Bismillahi Rahmanin Rahim. MADUBIN GOBE 1. Pharty Bb. Wattpad phartybb. "Nuratu! Nuratu?" Hajiya Sadiya dake zaune bakin katifar ƴarta tana ƙiran sunanta lokaci ɗaya tare da yaye abin da ta rufe jikinta dashi. Motsi tayi har lokacin bata buɗe ido ba. "Mami da sauran lokacin shan maganin, don Allah ki bar ni inyi bacci kaɗan, yanzu zan farka." "Ki tashi kisha ko in ɓata miki rai, tun ɗazu nake faman tashinki kin ƙi ji." Yaye abin da ta rufe jikinta dashi Nuratu tayi ta tashi ta zauna, tana mutsetstseke ido ta ce. "Yanzu Mami bazan taɓa kwana na wuni ban sha magani ba, shikenan rayuwata haka za ta ƙare." Sauyin yanayi da ta gani a fuskar mahaifiyarta ya sata yin shuru, ta karɓi maganin hannunta da ruwa. "Komai zai wuce Nuratu. Ƙaddarar mu gaba ɗaya kenan ba ke ɗaya ba. In sha Allah watarana za ki kwana ki wuni ba ki sha magani ba da yardar Allah. Ko kin manta me Dr Awwab ya faɗa." Girgiza kai Nuratu ta yi lokacin da ta saka ruwa a bakinta don kora maganin. Haka kullum ake faɗa mata cewa komai zai wuce amma ba ta taɓa kwana ta wuni abun da ya wuce bai faɗo mata a rai ba. "To kina tuna hakan. Maza ki tashi ki shirya makaranta, ke wasu in sun kusa fara final exam basa bacci basa zama amma ke banda bacci baki da aiki." "Ba ni da lecture ne ai, duk anyi closing, test ake yi." Tashi Mami tayi ganin tasha maganin ta fice ta barta. Ganin haka ya saka Nuratu komawa ta kwanta. Tunanin rayuwarta ta shiga yi, ganin abun zai ɓata mata rai don har kanta ya fara ɗaukar zafi ta miƙe da sauri tana shiga bathroom. Wanka tayi ta fito ta saka riga da skirt na lace ɗinta tare da mayafinta babba, za ka rantse matar aurece don yadda ta rufe jikinta ruf da shi. Ba tayi wani kwalliya ba ta ɗauki wayarta da jakarta na makaranta ta fita. A falo ta samu mahaifiyarta zaune tana kallon huɗubar Jumma'ah, gefenta yarinya dake taimaka mata tana gugan kayanta. "Mami zan leƙa makaranta, daga nan zan biya gidan Aunti Rahma?" "To kar ki jima dai, banda shiga hayaniya. Ki gaisheta." "Za taji." Nuratu tace tana ɗaukar mukullin motar Mami ta fice dashi da sauri. "Ki dawo min da mukullin nan." Mami tace da karfi, jin ba zata dawo ba ya sa ta cewa. "Kiyi tuƙi a hankali." Murmushi kawai Nuratu tayi da tsakanin Mami da ƴan uwanta take yi, sai wanda ta basu muhimmanci a rayuwarta suke ganin murmushinta, shekarun baya har ta mance menene murmushi balle dariya. Makaranta taje ta sama an manna time table, ganin babu wani abun ya sata fita ta nufi gidan yayarta Aunti Rahma. A waje tayi parking ɗin motar ta shiga. Sallama tayi kofar falonta kafin ta shiga, Rahma dake cikin ɗaki tana hutawa bayan sallamar ƴaƴan ta sun wuce makarantar taji muryar ƙanwarta da sauri ta fito tana murmushi. "Ashe dagaske za kizo." "Kin san dai bana ƙarya." Nuratu tace yayin da take zama saman kujera. Zama ita ma Rahma tayi suka gaisa tana tambayarta Mami ita kuma tana tambayarta sauran Yayunta da ɗanta Khair da yayunsa. Ruwa ta kawo mata da abinci, Nuratu ta girgiza kai. "Nayi breakfast tun 7, Mami bata yarda ta barni da yunwa." "Hakane autar Mami. Amma kuwa sai kinci abincin gidana" Rahma tace tana haɗa rai ganin haka ya saka Nuratu cin kaɗan ta bari. Suka hau hira dan sun kwana biyu basu haɗu ba. Su biyun in ka cire Aunti Hasiya mai bin Aunti Rahma da Rukayya wacce Nuratu take bi sun fi shiri, ko dan ta kasance ita ce babba ita ƙarama. Sai wajen ƙarfe ɗaya Nuratu ta fara shirin tafiya bayan ta taimaka Aunti Rahma da abincin rana ta mata sallama. Gida ta nufa ta samu Mami bata falon cikin sanɗa zata wuce ɗakinta taji Mami ta ƙirata. Juyawa tayi tana sosa ƙeyarta. "Sorry Mami." "Kinsan dai lokacin