuwa Noori." Ta faɗa lokacin da take miƙewa tsaye. Baɗɗo na zaune tana ganin ikon Allah. Sai da ta ga Habib sannan ta san a ɗazu ba haushin shi take ji ba, yanzu ne ta ke jin kamar ta rufe shi da duka da ta gan shi. Barin ma yadda yake bin Ummu da wani kallon banza ita ko baiwar Allah hannu ta miƙa za ta karɓi jakar hannunsa da sauri ya kauce ya kuma raɓa ta zai wuce ciki Baɗɗo ta ga ba za ta iya jurewa ta miƙe a fusace. "Habib." Ta kira sunan shi a kausashe, sai ya tsaya kafin ya juyo fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Yadda ya yi ma kamar bai taɓa ganin Baɗɗo ba. "Ina son mgana da kai." Tana kallon cikin idanuwansa ta faɗi haka. "SisNa kar ki ce masa komai don Allah." Ummu ta faɗa tana mai rike hannun Baɗɗo cikin magiya. "Bar ta ta faɗi abin da ke bakin ta, in tana tunanin za ta iya sauya tunanina ne akan mganar da za ta yi Bismillah." Ya ba ta amsa har yana wani ɗaga hannu, Baɗɗo ta kalle shi cikin wani yanayi shima kai tsayen yake kallon ta. "Na san ta faɗa miki abin da ke faruwa, in har ke yar'uwata ce da gaske gwara ki ba ta shawaran ta bi umarnina in tana so ta tsira da sauran abin da ya rage mata." Ya faɗa cikin gadara sannan yana nuna Ummu kamar ya ga abin ƙyama. "Domin ba ta da wani sauran wani abin da ya rage a tsakanin mu yanzu." Ba Ummu ba, hatta Baɗɗo sai da ta ji ta muzanta idanuwanta suka kawo ruwa sai ta yi saurin shanyewa. "Habib Allah ya fika." Haka kawai Baɗɗo ta faɗa ta ja hannun Ummu suka raɓa ta gefen shi, Ummu tirjiya take yi amma Baɗɗo ba ta sake ta ba sai da suka shiga cikin bedroom ɗinta ta kuma ma yar da kofa ta rufe, suna jiyo dariyan Habib na tura haushi. "Ki bar ni na je na ba shi haƙuri." Ummu ta faɗa tana nufar ƙofar Bedroom ɗin da ƙarfi Baɗɗo ta ce" Wallahi in kika fita daga ɗaki nan, sai na kira Baffa na faɗa masa duk abin da ke faruwa." Kalaman Baɗɗo suka sarƙe ta, ta kasa gaba ballanta baya, kuma yadda Baɗɗo ta ɗau alwashi ba za ta fasa abin da ta ce ba shi ya sa ta koma kawai ta kwanta a saman gado ta fashe da kuka. "Ina son Habib. Ina so na bashi hakuri mu dawo kamar baya." Dole Baɗɗo ta sauko ta fara lallashin Ummu domin ta fahimci tana son Habib kuma tana son cikin ta, ba ta da wata mafita ne a yanzu. Sun daɗe ba su yi barci ba Baɗdo na sake ba ta baki sai dai ta ba ta tabbaacin in har Habib bai daina yunƙurin zubar mata da ciki ba to ta koma gida kar ta sake zama yana wulakanta ta alhalin tana da gata. Ita ko Ummu a zuciyarta addu'a take yi Allah ya sassauta zuciyar Habib in ya rabu da ita ina za ta saka kanta tana ji gwara su cigaba da zama a haka ta tsira da shi, sannan ta tsira da cikin jikinta da auran ta gabaɗaya tunani take yi zuwa nan gaba kaɗan Habib zai yi nadama zai dawo ya ba ta haƙuri su gyara rayuwan auren su, in shi ba ya son ta ita tana son shi sannan za ta iya jure komai saboda ta tsira da auran shi, shi ya sa ba ta kaunar mganar ta je kunnen Baffa, in ya ji kamar duka yayyenta sun ji, in kuma akwai waɗanda za su yi shuru to akwai fusatattu irin su Hamma Kabiru da Hamma Abdulrahaman da ba su da wasa ko kaɗan tana da tabbacin ko za ta mutu sai sun raba auren ta da Habib, ita kuma tana son shi tana fatan ta rayu da shi har karshen rayuwarta. Washegari ma Baɗɗo ta yi ma Ummu abin da za ta karya kunin gyaɗa ta dama mata sai ta yi musu fanke. Habib da Baɗɗo sun haɗu lokacin da ta fito daga kitchen shi kuma ya yi shirin fita zai bar gida kowa ya yi kamar bai ga kowa ba Baɗɗo ta kitchen ta ke leƙen Habib har ya bar falon lalle Duniya juyi juyi na gaba ya koma baya yau wai ita ce Habib zai gani ya yi kamar bai gan ta ba, ita fa mamaki ta ke yi yadda lamarin nan ya sauya. A baya ganin irin dacen da Ummu ta yi sai ta ke mafarkin ta samu miji kamar sa, amma yanzu ta ji auren da namijin ma gabaɗaya sun fita kanta, ba su da tabbas ba su da garanti ka aminta da su su ha'in ce ka, ka ba su Amana su ci, sun san salon yaudara kala kala, su kuma ga su ba tukwane ba ne ballanta ka fara ƙwanƙwasa wa kafin ka ɗauka, ba ka isa ka gane manufar su ba sai ka shiga da ga ciki, tana aiki tana hawaye Habib ya cutar da zuciyar Ummu, sannan ya cutar da kuruciyarta suma na tare da ita ya cutar da zukatan su. Damuwarta ɗaya tunanin halin da Ummu za ta shiga matuƙar Habib ya sake ta ko in iyaye suka shiga mganar ba a samu masalaha ba, tana tsoron kar damuwa da zafin zuciya su yi ma Ummu illa. Sai da ta gama shan kukanta ta share hawayenta saboda kar Ummu ta fahimci ta yi kuka itama ta fara ta samu ta yi shuru ta daina kukan da ta kwana tana yi. Su na gama karyawa Baɗɗo ta wanke abubuwan da suka ɓata ta ɗan gyara mata gidan ta yi wanka ta yi shirin tafiya Ummu ta fara hawaye ita mai idanuwan kuka da cewa Baɗɗo ta ƙara kwana. "Aa ba zan sa ke kwana ba, kar mijin ki ya zo ya sake ganina, karon mu ba zai yi daɗi ba." Ummu ta na ji tana gani Baɗɗo ta yi mata sallama ta tafi ta bar ta, bayan ta jadadda mata ta kula da kanta ta riƙa samun hutu domin kiyaye dokar likita. Sannan in ta ga wata matsala kar ta zauna ta kira gida in tahowar ba zai yuyu ba Ummu ta amsa da to za ta kiyaye. Baɗɗo na tafiya ta koma ta kwanta tana ta kuka, kukan da ya fara zame mata jiki a acikin kwanaki nan. Bayan tafiyar Baɗɗo maimakon lamarin Habib ya gyaru sai ma ya sake lalacewa. Ba ya ma nuna cewa akwai wata hallita a gidan, in sau goma Ummu za ta yi masa mgana ba zai amsa ta ba, a cewarsa in ta ga ya dawo yana kula ta sai in har ta bi umarnin sa, umarnin da Ummu ta gwammace su zauna a haka da ta amince da buƙatar sa na zubar da cikin, cikin da duk duniya yanzu ba ta da wanda take so sama da shi. Ba ta san dare nawa ta ɓata tana kuka ba, ba ta san sau nawa ta duka a gaban Habib tana kuka akan cewa ya yi hakuri ya yafe mata. Amma bai kalle ta ba yana nan akan bakan sa, ko ta zubar da ciki ko kuma su cigaba da zama a haka kafin ya yanke hukunci a kanta. Baya cin abincin ta, ba ya neman ta bai damu da ita ba ko za ta mutu bai damu ba, ba shi da asara sai ya raba dare yake dawowa sannan ya zauna a falo ya yi ta waya cikin harshen turanci. Ummu ta yi kuka, kuka har ya zame mata jiki saboda halin da ta ke ciki. Wato ga ta jahila wacce ba ta jin turanci shi ya sa in zai yi waya sai ya sauya yare, ba kuma wai ba ta jin turancin ba ne, ta na ji daidai misali na iya karatun ta, mayarwan ne ke yi mata wahala ko in an faɗi wasu manyan kalamai a cikin turanci sai ta daburce shi kuma Habib ya iya turanci na fitina kamar wanda aka haifa a ƙasar waje. Har kuma gobe ba ta ji Fargar jaji ya kamata akan rashin cigaba da karatun ta ba, ra'ayin ta ne kuma har yau ba ta ji ta sauka akan wannan ra'ayin ba. Kullum sai Baɗɗo ta kira ta a waya domin ta ji lafiyan ta. Har Ummin ikki sun yi mgana ta yi mata sannu tun da Baɗɗo ta faɗa mata ba ta jin daɗi. Baffa ma suna waya amma ba su fahimci wani abu ba, tunda ba ta ba da damar haka ba. ** Zuwan Baɗɗo da kwana goma Shamsiya ta zo, kwatsam kamar daga sama domin sun daɗe ba su yi mgana da Ummu ba. Sannan ba ta kira ta ba shi ya sa ba ta san da zuwan ta ba sai dai ta gan ta, ashe sun samu hutun makaranta ta dawo gida shekaranjiya ta yi kewarta ne shi yasa ta zo domin ta gan ta. "Allah sarki Bestie ya makarantan? Ummu ta faɗa tana mai zama a gefen Shamsiya wacce ke zaune a saman kujera mai zaman mutum uku bayan ta kawo mata ruwa. Shamsiya Black beauty ce, sai dai siririya ce sosai da ba ta da wani tsarin jikin mata, a shekarun ta ba za ta wuce sa'ar Ummu Salma ba. "Alhamdulillah Bestie, mun gama mun dawo gida hutu muna komawa kuma za mu shiga aji uku." Shamsiya ta faɗa cikin mirmishi, Ummu ta sake rumgumeta tana yi mata fatan alheri. Shamsiya sai kallon Ummu take yi cikin alamun tambaya yadda ta ga ta koma amma ba ta yi mgana ba. "Ina Habib? Ko yana wajen aiki ne? Da kai Ummu ta amsa mata, ba tare da ta yi mgana ba. Sun fara hira Shamsiya dai ta ga ramar Ummu ta yi yawa sannan lokaci bayan lokaci tana ta shi ta shiga tiolet ta zubda yawu. "Bestie me ke damun ki ne? Kin rame! Tana so ta danne yanayin ta amma ta kasa domin damuwar nata ya fara bayyana a saman fuskarta. "Ko kina da ciki ne? Shamsiya ta tambaya lokaci ɗaya tana washe baki. Wannan karon ma kai Ummu ta sake ɗaga mata alamun haka ne, da sauri Shamsiya ta rumgume ta cikin tsananin farincikin da ya kasa ɓoyuwa daga zuciyarta ya bayyana har a saman fuskarta. "Congratulations Bestie na. Mun kusa zama iyaye ni da Baɗɗo." Ba ta sani ba Ummu kuka take yi, sai da ta ji tana shashesheƙa sannan ta ɗago ta sai ta samu fuskarta caɓe-caɓe da hawaye. "Subhanallah kuka kuma Bestie? Me ya faru? Shamsiya ta faɗa cikin harshen fillanci. Kasa mgana Ummu ta yi, ban da kuka ba abin da take yi kuka kuma sosai har da sauti. Hankalin Shamsiya ya tashi ta ruɗe gabaɗaya tana tambayan Ummu abin da ke faruwa. Sai da ta gama shan kukan ta sannan ta iya labarta mata abin da ya faruwa da wanda ke kan faruwa. Shamsiya ta yi tsam kafin ta ce" Topha, innalillahi shi Habib ɗin ne duk ya aikata miki haka Bestie? Ummu ta jinjina kai kafin ta ce'" Na yi duk abin da zan iya yi na gaza bestie. Ban san sau nawa na duka na ba ma Habib haƙuri ba amma ya ce yana nan akan mganarsa. In ina son mu cigaba da zama kamar baya har sai in na amince na zubar da cikin jikina." Shamsiya ta kalle ta kafin ta ce" To ki bi umarninsa mana Bestie" Cikin mamaki Ummu ta kalle ta kafin ta amsa cikin mamaki. "Na zubar fa kika ce? "Yes, ai ba matsala ba ce. Wata kila ba yanzu ya shirya ku haihu ba ki bi umarninsa ki zubar Bestie nan gaba za ki samu wani a lokacin da shi ya shirya ma hakan" Sai Ummu ta yi shuru tana mai kallon Shamsiya sai take ɗan hango ƙamshin gaskiya a kalamanta ganin haka ya sa ta riƙo hannayen Ummu cikin na ta tana cigaba da faɗin. "Kuma ina tunanin duk mganar da ya faɗa miki na ran shi so ko wani abu cikin fushi ne da haushin ƙin bin umarnin sa ne, amma ina da tabbacin Habib na son ki , ke ma kuma kin san haka" Kalaman Shamsiya suna shigar ta sai ta ji ta aminta da mganarta amna kuma tana son cikin ta ba ta son rabuwa da shi. "To amma Bestie ina son cikina fa." "Allah zai kawo miki wani, kin manta a baya ma kin samu ya zube, yanzu kuma ga shi Allah ya sake baki wani ba? To haka anan gaba zai sake baki wani in sha Allahu.'" Lamarin ba mai sauƙi ba ne, tana son auran ta, tana son ta yi komai saboda tsira da auren ta amma ba ta jin za ta iya zubar da wannan cikin da ta faro dukkan wata gwagwarmaya saboda shi ba. "Da na ce zan bi shawaran Baɗɗo ne na je gida na sanar ma Baffa watakila in ya shiga mganar komai zai yi daidai ba sai na zubar da cikin ba Bestie." Shamsiya ta yi shuru kafin ta ce" Kina da tabbacin in mganar ta kai wajen su Baffa komai zai yi daidai? Ni fa sai na ke ganin sako su a ciki zai iya ɓata komai, ki sake ɓata ran Habib har ya yanke miki hukunci cikin fushi." Ummu ta yi zuru tana kallon Shamsiya kamar wata doluwa cikin bugawar zuciya ta ce" Wani hukunci zai yanke a kaina? "Hukunci rabuwa da ke mana, kin ga ya cuce ki ya cutar da iyayenki ya sa kin zama ƙaramar bazawara." Gaban Ummu ya amsa! Tana son Habib ba za ta iya juran rasa shi ba. "Ki tsira da auran ki Ummu-Salma, kuma ni ban ga laifin Habib ba, haka na faruwa ko wata da muke ɗaki ɗaya a makaranta mijinta ya ce sai sun shekara biyar da aure za ta haihu kuma ta amince. So normal ne kawai fahimta ce tsakanin ma'aurata, ke kan ki Ummu nawa kike? Kina da sauran damarma ki masu tarin yawa ma anan gaba ni ban ga laifin Habib ba, ra'ayin shi ne kuma girmama ra'ayin juna a zamantakewa kamar dole ne." Ummu ta jinjina kai cikin sanyin jiki kafin ta ce'" Ina son aurena sannan ina son cikina Bestie." "To sai dai ki zaɓi ɗaya ko auran ki, ko cikin." Ummu ta kasa zaɓan wanda ya fi sauƙi a ciki, duk tana son ta tsira da su da auran da cikin jikinta. Shamsiya kuma ta yi ta nuna mata ba matsala in ta zubar yanzu gaba za ta iya samun wani a lokacin da suka shirya suna da dama, tun da lamarinn nan ya fara faruwa ba ta ji ta samu salama ba sai da ta yi mgana da Shamsiya sannan ta samu jin wani abu ya faɗa daga ƙirjinta. Shamsiya ba ta tafi ba sai da Ummu ta ba ta tabbacin za ta amince da umarnin Habib. Ita fa Shamsiya ƴar boko ce, sannan renon yan boko su a ganin su hakan ba matsala ba ne bayan tafiyar Shamsiya Ummu ta yi ta tufka tana warwara, shawaran Shamsiya ta fi zama mata sosai a cikin zuciyarta duk da tana son cikin ta amma kuma tafi son Habib a kan cikin, kamar yadda Shamsiya ta faɗa ne in tana son Habib to ta bi umarnin sa sai su zauna lafiya. Za ta amince da a zubar da cikin amma sai ya ba ta tabbacin zuwa yaushe yake son ta haihu ? Allah na gani tana son haihuwa har mafarkin tana shayar da jariri take yi. In har ba zai wuce shekara biyu ba to za ta iya haƙuri a zubar da wannan amma in dai ya gota ba za ta iya haƙuri ba. *** A RANAR. Habib Ya fito daga wajen aiki kenan misalin 4:40pm, ya tsaya tare da wani abokin sa suna magana. Ya ji saƙo ya faɗo wayarsa amma saboda suna mgana bai duba a lokacin ba sai da suka yi sallama kowa ya nufi in da ya yi parking ɗin motar shi ya shiga. Shi dai yana shiga cikin motar na shi jakar hannun sa ya sauke a gefen kujeran mai zaman banza. Sannan ya fiddo wayarsa dake cikin aljihun wandon shi saƙo ne daga M.S kamar yadda ya yi zato tun farko. "Habib lokaci yana ƙure mana fa, ina jin tsoro, tsoron kar maganar nan ta je kunnen iyayenta daga nan waliyanka su ji labari alalan mu ya yi ruwa, tsarin mu ya lalace ba yadda muka shirya ba. Don Allah ka yi wani abu da gaggawa ba mu da lokaci" Mirmishin sarari ya yi kafin ya tura mata da amsa. "Kar ki damu ba abin da suka isa su yi. Ba kuma wanda ya isa ya lalata mana shirin mu." "In cikin bai zube ba fa? "Ba wanda ya isa ya sa ni na karɓi abin da na ce bana so. Da gaske bana son ta sannan ba na son haɗa zuru'a da ita, in kuma ta cigaba da taurin kai to zan saka rayuwarta da na iyayenta a uku." Yana turawa ba jimawa sai ga wani saƙon ya sake shigowa. "Ka yi komai, in dai ka san ba zai hana shirin mu tafiya ba." "Zan yi." Da haka ya ma yar da wayar na shi cikin aljihun wondon shi ya kunna motar ya yi riverse ya bar haraban bankin, yana tafe yana wani tunani matukar Ummu ta cigaba da taurin kai to komai zai ƙare a tsakanin su, ta je can ta riƙe cikin sai ta zame masa uwa da uba.  Abin da ya sa ya aureta tuni ya gama samun shi babu kuma sauran wani abu da ya rage a tsakanin su ** Da wuri Habib ya dawo kamar ya san Ummu ta tsala kwalliya tana jiran dawowan shi, da yake ta ji sauƙi tana samun ƙarfin jiki ya sa har girki ta yi masa ta gyara gidan yana tashin ƙamshi. Lokacin da ya dawo tana falo tana zaman jiran shi, bai yi mata mgana ba sai ita ce ta ce masa ya tsaya ya saurare ta. "Na faɗa miki ba wani sauran mgana a tsakanina da ke malama." Ya faɗa a fusace yana ƙoƙarin shigewa ɗakin da yanzu ya ke rayuwa a ciki. "Ko da a ce maganar na amincewa da ɓukatar ka ne? Ta faɗa a sanyaye, ai yana jin haka da sauri ya juyo yana kallon ta. "Me kika ce? Ya tambaya yana ɗan rage ɗaure fuskar da ya yi. "Cewa na yi ko da maganar tawa na cewa na amince zan bi Umarnin ka ne?   Kamar walƙiya sai ga shi a gabanta yana mai sakin jakar hannunsa kafin ta yi wani yunƙuri ya rumgume ta ƙamƙam cikin matsanancin farinciki. "Haba ko ke fa Baby, sai yanzu na ji na samu natsuwa." Murna yake yi a zucci da sarari nan da nan ya fara sumbatar ta a ko'ina na fuskar ta, yana mai nuna mata farincikin sa bisa amincewa da ta yi da bukatar shi, zuciyar Ummu ya cika da farinciki ganin yadda Habib ya ke yi mata rawan jiki, ta faɗa masa ta amince da buƙatar sa amma zuwa wani lokaci ya shirya ya zama uba ita kuma ta zama uwa. "Nan da shekara ɗaya Baby. Lokacin duka mun shirya zamo wa iyaye amma by now mu cigaba da cin lokacin mu." Ya faɗa yana yi mata mirmishi, wannan mirmishin da shi ya yi amfani ya sace zuciyarta.   Sai ga shi ranar tare suka yi Dinner yana ba ta abinci a baki tana bashi, ganin ta ɗan yi sanyi sanyi ya sa ya ke sake jadadda mata kar ta damu zai kai ta asibiti a bata maganin da cikin zai zuɓe ba tare da an samu wata matsala ba yana faɗa mata cikin ƙarami ne ba za ta fuskanci wata matsala ba. Duk da Ummu ta amince da buƙatar Habib sai ta ji ta kasa samun natsuwa, a cikin zuciyarta ta kasa samun natsuwa cikin ta kawai take shafawa tana jin wani iri, sai take ganin kamar abin da za ta aikata ba alheri ba ne. "Ummu-Salma ki sake tunani." In ta amince aka zubar da cikin tana da garantin cewa Ubangiji zai sake ba ta wata damar! Ko kuma ranar gobe ƙiyama cikin da ta zubar ya tambaye ta a gaban Ubangiji da cewa wani laifi ya aikata mata da ta yi masa haka? Ba ta da amsa a wannan lokacin sai ta ji ta sare son cikin ta ya sake shigan ta, tuni ta ji ta sauya shawara gwara ta ce ma Habib ya yi haƙuri tun da cikin ya shiga ya bari in ta haihu sai su tsayar da haihuwar har zuwa lokacin da ya ke so. Da wannan tunanin ta tsayar da shawara tana ɗakin ta ne Habib ya je ɗakin sa ya dawo ba jimawa sai ga shi ya shigo da gajeren wando jikinsa ba ko riga tana so ta yi masa mganar amma bai ba ta dama ba haka ya fara naniƙarta da sam ta ji ba ta bukatar hakan amma ta kasa yi masa gaddama. Bai bar ta ba sai da ya samu yar natsuwa sannan ya ɗan dakata a gefenta yana mayar da numfashi. "Gobe Baby za mu je asibiti, ko kuma kawai na siyo miki mganin ki sha zai fi sauƙi ko? Ya faɗa yana leƙen fuskarta, sai ta yi shuru ta kasa mgana haka kurum ta ji zuciyarta ta karye. "Kin yi shuru." Sai da haɗiye miyau sannan ta ce" Habib na sauya shawara." Yadda ya miƙe zaune a firgice ne sai da Ummu ta ji tsoro itama ta tashi zaune tana mai rufe jikinta da bargon dake gefen ta. "Raina mini wayau za ki yi? Ya faɗa a fusace yana kallon ta. "Aa wallahi." "To me hakan ke nufi, mun gama mgana kuma yanzu kina faɗa mini wata maganar banza." Ya katse ta a fusace yadda ya ta so mata in ta yi wasa zai iya kai mata duka. "Ina so ne, ka bari sai na haihu." Ta faɗa hawaye na kece mata kanta na ƙasa domin kauce ma wani mugun kallo da Habib ke jifanta da shi. "Kin haihu a ina? A gida na? Ba ki isa ba.' Ya faɗa a fusace kafin ya diro daga kan gado. "Sau nawa zan faɗa miki bana son na haihu da ke ne Ummu-Salma, ? "Ai ka ce zan haihu  nan da shekara ɗaya shi ne na ce tunda ina da cikin yanzu ka bari in na haihu daga baya sai na bari sai lokacin da ka shirya sai in sake haihu." Kafa ya sa ya daki gefen gado cikin ƙaraji ya ce" Ke wata irin daƙiƙiya ce,? Da wani yare zan faɗa miki ki yarda da mgana ta? Ya faɗa kamar ya kai mata duka, Ummu ta takure waje ɗaya tana mai kuka ƙasa-ƙasa. "Na faɗa miki ba na son ki, bana son ki me ya sa ƙin ki gane hakan ne? Ummu ta ɗago tana kallon shi da idanuwanta masu zubar ƙwallah. "Ko ƙwaƙwalwarki kike so na buɗe na saka miki mganar ne sannan za ki fahimce ni? Ya gama faɗa yana dafe kansa. "To ka san haka me ya sa ka aure ni, ka nuna mini so kuma? Kamar zai dake ta haka ya taso mata da hargagi yana faɗin. "Ke wai har yanzu ba ki ba ma kan ki wannan amsar ba? Sai na faɗa miki dalilin da ya sa na aure ki da bakina sannan za ki yarda? Ya faɗa yana zare mata ido, Ummu ta runtse ido hawaye suka ke ce mata. "Sabo da ina so na ji daga bakin ka." Ta ƙarishe faɗa cikin kuka har da shessheƙa. "Sabo da ba ke na ke so ba, ban kuma aure ki domin ki zo ki haifa mini yara ba." Sai da ya kalleta sannan ya yi wata dariya kafin ya ce" Kawai ni jikin ki na ke so, auran sha'awa na yi da ke kuma Alhamdulillah na samu biyan buƙatata a wajen ki, ko a haka kasuwa ta watse na ci riba." Idanuwanta a runtse amma hawaye na ƙwaranya, kukan zucci ta ke yi, da Baɗɗo ta faɗa ta ji zafin mganar ta kuma kasa gasgasta hasaahen ta, sai da Habib ya faɗa sannan ta fahimci yadda komai yake, maganganunsa sun yi zaman da'ira a cikin zuciyarta cikin lokaci kaɗan suka fara yi mata illa, shi ya sa ashe take ta mamakin me ya sa kullum abu ɗaya? Ashe dalilin da ya sa ya aure ta kenan saboda jikin ta, kuma kamar yadda ya faɗa ne ko a haka kasuwa ta tashi shi ke da riba, tunda duk ya gama more wani albarkatun jikinta ya cuci rayuwarta ya lalata mata mata goben ta, tuni ta ji zuciyarta ta yi baƙin ƙirin ɗin da ta ji gwara da ba ta zubar da cikin jikin ta ba, wataƙila da shi ne kaɗai za ta iya tsira a rayuwarta da Habib ya lalata. Tana jin shi yana ta mganganu ya sake ba ta tabbacin shi bai taɓa son ta ba auran sha'awa ya yi da ita ba auren soyayya ko ta zo ta haifa masa yara ba. Akwai wacce ya yi ma wannan tanadin amma ba ita ba Daga ƙarshe ya ce ba zai sake ce mata ta bi umarninsa ba amma ta sani sai ta yi nadama daga nan ya bar mata ɗakin har yana banko mata ƙofa. Yana fita ta saki kukan ta a fili, kuka take yi kamar ranta zai fita, ji ta ke yi kamar zuciyar ta za ta fito waje saboda yanayin da ta ke ciki, mutumin da ta ɗauka a masoyin ta da bayan iyayenta  ba ta da kamarsa, mijinta sirrin rayuwarta wanda ta aminta da shi ashe ashe shi a zuciyarsa ba haka ya ɗauke ta ba, yana da manufarsa a kanta. Ta daɗe tana kuka kafin ta iya tashi ta faɗa tiolet ta tsarkake jikinta sannan ta fito ta saka wata doguwar riga, ta shimfiɗa darduma tana salla tana kuka, bayan ta idar da sallar isha'i ba ta san awannin da ta shafe a saman darduma tana kuka ba. Abu ɗaya ta sani ba ta ji ta tsani Habib ba, sai ma ji ta yi yanzu take son shi, amma dai ta yanke shawaran gobe za ta je gida ta samu Baffa ta faɗa masa halin da ake ciki. Sai dai za ta za ta roƙe shi ya kira Habib ya ba shi haƙuri, za ta faɗa masa tana son shi kuma ba ta son wani abu ya samu auran ta. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *07* Washegari. Ummu-Salma ta ƙulla ƙawance da kuka. Ta kwana yi ta yini yi, jiya ma kwana ta yi kuka shi ya sa ta tashi idanuwanta sun kumbura sun yi luhu-luhu, fuskarta ta yi jajir abin ka ga farar fata. Ba ta fito daga cikin ɗakin ta ba sai da ta ji fitan Habib daga gidan sannan ta fito domin tsoron haɗuwa da shi take yi. Ba ta iya tsinana komai ba, ga ciwon kai ga jikinta duk ba daɗi ruwan zafi ta dafa ta sha ruwan lipton saboda za ta sha magani sai da ta sha mgani ta ɗan ji ya kwanta mata sannan ta shiga ta yi wanka tana cikin shiryawa ne Hamma Sadam ya kira wayarta. Tana ɗauka ta ji yana faɗin. "Ke wai kin mutu ne? Ko an yi miki magana a WhatsApp ba kya dubawa. Sai yau na sake duba ki na ga kin kwana biyu ba ki hau ba." Mirmishi Ummu ta yi kafin ta ce"  Zan mutu ba ka sani ba ne Hamma? Ta ƙarishe faɗa cikin sanyin murya. "To na sani," Ya faɗa cikin ƴar dariya. Dariyan Ummu ta taya shi kafin ta ce" Ba ni da lafiya ne fa Hamma." "Oh haka ne kwanaki mun yi waya da Amma ta ce ba ki jin daɗi, shi ne har yanzu? "E." "Me ke damun ki? "Zazzaɓi ne Hamma." Ta faɗa cikin kasalan da ta ji ya sake rufe ta bayan ta yi wanka. "Sannu. Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da Amin. Shi kuma ya tambaye ta ko ta je asibiti. "E mun je" "Allah ya ƙara afuwa sannu." Ta amsa masa da yauwa. Habib ya tambaya ta ce ya fita aiki. "Allah ya ba mu sa'a." Daga nan ba daɗewa suka yi sallama da juna kowa ya kashe wayarsa. Ɗan wayar nan da suka yi da Hamma Sadam ya ɗan rage mata damuwa. Shi fa ɗan'uwa daɗi ne da shi. Ballatana Hamma Sadam irin mutanan ne masu amfani da social media sosai, duk gidan su ba kamar sa, komai na shi kowa ya sani, shi ne instagram shi ne Twitter, shi ne Facebook kullum ba shi da aiki sai posting ɗin hotunan shi komai yake yi sai duniya ta sani. Shi ya sa duk wani labarin da ke faruwa Hamma Sadam na da labarin shi da har hoton Baffa da Amma yana kafewa a Facebook Hamma Abdulrrahaman  ne ya yi masa faɗan akan ya daina posting ɗin hotunan su Baffa in zai saka na shi ya saka amma ban da na Ammah da Baffa shi ya sa ya daina amma na shi kam bai daina ba, a ko wani hali ya ke ciki kafin ya yi mgana posting ɗin shi ya bayyana halin da ya ke ciki. Kuma shi ba ma'abocin kiran waya ba ne amma za ku yini kuna chart bai damu ba. Shi ya sa ai Hamma Sadam kodayaushe yana online ne. Sai da ta ɗan kwanta domin sai ta ji amai yana ta so mata, sannan kasala duk ya rufe ta sai wajen goma da wani abu ta iya rarrafawa ta fita. Doguwar riga ta saka na wata Atamfa sai ta yi amfani da bakin mayafi, ƙaramar jakarta ta ɗauko in da ATM ɗin ta na Banki yake tun da ba kuɗi a hannunta sai ta cire, sai da ta biya ta wani shago ta cire 5k sannan ta samu mai Kekenapep ta yi drop zuwa gida. Bai sauke ta ko'ina ba sai ƙofar gidan su dake tsakiyar anguwan Zone 3. Ta sauka ta biya shi kuɗin shi sannan ta fara takawa ta tunkari baƙin get ɗin gidan na su, a baya ba baki ba ne da Hamma Lamiɗo ya sa aka gyara gidan ne a lokacin aka sauya get ɗin gabaɗaya. Ba ta tsaya ma ƙwanƙwasawa ba ta tura ta shiga sanin da ta yi get ɗin a buɗe yake, tuni Ammah ta ce a riƙa barin shi a buɗe saboda ba za ta iya wahalan kai da kawo tsakanin get da cikin gida ba shi ya sa a buɗe yake sai dai za a tura shi amma ba za a rufe ba tun da ba maigadi, tun tuni da man gidan Baffa ba mai gadi ballatana yanzu da rayuwa ta gangara. In ka shiga gidan haraba za ka fara gani, daga yamma kuma akwai wani flat ɗakunan mazan gidan ne falo ne da ɗakuna huɗu kuma kowanne da banɗaki a ciki. Hamma Sadam ke zaune a ciki yanzu amma in su Hamma Mustapha suka zo su kan sauka a wajen ko baƙi daga Mubi dangin Ammah ko Baffa. Daga nan sai bangaren kudu akwai ɗan korido da za ka bi zuwa cikin gida wanda ke ɗauke da tsakar gida daga gefe kuma kitchen ne Babba sai yamma kuma ɗakin Baffa sai daga gabas kuma Ɗakin Ammah ne mai ɗauke da falo da ɗakuna huɗu a ciki. Sai gefen can kuma falo ne sai ɗaki ɗaya a ciki da banɗaki. Ɗakin da Mami ta yi rayuwarta kafin ta yi aure sannan anan Ammah kan sauki baƙin da za su fi sati kafin su tafi. Ɗakin a gyare ya ke, tsab kamar yadda bangaren Ammah ya ke shima kamar ɗakin wata Budurwa. Kusan duk shekara Hamma Lamiɗo sai ya sauya mata tsarin falo, Amma ta yi ta faɗa tana cewa ya bari ita ya gama biyan ta tunda ya kai ta Hajji sannan ya kai ta Umra amma ba ya ji ba ta ma sani sai dai ta ga Hamma Kabiru ya zo yana zuwa to kamar shi ne ya zo tun da duk wani abu da Hamma Lamiɗo zai yi ma Amma na suprising ɗin ta, to da Hamma Kabiru zai fara tattauna maganar sannan Hamma Abdullahi ya gabatar. Tsakar gidan duk shimfiɗe yake da interlock. Tsakar gidan tas Amma ta share shi Ummu na ta sallama da ƙaramar muryanta ta ji shuru ta dai ta san Baffa baya nan tunda ba ta ga motar da ya ke hawa a haraba ba, ɗayan ta gani Benz ce tana lulluɓe da tamfol ya jima ma bai yi amfani da ita ba.   Jikinta ba karfi shi ya sa ta kasa ɗaga murya ƙarisowa ta yi kofar falon Ammah ta ɗaga labulen tana leƙen cikin ɗakin. "Ammah." Ta faɗa a hankali tana zagaya idanuwanta a cikin ɗakin amma shuru kamar ba kowa ashe ba ta sani ba Ammah na dakin Baffa. Amma ta fito daga ɗakin Baffa ita kuma Ummu Salma ta juyo sai suka yi ido huɗu. Mamaki ya kama Amma cikin mamakin a muryanta ta ce. " Ke kuma daga ina kamar an jeho ki? Ta faɗa tana nazarinta. Kafin ta wuce ta zuwa cikin falon ta. Ummu ta ja kafafunta sannan ta cire takalmin kafanta ta bi bayan Ammah zuwa cikin falon. Kan kujera mai zaman mutum biyu ta zauna tana mai mikar da kafarta ji ta ke yi kamar ta kwanta saboda wata gajiya da ta ke jin tana sauka a cikin gangar jikinta. Amma ciki ta shiga ba daɗewa sai ga shi ta fito ganin Ummu zaune a yanayin da ba ta gane mata ba yasa ta nemi kujerun gefen ta lokaci ɗaya tana faɗin" Ke lafiyan ki kuwa? Ta faɗa tana sake kallon Ummu da ke yamutsa fuska duk da ta san halinta amma yanayin ta ya nuna ba lafiya tun ballanta ganin ta rame ta sake yin fari. "Ina mgana kin yi mini shuru? Ammah ta sake tambaya cikin fusata da sauri Ummu ta ce" Ina kwana Ammah " Ta furta cikin harshen fillanci Amma ta amsa da sauri tana cigaba da faɗin" Ko jikin ne har yanzu? Sai kawai ta gyaɗa mata kai lokaci ɗaya tana bin shawaran zuciyanta ta kwanta a saman kujeren da ta ke zaune. "Sannu. Me ke damun ki hala? "Ammah zazzabi ne? Ta ba ta amsa, ita kuma sai ta sake kallonta abin da ta gani kamar ciki ne laulayi ne ke wahalar da Ummu, amma tunda ba ta faɗa mata ba sai ba ta nuna mata ta gane ba. "Kun je to asibiti? Wannan karon ma kai ta gyaɗa mata ba ta yi mgana ba,sabo da ba ta so Ammah ta fahimci wani abu ta san halin ta yanzu nan za ta rikita lamarin ya zama ba yadda take so ba gwara Baffa shi yana da sauƙin kai da fahimta. "Allah ya sauwaƙe, ya wajen shi Habibun!? Kuna nan lafiya dai ko? Amma ta tambaya lokaci ɗaya tana mikewa. "Lafiya lau." Ummu ta amsa cikin sanyin murya sai da Ammah ta kalleta na wani lokaci kafin ta girgiza kai, jikin Ummu duk ya yi sanyi kamar ba ita ba amma ba ta kawo aran ta ba sai ta ce wataƙila laulayi ne mai zafi shi ya sa duk ta sauya. "Baffa fa? Ba ya nan ne? Ta tambaya lokacin da Ammah ke shirin ficewa daga falon. "Yanzu nan ba daɗewa ya fita zuwa cikin Yola." "Yaushe zai dawo? Ba zai daɗe ba ko? Ummu ta tambaya a marairai ce, Amma ta fasa fita ta juyo tana kallon ta. "Tare da Abdullahi suka fita watakila ba za su daɗe ba." Sai ta jinjina kai lokaci ɗaya tana mai lumshe ido. "Ummu Salma." Ta ji Ammah ta kira sunanta  da sauri ta buɗe ido tana kallon ta duk da tana kiran ta da haka lokaci bayan lokaci amma na yau cikin wani irin amo ne da ya sa ta natsuwa. "Me ke faruwa ne? Haka Ammah ta tambaya lokaci ɗaya tana tsare ta da idanuwanta, da sauri ta dukar da kallon ta ga Amma kafin ta ce" Ba komai Amma." "Kuma kike tambayan Baffa? "Kawai fa ina son ganin shi ne" Ummu ta faɗa cikin yar shagwaɓa har tana ɗan turo bakin ta gaba. Amma ta yi ƙaramin tsaki ta fice tana faɗin" In kin gan shi sai ki haɗiye shi " Har sai da ta saka Ummu dariya Ammah shagali, tana nan kwance tana mirmishi lokaci ɗaya da tunanin yadda za ta fara taran Baffa da mgana tana tufka tana warwara ba ta san lokacin da barci ya kwashe ta ba, ita dai ƙamshin wani abu ne ya tashe ta, tana tashi sai ta ga Ammah ce ta dama kunu da ya ji kayan kamshi shi ya sa ƙamshin ya cika falon ta. "Amma zan sha kunun." Ummu ta faɗa lokaci ɗaya tana tashi zaune, ɗankwalin ta ya fita kanta kitso ne duk ya tsufa har ya fara zarewa da kansa. Ba ta da wata natsuwa ballanta ta iya tsefewa ta sauya wani. "Ga shi nan ki diɓa, da ma Abdulrrahaman ne ya ce na dama masa yana nan zuwa " Sai da ƙirjin Ummu ya amsa a cikin zuciyarta ta ce Allah ya sa lokacin da zai zo ta gama mgana da Baffa domin masifaffe ne in ya ji wannan mganar zai iya ɓata komai a lokaci ɗaya ba tare da ya damu ba. Tana kallo Ammah ta diɓa masa a cikin ƙaramin fulas sannan ta bar mata sauran a ƙaramin botikin da ta dama kunun da cewa in ta tashi za ta sha sai ta samu kofi ta diɓa daga nan Amma ta fice daga falon zuwa Kitchen. Tana son kunun ya biya mata rai, duk da tana tsoron amai haka nan ta tashi ta fita ta ɗauki kofi saman frizan Amma ta zuba kunun ta koma ta zauna tana sha, har wani lumshe idanuwana take yi saboda da daɗi, da man in dai Ammah ta yi girki ko da dama abu daɗi ne da shi ballatana garin kunun ta na daka ne, yana jin kayan ƙamshi in ta dama ma shi ya yi ta tashin ƙamshi. Kamar abun arziƙi ta shanye kofin da ta ɗiba daga farko har ta kara wani ma, sai dai tun kafin ta yi rabin shi zuciyarta ya fara tashi kafin ta yi wani yunƙuri amai ya taso mata ai da gudu ta faɗa ɗakin Ammah ta shiga toilet ɗin ta, ta fara kelaya amai gabaɗaya abin da ta ci sai da ta amayar da shi, tana cikin yiin aman ne Ammah ta shigo ɗakin har sai da ta leƙo ta. "Sannu." Ta ce mata sannan kumavta shiga ta kama ta bayan ta ɗauraye bakin ta, sai ta ce ta fita bari ta wanke wajen, kan gadon Ammah, Ummu ta faɗa tana ma yar da numfashi tas Ammah ta wanke tiolet ɗin sannan ta fito tana kallon Ummu da ke kwance kamar ruwa ba ta sake yin mgana ba ta kaɗa kai ta fice daga ɗakin. Ita kuma Ummu aman da ta yi duk ya sake sakar mata da jiki, kasalan da ta ke ji daga farko ya sake zuwa ya rufe ta da take jin ta kasa tashi sai kawai ta sake naɗewa a kan gadon Ammah ta jawo filo ta rumgume ta lumshe ido tana sauke numfashi sama-sama. Daga nan sai barci ashe ta daɗe tana barci ba ta sani ba. Sai bayan azahar ta farka. A lokacin ta iya tashi sai dai ta ji yanayin jikin na ta ya ɗan saki tiolet ta shiga ta sake ɗauro alwala ta yi salla ta idar kenan tana kan darduma Amma ta shigo. "Kin tashi? "E Amma sannu da aiki " "Yauwa, ga Baffan can ya dawo " Amma ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon Ummu. "Ki ci abinci tukunna shima abincin yake ci." Sai ta gyaɗa mata kai ba tare da ta yi mgana ba. "Bari na yi wanka." Haka Amma ta faɗa, lokaci ɗaya kuma tana tura kofar tiolet ɗin ta shiga. Shuru Ummu ta yi kafin ta yi saurin mikewa gwara ta je ta samu Baffa da maganar kafin Ammah ta fito daga wanka. Tana fita falo sanye da hijabin Ammah ta iske ta zuɓo mata abinci a kula da ruwa tana dubawa sai ta ga Dambun shinkafa ne da zogale. Allah sarki Ammah ta ɗauka har yanzu tana son dambun shinkafa da zogale ba ta san yanzu duk wani abu da take so a baya yanzu ya fita ran ta ba, amma ƙamshin gyaɗan da ke tashi a dambun ya sa miyan ta ya tsinke ba ta ci ba sai ta rufe da niyyar sai sun gama mgana da Baffa tukunna. Ta gode ma Allah da Hamma Abdullahi bai biyo ta gidan ba, ba ta son kowa ya san mganar nan sai Baffa ta fi amin ta da tunanin shi akan na kowa. Sallama ta yi a ɗakin Baffa ba ta shiga ba sai da ya amsa mata. Yana zaune a ƙasa a saman darduma yana cin dambun da Amma ta yi, gefe ɗaya da kunu da ruwa a saman wani faranti Tana shigowa ya ɗago yana kallonta nan da nan ya faɗaɗa mirmishin sa. "Autan Baffa" Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai cire hannun shi a filet ɗin Dambun. Itama cikin fara'a da farinciki ta zauna a gaban shi lokaci ɗaya tana faɗin. "Baffa." Ta faɗa cikin yar shagwaɓa, Baffa na dariya ya ce" Na dawo Amman ki ta ce kin zo kina tambaya na " "To Baffa na yi kewarka ne. Ba ni da lafiya daga kai har Ammah ba wanda ya zo ya duba ni" Da man ƙiris take jira sai hawaye, shi kuma ya shiga aikin lallashin ta da cewa suna shirin zuwa ne sai ga shi ta zo amma in ta koma zai matsa ma Ammah ta shirya su je su duba ta. "Da gaske Baffa? Ta faɗa tana kallon shi, shi dai ya je ɗakin ta sau ɗaya ɓarin da ta yi amma Ammah ba ta taɓa zuwa ba, shi ya sa take mamaki da ya ce mata za su zo. "In sha Allahu." Ya faɗa yana dariya, in ban da rigiman Ummu me zai kai su gidan ta, amma saboda ya san halin ta ya sa ya lallaɓata da za su zo, abincin ya ce ta zo su ci sai ta ce nata na ɗakin Amma, shima kaɗan ya ƙara ya ce ya ƙoshi. Ummu ta ɗauko masa wata roba ta zuba masa ruwa ya wanke hannunsa sannan ta kwashe kwanukan da ya yi amfani da su ta mayar kitchen ita saurin ta kafin Ammah ta fito ta sanar ma da Baffa abin da ke faruwa shi ya sa tana dawowa ta sake tankwashe kafafu a gaban shi tana kallon shi, yana kurɓan kunun sa lokaci ɗaya yana nazarin Ummu. Tambayanta jikinta ya yi ta ce da sauƙi. "Ya wajen shi Habibun? Fatan yana nan lafiya ko? Habibin da ya ambata kamar ya yi mata fami ne, sai ta fara marairaicewa kafin Baffa ya sake mgana Ummu ta kece masa da kuka cikin tashin hankali ya ajiye kofin hannun shi yana kallon Ummu. "Kuka Ummu? Me ke faruwa ne? Wani abu ne ya samu Habibun? Ya faɗa duka a jere, kai ta girgiza masa kafin ta kira sunan shi. "Baffa." "Naam Ummu Salma." Kukan ta ya ki tsayawa hawayenta suna zuba tana saka gefen hijabin jikinta tana gogewa. "Me ke faruwa ne? Baffa ya sake tambayan ta cikin kyakyawan lafazi. "Baffa." Kafin ya amsa ta cigaba da faɗin" Da ma, da ma ina da ciki ne." Sai kawai Baffa ya washe baki yana faɗin" Ma sha Allah. Wannan ai abun murna ne ba na kuka ba Autan Baffa." Kallon sa ta yi kafin ta ce" Baffa Habib ya ce ba ya son cikin fa" Baffa ya zuru yana kallonta cikin mamaki kafin ya ce" Ban gane ba ya son cikin ba kamar ya ya? Ummu-Salma ta sake fashe masa da kuka ƙasa-ƙasa ta kasa mgana. "Kukan kuma dai Auta! In ba ki bar kukan nan ba ta ya ya za ki yi mini bayanin da zan fahimce ki? Ya faɗa cikin damuwa saboda tunaninsa ya tsaya a dalilin kukan Ummu saboda mijinta Habib ne kuma ya shafi cikin jikin ta. "Baffa kai kaɗai ne za ka iya taimako na. Shi ya sa na zo wajen ka." Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce" In sha Allahu Auta sai dai abin da ya gagare ni, sai na bar ma Allah ya yi na shi ikon." "Baffa ina son Habib." "Na sani." Baffa ya ba ta amsa a ɗokance domin ya ƙosa ya ji dalilin Habibu na cewa ba ya son ciki. "Ba na so na rasa shi, ko na rasa aurena." "In sha Allahu alheri ne zai biyo baya Ummu-Salma.". Ya kira sunanta, suna mai darajan da ba ya iya kira saboda sunan mahaifiyar shi ce sai dai ya ce Ummu ko Autan Amma ko Autan Baffa amma tun da ta ji ya kira sunan ta tasan wasa kuma ya ƙare. "In ba ki yi mini bayanin abin da ke faruwa ba, ai ba zan iya taimaka miki ba Auta" Tana kuka tana shessheƙa ta labartama Baffa abin da ke faruwa amma ta ɓoye maganganun Habib a kan ta na cewa ba ya son ta auren sha'awa ya yi da ita sannan ta ɓoye hanyoyin da ya bi wajen mata barazanar ta zubar da cikin, ta dai  faɗa ma Baffa zaman su ya lalace domin Habib ya ce in har ba ta bi umarninsa ba, yanzu suka fara yar tsama a tsakanin su. "Innalillahi wa'innna ilaihirraju'un" Baffa ya dire salatinsa cikin mamaki yana kallon Ummu yadda take kuka kamar ran ta zai fita. "Baffa don Allah ka kira Habib ka yi masa faɗa na san yana jin maganarka. Ka faɗa masa ina son cikin nan ba zan iya zubar da shi ba" Ta sake faɗa cikin kuka Baffa ya yi shuru lamarin na ɗaure masa kai , ina aka taɓa haka? Ka yi ciki da kan ka sannan ka dawo ka ce ba ka so sai an zubar. "Don Allah Baffa." Ta sake roƙon shi, tausayi ta ba shi Ummu ta faɗa cikin kaddaran aure tun tana da ƙananun shekaru. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Abin da ban gane ba, me ya sa ba ya son ciki? Mene ne dalilin shi na cewa sai an zubar? "Baffa wai ba yanzu ya tashi haihuwa ba." "Ka ji wani shirmen banza. Da man shi ke da wannan tsarin ba na Ubangji ba ne? Habibu ya ba ni mamaki ina ɗaukan sa mai hankali ashe kallon kitse na ke yi ma rogo ban sani ba? Baffa ya faɗa cikin bayyana mamakinsa domin abin da ya yi, aikin jahilai ne mara sa ilimi da tarbiya. "Tun yaushe ne kuka cikin wannan yanayin? "An fi wata fa Baffa." Ta faɗa tana cikin dashewar murya lokaci ɗaya tana share hawayenta da gefen hijabin jikin ta. "Me ya sa tun a lokacin ba ki zo kin faɗa mini ko Amman ku ba? "Baffa na ɗauka za mu iya warware matsalan ne da kan mu." Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Ni lamarin ne ya ɗaure mini kai. Ban taba zaton haka daga Habibu ba." "Nima ban yi zato ba Baffa." Ta faɗa cikin sanyin murya. "Ki yi hakuri Auta. Amma ba ni ne zan yi ma Habib mgana ba. Ta in da aka hau ta nan za a sauka." Ya faɗa yana kallon ta, kafin ta yi mgana ya rigata da cewa." maganar ki zubar da ciki ma bai taso ba tun da lafiyan ki lau, saboda haka waliyin shi wanda ya karɓan masa auran ki za a yi ma mgana su za su kira shi su yi masa magana." "Baffa me ya sa kai ba za ka yi masa da kan ka ba? Kai tsaye Baffa ya ce" Maganar ba ta ni kaɗai ba ne, dole a sako waliyin shi a ciki " Ummu ta yi shuru kanta na ƙasa Baffa bai fahimci abin da take tsoro ba. Kamar ya san abin da take tunani ya kalle ta yana faɗin" Ki kwantar da hankalin ki, Baffan ki Umaru zan yi ma waya shi zai kira waliyin na shi mu ji me zai ce." "Baffa ina son Habib, ba na so a raba mu " Ummu ta faɗa cikin karyewan sauti kamar za ta sake fashewa da kuka. Baffa na shirin mgana su ka ji sallama, gaban Ummu ya amsa domin ta ji muryan Hamma Abdurrahaman. "Ammah ko ba ta nan ne? Ya faɗa daga tsakar gida, kafin kuma ya kariso ɗakin Baffa tun da ya ga motarsa ya san yana gida, balle ma ya yi waya da Ammah da safe ta ce ya fita tare da Abdullahi amma ba za su daɗe ba.   Jikin Ummu ya fara rawa lokacin da Hamma Abdulrrahaman ya shigo ɗakin Baffa da sallama ta kasa iya ɗago idanuwana ma ta kalle shi, fatan ta ka da Baffa ya sanar da shi abin da ke faruwa. "Abdulrrahman lale sannu da zuwa." Baffa ya faɗa cikin mirmishi, shima Hamma Abdulrrahaman ɗin cikin fara'a ya amsa yana mai zama kusa da Baffa a saman darduman da ya ke zaune sai a lokacin ya kula da Ummu. "Ke lafiya? Ya faɗa yana kallonta kafin ya juya yana kallon Baffa. "Baffa me ke faruwa ne? Saboda irin zaman da ta yi ne ya sa ya ji kamar jikinsa bai ba shi ba. "Lafiya lau. Ya aiki da wajen iyalan naka? Baffa ya faɗa yana mirmishi, ya amsa da duk suna lafiya yana sake nazarin Ummu da ke dukar da kai kamar munafuka. "Na zo nan kusa ne kan wata sharia da na kai ne a yanzu." "Allah ya ba ka nasara." Ya amsa da Amin. "Ke jira kike ni na fara gaishe ki? Hamma Abdurrahaman ya fada a ɗan zafafe. Baffa ya yi saurin tare shi da faɗin". To sarkin ƙorafi yaushe mu ka gama gaisawar ballanta ma ta samu damar gaishe ka? "Baffa kar ka kare mata, mintina na nawa da shigowa ɗakin nan? "A yi haƙuri." Baffa ya faɗa yana ɗan mirmishi. "Hamma ina yini." Ummu ta faɗa muryanta na rawa, lafiya lau ya amsa sannan yana sake kallon ta. "Kin yi ciwo ne? Ya faɗa daidai da ta tashi za ta bar ɗakin na Baffa. Sai ta juyo tana kallon shi duk da ya ɗan kwana biyu bai gan ta amma ta lalace da yawa. "Ta yi zazzaɓi kwana biyu." Baffa ya amsa mishi, kallon shi ya yi kafin ya sake kallonta ya ce" Baffa wannan ya wuce zazzaɓi, idanuwanta da fuskarta sun nuna tana cikin damuwa." Baffa na dariya ya ce" To lauya." Shima sai da ya yi dariyan da haka Ummu ta so ta sulale Hamma Abdulrrhaman ya tsare ta da cewa ta dawo ta zauna  jikinta na rawa gabanta na faɗi ta koma ta zauna a in da ta tashi. "Ke kina da wata damuwa ne? Ya faɗa yana mai tsare ta da ido, har yana sauke jakar hannunsa a ƙasa, sanye yake da suit ya tsuke, da man Hamma Abdulrrahaman in ya ta saka ka gaba ba ka iya ƙwatan kan ka, aikin lauyancin har a gida yana yi, in yafara jefa maka uban tambayoyi sai ka fara zufa ma ba ka sani ba. "Ko mijin na ki ne ke ba ki wahala! Kin rame sannan fuskarki ba ta cikin walwala." Ya sake tambaya kanta na kasa ta kasa mgana sai rawan hannu take fama da shi duk yana lura da ita. Baffa na so ya yi mgana ya katse shi da cewa" Baffa da wani abu ko! Wani abu na damun yarinyar nan kamar mai depression kalli yadda hannayenta ke rawa? Baffa na dariya ya ce" Kai ne ka saka ta rawan hannu. Daga zuwan ka, ka fara mata tambayoyi sai ka ce a kotu." Baffa na so ya ɗan shashantar da maganar amma Hamma ya ƙi yarda saboda ya fahimci akwai wani abu. "Baffa wani abu na faruwa, kai ma fuskar ka ta bayyana damuwa." Baffa ya kasa mgana, da gaske ne tun da Ummu ta faɗa masa abin da ke faruwa ya rasa abin da ke yi masa daɗi. "Ya kamata na sani Baffa? Ya tambayana yana kallon shi, Ummu kuma Baffa take kallo tana girgiza masa kai, karaf ko ya ganta da sauri ta mai da kanta ƙasa tana jin hancin jikinta na ƙalawa saboda tsoro. "Baffa me ke faruwa? Ya faɗa cikin  muryan da ba wasa a cikin ta. Baffa ya yi gyaran murya sannan ya shiga sanar da shi abin da Ummu ta gama faɗa masa. "Yanzu nan da ka gan mu, nima ta gama faɗa mini abin da ke faruwa kenan." Hamma Abdulrrahaman ya yi shuru kafin ya ce. " No wonder na ga yarinyar nan duk ta lalace, ba ma za ta rasa depression ba." Baffa ya yi shuru bai yi mgana Hamma Abdulrahaman ya kalli Ummu ya fara faɗin" Shi don uban shi bai shirya haihuwa ba yanzu ya zo ya aure ki? Ya san bai shirya haihuwa ba ya yi aure? Ji wani rashi tunani don uban shi ba a haihuwa shi aka haife shi? Ya ƙarishe faɗa cikin ɗaga murya jikin Ummu ya fara rawa kafin ma ta samu damar magana Ammah ta faɗo ɗakin tana faɗin" Waye kuma ba ya son haihuwa? Ta yi turus ganin Ummu zaune tana rawan jiki ga Hamma Abdulrrahaman na ta bala'i Baffa na zaune a gefe bai yi mgana ba. Ta ji zuwan shi lokacin tana salla ne amma yanayin da ta gan su  a ciki ya sa jikin ta ya yi san yi. "Baffa me ke faruwa,? Ta faɗa tana mai zama a gefen Ummu. "Me aka yi ma wannan ta ke rawan jiki? Ammah ta sake tambaya tana mai kallon Ummu da har ta fara hawaye. "Au kema ba ki sani ba? Hamma Abdurrahaman ya tambaya yana kallon Amma. "Mene ne? Ban sani ba" Ta faɗa cikin mamaki, Hamma Abdurrahaman bai tsaya ba ya kwashe komai ya faɗa ma Ammah yana fada mata tana sake kallon Ummu cikin mamaki. "Na zo na same ta durkushe a gaban Baffa kamar wata marainiya, ba ta so na ji mganar ba ne. Raina ya ɓaci sai da lokacin nan Kabiru ya yi ta cewa an yi gaggawa Baffa ko fa bincikan shi yaron ba a yi ba sosai in da an yi bincike sosai ta ina za a aura mata ɗan iska wanda ba ya son haihuwa. ? Wato in ma wajen zubar da cikin wani abu ya same ta shi ba shi da asara kenan ko? Ya sake faɗa har yana ta yar da jijiyan wuya. "Duk binciken da ya kamata a yi an yi Abdurrahaman kuma ba a same shi da wani abu na ashha ba." "To Baffa wannan dai abin assha ne, jahilci tsantsan da rashin tunani. Tunda cikin ya shiga sai ya bar shi ta haihu can tsakaninsu za su iya tsayar da haihuwa da fahimtar junan su duk ana haka ba matsala ba ne. Amma kawai ya ce sai ta zubar da ciki da karfin tsiya wannan ya saɓa ma doka. In muka yi ƙaran shi sai ya gane ba shi da wayau" "A'a ba za a yi haka ba." "To Baffa me ye amfanin zama da mara mutumci? A raba auren kawai." Da sauri Baffa ya ce" Na ce aa ko,  shi ya sa ban faɗa maka da farko ba sanin halin ka na saurin yanke hukunci." "To Baffa me kake so a yi? Hamma Abdurrahaman ya faɗa cikin sarander Ammah mamaki ne ya sa ta kasa mgana tunani take yi lokacin da Ummu ta yi ɓarin cikinta na farko yadda Ummin ikki ta ce ya damu, to yanzu kuma da ya kamata ya yi murna me ya sa zai ce ba ya so? "Baffan ku Umaru zan kira, shi zai kira waliyin shi ya faɗa masa sai mu ji abin da ya kamata mu yi nan gaba." "Baffa ya fa san da waliyin na shi ya ce sai ta zubar da ciki. Ni ina ganin a biyo da shi ta hanyar da ya biyo, ka ji fa ta ce yana azabtar da yarinya yana so ya yi mata dole." Baffa ya tare shi da cewa" Duk da haka dai a fara sanar da su, a bi komai a hankali." Amma ta jinjina kai kafin ta ce" Baffa ya yi gaskiya a fara sanar da su a ji su kuma na su hukuncin. Amma dai Habibu ya ba ni mamaki ban zaci haka daga wajen shi ba." "Nima haka wallahi." Baffa ya faɗa shima cikin ɗan damuwa Ummu kuma hawaye ta ke sharewa ta kasa mgana. "Ni da man na san za a yi haka. Yaro ne fa ƙarami Baffa yarinyar nan da karatunta ta cigaba amma ta na ce ta ce aure za ta yi ai ga shi nan kin fara ganin uwar da ke cikin auren." Baffa sai da ya yi dariya Amma ta kauda kai ba ta yi magana ba. "Ba yadda ba mu yi da ke ki cigaba da karatu ba kika ƙi, kika ce ke aure ke yar soyayya to yau duk ina soyayyar! Tun da kin samu ciki ya ce dole sai kin zubar? Kin ga wawancin da muke faɗa miki kin yi ko a wancan lokacin ko? Auran ki ko shekara bai yi a ce su Baffa sun fara sulhu tsakanin ku? Da yau karatun ki kike yi da ba ki yi kuka ba" Ya sake faɗa yana kallon Ummu yadda take kuka har yana fidda sauti. "Na so ki cigaba da karatu, na so ki yi karatu. Nawa kike Ummu? Just 24 to 25 kina da sauran damarmaki masu yawa amma kika ƙin jin maganar mu, Baffa da Hamma Jibo suka mara miki baya. Yanzu don Allah ina amfanin a fara kiran su Baffa Umru da magarnar ki? Yaron ma ba shi da mutumci in har ba zai sauke kudirinsa ba ya sake ki kawai " Ummu ta sake jin kuka ya taso mata, domin ta san  ko giwar wake ta sha ba ta isa ta ce ma Hamma Abdulrrahaman tana son Habib ba ta son rabuwa da shi ba, ta tabbata sai ya yi ball da ita shi ya sa ta yi shuru tana ta kuka shi ko yana ta faɗa da masifa Baffa ne ke tausan shi amma bai haƙura ba. "Kaddara ta riga fata fa, Abdulrrahaman. Fatan mu dai Allah ya sa lamarin ya zo da sauƙi." Ammah ta faɗa, ita tausayin Ummu ta ke ji. Ita mace ce sannan ƙarin tausayin ta da fatan ta kar Ummu ta fara fuskanta kaddaran aure da ƙananun shekarunta. Ita ta zauna da Fatima lokacin da kaddaran aure ta faɗa mata da shekarunta sha bakwai a duniya ita kaɗai ta san siraɗan da fatima ta tsallake kafin ta iya tsayuwa da kafafunta. Fatan ta Ubangiji ya zaunar da Ummu a ɗakin auren ta na har abada ya kuma sassauto da zuciyar Habib a kan ta. Kar Allah ya sa ta ɗanɗana zafin zawarci har abada a rayuwarta. "Fatan da za mu yi kenan tun da mai afkuwa ta faru. Kuma bawa bai isa ya sauya zanen kaddaran sa ba." Baffa ya faɗa, amma shi fa Hamma Abdulrrahaman bai yarda ba faɗi yake yi har da kuskuran su Baffa. Amma ta ga Autar ta nata kuka ya sa ta shigar mata. "Don Allah ka kyale ta Abdurrahaman ba ta ko da cikakkiyar lafiya!. Ke ta shi ki je ki ci abinci" Ammah ta cece ta, ta samu ta bar ɗakin Baffa tana kuka zuwa falon Ammah ta faɗa saman kujera ta saki kukan ta shike nan abin da take gudu ya faru ya za ta yi ma Hamma bayanin yadda take son Habibu ta ke kuma son cikin jikinta da aurenta. Ta tabbata ba zai taɓa ganewa ba gwara Baffa shi ne zai fahimce ta da halin da ta ke ciki ba amma ba su Hamma Abdulrrahaman ba da daman yana cikin yan adawa da auran ta da Habib. Ummu ba ta sake fitowa daga falon Amma ba har sai da Hamma Abdulrrahaman ya tafi, la'asar na yi ta yi salla ta ce ma Ammah za ta tafi da ta ce mata tun yanzu sai ta ce za ta biya gidan Ummin ikki, dambun ma ba ta ci ba ta ɗauka ta ce sai ta je gida Baffa ma ya fita masallaci bai dawo ba ta tafi, Amma dai ta faɗa mata an kira Baffa Umaru ba a same shi ba amma Baffa ya ce zai sake kiran shi. Har haraba Amma ta raka ta, tana ta sake jadadda mata ta kula da kanta. Gida ta koma da man dai ta ce ma Ammah za ta je gidan su Baɗɗo ne saboda kar ta ce ta tafi da wuri, nan ko hankalinta ne ke tashe ba ta san yadda Habib zai yi in ya ji mgana ta kai wajen waliyin shi ba, tsoro ta ke ji shi ya sa ta kasa zaman gidan sannan da fargaban kar wani ya sake zuwa Baffa ya sanar da shi abin da ke faruwa a sake sauke mata wani masifan. A waya kawai ta kira Baɗɗo suka yi mgana ta sanar da ita ta je gida ta faɗa ma Baffa. "Gwara hakan, in manya suka shiga ciki sai asan mafita." Ita dai ba ta ce komai ba ta ma kasa ba ta labarin karon ta da Hamma Abdulrrahaman Ranar da Habib ya dawo tana ta jiran ko za ta ji ya yi mata wata mgana ba ta ji ba, yadda ya saba mata haka ya yi na mantawa ma da wata hallita a gidan. Washegari Shamsiya ta kira ta, tana tambayanta yadda ake ciki , tana kuka ta sanar da ita halin da ake ciki. "Kash. Bestie kin yi kuskure na so ki yi amfani da shawara ta kafin maganar ta kai wajen su Baffa." Ummu ta rantse mata da cewa bata san cewa haka lamarin zai koma ba, sannan ita dai tana son cikin jikinta ba za ta iya rabuwa da shi ba. Shamsiya dai ita tana ganin laifin Ummu ne Habib ne ke da gaskiya. Ita a ganin ta ahakan ba wani abu ba ne, normal ne. Tunda yanzu yin tsarin iyali domin taƙaita haihuwa ya zama ruwan dare. *** A ranar Baffa bai samu Baffa Umaru a waya ba sai a washegari ya same shi sannan ya sanar da shi abin da ke faruwa. Shi kan shi Baffa Umaru faɗa ya hau yi yana cewa ai wannan shirme ne. Suna gama waya da Baffa nan take ya lalubo lambar waliyin Habibu kanin mahaifinsa Alhaji Sheriff, tun lokacin neman aure suke da lambar juna. Yana kiran shi bayan gaisuwa da tambayan iyalan juna. Sannan Baffa Umaru ya zayyane masa halin da ake ciki. "Wani shirme ne haka Habibu ya aikata? Shi ba a haihuwa iyayen shi suka haife shi? Kuma ya san ba ya son haihuwan yanzu bai ɗau mataki ba sai da cikin ya samu? Ai ko bai isa ba " Sun yi sallama da juna akan cewa zai yi ma Habibun waya ya ce ya zo gida ya same shi. Yadda suka yi zai kira shi, nan take ya kira Baffa ya faɗa masa yadda suka yi da waliyin Habibu shima suka rabu da cewa sai yadda ta yuyu in ya kira shi zai sake kiran shi. Habibu kuma bai san abin da ke faruwa ba kiran Alhaji Shariff kawai ya samu da cewa ya zo gida yana son ganin shi, a ranar ya je bayan ya taso daga wajen aiki ya ji mamakin jin maganar cikin Ummu a bakin shi, faɗa ya yi masa kaca kaca da cewa bai isa ya sa a zubar da cikin ba. Tunda ya bari aka samu cikin sai an haife shi Kuma kar ya sake jin wata magana nan da nan Habib ya ce shi bai tilasta mata sai  ta zubar da ciki ba. Shi kuma Baffa Umaru ya ce Habib ɗin ya turtusa ma Ummu akan ta zubar da ciki, jin haka ya sa Alhaji Sheriff ya kira Baffa Umaru ya ce ya zo garin su haɗu a gidan Baffa tare da su Habibun a yi magana gabaɗaya.   Shi kuma ya bashi tabbacin, zai zo cikin satin in sha Allahu. Habibu dai ya san matsayar mganar tun da Alhaji Sheriff ya faɗa masa ga matsayar da aka tsaya. Ita dai Ummu ce ba ta sani ba sai ana gobe zaman Baffa ya kira ta a waya ya faɗa mata ba domin shi ba da ba za ta sani ba. Tunda Habib ba ya magana da ita ballanta ya sanar da ita. Kuma adaran ta fito shan ruwa suka haɗe da Habib ya fito daga tiolet tana ganin shi sai da gaban ta ya faɗi tunda yanzu ganin sa ba alheri ba ne a wajen ta. Ta yi saurin faɗawa Kitchen tana sauke numfashi, ta ɗan jima kafin ta fito bayan ta sha ruwan sai dai me tana fitowa ta ga Habib na zaune a falon abin da ya daina yi tun bayan lalacewar zaman su, sun haɗa ido ya yi mata wani kallo gabanta na faɗuwa ta dukar da kai za ta wuce ta ji maganar sa a sama. "In da kike tunanin kin kaini da niyar na fasa ƙudirina to kin yi kuskure domin nan duniya ba wanda ya isa ya sauya mini ra'ayi na " Ummu ta ɗago tana kallon shi cikin mamakin kalaman shi.. Ido ya zare mata sannan ya gyaɗa mata kai alamun tabbatarwa. "Haka na faɗa, saboda haka kin yi kuskure kuma sai kin yi nadama." Yana gama faɗin haka ya yi tsaki, ba domin ta matsa ba da ya ture ta, in kuma ta faɗi ba shi da asara. Da kallo ta bishi na tsantsan mamaki da al'ajabin maganganunsa yana nufin iyayen ta da iyayen shi, ba su isa da shi ba kenan. Ta tabbata Habib da gaske yake yi tun tana tunanin lamarin shi wasa ne har dai ta amince da cewa Habib ya sauya duk abin da ya faɗa akan ta gaskiya ne tunda ga shi nan yana aikatawa a aikace. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *08* Asabar. *8:30am* Washegari ta kama asabar ɗin karshen mako ne, tun ƙarfe takwas da rabi na safe Alhaji Sheriff ya kira Habib da umarnin ya zo gida yanzu-yanzu yana son ganin shi, yana barci ne ma ya tashe shi haka nan yana tura baki da ƙunƙuni ko wanka bai tsaya yi ba ya sauya kaya ya fita. A tunanin shi ma ko ya kira shi daga can su wuce gidan su Ummu Salma ne, sai kuma ya ji akasin haka. Domin ɗaki Baffan na shi ya saka shi yana ta yi masa faɗa da jan kunne. "An juma za mu haɗu acan gidan su iyalin naka. Habibu kai da kanka ka zo ka same ni cikin girma da arziƙi, ka ce kun daidaita da wannan yarinya mu je a nema maka auran ta, ga shi iyayenta masu mutumci da dattako ne. Ba za ka dawo daga baya ka kunyata kanka sannan mu ma iyayenka ka kunya tamu ba, don Allah in mun je ka ba ma iyayenta haƙuri maganar ciki kuma tunda har ka ɗiga shi to sai dai ka yi haƙuri bayan ya fito duniya daga baya in har kun gama daidaitawa da matarka to wannan ruwan ku ne, ku tsayar da haihuwa har na tsawon shekarun da kuke so ba ruwan mu a aciki. Amma yanzu maganar zubar da ciki ka janye ta Habibu." Shuru kawai ya yi yana sauraran shi, amma ba ya jin zai iya aikata abin da ya ke so bai shirya ba. Ko ma ya shirya to ba da Ummu ba amma sanin ko ya zauna yana yi ma Baffan na shi bayani ba zai gane ba shi ya sa kawai ya yi musu shuru, sai dai maganar zubar da ciki ba gudu ba ja da baya. "To Abba in sha Allahu" Haka Habib ya faɗa ba wai domin ya saduda ba yana nan akan bakan shi. "Allah ya yi maka albarka." Ya amsa da amin kansa na ƙasa. "Abba ko za ka shirya ne sai mu je daga nan? Habib ya tambaya nan take ya ce masa aa ya koma gida ya ɗau matarsa su haɗu acan ƙarfe goma ne kar su makara. Habib ba haka ya so ba domin shi ba ya ƙaunar ma Ummu Salma ta sake zama a kusa da shi, yadda ba ya son ta haka ya tsani ya gan ta a kusa da shi amma saboda kar ya yi masa gaddama a yanzu anan gaba ya ƙi yi masa amfanin da yake so shi ya sa ya amsa masa da to. Yana fita daga gidan ƙanin mahaifin na sa, ya shiga mota ya bar anguwa yana hanya ya ɗau waya ya lalubo lambar wayar Ummu Salma da tuni ya daɗe da blooking ɗin ta shi ya sa ko ta kira shi ba ta samun shi, wayar tana ta ringing gabda za ta yanke ta ɗauka murya a cunkushe ta yi masa sallama da mamaki a muryanta na dalilin me ya sa Habib ya kira ta kuma yau? "Kar ki fita ki jira ni gani nan zuwa." Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya ya yanke kiran yana mai sakin tsaki shi kaɗai, ba domin yana da wata manufa anan gaba ba, da ba wanda ya isa ya saka shi zuwa gidan su Ummu shi fa ya daɗe da gamawa da ita, sai dai in ya yi gaddama nan gaba ƙwaɓarsa za ta iya yin ruwa shi ya sa yake bi a hankali a yanzu. *** Kiran da Habib ya yi mata a waya ya ɗaure mata kai. Yaushe rabon da ya kira ta a waya har ta manta. Da man tana ɗan share falon ne ganin ya yi ƙura ta ɗan jima ba ta share ba tana fama da kanta ta ji ana kiran wayarta a ciki tana zuwa ta ga shi ne, tunda ya ce ta jira shi gabanta ya yanke ya faɗi ta kasa sukuni domin ba ta san da abin da zai zo da shi ba. A haka ta gama sharan ta yi wanka tana cikin shiryawa ya shigo gidan bai neme ta ba ya shiga ciki sama da mintina talatin ya fito sannan tana jin ya sake fita amma bai neme ta ba, tana zaune gefen gado ta yi tagumi ya sake kiran ta a waya. "Malama ki fito ina waje" Haka ya faɗa a fusace kamar zai kai mata duka ta cikin wayar, jikin ta a sanyaye ta ɗau hijabin da ta fito da shi dogo jalbab, ta zura lokaci ɗaya tana rataya baƙar jakarta haka ma takalmin kafanta ma baƙi ne keys ɗin gidan ta ɗauka sannan ta fita ta kulle ƙofar baya cikin haraban gidan a can wajen get ta gan  shi yana jiran ta a cikin mota. Tana zuwa ta buɗe ta shiga a sanyaye ko kafin ta gama ma rufe ƙofar motar ya fizgi motar a guje sai da ta firgita. Kallon shi ta yi ya haɗe fuskar nan kamar hadari, da sauri da kauda kanta saboda hawaye sun kawo mata sai ta yi saurin shanye su. "Ina kwana." Ta faɗa muryan ta a sanyaye, yau da ta ga Habib sai ta ji ba za ta iya ɗaukan kaddaran rasa shi ba, tana son shi kuma tana son ta ƙarishe sauran rayuwanta da shi har abada. Da ta gaishe shi da farko bai amsa ba sai ta sake gaishe shi nan ma sai ya yi mata banza kamar bai san tana ma cikin motar ba, ita kuma tana ce sai ta gaishe shi ya amsa. "Ina kwana Noori? Ta sake faɗa cikin marairaicewa. Wani kallo ya yi mata na tsana da takaici ita wai ba ta da zuciya ne haka ya faɗa a cikin zuciyarsa? Duk yadda ya ke share ta da nuna mata ba ta da wani muhimmanci a rayuwarsa bai sa har yanzu ta fahimci da gaske yake yi ba, watakila sai ya sake nuna mata matsayinta sosai wataƙila a lokacin za ta fi gane matsayin ta. Kallon da ya yi mata ne ya sa ta kama bakinta ta yi shuru, har suka isa gidan su dake anguwan Zone 3, da suka iso ta ga bai fito daga motar ba ya dai yi parking a bakin get ɗin su, itama ganin bai fito ba sai ta zauna shi kuma ya ɗauko wayarsa yana dubawa shuru ya ji ba ta fita daga motar ba sai ya juya yana mata wani kallo cikin mamakin ta. "Sai na ce ki fita za ki fita? Ya faɗa yana ware mata idanuwanta da sauri Ummu Salma ta buɗe motar ta fita tana kallon shi, kauda kansa ya yi lokaci fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Jikinta a sanyaye ta taka ta nufi get ɗin su, ta tura ta shiga ciki amma sai da ta tsaya a haraba ta daidaita kanta sannan ta shiga cikin gidan. Ammah da Baffa tare da Baffa Umaru suna cikin ɗakin Baffa suna ta hira can ta nufa ta shiga da sallama ta duka a gaban su tana gaishe shi. "Auta kin iso? Baffa ya faɗa, sai ta gyaɗa masa kai, ba su daɗe da gama karyawa ba tunda ga kayan karyawan nan a gaban su Ammah ba ta ɗauke ba. Sannan tun wajen tara  na safe Baffa Umaru ya iso Jimeta. "Sannu Ummu Salama." Baffa Umaru ya faɗa yana kallon ta ganin yadda ta ɗan rame,  yana shigowa Jimeta Harkokinsa sosai kuma yana zuwa gidan ɗan'uwan na shi, kuma duk abin da ya danganci yaran Baffa na ba shi girman shi yana saka shi a ciki. Kan Ummu na ƙasa ta amsa ta kasa mgana, Ammah ta kalle ta ta gefen ido kafin ta ce" Ke kaɗai kika zo? Ina shi Habibun? "Yana waje." "Bai shigo ba kuma? In ji Ammah sai ta gyaɗa kanta kafin ta ce" Zai shigo daga baya." Ammah ba ta sake magana ba ta miƙe ta kwashi farantin kwanukan da su Baffa suka yi amfani da shi ta fita zuwa kitchen. Baffa Umaru ya sake tambayan Ummu Salma abin da ke faruwa ta sake warware mishi kamar yadda ta warware ma Baffa a farkon maganar. "Wannan ai ba mgana ba ne, shi ma bai taki gaskiya ba." Ya faɗa cikin ɓacin rai Baffa na gefe ya kaɗa kai kafin ya ce" Kuma tunda har an samu cikin maganar a zubar da shi ai bai ma taso ba." "Sosai, bari Baban na shi ya ƙariso a zauna zan faɗa masa ba mu yadda da wannan tsarin ba." Ita dai kanta na ƙasa ba ta yi magana ba ganin sun faɗa wata hiran ya sa Baffa ya ce ta je  wajen Ammah kafin waliyin Habib ya iso, sai ta tashi a sanyaye ta koma ɗakin Ammah ta isketa tana shara, ta yi saurin ijiye jaka za ta karɓa da sauri Amma ta ce" Ke bar shi, ba ki jin daɗi je ki kwanta ki huta" Fir Ammah ta ƙi sakar mata sharan dole ta haƙura ta koma ta zauna a saman kujera ta yi tagumi. "Kin ci wani abu kafin ki fito? Sai ta girgiza ma Ammah kai amma ba ta yi magana ba. "Akwai kunun gyaɗa da kosai za ki ci? Da sauri ta ce" Zan sha Ammah." Saboda tana son ƙosai ta daɗe ma ba ta ci ba kunun ɠyaɗan ma tana son shi har ƙamshin ɠyaɗan take ji yanzu a hancin ta. Ammah da kanta ta ajiye sharan da take yi ta je Kitchen ta zubo ma Ummu kunun sannan ta zuɓo mata ƙosan a wani faranti, ta kawo mata har ɗaki aiko ta zauna ta shan kunun tana cin ƙosan har wani lumshe idanuwanta take yi saboda da daɗi addu'a take yi a cikin zuciyarta Allah ya sa kar ta yi amai, Ammah na ta kallonta ta gefen ido. Tana sake tausaya ma rayuwar Ummu ta sake ramewa bisa ranar da ta zo har a cikin zuciyarta ta ke jin tausayin Autar nata kuma tun da ta ji wannan lamarin ba ta sake barci   tun daga dare har safe ba, addua'a take yi ba dare ba rana, tana roƙon Ubangiji da kar ya kaddara ma Ummu zawarci da kaddaran aure, domin kaddaran tana da nauyi Ummu Salma ta yi ƙanƙanta da fuskanta hakan. Allah ya taimaki Ummu har ta gama shan kunun ta da ƙosai ba ta ji amai ba Ammah kuma ta gama sharan ta ta shiga wanka kafin ta fito har Alhaji Sheriff ya iso ashe shi Habib ya jira daga waje su Baffa suka fito sai suka shigo da su, ba daɗewa sai ga Hamma Abdullahi, Ummu ba ta ji wani fargaban zuwan shi ba tunda shi ɗan ba ruwan mu ne ɗakin Ammah ya leƙo duk da sun daɗe ba su haɗu ba, ko a fuska bai yi mamakin ganin ba, ballatana ya fahimci tana cikin wani hali. "Ina kwana Hamma" Ummu ta faɗa tana gyara zamanta kallonta ya yi kafin ya ce" Aa Ummu ke ce? Sai ta gyaɗa mata kai. Gaisawa suka yi sannan ya tambayi Amma sai ta ce tana wanka ficewa ya yi duk da ya yi mamakin ganin Ummu da mijinta tare da ƙanin mahaifinsa ya san da matsala amma bai tsaya tambayan matsalan ba, mgana ya zo su yi da Baffa amma ganin sa da ɓaki ya sa kawai ya bar gidan, ƙarin mamakin shi ganin har da Baffa Umaru ya ta so daga Mubi lamarin ya girmama a cikin zuciyarsa dai ya yi fatan koma mene ne Allah ya daidaita. Kafin Amma ta fito wanka Baffa da kansa ya leƙo falon Ammah ya kira Ummu, hijabin ta sanya sannan ta bi bayan Baffa zuwa cikin ɗakin sa. Kan ta a ƙasa ta shiga cikin ɗakin a gefen su Baffa daga hannun dama ta zauna a saman cafet sannan ta ɗan ɗago kanta tana gaishe da Alhaji Sheriff wanda ke zaune shima a ƙasan cafet gefen shi kuma Habib ne ƙansa na ƙasa kamar na gari. "Lafiya lau, kina lafiya dai ko? Alhaji Sheriff ya faɗa bayan Ummu ta gaishe shi. Kanta na ƙasa ta amsa da lafiya lau. Bayan buɗe taro da addu'a, da Baffa Umaru ya yi sai ya maimaita abin da Baffa ya kira shi ya sanar da shi kan matsalan da ke faruwa tsakanin Ummu da Habib. "Tabbas haka ka kira ni ka faɗa mini nima, nima na kira shi na yi masa mgana. Saboda ma a samu daidaito shi ya sa na ce gwara mu haɗa su gabaɗaya." Alhaji Sheriff ya faɗa Baffa Umaru ya amsa da haka ne Baffa dai na gefe bai saka baki ba, Habib kuma kansa na ƙasa bai ɗago ba sai yanzu ya fahimci Ummu ta ɓoye ma iyayenta wasu abubuwan. Sai da ya murmusa lalle ta yi kuskure wataƙila da ta sanar da su duka abin da ke faruwa da sun sauƙaƙa mata wasu abubuwan da suke jiran ta anan gaba. "Yanzu maganar zubar da ciki ba ta, na yi masa faɗa sosai kuma ya yi mini alƙawarin in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba" Alhaji Sheriff ya sake faɗa cikin taushin murya, Ummu ya sake kallo kafin ya cigaba da cewa" Ki yi haƙuri kin ji ko? Sai ta gyaɗa kanta hawaye na kece mata ta saka gefen hijabin ta share da sauri. "To Alhamdulillah mun ji daɗin da aka samu masalaha cikin lokaci. Kai Habibu abin da ka yi ba ka yi daidai ba tunda har cikin nan ya shiga ba ku ɗau wani mataki daga farko ba, to sai dai ka yi hakuri Ummu Salama ta haihu, daga baya in kuka zauna kuka samu fahimtan juna za ku iya bari sai a lokacin da kuka sake shiryawa ku sake haihuwa wannan tsarin ku ne, ba ruwan mu a ciki amma mganar a zubar da ciki bai yi daidai ba kuskure ne mu kuma a matsayin mu na iyayen ku ba za mu bari ku kauce ma hanya ba shi ya sa muka shiga ciki domin mu samar muku da masalaha kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu." Habib ya yi shuru yana sauraran Baffa Umaru har ya gama jawabinsa. Baffa da ba zai yi mgana ba Baffa Umaru ya ce ya ɗan tofa wani abu mana. "Ni ba ni da wani abin da zan ce duk abin da zan faɗa kun gama faɗa sai dai ba zan fasa tunsar da su abubuwa guda uku zuwa huɗu ba." Habib ya kalla sannan ya kira sunan shi. "Habibu." Sai da ya ɗago kansa sannan ya amsa da Naam Ummu ma ya juya ya kira sunan ta. "Auta." "Naam Baffa." "Ku sani aure ibada ne, kuma shi da man ibada sai an ɗaure za a samu riba, dukkan ku saboda kun aminta da juna kuke zaune a inuwa ɗaya na aure. To ina so ku sani sai kun yi hakuri kun girmama junan ku , sannan za ku samu fahimtar juna. Ku sani ibadar da kuke yi sakamakon ku na wajen ubangijin ku, saboda haka in kuka yi wani abu saɓanin umarninsa ma duk yana sama yana kallon ku. Daga karshe ina mai sanar da ku da cewa ku ji tsoron Allah. Ku zaauna lafiya ku girmama zamantakewarku Allah ya yi muku albarka ya sake kaɗe fitina a tsakanin ku." Gabaɗaya su Baffa suka amsa da Amin, Ummu ma ta amsa a cikin zuciyarta Habib ne bai amsa ba domin kalaman Baffa sun shiga ne sun kuma fita, domin gani yake yi kamar ba su da amfani a wajen shi, bai so ya yi magana ba sai da Alhaji Sheriff ya ɗan zungure shi sannan ya ɗan yi gyaran murya yana faɗin. "Ku yi haƙuri Baffa in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba." Habib ya fada yana ɗan cije baki, Baffa ya ɗan jinjina kai kafin ya ce" Na ji daɗin haka. Ubangiji  ya zaunar da ku lafiya." Zaman bai wani ɗau lokaci ba tunda an samu matsaya, Baffa ya ce Ummu ta tashi ta bi mijinta ta koma gidan ta, tun da dalilin da ya kawo su an samu masalaha, Ammah ba ta fito ba kuma Habib bai neme ya shiga ya gaishe ta ba suma su Baffa ba su buƙaci haka ba, Ummu kaɗai ta shiga ta yi ma Ammah sallama. "Ki kula da kanki kin ji ko? Sai ta gyaɗa ma Amma kai kafin ta ce" In sha Allahu Ammah" Daga nan suka yi sallama har ƙofar gida su Baffa suka raka su, Alhaji Sheriff ya shiga motarsa shi ya fara tafiya sannan su daga baya, har sun shiga mota Baffa ya ƙwanƙwasa ma Habib gilashin mota ta bangaren sa, bayan ya zuge gilashin Baffa ya kalle shi lokaci ɗaya yana kallon Ummu kafin ya kira sunan shi. "Habibu" Ya amsa ƙansa na ƙasa amma a cikin zuciyarsa faɗi ya ke yi an fa dame ni "Kai ne da kanka ka zo ka ce kana son Auta na kuma ba ka ita cikin yaƙinin cewa za ka iya riƙe mini ita amana. Ko ba haka ba? "Haka ne" "To ina so ka sani amanarta da na baka tun ranar da ta tashi a ƙarƙashin ikona na ke so ka sake tunawa. Habibu kar ka saka na ji na sare bisa yaƙinina akan ka, don Allah ka riƙe mini Ummu bisa amana da gaskiya." Baffa ya ƙarishe faɗa cikin magiya, Habib ya kalle shi yana masa mirmishin yaudara da bai kai zucci ba kafin ya ce" In sha Allahu Baffa" Baffa ya ji daɗi har ya miƙa masa hannu suka sake musabaha yana ɗaga musu hannu suka bar ƙofar gidan  Baffa Umaru yana gefe kamar an kira shi a waya ne yana ta mgana. Suna fita daga kwanar anguwan Habib ya kalli Ummu kafin ya ce" Me ya sa kika ɓoye ma iyayenki gaskiyan manufata a kan aurana da ke? Ummu ta ɗago tana kallon shi cikin mamaki murna take yi na ganin komai ya daidai ta tsakanin ta da Habib amma kalamsa sai suka ruguza murnan ta da saka ranta. "Me ya sa ba ki faɗa musu cewa bana son ki ba sannan kin rufe musu ba auran soyayya na yi da ke ba, auren shaa'awa ne. Me ya sa ba ki sanar da su gaskiyan mganar ba? Ya sake jefo mata tambayoyi, kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabinta ta ce" Saboda ina tunanin ba gaskiya ka faɗa ba, kana dai fadin haka ne saboda na ƙi bi umarnin ka na zubar da cikin jikina." Habib ya kece da wata dariya kafin ya ce," Har yanzu ke a tunanin ki wasa na ke yi dake Ummu Salma? Lalle ko ba ki da hankali na kuma yadda ke ɗin shashasha ce." Ya fada har yana buga sitiyarin mota, Ummu ta kalle shi idanuwanta da hawaye kafin ta ce" Ka kirani da kowani suna ban damu ba. In dai har zan cigaba da zama a ƙarkashin ka, sannan zan tsira da cikin jikina na yarda ka kirani da kowa ni suna har wanda ma ya fi shashasha" Kallon ba ki da hankali yake yi mata ita kuma kawai sai ta kece masa da kuka. "Habib ka san ina son ka? Kai ma kana sona me ya ka sauya! Ni ce fa Ummu salman ka? Ta ƙarishe faɗa cikin kuka, sai ya sake yin dariya kafin ya ce" Lalle ba ki da hankali." Haka kawai ya ke faɗa lokaci ɗaya yana kallonta kuma yana dariyan haushi da takaici. "Na ji ba ni da hankali in dai akan ka ne Habib. Na ji ka ma ce na haukace duk na yarda da haka amma don Allah ka saurara mini haka nan na azabatu don Allah Noori." Yadda take marairaicewa ne ya sake tunzura shi, a fusace ya daka mata tsawa. "Wallahi bana son ki, bana sha'awan sake wani sauran zama a tsakanina da ke." ƙasaƙe Ummu ta yi tana kallon shi hawaye na kece mata wasu na zuba wasu na sake tunkuɗowa. Gefen titi Habib ya gangara ya kashe motan ya gyara zama yana sake kallon Ummu tana kuka kamar ran ta zai fita. "Ko zuwa gidanku da kike ganin na yi kina jin daɗin watakila na sauka daga kan kudiri na ne, to gwara ki daina murna ki dawo cikin hayyacin