shan maganin ki ya kusa wucewa amma ki kayi zamanki. Na ƙiraku dukkan ku ke da yayarkin ba wanda ya ɗauka." "Kiyi hakuri Mami. Muna aikine ba mu ji ba. Magani kuma yanzu zan sha." "Lafiyar ki nake nema miki Nuratu, kin fini buƙatar hakan sanin kan ki ne." Shuru Nuratu tayi cikin sanyin jiki. Gaskiyar Mami, ta fita buƙatar lafiya duba da abubuwan da suka faru a rayuwarta. Ƙoƙarin ta kullum ta ganta tana walwala da farin ciki tamkar sauran al'umma. Wani lokaci ko tasha maganin in ta fara tunanin abin da ya wuce, ko yazo mata kanta, ko tayi tozali da makamancin shi zata wuni tamkar bata sha magani ba domin ciwon zai nuna alamu zai tashi, sai dai Mami tana bakin ƙoƙarinta ganin ta kawar mata shi a ranta walwalarta ya dawo. "Kiyi hakuri Mami." Nuratu tace ganin Mami ta nufi ɗakinta. "Ya wuce." Ta bata amsa dashi ta shige ɗaki ta barta. Tana son ƴartan duk cikin ƴaƴanta. Su biyar ta haifa amma duk ciki tafi sabo da ita sun fi shaƙuwa. Ko dan a gabanta ta taso ita ɗin. Abubuwan da suka faru a rayuwarta ita da Nuratu Ƙaddarar suce da Allah ya rubutu musu ba daman kaucewa. Ita ƙaddara rubutacciyar shafine a rayuwar ko wani bawa da baya tsallakewa. Tare suka sha wahalar su duk da sauran yaran sun tausaya musu halin da suka shiga a shekarun baya haka ma mahaifinsu da ba tayi tsammanin haka daga gare shi ba. Amma daga baya komai ya ƙara lalacewa yaci gaba da tafiya kamar da. Tana son Nuratu tana tausayin ta kuma tana bata taimako dai-dai gwargwado da zata iya bata a matsayin ta na mahaifiyar ta. ... 11/03/1996. DAMATURU, YOBE STATE. Sallamar da mai gidanta yake kwalawa shi ya sata fitowa da sauri a ɗakinta. Zaune ta same shi a falo ya kurawa talabijin idanu. "Sannu da zuwa." Sadiya tace yayin da take zama kusa dashi sai lokacin ya farga daga tunanin da yake ya kalleta bai ce komai ba. "Lafiya Abban Rahma?" Shine tambayar data mishi ya kawar da idanuwanshi daga kanta yana girgiza kansa. "Ba lafiya, amma komai allahamdulillahi." "Ba lafiya? Ko dai bamu samu matsayin da muke nema bane?" Ta faɗi hakan dan son sanin abinda ke faruwa. "Ban samu ba Sadiya, sai dai fatan muyi addu'a Allah bamu Sa'a wani shekaran." Cikin sanyin jiki tace. "Ameen.' Dan tasan yadda mijinta yaci burin samun babban matsayi a wajen aikinsa. Maganar mijinta Alhaji Mamman Bashir shi ya sata dubanshi. "Mai aka ce miki a asibitin?" Murmushi tayi kamar mai jin kunya tace. "Juna biyu ne kamar yadda kake zargi." Murmushi yayi dan yana son ƴaƴa. Jin ciki jikin matarshi ya ji damuwarshi ta kau yace. "Allahamdulillahi Allah raba lafiya. Amma zaki yaye Rukayya ko?" "A'a, dana sanar dasu in nayi yaye in na samu ciki yaran suna jinya sai suka ce this time kar nayi yayen sai na kusa haihuwa." "To hakan yayi. Allah kaimu lokacin." Ameen! Ta amsa dashi suka taɓa hira wajen sha biyu yace zai leƙa wajen kasuwancin shi ba zai jima ba zai dawo. ... Alhaji Mamman Bashir. Ɗa na ƙarshe wajen iyayen shi. Su shida suka haifa mata huɗu maza huɗu, maza biyu sun rasu saura su huɗu. Mahaifinsu ya jima da rasuwa amma da wayonsu sai mahaifiyar su da itama bata fi wata da rasuwa ba. Duk sunyi aure da ƴaƴansu. Ɗan asalin fulanin Gombe mazauna Gombe. Sunyi karatun boko da islama ba laifi. Alhaji Mamman Bashir ya karanci harkar kasuwanci in da ya kammala karatun shi bai samu aiki ba kuɗin gadonshi ya fara sana'a dashi Allah ya sawa kasuwan albarka ya fara bunƙasa Allah yayi zamansa a garin Damaturu jihar Yobe, anan yaci gaba da kasuwanci shi har lokacin yana neman aiki. Shiga da fita da yake yi tsakanin garuruwa a wata tafiyarshi ƙasar Nijar ya haɗu da Halimatul Sadiya ƴar asalin fulanin Nijar. Auren soyayya su kayi bayan soyayya da su kayi na shekara ɗaya ta tare gidan mijinta dake cikin garin Damaturu jihar Yobe. Halimatul Sadiya marainiya data taso gaban kakarta. Iyayenta sun rasu a hatsarin mota sun barta da yayunta maza uku, biyu sunyi aure a ƙasar Libya ɗaya yana aure a Doso jumhuriyar Nijar. Tsakanin miji da matar ba laifi suna zaman lafiya dan Alhaji Mamman Bashir ba abinda ya rageta dashi yana bata kulata kuma yana son matar shi. Arziki ya ƙaru kasuwanci ya zauna masa a lokacin ya samu aiki a Company shiga da fita na kayan abinci. Samun aikin shi ya sashi neman yaron shago dan kula mishi da aikin kasuwancin, shi kuma ya fara kula da ofishin sa sai lokaci zuwa lokaci yake duba shagunan sa. Shekara uku da auren Alhaji Mamman Bashir da Halimatul Sadiya kafin Allah ya bata haihuwar ƴa mace suka saka mata suna Rahma. Daga nan haihuwar ya buɗe dan ranar da Rahma ta cika shekaru biyu ta haifi ƴa mace Hasiya, shekaran Hasiya ɗaya ta samu cikin Muhsin shima yana cika shekara uku ta haifi Rukayya da yanzu watanta goma ta samu cikin wata ɗaya. Duk saurin haihuwarta Alhaji Mamman bai taɓa gajiya ba dan yana son ya'yansa. Arziki ya linku ya zama wani Alhaji. Ya kai su Hajj sun sauƙe farilla shi da matar shi. Wannan cikin ma tun sati ɗaya da ya wuce yake roƙarta taje asibiti shi fa bai yarda da ita ba. A jikinta taji cikine da ita amma bata son zuwa. Ganin ya damu da hakan yasa taje ta tabbatar da hakan. A yau kuma yake saka ran samun cigaban wani matsayi a gurin aikin shi da Allah bai nufa zai samu ba. .... Hayaniyar Rahma da Hasiya sun dawo daga makaranta ya sata barin kitchen ɗin Muhsin yana bin bayanta. Yaran ta samu cikin falon suna ta surutu ga Rukayya gefensu tana bacci. "Kai zaku data min ita, maza ku wuce ɗakin ku ina zuwa zan cire muku kaya." To yaran suka amsa dashi suka kwashi jakansu da takalma su a hannu suka wuce ɗakinsu ta koma kitchen ɗin ta sauƙe miyarta ta wuce ɗakin yaran. Kayansu ta canza musu zuwa na gida kafin su fito. "Mami abinci zanci, yunwa." Faɗin Hasiya tana tsalle saman kujera. "Haka dai kullum kina cikin ci sai ƙiba kike ƙarawa." Mami tace ta wuce kitchen ta zuba musu a babban tray ta kawo falon ta ajiye a tsakiya. "Sauƙo Rahma, Muhsin kai ma ka haɗu dasu kuci." Mami tace ta komawa kitchen ta kawo musu ruwan sha dana wanke hannu. Gaba ɗaya suka wanke hannunsu suka zauna suka fara ci. Kitchen Mami ta wuce ta haɗa na mijinta a food flask mai kyau da plate da spoon kafin ta fito ta wuce ɗakinta dan wanka. Bayan ta gama ta yi sallar azahar da har lokaci ya ɗan gota, ta fito falon ta samu sun gama cin abincin Rahma tana share gurin. Gefe kuma Alhaji Mamman Bashir yana jijjiga Rukayya da surutunsu ya farkar da itatana kuka. "Mun leƙa kina wanka." Cewar Alhaji Mamman yana miƙa mata Rukayya. Hannu tasa ta karɓeta yayin da take zama tace. "Wallahi Abban su bayan na gama aikin zafi ya dame ni, ga zirga zirga na asibiti duk na gaji shine na watsa ruwa." Zama yayi gefenta yayin da take shayar da Rukayya take tambayar shi ya kasuwa. "Babu daɗi, ashe kayanmu duk sunyi expire yaron nan bai sanar dani ba. Fitana sai da na cire miliyin ɗaya da rabi na bashi ya ƙara da sauran cinikin da yayi ya sari wasu kayan." "Bai kyauta ba, irin haka sai ya sanar da kai tun wuri kafin lokacin." Hajiya Sadiya tace cike da jimamin abinda ya faru. "Ai na mishi faɗa sosai shi da sauran yaran, wai dama akan zai sanar dani jiya ne kuma ya mance." "Allah mayar da alheri." Hajiya Sadiya tace tana zare Rukayya daga abincinta ganin ta ƙoshi ta miƙa Abban ta ya karɓeta yana amsawa da ameen. "Bari in kawo maka abinci." Kai ya