ki, sannan ki sake buɗe kunnuwan ki da kyau ki saurare ni." Ya faɗa yana karkaɗa kunnunsa guda ɗaya sannan ya cigaba da faɗin" Na bi umarnin Abba ne saboda shima nan gaba zai yi mini wani amfani saboda ke kuma ba zan ɓata gobe na ba, amma wallahi tallahi ban sauka daga kan kudirina ba. Bana son ki sannan ba na son cikin dake jikin ki, sai dai ina so ki sani daga yau ba zan sake matsa miki akan zubar da ciki ba da kanki za ki yi nadamar taurin kan da kika yi mini. Ke ba ki ga komai ba yanzu ne za a fara wasan Ummu Salama." Ya ƙarishe faɗa yana yi mata wani irin kallo har yana kashe mata ido ɗaya. "Ka san da haka me ya sa ka amsa ma  Baffa da cewa za ka riƙe ni bisa Amanar da ya ba ka? Ta tambaye shi cikin kuka, ƴar dariya ya yi kafin ya ce" Ummu in kin koma gida ya kamata ki koma makaranta ki yi karatu mai zurfi wataƙila zuwa lokacin za ki fahimci komai." Kallon ban gane maka ba ta yi masa sai ya girgiza kai lokaci ɗaya ya ta da motar suka fara tafiya. "Har sai na faɗa miki maganganun babanki da na yayansa ne ma ko ƙaninsa duk sun shiga ne sun fita? Sai na faɗa miki ni da man ban karɓi amanarki tun farko ba, abin da ya sa na aure ki jikin ki, kuma sadaki na biya sannan more komai, ai amanar kenan bayan na gama amfana dake zan mayar masa dake gidansa." Ummu ta yi ƙuru tana kallon Habib, hawaye suna kwaranya a saman kumatun ta. "Don Allah kar ka rabu da ni Habib.' Ta faɗa cikin matsanancin kuka. "Kar ki damu da sauran lokaci ai ba ki gama yin nadama ba. Sai na tabbatar da kin yi nadaman taurin kan da kika yi mini sannan zan ba ki sakamakonki ki ƙara gaba. Wataƙila a lokacin za ki ji kin tsane ni har ki fahimci da gaske na ke yi wannan manufar tawa da gaske na ke yi a kan ki." "Habib kar ka lalata mini rayuwata don Allah" Ummu Salma ta faɗa tana ji kamar ranta zai fita daga gangan jikin ta. "Ni kuma in ban yi haka ba tawa rayuwarce za ta lalace ki gane mana. Ni tawa rayuwar ban ma fara ba ke kuma tunda kin fara taki ki bari kawai na ƙarisa lalatata gabaɗaya kowa ma ya huta." Ya ƙarishe faɗa har yana shafa kumatun ta, kuka kawai Ummu Salma take yi kamar za ta shiɗe mai fitar da sauti. Habib na ta dariyan nishaɗi daga ƙarshe ma sai ya ƙure wakar Auta waziri na Autar mata ba ya son jin kukan ta, tana damun shi har suka isa gida ba ta daina kuka ba ta ɗauka yana ajiye ta sai juya amma ina tana saka ƙafa a bedroom ɗin ta yana shigowa tun da ta ga ya tura ƙofa yana nufota ta san manufarsa. "Tunda ka ce ba ka sona to jikina ya haramta a gare ka Habib." Ta faɗa lokaci ɗaya tana kuka samnan ta ƙamƙame jikinta da hannayen ta. "Allah? To ai saboda jikin na ki na aure ki, kin ga kenan ba ki isa ki hana ni more abin da na biya sadaki saboda shi ba." Yana gama faɗin haka ya tura ta , ta faɗa saman gado ya bi ta ya danne da ƙarfin tsiya yake so ya haye mata ta fara mutsu mutsun hana shi cimma burin shi a zafafe ya kifa mata maruka biyu a saman fuskarta. "Saboda jikin ki na aure ki, saboda haka in kika kuskura kika sake saka mini hannu sai na yi miki illah." Ummu-Salma ta ji kamar duniyar ta tsaya mata cak, tana mai kallon Habib da idanuwanta masu zubar da ƙwalla, ko motsin kirki ba ta ƙara yi ba har Habib ya raba ta da kayan jikinta ya biya buƙatan shi son ran shi ya tashi ya bar ta nan, hawaye ne masu zafi suke zubo mata ta gefe da gefen fuskarta. A cikin zuciyarta take jin wani irin zafi zafin da ba ta taɓa jin irin shi ba tun da Amma ta kawo ta duniya, ta yi kuka ta yi kuka kukan nadama da baƙin ciki sannan a karon farko ta ji ta fara tsanar Habib, tunda har ya iya kai hannun shi jikinta sannan ya haiƙe mata ba da son ran ta ba, ta daina faɗa da shi ne domin a yadda ya zuciya zai iya yi mata illa ita da abin da ke cikin ta, ta fi awa biyu tana kwance tana kuka ta kasa tashi sai da ta ji ana ta sallar azahar a masallatan kusa sannan ta iya jan kafafunta zuwa tiolet ta tsarkake jikinta sannan ta yo wanka da alwala azaune ta iya yin salla har kuma ta gama ba ta daina hawaye ba. Fuskarta ta yi jajir in da Habib ya mare ta har da tashin hannayensa zuciyarta ta yi duhu tana mata suya haka ta yini a cikin wannan halin bai kuma hana Habib dawowa gare ta da daddare ba, ba ta sake ƙoƙarin hana shi ba ta bar shi ya yi duk abin da ya ga dama da ita ya tsallake ta ya barta tana fama da suyan zuciya da hawayen bakin ciki da tausayin kanta. Domin ba ta isa ta hana shi abin da ya aura sabo da shi ba. Tun daga ranar zaman su ya sake juya teburi. Hatta kayan abinci kaf Habib ya kwashe su a gidan nan ma'ana ta dinga ci da kanta, store ɗin ta bai bar ko ƙwayan abinci ba sai abin da ba a rasa ba da kuma ta gani ba ta yi mgana ba domin ita ta riga ta gama aminta da duka kalaman Habib, da gaske ba ya son ta sannan saboda jikinta ya aure ta kuma tana bashi yana cigaba da mora. Duk lokacin da ya ji bukatarta zai zo gare ta ita kuma za ta kwanta ta buɗe masa har ya yi ya gama abin da zai yi ya tashi ba zai yi mata mgana ba itama ba za ta yi masa ba, tun in yana yi tana kuka har ta samu nauyin zuciya ta daina kuka sai dai idanuwanta na kallon rufin sama tana mai jin suya a cikin zuciyarta. Ta ɓoye ma kowa halin da ta ke ciki har Baffa Umaru sai da ya kirata ta ce masa komai ya daidai ta, ta riga ta gama sarewa da rayuwarta, gwara ta zauna a duk wani tsanani daga Habib kar ta yadda ya sake ta saboda in ya sake ta a yanzu ya gama cutar da ita. Duk wani abu da mace za ta yi taƙama da shi Habib ya ɗauke da ga wajen ta, ba ta da komai sai rai kawai sannan ba za ta koma gida ta bar ma su Baffa abin faɗe a anguwa da dangi ba gwara ta cigaba da zama a yadda Ubangiji ya zaɓa mata rayuwa. Za ta zauna da Habib ta ba shi abin da yake so matukar zai barta ta cigaba da zama da auran shi a kanta Ko da yaushe Ammah za ta kirata tana tambayanta yadda take sai ta ce suna lafiya haka ma Baffa, har Hamma Abdulrrahman sai da ya kirata yana mata jan ido da cewa Baffa ya faɗa masa an samu masalaha yana ta jan ta mganar cewa in Habib bai daina maganar zubar da ciki ba kar ta ɓoye masa ta faɗa masa shi zai tsaya mata, amma ta ce komai lafiya bayan sum gama waya ta yi ta kuka, da ma a ce za ta iya da ta faɗa masa komai amma ba za ta iya ba suna zaman su lafiya ba za ta zama silan matsala da damuwa ga iyayenta da ƴanuwanta ba. Tun tana jin Habib a ranta har ta daina jin sa kwata-kwata ya tozarta ta ya ci mutumcin ta, ta koma sai ta fita ta siyo dan abin da za ta ci kuɗaɗe ne a hannunta sama da dubu ɗari amma sai da suka ƙare a wajen ciyar da kanta da zuwa asibiti, tunda ta sake komawa cikin ta har ya shiga wattani uku sannan ga shi likita ya ce jininta ya yi ƙasa tana ɓukatar cin ganyayyaki saboda inganta lafiyanta da abin da ke cikin ta, ba saboda kanta ba saboda gudun jinin dake tare da ita, shi take so domin duk halin da ta faɗa saboda kare shi da ta yi ne shi ya sa nan duniya babu abin da take so da ƙoƙarin karewa sai cikin jikinta. Kuma a haka dare na yi Habib zai zo ya biya buƙatar shi da ita ko a jikinsa. Tabbas saboda jikinta ya aure ta, kuma yana moran abin shi son ran shi, Ummu ta gama sakawa a ranta jikin ta ne kuma da man Habib ya kusa kai sa zuwa ga expearing date ɗin shi, gwara ta bar masa komai ya ƙarisa shi tundaa shi ya fara. Baɗɗo ba ta nan ta tafi gidan kakanin ta a Mubi, Shamsiya kuma ta kwana biyu ba ta ji ta ba, ba ta kiran kowa wanda ya kira ta kuma ta yi masa ƙaryan tana lafiya. Mami ma ta kirata tana ba ta haƙurin cewa ba za su samu zuwa jimeta ba za su je Paris ita da megidanta da yara sai dai in sun dawo ko ita kaɗai za ta zo ta duba su. Sai ta ji daɗin haka domin ba za ta so wani na ta ya zo ya ganta a cikin wannan halin ba, kuma ta tabbata in Mami da diro Jimeta sai ta zo gidan ta kamar yadda ta saba abu ɗaya take yi da ke saka ta farinciki kallon girke-girke a wayanta sai ko salla da karatun Qur'ani amma Allah kaɗai ya san girman nauyin da ke cikin zuciyarta ita kaɗai ta san abin da ke muƙurƙusanta a cikin zuciyarta ƙarfin imani ne kawai ke riƙe da ita. **** Shafewar sama da kwanaki arba'in Ummu Salma na cikin wannan halin rayuwan Ammah ta kira ta a waya ta shaida mata zuwan Hamma Jibo tare da matarsa da yara. Sai ta yi saurin ce ma Amma za ta zo ta gaishe su, a lokacin ma ba ta da ko sisi ballanta ta yi kuɗin abin hawa, duk kuɗaɗen dake cikin acct ɗin ta ta gama kashe su a hidimar kanta. jiya ma waken da take dafawa ta haɗa da allaiyahu ya ƙare, kuma tun jiyan ba ta ci komai ba sai ruwan zafi kawai take sha cikinta na ɗagowa. Farkon cikin ne take laulayi ba ta iya cin abinci yanzu kuma da ta ɗan samu sauƙi tana ci ko da za ta yi amai haka likita ya ce saboda abin da ke cikin ta. Ba ta da kuɗi ta kuma rasa yadda za ta yi Allah ya dube ta a washegari Hamma Mustapha ya tura mata 10k kamar ya saka ta a aljannah haka ta ji ta kira shi tana yi masa godiya kamar za ta yi masa sujjuda. Kuɗin sun zo mata a lokacin da take cikin matukar buƙatar su shi ya sa gari na wayewa ta shirya ta tafi kasuwa. Sai ta kwana uku ba ta sa Habib a idanuwanta ba wata rana ma ba ya kwana a gidan sai ranar da yake da buƙarar ta to tana ganin shi, shi ya sa game da fita neman abin da za ta ci da lafiyanta, in za ta fita za ta ce Allah kana gani na fita da izinin ka domin lafiyata da abin da ke cikina, sai ta saka kafarta ta fita to haka ta yi ranar ta je kasuwa ta kaso dubu takwas sauran ta dawo dasu domin ta yi na abun hawa zuwa gida gobe. Abin da ba ta sani ba tana fita ba daɗewa motar Hamma Jibo ɗauke da Matarsa Nauwara da yara suka shiga haraban gidan su, suka iske ƙofar bangarenta a rufe kuma Hamman na ta kiran wayan ta, tana ringing amma ba ta ɗagawa. Megadi ya tambaya shi ya ba su tabbacin ta fita amma yana tunanin ba za ta daɗe ba sai Nauwara ta ce su zauna a mota su jira ta. Haka ko aka yi suna cikin mota suna hira Ummu Salma ta shigo gidan tana tafiya kamar za ta faɗi hijabi ne a jikinta amma duk wanda ya santa in dai ya ganta sai ya firgita da raman da ta yi sannan ta ɗan yi duhu hasken ta ya ragu, hannunta ɗauke da ledojin da ta auno shinkafa da fulawa sai wake da manja sai kayan ganye tun da yanzu ta daina cin mangyaɗa saboda ta fahimci in dai ta ci abincin mangyaɗa to ba za ta kwana lafiya ba bayan amai ta yi ta fama da tashin zuciya. Ko kaɗan ba ta ma lura da motar dake bakin bangarenta ba, har ta nufi ƙofarta ta sauke kayan hannunta tana neman maƙulli a cikin jakar ta sai ji ta yi an kira ta kuma da sunan da aka kirata yan gidan su ne kawai ke kiranta da sunan sannan kuma ta jiyo murya kamar ta Hamma Mustapha. "Auta." Da sauri ta juya ba Hamma Mustapha ba ne, Hamma Jibo ne mamaki ya kamata sai da daburce. "Hamma." Ta faɗa cikin sauri nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa da ta gan shi sai ta ji kamar ta warke da duka matsalolinta. Hamma Jibo ya kalli Nauwara itama ta kalle shi amma ba su yi mgana ba ya fara takawa zuwa ga Ummu sai ya ga ta kwaso gudu zuwa gare shi, ko da take gida in ya zo tana murna da ganinsa har ta zo ta riƙe mishi hannu amma ba ta taɓa faɗawa jikinsa irin na yau ba sannan lokaci ɗaya ta kece masa da kukan da ya ɗaga masa hankali. "Hamma." Ummu-Salma take faɗa cikin muryan kuka rike ta ya yi a zuciyarsa yana jin wani iri, me ya samu Ummu ne duk ta rame ta lalace haka? Ɗago kanta ya yi lokaci ɗaya yana share mata hawaye da tafukan hannayen sa "Ya isa haka Auta. Ya isa haka." Ya ke faɗa yana sake share mata wasu hawayen da suka kwaranyo. Nauwara na gefe ita da su Saudat duk jikinta ya yi sanyi yaran ma sun raɓe a jikinta suna kallon Babansu da Annin su, duk da yara ne amma suma sun ji wani iri fuskar su ta yi ɗif alamun damuwa. "Me ya same ki Auta? Ko kin yi ciwo ne? Ya faɗa yana kallon ta, sai ta basar da tambayan tana sakin shi wajen Nauwara ta nufa tana gaishe ta. "Adda Nauwara ina shirin zuwa na gaishe ku ne fa." "To ai duk ɗaya ne mu ba ga shi mun zo ba."  Ta ba ta amsa suna gaisawa ta jawo Saudat jikinta tana yi mata fillaanci sai ta ba ta amsa itama da fillancin amma ta haɗa da turanci. Ummu ta yi dariya ta ba ta hannu suka tafa lokaci ɗaya tana faɗin. "Lalle za ku shirya da Amma yanzu." Suka yi dariya gabaɗayan su Ammi na gefe ta yi karaf ta ce itama ta yi iya fillanci Ummu ta ce ta yi mata ta ji, bayan ta tambaye ta ina su Isma'il? ganin ba ta gansu ba da yaren fillanci sai kawai Ammi ta ma yar mata da amsar tambayanta da turanci. Da cewa suna gidan wajen Ammah. "Ke kam Ammi za ki ko shirya da takwaran na ki kuwa ? Ammi ta tura baki tana rantsuwan ta iya, Saudat na cewa ba ta iya ba sai kawai Ammi ta fara kuka sai da Ummu ta rumgumeta tana lallashinta. Hamma Jibo ne ya ce a waje za su cigaba da tsayuwa sannan Ummu ta tuna da suna waje ne  da sauri ta wuce gaba suka bi bayan ta, tana can ƙokarin neman maƙulli Hamma Jibo ya duƙa ya kwaso mata ledojin da ta ajiye a ƙasa. "Auta Kasuwa kika je ne? Ya faɗa lokaci ɗaya yana duba ledojin hannunsa "E Hamma." Ta faɗa lokacin da ta ɗauko key din tana ƙoƙarin buɗe ɗakin, shi ko jikinsa ne ya yi sanyi har sake leƙa ledojin ya yi ganin abubuwan dake ciki, sai ya sake ɗagowa yana kallon Ummu lokacin da ta buɗe ɗakin tana cewa su shigo,  kallon matarsa ya yi itama ta kalle shi domin tana kusa da shi ne ta ga ƙulle ƙullen su manjan da ke ciki da shinkafa da wake da in an haɗa duka ba su wuce tiya ba.   Sai da suka shiga falon suka zauna ita kuma ta kwashi kayanta zuwa kitchen sannan ta kawo musu ruwan a jug na famfo ne da ta siya, Hamma Jibo ya sake shan mamaki a ran shi sai yana tunanin ko dai mijin Ummu ya samu matsala ne a wajen aiki? Nauwara ma tunanin da take yi a cikin ranta kenan amma ba ta furta ba. "Anni ni swanwater na ke so na sha ba wannan ba" Cewar Saudat. Da ya ke da Annni ƴa'ƴan yayyenta suke kiranta a matsayinta na ƙaramar uwa a gare su. Ammi na jin haka itama ta ce" Anni ni kuma hollandian zan sha." Ta faɗa da harshen turanci, Ummu ta kasa mgana ta yi wani wiƙi-wiƙi  da idanuwana duk Hamma  na lura da ita. "To yanzu dai ba ni dashi ku fara shan wannan sai na fita na siyo muku." Ummu ta faɗa cikin yaƙe da dariya. "Haba. Ƙyale su Auta rigima ce" "Adda ki bari na fita ko megadi na ba ma saƙo ya siya musu." Hamma Jibo ne ya saka baki ya ce Aa, yaran ma ya yi musu jan ido ya ce su ɗau ruwa su sha in ba za su sha ba su bar shi, dole suka ɗauka suka sha kaɗan Hamma ma ya sha shi da Nauwara, miƙewa ta yi tana faɗin me za su ci ta dafa musu? Da sauri Hamma Jibo ya ce" Sai da suka ci abinci muka fito fa, Auta ki yi zaman ki kawai." "Dad ni egg zan ci " Ammi ta faɗa kamar za ta yi kuka wannan karon Nauwara ce ta balla mata harara kafin ta ce" Ba shi kike taso kika bari a gidan Ammah ba? Zan zane ki fa" Ta faɗa mata cikin harshen turanci lokaci ɗaya tana hararanta Ummu duk ta zama wata iri sai yaƙe take yi amma da ka ganta tana cikin damuwa. "Auta taho nan ki zauna kusa da ni." Ya faɗa mata yana mai nuna mata kusa dashi jikinta a sanyaye ta zo ta zauna kusa da shi kanta a ƙasa. "Auta me ke faruwa ne? Ya tambaya yana kallon ta, sai ta ɗago tana kallon shi cikin yaƙe kafin ta ce" Me ka gani Hamma? Lafiya ta lau na yi ta zazzaɓi kwana biyu ne " "Haka Ammah ta ce sannu? Nauwara ta faɗa tana kallon ta, Amma ta faɗa mata Ummu na da ciki shi ke ɗan ba ta wahala wataƙila shi ya sa duk ta rame. Hamma Jibo ya yi shuru yana kallonta ya kasa magana. "Hamma ba fa komai Allah." Ummu ta sake faɗa tana faɗaɗa mirmishinta wanda ba ta san bai boye damuwarta ba. "Megidan na ki ba shi da aiki ne yanzu? Cikin mamaki ta ce" Yana aiki me ka gani Hamma? "Na ga kin siyo abinci Auta." Ya faɗa kai tsaye yana kallon ta cikin nazarin ta. Sai ta kasa mgana, kanta na ƙasa amma hawaye take yi ganin haka ya sa Hamma Jibo ya ce Nauwara ta kwashi yaran su shiga ciki zai yi magana da Ummu Salma. Da sauri ta bi umarnin sa ta kwashi yaran suka shiga bedroom ɗin Ummu suka zauna. "Auta ki faɗa mini abin da ke faruwa ni fa ɗan'uwan ki ne, zan yi komai  domin ganin kin yi farinciki." Kalamansa sake sake ruguza  rauninta ta sake fashe masa da kuka, kanta ya dafa yana ɗan bubbugawa alamun lallashi, sai da ta yi kukan ta ya ishe ta sannan ta warware masa komai amma shima ta ɓoye masa abubuwa da yawa kamar yadda ta ɓoye ma su Baffa, sai dai ta bayyana masa ita ke ciyar da kanta tunda har ya gannin ma idanuwansa ƙarya ba na ta ba ne. Har da haɗa sun da aka yi waje ɗaya kamar an samu masalaha duk ta sanar da shi. Hamma jibo ya ji wani abu ya kama shi na tausayin ƙanwarsa da jin haushin Habib cikin faɗa ya ce" Kuma kike zaune yunwa za ta kashe ki Ummu ga su Baffa a kusa? Tana kuka ta ce" Hamma ina son aurena sannan ina son iyayena ba na so na saka su cikin damuwa." "Ai cutar da kanki da kike yi shi ne zai saka su a damuwa Auta." Ya faɗa yana kallon ta, tana hawaye ta ce" Ka yi hakuri Hamma." Kanta ya jawo a saman kafaɗanta yana lallashin ta. "Ya nuna ba ya jin maganar na gaba da shi tunda an masa mgana ya nuna ya ji amma bai ji ba, sakarai ne shi? Ta ina aka taɓa haka? Kawai sai ya ce sai kin zubar da ciki saboda ba shi da tunani? Ya cigaba da faɗa Ummu na ta kuka tana faɗin Hamma ka yi haƙuri. "Ya zama dole su Baffa su sake sanin halin da ake ciki." Ya faɗa yana sakin ta lokaci ɗaya yana ƙokarin ɗauko wayarsa. "In ba haka ba wata rana zaki mutu ba a sani ba, kin ga yadda kika rame? Kuma kina da juna biyu in wani abu ya same ki fa? Da sauri Ummu ta sauko ƙasa ta duƙa tana faɗin" Don Allah Hamma ka yi haƙuri, kar ka sanar ma da su Baffa ba na so hankulansu ya sake tashi." Tsayawa ya yi yana kallon ta cikin mamakin ta. "Hamma ina son na tsira da aurena ba abin da ya rage mini a yanzu. Don Allah kar ka bari su Baffa su san abin da ke faruwa." Ya rasa yadda zai yi da ita ganin tana ta kuka shi ya sa sai ya mayar da wayar shi aljihu yana faɗin" To na ji ya isa." Ya saka hannu ya ɗago ta yana share mata hawaye miƙewa ya yi yana ce mata bari ya je ya dawo. "Hamma." "Zan dawo yanzu." Yana gama faɗin haka ya fice, nan ta zauna tana kuka Nauwara ta fito ta same ta, tana kuka ba ta tambayi ba'asi ba ta zauna tana ta lallashinta Ammi ta yi barci Saudat ne idanuwanta biyu da ya ke akwai wutar nepa sai Nauwara ta kunna mata cartoon zaman shuru suka yi Ummu ta daina kukan amma ba ta daina ajiyar zuciya ba. Ba daɗewa sai ga Hamma Jibo ya dawo Allah sarki ɗan'uwa. Kayan abinci ne ya siyo mata mai yawa kuma shi ya dinga ɗauka yana shiga mata da shi cikin store, Ummu ta yi hawaye ta yi kuka tana yi masa godiya ba abin da bai siya mata ba har kayan tea sannan ya tura mata 100k ya ce ta riƙe a hannunta. Ba su daɗe ba ya ce su tashi su tafi da alƙawarin zai faɗa ma Baffa halin da take ciki amma ba zai bari a kashe mata aure ba, sai dai za a sake kiran Habibu a ji dalilin shi na yi mata horan yunwa. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *09* Suna tafe a mota za su koma gidan Ammah, Nauwara ta fahimci mijinta na cikin damuwa tun fitowan su daga gidan Ummu fuskar shi ta nuna damuwar da yake ciki, ta fahimci akwai matsala amma ba ta so ta yi shisshigi tunda bai sanar da ita komai ba. Ga kukan da Ummu Salma ta yi ta yi, sannan ga kayan abincin da ya siya mata shima wani alama ne da cewa wani abu na faruwa. Hannunta ta ɗora saman hannunsa dake saman sitiyari, ta riƙe ta ɗan matsa da ya sa ya kalleta lokaci ɗaya yana ma yar da hankalin shi kan tukinsa su Saudat na baya suna ta wasa ba su ma fahimci abin da ke faruwa a gaban motan ba. "Ina fatan ba wata matsala ba ne game da Auta ba ko? Nauwara ta faɗa cikin kwantar da kai tare da kulawa ga mijinta Jibril Hadi Baba. Kai ya gyaɗa mata kafin ya sauke ajiyar zuciya. "In sha Allahu komai zai yi dai dai." "Allah ya sa. In sha Allahu." Ta amsa masa cikin jinjina masa kai lokaci ɗaya tana yi masa mirmishi,  shima sai ya mayar mata da martanin mirmishin nata, amma gabaɗaya baya cikin natsuwarsa halin da ya iske Ummu Salma a ciki ya gama ta yar masa da hankali shi ya sa suna komawa gida sun ci sa'a Baffa ya dawo lokacin ɗakinsa kawai ya shiga Nauwara kuma da yara suka ya da zango a falon Ammah in da suka iske su Hassan da Hussaini na ta wassani isma'il ne ma ya yi barci. Baffa ya razana da labarin da Hamma Jibo ya sanar da shi, ya yi masa zuru yana kallon sa cikin ɗimuwa da mamakin labarin da ya ba shi, wai Ummu na yini da yunwa saboda ba abinci ya tuna yadda store ɗin su yake rumbatsa da kayan abinci wani ba ya karewa ake sake kawo wasu, Baffa ba zai iya kirga shekarun da ya ɗauka bai siya hatsi ba, haihuwa ce ta yi masa rana har da ma waɗanda bai haifa ba suna yi masa, amma a ce ɗiyarsa na aure a garin nan amma tana kwana da yunwa saboda son rai da mugunta da zalunci irin na Habibu. "Innalillahi wa'inna alaihirraju'un." Baffa ya samu kan shi da furtawa saboda hankalin shi ya tashi matuƙa. "Baffa wallahi hankalina ya tashi da yadda na ga Auta. Ba zan ɓoye maka ba sam ban ji daɗin ganin ta ba, tunda na baro gidan ta na ke cikin damuwa. Baffa Auta ta sauya tana neman mutuwa a cikin gidan nan ba wanda ya sani." Ya karishe faɗa kamar ya yi kuka, da man shi yana da tausayi da rauni. "Baffa ina tambayanta sai kawai ta fashe mini kuka, Baffa ka ga yadda Auta ke kuka, kamar ran ta zai fita amma a haka roƙona take yi kar na faɗa muku wai ba ta so hankalin ku ya tashi ni kuma na ce sai na sanar daku domin dole ne a yi wani abu tun kafin Auta ta samu wata matsalan a dawo ana wallahi tallahi Baffa." Ya dire maaganarsa yana shafa naman goshin sa cikin damuwa. "Gwara da ba ka rufe ni ba Jibo. Ai wannan ba mganar da za a yi shuru ba ne. Tunda tun farko mun sako waliyin shi a ciki nan aka kira shi ya ce ya bar mganar in sha Allahu ashe yaudaran mu ya yi, ya koma ya sauya wani tsarin to Jibo horon yunwa fa? Kashe mana Auta yake son yi ko mene ne manufarsa? Baffa ya faɗa yana kallon Hamma Jibo cikin damuwa muraranta da ya bayyana a saman fuskar shi. "Mene ne mafita Baffa? Baffa ya yi shuru yana tunani kafin ya ce" Wannan karon ba zan jira ma Baffan ku Umaru ya zo ba, zan kira shi na ce ya tura mini lambar shi waliyin Habibun zan kira shi na ce masa ina son mu haɗu ni da kaina zan warware masa komai sannan na faɗa masa ya sanar da ɗan shi in har ba ya son Ummu ne ya dawo mini da ita gida ni ina da abincin da zan ciyar da ita ba wai ya gagare ni ba ne" Yadda Baffa ke magana kaɗai ya isa ka fahimci ya kai makura a takaicin Habibu, ba abin da ya fi ƙona masa rai  a ciki irin horan yunwa ga ciki a jikinta amma ya barta tana wahala saboda wata manufarsa ta banza da wofi. To shi ba zai ɗauka ka ba, ba a dole ya sako masa yarsa in ba zai iya rike amana kamar yadda ya ɗau yaƙini ba. "Baffa na lura Auta na son mijinta. Kar a yi gaggawan raba su a tsaya dai a sake samun masalaha." Baffa ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce" To son banza Jibo? Me son ya tsinana mata balle mu iyayenta! Kuma ni na ma fara tamtama in har yanzu yaron nan Habibu na son Auta. Domin mai son ka zai so haɗa zuru'a da kai, sannan ba zai taba wulaƙanta ka ba, ballanta har yana da shi da gangan ya yi maka horo da yunwa." "Haka ne Baffa" Hamma Jibo ya faɗa cikin gamsuwa da mganar Baffa amma yadda Ummu ke kuka har yanzu hoton ya kasa ɓace masa. "Ko tana son shi, in shi ya nuna baya ra'ayin ta ai dole ta haƙura." Hamma Jibo ya yi shuru duk jikinsa ya yi sanyi. Nan take Baffa ya kira ɗan'uwansa Baffa Umaru bayan sun gaisa ya ce masa yana son ya tura masa lambar waliyin Habibu mijin Auta Ummu Salama. "Hadi lafiya kuwa? Baffa Umru ya tambaya daga can bangaren cikin mamaki, domin shi a tunanin shi an samu masalaha tsakanin Auta da mijinta tun bayan zaman da suka yi. "Zan sanar da kai daga baya. Yanzu dai ka turo mini lambar ina jira.' Sai bai matsa masa ba ya amsa masa da to zai tura masa, suna yanke wayar mintina biyar tsakani ya turo masa lambar, Hamma Jibo ya ba ma wayar ta sa ya ciro masa lambar ya saka a cikin wayar sannan ya ce ya kira ya ba shi zai yi mgana da shi. Kira ɗaya ba ta ko daɗe tana kara ba Alhaji Sheriff ya ɗaga wayar da sallama Baffa ya amsa bayan gaisuwa sai Baffa ya gabatar da kansa. "Sunana Alhaji Hadi Baba ni ne mahaifin Ummu Salma, matar yaron wajen ku Habibu." Nan da Alhaji Sherif ya washe baki kamar yana ganin shi, suka sake gaisawa tunda ba su da lambar juna, daman da Baffa Umaru ne suke magana tun neman auren. "Alhaji lafiya kuwa? Ina fatan ba wata matsala ce ta sake tasowa daga bangaren yaran ba? Alhaji Sheriff ya tambaya daga can bangaren, domin ya ji mamakin kiran na sirikin Habibu a wannan lokacin. "Lafiya lau, in ba damuwa adireshin gidan ka za ka turo mini zan zo har gida da safe na same ka, akwai mganganun da za mu tattauna ne." Baffa ya faɗa cikin dattaƙon sa. "Haba Alhaji ai ba sai ka zo ba. Ni zan zo na same ka a gobe da safen in sha Allahu." Amma Baffa ya ce aa shi ya yi niyar zuwa saboda haka ya bar shi kawai ya zo, dole ya amince suna gama waya da Baffa nan take ya tura masa adireshin gidan shi da ke At Unit cikin gari, ya yi zuru shi kaɗai yana tunanin me kuma ya sake faruwa? Amma jikinsa ya ba shi koma me zai kawo surukin Habibu wajen sa to ba zuwan lafiya ba ne, in ko haka ne Habibu ya gama kunyata shi da girman shi. Bangaren Baffa kuma, da shi da Hamma Jibo suka shirya za su je gidan Alhaji Sheriif da safe Baffa ya ce kar Hamma Jibo ya sanar ma da Ammah komai sai zuwa nan gaba har sua ga abin da zai je ya dawo. Shi ya sa ya yi shuru bai faɗa mata ba shima Baffa ko a fuska bai nuna mata wani abu ba, tausayin Ummu ya dame shi shi ya sa ko a waya ya kasa kiran ta, baya so ya ji muryanta sai ta saka shi kuka. Ammah ko ba ta san abin da ke faruwa ba, da ta tambayi Nauwara yadda suka baro Ummu sai ta ce tana nan lafiya Hamma Jibo ma haka ya ce mata su Saudat kuma Allah ya sa yan surutun ba sa kusa da ta ce ta ga Anni na kuka kamar Allah ya rufe mata baki ita da Ammi ba su yi surutun ba. Baffa kwana ya yi bai yi barci ba. Ba kan Ummu farau zawarci ba ya san shi take tsoro, shi ko da ya bar yarsa ta mutu a gidan wanda ba shi da asara gwara duniya ta zage shi , zai ajiye wani fillanci ya tsaya mata. Shi me ye bai gani ba? Nan ƙanwarsa Fatima ta dawo masa da yaro a cikin jinin haihuwa da takardan saki kuma ya karɓeta ya riƙe ta gam, to ba wani sabon abu ba ne in Ummu ta dawo masa da ciki gida, a wannan karon ma godiya zai yi ma Allah ya karba duka kaddaransa, daga karshe da ya gaji da juye juye sai ya tashi ya shiga tiolet ya ɗauro alwala ya yi nafilfilu, tare da addu'o'i ma su yawa akan in har babu alheri a auren Auta da mijinta Allah ya sauƙaƙa mata kaddaranta. Da Ammah ta farka ta gan shi yana ta salla, sai itama ta mike ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta jera a gefen shi, ta tayar da salla ba su suka koma suka kwanta ba sai wajen uku na dare, asuba na yi Baffa ya ta da Ammah shi kuma ya yi alwala zuwa masallaci. Nauwara da yara suna bangaren Ammah, Hamma Jibo na can bangaren haraba, Baffa na fita sai ga shi ya fito tare suka fita zuwa masallaci. Wajen shidda na safe suka dawo tunda sun ɗan tsaya liman ya yi tunatarwa kan riƙo da zumunci da yaƙana ko da suka dawo Nauwara ta share gidan tas ta gyara ɗakin Ammah sannan ta yi ma yaran wanka Amma kuma na kitchen tana sama musu abin ƙaryawa. Fanke ta soya sai ta dama kunun tsamiya, ta dafa indomie saboda yan biyu da dafaffen ƙwai, kawai sai Ammi ta saka rigiman sai an soya mata ƙwai, Amma ta ce ta yi abin da za ta iya  uwarta ta fito ta soya mata Baffa da Hamma Jibo suna ta dariya Ammah ko ta haɗe rai tana faɗin yara sai iyayin tsiya. Suna gama karyawa Baffa ya yi wanka shima Hamma tuni ya shirya. Jibi yake so su koma saboda aikin sa shi ya sa yau ya ce Nauwara da yara su shirya su je su gaishe da Ummin ikki, da gidajen su Hamma Abdullahi da Abdulrrahman har Mubi ya so su je su gaishe da su Ummu Balki, amma ba lokaci watakila sai hutun karshen shekara. Ammah ta ɗan yi mamakin ganin Baffa da Hamma Jibo za su fita tare amma sai Baffa ya ce mata fitan na shi ne Jibon zai tuƙa sa ne, ba daɗewa za su yi ba sai ta yi musu fatan dawowa lafiya. Hamma Jibo na fitowa da mota waje Baffa na shirin shiga sai ga Hamma Abdullahi ya kariso a mashin ɗin da ya siya, yana da mota amma in ba tafiya mai nisa ba ya fi yawo a mashin. Mamaki ya kama shi na ganin Baffa sun fita da Hamma Jibo saboda kafin ya kariso da mashin ɗin kofar gida har Baffa ya shiga mota sun bar wajen agogon hannun shi ya duba tara ta gota shi kaɗai yana mamakin ina za su je da safen nan haka? Ya shanye mamakinsa ya ƙarisa cikin gida bayan ya shiga da mashin ɗin sa har haraba. Tun kafin ma Ammah ta ce masa Baffa baya nan ya ce mata ya gan su za su fita tare da Hamma jibo a ƙofar gida. "Ammah ina su Baffa za su je ne? "Bai faɗa mini ba Baba " Da yake yana da sunan mahaifin Baffa shi ya sa Amma ba ta iya faɗin sunan shi har gwara ma Baffa yana kiran shi da Abdullahi wani lokacin. Ta ba shi amsa da harshen fillanci, bai sake tambaya ba, yana cikin falon ne zaune su Saudat na ta yi masa hira yana biye musu Nauwaran ma ta fito sun gaisa Ammah ta ce ai duk yau za ta leƙa gidajensu shi  Abdulrrahman. "Itama yau take yi mini mganar tana so ta zo su gaisa." Ya faɗa yana kallon Ammah. "To ai ta yi zaman ta yau Jibon ya ce duk ta leƙa ku." Sun ɗan taba hira ya so ya jira su Baffa ne sai aka kira shi a waya wani abokin shi ya zo gida nemansa sai ya yi ma Ammah sallama da cewa zai tafi. "Ba za ka jira Baffan ba? "Amma na yi baƙo a gida. Zan dawo zuwa anjuma da man magana za mu yi kan injinan mu da zan je kwatano na taho da su." "To ko Nauwara za ta taho ka sauke su tun da gida za ka koma? Da sauri ya ce" Da mashin na zo Ammah ba da mota ba." Sai Ammah ta yi shuru, har su Hassan suna rigiman sai sun bi shi. "To ku jira baban ku wannan uban na ku bai zo da mota ba" Yara sai suka fara kuka suna sai sun bi Bobo, haka yaran Hamma Jibo ke kiran duka ƙannen ubansu maza. "Bari kawai Ammah na tafi da su Hassan sauran Mamansu sai ta taho da su." Haka ko aka yi yan biyun ya ɗauka a mashin, da Isma'il a gaba domin shima rigima ya saka sai ya je, ga shi karami ɗan shekara 4 amma ya iya rigima Ammah ta yi ta tsaki tana faɗin iyayensu sun sangarta su. Saudat aka bari da Ammi za su taho tare da Nauwara da ta ce in ta ga Hamma Jibo ya daɗe za su hau kekepep ne su tafi. ** Gidan Akhaji Sherif bai da wuyar ganewa suna shiga anguwar tambaya ɗaya suka yi aka kawo su tunda sananne a anguwa sakamakon fitattacen ɗan kasuwa ne, suna zuwa ƙofar gidan Baffa ya kira shi ya ce sun ƙariso da man shi yake jira ba daɗewa sai ga shi ya fito ya tarbi Baffa. Hamma Jibo ma ya gaishe shi ya amsa cikin sakewa yana kallon shi "Jibril jibo kenan babban yaro na ne, yana aiki Abuja." Nan da nan Alhaji Sheriff ya washe baki suka yi musabaha da Hamma lokaci ɗaya yana cewa' Ai na ga kama " Da ya yi ma Baffa ta yin shiga cikin gida cewa ya yi ba zai shiga ba sai da ya yi masa magiya sannan ya amince suka shiga falon gidan Alhaji Sherif an kawo musu ruwa Baffa ne kaɗai ya sha ban da Hamma Jibo. "Alhaji ina fatan lafiya ko? Duk da dai lafiya ba za ta saka ka taso da kan ka zuwa wajena ba." "Wannan gaskiya ne." Baffa ya faɗa kafin ya gyara zama yana faɗin" Alhaji a matsayin ka na waliyin Habibu kai muka sani a matsayin wakilinshi shi ya sa da lamarin zubar da ciki ya taso muka neme ka, domin ka tsawatar masa." "Gaskiya ne wannan." Alhaji Sheriff ya fafa cikin gamsuwa da kalaman Baffa. "To a wannan karon ma shi ya sa na sake neman ka." "To. Me ya faru? Ya tambaya cikin son ya ji  kuma wani abu Habibu ya sake fitowa da shi. "Ko maganar zubar da cikin ne bai barta ba har yanzu? Alhaji Sheriff ya sake tambaya yana mai kallon Baffa. "Ba shi ba ne, amma kuma ya fito da wani tsarin ne, ya fara yi mata horo da yunwa a takaice dai ya bar ta, tana ci da kanta jiya ɗan'uwanta ga shi nan ya je gidanta ya dawo mini hankali tashe. Ya rantse mini har ga Allah bai ji daɗin ganin Auta a cikin yanayin da ya gan ta ba." "Horon yunwa kuma? Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Alhaji Sheriff ya faɗa cikin tashin hankali Baffa kuma ya cigaba da warware masa duka halin da ake ciki. "Habibu bai sauya ba, duk abin da ya faɗa a gaban mu a gaban ka duk yaudara ce ya san tana da ciki kuma yana mata horon yunwa in yana tunanin wahala zai iya sanadin ciki ba ya tunanin halin da Ummu za ta shiga! Tsakani ga Allah Alhaji na kasa haƙuri da wannan rashin imanin horon yunwa ga mai juna biyu hatsari ne, bai rasa abin da zai ba ta ta ci ba, sai na fahimci kawai mugunta ne da son zuciya irin na ɗan adam " Alhaji Sheriff ya ji zufa na keto mai saboda nauyi da kunya. "Assha wannan lamarin bai yi daɗi ba Alhaji." Ya faɗa cikin takaici da baƙin ciki. "Wallahi bayan mun zauna da ku, ni da kaina na sake kiran shi na yi masa faɗa ya ce mini komai ya wuce, ko shekaranjiya mun haɗu a gidan su a gaban mahaifin shi na tambaye shi komai lafiya ya amsa mini da lafiya lau ashe ya yaudare mu ne ba mu sani ba" Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Tabbas ya yaudare mu, bai saduda ba." "Kai, amma Habibu ya ba ni mamaki,." "Mu ma duk ya shayar da mu  mamakin sa." Baffa ya faɗa yana kallon Alhaji Sherif da Habibu ya gama kunyatawa a idanuwan su Baffa. "Ka yi hakuri Alhaji bari na kira shi yanzu." Da sauri Baffa ya ce" A'a ba sai ka kira shi yanzu ba. Ga dai saƙo na a gare shi in ya zo ka faɗa masa." Shuru Baffa ya yi na ɗan lokaci kafin ya cigaba da faɗin" Ka sanar da shi in ya gaji da Ummu Salma ne to ya dawo mini da ita gida ni ban gaji da ita ba. Da ita da cikin jikinta duka suna da kyakyawan gurɓi a gidana." Alhaji Sheriff ya ce" Aa ba za a yi haka ba Alhaji." "Haka za a yi, sannan daga ƙarshe ka sanar da shi cewa lokacin da na aura masa Ummu Salma bai ganta cikin yunwa ba, saboda haka ba shi da hurumin yi mata horon yunwa a na shi gidan." Baffa na gama faɗin haka ya miƙe yana gyara babban rigan shadda faran dake jikinsa. "Jibo ta shi mu tafi." Ya yi gaba Alhaji Sherif ya biyo bayan shi yana ta bashi haƙuri har waje. "Don Allah Alhaji ka yi haƙuri. Wallahi ba da yawun mu Habibu ke yin wasu abubuwan ba tabbas ba san me ya sa ya koma haka ba." "Ba komai,  ba a dole in ba ya son ta babu matsala in ya dawo mini da ita." Alhaji Sheriff ya yi ta ban haƙuri Baffa ya nuna masa ba komai amma in har Habib ya gaji to ya dawo da Ummu gida. Sallama suka yi cikin girma kafin Baffa ya shiga mota Hamma Jibo ya tada motar suka bar layin. Sai da suka hau titi sannan Hamma Jibo ya kalli Baffa da ya yi shuru yana faɗin" Baffa kana ganin Auta ba ta yi ƙanƙanta da zaawarci ba? "In abin da Allah ya kaddaro mata kenan ai ba mu da yadda za mu yi Jibo amma tabbas yaron nan ya gaji da zama da Auta duk ya nuna alamun haka a bayyyane." Hamma Jibo ya yi shuru bai yi magana ba sai dai yana ta furzar da iska daga bakin shi alamun lamarin ya dame shi. "Kar ka damu, Fatima ta dawo hannuna a bazawara tana da shekaru sha bakwai ne, yau ina take? Tana can tana rayuwarta da mijinta da ya'yanta bai wuce ba, ya wuce Jibo sai dai mu tuna kawai. To itama Auta in hakan ta kasance da ita na san za ta ji ba daɗi amma in ta yi hakuri komai zai wuce ya zama wata rana sai labari." Hamma Jibo ya jinjina kai yana mai gamsuwa da maganganun Baffa tabbas gaskiya ya faɗa duk kaddaran da ta same ka, in ka yi haƙuri wata rana za ka tuna har ka yi dariya. Baffa ya yi ƙokari sosai ya san Baffa na da kara sosai amma akan ya'yan shi ko yan'uwan shi ba shi da wannan karan zai yi kawaici na farko na biyu ana uku kuma zai shiga gaba, sau tari in Baffa ya yi wani abun kamar ba jinin fulani a jikin shi, yana da kunya amma bai cika bari kunya na cutar da shi ba, Ammah ce mai kara da kunya kan ƴa'ƴan ta komai na su kuma da man Ummin ikki ne ke shigewa gaba. Ita in an ganta a gaba-gaba Lamiɗo ne da duk abin da ya shafe shi, in ko ba shi ba, ba ruwanta da sha'anin kowa ballatana ma ta shiga. Da suka koma gida Amma ta faɗa ma Baffa Abdullahi ya zo neman shi ba ya nan, nan da nan ya ɗaga waya ya kira shi ya ce ya zo gida ya same shi ya dawo. Hamma Jibo kuma Nauwara ya ɗauka a mota tare da su Saudat zuwa gidan Ummin ikki daga can zai wuce da su gidan Abdullahi. Ko da wasa Baffa bai sanar da Ammah abin da ke faruwa ba, duk da ya san ta da kawaici amma yana da tabbacin yadda ya iya shanye damuwarsa ita ba za ta iya shanyewa ba, za ta shiga damuwa sosai ko da ba za ta yi magana ba. *** Alhaji Sheriff tun fitan su Baffa daga gidansa yake kiran lambar wayar Habib amma ba ya samun shi har dare kuma bai same shi ba sai ya kira Malam Usman, ƙani yake gare shi, kuma shi ke bi ma mahaifin Habibu a haihuwa nan ya warware mishi komai, shi da yake ba shi da hali sosai Alhaji Sheriff duk a cikin su ya fi su rufin asiri. "Assha Habibu bai yi tunani ba ya ɓata wayon sa sam." Malam Usman ya faɗa cikin mamakin Habibu har da shi a cikin maganar auran nan na Habibu iyayen matarsa masu mutumci da ƙima ne. "Wallahi Usman Habibu ya gama zubar mana da mutumci, na yi ta kiran wayarsa ban samu ba in na same shi zan ce gobe goben nan mu haɗu gaban mahaifinsa da uwar riƙon sa, na maimaita masa saƙon uban matarsa a gabansa sannan na zare hannuna a sha'aninsa ya je can ya yi duk abin da ya ga dama tun da ba ya jin shawara." "Aa ba za a yi haka ba Yaya Sheriff. In ka ce masa haka ai sai ya sake lalacewa. Gwara dai mu taru mu sake jan kunnen sa, in ka same shi a waya ka sanar da ni, sai mu haɗu gabaɗaya mu sake jan kunnen sa." "Allah ya sa ya ji to. " Alhaji Sheriff ya faɗa cikin takaici sun cigaba da tattaunawa duk da dai akan mganar kafin su rabu da juna akan sai Alhajin Sheriff ɗin ya kira shi in ya samu Habib a waya. A ranar dai bai same shi ba sai a washegari, sai dai ya sanar da shi ba ya Jimeta yana Abuja a wajen aiki an tura su wata Seminar, kuma ba za su dawo ba sai gobe lahadi da yamma, nan take Alhaji Sheriff ya ce masa in ya dawo a daran su haɗu a gidan su bayan isha'i ya kashe wayarsa  ba tare da ya jira cewar Habib ɗin ba, ya bar shi cikin tunanin abin da ya faru, ya san abin da ya yi shi ya sa ya kawo tunanin maganar Ummu Salma ce. "Kai wannan yarinyar kamar mayya wai sai na ce mata na sake ta ne za ta gane na gaji da ita ne? Ya faɗa a fili yana dafe kai, a cikin kayattacen ɗakin hotel ɗin da bankin su ta kama musu. Da man ko ba a kira shi ba ya gama yanke shawaran in har ya koma ya ga yunwa bai saka Ummu tafiya gida ba to zai sallame ta, har ga Allah ya gaji da shiga damuwa akan ta. ** Hamma Jibo a ranar lahadin da sassafe suka ɗau hanya shi da iyalan shi, da yake tafiyar mota suka yi wannan karon shi ya sa suka fita da wuri, sun rabu da Baffa akan duk halin da ake ciki zai kira shi ya sanar da shi, sannan Ummu ma sun yi waya ya sanar da ita ya faɗa ma Baffa komai amma bai faɗa mata Baffa ya je wajen waliyin Habib ba, shi dai ya jadadda mata ta kula da kanta sannan ta zama jaruma ko da wani abu zai faru ta sani Allah ne ya jarabce ta ba wani ba. Ta amsa masa da in sha Allahu, domin ita tuni ta san wannan karatun ita da rayuwarta ta yi juyin waina cikin lokaci, Habib ma ba ya kwana a gidan yanzu ba ta san ya yi tafiya ba a tunanin ta tunda yanzu ba ya buƙatar ta shi ya sa ya daina ma kwana a in da take shaƙan numfashi. Kamar wasa a ranar tana zaune tana cin abinci  da yamma gabda mangariba sai ga Habib ya shigo gidan. Ko kallon ta bai yi ba ballantana ta saka ran cewa zai iya jin tausayinta bayan ya kalle ta, shigewa ciki ya yi ya barta anan tana tsiyayan hawayen da suka zame mata jiki, sai ta ma kasa cin abincin ƙwata-ƙwata sai juya shi cokalin take yi a hannun ta, shinkafa da wake ne da man da dafa sai ta saka allayahu sosai ya ji saboda dokar likita yunwa take ji tana zumuɗin cin abincin amma ganin Habib ya sa komai ya ƙwace mata. Hawaye suka kece mata wasu na gangara wasu na kawowa tana tuna irin rayuwar da suka gudanar ita da Habib tun daga soyayyarsu har zuwa auren su. Ta daɗe tana alfahari da buɗe kafaɗan cewa ba wata macen da ta kai ta dacen miji mai son ta da ƙaunarta. Ba ta taɓa tunanin nan kusa za ta fuskanci kuka da damuwa ba, ba ta taɓa zaton wata rana ita Ummu Salma za ta zama wacce Habib ya tsana ba ya son gani ba sai yanzu da yake faruwa, su Baɗɗo sun daɗe suna fata da ƙwatancen su zama kamar ita domin sun ɗauka tarihin soyayyarta ya kai a ba da labarin shi da zai sa mata da dama su ji suna jin haushi da yadda ta yi dace ta bar su, tabbas za a ba da labarin soyayyarta da na rayuwarta gabaɗaya Habib zai sa ta zama abin nunawa da kwatance a cikin dangi da anguwa gabaɗaya. Tana nan zaune tana kuka Habib ya sake fitowa, ta kifa kanta a saman hannun kujeran da take zaune tana ta kuka har yana fidda sauti, yadda ya shigo bai kalleta ba haka ya sake fita bai ko kalli in da take ba amma ita ta ɗan ɗago ta kalle shi ya yi wanka ya sauya kaya zuwa manya yana ta tashin ƙamshin turare. A baya in ta kalli Habib wani nishaɗi da alfahari take ji , wani irin son shi ke ƙaruwa in ta kalle shi amma sai ga shi yanzu in ta kalle shi sai ta ji nadama da baƙin ciki yadda in da za a ba da tarihin rayuwarta sai an fara da Habib watakila ma a ƙare da shi tunda Habib ya gama kassara rayuwarta gaba da baya ba ta kuma da sauran wata mamora. Abincin da ta hakura dashi kenan ba ta ci ba, sai ta mai da shi kitchen ta ajiye ruwa kawai ta iya sha ta koma ciki ta kwanta tana jan casbaha tana kuma kuka lokaci ɗaya. Addu'a take yi ubangiji ya yaye mata ƙunci da damuwar dake cikin zuciyarta Allah ya ba ta ikon cin jarabawanta, cikin da ke jikin ta Allah ya kare shi ta daina ma adduan Allah ya karkato da hankalin Habib kanta, ta yarda kuma ta amince da gaske Habib yake yi bai taɓa son ta ba, shi kuma wanda  ya furta ba ya son ka, to ba zai taɓa son ka ba har gaban abada. ** Habib na fita daga gidan anguwansu ya nufa yana hanya sai ya ji ana ta kiran sallar mangariba shi ya sa bai shiga gidan na su ba sai da ya tsaya ya yi sallar mangariba sannan ya shiga gidan na su ya gaishe da matan mahaifin shi sannan ya shiga ɗakin da mahaifin shi ke jinya ya zauna. Hatsari ya yi shekaru goma da suka wuce, ya bugu a kansa har ya shafi ƙwaƙwalwarsa sannan ƙugunsa ya samu matsala baya iya zama daga kwanciya sai kwanciya sannan baya mgana sai dai ya yi ta kallo ka kawai da idanuwana sannan kan ma da sauƙi. Har kusa da shi ya ƙarisa ya riƙe hannun shi yana gaishe shi yana ta dai kallon shi. Gwaggo ta shigo ita ce babba a matan gidan kuma ita ce ta riƙe Habibu, sai dai a gidan shi ne kaɗai ke da ɗan rufin asiri shi ne Namiji babba sauran duk mata ne suna gidan mazajen su shi ya sa duk ɗawainiyar gidansu tana wuyan sa, da laluran mahaifinsa na shekaru goma ana ta fama, a dangin mahaifin na shi ban da Alhaji Sheriff to kowa ma nema yake yi lamarin dai sai godiya. Gwaggo ta tambayi Ummu da ina tafisu, ya ce tana gida ta ce a gaishe su ya yi ƙarya. Itama ganin ta kwana biyu ba ta zo ba ne ya sa ta tambaya. Tare da Gwaggo suka yi ta hira a ɗakin Mahaifin na shi suna cikin hiran ne Alhaji Sheriff ya kira shi a waya yana tambayan sa ko ya dawo? Sai ya ce ma ga shi a gida kawai sai ya ce su haɗu a gidan bayan an yi issha'i shima zai zo gidan. Habib ya sha mamakin ganin har da Baba Usman ma ya zo, ya ɗauka ya zo duba ɗan'uwansa ne tunda yana zuwa amma sai ya ji yana tambayan shi ko sun yi waya da Alhaji Sheriff? Sai ya ce masa sun yi ya ce zai zo bayan sallan isha'i. Jin da ya yi Baba Usman ya ce to bari su yi sallan su jira zuwan shi ya sa sha jinin jikin shi. Tare da Baba Usman suka yi salla a masallacin kusa da gidan su suna idarwa suka dawo gidan sai suka iske Alhaji Sheriff ya iso da yake shi a anguwansu sukan riga nan anguwan yin sallan su, tun da Habib ya ga Gwaggo bayan sun gaisa da Alhaji Sheriff ta miƙe za ta fita ya ce ta dawo ta zauna maganar ta shafe ta daga nan ya san lamarin ya yi ƙamarin da ya wuce na shi lissafin. Ƙansa na ƙasa ya ji Alhaji Sheriff na jero maganganu Gwaggo na salati ya kwashe yadda abin ya faro tun daga farko har zuwan Mahaifin Ummu Salma wajen shi da yadda suka tattauna. "Habibu ba ka kyauta ba sam." Gwaggo ta faɗa tana kallon shi cikin mamaki shi dai kansa na ƙasa amma ransa ya ɓaci. "Ya ci amanar aure, abin na shi har ya kai ya fara yi ma iyalan na shi horan yunwa? Ga juna biyu in wani abu ya same ta iyayenta suka yi ƙaran shi a kotu ba? Yana da kalaman da zai iya kare kanshi da su ne? Baba Usman ya faɗa yana kallon Habibu da ya ji duk ya muzanta. Ga shi a gaban mahaifin shi suna ta maimaita maganar, duk da ba ya magana amma yana jin duk abin da ke faruwa a ɗakin. "To kun ji dai halin da ake ciki, tun da har na yi masa faɗa bai ji ba shi ya sa na ce mu taru anan ga mahaifin shi tare da ke mariƙiyarsa domin kun san halin da ake ciki. Mahaifinta ya ba ni saƙo na ba shi, ya ce in har ba ya son yar sa to ya dawo masa da ita shi bai gaji da ciyar da ita ba." "Yana da gaskiya." Gwaggo ta faɗa tana mai hararan Habib "Habibu me ya same ka! Kai fa da kanka ka zo ka ce kana son yarinyar nan aka je aka nema maka auranta, auren ko shekara bai yi ba amma an fara samun matsala, kana ɗan musulmi bafillace ka ce sai an zubar da ciki? An ya kana so ka yi albarka kuwa ba ka san ya'ya rahama ba ne! Ka san wanda zai ji ƙan ka anan gaba ne? Gwaggo ta faɗa tana kallon shi, ya ma kasa mgana jujjuya saƙon da aka ce mahaifin Ummu ya bar masa yake yi a cikin zuciyarsa. Lalle ko zai dawo masa da ƴarsa gida tunda  haka ya buƙata. "Kuma yana da tabbacin in ya zubar da cikin ubangiji zai sake ba shi wani damar a gaba ne? Yana da ilimin shi amma Habibu na neman ya yi ma kansa sakarci." Baba Usman ya faɗa yana zaune kusa da Alhaji Sheriff, amma har lokacin Habib bai tanka ba, ya sunkunyar da kansa kawai yana wani tunani. Ba zai ce komai da zai ɓata musu rai ba saboda nan gaba za su yi masa amfani. "Ni dai na gama iya ƙoƙarina na zare hannuna akan duk abin da ya shafi Habibu tun da ba ya jin magana. Ya je ya yi duk abin da zai yi amma ya sani in har ya gaji da zama da yarinyar mutane ne gwara ya sake ta zai fi alheri akan ya zauna yana azabtar da ita" Alhaji Sheriff ya faɗa yana nuna Habibu kafin ya cigaba da faɗin" Shi ya sa na tara ku gwara kun san abin da ke faruwa. Ke Aina'u ki yi masa mgana wataƙila ya saurare ki, ni dai na gama nawa" Yana gama faɗin haka ya tashi zai fita Gwaggo da Baba Usman suna ta ba shi haƙuri. "Ka yi hakuri Alhaji na ka ne fa ba yadda za ka yi. Don Allah ka dawo ka zauna zai ji maganar ka in sha Allahu." Gwaggo ta faɗa cikin tausasawa Baba Usman na ta ya ta. "Sai hakuri Alhaji, kai Habibu ka yi magana ka ba shi hakuri tunda ba ka da gaskiya." Habib ya tura hulan kansa baya yana shafa gaban goshin shi yadda yake jin zuciyarsa a lokacin kamar ya buɗe idanuwana ya ga Ummu Salma ya fara ƙwallo da ita ko zai wuce takaicin shi. "Ka yi haƙuri Abba ba zan ƙara ba." Ya faɗa yana ƙasa-ƙasa da kansa kamar na gari. Da ƙyar ya dawo ya zauna yana faɗin" Ni da na ce na cire hannuna ya je can ya yi duk abin da ya ga zai iya ai ya girma zai iya tafiyar da rayuwarsa yadda yake so." "Ka yi hakuri Alhaji. Habibu duƙa ka ba ma baban ka hakuri." Gwaggo ta faɗa tana kallon Habib, ko ba ta ce ba dole zai rankwafa ya ba shi haƙuri saboda kar nan gaba ya ce ba zai shige masa gaba wajen auren masoyiyarsa ba. "Ka yi hakuri Abba kuskure ne hakan ba zai sake faruwa ba" Habib ya faɗa yana sauke kansa ƙasa sai da ya yi ta ban haƙuri sannan Alhaji Sheriff  ya sassauto yana faɗin" Duk fa wannan  faɗan da ka ga muna yi maka Habibu don muna son ka ne, muna son rayuwarka ta zama abin sha'awa da ƙwatan ce" "Sosai. Kuma wanda ba shi da na gaba ai shi ke da kaico." Baba Usman ya faɗa shima. Shi dai Habib yana ta basu haƙuri kansa a ƙasa. "Ya rage na ka Habibu. Sai ka shirya ko gobe ne ka je gidan surukan naka ka ba su hakuri sannan kar mu sake jin wata magana ta sake tasowa. In hakan ya faru Habibu zan cire hannuna akan ka wannan karon." Alhaji Sheriff ya jaddada  masa, ya kuma amsa masa da cewa zai yi abin da ya ce sun daɗe suna yi masa faɗa da nasihu, ya yi kamar yana ji nan ko a kasan zuciyarsa shi kaɗai ya san abin da yake saƙawa an kawo gabar da ba zai iya kauda kai ba tunda ya ce in gaji da ƴarsa to ya dawo masa da ita, ai ko zai dawo masa da ita, da man duk ya nuna alamun haka sune ba su gane ba. Sai goma saura ya bar gidan duk da tun yana can ake ta kiran wayarsa da turo saƙo bai duba ba sai da ya fito daga gidan ya ɗau hanya sannan ne ne ya duba wayarsa. Da man ya san ita ce saboda sun yi da ita yau zai je wajenta amma bai samu zuwa ba, Ummu Salma ta ɓata masa kyakyawan daran sa, amma hakan ma ya yi yau zai yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda. "Habib wani abu ya faru ne? Saƙon da ya buɗe kenan bayan tarin kiran da ta yi masa bai amsa ba yana gaban su Abba. "Za ki iya aurena nan da wata biyar ? Haka ya rubuta ya tura, ba daɗewa ko sai ga shi an turo masa da amsa. "Me zai hana? Ni da man kai nake jira ni nawa matsalan mai sauki ne Habib." Mirmishi ya yi shi kaɗai kafin ya sake yin rubutu ya tura. Saboda haka har gefen titi ya gangara ya yi parking ɗin motar shi. "To ki shirya kin kusa zamo wa Amaryan Habib in sha Allahu." Yana gama turawa sai ya saka wayarsa a Aeroplane mode saboda ba ya so ta dame shi da tambayoyi abin da ya sani ɗaya ne a wannan daran zai yakice Ummu Salma daga rayuwarsa da ita da cikin jikinta har gaban abada ba ya fatan a sake danganta shi da su, zai fara sabuwar rayuwar da ya tsara ma kansa nan da wattani biyar. Tabbas kaddara ta riga fata. Da man zanen kaddaran su in ya fara tare to Ubangiji bai yi hukuncin labarin na su zai kamallah a tare da juna ba. Ummu Salma da Habib za su rabu a wannan  duniya amma kuma za su sake haɗewa a wata sabuwar duniyar. *littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗannan lambobin kamar haka.* 09069067488. 08032773332. *Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.* *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *10* *10:12pm* Ƙarfe goma da mintina sha biyu Habib ya shiga falon gidan shi, da ƙishin ruwa ya dawo shi ya sa yana shigowa falon bayan ya kunna hasken wuta. Da yake Ummu ta kashe komai kafin ta kwanta Kitchen ya zarce yana neman ruwa a firiza amma babu ruwa sai wani guda ɗaya pure water da ya gani a saman kantan kitchen ya ɗauka sha, ya manta bai bar komai a gidan ba, ruwan bai ishe shi ba amma haka nan ya haƙura har zai fita sai ya leƙa store bai yi mamakin ganin kayan abinci ba, daman dalilin da ya sa ta nace ta ƙi tafiya saboda iyayenta sun kawo mata kayan abinci ne tunda daman ta ji daɗin kai shi ƙara wajen iyayenta. Da gangan ya kwashe kayan abincin shi ya kai gidan su, a tunanin shi ai ba za ta zauna ta mutu da yunwa ba, in ta ga babu komai za ta koma gida ta sanar ma da iyayenta halin da ta ke ciki, su kuma kafin ma su kira shi zai aika mata da takardan sakinta, amma saboda maita da rashin zuciya ba ta tafi ba sai ma aka kawo mata kayan abincin saboda dole ne sai ta zauna a gidan shi, to ya gaji shima zai sauwaƙe ma kan shi ne, gida da man na haya ne kuma shekara ɗaya ne kuɗin hayar kuma na shekaran ya kama gidan saboda biyan buƙatan shi ya kuma samu biyan buƙatan shi to ba zai damu domin ya bar musu ragowan kuɗin hayar ba. A gidan kansa  zai gina wata sabuwar rayuwar da ya tanada shi da abar ƙaunarsa. A fusace ya fito daga kitchen ɗin ya shiga ɗakin da ya ke kwana ya nemo takarda da biro, yana fitowa ƙofar ɗakin da Ummu ke ciki ya shiga bugawa cikin sauri sannan da ƙarfi kamar zai ɓalla ƙofar sannan lokaci ɗaya yana kiran sunan ta. "Ummu Salma." "Ke Ummu Salma." Ya ke faɗa da muryansa a sama lokaci ɗaya yana cigaba da buga ƙofar da karfi. Kamar a mafarki ta ji bugun ƙofar domin har ta fara barci kanta ke ciwo saboda kukan da ta sha, sai ta sha pracetamol tana idar da sallar isha'i ta kwanta cikin ikon Allah barci ya kwashe ta da man wani lokacin tana samun yin barci a farkon dare amma in ta farka ne yake da matukar wahala ta samu nasaran komawa, wata rana ta tashi ta yi salla wata rana kuma ta yi karatun Qur'ani wata rana kuma ta yi kuka. Yau ma da wuri ta samu barcin amma bugun ƙofar da Habib yake yi ya katse mata barcin nata kuma a daidai lokacin daman mafarkin Habib ɗin take yi wai ya kira ta yana yi mata mgana ita kuma ta ɗuka har ƙasa tana bashi haƙuri har ya tashi zai tafi ta riƙo kafarsa amma ya juya ya ture ta a cikinta ta faɗi, sai ga jini na bin ƙafarta shi ya sa bugun ƙofar da mafarkin da ta yi suka samar mata da tashi a firgice tare da fargaba mai tsanani. "Ba za ki buɗe ba! Ke Ummu Salma." Ta ji muryan Habib yana magana, ta sake figicewa cikin gigita ta sauko daga kan gadon da take kwance, ta ma manta da hulan kanta da ya saɓule bayan ta kwanta sai da ta nufi ƙofar sannan ta shafa kanta ta ji ba ɗankwali ga shi kan ya yi datti goron kitso har ya ɓace saboda daɗewa, saboda ba ta kitso take yi ba. "Wai ba za ki buɗe ba? Na san fa kina jina." Habib ya sake faɗa kuma yana cigaba da buga ƙofar, yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke rawa domin ba ta san da abin da Habib ya zo a daran nan ba amma dai tafi tunanin abin da ke kawo shi wajenta ya zo nema jikinta, in shi ne kuma ya zo ga shi nan har sai ya gaji. Saboda saurin ta buɗe kofar har tana neman faɗuwa rigar jikinta ce ta harɗeta ta kusa kaiwa ƙasa sai da ta riƙe gefen wardrope ɗin dake ɗakin. Hannnunta na rawa ta murza key ɗin dake jikin ƙofar ta buɗe ɗakin, Habib ya tsaya yana kallon ta cikin bacin rai. "Ni za ki mayar ɗan iska kina ji ina kiran ki kina yi mini shuru? Kanta na ƙasa ta ce" Ka yi haƙuri ban ji ba ne" Ta ɗauka abin da ya saba kawo shi yau ma shi ya kawo shi ya sa tana gama bashi haƙuri ta juya za ta koma ciki. "Ki same ni a falo." Ta ji ya faɗa ta juya cikin mamaki shi kuma tuni ya bar wajen, zuciyar ta amsa na rashin sanin dalilin kiran Habib amma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta bi bayan shi zuwa falon, jikinta ya yi wani irin sanyi ne lokacin da ta ga Habib zaune kan kujera mai zaman mutum biyu ya harɗe kafafunsa kamar wani basarake ga littafi da takarda a hannun shi har da biron rubutu. Kasa ƙarisowa ta yi ta tsaya cak daga nesa tana kallon shi cikin bugawar zuciya, me Habib zai yi da takarda da biro? Allah ya sa ba abin da zuciyarta ke saƙa mata ba ne, in ko haka ne da ta ce ita yau Ummu Salma ta shiga uku ta lalace rayuwarta ta faɗa cikin mawuyacin garari, gararin da har abada ba za ta iya fita daga cikin sa ba. "Malama ki ƙariso kin tsaya mini a saman kaina " Salau-salau haka ta ƙarisa gaban shi, ta zauna a kasan cafet tana mai ƙura ma kwalliyan cafet ɗin idanuwanta, amma hankalinta ba ya wajen in da zai lura ma kafafunta da hannayenta ma rawa suke yi tsabar firgici. "Kin gama na ki aikin saura nawa aikin kuma Ummu Salma." Sai ta ɗago tana kallon shi amma ba ta yi magana ba. "Kin je kin haɗa ni da iyayena, kin yi ƙoƙarin ɓata mini gobe na sai dai burin ki bai cika ba." Ya sake fada yana mai kallon ta fuskar nan ba fara'a kamar bai taɓa dariya ba. "Me kuma na yi? Ummu ta faɗa muryanta na karyewa kamar ta fashe da kuka. "Ni kike tambaya abin da kika yi! Kin manta kin sake kai ƙarana wajen iyayen ki? Ke a tunanin ki za su iya sauya komai ne? Ta ma kasa mgana bakinta na rawa, shi ya sa kawai ta yi shuru amma har hawaye sun kece mata maganarsa ya ba ta tabbacin Baffa ya ji labarin halin da take ciki, magana ta kai kunnen iyayen Habib. "Ummu Salma ba ke kaɗai ne ba ki da tunani ba har da iyayenki ma." Da sauri ta ɗago ta kalle shi cikin mamakin kalaman shi, iyayenta ne marasa tunani?  Yau ita Habib ke faɗa ma iyayenta ne ba su da tunani? "E haka na ce ba su da tunani, in har suna da tunani ai ya ci ace zuwa yanzu sun fahimci bana ra'ayin ki, na nuna bana son ki a aikace duk domin su fahimta su sauƙaƙa mini aiki amma sun kasa fahimta ban sani ba ko a wajen su ne kika gado wannan kidahumancin na ki ba" Habib ya gama faɗa har yana nuna kanta cikin izgili. Ummu Salma ta yi ma Habib ƙuru da ido ta kasa mgana, domin sai ta ji kamar an zare mata duka lakkan jikinta. Yau iyayenta ne kidahumai a bakin Habib? Iyayenta fa? In ita ya zageta ta shanye, to ai bai kama ta ya taɓo bangaren iyayenta ba, domin ya san duk ɗa na gari ba zai zura ido ana cikin zarafin iyayenshi kuma ya yi shuru ba. "Na gaji da ke, na gaji da auren ki wallahi, ke kika fara cutar da iyayen ki tun da kika ɓoye musu gaskiyan manufata akan ki, su kuma rashin tunanin su da lissafin su yasa suke tunanin ina son ki, sannan iyayena suna da ikon sarrafa rayuwata ne? Ina, rayuwata ce ni ke da ikon zaɓa ma kaina yau n da gobe na ba wani ba, ba kuma wanda ya isa ya saka ni na zauna da abin da bana so, a farko ni ne na yi ra'ayin zama dake saboda ina son cimma burina, yanzu kuma na gama amfana dake, na cimma burina akan ki me kuma ya yi saura a tsakanina da ke? Ya faɗa yana zare mata ido. Ummu na hawaye har da majina, ta ce" Iyayena ba su yi maka komai ba Habib ka daina zagin su don Allah." Ta faɗa kukanta har yana fitar da sauti. Sai ya kwashe da dariya kafin ya ce"Oh kina jin zafi ne? To na dai na cewa basu da tunani suna da shi, amma dai ba zan fasa faɗa miki kin turo bagidajen tsohon ki wajen iyayena ba kuma ya zo, sannan kuma har ya bar mini saƙo " "Haba Habib." Ummu ta sake faɗa cikin kuka tana sakin shessheka domin ji take yi kamar ta shiɗe yadda maganganun Habib suke kassra tunaninta da sauran kuzarinta gabaɗaya. "Na faɗa wannan bagidajen uban naki ne, wai shi ne yake da zarran zuwa ya faɗa ma Abba cewa in na gaji dake ne na dawo masa dake gida" Ya gama faɗa yana wata dariya ta reni da wulakanci. "Shi yana ɗauka ya yi gwanin ta ne, ko kuma me ya ke takama da shi? Lauyan yayanki? Ko mai aikin filin jirgi? Ko mai fama da gwajin kashi da fitsari ko mai aiki da hukumar ruwa? Ko wannan yayan na ki mai bin tsohon ku saro tsoffin injina? Ko kuma wannan yayan naki mai karatun jami'a? Ko wanda ya tafi ƙasar waje da kuɗin tallafi? "Habibb.." Ta faɗa muryanta baya fita saboda kuka. Bai saurareta ba ya cigaba da faɗin. "Oh na tuna ko yana takama da wannan ɗan da bai haifa ba ne? Lamiɗon da dangin ku ke ji dashi, Yariman Daura ko? Wanda uwarki ke zuwa maula gidan sarki ko? Da shi yake taƙama da har zai zo wajen ƙanin mahaifina ya bar mini wannan saƙon?  To in ma gatse yake yi ya yi kuskure, a yau ba sai gobe ba zan cika umarninsa zan mayar masa dake kamar yadda na ɗauko ki daga gidan shi." "Habib ka bari, ka daina zagin iyayena." Ummu Salma ta faɗa tana kuka zuciyarta na ƙuna tana wani irin soya da irin wannan cin mutumcin da Habib ya zaunar da ita yana yi ma iyayenta da yan'uwanta. "Na faɗa ko za ki rama musu ne? Ya faɗa yana taso mata kamar zai dake ta sai ta yi shuru ban da kuka ba abin da take yi, yi take yi kamar zuciyarta zai fita, wani ɗaci na taso mata ɗacin an ci zarafin iyayenka a gaban idanuwanka amma ba ka da hurumin da za ka hana faruwan haka, miyan bakinta har kafewa ya yi saboda yadda zuciyarta ke tafarfasa. "Ni ce na yi maka laifi ba iyayena ba. Ni ce baka so ba su ba, to kuma su me suka yi maka da za ka ci zarafin su? Ummu ta faɗa cikin kuka mai ƙarfin da sautin shi yake fita sosai. "Ka yi mini abin da za ka yi mini zan jure Habib, ka tozartani iya tozartawa ba zan taba mgana ba, amma ba zan jure jin maganganun cin fuska ko na ɓatanci ga iyayena ba, kar ka sake ban zagi naka iyayen ba kai ma ba ka da hurumin da za ka zagi nawa iyayen." Tana magana yana mata dariya kamar ya ga wata mahaukaciya. "Me suka yi mini kike tambaya na? Tasowa ya yi zuwa gabanta ya durƙusa saitin kunnuwanta ya yi magana. "Saboda sun haife ki, laifin su kenan a wajena." Ya faɗa yana yi mata dariya, Ummu na tsiyayan hawaye tana kallon Habib tana jin son ta ji ta tsane shi, tana so ta daina jin ko da ɓurɓushin son shi a cikin zuciyarta amma ina, tunda ba ita ke da alhalin sarrafa zuciyarta ba har yau ba ta daina jin son Habib a ƙasan zuciyarta ba. Miƙewa ya yi ya koma in da ya tashi ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda har tsohon ki ya bar mini sallahun in na gaji dake ne na dawo masa dake shi bai gaji dake ba, to a matsayin shi na Surukina mahaifin matar da na aura na more albarkatun jikinta ya zame mini kamar wajibi na cika umarninsa." Kallon ban fahimce ka ba Ummu ke yi masa kamar idanuwanta za su faɗo kasa, ga shi suna masu zubar da hawaye. Takardan ya jawo a gefen shi ya ɗora saman cinyarsa ya ɗora biron a kai lokaci ɗaya yana faɗin" Zan sake ki kamar yadda mahaifinki ya ɓukata, duk da ya ɗan yi gaggawa, da a ce ya jira da ni da kaina zan sako masa ke ba sai ya wahalar da kansa wajen zuwa ya bar mini saƙo ba." Ummu Salma ta ji kanta ya sara, har ɗan dake cikinta sai da ta ji ya motsa saboda firgici da tashin hankali. "Yanzu Habib sakina za ka yi? Ummu ta tambaya muryanta cikin kuka kamar za ta shiɗe. "Kina tantama ne? Bari na rubuta na ba ki ki karanta sai ki samu tabbaci " Kawai sai ta ga ya fara rubutu da sauri ta rarrafa gaban shi cikin kuka tana faɗin" Don Allah Habib ka yi hakuri kar ka sake ni, don Allah ka taimaka mini ka rufa mini asiri ka da ka sake ni." Take faɗa tana wani irin gunjin kuka, ga ta duke kan gwiyoyinta tana mai zubar da hawaye tana haɗa shi da Allah akan kar ya sake ta. "Ai abin da tsohon ki ya bukata ne, duk da nima ina da niyyar yin haka amma ba yau ba." Ya faɗa yana nuna halin ko in kula, yana ma ƙoƙarin cigaba da rubuta abin da ya fara. Da sauri Ummu ta faɗa kan kafafun Habib ta riƙe shi gam tana wani gunjin kuka. "Ke miye haka? Ya faɗa yana fizge kafarsa har tana yin gefe amma ba ta haƙura ba sai da ta sake riƙo kafafunsa da karfi ta rumgume a ƙirjinta lokaci ɗaya tana faɗin. "Na tuba, don Allah ka yi haƙuri Habib kar ka sake ni." "Wallahi sai na sake ki, mutuwa ce kawai za ta hana na sake ki, itama sai in yanzu ta zo ta ɗau raina amma in dai ina raye a yau zan yada ƙwallon mangwaro na huta da guda." Ya gama faɗa yana sake fizge kafafuwanshi ya ɗora saman kujera ya bar Ummu duƙe a gaban shi tana wani irin kuka kamar za ta shiɗe. "Habib in ka sake ni ina zan je? Wa zai sake kwasa ta? Wa ye zai iya aurena bayan ba ni da komai. Don Allah ka rufa mini asiri kar ka sake ni, kar ka manta da gudan jinin mu dake rayuwa yanzu haka a cikin jikina, kar ka bari ɗan mu ya rayu ba tare da kai ba, ka yi haƙuri don Allah ka rufa mini asiri " Majina har zuba take yi a ƙasan cafet saboda kukan da Ummu ke rusawa amma ina Habib ba ya sauraranta rubutu kawai yake yi. "To na ji , wallahi zan yi duk abin da kake so. Na ji zan. Zan zubar da cikin." Ta faɗa cikin fitan hayyaci, har muryanta na dishewa saboda kuka. Ganin ya ɗago yana kallon ta, ya sa da sauri ta sake rarrafawa gaban shi tana rawan bakin faɗin " Da gaske na ji zan zubar da cikin in har zan tsira da aurena." Take faɗa cikin fitan hayyaci, domin ba ta ji ba ta gani, tunanin ta hangenta shi ne in Habib ya sake ta ya gama lalata mata goben ta, ya cuceta ya mai da ita ƙaramar bazawara, sannan tana son shi tana son aurenta za ta yi komai domin ta ga ta tsira da aurenta. "Kika ce me? Ya tambaya yana mata wani kallo "Na ce, e zan zubar da cikin wallahi na yarda." Ta faɗa hawaye na kwaranyo mata yadda ya ga ta ruɗe ne tana roƙon shi har tana cewa ta yarda za ta zubar da ciki ya sanya shi nishaɗi ya kwashe da wata dariyan jin daɗi. "Na yarda ko yanzu ne ma mu je a zubar amma don Allah kar ka sake ni " Ta sake faɗa tana haɗe hannayenta waje ɗaya alamun roƙo. "Yarinya kin makara." Ya faɗa yana dariya sannan ya cigaba da rubutun sa. "Wataƙila da wata ɗaya kafin yanzu ne kika ce mini haka da zan iya sauraran ki, amma yanzu lokaci ya kure miki, da man ai na sha faɗa miki sai kin yi nadama, a ranar da nadamar ba za ta yi miki amfani ba lokacin da na ke bin ki, kina mini yadda kike so ai ba ki yi tunanin rana irin ta yau za ta zo ba, duk ɗaukan maganganuna kike yi a wasa? Ummu ta kasa magana ban da kuka ba ta komai. Ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya cigaba da faɗin" Ni yanzu ban damu da ki zubar da cikin jikin ki , ko ki zubar ba ko ki haife shi duk wannan ya rage na ki, dake da cikin duka bana so, ba na kuma buƙatar ku a cikin rayuwata " Ya ƙarishe faɗa yana nuna ta da yatsa daga sama har ƙasa cikin ƙyama. Ummu ta gigice ta sake fashewa da kuka tana faɗin" To ba ka ce jikina kake so ba? To ai ga jikin nawa ai ba na hana ko? Ta faɗa tana yi kamar za ta haura a saman kujeran da yake zaune. "Ke kar ki hauro mini nan" Ya faɗa yana zare mata ido. "To to na zauna " Ta faɗa lokaci ɗaya tana zaman dirshan a gaban shi yanayinta kawai za ka gani ka fahimci ta rasa natsuwarta ba ta ma san abin da take yi ba, ballantana abin da take furtawa. Ganin ta cikin wannan yanayin yafi masa komai daɗi, nishaɗi da farinciki yake ji da man ya ce sai ta yi nadama to kaɗan ta gani. "Ai ni gama moran duk wani albarkatun jikin ki, babu wani sauran maiƙon da ya rage da ban gama lashewa ba." Ya faɗa yana dariya ƙasa-ƙasa har yana kashe mata ido ɗaya. Ummu na kuka tana kallon Habib kamar zai yi mata gafara tana rokon shi Allah da Annabinsa kar ya sake ta, amma ina bai ƙara sauraran ta sai da ya gama rubuta abin da ya yi niyya sannan ya miƙa mata , ta kasa karɓa lokaci ɗaya tana girgiza kanta cikin kuka. "Karɓi mana " Ya faɗa yana mai sake miƙa mata takardan. "Don Allah Habib. Kar ka. Sa ke ni." Ta ƙarishe faɗa kamar za ta shiɗe domin har numfashinta ya fara ɗaukewa. "Ai na ma riga na sake ki Ummu Salma." Zuciyarta ta tsinke, idanuwanta suka fara rawa, hannaunta ɗaya ya kama ya tusa mata takardan lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda dare ya yi na yi miki alfarman ki kwana amma gobe da safe ki tattara kayanki ki koma gidan ku, kayan ɗaki kuma suma ki zo ki kwashe kafin masu gidan su bukaci dakin su." Yana gama faɗin haka ya kwashi takardansa da biron sa ya wuce yana sake faɗin" Alhamdulillah." Har yana wani harba ƙafafuwansa, Ummu ta bi shi da kallo cikin zubar ƙwalla takardan ta matse a hannunta tana sakin kuka da ƙarfin iyawanta, kuka ta fashe da shi da duka muryanta da ubangiji ya ba ta, kanta a ƙasa kamar tana sujudda take rusa kuka kamar ranta zai fita Habib ya gama tozarta, irin tozarcin da bata taɓa jin labarin an yi ma wata mace ba, Habib ya sake ta da ƙaramin ciki bayan ya gama lalata mata rayuwa ya mayar da ita ƙaramar bazawara, ya kunya ta iyayenta ya cutar da ita sannan ya cutar da zuciyan ta. Koda ta ɗago daga durkushen da ta yi ruwan hawaye da majina ya gama jiƙa cafet ɗin gabanta sannan fuskarta har ta jirkice tsabar kuka da tashin hankali, a hankali ta miƙe tana jin jiri na ɗiban ta, kanta na sara mata da ƙarfi, cikinta ya cure waje ɗaya daƙyar ta iya jan kafafunta tana dafe bango ta koma ɗakinta tana matsanacin kuka takardan sakin na matse a hannunta ta kasa dubawa, ba ta son gani ba ta son ganin wannan baƙin rubutun Habib a gare ta, kukan ta kawai take yi da karfi ba ma tunanin ta yi shi a cikin zuciyarta, yi take yi tana shessheƙa, tana fidda sauti ga majina na shatata, ga ruwan hawaye kafin kace me gaban riganta ya jiƙe da hawaye, fuskarta ta kumbura saboda kuka idanuwanta sun tasa sun yi jajir kamar gawarshi, daga karshe ma da ta gaji da kukan dole ta haƙura ta koma ajiyar zuciya tana faman sauke numfashi a jejjere kamar wacce ta yi gudun tsere tana zaune a ƙasan tayels a gefen gado kanta na gefen gadon ta ɗora saman hannayenta lokaci ɗaya hawaye na kwaranya har a saman hannayen ta amma ta daina kuka da sauti sai dai a cikin zuciyanta take jin wani ɗaci da raɗaɗin da ba za ta iya misalta yanayin ba. Takardan sakin na jimƙe a hannunta ganin zufan hannunta ya fara jiƙa takardan ya sa ta ɗan ɗage zanin gado ta tura takardan ta koma ta kwantar da kanta tana ta tsiyayan hawaye yadda ta ga rana haka ta ga dare barci ko ɓarawo bai sace ta ba a cikin kunnuwanta aka fara kiran sallan asuba, duk kuma tana zaunen har wasu masallatan suja tayar da salla amma ta ƙasa tashi saboda kuka ga jikinta duk ya yi tsami kanta saboda ciwo ba ta ma san ma ɗago shi, sannan ga idanuwanta sun kumbura sumtum ko iya buɗe su ma ba ta yi, ko'ina na jikinta ya yi tsami saboda kwanan da ta yi a zaune cikin yanayi mara daɗi, da rarrafe kamar yar koyo ta shiga tiolet ta kama ruwa sannan ta wanke fuskarta da ruwan zafi ta ɗauro alwala haka ta fito da rarrafe nan domin ba za ta iya tashi ba ji take yi kamar kafafunta ba za su iya ɗaukan gangan jikinta ba. Salla ma a zaunen ta yi, ta daina zubar ƙwalla amma raɗaɗin dake cikin zuciyarta kaɗai ya isa ya yi ajalinta. Domin zuciyarta wani zafi take yi ga wani abu mai ɗaci da ya tokare mata a ƙirji tun jiya ya kasa wuce miyan bakinta ya daɗe da kafewa sannan bakin nata ya yi ɗaci kamar maɗaciya, sannan ga ciwon kai mai tsanani yunwa take ji amma a bakinta ba ta bukatar cin komai maranta ya cure waje ɗaya da ya haifar ma gangan jikinta rawa, bayan ta idar da sallan ta kura ma waje ɗaya ido tana ma rasa abin da take tunani, yanzu fa wata sabuwar rayuwa ce ta tunkaro ta bayan barin ta gida na wattani takwas a matsayin matar aure yanzu kuma za ta koma gida a matsayin bazawara har da ƙaramin yaron ciki, yanzu a wannan kadamin wa za ta kira? Ina za ta nufa? Rayuwarta ta gama lalacewa ba ta da sauran wani abu na mamora a tare da ita. Tuna gargaɗin da Habib ya yi mata ajiya ne ya sa ta rarrafa ta ɗauko wayarta dake saman side drower ɗin gadon. Gwara ta bar gidan tun kafin ya fahimci ba ta tafi ba ya yi mata wulaƙanci, agogon wayarta ta duba sai ta ga shidda ne da mintina biyu na safe wataƙila Baffa na masallaci sai ta kira wayar Ammah amma tana ta ringing ba ta ɗauka ba ta kira ta kamar sau uku amma shuru, sai ta mayar da akalan kiran zuwa ga Baffa, domin nan duniya su ne kaɗai ne suka rage ba za su guje ta ba, amma ta rasa komai na ta. zuciyarta na sake yin duhu in ta tuna yadda Habib ya zaunar da ita yana cin zarafin iyayenta da ƴan 'uwanta. **** *6:13am* Shidda da mintina sha uku Baffa da Hamma Saddam suka shigo gidan daga masallaci, jiya da yamma Saddam ya dawo daga makaranta can Bauchi. sun gama jarabawa za su yi hutun sati uku kafin su koma. Ɗakinsa ya wuce shi kuma Baffa ya ƙarisa cikin gida, ɗakinsa ya wuce kai tsaye yana shiga ya iske Ammah na zaune saman darduma da casbaha a hannunta bakinta na motsi, yana takawa zuwa gefen gado wayarsa dake cikin aljihun rigan jikinsa ta ɗau ruruwan kira, bai duba ba sai da ya zauna sannan ya fiddo wayar yana duba sunan mai kiran.. "Auta." Ya faɗa a sarari cikin mamaki, Ammah na lazimi sai da ta kalle shi cikin mamaki. "Auta kuma! Ummu Salma? Amma ta faɗa cikin ƙarin mamakin gabanta na faɗuwa, shima ita yake kallo amma sai ya aro jarumta a matsayin shi na namiji. "Bari na ji Allah ya sa lafiya." Ya faɗa shima cikin ƙarfin hali, kafin ya ɗaga kiran ma ya katse hannunsa na rawa yana ƙokarin sake kiran ta sai ga kiranta ya sake shigowa da sauri ya ɗaga kiran yana mai kiran sunan ta. "Auta" Ya faɗa yana jin bugawar zuciyarsa na ƙaruwa da sauri da sauri. Ummu Salma daga can bangaren jin muryan Baffa ya sa rauninta ya karu, hawaye ya kece mata mai hade da kuka Baffa sai jin sautin kukan kawai ya yi ta cikin wayar. "Ummu Salma." Baffa ya faɗa cikin tashin hankali, Ammah na jin yadda ya kira sunanta cikin sauri ya sa ta bar saman darduman ta dawo gefensa ta zauna ta kafe shi da idanuwanta cikin damuwa tana faɗin. "Baffa me ya faru da Auta? Ta faɗa tana jin jikinta na yin wani sanyi, haka kurum take jin faɗuwar gaba tun jiya da man kawai Autan ke faɗo mata arai ta so ma kiranta sai ta ga dare ya yi tana shirin da man yau ta kirata a waya ta ji lafiyan ta ne. Baffa ya kasa mgana jin yadda Ummu ke rusa masa kuka a waya gabaɗaya jikinsa ya gama yin sanyi amma sai ya yi jarumta komai ya faru daga gare ka ne Ya Ubangijin mu. "Ki bar kukan nan ki yi mini bayanin abin da ya faru Auta." Ya faɗa cikin lallashi a muryan sa Amma ta sake tsurewa a cikin zuciyanta tana maimaita kalmar kukan da ta ji Baffa ya ambata. "Baffa." Ummu Salma ta kira sunan Baffa muryanta a shaƙe da ƙyar ma take fita. "Naam Auta me ya faru ne? Ya faɗa cikin sauri domin ya kosa ya ji abin da ya faru duk da yana zargin wani abu amma bai yanke hukunci ba. "Baffa." Ta sake kiran sunan shi cikin matsannacin kuka duk ta ruɗar da Baffa, ga Ammah ma a gefen shi kamar za ta kwace wayan idanuwanta kawai ya kalla ya ga tsoro da firgici a cikin su. "Na'am ina jin ki Auta, ki daina kuka maza ki sanar da ni abin da ke faruwa bar kuka Auta kin ji ko? Ya ƙarishe faɗa muryansa na karyewa shima jin irin kukan da Ummu Salma ke yi a waya kamar ranta zai fita. "Baffa Habib." "Me ya samu Habib ɗin? Baffa ya katse da sauri kafin zullumi ya kashe shi. "Ya sa ke ni..." Ta faɗa tana sarƙewa cikin matsanancin kuka. Sai da Baffa ya miƙe da sauri kansa ya sara, idanuwansa suka ciko da ƙwalla hannunsa na rawa haka ƙafafuwansa shuru ya yi yana kiran sunan Allah a cikin zuciyarsa domin ya samu ya tattaro natsuwarsa. Ammah ta biyo shi a tsayen tana tambayan shi jin ya yi shuru sannan ba su yanke wayar ba, ta san waye Baffa shurun sa na nufin damuwa mai yawa ko a fuskarsa ma ya bayyana haka. Tana so ta yi magana amma sai ta kasa ta dai tsura masa ido kawai tana bin shi da kallo. "Baffa Habib ya sake ni, ya sake ni jiya da daddare." Ummu Salma ta sake faɗa cikin kuka jin Baffa ya yi shuru, bai ce komai ba. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un." Baffa ya samu bakin shi da furtawa cikin wata murya mai cike da tausayin Ummu. "Allahumma ajirni fimusibatihi. Daga gare ka muke Allah kuma a gare ka za mu koma." Baffa ya sake faɗa cikin yaƙinin da cewa akwai Allah da sanin sa komai ya faru kuma shi zai kawo sauƙin lamarin cikin gaggawa. Ummu kuka kawai take rusawa kamar ranta zai fita Baffa ya kasa jure jin kukan ta kawai sai ya kashe wayar, ya ma kasa kallon Ammah wacce ke bin shi da kallo, kansa ya juyar kawai ya koma ya zauna a gefen gado ya dukar da kansa lokaci ɗaya ya saka hannayensa duka biyu ya dafe kansa yana sake maimaita salati da muryansa cikin rauni da tausayi. "Allah ya ba ki ikon cinye wannan jarabar mai zafi da raɗaɗi Ummu Salma." Muryansa ta karye da man Baffa akwai rauni ko ciwo mutun yake yi sai ya yi kuka lokacin da Ammah ke haihuwa haka zai yi ta kuka asibiti in tana naguda, ganin yanayin shi kawai ya ba ta tabbacin wani abu ya faru mara daɗi amma ba ta tambaya ba, sai ta bishi ta zauna a gefen shi ta ɗora hannayenta saman kafaɗan shi tana ɗan matsawa alamun lallashi duk da itama ƙarfin hali take yi amma zuciyarta ta yi rauni ba ta so ta nuna ne. Shuru na wani lokaci kafin Baffa ya fesar da numfashi cikin hikima ya share ƙwallar da ta ɗan siraro masa ta gefen idanuwansa saboda kar Ammah ta gani abin da bai sani ba, ta riga ta gan shi, kukan sa kawai ya sake ba ta tabbacin Ummu ta fsɗa cikin kaddaran aure, kaddaran da take ta yi mata fatan kar Allah ya sa ta faɗa a cikinsa, domin ba ko wacce mace ba ce jaruma, ba ko wacce mace ba ce take iya tsallake wannan jarabawar sai jaruma sai sadaukiya amma Ummu ba za ta iya ba zuciyarta karama ce tana da rauni ba lalle ne ta fuskanci girman jarabawan da ya faɗa mata ba. Baffa ya ɗago kanshi suka haɗa ido da Ammaj sai kawai ta yi masa mirmishi, ita wai a dole ta nuna masa ba ta damu ba, fillanci na cin ta amma duk wanda ya kalleta ya san a cikin zuciyarta tsoro ne da fargaba ba ta tambaye shi ba shima sai ya kasa faɗa mata, illah hannayenta da ya jimƙe cikin nashi yana kallon ta amma ya kasa mgana a cikin zuciyarsa salati kawai yake yi da kiran sunan Allah. Itama sai ta jimƙe hannayen na shi cikin nata cikin karfin hali ta kira sunan shi. "Baffa." Bai amsa ba amma yana ta kallon ta. Sai kuma ta yi shuru ta kasa mgana tana so ne ta tambaye shi amma ta kasa, shi kuma ya san halinta ba za ta sake tambaya ba saboda kawaicin ta sai kawai ya yi kumdulan fada mata ita uwa ce ya kamata ta sani ko domin su yi tunanin mafita. "Jamila." Tunda ta ji wannan sunan a bakin Baffa ta san maganar da zai faɗa mata mai girma ne. "Habibu ne ya saki Auta jiya da daddare." Ya faɗa yana kallonta hannayenta na cikin na shi yana matsawa, shuru na wani lokaci yana kallon ta duk da ta tsammaci haka amma ai zato ne ba gaskiya ba yanzu da ta samu tabbacin sai ta ji zuciyarta ta yi duhu wani abu kamar ya sare daga kirjinta kwata-ƙwacin abin da ta ji a lokacin da Fatima ta zo gare su da tsohon dare ɗauke da jaririn da ko jinin haihuwa ba a wanke masa ba, a lokacin da ta ba ma Baffa takardan saki, abin da ta ji a lokacin a wannan lokacin ma shi ta sake ji. "Ta kira ni tana ta kuka Jamila. Gwanin ban tausayi " Ya sake faɗa muryansa har tana sauyawa, Ammah ta yi ajiyar zuciya kafin ta tattaro kalaman bakinta ta furta."  Allah ya sa hakan ya zame mana alheri gabadaya " "Amin " Ya amsa yana kallon ta. Shuru na wani lokaci kafin Amma ta yi ƙarfin halin cewa" Baffa wa zai je ya taho da Ummu? Ta faɗa tana kallon shi, sai yanzu ya tuna ya kamata wani ya je ya ɗauko ta zuwa gida a yanayin da ta ke ciki tana bukatar wani a kusa da ita. "Bari na yi ma Saddam magana ya tuka ni muje mu taho da ita." Baffa ys faɗa yana miƙewa da sauri Amma ta mike ta riko shi ganin duk ya daburce kallon ta ya yi yana cigaba da faɗin" tana ta kuka gwara na je da kaina " Ya faɗa yana laluban aljihun jikinsa "Ammah ina key ɗin mota ta? Ya faɗa yana waige-waige Baffa fa ba ya cikin natsuwarsa shi ya sa ta sake riko shi tana kiran sunan shi. "Baffa." Sai kawai ya tsaya yana kallonta "Jamila Auta tana can tana kuka ba ki ji muryan ta ba." Ya faɗa cikin karyewan sauti, kawai sai ta faɗa jikin shi, domin itama in ta cigaba da jin sautin Baffa cikin rauni za ta iya fashewa da kuka ba ta sani ba, jin ta a jikinsa ya sa ya yi shuru kawai yana sauke ajiyar zuciya, bayansa take ɗan tapping da hannunta alamun lallashi, kuma ta yi nasara domin sai ya ɗan samu natsuwar zuciya. "Ba kai za ka je ba Baffa." Ya ji Ammah ta faɗa da sauri ya dago ta kafin ya yi magana ta yi saurin cewa" ka kira Abdullahi ka sanar da shi abin da ke faruwa ka ce ya ɗau mota ya je ya ɗauko Aminiya zan kira ta yanzu na sanar da ita abin da ke faruwa, ita in suka je za ta shiga ciki ta taho da Ummu gida." Tabbas ya aminta da shawaran ta, gwara mace ta je zai fi akan namiji. "Hakan ya yi, amma ko na kira Abdulrrahman ne? "Aa gwara dai Abdullahi ka san halin Abdulrrahman  fusattace ne." Shi saboda tashin hankali duk ya manta da halin ƴa'yan na shi, wayarsa ya fara laluba Ammah ta ɗauko masa ita a gefen gado ta mika masa lokaci ɗaya tana faɗin" Ka kira shi yanzu, bari na je na kira Aminiya" Tana gama faɗin haka ta wuce ta fita daga ɗakin,  falon ta yana sakaye ne ta tura ta shiga wayarta a chaji ta sakata tun daran jiya hannanunta na rawa kamar yadda zuciyarta ke bugawa. Tana duba wayar sai ta ga ma Ummu ta kirata sau uku a lokacin da ta kira Baffa kenan, lambar Ummin ikki ta nemo wacce ta yi ma saving da Aminiya, duk da Ammah ba ta yi karatun boko ba amma sun yi yaki da jahilci shi ya sa ta iya karanta hausa, wani lokacin ma da fillanci take yi saving din lambobin wayarta. Sai dai tana kiran wayar sai ta ji a kashe, har sau biyu ba ta shiga ba sai kawai ta laluɓo lambar wayar Aisha(Baɗɗo). Tana kiranta ita sai ta shiga. Baɗɗo na kwance a ɗakin su bayan ta idar da sallar asuba gajiya ne a jikinta jiya wajen takwas na dare ta iso gida daga Mubi, tana idar da salla sai ta ɗan kishigiɗa barcin ya ɗan ɗauke ta kenan ta ji ringing ɗin wayarta dake gefen filon data ke kwance da barci-barci ma a idanuwanta ta zaro wayar sai dai ta wattsake ganin sunan Ammah tana kiranta, ido ta waro tana sake duban sunan mai kiran da gaske dai Ammah ce. "Wa ke kira hala ? Adda Kaltume ke tambaya ganin yadda Baɗɗon ta zaro ido kamar ta ga wani abun tsoro. "Ammah ce fa." Ta faɗa tana kallon ƙaramin agogon bangon dake ɗakin barcin na su, ƙarfe 6:32am na safe to ba lafiya. "Topha, ɗaga mu ji Allah ya sa dai lafiya" Adda Kaltume ta faɗa, daidai lokacin da Baɗɗo ta ɗaga kiran Ammah bayan ta sake kiran ta a karo na biyu. "Ammah ina kwana." Daga can bangaren Ammah ba ta tsaya amsa gaisuwar Baɗɗo ba da sauri ta ce" Aisha ina Aminiya? "Tana ɗakin ta " "Kai mata wayar zan yi magana da ita." Amma ta faɗa muryanta cunkushe, Baɗɗo ta mike tana amsawa da to Adda Kaltume tana ta mata tambaya me ya faru da hannu, ita kuma Baɗɗo tana ɗaga mata hannu alamun ba ta sani ba. Ummin ikki na cikin ɗakinta, itama da carbi a hannunta tana ja ne barci ya ɗan sace ta tana zaune tana ta gyangaɗi sai ta ji Baɗɗo a saman kanta tana faɗa mata ga Amma na son magana da ita. "To Allah ya sa lafiya " Ta faɗa tana leken waje ganin har lokacin gari bai ida sa wayewa ba. Tana karɓan wayan ta saka a kunnenta lokaci ɗaya tana faɗin" Aminiya Allah ya sa lafiya." Ummi ikki ta faɗa cikin fargaba kira da sassafe haka ba na lafiya ba ne. "Wayarki a kashe Aminiya ? Ammah ta faɗa, da sauri Ummin ikki ta ce" Tun jiya ban ga wayar ba, waya sani ma ko ta mace ba chaji ne." Amma tace" To ƙila." "Lafiya Aminiya? Na ji muryan ki wani iri ne" Amma ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Ki shirya ga Abdullahi nan zai zo ya ɗauke ki zuwa gidan Ummu" "Me ya faru da Ummun? Ummin ikki ta tambaya har tana waro ido, Baɗɗo na gefe tun da taji an ambaci sunan Ummu ta matso kusa da sauri tana son jin abin da ya faru. "Ya sake ta ne." Ammah ta faɗa tana runtse ido, kafafunta sun fara rawa da ya sa dole ta lalubi gefen kujeran dake gefenta ta zauna tana ƙoƙarin daidaita yanayin ta. "Ya sake ta fa ta kika ce Aminiya! Shi Habibun ne ya saki Ummu Salma? Ummin ikki ta faɗa da karfi da ya sa Baɗɗo ta yi zaman yan bori a gaban Ummin tana faɗin" Habib ya saki Ummu? Ta sake maimaitawa hannunta a saman ka cikin tashin hankali. "Ya sake ta Aminiya, Abdullahi na hanya za ku je ku taho da ita " "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un amma dai Habibu ya cuce mu Allah ya isa tsakanin mu da shi." Ummin ikki ta fada sai ga hawaye Ammah kashe wayarta kawai ta yi ta bar Ummin tana ta salati da tsine ma Habibu. Baɗɗo ta fashe da kuka tana faɗin" Innalillahi Ummi Habib ne ya saki Ummun? Ummun tawa? Take faɗa tana kuka, Ummin ikki ta ce" Wannan yaron ya gama cutar mu Allah sarki Ummu." Da man kuma Ammah ta sanar da ita zaman da aka yi na farko ta dinga zagin shi tana cewa mara albarka, to amma daga baya Ammah ta ce mata an daidaita ashe bai hakura ba sai da ya mayar da ƙaramar yarinya bazawara. Kukan Baɗɗo da hargagin Ummi ya fiddo da duka yaran gidan har mahaifin su Baɗɗo duk wanda ya tambaya aka faɗa masa abin da ya faru sai ya girgiza. "Subhanallah lamarin bai yi daɗi ba me ya faru ne? Baban su Baɗɗo na tambaya Ummi ba ma tsaya masa bayani ba ta miƙe tana faɗin Abdullahi na hanya zai zo ya dauketa za ta je ta taho da Ummu zuwa gida Baɗɗo na jin haka ta ce itama za ta je Ummi ta ce ba za ta je ba. "Ummi ki je da ita in Ummu ta gan ta za ta ji daɗi " Adda Kaltume ta faɗa cikin damuwa ta girgiza da jin wai Habib ya saki Ummu Salma, duk wanda ke gidan nan ya san waye Habib domin zuwa goma in Ummu za ta yi shi zai kawo ta ya kuma zo ya ɗauke ta kuma duk zuwa sai ya shigo ya gaida Ummi da Baba, tun kafin auren su ma bayan auren ma sai ya zama ɗan gida nan zai zo ɗaukan Ummu su zauna a falon Ummi da shi da Baɗɗo da Ummun suna ta hira suna dariya. Kowa sai jinjina lamarin yake yi, abin mamaki abin tausayi ga rayuwar Ummu, da wayar da Ammah ta yi da Ummin ikki ko minti talatin ba a yi ba sai ga Hamma Abdullahi bakwai saura mintina ya iso gidan yadda ya shigo kawai za ka san shima labarin ya dake shi, jallabiya ce a jikinshi a baibai ya sako ta ma domin yana barcin nan na bayan asuba ya samu wayar Baffa labarin da ya faɗa masa ne ya sa ya diro daga kan gado bai shirya ba, ya razana da jin wai mijin Ummu ya sake ta! Har ya kariso gidan Ummin ikki yana tunanin to me ya sa zai sake ta? To ta yi masa wani abu ne? Daga Ummin har Baɗɗo da hijaban jikinsu suka bi Abdullahi takalma kawai suka saka, suna tafe a mota Ummin ikki na sake kwashe ma Habib albarka Baɗɗo na daga baya tana ta sharan ƙwalla tausayin halin da Ummu take ciki a daidai wannan lokacin. "Ummi to wai me ya sa zai sake ta? Ko ta yi masa wani abu ne? Abdullahi ya tambaya jin yadda Ummin ke mgana da alamu ta san wani abu. "Ba ka san abin da ya faru kwanaki ba ne Abdullahi? "Ban sani ba Ummi, Baffa bai faɗa mini ba, haka ma Ammah." Nan fa ta warware masa komai mamaki ya kama shi sai ma ya kasa mgana wato shi ya sa kenan ya ga Baffa Umaru ya zo har da mijin Ummu da ita kanta ashe lokacin duk matsalan ne ya ta so. "Wai ba ya son ciki ka ji fa, sai ka ce shi uwarsa ba cikin ta yi ta haife shi ba wataƙila daga sama ya faɗo" Ummin ikki ta faɗa cikin takaici da haushi. "Allah ya kyauta." Kawai Abdullahi ya ce amma maganganu na yawo a cikin ranshi, ta ya ya mutum zai auri macen da yake so kuma ya ce ba ya son ciki? Cikin kuma  na shi ne, daga karshe hadda saki? Kai gaskiya yana tamtama an ya mijin nan na Ummu Salma yana son ta kuwa? Domin wanda ke son ka ba zai yi maka wannan tozarcin ba. Bai sake magana ba har suka isa gidan, a bakin flat ɗin Ummu suka yi parking ɗin motar, dukkansu kuma suka firfito, abin mamaki ƙofar falon Ummu ma a buɗe take har ga labule nan a waje shi ya sa kawai suka faɗa, Baɗɗo ce ta shige gaba da sauri Ummi a bayanta Abdullahi kuma sai ya tsaya daga waje bai shiga ba, a tunanin shi ko Habib ɗin na gidan abin da ba su sani ba tun wajen shidda da rabi ya tattara kayan shi kaf ya bar gidan a motar shi baya son ma wani cikin yanuwan Ummu su gan shi tun da abin da ya haɗa su ya raba baya fata ko son sake haɗuwa da duk wani abu da ya shafi Ummu Salma. Tunda ya ce ya gama da ita, to har abada ya gama da shafin ta. Yadda Baɗɗo ta ga Ummu Salma ya sake tsinke mata zuciya tana zaune a in da ta yi salla kanta jingine da wardrope, ta yi kuri kawai ba ta magana ba ta kuma kuka amma fuskarta da idanuwanta sun kunbura babu kyan gani. Rumgumeta ta yi ta fashe da kuka tana faɗin" Allah ya saka miki Ummu, da ikon Allah Habib sai ya ga sakamakon shi."   Ummu ba ta mgana tana dai kallon Baɗɗo kawai, Ummin ikki ta kasa mgana saboda tausayin Ummu har tana ƙwalla. "Baɗɗo kamata ta tashi, ki kaita falo ki zo ki ɗan haɗa mata kayan sawan ta." Da to Baɗɗo ta amsa, ta taimaka ta miƙar da Ummu tsaye ta riƙe ta zuwa falo, ta zaunar da ita a saman kujera ta zauna kawai tana kallon ta, bakin ma ya ɗinke ba mgana sai dai kawai ido. Baɗɗo na kuka ta juya ta koma ciki tare da Ummin ikki suka cika akwatin Ummu huɗu da kayan sawan ta, Ummin ikki ta ce duk a cire zannuwan gadon kar su yi ƙura a tusa su cikin wardrope kafin a ga abin da Ubangiji zai yi, Baɗɗo ce ta yaye zanin gado sai ga takarda ta faɗo ta ɗauka ta buɗe ta karanta. "Ummi." Ta faɗa cikin ƙaraji lokacin da ta gama karanta takardan sakin Ummu Salma. "Mene ne ya faru? Ummin ikki ta faɗa cikin tashin hankali tana kallon Baɗɗo.. "Ummi saki uku fa Habib ya yi ma Ummu." Ta faɗa tana nuna mata takardan hannunta "Innalillahi wa'inna alaihirraju'un." Ummin ikki ta faɗa kanta har yana sarawa. "Wannan wani irin sakin wulakanci ne da tozarci? Ta faɗa tana hawaye, Baɗɗo ba saki ukun take yi ma kuka ba illa maganganun da Habib ya rubuta masu alamu da tozarci da wulakanci bayan sakin Karɓan takardan Ummin ikki ta yi ta ce bari ta kai ma Abdullahi bayan ta umarci Baɗɗo da ta yi sauri ta naɗe zanin gado ta kuma jawo akwatunan Ummu zuwa falo. Abdullahi na tsaye jikin motar shi yana waya da Hamma Jibo. Jiya sai wajen goma na dare suka isa, yana shirin zuwa wajen aiki ne Abdullahi ya kira shi yana sanar da shi mugun labari, shi ne  suke tattaunawa yana ba shi labarin halin da ya je gidan Ummu ya same ta a ciki har zuwan  da suka yi  shi da Baffa gidan waliyin Habibun ashe duk bai ji ba shi ne ya yi mata sakin wulakanci, sai a lokacin Abdullahi ya tuna wato ranar da ya ga Baffa da Hamma Jibo sun tafi ashe can suka je. "Ni fa Hamma duk ban san abin da ke faruwa ba, kwanaki dai na ganta a gida duk ta rame to ni ban kawo cewa mata matsala ba ce." Abdullahi ya faɗa yana nusar da hannunsa a cikin sumar kansa. "An ɗauka za a iya gyara lamarin ne ashe bai zai gyaru ba." Hamma Jibo ya faɗa daga can bangaren cikin damuwa da tausayin ƙanwar tasu. Kafin Hamma Abdullahi ya sake magana Ummin ikki ta fito wajensa tana mika masa takardan hannun ta. "Abdullahi ka ji tozarcin da wannan yaron ya yi mana? Saki uku fa ya yi ma Ummu? Har Hamma Jibo ya ji abin da Ummi ikki ke faɗa a tare shi da Abdullahi suka saki salati cikin  firgici. Kashe wayarsa Abdullahi ya yi yana mai karɓan takardan hannun Ummi ya fara karantawa a bayyane. "Ni Habib Idris Mai Imani na saki matata Ummu Salma Hadi Baba saki uku, da ita da cikin jikinta bana ɓukatar su a rayuwata. Na sake ta ne saboda ni ban aure ta domin ina son ba, saboda jikinta na aure ta kuma na samu abin da nake so, shi ya sa na rabu da ƙwallon mangwaro na huta da kuda. Maganar ciki kuma sai da na ce ta zubar da shi ta yi taurin kai da a ce ta ji magana ta da ba haka ba, to ina so ku sani abin dake cikin Ummu Salma ba ni da alaqa da dashi har abada ba ni da danganta da abin da za ta haifa ballanta wata rana a neme ni saboda shi. Ni da Ummu mun rabu,rabuwa ta har abada ku ɗauka ma kamar ba mu taɓa sanin juna ba." "Hasbunallahi wa'imal wakeel" Ummi ikki ta faɗa tana mai riƙe kanta cikin baƙin ciki da takaici. Abdullahi ya ma kasa mgana ji ya yi lamarin ya yi masa nauyi wannan wani irin tozarci ne, lalle wannan yaron bashi da mutumci duk yadda Abdullahi ke da saukin kai sai da ya fusata ya harzuka da wannan sakin wulaƙancin da Habib ya yi ma ƙanwarsu. "Lalle wannan yaron ba shi da mutumci ba ɗan arziƙi ba ne. " Ya faɗa yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa. Baffa da Ammah kawai yake tunawa, in ya tuna da Ummu sai ya ji ya karaya, ya take ji yanzu? A wani hali zuciyarta take ciki, ya cuceta, ya cuce su sai dai Allah ya saka musu kawai. *littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗanan lambobin kamar haka.* 09069067488. 08032773332. *Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.* *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *11* *TUSHE, MAFARI*. Mafarin ya fara daga Abdullahi(AUDU BABA) bafillace haifaffan garin Mubi. ita kuma Mubi ƙaramar hukuma ce daga cikin Jahar Adamawa Yola. Garin Yola nan ne maƙyanƙyasan sa tun daga kakkannin shi dai bai san wani asalin tarihin iyayen shi ba sai da ya san su a haifaffun jahar Adamawa, wasu suna cikin yankunan dake zagaye da Adamawa kamar irin su girai, funfore, ganye da dai sauran su amma shi asalin iyayen iyayen shi a garin Mubi sukai rayuwa shima anan aka haife shi anan kuma ya yi rayuwarsa har zuwa auran shi na fari da bafillatan matarsa mai suna Asma'u. A matsayin shi na bafillace tsantsan na gaba da baya, kamar wajibi ne ya auri bafillatana yar'uwansa sannan da yake ba karatun boko matan suke yi da wasu mazan ba to ana yi musu aure ne suna da ƙananun shekaru, in har ka ga namiji ya yi karatu to sai in har fita ya yi cirani daga nan sai ya faɗa harkan neman ilimi , shima hakan ne ta kasan ce da shi yana da ƙarancin shekaru ya yi auran shi na fari kafin ya sake yin wani auren na gani ina so. Lokacin ya fara shiga jahohin Nigeria domin fatauci ya faɗa garin Daura na Jahar Katsina a can Allah ya haɗa shi Ummu Salma(Gwaggo) ita ɗin haifaffiyar baƙar bafillata ce yar nan garin Daura ce ta uwa da ta uba, tunda Audu Baba ya ƙyalla ido ya ga Ummu Salma ya ji duk duniya ba wacce yake so irin ta a lokacin itama shekarunta ba su wuce sha biyar ba yarinya ce ƙarama ya ɗauka zai sha wahala kafin ya same ta amma sai ga shi cikin lokaci ya samu abin da yake so, tun ballanta da Ummu Salman take son shi ta ga dogon bafillace jajir tas a tsaye jarumi kuma Sadauki tuni ta ce shi take so, su kuma iyayenta ganin duk tushe ɗaya ne sai suka aura ma Audu baƙo Ummu Salma ya tafi da ita can garin su Mubi. A lokacin ƴa'ƴan shi da Asma'u huɗu Hamza, sai Umaru, Salihu da Sha'aibu. Zuwan Ummu Salma ya sanya suka haɗe kansu suna zaune lafiya Ummu Salma ta ɗan jima ba ta haihu ba sai da aka yi ta karɓa mata taimako wajen shekaru biyar da auran su sannan ta haifi babban ɗan ta namiji wanda Audu Baba ya yi ma huɗuba da Hadi bayan shi kuma ba ta sake haihuwa ba har sun cire rai ma gabaɗayan su sannan ta samu Fatima wanda tsakanin su da Hadi shekaru sha bakwai ne. A lokacin da aka kawo Ummu Salma wacce kowa ke kiran ta da Gwaggo akwai wata maƙociyarsu da aka yi ma Gwaggo uwar ɗaki da ita tun lokacin da aka kawo ta Daura wacce ake kira Nenne tsada saboda hasken fatan ta duk yankin a lokacin ba mai jan ta, shi ya sa ake kiran ta Nenne tsada ita ta zama kamar uwa ga Gwaggo tun kawo ta garin zuwa yanzu komai nata da na ƴa'yanta Nenne take shigewa gaba ita Nenne Allah bai ba ta ɗa Namiji ba duka ya'ƴanta mata ne sannan in ta haihu sai su yi wabi a cikin yara goma da ta haifa huɗu kawai suka tsaya mata, Balki ce babba sai Salamatu sai A'i, sannan autar ta Jamila wacce a lokacin yar shekaru goma ce to bayan Jamilan ma ta sake haihuwa sau uku suma suna yin wabi su kaɗai ne ta samu suka tsaya mata, tunda da daɗewa megidanta ya rasu ita kaɗai ce ke gwagwarmayan riƙe marayun ƴaƴan nata. A lokacin Gwaggo tana cewa ta kama ma Hadin ta Jamila matsayin mata, tun ana ɗaukan maganar wasa har dai Gwaggo ta tabbatar da ita ba wasa take yi ba. Tun Jamila na ganin Hadi tana gudunsa har ta daina domin shi bai taɓa ɗaukan maganar Gwaggo da muhimmamci ba tun ballatana a lokacin shi ɗan gayu ne tunda yana makarantan boko, Jamila kuma karatun allo suke yi a lokacin sannan tana da wata Aminiya da suke tare tun suna yara mai suna Aisha. Gida uku ne ya raba tsakaninsu duk in da za su je tare ne sannan makarantan allo ɗaya suke zuwa iyayensu su san juna, ko kaya ne in za a yi ma Jamila sai an yi ma Aisha haka itama gidan su Aisha ba sa nuna cewa Jamila bare ce, Aminci ne mai karfi a tsakanin su tun suna yara har kuma girman su sai da Ubangiji ya saka aminta da yarda har a tsakanin ƴaƴan su.   Jamila na da shekara sha shidda a duniya bayan ta yi saukan Allo aka saka ta a lallen aure ita da Hadi. Shi a lokacin yana da shekaru ashirin da shidda ne, kuma yana gama sakandiri amma bai cigaba da karatu ba sai dai yana yin noma sannan yana kiwo. Auren gata aka yi musu auran da har bayan shekaru masu yawa suke zaune a ƙarƙashin kulawan iyayen su a garin Mubi suka fara gudanar da kyakyawan rayuwarsu a farkon auran su Hadi ba ya son Jamila amma da tafiya ta yi tafiya sai ya ji ya gode ma zaɓin Gwaggo har bayan ranta in ya tuna da abin alherin da ta yi ma rayuwarsa sai ya gode ma ta sannan ya yi mata addu'an samun haske a cikin kabarin ta. A shekaran auran su Jamila ta haifi yaron ta na farko mai suna Jibril ana haihuwan shi Gwaggo ta ce an samu Jibo shikenan sunan ya bi shi har girman shi, Jibo ya taso tsakanin iyaye da kakanni ne shi ya sa Jamila(Ammah) ba ta sha wahalan renon shi ita kaɗai ba sunan da Hadi(Baffa) Ammah ce ta fara kiran shi da Baffa har ya kama bakin yaran gabaɗaya, bayan Jibo ta sake haihuwan Mustapha tana da cikin Mustapha suka saka Aminiyarta a lalle Aisha ta yi aure a garin Girai duk da ba ta son auren amma hakan nan aka kaita kuma ta zauna sai ya kasance ba a gari ɗaya suke aure da Jamila(Amma) ba. Haka dai rayuwa ta cigaba da gudana cikin farinciki, Nenne ta fara rasuwa maciji ne ya sare ta a makewayi sai dai gawarta aka iske a kwance shike nan su Ammah sun zama marayu Allah ya sa ma dukkansu sun yi aure a cikin garin Mubi shi ya sa sai maraicin ya zo musu cikin gata Ammah ta fi kowa jin mutuwar Nenne amma samun Baffa kusa da ita ya sa ba ta daɗe ba ta warware uwa uba ga Gwaggo ga Baba ita yar gata ce gaba da baya ba sa barinta ta yi kukan rashin wani abu saboda soyayya da gata. Ga ƙanwar Baffa Fatima da kusan a tare suke rayuwa tun da ba wani tserayan shekaru ne a tsakanin su ba. Ta haifi Mustapha ko shekara bai yi ba suka sake samun wani rashin na rasuwar Audu Baba shima lafiya lau ya kwanta da asuba rai ya yi halin shi tsakanin shi da Gwaggo kwana arba'in, da man tun rasuwar Baba ba ta da lafiya ashe itama ajali ne Baffa da Ammah sun fi kowa shiga cikin tashin hankali gaba da baya maraici ya sarƙe rayuwarsu yanzu ba su da mai kula da su, Ammah ta rasa mai duba ta, mai kula da ya'yanta da duka rayuwarta sun yi kuka kamar ba za su daina ba. Ga Fatima da take ƙarama a lokacin abin tausayi da Baffa ya so ya karɓi riƙon tilon ƙanwarsa amma sai dangin Gwaggo da suka taho daga Daura suka ce za su tafi da ita saboda ita mace ce sannan Baffa kuma ba kai girman da zai iya rike wani ba shima yana da iyalansa tunda Baba baya raye yana ji yana gani suka tafi da Fatima Daura ko gadon su na Baba da Gwaggo da aka raba su suka tafi da shi, shi kuma ganin ba Gwaggo ba Baba sai ya fara tunanin barin Mubi duk da akwai Umma(Asma'u) da sauran ƴan'uwansa maza amma duk da haka sai garin ya yi masa ƙunci Ammah ma duk ba ta cikin walwalarta tun ballantana da Fatima ta bar Mubi zuwa Daura rashin ta dameta sosai tana kuka tana cewa za ta iya riƙe Fatima me ya sa Baffa ya bari aka tafi da ita? Lallashinta ya yi ta yi saboda shima bashi da tacewa a lokacin a matsayin sa na ƙarami sannan su Hamma Hamza a lokacin ba su hana ba to shi ma bai isa ya ce komai ba. Da kuɗin da aka raba musu gado Baffa ya fara bin matasa garin da sukan shiga cikin birnin Yola kasuwanci yana ɗan taba harkoki a can farko ya ɗan faɗa harkan siyar da siyarwa ne daga baya kuma ya fara haɗawa har da cinikiyar dabobbi irin su shanaye da raguna, duk abubuwan dai ba su tafi daidai ba sai ya faɗa harkan siyan tsoffin ƙarafan motoci ya fara daga ƙananun karafa ne sanadiyar wani abokin kasuwancin sa da suka haɗu a garin Yola shi ya ba shi tabbacin harkan ana samu sosai kawai sai ya faɗa kuma bai rufe shekara ba ya ga haske a cikin lamarin, yana daɗewa baya gida tunda ba iya Yola yake harkokinsa ba ko'ina har Lagos da ibadan suna haurawa neman ƙarafa sai dai in ya ga mai zuwa gida ya tura ma Ammah da su Umma saƙo wani lokacin sai ya yi wattani biyar ba ya gida amma duk da haka bai manta da tilon ƙanwarsa ba yana tura kuɗi can gida Mubi ya ce in an samu mai zuwa Daura akai ma Fatima sannan duk salla yana yi mata sutura tunda suna kawo ta salla ƙarama in kuma sallar layya ce Baffa da Amma ke zuwa can Dauran saboda dai kar Fatima ta yi maraicin rashin iyaye da ƴan'uwa. Kuma Alhamdulillah Fatima ta samu iyayen riƙo na gari. Wanda ke riƙon ta ƴaya maza suke da Gwaggo Madibbo shi Allah bai ba shi haihuwa ba ne har sun fara tsufa shi da mai ɗakin sa, sannan yana aiki a gidan Sarkin Daura shi ke kula da bargan dawakai na cikin masarautan gabaɗaya. Fatima ba ta yi karatun boko ba amma tana yin karatun addini. Shekaran su Gwaggo uku da rasuwa Baffa da Ammah da yaran su biyu suka yi ƙaura daga mubi zuwa garin Yola acan Baffa ya kama musu haya suka fara zama saboda harkokinsa suna daɗewa a can shi ya sa ya ga gwara ya ɗauko ta, ta dawo kusa da shi amma in salla ne ko aka yi wani abu ba su manta da mafarin su ba suna zuwa Mubi tunda can ne gabaɗayan yan'uwan suke Ammah ma duka yan'uwanta suna Mubi ga Aminiyarta dake aure a Girai sai dai har lokacin ba ta haihu ba amma in dai Amma ta je Mubi ta kan karisa can Girai su zumunci da amincewar Baffa kamar yadda ya saba bata dukkan wata dama ba ya tauye mata haƙƙin ta na aure ta kowani bangare godiya take yi ma Allah da ba ta auri Baffa ba da ta zama mai asara a cikin mata. Baffa da kansa ya je Daura ya taho da Fatima ya kawo ta Yola ta ga in da suke da zama ta yi kwanaki da su kafin ta koma kuma lokaci bayan lokaci tana zuwa duba su musamman Baffa zai tura mata kuɗin mota domin ta zo, yana ƙaunar ƙanwar shi, itama tana son yayan ta guda ɗaya da suka haɗa uwa saboda yana kula da ita sosai. Tana da shekaru sha bakwai kwatsam mariƙinta Madibbo ya aiko masa da cewa ya zo Daura yana son ganin shi akan Fatima ne ba ɓata lokaci ya shirya ya tafi yana zuwa sai ya ji labarin da ya girgiza shi wai Fatima ta samu miji, amma mijin ba kowa ba ne sai yaron Sarkin Daura. Sarkin Daura a lokacin Alhaji Muhammad Shitu Daura ne sarki na 49 a lokacin. Kuma ɗa ne ga sarki Alhaji Bashar Daura sarki na 39 a wancan zamanin, Sarki Alhaji Muhammad Shitu  yana da tarin ƴa'ƴa amma duka duka yaran shi maza guda biyu ne Babban ba shi da lafiya ana ta raɗen raɗen an haife shi da ɗan matsalan ƙwaƙwalwa, sai kuma na biyun Muhammad Nasiru(Hakimin Daura kuma Yarima mai jiran gado) domin tun a lokacin ana tunanin shi ne zai gaji sarauta daga mahaifinsa saboda zamowarsa tushen masauratan Daura. Mahaifiyarsa Hajiya Ruƙayya(Fulanin Daura) duk da fa a wancan lokacin ba ita ce uwargidan Maimartaba Alhaji Muhammad Shitu ba, Hajiya Rakiya Muhammad Shitu ce(Magiyar Yamman Daura) amma ita ce mafi soyuwa a gare shi tunda ita ce mahaifiyar Hakimin Daura sannan Yarima mai jiran gado. Labarin ga shi dai mai daɗi ne amma kuma ba shi da daɗi a mahanga da yanayin tsarin rayuwarsu na talakawa, ina Fatima ina Yarima mai jiran gado! Ai haɗin ma bai yi ba akwai tazara mai yawa su da ba kowa ba, sai talakawan gari ina su ina haɗa kafaɗa da masu garin gabaɗaya nan da nan Baffa ya nuna bai amince ba shi bai ma yarda son Fatima yake yi ba domin bai ga ta in da suka haɗu ba, ballanta har rayuwarsu ta haɗu waje ɗaya. Amma mariƙinta ya dage da cewa Yariman Daura mutumi ne na gari mai taimakon talakawa, mai alheri ga matasa mai son talakawaa kuma mutanen garin Daura suna son shi kamar yadda ake son mahaifin shi. Sai dai duk da haka Baffa bai amince ba duk sun faɗa masa a gidan Sarkin Yariman Daura ya ga Fatima lokacin da ta je kai ma Madobbi abinci kuma ya ji nan duniya ita yake so ya kuma je ya yi magana da mahaifinsa. Shi kuma Sarkin Daura a lokacin Marigayi Alhaji Muhammad shitu ya sa aka kira Maddibo mariƙin Fatima ya yi magana da shi a cewarsa da talaka da mai kuɗi da mai sarauta duk Allah ne ya yi su, sannan tunda dai Muhammad Nasiru ya ce yana son ta shi kuma ya yi alƙawarin samar masa da duk abin da yake so amma duk da haka Baffa bai amince ba haka ya dawo Yola cikin damuwa da Amma ta tambaye shi sai ya sanar da ita abin da ke faruwa itama ta ce gaskiya abin ma bai haɗu ba ta ina Fatima za ta kai kanta a matsayin auran ɗan sarkin? Sarkin gobe itama ta goya masa baya kan hukuncinsa saboda haka ma ya ce zai ɗauko Fatima ta dawo hannun shi ya saka ta a makaranta ta yi karatu nan gaba Allah zai kawo mata mijinta ta yi aurenta amma ba ya jin zai yi kasadan wasa da rayuwarta wajen kai ta in da ya fi karfin zuwan ire-iren su. Ba ƙwace Fatima ya yi daga hannun mariƙanta Modibbo ba amma dai ya nuna zai karɓe ta riƙon ta ya dawo hannun shi tunda Allah ya rufa masa asiri shi kuma Madibbo sai ran shi ya ɓaci da ganin kamar Baffa ya raina masa ne sai ya tara yan'uwansu dangin Gwaggo ya faɗa musu halin da ake ciki nan aka ba ma Baffa rashin gaskiya suka kuma hana shi ɗaukan Fatima daga ƙarshe suka yanke shawaran tura wakilan Sarki can Mubi wajen su Baffa Hamza domin su yi mgana tunda suma suna da haƙƙi, Baffa ba da yawun shi aka aminta da auran Fatima da Yarinman Daura ba lamarin bai yi mishi ba tun ballanta da yaji auren a matsayin auren sirri ba wanda zai ji labarin auran daga Daura a cewar Maimartaba saboda mahaifiyar Muhammad Nasiru in ta ji labari ba za ta bari hakan ya faru ba, hankalin Baffa dai bai kwanta ba sai da ya je har garin Daura ya yi kyakyawan bincike akan Masarautar Daura ya samu kyakyawan shaida akan Maimartaba da Hakimin Daura amma sam bai samu shaida mai kyau kan Fulanin Daura ba, mace ce mai ji da kanta da sarauta, ita ɗin babanta ya yi sarki kakanta ma Sarki ne sannan mijinta ma Sarki ne kuma ɗan ta ma zai yi sarauta, shi ya sa ba ta ƙaumar talaka ko mara arziƙi tana harkokinta da masu asali ne da sarauta a labarin da ya ji ma tana nema ma ɗan ta auren ɗiyar wazirin Daura ne a lokacin. Ba yadda Baffa bai yi da kar a yi auren ba amma ba wanda ya saurare shi, dangin Gwaggo suna ganin wata dama suka samu guda tak a kaf zuru'an su, suma su Baffa Hamza haka suke gani musamman shi da yake Babba mulki da kwaɗayi sun rufe masa idanuwa ganin irin dukiyar da Sarki yasa aka aiko wasu amintatttunsa da shi a matsayin Sadakin Fatima har da gwala-gwalai, Umma(Asma'u) a lokacin itama ta goyo bayan Baffa amma Baffa Hamza bai saurare ta ba, yana ji yana gani aka ɗaura ma Fatima aure da Hakimin Daura daddare domin sirrinta auren. Auren da aka ɗaura a garin Mubi sannan anan aka saka Fatima a lalle tana kuka tunda ko sau ɗaya bata taɓa sanin mijin ba, ta dai san Hakimin Daura a saman doki kansa da rawani idanuwansa kawai ta taɓa gani tunda suna zuwa kallon hawan salla lokacin shagulgulan salla a lokacin mace ba ta ikon cewa ba ta son wanda aka bata ko ba ta so dole za ta yi hakuri ta zauna kowa faɗa mata yake yi ta yi dace a dangin su kaf daga asalin tushen su ba wacce ta taɓa samu sa'ar da ta samu, Baffa ne kaɗai bai yi farinciki ba Ammah daga baya ta saduda ta riƙa lallashin Baffa da ya yi hakuri ya yi ma ƙanwarsa addu'an samun dacewa.  Da za a tafi da Fatima Daura a wani kebantttacen gidan Maimartaba da ba wanda ya san da shi za a ajiye Fatima cikin sirri, Baffa ya yi magana da ƙanwarsa ya yi mata nasihan ta yi ma mijinta biyayya amma shi dai a ƙasan zuciyarsa yana ta jin tsoro, tsoron faruwan abin da yake gudu kuma daga ƙarshe sai da ya faru ɗin   Tun Baffa na tunanin nan da wata ɗaya zai ji wani abu game da Fatima har dai aka kwarari wattani bai ji komai ba sannan tana yi masa saƙo da cewa tana nan lafiya lau. Sai hankalin shi ya kwanta ya ɗan samu natsuwa bai sake jin ya natsu ya samu kwanciyar hankali ba sai da Fatima ta zo ganin su a Yola tare da wani dogari amintattacen Hakimin Daura ya kawo ta Fatima ta yi kyau ta yi kiba har da wayar nan ta zamani a hannunta Handset sannan ta tabbatar ma da su Amma da Baffa cewa mijinta na son ta Sarki ma na zuwa dubata amma dai ba ta zuwa  ko'ina itama ba mai zuwa wajenta daga ita sai wata amintattaciyar Baiwa mai suna Zulai tare ma suka zo sai dogarai guda biyu masu gadin ta da direba, irin kayan alfarman da ta zo da su kawai ya isa ya ba su tabbacin abin da ta faɗa gaskiya ne sannan ta zo ma da Baffa da kuɗi da suturu shi da Ammah da yara ta ce daga Hakimin Daura. Baffa dai ba abin duniya ba ne a gaban shi, shi dai fatan shi da burin shi Fatima ta samu farincikin da zai dauwama. Bayan zuwan Fatima sun sake dawowa tare da Hakimin Daura mijinta sun zo yi musu sallama zai tafi wani cos na wattani biyar kasar waje kuma tare da Fatima zai tafi, Hakimin Daura har ƙasa ya duka ya gaishe da Baffa ya kuma ba shi tabbacin har iya numfashinsa na ƙarshe zai kare Fatima. A lokacin da suka bar kasar Fatima ta bar Ammah da cikin Kabiru ne itama acan ƙasar da suka je ta samu ciki kuma suna garin ba su dawo ba maganar auren Hakimin Daura ya tabbata da Ɗiyar Wazirin mai ci a lokacin dalilin haka ya sa Fulanin Daura ta tsara bikin da yana dawowa za a ɗaura aure a yi shagulgula. Auren da ya zagaya duniya, amma Baffa bai damu ba tunda Fatima ta tabbatar masa tana lafiya babu abin da auren nan ya rage ta ko shafe ta. Ita tunda auren sirri ne yanzu ne duniya ta shaida Hakimin Daura ya yi aure suka kuma tare a wani katon bangare a cikin masarauta. Fatima ta zo taron sunan Kabiru da tsohon cikin ta in da suka haɗu da dangi daga Mubi,  kowa ya ga Fatima sai ya rike baki ta yi wata kiba sannan duk in ta taka kunyanga na biye da ita riƙe da jakarta ta zama abar sha'awa a wajen dangi, tana ma Yolan ne ta samu labarin Maimartaba Sarki Muhammad Shitu ba lafiya an fita da shi ƙasar waje domin nema masa lafiya kuma tare da mijinta aka tafi, dalilin da ya turo direba ya ɗauke ta ya ma yar da ita Daura ta koma da kwana uku Allah ya yi ma Maimartaba rasuwa, mutuwar da ta saka ma suna da mutuwa mai tonon asiri, domin sanadiyar mutuwar maimartaba sirrin auran ta ya bayyana a masarautar Daura. Ranar da Hakimin Daura ya zo hankali tashe yana sanar da ita mahaifiyarsa Fulanin Daura ta saka ana bibiyansa ta gano komai saboda haka ta shirya zai saka a zo a ɗauke ta zuwa can Mubi har zuwa komai ya lafa ya fita ya barta cikin tashin hankalin da ya jawo mata gajeruwar naguda. Daga ita sai Zulai ta haifi kyakyawan ɗanta namiji mai kama da uban shi, tana ma nishin haihuwan Fulanin Daura ta dira gidan a daran tare da Mijinta Hakimin Daura. Fatima na kwance a cikin jinin Haihuwa Fulanin Daura ta umarci ɗanta da ya sake ta a cewarta zama da Fatima zai iya yi masa cikas da hawa karagan mulki ita kuma nan duniya ba abin da take muradi da fata kamar ta gan shi ya gaji mahaifinsa Fatima na kuka yana kuma yana roƙon ta amma Fulani ta ce ya zaɓa ko daraja da ƙimar masarautan Daura, Ko auren Fatima Ba shi da yadda zai yi anan take ya yi ma Fatima saki ɗaya sannan ko ɗan da aka haifa masa Fulanin Daura ba ta bashi damar ɗaukan gudun jininsa ba a daran ta saka aka ɗauki Fatima a mota ita da abin da ta haifa, a cikin jinin haihuwa ita kanta da tsamin naguda da jinin haihuwa a jikinta ta kamo hanyar Yola a daran ba ta je ga gidan mariƙanta ba , sannan ba ta je mubi ba Sai ta je ga Baffa da Ammah ƙarfe uku na dare Fatima ta isa ita da Zulai da wani dogari Baffa sai da ya yi hawayen tausayin Fatima. Suna kuma kawo ta ba su tsaya ba suka juya daga Umarnin Fulanin Daura bayan an basu kuɗaɗe da gwala'gwalai da cewa kar Fatima da abin da ta haifa su sake dawowa Daura har abada. Sannan su Madibbo ma sai da Fulani ta saka a ka sauya musu gari suka koma cikin garin kurfi a cewar ta, ba ta son duk wani da ya danganci Fatima ya zauna a garin Daura ba ta fatan nan gaba labarin Fatima ya fito har ya yi ma ɗanta cikas ɗin zamowar Sarki. Waɗanda ma suka sani a lokacin duk ta rufe bakin su, ta haramta musu ambaton labarin. Tabbas burinta ya cika, Hakimin Daura Muhammad Nasiru ya gaji mahaifinsa ya hau ƙaragan mulkin Daura bayan matarsa Gimbiya Shahida ya sake auran mata uku ya cike kofa a halin yanzu mata huɗu gare shi, ita kuma Fatima tana wajen Baffa tana rayuwa cikin kunci da baƙin ciki, dalilin Fatima domin ta samu kwanciyar hankali ya so da a ce shi mai kuɗi ne da zai yi nesa da garin Yola na har abada saboda Fatima ta samu kwanciyar hankali amma duk da haka sai da suka bar Yola suka koma cikin Jimeta da zama, kuma dawowar Fatima gida bai sa ya je Mubi ya faɗa musu abin da ya faru ba daga can ne Midibbo ya sanar da su ga abin da ya faru Baffa Hamza ya dawo yana wallahi tallahi, duk dai bayan an gama jajantawa ba wanda ya sake bi ta kan Fatima ballanta halin data ke ciki. Fatima ba ta mgana sai kuka sai damuwa ba ta cin abinci sai Baffa ya zaunar da ita yana ba ta baki da lallashi da nasiha kamar ta ji amma da ya bar wajen sai ta koma gidan Jiya. Muhammad Lamiɗo  da Baffa ya yi ma shaƙika da huɗuba wajen ma bashi Nono ma sai Baffan ya tsaya mata ba domin Ammah ba sai dai Lamiɗo ya mutu ba mai kula da shi, itace ta haɗa shi da Kabiru a lokacin mutane da dama suna tunanin ko y'an biyu ta haifa tunda tsakanin su bai fi kwana arba'in ba. Ammah ta sha wahala sosai ga Fatima ita kanta kula da ita ake yi Aminiyarta Aisha ce auren ta ya mutu a can Mubi kuma ana ta magana sai Amma ta yi ma Baffa mgana ya ce ta taho ta zauna da su na wani lokaci, ko domin ta riƙa taimaka ma Amma da kula da su Lamido ga Fatima. Ta zauna da su na tsawon shekara ɗaya a wajen su Ammah ta samu miji ta yi auren ta da Babansu Baɗɗo Malam Sani, mutumin Jada ne shima kasuwancin siyar da hatsi ne ya kawo sa Jimeta ba jimawa suka yi aure anan kuma cikin Jimeta suke zaune Amma ta fi kowa murna Aminiyarta ta dawo kusa da ita. Haihuwan ta na fari mace ta haifa mai suna iklima shi ne dalilin da ya sa ake kiran ta da Ummin ikki. Fatima ta sha gwargwarmaya kafin ta dawo daidai. Daga lokacin ta tsani duk wani abu da ya shafi sarauta, ta tsani har garin Daura gabaɗaya. A daddafe ta yaye Lamiɗo ta sakar ma Ammah ita kuma da taimakon Baffa ta koma makaranta a zaman ta a gidan Baffa har deperession sai da ya kamata Allah ne ya taimake ta tana da sauran kwana a gaba, zuciya da takaicin abin da aka yi mata ya sa ta ji tana so ta tashi daga Fatima yar ƙauyen Mubi zuwa Fatima mai ilimi wacce za ta nemi ilimi domin gobenta ta yi kyau. Daga SS1 ta fara karatu sannan tana zuwa lesson haka saboda taimakon kanta tunda daga sama ta faro karatun kamar ba za ta iya ba domin ta sha wahala kafin ta fara ganewa ko za ta sare sai ta ba ma kanta ƙwarin gwiwa ta cigaba. Ta zana jarabawa kuma ta ci sai ga ta da taimakon Baffa ta samu gurbi a Federal Collage of Education Yola Jimeta. Saboda ma ta yi karatun a cikin makaranta take zama sai bayan wata ɗaya take zuwa ganin su Baffa Lamiɗo ko tun da ta yaye shi ta sakar ma Ammah ta ce ta bar mata shi halak makal a matsayin ɗan ta. Shikenan ta koma kamar ba ita ta haife shi ba shi ma yadda ba ta ta kansa shima Ammah ya sani a matsayin uwa tun yana ƙarami. Fatima ta mayar da hankalinta a kan karatunta da taimakon Baffa. Bayan ta gama NCE ba ta zauna ba ta nemi gurbi a jami'ar Maddibo Adama University, tun a lokacin tana Federal University of Tecnology. Shima saboda nisa a garin Girai jami'ar take can take zama a hostel sai ta samu hutu take zuwa gida kuma tana karantar Biology ne. Fatima ta saka kanta da cewa za ta iya ta yi dakiya ta yi naci kuma Allah ya taimaketa ta cika burin ta. **** SHEKARU TALATIN DA SUKA SHUƊE A BAYA. Bayan shuɗewar wasu shekaru Talatin a baya Rayuwa ta daidaita. Tunda Baffa harkokinsa sun buɗe ya yi arziƙi da kasuwancin sa na siyan tsoffin ƙarafa yana siyarwa sannan shekaru goma a baya ya fara haɗawa da siyar da motoci tun haɗuwarsa da Alhaji Isa Ɗan marke bazamanfare mai siyar da motoci wanda ke da kamfani a garin Kaduna sun daɗe suna kasuwanci kuma dalilin shi Baffa ya samu alheri masu yawan gaske. Baffa ya gina katon gida a anguwan Zone 3 in da iyalansa ke zaune har yanzu. Shima Alhaji Isa Ɗanmarke a dalilin Baffa ya samu matar aure. Ya auri Fatima tana da shekaru talatin da biyar mai kwalin karatun Degree da masters a lokacin. Matarsa ta rasu kuma ba su taɓa haihuwa ba yana ganin Fatima a gidan Baffa ya ce ya yi mata Baffan kuma ya bashi domin a lokacin shi ke da alhakin aurar da Fatima da duk itama tana da haƙƙi tun da ita bazawara ce. Fatima ta auri Alhaji Isa ta kuma tare a gidan shi dake Kaduna. Suna kuma yin auran ta ɗora karatun ta na PHD a jami'ar Amadu Bello dake Zaria wato ABU ZARIA. Tana cikin kuma karatun ne ta samu ciki ta haifi yarta mace Islam(Fatima) bayan ita sai da ta gama karatu da shekaru biyar sannan ta haifi Faruk(Umar). Tun bayan barowan ta Daura ba ta sake komawa ba amma su mutanen Dauran sun neme ta daga baya saboda Lamiɗo. Baffa kuma ya tara zuru'a sai son barka. Hamma Jibo ne babba wanda ya yi karatu har matakin Master mazaunin Abuja da iyalansa shekarunsa na haihuwa 40. Sunan matarsa Nauwara da yaran su huɗu, Saudat, Jamila(Amma) sai yan biyu Hassan da Hussaini sai Isma'il. Sai Hamma Mustapha shima ya yi karatun boko har matakin Degree yana garin Gombe tare da iyalansa yana aiki da hukumar ruwa(Water resourses) shekarunsa na haihuwa 38. Sunan matarsa Aisha(Momi) ya'yansu uku Fatima(Mahma) Zainab sai Hadi(Baffa). Sai Hamma Kabiru shima ya yi degree a kan medical lap, yana aiki da asibitin Federal hospital Jalingo. Shi kuma shi da Lamiɗo suna cikin shekaru na 35 ne. Sunan matarsa Safinatu yaran su biyu, Muhammad da Yusra, kuma a can Jalingon yake zaune da iyalansa. Sai Hamma Abdulrrahman lauya ne mai zaman kansa yana zaune  a garin Jimeta shekarunsa 33. Matarsa Ummu Sulaim da ya'yan shi biyu duka mata. Mariya da Jamila(Mimi) sai Hamma Abdullahi tare suke kasuwanci da Baffa shima ya yi karatun Boko ya karanta harkan kasuwanci shekarunsa 31 babu nisan haihuwa tsakanin a duka yaran Amma. shima yana zaune da matarsa Suwaiba da ɗansa ɗaya Umar(Maddibo) sai Hamma Abdulrahim shi kuma yana can ƙasar singphore yana karatun likitan ci, ɗan kimanin shekaru 29. Wanda Hamma Lamiɗo ya ɗauki nauyin karatun na shi. Sai Hamma Saddam wanda ke karatun mass com a jami'ar ATBU BAUCHI yana aji uku, tsakanin Saddam da Auta Ummu wata ashirin ne. Shi yana cikin shekaru na 27 ne. Sai Auta Ummu Salma wacce iyakar ta sakandiri ta tsaya aka yi mata aure. Zuwa lokacin rayuwa duk ta yi kyau, a can Mubi ma Baffa Hamza ya rasu haka ma Umma(Asma'u) a gidan su Baffa yanzu Baffa Umaru ne Babba duka kuma a gidan su ke zaune da ƴa'ƴansu da iyalansu, su dai ba su bar Mubi ba suna nan a cikin ta amma dai Baffa da iyalan shi suna zuwa Mubi akai akai in an yi wani abu Amma ma tana da zuru'a a can tun da su Umma Balki sun tara iyalai masu yawa a can Mubi ɗin. A nan kuma ita da Ummin ikki ne suka tara iyalai, sai son barka Ummin ikki ta aurar da matan ta huɗu, iklima, Saratu, mai sunan Amma Jamila, sai Binta sannan kaltume da Baɗɗo(Aisha) su ne yanzu a gabanta ita Allah bai ba ta namiji ba amma Mallam Sani ya kara aure amaryan ta haifa masa maza uku. Amintansu da Ammah sai ma abin da ya yi gaba sai dai duk amintan dake tsakanin Ammah da Ummin ikki Baffa da Mallam Sani ba sa Aminta sosai amma suna da kyakyawan alaqa da juna sai dai ba kamar Aminta da shakuwa irin na matan su ba Abin da Mami(Fatima) ba ta sani ba shi ne tun Lamiɗo na ƙarami Mahaifin shi Maimartaba Sarkin Daura Alhaji Dr Muhammad Nasiru na tura kudaɗe duk wata domin hidimarsa a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba sannan duk in da Baffa suke yana sakawa ana bibiyan su Da shawaran ƙanwarsa mai bi masa Hajiya Zaliha(Magajiyar Sanda Mata) kuma ita ke auran Madakin masarautan Zazzau, tun faruwan lamarin ita ce kawai ta nuna rashin kyautawar Fulanin kan abin da aka yi ma Fatima. Amma sauran duk sun goyo bayan Fulani a wancan lokacin. Ita ce ta bashi shawaran ya nemi in da Fatima take domin gudan jinin dake tsakanin su, ya sani Fulani ba yadda za ta yi domin Ubangiji mai haɗawa ya riga ya haɗa danganta a tsakanin shi da Fatima ta sanadiyar Lamiɗo. Tunda ga haihuwar Lamiɗo har girman shi da komai da komai Marmartaba yana da labarin komai sannan shi ya saka a ka samo masa lambar asusun bakin Baffa yana tura masa kuɗi, a saƙon da ya taɓa tura masa na farko ne ya yi bayanin kan shi sannan ya roƙi Baffa da cewa kar ya ce ba zai karɓi kuɗin ba, har abada ba zai taba karɓan Lamido daga hannun su ba, shi ko Baffa daman ko bai roƙe sa ba, ina shi ina ma yar ma da sarki kuɗi kuma ko ya ce zai karɓi Lamiɗo ai ba shi da ta cewa ba zai iya ja da masu mulki ba, shi ya daɗe da yafe komai da man sanadin Fatima ne, yanzu kuma Fatima ta samu komai na rayuwa kuma yawancin mutanen da suka yi ruwa da tsaki a kan auran ba sa raye. Hatta mariƙan Fatima na Daura sun rasu da daɗewa amma dai har yau akwai wasu daga cikin ahalin Gwaggo a garin Daura Baffa dai kan tura musu saƙo amma shima ba zuwa yake yi kamar yadda Fatima ta tsani garin haka shima ya ji ya fita kan shi gabaɗaya. Mami ba ta san Maimartaba ke ɗauke da nauyin Lamido ba sai da ya tafi ƙasar Malesia karatu a lokacin Baffa ya sanar da ita komai saboda ta san ba shi da kuɗin da zai kai Lamiɗo waje domin ya yi karatu kuma kaf cikin yaran ba a kai kowa ba sai shi. Ta sha kuka tana faɗin ita har abada ba ta da alaqa da waɗanan mutanen Baffa ya nuna mata ita ko ke da alaqa da su, tunda akwai jininsu a tare da ita. Da ta yi bore Ammah ta ce ba ruwanta tunda daman tuntuni ta ce ta bar mata ɗan, jin haka yasa ta cire bakin ta akan Lamiɗo da man kuma ba saka bakin take yi ba. Rayuwa ta gangara har Lamiɗo ya gama karatun shi na degree da Master akan Nautical Sceinces a jami'ar Akademi laut Malaysia. Ya samu ƙwarewa da horo kan tuƙin jirgin ruwa kuma lokacin ne Fulanin Daura ta buƙaci Jikan da ta juya ma baya tun a farko. Saboda duka ƴa'yan sarakunan da ta aura ma Maimartaba ba su ba ta jika namiji ba sai mata ita kuma tana so zuru'an ta su ƙare a zamowa sarakuna ne shi ya sa ta ɓullo da maganar nemo Fatima da abin da ta haifa shi kuma da man Maimartaba yana neman dama ne sai ga Fulanin Daura har falon Ammah tare da manyan ƴa'ƴanta mata ta duka tana ba ma su Baffa haƙuri, Baffa ya ce shi ya daɗe da yafewa Fatima za ta roƙa gafara. Mami kuwa ta ƙi yafe musu har sai da Fulanin Daura ta je har falonta a gidan mijinta dake garin Kaduna. Dalilin mijinta Alhaji isa ya sa ta yafe ma Fulani da ɗanta amma game da Lamiɗo ta ce ba ruwanta a ciki ta nemi Baffa da Ammah sune iyayen Lamido. To shima dai Lamiɗon  ya yi taurin kai duk da daman ya san ba Baffa da Ammah ba ne suka haife shi ba. Maimartaba na zuwa Jimeta a ɓoye Baffa ya kai masa Lamiɗo ya gansa sannan da yana Malaysia yana zuwa ganinsa tare da Hajiya Zaliha(Mahma) A haka ne sabo ya shiga tsakanin su kuma Maimartaba da kansa ya zaunar da Lamiɗo ya bashi labarin duk abin da ya faru shi ya sa ya fi jin haushin Fulanin Daura. Bai amince da komawa Daura ba sai da Ammah ta saka baki sannan ya koma Daura da zama a cikin Masaurata. Gari ya ɗauka domin waɗanda suka san da auran aminttun sarkin a wancan zamanin duk sun rasu sai mutum ɗaya ne ya rage a lokacin shi ne ya ba da shaidan Lamiɗo ɗan Masaurata ne balle ma kamanninsa da kowa ya gani ba sai ya yi magana ba, kamar Maimartaba yana tashen ƙuruciyarsa. Bai daɗe da komawa Daura ba ya kama aiki gadan gadan da kamfanin Nigerian Port Authority a matsayin matuƙin jirginsu Captain bayan ya karɓi licence ɗinsa a matsayin pilot matuƙin jirgin ruwa By Nigerian Maritime Administration and Safety Agency (NIMASA) Sai ya zamana baya samun zama sosai amma duk salla a Daura yake yin ta saboda za a gudanar da hawan salla tare da shi, kuma uwa uba yana da wasu yan'uwan da suke uba ɗaya duk da ba su tashi a gida ɗaya ba amma dai yana son su tunda su ɗin jininsa ne. Sai da ya auri ƴar Sarkin Kano sannan aka na ɗa shi Yariman Daura mai jiran gado duk da abubuwan sarauta ba su dame shi ba amma Muhammad Lamiɗo mutum ne nagari mai kirki kamar mahaifinsa. In dai ya na Daura talakawa da matasa na cikin alheri yana da alheri sannan ga ƙokarin samo ma matasa ayyukan yi. Duk da shi miskili ne mara sakewa amma kuma mutanen garin Daura suna son shi saboda yana da kyautawa. In dai ya zo Daura to tare da shi ake zaman Fada a dole sai an koya masa abubuwan da suka shafi sarauta, abin da ba su sani ba shi bai taɓa sha'awar Sarauta duk da ko bai faɗa ba mutane da dama in suka gan shi da yanayin shi sai sun ce yana da jinin sarauta a jikin shi. Sannan in dai ya zauna da Maimartaba to ba su da hira sai hiran sarauta da tarihin masaurata da sarakunan da suka gabata. Haka ma Hajiya Zaliha ko da wani lokaci suka haɗu girman matsayin shi take nuna masa, da lissafinta na cewa wata rana shi ne a kan ƙaragan da mahaifinsa ke zaune yanzu. Shi sai dai ya ji su kawai kwata-kwata baya son mulki kuma ba zai taɓa sha'awa ba, saboda mulki hayaniya ne da damuwa tare da nauyi shi kuma ba ya so. Hajiya Zaliha(Mahma) tana son Lamiɗo sosai saboda ba ta taɓa haihuwa ba shima yana son ta ko domin yadda take ji da shi ya sakata cikin jerin mata masu muhimmanci a rayuwarsa. Fulanin Daura da ta tsufa yanzu ba ta da abin so kamar Lamiɗo tana ji da shi kamar tsoka ɗaya a miya. Shi ko ba ya wani ta kanta amma dai yana zuwa wajenta ya zauna na wani lokaci in dai ya zo garin. Itama in ya je wajenta haka za ta zaunar da shi tana ta yi masa hira da labarin Masarautar Daura har ya gaji da ji ya haddace. Da yana jin haushin ta akan abin da ya faru amma daga baya ya daina tun da ita kanta Mami ta na can tana wata sabuwar rayuwar da shi da Ahalin na shi duk ba sa gabanta shi ya sa ya bar komai ya wuce ya kuma rumgumi ahalinsa. Ba a sauya ma tuwo suna duk a je a dawo abin faharin shi da asalin shi garin Daura ne. Dalilin abin da Fulani Daura ta aikata ne daga baya Fargar Jaji ya kamata ta yi nadama. Saboda haka ya sa duk wani abu da zai faru a Masarautan Daura za a sanar ma da Ammah da Baffa saboda Lamiɗo zumunci mai karfi ne a tsakanin Ammah da Gimbiya Shahida uwar gidan Maimartaba da man duka sauran matan na shi. Sannan Fulanin Daura yadda ta dauki Lamiɗo da muhimmanci haka ta dauƙi Ammah da Baffa. Mami ce tun da ta ce ba ta da alaqa da su haka ɗin take ba ta ma nuna ma ita ta haifi Lamiɗo ballanta wani abu ya sa a sako ta a ciki. Shima kuma ba ya taɓa nuna Mami a matsayin mahaifiyarsa Ammah ce uwar sa har gaban abada. Lamiɗo kawai suka sani da marikan shi da suke tamkar iyayen shi, shima Lamiɗon ba ya ɗaukan kowa a matsayin iyayen shi sai Ammah da Baffa Mami dai kawai sunan ta uwa ne amma babu shaƙuwar ɗa da uwa a tsakanin su. Dalilin Lamiɗo har Hajji Masarauta ta kai Ammah da Baffa suka je suka sauke farali. *** Ummu Salma ta kasance a wajen Ammah da Baffa a matsayin yar Auta. Ta taso cikin zaratan yayyen ta maza bakwai ko na ce takwas ga Lamiɗo sannan ita mace, shi ya sa in dai ana maganar gata sai dai a yi kwataance da Ummu Salma.   Tun tasowar Ummu ta tsani karatun boko, domin kanta gaskiya ba ya ja, kusan na kusa da na ƙarshe take ɗaukowa a makaranta. Duk gori da zagin da su Hamma Kabiru ke yi mata bai sa ta gyara ba. Kuma makaranta mai tsada take yi ta Ahmadu Ribaɗo Collage a garin Yola. Amma sai a saran kuɗi ake yi kwaƙwalwar Ummi ba ta fahimtar komai har gwara ma bangaren islamiya shi ba laifi amma na bokon nan ne sai a hankali. Ita kawai karatun boko na wahalar da ita ne, duk ko yadda ba ta iya shan inuwa ɗaya da su Hamma Kabiru a cewar su daƙikiya ce ita kar  Hamma Lamiɗo  ya ji labari ita tun zaman shi a gidan su jininsu bai taɓa haɗuwa ba, wata maganar arziƙi ba ta taɓa haɗa su ba shi ba ya magana ma. In ka gan shi yana mgana to da Ammah ne ko Hamma Kabiru, tun tana yarinya ta san shi ba ɗan Ammah da Baffa ba ne saboda su suna kama da juna amma shi kamininsa na dabam ne, duk da ba ta son shi amma kuma akwai shakuwa a tsakaninta da mahaifiyar shi Mami, wacce ita ta yi renon ta bayan Ammah ta haifeta kafin auranta sannan bayan ta yi aure tana yawan zuwa Kaduna gidan Mami ta yi hutu, Mami mace ce mai fara'a sannan ita da mijinta suna ji da ita in suka je kasashen waje haka Mami za ta ciko mata jaka cike da kayan sawa na alfarma sai wanda ya gani. Ta sha zama ta yi ta mamakin yadda Mami ta iya haihuwan Hamma Lamiɗo ita ba ta ga ta in da ma suka haɗu ba, shi dabam ita dabam ita mai fara'a ce mai kirki da son Jama'a saɓanin Lamiɗo da ba shi da fara'a ba shi da son mutane sannan ba shi da kyakyawan mu'amala. Ummu Salma ta taso ta ga Aminci tsakanin Amma da Ummin ikki shi ya sa itama Aminta ya haɗa ta da Aisha(Baɗɗo) a yayin da makaranta ya haɗa ta da Shamsiya(Bestie) su suna da son karatu kuma suna ganewa ba kamar ita ba tun da kuma ta fahimci ba ta gane karatu ta ce ba za ta ci a karatun boko ba, daga lokacin ta saka ma kanta tunanin daga sakandiri ba za ta cigaba da karatu ba. Kuma haka aka yi ba yadda ba a yi ba amma Ummu Salma ta ce ta gama Baffa kuma da Ammah suka goya mata baya. Abu ɗaya Ummu ta fi mayar da hankali shi ne girken-girken zamani, ta bakin Hamma Kabiru ya ce shi kaɗai take ganewa. Bayan ta gama sakandiri ta je Kaduna ta yi wattani huɗu a wajen Mami saboda tsangwaman su Hamma Kabiru akan sai ta cigaba da makaranta tun ballanta ganin kawayenta Baɗɗo da Shamsiya sun cigaba. A can kaduna ta yi ta shiga catering School tana samun ƙwarewa  bayan ta dawo Jimeta ma ba ta zauna ba yayyenta sun gaji da magana sun ƙyale ta tun da Baffa yace boko ba dole ba ne, shi bai yi ba Ammah ma ba ta yi ba amma ba su mutu ba sun rayu saboda haka a bar Auta ta sarara. Kadunan ma da ta gudo saboda Mami ta fara zaunar da ita tana kwatance a kanta na amfanin karatu tunda ta ji haka tace za ta koma gida saboda Mami za ta iya jan Ra'ayin ta in kuma hakan ya faru ko ta shiga ba za ta iya ba gwara maganin ayi kar a fara. Sai da ta yi zaman shekaru uku a gida ba makaranta ba ta da aiki sai girke girken zamani a gida duk abin da ta koya sai ta gwada shi tun ballantana abubuwan da take gani a waya tunda Mami ta siya mata waya Samsumg babba ta zamani, ko da yaushe tana cikin kwabin fulawa ita ce Cake ita ce donot wani abun ta yi ya yi daɗi wani kuma ya lalace Amma ta yi ta masifa Baffa ne mai supporting ɗin ta. Ummu Salma Bata taɓa tunanin za ta haɗu da Habib ba sai ga shi Allah ya haɗa su, wata rana ta dawo daga gidan su Baɗɗo ya biyo ta. Duk da a ganin farko ta ji ya yi mata ba ta ɗauka soyayyar da ya nema a wajenta zai kai su ga aure ba sai ga shi komai ya faru cikin lokaci. Ummu Salma da Habib sun yi soyayya kamar su lashe juna kafin aure ya nuna mata duk duniya bai so wata mace sama da ita ba, yayyenta suka yi ta mganganun cewa bai kamata a yi mata aure a lokacin ba, amma Baffa ya ce tunda ta samu miji kuma ya bincika yaron nagari ne zai aurar da Ummu sun yi adawa sosai amma kuma sun haƙura daga karshe. Cikin wattani biyar aka yi auran Ummu Salma da Habib auran ya zama abin kwatance kowa na ganin Ummu ta gama yin dace, ko bayan auran Habib ya nuna ma Duniya Ummu Salma ce duniyarsa, zaman lafiya da soyayya da ƙauna shi ya rike su a cikin wattani takwas ɗin da suka yi da aure. Duk masu adawan auren ta sun haƙura ganin tana zaune lafiya da mijinta. Ummu Salma ta ɗauka ta gama dacewa. Ta ɗauka bayan ita da wahala a samu mace irin ta a cikin tsara. Sai ga shi cikin wattani uku Habib ya yi ma rayuwarta juyin waina daga sama ta koma kasa. Cikin wattani tara zuwa goma da auran su ya yi ma rayuwarta katon taɓon da har ta koma ga Allah ba za ta manta ba. *littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗanan lambobin kamar haka.* 09069067488. 08032773332. *Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.* *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *12* Hamma Abdullahi ya ɗauko  Ummin ikki a mazaunin gaba na motarsa sai Baɗɗo da Ummu dake zaune a gidan baya akan hanyar su ta zuwa gidan Baffa. Baɗɗo ne ke ta kuka saboda in ta kalli Ummu sai ta ji rauni ya dabaibaye ta, ita ma Ummin ikki hawayen take yi tana sake rantsuwan ba za su yafe ba sai Allah ya yi ma Ummu sakayya akan tozarcin da Habib ya yi mata. Hamma Abdullahi ko baya magana tuƙinsa kawai yake yi amma in da za a tona zuciyarsa da wataƙila an fahimci halin baƙincikin da yake ciki, takardan sakin tana cikin aljihun jallabiyan jikinsa har wani ɗaci yake ji a ran shi na tozarcin kalaman Habib yanzu ya ya Baffa da Amma za su ji? Ummu ma ba a maganar ta, tana zaune kawai ta ƙura ma gabanta idanuwana sai ta daɗe ba ta kyafta idanuwana ba kamar wacce ta zama gunki ba ta kuka ba ta motsi sannan babu hawaye sai dai ido kawai yana kallonta, ta cikin madubin motarsa na gaba gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi kamar an masa wanka da ruwan sanyi, addu'a kawai yake yi mata Allah ya ba ta ikon cin wannan jarabawan domin jarabawan mai zafi ne sai wanda ubangiji ya so zai iya tsallakewa. Har suka isa gidan Baffa dake Zone 3 suna cikin wannan yanayin har cikin haraba Hamma Abdullahi ya shiga da motar Baɗɗo ta kama Ummu ita da Ummin ikki suka shiga da ita cikin gida yayin da Hamma Abdullahi ya buɗe boot ya kwaso akwatin Ummun guda huɗu ya bi bayan su da shi. Amma na zaune a falonta tun bayan fitowarta daga wajen Baffa ba ta koma ba, ba ta so ya fahimci tana cikin gigita shima kamar ya sani sai ya bata lokaci tunda suka gama waya da Aminiya take zaune cikin mutuwar jiki da na zuciya na tsawon lokaci kafin ta ji sallama a tsakar gida zumbur ta miƙe jikinta ba in da ba ya rawa ɗago labulen da aka yi ne yasa Amma ta yi saurin komawa ta zauna tana ɗan daidaita yanayin ta. Lokacin da suka shigo da Ummu a riƙe kallo ɗaya Amma ta yi mata ta ji ta sare, kafafunta sun yi mata nauyi da ta kasa ma miƙewa Ummu ce ta koma haka! Idanuwa sun kumbura fuskarta ta yi wani irin jajir, tana zaune kawai tana kallon su, suka zaunar da ita a saman kujera Baɗɗo ta zauna a gefenta ta jawo ta a gefen kafaɗanta tana ɗan tapping bayanta alamun lallashi, duk in da aka bi da ita can take bi kamar wata doluwa ko yarinya ƙarama. Ummin ikki ta ƙarisa kusa da Amma ta zauna tana faɗin" Aminiya yau mun tashi cikin jarabawar Ubangiji." Amma ta kalleta kafin ta ɗan motsa bakinta a hankali tana faɗin" Allah ya sa hakan ya zame mana alheri gabaɗaya" Ummu ikki ta amsa da Amin kafin ta fara goge ƙwalla tana cigaba da faɗin" Wannan yaro ya cuce mu. Da ikon Allah sai Allah ya saka mana." Ta faɗa tana kallon Ummu har a lokacin kawai waje ɗaya take kallo ko kiftawa babu, kafin ta sake cewa wani abu Hamma Abdullahi ya yi sallama ya shigo cikin gida sun amsa sannan ya shigo falon Ammah, sanda suka taho da su Ummin ikki Hamma Jibo ne ya kira wayarsa shi ya sa ya ɗan dakata suka yi magana ya sanar da shi ya kawo su gida yanzu. Akwatin hannunsa ya jera anan tsakiyar falon Ammah ko zama bai yi ba ya kalli Ummu na wani lokaci kafin ya ɗan girgiza kansa. "Ina kwana Ammah." Ya faɗa cikin sanyin murya. "Lafiya lau Baba ya iyalan naka? Ta amsa masa amma ba ta kalle shi ba kanta na ƙasa ba ta so shima ya fahimci halin da take ciki, ko ba ta fito ta nuna ba ko ta ɓoye Ammah fa uwa ce ga Ummu Salma yadda lamarin nan zai daki kowa barin ita ne. "Suna lafiya." Ya faɗa sai kuma ya yi shuru, Ummin ikki na ta sharan ƙwalla Baɗɗo ko hawaye ne wasu na zuba wasu na sake tunkuɗowa. "Ba komai in sha Allah zai wuce." Hamma Abdullahi ya faɗa domin a lokacin shima ya rasa kalaman da zai faɗi falon ya yi shuru kamar mutuwa ta gifta tun ballanta shessheƙan kukan Baɗɗo da na Ummin ikki. Ummu dai ba ta kuka da man an ce wani baƙin ciki in ka yi kukan daga baya in kukan ya ɗauke shike nan sai dai zuciya ta dinga ƙuna da raɗaɗi to hakan ce take faruwa da Ummu tunani take yi kamar ba gaskiya ba ne abin da ke faruwa gani take yi kamar komai a mafarki ne in ta farka za ta ganta a cikin ɗakin auren ta, tare da Habib amma ina duk lokacin da ta kifta idanuwanta a falon Ammah take sake ganin ta. "Ammah Baffa fa? Ya faɗa ganin Ammah ta yi shuru kanta na kallon ƙasa. "Yana cikin ɗakin sa." Ammah ta amsa masa cikin ajiyar zuciya. Ya kama hanyar barin falon ne sai ga Baffa ya shigo da sallama daidai lokacin da Hamma Abdullahi ya ɗaga labulen falon Ammah sai ya koma da baya ya ba ma Baffa waje domin ya shigo. Baffa ya shigo har falon Ammah ya yi tsaye kawai yana kallon Ummu Salma sanye yake da manyan kaya tun da ya saka ne zai je masallaci da asuba. Tun ɗazu ya ji shigowarsu amma ya kasa tashi ne, bai san adadin hawayen da ya share a ciki kafin ya fito ba. Bai san a wani hali zai ga Ummu ba! Abin da ya faru da ƙanwarsa Fatima ya dawo masa sabo, shi kaɗai ya san dararan da ya ɓata idanuwan shi biyu yana kukan tausayin Fatima tausayin jarabawan rayuwan da ta faɗa sai ga shi kwatan kwacin haka ya sake faruwa da gudan jininsa Ummu Salma, amma bai yi butulci ba sai ya yi ma Allah godiya domin ba wai ba ya son bayin shi ba ne don ya sake jarabtansu, ya yi haka ne domin ya sake jaraba imaninsu, yana fata da tunanin in Habib ya zama mafarin Ummu Allah ya kawo mata wanda zai wanke mata duk wani dattin zuciya da Habib ya sanya mata.   Ko da yake tsaye a gaban ta, ba ta nuna alamun ta san ma yana wajen ba, kawai gabanta take kallo babu ko ƙyaftawa. Falon ya sake yin shuru kamar ba kowa a ciki Baffa ya duƙa a gaban Ummu yana kallon ta amma ita ba shi take kallo ba kawai gabanta ta ƙura ma idanuwa ba ta ko motsi daga in da take zaune Baɗɗo na rumgume da ita. "Ummu Salma." Baffa ya kira sunan ta cikin kulawa na musamman. Shuru ita ba ta amsa ba sannan ba ta kalle shi ba, ya sake kiranta a karo na biyu nan ma ba ta ɗago ta kalle shi ba sannan ba ta amsa ba. "Ummu Salma." Shuru falon ya sake ɗauka kowa hankalin shi na wajen Ummu cikin tausayi. "Kalle ni nan Ummu Salma." Baffa ya sake faɗa lokaci ɗaya yana riƙo hannunta guda ɗaya, abin mamaki haka ya riƙe hannunta da ya ji sa ya yi sanyi sosai amma Ummu ta kasa iya rike Baffa sai ta ji kamar duka kasusuwan hannun nata ba sa aiki, daƙyar ta iya ɗago idanuwanta ta kalli Baffa. ta ƙura masa ido  ba ko kiftawa tana ta kallon shi. "Ummu Salma." Baffa ya sake kiranta yana mai matse hannunta a cikin na shi hannun, yana ji kamar ya fashe da kukan tausayin ta amma in ya yi kuka ita za ta sare a yanzu a wannan kadamin su ne ƙarfin gwiwanta in suka rushe itama za ta rushe. "Ummu Salma." Ya sake kiran sunan ta, sai ta motsa idanuwanta. Ta kifta ta sake kiftawa sai ga hawaye sharr sun kwaranyo mata a saman kumatun ta. Ganin Baffa kawai da ta yi ya duƙa a gabanta yana kiran sunan ta ya sa hawaye ya kawo mata. Ya Baffa zai ji? Wani hali zuciyarsa take ciki? Ta yi aure ta tafi ita kaɗai sai gashi ta dawo  musu da ciki a cikin jikinta, Ammah ma ta san tana cikin firgici kawai tana ɓoyewa ne. Kuka fa ake yi saboda abin da ya same ta. Ita ko in ba ta ce tana cikin bala'i ba me za ta ce? "Allah ya ba ki dangana Ummu Salma. Sannun kin ji ko? Baffa ya faɗa yana sake jinjina hannanunta dake cikin na shi. Sai ta sake kifta idanuwanta hawaye suka sake zubo mata. "Ai gwara ta yi kukan ko za ta samu sauki. Tunda muka je yarinyar nan ke cikin wannan yanayin." Ummin ikki ta faɗa cikin rawan murya. Baffa ya yi shuru kansa na ƙasa kafin ya saki hannun Ummu ya miƙe yana kallon Baɗɗo na saka tafukan hannayenta tana mai share ma Ummu hawaye. Hamma Abdullahi da tausayin Ummu ya kama shi sai ya ji kamar ya yi mata ƙwalla amma duk da haka idanuwansa sun kala sun yi jajir kamar gwarwashi saboda bacin rai. "Baffa ina kwana? Ya muka ji da wannan al'amarin kuma da muka tashi da shi yau? Ummin ikki ta faɗa tana faman goge ƙwallah. Baffa ya sauke numfashi kafin ya amsa mata. "Lafiya lau. Ya za a yi da sanin Allah komai zai wuce in sha Allahu." Baffa ya faɗa cikin karfin hali kafin ya sake kallonta yana faɗin" Sannu da kokari mun gode sosai Allah ya bar zumunci." "Amin yiwa kai ne Baffa. Allah ya saka ma wannan yarinyar." Kowa ya yi shuru bai ce komai ba, sai da Baffa ya sake jan numfashi kafin ya ce" Ba komai. Komai zai wuce." "In sha Allahu." Hamma Abdullahi ya faɗa cikin damuwa. Ammah dake zaune tun ɗazu ba ta ce komai ba ta ɗago tana kallon Baffa kafin ta ce" Baffa ko za ka kira waliyin Habibun. Watakila su shiga ciki su iya gyara al'amarin." Hamma Abdullahi na shirin magana Ummin ikki ta yi saurin cewa" Tab wani gyara kuma Aminiya? Ammah ta kalleta cikin mamaki ba ita ba har Baffa ma. "Saki uku fa ya yi mata." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un." Baffa ya yi saurin faɗa cikin fitan hayyaci, Ammah kuma sai ta kasa magana amma bakin ta na motsi. "Wallahi tozarcin da yaron nan ya yi mana kenan. Takardan sakin ma tana hannun Baba." Ummin ikki ta gama faɗa tana nuna Hamma Abdullahi shi ko bai yi magana ba ya zaro takardan sakin cikin aljihun wandon sa ya mika ma Baffa, hannunsa na rawa ya karɓa haka fa ya karɓi na Fatima shekaru talatin baya yau ma gashi zai sake karɓan na Ummu Salma, Allah kana gani. Nan take Baffa ya warware takardan ya fara karantawa a bayyana ne, kafin ya gama ya jiƙe da zufa kafafuwansa sun gaza ɗaukansa sai da ya yi ɗan baya ya samu damar jingina da bangon ɗakin Ammah. Ummi ikki sai ta hau kuka tana jero ma Habib addu'an Allah ya sa, Ammah ko wani nauyi ta ji daga ƙasan zuciyan ta. Ganin ta ya yi duhu sai kawai ta dafe kanta ta kasa mgana. "Lalle wannan yaron ba shi da mutumci." Ummin ikki ta faɗa cikin cizon yatsa, Ummu na zaune a yadda take amma abin da Baffa ya karanta ya yi mata fami a gyambon ta wataƙila da Baffa ya san ba ta san abin dake cikin takardan ba da bai karanta kowa ya ji ba, ita ba kanta take ji ba su Baffa ya za su ji? Ita ta riga ta gama Haddace kalaman Habib na baya son ta sannan ta daɗe da fahimtar manufar auran ta zuwa gare shi, su ne suka rage su sani duk kuma yadda ta kai ga yi ma maganar rufa rufa Habib ya fallasa komai. Baffa ya yi shuru kawai da takarda a hannunsa ya kasa magana. Zuciyarsa na wani tafarfasa in da a ce zai iya wallahi da sai ya yi shari'a da Habibu amma kuma ba zai kai shi kara a kotun duniya ba sai dai ya kai shi a kara a kotun Allah. Ya gama cutar su ya cuce Ummu Salma ya gama da rayuwarta ko da sun yi ƙaran shi a gaban hukuma wani ɓata lokaci ne, sannan tonuwar asirin auran Ummu ne ga duniya amma a ƙotun Allah ne kaɗai zai karɓi sakamakon abin da ya aikata. "Baffa bai kamata a bar yaron nan ya tafi haka ba gaskiya." Hamma Abdullahi ya faɗa cikin jin haushi. "In ya saki Ummu ba mu yi jayayya ba, amma maganar ya bar mata ciki ba shi da alaqa da shi bai ta so ba, tunda har shi ya yi cikin nan bai isa ya ce babu ruwan shi ba in ya yi taurin kai ai akwai hukuma sai mu yi ƙaran shi " Ya faɗa yana kallon Baffa da ya yi shuru ya kasa mgana. "Gaskiya magana, ita in mun ƙarbeta tamu ce amma ai cikin na shi ne bai isa ya ce babu ruwan shi ba" Ummin ikki ta faɗa Baffa dai ya yi shuru bai yi magana ba sai kawai ya zura hannu a cikin aljihun wandon sa ya zaro wayarsa. "Wa za ka kira Baffa? Hamma Abdullahi ya tambaya sai kawai Baffa ya ɗaga masa hannu ba tare da ya yi magana ba. Lambar Alhaji Sheriff ya nemo lokaci ɗaya ya kira shi ya kara a kunne tana ta ringing bai ɗaga kiran ba sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga wayar daga can bangaren da sallama, Baffa ya amsa cikin dattakon sa ran shi a ɓace yake shi ya sa bai tsaya ma wata doguwar gaisuwa ba. "Alhaji kana da labarin ɗan ku Habibu ya saki Ummu Salma saki uku? Daga can bangaren Alhaji Sheriff dake zaune a ɗakin da mahaifin Habib ke jinya a cikin gidan su ya miƙe a razane cikin firgici ya ce" Innalillahi yaushe? Wallahi tallahi Alhaji ban sani ba." Ya faɗa cikin tashin hankali to da man ai ba zai sanar da kowa in zai aikata abu mara kyau ba a yanayin maganar Alhaji Sheriff za ka fahimci bai sani ba sannan maganar kuma ta dake shi matuƙa. "To ya sake ta saki uku gata nan ma na saka an je an taho da ita." "Hasbunallahi wa'imal wakel. Alhaji wallahi bamu sani ba. Ba mu da labarin wannan hukuncin da Habibu ya yanke" Alhaji Sheriff ya sake faɗa cikin ɗimuwa da tashin hankali tare da nadamar yadda ya shiga lamarin Habibu, da yau bai shiga ba tuni bai ji kunyar da ya ji yau ba. "Ba komai Alhaji kar ka damu na san da man ba ka sani ba, da man dalilin da ya sa na kira ka wani saƙo zan ba ka zuwa ga Habibu sannan na kafa shaidata akan maganata da kai " Alhaji Sheriff ya ma kasa magana Gwaggo ma ta dawo ɗakin da man ta ɗan fita ne, jin wayar da Alhajin yake yi yana rantsuwan bai sani ba sannan yana ambaton sunan Habibu ya sa ta tsaya ta kasa fita cikin zullumin abin da kuma ya sake faruwa. "A cikin takardan sakin ya rubuta cewa da man ba son Ummu Salma yake yi ba, jikinta ne ya sa ya aurete kuma yanzu tunda ya gama moran abin da ya aura domin shi, shiyasa ya sake ta." Baffa ya faɗa yana jin ƙuna a ƙasan zuciyarsa. "Lailahaillallah." Alhaji Sheriff ya faɗa cikin tsorata da lamarin Habibu. "Sannan kuma ya ce cikin dake jikinta ba ya so, shi ya sa ya ce ta zubar amma ta yi taurin kai. To saboda haka ya bar mata cikin kar wata rana a danganta shi da cikin har abada" "Wannan ne kuma bai isa ba ƙarya yake yi. Tunda har ya amince da cikin na shi ne to ko ya mutu ne sai an danganta shi da wannan cikin." Alhaji Sheriff ya faɗa cikin fushi mai tsanani saboda ya fahimci Habibu ya raina musu wayau yana wasa da hankalin su. "Ai ba a dole Alhaji tun da har ya ce ba ya so to ba wanda zai masa dole akan haka. Tunda har da kansa ya yi ikirarin cewa har abada kar mu danganta shi da cikin jikin Ummu, to nima Alhaji Hadi Baaba a matsayina na mahaifin Ummu Salma na yi alƙawarin ko bayan raina kar Habibu ya kusanto ni ko ya kusanto Ummu Salma ko abin da za ta haifa nan gaba kamar yadda ya haramta ma kansa dangantakar shi da cikin jikinta nima na haramta masa ya danganta kan shi da Ummu Salma ballanta cikin dake jikinta, ni da man uba na ke ga Ummu Salma har abada sannan zan sake zama uban abin da za ta haifa. Har abada bana son na sake ganin fuskar Habibu." Baffa ya gama faɗa yana jin zuciyarsa na tsalle saboda ɓacin rai da baƙin ciki. Alhaji Sheriff daga can bangaren ya ruɗe yana ƙoƙarin magana amma tuni Baffa ya katse wayarsa ya bar shi tsaye cikin  mutuwar jiki da nadama mai yawa. "Alhaji me ya faru ne? Gwaggo ta tambaya cikin tashin hankali. "Habibu ne ya saki matarsa saki uku." Ya ba ta amsa kai tsaye ai sai ta saka salati tana ɗauka tana direwa. "Wai ko Habibu ya fara shaye-Shaye ne? "Babu abin da yake sha, kawai yaron ba shi da mutumci ne." Ya faɗa yana ta neman lambar Habibu amma sai dai ta yi ta ɗif ɗif ba ta shiga. Mahaifin Habibu na kwance yana jin duk abin da ke faruwa ba mgana amma hawaye sun taru a idanuwansa har suna kwaranya ta gefe da gefen idanuwansa. "Uhm wallahi na yi nadamar shiga maganar auren Habibu. Ba ki ji kunyar da na ji ba, yau na ji kunyar Uba, nima fa uba ne ya zan ji in aka yi ma ƴata abin da Habib ya yi ma ta su ƴar? Ya faɗa cikin bayyana takaicinsa lokaci ɗaya yana saka wayarsa cikin aljihun rigansa. "Bai kyauta ba, sam ba daɗi kai innalillahi ga shi saki uku ne ballanta a gyara lamarin." "Ai ko saki ɗaya ne ni da kaina zan ba ma mahaifinta shawaran kar ya mai da ma Habibu ita. Ballanta ya cika gudirinsa tunda da man ya ce ba sonta yake yi ba jikinta ya aura kuma ya gama mora shi ya sa ya sake ta." "Eyye." Gwaggo ta faɗa tana zare ido cikin mamakin Habibu. "Haka mahaifinta ya ce ya rubuta a cikin takardan sakin. Sannan ya ƙara da cewa ba ya son cikin jikinta. Su kuma sun ce tunda ba ya so to su sun karɓa amma ya sani har abada ba shi da hurumin sake danganta kan shi da abin da ke cikin yarinyar." "Ba za a yi haka ba Alhaji." Gwaggo ta faɗa har ta fara hawaye. "An ma yi. Domin hukuncin ya yi mini daidai ko ni ne a matsayin su wallahi tallahi abin da zan yi kenan." "Alhaji k.." "Ba sai kin roke ni ba, ai magana ta kare Aina'u Habibu ya fara komai kuma ya ƙarƙare komai. Saƙon da mahaifinta ya bani ne na sanar miki, in ya zo gidan ki isar masa." Yana gama faɗin haka ya saɓa babbar rigansa zai fice daga ɗakin. "Alhaji  ka tsaya ka ji don Allah.' "Har abada in dai maganar Habibu ne na fita daga cikin ta, amma ba wai ina nufin na fita daga sha'anin ɗan'uwa na ba ne, ba Habibu  ne ya haɗamu ba. Ubangiji ne ya kawo mu duniya a mahaifa ɗaya. Zan shiga sha'anin duka yaran gidan amma ban da Habibu ai ya isa kan shi saboda haka ya je ya yi rayuwarsa Allah ya ba da sa'a." Yana gama faɗin haka ya saka takalminsa ya bar gidan ya bar Gwaggo na hawaye. Haka ma mahaifin shi ke kuka daga in da yake kwance, an ya Habib zai ga daidai a rayuwasa kuwa? *** *ZONE 3.* 2:30PM. Har zuwa lokacin su Ummin ikki na gidan ba su tafi ba, ita Baɗɗo tana tare da Ummu a ɗayan bedroom ɗin dake kusa da na Ammah nan aka sanya mata kayanta. Daman kuma nan ne ɗakin da ta yi ƴanmatancinta kafin ta yi aure, komai yana nan Ammah ba ta kauda shi ba ko baƙi ta yi ba ta cika sauke su anan ba duk wasu littafan makarantan Ummu Salma da tarkacenta duk suna ɗakin Ammah ba ta kauda su ba. Sai ga shi Ummu Salma ta sake dawowa cikin shi a karo na biyu. Ammah kuma suna tare da Ummin ikki tana ta ɗan jan ta da magana saboda ta kwantar mata da hankali, duk da tana nuna mata ba komai. Baffa kuma tun da ya gama waya da Alhaji Sheriff ya shige ɗakin sa Hamma Abdullahi ya bi shi ya ɗan jima a ciki kafin ya fito ya yi musu sallama ya tafi gidan shi. Tun kuma daga lokacin Baffa bai sake fitowa ba sai da zai je sallan azahar. Ammah kuma aikinta ta fita tana yi kamar ma ba ta damu ba, ba wanda ma ya tsaya bi ta kan ba ta damu ba domin an san ta damun. Aminan junan tare suka share gidan suka yi girki shinkafa da wake jallop mai allayahu Ammah ta kai ma Baffa na shi amma ya ce mata ba zai iya ci yanzu ba. Na su Ummu ma yadda ta shiga da shi ciki haka ta koma ta gan shi daga Ummu har Baɗɗon ba su taɓa ba. Ummu Salma na zaune a in da ta yi salla a saman darduman tana nan dai a yadda take. Ba ta magana sai dai kallon waje ɗaya kawai tunda suka zo ko tari ba ta yi ba. Baɗɗo ma ta kasa iya shan ko ruwa ne tana zaune a gefen gado ta yi tagumi kawai tana kallon Ummu cikin tausayawa. Ummin ikki ta zo tana ta yi ma Baɗɗo fada akan cewa ta matsa ma Ummu ta ci abinci. "Ummi tun ɗazu na ke yi mata mgana ba ta kalle ni ba." Baɗɗo ta faɗa idanuwanta na tara ƙwalla. "Ummu daure ki ci abinci kin ji ko? Kar ki manta ba ke kaɗai ba ne ko domin abin da ke cikin ki." Ummu Salma ba ta ko kalleta ba sannan ba ta motsa ba,har tea Ummin ikki ta haɗo mata mai zafi tana ta lallashinta da nasihan cewa ta sha ruwan zafi ya ɗan jiƙa mata maƙoshi kafin ta ci abinci amma kamar da dutse ake magana. "Haba Ummu Salma kar ki ja da hukuncin Allah, Ubangiji yana sane dake, ki yi haƙuri ki sha ruwan zafin nan kin ji ko? Har bakinta ta kai mata kofin amma ta kauda kai ba ta yi magana ba. "Me ya sa kike haka ne Ummu? Ba fa ƙarshen rayuwarki ba ne ya zo domin Habibu ya sake ki. Ki yi haƙuri ki yi hakuri ki daure ko domin abin da ke cikin ki Ummu Salma ki sha wani abun don Allah." Sai a lokacin ta kalli Ummin ikki da luhu luhun idanuwanta. Ƙarshen rayuwanta ne ya zo mana. Me ya rage mata? Habib ya sake ta me kuma ya yi mata sauran ita Ummu Salma a wannan duniyan babu shi. Duk magiya da lallashin Ummin ikki bai saka Ummu ta kurɓi ko ruwan tea ɗin ba Ammah ce da ke ƙofar ɗakin tun ɗazu tana jin duk magiyan da Ummin ke yi mata amma ba ta karɓa ta sha ba. "Aminiya ƙyale ta. ." Haka kawai ta faɗa ta juya ta koma cikin ɗakin ta. In ta ce Habibu zai ga daidai a rayuwarsa ta yi ƙarya tana so Allah ya wulaƙanta rayuwarsa ya farraƙa jin daɗinsa kamar yadda ya farraƙa jin daɗin ɗiyarta mace ƙwara ɗaya da Allah ya bata, ji Ummu Salma cikin kwana ɗaya ta fita kammaninta da Hayyacinta. Ita ko a matsayinta na uwa wani fata ko addu'a za ta yi ma Habibu face na Allah ya ɗanɗana masa ƙwatanƙwacin irin zafi da raɗaɗin da Ummu Salma ta ɗanɗana a dalilin shi, Allah ya haɗa shi da firgici da baƙin ciki irin kwatanƙwacin yadda ya haifar musu tare da duk wani masoyan su. Har Ummin ikki ta shigo ta zauna kusa da ita ba ta sani ba sai da ta yi magana. "Ta ƙi shan ruwan zafin abincin ma haka." "Barta in ta gaji za ta sha ai ba za ta zauna ta mutu ba." Ammah ta faɗa tana cije bakinta saboda ɓacin rai. "Aa Aminiya ko saboda abin da ke tare da ita ya kamata ta ci wani abu. Yanzu haka tun jiya rabon ta da wani abu." "To ba kin faɗa mata ba ta ji ba Aminiya? Ai tafi ki sanin ba ta ita kaɗai ba ce. " Ammah ta sake faɗa har tana girgiza ƙafa, ji take yi kamar ta rufe Ummu da duƙa ko ta huce baƙin cikin ta. Akan wannan ɗan iskan yaron da ya tozarta ta koma haka? Kawai ta yi shuru ne ba ta so ta yi magana ace ba ta tausayin Ummu. Ita a yadda take jin zuciyarta bai kamata Ummu ta sake kuka saboda Habib ya sake ta ba. Godiya ya kamata ta yi ma Ubangijinta domin bai kaddara mata rabon wahala anan gaba ba. Tunda Baffa ya karanta takardan sakin nan da kalaman dake ciki ta ji nan duniya ba wanda ta tsana sama da Habibu ta yi masa addu'an bala'ai kala kala a cikin zuciyarta da fatan ya tozarta kamar yadda ya tozarta su. "Aminiya sai fa haƙuri yanzu sabon reno ne za ki yi Ummu kafin ta warware har ta cire abin a cikin zuciyarta " Ummin ikki ta faɗa sanin halin Aminiyarta ta, ba ta ɗaukan reni da ɓata lokaci akan abu ko kaɗan. "Aminiya." Ammah ta kirata ta amsa tana kallon ta. "Ba zan lalace akan lallashin Ummu Salma ba. Ita ba yarinya ba ce ta san illan yunwa da abin da damuwa ke haifarma gangan jikin ɗan adam." "Ba za a yi haka ba Aminiya." Ummin ikki ta faɗa da sauri, kafin ta ɗora da maganarta Ammah ta miƙe da sauri za ta bar ɗakin Ummin ikki ta riƙo hannunta amma taƙi juyowa saboda kuka take yi ba ta so ta ganta tana kuka. "Ki yi kuka Aminiya ko za ki samu sauƙi na fi kowa sanin ki na san yadda zuciyarki ke ciki a halin yanzu." Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta isa ga Ammah wacce tana ganin ta sai ta juyo ta ɗora kafaɗanta a saman na Ummin ikki ta fashe da kuka. "Me ya sa za ta damu don ya sake ta? Da man bai dace da rayuwarta ba. Tana so ta kashe kanta saboda wanda bai san darajan ta ba? Ko so take yi wani abu ya same ta muma zullumi ya kashe mu a tsaye Aminiya? Amma take faɗa cikin kuka Ummin ikki na bubbuga bayanta alamun lallashi sai da ta yi kukan ta fidda hawaye sannan ta ɗago ta share hawayenta. "Ki kalli yadda Ummu ta koma Aminiya? In ta cigaba da zama a haka wata cutar za ta kama ta." Ammah ta faɗa cikin rawan murya. "Lallashi ba zai sa ta ji ba. Ki yi mata faɗa ne ki zare mata ido in ba haka ba za ta cutar da kanta sannan ta cutar da abin da ke cikin ta." "Zan yi mata, kar ki damu ba abin da zai same ta " Ta faɗa tana kallon Ammah da duk ta yi zuru zuru a yini ɗaya kawai ta faɗa, lamarin nan ya dake ta sosai. "Haka na riƙa yi ma Fatima a wancan lokacin. Tunda duk lallashin Baffa ba ta ji, amma da ta ga na buɗe mata wuta na fara masifa za ta yi shuru ta ɗau abinci tana ci." Ta faɗa tana kallon Ummin ikki, kai ta gyaɗa mata kafin ta ce" Za ta warware sai a hankali Aminiya." Kafin Ammah ta ce wani abu suka ji muryam Saddam ya shigo cikin ƙaraji yana kiran sunan Amma. "Ammah" "Amma kina ina ne? Da sauri  Amma da Ummin ikki suka fito falo, ita Ammah ta ma manta da yana gidan kwata-kwata. "Saddam? Da man kana gidan? Ummin ikki ta faɗa cikin mamakin ganinsa. Bai ko damu da tambayanta ba ya kalle su ita da Ammah yadda suka ƙura masa ido da yanayin Amnma kawai ya sa ya samu tabbacin abin da Hamma Jibo ya faɗa. "Da gaske ne kenan? Ya tambayana yana kallon su. "Me fa? In ji Ammah tana kallon shi. "Yanzu na buɗe data kawai sai ga saƙon Hamma Jibo a Family group namu wai mijin Ummu Salma ya sake ta saki uku." Ammah ta wucesa zuwa kan kujera ta zauna ba tare da ta yi magana ba. "Da gaske ne Saddam kai dai bari " Ummin ikki ta faɗa cikin sanyin murya. Zaro ido ya yi kafin ya ce" Da gaske ne? To ni duk ina ina hakan ta faru ban sani ba, kuma yau ne abin ya faru? Ya tambaya cikin ɗimuwa da mamaki "E yau ne da asuba nan." Ummin ikki ta faɗa kafin ta cigaba da faɗin" To kai kana ina ne duk ba ka ji zuwan mu ba."? "Ummi ina can cikin ɗaki mun gama exams ina biyan bashin barci, tashi na kenan na yi salla sai na ga saƙo a group ina shiga kawai na ga Hamma Jibo na faɗin wai mijin Ummu Salma ya sake ta " Ya gama faɗa yana sake duba wayarsa. Abin da ma yasa ya saurin duba saƙon a group ɗin sai a yi wata uku ba wanda ya yi ko sallama a ciki kwata-kwata group ɗin ba ya active kuma duk suna ciki hatta da  Hamma Lamiɗo, kuma shi da kan shi ya buɗe group ɗin shekaru biyu da suka gabata ya sanya masa suna AMMAH AND BAFFA HAPPINESS. su takwas ɗin su cur ƴa'ƴan Ammah da Baffa suna ciki da Hamma Lamiɗo cikon na tara domin ba wanda ya isa ya cire shi a cikin jerin ƴa'yan Amma da Baffa. Ba su fita ba amma ba mai magana farko farkon ma buɗewa Saddam na raya group ɗin da ɗan turo jumma'at mubarak, ko irin short-short vedio haka na ban dariya kawai ranar Hamma Kabiru ya fito ya yi Viocenote na kusan sakwan hamsin a ciki yana yi ma Saddam faɗa da jan kunnen cewa daman ya buɗe group ɗin ne ya tara su domin ya riƙa turo musu Vedios ɗin ban dariya! Hala yara ne su irin shi ko marasa aikin yi kamarsa! To in dai abin da ya sa ya buɗe group ɗin kenan gwara ya gaggauta cire su ya rufe group ɗin su suna da abin yi. Wannan maganar ta ɗan muzanta Saddam ya ji zafi, tun ballanta yadda Ummu Salma ta kira shi tana masa dariya da ya so ya cire kowa ya rufe group ɗin ne amma sai bai yi haka ba da Hamma Jibo ya kira shi ya lallasheshi da cewa ya san halin Hamma Kabiru da gwasala ya ƙyale shi kawai. Dalilin da ya sa bai rufe ba kenan amma ya kama kan shi, bai sake tura komai a ciki ba, ko addu'an jumma'at mubarak ya daina turawa kuma ba wanda ya yi cigiyarsa tun daga ranar ya san ba su damu da turowan nashi da rashin shi ba, tun daga lokacin sai group ɗin ya yi wata sama da uku ko sallama ba wanda ya yi wasu ma mantawa suke yi da shi, akwai ma waɗanda ba su taɓa magana ba irin su Hamma Lamiɗo, shi wataƙila ma ba lalle ya san an buɗe ba mutumin da sai ka yi masa mgana a chart sai ya yi sama da sati biyu yake dubawa ba kuma lalle ne in ya duba ya baka amsa a lokacin ba sai a lokacin da ya samu dama. Hamma Jibo ne daman ko Hamma Mustapha kan ɗan sanar da wani ƙaruwa ko jaje in ya samu ɗaya daga cikin su, suma ɗin suna dai yi ne kawai saƙon da sai su tura ya yi sama da sati ba wanda ya nuna ma ya gani ballanta ya tanka alhalin akwai waɗanda suka gani ɗin amma su yi magana suna ganin ɓata lokaci ne. Shi ya sa yau yana ganin saƙon ya shiga da sauri sai ya ciro karo da labarin da ya razana shi. "To wai me ta yi masa ya yi mata wannan sakin a lokaci ɗaya? Ya faɗa saboda mamaki shi abin yake ba shi. Ummin ikki ce ke bashi labarin yadda lamarin ya fara har zuwa yau Ammah ba ta yi maagaana. "Kai innalillahi." Ya faɗa yana mai zaro ido. "Wallahi ai yaron nan ya gama cutar mu." Hamma Saddam ya yi shuru kafin ya ce" Ni gabaɗaya ma na rasa abin cewa. Kamar ba zaai aikata ba sumu sumu da shi munafuki.". Shuru ba wanda ya tanka shi. "To yanzu ina ita Ummun? "Tana cikin ɗakin ta." Ummin ikki ta faɗa tana nuna masa ɗakin da hannunta da sauri ya wuce ya shiga a bakin kofa ya tsaya yana kallon Ummu na zaune kawai tana kallon waje ɗaya. Baɗɗo na gefenta ta yi tagumi ɗakin shuru ba ka jin motsin kowa kamar an yi mutuwa. Sai jikinsa ya sake yin sanyi jiki a sanyaye ya ƙariso ɗakin. "Baɗɗo." Ya kira sunan ta cikin sanyin murya. Kallon shi ta yi kafin ta amsa itama a sanyaye. "Naam Hamma Saddam yanzu ka dawo? "Tun jiya fa na dawo" Ya bata amsa yana kallon Ummu da ya ga ba ta ko motsi "Ta ƙame ne? Ya faɗa yana ɗan ware ido. "Ko ta suma ne a zaune? Ya sake faɗa yana ɗan yawo da hannunsa a wajen idanuwanta sai ya ga ta ɗan kifta ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Ummu sorry amma don Allah ki daina damuwa kin ji ko? Shege mara mutumci kawai " Ya faɗa yana kallon ta, kallon shi ta yi da luhu luhun idanuwanta na wani lokaci kafin ta ɗauke ba tare da ta yi magana ba "Ummu" Shuru ba ta amsa shi ba ya saka hannu ya dafa kafaɗanta nan ma ba ta sake kallon shi ba, Baɗɗo ya kalla cikin mamaki da sauri ta ce" Tunda muka je muka ɗaukota haka take ba ta yi kuma magana ba." Hamma Saddam ya ware ido kafin ya ce" Kar fa shock ya kamata zuciyarta ta buga ba a sani ba." Baɗɗo ta yi shuru tana kallon shi, hannun Ummu ya kama ya riƙe yana kallon ta. "Ke Ummu kina jina? Ya faɗa lokaci ɗaya yana saka ɗayan hannunsa ya ɗan taɓa kumatunta sai ta runtse idanuwanta na wani lokaci kafin ta buɗe sai ga hawaye sharr, ajiyar zuciya ya saki kafin ya ce" Gwara dai a dinga ganin alamu zuciyarta na tafiya." Ya faɗa yana share mata hawaye da gefen jallabiyan jikinsa "Ki daina kuka kin ji, a matsayina na yayanki sai na rama miki abin da ya yi miki." Yake faɗa yana sake share mata hawaye. "Shi ne zai ce ba ya son ki? Kaf duniyan nan akwai wacce ta kai ki kyau ne da zati? Sai da ta kalle shi, hawaye suka sake kwaranyo mata. Duk da kyan da zatin shi Habib ba shi yake so ba jikinta yake so kuma tunda ya gama amfana shi ya sa ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda kamar yadda ya faɗa sannan ya jaddada mata. "Wallahi sai mun rama miki. Mugu kawai." Ya sake faɗa yana kallon ta yana yi ne domin ta ji sanyi a zuciyarta bai san a lokacin ma jin wani irin zafi take yi yana ta so mata ba ta so ana zagin shi domin har yanzu tana jin soyayyarsa a cikin zuciyarta "Ta ci abinci? Ya faɗa yana kallon kulan abincin dake gefe. Da kai Baɗɗo ta amsa masa da Aa ba ta ci ba "To ya za a yi ta zauna da yunwa" Ya faɗa yana jawo abincin. "Ta ƙi ci Ummi har tea ta haɗo mata ta zauna tana lallashin ta amma ba ta karɓa ba. Ga shi kuma ina jin tun jiya ba ta ci komai ba." Ta faɗa hawaye suna kawo mata, Hamma Saddam ya kalle ta kafin ya ce" To ke ma kina kuka ita wa zai lallashe ta? "Wallahi ina tausayin Ummu. Ina tausayin halin da za ta shiga." Baɗɗo ta faɗa tana kecewa da kuka, shi ma ba domin yana namiji da shima ya kece da kukan tausayin Ummu amma shi namiji ne ya kamata ya daure. "To ki yi haƙuri ki daina kuka. Ke za ki zama ƙarfin gwiwanta." Shuru ta yi tana cigaba da kukanta mai sauti yayin da na Ummu sai dai kawai zuɓar ƙwalla. "Ummu ya kamata ki ci wani abu." Ya faɗa yana kallon ta, sai ta kalle shi amma ba ta yi magana ba. "In haɗo miki tea ɗin? Shuru ta yi masa amma tana kallon shi. "Kina da juna biyu Ummu kar wani abu ya same ki" Ya faɗa yana sake kallon ta. Sai ta lumshe ido hawaye na kwanranyo mata. "Na kawo miki tea ɗin? Karo na farko ta girgiza masa kai. "Me ya sa Ummu? Za ki zauna ki mutu da yunwa ne. Mai faruwa fa ta faru sai dai mu yi haƙuri kawai.". Ya faɗa cikin sigan lallashi duk dai ta samu ta jiƙa maƙoshin ta. "Na kawo miki? Ya faɗa cikin sanyin murya. Sai ta sake girgiza masa kai a karo na biyu. "Haba mana Ummu." Ya faɗa yana miƙewa tsaye. "Bari na je na haɗo miki, ki sha ko kaɗan ne." Yana shirin barin ɗakin a karon farko Ummu ta yi magana. "Ba z.. zan sha ba." Ta faɗa cikin dashewar murya. "Ko kaɗan ki sha Ummu" Baɗɗo ta faɗa tana kallon ta. "E ko kaɗan kin ji? Hamma Saddam ya sake faɗa domin a yadda bakin ta ya bushe ya tabbata ma cikin ta a bushe yake. "Na ce ba zan sha ba. Ba zan sha ba don Allah ku ƙyale ni." Ta faɗa lokaci ɗaya tana kecewa da wani irin kukan, muryanta ma baya fita sosai. "Zan mutu, ina ji kamar zan mutu zuciyata ke zafi ciwo take yi.." Haka ta faɗa tana nuna saitin zuciyarta cikin kuka. "Zuciyata na zafi, ji nake yi kamar na kashe kaina." Ta faɗa cikin kuka kafin ta fara buga saitin zuciyanta da hannu tana wani irin kuka da gudu Baɗɗo da Hamma Saddam suka yi kanta suna riƙe ta amma kamar an ƙara mata karfi tana fizge kanta tana kuka tana faɗin su bari ta kashe kanta, hayaniyarsu ya kawo su Ammah ɗakin ganin abin da ke faruwa ya sa ke raunana Ummin ikki ta fara kuka ita kuma Ammah ta fita tsakar gida da sauri domin ta kira Baffa sai suka ci karo da juna "Me ke faruwa ne! Na ji kuka? Ya faɗa cikin tashin hankali. "Ummu ce ke kuka tana faɗin za ta kashe kanta." Ammah ta faɗa cikin rawan murya. "Innalillahi wa'inna alaihirraju'un." Ya faɗa da gudu yana faɗawa falon Ammah. Daidai lokacin da Hamma Abdulrrahman ya shigo tsakar gidan da sallama. Lokacin da ya ga saƙon Hamma Jibo fitowar shi kenan daga wata sharia da ya jagoranta. Shi da man ya san sai an zo wannan matakin. "Ammah" Ya kira sunanta ganin ta cikin wani yanayi. Tana ganin shi ta nufe shi da sauri. "Abdulrrahman." "Ammah" Ya amsa yana kallon ta cikin mamakin ganin yanayin ta. "Ummu Salma ce." Ido kawai ya sakar mata yana kallon ta. "Tana ciki tana kuka wai za ta kashe kan ta." "Za ta kashe kanta? Ya maimaita cikin mamaki. Sai Ammah ta gyaɗa masa kai, goshinta har yana tara zufa saboda damuwa da firgici. "Mu je na ganta. In ta fasa kashe kanta saboda wani banza ta ci ubanta." Ya faɗa yana yin gaba zuwa cikin falon Ammah cikin fushi da fusata. Saboda wani banza sakarai ne za ta zo tana yi ma mutane sakarci in ta fasa kashe kanta ta ci bura uban ta in ji shi Abdulrrahman Hadi Baba, in ba ta kashe kanta ba ta ci uban ta. *littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗannan lambobin kamar haka.* 09069067488. 08032773332. *Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.* *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *13* Ammah ta bi bayan Abdulrrahman da sauri zuwa cikin ɗakin, dukkansu sun dukufa kan Ummu Salma har Baffa shi ne mai yi mata addu'a yana tofa mata, Saddam da Baɗɗo da Ummin ikki sun rirriƙeta tana ta fizge-fizge tana wani gunjin kuka har a lokacin ba ta daina maganganu ba kamar wacce ta fita daga hayyacin ta. "Baffa zuciyata zafi take yi. Baffa ba zan iya rayuwa a haka ba. Ku bar ni na kashe kaina na huta." Haka take faɗa tana rera wani irin kuka wanda ke kassara zuciyar mai sauraranta. Ummin ikki haka take hawaye Baɗɗo har da majina Hamma Saddam ma idanuwansa sun kala saboda tashin hankali Baffa kam har da ƙwalla kwance a idanuwansa. "Ummu ki daina faɗin haka. Ki yi ta maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.." Baffa ya faɗa lokaci ɗaya yana dafe kanta yana karanto mata addu'o'i Fatima kawai yake tunawa da irin wahalan da ta sha kafin ta iya karɓan kaddaranta amma Fatima ba ta taɓa cewa za ta kashe kanta ba. In har aka bar Ummu ita kaɗai wata rana za ta iya yin abin da hankalinta zai gushe ba a sani ba. "Ku sake ta " Suka ji an faɗa daga bayan su. Gabaɗayansu suka juya cikin mamaki sai suka ga Hamma Abdulrrahman tsaye shi da Ammah a bakin ƙofar ɗakin. "Na ce ku sake ta don Allah.". Ya sake faɗa lokaci ɗaya yana shigowa cikin ɗakin sanye yake da suit masu ruwan toka ya matse wuyan sa da tie. Gefen kafaɗansa kuma jakarsa ce ta aiki. "Cewa take yi za ta kashe kanta fa Hamma." Saddam ya faɗa yana kallon yayan na shi cikin mamaki. "To ku saketa ta kashe kan nata mana" Ya faɗa cikin halin ko in kula ba su Baffa ba har Ummun dake fizgewa sai da ta natsu idanuwanta na lumshe sai da ta buɗe su ciike da hawaye tana kallon Hamma Abdulrrahman tsaye a gaban su fuskar nan ta sa babu fara'a ko kaɗan hannayensa duka suna cikin aljihun wandon suit ɗin sa. "Haba Abdulrrhaman me ya sa za ka ce haka! A wannan yanayin da take ciki za ta iya yi ma kanta illa ba tare da ta sani ba." "To ku kyaleta Baffa ta yi ma kanta illa saboda wani wanda ya cire ta daga rayuwarsa cikin tozarci da wulaƙanci. Ku barta in ba ta kashe kanta ba, ba ta haifu ba." Baffa ya yi shuru kawai yana kallon ɗan nashi. "Kai sake ta." Hamma Abdulrrahman ya ba ma Saddam umarni. Da sauri ya saki Ummu ya miƙe tsaye, tun kafin ma ya sake magana Ummi da Baɗɗo suka saki hannayen Ummun Salma suka matsa gefe suka bar Baffa kaɗai a durƙushe a gaban ta. "Baffa kai ma don Allah ka tashi daga durƙushen nan." "Abdulrrahman." "Baffa don Allah." Hamma Abdulrrhaman ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Baffa cikin ɓacin rai,  ba lallashi take bukata ba fata fata za a yi mata sannan za ta dawo cikin hayyacin ta. Baffa ya ƙi tashi sai da Ammah ta shigo ta kira sunan shi. "Baffa." Kallonta ya yi kawai sai ta gyaɗa masa kai, dole ya tashi jiki a sanyaye amma sai da ya kalli Abdulrrahman yana faɗin" Ka yi mata a hankali." Ya faɗa yana dafa kafaɗan shi ya ɗan bubbuga. Fita ya yi daga ɗakin ya koma falo Ammah ta bi bayan shi ganin shi cikin damuwa. Hamma Abdulrrahman ya yi tsaye a gaban Ummu Salma da ta natsu kamar ba ita ce ya shigo ya ga ana rirriƙeta ba, amma yanzu ta yi shuru sai dai kawai hawaye take yi wasu na zuba wasu na karanyowa. "Kin fasa kashe kan na ki ne? Ya faɗa yana kallon ta, kawai sai ta fashe masa da kuka. "Ban hana ki ba, go ahead ki kashe kanki Ummu Salma.". Ya faɗa yana sassauta fushinsa. "Hamma.." Ummu Salma ta kira sunan shi cikin kuka da fitan hayyaci. "Na ce ki kashe kan naki don Uban ki." Ran maza ya ɓaci a gabanta ya duƙa lokaci ɗaya yana kallonta. "Ai sai kin kashe kanki za ki nuna mana kaf ɗin mu ba mu da amfani ko matsayi a wajenki Ummu Salma." Ya faɗa cikin ɗaga murya. Ta ɗago jajayen idanuwansa tana kallon shi, bai dagata ba ya cigaba da faɗin. "Ammah da ta yi cikinki na tsawon wata tara ta kawo ki duniya ta rene ki, da Baffa da ya yi ɗawainiyar rayuwarki tun daga ranar farkon ki a duniya har zuwa girman ki. Da mu y'an'uwanki da muka yi rayuwa dake sama da shekara ashirin duk yau bamu da muhimmanci, wannan dai banza a banza da ba ki da amfani a wajen shi, wanda kika haɗu da shi a baya baya shi ne kike ikirarin kashe kanki saboda shi Ummu Salma? Hawaye kawai ke shatata ta kasa magana, tana so ta yi ma Hamma bayanin yadda take ji amma ta kasa wataƙila ba zai saurareta ba, saboda bai taɓa riskan kansa a cikin halin rayuwar da take ciki a yanzu ba. "Are you stupit? Ko kuwa kin rasa tunanin ki ne saboda wanda ko shekara biyu ba ki yi da sanin shi ba?  Da kin san shi? Ba ki san shi ba kuma kin yi rayuwa Ummu Salma ba ki mutu ba to yanzu ma haka za ki cigaba da rayuwa ba za ki mutu saboda wani wanda bai dace ya fita daga rayuwarki ba." Ya karishe faɗa yana kallon ta, duk da tausayinta na kama shi amma ba zai nuna mata ba gwara ya yi mata jan ido domin ya ga ba ta da hankali. "Za ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kika fara tun farko. Bai hallata ki cigaba da kuka ko damuwa akan wanda bai damu dake ba, wanda ya yi miki sakin wulakanci har uku sannan ya sake ki da cikin shi a jikin ki ba tare da ya damu ba. To ki sani in kika sake cewa za ki kashe kanki saboda shi, to kin nuna ma duniya cewa ke ba y'ar halas ba ce." Shuru ya yi yana kallonta tana ta kuka har da gunji. "Wanda ke son ki ba zai ƙi haɗa jini dake ba Ummu Salma." "Ai ya ma ce ba sonta yake yi ba mara mutumcin." Ummin ikki ta katse shi ya ɗago yana kallonta. "A takardan sakin abin da ya rubuta kenan maganganu masu muni ai tsakanin mu da wannan yaron sai Allah ya isa." Ummin ikki ta sake faɗa tana matsar ƙwalla. Hamma Abdulrrahman ya miƙe cikin mamaki yana faɗin" Ina takardan sakin? "Ko yana hannun Baffa? Ya sake faɗa. Sai Ummin ikki ta amsa mishi da cewa yana hannun Baffa. Da sauri ya bar ɗakin yana zuwa falo ya ga Ammah da Baffa, yana ganin shi ya miƙe yana kallon shi. "Baffa ina takardan sakin? Ya tambaya yana miƙa masa hannu, bai yi musu ba ya laluba aljihun rigan shi ya ɗauko ya mika masa. Ya karɓa daga tsayen ya fara karantawa bai ko kai ƙarshe ba ya yi wurgi da jakar hannunsa da takardan yana faɗin. "Wannan yaron so yake mu nuna masa matsayin mu Baffa." Ya faɗa a fusace lokaci ɗaya yana ɗauko wayarsa daga aljihun wandon shi, da sauri Baffa ya riƙe shi yana tambayan shi abin da zai yi sanin halin shi rudaɗde ne in ran shi ya ɓaci. "Abokin aikina zan kira. Baffa dole fa mu yi ƙaran wannan yaron mara tarbiya." Ya faɗa har jijiyon kansa na miƙewa raɗau saboda ɓacin rai. "Aa" "Baffa za mu shigar da ƙara sai  mun yi shari'a da shi sai kotu ta karɓo ma Ummu Salma haƙkin ta." Ya faɗa cikin ɗaga murya. "Na ce maka A'a." Shima Baffa ya katse shi a tsawa ce lokaci ɗaya yana ƙwace wayar hannun shi, Abdulrrahman ya fusata kawai sai ya fara zagayen falon yana ciccijewa saboda ɓacin rai, Baffa ya bishi ya riƙo shi yana faɗin ya je ya zauna ya samu natsuwa. "Baffa wai ba ka karanta maganganun dake cikin takardan nan ba ne? Raina mu ya yi da zai rubuto mana haka? Ya faɗa yana kallon Baffa cikin fusata. Ammah na gefe zaune ba ta yi magana ba daman ta san sai an yi haka don ma ɗayan fusattacen bai zo ba Kabiru ai da Baffa ba zai iya da su shi kaɗai ba. "Zo ka zauna ka natsu mu yi magana." Da lallashi da ban baki ya amince ya zauna Baffa ya zauna a gefen shi. "Kwantar da hankalin ka Abdulrrahaman." Baffa ya faɗa yana kallon sa ganin yadda yake huci ba abin da ke yi masa yawo wai sai don jikinta ya aure ta kuma tunda ya gama mora shi ya sa ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da kuda. Tuna hakan da ya yi ya sa ya sake miƙewa a zuciye yana faɗin" Kai ina! Bai isa ya ci bulus ba, dole ne mu nuna masa kuskurensa yadda ko nan gaba ya ji an ambaci sunan gidan nan sai ya fara mazari don uban sa." Da sauri Baffa ya sake riko shi yana ba shi haƙuri. "Baffa ka bari mu koya masa hankali. Ko nawa zan kashe daga nan har kotun ƙoli so kawai na ke yi na ga ya wulakanta." Abdulrrahman ya sake faɗa yana ta da jijiyoyin kansa saboda ɓacin rai. Mirmishi Baffa ya yi kafin ya ce" Abdulrrahman" Ya kira sunan shi yana mai kallon shi. "Ba za mu je kotu ba, ba za mu je mu buɗe ma duniya cikin mu ba. Shi fa namiji ne ita kuma Ummu mace ce, ita ce za ta zama abin nunawa ba shi ba. Gwara mu kai shi kotun da ba wanda ya isa ya kwace daga zaluncin da ya yi ba wannan mahaluƙin in dai ka yi zalunci sai ka karɓi sakamakon ka, daidai da abin da ka ka aikata." Hamma Abdulrrahman ya kalle shi cikin mamakin kalaman shi shi kuma Baffa ya jinjina masa kai kafin ya cigaba da faɗin" Kotun Allah Abdulrrahman. Mu bar shi da Ubangijinsa shi zai yi ma Ummu faɗa shi zai saka mata in sha Allahu." Sai ya yi shuru yana sauraran Baffa ta wani fannin gaskiya ya faɗa. "Za mu iya kai shi kotu mu yi nasara amma zafi da baƙin cikin dake zukatan mu ba za su gushe ba Abdulrrahman. Kuma ba za mu iya sauya cewarsa na baya son yar mu ba, duk abin da za mu yi sai dai mu yi ba mu isa mu ƙanƙarema Ummu bakin cikin zuciyarta ba amaimakon mu saukaka mata sai mu sake dagula mata lissafi." "Haka ne Baffa." "To ka yi hakuri da maganar shigar da ƙara. Ba wai don ba za mu iya sharia da shi ba ne. Aa sai domin mu taimaka ma Ummu wajen mantawa da shi, shi kuma Allah ne ya hana zalunci kuma ya yi, to ko Ummu ba ta furta Allah ya saka mata  ba wallahi sai Ubangijin adalci ya yi mata sakayya ko a nan duniya ko a ranar gobe ƙiyama.". "In sha Allahu." Ammah ta faɗa cikin sanyin murya Hamma Abdulrrahman ya yi ajiyar zuciya kafin ya yi magana Baffa ya dafa kafaɗan shi yana faɗin." Ina fatan ka fahimce ni yanzu ko? "Na fahimta Baffa. Allah ya kyauta na gaba." Ya faɗa yana jin fushin sa na sauka. "Allah ya yi maka albarka " "Amin Amin Baffa " Ya amsa a sanyaye shuru na wani lokacin kafin Baffa ya tambaya Ummu. "Na yi mata faɗa, Baffa ba a lallashi a irin haka, ba ta da hankali sai zuciya ta zuga ta." "To yanzu dai ka koma ka matsa mata taci wani abu. Amman ku ta ce tunda suka zo ba ta ci komai ba, kuma ka ga ba ita kaɗai ba ce " "To Baffa." Ya amsa yana kallon shi. "Baffa cikin fa? Mu za mu riƙe shi ko bayan ta haihu za a mayar da shi wajen uban shi? Baffa ya girgiza kai kafin ya ce" A'a ba ka ji abin da ya ce a takardan ba ne?. Ba ya bukatar cikin shima " Nan Baffa ya sanar da shi yadda suka yi da waliyin Habib da hukuncin da ya yanke. "Baffa saboda dai ka ƙi yarda ne amma ai Ummu kaɗai muka aura masa ba da ciki ba. Bai isa ya ƙi karɓan abin da yake nashi ba ne ƙaryan shi tasha ƙarya" "Ba komai. Ai Ummu ce za ta haifi koma mene ne, saboda haka ba za mu ƙi jinin ta ba." Hamma Abdulrrahman ya jinjina kai amma da ace Baffa zai bari wallahi ba za su karɓi cikin nan ba sai an je kotu alƙali ya yanka mai kuɗin ɗaukan ciki da reno tana haihuwa bayan ta yaye ya zo ya karɓi abin ya ɗiga shi. Rayuwar Ummu ba za ta kare wajen wahala ba tunda ba shi da mutumci. Umarnin Baffa ya bi ya koma ciki ya iske gabaɗayan su har da Saddam sun tasa Ummu kowa yana bata baki amma ba ta ji ba kuka kawai take yi tana gunji ko tsayawa ma jin kukanta bai yi ba ya ce a haɗo mata tea mai zafi a kawo masa ba musu Baɗɗo ta mike ta je ta haɗo mata daman akwai ruwan zafi a fulas ta ciko wani jug ta kawo ma Hamma Abdulrrahman ba wasa a fuskar shi yana miƙa ma Ummu jug ɗin ta karɓa hannunta na rawa. "Shanye shi duka ki ba ni Jug ɗin ina jiran ki " Ya faɗa ba wasa a maganarsa jiki da hannu na rawa ta karɓa ba ko gaddama ta kafa kai ta kwankwaɗe shi ta dire kofi su Baɗɗo na ta murna. "Yauwa ko ke fa Ummu Salma yanzu ai kya ji dama-dama" Ba ta gama rufe baki ba Ummu ta yunkura da sauri kafin ta iya miƙewa amai ya biyo baya duk kuma ruwan shayin da ta sha sai da ta amayar da shi a wajen nan Hamma Abdulrrahman ya matsa baya yana rufe hancin sa, saboda ba ya son ganin amai ko ya shaƙa yanzu nan shima zai fara fita ya yi ya ce in sun gyara wajen su sake haɗo mata wani shayin. Hamma Saddam ma ya bi bayan shi aka bar Ummin ikki ta kama Ummu zuwa tiolet ita kuma Baɗɗo tana gyara in da Ummu Salma ta yi aman. Sai da aka gyara wajen aka kunna turaren tsinke ɗakin ya ɗau ƙamshi ita kuma Ummu Salma wanka Ummi ikkin ta yi mata domin jikin na ta ba karfi sannan duk ta ɓata kayan jikinta kawai sai ta taimaka mata ta yi wanka bayan ta fito Baɗɗo ta ɗauko mata wata doguwar riga cikin kayanta da suka zo da shi. Hamma bai tafi ba ya sake dawowa da wani kofin cike da ruwan tea ya ce Ummu ta sake shanyewa sai ta fara hawaye tana faɗin. "Hamma zan yi amai." "Ko sau ɗari za ki yi amai sai kin sha, in dai zai zauna a cikin ki." Ta san halin shi in yana magana da lalama a yi abin da yake so in ya birkice bashi da kyau dole ta karɓa ta shanye. Ya karɓi jug ɗin yana faɗin" Good. Ki riƙa cin abinci sosai kar ki bari na ji labarin kina zama da yunwa kin ji ko ba ki ji ba? Sai ta gyaɗa kanta tana mai zubar ƙwalla "Ba ki da baki ne? "Na ji." Ta faɗa tana danne kukanta. Sai ya miƙe lokaci ɗaya yana faɗin" In ma kina so ki mutu ne ki yi mutuwar da Allah ya tanadar miki, amma in har saboda wancan  ne to ki sani har abada rayuwarki ba ta da wata amfani a wajen shi. Ki riƙa tuna hakan a cikin zuciyarki." Daga haka ya fice ya koma falo ya yi ma su Ammah sallama da cewa zai tafi. "Ka tsaya ka ci abinci mana." "A'a Amma bana jin cin wani abu." Jakarsa ya ɗauka ya rataya ya ce zai shigo gobe da safe kafin ya wuce wajen aiki in dai ba ta ci abinci da yamma ba Ammah ta yi masa waya zai sake dawowa da haka suka yi sallama ya fice Baffa ya koma ɗakin sa can ya bi shi suka yi sallama sannan ya fice daga gidan cikin tausayin Ummu har da su Baffa gabaɗaya gwara Baffa na bayyana damuwarsa Amma ce ke ɓoye abu kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci ta rame a tsaye cikin yini ɗaya.   Ranar sai dare Abdullahi ya kai Ummin ikki gida. Daman da ya dawo da yamma tare da matarsa Adda Suwaiba da Madibbo ya zo. Ita ce tare da Baɗɗo suka zauna da Ummu suna ta ɗan ba ta baki ta daina kuka sai dai suyan zuciya kawai. Baɗɗo nan ta kwana tare da Ummu matar Abdullahi sai wajen sha ɗaya na dare suka koma gida. Washegari ma wajen ƙaryawa sai da Baffa ya zauna ma Ummu ta ɗan sha tea kaɗan shi ma ba daɗewa sai da ta yi aman shi, da rana faten wake Amma ta yi mata amma ba ta iya ci ba sai da Hamma Abdulrahman ya zo ya tsaya mata sannan ta tsakura haka da daddare ma sai da ya tsaya mata tunda suna gidan har dare tare da Adda Suwaiba kowa Ummu yake tausayawa. Habib kam ya sha tsinuwa da mugun baki Ummin ikki ma tana gidan har dare ita da Kaltume washegari kan Ammah ta fara karɓan baƙi masu zuwa mata jaje, yayyen Baɗɗo dukkansu sun zo Iklima har dare sannan ta tafi. A waya ma Ammah tana ta samun wayoyin sauran yaranta da matan su. Hamma Jibo ya ce sai karshen sati Hamma Mustapha dai ya ce sai karshen wata za su shigo har Baffa duk sun kira suna mai jajanta musu da wannan lamarin da ya faru su da yake suna da sauƙin kai sun ce hukuncin Baffa ya yi daidai. Kuma duk sun yi magana da Ummu Salma ta wayar Ammah suna ta bata baki amma har yanzu Ummu ba ta daina kuka da damuwa ba. Hamma Kabiru ne ya yi ta masifa a waya yana faɗin ba za su karɓi wannan cikin ba, ba wanda ya saurare shi daga AmmaH har Baffa sanin halin shi shi ma dai ya ce yana tafe a karshen satin nan. Saboda hankula ba'a kwance yake ba shi ya sa Amma da Baffa suka manta da maganar kwaso kayan auren Ummu Salma.  Sai da su Umma Balki suka zo daga Mubi suke maganar kwaso kayan tunda duk Ammah ta sanar da su, abin da ke faruwa. Da Ammah ta yi masa mganar kwaso kayan Ummu sai Baffa ya ce za a je a kwashe in zukata sun samu natsuwa. Kwanan su ɗaya suka juya cike da alhini. Baffa ma ya sanar da su Baffa Umaru kowa ya ji labari sai jikinsa ya yi sanyi barin ma in suka zo suka ga yadda Ummu ta koma cikin kwana biyar ta faɗe ta rame ta lalace abinci in ba Baffa ko Hamma Abdulrrahaman suka tsaya mata ba, ba ta ci in kuma ta ci ba ya zama a cikin ta za ta amayar da shi. Sannan Baɗɗo ta ce Ummu ba ta samun barci da daddare. Abdullahi shi kan shi ya ga ɗashewar Ummu Salma ya ce ya kamata a kaita asibiti a duba lafiyanta. Shima Baffa ya ga haka saboda komai ta ci baya zama a cikin ta. Ranar Jumma'a da Safe Baɗɗo da Ummin ikki da Hamma Abdullahi suka kai Ummu Salma asibiti Boshin clinic in da take da fayel, suna zuwa likitoci suka riƙe ta acan suka ba ta gado likita na ta faɗa jininta ya hau ga maleria ga rashin cin abinci. Yana ta faɗan cewa yanayin zai iya zama barazana ga cikin jikinta. Baɗɗo suka bari da ita, Ummin ikki da Abdullahi suka koma gida suka sanar da su da halin da ake ciki sannan suka zo da mata da wasu kayan sawa sai fulas ɗin ruwan zafi da kayan tea. Kwanta ɗaya a asibitin sai ga Hamma Kabiru ya zo shi kaɗai ya shigo garin daman Baɗɗo ne ta kwana tare da ita da safe Ummin ikki ta je tana taya ta zama sai Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim da suka zo da rana su ɗan taya su zama. Hamma Kabiru ya zo har asibitin ya duba Ummu Salma shi da Abdulrrahman da Saddam nan suka bar ma Saddam ɗin suka tafi, tana ta barci saboda an yi mata alluran barci tana ta samun barcin da ta yi kwanaki ba ta samu ba. Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahman suka koma gida suka samu Baffa shi Hamma Kabiru faɗa yake yi don mai Baffa zai ce a karɓi ciki ai tun da dai ya amince shi ya ɗiga shi to bai isa ba. "Baffa Ummu ta koma kamar wata horror tsabar rama da fari." Ya faɗa cikin damuwa. "Nima na ce Baffa ya bari a yi ƙararsa amma ya ce ba za mu yi ba." "Baffa ka bari mu yi amfani da kuɗinmu mu jijiga duniyarsa kamar yadda ya jijjiga rayuwar ƙanwar mu." Baffa dai ya yi shuru yana jinsu suka gama bambamin faɗan su suka sauka sannan ya yi magana da su kalaman dai da ya faɗa ma Abdulrrahman shi ya faɗa ma Kabiru ya dai bar maganar ne amma ba wai don ya fahimci Baffa ba, ai tunda ya nuna shi ba shi da mutumci gwara suma su nuna masa yan zamani ne, bai karanta takardan sakin ba amma duk kalaman dake ciki Abdulrrhaman ya karanta masa tun yana Jalingo. Ba kwana zai yi ba a ranar yake so ya koma amma ya ce zai dawo tare da Adda Safinatu da yara su duba Ummu su ɗan kwana biyu. Hamma Abdulrrahman ya tafi saboda akwai in da zai je shi kuma sai ya shiga falon Ammah su sake gaisawa tun da lokacin da ya shigo gidan tana da baƙi, labari kamar ana ta aike maƙota duk sun ji labari ana ta shigowa yi ma Amma jaje har Baffa in ya fita haka za a tsayar da shi ana masa jaje, to ai tunda lamarin ya faru ba wanda ya isa ya hana a yaɗa labarin Ko Ammah abin da Hamma Kabiru ya ke faɗa mata kenan ta lallashi Baffa ya bari su yi ƙaran yaron nan. "Baffa ba zai amince ba Kabiru ku bar maganar nan kawai." "Ammah to sai ya kashe mana ƙanwa! Kin ga yadda Ummun ta koma ne? Amma ta yi shuru tunda ita dai ba ta je asibitin ba Baffa ma ya kasa zuwa amma dai sun yi waya da Ummin ikki ta ce mata ta samu sauƙi tana ta barci dai. Gwara ta samu barcin ko za ta samu yar natsuwa. "Kawai Baffa ya koma gefe ya bar mana faɗan nan. Wallahi ko ba mu tura yaron nan gidan yari ba sai ya gane ba shi da wayau sai ya san ba a taɓamu a zauna lafiya. Ɗan iska kawai ni da man bai yi mini ba yana wani sunkunyar da kai kamar nagari Ammah ki tsoraci mutum mai kirki da surutun tsiya daga baya sai ya aikata mugun abu. Nonsense kawai" Amma ta ɗan murmusa ba ta yi magana ba, in dai Kabiru ne da man karatun sa kenan ta kiyayi mutumin da ya cika kirki ba shi da gaskiya. Sake gyara zama ya yi yana kawo maganar da ta wuce wai bai so da man a yi ma Ummu aure ba kamar ya san abin da zai faru daga karshe kenan. "Yanzu Ammah ina daɗin abin da ya faru? Ummu ƙaramar yarinya ta zama bazawara ga ƙaramin ciki. Haba don Allah in da a ce yarinyar nan ta ji maganar mu da yanzu ta kusa gama Degree ɗin ta da yau ba ta can akwance rai a hannun Allah saboda wani stupid irin yaron da ta aura" Amma dai ta yi shuru tana sauraran shi yana ta faɗa yana nuna mata harda kuskuren Baffa da itama ma kanta tunda Baffa na jin maganarta ba ta hana a yi ma Ummu aure a wancan lokacin ba. "Kabiru ka ishe ni fa. Baffan ne ke da laifi? In ya tara sani  zai aura ma ta shi? Kaddara ne kuma mu duka musulmai ne musan karɓan kaddara gare mu wajibi ne." "Amma ki gane magana ta mana. Me ya sa aka goya mata baya! Da a lokacin ke da Baffa kun dage mata wallahi da ta koma makaranta ta bar ra'ayin aure. But kalli abin da ya faru at the end Ammah Rayuwarta ta da dawo baya fa." "Haka Allah ya hukunta Kabiru ni ko Baffan ka ba mu isa mu sauya faruwan haka ba" Shi dai sai wani kawo na shi tsarin yake yi Ammah ta gaji ta yi masa tsawa tana faɗin" Kabiru zan ci maka mutumci ba za ka bar ni na ji da damuwata ba, ka zo kana damuna da turancin ka na banza da wofi." Domin daga karshe sai ya koma yana yi mata mgana da turanci sai da ya ji Ammah ta buɗe masa wuta sannan ya ɗaga hannuwa sama yana dariya. "Afuwan Ammah na yi shuru." Ya faɗa cikin harshen fillanci wata uwar harara ta maka masa da ya sa ya ɗinke bakin shi, shuru na wani lokaci sai da ta sauka don kanta ta tambayi Safinatu da yara, duk da ta kira ta waya ta yi mata jaje, ya ce duk suna lafiya yana tunanin za su zo karshen wata su yi musu ko kwana biyu ne Ammah ta ce Allah ya kaimu ya amsa da Amin. "Ammah gaskiya ya kamata in Ummu ta haihu ta koma makaranta." "To Baffa." Ta faɗa cikin gatse tana hararan shi sai ya yi shuru yana dariya. "Amma shawara ce fa." "Ba'a son shawaran naka" "Allah ya ba ki haƙuri Amman mu." Ya faɗa yana ɗan mirmishi, sake maka masa harara ta yi shi kuma sai ya kwashe da dariya. "Allah ya huci zuciyar Amman Lamiɗo" Kamar ya sani sai ko ga shi ta yi mirmishi dariyan ya sake yi kafin ya ce" Da man na sani sunan Amini ne kaɗai zai saka ki dariya." Amma ta yi mirmishi kafin ta ce" Kwana biyu ma ba mu yi waya ba. ya ko san abin da ya faru na Auta? "An ya! Kamar bai sani ba don ko shekaranjiya mun daɗe muna waya kuma ban ji ya yi mini magana ba ina tunanin bai sani ba." Amma ta jinjina kai kafin tace" Ko jiya na gwada lambarsa ba ta shiga. Haka ma Fatima itama ba na samun ta a waya." "Mami fa kamar ba ta ƙasar, kwanaki mun yi chart da ita tace mini suna Paris." Amma ta ce" An yi haka na manta Baffa ya faɗa mini sun yi tafiya. Lamiɗon ne na damu amma tunda har ka yi magana da shi yana lafiya Alhamdulillah." Hamma Kabiru ya ce" Lafiyan shi lau Amma ga ma wani labari mai daɗi." "Me ya faru? "Kin kusa fara ganin ɗanki yanzu akai,-akai." Amma ta washe baki tana fafin" Kai don Allah? Hamma Kabiru ya gyara zama yana faɗin." Wallahi a shekaranjiyan da muka yi waya yake faɗa mini kamfanin Chevron da ya nemi aiki da su daman can kwanaki ya faɗa mini sun yi online interview. To sun ba shi aiki nan da wattani biyu zai fara aiki da su in sha Allahu." Amma ta washe baki kafin ta ce" Ma sha Allah. To shi wannan kamfanin anan ne ko? Ba sai ya yi ta yawo a cikin jirgin ruwan ba ko? Hamma Kabiru ya yi dariya kafin ya ce" Ammah duka kamfanonin na gida Nigeria ne, sai dai shi wanda Lamiɗo ke aiki da su yanzu kamfanin Nigerian Port Authority su jirgin da yake tuƙawa suna jigilan mutane ne da kayan masarufi suna zuwa ƙassashe da yawa kuma suna ɗaukan lokaci shi ya sa yake daɗewa bai zo ya ga mutane ba. Ammah ko a can Lagos ko Balkisu ba ta cika ganinsa ba sai su zo Tashar jirgin ruwa dake Apapa Lagos sau nawa bai je gida ba saboda aikin yana da ɗan tsauri shi ya sa na bashi shawaran gwara ya sauya kamfani wanda zai dinga zuwa gida bayan sati biyu ko uku in ya daɗe ne wata ɗaya." Ammah ta gyaɗa kai tana faɗin" Haka ne, ya fara tara iyalai bai kamata yana yin nisa da gida lokaci mai tsawo ba gaskiya ka ba shi shawara mai kyau Kabiru." Hamma Kabiru ya karɓa da cewa" Shi ne fa har sun ɗauke shi aiki yanzu ya rubuta takardan ajiye aiki da kamfanin da yake yi ma aiki yanzu sun ƙi saka hannu. Kin san Lamiɗon naki gifted ne suna son shi duk cikin matuƙan jiragensu ba kamar shi, yana musu aiki tukuru sannan yana da jajircewa akan aikin shi aiki yake yi musu tukuru bai damu da jikinshi ko gajiya ba shi ya sa ba sa son rabuwa da shi." "To ai sai dai su yi haƙuri mu ma muna son ganin shi sannan muna son ya riƙa hutawa" Ammah ta faɗa tana dariya. Tun bayan faruwan al'amarin Ummu sai yau Amma ta saki ranta hiran Lamiɗon da suka yi da Hamma Kabiru. "Ai zai samu hutu da lokaci ishasshe sosai Ammah. A yadda na yi binciken sabon kamfanin da zai fara aiki da su, suna sauyin matukan jiragen in wannan yaje ya yi kamar wata ɗaya to za a bashi kamar break na sati ɗaya yaje gida ya gana da iyalai da yan'uwa sannan ya dawo kuma kin ga su babu daɗewa sosai kamar na wannan aikin." "Gaskiya wannan ɗin yafi Kabiru to shima duk tuƙin jirgin ne? Hamma Kabiru ya sake gyara zama yana faɗin" E mana shi ma kamfani ne kamar wanda yake aiki da shi a yanzu amma suna da ɗan bambamci. Shi wannan kamfanin na Chevron Nigerian Limited. Kamfanin dake da alhakin fitar da Mai kasashen waje domin a cire su kalanzir, fetur, dessel, LLG. Suna da jirage da matuƙa jiragen dake da alhakin fita da man zuwa waje da dawowa dashi bayan an tantance shi. Su kawai aikin su fita da man zuwa ƙasar waje domin a tantance a cire abubuwan da na lissafa miki, kamfanin na haƙo Mai ne kuma suna da jirage da matuƙan da ke jigilan Mai zuwa in da za a tace shi a fidda abubuwa masu amfani a jikinsa yadda za a dawo mana da shi mu samu damar amfani da shi kin gane Ammah.? "Na fahimta Kabiru. Ubangiji ya tsare mana ku. Shi kuma Lamiɗo Allah ya sa ya fara a sa'a Allah ya taimake shi ya tsare shi." Ammah take faɗa Hamma Kabiru na amsawa da Amin Amin. " Ya ce ƙarshen watan nan ko ba su saka masa hannu ba zai dawo gida ya yi hutu sosai kafin ya fara aiki da sabon Kamfanin." "Allah ya amince. Allah ya ba shi nasara." Sun ɗan jima suna ta hira rabin hiran ta su duk akan Lamiɗo ne sai wajen biyar saura Hamma Kabiru ya yi sallama da Ammah da Baffa ya kama hanyar Jalingo tunda motarsa ce tafiyar awa uku ce zuwa da rabi. Ummu kuma sai da ta yi kwana huɗu a asibiti sannan aka sallame ta tare da dokokin likita, ta riƙa samun hutu da barci sannan sun ba ta bedrest ga maganguna har da na barci tunda an faɗa musu ba ta samun barci cikin ta kuma ya na gabda shiga wattani huɗu likita ya ce tana buƙatar kulawa da an ga wata matsala a dawo da ita asibiti sannan ta riƙa cin abinci mai gina jiki saboda inganta lafiyan abin da ke cikin ta. Bayan sun dawo gida Hamma Abdulrrahman ya sake zaunar da ita daga shi sai ita a ɗaki ya sake yi mata faɗa daga karshe ya koma lallashi ya faɗa mata ga dokokin likita sai ta kiyaye ma kanta da shiga damuwa in tana son ta tsira da abin da ke cikin ta, bai barta ba sai da ta yi masa alƙawarin za ta daina damuwa sannan za ta kula da kanta ko domin abin dake cikinta da take jin wani son shi na ƙaruwa a tsakiyar kirjinta ba kukan sakin da Habib ya yi mata take yi ba har yanzu  kukan bakin ciki da faɗa da zuciyarta da har lokacin ba ta daina son Habib da tunaninsa ba. Tana yi iya yin ta domin ta manta da shi amma ta kasa da ta keɓe shikenan za ta yi ta tunanin shi da irin good momories ɗin su tare da juna ba ta ma sanin lokacin da ta ke fara kuka. Ba za ta taɓa mantawa da Baɗɗo ba sai da ta kwana goma da ita tana kula da ita sannan ta koma gida tunda sun koma makaranta. Sannan Ummin ikki ma kullum sai ta leƙo kowa dai burinsa ta samu ta sake ta fara walwala. Ga Baffa da duk ya sakar ma Hamma Abdullahi harkokinsa yana zaune a gida saboda ita. Shi dai nasihan shi ta daina damuwa ta yadda da kaddaranta. Ammah ma tana nuna nata kulawan amma in ta yi lallashin ta gaji za ta fara masifa ne da faɗa, ga Hamma Saddam ma yana iya bakin ƙoƙarin shi wajen zama da ita yana yin duk wani abu da zai sanya ta farinciki, haka ma Hamma Abdulllahi, da matan su in ba su zo ba yau ba za su zo gobe su Hamma Jibo duk da ba sa kusa duk ranar duniya sai ta yi magana da su ta wayar Amma tunda ita wayarta tana cikin kaya ta kashe kanta ma ba chaji, ganin yadda kowa ya damu da ita ya sa ta rage damuwa amma Allah kaɗai ya san halin da zuciyarta ke ciki tare da Ammah suke kwana Baffa ne ya ce ta riƙa kwana da ita amma in ba magungunanta ta sha ba tana daɗewa tana juye-juye ba ta samu barci ba gani take yi kamar a mafarki wai yau ita ce a gida a matsayin bazawara. Ba ta sare ba tunani take da yaƙinin cewa Habib zai dawo ya neme ta, tana ma mantawa da cewa har abada yanzu ta haramta ga Habibu ita soyayyar shi ta gama rufe mata ido da duk abin da ya yi mata ta kasa jin tsanar shi ta kasa daina son shi, duk da tana son ta tsane shi ɗin amma ta kasa tunda ba ita ke da alhakin sarrafa zuciyar ta ba. Hamma Abdulrah. yana can kasar turai ya ji labarin abin da ke faruwa shi auren ma baya nan aka yi sai ga shi yana can komai ya ƙare. Ya shiga damuwa sosai barin ma da Saddam ke ba shi labarin yanayin da Ummun ke ciki Vedeo call ya kira aka bata ya yi magana da ita kuka kawai take yi tana ma kasa mgana shima daga ƙarshe kashewa ya yi ya fashe da kuka, yana da saurin kuka da tausayi shi ya sa bai sake kira ba sai dai duk lokacin da ya yi magana da wani na gida zai ce a gaishe masa da Ummu, ba ya son su sake magana ta saka shi kuka ga shi yana shekaran ƙarshe ne karatu yake yi kamar injin ya yi ya gama shima ya dawo gida cikin ahalinsa. Mami ma suna Paris Hamma Saddam ya faɗa mata halin da ake ciki ai a daran ta matsa ma Abban islam cikin kwana biyu suka dawo gida Nigeria. Washe gari kuma suka sake biyo jirgi zuwa Jimeta. Tun da Mami ta zo ta ke kuka kowa ya san kukan da take yi kuka ne na fami daga tsohon gyambon dake zuciyanta. In ta kalli Ummu sai ta ji kukanta ya kasa tsayawa ta yi kuka kamar ranta zai fita sai da Baffa ya zauna yana ta ba ta baki Abban islam na gefe domin ko ya ba ta baki ba ta yin shuru sai ta ce wai ba zai gane yanayin ba ne. Ummu Salma kukanta ya dawo sabo da zuwan Mami da kukan da take yi, tausayin Ummu Salma take ji duk da ta ɗan fi ta shekaru ita lokacin ko ashirin ba ta cika ba ta faɗa wannan kaddaran amma duk yadda za a fassara lamarin ba wanda zai gane yanayin sai wanda abin ya faru da shi. "Baffa yaron nan ya cutar da Ummu Salma. Muma ya cutar damu kuma wallahi sai Allah ya saka mata." Mami take faɗa tana kuka kamar ranta zai fita. "Ummu ki yi kuka ki yi ta kuka ko za ki sami salama. Amma kar ki yi dogon damuwa cuta za ta kama ki, in kuma hakan ta faru za ki samu cikin damuwa." Haka take ta faɗa ma Ummu lokacin da ta rungumeta a jikin ta dole Alhaji Isa Ɗanmarke ya nemi hotel ya kwana washegari ya juya Kaduna tunda yara na gida tare da su Baraka, ya bar Mami a Jimeta ita ta ce ya tafi kawai za ta zo daga baya. Zuwan Mami ya tado ma Ummu taɓon ta amma kuma ta samu sauƙi saboda Mami ta zaunar da ita, ta ba ta labarin rayuwarta da yadda ta yi gwagwarmaya da kaddaranta daga ƙarshe ta yi nasara da yadda Ammah da Baffa suka yi ta ƙoƙari a kanta. "Ummu Salma akwai zafi na sani amma sai kin daure. Yanzu ki sani ke uwa ce a gobe. Ki kula da kanki saboda abin da ke cikin ki, ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki cire damuwa a ran ki, in kin ji kuka ki yi kuka domin shi kaɗai ne zai samar miki da salama." Haka take ta faɗa mata cikin ƙarfafa mata gwiwa. "Za ki ci wannan jarabawar Ummu. Za ki yi nasara kamar yadda na yi. Muna nan dake Allah zai kawo miki wanda zai share miki hawaye. Shi kuma Habib sai ya yi Fargar jaji da ikon Allah." Ummu Salma tana kuka ta nuna ma Mami jikinta tana kuka take faɗin" Mamina wa zai aure ni a haka? Me na ke da shi? Ba ni da budurci ba ni da jiki mai kyau, nonuwana sun kwanta, ciki gare ni Mami nan da wata biyar zan haihu na buɗe na zama uwa na shayar da jariri, Mami ki faɗa mini wa zai kwashe ni a haka? Me ya sa shi da ya fara bai ƙarisa ba Mami na? Haka Ummu ke faɗa tana ta gunjin kuka. "Allah zai kawo shi, wanda ba jikin shi yake so ba ke yake so Ummu in kina tunanin ba zai yuyu ba ki riƙa duba rayuwata. In kika kalle ni za ki samun ƙwarin gwiwan cewa ke ma komai zai wuce zai zama sai labari, sai dai ki tuna ki yi mirmishi ko kin yi kuka sai dai ki yi kukan farinciki da tuna rayuwar baya." Ita dai Ummu Salma jin Mami kawai take yi ba ta san irin yadda zuciyanta ta so Habib ba ne. Ba ta san yadda jikinta da rayuwarta ya saba da shi ba ne, shi da ya fara me ya sa bai ƙarisa ba? Me ya sa ya rabu da ita? Ta amince za ta zauna da shi ya yi ta moran jikinta har illa masha Allah, amma yanzu da ya sake ta ina za ta je? Ji take yi kamar ta rasa komai na rayuwanta ne in ta ce komai tana nufin komai, mafarkin ta burukanta da dukkan wani tanadinta na rayuwa Habib ya yi sanadiyar da yau ita Ummu Salma ta dawo ba komai ba, ya kuma ma yar da rayuwarta kwanko babu wani abin mamora a rayuwarta a yanzu. Kwanan Mami biyu da zuwa Jimeta sai ga Hamma Mustapha da iyalan shi a rana ɗaya suka zo da Hamma Jibo amma shi kaɗai ya zo bai zo da su Nauwara ba, jirgi ya biyo ma. Suma dai duk haƙuri da nasihan suka yi ta Ummu Salma ganin yadda duk ta faɗe ta rame ba ta mgana. Daman a wannan lokacin kowa haƙuri yake ba ta, domin babu wani abu da za a yi mata. Zuwan su Hamma Jibo aka yi maganar kwaso kaya. Mami da Ummin ikki ne suka je gidan tun da key ɗin gidan da man su Baɗɗo sun taho da shi kaf aka haɗa kayan ta waje ɗaya babban mota mai budaɗɗen baya ta zo ta kwashe zuwa gida a ɗakin kusa da na Ammah mai ciki da falo aka saka kayan aka rufe, kayan abincin da Hamma Jibo ya siya mata jibgi haka aka kwaso su sai dai aka kai su store ɗin Baffa. key ɗin kuma suka ba ma maigadi sallahu in megidan ya zo ya bashi ko masu duba gidan tun da suna zuwa duk sati kayan Habibu ko ɗaya ba su samu a gidan ba tun washegarin ranar da ya yi sakin kafin ya tafi sai da ya kwashe duk abu da yasan na shi ne daman iya kayan sawa ne da takalma sai takardunsa duk ya kwashe su. Ranar da aka kwaso kayan kwana Ummu ta yi tana kuka. Ba kuma wanda ya hana ta Mami ta ce a ƙyaleta ta yi kukanta ko za ta samu suƙuni kar baƙincikin ya ƙume mata a zuciya ta samu matsala. Tunani take yi shike nan komai ya ƙare tunda gashi an kwaso kayan ta, shike nan ta rasa komai ba ta da wani abu kuma da ya yi mata saura. Cikin dake jikinta ne kawai ya rage mata shi kaɗai ne abin da ya rage ta ƙarisa a halin yanzu. Habib ya cuce ta, Habib ya gama da rayuwanta. Habib ya yi ma duniyarta kaca-kaca, Habib ya yi sanadiyar da labarinta ya shiga bakin mutane ya mayar da ita bazawara ya sanya kanta a cikin mata masu taɓo a zukatan su, ya jijjiga duniyanta sannan ya bar ta da abin tunawa har na tsawon rayuwarta na har abada. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t *14* Sai da Mami ta shafe sati ɗaya a garin Jimeta kafin ta koma Kaduna. Kuma zaman ta ya yi amfani tunda Ummu na jin maganarta sannan tana sauraranta, zamanta a gidan kafin ta tafi ya taimaka ƙwarai wajen sake dangana a zuciyar Ummu Salma, tana cin abinci tana kuma samun hutu sannan koke-koken da take yi ya ɗan ragu sai dai abin da ba'a rasa ba. Mami ta so Baffa ya amince ta tafi da Ummu Salma Kaduna wajenta ta zauna na wani lokaci saboda yanzu garin Adamawa gabaɗaya ya yi mata ƙunci in ta yi nesa za ta fi samun sukuni da jin daɗi lokacin Hamma Jibo na nan shi bai koma ba ya yi na'am da shawaran Mami har Ammah ma ta ce gwara ta ɗauketa su tafi na ɗan lokaci har zuwa komai ya lafa, shi kan shi Baffa ya fahimce su amma sai ya yi tunani a matsayin shi na Babba, bai ba ta Ummu ta tafi da ita da farko ba amma ba wai ya hana ta ba ne. "Fatima Auta fa ƴ'arki ce, ni ko Amman ku ba mu isa mu hana ki tafiya da ita ba. Sai dai ya kamata mu yi abin hankali, ke fa matar aure ce kina da miji da kike zaune a ƙarkashin ikon sa, bai kamata ba tare  da sanin shi ko izinin shi ba kawai ya ga kin zo da yarinya ba. Ya kamata ki yi shawara da shi in ya amince ki zo ga Auta nan halak malak Fatima ba wanda ya isa ya yi miki iko da ita." Abin da Baffa ya faɗa mata kenan ana gobe za ta koma da ta same shi da maganar son tafiya da Ummu Salma gidanta dake Kaduna. "Baffa ka fa san Abban Islam ba shi da wata damuwa. Mun yi ma magana da shi a waya shi ya ma kawo wannan shawaran na cewa ko zan taho da ita ne ta ɗan samu natsuwa? Shi fa ko har abada za ta zauna damu ba shi da wata damuwa." Mami ta amsa ma Baffa cikin magiyan ya amince ta tafi da Ummu amma ya hana ta, ba da niyyar ba ta da hurumi ba sai da niyyar ta bi komai a hankali da cewa ta koma su tattauna da mijinta in ya amince daga baya sai ta zo ta tafi da Ummu sun ba ta ita har abada. Dole Mami ta amince amma ba haka taso ba, ita ma ta ce ba domin wajen aiki ba, da sai ta yi wata a garin Jimeta amma saboda aiki ya sa ta yi shirin komawa. Kafin tafiyarta haka ta zaunar da Ummu  ta sanar da ita za ta koma Kaduna amma ba daɗewa za ta dawo ta tafi da ita can ta zauna tare da ita. "Mami me ya sa ba yanzu ba? Ummu ta faɗa cikin raunin murya har ta fara hawaye. Za ta fi son Mami ta tafi da ita, domin garin nan da mutanen cikin ta sun gama fita da zuciyarta, wani ƙunci take ji da duhu daga cikin zuciyarta watakila da za ta yi nesa da gida da garin gabaɗaya za ta fara mantawa da kaddaranta har ta manta da Habib daga zuciyarta gabaɗaya. "Ni ma haka na so, to amma kin san halin Baffa ya matsa sai na koma gida na yi magana da Abban Islam." Ummu tana ta kuka har da shessheƙa, Mami ta yi ta lallashinta da ban baki, ba ta so Mami ta tafi tana son zama da ita domin ita ce kawai ta fahimci halin data ke ciki, ita ce kaɗai ta san irin raɗaɗi da zafin da kaddaran take da shi, ita ce kuma ta san irin yanayin da ake shiga in ka rasa dukkan wata dama ko mafitar daka ke tunanin ka kama ko ka dafe tuntuni amma sai daga baya ba ka shirya ba, ba zato ba tsammani komai ya kubce daga hannun ka. "Ki yi haƙuri Daughter in sha Allahu zan dawo na tafi dake. I promise you in sha Allahu." Da haka ta samu ta lallasheta ta daina kuka. Sannan ta bi ta da kalamai masu sanyaya zuciya da alkawarin ko bayan ta tafi ba za ta cigaba da damuwa ko kuka ba, sannan ta riƙa cin abinci saboda lafiyanta da inganta abin da ke cikinta kuma ta yi mata alƙawarin duk za ta ji maganarta. Sannan ta umarce ta da duk abin da take so kar ta yi ma Baffa ko Ammah magana ta kirata ta sanar da ita, ita kuma ta yi mata alƙawarin komai take so in dai bai fi karfinta ba za ta yi mata. Ranar Jumma'a da misalin ƙarfe goma na safe jirgin da Mami ta shiga ya ɗaga zuwa Kaduna. Abdullahi ne ma ya tuƙa ta zuwa filin jirgin, bayan tafiyarta Ummu ta yi ta kuka ba wanda ya hana ta kowa ya san akwai shaƙuwa mai tsanani tsakaninta da Mami, balle itama Mamin lokacin da za su yi sallama har tana sharan ƙwalla kamar kar ta tafi haka take ji. Bayan tafiyar Mami kamar Ummu ta saduda sai kuma ta koma gidan jiya, ita kenan sai kwanciya tana kuka ba ta cin abinci sai Ammah ta shigo ta yi magana ta tsakura kaɗan, ko Baffa in ya tsaya mata ko kuma ta ji zuwan Hamma Abdulrrahman, ga ta da juna biyu amma ba ta taɓa cewa yau ga abin da take sha'awa ba ko Ammah ta tambayeta ba ta magana sai ta ce komai aka ba ta za ta ci, ita a ganinta ba ta da wani sauran zaɓi kuma a rayuwarta tunda Habib ya sake ta kamar tara sa dukkan wata damarta ne. Koda Baɗɗo ta koma gida saboda makaranta tana yawan leƙewa duba Ummu Salma, wata rana ma in ta yi dare nan take kwana da safe ta wuce makarantan daga nan haka ma Ummin ikki koda yaushe tana kan hanyar zuwa domin duba Ummu, kuma in dai ta zo sai ta zaunar da ita tana yi mata nasihan haƙuri da ɗaukan kaddara zuwa lokacin tuni Ummu Salma ta yarda da kaddaran Habib ya sake ta amma ta kasa gasgasta kaddaran cewa ya rabu da ita har abada, gani take yi zai zo gare ta ko da take gida zai dawo gare ta, ta kasa ba ma zuciyarta hakuri da fahimtar cewa Habib ya yi mata nisa har lokacin ba ta sare ba, saboda tana son shi duk abubuwan nan da suka faru ba ta jin haushin shi sai ma soyayarsa dake sake kassara tunaninta kuma ko yanzu ya dawo gare ta, za ta iya yin komai domin itama ta koma gare shi. Habib kaɗai ta sani shi ne fa Duniyarta ya za a yi ta fara yin wata sabuwar rayuwar da ba shi a cikin ta. Gaskiyan da Ummu Salma ta kasa karɓa kenan gani take yi ba ta da wani sauran jin daɗi kuma tunda dai ba tare da Habib, ta lamkaya jin daɗin ta da samun komai na duniya a lokacin da take Matar Habib ba a yanzu da ta ƙare ba ta da komai ba. Tafiyar Mami da kwana goma sai ga Shamsiya afufujan tana kuka wiwi tana faɗin ita ba ta san abin da ke faruwa ba kenan ta yi tafiya zuwa Taraba gidan Sister ɗin ta, tun a can take faman kiran wayar Ummu a kashe kuma ba ta ganin ta a chart hankalinta ya tashi shi ne fa ta kira Baɗɗo ita ke faɗa mata wannan mugun labarin mara daɗi. "Bestie Habib ya sake ni." Ummu ta faɗa hawaye suna kece mata. "Ya sake ni Bestie." Ta sake faɗa tana mai kwantar da kanta saman cinyar Shamsiya dake zaune a saman gadon ɗakin da Ummu Salma take. "Na yi komai domin na tsira da aurena amma na kasa Bestie. Na kasa na faɗi.." Take faɗa tana wani irin gunjin kuka Shamsiya na ɗan bubbuga bayanta alamun lallashi take faɗin" Sai da na ce ki bi umarninsa Bestie amma kika yi taurin kai, da a ce kin zubar da cikin da yanzu kina gidan mijin ki, da yanzu ba ki zauna kina kukan nadama da dana sani ba." Take faɗa tana sharan kwalla itama, amma ba ta fasa faɗa ma Ummu ita ce ke da laifi ba, ita ba ta ganin laifin Habib a wannan maganar. "Bestie su fa iyayenmu tunanin su da namu ba ɗaya ba ne. Ban so ki kawo maganar gida ba, da kawai kin bi umarninsa kin zubar da cikin da yau duk ba a yi haka ba. Da kina can gidan mijin ki ba wanda ya san abin da ya faru." "Besite ko na zubar da cikin nan ko ban zubar ba Habib ya gama samun duk abin da yake so a wajena. Ba zai ɗaga mini kafa ba sai ya sake ni, da man kawai cikin ya zo a gabar da ya fake da dalilin shi ne, amma ba ya so na ya ma faɗa mini da bakin shi." Ummu ta faɗa tana cigaba da kukanta. "Ni fa ban yarda Habib ba ya son ki ba Bestie kawai kin ɓata masa rai ne da kuma shigowar su Baffa cikin maganar, amma ke kanki kin san cewa Habib na son ki Bestie." Shuru kawai Ummu ta yi mata, ba za ta gane ba ne, amma tunda har ita ta furta mata cewa Habib ba ya sonta to ai ya kamata ta yarda da ita. Itama da fari ba ta gasgasta ba amma daga baya da abubuwa suka yi ta faruwa dole ta aminta ta kuma gasgasta cewa Habib ba ya sonta , sannan saboda jikinta ya aureta kuma tun da ya gama biyan bukatar shi ai ba ta da wani amfani a wajen shi kamar yadda ta faɗa. "Shima ya yi kuskure me ya sa ya yi saki uku? Ai da ya yi ɗaya ne in iyaye suka shiga ciki sai a gyara lamarin. Ni fa har kiran shi na yi ta yi bai amsa kirana ba daga karshe ma kamar ya rufe ni ne kwata-kwata bana samun shi." Ta faɗa tana kallon Ummu Salma wacce ta miƙe daga kwancen da take, tana kallon Shamsiya da mamakin maganganun ta. Ta buɗe baki za ta yi magana kenan Shamsiya ta katse ta. "Ban ji dadin faruwan wannan lamarin ba Bestie. Na yi miki kaico domin da wahala ki samu kamar Habib. Ba ma tamtama ba za ki taɓa samun kamar sa ba har Abada Ummu Salma." "Za ta samu, za ta samu wanda ya fi shi komai da komai in sha Allahu." Suka ji magana a bayansu, suna juyawa gabaɗayansu suka ga Ammah ta shigo da kulan abinci ba da niyyar laɓe ba ne, amma ta daɗe tsaye a kofar ɗakin tana jin irin maganganun da Shamsiyan ke faɗi. "Ammah." Shamsiyan ta faɗa lokaci ɗaya tana saukowa daga saman gadon. Kulan abincin hannun Ammah ta amsa tana faɗin" Sannu da aiki Ammah." Ta sakar mata lokaci ɗaya tana cewa" Yauwa." Sai kuma ta kalli Shamsiya da take sauke kulan a saman side drower ɗin gadon tana mai ɗagowa, Ummu Salma ta kalla ita kuma tana ta kuka har da sauti. "Shamsiya." Ammah ta kira sunanta sai ta ɗago tana amswa cikin ladabi. "Don Allah ki daina tuna ma Auta da wani Habibu. Ba shi da wata amfani yanzu a sabuwar rayuwarta. A matsayin ki na ƙawarta ki lallasheta ne ba wai ki zaunar da ita kina nuna mata kamar ta ci baya ba. Habibu da man bai cancanta da zamowa abokin rayuwar Auta ba, kaddara ce ta aura mata shi kuma yanzu ta raba su. Ina mai baki tabbacin shi ne ya yi asara shi ne kuma har abada ba zai taɓa samun madadin ta ba, amma a gare ta za ta samu ire-iren su masu tarin yawan da sai ta zaɓa ma, kuma ni na faɗa miki Ummu Salma za ta sake yin farinciki fiye da irin farincikin da ta yi a farkon rayuwarta da Habibu." Ammah ta gama faɗa tana mai kallon Shamsiya, ta ma ɗan kausasa maganganunta, amma har cewar da ta yi da Ummu Salma ta bi umarninsa ta zubar da ciki duk ta ji, kamar a mganganunta ita ba laifin Habibu take gani ba, laifin Ummu ne ita da su iyayenta. Ai ko ba ta san Ummu bai kamata ta faɗi haka ba, ballanta Ummun ce silan da ya sa ta ma san Habibun gabaɗaya. "Haka ne, in sha Alkahu Ammah ba zan sake tayar mata da maganarsa ba." Shamsiya ta faɗa kanta na ƙasa cikin jin nauyin Ammah. "Yauwa na gode da kika fahimce ni, ga abinci nan bari na kawo muku farantai da ruwa." Tana gama faɗin haka ta juya har za ta fita sai kuma ta sake juyowa tana kallon Shamsiya. Duk da suke ƙawance da Autar ta ba ta taɓa jin ba ta natsu da ita ba sai yau, haka kurum yau sai ta ji maganganunta sun bambamta da yanayinta. "Maganar zubar da ciki kuma." Sai ta dakata tana kallon Shamsiya da ta yi tsuru tsuru. Ummu ma ta daina kuka tana kallon Ammah ta san halin ta ba ta ɗaukan wani reni ko sakarci ko waye kuwa sai ta faɗa masa gaskiya ita kanta ta ji maganganun Bestie yau sun ɗan yi tsauri amma ba ta ga laifinta ba yanayi ne da tsarin gidan da ta taso kowa abin da ya ga dama yake yi babu takura. "Na jinjina ma Auta da ta yi wannan jarumtar. Har yau mu iyayenta ba ma cikin nadaman dawo mana gida da ta yi da ciki a jikinta. Tunda dai cikin  kowa ya san uban shi to ai an gama magana. Da Ummu Salma ta tashi a ranar lahira cikin waɗanda Allah zai tuhuma da kashe rai gwara ta mutu wajen haihuwa a tashe ta a matsayin shahidiya." Ammah na gama faɗin haka ta fice daga ɗakin ta bar Shamsiya da ajiyar zuciya. "Kamar Ammah ba ta fahimce ni ba Bestie" Ta faɗa lokaci ɗaya tana zama a gefen gadon tana kuma kallon Ummu Salma. "Ki yi hakuri. Watakila ba ta fahimci maganarki ba ne" Ummu ta faɗa cikin wani irin amon mai sauti mai cike da rauni. Sai Shamsiya ta yi mirmishi kafin ta ce" Ba damuwa. Na san anan gaba za ta fahimci in da maganganuna suka dosa." Ta faɗa  tana sake kallon Ummu cikin mirmishin da ya kasa ɓacewa a saman fuskarta Sai ga Ammah ta dawo ɗakin ɗauke da filet da cokula guda biyu sai ruwan gora guda biyu ta kawo ta ajiye tana faɗin Shamsiya ta sauko ta zuba musu. "Sannan ki matsa ma ƙawar ta ki ta ci abinci." "To Ammah." Ta faɗa cikin ladabi, kuma ta yi abin da ta saka ta,ta matsa ma Ummu ta ci abinci taliya da miyar jajjage ne. Ummu ta ji daɗin taliyan nan saboda miyan na ta ƙamshin kayan kamshi ta kuma soyu sosai, ga cikin ta ya cika amma bakin ta bai daina son ci ba sai ta koma tana lasan miyan saboda ta yi mata daɗi a bakin ta. "Bestie ki bar lasan miyan nan kar ki yi amai ko cikin ki ya lalace fa." Shamsiya ta faɗa tana kallon Ummu Salma na ta lasan miya "Bar ni na sha, na ji daɗinta ne sosai " Jin haka yasa sai ta ƙyale ta, sai da ta shanye duka miyan da ta rage kuma Allah ya taimake ta, ba ta yi amai ba. Shamsiya na gidan har yamma sai gabda kiran mangariba ta tafi lokacin Baffa ya dawo tun safe daman suka fita da Abdullahi har ɗaki Ummu ta kai Shamsiya ta duƙa ta gaishe shi. "Lafiya lau Shamsiya, ya kwana biyu ya makaranta? Ta amsa da lafiya lau mahaifinta ya tambaya Dr. Nura babban ma'aikaci ne a minitary of Education na Jahar Adamawa. "Ashe kuma abin da ya faru da ƙawata kenan? "Wallahi Kuwa Shamsiya " Baffa ya ba ta amsa. "Allah ya kyauta na gaba. Allah ya saka mata." Baffa ya amsa da Amin yana faɗin" Ya za a yi da lamarin da Ubangiji ya hukunta kenan. Zai wuce in sha Allahu." Da za ta tafi ya yi ta mata addu'an Allah ya kawo mata miji na gari mai albarka nagartattace. Domin duk wanda ya san Ummu Salma a dangi ya san ta da ƙawarta Shamsiya tun suna yara. Kamar yadda aka san Shamsiya a gidan su Ummu haka aka san Ummu Salma a gidan su Shamsiya duk da mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama matar mahaifinta da suke kira Anty ke riƙonta. Da za ta tafi bayan ta yi ma Ammah sallama ta ce ta gaida mutanen gidan. "Ammah don Allah ki yi haƙuri da maganganun da na yi ɗazu ba ki fahimce ni ba ne ba da wata manufa na yi maganar ba na damu da abin da ya faru da Ummu Salma sosai Ammah." Shamsiya ta faɗa bayan ta duƙa har kasa a gaban Ammah. Ammah ta yi mirmishin su manya kafin ta ce" Kar ki damu na fahimce ki. Ki gaida gida mun gode." Har haraba Ummu Salma ta raka ta. Direban gidan su da ya saba kawo ta shi ne ya zo ɗaukan ta. Sai da suka tafi sannan Ummu dawo cikin gida ta iske Ammah na zaune a falonta kamar yadda suka bar ta. "Har ta tafi? Ammah ta tambaya tana kallon Autar na ta "E ta tafi Ammah." Ta faɗa a sanyaye cikin dashewar murya kamar ba ta son magana. Sai Ammah ta ɗan gyaɗa kanta amma ba ta yi magana ba. Shuru na wani lokaci Ummu na tsaye ita ba ta koma ɗaki ba sannan ita ba ta zauna ba Ammah na lura da ita amma ba ta nuna alamun ta fahimci tsayuwarta a wajen ba sai ma ta yi kamar hankalinta na wajen tibin da yake ta ɓaɓatu. Nan ko tana lura da duk motsin Ummun, tana kare mata kallo daga tsaye har cikinta ga shi nan ya fara turowa ta cikin doguwar rigar dake jikinta amma fa Ummu ta zube ta rame duk ta lalace kullum sai jan fuska da kumburarrun idanuwana saboda kuka, tausayinta take ji in ta kalleta sai ta tsine ma Habibu tsinuwar da ba ta so ya koma ga Allah bai ga sakayya tun a duniya ba. "Ammah." Ummu Salma ta kira sunan Ammah, ba ta amsa ba amma ta ɗago tana kallon ta. Sai kuma ta yi shuru ta kasa magana. "Me ya faru? Ammah ta tambaya tana mai tsare ta da idanuwanta lura da cewa kamar akwai magana a bakin ta. "Da ma Ammah.." Sai ta yi shuru ta kasa mgana. "Dama mene ne? Wani abu kike so? Ammah ta tambayeta cikin kulawa. "Aa dama mganar da kika ji Shamsiya na yi ne." "Uhm sai aka yi ya ya? Ammah ta faɗa har lokacin ba ta daina kallon ta ba. Sai Ummu ta daburce kafin ta fara mgana tana in da in da. "Da ma, zan ce ne kar ki ji haushin ta, ba da wata manufa ta faɗi haka ba." "Madallah." Ammah ta yi saurin katse Ummu Salma saboda ba ta son ma tana tuna mganganun yarinyar suna kona mata rai, suna sakawa tana jin kamar yarinyar za ta fita daga zuciyarta. Ta so ma ta ce mata in saboda su ko Ummu take kiran Habibu to kar ta sake sai kuma ta ga kamar ta yi tsauri da yawa shi ya sa ba ta yi maganar ba, amma sam maganganun yarinyar ba tausayawa ga halin Ummu ke ciki sam. Ummu Salma ta gaji da tsayuwa, ganin Ammah ta yi mata banza daga ƙarshe ma cikin ɗakinta ta shiga ta ce za ta yi salla dole itama ta koma ciki ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Bayan ta idar sai ga Baffa da Hamma Saddam sun shigo falon Ammah, sai ta fita falon ta duƙa ta gaishe da Baffan tun da tun safe sai yanzu suka sake samun zama "Auta ya karfin jikin? Kanta na ƙasa tana sanye da hijabinta dogo da ta yi salla da shi ta amsa cikin sanyin murya. "Na ji sauƙi Baffa." "Kin tabbata ba in da ke yi miki ciwo? Sai ta gyaɗa kanta sannan ta amsa da cewa ba in da ke yi mata ciwo. "To Baffa ka tambayeta tana cin abinci? Hamma Saddam ya faɗa yana yar dariya, da a baya ne harara zai sha a wajen Ummun amma yau kallon shi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba. "Tana ci mana ko Auta? Ya tambaya yana kallon ta. "Ina ci Baffa, yau ma ba ka ga taliyan da na ci ba." Ta faɗa da ɗan mirmishi. Sai ta ga Baffa na dariyan jin daɗi da man abin da take son gani kenan. "Madalla da Auta. Sannun kin ji? Allah ya raba ki da cikin jikin ki lafiya." Kanta na ƙasa ta amsa da Amin a cikin zuciyarta, sai dai idanuwanta sun cika da kwallar tausayin kanta da na iyayenta. "To gwara dai ki riƙa ci Ummu ko za ki yi kumari, kin gan ki kuwa? Kin ga ƙasusuwan da ke wuyan ki kuwa? Ya faɗa yana yar dariya cikin zolaya sai a lokacin ta ɗan murmusa kanta na ƙasa. "Kyale shi Auta. Za ki yi kiba har sai ya ce ki bar ta yi yawa." Ita dai kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabinta. Baffa da Hamma Saddam suna ta hiran su, lokaci bayan lokaci suna ɗan sako ta a ciki koda ba za ta yi magana ba har Ammah ta idar da salla ta fito suka cigaba da hiran tare. "Yaushe hutun na ku zai ƙare ne Saddam? Baffa ya tambaye shi, kai tsaye ya ce sati na sama za su koma zai bari sai upper week sannan zai koma makaranta. Baffa da Ammah suka yi masa fatan alherin da suka saba a koda yaushe suna nan zaune suna hira har aka kira sallar isha'i Baffa da Saddam suka tafi masallaci itama Ammah ta shiga ciki domin ta gabatar da na ta, sai ita ma Ummu Salma ta tashi ta koma ciki tana da alwalanta ta tayar da salla. Bayan ta idar ta fita tsakar gida zuwa kitchen ta zubo taliya ta ciko miya saboda cikinta kamar an yi yasa yanzu tana yawan jin yunwa sosai ba kamar baya ba. Tas kuma ta cinye tana suɗan kwano, har Hamma Saddam na yi mata dariya Baffa ya ce in bai isheta ba ta je ta ƙaro ta ce ta koshi da yake a falon Ammah ta zauna tana cin taliya su kuma suna dawowa masallaci nan suka sake yada zango.   