ɗaga mata yana ma Rukayya wasa yasa ta wuce kitchen. Ɗaukowa tayi a babban tray har da ruwan zobo data haɗa masa ta kawo mishi falon. Tare su kaci kasancewar ita ma bata ci abincin rana ba. Bayan sun gama ta tattare gurin. Washegari ranar Alhamis da asuba ta samu ɗan saƙon ya sanar mata ƙiran da ake mata daga garinsu. Bayan ta sanar da mijinta yace ta shirya taje ta ji lafiya sai tayi kwana biyu. "Ji nake kamar ba lafiya ba Abban su." "InshaAllah lafiya lau." Girgiza kai tayi tana cewa. "A jikina nake jin ba lafiya. Zan tafi dasu Rahma." "Makarantar su fa da islamiyya." "Yau da gobe suyi hakuri, asabar sai mu dawo su samu zuwa islamiyya Lahadi." "To shikenan Allah kiyaye hanya." Yace ya ɗauki dubu hamsin ya ajiye mata. "Ga wannan ki riƙe a hannunki. Ilyas ya kai ku zan bashi kuɗi yayi full tank." "Nagode. Nagode sosai Abban su." Hajiya Sadiya tace tana murmushi amma cikin zuciyarta haka kawai take jin yana bugawa. Fita tayi ta shirya yaranta ta haɗa kayansu ta haɗa nata suka fita lokacin Ilyas ya dawo daga shan mai. Sai da Abba yaga tafiyarsu yana ma ƴaƴan shi bye bye kafin ya koma gidan shima ya shirya ya wuce aiki. .... ƊANƊANO. Labarin MADUBIN GOBE kenan dana dawo dashi. MADUBIN GOBE 2. Pharty Bb. Wattpad phartybb. ... Ƙarfe ɗaya da mintuna na rana suka isa gidan, tafiyan awanni bakwai su kayi a hanya dan tsaye tsaye da suka yi. Shigarta cikin gidan da yaranta ta samu yayanta wanda take bi ya zo, fuskar sa cike da damuwa da taji zuciyarta ya ƙara karaya. "Yaya Muhammadu ina kaka tana lafiya?" Girgiza kai yayi yana duban ƙanwarshi data zama wata Hajiya ga yaranta yan gayu. "Lafiya lau Sadiya ki shiga tana ciki." Da sauri ta faɗa ciki, yaran zasu bita ya hana su da Rukayya kawai ta shiga. Wani ɗaki ya kai su ya saka aka kawo musu abinci da ruwa. Rahma ce taci abincin kaɗan Hasiya da Muhsin sun kasa ci sai kindirmo da suka sha. Hajiya Sadiya da kuka ta fito ganin halin da kakarta take ciki. Tamkar mahaifiyar ta take kallonta. "Hakuri za muyi Sadiya muyi ta addu'a Allah zai bata lafiya." Yaya Muhammadu yace dan kwantar mata da hankali. Hawayenta ta share. "Yaya Muhammadu ji nake kaka ba zata tashi ba." Shima yana jin hakan saboda yadda jikinta yayi tsanani. Daren ranar basu iya runtsawa ba. A cikin gidan aka ba Hajiya Sadiya ɗaki ita da yaranta suka kwana. Kwana tayi tana sallah da rokan Allah ba kaka lafiya. Yaya Muhammadu a kanta ya kwana, da asuba kaka ta karɓi shahada a bakin jikinta Yaya Muhammadu. Hajiya Sadiya tana yin sallar asuba ta shiga dubata ta samu rasuwarta. Kuka ta dinga yi tana mata addu'a. Kafin karfe goman safe gidan ya cika da dangi da ƴaƴan Kaka, da suka kasance yayun mamarsu Hajiya Sadiya da yaya Muhammadu. Ƙarfe sha ɗaya a kayi jana'izar ta aka kaita gidanta na gaskiya suka bita da addu'a. Daga nan gidan ya zama gidan makoki aka fara shigowa musu ta'aziyya. Alhaji Mamman Bashir bai samu labarin da wuri ba sai washegarin ya taho. Bayan ya musu ta'aziyya washegarin ya koma. Sai da a kayi sadakan bakwai kafin Hajiya Sadiya ta fara shirin tafiya dan makarantar yaranta. Haka ta taho ta bar su har lokacin yayunsu maza biyu basu zo ba sai waya da su kayi. ... Bayan wata biyu da faruwar haka Hajiya Sadiya ta fara mance rasuwar kaka sai addu'a da take mata. Tsakanin ta da mijinta komai lafiya haka yaranta. Rukayya sai girma take tana wayo abinta ta fara tsayawa, cikin jikin Hajiya Sadiya watanshi uku. *** Cikin fushi ya shigo gidan ranshi ɓace abin da yaron shagon shi ya mishi ya mutuƙar ɓata masa rai. "Lafiya Abban su?" Hajiya Sadiya tace tana miƙa masa ruwa a cup ganin ranshi ɓace yayin da suke zaune. Sai da