Har wajen goma na dare tana falon tare da su Baffa suna ta hira, ita dai ba ta magana amma kuma zama cikin su yana rage mata damuwa da shiga tunani da ɗaki take shigewa zuwan Mami ne yasa dolenta ta fara fitowa falo. Sai da ta fara hamma wajen sha ɗaya saura na dare sannan Baffa ya ce ta je ta kwanta Hamma Saddam ma ya yi musu sai da safe ya wuce ɗakin sa. Ummu kuma bakin ta kawai ta wanke ta sha magungunanta ta kwanta ba daɗewa sai barci. Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi. A bangaren Ummu Salma rayuwa ba daɗi amma tunda ita musulma ce ta yarda da kaddara kuma tunda tana da rai da lafiya dole za ta cigaba da rayuwa a hakan nan, ta ɗan rage kuka yanzu amma duk lokacin da ta tuna sai ta koka ita kaɗai a ɗaki ta yi kukanta har sai ta ƙoshi sannan ta share hawayenta ta dangana tunda ba ita isa ta mayar da hannun agogo baya ba. Mai afkuwa ta afku ba ta kuma da yadda za ta yi ta gyara abubuwan da suka riga suka lalace tun daga farko. Har yau kuma Ummu ba ta bi ta kan wayarta ba, tana nan a kashe a cikin kayanta. Duk wanda zai yi magana da ita sai dai ta wayar Ammah. Baɗɗo ce ta ce ta ɗauko wayar ta dawo amfani da ita wataƙila za ta deɓe mata kewa, amma ina ba za ta iya sake amfani da wannan wayar ba matuƙar akwai abubuwa da dama da za su iya tuna mata da Habib da irin rayuwar da suka yi mai daɗi a baya shi ya sa ba ta jin za ta iya amfani da wayar a yanzu in ma za ta yi amfani da waya sai dai sabuwar waya da sabon layin da ba zai tuna mata da komai ba. In ta zauna tana tunanin farkon rayuwarta da Habib har zuwa ranar ƙarshe da komai ya ƙare. Sai ta ji da man ace ba ta san shi ba, domin sanin shi bai ƙare rayuwarta da komai ba sai ci baya. Ya shigo rayuwarta domin ya lalata mata gobenta kuma ya yi nasara. me take yi haka? me ya sa ta kasa tsanar Habib? me ya sa ta kasa mantawa da shi? me ya rage mata, ba ta da komai domin bai bar ta ba sai da ya ƙwace duka martabanta ya lalata mata rayuwarta ya juya baya ga gudan jinin su? me ya sa ba za ta yanke tsammani ba, ba ta da wani abu da zai sake jan hankalin wani namiji a kanta HABIB ya riga da ya lalata duk wani ƙwanjinta akan ko wani namiji a duniyar nan. **** * SATURDAY:MURIVILL HOTEL YOLA, ADAMAWA OFF GIREI ROAD. ROOM:226. *8:21Pm* Habib ne tsaye a gaban madubin dake ɗakin Hotel ɗin da ya zama gidan shi a halin yanzu tun bayan rabuwar su da Ummu Salma. Turare yake fesawa bayan ya gama ya ɗauko wata hula baƙar dara ya ɗora saman sumar kansa da ta sha gyara tunda ya ɗan tara suma. Jikinsa kuma wata farar shadda ce tana maiƙo da yarari daga ganin ta ma sabuwa ce yau ya taɓa sakata saboda yadda take maiƙon sabunta. Kallon kansa kawai yake yi a madubi yana mirmishi shi kaɗai saboda yau ranar ta musamman ce a gare shi da abar ƙaunarsa. Yau ne rana ta farko da za ta gabatar da shi a wajen mahaifinta a matsayin wanda take so kuma take mafarkin aura. Gabaɗaya jin sa yake kamar yana yawo a saman gajimare saboda tsabar farinciki. Ya saka kaya sama da kala goma ba su dace da ranar yau ba, ga su nan duk ya zube su a saman gadon dakyar ya samu waɗanan na jikinsa suka dace da yanayin yau ɗin.   Agogon fata baki ya saka a tsitsiyan hannunshi na hagu yana sake kallon kanshi a madubi yana sake yin sakin ɗan mirmishi. Ya ɗauko wani bakin booth ɗin takalmi yana sakawa kenan aka kira wayarsa tun kafin ya duba ya san ita ce domin sun yi magana da ita bayan ya fito wanka ya tabbatar mata da mintina goma zai gama shiryawa ya fito. Sai da ya gama saka takalmin sannan ya ɗauki wayar dake gaban madubin farinciki ya sake dabaibaye shi ganin ita ce ta kira shi. "Gani nan zuwa Sweety." Ya faɗa cikin wani amo bayan ya ɗaga kiran. "Kar ka bar ni na saƙe wajen jiran ka Habib." Daga can bangaren ta faɗa cikin muryan shagwaɓa. "Gani nan zuwa In sha Allahu." Daga haka suka yi sallama, suna katse wayar ya turata cikin aljihun wandonsa tare da wallet ɗinsa bai tsaya kwashe kayan da ya watsar a tsakiyar ɗakin ba ya suri key ɗin motar shi da na ɗakin ya fice bayan ya rufe ƙofar ya tura komai cikin aljihun wandon sa ya sauka ƙasa zuwa haraban hotel ɗin suna ta gaisawa da ma'aikatan wajen a wattani biyun da ya kwashe a hotel ɗin ya saba da duka ma'aikatan wajen ba laifi, Tun ballanta ƴan ƙananun kyatttukan da yake yi musu, yau ma saboda yau ɗin rana ce ta musamman a wajen shi. motarsa ya shiga da yau ya kaita wanki ta yi fess yadda motar take  fess shima haka yake fes, ya fiddo kuɗin sabbi yan ɗari biyar biyar ya kira wani ma'aikacin hotel ɗin yana daga cikin masu kula da tsaftan ɗakunan Hotel ɗin sunan su ɗaya shima Habibu sunan shi, kuma in dai ya ga Habib ya yi ta masa kirari kenan shi ya sa tasu ta zo ɗaya. Kuɗin sun kai 20k ya ba ma Habibu ya ce ya raba shi da sauran ma'aikatan gabaɗaya. Har ƙasa ya duka yana godiya lokaci ɗaya yana masa kirarin da ya saba. "Allah ya taimake ka ranka ya daɗe Allah ya ƙara arziƙi da wadata." Habib ya yi dariyan nishaɗi kafin ya ce" Amin Habibu na gode da addu'arka kamar ka san yau rana ce ta musamman a waje na." "Allah ya kara maka farinciki da wadata Megida." Ya riƙa amsawa da Amin kafin ya rufo motar ya daidaita zaman shi sannan ya tayar da motar ya yi riverse ya yi hon megadi ya buɗe masa get ya fita, yana tafe yana jin nishaɗi har redion motar ya kunna da wakar Auta waziri yana tafe yana kaɗa kai kamar wani kadangare. Tun a daran ranar da ya saki Ummu Salma bai yi barci ba sai da ya gama haɗa dukkan abin da yasan mallakan shi ne gari na wayewa karfe shidda na safe ya kwashe komai zuwa mota ya bar gidan. Yadda suka rabu haka yake so alaƙarsu ta ƙare na har abada. Hotel ya je ya kama ya saka kayan shi a ciki, tunda gidansu yanzu ba shi da mazauni kuma ba shi da in da zai je ya zauna, gidanshi da yake ginawa ba a gama ba, gidan da Ummu Salma ta yi ta mafarkin shi a matsayin ita ce za ta shige shi abin da ba ta sani ba bai kafa ginin gidan nan da sunan ta ba sannan zanen gidan ma ba zaɓin ta ba ne na masoyiyarsa ne da suka shirya sabuwar rayuwa tare, an kusa gama ginin gidan tunda yanzu tayels ake sakawa na ɗakuna da tiolets da an gama za a yi filista da fenti shike nan shi kuma a yadda yake so bikin shi kar ya wuce wata biyu saboda ya ƙosa ya mallaki masoyiyarsa sannan yana son ya samu natsuwa. Tunda har yau za ta gabatar da shi ga mahaifinta an gama mgana, da man a cikin wata ɗaya ta bayyana shi a wajen iyayenta da y'anuwanta mata a matsayin wanda take so yana zuwa gidan su zan ce yau ne za su haɗu da mahaifinta. Jin sa yake yi kamar sabon haihuwa saboda farinciki kamar bai taɓa aure ba. To kamar bai taɓa ba ne domin Ummu Salma amfani ta yi masa kuma tunda ta gama amfaninta ya fitar da ita daga rayuwarsa, sai yanzu yake jin kansa sakayau kamar bai da wata damuwa. Duk da ya ɗan fuskanci ɓacin rai daga wajen Gwaggo da Abba Alhaji Sheriff amma duk ya jure. Gwaggo haka ta yi ta masa faɗa bayan an ɗan lafa da faruwan lamarin ya je gidan, ba shi da masaniya amma ya san labarin rabuwansa da Ummu Salma zai je musu kuma zargin shi ya tabbata. Mahaifinsa dake kwance haka ya riƙa son ya yi magana da shi amma ya kasa sai kuka hawaye na ziraro masa ta gefe da gefen idanuwansa. Ransa ya ɓaci ya yi baƙin ciki sannan ya sake jin tsanar Ummu Salma a cikin zuciyarsa. Sanadiyarta iyayensa sun yi fushi da shi. Gwaggo ma sai da ta yi kwanaki ba ta amsa gaisuwarsa har ƴan'uwansa mata wasu sun nuna ba su ji daɗin abin da ya aikata ba shi kuma sai ya ce ai ita ce ta ci ƙwalan shi ta ce in ya cika haihuwan uwarsa da ubansa ya saketa shi ne ya sake ta. Wasu dai sun yarda wasu kuma ba su aminta da maganganunsa ba, kamar Gwaggo da jinsa kawai take yi ta san ya faɗa ne domin ya kare kansa. Haka ya yi ta zuwa Gidan Alhaji Sheriff kusan sau uku amma ba ya ganin shi ya ƙi bari ma su haɗu kwata-kwata, amma duk da haka bai haƙura ba sai ya bi ta hannun Baba Usman da lallashi da daɗin baki ya samu shi ya saurare shi, duk ya ɓata ma Ummu Salma suna a idanuwansa da cewa ba ta da tarbiya rashin kunya take yi masa shi ya sa ya sake ta kuma ma ita ce ta neme sakin, Baba Usman ne ya shiga tsakiya ya sulhutansu da Alhaji Sheriff ya kuma haɗa su waje ɗaya suka yi magana. Habib ya duka yana ta bashi haƙuri Baba Usman na kora wajibin cewa yarinyar ce ashe ta ce sai ya sake ta shi dai Alhaji Sheriff jin su kawai yake yi yasan ƙarya Habibu yake yi ya dai faɗa ne domin kawai ya samu hanyar kare kan shi. "Koma mene ne wannan ya zama tarihi tunda ya sake ta ta koma gidansu magana ta kare. Habibu kai ba yaro ba ne daidai gwargwado kana da ilimin ka, ka san abu mai kyau da aka sin shi. To ka sani in har kai ne ka yi zalunci Allah ba zai barka ba, in ma ita ce ta zalunce ka duk Ubangiji na gani kuma zai yi ma duk wanda aka zalunta sakayya" Abin da ya faɗa masa kenan a lokacin da ya sake rankwafa yana sake bashi haƙuri sai ya ɗaga masa hannu yana sake faɗin. "Ni fa ba ka yi mini komai ba Habibu. Ka je kawai Allah ya kyauta na gaba." Duk da haka bai haƙura ba yana zuwa gidan shi sannan yana kiran shi a waya har dai ya samu ya ɗan sauko daga fushin da yake yi da shi, shi da man burin shi kenan saboda nan da lokaci kaɗan amfanin su zai ta shi kuma in babu su ba zai samu cikar burin shi ba shi ya sa bai gaji ba sannan bai sare ba, Baba Usman ma duk ya siye shi da kuɗi sannan haka ya yi siyayyan kayan abinci ya kai masa, gidansu ma duk ya kashe bakin su da kuɗi suma ɗin kayan abinci ya siya musu duk da daman ya saba yi, yan'uwansa mata kuma duk ya kashe bakin su da kyauttuka har Gwaggo ma bakin ta ya yi shuru shike nan babin Ummu Salma ya kare a gidansu da zuru'an su gabaɗaya yanzu ne zai sake buɗe ma rayuwarsa wani sabon shafi. Kai tsaye anguwar Barraks road ya nufa, ya yi parking ɗin motarsa a wani babban gidan bene mai makeken bakin get. Bai yi hon ba sai da ta ya kira ta ya ce ga shi nan a ƙofar gida sai ta ce kawai ya shigo gata nan fitowa. Sai a lokacin ya yi hon megadi ya leƙo shi kuma sai ya zuge gilsshin bangaren  da yake zaune  ya gane shi baƙon gidan ne tunda yana zuwa kuma ya san shi, har ma wani lokacin yana yi masa kyauta "Alhaji barka da zuwa." Bafullatanin maigadin ya faɗa da hausar sa irin ta fulani. "Yauwa." Habib ya faɗa yana mirmishi, get ɗin ya ruga ya buɗe masa shi kuma ya sulala motar tasa zuwa cikin haraban gidan da ga motoci nan guda uku a haraban gidan, alamun megidan yana ciki tunda yaran gidan ba sa tuka kansu a mota sai in kin yi aure baban zai ba ki mota amma in dai kina gida direba ne zai kai ki duk in da za ki je, kuma ya koma ya dawo da ke. Habib ya daɗe yana tunanin kamar gidan da ya zo sun fi ƙarfin shi amma in ya tuna yadda soyayyar su ta fara sai ya ji ya samu ƙarfin gwiwa da yadda abar kaunarsa ta ba shi tabbacin duk abin da suke so shi mahaifinsu ke so, kuma shi ya yarda da kan shi duk da shi ɗan talakawa ne amma yana da ilimi da dukkan nagartan da duk in da ya je za a ba shi aure. Bayan ya daidaita motarsa a haraban gidan ya ɗau wayarsa ya yi kira. "Gani na iso haraba." Ya faɗa yana mirmishi. Daga can bangaren aka ce. "Na ga zuwan ka, ina sama ina hangen ka a cikin mota." Jin abin da ta ce ne ya sa ya ɗaga kai yana kallon saman, dai dai lokacin da aka saki labule aka juya. Mirmishi ya yi zuciyarsa har wani rawa rawa take yi saboda yadda yake daraja wannan ranar. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t *15* *DUALA ROAD. APAPA LAGOS NIGERIA* *NO:447.* Teusday, 2:30pm. Wata baƙar mota ƙiran TOYOTA(PRIUS) ta fito daga General Hospital dake Apapa Lagos (C9R9+QG7 Abaraham adesanya road) da misalin ƙarfe biyu da rabi na ranar talata gabaɗaya gilasan motan tintec ne shi ya sa ba lalle na waje ya iya ganin na ciki ba. Gudu motar ta yi ta shararawa a kan shararen titunan da ke Apapa na garin Lagos ba daɗewa sai ga shi  motar ta iso anguwan Duala road a bakin wani katafaren gida mai blue ɗin get lambar gidan 447. Hon motar ta yi ba ɓata lokaci kawai get ɗin gidan ya wangale motar ta sulala cikin haraban gidan, kusa da wata mota itama kirar toyota amma camry dake fake a haraban gidan motar ta tsaya. Daga can cikin parking space kuma akwai wata ɓakar RAVA ita ma ƙirar Toyota. Yanayin parking ɗin da ta yi ba ta daidaita tsayuwar motar ba Da gudu bayarben megadin tare da wani matashi suka rugo a guje har suna bangazan juna wajen buɗe murfin motan sannan bayan sun buɗe suka rankwafar da kawunansu a ƙasa a tare suka haɗa baki wajen faɗin. "Welcome Mah." Haka suke faɗa, kuma ba su daina faɗa ba, sannan wacce suke kira da Mah ɗin har a lokacin ba ta sauko daga motar ba, sai da tafi mintina goma sannan kafaarta ɗaya ta fara saukowa farar kafa da wani takalmi mai igiya baki hill mai tsini sannan ta sake sauko da ɗayan kafar nan ma sai da ta ɓata lokaci kafin jikinta da ita kanta su bayyana a waje. Farar mace ce doguwa mai kaurin jiki jikinta sanye da riga da wando suit na mata masu ruwan toka, wondon yana da buɗewa ta ƙasa, saman rigar jikinta rigan likitoci ne, a jikin ɗan wani anini da ke jikin rigan an rubuta DR. BILKISU BAYERO. Sannan kanta ta yane shi da wani baƙin mayafi mai santsi idanuwanta ɓoye cikin wani baƙin glass. Kyakyawa ce domin fuskarta doguwa ce ga dogon hancin ta har baƙa yanayin fuskarta ba wani fara'a, hannunta riƙe da jakarta na hannu ƙarama baka yatsunta sanye da zabban gold guda biyu masu kyau da tsari. Taku ta fara yi cikin taƙama da isa kamar yadda ya zame mata jiki da daɓi'a, ko kallon ma'aikatan da suke rankwafe suna yi mata sannu da zuwa ba ta yi ba ta yi wucewarta ta nufi wata ƙofa babba mai kyau da tsari sai da ta saka password sannan kofar ta buɗe ta shige kuma ta rufe kanta, sai da ta ɓace ma ganin su sannan Maigadi Baban Adila ya koma wajen aikin shi da sauri ya yin da James mai kula da tsaftan haraban gidan sannan kuma shi driver ne shi ke kai yara makaranta ko ya kaisu wajen wassani ko kuma in fita ya kama ma'aikatan gidan, Uwar ɗakin na su ba kodayaushe take yadda a tukata ba ita ke tuka kanta wani lokacin Megidan kuma ba mazauni ba ne, in ma ya dawo ba ya fita ko'ina in kuma fita ta kama shi ba na kusa ba sai dai na nesan da filin jirgi kawai ake kai shi. Shi ya tsaya ya shiga cikin motar ya gyara parking ɗin sannan ya ciro makullin ɗin lokaci ɗaya yana fitowa ya kuma rufe motar. Ita kuma tana shiga makeken falon gidan mai ɗauke da kayattatun kujeru saiti biyu, sallaman ma da ta yi a ciki- ciki ta yi amma ƙaran tsinin takalminta ya bayyana shigowarta falon yan aikin ta suka rugo zuwa gare ta. Sabuwa wata yar dattajiuwa ta karɓi jakar hannunta sannan ta duƙa tana faɗin" Barka da dawowa Uwar ɗakina." Hadiya kuma yar yarinya ce matashiya itama duƙawa ta yi tana faɗin" Barka da dawowa ranki ya daɗe." Ma'aikatan cikin gida huɗu ne Sabuwa da Hadiya daga masaautarsu ta taho da su tun auranta da Lamiɗo aka ba ta su, sai  Anitha da Debora anan garin ta ɗauke su, Anitha ce mai kula da Sultan da Beena duk abin da ya danganci abincin da za su ci, kwanciyar su ta shin su, aikin makaranta da shirya su komai da komai dai yana sarƙe a wuyan ta ne, Karatu na musamman ta yi akan sanin kula da yara. Ita kuma Debora mai kula da girkin gidan gabaɗaya cikakkiyar Chef ce da ta karanci nau'in girki a jami'a ita ce ke da alhakin kula da duka wani abinci a gidan. Sabuwa kuma amintattaciyar hidiman Dr. Balkisu ce, duk wani abu da ya shafe ta yana wuyan Sabuwa ne, gyaran ɗakin ta gyaran kayan ta, cin abincin ta da duk wani abu da za ta bukata Sabuwa ke kula da shi, ita kuma Hidaya ita ce mai kula da share share duka gidan da tsabtace ko'ina har ɗakin mai gidan ita ke da alhakin tsabtar gidan ko'ina ya yi kal yana tashin kamshi wannan nauyin yana wuyan ta ne. Har ta zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun falon ba ta amsa musu gaisuwar su ba. Debora ce ta ɗibo ruwa mai sanyi daga despenser a wani kofin tangaran mai kyau da tsada ta kuma ɗora shi saman wani kyakyawan faranti mai kyau ɗan caras da shi. Shi ta kawo mata bayan ta rankwafa ta miƙa mata tana faɗin" Welcome Mah." Sai da ta yi kamar ba za ta miƙo hannu ba sannan ta mika ta karɓa ta ɗan kurɓa kaɗan ta miƙa mata da sauri ta tashi cikin girmamawa ta bar falon. Da kai kawai ta amsa ma Hidaya da Anitha da ke faman gaishe ta sannan ta ɗaga musu hannu alamun su watse, ba sai ta yi magana ba zaman su da ita na tsawon shekaru uku ko sama da haka ba sai ta yi magana ba sun san abin da take nufi. Sabuwa ce kawai ta rage a wajen itama tana jiran uwar ɗakin nata ne, sai da ta gama zamanta shuru kawai idanuwanta a lumshe tana ɗan hutaawa sannan ta miƙe da sauri Sabuwa ta rigata mikewa ta yi gaba da sauri wani korido suka shiga, Sabuwa ta buɗe wata ƙofa tana biye da ita a baya suka bayyana a wani ƙaramin falo kayattace. Nan ɗin ma ba su tsaya ba wata ƙofa Sabuwa ta sake buɗewa sai ga su a wani babban bedroom mai ɗauke da gado wanda ya ji shimfiɗun alfarma da wawaken wardrope daƙin very neat,  sannan yana tashin wani ƙamshi mai daɗi ga wani sanyi sanyi mai shiga ƙashi yana saka natsuwa da jin daɗi. komai dai na cikin muhallinsa tana shigowa a gefen gado ta zauna lokaci ɗaya tana warware mayafin da ta yane kanta da shi, ita kuma Sabuwa sai ta isa ma'ajiyar jakunkunanta ga su nan a jikin wani ɗan katako dogo sama da guda ashirin ta ajiyeta a muhallinta sannan ta koma da sauri ta duka a gabanta ta cire mata takalmin kafar nata shima ta koma ta ajiye shi a wani ɗan dirowa mai faɗi in da takalmin suke a jere resas ba adadi ga su nan kala kala iya kallon ka har ka ɓace ƙirgawa. Sai da Sabuwa ta kwashe komai da Balkisu ta watsar a saman gadon mayafinta da jaket ɗinta tare da glass ɗin ido ta shiga clotheset ta mayar mata a jikin hanger sannan ta rankwafa tana faɗin" A fito lafiya Uwarɗakin" Ta faɗa cikin ladabi da kai ta ɗan amsa mata lokaci ɗaya tana ɗan mikar da kafafunta a saman tattausan cafet ɗin da ke malale a kasan Bedroom ɗin. Alamun gajiya a tare da ita har Sabuwa ta buɗe kofa za ta fice Balkisu ta kira sunanta a hankali. "Sabuwa." Da sauri ta juyo ta dawo da gudu ta duka a gabanta tana faɗin" Uwar ɗakina" Ta faɗa cikin ladabi da ƙaskantar da kai kallonta ta yi na wani lokaci idanuwanta manya suna mai lumshewa suna buɗewa cikin sanyin murya ta ce" Bai fito ba? Ta faɗa tana ɗan sauke kallon ta akan Sabuwa. "Bai fito ba, tunda kika fita bai fito ba Uwarɗakina." Sabuwa ta faɗa cikin ladabi, Balkisu ba ta bukatar ta yi magana ko hannu ta nuna sun san abin da take nufi Ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta ce" Na sallame ki Sabuwa zan huta" Ta faɗa cikin sanyin murya kasa ƙasa kamar ba ta son yin magana "To to a huta lafiya Uwar ɗakina." Tana gama faɗin haka ta miƙe da sauri ta fice lokaci ɗaya tana rufo ƙofar saboda Uwar ɗakin nata ba ta son sauti ko ƙara ko hayaniya hatta ƴa'ƴanta sun san yanayin gidan duk da suke yara suna da natsuwa sai gidan ya yini tsit ba ka cin motsin kowa, kowa na bangaren shi yana gudanar da rayuwarsa suma ɗin ma'aikatan gidan suna shashen su luf, sanin masu gidan duka ba sa son hayaniya sun fi son su ji ko'ina shuru. Bayan fitan Sabuwa ta daɗe zaune tana ɗan daidaita jikinta kafin ta miƙe tiolet ta shige  bayan mintina goma sai ga ta ta fito sanye da rigan wanka fara sama sama ta ɗan shafa lotion a saman fatarta wacce ke wani irin shining ds glowing na jin daɗi da hutu clotheset ɗin ta buɗe ta shiga ba daɗewa sai ga shi ta sake fitowa sanye da wani riga da wando pick, wando dogo ne ya na da ɗan faɗi ta kasa rigar ma haka ba ta kama ta ba amma kayan suna da laushi da ɗan shara shara tunda har ana iya ganin farin pant ɗin jikinta da brazeya ɗin da ta sanya. Gashin kanta a tsife yake yi ba ta da wani suma amma saboda yana shan gyara yana nan mai kyau da shi, ta ɗaure shi da band sannan ta saka wata hula pick tsakiya a buɗe daga saman ne an yi tuntu na kwalliya mai zanen heart. Ta manta da wayarta a jikin jakar da ta shigo da shi sai ta isa wajen kafafunta na lumshewa a cikin lausasan cafet ɗin da ke Bedroom ɗin mai buzu buzu, ta isa wajen jakar ta ɗauko a hankali ta ciro wayarta ƙiran Iphone 16, sannan ta sauke jakar a in da ta ɗauke ta. Kan makeken gadon da ke bedroom ɗin ta kwanta sannan ja jawo farin bargo mai laushi ta rufe kafafunta, ta ɗan duba wayar na wani lokaci kafin ta sauke ta a gefenta ta juya ta sake juyawa sannan idanuwanta suka fara lumshewa a hankali a hankali kafin barci mai nauyi ya ɗauke ta na gajiya domin tun safe yau take asibiti tana ganin patients. *** Ƙarfe 3:45pm Balkisu ta tashi daga barci, har an fara kiran salla a wasu masallatan dake kusa da su har da ma waɗanda ke nesa. Duk nauyin barcinta lokacin salla na yi kamar tana ji a jikinta za ta tashi. Shi ya sa in za a tambaye ta a zamanta da Lamiɗo na shekaru shidda wani hali mai kyau ta koya daga gare shi za ta ce tsaida salla a kan lokacin ta. Tunda take da Lamiɗo ba ta taɓa ganin lokacin salla ya wuce sa da gangan ba. Mutum ne mai kiyayewan lukatan salla duk abin da yake yi koma mene ne salla na gaba da komai, ta taɓa tambayan shi ya ya yake yi in lokacin salla ya shiga kuma sai aka yi rashin sa'a yana tuki a lokacin? sai ya ba ta amsa da cewa in ya zo bakin gaba zai tsaya ba zai cigaba da tafiya ba sai ya yi salla, ko ya san wannan ka'idar shi ne in dai a lokacin tukinsa ne. Tun ba ta saba ba har itama yanzu daɓi'an ya zame mata jiki, tana kokarin kiyayewa lukatan salla. Yanzu ma mika ta yi sannan ta sauko da fararen kafafunta daga saman gado lokaci ɗaya tana mikewa. Tiolet ta shiga ta dauro alwala sannan ta fito ta daidaici gabas ta shimfiɗa darduma babba a ɗan koridon cikin bedroom ɗin nata, ta ɗauki dogon hijabin da take salla da shi a goge a saman side drower ɗin gadon. bayan ta idar da sallar ta ɗan ɓata lokaci tana kirga yatsun hannunta kafin ta shafa adduar'ta a fuskarta lokaci ɗaya tana mikewa ta ninke darduman da hijabin jikinta ta mayar da su ma'ajiyar su. Wayarta ta ɗauka ta sake duba lokaci. Huɗu har da mintina goma, wani takalmi ta saka mai taushi na zaman cikin gida sannan ta buɗe kofar bedroom ta fita ba ta zauna a falon bangarenta ba sai ta fita can main falo in da ta iske Debora na faman kwashe lunch ɗin da ta dafa tun ɗazu amma daga matar gidan har Maigidan da ya dawo jiya ba su sauko ba, kuma a ƙa'ida ba za su ci ba sai dai a kwashe a sake jera Dinner wanda aka sake dafawa. Cikin ladabi Debora ta rankwafa tana yi ma Balkisu barka da fitowa cikin harshen turanci. Ba ta amsa ba sai da ta zauna saman kujera mai zaman mutum biyu. Sannan ta ɗaga mata hannu. Wayarta ta ɗauko tana ɗan dubawa ita kuma Debora ta gama kwashe komai zuwa katon kitchen din da ke can yamma da falon sannan ta dawo ta duka gaban Balkisu tana tambayanta ko akwai abin da take so cikin harshen turanci, domin gidan ba a cika yin hausa ba, matar gidan turanci take yi haka ma yaranta. In har ta yi hausa sai dai in za ta yi magana da Sabuwa ko Hidaya su da suke yan kauye ba arabi babu boko. Amma kaf ma'aikatan gidan masu ilimi ne, kamar yadda ma mallaka gidan suke da tarin ilimi da nasaba. "Coffea." Haka ta faɗa kamar bakinta na ciwo, in da sabo sun saba da yanayin ta. Gidan nan kamar wata masarauta ce ta yan boko domin sarauta da ji da kai tare da takama da ƙasaita masu gidan sun iya shi, to yar Sarki ce fa jinin sarauta a jininta yake yi, maigidan ma jinin sarauta ne, kamar ma ya fi matar gidan ji da sarauta komai na shi na dabam ne. Da sauri Debora ta koma kitchen ta haɗo mata coffea a cikin wani karamin jug mai kyau sannan ta ɗauko wani karamin faranti fari ta ɗora akai sannan ta kawo mata ta kuma jawo mata ƙaramin table din tangaran ɗin da ke falon ta ɗora komai a kai sannan ta duka ta zuba mata ta zuba kaɗan ta ji Balkisu ta ce " Is ok." A hankali. 'Yes Mah." Debora ta faɗa lokaci ɗaya tana mika mata, sai da ta yi sama da sakwan goma sannan ta miƙa dogon hannunta ta karɓa ta rike a hannunta amma hankalinta na wajen wayarta sannan duka kafafunta suna miƙe a saman kujeran da take zaune ne. Har Debora ta kwashe komai ta koma kitchen mug ɗin na hannun Balkisu ba ta fara sha ba sai can sama da minti uku sannan ta iya kai shi bakinta ta ɗan kurba sau ɗaya ta mayar da shi saman ɗan teburin gabanta ta ajiye ta cigaba da duba wayarta. Gidan ya yi wani irin shuru sai wucewar iskar A.C ko tibi ba a kunnawa a gidan yara ne kuma suna da shi a ɗakin su, suma ba sosai suke kallon ba in ma za su yi volume kaɗan ne ko na falo ba mai jiyowa, Balkisu ba ta son hayaniya shi ya sa duk abin da zai saka ta ta ji ta takura ba ta yin shi, to ita data ke ma kwana a gidan koda yaushe kenan ba maigidan da sai ya yi wattani biyu uku ba shi a gidan ba. Ta yi zaman sama da awa ɗaya a falon nan bayan Debora ba wanda ya sake giftaawa. Sau uku ta kurɓi coffea ɗin da aka kawo mata daga nan ba ta ƙara ba. Agogon wayarta ta duba biyar da mintina an kusa tashin su Sultan daga makaranta. Dan ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauko da ƙafafunta ta sauke su a saman wani cafet mai taushi da kyau a ido. James ba ya bukatar sai an tunasar da shi lokacin tashin su Sultan ya fi kowa sani tunda alhalin kai su da ɗauko su yana wuyansa ne, tana zaune ta ji an buɗe get an fita daga gidan ka'ida ne da wuri yake zuwa yana bakin makaranta yana jiran su za a tashe su sannan ya ɗaukosu su dawo gida. Karfe ,5:30pm na yamma ake tashin su kuma tun 7am suke tafiya makaranta tana haɗe da boko da islama ne mai suna AL.TASLEEM ISLAMIC SCHOOL. Suna karatu tun daga saturday har Wednesday. Thurday ne da Friday ba sa karatu. Miƙewa tsaye ta yi ɗauke da wayarta a hannunta sannan ta fara takawa cikin wani irin taku na ɗaya bayan ɗaya kamar ba za ta taka ƙasa ba, lokaci ɗaya ƙafafunta dake sanye cikin tattausan takalmi suna nitsewa cikin lallausan cafet ɗin daya malale falon gabaɗaya wata kofa ta nufa daga kudu, sai ka ma lura sosai sannan za ka fahimci akwai ƙofa a wajen tana zuwa ta buɗe a hankali ta shiga, sai ga ta a wani dogon korido tana zuwa karshen koridon sai ga wata ƙofa itama tana buɗewa ta shiga sai ga ta cikin wani falo mai girma da ya ji kayan alfarma sai dai falon ya yi duhu tunda gabaɗaya labulanyan falo da windows ɗin suna rufe ne, ba ka jin motsin komai a falon sai dai na sanyi-sanyi da ƙamshin turaren wuta mai shiga hanci sannan kuma mai sanyaya zuciya. Daga gabas da falon akwai wata ƙofa ita ta nufa ta ɗan tsaya sannan ta ɗan ƙwanƙwasa shuru ba wani motsi na wani lokaci sannan ta murɗa handel ɗin ta shiga cikin ɗakin. Bedroom ne shima kamar falon ya yi duhu dum, tunda shima duka windows ɗin a rufe suke sannan labulayan a sake suke. Tana tafiya takalminta na taka cafet din da ya malale bedroom ɗin idanuwanta na hango masa shi sambal cikin bargo, ba a ganin fuskarsa tunda ya yi kwanciyar gefen dama ne ya danne fuskarsa da filon da ya rumgume a hannun shi da shi. Har ta iso gaban shi bai sani ba domin barcin sa kawai yake yi, amma fa ko hucin numfashin sa ba ka ji hakan zai alamta maka ko barcinsa cikin natsuwa yake yi Ta ɗan jima tsaye tana kallon shi, kafin ta ɗan matsa baya ta isa jikin window ɗin ɗakin ta zage labule gefe da gefe sannan ta buɗe glass ɗin haske ya shigo. Kan drowers ɗin gefen gadon ta ɗau remot ta rage karfin A.C ɗin. Ta rasa yadda aka yi Lamiɗo ke son sanyi haka da yawa daga ɗan shigowarta ɗakin barcinsa sai da ta ji sanyin har kasusuwan jikinta. Shi fa ko hatta handel ɗin kofar ɗakin shi in ka taɓa sanyi ne ƙalau saboda ko yana nan ko baya nan  ba a kashe A.C ɗakin 24/7 cikin sanyi yake yi, ita ta yi ta cewa sanyin ya yi yawa amma shi haka yake so duk da bai taɓa faɗa mata yana son sanyi ba a zamansu na shidda biyar ta fahimci haka, in ta zo ta ga ya ƙure sanyin za ta ɗauka ta rage ba zai yi mata magana ba amma tana barin wajen zai ƙara karfin gudun sanyi, tun ba ta fahimta ba har ta gane, daga baya sai ta fahimci haka Allah ya yi sa yana son rayuwa cikin sanyi, in ta ma tuna shi da yake rayuwa a saman ruwa ya saba da sanyi ba lalle ya yi masa illa ko cutarwa ba. Har ta dawo ta zauna a gefen gadon saitin da kafafunsa ke shimfiɗe bai sani ba. Bargon ya ɗan yaye kafarsa doguwa fara sambal mai cike da gargasa mai yawa ta bayyana a waje, ɗan mirmishi ta yi har bakinta na matsowa wayarta ta ajiye a gefenta sannan ta saka taussaun hannayenta ta ɗago kafar tasa ta ɗora a saman cinyarta, lokaci ɗaya tana jan yatsun kafafunsa da suke wasu irin dogaye tafin kafarsa wani irin taushi kamar bai taɓa taka k Ƙasa ba saboda yadda suke wani ja ja da fari fari kal, haka kumbunansaa kamar kumba bai taɓa fitowa ba tsabar yadda suke tas da su. Har ta gama jan yatsun na shi kuma duka sun yi ƙara, ita haka kurum tana son kafafun Lamiɗo balle ma in ta yi ta jan 'yan yatsunsa suka yi ta ƙaran nan yana saka ta a cikin nishaɗi. Ɗayan ta jawo daga cikin bargo itama ta ɗaura a saman cinyarta itama kamar ɗayan haka ta yi mata amma ko motsi ma mallakin kafar bai yi ba duk da ta san zuwa yanzu ya san da wanzuwarta a ɗakin tunda ba shi da irin nauyin barcin nan. Gargasan kafarsa guda ɗaya ta ja da ƙarfi har sai da ta tsinke, hakan da ta yi ne ya sa ya ɗan motsa kafarsa guda ɗaya sai ta kalle shi da mirmishi a fuskarta kafin a hankali ta ce. "Ranka ya daɗe ka tashi haka nan yamma ta yi " Ta faɗa wani wani irin omo mai cike da aji da sanin ciwon kai Shuru kamar ma baya jin ta, domin bai kara motsawa ba "Tun jiya da daddare da ka shigo gidan nan kake barci har wayewar garin yau. Ba ka ci komai ba fa Ranka ya daɗe? Ta sake faɗa tana ɗan jan gargasan kafarsa guda ɗaya. Sakwan goma sannan ya iya motsawa daga kwanciyar lokaci ɗaya yana cire filon da ya rufe fuskar shi ya mayar da shi bayan shi, sannan ya miƙe a hankali kamar bayansa ya samu matssala bakinsa na ɗan motsi yana karanta adduar tashi daga barci, lokaci ɗaya kuma yana sauke kafafunsa daga saman cinyarta ya samar musu mazauni a saman lallausan cafet ɗin ɗakin. Kafin kuma da sauri ya saka hannu yana kare fuskarshi saboda hasken waje ya ɗan shigar masa ido. "Ni na buɗe windows saboda haske ya shigo kaɗan." Ta faɗa cikin sautin ta, akwai wuta amma ba ta kunna gulop ba sanin ba ya son haske sosai.  Miƙewa ta yi ta ɗuka a gaban shi hannu kawai ta ɗan zira kasan gadon sai ga shi ta jawo masa wani ttatausan takalmi na maza zuwa wajen kafafunsa. Ba musu ya zura dogayen kafafunsa a ciki sannan ya yunkura ya miƙe lokaci ɗaya itama tana miƙewa sai ga ta a gaban shi yar firit.  Kallon shi take yi tana mirmishi a fuskarta shima ya kalleta da idanuwansa masu ɗan girma kaɗan kafin ya ɗan rusuna su, mirmishi ya yi mata amma daga gefe da gefen bakin shi ne kawai ya ɗan motsa. Muhammad Nasiru Muhammad (Lamiɗo) Sannan kuma Yariman Daura, magajin mai Maimartaba Yarima mai jiran gado. Wani irin dogon namiji ne faffaɗa, ga tsaho ga jikin murjewa ta cikakkun maza. Lamiɗo na da tsawo sosai domin ko size ɗin takalminsa 45 ne, kuma wannan tsahon na zuru'ar sarkin Jafaru ne, sarki na 11 a tarihin masarautar Daura, shi ne asalin tsatson su har kawo yanzu. Su ke da wannan tsawon kamar ƙiran samudawan farko, sannan suna da girman jiki matansu da mazan su. To Lamiɗo haka yake har ma yafi mahaifinsa Maimartaba Alhaji Dr Nasiru Muhammad Daura cika ido da ƙwarjini. Ahalinsa na Daura ba su da hasken fata sosai amma shi Lamido fari ne jajir, saboda Mami farar bafullatana ce kyakyawa, a wajenta ya ɗauko dogon hanci amma fuskarsa tana da ɗan faɗi ita kuma ta mahaifinsa ce, amma sumar kansa mai santsi da cika ta Mami ce, da yake shi ma'abocin tara suma ne gashi nan sumar ta yi yawa ta kwanta luf tana shan gyara. Sannan bakin sa yana da ɗan faɗi kaɗan zagaye da sajensa da ya zagayo har gemunsa da ya yi ɗan tsawo. Lamiɗo tun yana saurayinsa yana son tara sumar kai da barin gemu har kuma yanzu bai sauka daga kan wannan daɓi'an nasa ba. Ko a yanzu ma gashi duk ya cika fuskarsa amma duk da haka kyawunsa da cikar zatinsa sun bayyana. Balle ma da ya fara tafiya ya bar gaban Balkisu cikin tafiyarsa ta gif gif ta cikkakun mazan duniya kallo ɗaya za ka yi masa ka shaida Muhammadu ɗan Nasiru da Fatima Sadauki ne, kuma jarumi ne yanayin sa irin na fusattatun maza ne giant masu mazantaka da ke dukan zuciyan duk wanda ya kalle su, jarumatar su ba ya ɓoyuwa, sannan suna iya rike numfashin wanda ya kalle su gaba da gaba na wani lokaci saboda ƙwarjini da haibar da baiwa ce Allah ya ba su, sannan yanayin su komai karatun mutum akan sanin hallayan ɗan adam baka isa ka fahimci yana yin su ba, ko ka ce ga abin da suke so ko ba sa so ba, irin su Lamiɗo sai zama ya haɗaku na shekaru masu yawa shi ne har za ka iya fahimtar lamuran rayuwarsu, amma ba wai don su furta da bakin su ba. "Wanka za ka yi ranka ya daɗe? Balkisu ta faɗa tana mai kallon bayan shi. "E.." Ya amsa mata cikin dakakkiyar muryansa amma cikin sanyin amo a karon farko sannan ya tura ƙofar tiolet ɗin ya shige ya rufo.   Numfashi ta fesar tana mai sake bin bayan shi da kallo bayan ya shige. Sanye yake da bakin wando wanda iyakarsa gwiwan kafafunsa sannan jikinsa wata farar riga ce mai dogon hannu tana da botira a gaba amma bai saka boturan ba, ƙirjinsa mai cike da gargasa ya bayyana a waje kuma tasan ma dalilin da yasa ya yi saurin barin in da take tsaye saboda haka ne. Tunda take ba ta taɓa ganin namiji mai kunya irin mijinta Lamiɗo ba Yau shekaran su shidda da auren su tare da albarkan ya'ya biyu amma bai taɓa yarda ta gan shi daga sama har ƙasa naked ba, itama za ta yi rantsuwa bai taɓa kallonta haka ba. Da farko ta ɗauka ko ba ya son ta ne yasa yake yin haka sai da zaman su ya mika ta fahimci haka Allah ya yi shi, yana jin kunyar tsaraici shi ya sa ko kayan barci baya sakawa masu sharara, in zai kwanta sai ya saka dogon wando, da riga mai dogon hannu ya rufe jikinsa ba ya so ya fidda wani tsaraici na jikinsa duk ko da ita ɗin matarsa ce, yana jin nauyi da kunyar ta gan shi a haka, shima bai iya mata dogon kallon matukar ta fidda masa tsiraici, domin akwai wani lokacin tana da cikin Sultan suna gudanar da Sunna ta kudiri niyyar sai ta ga abin da Allah ya hallata mata. Ita da mijinta amma ace ba ta san girman shi ba, sai da ta bari sun natsa cikin harkan sannan ta kunna hasken ɗakin, ranar ta ga abin mamaki da saurin gaske ya faɗa gefenta cikin zafin nama ya jawo bargon dake gefe ya rufe jikinsa, sannan ya juya mata baya cikin wani sauti amon murya ya ce itama ta rufe jikinta. Ta daɗe lamarin yana ba ta mamaki kuma ta ji haushi har sai da ta yi masa magana da cewa ita fa matarsa ce halaliyarsa amma yana jin kunyar ta ga jikinsa, ko shima ya ga jikinta. Har ta gama maganganunta bai ce mata komai ba, bai ma sake tayar da maganar ba sai da ya tafi ne ya tura mata da saƙon cewa ta yi haƙuri daga haka bai ce komai ba kuma bai sauya ba, dole ita ta bi shi a yadda yake tunda haka Allah ya hallice shi, hallayan shi ne a haka kuma ba zai iya canza kan shi ba. Gadon ta ɗan kakkabe tana ninke farin bargon. Gabaɗaya ɗakin kalan baki da fari ne Lamiɗo na son abu fari kuma yana son baki ko kayan shi rabi farare ne rabin su kuma baƙaƙe ne, bayan ta gyara gadon ta ninke bargon ta ɗan saka shi a gefen gadon ya ɗan ba da styel, itama sai ta koma ta zauna tana ɗan mirmishi. Tana son mjinta tana son Lamiɗo, lokacin da mahaifinta ya kirata akan Lamiɗo ta ji wani iri, da jin labarin Baban shi ne ya yi gadon Sarauta, mahaifiyar shi ba yar kowa ba ce. Bata taɓa tunanin haka za ta ga Lamiɗo ba, sai da ya zo haɗuwar su ta farko anan ta fahimci ko a cikin maza shi na dabam ne, ko ita da take jinin sarauta gaba da baya tunda kakanta na bangaren uwa ya yi sarautan Kano, to ba za ta nuna ma Lamido iko da sarauta ba, tafiyar shi, maganar shi, yanayin tsarin rayuwarsa kaf kamar wanda aka haifa a gidan sarauta ya kuma girma acan, sai ga shi ta ji labarin shi bai ma zauna a Daura ba sai da ya girma ya zo. Kenan duk wani abu na hallayar shi ko yanayinsa halitar shi ce haka Allah ya yi shi. Ba auren soyayya suka yi ba kakar sa Fulanin Daura ce ta zo ta nema masa auran ta, saboda kyayawan alaqan da ke tsakanin masarautun ba jayayya aka amince, kuma daman a zamanin da muke ciki ƴa'ƴan sarakuna sai ƴaƴan sarakuna ƴan'uwansu ko kuma ƴaƴan masu riƙe da madakan ikon a kasar gabaɗaya. Shi ya sa sai haɗin ya yi daidai duk da ana ta cewa mahaifiyar Lamiɗo ba ƴar sarauta ba ce wataƙika ba zai yi gadon Sarauta ba amma kwarjinsa da tasirinsa bai gushe ba. Balkisu ma tun a ganin farko da ta yi masa ta ce ya yi mata tana son shi. Duk a tunanin ta wannan shuru shurun na shi, da wannan ji da kan duk zai sauke su bayan aure. Itama jinin sarauta ne tana ji da takama da girman kai amna haɗuwarta da Lamiɗo sai ta sara ta kuma jinjina masa ta san ita ba ta yi komai ba. Bayan auren su babu abin da ya sauya Balkisu ta yi tunanin za su yi soyayya ta kwatance a yanayin yadda take, yar gayu wayayyiya mai ilimi. Amma sai ta ga sabanin haka, shi fa ba ka iya gane yanayin da yake ciki yana son abu ko ba ya so duk ba ka isa ka gane ba. Ta sha wahala sosai kafin ta fahimci Mijin data aura, komai in za ta yi masa ko ya yi masa ko bai yi masa ba, ba zai taɓa magana ba in ya yi masa ba zai nuna alamu ba, in ma bai yi masa ba, ba zai nuna ba. SSai da ta yi ta karatun nazarin hallayan Lamiɗo sannan ta fahimce shi, shekaran su shidda da aure ba ta taɓa jin ya ce yana son ta ba, sunan ta ma bai wuce sau goma ya taɓa kira ba, in ma magana ta kama sa dole sai dai ya yi maganarsa kawai kai tsaye, da yawan lukata baya gida in ya kirata a waya suna gaisawa ya tambayi yara bai kara cewa komai sai dai in ita ce ta dauko masa hira. In ya dawo za su zauna a gida ɗaya amma bayan gaisuwan safe in dai ba itace ta yi masa magana ba za su iya yini su kwana ba su sake yi ma juna magana ba. Zai iya yini a bangarensa bai fito ba, wani lokacin sai dare in ya fito cin abinci tare da yara. Tunda duk da yanayin shi yana son yara yana wasa da su Sultan, suma ɗin akwai lokacin haka in yana son kaɗaici ma ba zai fito daga bangarensa ba yana son shuru fiye da komai a rayuwansa. Bangaren abinci kuma sai da Ammah ta taimaka mata ta ɗan ba ta satar amsa, duk da ba ita ke yin abincin ba sai dai ta ba da umarnin a dafa masa. Lamiɗo na cin tuwo amma ba ya shan duk wata miya mai yauƙi, ba ya son yaji ba ya son mai ya yi yawa. Ba ya cin naman jan akuya sai kaza ko kifi, kuma ba ya cin shinkafa tsura ko wani abu sai da miya, miyar ko wata iri amma ban da miyar yauƙi, yana son ganye sosai. Da Balkisu ba ta sani ba ta yi ba shi miyar yauƙi sannan ita tana son cin yaji. Gashi dai ba ya so amma ba zai taɓa magana ba, sai dai ta ga baya ci da yawa sai dai ma wani lokacin ya yi ta cin abun gaya ba miya, in ta yi masa mgana sai dai kawai ya yi mata shuru, Ammah ce ta taimaketa anan ne ta san ba ya shan miyan yauki. Shi fa in dai shi zai fada maka abin da yake so da bakinsa to ba za ka taɓa sani ba. Tuni Balkisu ta sauke jin kai da sarauta ta fara karantan mijinta domin ta san cewa ba irin mijin kowa ba ne, Lamiɗo mijin Balkisu na dabam ne a cikin maza. Da haka ta samu ta karance shi tsab har suke zaune lafiya cikin mutumtawa. Ko bai furta da bakin shi yana son ta ba, tana ganin haka a aikace. Ba ta damu ba ta amince da na shi salon nuna son ne a haka bai taɓa danne mata hakkinta na aure ba, tana daga cikin sahun gaba a matan da suka yi sa'an aure, ta samu miji na nunawa sa'a ga shi gwarZo kuma jarumin namiji mai iyawa da duka bukatunta, farkon auren su sai ta zauna jiran sai ya zo gareta ta yi ta cutuwa shi kuma ko yana son abu ba ya nema. Ba ma ka gane yana so ko ba ya so. Shi ya sa da ta fahimce shi ta riƙa ba da kai bori ya hau abin mamaki kuma sai ya fi ta ma rawan jiki da son nuna jin daɗinsa, tun daga lokacin ba ruwanta in tana bukatarsa za ta je gare sa shi kuma a kowani hali yake ciki bai taɓa tankwafar da bukatarta ba sai ya tabbatar da ta samu gamsuwa ɗari bisa ɗari. Ta yi nisa cikin tunaninta ba ta ji karan buɗe kofar toilet ba sai dai kawai ta gan shi ya fito sanye da rigan wanka baka, gaban rigan ta ɗan buɗe, ganin ta a zaune kuma sun haɗa ido.  Da sauri ya juya baya lokaci ɗaya yana jan rigar wankan ya rufe ƙirjinsa. "Me za ka ci na sa Debora ta dafa maka." Ta faɗa cikin harshen turanci lokaci ɗaya tana mikewa tsaye. "Anything is ok. Buh zan fara da Coffea mai zafi." Shima ya mayar mata da martanin maganarta cikin harshen turancu muryansa mai kama da ta jaruman maza. "Okay" Ta faɗa, bai ma jira ta fice ba shi ya fara shigewa cikin clothset ɗin sa, domin ya sauya kaya. Ita kuma sai ta fice tana zuwa main falo su Sultan na shigowa falon James na bin bayansu ɗauke da jakunkunansu da basket ɗin su na makaranta Suna ganinta Beena yarinya yar shekara uku Yar ajin Baby class dabar dabar da lukutun jikinta na yara ƴan hutu ta nufe ta da gudu da karamar muryanta tana kiran sunanta "Momi." Da sauri ta tarbeta ta ɗaga ta sama tana nishi, tunda Beena akwai jiki kamar kazar turawa. "My Beena." Ta faɗa tana jan kumatun ta, ita kuma ta tsinke da magana tana fada mata ta ci egg a makaranta da plantain, da muryansu ta yara da turanci tana jinta tana dariya, Sultan kam a natse shi ya kariso falon yana faɗin. " Good Afternoon Momi." "Afternoon My Sultan. How was school?. Ta faɗaa tana ɗan shafa kan shi. Shi nursery 1, yake shi ne sak Lamiɗo Beena ce ke kama da ita. Ya amsa mata da lafiya lau da turanci yaro ne ɗan shekara biyar amma yana da tsawo da ɗan kiba shi ya sa sai ka yi zaton shekaransa takwas in ba ka san shekarunsa ba. Anitha ta fito daga wani korido daga yamma da sauri domin ta na sane da lokacin dawowar yaran tunda alhakin kula da su yana wuyanta ne suna ko ganinta Beena ta ƙwace a hannun uwar ta nufeta ita kuma ta tarbeta tana mata oyoyo. James cikin ladabi ya gaisar da Balkisu sannan ya  sauke kayan hannunsa ya fice daga falon. Har Anitha ta ja Beena zuwa cikin ɗakin su Sultan yana bin bayan ta Balkisu ta kira shi yana juyowa ta ce "Ku sauya kaya ku ci abinci Papa is at home." Jin ta ce Papa ya sa ya fara tsalle yana murnan Papa ya dawo ya bi bayan Anitha har suka ɓace ma ganin ta, tana tsaye tana kallonsu tana mirmishi,. Ba su san ya dawo ba tunda a jiyan ma cikin dare ya iso gidan kuma ya kwanta yau yana ta barcin gajiya ba su haɗu ba. Kitchen ta shiga ta iske Debora na ta aikin Dinner tana ganin ta ta rankwafa tana gaisheta ba ta amsa ba ta ce ta haɗa ma Baban su Sultan coffea mai zafi nan da nan ta amsa falo ta fita ta zauna ba daɗewa sai ga shi ta haɗo ta kawo mata a cikin wani karamin fulas fari da karamin mug fari da faranti, Balkisu ta karɓa ta wuce da shi ɗakin Lamiɗo ta iske shi ya sauya kaya zuwa wani wando blue da farar riga mara hannu yana gefen gado yana kunna wayarsa da tafi sati a kashe. Karamin teburin tangaran ɗin da ke cikin bedroom ɗin ta jawo ta sauke farantin hannunsa. "Thanks" Ta ji ya ambata a saman leben shi, halin shi ne duk abin da za ta ba shi ko za ta yi masa zai yi mata godiya wannan daɓi'an shi ne.. Zuba masa ta yi ɗan daidai a mug ɗin sannan ta miƙa masa ya karɓa yana sake yi mata godiya wannan karon da harshen fillanci, duk da ba ta ji amma tana tsinta a bakin shi da bakin yaran tunda yana yi musu magana da fillancin. Gefen shi ta koma ta zauna shi kuma sai da ya kunna wayar sannan ya kai mug ɗin baki ya kurɓi coffea ɗin. Tun safe bai saka ma cikinsa komai ba rabon sa da wani abu tun jiya da daddaren da ya dawo ya sha tea. Barci ya yini yi na gajiya yanzu haka ma yana jin kamar kasusuwan shi suna naɗe tsabar gajiya. Sama da wata ɗaya shi ke tuƙi saboda zai bar aiki da kamfanin don kar su bar shi ya tafi haka shi ne sai da suka wahalar da shi, yanzu dai ya samu sun karɓi takardan barin shi aiki sun saka hannu shi ne dalilin dawowar shi gida, nan da wattani biyu zai fara aiki da abon kamfani amma yana da sauran hutu kafin ya kama aiki. Yana kurban tea din yana ɗan duba saƙonnin dake reto a saman wayarsa. "In ka samu natsuwa ka kira Maimartaba da Fulani sun kirani suna tambayana kai, da cewa ba su same ka a waya ba" Balkisu ta faɗa tana kallon shi. Kamar ba zai yi magana sai kuma ya ce a hankali "Har su Ammah ban yi magana da su ba." Sai kuma ya yi shuru ya ɗan ka fasali kafin ya cigaba da faɗin." Zan kira su, " Sai kuma ya kalleta kafin ya ɗan kurɓi tea ɗin hannun shi "Ina so ma na je," Ta san bai gama maganarsa ba shi ya sa ba ta katse shi ba. "Na samu sauyin kamfani. " Numfashi ya fesar a hankali sannan ya a jiye mug ɗin hannunsa a saman teburin gabansa. "Zan yi hutun 2 month." Jin ya yi shuru ya sa ta san ya gama magana. "Ranka ya daɗe dogon hutu haka? Har Daura za mu je? Ta tambaya cikin fara'a. Kai ya ɗan daga mata kafin ya ce" In sha Allahu." "Har da ni za a yi tafiyar? Ta tambaya "In za ki je.". Shima ya ba ta amsa a yanayin maganarsa. "In ba za mu daɗe ba, zan iya ɗaukan excuse a wajen aiki " Sai ya jinjina mata kai, ta san halin shi zai ce in da takura ta yi zamanta "Har da su Sultan? Bai kalleta ba, amma dai ya ɗan motsa kan shi alamun e, sai ta fara yi masa bayanin sun koma makaranta, amma dai ba matsala in dai ba za su dade ba "Sai ki dawo tare da su." Ya furta daga haka kuma ya tsuke bakin shi. Ma'ana shi yana can ita za ta iya dawowa da yara. Tana da murna da jin daɗi za su samu tafiya ita da shi da yaran su abin da ba sa samu sai a shekara bai wuce sau ɗaya ba. Duk da ba hira suke yi ba amma tana tare da shi har aka kira mangariba sannan ta kwaso fulas da mug din zuwa kitchen shi kuma ya sauya kaya zuwa jallabiya ya fita masallaci. Bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi isha'i bayan ya shigo ya ɗan bata lokaci a haraba suna gaisawa da su Baban Adila da Jamess, Lamiɗo kowa ya san shi mutum ne mara ƙyamar mutane duk da yanayin shi, da ya shigo falon ma haka su Sabuwa suka yi layi suna gaishe shi kansu a kasa duk ya amsa musu cikin yanayinsa. Kafin ya dawo Debora ta shirya tebur da abinci sama da kala uku, Balkisu kuma ta sake wanka ta sauya kaya zuwa material doguwar riga. Tana fitowa ta iske shi a falo tare da su Sultan suna masa hira Beena na hawa jikinsa tana sauka. Sultan ko faɗi yake yi Papa zan sha icream, papa zan ci shawarma Papa sai hira yake yi masa shi dai sai ya yi ta uhm kawai yana ɗan mirmishi, Beena kam tana ta wasa da gashin kansa kuma bai hana ta ba. Balkisu ta kalle su cikin alfahari. Tare suka yi Dinner jalop rice mai kaza sai kuma mandirice, shi Lamido Jalop din ya ci sai ya sha lemun abarba. Su kuma ita da yaran suka tsakura sauran abincin Beena ma madaran Naan na yara ta sha, Sultan kuma pepe chicken ya ci Bilkisu kum ta ci Mendi rice din da lemu. Bayan sun gama cin abincin  ba daɗewa Anitha ta zo ta tafi da su domin su yi shirin barci gobe makaranta, suma ba daɗewa suka shige ciki. Debora kuma ta zo ta kwashe komai na saman dining ɗin zuwa kitchen, abincin gabaɗaya ake dafawa su ɗiba na su da na su James ba shamaki, sannan Balkisu ba ta son a gama cin abinci a bar shi a wajen shi ya sa da sun gama take yin saurin kwashe komai zuwa kitchen. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t *16* *Zone ,3. Jimeta* BAYAN SATI ƊAYA. Ummu Salma na zaune a tsakar gida a saman kujera yar tsugunno da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safiyar ranar talata. Farin wake ne a cikin wani farantin silba tana gyarawa Ammah kuma na daga cikin kitchen tana ɗora sanwa amma jefi-jefi tana yi ma Ummu hira wacce ta yi shuru kamar ruwa ya cinye ta. Ammah ce ke ta maganarta ita kaɗai. Baffa baya nan tun jiya suka tafi ibadan shi da Hamma Abdullahi. Gidan sai ya rage daga Ammah sai Ummu Salma, Saddam ma ya koma makaranta shekaranjiya. Gajiya da kwanciya ya sa take ɗan fitowa tsakar gida ko za ta samu abin da za ta iya taimaka ma Ammah da shi amma ba ta barinta ta yi komai sai ta ce ai Likita ya bata hutu, ita kuma ta bata tabbacin ta warke, jiya ne ma Hamma Abdurrahaman  ya zo ya ji suna wannan takaddaman, shi ya yi ma Ammah magana ya ce aikin da za ta yi daga zaune ta riƙa bata saboda ta riƙa ɗan motsa jikinta hakan ma lafiya ce ga abin da ke cikinta shi ya sa yau ɗin Ammah har ta amince ta bata wake ta ce ta gyara mata. "Saura fa kwana biyu zuwan su Lamiɗo Auta, daga yau sai gobe jibi ne ya ce mini za su taho." Ummu ta yi shuru hankalinta na kan waken da take gyarawa amma kuma hankalinta da tunanin ba ya wajen ta tafi duniyar tunanin rayuwarta. Yau wajen kwana uku kenan Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye murnanta ya kasa ɓoyuwa tunda Hamma Lamiɗo ya kira ta ya ce za su zo shi da matarsa da yara ranar al'amis kuma za su ɗan kwana biyu ta kasa sukuni tun jiya ta tura matan su Hamma Abdullahi su Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim suka je gidan shi dake anguwan Jambutu Haske suka gyara suka yi share-share. Sannan yau da safen nan ta ji Ammah na waya da Hamma Abdullahi tana tunasar da shi Hamma Lamiɗo ya ce ya ɗauki motarsa ya kai ta wanki sannan a ɗan duba ta tunda ta yi wattani a ajiye ba a hauta ba, tana can gidan lullube a cikin tamfol. Alhalin ba Ammah ya bama saƙo ba da kan shi ya kira Hamma Abdullahin ya faɗa masa, shi ma jiya ne kafin su wuce da Baffa yake mata maganar shi ne yau ta kira shi tana sake tunasar da shi har da cewa in ba za su dawo ba ne ya kira Abdularrahaman shi ya je ya ɗau motar ita dai maganarta kar shalelenta ya iso garin nan ba a yi masa abin da yake so ba. "Da man Kabiru ya faɗa mini zuwan nan da ya yi kwanaki Lamiɗo ya samu sauyin wajen aiki yanzu zai dinga samun hutun sosai tunda ya sauya wajen aiki." Ammah ta sake faɗa tana daga cikin kitchen. Ummu Salma dai na jin ta amma har a lokacin ba ta yi magana ba, tunani take yi in da ace tana da in da za ta je ta ɓoye ma ganin Hamma Lamiɗo da matarsa za ta je, har sai sun tafi sannan ta dawo, tana jin kunya da nauyin su zo su ganta a haka,  su ga yadda rayuwarta ta dawo baya, yanzu kunyar mutane take ji da Ammah tayi baƙi ko tana falo za ta shige ciki tana jin nauyin haɗa idanuwana da Jama'a ko yayyenta kunyar haɗa idanuwana take yi da su, tana ganin kamar ita ba ta da sa'ar rayuwa ta tafi gidan aure amma ga shi ta dawo musu ba ma ita kaɗai ba tare da nauyin cikin jikinta. Duk da Ammah ta ce ba ta faɗa masa ba amma in ya zo ya gan ta ko bai ta tambaya ba Ammah za ta iya faɗa masa dalilin zamanta a gida tunda shi tambaya ba ɗabi'ansa ba ne ko zai shekara yana ganinta ba zai damu da ya tambayi dalilin zamanta ba. Ta yi nisa cikin tunanin ta ba ta ma san Ammah ta fito tana yi mata magana ba, sai da ta ji ta taɓa ta sannan ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. "Ammah kina magana ne? Ta faɗa tana kallonta lokaci daya tana koƙarin shanye hawayen da suka cika mata kwarmin idanuwanta. "Auta" Ammah ta kira ta, sai ta sunkunyar da kanta tana jin kamar ta kace da kuka. "Ba an hana ki shiga zurfin tunani ba, sai yaushe ne za ki saduda ki fahimci duk abin da Ubangiji ya yi daidai ne? Sai yaushe za ki dogara da Allah ki san cewa Habibu ya shuɗe daga rayuwarki Ummu Salma.? Ammah ta gama faɗa tana tsaye tana kallon Ummu wacce har ta fara tsiyayan hawaye a saman ƙuncinta "Wallahi in na ga kina kuka da damuwa kan wannan yaron haushinki na ke ji, bai ma kamata kina yi masa kuka ba, an san da damuwa amma haƙuri ake yi tunda damuwa da kukan ba zai sauya komai ba. To gwara a yi hakurin yafi alheri in kika yi hakuri wata rana za ki ci riban haƙurin ki Auta." Ummu Salma ta rushe da kukan da take ta riƙewa. Ammah ta duka a gabanta lokaci ɗaya tana dafa kanta. "Ki yi hakuri Auta kin ji ko? Sai Ummu ta gyaɗa mata kai amma kukanta ya kasa tsayawa. "Mu kan mu muna cikin damuwar abin da ya faru, amma yanzu mu damuwarmu taki ce Auta. In ba ki kwantar da hankalin ki ba, muma hankalin mu ba zai kwanta ba. Samun kwanciyar hankalinki shine farincikin mu da mu da yan'uwanki  gabaɗaya, tunda dai ba mu isa mu sauya abin da ya faru ba, to gwara mu taru mu yi haƙuri gabaɗaya mu fauwalla ma Allah duka lamuranmu da sannun komai zai wuce sannan kuma zai yi miki sakayya in sha Allahu " Duk wannan dogon nasihan da Ammah ke yi mata ba ta ji ba kuka kawai take yi har da gunji. "Yanzu shike nan Habib ya rabu da ni har abada Ammah? Ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon Ammah idanuwanta suna masu zubar da ƙwalla. "Shike nan Habib ya rabu da ni. Shike nan ya gama da ni Ammah? Amma ta yi kasaƙe tana kallonta cikin takaicinta. Ba ta son ta yi ta ma yaro magana yana yi mata taurin kai. "Ammah ina son Habib. Ina son na sake rayuwar aure da shi. Wallahi ina son shi, na kasa mantawa da shi sai na ke ganin kamar tunda ya rabu da ni har abada ba zan sake farinciki ba Ammah." Ta ƙarishe faɗa tana mai sakin wani marayan kuka mai fitowa da shessheƙa Ammah da takaici ya ƙume ta, ture ta ta yi kafin da sauri ta miƙe tana faɗin" Ke kam dai an yi sakara Ummu, wallahi in da kin san yadda na tsani sunan yaron nan da baki yi gangancin ambaton shi a gabana ba. Haba don Allah yaron da ya yi miki wulakanci ya tozarta ki kike ikirarin har yanzu kina so saboda ba ki da zuciya Auta? Ta faɗa lokaci ɗaya tana balla mata harara. Ummu ta danne kukanta sanin halin Ammah yadda ta fusata sai ta iya kai mata duka ma in ba ta yi wasa ba. "Yaron da tunda ya sake ki bai sake waiwayoki ba, ba ruwan shi da ke ballatana yadda kike rayuwa, cikin dake jikin ki ma bai damu da shi ba ballatana ke, amma saboda wawanci ke kina nan kina kuka kina cewa wai kina son shi, to Allah ya tsine ma wannan son Ummu ba shi da albarka tunda bai tsinana miki komai ba sai tozarci da wulakanci" Yadda Ammah ta harzuƙa tana ta faɗa ne yasa Ummu tana hawaye ta ce" Ki yi haƙuri Ammah." "Ke kika sani wannan kuma ruwanki ne, ki yi hakuri ki rumgumi kaddaranki, ki sani yanzu rayuwarki ta sauya ki rika tuna Habibu a matsayin wani darasi ne wanda ya shuɗe daga rayuwarki, sannan ki riƙa tuna ba ke kaɗai ba ce nan da wani lokaci za ki zama uwa. Abu na ƙarshe kuma ki zauna ki yi ta kuka da damuwa kar ki yi farinciki a kan wanda har abada bai san kina yi ba sannan bai damu da rayuwarki ta cigaba ko ta tsaya ba. " Ammah ta gama faɗa tana barin wajen zuwa kitchen ta bar Ummu na kuka wurjajan lokaci ɗaya tana faɗin" Ki yi haƙuri Ammah." Ammah na jinta ta yi mata banza takaici duk ya kumeta, tana jin baƙin ciki in ta ga Ummu Salma na kuka saboda wannan yaron mara mutumci, wanda bai san kana yi ba har da cewa wai tana son shi, Allah ya tsine ma wannan soyayyar domin su kansu iyayenta bata amfanesu da komai ba. Nan Ummu ta bar ma Ammah gyaran wakenta ta shige ɗaki ta kwanta a saman gado ta cigaba da rusan kuka kamar ranta zai fita kowa yaƙi ya fahimceta, kowa ya kasa gane yanayinta. Ko za ta manta da komai ba yanzu ba,  wataƙila sai an ɗauki wani lokaci su yi mata uziri su gane yanayinta har gobe mafarkin Habib take yi sannan tana begensa ba laifinta ba ne laifin zuciyarta ne da ta kasa tsanar shi har yanzu. Ranar yini ta yi kuka fuskar duk ta yi ja, idanuwana sun tasa Ammah ba ta sake bi ta kanta ba ko abincin da ta shigo mata da shi cewa ta yi in ta gama dama ta tashi ta ci in ba ta ga dama ba ta cigaba da kuka saboda wanda bai san tana yi ba, ba ta sake bi ta kanta ba ballanta ta lallasheta. Ita ce don kanta ta haƙura da kukan ta sauko ta ci abinci jin cikinta na ta murɗawa, su Baffa ba su dawo a ranar ba sai washegari da rana, Ammah kuma ba ta sake mata magana ba, tun bayan gaisuwan safe, itama sai ta kama kanta ta daina kuka amma a ƙasan zuciyanta dankare take da damuwa. Da ta je gaishe da Baffa idanuwanta ya kalla kawai ya fahimci ta yi kuka. "Auta har yanzu dai ba ki daina koke-koken nan ba? Sai ta kasa yi masa musu, tunda gaskiya ya faɗa shuru ta yi kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabin jikinta "Har yaushe ne za ki kai kina wannan kukan Auta? Kuka fa ba zai yi miki magani ba sannan ba zai taɓa dawo miki da abin da kika rasa ba. Hakuri da tawakwalli shi ne mafita ki samar ma da kanki lafiya ki bar zuciyarki ta huta sai gangar jiki ta amshi canjin ki Auta. Juna biyu kike da shi halin da kike ciki zai iya shafar abin da ke cikin ki, in hakan ta faru kuma kema kina cikin matsala, faruwan haka kuma daidai yake da muma kin saka mu cikin damuwa Auta" Tunda Baffa ya fara magana ta fara hawaye. "Ki yi hakuri Auta ki yi tawakalli. Ubangiji yana sane dake, shi ya haɗa ki da Habibu a karon farko, kuma da saninsa ya raba ku, in kina yin haka sai ki yi masa bultulci, ki sani in kika yi hakuri Ubangiji mai rahama ne mai jinƙai, watakila ya yi ma rayuwarki wani kyakyawan canji anan gaba. Canjin da zai goge miki dukkan wani bakin cikin da kika taɓa shiga a rayuwarki." "Ka yi hakuri Baffa." Ta faɗa cikin kuka tana toshe bakinta da hijabin hannunta. "Ka yi hakuri Baffa, in sha Allahu na daina." Ta sake faɗa cikin kuka. Baffa ya ji daɗi ya jinjina kai kafin ya ce" Allah ya sa Auta. Ina fatan Ubangiji ya sake sauƙaƙa miki." Ta amsa da Amin a hankali tana mai sharan ƙwalla ta jima a ɗakinsa yana ta yi mata nasihan kafin ta koma ɗakin Ammah. Ammah ko sai da Ummu ta bar ɗakin Baffan sannan ta shiga tana faɗan cewa Ummu Salma ba ta bukatar lallashi, in ba ta bayan gida aka fito mata ba haka za ta zauna tana neman kashe kanta saboda wanda bai san tana yi ba. "Jamila." Baffa ya kira sunanta, ta kalle shi amma ba ta yi magana ba. "Ki yi haƙuri da Auta, don Allah ki yi haƙuri da ita domin a halin da take ciki tana bukatar lallashi da ban baki ba faɗa ba." Ammah ta yi shuru ba ta yi magana ba. "Na san kina ƙoƙari amma don Allah ki ƙara kin ji ko? Ya sake faɗa yana riƙo hannunta guda ɗaya. "Ba ki ce komai ba.' Ammah ta yi jim kafin ta ce" Baffa cewa fa take yi wai har yanzu tana son yaron nan wai kuma tunda ya rabu da ita ba za ta sake yin farinciki ba," Ammah ta faɗa cikin takaici in ta tuna maganar sai ta ji zuciyanta na zafi. "To ai wannan sai a hankali Ammah, a sannu sannu duk za ta manta da komai. Ke dai kawai ki ɗan bata lokaci." Ammah ta ɗan ɓata rai kafin ta ce" To Baffa wani irin so kuma! Kalli fa wulaƙanci da tozarcin da ya yi mata amma ita har yanzu son shi take yi? Baffa ya yi mirmishi kafin ya jinjina hannunta a cikin na shi yana fadin" Ina ruwan zuciya Ammah, ba laifin Auta ba ne bata da alhakin sarrafa zuciyarta. Amma lokaci ne wallahi tallahi za ta manta da komai, watakila sai dai in ta kalli abin da ke cikinta bayan ya fito duniya ta iya tuna da shi" Ammah ta yi shuru tana kallon shi sai ya gyaɗa mata kai kafin ya cigaba da faɗin" Na baki tabbacin haka, ki dai kawai ki ɗan kara mata lokaci." Sai Ammah ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Shike nan Baffa Allah ya ba ta dangana." Ya amsa da Amin yana faɗin" Ko ke fa matar Baffa" Ammah ta yi mirmishi ba tare da ta yi magana ba. Fita ta yi zuwa kitchen ta shako wani ƙaramin faranti da kulolin abinci sai ruwa da kofi ta kai ma Baffa yana ci suna ɗan taba hira kaɗan kaɗan ita kuma tana gefen shi tana yi masa fitita da mafici tunda ba wuta sun ɗauke. "Baffa gobe fa su Lamiɗo na hanya." Kai ya ɗan jinjina kafin ya ce" Na ji Abdullahi na maganar shi zai je fillin jirgi ma ya taho da su." Ammah ta washe baki tana faɗin" Haka ya ce mini, Baffa Lamiɗo fa ya fi wata biyar rabon shi da garin nan" "Zai yi gaskiya." Ya faɗa yana kai cokali bakin shi cike da shinkafa da wake jallop. Ammah ta cigaba da faɗa masa ta kira Ummin ikki ta faɗa mata gobe za ta zo ta taya ta girkin da za ta yi musu na tarba. "To ke ki bari surukan ki su zo su yi girkin mana." Da sauri Ammah ta ce" A'a Lamiɗo ya ce na yi masa tuwon shinkafa miyar zogale. Kuma kasan in bani na yi girki ba yana ganewa." Baffa ya kalleta kawai ya yi ɗan mirmishi. "To uwar Lamiɗo." Ammah ta kwashe da dariya Baffa na kallonta yana jin sanyi a ran shi, gabaɗaya ta faɗa damuwar halin da Ummu ke ciki na ta sukanta a ciki, shi ya sa ta yi ta rama a tsaye amma yau saboda zuwan Lamiɗo ta saki har yana ganin dariyanta kuma farincikinta ya kasa ɓoyuwa shi kan shi ya tabbata Ammah renon ɗa na cikinta ta yi ma Lamiɗo shi ya sa take jin sa fiye da ƴaƴan cikinta. Shi dai har ya gama cin abincin Ammah na yi masa hira kan zuwan Lamiɗo yana jinta kawai yana mirmishi. Suna cikin ɗakin ne ma Baɗɗo ta zo gidan, har ɗakin Baffa ta shiga suka gaisa ta ce daga makaranta take ta biyo. "Sannu Baɗdo, Ammah ba ta abinci ta ci.". Baffa ya faɗa yana kallon Ammah. "Ta je Kitchen ta ɗiba mana" Baɗɗo ta amsa da bari ta yi salla tunda tana makaranta aka yi la'asar kuma tana sauri ba ta tsaya ta yi acan ba. Ɗakin Ammah ta shiga Ummu na kurya cikin ɗakinta kwance tana tunani ba ta ma ji shigowar Baɗɗo ba sai da ta ji ta faɗo saman gadon sannan hankalinta ya dawo kanta. "Kina kwance kullum kullum dai Sisna? Ta faɗa tana mai kallon Ummu Salma da ta ɗan tashi zaune tana kallon ta. "Daga makaranta kike? Ta tambaya, daidai Baɗɗo na sauke jakar hannunta lokaci daya da yaye mayafin jikinta. "E na ce bari na ɗan leko ki kwana biyu? Ya jikin! Ina fatan dai ba wata matsala,? "Babu." Ta faɗa a sanyaye. "Kin tabbata? "Allah bana jin komai, sai yar kasala ne da ɗan ciwon kai." "To magungunanki sun ƙare ne? Sai ta ɗan jinjina kai kafin ta ce" Bai wuce in na sha yau da gobe ba." "Yakamata mu koma asibiti " Baɗɗo ta faɗa tana kallon cikin jikin Ummu. "Cikin fa har ya ɗan turo" Ummu ta bi cikinta da kallo saboda riga da sikat ta saka shi ya sa sai cikin ya ɗan turo Shuru kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba "Kila fa in muka koma su ce ki fara zuwa awo". Ummu ta kalli Baɗɗo na wani lokaci nan ma ba ta yi magana ba. "Me ya faru? "Sai na haihu har abin da na haifa ya girma bai san uban shi ko ba ta san uban ta ba? Ta tambaya idanuwanta na cikowa da ƙwallah. Baɗɗo ta ce" To wa ya ce ba zai san uban shi ba? Za a faɗa masa komai har labarin tun yana ciki uban ya ce ba ya bukatarsa." Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa. "Bari na yo alwala' Tana gama faɗin haka ta shige tiolet domin ba ta san ma ta tsaya Ummu Salma na damunta da mganganu kan Habib wallahi ta tsane shi ta tsani ma jin sunan shi Fatan ta yadda ta tsane shi itama Ummu ta tsank Habib amma ina, ita har gobe tana begensa tana ganin zai iya neman ta, ta manta da cewa ya ce ya riga ya gama amfana da ita. Alwala ta ɗauro ta zo ta yi salla bayan ta idar ta fita ta je ta ɗibo abinci ta zo  ta hau gadon tana ci suna ɗan taɓa hira da Ummu, ko da ta kawo mata maganar Habib Baɗdo za ta ɓata rai ta kauce da hirar. "Har yanzu Habib bai kira ki ba? Ummu ta tambayeta tana kallon ta. "Ni bai kirani ba, tunda ya sake ki na goge lambar shi a cikin wayata." Ta ba ta amsa tana mai cigaba da cin abincinta. "Me ya sa kika yi saurin gogewa? Da kin kira shi, kin tambaye shi me ya sa ya yi mini haka? Baɗɗo ta kasa haɗiye abincin da ta saka a bakinta tana kallon Ummu da mamaki. Ganin har ta fara hawaye. "Baɗɗo na kasa mantawa da Habib. Wallahi a mafarkina da farke na duk tunaninsa ne." Ta karishe faɗa cikin kuka. "Kowa laifina yake gani, ba laifina ba ne, zuciyata ne har yau tana son Habib na kasa jin na tsane shi. Nima ina so na tsane shi, amma na kasa ya zan yi? Na rasa yadda zan yi da rayuwata." Ta ƙarishe faɗa tana mai fashewa da kuka Baɗɗo ta yi shuru ta ma kasa mgana, maganganunta sun ƙare duk wani kalami na lallashi ta gama zayyana ma Ummu amma har yau ba ta gane annabi ya faƙu ba. "Ni ba ni da abin da zan kira Habib na faɗa masa. Domin duk wani abun da za mu sani ya sanar damu. Ummu ki saka a ranki ko da ganganci Habib ya kira ni sai ya yi nadama wallahi, domin ba zan raga mishi ba. Tunda shi batulu ne kuma mayaudari, sannan maganar kina son shi, ko kin kasa tsanar shi duk bai ta so ba, ki yi ma kanki faɗa Ummu cewa fa ya yi bai taɓa son ki ba, don jikin ki ya aure ki. Kuma ya gama amfana da ke shi ya sa ya sake ki, da cikin shi amma bai damu ba, to ke ki yi tunani da hankalinki wanna mutumin da ya gama yi miki haka ne zai dawo gare ki? To ko ma ya dawo da sunan mene? Bayan abin da ya haɗa ku ya riga ya kawo karshensa duka. Ko kin manta saki uku Habib ya yi miki ne Ummu Salma? Ta gama faɗa tana kallonta. Ummu tana hawaye ta ce" Ban manta ba" "To gwara ki tuna cewa har abada aure ya haramta tsakaninki da Habib a yanzu. Kuma koma bai haramta ba shi baya sonki ba kuma zai dawo gare ki ba, in ma za ki yi daina tunanin ki cire sa a cikin zuciyarki ki cire shi, in kuma ba za ki iya ba har yanzu kina son shi to ki ba da himma. Amma ina so ki sani ko mutuwa kika yi wallahi tallahi Habib ba zai damu ba domin ba shi da asara." Baɗɗo ta faɗa tana zare ma Ummu Salma idanuwanta domin yau itama ta kai ta bango. Ummu ba magana sai kuka, tana faɗin kowa haka yake ce mata ko jiya ma Ammah ta yi mata faɗa yau ma Baffa ya yi mata nasiha. "To ai duk muna son ki ne, gaskiya ce mai ɗaci muke faɗa miki. Bayan mu masoyan ki, ba wanda ya san zafin ki Ummu Salma." Ta faɗa tana ɗan sassauta fushinta. Ummu na kuka take faɗin" Ina so na manta nima ina so manta. Amma na kasa." Sai gunjin kuka, tausayinta ya kama Baɗɗo dole ta sauke filet ɗin abincin hannunta a saman dirowan gado ta karisa wajen Ummu ta rumgumeta tana lallashinta. "Ki yi hakuri, ke ce za ki yi ma kanki wannan yaƙin. Ki koma ga Allah ki roƙesa ya cire miki, in sha Allahu zai cire miki." Ummu ta amsa da cewa wallahi tana yi tana addu'a amma kamar sai kara gaba tunaninta akan Habib yake, ita kuma Baɗɗo na sake ba ta tabbacin kar ta gaji ta cigaba da kai kukanta wajen Allah zai kawo mata ɗauki. Da lallashi da ban baki Ummu ta yi shuru. Sannan Baɗɗo ta karishe cin abincin ta ta fita da filet ɗin zuwa kitchen ta haɗa wanke-wanken ta wanke sannan ta share tsarkar gidan Ammah na ta saka mata albarka. Sai da ta yi mangariba sannan ta yi shirin tafiya. "Ke wai na ji Ummi na faɗin gobe Hamma Lamiɗo zai zo tare da iyalansa." Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana gyara zaman jakarta a saman kafadanta. Suna tsaye a tsakar ɗakin Ummu ta zumbuɗa hijabin da ta yi salla da shi za ta ɗan rakata haraban gida.. "Uhm haka na ji Ammah na faɗa." Ummu ta faɗa cikin basarwa. Bata son ya zo, haka kurum ba ta son su samu baki anan kusa, ita dai da Baffa ya sani ya barta ta bi Mami Kaduna da ta fi samun kwanciyar hankali. Dazu ma da Baɗɗo ta yi mata maganar waya ta ce sun yi waya da Mami ta ce za ta aiko mata da sabuwar waya da layi, wayarta ba za ta iya amfani da ita a yanzu ba. "Ai Ummi ta ce tun safe tana nan gidan Ammah ta ce ta zo ta taya ta abincin tarban shalelen Ammah.." Ta faɗa tana yar dariya Ummu ta kalleta kafin ta ce" Uhm kin san halin Ammah, in ban da ma ɗaukan ma kai, girki ko su Adda Suwaiba ba za su yi musu ba? In su Hamma Jibo ne za su zo ban taɓa ganin ta yi musu girki na musamman ba amma Hamma Lamiɗo duk abin da yake so ita ce za ta yi masa." Ummu ta karishe faɗa da jin haushin Ammah haka kurum mutum kato da iyalansa amma har yau ba ta daina wahala a kan shi ba "Ke ko ɗan gaban goshin Ammah ne, naji ma Ummi na faɗin za su kwana biyu." Ummu ta yi shuru ba ta sake magana ba tunani take yi in da hali ta guje ma gidanan har sai sun tafi, duk da ba dariya za su yi ma kaddaranta ba, ita kawai tana kunyar ya zo ya ganta a gida kawai a ce mijinta ne ya sake ta sai abin ya yi mata wani iri. Bayan Baɗɗo ta yi ma su Baffa sallama Ummu ta tafi rakata har haraban gidan, suna tafe Baɗɗo na tambayan ko Shamsiya ta zo? Ummu ta ce ta zo kwanaki ta ma ce za ta dawo amma ba ta dawo ba. "To watakila ta koma makaranta ne" Baɗɗo ta faɗa Ummu ta yi shuru kafin ta ce" An ya! Ko dai ta ji haushin mganganun da Ammah ta faɗa mata ne" "Me kuma ya faru? Baɗɗo ta faɗa tana zare idanuwaanta. Nan Ummu ta kwashe komai ta faɗa mata. "Kin san halin Amman taki, ba ta da haƙuri ta yi ta masifa." Ta karishe faɗa tana kallonta. "To ai ban ga laifin Ammah ba, itama dai Bestie ba ta yi nagana mai kyau ba duk wannan abin da Habib ya yi miki sai ta ce laifin ki ne?  Haba ko Habib ta sani ba ke ba ai ta faɗi gaskiya ballanta ta sanadinki ta san Habib ɗin, ai wallahi Ammah ta yi mini daidai ko ni ce a wajen haka zan yi mata." Ummu ta kalleta kafin ta ce" Ku yi ma Bestie uziri kin san yanayinta da gidan su." Baɗɗo ta taɓe baki kafin ta ce" Haba koma dai mene ai ke tata ce, in ba ta tausaya miki ta ba ki baki kan abin da ya same ki ba, bai kamata ta zauna a fuskarki tana cewa ke ce da laifi ba, kuma har tana fadin cewa ba za ki samu kamar Habib ba ni wallahi kalamanta ma sun saka ta l zube mini a idanuwana Habib ɗin banza? Wallahi sai kin samu wanda ya fi shi kuma ta jira ta sha kallo." Ummu dai ba ta kara magana ba ganin Baɗɗo ta ɗau zafi ta samu suka yi sallama ta tafi, ita kuma ta dawo cikin gida. Itama fa kalaman Shamsiyar sun ba ta mamaki ita ce ta farko da ta fara cewa Habib ba shi da laifi. Sannan ta yi mamakin rashin dawowarta sannan ko a waya ba ta kirata ba, ai tana da lambar Ammah. amma ba ta kawo komai a ranta ba, Ammah na ɗakin Baffa ta ɗau wayarta ta kira ta har sau biyu ba ta ɗauka ba, sai daga baya ta kirata tana ce mata ba ta gida ne da yake ta koma makaranta. Sun ɗan jima suna hira Shamsiya ta bata hakuri kan cewa komawarta makaranta ne ya zo a gaggauce shi ya sa ba ta dawo ba. Amma kafin su yi sallama sai da ta yi ma Ummu tambaya. "Yanzu Bestie haka za ki yi renon cikin nan ki haife shi a ƙasƙantan ce! Alhalin uban cikin ya ce ba ya so? "In shi ba ya so ai ni ina so. Kuma da ikon Allah zan haifi abin da ke cikina da goyon bayan iyayena da dangina" Ummu ta bata amsa muryanta a raunane domin kuka na shirin ƙwace mata.. "Tabɗijam. To Allah ya kyauta." Ta faɗa cikin ganin karfin halin su tunda wanda ya yi cikin nan ya ce ba ya so to me kuma za a jira da shi? Kafin su yi sallama ma wayar ta katse kamar katin ta ne ya kare. Ranar kamar an yi ma Ummu Salma fami kan damuwarta ta kusa raba dare tana koke-koke ballanta da Ammah ba a wajenta ta kwana ba, ganin ta yi kuka ba zai fissheta ba ya sa ta tashi ta je ta ɗauro alwala ta fara salla daga zaune domin jiri take gani addu'a take yi Allah ya cire mata soyayyar Habib a cikin zuciyanta ko za ta samu salama. Ba ta samu barci ba sai da ta yi sallar asuba shima ba daɗewa ta tashi da ciwon kai da jiri, tana kuma karyawa sai amai kamar za ta yi amayar da hanjin cikinta, sannan da ta shiga tiolet sai ta ga jini a ruɗe ta fito ta faɗa ma Ummin ikki da ta zo gidan tarban su Hamma Lamiɗo. Baffa baya nan ya shiga cikin gari tare da Abdullahi can harkokinsu. Sai kawai Ammah ta ce Ummin ikki ta raka Ummu zuwa asibiti, tare suka tafi har da Adda Suwaiba da tun safe suna gidan. **** Ƙarfe biyu saura na rana Hamma Abdullahi ya je filin sauka da tashin jirage na YOLA INTERNATIONAL AIRPORT JIMETA. da kuma motar Hamma Lamiɗo wata hilux ƙiran Toyota da alamu dai Hamma Lamiɗo na son mu'amala da motocin kamfanin Toyota. Lokacin da suka iso gidan su Ummu ba su daɗe da dawowa daga asibiti ba, cikinta ya shiga wattani huɗu amma likita ya ce ya yi rauni ta riƙa samin hutu sannan jininta ya yi sama again, ba kuma ta samun isasshen barci. Amma dai ya rubuta magunguna sannan ya ce nan da sati uku za ta fara zuwa awo, suna son ta samu hutu sosai sannan ta riƙa cin abubuwan da za su gina mata jiki, amai kuma da kasala laulayi ne za ta bari in cikin ta ya yi girma watakila ma sai ta haihu ya danganta da yanayin ta. Ummu Salma na kwance a cikin ɗakinta lamo akan gado tana sauke ajiyar zuciya tana ji daga falon Ammah ana ta yi ma baƙi maraba. Har da Adda Ummu Sulaim, duk tare suka taimaka aka gyara gidan girki dai Ammah ta yi a cewarta Lamiɗo na ganewa in ba ita ta yi mishi abinci ba. Ga muroyoyin su nan har na Ammah amma ko tarin Hamma Lamiɗo ba ta juyo ba, kuma yana falon tunda ga Ammah can na ta masa maraba kamar ta goyasa. Da ga cikin ɗakin dai ta ji na matarsa cikin yauki da yanga kamar yadda ta saba tana gaishe da Ammah da su Ummin ikki. Barci ne ya kwashe ta daga nan ba ta farka ba sai wajen biyar saura shima ɗin ta tashi ne don kanta, Adda Suwaiba ta gani a ɗakin tana zaune tana ba ma ƙaramar yarinyar ta Mimi mama. "Adda an yi salla ne? "Tun ɗazu. Biyar ma ta kusa." Ta bata amsa. Sai ta miƙe da sauri tana faɗin. "Shi ne ba wanda ya tashe ni? "Ummi ta ce a kyale ki likita ya ce ki huta sosai." Ba ta sake magana ba ta shiga tiolet ta yo alwala ta zo ta yi salla. An riga an shigo mata da abincinta ta ja ta zuba tuwo ɗaya a filet ta fara ci, miyar ma daɗinta na musamman ne saboda zuwan Hamma Lamiɗo. Tana jiyo muryan Hamma Abdullahi da na Hamma Abdulrrahman, har da na Ammah da Baffa amma ba ta jiyo na Hamma Lamiɗo ba. Sai ta yi tunanin ko har sun karisa gidan na su ne? "Adda su Hamma Lamiɗo sun tafi gidan su ne? "Aa ba su tafi ba, ga shi can shi a falo suna hira da su Baban Mimi a falo, har da Baffa ma." Ummu ta yi shuru ba ta sake magana ba. "Balkisun kuma tana ɗakin Ammah tare da hadiman ta da suka zo tare." Ummu ta ɗan gyaɗa kai, da man in dai za ta zo, tana tare da hadimanta. Nan Adda Suwaiba ta fita ta barta bayan ta gama cin abinci tana son shan ruwa amma ba za ta iya fita falo ba tana jin kunya. Sai kawai ta yi zaman ta. Har fa mangariba duka suna gidan ba su tafi ba. Ummin ikki ce kawai ta tafi gida. Bayan mazan duk sun fita sallan magariba itama ta idar kenan Ammah ta leƙo ta ganta saman darduma tana lazimi. "Ke kam ba ki ji zuwan yayanki tun ɗazu ba ne? Ko da yake kina ta barci." Kafin Ummu ta yi magana Ammah ta riga ta da cewa. "To taso ki gaishe da matar yayan naki, kafin su dawo daga masallaci." Ba ta isa ta zille ba domin Ammah ba a yi mata wasa. Dole ta miƙe ta bi bayanta zuwa ɗakin Ammah in da ta iske Balkisu da ya'yanta tare da Sabuwa da Anitha Da ta gaisheta ta amsa tana kallonta. "Ba ki da lafiya ne? Ta faɗa cikin yanayin maganarta. Ta kasa mgana, domin ba ta san me za ta ce ba. "Uhm ba ta da lafiya ai tana ma gida ne sun rabu da mijin" Balkisu ta yi salati cikin yanayinta ta ce. "Subhanallahi." Nan fa Ammah ta gyara zama ta shiga ba ta labarin abin da ya faru. Ummu ta kasa zama ganin har Sabuwa na yi mata wani kallo, Anitha ma ta kafe ta da kallo kamar ta san me ake faɗa. Sai kawai ta tashi za ta fita Beena ta biyo ta a baya tana magana ba ma ta jin me take faɗa, ba shaƙuwa da yaran ta yi ba ko a baya suka zo gidan ba ta ta kan su. Tana fitowa daidai su Hamma Abdulrahaman suna shigowa falon Ammah. Sun riga sun ganta ba ta da yadda za ta yi, ga Beena ta rike mata gefen hijabi tana fadin egg za ta ci. Kanta na ƙasa ta ma kasa ɗagowa tsabar kunya da nauyi. "Ummu kin ta shi? Na leƙo ɗazu aka ce kina barci. Sannu ya jikin? Hamma Abdullahi ya faɗa "Ba ta da lafiya ne? Hamma Abdulrrahaman ya faɗa yana kallon ta. "E sai da suka je asibiti da Ummin ikki." "Allah ya sauwake. Sannu " Shima ya faɗa yana kallonta. "Papa." Beena ta faɗa ganin babanta sai kuma ta saki Ummu ta nufe sa ta faɗa jikinsa. Kamar tsautsayi Ummu ta ɗago kanta karaf sai a idanuwan Hamma Lamiɗo da yake zaune saman kujeran zaman mutum biyu da ke falon Ammah. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t *17* Sanye yake da wani baƙin yadi mara kauri domin in ka ƙura ido sosai za ka iya hango farar vest ɗin dake jikin shi ta ciki. Ɗinkin zamani ne amma rigar ta kai har wajen gwiwan ƙafafunsa, kansa da hula amma saboda ya tara suma sai hulan ta samu matsugguni a saman gashin kan nashi, sannan gefe da gefen fuskar shi sumar ta ɗan bayyana. Ummu ta yi saurin kauda kanta, shi da man bai nuna ma ya ganta ba, Beena ce ke yi masa raɗa a kunne yana sauraranta. Ummu ta so ta yi sauri ta koma ɗakinta ne amma ina ta juya za ta shige kenan kawai ta ji Hamma Abdullahi ya kira ta. "Ummu" Ta juyo tana kallon shi. "Ba ki ga Lamiɗo ba ne? Na ji ba ki gaishe shi ba ne" Ummu ta runtse ido tana cije baki Hamma Abdullahi ya kwafsa mata, ita fa ba ta so ma ya ganta ba, ballatana ma har gaisuwa ya haɗa su ita a fatan ta ma har su gama zaman garin su koma ma ba za su haɗu ba sai ga shi tun a ranar farko Allah bai cika mata wannan manufar ba "Sannu da zuwa Hamma, in yini? Ta faɗa daga in da take tsaye. Amma Hamma Lamiɗo ya yi kamar bai ji ta ba. Da man halinsa ne ko a baya sai ka yi ta gaishe shi yana ji ya yi kamar bai ji ba in kuma ya amsa to a gajarce ne. "Anan kuma! Ƙariso ciki wataƙila bai ma ji ki ba." Hamma Abdullahi ya sake faɗa. Kamar Ummu ta fashe da kuka har hawaye sun kawo mata cikin kwarmin idanuwanta. Haka nan jikinta a sanyaye ta ƙariso tsakiyar falon ta ɗan rankwafa daga gefe jikin kujera "Ina yini Hamma". Ta faɗa cikin rawan murya. "Fatan an zo lafiya? Ta sake faɗa kanta na ƙasa. Nan ma shuru ya yi kamar bai ji ba sai da Hamma Abdullahi ya ce ana gaishe shi sannan ya ɗago yana kallon shi, Ummu ya nuna masa yana faɗin" Autar Ammah ke gaishe ka." Kanta na ƙasa ba ta ɗago ba, saboda haka ba ta san ko ya kalleta ba ta ji dai ya amsa da lafiya da muryansa nan na shi a ginshiƙe kamar ba zai yi magana ba. Zumbur ta miƙe ta bar falon har tana harɗewa da hijabin jikinta sai da ta ɗan laɓe daga can korido tana so ta ji ko zai tambaya me ya sa ya ganta a gida? Duk da ta san ba zai taɓa tambaya ba. Bai yi magana ba suma su Hamma Abdullahi ba su yi masa maganar ba sai ma suka shiga wata hirar ta dabam hakimin yana zaune yana sauraransu yana amsa musu ɗaya bayan ɗaya a ginshike cike da kasaita. Ita dai tunda ta shige ɗakinta ba ta sake fitowa ba, ana yin sallar isha'i ta tashi ta yi Adda Suwaiba ta ɗauko mata ruwa ta sha magungunnan ta, ƙila akwai na barci ne a ciki nan da nan barci ya ɗauketa. Cikin barci sama-sama ta ji Baffa ya shigo duba ta, ba ma za ta iya tuna me ta ce masa ba, shi dai ta tuna yana ce mata Auta ya jikin naki? Daga nan sai asuba ta iya farkawa shima wasu masallatan sun sallame salla. Gidan shuru ashe tun jiya da daddare da baƙin da suka zo da yan gidan duk sun tafi gidajen su. Da safen ma Ammah ta yi abin ƙari Hamma Abdullahi ya zo ya ɗauka bayan shi ma Adda Ummu Sulaim ta yo, sannan haka ma Adda Suwaiba ta kawo duka ya haɗa ya tafi da shi gidan Hamma Lamiɗo dake Jambutu haske. ** *Jambtutu Haske* Gidan Hamma Lamiɗo babban gida ne, mai ɗauke bangare biyu manya manya. Ɗayan bangaren an gyara shi amma babu kayan amfanin yau da kullum yana ma rufe ne ɗayan bangaren ne suke sauka in har sun zo garin. Kayattacen gida ne mai kyau wanda ya dace da zamani Ko da Hamma Abdullahi ya kai musu abin ƙari ya daɗe yana knooking ɗin gidan ba a zo an ɓude ba. Kuma ya yi ta kiran wayar Lamiɗo tana shiga amma ba a ɗagawa. Har ya yi niyyar juyawa sai ga Sabuwa ta zo ta buɗe gidan ganin shi ne yasa ta rankwafa tana gaishe shi ya amsa lokaci ɗaya yana miƙa mata kwandunan dake hannunsa masu ɗauke da abincin ta karɓa tana yi masa godiya. "Uwardakina da Ranka shi daɗe ba su tashi ba." Ta faɗa tana kallon Hamma Abdullahi Agogon fatan dake tsitsiyan hannun shi na hagu ya kalla ƙarfe 9:50am  da man ya yi tunanin haka su ai yan Lagos ne ba sa buƙatar tashi da wuri ba irin su da sukan fita ƙwadago da sassafe ba. "Ba matsala in sun tashi ga saƙo nan daga Ammah." "Allah ya saka da alheri. Madalla mun gode." Sabuwa ta faɗa sannan suka yi sallama ya wuce zuwa motarsa ita kuma ta rufe gidan ta koma cikin gidan Duk wanda ya san matar Lamiɗo ya san ta da amintattaciyar hadimanta Sabuwa tunda duk in da ta saka kafa nan itama take sakawa shi ya sa kowa ya san ta a bangaren Ammah itama tas tasan kowa, haka ma Anitha mai kula da su Sultan duk in tafiya ta kama Balkisu ko na kwana ɗaya ne in dai tare da yara za ta yi tafiyar Anitha na tare da ita saboda kula da yaran shi ya sa itama ta san kowa kamar yadda kowa ma in ya ganta ya san amfaninta ba sai ya yi magana ko tambaya ba Hidiya da Debora kaɗai da su James ake bari a gida. Hidiya ana tafiya da ita amma sai in Bilkisu za ta je kano haka ganin gida ko kuma in za su je Daura amma yawan cin tafiye-tafiyenta ta fi yin su tare da Sabuwa da Anitha. Kitchen Sabuwa ta kai kwandunan abincin tunda masu gidan ba su tashi ba sai sha biyu na rana su da ƴaƴan su. Sai da suka yi wanka suka shirya sannan Sabuwa ta jera musu abin karin a saman dinning Akwai ruwan zafi da kayan tea sannan akwai kunin ɠyaɗa da soyayyen fanke wannan na Ammah ne, sai soyayyan ƙwai da daffaffe, sai soyayyar indomie, na gidan Hamma Abdullahi kenan na gidan Hamma Abdulrrahaman kuma soyyayar doya ce da ƙwai da plantain sai ruwan zafi, Bilkisu ta ba da umarnin Sabuwa ta ɗibar musu ita da Anitha tunda abincin ya yi musu yawa. Ita dai tea ta sha da soyayyan doya yaran kuma sun ci ƙwai da plantain Lamiɗo kuma kunun ɠyadan shi ya sha da fanke, har wani jin daɗi yake yi domin ya yi kewar abincinka Ammah na'u'i masu daɗi, ta san yana so shi ya sa ta yi masa, shi fa har gobe yana faɗa babu wacce ta san shi dari bisa ɗari irin Ammah, ko bai yi magana ba ta san abin da ya fi so da wanda ba ya so. Sai da suka gama karyawa sannan suka koma cikin ɗakin barcin su, yaran kuma Anitha ta ja su falo ta kunna musu tibi suna kallon cartoon aka bar Sabuwa da gyara in da suka ci abincin. Tunda suka koma cikin ɗakin barcin su, magana ko ta fatar baki ba ta sake shiga tsakanin miji da matan ba, shi yana zaune a wata kujera kwara ɗaya dake cikin bedroom ɗin ita kuma tana kishiɠide a gefen gado tana duba wayarta shi ma ɗin ya duba wayar tasa har ya ga Abdullahi ya yi ta kiran shi amma bai bi bayan kiran ba. Kansa kawai ya ɗan jinginar a jikin kujeran ya ɗan yi balance kafafunsa na lumshe a cikin tattausan cafet ɗin da ke cikin dakin barcin. Idanuwansa na lumshe kamar mai barci sai dai ba barcin yake yi ba, a halin shi ko awa uku zai iya yi a haka ba tare da ya gaji ba shi dai kawai yana son shuru fiye da komai a rayuwarsa. Sanye yake da riga da wando bakake, rigar mai gajerun hannu ne tana da ɗan taushi sai wandon iyakarsa gwiwan kafarsa, gargasan da ke kafafun nashi duk sun bayyana a waje. Kansa ba hula sumar kan ta kwanta haka gemunsa da sajensa, Balkisu ta ajiye wayarta kawai tana kallon mijinta tana mai jin wani alfahari. Da farko ta ɗauka tara gemu da saje ba na manyan mutane ba ne ta ɗauka na talakawa ne irin uztazan nan sai da ta haɗu da Lamiɗo ta san tara gemu ma baiwa ne da ƙasaita saboda shi ya sa take son gemu da saje. Kuma itama ta fahimci yana so, wai a haka ma yana ragewa in yana wajen aiki in suka yi video call gashi duk ya cika masa fuska sai ta ce ranka ya daɗe ya kamata a yi aski kai kawai yake ɗaga mata baya magana, tana so ta riƙa rage masa amma baya barin ta, sau ɗaya ya taɓa bari ta rage masa shima ita ce ta matsa daga ranar kuma ko ta ce za ta ce za ta yi masa sai ya ce a'a. Ita da ta so har private part ɗin sa ta dinga masa sheving amma ina ta san ba zai taɓa aminta ba. Ko fa kaya ta saka in dai jikinta ya bayyana ba ya son kallonta sai ya dinga wani kauda kai in ta matsa kuma sai ya runtse ido yana faɗin Ki je ki sauya kayan jikin ki mana" Yau ma wata riga ce a jikinta mai santsi tana da yar ciki da jaket. Da za su fita beakfast sai ta saka jaket din suna dawowa ɗaki ta cire ta zauna daga ita sai ta cikin mara hannu ta ɗan kamata amma tana da ɗan tsawo tunda ta kai wajen gwiwan kafafunta, kanta kuma da man mayafi ne ta saka ta yi rolling shima tuni ta cire, ta bar suman kan nata da ya sha gyara sai ƙamshi yake yi yana ƙyalli. Mirmishi take yi ita kaɗai tana tuna daran jiya. Ba ta ɗauka zai kula ta ba, ganin sun yini gidan Ammah kuma ga gajiyan tafiya amma suna yin shirin barci ta shige jikinsa ta lafe masa tana sauke numfashi ya birkice mata, in ta tuna irin yadda ya yi mata rawan jiki sai ta ji wani irin daɗi ya kamata. A baya kafin ta fahimce shi sai ta yi ta kuka tana tunanin ko ita mijinta baya jin daɗin ta ne ? Mata da yawa ƙawayenta ƴaƴan sarakuna da abokan karatunta masu aure suna irin hiran yadda ko gyara suka yi irin yadda mazajensu ke ruɗewa har da waɗanda ake yi ma kuka da ihu, amma ita mijinta bai taɓa mata ko sambatu ba, kuma in zai dawo haka za ta yi ta shiri ta gyara ciki da waje, daga can Kano Umma me aiko mata da kayan gyara da yawa ta yi ta sha ammah in ya dawo suka kaɗaice ba ta ganin wani canji. Sai da ta ga wani rubutun wani likitan kan maza yana bayani kan kashe kashe da rukunin maza da ta bi rubutun sa anan ne ta gano mijinta a cikin rukunin maza. Namijin da ba ya iya bayyana ƙololuwar jin daɗinsa ko da daɗin zai kashe shi ne, amma zai yi rawan jiki sannan zuciyarsa za ta tsananta bugu sannan zai ta yin zufa amma ba wai ya yi kuka ko sambatu ko wata alama ba, daga lokacin ta samu salama tunda ta fahimci duk yana yin haka kawai dai sambatu ne da ihu ba ya yi, jiya ma da ta tafiyar da ragamar ya yi ta mata nishi kamar numfashinsa zai kwace daga ƙirjinsa. Shi dai in har wajen zai yi duhu to zai iya sakin jiki a yi komai sai bayan sun natsa ne in haske ya gauraye ɗakin ya yi kamar ba shi ba, kai tana son Lamiɗo domin ta san ta yi ma sauran mata zarra samun namiji  mai kama da maza ɗari a waje ɗaya. Tana so su dinga zama suna hira duk da itama ba ta da surutu amma tana so ta ga tana yi masa hira ko ba zai yi magana ba ya yi ta kallonta da yanayin kallon shi mai narkan mata da zuciya. Amma matsalan itama ba ta iya hiran ba, da ta fara sai ta rasa me za ta ce, in dai ba hiran can Daura ba shima sama sama, har gwara ma in tana yi masa hiran Ammah har mirmishi za ta ga yana yi mata sannan in ta yi tambaya yana bata amsa jefi-jefi. Ta daɗe da shaida cewa Lamiɗo na kaunar Ammah ninki da yadda yake son mahaifiyarsa Mami ita kuma kowa ya shaida yadda take ƙaunarsa, shi ya sa itama kamar ta lasheta saboda ita ɗin Matar Lamiɗo ce, tana gani in ta je matan su Hamma Abdulrrahaman Ammah ba ta yi ta kan su, amma ita da yaranta da jikinta da komai take yi musu wahala. Da farkon auren su ba ta san dawan garin ba duk da ta san a hannun Uncle ɗin sa ya taso yayan mahaifiyarsa. Ta ɗauka mahaifiyarsa na da tasiri a rayuwarsa sai daga baya ta fahimci komai domin lamarin ma a bayyane yake. Mami da Lamiɗo in suka haɗu ban da gaisuwa ba abinda ke sake haɗa su, a waya ko sai su yi sama da wata ba su yi magana ba in ba wani abu ba ne ya taso ya kirata ba. Musamman ma dai ya fi kiranta ya gaisheta in su Islam na gida ya ce a ba su wayar shi dai yana da son yara duk da baya son hayaniya. Wayar ma da yake yi mata Ammah ce ta ce ya riƙa kiranta yana gaisheta mahaifiyarsa ce, amma mijinta Alhaji Isa akwai girmamawa mai girma a tsakanin shi da Lamiɗo shi har ya fi Mami ma jawo shi a jiki amma ita kamar ba ɗan ta ba, ko da yake da man ta ce ba ɗanta ba ne ɗan Ammah ne. Da fari har ita tana kira ta gaisheta lokaci bayan lokaci ranar dai Mami ta faɗa mata gaskiya da cewa in za ta yi kamun kafa ne ta je ta kama kafar Ammah ita  uwar Lamido ce kawai a haihuwa amma nan duniya ba shi da iyayen da suka wuce masa Ammah da Baffa kuma ta ga haka, domin a wajensa shima ba shi da iyayen da suka fisu, akwai wani zuwan da suka yi Daura ta tambayi Fulani Daura ita ta zaunar da ita ta bata labarin mafarin komai ta kuma shaida mata Mami ta yanke alaqa da duk wanda ya danganci Lamiɗo da su Ammah kawai suke zumunci, kuma ta ga hakan in za su haɗu sau nawa bayan gaisuwa ba ta taɓa ganin sun yi wata magana ko da mintina goma ba ne, Mamin ma kwata kwata ba ta yi ta kansu, ko su Sultan a matsayin jikokinta ba ta taɓa ganin ta ja su jikinta ba. Tun lamarin na ba ta mamaki har yanzu daga baya ya zame mata jiki. Ta riƙe Ammah a matsayin uwar mijinta da Baffa a matsayin uban mijinta, sannan ta riƙe Maimartaba a matsayin uba sannan ta riƙe Gimbiya Shahida a matsayin uwa Fulani Daura kuma a matsayin kaka. Mami kuma sai ta saka ta a cikin sahun wasu makusanta Lamiɗonta. Tashi ta yi tana yanga kamar yadda ta saba ta karisa kujeran da yake zaune ta zauna kusa da shi, kanta ta ɗora saman kafaɗan shi tana sauke numfashi jikinta da gashin kanta suna fitar da wani sihirtattacen ƙamshi mai daɗi. Ya ɗan motsa amma bai buɗe idanuwansa ba tun da ya san ita ce, hannunta ta tusa cikin yatsun hannunsa guda ɗaya ta jimƙe shima sai ya taya ta suka jimƙe yatsun hannunsu a tare, mirmishi ta yi har yana fidda sauti kafin ta sake lafewa daga gefen kirjinsa. Sun fi minti goma a haka sai ita ce ma ake jin sauka da hawan numfashinta amma shi ba ko a jin motsin na shi numfashin, in za su kai gobe a haka ba zai ce mata komai ba. Ta san shi ta san waye Lamiɗo, ko mai za ta yi ba zai taba cewa aa ba, mutum ne mai girmama zamannsu mai daraja aure da sauke haƙƙoƙi. Ta tuna bayan haihuwan Beena ta faɗa masa ta yi planning tunda ta samu haihuwan a jere da juna, ko faɗa bai yi mata ba ko irin ya ce me ya sa ba ta faɗa masa ba. Shi ba wanda ya isa ya gane ya ji daɗi abu ko bai ji daɗi ba fuskarsa ta iya shanye komai ba ta kuma bayyana abin da ke fuskarsa. Hausawa na cewa wai labarin zuciya a tambayi fuska to shi Lamiɗo labarin zuciyarsa sai dai a tambayi bakinsa, domin komai bin kwafkwafin ka ba ka isa ka fahimci abin da ke cikin zuciyarsa ba. "Ranka ya daɗe." Ta kira shi kamar yadda ta saba kiran shi. Bai amsa ba kuma bai buɗe idanuwansa ba, ta ɗan ɗago ta kalle shi ta san ba zai yi magana ba amma tana da tabbacin yana jin ta. "Ashe kuma abin da ya faru da Autan Ammah kenan? Ta faɗa lokaçi ɗaya tana ɗan wasa da gargasa hannun shi, da hannunta guda ɗaya. Shuru na wani lokaci sannan ya buɗe idanuwansa da suka ɗan ƙanƙance sun ɗan kuma sauya launi. Kallon shi ta yi, shima sai ya kalleta yadda ya kalletan ne ya sa ta san bai san komai ba. "Ba ka sani ba? Ta faɗa cikin sanyin murya lokaci ɗaya tana goga masa gashin kanta samana kirjinsa cikin wani salo. Bai yi magana ba amma ta ga ya ɗan jinjina mata kai alamun bai sani ba. Sa sauri ta tashi daga kan kirjinsa tana fuskanshi. "Jiya da na ganta wani iri na tambayeta ko ba ta da lafiya ne? shi ne fa Ammah ke ba ni labari." Ya yi mata kuri da ido yana son jin ƙarshen maganar..ita kuma sai ta yi shuru tana nazarin shi, yana so ya ce mata me Ammah ta ce? Amma kuma bakin shi ya gaza furtawa. "Uhm labarin fa ba daɗi ga tausayi yaron nan ya zalunci Autar Ammah" Ta faɗa tana matse hannunta cikin na shii. Idanuwansa ya ke buɗewa a kanta, zuciyarsa har wani tsalle ta yi amma bai nuna ba, yana nan a yanayin shi tun farko. Ita kuma Bilkisu ba ta fahimci ya matsu ya ji labarin ba sai ta cigaba da faɗin" Ta rame fa duk ta yi wani iri. Ai ka ganta ko? Ta gama faɗa da sigan tambaya. Ya yi shuru kawai yana kallon ta. "Ko ba ka gan ta ba? Ta sake tambaya tana kallon shi, sai da ta ja yatsunsa sannan ya ɗan lumshe ido ya buɗe lokaci ɗaya yana mai jinjina mata kai alamun e ya gan ta. "To ba ka ga ta rame ba? Duk ta yi fari ashe ma da ciki ya sake ta." Hannunta dake cikin na shi ya matse har sai da ta ɗan kalle shi lokaci ɗaya kuma ya zare hannun shi ya yi shuru ba tare da ya yi magana ba. Bilkisu kuma ta shiga ba shi labarin da Ammah ta ba ta ganin kamar Lamiɗon ya tattara hankalin shi a kanta. Har ta gama bai ce komai ba amma hankalinshi da natauwarshi yana kanta ya yi mata kuri yana kallonta kuma yana sauraranta. "Ammah ta ce hankula sun tashi sun shiga damuwa amma dai yanzu da sauƙi tunda an kwarari wata biyu cikin na uku. Ummu Salman ce sai a hankali har yanzu ba ta daina yan koke koke ba.". Ta gama ba shi labarin kuma ya saurare ta amma bai ce mata komai ba. "Wai ko Ammah ba ta faɗa maka ba? Ta sake tambayan shi. Sai wannan karon ya yi magana "Ba ta faɗa ba." Kawai ya iya cewa sannan lokaci ɗaya ya miƙe yana kallonta kafin ya ce" zan yi wanka" Da ga haka ya wuce ta ya fara tafiya a hankali cikin takunsa har ya shige tiolet ta bishi da kallo, ko maganar ta dame shi ne ko ba ta dame shi ba, ba za ta iya sani ba. Amnma ta yi mamakin yadda bai sani ba ko Ammah ba ta faɗa masa ba ta yi tunanin amininshi KB zai faɗa masa, ta wani fannin kuma ba ta yi mamaki ba sanin halin mijin nata, ba ko da yaushe kake samunsa ba. Za ka iya tura masa saƙo sama da wattani bai gani ba, kuma sanda aka yi abun yana can wajen aiki ba lalle ya sani ba, ita dai ta tausaya ma Ummu Salma, ƙaramar yarinya ta haɗu da jarabawa, ita fa ta ga ƙokarin su Ammah yadda suka yi ma Ummu auren wuri haka a lokacin ta yi ta ce ma Lamido ta yi ƙarama da aure bai ce mata komai ba, ga shi nan ya sake ta ya wulakanta ta da ƙananun shekarunta. Ta shi ta yi ta ɗau wayarta ta bar ɗakin domin ta san in gogan ya fito ya iske ta ba zai ji daɗin shiryawa ba, shi ya sa ta bar masa ɗakin ta koma ɗayan bedroom ɗin ta ɗan kwanta. Shi ko bai wani daɗe ba ya fito daga wankan, sai da ya tabbatar da Balkisu ba ta ɗakin sannan ya saki jikinsa da ga shi sai towel ɗaure a kugunsa ya fito ba ya ɓata lokaci wajen shiryawa yanzu ma cikin lokaci ya shirya ya saka farar shadda gezner ɗinkin zamani riga da wando, rigar yau har ta fi sauka masa saboda yau jumma'a za su je masallaci tare da su Baffa, wani nishaɗi yake ji tun safe na tunowa da rayuwar baya amma labarin da Balkisu ta bashi ya ɗan hanashi sukuni. Taje kansa ya yi da gemunsa da yake tunanin yau zai je gyaran fuska a rage masa gashin fuska. Turare ya fesa kaɗan saboda shi ba ya son kamshin turare ya yi masa karfi da yawa yanzu kan shi zai fara ciwo, ko Balkisu ta cika turare har kansa yake hawa in kuma ya shaƙa da yawa haka zai yini da ciwon kai, bai taɓa ce mata ta daina sawa ba, saboda shi a tunanin shi saboda abin da ba ya so shi kaɗai ba zai tauye mata haƙkinta tunda ita tana so ba. Shi ya sa ko ba ya son abu ba ya faɗa, gani yake yi kamar son kai ne. In kuma yana son abu shima ba ya faɗa gani yake yi don shi kaɗai yana son abu kaza kamar ya shiga haƙƙi ne ya ce kowa sai ya so abinda yake so ko ya zama irin sa ba. Sai ita Bilkisun ce da kanta ta gano ba ya son mu'amala da turaruka tunda in ya yi birthday tana siya masa a matsayin gift zai karɓa amma sai shekara ta sake zagayowa bai taɓa amfani da shi ba, uban turarukan dake ɗakin shi kamar za a buɗe shago amma baya amfani da su tun daga lokacin ta fahimci bai cika son ƙamshi ba, ita kuma gata tana son ƙamshi tana mu'amala da turare sosai in ka yi mata kyautar turare ba ta mantawa. Ba ta daina amfani da shi ba amma in suna tare sai ta yi amfani da mai sauƙin ƙamshi, ita fa koda yaushe jikinta a cikin ƙamshi yake duk bayan wata ɗaya tana zuwa a yi mata gyaran jiki na skin care. Shi ya sa fatar ta kamar ta turawa wajen taushi da santsi sannan ba aikin da take yi, daga zuwa asibiti ta duba patients shike nan ta dawo gida ta kwanta. Sannan gaba da baya tana cikin jin daɗin rayuwa. Kan kujeran da ya tashi ya koma ya zauna da wayarsa a hannu ƙiran samsumg ita ce wayar da yake amfani da ita na Family, shi in ba zai yi kira ko an kira shi ba sai ta yi kwanaki bai yi amfani da ita ba, a wajen aiki kuma suna da wayoyin aiki shi ya sa. Yana so ya tambayi wani labarin abin abin da ya faru amma ba zai iya ba. WhatsApp ya buɗe ya shiga, 24/7 datar shi tana buɗe ne tun a can ma wajen aiki suna da wifi a Lagos ma haka. Ta kwana a kunne saƙonni su yi ta shigowa amma sai a fi wata bai duba ba. Tun ballatana in yana wajen aiki bai cika duba wayar ba. Wasu saƙonnin ma sun fi wata biyu bai duba ba. Ya ga saƙon Mahma tana tambayan lafiyan shi? Giransa guda ɗaya ya sosa da hannu ɗaya yana jin nauyi , bai kyauta ba ya kamata ya kira Mahma. Har da saƙon Maimartaba yana faɗin sun ji shuru kwana biyu ba a samun wayarsa Fulani ta damu. Bai amsa ma wannan ba tunda lokacin da ya koma Lagos ya yi magana da su gabaɗaya. Ƙasa ƙasa ya yi ta yi, can ne ya gano group ɗin Ammah da Baffa ya dai san an buɗe amma bai taɓa bibiya ba sai yau ya shiga ya ɗan duba saƙonni. Ya ga Date ɗin da Hamma Jibo ya sanar da labarin da Balkisu take faɗa masa an kwarari wata biyu cikin na uku ma. Sake sosa giran shi ya yi, haka ne ƙololuwar nuna damuwarsa, tunani yake yi ko shi ya sa daga Baffa har Ammah duk suka rame masa a ido, bai yi magana ba ne amma a zuciyarsa sai da ya ce duk sun rame amma sai ya danganta haka da ɗan daɗewar da ya yi bai gan su ba. Fita ya yi daga group ɗin, ya je ya nemo KB da sunan shi ke a matsayin Friend a wayar Lamiɗon. Sai ya ga ma ya yi masa mgana. "Amini mutanen Jimeta." Haka ya rubuta masa dubawa ya yi sai ya ga yana online. Rubutu ya fara yi na wani lokaci kamar zai rubuta wani abu ashe kalma ɗaya ne ya rubuta. "Amini." Ya ɗan ja fasali kamar yana ganin sa. "Me ya faru..? Ya sake rubutawa ya tura masa sai kuma ya dakata kawai yana kallon wayar. "Naam Amini ya gajiya! Ya baƙun ta? "Me ne ya faru kuma!? A ina? Duk wayar na hannunsa saƙonnin suna ture juna suka shigo Sai ya fara rubutu sai ya goge ya yi ya kai sau uku sannan ya samu ya rubuta. "Ummu Salama." "Me ya samu Ummun? Hamma Kabiru ya turo masa cikin mamaki. Haushin chart ɗin Lamiɗo yake ji magana ba magana ba ya rabata ya ɓata maka lokaci. Kawai sai ya kira shi Video call kamar ba zai ɗauka ba sai dai ya ɗaga kiran. Hamma Kabiru ya bayyana a cikin lap na asibitinsu yana sanye da suit da farar rigar lapcot ɗin sa. A jikin lapcop din an rubuta sunan shi.. Kabiru Hadi Baba. "Amini wai me ya faru da Ummun ne? Ya faɗa yana kallonsa, shuru ya yi masa yana kallonsa sanin halin shi ya sa ya ce" Wai ko maganar abin da ya faru da sakinta da ɗan iskan yaron nan ya yi? Sai da ya ɗan lumshe idanuwansa sannan ya ɗan gyaɗa masa. "Kai ai an kwana biyu Amini, lokacin kana can wajen aiki shi ya sa ban faɗa maka." Nan shima ya shiga sanar da shi duk abin da ya faru "Amini na so Baffa ya cire hannunsa mu kai yaron nan kotu amma kasan dai halin Baffa, Ammah ma ta goya masa baya. Ya sako yarinya ga shi ya barta da wahalan ciki tunda ya sake ta an ce ba ta kara lafiya ba, kullum kuka da rashin cin abinci, ita a damuwa su Baffa ma cikin damuwa. Amini da a ce su Baffa sun matsa ma Ummu Salma ta cigaba da karatunta da yanzu duk wannan abubuwan da suka faru wallahi ba su faru ba." Ya karishe faɗa yana jin haushi in ya tuna cin mutumcin da Habib ya yi musu. Shuru kawai Lamiɗo ya yi yana jinsa ba tare da ya yi magana ba. "Wai yaron nan ne zai ce shi ba son Ummu yake yi ba auren sha'awa ya yi da ita yanzu kuma tunda ya gama moranta bari ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda" Lamiɗo ya sake sosa giran shi na dama wannan karon kansa ya duƙar ƙasa bai kuma yi magana ba "Ya ce ba ya son cikin jikinta tunda ya ce ta zubar ba ta zubar ba. Baffa kuma ya ce ta haifa su suna so kuma za su riƙe, ka ji halin da ake ciki ni tun zuwan da na yi ma ban koma ba, ga tausayi in ka ganta amma haushinta zai sa in kana kusa da ita ka yi mata dukan tsiya" Lamiɗo ya ɗago yana kallon shi. "Me ya sa? Ya tambaya a hankali kamar ba ya son magana. "To Abdulrrahaman na faɗa mini har yanzu tana son wannan shegen bayan ya gama tozarta ta, saki uku fa ya yi mata Amini bayan ya haɗo ta maganganun cin mutumci, shi ne har yanzu take so? Wallahi da ina garin nan sai na taka wuyanta tunda ita shashasha ce." Sai da Lamiɗo ya motsa bakinsa ya ɗan murmusa. Amma dai bai yi magana ba shi kuma Hamma Kabiru ya shiga faɗa ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, shi dai kawai su Baffa yake ba ma laifi da ba su yi ma Ummu aure ba da duk haka bai faru ba ya manta da zanen kaddaran bawa ba ka iya guje masa. Gajiya Lamiɗo ya yi ya motsa bakinsa ya katse Hamma Kabiru sanin halin shi in ya fara kawo hujjojinsa sai fa kowa ya fahimce sa. "Ammah ta damu ko? Shi ya sa ta rame ita da Baffa." Ya tambaya ɗaya bayan ɗaya. "Ai damuwa ta zama dole Amini, gwara ma Baffa ana iya gane damuwarsa Ammah ce sai dai ta kunshe ita kaɗai." Shuru ya yi, Ammah tana cikin damuwa duk ta rame baiwar Allah. Ko saboda Ammah da yana nan aka yi haka sai ya saka an yi ma yaron nan ladabi tun da ya saka Ammah damuwa ita da Baffa. Lamido gajiya ya yi da tsarin Kabiru ya kashe wayarsa ya ce zai je gida za su je masallacin jumma'a da su Baffa, amma ya ce in ya dawo gida za su yi magana. Hula ya baƙa saka da wani rufaffen takalmi mai rufewa. Har ɗaki ya bi Balkisu sai ya isketa ta yi barci har bargon ya ɗan gyara mata sannan ya fita. A falo ya iske su Sultan suka naɗe shi suna kiran sunan shi, kaya ya ce Anitha ta sauya musu tare da su zai fita ba daɗewa aka shirya su Sultan ma kamar ubansa farar shadda ya saka har da hula Beena kuma wata riga ce yar kanti a jikinta pick colour ga takalminta na mata cover mai kalan pick, gashin kanta an kama mata da kananun ribbors masu kala-kala. Ganin ba a saka mata hula ko hijabi ba ya sa ya ce Anitha ta nema mata hula saboda Ammah za ta yi magana ko Baffa in su ka ganta ba ɗankwali ko hijabi. Shi ya tuka su zuwa gidan Baffa, Ammah na ganinsa da yara ta tarbesu. Sultan da Beena sun saba da kakarsu suka make suna kiranta da Ammah. Ita kuma ta rumgume su tana murna. Da su kaɗai Ammah ke wasan jika da kaka domin tana ta ce ma Sultan ya yo wanka yana so ya kwace ma Baffa gwammati a wajenta ko? Baffa ma da ya fito cikin manyan kaya ya ce ina ai ba wanda ya isa ya ture gwamnatinsa. Ummu na cikin ɗaki tana jin su amma ba ta fito ba. Tana jin zuwan su Hamma Abdulrrahaman da tafiya su masallaci su huɗu har da Hamma Abdullahi. Sultan ma sun tafi da shi Beena kawai aka bar ma Ammah tana ta fama da ita, yarinya akwai shagwaɓa ta ce wannan za ta ci sai an bata ta ce wannan Ammah kuma ba ta gajiya. Kafin su dawo Ummu ta fito ta shigar da ruwa ɗakinta karma ta nema daga baya, ba ta kaunar ma su sake haɗuwa har sai sun tafi. Nan gida suka dawo a falon Ammah suka ci abincin suna ta hira duk da shi ɗan kasaitar ba a jin muryansa sai dai ta su Hamma Abdulrrahman. Sai can yamma suka watse, Allah ya taimaketa har suka bar gidan ba ta fito ba kuma ba wanda ya neme ta sai Baffa shima sai bayan ya dawo sallan mangariba ya zo ya duba ta. Kusan satin su Lamido ɗaya a jimeta suna hutawa. Kullum sai ya zo gidan Ammah shi da yara Balkisu kuma bai wuce sau uku ta zo ba, tana gida tana hutawa amma dai ta leka gidajensu Hamma Abdullahi Lamiɗon ma Ammah ta tura su tare da matarsa ta shi gidan Ummin ikki sun gaishe ta. Ranar da suka yi sati suka tafi Jalingo gidan Hamma Kabiru kwanan su biyu suka dawo daga nan Ammah ta ce ya kamata su je Mubi ana ta tambayan shi tunda ya daɗe bai je ba, suka shirya tafiyan da Hamma Abdullahi da matarsa sai shi Hamma Lamiɗo da iyalan na shi a helux ɗin Lamiɗo suka tafi suka yini suka dawo. An ce Hamma Lamiɗo ya yi ta rabon kuɗi ga su Baffa Umaru da iyalansu har gidajen su Umma Balki duk ya je haka Hamma Abdullahi ya zo yana faɗa, shi daman mai  wuyar Ammah ta yi magana ko bai yi ra'ayi ba zai je. Ummu dai ba ta sake bari sun haɗu ba amma dai sun sake haɗewa da Balkisu da yaran tunda ko da yaushe suna gidan. Lamiɗo bai yi ma Ammah maganar Ummu kai tsaye ba ya dai ce ta daina saka damuwa a ranta kar cuta ta kamata ta ce za ta daina in sha Allahu. Bai kara ganin Ummu Salma ba, sannan bai sake tambayan wani game da ita ba, suma mutanen gidan ba wanda ya yi masa hiran abin da ya dangan ce ta. Suna da kwana goma da zuwa suka tafi Daura. Daga can Balkisu za ta koma Lagos da yara saboda aikinta da makarantan yara amma shi Lamiɗo zai dawo ta Jimeta kafin ya koma Lagos. **** *KATSINA STATE, DAURA.* *MASARAUTAR DAURA.* Garin Daura karamar hukuma ce da ke cikin Jihar Katsina. Garin yana cikin jihar katsina ne a arewa maso yammacin Nigeria, kuma ya yi iyaka da jamahuriyar Nijar ta wajen Damagaram daga arewa. Masarautar Daura Jiha ce ta addini, da ta gargajiya a Arewacin Nigeria. Sannan an kira Masarautar Daura a matsayin ɗaya daga cikin kasashen hausa bakwai, domin itace tare da Biram, Kano,Katsina, Zazzau, Gobir da Rano. Wanda zuriyar ƴa'ƴan Bayajidda suka yi mulki, tare da Daurama da magira,(matarsa ta farko)Jami'ar calfornia's Afircan. American studies na nufin Daura, da kuma Katsina a matsayin tsofaffin kujeru na al'adun musulunci  da ilimantarwa. Akwai al'adan da suke gudanawar a garin Daura bikin hawan sallar gani na ɗaya daga cikin bukukuwan da masu sarauta da dawaki ke kece reni a cikinsa, wanda kuma za a iya cewa ya samo asali ne daga Daura sannan garin ya fice wajen gudanar da wannan al'adan. ** Tun zamanin sarkin Jafaru ɗan Umaru zuru'an su Lamiɗo ke mulkin Daura sama da shekaru sittin da suka gaba ta. Mai martaba Sarki Alhaji Dr. Nasiru Daura ya yi hau karagan mulkin Daura shekaru talatin baya sannan shi ne sarki na 42 a lissafin masarautar. Kuma ya samu nasaran hawa karagan ne bayan rasuwar mahaifinsa tsohon sarki Mai martaba Muhammad Shitu. Masarautar Daura kayattaciyar masarauta ce mai ɗimbin tarihi. Lokacin da suka iso filin jirgi na Umaru Musa yar'aduwa da yake an san da zuwan su tuni wasu aminttatun Mai maitarba irin su Waziri da wambai tare da rakiyan dogarai sai ƙanin Lamido Saleem(Sardaunan Daura Hakimin Daura) suka zo tarban su. Shi kaɗai ne ke karatu a Nigeria shi ne kuma ke gida Daura tare da Maimartaba kuma yawancin yana wakilta shi zuwa wajen taro ko wani abu da ya shafi sarauta, mutanen garin Daura suna tunanin Saleem(Hakimin Daura) ne zai gaji Sarki duk da yana da karancin shekaru domin bai wuce 26 ba amma yana da hikima da hangen nesa sannan mai fara'a da son mutane saɓanin Lamido da ba shi da fara'a sosai, sannan ba mazaunin masarauta ba, amma shima an yi shaidarsa da kyakyawan zuciya da son takalawa da matasa, duk da kuma shi ke da Sarautan Yarima Daura mai jiran gado hakan bai hana  wasu tunanin Hakimin Daura a matsayin wanda ya cancanta ba, duba da shi jinin Sarauta ne gaba da baya saɓanin Lamiɗo da iya bangaren uba ne sarautarsa take da ƙarfi. *FARGAR JAJI SECOND PROMO.* KU BIYA #800 A MADADIN 1K, TURA TA WANNAN ACCT ƊIN. 9069067488. JAMILA UMAR OPAY. 08032773332. 09069067488. VALID 24HOURS. MUN GODE. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" *FARGAR JAJI SECOND PROMO.* KU BIYA #800 A MADADIN 1K, TURA TA WANNAN ACCT ƊIN. 9069067488. JAMILA UMAR OPAY. 08032773332. 09069067488. VALID 2HOURS. MUN GODE. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t *18* A mota ɗaya Lamiɗo da Saleem suke cikin wata baƙar Hilux, tana daga cikin motocin Mai martaba. saboda Lamiɗo ne, ya sa a motocin alfarma ake zuwa tarbansa in dai ya zo Daura. Ba sai Mai martaba Sarki ya yi magana ba kowa ya shaida yadda yake son Lamiɗo ba ga iya ahalin masarauta ba har jama'an gari saboda yadda yake yawan zencen sa ko yana nan ko ba ya nan. "Ranka ya daɗe barka da zuwa Garin Daura." Saleem ya faɗa yana mai kallon yayan na shi wanda tunda suka shiga mota suka fara tafiya bai yi maagana ba. Balkisu da yara suna motar gaban su tare da hadiman Mai martaba. "Saleem" Ya kira sunan shi cikin yanayin maganarsa. "Ranka ya daɗe an iso lafiya? Saleem ya sake faɗa, sanye yake cikin rawaninsa tsaf ya fito a Hakimin Daura kuma Sardauna. "Mun same ku lafiya? Ya makaranta? Lamiɗo ya faɗa yana kallon shi. "Lafiya lau. Allah ya taimake ka. Allah ya kara maka lafiya da arziƙi Allah ya tsare mana kai Yarima." Saleem ya gama faɗa har yana jinjina masa hannu. Mirmishi ya yi har sai da fuskar ta nuna kafin ya jinjina kai. "Ka san ba na so ko? "Tuba na ke, a gafarce ni ranka ya daɗe" Lamiɗo ya yi wani mirmishi mai tsada kafin ya ce" Hakimin Daura" "Naam Allah ya taimake ka." Saleem ya faɗa har yana ɗan rusunawa cikin girmamawa. Kafaɗansa Lamiɗo ya dafa yana sake kallon shi. "Sardaunan Daura." Ya sake faɗa a hankali kamar ba ya son magana. Ko direba da Wambai dake gaban motan ba za su iya cewa ga abin da Lamiɗo yake faɗi ba. "Allah ya ja da zamanin Yarima." "Ka daina mu'amalanta na kamar sauran mutane." "Tuba na ke yi ranka ya daɗe." "Am your brother, mu yi mu'amala kamar yan'uwan juna." "A yi mimi afuwa. Tuba na ke yi Ranka ya daɗe." Ya sake faɗa yana mirmishi ba zai dai bari ba kenan. Lamiɗo ya ɗan sake dukan kafaɗansa ba tare da ya sake magana ba "Allah ya taimake ka. Tuba na ke yi. Tuba na ke Yariman Daura. Yarima mai jiran gado" Ya san ba ya son wannan kirarin shi kuma yana yi masa ne saboda ya yi magana. Ba uwa ɗaya suke ba, ba kuma su san juna a shekarun baya ba amma yanzu da suka san shi a matsayin ɗan'uwa na jini suna son shi, musamman ma Saleem ɗin jin Lamiɗo yake yi kamar uwa ɗaya uba ɗaya saboda kyawawan hallayansa duk da ba ya da yawan magana da son hayaniya akwai kyakyawan alaqar Yaya ga ƙaninsa a tsakanin su, suna waya sannan in dai ya zo garin kuma Saleem na nan a lokacin har ya koma duk in za su je suna tare. Shuru ya yi kawai yana kallon sa ya ɗan kwantar da kansa a jikin kujeren motar. idanuwansa na lumshewa lokaci ɗaya yana kallon hanyar da suke wucewa zuwa Daura, yana jin wani alfahari na samun Lamiɗo a matsayin ɗan'uwa. Shi ko Lamiɗo hanya yake kallo iska na ɗan shigarsa, wani natsuwa ya je ji na kama sa a duk lokacin da ya zo Daura. Ba domin ba ya son duk abin da ya shafi sha'anin Sarauta ba da ace shi ba ɗan kowa ba ne to da ya ji daɗin rayuwarsa a Daura. Ya yi rayuwa a Jimeta amma yadda yake son yanayin garin Daura da jama'ar cikinta na musamman ne, a cikin zuciyarsa komai na garin ya yi masa damuwarsa ɗaya abubuwan sarautan nan mai hana kunnuwan mutum su huta, in ya je Daura har ya koma cikin ganin jama'a yake yi, in kuma za a yi taron Fada Mai martaba sai ya matsa masa ya je, kafin a gama zaman fada ya shiga mummunan takura a rayuwarsa. Shi ba ya son hayaniya, ba ya son magana ya fi daraja ya ji duniyar ma ta yi tsit gabaɗaya. Amma in dai yana amsa sunan Muhammad Nasiru(Yariman Daura) ba zai iya guje ma abubuwan da suka shafi sarauta ba a baya ya yi haka amma jini da sarauta suna cikin jinin jikinsa ne ko ba a Daura ba shi ɗin kasaitattace ne. Har suka iso garin Daura magana ba ta sake haɗa shi da ɗan'uwansa ba shima kuma kanin na shi ya san waye shi bai takura masa ba shima a cikin motan lamo ya yi kamar baya ciki. Motocin da su Bilkisu ke ciki kofar shashen cikin gida ta nufa, su kuma direct motar su fada ta nufa, tuni bushe-bushe da kaɗe-kaɗe suka cika fada na zuwan Yariman Daura. Motarsu ko gama fakin ba ta yi ba dogarai suka yi caa,tuni yar natsuwanr da ya fara samu ta yi ta kanta ga hayaniyar mutane ga busa wanda ya ke sake bashi tabbacin ya shigo garin Daura rayuwarsa ta sauya ya tashi daga Muhammad matuƙin jirgin ruwa ya koma Muhammad Nasiru(Lamiɗo) mai sarautan Yarima mai jiran gado duk da dai shi kam ya san ba wani gadon da ya je jira ba zai iya yin wata sarauta ba domin ba zai iya ba. A guje dogarai suka buɗe musu ƙofofin motar shi da Saleem, da yake a tawagan da suke je ɗauko shi har da masu kakin masarauta. Tun kafin ya fito daga motar dogarai suka zube a kasa suna faman kawo gaisuwa.. Daga lokacin ya ji kamar ana sauya shi komai na shi ya sauyawa kamar ba shi ba. Shi ya sa aka ce in dai kai jinin sarauta ne, duk in da ka shiga ba zaka ɓuya ba. Tuni Lamido ya rikiɗe ya fito a Yariman Daura sak. Kafafunsa farare masu cike da gargasa ya fara sawowa waje masu ɗauke da takalma rufaffu bakake na fatar damisa masu kyau, sannan gangar jikinsa ta fito. Dogon Yarima mai ƙwarjini da Haiba. Haka wani dogari ke faɗi kamar zai saka kansa a kasa saboda girmamawa. Sanye yake da wani baƙin yadi mai ɗan santsi ɗinkin riga da wando amma tazarce, sai ya ɗauki jaket baƙa na saƙin sarauta a jiki ya ɗora a sama. Kansa da hula baƙa ta dara shigar bakake ya yi daga samansa har ƙasa, ya rage gashin fuskarsa sai haibansa ta sake fitowa amma suman kansa na nan domin hulan ma a saman sumar ta zauna sannan gefe da gefen wajen kunnuwan shi kana ganin suman da ya tara da ɗan yawa. "Barka da zuwa Yariman Daura. Sauka lafiya Namijin fama. Sauka lafiya Yariman matasa. Farin Yarima kake dogo ɗan Nasiru jikan Shitu, barka da zuwa shalelen Masarautan Daura. Barka da zuwa kasaitattacen Yariman Daura. Jama'ar Daura na yi ma dogon Yarima barka da zuwa." Hannu kawai yake ɗaga musu ba ya magana fuskar nan ta sa ta sake ginshiƙewa saboda jinin mulki ne ya motsa a cikin jininsa. "Takawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki. Angon Balkisu Baban Muhammadu, takawarka lafiya Amintattace, takawarka lafiya mai alheri takawarka lafiya Yarima Allah ya ƙara tsawon kwana Allah ya tsare gaban ka da bayan ka." "Barka da isowa Hakimin Daura takawar ka lafiya Sardaunan Daura." Suke ta faɗa kamar za su shiɗe suna mai ƙanƙantar da kan su. Hannu kawai ya ɗaga musu ya wuce tawagan suka bi bayan shi zuwa fadar Sarki Mai martaba Alhaji Dr Nasiru Daura in da yake gudanar da zaman fada a daidai lokacin. "An gaishe ku. Yariman Daura ya amsa muku." "An gaishe ku. Hakimin Daura ya gaishe ku." Haka shugaban dogarai yake ta faɗa. Da irin takunsa na jaruman maza gif! Gif suka shiga fada, suna shigowa suka duƙa gaban Mai martaba da ke zaune kan wata kyakyawan karaga cikin naɗi idanuwansa ne kawai a ake gani su kuma su Wambai suka jeru cikin masu zaman fadan da suka sha rawani. "Allah ya ja zamanin ka na kawo Yarima gida kamar yadda ka bukaci na jagoran ci haka." Saleem ya faɗa cikin ɗan rusunawa. Jinjina kai Mai martaba ya yi alamun gamsuwa, ko da ba a ganinsa fuskar sa amma kowa ya shaida yau yana cikin farinciki. "Sarki ya gode ma Hakimin Daura. Allah ya ja zamanin Sardaunan Daura." Lamido ne ya ɗan rankwafa cikin yanayin maganarsa ya ce. "Allah ya tamaimaki Mai martaba fata duk mun same ku lafiya? Maimartaba ya sake jinjina kai. Dogarai suka ɗauka. "Sarki ya gaisheka Yarima, sannan yana yi maka maraba da sauka a masarautar Daura." "Na gode. Allah ya kara yawan rai da lafiya mai ɗorewa." Lamiɗo ya faɗa yana ɗan jinjina kansa. "Amin Yarima. Allah ya ja zamanin ka, Mai martaba ya amsa." Ɗaya bayan ɗaya Lamido ya juya yana kai gaisuwa ga walikan fada suna amsawa da an gaishe da Yariman Daura barka da sauka, Duk da haka fuskar nan ta shi ta nan a ginshiƙe cikin irin yanayin sa. Yarima ya amsa, Yarima na godiya. Wani dogari ke ta amsawa. Ba su daɗe a fadan ba Mai Martaba ya ba da Umarnin Hakimin Daura ya raka Yarima zuwa bangarensa domin ya huta. Bangaren Yarima in da yake sauka in ya zo Daura. Shashe ne mai girma a cikin masarautan. Har kofar shashin Saleem ya raka shi. "A fito lafiya Ranka ya daɗe." Kai ya jinjina masa kafin su rabu shi ya juya shi kuma ya shige ciki tuni falon ya cika da hadimai mata wasu na jera abinci wasu na shigowa da shi. "Barka da sauka Yarima. Barka da isowa ranka ya daɗe." Magajiyar hadiman Fada ta faɗa cikin ladabi bayan ta zube kasa, haka ma sauran hadimai mata suka yi suna mai zubewa a gaban shi. "Yauwa na same ku lafiya? Ya faɗa a iya fatar bakinsa sannan ya shige wani korido. Ba wacce ta sake motsi sai da ya nisa da in da suke sannan Magajiyar hadimai ta miƙe tana ba su umarnin su yi sauri su jera komai Yarima ya shigo. Dattijuwa ce ita ce shugaban hadimai mata na gidan Sarki gabaɗaya, sannan amintataciya ce a wajen Uwargidan Maimartaba Gimbiya Shahida da umarninta ne ta ce ta yi jagoranci a tanadar ma Yarima da iyalansa duk abin da za su nema. Cikin lokaci suka gama shirya komai suka bar shashen gabaɗaya. Shi ko Lamiɗo ɗakin shi na musamman ya shige ya yi wanka ya ɗan kwanta. Shashen na da girma ga dakunan barci ne ba adadi shi ya sa har ya yi barcinsa ya samu natsuwa ya tashi kafin La'asar bai ji ko motsin Balkisu da yara ba suna wani shashe a cikin bangaren na dabam ita da su Sabuwa. Alwala ya yi ya fita sanye da jallabiya fara wannan karon sai ya dora rigar sarauta mai ruwan zuma haka ma hulan kansa ta sakin gidan sarauta ne haka ma takalmin kafarsa na irin takalman da yayan sarakunan kan saka ne, ga kaya nan birjit a cikin clothset dinsa na bangaren gidan Sarki sai wanda ya zaba sai saka. Yana fita suka haɗe da Saleem shima da shirin zuwa masallacin. "Barka da fitowa Ranka ya daɗe." Lamido bai yi magana ba amma ya jinjina kai. Yana daga cikin shaidar da ya samu, Lamido mutum ne mai daraja lokacin salla bai taba zuwa garin Daura ya yi fashin salla cikin jam'i ba. Tare suka yi salla da Mai martaba a sahun gaba sai karamin kanin su Mujahid(Amir) ɗan shekara goma sha shidda , Mai martaba ransa fes ga shi zagaye da yaran shi maza yamma da kudu. Bayan an idar da salla limamin masallacin ya yi ɗan tunsarwa akan zumunci da falalar nasu sada shi, daga nan Lamido da Saleem suka koma bangaren shi duk da jama'a na son ganin shi amma Hakimin Daura ya ce Yarima na hutawa ne sai zuwa gobe. Tare suka ci abinci a bangaren Lamiɗo  kamar yadda suke yi in ya zo garin tare da Mujaheed da suka taho tare da shi, ita Balkisu sun riga sun ci na su abincin tuni har an raka ta shashen ɗakunan matan gidan daga ƙarshe ta ci burgi a bangaren Fulanin Daura. Bayan sun gama cin abincin sun ɗan natsa Lamido ya sauya kaya farar shadda har da babban riga, kayan da in ba a Daura ba, ba ya mu'alama da su. Da rakiyar Salem da Muhajeed ya fara isa bangaren Uwar gidan Mai martaba yar kuma tsohon wazirin Daura. Gimbiya Shahida, ita ce mahaifiyar Saleem kuma ita ce Fulani ta aura ma Mai martaba lokacin yana tare da Fatima. Gimbiya Shahida ya'yanta huɗu ne uku mata namiji ɗaya. Sakeena ce babba tana auran jakadan nageria a England. Tana can tare da iyalanta(ita ce kuma ke da sarautan Magiyar Gah mata na garin Daura) Sai Munnira(Magajiyar Hah matan garin Daura) auren zumunci aka yi mata tana auren yaron Hajiya kilishi yayar Mai matarba Sarki Nasiru. Sai Saleem Hakimin Daura, sai auta Badi'atu wacce ba ta daɗe da yin aure ba. Ba su wani jima a shaahenta ba bayan gaisuwa da yi masa maraba ya yi mata sallama sai kuma bangaren Gimbiya Hadiza wacce ke bin ta. Ita kuma ya'yanta uku. Ita ɗin jikar sarkin Kano ce. Hajiya Sadiya(Bata tuman Daura) tana auren yaron Wambai ne, suna kasar portugal da zama. Sai Hajiya Zainab(magajiyar Jah mata) Tana aure anan cikin garin Daura, sai Hajiya Safiyya(Yakumon Daura) tana aure a masarautar Gusau. Itama bayan gaisuwa suka bar nan zuwa shashen mai bi mata. Gimbiya Maimuna ɗiyar marigayi sarkin katsina da ya rasu. Ya'yanta uku Yazeed(ɗan ruwatan Daura hakimin Babban mutum) yana can kasar waje yana karatu. Sai Sagir(ɗan burum ɗin Daura) shima yana can kasar wajen yana karatun lauya. Sai Auta Hafsat tana sakandiri. Sai shashen ta karshe Gimbiya Amratu. Ita kuma kakanta ƙani yake wajen marigayi Mai martaba Sarki Muhammad shitu kenan kakkani suka haɗa da Mai martaba sarki na yanzu, ita ɗin yar Daura ce kuma yar masarauta. Yaranta biyu ƙanana ne Mujaheed(Amir) da Mujadala(Amira) Nan ma gaishe ta suka yi suka fice, lamarin mulki da saurata sai wanda aka haifa a cikin shi ko gaisuwan ma ba wani mai yawa ba ne, shike nan an yi an gama. Daga nan sai suka ci burki suma a katon bangaren yar Sarki jikan Sarki, matar Sarki sannan uwar Sarki. Hajiya Raƙayya(Fulani Daura). Fulani na da mayan ya'ya mata amma namijinta kwara ɗaya ne Mai martaba Muhammad Nasiru Daura, duk da a wancan lokacin maigidanta Marigayi mai martaba tsohon Sarki yana da wata matar kafin ita mai suna Hajiya Rakiya. Tana da ɗa namiji babba amma an haife shi ba shi da lafiya daga karshe ma ya rasu bayan mahaifiyarsa ta rasu ba daɗewa. Akwai yaranta biyu yayyen Mai martaba ne da Fulanin Daura ta riƙe su. Hajiya Kilishi ita ce babba kuma tana da sarautan(Magajiyar garin Daura) Tana kuma auren shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin katsina ne. Sai Hajiya Balaraba(Magajiyar zama Daura) Tana auren wani babban general ne a hafsan sojan ƙasa tana zaune a garin Abuja da iyalanta. Sai ya'yan Fulani ƙannen Mai martaba mata Wacce ke bi ma Mai martaba Hajiya Zaliha wacce Lamiɗo ke kira da Mahma ita ce(Magajiyar sanda mata) Kuma tana auren madakin masarautar Zazzau ne tana can garin Zariya. Ita ce kamar 5 and 6 na Mai martaba Sarki komai zai yi sai ya yi shawara da ita ga shi ba ta taɓa haihuwa ba shi ya sa take son Lamiɗo kamar ran ta. Sai mai bi mata, Hajiya Zeenatu(Magajiyar Gabas) Tana auren shugaban yan sandan na ƙasa gabaɗaya. Sai Hajiya Zannura,(Magajiyar Yamma) Tana auren ɗan sarkin Katsina. Sai ta ƙarshe Hajiya Binta(Magajiyar sha wata Daura) Tana auren ɗan sarkin muslmin garin sokoto ne can take zaune da iyalanta. Fulani an tsufa amma jinin mulki na nan a jikinta ko da suka shiga tana kishigiɗe Sultan da Beena na jikinta kamar za ta mai da su cikin ta saboda so. sun iske su suna ta hira da Balkisu, wacce Saleem ya rankwafa shi da Amir suka gaisheta ta amsa cikin sakewa. "Maraba da Yarima. Maraba da Muhammadu Lamiɗo." Fulani take faɗa cikin farincikin da ya saka ɓoyuwa a saman fuskarta. "Ranki ya daɗe ga Yariman Daura nan na kawo miki mene ne tukwaici na? Saleem ya faɗa yana zama a shimfidar da take zaune. "Na baka farin doki na Hakimin Daura." Ta faɗa cikin fara'a shi ko sai ya washe baki yana faɗin" Hakimin Daura yana godiya. Allah ya kara tsawon kwana Fulanin Daura." Tana son farin dokin nan ta ce gadon shi ta yi wajen babanta ba ta bari kowa ya hau in ba Mai martaba ba, amma yau ta yi masa kyautarsa saboda zuwan Yarima Lamido. "Barka da hutawa ranki ya daɗe." Lamido ya faɗa yana mai zama a gefenta cikin ladabi. "Papa." Sultan da Beena suka faɗa a tare ganin babansu, Saleem ne ya amsa musu yana mai jawo su jikinsu sun san shi tunda ai suna yawan zuwa in Lamido bai zo ba Balkisu na zuwa in ta samu dama. "Lafiya lau Yarima, ya wajen su Baffan naka? Ya amsa mata duk suna lafiya cikin girmawawa. "Barka da zuwa Muhammadu Lamiɗo. Masarauta ta ji daɗin zuwan ka" Mirmishi kawai ya yi bai yi magana ba Bilkisu tafiya ta yi ta bar su tare da Fulanin Daura. Da yaran nan fa ta shiga abin da ta saba tana ta ba su labaran tarihin masarautan Daura da ya shude shi dai Lamiɗo zaune yake amma ba ya ma jin ta, kanshi har ya fara ciwo Saleem kuma yana ta su Sultan ne Amir ne ke mata tambayoyi. Kiran mangariba ya fitar da su daga shashen Fulani. Da suka fita salla har wajen tara na dare Lamido na waje yana gaisawa da mutanen fada. Goma saura na dare Lamiɗo ya shiga keɓantattacen ɗakin Mai mairtaba na cikin turakansa a shashensa. In da za su yi ganawar da suka saba daga shi sai shi sai Allah in dai ya zo garin. Bayan sake gaisuwa. "Ya wajen iyayen naka na Adamawa? Maimartaba ya tambaya yana zaune a saman wata darduman dake cikin ɗakin barcinsa. Sanye yake da jallibiya ba rawani a jikimsa sai fuskarsa ta bayyana kamar ta Lamiɗo, sai dai ya nuna masa yarinta da cikar maza amma har yanayin maganarsu ma iri daya ne, sai dai shi Lamido fari ne yayin da Mai martaba yake da duhu amma ba baki ba ne sosai. "Duk suna lafiya sun ce a gaishe ku." "Muna amsawa. ' Daga nan ɗakin ya yi shuru na wani lokaci. Sai da Maimartaba ya kira sunan shi sannan ya dago. "Muhammad Lamido." ''Allah ya taimake ka." "Don Allah ka dinga zuwa gida akai- akai.  Kar ka manta kai ne Yarima mai jiran gado, ka zo gida domin ka koyi sarauta tun kafin ta Allah ta kasance a kaina." Mai martaba ya faɗa cikin wani irin amo. Kan Lamido na kasa bai yi magana ba "Shekaru sun gangara Lamido. Ya kamata ka yi tunani." "Allah ya kara maka yawancin rai," Lamiɗo ya faɗa kafin ya ɗan yi shuru. "Zan din ga zuwa" " in sha Allahu." Ya sake faɗa a rabe, Jinjina kai Mai martaba ya yi kafin ya ce" Na ji daɗin haka. Allah ya yi ma rayuwarka albarka." "Amin." Lamiɗo ya amsa a kasan lebensa. "Ya wajen aikin naka? "Alhamdulillah." Lamiɗo ya sake faɗa. "Madallah. Ina ita iyalin naka? Ina takwara na? Ina jiran shi zan yi masa hakimi dawakin Daura nan gaba in ya sake girma." "Allah ya taimake ka." "Suna cikin gida," "Za su zo gaishe ka da safe in sha Allahu." "Allah ya tashe mu lafiya." Maimartaba ya faɗa cikin ɗan mirmishi. Sai kuma ya yi shuru. Dakin ya yi wani tsit kamar ba kowa a ciki. "Sultan har yanzu yaro ne" Mirmishi Mai martaba ya yi na manya da masu sarauta yana kallon ɗan na shi. "Na ce in ya kara girma Lamiɗo." Ya faɗa yana kallon sa. "Tuba na ke yi ranka ya daɗe." "Ba ka yi laifi ba Lamiɗo." Ya sake faɗa yana kallonsa. Fuskar Batula na gilma masa. "Ya wajen Batula? Lamiɗo ya dago yana kallon mahaifin na shi. Ya san wace ce ya ke kira Batula ba kuma mamaki ya yi ba domin in dai suna magana da Mai martaba sai ya yi hiran Batula. "Ka je wajen ta? Ya tambaye shi cikin kulawa. "Ban samu zuwa ba ranka ya daɗe." Ya faɗa yana ɗan sosa giran shi. "Lamiɗo." Ya kira shi ya amsa. "Allah ya ba ka nasara." "Muhammadu." Ya sake kiran shi a karo na biyu. "Allah ya ba ka yawan rai." Lamiɗo ya sake faɗa cikin rusunawa. "Ka bi Batula. Ka yi ta bin ta domin ita ɗin mahaifiyarka ce." "To in sha Allahu." "Duk yadda za ta nuna ma duniya ba ta damu da kai da abin da ya shafe ka ba. To ka sani tana sonka. Ta fi kowa sonka." Lamiɗo ya yi shuru bai yi magana ba amma a zuciyarsa sai dai ya ce ba ta kai Ammah sona ba. "Saboda ita ta haifeka. Cikin ka ta ɗauka na wata tara ta yi nagudar ka ta haifeka ta kuma rene ka." "Ammah dai ta rene ni Allah ya ba ka nasara." Ya yi saurin katse Mai martaba. Domin shi dai da yawon sa Ammah ya sani a komai na shi ba Mami ba. Mirmishi Ma imartaba ya yi har tana fidda sauti. "Saboda tana sonka ne, ta ji zafin abin da aka yi mata shi ya sa ta cire ka daga rayuwarta. Amma Batula tana sonka Lamiɗo wata rana ko bayan raina za ka ga hakan." "Allah ya taimake ka,.'" Lamiɗo ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin. "Ammah ce uwata ranka ya daɗe ita ce ba ta taɓa wofantar da sha'anina ba har gobe." Shurun ya sake yi kansa na kasa kafin ya cigaba da fadin. "Amma ban musa cewa Mami ce ta haifeni ba. Amma ni Ammah ce na sani a mahaifiyata." Mai martaba ya sake yin mirmishi cikin kasaita kafin ya ce" Ba shakka duka uwayenka ne Lamiɗo amma Batula ce ta haife ka " "Tuba na ke yi ranka ya daɗe, in na faɗi wata magana ba daidai ba." Mai martaba ya sake ɗan yin mirmishi kafin ya ce" Ba ka yi laifi ba Lamiɗo " Sai ta sake kallon shi kafin ya ce" Magana ta shi ne kar don ba ta shiga sha'aninka kai ma ka daina shiga nata. Hakki ne a kanka, ka bita ka yi mata biyayya." "In sha Allahu ranka ya daɗe." "Allah ya yi maka albarka. Allah albarkaci zuru'anka Muhammadu Lamiɗo " "Amin Allah ya kara maka lafiya da yawancin kwana ranka ya daɗe." Shi kan shi Lamiɗo ba ya sanin a ina ya koyo wasu abubuwan na sarauta sai dai kawai ya samu kanshi cikin aikatawa. Sun daɗe suna tattaunawa sai sha ɗaya da rabi Mai martaba ya sallamesa ya koma bangarensa. Duk ya gaji ga ciwon kai da rashin natsuwa wanka ya yi ya sha tea kawai ya kwanta ko Balkisu bai nema ba saboda gajiyar dake jikinsa rabon shi da ita tun a falon Fulani. Washe gari ma bai samu zama ba da shi aka yi zaman fada sannan da yamma kuma ya fita cikin gari shawagi a saman doki shi da Saleem da Amir. Ya yi ta kuma ganawa da mutane, kuɗi ne bai san adadin su ba ya fita da su amma duk sun kare tun daga ma'aikatan gidan da dogarai haka ya yi ta musu alheri. Lamido is a giver duk da ba shi da fara'a amma yana da kirki da kyauta. Tun da suka zo Daura bai zauna ba, kullum yana fada ko sun fita gari gabaɗaya ya gaji ya takura amma ba shi da mafita ranar da suka yi kwana huɗu ya fita shi da Saleem da wasu dogarai a dawakai ya sha rawani da kayan sarauta yana ta gaisawa da mutane. Washe gari kuma Balkisu da yara tare da hadimanta suka koma Lagos. Da shi da Saleem da wasu dogarai suka kai ta filin jirgin katsina. Ta na so ta rumgumi mijinta saboda ta yi kewarsa amma ba hali yana cikin mutane kuma a halin Lamiɗo in ta rike sa a nan shi ne kunyanta shi na farko da ta taɓa yi a rayuwarsa. Tunda suka zo bai samu lokacinta ba sai jiya da daddare da za su yi sallama. Mamah ma ta zo daga zaria, ba ta kwana ba ta juya sannan shi kuma ya je katsina gidan Hajiya Kilishi shi da Saleem da wasu hakiman Mai martaba daga nan suka karisa masarautar Katsina suka yi gaisuwa Hajjya Zannura ba ta kasar ta raka mijinta domin a duba lafiyansa. Ya ji maganar Mai martaba ya nemi Mami, da man kuma Ammah ta matsa masa ya je Kaduna ya gaisheta. Sai dai ko da ya kira ta sai ta ce ba sa nan suna Zamfara ita da megidan da ya ce ya zo ne zai zo ya gaisheta kafin ya koma sai ta ce ta yafe masa gaisuwan Bai damu ba domin ta ma hutar da shi, sai da ya shafe kwanaki goma a Daura sannan ya samu ya komawa Jimeta. Gabaɗaya tunda ya je Daura bai huta ba, da ya dawo Jimeta ya yi hutu sosai domin akwai ranar da tun safe har dare bai zo gida ba Ammh ta ɗaga hankalinta gashi ana ta kiran wayarsa ba ya ɗauka.  Ta kira Hamma Abdullahi sai da ya je gidan ya gano mata, lafiyansa lau kawai yana barcin gajiya ne. Sannan hankalinta ya kwanta. Bai koma Lagos ba sai da ya yi hutun wata ɗaya cur duka a haɗe da zuwa Jimeta da Daura. Washegarin ranar da ya koma Hamma Abdullahi ya kawo atamfofi guda hamsi cur daga Lamiɗo Ammah ta raba ma yan'uwa da dangi sannan an cika store din Baffa da kayan abinci sannan an siya masa sabuwar mota camry, Amma kuma ya siya mata waya sabuwar kiran samsumg sannan ya ce ta shirya za ta je Umra. Ammah sai kuka kukan farinciki, da man in zai yi musu abu sai ya bar garin a cewarsa ba ya son godiya. Da Ammah ta kira shi a waya tana ta masa addu'a. Ya dinga amawa da Amin yana faɗin" Ammah ki je Madina ki yi addua'a sannan ki samu natsuwa." Shi duk ƙokarinsa tana cikin damuwa ta tafi can ta samu natsuwa. "Na gode Lamido. Ubangiji ya yi maka albarka " "Amin Ammah ta." Baffa ma da ya kira shi sai ya ce masa" Na gode Lamiɗo amma ni ba Ammah ba ce godiya zan yi ba sai na yi kuka ba." Baffa na ta dariya shima sai da ya murmusa. "Na gode Baffa. Allah ya kara girma." Kalamansa kenan domin har abada ba zai iya biyan abin da suka yi masa. Hamma Saddam ma dake makaranta an shaka masa kuɗi tunda Ummu Salma ta ga yana ta yin status yana wasa Hamma Lamido, har su Hamma Abdulrahaman duk sun samu kyautar ban girma Ummu Salma ce ko abin da ba a so bai ma nuna ya san tana gidan ba. Itama ba ta damu ba, wani abun duniya yanzu duk ba ya gabanta halin data ke ciki kawai ya ishe ta. Har kuma ya gama zaman shi ya koma ba ta yarda sun sake haɗuwa ba. Tuni Ammah ta shiga rabon zannuwa, na mutanen Mubi sama da guda ashirin Ummin ikki da yayanta matan su Hamma Jibo duk ta aje musu, har Ummu an ba ta turmi ɗaya ta karba domin in ta ce ba ta so Ammah za ta yi mata masifa shi ya sa ta karɓa ta ajiye. Addu''oin godiya da fatan alheri kam Hamma Lamiɗo na shan su. Mami ta aiko ma da Ummu Salma waya sabuwar samsumg iri ɗaya da ta Ammah har da sabon layi. Da ta fara amfani da wayar amma ban da lambar yayyenta da ta Mami sai ta Baffa da Ammh sai na Baɗdo da shamsiya ba ta da ta kowa, wayar ma da komai duk sun fita kanta ita dai gata nan ne tana dai rayuwa. Ba ta buɗe whatsApp ba balle tiktok wayar ce kawai a hannunta. Ta fara zuwa awo Hamma Abdullahi ke kai ta tare da Ummin ikki. Karfin addu'a da kulawan mutane ya ke riƙe da Imanin Ummu amna fa zuciya ta raunana, wani rami ne a zuciyarta wawake da Habib ya yi mata haƙon shi, taɓo ne da ba zai taɓa warkewa ba. Tafiyan Ammah zuwa Umra ya tashi sannan ta Lagos za su tashi ana ta shirye-shirye. An yanke shawaran Mami za ta zo ta tafi da Ummu, tuni har ta haɗa kayanta tana murnan tafiya Kaduna. Ana cikin haka ne mijin Mami Alhaji Isa ya yi hatsari  ya samu karaya a kafarsa an ba shi gado a asibitin 44 dake Kaduna. Mami ba ta da natsuwa sai kawai Baffa ya ce Ummu ta yi zamanta duk da Mamin ta so ta je amma Baffa ya hana wannan karon da cewa tana da majinyaci ta zauna ta kula da shi. Shikenan tafiya Kaduna ta sha ruwa, Ummu ta so ta yi nesa da garin Jimeta amma tunda Allah bai so ba sai ta hakura. Da Hamma Abdulrrahman har cewa ya yi ta koma gidan shi da zama har Ammah ta dawo sai ta yi tunanin ai ga Baffa a gida gwara ta yi zamanta kawai. Ammah ma ta kawo ƙorafin a asibiti an ce ta huta kar ta yi aikin wahala ita kuma ta dage za ta iya domin tana ganin cewa har zuwa yaushe ne za ta yi ta zama takura da lalura ga yan'uwanta da iyayenta,? Shi ya sa ta ɗau niyyar canzawa domin samar ma da zukatan dake zagayeta da ita salama. Hamma Abdullahi ne ya raka Ammah har lagos gidan Hamma Lamiɗo ta sauka baya ma nan ya fara aiki da sabon kamfaninsa, amma an gama dukkan komai kwana biyu Hamma Abdullahi ya yi a Lagos sannan ya dawo bayan a safiyar ranar jirgin su Ammah ya daga zuwa Jidda. Da man da Hamma Saddam na nan ne shi zai rakata to in baya nan Hamma Abdullahi ne komai na gida duk wanda zai yi sako ma ta hannunsa ne. Kafin tafiyar Ammah Ummu ta roke ta da in ta je ta yi mata addua a ka'aba Ammah ta ce tana daga cikin dalilin da ya sa ta yi farinciki da Lamiɗo ya biya mata Umra. Ta tafi da niyar za ta yo ma Ummin addu'an Allah ya ba ta dangana ya sauketa lafiya sannan ya sauya rayuwarta daga kunci zuwa farinciki. Sannan ta bar ma Ummin ikki amana duk da ga Baffa a gida. Kuma ta karɓa tunda kullum za ta zo ta duba Ummu, Baɗdo ma tana zuwa sosai kuma tana jin daɗin ganin yanayin Ummun na sauyawa. Makaranta ne ma yasa ba ta kwana tunda bayan ta gama ND Sai wannan shekaran ne ma ta ɗora Degree ɗin ta(HND). Tun bayan tafiyar Ammah Ummu ce ke da alhakin gyaran gida da yin abincin Baffa na ganin ba za ta iya ba sai ga shi ta ware, kuma sai aikin ya ɗan rage mata damuwa balle ma da take yiin girke-girke kala kala, abin da ba ta gane ba ta ɗau wayarta ta faɗa Youtube ta duba. In Baffa na gida ya yi ta kambama ta komai ta yi ta bashi ya yi ta santi. "Auta shi kuma wannan abin da me kika yi shi? Ita kuma tana jin daɗin in yana santi sai ta zauna ta yi ta faɗa masa yadda ta yi. Haka ma Hamma Abdullahi in ya zo gidan ta yi wani abin ta zuba masa. "Ummu da me wai kika yi wannan? Haka yace ranar da ya zo da safe ta yi musu Naan bread, mai nama a ciki shi da Baffa suna santi ita kuma tana jin daɗi. Haka ko su Adda Suwaiba suke cewa in suka zo gidan, ita ce yi musu kosan rogo, wainar fulawa, gurasa fanke cake da su samosa tunda duk abubuwan baking ɗinta suna nan ɗakin cikin kayanta kawai buɗewa ta yi ta ɗauko su tana amfani da su. Cikin wata ɗayan da Ammah ta yi a Saudiya Ummu ta sauya ta ware ta fara maida jikinta ga cikinta ya turo wattani biyar har da wasu kwanaki tana kuma zuwa asibiti in lokacin awonta ya zo. Zirga-zirgan da take yi da kai da kawo sai ya rage mata tunani, sannan ta dage da addu'a in ta ji damuwa ko tunanin Habib yanzu za ta kunna karatun Qur'ani tana bi tana saurara tana aikinta. Kowa ya zo ya ganta sai ya ji daɗin ganinta. Haka ma Ammah ranar da ta dawo ta ce Auta ta sauya ta yi kumari kamar ba ita ba. Ta Lagos din Ammah ta sake sauka, sai da ta huta a gidan Hamma Lamido sannan ta dawo Jimeta. Itama ta yi shar kamar ba ita ba. Tana cewa me Baffa ke ci da ba ta nan ta ga ya yi kiba ne. Shi kuma ya ce itama da ɗanta ya biya mata Umra ta tafi ta barshi, to ai shima Auta nan nan na jiyar da shi kayan daɗi ana ta dariya. Sai bayan Ammah ta dawo ne suka je Kaduna ita da Ummin ikki duba mijin Mami su Baffa tun lokacin da aka yi hatsarin suka je. Bayan sun dawo Ammah ta ce Ummu ta haɗa kayanta ta je Kaduna. An sallami mijin Mami yana gida. Lokacin Ummu ta ji ma gwara ta yi zamanta gabansu Baffa sai kawai ta ce ita ba ta son zuwa yanzu watakila sai nan gaba. Mami ta fahimceta ba ta matsa mata ba, suma su Baffa ba su matsa mata ba sun kyaleta ganin ta fara dangana da komawa kamar Ummu Salma farko kafin Habib ya shigo rayuwarta. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No. 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supplements wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. *19* *BAYAN WATA BIYU* Wattani biyu sun zo sun shafe kamar ƙiftawan ido, rayuwar dai ta cigaba da tafiya cikin godiyar Ubangiji, haka yake a bangaren Ummu Salma sai godiyar Allah an samu canji sosai daga yanayinta yanzu Ummu za ta zauna ta yi hira har da dariya, ta saki jikinta tana ƙokarin yaƙi da kaddaranta. Duk da ba ta manta ba amma ta aro jarumta ta yafa ma rayuwarta saboda iyayenta da ƴan'uwanta, tana so ta ga farinciki a fuskokinsu kuma in dai tana son ganin haka sai ta aro ma rayuwarta farinciki, kuma da ta yi hakan ta ga canji Baffa da Ammah sun rage damuwa ganinta cikin farinciki ba abin da ke damunta ko ma yana damunta tana yaƙi da shi. Za ta fito ta yi ta nuna farinciki a fuskarta amma a zuciyarta Ubangiji ne kaɗai ya san irin ciwon da take ciki, sai dai in abin ya taso mata sai dai ta shige ɗaki ta yi ta kuka ba ta yadda ta fito sai ta wanke fuskarta. Za ta manta amma ba da wuri haka ba domin taɓon da Habib ya yi silan saka mata a cikin zuciyarta ba mai warkewa ba ne da wuri tana tunanin nan da shekara goma wataƙila har abada ma. A yanzu a ƙalla cikin ta ya kai kimanin wattani bakwai ne, kuma da ita da cikin jikinta duk suna cikin ƙoshin lafiya. Ba abin da za ta ce ma Iyayenta da yan'uwanta sai godiya, domin sun tsaya mata sun kula da lafiyanta da cikin da Habib ya ce ba ya so. Tana zuwa asibiti awo kuma Ummin ikki ke rakata duk lokacin da za ta je, sannan Hamma Abdullahi ke kai su sai dai in baya nan sai su hau kekenapep, su je su dawo kuma komai za a yi na laluranta kafin ma Baffa ya ba da yayyenta sun ba da ta yi komai da shi, cikin ya yi girma tsini gare shi ya yi wani ƙasa, Ummu Salma ta yi baƙi sosai ga kuraje duk sun lalata mata fuska kafafunta sun kumbura gabaɗaya dai hallitan ta ya sauya, jiki duk ya yi wani iri alamun rai na rayuwa tare da kai, Har kuma yau Habib ko wani ahalinsa ba su nemi Ummu ko iyayenta ba, su ma kuma kamar yadda Baffa ya ce ba wanda ya sake neman su, da farko Baffa Umaru ya so ya sake neman su Baffa ya ce har abada kuma shima baya fatan su neme shi nan gaba. Ammh ba ta barinta ta yi aiki sai dai ita ce ke matsawa sai ta yi aikin tunda a asibiti an ce ta riƙa yawan motsa jikinta girman cikin ya sa kowa ke tunanin namiji za ta haifa, kuma ko a scanning ɗin da ta yi namiji ya nuna amma ita ba ta damu ba ita dai a koda yaushe fatan ta ta sauka lafiya namiji ko mace duk wanda Allah ya bata tana so, domin bayan cikin ba ta da wani abu na rayuwarta da ya yi mata saura, sannan ba ta zuwa ko'ina daga asibiti sai gida ko kwanaki Umma Salamatu ta aurar da Autarta Ammah ta so sai ta je bikin nan wai in ta ga y'anuwa za ta sake sosai ita ko ba ta son zuwa ko'ina ba, ba ta so ta je ana kallonta ana nuna ta cikin tausayi ana cewa Allah Sarki shi ya sa ta ce ba za ta je ba Baffa kuma ya goya mata baya sai dai Ammah ce ta je aka yi biki ta dawo. Ko a anguwa an gama yawo da maganar an hakura  tunda da dawowar Ummu yanzu wajen wata biyar kenan tuni zukata sun haƙura. Komai na bukatar haihuwa Mami ta siya mata kaya masu kyau da yarari, domin ta ce duk abin da Ummu za ta haifa ita ce uwarsa da ubansa. Wasu kayan ma duk yan waje ne Mami ta siya mata kwanaki ma da suka je London ta siyo mata wasu kayan yara masu kyau sannan itama ta zo mata da dogayen riguna masu kyau sama da kala biyar tunda yanzu su take sawa kayanta duk sun yi mata kaɗan, balle ma tunda ta dawo gida ta daina amfani da kayan lefen Habibu kayanta tun na gida take sawa kuma yanzu ba sa shiganta sai dogayen rigunan da Mami ta siya mata take bumjumawa a cikin gida sannan atamfan wajen Hamma Lamiɗo da Ammah ta ba ta ta raba shi uku duk ta yi zannuwa faya tana ɗaurawa a gida biyun kuma suna cikin ɗan kit ɗin kayan haihuwan da Mami ta yo mata. Ba mai zuwa wajenta sai Baɗɗo Shamsiya ma ta ja baya da ita ba ta san dalili ba. Sun daina waya kamar yadda suke a baya sannan tun bayan dawowanta gida sau uku ta zo, na ukun ma cingham da minti ta kawo mata wai an saka ranar aurenta ta daɗe tana faman mamaki, ita dai kamar yadda Shamsiyan ta faɗa mata gidan su ba ka yin aure sai ka yi Degree ka yi bautar ƙasa kuma haka ne tunda duk yayyen Shamsiyan ba wacce ta yi aure tana cikin karatu sai da suka gama, amma za ki iya ɗora karatunki na gaba a gidan mijin ki,  amma sai ga shi ita tana aji uku ne ma a lokacin amma za ta yi aure sannan ƙarin mamakinta ba ta san Bestie na da wani saurayi ba, saboda dokar gidan su amma sai ga shi ta kawo mata mintin saka rana, sannan ita ko a labari ba ta taba faɗa mata ta samu miji ba, da Ummun Salma ta yi mata ƙorafin  ta samu miji amma tana ƙawarta na kusa da ita ba ta sani ba? Sai ta ce ta yi hakuri ganin tana cikin damuwa shi ya sa ba ta faɗa mata ba, kuma ba su daɗe da haɗuwa da mutumin ba. Har tambayanta ta yi ya aka yi mahaifinta ya amince ta yi aure ba ta gama makaranta ba.? Sai da Shamsiyar ta yi wata bazawaarar dariya kafin ta ce dangin mahaifiyarta ne suka shige mata gaba, sannan shima mahaifin na su yana sonta saboda maraicinta shi ya sa ya yi mata abin da take so. Ummu ta yi mata fatan alheri  da cewa ta bi dai a hankali domin yanzu maza ba a gane musu sai ka shiga kuma zence ya sha bambam. "Bestie ki kwantar da hankalinki. Sweety yana sona, ni ce kusan rayuwarsa nima kuma shi ne rayuwata. Kuma ki cire ma kanki tunanin wai don ke ba ki yi sa'ar aure ba ki yi tunanin koma ba zai yi sa'a ba. Ke dai kawai ba ki yi dace ba ki bar shi a haka amma ni na san abin da na zaɓa ina mai bakin tabbacin na yi kyakyawan zaɓi kuma na yi dace.". Kalamanta su ɗan yi ma Ummu tsauri amma ba ta nuna mata ba, ta yi mata fatan alheri da ta tambayan ta yaushe ne lokacin bikin! Sai ta ce ba a saka date ba amma in an sanya za ta faɗa mata har Ummu ta yi fatan cewa Allah ya sa lokacin ta haihu yadda za ta samu zuwa, domin ko ta daina fita ba za ta ƙi zuwa bikin Shamsiya da Baɗɗo ba su ne suka yi mata komai a nata bikin da Habib. Ko Baɗɗo da ta zo Ummu ta faɗa mata an sanya ma Shamsiya ranar aure sai da itama mamaki ya kamata har sai da ta maganta da cewa ita da ta ce a dokar gidansu sai ka gama Jami'a za ka yi aure, nan fa Ummu ta karanta mata abin da ta ce mata bayan itama ta yi mata wannan tambayar. "Tab. Ni ko ta ba ni mamaki duk yadda kuke bai kamata a ce sai dai ta zo kawo miki minti ba." A lokacin Ummu shuru ta yi ba ta yi magana ba, Baɗɗo ta yi ta faɗa tana cewa Shamsiyar ta sauya tunda Ummun ta dawo gida. "Ko saboda yanzu kin yi aure kin fito shi ya sa ta ja baya dake? "Kin san tana makaranta, ba ta samun lokaci." Daƙyar Ummu ta samu Baɗɗo ta bar maganar saboda kar Ammah ta ji daman da ta ce mata an sanya ma Shamsiyar ranar aure ga ma mintin da ta kawo mata nan ta nuna mata taɓe baki ta yi ta ce shi ya kawo ta kenan? Domin ita Ammah ta ce tun maganganun da ta ji tana yi yarinyar ta fita zuciyarta. Ita kanta Ummun ta san alaqar su da Shamsiya ta ja baya kuma kamar Shamsiyan ne ke gudunta tunda ita tana kiranta amna ba ta ɗauka, sai a yi kwana huɗu sama da sati sannan za ta kirata da cewa karatu ya yi zafi shi ya sa ba ta samun lokaci itama daga baya da ta ga haka sai ta kama kanta amma ranar ta yi kuka, yau ace mutane sun fara gudunka saboda kaddara ta faɗa maka, tana tuna a baya yadda kowa ke haba haba da ita saboda tana gidan mijinta yanzu kuma duk abin da take tunanin ta samu sai da Habib ya dawo da ita baya ba ta da komai a rayuwarta in ta tuna yadda rayuwarta ta sauya lokaci ɗaya sai ta yi kuka sosai, har kuma yau yana nan a cikin zuciyarta duk da tana ta addu'an Allah ya cire mata tunanin shi da soyayyarsa a cikin zuciyanta. Tana ta samun sauƙi amma kuma bai fita duka ba, ta dai dangana ta kuma aminta da cewa wataƙila Habib ya yi nisan da ba zai taɓa dawo gare ta ba. In ta kalli kanta a madubi da katon ciki, mara duk ta yi baƙi fuska ta lalace komai dai na ta ya sauya sai ta yi ta zubar ƙwalla. Tabbas ta rasa komai Duk wani abun sha'awa da namiji zai gani a jikin mace ya yaso ta, ta rasa shi. Da gaske Habib ya lalata mata gobenta wataƙila ma har da jibinta. Ya raba ta da martabamta na har abada. Ba za ta taɓa komawa Ummun Salman baya ba, ko shekaru tun tura ta na nan a yadda Habib ya sako ta. Sai dai za ta haihu kuma za ta shayar da abin da za ta haifa komai na jikinta zai saki to wani kuma taƙama gare ta? Ba ta da komai sai godiyar Allah da imani kawai. In tana kuka sai ta yi hamdala ta ce Ya Allah Ummu Salma ta gode,  domin ya barta da rai da lafiya ya kuma ba ta iyaye masu jajircewa yau da babu su ba ta san wani hali za ta shiga ba wata kila da ta kashe kanta cikin ƙunci da baƙin ciki. *** Hamma Saddam ya sake zuwa gida sun ɗan smu misSemister break, dawowar shi ne ya matsa ma Ummu sai da ta amince ya buɗe mata WhatsApp, ganin ya nace ne ya sa ta ce ya buɗe mata da sabuwar lambar nata. Nan take ko ya buɗe mata ya kuma yi adding ɗinta a family group ɗin su, tunda ya buɗe mata ba ta ma shiga saboda yanzu ta saba da rayuwarta ba waya. Ba ta da lambobin kowa sai na yan'uwanta. In ta ma duba chart ɗin sai dai ko Baɗɗo in ta yi mata magana sai Shamsiya da yanzu a chart ɗin suna ɗan gaisawa jefi jefi, sai Hamma Abdulrahim tun da shi yana can wata ƙasar suna yawan magana da su Hamma Jibo suna ɗan jan ta da mgana. Hamma Kabiru da ta yi masa sallama sai da ya yi sati sannan ya buɗe. Kuma bayan ya amsa sallaman ta gaishe shi ya ga saƙon amma bai sake yi mata magana ba itama ba ta sake bi ta kansa ba sanin halin shi Sun zo shi da matarshi da yaran shi suka yi sati suka koma, Hamma jibo ma da Hamma Mustpaha sun sake dawowa har Hamma Lamiɗo ya zo shi kaɗai kuma bai kwana ba a ranar ya wuce Daura da kuma zai wuce bai sake biyowa ta nan ba, Ammah ke ta faɗin yanzu ya sauya ma'aikata ba zai riƙa daɗewa ba a gan shi ba sanda ya zo ma Ummu na asibiti ta je awo ita da Ummin ikki sai da suka dawo suka ga Ammah da kuɗi sabbin yan dubu dubu ta ce ba daɗewa da fitan Lamiɗo ya wuce Daura duba kakarsa Fulani ba ta ji daɗi ba. Akwai wata class mate ɗin su ita da Shamsiya da suka yi Ahmadu Ribaɗo tun primary har sakandiri duk da dai ba sa wani yi da Ummu amma suna ɗan gaisawa a chart sannan lokacin tana group ɗin su na makaranta da wancan layin suna ɗan magana, shi ne da ta ga ba ta ganin Ummu a online da wancan lambar kuma ta yi ta kiran wayar a kashe sai ta yi ma Shamsiya magana. Ita kuma sai ta ce mata Ummu ta sauya layi ne sannan kuma ta ba ta sabon layin na ta, sai dai kawai ta ga Madina Jafar ta yi mata magana suka gaisa ta kuma ce Shamsiya ce ta ba ta sabuwar lambarta. Ba tare da izinin Ummu Salma ba Madina ta saka ta a cikin group ɗinsu na makaranta da sabuwar lambarta tunda su Madinan su ne ke jagoranta group ɗin, ba ta ma sani ba domin ta yi kwana biyu ba ta hau ba, ba kuma don ba data ba kawai dai wayar ce ta fita daga zuciyanta. Data sai tana yin expering a wayarta yayyenta da sun ga ba ta online za su saka mata kati ma ya fi na dubu biyar a wayarta ba wanda take kira da shi. Sai can da ta hau ne ta ga ta saka ta, tsoro take ji kar ya zo sun samu labarin abin da ya faru da ita, ba ta son ta zama abin dariya a wajen ƙawaye kamar za ta yi left sai kuma ta fasa lura da cewa kamar ba su sani ba, tunda Madina na yawan tambayanta ya Oga sai ta ce yana lafiya. Shi ya sa ta ɗan saki jikinta suke ɗan gaisawa kuma ba ta yi left a group ɗin ba. Ranar da daddare ta kunna data suka yi video call da Hamma Abdulrahim har da Ammah da Baffa ma duk sun yi magana da shi ya zama kamar ɗan turawa saboda zaman turai yana ta murna shekara mai zuwa zai dawo gida ya gama karatunsa na likitan ci gabaɗaya. Ta ga Baɗɗo ta yi mata saƙo da Madina amma ba ta duba ba sai da safe. Baɗɗo lafiyanta ta tambaya ta ce tana lafiya saƙon Madina ne ya ɗan ba ta mamaki. "Ya shirye shiryen biki? Ta yi mamakin tambayan cikin mamaki itama ta mayar mata da tambayar shirye shiryen me? Madinan ba ta online itama daga nan ta sauka ba ta sake hawa ba sai bayan kwana biyu. "Bikin Bestie ki mana, ba farkon watan gobe ba ne ko an ɗaga ne? Sakon da ta ga Madina ta tura mata kenan a gabanin tambayar da ta yi mata tun ranar. Mamaki ya kamata,yanzu har bikin Shamsiya ya zo amma ba ta sani ba, wayance ma Madina ta yi da cewa ba ta gane tambayar ba. Ta so ta yi ma Shamsiyar magana sai kuma ta fasa a zuciyarta ta ce za ta tsaya ta ga ni shin Shamsiya za ta faɗa mata, in ba ta faɗa mata ba sai ta samu tabbacin zarginta na cewa ta ja baya da ita tunda ta zama bazawara sannan ba ta son yadda ta zama cukus ta je bikinta to in har hakane itama ba cewa ta yi za ta je ba Allah ya sa a yi lafiya a gama lafiya. Abin ya dame ta amma ba ta faɗa ma kowa ba ta yi shuru da bakinta sai dai har watan ta gangara Shamsiya ba ta yi mata maganar ba ranar har ce mata ta yi har yanzu ba a saka date ba tace mata ba a saka ba, ai ta ce in har sun saka za ta yi mata mgana. Tun daga ranar ta yi ma kanta alƙawarin ba za ta sake yi mata magana ba, in ma har an yi bikin ne ba ta fada mata ba, ba za ta zargeta ba sai dai ta yi kudirin za ta kirata a waya ta yi mata fatan alheri. Amma fa zuciyarta ta yi mata nauyi yau wai Bestie ce ke gudunta to waye ya yi saura yanzu da ba zai guje ta ba. Har Ammah ta ɗan fahimci tana cikin damuwa har sai da ta yi magana amma ta ce mata ba komai. **** Thursday. A farkon watan da cikinta ya shiga wata na takwas ta koma awo, ranar Ummin ikki ba ta nan ta je Mubi Baɗɗo ce za ta raka ta ita kuma an kira ta suna da test a makaranta sai ta tafi. Baffa ya ce Ammah ta rakata ta ce ba za ta je ba, da man shima ya san ba zuwan za ta yi ba saboda kawaici maganar cikin dake jikin Ummu ba ta yadda a yi maganar da ita in dai tana wajen saboda kawaici. Ummu Salma Ita kaɗai ta je da aka yi mata awon sai da likitan ta sake yi mata faɗa kan yanayin kwanciyar da take yi, na ringigine da man wancan awon da suka zo da Ummin ikki sun ce kwanciyar jaririn jikinta ya jirkita kuma a wattanin cikinta ya kamata a ce kanshi ya dawo kasa, da yana kasan ne daga baya ne ya jikirta. Kuma ta ce saboda yanayin kwanciyar da take yi ne. "Dr to yanzu ya zan yi? Ta tambaya cikin damuwa, ba ta san wani abu ya samu cikin jikinta. Saboda shi ta rasa komai na ta "Kar ki damu in dai kika kiyaye irin kwanciyar da mai ciki bai kamata ta yi ba zai komai daidai in sha Allahu." Ta faɗa mata ta daina kwanciyar ringigine gwara ma na gefe da gefe saboda lafiyan abin da ke cikinta. Sannan sun ba ta yanzu bayan sati biyu za ta dinga zuwa awo tunda ta kusa haihuwa. saɓanin da sati uku ne. Da za ta dawo Kekenapep ta hau ta dawo da gida, haka ma ta hau da za ta je Hamma Abdullahi ba mota a hannun shi sai mashin, ita kuma ba za ta iya hawa mashin a yanayin ta ba. Ta dawo gida wajen sha biyu na rana ta samu Ammah har ta gama abincin rana. Da man da yunwa ta dawo jikinta har rawa yake yi in ta na jin yunwa yanzu. Sai da ta ci sannan ta ɗan kwanta saboda a gajiye take daga nan barci ya ɗauke ta. Sai wajen biyu saura na rana ta iya tashi ta yi salla. Haka kurum ta ke jin kasala jikinta ba daɗi zuciyanta tana ta tsinkewa sai ta ɗauko Qur'ani ta yi karatu, sannan ta ɗan samu salama Baffa ba ya nan sai Yamma ya dawo. Daga ita sai Ammah a gida kuma ba hira suke yi ba, kowa na ɗakin shi. Misalin shidda na yammah tana cikin ɗaki ta ji maganar Hamma Abdullahi sai bayan ya bar gidan ne ta fito ta ga Ammah baki har kunne. "Ammah Me ya faru ne?  Kamar muryan Hamma Abdullahi na ji yanzu? Ta tambaya tana kallon Ammah. "Baba ne ya zo yana faɗa mini Yayanki Lamido ya kira shi, da cewa ya je filin jirgi ya ɗauke shi yanzu nan." Ummu ta yi shuru ba ta yi magana ba. "Zuwa ba sanarwa, ai da ya yi magana da ko gidan na shi an je an ɗan share" Ammah ta faɗa tana miƙewa. "Amma dai nace Baba ya yi ma matarsa mgana ya ɗan kaita ta je ta ɗan gyara gidan kafin ya iso " Ummu ta ɗan yi yaƙe ba ta yi magana ba. Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye tana tunanin abin da za ta dafa masa. "Ummu ko na yi masa tuwo ne? Kin san yana so" "Kai kuma yamma ta yi gaskiya." Ita kaɗai take ta maganganunta Ummu Salma na jin ta ba ta ce mata komai ba shigowar Baffa ne ya katseta sai ta juya tana faɗa masa halin da ake ciki. "Ba laifi ga Ummu nan ta ɗan yi masa abinci nan da take yi mana na yan gayu." Ya faɗa yana kallonta, mamakin Baffa ya hana ta magana wannan ne zai ci abincinta. Ta ma san Ammah za ta ce aa ga mamakinta sai Ammah ta juya tana ce mata ta ɗan sama masa wani abun. "Za ki iya ko? Ba ta da magana in ta ce ma ba za ta iya ba Ammah ce za ta ɗaga hankalinta. "Zan iya Ammah." Ta faɗa a fili amma a zuciyanta sai ƙunƙuni take yi tana faɗin sai kawai mutum ya zo ba sanarwa da man halin shi ne ya yi ta abu gaban kansa. Haka nan ta shiga kitchen chinese rice ta ce za ta yi, Allah ya sa akwai cefanen kayan lambu shekaran jiya Hamma Abdulrahaman ya kawo, amma sai da ta dafa ganyen zoɓo sauran nata ne ma da aka dawo da shi ta fito da shi tana yi musu zoɓo lokaci bayan lokaçi. Girkin kaɗan ta yi tunda suna da sauran taliya da miyan da Ammah ta dafa shi da rana, gogan ne ba zai ci ba tunda shi na musamman ne. Bayan mangariba ta gama aikinta tunda gas ne Ammah na da gas na tsaye mai uku da electric da shi ake amfani, shi ya sa aikin ya yi mata sauri zobon ta zuba a wani jug na tangaran ta saka a firiza, abincin kuma ta zuba a ƙololin Ammah sabbi ne ma a kwalin su da ta je bikin Autan Umma Salamatu ne ta zo da su ko Baffa ba a taɓa sanya masa abinci a ciki ba amma yau Ammah ta ce ta ɗauko a zuba ma Lamiɗo a ciki. Ta gama komai ta jera saman faranti sauran kuma ta zuba ma Baffa a ranta tana faɗin ai nima sai ubana ya ci tunda Ammah ba ta kanshi take yi ba. Har ta koma ɗaki ta yi alwala ta yi sallan Mangariba shuru ba Hamma Abdullahi ba ɗan Ammah, sai da Ammah ne da kanta ta leƙo tana ce mata ta kira mata Baba a waya ta ji ko lafiya ba su kariso ba ita wayarta kamar ba kati ta dai ki shiga. Hakanan ta ɗau wayarta ta kira shi sai ga shi ta shiga ta ba ma Ammah suka yi magana. Ashe Hamma Lamidon bayan an ɗauko shi daga filin jirgi gidan shi ya ce a wuce da shi zai yi wanka. Sannan ya ce ma Hamma Abdullshi ya koma gida in ya gama abin da yake yi zai tuƙo kansa zuwa gida. Haka Ammah ta ke faɗa mata ita da Baffa da bai daɗe da dawowa daga masallaci ba. Abincinsa Ummu ta kai masa ɗaki sai ya wuce can Ammah kuma ta bi bayan shi. Ita kuma sai ta koma cikin ɗakinta da tsinin cikin ta a gaba wayarta na hannunta kamar an ce ta buɗe data sai ta ja sama ta kunna ba wasu saƙonni ne masu yawa take samu ba tunda sabuwar lamba ce ba kowa ya santa da lambar ba. Sai dai saƙonnin da ta gani a group ɗin makarantar su ne ya ɗan ja hankalinta, kuma ta ga har tagging ɗinta an yi sai ta shiga. Sai ta ga ana ta fatan alheri da Allah ya ba da zaman lafiya. "Ga wacce za ta dinga amsa addu'o'in ku nan." Madina ta faɗa bayan ta yi tagging ɗinta akan an ce ana ta fatan alheri amarya ta yi shuru ba ta amsa ba. abin ya sake ɗaure mata kai ganin Shamsiya ake tagging ana mata fatan alheri kasa wasu hotuna ne guda uku jikinta har rawa yake yi wajen dannawa ta buɗe hotunan domin ta ji suna ta cewa Allah ya sanya alheri ya kuma kai mu lokacin Zuciyanta ya ba ta cewa auren Shamsiya ya zo ba ta faɗa mata ba. Sai dai me katin biki ne ya fara buɗewa da farko. Ba ta ko tsaya duba sunan angon ba ta fara duba date ɗin bikin jibi ne ɗaurin auren. Mamaki ya sake kamata da al'ajabi kenan da gaske ne Shamsiya ta ja baya da ita sannan da gaske ne zargin da take yi a kanta cewa tunda yanzu ta zama bazawara ba ta bukatar ta. Tana ta hawaye ita kaɗai tana zaune da waya a hannunta. Jikinta ya fara karkawa ne lokacin da hoton ƙasa suka buɗe. Sai ta ga kamar ko idanuwanta ke yi mata gizo ba gaskiya ba ne. Har sake murza idanuwanta ta yi ta sake ƙura ma wayar idanuwanta cikin fitan hayyaci. Zuciyanta ne ya tsaya da bugu na lokaci ɗaya. Me take gani haka? Shamsiya ce da Habib cikin shigar alfarma a cikin hotunan nan guda biyu. Ɗaya ya kwanto ta bayanta ya haɗe hannayensu a saman cikinta. Dayan kuma tana zaune a kan kujera shi kuma ya tsaya a bayanta suna masu kallon juna suna mirmishi cikin yanayin da amarya da ango kan yi a lokacin yin hotunan pre-weeding pic, tamtama take yi kamar ba Habib ta gani a jikin hoton ba sai dai kuma ina shi ne domin ba za ta taɓa mantawa da kamaninsa ba har abada. Habib ne mijin da Shamsiya za ta aura? "Kai gaskiya sun dace." Ta ga saƙon wata Hamdiya" Kar dai a ce Shamsiya Habib za ta aura tunanin da take yi kenan zuciyanta na sake tsinkewa. Ko ba ta san Habib ba ne? Ko ba ta san Habib shi ne mijin da ta aura ba? To ai in mijinta ne a da a yanzu ba mijinta ba ne sun rabu. Ba kuma za ta ce Habib bai san Shamsiya ƙawarta ba ce, ba kuma za ta ce Shamsiya ba ta san Habib ba. Dukkansu sun san juna, kuma shi ne za su yi aure! Da man shi ne mijin da ta samu lokaci kaɗan? Ko da man shi ne dalilin da ya sa ta ja baya da ita. Ta sani ta san Habib ne za ta aura ta sani kuwa. Zuciyan Ummu ya daina aiki kwata-kwata kanta na sarawa ta ma rasa tunanin da za ta yi, wayar na hannunta addu'oin fatan alheri ke ta shigowa ga Shamsiya da mijinta Habib, tun tana tunanin mafarki take yi har ta gasgata a zahiri ne yake faruwa. Ta kashe wayarta yafi sau uku tana sake kunnawa amma still in ta sake shiga hotunan take gani hoton Habib da Shamsiya a cikin yanayin farinciki. Ta kasa zama ta kai gauro ta kai mari a cikin ɗakinta. Tana jin har abin da ke cikinta yana juyawa tsabar halin datake ciki. "A'a Bestie ba za ta auri Habib ba." "Ba za ta aure shi ba." Take faɗa tana kallon hotunan lokaci ɗaya tana faman girgiza kai. An ce kuka ma Rahama ne ta kasa kuka amma a kasan zuciyanta take jin wani irin zafi zafin da ba ta taɓa jin irin shi ba har ya ninka irin zafin da ta ji lokacin da Habib ya sake ta. Ta kasa gasgata gaskiyan abin da ta gani, in har auren ne da gaske to watakila Shamsiya ba ta san Habib ba ko shi ne bai gane Shamsiya kawarta ba ce, ga shi dai zuciyanta na cigaba da hasko mata hotunan su a lokutan da Shamsiya da Habib suka sha haɗuwa tun kafin aurenta da shi har ma bayan auren amma wani shashi na zuciyanta faɗa mata yake kila dai kuskuren fahimta ne ba abin da idanuwanta ke ganin mata ba ne. Saboda ma ta samu tabbacin abin da ta gani sai ta sake duba katin bikin ga sunan Habib Idris Mai imani nan raɗau a jikin katin tare da na Shamsiya. "Aa No.." "Ba gsskiya ba ne." Ta faɗa kamar mahaukaciya. Ba ta yarda ba zuciyanta ba ta aminta da abin da ta gani ba tana bukatar wani ya yi mata karin bayani Jikinta da hannunta na rawa ta lalubo lambar Shamsiya ta kira ta amma kira sama da sau goma ba ta ɗaga kiran ta ba, in wayar na ringing tafiya yake yi da bugun numfashin Ummu Salma tsabar tashin hankalin data ke ciki. Ganin da ta yi tana ɓata lokaci a daran nan a wannan lokacin take son karin bayani take kuma son sanin gaskiyan komai tun kafin zullumi da fargaba su saka zuciyanta bugawa. Wani dogon hijabin da take salla ta raruma ta saka a saman bakar doguwar rigar jikinta. Har ta fito falo sai ta tuna ba ta ɗauki kudi ba sai ta koma da gudu ta yayo mu ƙaramar jakarta dake saman madubin dakin, tunda ta dawo daga asibiti ta ajiyeta a wajen wayarta na hannunta ta fito, takalmin Ammah dake kofar ɗaki wani na roba na zirga-zirgan tsakar gida ta zura ta fice daga gidan ba tare da tunanin komai ba, tana jiyo hiran Ammah da Baffa a turakansa amma ko waiwayowa ba ta yi ba, a lokacin hankalinta ya bar  gangan jikinta. So kawai take yi ta buɗe idanuwanta a cikin na Shamsiya ta nuna mata hotunan da ta gani ta ji shin abin da ta gani gaskiya ne ko ƙarya ne? Ba ta ko ganin gabanta kafin ta isa titi ba ta san adadin sau nawa ta ci tuntuɓe ba, amma ba ta damu ba Kekenapep ta tsayar ta shiga ta ce ya kai ta barraks road suna tafe amma ji take yi kamar ta yi tsuntsuwa ba ta taɓa ganin nisan gidan su Shamsiya ba sai a ranar suna isa tun daga kofar gidan ta san ana sha'ani domin get ɗin gidan ma yana buɗe ne ga motoci nan birjit a haraban gidan wasu har waje, ba ta damu da kowa ba, ita dai ta san ta fiddo kuɗi da ba ta san ko nawa ba ne ta mika mai nepep ɗin daga nan sai kawai ta tsinci kanta a falon gidan su Shamsiya akwai mata ga sunan da yawa amma idanuwanta ba su tsaya tantance fuskokinsu ba. Waige-waige kawai take yi ba wacce idanuwanta ke son gani irin Shamsiya. "Wa nake gani kamar Ummu Salma." Ta ji an faɗa daga bayanta tana juyowa sai ta ci karo da Anty marikiyar Shamsiya. Mirmishin dole ta yi mata wanda ya tsaya iya saman fuskarta. "Ni ce ina yini Anty" Ummu ta faɗa tana sauke numfashi. "Lafiya lau sannu Ummu Salma." Ta faɗa tana kallonta daga sama har ƙasa. "Ai na yi ta cewa Shamsiya za ta rako ni gidanku na yi ma Umman ki jajen abin da ya faru ban samu dama ba." Ummu ta sunkyar da kai, amma tana ta kalle kalle domin hango ta in da za ta ga Shamsiya. "Allah ya kyauta na gaba. Allah ya zaɓa mafi alheri." Ko amsata Ummu ba ta yi ba domin ba ta ita take yi ba. "Kin samun kin rarafo kenan? Da man da na ga ban ganki ba Shamsiya ta ce ai kin yi nauyi." Da gaske kenan Shamsiya za ta yi aure, amma dai da tabbacin Habib za ta aura ne ba ta sani ba kuma shi ta zo ta sani daga bakin ita Shamsiyar. "Shiga ciki tana cikin ɗakinta ba ta ma daɗe da dawowa daga wajen gyaran kai ba" Ko kafin Anty ta gama magana Ummu ta wuce ta zuwa cikin ɗakin Shamsiyar da dama ta san ɗakin. Kofar ma tana buɗe suna ta hayaniya ta san ta shiga cikin ɗakin kuma ta ga harda yayyen Shamsiyar a ciki amma wacce idanuwanta ke son gani ta nema sai ko suka haɗa ido tana zaune gefen gado ta buɗe kanta yan'uwanta na duba gyaran kan da aka yi mata. "Kai Ummu kin rarrafo kin zo? Badawiyya yayar Shamsiya ta faɗa bayan duk hankula ya dawo kanta. Ita dai kawai tana yaƙe ne amma hankalinta da natsuwarta na kan Shamsiya. Wato ta ce ba za ta samu zuwa ba ne saboda ta yi nauyi to ai ba ta yi ƙarya ba tabbas ta yi nauyi tunda ga nauyi nan a gabanta tana fama da shi. "Bestie sannu da zuwa." Shamsiya ta fada bayan ta taso zuwa gare ta har tana riƙo hannunta. Ta kuma ja ta har gefen gado ta zaunar da ita, ita kuma kamar gaula ta zauna. Suna ta yi mata sannu ta kasa amsawa kawai Shamsiya take kallo ko a jikinta sai jikinta ya bata wata kila ba gaskiya ba ne Shamsiya za ta yi aure amma ba Habib ne mijin da za ta aura ba. "To mu je ko mu bar Bestie ta gana da Bestien ta." Badawiyyya ta faɗa tana tattara sauran yan matan dake ɗakin, wasu ta san su yan'uwan su Shamsiya ne wasu kuma ba ta ma tsaya iya gane su ba. Tunda in dai na kusa da Shamsiya ne ta san su kamar yadda itama ta san duk wani da ya shafe ta. Kamar yadda Shamsiya take zuwa gidansu itama haka take zuwa nan gidan wajen Shamsiya tun ma kafin ta yi aure. Dukkansu suka fita sannan suka rufe ƙofar, suna fita Shamsiya ta kalle ta, tunda daman ita Ummu tunda ta shigo take kallon ta. Mirmishi ta yi mata irin mai ƙayatarwa nan kafin ta ce" Tunda na ganki na san cewa zuwa yanzu kin ji komai ko kin ga komai." Ta faɗa tana mai yi ma Ummu wani kallo. Cikin wani yanayi Ummu ta ce" Na ji mana, na ji za ki yi aure amma ba ki faɗa mini jibi ne bikin ki ba." Ta faɗa kafin ta ɗan ja fasali. "In ba ki so na zo bikin ki Bestie ba sai kin ɓoye mini ba nima a wannan halin ba zan zo ba ballatana har na na ɓata miki bikin ki." Ta faɗa cikin rawan murya, tunani kawai take yi ba gaskiya ba ne , ko dai ita ce ba ta gani daidai ba ko kuma an samu wani kuskuren. Shamsiya ta sake kallonta kafin ta kwashe da dariya. Ummu ta yi jagale tana kallonta ganin tana yi mata dariya "Wai akan me kike magana? Ta faɗa lokaci ɗaya tana mikewa.. "Kin ce ma su Anty na yi nauyi shi ya sa ba zan samu zuwa bikin ki ba, alhalin ni ba ki faɗa mini ranar bikin ba." Shamsiya ta sake kwashewa da dariya tana nuna Ummu kafin ta ce" Wai da man ba abin da nake tunani ya kawo ki ba? "Me kike nufi? Ummu Salma ta tambaya cikin shan jikin jikinta. "Ba ki san abin da na ke magana akai ba? Ko dai kin sani kin zo ki tabbatarwa ne kina yi mini alaye" Ta faɗa tana mai kallonta cikin kurullah. "Me me kenan? Ummu Salma ta tambaya har bakinta na harɗewa. Shamsiya ta dauko wayarta a gaban madubi ta yi danne danne ta miƙa ma Ummu wacce ta yi tsai tana kallonta. "Karɓi ki duba." Hannunta na rawa ta karɓa. Tana dubawa, sai gata ta sake ƙamewa a zaune. Ba sabo ba ne a idanuwanta hotunan nan ne dai da ta gani ɗazu ta kasa gasgatawa. "Ki yi ta yin gaba, hotuna ne ne ni da mijina in sha Allahu" Hannun Ummu na rawa zuciyanta na bugawa, haka ta rika wucewa tana kallon hotuna kala kala sama da kala goma ba ta ko gama gani ba ta ɗago idanuwanta cikin wani yanayi tana kallon Shamsiya. "Da ma. Da ma da gaske ne? Ta faɗa cikin rawan baki da na zuciya. "To da kin ɗauka karya ne? Shamsiya ta faɗa tana ɗan dariya. "Habib ne fa! Ko ba ki gane shi ba ne? "Habib ne, na gane shi Sweety ba." Shamsiya ta katseta cikin ba ta tabbaci. Ummu ta kasa magana bakinta na rawa, tare da jikinta Shamsiya kuma ta ɗaure fuska tana kallon Ummu kallon kasƙanci. "Ga shaida nan na nuna miki. Jibi uwar haka ina gidan Habib a matsayin matarsa in sha Allahu." Ta sake faɗa tana sakin wani mirmishi. "Habib fa! Habib miji." "Kul ɗinki. Kar ki sake kiran shi da mijin ki domin Habib ba na ki ba ne nawa ne. Ummu Salma." Ta faɗa tana taso mata a fusace Kafafun Ummu har gara suka yi saboda jin abin da ba ta taɓa tsammani ba. "Ban karya ta cewa ke kika fara sanin Habib kafin ni ba, amma zan baki tabbacin ni na baki aron shi har kika aure shi kika kuma yi zaman aure da shi." Ta dawo gaban Ummu Salma ta tsaya sannan ta nuna cikin jikinta da yatsunta guda ɗaya. "Ni ce har na baki damar da kike da wannan cikin a jikin ki. In da na so da baki aure Habib ba, in da na so da yau ba ki rigani ɗaukan cikin shi ba" Ummu ji take yi kamar mafarki amma da ta runtse ido sai ta sake ganin ta a gidan su Shamsiya kuma ga ta a gabanta tana faɗa mata wasu maganganu waɗanda ta kasa yarda da su. "Ke Habib ya fara gani yana so, ranar da kika nuna mishi a matsayin saurayin ki na ji dama ace shi ɗin nawa ne, bani na fara kai kaina ga Habib ba shi ya kawo kansa gare ni da cewa sai da ya ganni ya san ba sonki yake yi ba sha'awarki ya ke ji, tun a lokacin muke tare muna soyayya a ɓoye, saboda ke ba zan hana zuciyata abin da take so ba Ummu Salma." "Me ya sa to ya aure ni baI aure ki ba? Ummu ta samu karfin gwiwan tambayan Shamsiya domin ko hawaye ma ba ta ji ya kawo mata ba zuciyarta ke suka tana hasaso mata wasu abubuwan, au da man Shamsiya ce masoyiyarsa da yake ta magana a kanta ita ko me ta yi ma su Habib da suka zaɓi su yi mata wannan yankar ƙaunar. "Ina son Habib ina son abin da zai saka shi farimciki. Yana tsananin sha'awarki kuma yana so ya kauda wannan sha'awar ni kuma a gida ba za a bari na yi aure a lokacin ba. Shi ya sa na ba shi daman ya aure ki amma na shekara ɗaya ya yi amfani dake son ranshi ya sake ki zuwa lokacin ni kuma na shawo kan matsalata a gida.  Mun yi da shi ba zai bar ki ki samu ciki ba, amma sai da kika ɓata mana plan din mu." Nan ta shiga ba ta labarin duk yunkurin zubar da cikin da Habib ya yi mata da saninta domin tare suke shirya komai. "Ki ma gode ma Allah na baki aron shi, ki kuma jinjina mini yadda na bari kika fara ajiye ƙwaan Habib a mahaifarki kafin ni, saboda haka godiya ya kamata ki yi mini Ummu domin na ba ki aron abin da na fi so a duniya." Ta gama faɗa tana fuskanta ta. Ummu ta yunƙura ta miƙe tana jin ɗan cikinta na haɗewa waje ɗaya saboda halin da ta ke ciki, cikin ido ta kalli Shamsiya kafin ta ce" Ai ban neme da ki ba ni aron shi ba Shamsiya. Me ya sa kuka yi mini haka? Riban me za ku samu? Ta faɗa cikin soyewar zuciya. "Na samu riba, domin Masoyina ya biya bukatarsa, ni ma kuma na samu nawa biyan bukatar, ga shi za mu yi aure." "Shamsiya mijin da na au" "Haramun ne? Ai ya sake ki, kuma ko bai sake ki ba zan iya auransa in na ga dama. Amma ni ba zan iya zaman kishi dake ba shi ya sa nace ya sallame ki daga rayuwar mu." "Da man ba don Allah kike tarraya da ni ba? "A baya don Allah na ke zaune dake amma daga lokacin da kika auri Sweety na tsane ki Ummu Salma." Ta dakata tana kallon Ummu da ta koma tana mirmishi kamar mahaukaciya "Kuma na ja baya dake ne saboda bana son alaqar mu, bana son ki a rayuwata. Ki je ki cigaba da rayuwarki amma ki manta da kin taɓa sanina ballatana Habib. Mu zama kamar mun shuɗe daga tunanin ki." Ummu ta girgiza kai ba za ta iya fassara a yanayin da ta ke ciki ba. "Sannan kar ki damu kaf dangina ba su nan kin auri Habib ba, sun san shi ne kawai a matsayin sa na mijina." Ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya cikin dariyan shaƙiyanci. "Na gode, da man tabbacin nake son sani tunda kuma na same shi daga wajen ki ba komai." Ummu ta faɗa cikin aro jarumta. Kawai sai ta juya za ta bar ɗakin tana jin maranta na daurewa a waje daya, ga ɗakin na juyawa mata amma ta daure. "Ba ki ji ba." Ummu ta juyo tana kallon ta. "Na so ki zubar da cikin nan,  watakila da kin iya samun wani wanda zai kwashe ki, amma kika yi taurin kai ki ji be ki fa yanzu? Wa zai kwashi bazawara mai ɗa, ɗan ma mai kama da ɗan shege tunda uban cikin ya ce ba ya so" Ta gama faɗa tana kwashewa da dariya har tana tafa hannuwanta Juyawa kawai Ummu ta yi ta fice daga ɗakin tana jan kafa, ita dai ta san ta bar gidan ta kuma yi tafiya mai nisa a hanya kafin ta samu abin hawa. Ta san kamar hankalinta ya gushe domin ba ta ma san har ta faɗi sunan anguwarsu ba, ita dai an sauke ta a bakin titin gidansu ta sauka ta ba shi kuɗinsa sannan ta yi tafiya zuwa gida da kafafunta. Ba ta kuka ba ta komai amma tana ji kamar yau za ta bar duniya. Masallatan anguwan har sun idar da sallar isha'i wasu ma sun daɗe da idarwa. Ta shiga gida ba ta damu da Ammah ko Baffa su ganta ba. Ba ta damu da su tuhumeta ba. Kawai ta faɗa ne kai tsaye. Hamma Lamiɗo na tsaye wajen ɗakin Baffa yana waya ya juya baya. Ba ta san shi ba ne sai da ya juyo shima ya ji ana ta jefa kafafuwa ne yaraf yaraf shi ya sa ya juyo. Ido huɗu suka haɗa domin akwai hasken wuta a tsakar gidan. Mamakin ganinta yake yi ga ciki a gaba sannan yarkace-yarkace kamar ba ta cikin hayyacinta. Ta kalle shi cikin wani yanayi shi dai juyawa kawai ya yi ya cigaba da wayarsa ita kuma ba ma ta shi take yi ba da sauri ta faɗa falon Ammah. Tana shigewa ya bi bayanta Da kallo  cikin mamakin me ya fitar da ita a cikin wannan daran? Me ya same ta ya ga kamar ba ta da lafiya. Duk da fa ya daɗe bai ganta ba, ba haka take ba. Sai kuma ya yi tunanin watakila ciki ne ya mayar da ita haka. Yana gama wayarsa ya koma cikin ɗakin Baffa abinci yake ci aka kira shi a waya ya ta shi. Ammah kuma ta shiga ciki ta je yin sallah. Komawa ya yi gaban abincin shi Baffa na gefen shi da man Ammah ce ke hiran bayan ta tashi sai ɗakin ya yi shuru. Shi Lamido da man bai iya hira ba shi kuma Baffa sanin halin shi ya sa bai ma bata bakin shi ba Ammah na ɗakinta ta idar da salla ta ji kamar an shigo Ta fito haka dai daidai lokacin da Ummu ta shige ɗakinta ta rufe kofa. Sai Ammah ta ɗauka ita ce ta fito falo ta koma, domin ba ta san Ummun ba ta a gidan ba, bayan fitan ta Lamiɗo ya zo suna ɗakin Baffa gabaɗaya. Daga nan kawai ta fice ta koma ɗakin Baffa. Ummu ta sulale a kasan cafet tana jin zuciyarta na zafi kamar za ta mutu. Abubuwa suna gilma mata. Shamsiya da Habib. Me ta yi musu da za su lalata mata rayuwarta haka?. Shamsiya fa da suke ƙawance tun suna yara ita ce ta ci amanarta da namijin da ta ba ma Amanar rayuwarta. So take yi ta daina jin zafin da ke ji a cikin zuciyanta. So take yi duk wani damuwarta da take ji ta daina jin su, so take yi ta bar duniyan nan ko za ta samu yar salama. Amsar kuwwan Kalaman Shamsiya sun kasa barinta ta huta, sun saka ta jin gwara kawai ta ji shuru gwara ta sama ma kanta natsuwan zuciya. Miƙewa ta yi tana layi ta isa gaban madubi ta ɗauki reza sabuwa a cikin kwalinta ta buɗe. Rezan ba na ta ba ne na Ammah ne kwali ɗaya take siyab itama shekaranjiya cizgiya ne ya fito mata a gefen hannunta sai ta yi ma Ammah magana ta bata, bayan ta cire sai ba ta mayar mata ba sai ajiye a saman madubin ɗakin. kallon kanta take yi a madubi tana tunanin yanzu rayuwarta ba ta da amfani hijabin jikinta ta cire ta na kallon cikin jikinta. Ba amfanin ta haifa ma Habib yaro ko yarinyar dake cikinta domin bai cancanta ba, yadda zuciyanta ke zafi ne take son kawai ta hutar da kanta. Ba tare da tunanin komai ba ta ciro rezan ta daidaita tsitsiyan hannunta na hagu za ta yanka lokaci ɗaya tana mai runtse idanuwanta hawaye na wanke mata fuska, sai ƙaran vibration ɗin wayarta ya dakatar da ita wayar na kan madubin ne, idanuwanta na ganin duhu amma sai da ta ga sunan mai kira, Sisna Baɗɗo ce take kiranta a lokacin da ba za ta saurare ta ba, a lokacin da ba za ta iya amsa wayarta ba. Tana mai zubar ƙwallah wasu na fitowa wasu na ƙoran wasu ta sake daidaita hannunta ta yanka sai ga jini ya tsartsu, ta runtse ido tana jin wani irin zafin azaba na ratsa ta daga ƙafafunta har saman ƙwaƙwalwarta. Sake yanka hannun nata ta yi a karo na biyu jini ya sake tartsuwa, ta sake runtse ido sabo da azaba mai raɗaɗin da ya dabaibaye jinta da ganinta tana gani jininta na zuba a kan madubi yana gangarawa a kasan cafet da gudu kamar an buɗe famfo. Azaba take ji amma kuma tana jin daɗi yanzu za ta daina jin abin da take ji a cikin zuciyanta. Gwara ta mutu in ta mutu za ta huta. Tana mai kallon kanta a madubi tana hawaye ta fara ganin kanta biyu biyu kafin ta ji jiri ya kwashe ta, ta yi baya ta dafa gado amma ina ya rinjayeta, tuni idanuwanta suka hau lumshewa jikinta ya saki da ta kasa iya riƙe kanta nan ta sulale ta faɗi kasa ta gefen hagu. Hannunta kuma har a lokacin bai daina zubar da jini ba, ga rezan da ta yanka kanta nan a yashe a gefen ta Ta ji daɗi domin jinta da ganinta ya tsaya cak zuciyarta ta daina aiki ta daina jin komai ta samu salaman da ta ke fata. Ta ji ɗif, ta samu natsuwa ta samu hutun zuciyan da take muradi. *1k on Telegram 09069067488* *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No. 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supplements wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. *20* *DAAMA SPECIALIST HOSPITAL* NO:70 72 Abubakar Atiku Rd. Jimeta Adamawa. VIP:Room 23. Ta daɗe tana jin wucewar iska a cikin kunnuwanta. Sannan kanta ya yi mata nauyi sosai tana ji kamar an ɗora mata katon dutse, idanuwanta take so ta buɗe amma ta kasa ji take yi kamar an danne idanuwanta nata da wani abu mai nauyin gaske. Tana ta ƙokarin motsa gangar jikinta lokaci ɗaya da fitar da numfashi sosai amma ta kasa jikinta ya tamke, ko ɗan yatsanta ba ta iya ɗagawa sai ma take ji kamar wuyanta ya rabu da gangan jikinta ne. Sannan bakinta da wani abu an yi mata takumkumi da ya hanata damar iya sakin numfashi sosai. Tana jiyo ɗan maganganu daga can nesa da ita amma ba za ta tantance komai ba, tana cikin kamar tsakanin rayuwa da mutuwa ne. Komai daga nesa take jin sa kamar ba a kusa da ita ba ne, tunani take ko dai ta mutu ne tana cikin kabari, tabbas ta mutu ƙasa ne ya danne ta da ya sa ta kasa motsa gangan jikinta. "Innalillahi wa'inna alaihirraju'un." Ta furta a cikin zuciyanta, tana ta ƙokarin buɗe idanuwanta ta kasa sai da ta daddage sannan ta samu nasaran buɗe kumburarrun idanuwanta da suka yi mata nauyi kamar an ɗora mata jakan duwatsu a sama, dishi dishi ta fara gani kafin ganin ta ya ɗan fara washe. Farin POP ta fara cin karo da shi lokaci ɗaya da karamar farar fanka a sama tana gudu sosai, shi ne iskar da take jin ƙaran wucewarsa a a cikin kunnuwanta. So take yi ta tuna abin da ya faru da ita amma ta kasa tuna komai, tunanin ta ya fi karkata da cewa ta mutu ne, to amma in har ta mutu to nan ba a cikin Kabari take ba, domin a cikin kabari babu rufin ɗaki sannan babu fanka. A hankali a hankali ganin ta ya fara washewa. Daƙyar ta iya ɗan waiga damanta da hagunta, daga lokacin ne ta fahimci kamar tana asibiti ne domin a yanayin ɗakin ita kaɗai ne a kan ƙaramin gado sannan ta ga tsitsiyan hannunta guda ɗaya da ƙarin ruwa. Me ya same ta? Me ta sa take kwance  a asibiti? Tana so ta yi tunanin yanayinta na ƙarshe amma ta kasa, kanta ya yi mata nauyi kamar ba na ta ba. Tsil ta ji daga gefen cikin ta, sai ta ɗan daga idanuwanta, ciki ta gani ya yi tsini a jikinta gabanta ya faɗi ras! A lokaci ɗaya kuma tunanin abin da ya sameta ya fara dawowa cikin kanta daki daki. "Hasbunallahi wani'mal wakeel." Hawaye ne masu zafi suka fara gangaro mata ta gefe da gefen idanuwanta masu raɗaɗi sai a yanzu ta samu damar kuka sai a yanzu ne nadama da dana sani suka rufeta sai a yanzu ta ke tunanin da a ce ta mutu fa? Shike nan ta mutu a kafira sai a yanzu ta tuna da Baffa da Ammah, sannan sai a yanzu ne ta tuna da sauran yan'uwanta amma a lokacin idanuwanta sun rufe zuciyanta ta ƙuntata fatan ta kawai ta yi nesa da jin zafin zuciya da raɗaɗi burinta ta samu salama da raɗaɗin dake taso mata a cikin kasan zuciyanta. Amma ina haƙanta bai cimma ruwa ba, ga in da ta kare nan, wataƙila Allah ne yake son ta shi ya sa ya ba ta wata damar. Ƙokarin tashi take yi amma ta kasa tana cikin wannan yanayin ne aka buɗe kofar ɗakin lokaci ɗaya wata nurse da fararen kaya ta bayyana a cikin ɗakin. Cikin ruwan hawaye Ummu Salma ta ɗago kanta tana kallon Nurse ɗin da ta shigo. "Laa kin farka? Nurse ɗin ta faɗa tana kallon Ummu kafin lokaci ɗaya ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Ummu ta bi ta da kallo a tunaninta in ta ƙariso za ta ce ta taimaka mata ta zauna sannan ta cire mata wannan igiya mai takumkumi da yake hanata numfashi da magana. Tana cigaba da ƙoƙarin tashi zaunen aka sake buɗe kofar aka shigo. Wannan karon ba iya mutum ɗaya ba ne,  likita ne akan gaba sanye da rigansu na likitoci da zugan wasu Nurses guda uku daga bayansa ciki har da wacce ta fara shigowa da farko. "Ma sha Allah" Ta ji ya faɗa lokaci ɗaya yana ƙarisowa gaban gadon da take kwance. Kallon shi ta yi da idanuwanta da suka shige ciki mamaki ta yi da jin abin da ya faɗa ba ta yi tunanin ma musulmi ba ne sai da ya sake magana sai ta sake shan mamaki. "Sannu ko? Ya sake faɗa yana kallonta da ɗan mirmishi a saman fuskar shi. Bayan musulmi ne, ashe ma yana jin hausa ba ta ɗauka ma yana ji ba ganinsa jajir kamar bature. Idanuwanta ta ɗan motsa tana cigaba da ƙokarin tashi ta zauna. "Kina so ki zauna ne? Ya tambayeta. Ita kuma sai ta lumshe idanuwanta ta sake buɗe domin ba zata iya ɗaga kan ta ba, ji take yi kamar kanta zai rabe gida biyu. "Okay.." Ya faɗa lokaci ɗaya ya kalli Nurse ɗin dake gefensa da ido kawai ya yi mata magana nan da nan sai gata ta nufo ta,  ta saka hannu ta cire mata abin da ya tare bakinta daga magana da shakar numfashi da kyau. Sannan kuma ta cire mata zaren karin ruwan dake tsitsiyan hannunta na hagu, amma ba ta cire canula ɗin ba sai a lokacin ma ta lura hannunta ya kumbura sosai watakila an yi ta fama kafin a samu jijiyar ne. Hannunta na dama Nurse ɗin ta kama za ta ɗan dago ta, ita kuma sai ta yi amfani da hannunta na hagu ta ɗan dafa gefen gado lokaci ɗaya ta ji wani mugun zafi ya ziyarce ta har ƙwaƙwalwa. "Wash..! Ta faɗa cikin fitan hayyaci murya a dashe. "Sorry, ki yi a hankali kin san left hand ɗinta akwai  rauni." Sai da ya faɗa haka sannan ta iya duba hannun nata na hagu, dai dai ta ɗan ɗagota ta zauna tana jin bayanta na sagewa saboda kwanciya. Rabin hannunta na hagu yana nannade da bandeji ne, ƙura ma hannu ido ta yi tana kallo hawaye na sake biyo kumatunta kamar an buɗe famfo. "Sannu ko? Ta ji an sake faɗa sai ta ɗan dago tana kallon likitan lokaci ɗaya ta na ɗan gyaɗa kanta dakyar. Kujera suka matso masa da shi wata fara ya zauna a gabanta, ɗaya Nurse ɗin ta miƙa masa Fayel ɗin Ummu Salma a hannun shi ya buɗe yana dubawa. "Ummu Salma Hadi Baba right? Dr. Ahmad ya faɗa yana sake kallonta ta cikin farin gilashin dake fuskarta. Nan ma kai ta gyaɗa masa cikin karfin hali, jin ta take yi kamar ba ita ba komai na jikinta ya yi mata kamar ba nata ba. Doguwar rigar dake jikinta ne na ranar da abin ya faru amma an yanke duka hannuwanta watakila da aka kawota asibiti ne wajen sauƙaka ma likitoci aiki ne ya sa suka yanke sannan mamaki take yi anan ta kwana ne? Tunda dai dai ta san lokacin da ta yi ma kanta illa, dare ne amma yanzu tana facing window ɗin ɗakin tana kuma ganin haske alamun kamar yamma ne ko rana. "Ba abin da ke damun ki ko? Ta ji likitan ya sake faɗa yana kallonta kuma da harshen hausa yake yi mata mgana. Idanuwanta ta lumshe ta sake buɗewa alamun babu abin da ke damunta, sai nauyin jikinta da ciwon kai. Dakyar ta iya buɗe baki ta ce" Kai na " "Sannu." "Da jikina kamar ba nawa ba." Ta faɗa lokaci ɗaya hawaye na kece mata wasu na zubowa wasu na sake tunkuɗowa. "Sorry duk zai bari in sha Allahu." Ya faɗa yana mai kallonta. "Ya hannun ki? Ba wani pain? Sai ta ɗan bi hannun da kallo kafin ta ɗan gyaɗa masa kai. "Babu." "Ya kike jin cikin jikin ki? Ba wata matsala dai ko? Ya tambaya yana mai sake nazarinta. Yana kallonta a matsayim mai sa'a a halin da aka kawo ta, bai ɗauka za ta tashi ba. "Babu," "Amma ina jin motsi." "Lafiyan jaririyan dake cikin ki ne, mun yi miki scanning mun gamsu da cewa jaririn dake cikin ki bai shiga hatsari ba." Ya faɗa yana ɗauko biro daga gaban aljihunsa ya fara rubutu a cikin fayel ɗin dake hannunsa. "Ummu Salma." Ya kira sunanta yana cigaba da rubutunsa. "Naa'm" Ta amsa cikin dashewar murya. Shuru ya yi bai sake magana ba, ita kuma tana hawaye tana tunanin ita kaɗai ne? Ina Ammah ina Baffa? Ina sauran danginta? Ba ta gansu ba. "Ina iyayena? Ta faɗa gashin idanuwanta jike da ruwan hawaye. Sai da ya gama rubutun shi sannan ya ɗago yana kallonta lokaci ɗaya yana mika ma Nurse ɗin dake gefen shi fayel ta rankwafa ta amsa cikin ladabi. "Duk suna waje." Ya faɗa yana nuna mata kofa. "Suna jiran mu gama aikin mu sai mu ba su damar su shigo su duba ki." Ya sake faɗa yana ɗan wasa da biron hannunsa. Kuka kawai Ummu take yi hawaye har sun jika mata gaban riganta, wannan ɗacin da zafin da ta so ta kashe kanta saboda shi, shi ne yanzu ya taso mata yana yi mata maƙakin a kasan zuciyarta ga shi yanzu ta sanya iyayenta da yan'uwanta a cikin damuwa. "Ummu Salma." Ya sake kiran sunanta. "Za ki iya tuna dalilin da ya sa kika tsinci kanki a asibiti? Ya tambaya kai tsaye yana mai kallon ta. Hawaye suka sake kece mata zata tuna mana. Za ta tuna cin amanar da ƙawarta Shamsiya ta yi mata tare da Habib, wadanɗa suka ba yar da guddumuwa wajen gurguta yau ɗinta da gobenta. Har a yanzu kalaman Shamsiya na yi mata amsa kuwwa a cikin kanta ba za ta taɓa mantawa da abinda ya same ta ba, domin wannan baƙin cikin watakila in bai yi ajalinta ba, to har ta koma ga Allah yana nan a cikin zuciyarta kuma yana saka ma gangar jikinta ciwo. "Kiin tuna? Ya sake tambayanta Kai ta gyaɗa masa cikin kuka da hawaye, shessheƙa take yi tana jin zuciyanta na bugawa da sauri da sauri. "Kin san cewa tun shekaranjiya da daddarre aka kawo mana ke ba kya numfashi? Ummu ta kalle shi cikin mamaki. "Tun shekaranjiya? Ta maimaita a saman laɓbanta. "Daƙyar muka iya ceto rayuwanki, ga shi kina da juna biyu ga shi kin zubar da jini kin shiga hatsari sosai da yasa ko bayan mun ceto numfashin ki, mun sanya miki oxygen amma ba ki farfaɗo ba sai yanzun nan." Majina ta ziraro ma Ummu amma ta kasa iya wani numfashi. Kuka kawai take yi hawaye suna zubowa wasu na sake kwaranya. Nadama take yi, dana sanin me ya sa ta aikata abin da ta aikata? Lalle Allah na son ta da ya sake ba ta wata damar a karo na biyu. "Kin yanka hannun ki sau biyu kuma yanka mai zurfi. Kin zubar da jini sosai da ya sa sai da ɗan'uwanki ya ba ki jininsa leda biyu muka sanya miki. Ba domin shi ba, da wataƙila wajen neman jinin lokaci ya ƙure har ki mutu bamu samu damar ceto rayuwarki ba." "Allah sarki ɗan'uwa. " Ta san ma Hamma Kabiru ne ya bata jininsa kamar yadda a baya ya taɓa bata jininsa. "Me ya sa kika yi yunkurin kashe kanki Ummu Salma? Dr Ahmad ya tambayeta kamar yadda yake a rubuce a jikin ɗan aninin dake jikin rigan likitancin jikinsa. Kuka Ummu Salma ta fashe da shi muryanta baya fita, bai hana ta ba gwara ta yi kukan ko zuciyanta za ta samu salama. Yadda take rera kukan ne, abin tausayin duk wanda ke kusa da ita yake kuma sauraranta. Kuka ne mai taɓa zuciya kukan nadama da bakin ciki. Nurses ɗin dake gefensa har akwai wacce ta yi ƙwalla jikinsu duk ya mutu. "Ke fa musulma ce, kin ta so gidan tarbiya da gata, ko daga yadda yan'uwanki suka cika asibitin nan saboda ke na shaida ke yar gata ce, wani dalili ne zai sa ki yi yunkurin kashe kanki? Kin manta duk wanda ya kashe kansa kafiri ne? Ko kin manta cewa da kin mutu a lokacin wutar jahannnama za ki shiga? Tsoro da wani irin imani suka sake kama zuciyar Ummu, ba ita kaɗai ba hatta Nurses ɗin dake ɗakin. "Komai ya faru dake ki gaya ma Allah Shi zai yi miki mganin komai. Mu musulmai ne mun san yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau yana cikin imani ne. " Ya sake faɗa yana mai kallonta. "Ina so ne, ina so ne na daina jin zafi da radaɗin dake cikin zuciyata." Ummu ta faɗa cikin matsanancin kuka majina da hawaye na kwanraya. "Me ya sa ba ki karanta Qur'ani ba? Me ya sa ba ki kira sunan Allah ba! Yana sane da halin da kike ciki, da kin daga hannun kin roƙesa salama da amimci da ya sama miki ba sai kin yi tunanin kashe kan ki ba Ummu Salma." Kuka kawai take yi tana jin kamar ta  mayar da hannun agogo baya. "A lokacin da kika yanke shawaran kashe kanki ba ki yi tunanin wannan ran dake motsi a cikin ki ba ? Da kin mutu fa? Da kin kashe rai biyu? Sannan kin manta da iyayenki da dangin ki? Kin yi tunanin yadda za su dauwama cikin kuka in har kika bar rayuwwansu? Ummu ta fara girgiza kanta tana cigaba da kuka. "Mahaifiyarki ana taho dake ta faɗi, kina ciki muna ceto rayuwarki ita kuma tana kwance ana daidaita numfashinta." "Wayyo Ammah." Ummu ta faɗa kamar za ta shiɗe." "Mahaifinki duk da ya yi dauriya amma kuka yake yi yana fargaba rasa ki, yayyenki maza duk da suna da jarumta sun shiga damuwa saboda ke, yau da ace kin mutu kina tunanin za su manta irin mutuwar da kika yi? To har abada ba za su taɓa mantawa ba." Ummu na kuka tana numfarfashi, ba ita kaɗai ba hatta Nurses ɗin nan suna ta goge ƙwallah "Kin yi sa'a. Allah na son ki ya sake ba ki wata dama. Ina so ki sani ki yi ta neman gafaran Allah ki kuma tuna kowani tsanani akwai sauƙi a wajen Allah." "Astagafurullah" "Allah na tuba." Ummu ta faɗa cikin matsanacin kuka kamar ranta zai fita. "Daga yau in tunanin kashe kanki ya sake zuwa cikin tunaninnki. To ki tuna da abubuwa guda uku, na farko yadda za ki koma gaban Allah a matsayin asararriya na biyu kuma halin da iyayenki za su shiga saboda ke. Na uku kuma ki tuna ke musulma ce, kuma duk musulmin kwarai yana da imani sannan ya yarda kaddara mai kyau ko mara kyau." "Na tuba Allah ka yafe mini." Take faɗa tana jin wani irin tsoro na sake shiga cikin zuciyanta. "A matsayina na likitan da ya karɓi case ɗinki har ya ceto rayuwanki, shi ya sa na baki shawara sannan a matsayina na musulmi na tunasar dake abin da kika manta, in kin shiga damuwa ko baƙin ciki ki yi kuka har sai kin gaji amma ki yi addu'a ki karanta Qur'ani ki samu salama, kar ki yadda ki bari tunanin sake aikata irin haka ya sake shigarki, ki sani in a wannan karon kin rayu watakila na gaba ba za ki rayu ba Ummu Salma." Ya gama faɗa lokaci ɗaya yana mai mikewa tsaye. "Na gode Dr." "Sunana Ahmad Salisu." Ya faɗa yana kallonta. "Ya isa haka, ki sassaita kukan ki saboda yanayin jikin ki." Kai ta gyaɗa masa hawaye na kece mata. "Allah ya ba ki lafiya." Ta amsa da Amin Kafin ya wuce nurses ɗin suka bi bayan shi jiki a sanyaye. "Ku ba ma Family ɗinta damar ganin ta." Ya faɗa ma Nursea ɗin kafin ya fice daga ɗakin su bi bayan shi. Bayan fitan shi kuka Ummu Salma ta cigaba da yi har da shessheƙa. Sai dai kukanta ya tsaya ne lokacin da ta ji an buɗe kofa ta ɗago jiƙakkun idanuwanta tana kallon kofar shigowa. Sai da ta ga yan'uwanta suna shigowa. Wani na ture wani, Mami ce akan gaba sai Baɗɗo bayan ta Adda Suwaiba ce, sai Adda Ummu Sulaim, Sai iklima sai Umma Balki sannan mazan suka biyo bayan su. Hamma Abdullahi ne ya shigo bayan sa kuma Hamma Mustpaha, Hamma Abdulrrahman sai Hamma Kabiru ne ya zama karshen shigowa. Ba Ammah ba Baffa haka Ummu ta faɗa a cikin zuciyanta, a tunaninta ko suna baya ne ba su shigo ba amma sai ta ga Hamma Kabiru da ya zama karshen shigowa ya rufe ƙofar sannan ba ta ga Hamma Jibo ba, sannan ba ta ga Hamma Saddam ba, shi da man baya nan ya koma makaranta. Baɗɗo da Mami suna rige-rigen ƙarisawa gare ta cikin wani yanayi a saman fuskokinsu. "Ma sha Allah. Sannu Daughter." Mami ta faɗa tana zama gefen gadon data ke kwance har tana rumgumota ta gefen hannunta na hagu. Jin ta a jikin Mami kawai sai ta saki kukanta wiwi kamar karamar yarinya nadama ya sake kamata ta. Ta saka kowa ya zo, zuwam kuma ba na lafiya ba, ba kuma zuwan shiri ba. "Shii is ok. Mun gode ma Allah tunda kin farfaɗo, kukan ya isa haka." Mami take faɗa tana bubbuga bayanta. Baɗɗo ma kusa da Mami ta zauna tana mai kallon Ummu idanuwanta cike da hawaye ga shi sun kumbura. Tun shekaranjiya take kuka ba ta daina ba. Sai aka koma ita ake ba hakuri ana lallashi. "Sisna" Baɗɗo ta faɗa tana mai riƙe hannun Ummu wanda aka cire ma ƙarin ruwa. "Sisna me ya sa? Baɗɗo ta sake faɗa lokaci ɗaya tana mai fashewa da kuka. Ummu ma hawaye suka sake kece mata kamar an ɓude famfo. "Ku yi haƙuri." Ta faɗa a hankali bakinta na rawa. "Shii. Ya isa nan asibiti ne." Mami ta faɗa tana mai share ma Ummu hawaye da mayafinta jikinta har da majina. "Bar kuka kin ji ko? Mun gode ma Allah da kika rayu." Mami ta sake faɗa tana share mata hawaye. "Mami." Ta kira sunanta cikin dashewar murya da kuka. "Naam My First Daughter." "Ku yafe mini Mami." Ta sake faɗa lokaci ɗaya tana mai fashewa da kuka. Sake rumgumota Mami ta yi, itama hawaye sun kawo mata saboda tausayin halin da Ummu ke ciki. "Ya isa, is ok kin ji.? Ta sake faɗa tana mai ɗan tapping ɗin bayanta alamun lallashi. Sannan ta sake ɗagota tana mai share mata hawaye da gefen mayafinta. "Sannu Ummu kin auna arziƙi." Umma Balki ta faɗa cikin wani yanayi. "Amma dai abin da kika yi sakarci ne, gabaɗaya kin ɗaga mana hankali? Haka ake yi? Kan ki farau mutuwar aure? Ta faɗa cikin faɗa, da man ita da Ammah ne a ɗakinsu suke da faɗa "In da kin mutu fa? Wani hali iyayenki za su shiga! Jamila tana ganin halin da aka kawo ki rai ƙwai kwai ta yanke jiki ta faɗi yanzu in da ya zo da karan kwana fa? Me za ki faɗa ma Allah, ke kin kashe kanki bakincikin ki ya kashe uwar da ta haifeki duk saboda namiji? Namijin banza, namijin ƙanin ajali to ni a matsayina ta uwarki na ce in kika sake ma tuna wannan maci amanan ba mu yafe miki ba shashasha kawai." Ta gama faɗa har tana nuna ma Ummu Salma ɗan yatsa wacce ta lafe a jikin Mami tana ta kuka. "Umma ku yi haƙuri." "Kaniyarki da haƙurin, sakarya, ba ki da tunani ne! Ina ilimin ki da hankalin ki yake Ummu Salma? Kawai ki yanka kanki kamar a wasan ƙwaiƙwayo" Ummu kuka take yi har yana ba da sauti ga hawaye ga majina. "Na yi nadama." Ta ke faɗa muryanta na shaƙewa. Mami ke lallashinta amma faɗan Ummu Balki ne ya sa kukanta yaƙi tsayawa. "Umma Balki don Allah ki yi haƙuri a bar maganar nan tunda dai ya faru kuma an ci sa'a abin ya zo da sauƙi ba sai a yi hakuri ba." Mami ta faɗa tana kallon Umma Balki. "Ke ma Fatima kaniyarki? Ke ce ke ɗaure mata kugun ta yi sakarci sannana za a yi mata faɗa ba? Kenan ma abun da ta yi mai kyau ne." Mami ta yi shuru jin an zage ta. Su Hamma Mustapha da suke ɗakin sun yi shuru kamar ruwa ya ci su. "Ki yi haƙuri Umma tunda muna asibiti ne." Adda Suwaiba ta faɗa, itama tsaraban hararan ta samu da ya sanya ta kama bakinta ta yi shuru. "Ai Umma abin da kika yi ya yi daidai. Ni ba domin na lallashi kaina ba, na so ne ina shigowa na falla mata maruka goma sannan na taka wuyanta sai ta kusa mutuwan da gaske sannan zan ƙyaleta." Hamma Kabiru ya faɗa cikin kaushin sa. "Yauwa, faɗa mata ina daɗin shi ai ko ba a mare ta ba, a yi mata faɗa shi dukan in ta warke a yi mata tunda ba ta da tunani haka kurum, kin tayar mana da hankali mun kasa sukuni da fargaba." Umma Balki ta sake faɗa cikin yanayin faɗan ta. "To a dai yi haƙuri tunda muna asibiti ne." In ji Hamma Mustapha da ya faɗa yana kallon Ummu dake kuka kamar ranta zai fita duk tausayin ta ya gama kashe masa jiki. "Ni ban taɓa tunanin Ummu za ta iya yin wannan sakarcin ba wallahi." Hamma Abdullahi ya faɗa yana ɗan cije leɓensa na ƙasa. "Ni wallahi wani takaici na ke ji in ma tuna akan wani sakarai wanda rayuwarta ba ta da amfani a wajen shi ta so kashe kanta. Wallahi ji nake yi kamar na kamata da duka." Hamma Abdulrahaman ya faɗa yana mai jin takaici na taso masa. "Don Allah ku bar wannan maganar har mu koma gida." Mami ta sake faɗa tana kallon su Hamma Abdullahi. "Gaskiya ko don natsuwar ita Auta." Ummu Sulaim ta faɗa tana kallon Ummu cikin tausayawa. "Sai fa mun faɗa mata Mami, mu dai kar ta yi sanadiyar mutuwar Ammah, in hakan ya faru wallahi ba za mu yafe mata ba." Hamma Kabiru ya faɗa yana balla ma Ummu Harara kukan banza take yi, shi da za a bar shi da ya lallasa ta, in aka tsaya ana jin tausayinta gaba ma za ta sake aikata irin haka. Dukkansu suna wajen aikinsu ta ɗaga musu hankali ta sanya sun baro komai sun taho saboda ita. "Hamma." Ummu ta faɗa cikin matsanancin kuka. "Ina Ammah? Ta faɗa tana ware idanuwanta akan dukkansu. "Tana gida tare da Ummi." Iklima ta faɗa cikin sanyin jiki. Halin da ta ga Ummu ya sake tsoratar da ita ga lamarin maza. "Kar ki damu ba abin da ya same ta, suma ne ta yi tana farfaɗowa suka koma gida." "Baffa fa? Ta sake tambaya cikin muryan kuka. "Yana gida amma Baba ya kira shi a waya ya sanar da shi farkawanki na san yana tafe." Mami ta fada tana mai sake share ma Ummu hawaye. "Ki daina wannan kukan, likita ya ce kar mu saka ki kuka, su na son ki samu hutu saboda jinin ki ya ɗan yi sama.". Kanta ta ɗan gyaɗa, a tunanin ba su san abin da ya saka ta yanka kanta ba, ta ɗauka kawai suna tunanin saboda sakin da Habib ya yi mata ne. Gabaɗaya suka yi ta masa sannu tana amsawa. Ba su wani daɗe ba mazan suka fita tunda ta farfaɗo zaman asibiti kuma ya kare, Baɗdo kawai aka bari da Mami, su Adda Suwaiba ma sun bi mazajensu zuwa gida tunda tun safe suna asibitin. Ummu ta tambayi Baɗɗo karfe nawa ta ce mata biyar da rabi na yamma. Sai ta ɗan runtse idanuwanta sannan ta sake buɗewa tana kallon Baɗɗo, an samu sa'a Umma Balki ta bi su Hamma Abdullahi zuwa gida. Mami kuma mijinta ya kirata a waya sai ta fita daga ɗakin bayan fitan su ne Ummu ta kalli Baɗɗo lokaci ɗaya tana fadin" Yanzu kwana biyu na yi a asibiti ban san in da kaina yake ba? Ta faɗa cikin sanyin muryan da ta disashe da kuka. "E, tunda aka kawo ki kina emargency sai yau ne ma da safe suka kawo ki wannan ɗakin." Ummu ta dukar da kanta saboda hawayenta da suka kawo "Allah na tuba." Ta faɗa tana kecewa da kuka wannan karon Baɗdo aka bari da lallashi. "Why Ummu Salma? Akan Habib ko akan Shamsiya? Da sauri Ummu ta kalleta cikin mamaki. "Da man kin sani? Ta tambayeta cikin raunin murya. "Na sani, ai dalilin kiran da na yi ta miki a daran shekaranjiya kenan ba ki ɗaga kirana ba. Nima a status ɗin wata course mate dina na gani, ban taba tunanin Shamsiya za ta iya cin amanarki ba. Amma ban yi mamakinta ba, daga baya ta sauya dake sai da haka ta faru na fahimci dalilinta na kare ma Habibu ashe maciya amana ne." Ta gama faɗa cikin bakinciki da takaici. Kuka kawai Ummu ke yi kamar ranta zai fita. "Na tsani Habib, na tsani Shamsiya. Ba zan taɓa yafe musu ba.' Ummu ta faɗa majina na zilalo mata. "Ki tsane su, amma ki fara cire su daga tunanin ki da rayuwarki gabaɗaya. Ba su da amfani kuma in dai amanace da suka ci taki su je ga su ga duniyanan nan da ikon Allah sai Allah ya saka miki." Baɗdo ta sake faɗa itama tana hawaye "Shamsiya fa? Ashe duk abin da Habib yake yi mini da sanin ta.". Nan Ummu ta fara ba ta labarin yadda suka yi da Shamsiya a gidan su. "Ni dai na san na dawo gida cikin baƙinciki, ina so na ji zuciyata ta daina kuka, baɗdo ban san me ya sa na yi tunanin kashe kaina ba ni dai kawai ina so na samu salama ne a cikin zuciya ta." Ta faɗa tana mai gunjin kuka. Baɗɗo ta rumgumeta ta gefe tana ɗan bubbuga bayanta alamun lallashi. "Ni ce na fara iskoki kwance jini na tsiyaya a hannun ki. Daman da na yi ta kiran ki baki ɗaga a daran na ce ma Ummi zan zo wajen ki, ina zuwa na samu Ammah da Baffa tare da Hamma Lamiɗo a dakin Baffa bayan mun gaisa sai na shigo ɗakin ki na iske ki kwance ba numfashi a tare dake nan fa na fasa ihu su Baffa suka rugo zuwa ɗakin ki." Ummu na cigaba da tsiyayan hawaye tana sauraran Baɗɗo Baffa da Ammah sun shiga tashin hankalin da suka kasa iya baki wani taimako. Ba domin Hamma Lamiɗo na nan ba da watakila jininki ya tsiyaye mu ba mu samu mafita ba." Cak kukan Ummu ta tsaya ta da kukanta ta yi kasaƙe tana kallon Baɗɗo cikin mamakin jin sunan wanda ta ambata. Tabbas a ranar ya zo, amma ita tama manta da shi kwatakwata. "Shi ya yanki zanin ki ya ɗaure hannun ki zubar jinin ya tsaya. Sannan shi ya ya ɗauke ki cak zuwa mota da ni da shi da Ammah da Baffa muka kawo ki wannan asibitin cikin tashin hankali." Ummu ta sake ƙura mata ido cikin mamakin wai Hamma Lamiɗo ne ya yi mata haka? Da man yana da tausayi.? Ita kallon mara tausayi take yi masa wanda bai damu da kowa ba. "Dakyar suka karɓe ki, sun ce case ne na hatsari suna bukatar yan sanda Hamma Lamido ne ya yi cuku cukun da suka karbe ki. An yi nasaran ceto numfashin ki amma suka ce sai an sanya miki oxygen kuma kina bukatar jini, ga shi Hamma Kabiru ba ya kusa ana maganar a je a duba a lab a ko za a samu wanda zai dace dake, kawai Hamma Lamiɗo ya ce jininsa O ne, nan take kuma aka je aka gwada shi ba wata matsala aka ɗibi leda biyu aka sanya miki a daran nan." Ummu sai da ta yi yar shaƙuwa. "Daman ba Hamma Kabiru ba ne ya ba ni jininsa ba? "A daran ta ina Hamma Kabiru zai taho? Yau ne ma ya samu zuwa ba daɗewa. Hamma Lamiɗo ne ya ba ki jininsa Sisna, ni kaina lamarin ya ba ni mamaki ban taba tunanin yana da tausayi haka ba" Ummu Salma ta haɗiye wani miyau a maƙwagaronta. Jikinta take kallo tana jinjina kai wai akwai jinin Hamma Lamiɗo a jikinta yanzu haka. "Kin ga farar shaddar jikinsa duk ta ɓaci da jinin ki, Baffa ya yi ta cewa ya je gida ya sauya bai tafi ba saboda faɗuwar da Ammah ta yi shi ya zauna da ita har asuba aka sallameta sai ya ɗauketa zuwa gida ni da Baffa kuma muka kwana dake sai da safe ne Ummi ta zo sannan ya koma gida." Ummu ta share hawayenta da gefen hannunta na hagu, hannunta na dama take kallo dake dauke da bandage ya kumbura "Ɗinki aka yi miki. Likitan ya ce Allah yasa yankar bai yi zurfi ba." Ummu dai sai sharan kwalla ba magana. "Kin faɗa musu abin da ya faru ne? Ta tambaya tana kallon Baɗɗo "Na faɗa musu, kawarki Shamsiya ce ta za ta auri Habib shi ne kika yi yinkurin kashe kanki." Ummu ta runtse idanuwanta tana jin kalmar kashe kanta ita ta aikata amma nadamar take yi, tsanar kalmar take yi. "Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrahaman sun yi ta faɗa, Baffa na fama da kansa bai ma yi musu magana ba zuwan Mami ne ma da ta yi musu mgana suka ɗan yi sauki da faɗan na su, amma kaf din su sun shiga damuwa ana kiransu a safiyar jiya suka cika asibitin nan tare da matan su, Mami ma ajiyan ta iso da rana. Hamma Jibo ne kaɗai bai zo ba saboda aiki Hamma Sadam na makaranta bana ma tunanin ya san abin da ya faru." Ummu ta yi shuru kafin ta ce" Baɗdo na yi nadamar sanin Habib na yi nadamar sanin Shamsiya a rayuwata." "Ki bar su da Allah, yau ne daurin auran an ma ɗaura tun dazu ta je ga ta ga Habib ɗin shima ga shi ga Shamsiyan in dai don sun tozarta ki ne suka samu damar auran juna. To da ikon Allah suma sai Allah ya tozarta su." "Allah ya isa, ba zan taɓa yafe musu ba, sun lalata mini rayuwata. Me na yi musu? Ummu ta sake fada tana kuka. "Ba ki yi musu komai ba, ki dauka a haka a matsayin kaddaran ki. Ki bar masa faɗan shi zai saka miki " Ummu ta cije lebenta na kasa tana jin wani irin turiri a zuciyanta. Ta tsani Habib ta tsani maza ma gabaɗaya dalilin shi yau take kwance akan gadon asibiti ta gode ma Allah da ya sake ba ta wata damar da yanzu ta mutu shikenan ta mutu a kafira ta yi asaran rayuwanta saboda Habib da Shamsiya da man burinsu kenan. In dai haka ne ba za ta sake ba su wannan damar ba, za ta cire su daga duniyarta har abada amma ba lalle ne abin da suka yi mata ya bace daga zuciyarta ba, har abada sun riga sun dasa masa ciwo mai wuyar warkewa a zuciyanta. "Ki yi hakuri, ki yi hakuri amma don Allsh kar ki sake tunanin kashe kanki Ummu Salma." Baɗdo ta faɗa cikin karaya. "Ba zan kara ba, in sha Allahu ba zan kara ba." Ta faɗa cikin kuka da hawaye shaɓe-shaɓe. Suka rumgume juna Ummu na kuka da shessheƙa Baɗɗo na hawayen tausayin Ummu. A haka Mami ta dawo ta same su, sai ta fara faɗan ya haka kuma? Ita Baɗɗo da za ta yi lallashi sai ta bige da kuka nan take tace su bari ba ta so. Dole suka share hawayen su, sai dai ajiyar zuciya. Sai mangariba likita ya dawo suka sake ɗaura ma Ummu karin ruwa sannan suka yi mata allura. Mami ta koma gida da Hamma Abdullahi ya kawo Baffa ya duba Ummu ya sameta idanuwanta biyu tana kuka ta rirriƙe hannayen Baffa tana cewa ya yi hakuri. "Bakomai Auta, na yi ma Allah godiya da kika kuɓuta ina sake masa godiya." Da yakee an yi mata allura ashe akwai na barci ba daɗewa sai barci ya kwashe ta. Baɗɗo ne da Mami suka kwana da ita, can dare Mami ta dawo da abinci da kayan da aka samu aka sauyawa Ummu. Sai a daran Ummu Salma ta sha tea cikin ta ya warware sannan ta ɗan ci abincin kaɗan. Washegari ma yan'uwa suna ta zuwa duba ta, don ma nurses ɗin suna hanawa, sai a ranar aka ɗan rike Ummu zuwa tiolet ɗin Mami ta ɗan yi mata wanka amma ba a bari ya taba hannun ba. Bayan sun fito Baɗɗo ta kama mata suka sanya mata wata doguwar riga mai bubu, ta samu ta rarrafa ta yi rama sallolin da suka suɓuce mata daga zaune. Wasa wasa sai da Ummu ta yi sati a asibiti sai da ta yi ras suka tabbatar da ba wata matsala sannan suka ba su sallama bayan an cire bandejin hannun ɗinkin ya fara shigewa ciki ya ɗan yi baƙi wajen sun ce ta samu hutu saboda jininta ya hau da kuma lafiyan jaririn jikinta. Har aka sallameta Mami ne da Baɗdo ke jinyarta Ammah ta zo ta duba ta sau daya itama haka ta riƙeta tana kuka tana cewa ta yafe mata Ammah ta ce ba komai amma ta sani in ta kashe kanta saboda Habib ko Shamsiya ta sani ba za ta taɓa yafe mata ba. Yan'uwan Ammah duk sun zo har su Umma Salamatu. Bangaren su Baffa Umaru dai Baffa bai faɗa musu ba yace kar a tayar musu da hankali. Hamma Kabiru da Hamma Mustapha sun koma wajen aikinsu tun kafin a sallami Ummu ganin ta samu sauki sosai. Ummu tana so ta tambayi Hamma Lamiɗo domin ba ta ganin shi ba tun bayan da ta farka amma ba ta samu hali ba, sai a daran da suka koma gida ta ji Ammah na faɗa ma Hamma Jibo a waya da cewa komai na asibitin nan shi ya biya. Ashe baya nan tun washegarin ranar da abin ya faru ya koma Lagos, amma yana kiran Ammah da Baffa yana jin yanayin da ake ciki. Ummu Salma kunya take ji in aka ba ta waya za a gaisheta sai ta yi ta tunanin shike nan yanzu kowa ya ji labarin ta kusa kashe kanta. Har matar Hamma Lamiɗo ta kira a wayar Ammah an ba ta sun gaisa, haka ma Hamma Jibo da Adda Nauwara amma ba a fasa zahirin abin da ya faru ga kowa ba. Hamma Saddam da Hamma Abdulrahim ba a gaya musu ba. Saboda suna nesa ba amfanin yayata maganar tunda lamarin ba mai daɗi ba ne. Ummu ta yi nadama ko da yaushe kuka take yi tana neman gafaran Allah tun ballanta da Baffa ya kirata ya zaunar da ita ya sake tunasar da ita abin da ta manta. Ya horar da ita hakuri da imani, Ammah kuma faɗa ta yi ta yi, domin daman ta ce tun lokacin da ta ji Shamsiya na wannan maganar ta ɗora mata ayar tambaya. Ta kuma ce in Ummu Salma ta haifu to ta manta da Habib ballanta Shamiya har a gaban Ka'aba ta yi ma Allah kirari da kukan cewa Allah ya saka musu, yadda Habib ya wulakanta su shima Allah ya mayar masa da abin da ya yi musu. Ita dai Ummu sai kuka ta yi nadama sanadin Habib ta goga ma kanta taɓo, yankan hannunta ko da ya fara warkewa har abada za ta koma ga Allah da wannan tabon a hannunta in ta kalli hannunta sai ta tuna da wannan bakar ranar. Baɗɗo ta cika ƙawa kuma yar'uwa domin bayan ta yi jinyarta a asibiti da suka dawo gida kullum sai ta zo, makaranta ma daina zuwa ta yi a cewarta karatu kawai suke yi wacce suke tare ke saka mata attendence in za a yi test kuma tana yi mata, Ummu ta riƙe alherin Baɗɗo a cikin zuciyanta, tana fatan nan gaba kafin ta mutu Allah ya ba ta ikon da za ta iya saka ma Baɗɗo da tarin alherukan da ta yi mata. Ba Baɗɗo ba hatta Ummin ikki ba ta zauna ba ita ke zaune da Ammah a gida lokacin Ummu tana asibiti. Ita da zuru'anta ba aminta ba sun zame ma Ammah ahali ita da ya'yanta da ƴan'uwanta gabaɗaya. Mami dai wannan karon ta ce kafarta kafar Ummu Salma. Za ta ɗauke ta gabadaya daga Jimeta ta koma Kaduna a can kuma za ta haihu. Baffa ma wannan karon bai yi gaddama ba, shima zai so Auta ta ɗan yi nesa da wannan garin na wani dogon lokaci duka yayyenta ma sun amince da haka domin sauya muhalli da jama'a da yanayin iskar gari na kawo kwanciyar hankali. Ummun ma ta aminta daman ko Mamin ba ta ce kafarta kafarta ba ita za ta ce za ta bita domin ta gaji da Jimeta ji take yi gabadaya tana kuntace ne da zaman garin, da Umma Balki ce ta ce za ta tafi da Ummun Mubi Mami ta ce Kaduna za ta tafi da ita har sai da ta ji haushi wai a cewarta ita kanta Mamin yarinya ce ba za ta iya kula da Ummun ba sannan biye mata za ta yi ba za ta yi mata faɗa in ta yi ba daidai ba. Baffa ya yi ta dariya ya na ce ma Umma Balki mai ɗa kamar Lamiɗo ne yarinya? Ta ce E mana ai auran wuri ta yi ta haife shi Lamiɗo ai ɗan yarinya