ya shanye tas ya ajiye cup ɗin alama ta ƙara masa. "Salisu yana nema ya fara min wasa da dukiya, ganin shi ɗaya ne na yarda dashi." "Wani abun kuma ya maka?" "Wai yaron nan aure zai yi. Ya sanar dani in cire kuɗi cikin kuɗin jikina in bashi yaƙi ya ɗauki kuɗin cinikin mu yayi abinda zai yi dashi. Kuɗin da sai mun cinye shekara kafin mu mai da. Zan nemi wani kawai, zan nemi wani yaron." "A'a Abban su kayi hakuri, ka sanar dashi laifin shi ya kiyaye gaba kuma ya mai da hankali bisa kasuwanci dan dawo da kuɗaɗen." "Shikenan hakan zan yi dan ɓacin rai na kasa mishi magana wallahi." "Hakuri za kana yi. Dana mu'amala da mutane haka ya gada komai daɗewarka da mutum." Maganganun kwantar da hankali Hajiya Sadiya tayi tawa mijinta har ya sauƙo. Kullum yana godiya ga Allah da alfahari da samun mace kamar Sadiya. ... Bayan sati biyu. Bayan sati biyu da faruwar haka Alhaji Mamman Bashir ya ma Salisu faɗa akan abinda ya aikata yaron yaji haushi amma bai nuna ba. *** "Alhaji Mamman I'm sorry about what happen. Babu sunan ka cikin masu tafiya." "What!." Yace da ƙarfi yana tashi tsaye sai ya tuna gaban oganshi yake ya koma ya zauna. "Ta ya hakan zai faru?" "I don't know. Daga can Thailand suka turo sunan wanda suka zaɓa." Zai yi magana abokinsa dake gefenshi ya mishi alama da kar yace wani abu. Haka yasa ya hakura ya miƙe. "Shikenan Sir." Daga haka ya fice ranshi ɓace. Rayuwar shi ta fara canzawa tsawon watanni biyu kenan. Komai ya nema baya samu sau biyu kenan. "Alhaji Mamman! Alhaji Mamman!" Faɗin Alhaji Tukur kenan wanda suke aiki guri ɗaya da shi kuma abokinsa daya yarda dashi. Dakatawa yayi yana duban shi har ya ƙarasa wajen shi. "Sorry na tsayar ka, I'm sorry for what happen." "It's ok ba komai." Alhaji Mamman yace zai wuce yaji Alhaji Tukur yace. "Sai dai kamar naga ka shiga damuwa da faruwar hakan." "Muje office." Abinda Alhaji Mamman yace yayi gaba da sauri Alhaji Tukur ya bishi. "Sau biyu ina neman abu cikin Company nan bana samu, na rasa mai yasa hakan yake faruwa dani." Alhaji Mamman yace kenan ya sanar da Alhaji Tukur abinda yake faruwa dashi. "Lallai akwai ayar tambaya kan lamuranka, amma ba komai in har ka yarda dani zan taimaka maka?" "Wani irin taimako kuma Alhaji Tukur?" Alhaji Mamman ya faɗa cike da ƙaguwa. "Zan taimaka maka inshaAllah. A weekend mu haɗu zan maka bayani." "Kai da naji daɗi wallahi, domin abubuwan nan sun fara ishana sosai." "Kai dai kar ka damu." Alhaji Tukur yace ya miƙe tare da fita. Sai lokacin hankalinshi ya kwanta. In har zai taimaka mishi ya samu cigaba a aikin shi yaji daɗi kuma dole ya mishi alheri. Sati biyu kenan da aka ɗauki sunan masu zuwa ƙasar Thailand dan saro wasu kaya a company nasu ya saka sunansa, yaso zuwa amma yanzu ya samu labarin babu sunanshi cikin wanda aka zaɓa. Da ya koma gida bai sanar da Hajiya Sadiya ba amma ta lura yana cikin damuwa. Haka yasa tayi ta ƙoƙarin sashi nishaɗi. An wayi gari da mummunar labari bisa gobara da ya tashi a kasuwa yau ya koma shagunan mutane da dama. Ciki har dana Alhaji Mamman Bashir da haukane kaɗai bai yi ba da yaga yadda wuta ya masa da kaya. Rabi da kwata duk kayan abinci ya ƙone ya farfashe. Gari duk ya kaure da wannan hatsari daya faru. Tuni aka fara ƙira ana mishi jaje wasu har gida. Hajiya Sadiya ta shiga ruɗu da jin babban shagon mijinta mai faɗinshi babba ga kaya dayawa ya ƙone. Ta mishi jaje da addu'ar Allah yasa wani hau ya tare. Ƴan uwa da suka samu labari har gida suka zo mishi jaje. Kwana biyu da faruwar haka Alhaji Mamman Bashir ya fara gyaran shagon shi bai jira gomnati ta taimaka musu ba. Cikin satin bai samu zuwa aiki ba kuma basu mishi magana ba dan sun san uzurin shi. Shagon shi ya gyara ya ƙara buɗa ginin a kayi painting, ya zuba kuɗi aka saro sabin kaya. *** "Wallahi Alhaji Tukur abin nan ya fara ishana. Ace daga wannan sai wannan cikin lokaci ɗaya. Daga kasuwar da aikin ofishin duka haka." Alhaji Mamman Bashir kenan yake faɗar haka ga abokinsa Alhaji Tukur bayan gaisuwa da ƙarin jaje da Alhaji Tukur yazo mishi da ganin sabon shago. "Ai tashi za kayi tsaye abokina. Ba'a zama yanzu, yan sa ido sun yi yawa masu ruwa ana kirgawa, kaga wannan sauran arzikin shima sai ka rasa su in akwai masu mugun ido da baki." "Allah ko Alhaji Tukur?" "Sosai ma bana faɗa maka ba. Shawarace dama zan baka muje ka karɓi maganin bakin duniya ka tsare kan ka da dukiyar ka." "Kamar yaya?" Alhaji Mamman yace yana neman ƙarin bayani. Zama Alhaji Tukur ya gyara. "Akwai wani da yake mini aiki, can za muje. Dubiya kawai zai maka ya baka maganin tsari." "Anya kuwa?" Cewar Alhaji Mamman. "Ba zaka iya ba kenan?" Shuru yayi kafin yace. "Zanyi tunani a kai." Basu jima ba bayan ya gama ganin shagon suka rabu. Da Alhaji Mamman ya koma gida ya sanar da Hajiya Sadiya yadda su kayi da Alhaji Tukur. "Wajen boka zai kai ka Abban su." "Boka dai Sadiya. Maganin bakin duniya kawai zai bani, baki ga yadda aka kasa dukiyar nan gaba ba." "Ni kam ban amince da wannan duk abubuwan ba, jarabawa ce ko Ƙaddarar Allah dan ya jarabci imaninka, dan Allah kayi hakuri ka cinyewa wannan jarabawar kar ka kai kan ka halaka, duk in da kaji an ce dubiya wallahi shirka ne." "Ya isa Sadiya, je ki kawai." Yace yana haɗa rai. Ganin haka ta miƙe ta fita. Daga faɗa masa gaskiya shine zai nuna ɓacin rai. Fushi su kayi na kwanaki kafinsu shirya abinda basu taɓa yi ba. Shima sai da yace mata ya fasa kafin ta sauƙo. Ƙasan ranshi kuwa jira yake yaga wani abun zai faru ya nemi hanyar zuwa. Wata biyu shuru lafiya suka ci gaba da rayuwarsu. Sai lokacin hankalinshi ya kwanta dan ganin babu abun da ya sake faruwa. ... Tashin hankali da ba'a sa mishi raba. Daren jiya ne barayi suka ɓalla shaguna suka kwashi kuɗaɗe da wasu abubuwan amfani. Tun asubanin ranar Alhaji Mamman ya samu labarin amma bai bawa labarin muhimmanci ba kasancewar yasan Salisu baya barin kuɗi a shago gida yake wucewa dasu. Sunyi ta jajantawa mutane a gida da matarshi Hajiya Sadiya har yana cewa Insha Allah babu komai Allah ya taimaka shi dan ya san Salisu. S ai wajen ƙarfe goma ya fita bai biya office ba ya wuce kasuwa dan jajantawa maƙotan shagon shi. Mutane turum ya tarar bakin titin da yake shagon shi sai yaji hankalinshi yana neman barin jikin shi yayi sauri ya fito yana shiga cikin mutanen da wasu har sun fara miƙa gaisuwa da bama ji yake ba. "Salisu mai ya faru?" Shine kalmar daya faɗa kenan lokacin daya ganshi gaban Salisu. Salisu da yaji cikinshi ya murɗa kaɗan ya sake fitsari ganin ubangidan shi sai gumi yake ya kasa bashi amsa har sai da ya daka mishi tsawa. "Na ce maka mai ya faru?" "Alhaji sun kwashe mu. Jiya na barwa Idris shagon akan in ya rufe ya saka kuɗin a Safe, to sun haɗa da namu." Salati Alhaji Mamman ya saka yaji hajijiya na neman faɗar dashi har sai da ya dafa abu. Mutanen gurin suna mishi sannu ya bi a hankali. "Salisu ka gama dani, ka cuce ni. Ina Idris ɗin?" "Bai samu fitowa ba, labarin jiya ya sauƙar masa da zazzaɓi wallahi." "Ba laifin ku bane." Cewar Alhaji Mamman da furucin ya tsorata Salisu, mutanen gurin ya basu mamaki. "Ba laifin ku bane, Laifi na ne." Daga haka Alhaji Mamman ya kaɗa babban rigarshi ya fita a shagon ko takan mutanen da suke masa magana bai bi ba. Motarshi ya shiga ya ja bai tsaya ko ina ba sai Company