ne. Baffa kamar cikinsa zai kulle Mami dai tana jin ta ba ta saka baki da man tun tana gida kafin ta yi aure a Kaduna in dai Umma Balki ta zo gidan sai sun yi tsiya ba ta gani ta ƙyale. Baffa ya raba gaddama ya ce Auta ta zabi in da za ta je ita kuma ta ce Kaduna. Umma Balki ta ce Allah ya kiyaye hanya amma ba haka taso ba. Hamma Abdulrahaman ya ce itama dai Umma Balki da rigima nauyi kawai Ummu za ta kara mata, gwara dai Mamin ta tafi da ita can Kaduna zai fi. Haka ko aka yi tuni suka fara shirin tafiya Kaduna kayan Ummu masu dan kyau kaɗan Mami ta ce za ta tafi da shi sauran har na wajen Habib ta ce duk Ammah ta aika da su Mubi a kyautar da su in suka je can Kaduna za ta yi mata sabbin ɗinkuna. Alhaji Isa ne zai zo da yara ranar asabar in suka kwana lahadi sai su koma gabaɗaya tare da Ummun da Mami. Shi ya sa ranar jumma'a da safe Mami ta ɗauketa suka je can asibitin da take awo Hamma Abdullahi ya kai su ta yi musu bayanin za ta tafi da Ummu tana son report na bayananta saboda in sun koma can in za ta fara zuwa sabon asibiti sai ta nuna musu. Abu na kuɗi ba daɗewa suka rubuta duka bayanan suka ba ta, wajen sha ɗaya suka dawo gidan nan Ammah ke faɗa musu Hamma Lamiɗo ya zo bayan fitan su ba daɗewa sun fita tare da Hamma Abdulrrahman. Gaban Ummu sai da ya faɗi saboda jin sunan Lamiɗo, in ta tuna da shi sai ta tuna da cewa jininsa na yawo a cikin jinin jikinta sai ta ji wani iri a acikin zuciyanta. Ita dai ciki ta shige ta ɗan cigaba da kimtsa kayanta, ta ɗauko tsohuwar wayarta bayan ta cire layin ta karya ta ba ma Ammah tace ta kyautar. Ta sake komawa ciki tana cikin har aka yi azahar Mami na falo suna ta hira da Ammah. Ta idar da salla kenan ta ji shigowar su gidan ba ta ji dai muryansa ba amma ta san da shi tunda ta ji Ammah na kiran sunan shi Ba ta aikin komai yanzu tunda dai ba ta fara amfani da hannunta na hagu ba, duk da dai ɗinkin ya shige kuma wajen yana warkewa. Saboda Hamma Lamiɗo ta ki fitowa ga shi tana jin yunwa ta so ta je ko kitchen ne ta samu abincin tunda Ammah ta gama shinkafa da miya tun ɗazu, amma ba ta son kallon Hamma Lamiɗo kunya take ki shi ya sa ta kasa fita, ta aikata abu yanzu kuma daga baya tana jin matsanacin kunya idan aka danganta ta da abin da ta aikata. Allah ya sa ma ba a yayata lamarin ba iya na gida ne da na jiki jiki na kusa suka san meke faruwa ko can su Baffa Umaru da suka ce sun ji cewa Auta ba lafiya sai Baffa ya ce kawai rashin lafiya ne ta yi, to babu amfanin faɗin komai tunda dai ba abin daɗi ba ne. Haka ta naɗe yunwarta a cikin ɗaki ba wanda ya tuna da ita tana jin hiransu a falo da alama ma abinci suke ci domin tana jin Hamma Abdullahi na cika baki da abinci yana magana yau daga Ammah har Mami sun manta da ita, to ai gwara Mami yau watakila ta sha'afa ne Ammah kuma yau tunda Lamiɗo ya zo ko Baffa sai ta manta da shi ba ma ita ba. Tana cikin halin yunwar nan Mami ta shigo yin salla ita ce ta taimake ta, bayan ta idar ta ce mata yunwa take ji sai ta fita da sauri ta je ta zubo mata abinci ta kawo mata sannan ta fita falo ta ɗauko mata ruwan gora da ake ajiyewa saman frizan saboda Ummu ba ta shan ruwa mai sanyi ba duka ake sanyawa a firizan ba. Tana jin Hamma Abdulrrahman na ce ma Mami wai tana shagwaɓa ta, ta kai mata abinci har ɗaki ruwan ma da shi za ta bita. "Kafafunta ne ke ciwo? Haba Mami." Amsar da Mami ta bashi ne yasa tana cin abinci sai da ta yi dariya sai da ta kusa ƙwarewa. "Ina ruwan ka? Nan kuma Ammah ke rawan jiki da ku ban yi magana ba, ta manta da mai juna biyu, nima shine na miƙe na ke kula da ya'ta." "Ah Mami ki ce dai kawai kishi kike yi da mu kawai." Hamma Abdullahi ya faɗa yana dariya. "Ku dai kuke kishi da Auta, ku ana kula da ku, tun shigowarku Ammah ta ba ku abinci ita mai yaron ciki ta manta da ita." Ammah na dariya ta ce" To ba kin fanshe ni ba, ina nan ina ji da mazan ke kiji da macen ba shike nan ba." Mami ta yi wucewarta ta bar suna mata dariya. Lamido na zaune a gefe ko tak bai ce ba, dukkansu shigar fararen kaya suka yi. A saman cafet din Ammah suka baje suna cin abincin Lamiɗo salat kawai ya ke ci da miyan shinkafan kaɗan yake ɗibaa, duk hiran da ake yi ba kasafai yake saka musu baki ba. Ko Mami sun gaisa irin gaisuwan da suka saba, ya tambayi su Islam tace ai za su haɗu gobe za su taho tare da babansu, ya kasa ce mata shi yau zai koma Lagos, sai kawai ya yi mata shuru. Baffa kuma ba ya nan ma ba a masallaci ɗaya suka yi sallar Jumma'a da shi ba, da wuri ya tafi yace akwai wanda zai gani ne. Ita dai Ummu sai da ta gama cin abincin ta sha ruwa sannan ta ji ta ta dawo daidai, sai cikinta ya sake yin ƙasa saboda ta ci Abinci kwanciya ta yi ta gefe tana ɗan sauke numfashi ta kasa zama saboda tana jin cikinta ya cika. Mami ne ta sake shigowa ta shiga tiolet tana yi ma Ummu sannu ta amsa dakyar. Shigan ta ba daɗewa Ammah ta leƙo ganin Ummun kwance ya sa ta ce" ke kuma daga ci sai kwanciya." Ummu ta yunkura ta tashi zaune kafafunta a kasan cafet duk sun kumbura. "Ammah na kasa zama ne." "Da dai kin daure." Ta faɗa tana ɗan kallonta ganin tana ɗan cije baki. "Sannu." Ammah ta ce cikin tausayawa tana kallonta. "Ga Lamiɗo nan zai wuce ya ce zai shigo ya sake duba ki.' Sai Ummu ta fara kifta idanuwana saboda mamaki. Hamma Lamiɗo ne zai ce zai shigo ya duba ta, abin da ba ta taba zato ba. Ta tuna wani lokaci a baya can tun ba ta yi aure ba, ta taɓa wani irin ciwo kamar za ta mutu na typiod , kowa ya yi mata sannu ya duba ta amma ban da shi, ita tana jin ma sannu na ciwo bai taɓa shiga tsakanin su ba. Kafin ma ta yi wani yunkuri Ammah ta fita, ta miƙe dakyar domin ta nemi hijabi ta saka sai ga Ammah ta dawo bayanta kuma Hamma Lamiɗo ne ya sawo kai cikin ƙwarjininsa. "Gata nan ai hannu ya ɗauko warkewa." Ammah ta faɗa tana nuna masa Ummu Salma da ta sandare a tsaye ga ciki a gaba kanta ba ɗan kwalli wani tujajjan kitso ne da ba ta san ma daɗewar shi ba, tun dawowarta gida tana jin sau ɗaya ta taba yin kitso shima Baɗɗo ce ta ga kan ya tsufa ta tsefe ta ɗan yi mata duka baya guda goma kitson bai wani kamu ba, shi ya sa duk ya zare da wuri. Ummu kunyar duniya duk ya kamata sai kawai ta dukar da kanta ta koma tana wasa da zaren adon rigan jikinta doguwa mai kalan purple. "Auta ba ki gaishe da yayan na ki ba, jininsa ya cece ki daga mutuwa don kaniyarki" Ammah ta faɗa cikin ɗan zolaya. "Ina yini Ha. Hamma." Ta faɗa cikin ɗan rawan murya. "Lafiya." Ya amsa a saman leɓensa. Hamma Abdullahi ne ya kira Ammah daga falo sai ta fita ta bar Ummu da Lamiɗo a ɗakin. Tuni ta ji jikinta ya fara rawa, haɗa inuwa ɗaya da Hamma Lamiɗo ma tashin hankali ne zuciyanta taji tana tsinkewa kamar kasa ta tsage ta shige. Shuru na mintina biyar ta ma ɗauka ya bar ɗakin ne tana ɗagowa suka haɗa ido, ya kafeta da kaifaffun idanuwansa hannayensa duka zube a cikin aljihun wandon farar shaddar jikinsa. Kafarsa akwai safa amma bai ɓoye zarazarab yatsun kafafunsa ba. Da sauri ta sake sadda kanta ƙasa jikinta na sake ɗaukan bari, har ɗan cikinta sai da ya motsa. "Ashe ba ki da wayau." Ya faɗa cikin muryansa cike da ƙasaita "Ban sani ba " Ya dire maganarsa yana mai kafe ta da idanuwansa. Ummu ta kifta ido ta buɗe sai hawaye sharr suka kece mata ba ta son ana tuna mata shirmen da ta yi, ba ta so. "Kin san abin da kika yi." Numfashi ya ja kafin ya dire. "Ya saka Ammah Suma." Ya dire maganarsa abin na sukan zuciyansa. Yana tuna lokacin da Ammah ta zube a kasa a bakin emergency, ya ji tsoro ya kuma ji fargaban in wani abu ya same ta ya zai yi?? "Kina so ki kashe mini uwa ne.? Ya faɗa ya ɗan ɗaga murya. Wai uwa, itama ai mahaifiyarta ce. Tuni har ta fara kuka har yana sauti "In kin shirya mutuwa saboda wani rubbish, " Ya dakata yana ɗan sauke numfashi domin ya fara harzuƙa in ma ya tuna dalilin da yarinyar nan ta nemi kashe kanta "To ki mutu, amma kar ki bari sanadin haka ya taɓa Ammah ko Baffa." Ummu ta fashe da kuka sai ga ta duke ganin ta ƙasa durƙusawan zai yi mata wahala sai kawai ta baje a zaune tana kuka har da gunji. Mami na makewayi sai faman Uhm uhm take yi amma Lamiɗo bai saurare ta ba, bai ma nuna yaji ba. "Hamma ka yi.." "Will you keep your mouth shut." Lamiɗo ya faɗa cikin murya mai amo da ta yi sanadiyar shigowar su Ammah ɗakin cikin mamaki, kafin ka ji muryan Lamiɗo a sama ahaka ana daɗewa sai in ranshi ya ɓaci ganin Ummu durkushe tana kuka ya ba su amsar tambayar su. "Ai gwara kai ma ka yi mata faɗa yarinya kamar wacce ba ta yi makaranta ba? Har gobe in na tuna da abin da ta yi sai na ji kamar na mutu saboda bakin ciki. Baffa da Mami sun yi tsaye sun hana a yi mata faɗa." Hamma Abdulrrahaman ya faɗa cikin jin haushi, shi ya ji daɗi domin har gobe bai huce ba tunda ba a bari ya yi mata duka ba. "Me ya sa kike kuka? Ya cigaba da mgana cikin kaushin muryasa. "Me ya sa lokacin da za ki aikata ba ki tuna da komai ba.? Ummu dai ta daina kuka ta haɗiye shi, tun tsawar da ya yi mata da farko. "Tunda ya ce ba ya sonki ya sake ki." "Dole ne." "Za ki yi pushing kanki in to a relatioship ɗin da ba ki da amfani ne a wajen ne? Are you Stupid? Ko ke ba ki da wata daraja matsayinki ta ƴ'a mace ne? Ya gama faɗa a jere yana haki cikin ɓacin rai. "Faɗa ma ta dai Lamiɗo " Ammah ta faɗa cikin bacin rai, ba ta ma son tuna abin saboda ɓacin ran da ta ke shiga "Ki sani kina da komai ba ki kuma rasa komai va saboda haka ki sani wannan abin da kika yi is a stupidity, kuma kar ki sake." Ya faɗa har yana ɗaga murya. "Domin in kika sake ba mgana zan tsaya ina yi dake ba. I will deal with you. " Ya faɗa yana ɗan jinjina kansa. Ummu kuka har da majina. "Ku yi haƙuri." Take faɗa, tana kuka Hamma Abdulrrahman ya cigaba da faɗa yana masifa. Daidai lokacin Mami ta fito daga tiolet, cikinta ne ya karta tun ɗazu take Allah Allah ta fito, saboda ta ga an yi ma Auta taron dangi. "A'a Lauya bari, shi ya yi na shi ya gama kai kuma sai ka ɗora naka! Wallahi ku fita daga idanuwana na rufe." Mami ta fada tana isa gaban Ummu ta duka tana fadin" is ok ya isa yi shurun ki" Hawaye take share mata da hannayenta. "Fatima ki bari a yi mata faɗa don Allah." Ammah ta faɗa da ya sa Mami ta tashi a fusace tana fadin" To duk ba an yi mata ba, kuma ta yi nadama don Allah ku ko kukan da take yi bai ba ku tausayi ba? "Wani tausayi? Mu ma ai haka ta ɗaga mana hankali." "To ta ji, ku fita kawai." Mami ta katse Hamma Abdulrraahman tana nuna musu hanyar fita, Lamiɗo ya juya zai fita Mami ta jawo hannunshi tana fadin" Kai ne ka fara ko? Kai ba ka san na saka dokar kar wanda ya yi ma Auta mgana ba? Kalli yadda ka sanya ta kuka juna biyu gare ta ba fa" Mamaki ya kama shi sai kawai ya tsaya yana kallon Mami bai yi magana ba. "Ammah ja zugan yayanki ku je falo. Ganin su ma firgita mini yarinya yake yi " Ta faɗa tana sakin hannun Lamido ta juya ga Ummu. Ya daɗe yana kallon hannun shi da ta rike, kafin ya juya ya bar ɗakin. Ammah ta ce su fita kawai. "Ke ma dai Fatima ki zama mai gaskiya " "Gaskiyan kenan Ammah." Ta faɗa bayan sun fice. Nan suka bar Mami da zaman lallashi, Ummu ta yi ta kuka tana ce ma Mami ta yi nadama ba za ta kara ba.. Haka Mami ta yi ta masifa, da  hamma Abdulrahaman shi dai Lamiɗo ya gudu Hamma Abdullahi ya tafi kai shi filin jirgi. "Wai ina ganin Basamuden ɗan Ammah da ba ya magana, shi ne zai zo ya tasa ya'ta yana yi mata faɗa, wallahi da ina kusa bai isa ba." "Kar ku manta dai ya ba ta jininsa, ba domin shi ba da yanzu kina zaman makoki.," Ammah ta faɗa tana dariya. "To sai me! Ai don Allah ya yi kuma ba a saka shi ba, da sai ya bari a saka mata na siya " Ammah na ta dariyan Mamin ganin ta da karfin hali. "Shima ɗana taimako ya yi, kuma fadan da ya yi mata na ta so kanta ne." "To ina ruwan shi? Sai da ta warke ne zai  zo da wani tsawonsa kamar falla waya yana yi ma mutane faɗa " Mami ta sake faɗa cikin kufululewa. Ammah ta yi wucewarta ɗakin Baffa domin ta gyara tana ce ma Mami. "Ku kuka sani dai Fatima." Mami ita kaɗai ma faɗanta ta dinga yi. Hamma Abdulrrahaman ya sulale ya gudu shima Abdullahi daga filin jirgi bai dawo gidan ba. Faɗan da Mami ta yi ranar har dare, sai da Ummun ta koma ba ta hakuri. "Gwara na tattaraki mu tafi can su daina ganinki, tunda Ammah ta daure musu kugu, Baffa kuma ba zaman gidan yake yi ba, balle ya tsaya miki " Haka da Baffa ya dawo ta tare shi da cewa Ammah ta yi gayyar yayanta sun saka Auta kuka. "Baffa har da wannan ɗan nata kamar basamude, shi ya fara zuwa ya yi mata kerere a gaba yana ta masifa, ashe karyan miskilanci yake yi tunda yana faɗa, Ammah na gefe da sauran yayanta suna cewa ya yi daidai." "Ba su kyauta ba " Baffa ya faɗa yana danne dariyansa. "Ammah ce fa ba ta tsawarta musu ba." "Ammah ma ba ta kyauta ba." Ya sake faɗa yana dariya. Ammah ta shigo ɗakin kawo ma Baffa abinci ta ce" An zo an kawo ƙarana kenan? "E wai har da basamuden danki kika kira ya zo ya yi ma Auta faɗa." Ammah ta kwashe da dariya Baffa na ta yata. "Allah ya shirye ki Fatima." Ammah ta faɗa tana ficewa daga dakin. "Gwara ki dauki yarki ku koma Kaduna sai kun shekara ba su ganta ba, ina ce va shike nan ba, sai na ga wanda ya'yan Ammah za su yi ma faɗan" "Ai Baffa ka bar su da ni, boko ce suke gwada mana, nima yar bokon ce sai dai mu buga ta." Baffa na dariya sosai ya ce" A gaida Fatima Baba, Fatin Gwaggo. Yau da ma suna raye su ga yadda Ubangiji ya mayar da Fatin su." Sai kuma suka koma tuna rayuwarsu ta baya tare da yi ma iyayensu addu'a daga karshe ma tare suke cin abincin Ammah ta sake dawowa ganin suna cin abinci ya sa ta rike baki tana fadin" Fatima kin zo kin ƙwace mini Baffa, miye nufin ki? "Jibi za mu bar muku gidan." "Umma ta gaida Aisha." Baffa dariya kawai ya yi yana girgiza kansa. Ammah itama zama ta yi suna cin abincin su uku daga faranti ɗaya, in ya kalle su sai ya tuna a shekarun baya shikenan raba faɗa a tsakanin Mami da Ammah, amma shaƙuwa ce mai tsanani a tsakaninsu, wacce ma alƙalami ba zai iya rubutawa ba. *1k on Telegram 09069067488. *Janafty* *FARGAR JAJI.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:JamilaUmarJanafty* "To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude" https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC *21* Washegari asabar Alhaji isa ya iso Jimeta tare da Islam da Faruk. Mami da kanta tare da Hamma Abdullahi suka je filin jirgi suka ɗauko su zuwa gida. A shashen mazan gidan daman ya kan sauka in ya zo duk da in kwana ya kama shi hotel yake tafiya yau ɗin ma a bangaren su Hamma Saddam Mami ta sauke shi sai bayan ya ci abinci ya natsa sannan ya shigo cikin gida suka gaisa shi da Amma, Baffa ba ya nan ya je cikin garin Jalingo sai can yamma ya dawo tare suka yi sallar mangariba da Alhaji isa har isha'in ma daman abokan kasuwanci ne tun a baya sannan megida ne da yaronsa. Yanzu kuma har da surukanta da ya haɗa su dalilin auran Mami, duk da hakan zumumcin da ya haɗa su bai yanke ba yau ɗin ma bayan sun dawo daga masallaci a tsakar gida Ammah ta yi musu shimfiɗa ta kuma haɗe musu abinci waje ɗaya suka zauna suna ci suna hira, irin ta su ta masu kasuwancin ƙarafa da siya da siyarwan motoci daga jin yadda suke magana a tsakaninsu za ka fahimci akwai kyakyawam alaqa a tsakanin su. Mami kuma da Ammah suna falo suna kallo tare da Faruk jefi-jefi suna taɓa hira a tsakanin su, Ummu kuma tana cikin ɗakin ta tare da Islam sarkin surutu tunda suka iso tana makale da ita tana yi mata zence, ta sha labarai kala-kala har sai da ta gaji, tamboyoyi har ta gaji da amsa mata su. Tun a can Kaduna Babansu ya sanar da su Ya Ummu za ta koma gidan su da zama to fa suna sauka ɗakinta ta fara zuwa tambayanta na farko shi ne. "Ya Ummu wai da gaske gidanmu za ki koma da zama? Ummu Salma na mirmishi ta ce. "In sha Allahu Islam." Nan fa ta fara murna da tsalle, Islam yarinya ce mai shiga rai, tana da son mutane da mgana kamar Mami yar kimanin shekara sha biyu 12, Faruk kuma ɗan shekaru bakwai ne 8, shi bai da surutu sai dai rigima ce da shi sosai kamar yaron goye. To duk bayan mintina sai ta zagayo ta ce"Ya Ummu da gaske za ki bi mu gidanmu? In ta amsa mata da E bai hana anjuma ta sake dawowa da irin wannan tambayan har sai da ta gaji da amsa mata. Mami ma cewa ta yi ta kore ta daga ɗakin ta ce a ƙyaleta, ganin ta da surutunta na sanyata nishaɗi, kuma ta tabbata ko can ta je islam da Faruk ba za su barta ta yi kewa ba, domin samun yara a gida yana haskaka gida tare da samar da walwala ga mazauna gidan gabaɗaya. A can tsakar gida kuwa bayan su Baffa sun gama cin abinci sun wanke hannuwansu a roban wanke hannun da Ammah ta ajiye musu, suka ɗan shiga hiran yadda kasuwancin siyar da tsoffin karafan motoci ya yi kasa yanzu ba kamar a baya ba, Baffa na mganar kasuwancin motocin da sabbin ƙarafan ma sun fi tafiya a yanzu shi kuma Alhaji Isa na sake kora masa jawaban, tun da shi dila ne kamfani guda gare shi na siyar da motoci wani lokacim ma su Baffa kan siya motoci a wajen su in hakan ta kama. A cikin hiran ne Baffa ya kalli Alhaji isa cikin nisawa kafin ya ce" Alhaji ina son mgana da kai, duk da na san kun gama mgana da Fatima amma amatsayina na wakilin Fatima, uban Ummu Salma ya kamata na yi magana da kai." "Ina jin ka ina fatan ba kan maganar zaman Ummu a wajen mu ba ne ko Baffa? Tunda shima Baffa yake kiran shi tun ma kafin aure su da Fatima, abokan kasuwancin Baffa duk da wannan sunan suke kiran shi. "Akan maganar ne." Baffa ya amsa masa cikin ɗan sanyin magana. "Haba Baffa, ai ina ce mun wuce haka a tsakaninmu. Ko ban auri Fatima ba ni mai riƙe Ummu Salma ne, ballantana ina auren Fatima. Ba ka da sauran haufi ko tsoro. Ummu Salma za ta samu sauyin rayuwa tare damu na ba ka tabbacin yadda zan yi ma Islam da Faruku haka zan yi ma Ummu Salma. Sannan haka itama Fatima saboda haka ka kwantar da hankalinka ba abinda zai sake faruwa da yardan Allah." Yana mgana Baffa na ta gyaɗa kansa cikin gamsuwa. Yana direwa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. "Na gode sosai, Ubangiji ya yi ma arziƙin ka albarka. Da man tsoro na ke ji, kar Auta ta sake tunanin kashe kanta a karo na biyu" "Hakan ba zai sake faruwa ba in sha Allahu." Alhaji Isa ya sake ba shi tabbacin sa. "Allah ya sa haka. Ubangiji ya sa tafiyarta ya zama mabuɗin alherin rayuwarta." Suka amsa da Amin a tare, tare da su Ammah daga cikin ɗaki domin sun rage ƙaran talabijin ɗin Faruk ne ma ya matsa sai da aka mayar masa da tashar carttoon, shi ya sa hankulansu ya ɗan karkata kan mganganun Baffa da Alhaji Isa. Wajen goman na dare Alhaji Isa ya tafi makwanci ya kwanta daman jirginsu karfe sha ɗaya na safe zai ta shi zuwa Kaduna. Shi ya sa sai wajen goma ya zo gidan abin karyawa ma tun a waya ya ce ma Mami kar ta wahalar da kanta, ya riga da ya yi breakfast a hotel ɗin da ya kwana. Ko da ya zo gida cike da yan sallama. Ummin ikki da Baɗɗo, tare da matan su Hamma Abdullahi da yayan su, Hamma Abdullahin ma yana nan tunda shi zai kai su filin jirgi, Hamma Abdulrrahaman ne matarsa ta ce ya yi sammakon fita yana da wata sharia da yake jagoranta. Ko da garin Allah ya waye daman Ummu Salma ta ji kamar ta buɗe idanuwanta ta ga ta yi nesa da garin Jimeta gabaɗaaya garin ya fita da ga zuciyanta a baya ba ta taɓa tunanin wata kaddara za ta iya raba ta da mahaifarta ba sai ga shi kaddaran Habibu ta sa za ta yi nesa da iyayenta da duka yan'uwanta domin tsira da salamar zuciyarta, ta tsani garin Jimeta da duk wani farincikin da ta samu a cikin ta dalilin Habib.. Sai ga shi suna sallama da Baɗɗo tana hawaye itama tana hawaye. "Zan yi kewar ki Sisna. In sha Allahu in muka samu hutu zan dinga zuwa ina ganin ki." Baɗɗo ta faɗa tana sharan ƙwallah. "Na gode Aisha. Ba zan taɓa mantawa da alherinki ga zumuncin mu ba, nima Allah ya ba ni iko da tsawon rayuwa domin na samu damar saka miki." Ummu Salma ta faɗa cikin kuka sannan suka sake rumgume juna. Dakyar suka saki juna, Ummin ikki ma ta rike hannuwanta tana fadin" Ki je can ki sake sabuwar rayuwa. Kar ki dawo mini sai da sabon suruki kin ji ko Ummu? Ta faɗa cikin mirmishi a zuciyan Ummu Salma faɗi take yi wa zai sake sona a haka Ummin ikki? Amma a fili mirmishi ta yi lokaci ɗaya tana gyaɗa kanta cikin fitan hawaye. Ammah ce kawai ba ta yi kuka ba, ita da ba a ganin raunin ta. "Ammah zan tafi, ki yafe mini." Ummu ta faɗa bayan ta duka a gaban Ammah tana zubar ƙwalla." "Ba ki yi mini komai ba, ki je na yafe miki duka laifukan ki da wanda na sani da wanda ban sani ba.  Ina so ki tuna da cewa rabuwa da Habibu ba shi ne ƙarewar rayuwarki ba Auta, ki sani Allah na tare dake in kika mika masa lamuran ki, shi zai kawo miki agaji, don Allah ki cire komai a zuciyarki ki yi rayuwarki cikin farimciki." "Zan yi haka Ammah." Ta sake faɗa tana ta kuka kamar ranta zai fita. Baffa ne ya ɗagota yana share mata hawaye. "Bar kuka Auta, can ma Kaduna ai duk gida ne, kuma duk lokacin da kika ji kina son dawowa ai za ki dawo gida kin ji ko? Sai ta gyaɗa masa kanta tana mai sake zubar da ƙwallah. "Baffa ka yafe mini." "Ban taɓa rike ki ba Auta. Ki tuna da Ubangiji a dukkan sakannin numfashinki, shi kuma ba zai barki ba, in sha Allahu." Kanta ta gyaɗa tana sake sakin kuka har da jan majina. "Allah ya tsare ku, ki yi ma Fatima Biyayya, ki riƙe Alhaji a matsayin Uba a gareki, domin yanzu alhakin komai na rayuwarki yana hannunsa ne." "To Baffa.' Ta faɗa tana sharan ƙwallah "Fatima kama hannun ɗiyarki ku je. Allah ya sada mu da alherinsa." Baffa ya faɗa idanuwansa na kawo ƙwalla sai ya bar ɗakin bayan ya danƙama Mami Hannun Ummun Salma, Ammah kuma ba ta ga tafiyar su ba ɗaki ta shige tana sharan ƙwalla a zuciyanta tana yi ma Ummu Salma fatan samun kwanciyar hankali da salama a in da zama zai sake cilla ta. Masu rako har ƙofar gida akwatina biyu na kaya Ummu ta tafi da su sai kayan haihuwa sauran Mami ta ce ta bar su in suka isa can za a siya mata wasu. Har da Baɗɗo aka tafi filin jirgi rako. Karfe sha ɗaya daidai jirginsu ya ɗaga zuwa garin Kaduna. A first class suka zauna hatta da Faruƙu da Islam da kujerunsu, Mami da Alhaji suna waje ɗaya tare da Faruƙu ita kuma Ummu Salma a bangaren window, Islam na gefenta yaran nan ko a jikinsu daga gani sun saba shiga jirgi, ita ko da ba ta saba ba sai da cikinta ya karta sau ɗaya ta taɓa shiga jirgi lokacin da suka je Daura naɗin Sarautan Hamma Lamiɗo shi ya turo musu kuɗin jirgi ita da Ammah suka tafi shi ne na farko sai wannan na biyu Lokacin da ta fara ganin gajimare, jirgin ya daidaita a sama ya fara tafiya. Hawaye suka sake kece mata, tana jin shuuuu alamun jirgi na tafiya sai take jin komai na rayuwarta kamar yana gogewa, tabbas haɗuwarta da Habibu a baya tana kallon shi a wani nasara ne amma a yanzu tana cikin fargan jajin shigowarsaa rayuwanta. Saboda shi ya sa ta tsani duk wani ɗa namiji, tana ganin duk halinsu ɗaya saboda Shamsiya ya sa ta ƙara tsorata da lamuran mutane da ƙawaye, sun yi dalilin da ta gudu ta bar in da aka haifeta sun yi sanadiyar haifar mata da ciwon da har abada ba zai taɓa warkewa daga zuciyanta ba. Amma ta yi ma kanta alƙawarin manta da duka rayuwanta a garin Jimeta. Za ta koma Kaduna a wata sabuwar Hallita. Za ta manta da Habibu da duk abin da ya dangance shi cikin jikinta kuma za ta haife shi, tana son shi amma baƙin cikinta ɗaya in ta tuna akwai jinin Habibu a jikin abin da ke cikinta. Ba ta fatan wata danganta ta sake shiga tsakaninta da Habibu, ba ta ƙaunar sake ganinsa a rayuwanta shi ya sa ta kudirta a ranta cewa za ta yi nesa da rayuwar Habibu da duniyarsa yadda ba zai taɓa cin mata ba har abada. Cikin daman ya ce ya bar mata to babu sauran wani abu da ya rage a tsakaninsu Tana hawaye wasu na korar wasu, amma tana ji kamar komai na ta na sauyawa. Tabbas dole ne ta manta komai in dai har tana so ta sake cigaba da rayuwa a matsayin Ummu Salma Hadi Baba Tana kallon gajimare da gizai-gizai tana kuka tana jin ta bar Jimeta har abada sai da ta zo da ziyara amma garin ya bar mata wani wawaken taɓon da ba zai taɓa cikewa ba har gaban abada. Wataƙila tafiyar Ummu na ɗan lokaci ne, amma Jimeta za ta sake maraba da ita a lokacin da ta yanke dukkan tsammani da samun rayuwa mai inganci. *** *ANGUWAN DOUGIREI* JIMETA. 9:50pm A kayattacen sabon gidan Habib shi ne zaune a saman kujera mai zaman mutum ɗaya kan jikin shi kuma Shamsiya ce a lafe marabanta da tsirara kaɗan ne saboda yanayin ƙaramar rigar dake jikinta da ba ta iya ɓoye sirrukan jikinta ba. shima ɗin ba shi da riga daga shi sai ƙaramin wando amma falon akwai duhu da yake dare ya ɗan fara shiga. Ba kuma don ba wuta ba ne ya sa falon ya yi duhu ba, masu gidan ne suka rage hasken falon suka bar na talabijin ɗin da suke kallo wanda ke ɗan haskaka falon kaɗan-kaɗan. Hira suke ƙasa-ƙasa ba tare da sun yi wani motsi ba ballatana aji abin da suke furta ma juna, talabijin ɗin ma shi yake ta ɓaɓatu shi kaɗai akan tashar MBC2, su hankulansu na kan junan su lokaci bayan lokaci kuma suna sumbatar bakunan junansu cike da soyayya tare da muradi mai girma. "Sweety ina son ka, kai ne rayuwata." Shamsiya ta faɗa cikin irin amo a muryanta. Kanta na saman kirjinsa yana shafa suman kanta dake tsefe har zuwa ƙasan wuyanta zuwa ƙirjinta tunda rigan mai budaɗɗen wuya ne. "Nima ina son ki Sweety,da ban same ki ba da na zama mai asara." Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai ɗago fuskarta ya sumbaci bakinta itama sai ta ba shi dama suka rike kan juna suna masu sumbatar juna kamar za su cinye bakin juna lokaci ɗaya hannayensu na kara kaina a kan jikunna junansu cikin soyayya da muradi mai girma. Sun daɗe cikin wannan yanayin kafin su saki bakin juna su koma su sake curewa waje ɗaya suna masu sauke ajiyar zuciya a jejjere, Habib ya sake matse Shamsiya dake kan jikinsa kamar ya mayar da ita cikinsa haka yake ji, bai san haka yake son ta ba sai da ya mallaketa bai san bai taɓa son Ummu Salma ba sai da ya auri Shamsiya daga lokacin ya fara ganin tarin bambamcin dake tsakanin su. Shamsiya sonta yake yi da dukkan zuciyarsa zai iya zama da ita na har abada in dai tana tare da shi ba tare da ya takura mata ba. A farkon auren shi da Ummu Salma shi kan shi ya ɗauka yana daga cikin harijan maza ma su yawan buƙata domin yadda yake hakarta kamar Allah ya aikosa sai da ya auri Shamsiya ya ƙaryata haka, yau kimanin sati uku da auran su amma komai na rayuwarsa ya sauya. In dai zai ganta ga ta gashi ko ba za su yi wani abu ba farinciki ya ishe shi, sonta ne ke masa nauyi a zuciyarsa ba sha'awanta ba shi ya sa ko bayan faman da ya yi kafin ya mayar da ita cikakkiyar mace bai wuce sau uku zuwa huɗu suka marabanci juna ba tsausayinta yake ji ba ya so ya ba ta wahala, ita kaɗai ne ya ke jin daɗin yin wasanni da ita aamm a lokacin Ummu Salma wannan ba ya yi masa shi dai kawai sha'awanta ne ke azalzalansa so kawai ya ke yi ya marabance ta domin kauda wannan kaifin sha'awan a zuciyarsa wani abu kamar asiri in yanzu zai gama to yana sake kallonta zai ji yana son ƙari, har yanzu in ya kwanta barci ko in ya kaɗaice tana yawan faɗowa tunaninsa ko da ya saketa ba wai wannan ƙishiruwan sha'awan nata da yake ji ya gushe daga zuciyarsa da gangan jikinsa ba ne, kawai ya rabu da ita ne saboda lokaci ya yi amma karya yake yi har gobe akwai sauran abin mamora a jikin Ummu Salma. "Sweety' Kamar daga sama ya ji Shamsiya na kira sunan shi ya faɗa dogon tunani sannan ne fa ya yi saurin dawowa cikin hayyacinsa. "Naam Sweety me ya faru? Ya faɗa yana mai kallon fuskarta ta cikin duhun ɗakin. Baki ta tura masa kafin ta ce" Gani a tare dakai tunanin me za ka yi kuma? Sumbatar bakinta ya yi yana yi mata mirmishi kafin ya ce" Ai ke ce tunanina kuma ga ki a tare da ni Sweety na" Itama sai ta sake sumbatar bakin shi tana yi masa wani irin kallo. "I love you mai tsada na." "Love you too madara ta." Ya mayar mata da martaninta yana mai shafa bayanta zuwa ƙugunta. "Ko tunanin tsohuwar matarka kake yi ne? Ta faɗa tana masa dariya. Fuska ya haɗa kafin ya ce" Kin fara ko? Ɗan gemunsa ta ja kafin ta ce" Ai kun yi zaman aure ba laifi ba ne in ka tuna good memories ɗin ku tare da juna." Hannunta ya ture daga fuskarsa. Sannan ya kalleta yana faɗin" In ina tare dake ina mantawa da kaina ne Sweety,  ki sani ko da tana nan ke ce tunanina bayan ba ta ma ke ce tunanina, ni na ma manta da ita ko tana ma wani hali oho." Ya faɗa cikin alhini da amon tausayi. Shamsiya ta kwashe da dariya har tana sarƙewa sai da ya riƙa bubbuga bayanta yana yi mata sannu. "Kin gani ko? Ki yi a hankali kin ji ko? Yake faɗa yana ɗan shafa bayanta har da ma kirjinta. Amma duk da haka ba ta daina dariyan da ta fara ba. "Me ya saka ki dariya! Ya tambaya shima yana ɗan taya ta dariyan kaɗan. "Ummu Salma na tuna, baiwar Allah har gobe tana tsananin son ka." Sai ta sake kecewa da dariya. Shima dariyan ya ɗan saki kafin ya ce" To ai yanzu dolenta za ta cire ni a zuciyanta domin ta fahimci ba a hallice ni don ita ba, an hallice ni don ke ce kawai. Ke kaɗai ba ki da abokiyar tarayya." Ya gama faɗa yana sumbatar saman sumar kanta. "Abin da ke bani dariya in na tuna, ta zo gidammu ana jibi bikin mu ta ga hotunan auran mu amma wai ta kasa gasgata gaskiya ne, ta yarda da ni ta aminta da soyayyar da take yi maka a wautar ta tana tunanin wata rana za ka dawo gare ta? Ka daɗe kana ce mini yarinyar nan ba ta da tunani ban taɓa yarda ba sai ranar." Ta gama faɗa tana sake kwashewa da wata dariyan daga gani tana cikin nishaɗi da labarin da take bayarwa. Nan fa ta cigaba da faɗin maganganu marasa daɗi a kan Ummu Salma labarin zuwanta gidansu da duk abin da ya kwana kullum sai ta tuna ta yi dariya kamar ya zama abun tunawarta ta yi nishaɗi. "Wawancin iyayenta na gani, suka barta da cikin jikinta alhalin wanda ya yi cikin ya ce ba ya so, to mene ne amfanin haihuwar da za ta yi? Ta faɗa tana kallon shi, sai ya ɗan juya mata ido alamun bai sani ba. "Ni dai har abada ba za ka kawo mini jinin da ba nawa a gidana ba, ba mu yi wannan alƙawarin ba." "Ba ma zan kawo ba? Me zan yi da abin da ta haifa! Ke da za ki yi ta haifa mana yara? Ya gama faɗa yana ɗan jan hancinta mirmishi ta sakar masa har tana sumbatar gefen kumatunsa. "Da gaske na ke yi na bar ma Ummu Salma da iyayenta wannan cikin har abada ba ni da alaqa da shi" Ta jinjina kai cikin farinciki. "Wayyo ta ba ni tausayi, " Ta sake faɗa tana sake saka dariya. "Lokacin har wani ɗaga kafaɗa take yi. Bestie Allah kuma ya ba ku miji wanda ya fi Noori na ma komai da komai." Ta gama faɗa tana kwaikwayon muryan Ummu Salma daga shi har ita sai da suka sake tsintsirewa da dariya. "Ko haihu ta yanzu? Domin ganina da ita na karshe na ga cikin ya yi kasa. Ko da yake ina ruwanmu ko Sweety? Ta tambaya tana kallon shi. "To ai ke ce ke ɗauko maganarta. Ni tuni na gama da babinta." "Labarinta na sanya ni nishaɗi ne." Ta sake faɗa tana dariya. "Na san zuwa yanzu kowa ya san na aure ka, na san na sha tsinuwa wajen yan'uwanta barin ma uwarta din nan bafullatanar banza, da wannan yayanta na ta lauya masifaffe da shegiyar ƙawar nan nata Baɗdo ba ta da mutumci, ka ga saƙon cin mutumcin da ta turamini ranar biki! Wai duk abin da ya samu Yar uwanta ni da kai Ubangiji ba zai ƙyale mu ba to ina ruwan mu? Daman ai aro na ba ta kai kuma na zo na karɓi kaya na sai aka ga laifina Sweety? "Bai kamata a ga laifnki ba, ai su ba su nan abin da ya faru ba ne." Ya faɗa cikin sanyin murya. "Ko da Ummu Salma ta riga ni haɗuwa da kai. Amma ai ni ka zaɓa sama da ita ko? Ta sake tambayan shi tana ɗan kallom shi. "Tabbas." Ya faɗa abin da ya faru a lokacin yana dawowa masa. "Wallahi tun a ganin farkon da na fara yi maka kishi da hassada suka kume ni, a raina ina faɗin me ya sa sai Ummu ce za ta fara haɗuwa dakai? Ranar na koma gida da baƙinciki ina ganin kai ne irin namijin da nake burin aure ban taɓa tunanin za ka kawo kanka gare ni ba wallahi tallahi da ka makara ba ka zo ba, ni da kaina zan neme ka na yi maka tallar kaina sannan na sanar dakai na fi Ummu Salma bukatar ka a rayuwata." Ta gama faɗa cikin wani yanayi kamar ta yi kuka. "Sweety wallahi ina sonka." Sake rumgumeta ya yi a jikinsa yana faɗin" Na sani, nima ai kinsan ina son ki! In kika yi duba da tsawon lokacin soyayyarmu da yadda na cika alƙawarin kema za ki san bayan ke ba na son kowa a duniyar nan a matsayin matar auran da zan zauna da ita. Na fuskancin komai saboda na mallake ki " Ta sake ƙamƙame shi tana faɗin" Na sani Sweety na sani wallahi." Sumbatar sumar kanta ya yi kafin ya ce" Ki bar tuna duk abin da ya wuce, rayuwarmu ce yanzu kawai a gabanmu Sweety, mu zauna mu gina sabuwar rayuwa wacce za ta yaɗu zuwa nan da wani lokaci kaɗan. Can wait na ga ranar da za ki haifa mini ɗa ko ƴa daga mahaifarki." Ya faɗa yana kai hannunsa ƙasan maranta ita kuma sai ta noƙe wai tana jin kunya. "Ke ce na zaɓa ki zama uwa ga ƴa'ƴana. Kuma ba zan sauya miki ba." Gabaɗaya ya gama kashe mata zuciya da kalamansa. Sai ta sake narke masa cikin shagwaɓa shi kuma yana biye mata sun daɗe a haka domin da ya ce su je ɗaki su kwanta sai taƙi karshenta a saman jikinsa ta yi barci ta bar shi da sake shuga tunani mai zurfi. Tabbas a ganin farko da ya yi ma Ummu Salma ya ji yana son ta amma lokacin da ya haɗa idanuwansa da na Shamsiya sai ya fahimci ashe ba so ya ke yi ma Ummu ba sha'awanta yake yi, in yana tare da ita burinsa kawai  jikinta ne a gabansa amma in yana tare da Shamsiya burinsa kawai ya dauwama tare da ita ko da ba za ta amfanesa da komai ba, tun bai fahimci karatun ba har dai ya fahimta ba shi da mafita illa ba ma zuciyansa abinda take so sai kuma aka yi saa itama shi take so, kawai sai suka jone suka kuma tsara komai. A lokacin a gida ba za a aurar da Shamsiya ba sannan shi kuma yana son auran Ummu Salma saboda ya cire wannan kwaɗayim nata a zuciyarsa shi ya sa ya yi ma Shamsiya alƙawarin zai yi auren shekara ɗaya ya sake ta sannan ya zo su yi aure daga baya ta aminta amma babu sharaɗin haihuwa, kaddara ce ta gifta har wannan cikin ya zama rai a cikin Ummu Salma amma ba shirin su ba ne, bai samu matsala a bangaren iyayen Shamsiya ba saboda dangin mahaifiyarta sun tankwasa mahaifinta, kuma gidan yan boko ne ba wani damuwa aka yi da dogon bincike ba tunda aka fahimci shima yana da iliminsa da aikinsa sannan ko da aka ce ya saki matarsa ta farko ba wanda ya yi bincike mai tsanani akan haka, kuma a cikin ahalin Shamsiya ba wanda ya san shi a matsayin mijin kawarta, shi kawai a san shi ne a matsayin mijinta na yanzu. Ya so ya samu matsala da Alhaji Sheriff shi ne ya ce ba zai sake zuwa ya nema masa aure ba, amma Baba Usman da su Gwaggo duk ya siye su da kyauttuka tuni suka manta da komai, shi ma dai Alhaji Sheriff ɗin da magiyan Habib ɗin da Baba Usman da Gwaggo ya amince ya je ya nema masa auran Shamsiya har aka ba shi amma da sharaɗin in wani abu ya biyo baya kar ya saka shi a ciki. Shi kuma ya amince a tunaninsa me zai biyo baya? Masoyiyarsa fa ya aura, yana tunanin dukkan wani buri na shi zai cika, ya gama samun farinciki bayan ya watsa farimcikin wata,bai san cewa watakila farincikin na shi na lokaci kaɗan ba ne, ƙila nan gaba kaɗan Fargar jaji zai kama shi ya fara nadaman abin da ya aikata nadama mara amfani alhalin kuma lokaci ya sare masa. **** *NDC QUATERS KADUNA NAGERIA.* *BAYAN SHEKARU BIYU.* "A Yau na koya mana yadda za mu sarrafa shinkafar mu zuwa chinese rice, za ki yin ta da kowani shinkafa amma ta kasance mai kyau ce saboda gudun caɓewa. Uwargida da Amarya har da ma ƴan'mata tare da zawarawa duk a yi pratical ma'ana gwaji domin da gwaji ne ake ƙwarewa ni ce dai taku ɗin nan HANAN DELICIOUS sai mun sake haɗuwa daku a wani sabon video na gode kar ku manta ku yi like in yau kika fara kallon videos ɗina to kar ki manta ki bibiya duka shafukana a Facebook Hanan B Jimeta a Youtube channel ɗina za ku kama ni a Hanan Delicious, in kuma a instergram ne za ku iya kama ni a Hanan B Jimeta, in kuma a Tiktok ne za ku iya kama ni a Hanan Delicious domin samun kayattacen videos ɗina akan girke girke masu  kayatarwa tare da snacks na zamani domin jin daɗin ku. " "Mahmah..." "Mahmah.." Ta ji ana kiranta daga falo, ta kuma san yanzu za ta shigo kitchen ɗin in kuma ta shigo za ta ɓata mata Video ya sa da sauri ta ce. "Bissallam. Sai mun sake haɗuwa. Bye." sannan da sauri ta matsa wajen ringligt ɗin da ta ɗaura a wayarta ƙiran iphone 15 ta  yi saving ɗin Video ɗin dai dai lokacin da ƙaramar yarinyar ta ƙariso cikin kitchen ɗin. "Mahmah." Aka sake faɗa cikin murya irin ta yara masu shagwaɓa. Da sauri ta baro in da take tsaye sanye da abaya baƙa ta yi rolling ɗin mayafin J.c mai ruwan madara kyakyawan farar fuskarta da dogon hancinta ta yi kyau sosai. Sama ta ɗaga yarinya tana faɗin "Waye ya taɓa mini Hanan ɗina? Ta faɗa tana share mata idanuwanta ganin hawaye. Dakyar ta lallaɓata ta yi barci sannan ta zo ta fara Video ɗin nan, da ta kwana biyu ba ta ɗora komai a shafukanta ba  Hannan da man akwai rigima balle kuma ba ta da lafiya tana ɗan zazzabi ga zawon haƙori na can gefe da suke fitowa shi ya sa rigimanta ya ƙaru kuma rigiman saboda ta san sun kwanta tare kuma ta farka ba ta ganta a gefenta ba shine ta taso tana kuka. Sanye take da bulawus ta yara mai kyau, kanta kuma kitson kalaba ne an kama da band ga ta dai yarinya yar kimanin shekaru biyu amma tana da suma kai da gashi ga ta fara jajir da ita amma ko kusa ba ta kama da Ummu Salma, kamaninta da komai kamanin mahaifinta ta ɗauko, wanda kullum in Ummu ta kalleta sai ta ji baƙin ciki, ba ta so ta sake cin karo da mai irin fuskar wannan mutimin ba, amma sai ga shi tilon yar da ta haifa ta ɗauko kamaninsa "Mahma" Ta sake faɗa tana sake lafewa a jikin uwar ta ta,. "Gani nan kukan na mene ne? Ko yunwa kike ji ne? Sai ta gyaɗa kanta. "Tea Mahma." Ta ce tea za ta sha, nan da nan Ummu ta saɓa ta a baya tana faɗin" Hau bombu yanzu na haɗa miki tea ɗin ki sha." Nan da nan ko ta lafe a bayanta ita kuma da haka ta yi amfani ta saka ruwan zafi a wata butar a kitchen ɗin tunda suna da wuta su da sai su yi sati ba a ɗauke musu wuta ba koma an ɗauke akwai solar ba ka gane ma akwai wutar ko babu. Tana cikin tattara kayan video ɗin ta Basira ta shigo Kitchen ɗin. "Ya Ummu da kan ki kika goya wannan yar rigimar!" Ta faɗa tana dariya Ummu ta juya tana kallon Basira yar matashiya ce ko za ta girmeta bai wuce da shekaru biyu ba, itama kaddaran aure ne ya faɗa mata suka rabu da mijin watanni kaɗan da auran su, ita ce wacce Mami ta sake ɗaukowa daga can garin su Daddy ɗanmarke bayan sun mayar da Baraka an yi mata aure. "Ba ruwan ku a ciki Basira." Ummu ta faɗa tana sake zumkuɗa Hannan a bayanta. "Yi kwanciyarki Hanan kar ki biye ta Basira." Saboda suna yin ta Hanan kiyuwa da rigima Basira kuma faɗa ta yi ta janta tana saka ta kuka amma bai hana anjuma Hanan ɗin taje wajenta da zanin goyo tana faɗin bombu. Hanan na son goyo sosai ko domin da aka haifeta ta sha goyo ne? Lokacin Baraka nan nan ko da yaushe tana bayanta Mami ma in tana gida za ta goya ta haka ma Islam har Faruku rigima yake yi a lokacin sai an goya masa shima. "Ke sauko ki kyale Ya Ummu ta huta, ta ho nan ki hau nawa bayan da kika saba hawa.." Basira ta faɗa tana leka Hanan sai ko ta makale bayan uwarta tana kallon Basira. "Ba ki tahowa ko? Ta faɗa tana miƙa mata hannu kawai sai ta saka kuka tana kiran Mahmah, Ummu na dariya ta ce"Hanan ke da Basirun na ki." Haka Hanan ke kiranta su yi ta dariya ita da su Mami Basira tun tana masifan cewa ni da na reneki ki san sunan kowa daidai amma ni basiru kika mayar da ni har ta zo ta haƙura domin ya kama bakinta. "Ba ruwana in ta ce ba za ta sake goya ki ba." Ummu Salma ta faɗa tana dariya. Kamar kuma tana ji sai ta daina kuka ta kura ma Basiran ido tana kallonta sai ga shi da kanta ta miƙa mata hannu ita kuma ta kama tana faɗin" Yauwa Hannatuna." Tana dariya dariya yarinyar ta bar bayan uwar tata ta haye na bayan Basira tana zillo. "Basiruu." "Ke ni sunana Basira ba Basiru ba." "Basiru.." "Kai wannan yarinyar, to ke ma Habu ba hannatu ba." Ummu na gefe tana cin dariyanta. "Ku je falo Basira bari na haɗo mata tea ɗin." "To, na ji jikinta da ɗumi ya kamata ta sha maganinta na rana." "To ta sha tea ɗin sai na ɗauko mganin ki ba ta yar rigimar nan ai sai ke Basira." Ta fice tana dariya. Basirace ta taimake ta har ta samu ta haɗa mata tea ɗin bayan ta kawo mata ta bata ta sha, sannan wajen shan mgani sai da aka yi mata ɗure ba ta son magani tana ta kuka da rigima bayan nan Basira ta yi mata wanka ta sauya mata kaya sai barci bayan ta goyata ram a bayanta da zani. Mami ba ta nan ta shiga cikin makaranta gidan daga Ummu ne sai Basira Faruku na makaranta sai biyar da rabi zai dawo tunda nan Al'areeb yake yi a Kaduna yana primary 6, Islam dai ana bording  zaria can FGGC BASAWA tana jss2 yanzu sai an yi hutu take zuwa gida amma suna zuwa yi mata visiting zuwa ma biyu duk Ummu ke zuwa ita da Basira da Faruk Hamisu ke tuƙasu. Daddy kuma ba ya nan ya yi tafiya kasar Turkey ya fi sati acan. Sai a lokacin itama Ummu ta samu ta ɗan sake yin wanka ta sauya kaya wayarta ta ɗauka ta shiga shafukanta tana ganin video ɗin da ta yi ɗazu ta fara ɗora shi a kan Youtube sai kuma nan da nan ta yi sharing ɗin shi zuwa Handles ɗinta na sauran shafukan sada zumumta an yi mata comments amma duk akan godiya da yabawa ne sannan da masu cewa suna gane koyarwaanta don Allah ta buɗe musu online class mana, itama tana so ta buɗe amma ba yanzu ba sai ta sake tara yawan mabiya. Bayan ta gama duba shafukanta sai ta shiga kan whatsApp ɗin ta, tana duba saƙonni, ko wata biyu ba su yi da dawowa daga Jimeta ba tun bayan barin ta gida sai a lokacin ta sake komawa Jimeta shima ya kama dole ne Baɗɗo ce ta gama makaranta shi ne ta je mata graduation Mami ba ta samu zuwa ba daga ita sai Hanan suka tafi kwananta goma ta dawo Kaduna duk da ta yi kewar garin amma ba ta jin za ta sake zaman garin ya wuce na sati biyu ba, yanzu Ummu Salma yar kaduna ce ba yar Jimeta ba. Hamma Saddam ne ya yi mata sako tana dubawa ta ga ya ce" Ke nifa ina Lagos." Mamaki take yi sai yanzu ta san dalilin da ya sa Hamma Saddam ya zaɓi shiga Camp a garin Lagos. Ashe saboda ya je ya huta a gidan Hamma Lamiɗo ne. Hotuna ne ya turo mata sama da goma, har da wasu ma yana driving a wata mota mai kyau da tsada. "Ni fa har motar Hamma Lamiɗo nake hawa yanzu" Ta tuna mganarsu ta kwanaki da ta tambaye shi motar waye yake aro yana ta wayon gari ya ce tashi ce ashe wasa yake yi mata. Yanzu ma hotunan shi ne a bakin ruwa kala kala. "Ya mutanen gidan? Haka kawai ta rubuta masa saƙon ya maka biyu domin ta san yana online, Hamma Saddam da waya kamar 5 and 6 ne. Tun bayan barin ta Jimeta ba ta sake ganin Hamma Lamiɗo ba wataƙila Mami na haɗuwa da shi tunda ta je Jimeta sosai a wannan shekaran amma ita ba ta sake ganinsa ba kuma ba ta sake bibiyan labarin shi ba, ta dai san ya biya ma Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrrahaman tare da matansu sun je Umra tare da Ummin ikki da babansu Baɗɗo, a shekaran da ta dawo Kaduna itama Daddy ya biya musu sun je gabaɗaya acan suka haɗe a masauƙi ɗaya ma suka sauka ta kan ji ana hiran ya yi kaza ya yi kyauta kaza amma ita dai tunda bai taɓa yi mata ba, ba ta taɓa damuwa da shi ba. Hamma Abdulrahim ne ta ga ya saka hoton shi cikin likitoci turawa kamar yana can ƙasar waje alhalin yana Abuja yana Housemanship ɗin shi a asibitin NIZAMIYE HOSPITAL ABUJA. Bayan ya dawo ya yi jarabawa ta Medical and Dentel council of Nigeria. (MDCN) Sau ɗaya ya yi kuma ya samu nasara. Abdulrahim kamar wani bature daman ga shi jajir da shi ɗabi'unsa ma da komai na shi ya koma na turawa, hausa ma tana neman ɓace masa magana kaɗan turanci fillanci ko har ya fara mantawa shi da ya shafe sama da shekara bakwai a kasar Singpore. Da ya dawo Ammah ta yi ta masifa, in suna hira ya dinga yi mata turanci. "Buraubaka, tir da wannan kasar turawan tunda ya sa ka manta da al'adanka ka kwaso mana daɓi'an turawa." Lokacin da ya zo Kaduna ne ya ke ta ba ma Ummu labari tana cin dariya. Har waliman dawowarsa an yi amma Ummu ba ta je ba Har Mami taje shi ne bayan ya natsa ya huta ya zo ya ganta kwana biyu ya yi suka sha hira suka fita yawo cikin gari kafin tafiyarsa. Tun da yanzu Ummu har driving ta koya kuma ta iya, tana tuƙa motar Mami wani lokacin. Ummu Salma ba ta taɓa tunanin da gaske rayuwarta za ta sauya ba sai ga shi Ubangiji ya sauya mata rayuwa, rayuwar da ba ta yi hasashe ba, lokacin da suka zo Kaduna ga shi dai gidane amma ta yi ta baƙunta da rashin Sabo ba abin da za ce da Mami da Daddy sai godiya domin sune tsanin da rayuwarta take kai a yanzu. Sun kula da ita da lafiyanta da ita da abinda ke cikinta, da karfi da yaji suka yakice damuwa da tunani a zuciyanta. Kwanan ta arba'in a Kaduna ta haihu a asibitin kuɗi na Garkuwa, aiki aka yi mata domin ta yi doguwar naguda, an samu nasaran ciro mata ya mace wacce ta saka ma suna Hannatu suna kiranta Hanna, Daddy da Mami su suka yi mata komai, raguna biyu Daddy ya yanka mata kuma ya shirya taron suna. Baɗɗo da su Ummin ikki da matan su Hamma Abdullahi duk sun zo Kaduna taron suna Umma Balki da Umma A'i ma sun zo Umma Balki sai da aka yi arba'in ta koma Mubi ita ta yi ma Ummun wankan jego mai tsada, Baffa ma ya tako har Kaduna ya ga Hanna amma ban da Ammah sai dai ta gan ta a hoto. Kaf yayyenta ba wanda bai kira ta ba, sannan sun tako tare da iyalansa ita da Hanan sun ga gata sosai, kuma ga shi yarinyar ta taso da ƙiriniya kowa na son ta Daddy ko kamar shi ne mahaifinta yadda in dai yana gida tana tare da shi haka ma Mami shi ya sa su ta fara kiran sunayensu bayan ta fara iya magana sai Faruƙu da Ilam wato Islam ko Mahma sai daga baya ta fara iya faɗa, gata na duniya Hanan ta na gani kuma tana kan gani komai na rayuwa ba abinda suka nema suka rasa Daddy ne da Mami ke tsaye kanta ita da yarta. Har kuma gobe Habib bai nemeta ba, itama ta manta da wanzuwarsa a rayuwanta ba za ta ce ta manta gabaɗaya ba, domin ba zai mantu ba, amma ta kan daɗe ba ta tuna ba  in ta tuna ita kaɗai ta yi ta kuka, Rayuwarta ta ya sauya a Kaduna Mami macece mai kirki da yaƙana kaunar da take yi mata ko rabin shi ba ta nuna ma Lamiɗo, ba ta zuwa ko'ina tana gida daga baya ne ma ta fara bin Mami zamfara in za ta je ganin Dangin Daddy, bikin Baraka ne farko, amma ba ta bin ta Jimeta itama ba ta matsa mata  tunda ga waya tana mgana da kowa daga gida. Tun kafin ta yaye Hannan Hamma Kabiru ya matsa wai sai ta koma makaranta ita kuma har abada ba ta son karatu shi ya sa a wannan karon ma ta turje, Daddy da Mami suka goya mata baya dole suka ƙyaleta, da ta watsar da girke-girkenta sai dai kawai tana yi a gida, tunda ta hana Mami ɗaukan mai girki tace ita za ta dinga yi, Mami ce ta matsa mata ta dawo dashi, ta kuma ce za ta neme mata catering school ko wani program haka ta shiga domin ta sake ƙwarewa haka ko aka yi Mami ta nema mata ta shiga yanzu haka a Kaduna tana da certifacate sama da huɗu na catering da program kan abin da ya shafi girke-girke kuma da shawaran Mami da na Baɗɗo tare da na Hamma Saddam tare da Hamma Abdulrahim ta ƙirkiri sabon account da sabon suna lokaci ɗaya kawai tunanin yin amfani da sunan Hanan ya zo mata. Hanan Baba Jimeta sai ta ke amfani da Hanan B Jimeta. Ta fara video tana ɗorawa a youtube na girke-girke duka-duka wattani shidda ne da fara abin amma har ta ɗan fara tara mabiya da farko har ta sare da karfin gwiwansu ta cigaba a hankali ta buɗe sabbin accounts a Tiktok da instagram. Daddy kuma ya gwangwajeta da sabuwar waya Mami kuma ta siya mata ringlight kayan girki da komai akwai su a kayattacen kitchen ɗin Mami, wanda wasu ma saboda kyan kitchen ɗin ya sa suke kallon Videos ɗin Hanna Delicouis ba a ganin fuskarta in ta ɗora videos ɗon sai dai a hangi rigarta daga ƙasa haka sai maganarta, ga shi yanzu wasa wasa videos ɗinta suna ta tafiya a kafafem sada zumumta mata da dama suna ƙaruwa da ita saboda ta iya koyar da komai a saukaƙe. A dalilin Mami da Daddy ta je Umra sau ɗaya ta je Niger sun je Ghana, a Nigeria kuma sun je Abuja da Kano. Daddy  na da gidaje a Kano da Abuja haka kawai in yara sun samu hutun makaranta zai kwashe su suje su huta na kwanaki, idanuwanta sun buɗe tunda suna yawan fita yawon buɗe ido, babu in da ba ta sani a garin Kaduna ba. Wani lokacin ma har cikin makaranta ta sha raka Mami, zuwanta Jimeta wannan karon sai da ta zama abar kallo, Baɗɗo ita kanta ta zo Kaduna sau biyu sai da ta yi mamakin ganinta. Ta yi kiɓa ta sake fari ta zama wata babbar mace lalle kwanciyar hankali ma ni'ima ne. "Auta ke ce kika zama giwa haka? Ai ke da uwar taki ma sai a rasa uwar da yar." Ammah ta faɗa domin in suka jera da Mami kamar yaya da ƙanwa a jami'ar da Mami ke koyarwa da suka fara ganin Ummu sun ɗauka kanwarta ce, sai da ta ce ɗiyar yayanta ne suka saki baki, Baffa kam bakinsa yaƙi rufuwa. "Auta Auta an zama uwa manyan mata." Haka yake faɗa, Hanan ko kiyuwa ta fara yi musu farkon zuwan su, sai da Ammah ta yi mata jan ido sannan ta shiga taitayinta ta yi ta kuka tana rigima Baffa me mai lallashi ya ce shi kan ai ya ga mata, dole ya yi biyayya Ammah ko ya ce kishi take yi ta ga wacce ta fi ta jan fata. Ammah cikin gatsale ta ce bai ko yi dace ba ana ta dariya. Hanan kuma ba ta iya kiran sunan Baffa ba sai dai ta ce Bacca. Ammah ta yi ta masifa tana faɗin ke ba sunan mijina Bacca ba sunan shi Baffa in ba ki iya faɗa ba ki yi shuru ki bar ɓata masa suna, sai suka koma suna ba ma mutane dariya. Kowa ya zo ya ga Ummu sai ya yi magana haka da ta je gidan su Baɗɗo su kaltume suna ta mamakin sauyawarta ta zama wata mai tsada da ita. Ummin ikki sai da ta ce ina surukin da take jira, Ummu ta yi dariya ba ta ce komai ba, domin ita a zuciyanta ma ba ta son duk wani namiji in dai da aure ne, aure ya fita kanta gabaɗaya. Yadda ta tsani Habib haka ta tsani kalmar aure, ta je Mubi saboda an yi rashi ɗiyar Umma Salmatu ce ta rasu wajen haihuwa, nan ma suka yo ma ta caa kan maganar aure har da su Baffa Umaru shi ya sa ta baro musu garin ma gabaɗaya. Ita yanzu me za ta sake tsinta a aure da za ta sake yi? Ai tana jin babu sauran wani abun da ba ta gani ba, yanzu abin da ke gabanta kawai ba ma Hanan tarbiya amma a zuciyanta ta yi kudiri ita da aure har gaban abada. Tana ganin ta rasa komai, ba ta da wani sauran wani abu da rage mata da za ta sake takama da shi, Habib ya gama da komai kafin ya cire ta daga rayuwarsa. *** Sai bayan la'asar ta fito daga cikin ɗakin ta a baya a ɗaki ɗaya suke kwana da tare da Islam amma tun bayan da ta haihu Mami ta gyara mata ɗakinta ita kaɗai, balle ma yanzu da Islam an fara zama yan mata shekarunta sha huɗu, Faruƙu ne goma. Kicthen ta shiga ta duba abin da za ta sarrafa na dare yau ko abincin rana ba su yi ba ita da Basira tea suka sha  Hamisu kuma da kuɗinshi ba zai  jira su ba, Sunusi kuma ya yi aure matarsa na aiko masa da abinci, Mami ma tana maganar za a gyara musu bangaren waje kawai ta dawo kusa da shi. Alele kawai ya faɗo mata a rai sai ta ce bari ta yi musu mai nama a ciki sai ta yi musu miyar source ɗin ƙwai store ta shiga ta ɗobe waken suna da ƙaramin turmi ta ɗan saɓa shi ta wanke ta niƙa shi a blander wani katon friza ne a kitchen din cike da kayan amfani, nau'ikan nama ba wanda babu sai dai kawai a ɗauka in za a yi amfani da shi. Tana kitchen ɗin tana aiki Mami ta shigo gidan ba ta sani ba sai da ta leƙo kitchen ɗin ta yi mgana. "Ya Ummu sannu da aiki." Haka Mami da Daddy ke kiranta hatta Hanan ta kama wani lokacin haka take kiranta. "Laa Mami yaushe kika dawo? Ta faɗa tana kashe blander ɗin tunda ta gama niƙa waken. "Yanzu na shigo me aka yi mana ne na fara jin ƙamshi? Mami ta faɗa tana ɗan shigowa kitchen ɗin kaɗan. "Mami alele mai nama zan yi mana ko kina son wani abu ne? "Aa ki yi mana yaushe rabo na da alala, amma ki yi mana na manja." "To Mami." "Ina Hanan yar rigima? Ya zazzaɓin ya sauka? Ta tambaya tana buɗe fridge ta ɗauko rowan gora Ummu kuma ta ɗauko mata kofin tangaran a wani dirowan kitchen ɗin ta mika mata ta tsiyaya ruwa. "Ta ji sauƙi ta na can bayan Basira." "Ban gan su a falo ba." Mami ta faɗa bayan ta gama shan ruwan. "Ƙila suna bangaren Basira." "To bari na je na watsa ruwa. Kafafuwana sun gaji Ya Ummu." "Mami za a yi tausa anjuma." "Yauwa yar albarka." Mami ta faɗa tana dariya sannan ta fita, Ummu ta amsa da Amin tana ɗan mirmishi har ta fita sai kuma ta dawo tana faɗin" Baffa ya kira ki kuwa? Ta tambaya tana tsaye a ƙofar kitchen. "A'a Mami." Sai ta kalleta ganin ta yi shuru. "Me ya faru Mami? Ta tambaya a ɗan tsume. "Aa ba komai, kawai na tambaya ne." Tana gama faɗin haka ta wuce tana faɗib" Na shiga ciki." Mamaki ya kamata, me ya faru ne? Mami ba ta saba mata irin waɗanan tambayoyin ba, suna waya da Baffa kusan ko da yaushe yana kiranta amma itama tana yawan kiran shi saboda yadda suke daɗewa suna hira, saɓanin Ammah da suna gaisawa da tambayan yara hiransu take katsewa. Sai ba ta saka tunanin komai ba, sai ta ɗauka ko Baffa ne ya kira ta yau shi ya sa take tambaya kanta tsaye ta cigaba da aikinta tana sanye da riga da wando kalan ruwan ƙasa yan pakistan Mami ce ta siya mata su a Saudiya ta ce ma zaman gida ne. Mami kuma na shiga bedroom ɗinta dake saman bene ta watsa jakanta saman gado lokaci ɗaya ta ciro wayarta ta kira wata lamba, sai da ta katse ba a ɗaga ba ta sake kira nan ma shuru. "Kai." Ta faɗa tana cije baki, tiolet ta faɗa ta yi wanka ta fito kenan ɗaure da babban towel a ka kira wayarta ganin mai kiran yasa ta ɗauka da sauri. "Na ji shuru har yanzu." Magana aka yi mata daga can bangaren sannan ta gyaɗa kai tana faɗin. "To ka tabbata dai cikin satin nan, ba fa da wasa  na ke yi ba da gaske nake yi." Daga haka ta katse wayarta tana ɗan wani nazari kafin lokaci ɗaya ta saki mirmishi ita kaɗai. Daga ita sai Allah sai zuciyanta sai wanda suka yi waya suka san abin da take ƙullawa. **** *Sunday* Daddy bai dawo ba, Mami ta ce akwai wasu sabbin shigowan motoci ne da zai yo oder shi ya sa ya ɗan jima, sun saba duk karshen sati su kan ɗan fita yawo cikin gari tare da Mami da Barira da Faruƙu, yau ma ko da Daddy baya nan sun fita bayan la'asar suka je Shoprite su ɗan biya store suka yi tsince tsince, suna mota a hanyar dawowa gida Hamisu ne ke tuka su a wata mota ƙiran toyota RAV4, Baffa ya kira wayar Mami sun daɗe suna mgana abin da ma yasa Ummu ta gane Baffa ne ta ji Mami na ambaton sunan shi duk da ba ta fahimci kan me suke magana ba, tunda ita Mami faɗi kawai take yi" Kuma ka yarda da maganansa Baffa? Ni dai Allah ban yarda da shi ba." Abin da kawai taji tana faɗi kenan. Sai kuma in da ta ce" Baffa ni fa ba wai na ƙi mganar ba ne, sam shi da ƴata ba su dace ba. Ba za ta iya da halin bamuden ɗan Ammah ba." Kamar ta so ta ɗau saunar mganar, Hamma Lamiɗo ne Mami ke kira da wannan sunan amma kuma yarta ta fa? Wacce take nufi. "To Baffa muna hanya ne, zan kira ka in mun koma gida" Bayan ta katse wayar kuma ba ta ba da wata kafa da za a fahimci wani abu ba, sai ta bige da jan Ummun da wata hiran da ya sa ma ta manta da wayar Mamin, bayan sun koma gida kowa ya shiga ɗakinsa, daga nan ba ta sake jin wata mgana ba. Bayan isha'i sai ga Baffa ya kira Ummu Salma a waya bayan sun gaisa kamar kullum ya ce ina amaryansa Ummu ta ce ta kwanta. "Ummu Salma." Tunda ta ji Baffa ya kira sunanta  ta san akwai magana a bakinta. "Naam Baffa." "Wane ni a wajen ki? "Kai mahaifina ne" "Alhamdulillah kin san duk abin da zan yi ga rayuwarki ba nufin na cutar dake ba ne ko Auta? "Na sani Baffa." Har idanuwanta sun fara tara ƙwalla saboda ba ta son me ya faru ba. "A lokacin auran ki na farko ban yarda an yi miki dole ba. Duk abinda kika nuna baki so ni ma zan ce bana son shi. Har kuma yanzu da kike bazawara kina da haƙƙin sake yi ma kanki zaɓi a karo na biyu." Baffa ya yi shuru yana jan nunfashi. Ummu har ta fara kuka, tsoro take ji kar Baffa ya ce ta yi aure, ba za ta iya masa gaddama ba amma tabbas hakan cutuwa ne a gare ta. "Ummu Salma." "Naam Baffa." "Jiya an zo neman auran ki a wajena." Gabanta ya amsa ras! Jikinta har ya fara rawa. "Kuma wamda ya zo ɗin ba zan iya hana shi ba, na hango miki kyakyawan rayuwa tare da shi." "To Baffa." Ta iya faɗa tana kuka. "Ba dole zan yi miki ba, amincewarki  nake nema Auta, in har kin amince gobe da safe ni da yayyenki dake kusa zamu jagoranci ɗaurin auran ki." Wannan ba amincewa ba ne, Umarni ne Baffa ke ba ta amma a fakaice duk yadda ta tsani aure ba ta isa ta yi ma Baffa gaddama ba su suka tsaya ma rayuwarta kuma ba ta isa ta bijire ma mganarsa ba. "Kar ki damu in ba ki amince ba, ba komai sai na bashi haƙuri." Ya faɗa cikin wani yanayi a muryansa akwai zumuɗi daga a farko, daga karshe shurunta sai ya sanyaya ma muryansa ƙarsashinta. "Baffa." Ta kira shi cikin muryan kuka. "Naam Auta, kuka kike yi ne? "Aa Baffa." Ta faɗa tana share hawayenta da hannunta. "Kar ki damu na ce in ba ki amince ba sai na ba shi haƙuri." "Aa Baffa." "Kin amince? "E Baffa." "Kin tabbata? "Na amince Baffa, in dai ka amimce nima ba ni da ja." "Na amince da shi Auta, wallahi ina mai yi miki rantsuwan da cewa yadda zai kula da kansa haka haka zai kula da ke Auta." "To Baffa." Ta faɗa tana danne kukanta "Allah ya yi miki albarka Ummu Salma, yadda kika karɓi tayina Allah ya wanzar da farimciki a rayuwarki ta har abada. Na gode miki Allah ya gode miki Auta." "Amin Baffa." Ta faɗa tana jin sanyi a zuciyanta. Baffa kuma jin ba ta tambayi ko waye ba shi ya sa bai faɗa mata ba suka yi sallama suna gama waya ta tashi da gudu ta fita ta haura sama zuwa ɗakin Mami tana kuka, Mami na zaune gefen gado waya take yi sanda Ummu ta faɗo tana gunjin kuka ai sai ta saki wayar saman gado ta nufeta cikin rawan jiki. "Subhanallah Ummu me ya ke faruwa ne? "Mami." Ta faɗa cikin gunjin kuka lolaci ɗaya tana faɗawa jikinta. "Shi, bar kuka yi mini bayanin abin da ya faru." Ta faɗa tana janta gefen gado suka zauna. "Mami aure Baffa zai yi mini" Mami ta zaro ido kafin ta ce" Aure kuma? Da wa? "Ban sani ba Mami" Ta faɗa tana tsiyayan hawaye. "Yanzu Baffa bai bar mganar nan ba? Na ce nima ban amimce ba. Yanzu ma da Abban Islam muke mgana shima ya kira shi ya faɗa masa, kuma da alamu ya goya ma Baffa baya." Kukan Ummu ya ɗauke kenan kowa daman ya sani? Har Daddy ma ya amince kenan "Bar kuka, in dai ba ki so ba wanda zai yi miki dole." Wayarta ta jawo za ta kira Baffa. "Baffan zan kira." Da sauri Ummu ta riƙe mata hannu lokaci ɗaya tana mai girgiza mata kai. "Ki bari na kira shi na ce ba ki so." "A'a Mami, ki bar shi kawai." "Me ya sa? Kin amince kenan? Ummu na hawaye ta ce" Na amince Mami, ba tilas ba ne sai da Baffa ya nemi zaɓina." "Tilasa ne mana ai ba ki ga wanda za a aura miki ba, ballatana ki ji kina son shi har ki amince da shi." "Mami ba komai in dai Baffa ya amimta da shi a wajena Amintattace ne." Mami ta yi shuru tana kallonta. "Kin tabbata? In dai ba ki so zan ta da auran nan" Da sauri ta sake girgiza kanta. "Aa ina so Mami kar ki yi mgana." Sai Mami ta sake yi mirmishi. "To share hawayenki, ɗiyar albarka" Sai ma ta taya ta ta share hawayenta. Sannan ta riƙe hannuwanta tana faɗin" Ki natsu kin ji ko? Ki yi ta addu'a in sha Allahu kin samu sauyin rayuwa. Ina tare dake har numfashina na ƙarshe." Sai Ummu ta fashe da kuka ta faɗa jikin Mami. "Mami Allah ya bar min ke." "Amin ɗiya ta." Ta daɗe a ɗakin Mami suna ta hira, sai daga baya ta koma ɗakinta, ranar ta sha kuka amma ta kwana salla da addu'an neman zaɓin Allah. Kuma da garin Allah ya waye ta samu natsuwa amma tana cikin fargaba, tun safe Mami ta fita Faruku ma na makaranta daga ita sai Baraka. Ba wanda ya kira ta ballatana ta ji ko an ɗaura auren ko ba a ɗaura ba Can wajen huɗu da wani abu na yamma tana ma zaune ne ta idar da sallar la'asar ne  Daddy ya kira ta da lambarsa tana ta mamakin yaushe ya dawo? Amma abin da ya tambayeta ne ya sa ta fara rarraba ido. "Ummu Salma gamu a masallaci za a ɗaura auran ki, nawa kika yanke Sadakin ki? "Naam" Ta faɗa cikin rashin sanin madafa. "E nawa kika yanke masa? "Daddy duk abin da ka ce." "Aa haƙƙin ki ne." "Dubu dari." Ta ji bakinta na faɗa. "Tana jin Daddy na maimaita ta ce Dubu ɗari daga nan ta ji mganganun mutane ta cikin wayar sannan Daddy ya kashe wayar, abin mamaki yaushe Daddy ya dawo? Ba daɗewa Mami ta dawo da ta ba ta labarin Daddy ya kirata kamar fa yana Jimeta. "Yana can, Baffa ya ce sai ya dawo shi zai ba da auran ki." Mami ta faɗa cikin fara'a. Daga gani abun ya yi mata daɗi. "Shi ne ya ta so a yau, saboda shi ne ma ya sa daurin auran ya kai bayan la'asar." Ta sake faɗa tana kallonta. Ummu dai ta kasa magana saboda yadda jikinta ya yi wani sanyi ƙalau Mami ta shiga kiran Basira wacce ta fito tare da Hanan biye da ita tana ganin Mami ta nufeta tana kiran sunanta. "Mami oyoyo." "Oyoyo Hanan." Mami ta faɗa tana cafe ta, tare suka zauna saman kujeran falon tana shafa kanta. "Barka da dawowa Mami." 'Yauwa basira." Sai ta kalleta yadda ta ɗan rankwafa cikin ladabi Ummu ta juya za ta bar falon kenan Mami ta kalli Basira tana faɗin" rangwaɗa ma Ya Ummu guɗa yau an ɗaura mata aure Basira." Ai Basira na jin haka ta miƙe ta rangwaɗa guda har sai da Uummu ta toshe kunnuwanta ta bar falon da gudu Mami ta bi ta dariya Hanan ma na ta yata. "Ma sha Allah, Allah ya sanya alheri Mami." "Amin Basira.  Yau ki shiga kitchen Amarya ba yanayi gobe ayi abinci da yawa Hamisu zai kawo takeway, za a fita a yi sadaka." "Allah ya biya ki Mami." Ta amsa da Amin nan ta bar falon tana ta ya Ummun Murna domin ta ɗan san wani labarinta, tana tausayin kanta amma tana tausayin Ummu Salma duk da tana cikin gata. Ummu Salma ɗaki ta shige tana ta kuka, ba ta taɓa hasaso ma kanta a aure awannan tsakanin ba, sai ga shi kaddara ta sake juya rayuwarta a karo na biyu, wayarta ma kasheta ta yi domin ba ta son ma a dame ta. Mami ma ba ta sake nemanta ba, sai dare da Daddy ya dawo ya kirata. "Ga Sadakin ki, na ba da auranki akan dubu ɗarin da kika lamince." Daddy ya faɗa bayan ta karɓi kuɗin a farin takarda. Mamaki take yi, kenan da gaske ne? "Allah ya ba ku zaman lafiya. Kin yi dacen samun nagartattacen miji Ummu Salma." Kowa na faɗin ta yi dace amma ba a faɗa mata waye mijin ba, itama ba ta son sani shi ya sa ba ta tambaya ba. Har da goro da dabino da minti duk Daddy ya taho da su, ita dai kuɗin kawai ta karɓa ta koma ɗaki ta tasa su gaba tana sharɓan kuka komai ya dawo mata sabo, yanzu kuma ina za ta je? Wata rayuwa za ta sake faɗawa? Menene makomar Hanan? Washegari tun safe Mami da Basira suka shiga kitchen jalop din shinkafa da nama suka dafa aka saka a takeway ɗari har da matar Sunusi ta zo ta taya su aiki Ummu na ciki ba ta fito ba, ta dai fito sun gaisa da Mami, ba ta kawo dalilin auran ta ne ya sa Mamin yin Sadaka ba, da yake ta san suna yi duk karshen wata amma yau ɗin na daban ne har da drink da ruwa. Hamisu ya fita da shi a mota zai je makarantan almajirai a hayin banki zai raba musu. Ummu abincin ma ba ta ci ba sai da Mami ta leƙo ta yi mata mgana sannan ta fito ta sha tea, ga shi dai ita ta amimce amma kuma abin duk ya dame ta. Ta yi na farko ba ta dace ba yanzu kuma ba ta san wata irin kaddara za ta sake faɗawa a karo na biyu ba. Sannan da ta kunna wayarta kowa fatan alheri yake yi mata cikin yayyenta,  Hamma Jibo har da cewa Amarya, shi ko Hamma Mustapha wani suna ya kira ta da shi our princess amma ba wanda ya kira sunan mijin da  aka aura mata, itama ba ta tambaya ba har Baɗɗo da suka yi waya murna take yi mata. "Sisna, tabɗijam kin samo mai zafi wannan karon. Cancaɗi." Amma ba ta faɗa mata waye ba, itama ba ta ce tana son sani ba. "Sisna, ni fa bana son auren nan. Ban zan iya ma Baffa Gaddama ba ne." "Sisna, ai wannan auren na musamman ne, ya doke wannan auren naki na farko, tab ai tazaran kamar tazaran kasa da sama ne, Habibun banza shi ko a hanya bai isa ya haɗa kafaɗa da mijin ki na yanzu ba wallahi." Ummu dai ba ta biye ma Baɗɗo ba, ba ta son ma tana jin sunan Habibu saboda tsanar da ta yi masa. Har Ammah da suka yi waya ba ta nuna mata wani abu ba sun dai gaisa kamar Yadda suka saba, kuma ta ji ta duk a cunkushe ba cikin walwala ba. Baffa ne ma da suka yi waya ya dinga saka mata albarka cikin farincikin da ta jima ba ta ji shi a cikin sa ba. Sati ɗaya da ɗaurin auran ta, har a lokacin ba ta saki jikinta ba. Sukuku take, da gaske ne ta tsani aure domin ta tabbata ba komai cikinsa sai baƙin ciki da da dana sani, ta fa gwada kuma ba ta dace ba. Amma ba ta da yadda za ta iya tunda ta amsa ma Baffa an riga kuma an ɗaura baƙin alƙalami ya riga da ya bushe. Mami kamar murna ma take yi domin ba ta ga alamun ta damu da ganin yanayin ta ba, tunda aka ɗaura auren nan duk dare sai ta yi kuka, so kawai take yi ta samu wani dalilin da za ta sauwaƙe ma kanta wannan auren, in ta tuna auren sai ta tuna makomar rayuwanta anan gaba, ba ta san mijin ba amma ta fi karkata tunaninta da wataƙila daga can Mubi ne tunda ta ga kowa ya san shi. Ranar Ummu ta yini  cikin nazari, duk hanyar da za ta ɓulle da ita sai kuma ta je karshe ta iske a toshe take, yini ta yi a ɗaki ba ta fito ba kamar wata mara lafiya Hanan na wajen Basira, kamar ta san yanayinta na yau ba ta zo ta yi mata rigima ba. Tana kwance Basira ta zo tana faɗa mata Mami ta yi baƙo, mamaki ya kamata wani irin baƙo kuma? Kuma Basira ta ce yana Falo, kafin ta fita ta yi ta kiran wayar Mami ta ji ko ta san da zuwan baƙon amma wayarta ba ta shiga shi ya sa ta saka mayafin abayan dake jikinta ta fita zuwa falon Mami. Duk a tunaninta tunda aka ce ya shigo har falo to ko daga Jimeta ko daga cikin dangin Daddy shi ya sa ta fita kanta tsaye ba fargaba. Mamaki ya sandarar da ita lokacin da ta yi arba da ganin Hamma Lamiɗo zaune a falon Mami yana ɗauke da Hanan a jikinsa tana ta wasa da sajen fuskar shi. Sanye yake da farar shadda, har tana ƙyalli kansa da hula amma saboda suma a saman gashin hulan tasa baƙa ta tsaya. Ya ji shigowarta amma bai iya ɗagowa ya kalleta ba. Ummu ta ce a ranta lalle Mami na da Babban baƙo Domin tunda ta zo gidan ba ta taɓa ganin ya zo ba sai yau. Me ya kawo shi? Ta tambaya a cikin zuciyarsa. "Ko kin manta Mami mahaifiyarsa ne? Wata zuciyar ta tunasar da ita abin da ta manta. Har ga Allah mantawa take yi da Mami ce ta haifi Hamma Lamiɗo. "Barka da zuwa Hamma Lamiɗo." Ta faɗa bayan ta ɗan ƙariso falon. Da farko ta so ta yi wucewarta ne saboda Mami ta tsaya da kuma tuna ya fa taimake ta, da jininsa take rayuwa a yanzu. "Lafiya." Ya amsa mata, sau ɗaya ya kalleta bai sake ba, wasa yake yi ma Hanan. Ta so ta yi komawarta ɗaki ne domin ita yanzu neman ma kanta mafita take yi amma ganin yadda ya ɗauki Hanma ya sa ta ji sanyi a zuciyarta, ko ita bai yi mata kallon Daraja ba ta ji daɗi da ya yi ma Hannan kallon mutumci shi ya sa ta je kitchen ta haɗo masa ruwa da lemu, Daddy ba ya nan ya je Abuja tun jiya amma a yau Mami ta ce zai dawom Har ta kawo ruwan ta ajiye ta fita falon bai ɗago ba, itama ba ta damu ba ɗaki ta koma ta yi kwanciyarta tana cigaba da sabon lissafin da ya kamata tun bayan auran da aka ɗaura mata, tunani take yi me ya sa Allah bai amsa addu'arta ba? Ita da har a masallacin Madina ta roƙesa da Allah ya sa ta mutu ba ta sake aure ba. Me ya sa kuma Kaddara ta sake buɗe mata wani sabon shafin rayuwa? Ba ma batun ba ta son mijin da aka aura mata ba, auren ne gabaɗaya ba ta so. Ta ma manta da baƙon Mami ta na ciki tana tufka tana famam warwara Har Mami ta dawo  ba ta sani ba sai da ta shigo ɗakinta sannan a lokacin ta san ta dawo "Kika zo nan kika kwanta Ummu? Mamin ta faɗa tana kallon ta. "Mami sannu da zuwa Yaushe kika dawo? Ummu ta faɗa tana ɗan miƙewa zaune a saman gadon data ke kwance. "Ban daɗe da dawowa ba. Sai kika bar baƙo shi kaɗai a falo Ummu? "Mami to na ga Hamma ne ya zo, kin san shi ba ya son hayaniya shi ya sa na baro falon na dawo ɗaki ." Ta faɗa tana ɗan mikewa zaume. "To mijin ki ne, in ba ki zauna ba ai ba za ku fahimci juna ba." "Na'am" Ummu Salma ta faɗa tana kallon Mami domin sai ta ji kamar ba ta ji daidai ba. "Ko ba ki san baƙon ki ba ne? Mami ta sake faɗa tana kallonta. Ummu ba ta son ta dire ƙasa ba sai da ta ganta a tsaye kan kafafunta. "Baƙo na kuma? Ta faɗa cikin mamaki. "Baffa bai kira ki ba? Mami ta sake tambaya, domin sun yi mgana da Baffa shi ya faɗa mata Lamiɗon zai zo su yi magana da Ummun a tunanin ta Baffan ya kira Ummun ya sanar mata. "Mami." Tana ta yi magana amma ta kasa jikinta ya yi wani irin sanyi. "Ki gyara jikin ki, ki je ki same shi." Mami ta faɗi haka da sauri lokaci ɗaya kuma tana barin ɗakin. Ai sai Ummu Salma ta ji kamar ta daina jin mgana ta kurmance, kamar shiga da fita haka ta ji kalaman Mami. "To mijin ki ne, in ba ki zauna da shi ba ta ya za ku fahimci juna? Idanuwanta sun fito waje saboda firgici da razana, in dai har ta ji daidai to Mami na nufin Hamma Lamiɗo ne mijin da aka aura mata. Innalillahi wa'inna ilaihirraju"um." Ta faɗa a zucci da sarari lokaci ɗaya ta ɗora hannu akai ta fashe da kuka. "Ina ni ina Hamma Lamiɗo, wallahi bana son shi." Take faɗa tana kuka lokaci ɗaya ta koma ta zube kan gado, ji take yi kamar ta yi hauka, ina, ina za ta iya zaman aure da Hamma Lamiɗo, ai an gudu ne ba a tsira ba, sai ta ke jin kamar ta fita ta yi ta gudu kar ta tsaya, ita da ko inuwa ta minti goma ba ta taɓa haɗawa da shi ba, ta ya ya za ta iya haɗa inuwar aure da shi? Mafitan ta na ƙarshe shi ne ta samu mijin ta roƙe shi ya sauwake mata domin ba za ta iya masa biyayya ba, amma jin wai Hamma Lamiɗon ne mijin tuni lissafinta ya ƙwace. Ko burkutu ta sha ba za ta iya doguwar magana da shi ba, in tunanin ta ma ya kawo mata sunan shi ji take yi kamar ta haukace. Innalillahi ta shiga ta uku ta lalace. Ita Ummu Salama ina ita ina Hamma Lamiɗo? Ƙarshen littafi na ɗaya. Akwai sauran tafiya, mun gama shimfiɗa yanzu muka kwarari doguwar tafiya. Ga dai Lamiɗo ga Ummu Salma, mu je zuwa domin ganin yadda tafiyar za ta kai su. Ku biya kuɗin karatun ku na La shakka babu nadama a cikin wannan tafiyar in sha Allahu. *littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗanan lambobin kamar haka.* 09069067488. 08032773332. *Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.* *Janafty* *27/04/2026*