nasu. Mutanen da suka ganshi suka samu labarin abinda ya faru suna mishi magana bai kulasu ba ya wuce ofishin Alhaji Tukur. "Yanzu nake shirin zuwa wajen ka. Ya abinda ya faru?" Cewar Alhaji Tukur ganin Alhaji Mamman ya shigo a hargitse. Bai iya zama ba dan tashin hankali yace. "Alhaji Tukur tashi muje. Muje a dubamin wannan abubuwan ba banza aka barni ba, ko ba sa hannun wani to da bakin mutane " Miƙewa Alhaji Tukur yayi yana ɗaukar mukullin motar shi. "Muje to." Daga nan suka fita a ofishin da Company gaba ɗaya, kowa a motar shi suka tafi, Alhaji Tukur a gaba Alhaji Mamman a baya yana binshi. A wani unguwa ya tsayarsu mai suna AJARI. Unguwar tsofin kanurai malamai da kallo ɗaya ka musu kasan malaman tsubbu ne. Ƙofar wani gida ya tsaya ya sauƙa shima Alhaji Mamman ya sauƙo suka nufi cikin gidan tare da sallama. A soro suka tsaya aka sanar da wanda suka zo gurin shi kafin ya basu izinin shiga ciki suka shiga. ..... Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE 3. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... "A taimaka a duba mini mai ke faruwa da rayuwata da dukiyana cikin shekarar nan." Faɗin Alhaji Mamman bayan ya gama zubawa Malam Kalla bayanin abubuwan da suke faruwa dashi kwanan nan. Shuru ɗakin ya ɗauka, Mallam Kalla ya ja carbi kamar sau goma ya ajiye yace Alhaji Mamman ya ɗauka da yatsa ɗaya. Da bismillah ya ɗauka ya miƙa masa ya karɓa yana dubawa. "Karayar arziki yanzu ka sa a gaba Alhaji." "Kamar ya?" Alhaji Mamman yace cike da tashin hankali. "Wato kana ji ba, akwai wani abu da zai shigo rayuwarka da duk dukiya da abinda kasa a gaba ba zaka samu ba, dukiyar ka kuma sai ya ƙare tas. Ko kasan farar ƙafa da ake faɗa?" Cewar Mallam Kalla yana duban Alhaji Mamman da gumi kawai yake sharewa. "Na..na.. na sani." Ya faɗa da kyar yana haɗiye wani yawu mai zafi. "To shine zai shigo rayuwarka, kuma kayi gaggawar ɗaukar mataki." "Ta yaya Mallam?" Alhaji Mamman ya faɗa yana tunanin neman mafita. Nan Mallam Kalla ya ja carbi ya ajiye yace ya ɗauka da wani yatsar bana ɗazu ba. Hannu na rawa Alhaji Mamman ya ɗauka ya miƙa masa. "Matar ka tana ɗauke da juna biyu?" Mallam Kalla ya tambayi Alhaji Mamman. Gada kai yayi yace Eh. "To abinda zata haifa kayi nisa da ita ko shi, in kuma ba haka ba za kayi kuka da idanuwan ka. Shine kawai mafita." 'Innah lillahi wa innah ilaihin rajiun.' Kawai Alhaji Mamman yake furtawa jin abinda Mallam Kalla ya sanar dashi, yama rasa wani irin tunani zai yi. Godiya suka mishi ya cika shi da alheri kafin su tafi. Suna isa wajen aikinsu Alhaji Tukur ya dubi Alhaji Mamman da ya faɗa tunani. "Shawarar mai ka yanke?" "Na rasa mafita Alhaji Tukur. Ina son Sadiya ina son ƴaƴan mu, amma dubi abinda yake faruwa dani, kuma zai ci gaba da faruwa in har ta haifi abin cikinta." "To in baka shawara mana." Cewar Alhaji Tukur. Jin haka ya saka Alhaji Mamman juyowa yana dubanshi da kyau. "Ina jin ka?" "Ku zubar da cikin kawai ku huta." Girgiza kai yayi da sauri. "Ina son ƴaƴa na, ba zan iya bari Sadiya ta zubar da cikinta ba." "Dama shawara ce na baka, in kuma baku zubar ba to sai dai ku rabu. Ma'ana ka saketa kawai." Wani kallo Alhaji Mamman ya watsa masa. "Kai ma zancen ka ke, kasan dai ba zan iya sakinta ba." Kafaɗa Alhaji Tukur ya ɗaga alamar ko a jikinshi. "Shikenan dama Shawara ce. Yanzu dabara ya rage maka." Daga haka kowa yayi shuru, Alhaji Mamman ya ɗauki motarshi yana wucewa gida. A filin gidan ya samu yaranshi suna wasa, Rahma tana koyawa Hasiya keke, Muhsin yana gefe yana kallonsu yana musu tafi shima yana so. Suna ganin mahaifinsu da gudu suka mishi oyoyo ya ɗauki wannan ya sauƙe karshe suka wuce ciki yana ɗauke da Muhsin, Rahma da Hasiya suka bi bayan su. A falo ya tarar Hajiya Sadiya zaune taci kwalliya tana jiran shi, idon shi kai tsaye cikin jikinta ya kai ɗan wata biyar. Abin da bai taɓa faruwa a rayuwar shi ba yaji ya tsani cikin tun kafin a haifa. Idonshi ya kawar gefe yana zama. Rukayya data ganshi tayi ta miƙa hannu ya ɗauketa yana mata wasa. Lokacin ɗaya yaji yafi son dukkan sauran yaran akan abin da za'a haifa. Har dare Hajiya Sadiya ta kasa gane kan mijinta dan ko kallonta baya juran yi. Baccin kirki ya kasa dan nema kanshi mafita. Da safe yace ta shirya za suje asibiti bayan yara sun wuce makaranta. Tayi mamaki amma ba tayi magana ba ta shirya suka fita. Shawarar da Alhaji Tukur ya faɗa mishi na farko kawai zai ɗauka, ya saka a zubar da cikin duk da ya girma, dan yana son Sadiya ba zai iya rabuwa da ita ba. Ciki ne in ta zubar zata samu wani. Kai tsaye asibiti suka nufa bayan yankan kati suka shiga ganin likita. "Mai ke tafe daku?" Likitan yace yana duban su. "Cikin jikinta za'a zubar mata, tana shan wahala sosai, bayan laulayi mai zafi da take fama dashi." Baki sake Hajiya Sadiya take jin maganganun mijinta da suka ɗaga mata hankali. Tun da suke bai taɓa nuna rashin son haihuwar da take a kai a kai ba. Hasalima murna yake in ya samu labari. Shi ya hanata planning dan yadda yace yana son ƴaƴa amma yanzu rana tsaka yace a zubar mata da cikin jikinta da ya shiga watanni na biyar. Likitan kanshi yayi mamaki yana duban Hajiya Sadiya da ita hankalinta yana gurin Alhaji Mamman da ranshi haɗe kamar bai taɓa dariya ba. "Hajiya wata nawa ne?" Faɗin likita. "Wata biyar ne, amma ba zan iya zubar dashi ba likita. Abban su kayi hakuri amma bazan iya aikata haka ba." Hajiya Sadiya ta faɗa tana miƙewa tare da dafa kujeran da take zaune dan jiri da taji yana ɗibanta. "Sadiya koma ki zauna." Alhaji Mamman yace yana miƙewa tsaye. "Bazan zauna ba, akan me za kace in cire cikin jikina, in baka so ni ina so, kasan zunubin da zamu kwasa ko kasan wahalar da zan sha wajen fitar shi. Wata biyar fa ba kwana biyar ba." "To sai dai ki haifa a wani gidan ba gidana ba." Daga haka yasa kai ya fita. Itama Hajiya Sadiya ta ɗauki Rukayya dake kuka suka fita tama kasa lallashin yarinyar dan haushin ubanta ya shafeta. Samu tayi ya bar cikin asibitin da motar shi, taxi ta tara ta shiga ta nufi gida. A filin gida ta samu motarshi ta shiga falon ta same shi zaune da Muhsin saman cinyarshi yana mishi wasa, kasancewar ta barshi wajen mai aikinta. Wato dai cikin jikinta ya tsana ba ƴaƴan ba. Ko kallon in da yake bata yi ba ta nufi ɗakinta. "Ga takardar ki yana jiran ki, ki je wani gidan ki haifa sai ki ajiye ki dawo." Cak Hajiya Sadiya ta dakata da tafiyar da take yi ta juyo a mutuƙar razane dan jin furucin mijinta ta kasa cewa komai balle barin gurin. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai. "Kinji mai nace ai, ga takardar ki." Daga haka ya ɗauki Muhsin suka wuce ɗakin shi. Hajiya Sadiya da taji kanta yana juyawa ta ɗaga ƙafarta dakyar ta isa gurin da papern yake ajiye, hannu na rawa zuciyarta na bugawa ta ɗauka ta bude. Saki ɗaya ta gani jiki. Hawayen da bata san yaushe ya taru a idanuwanta ba suka zubo bisa kumatunta. Linkewa tayi ta wuce ɗakinta cikin zafin rai. Kayanta ta haɗa gaba ɗaya cikin manya manyan akwati biyu da jaka da duk Ƙadaranta da abun buƙata ta jawo ta fito falon. Rukayya ta ajiye yarinyar sai kuka take ta fice ta barta, itama tana hawayen barin ƴaƴanta. Ta san dai ko dansu zai dawo da ita. Kukan Rukayya shi ya fito da Alhaji Mamman daga ɗakinshi ga Muhsin na mishi kukan yunwa. Ganin yarinya ajiye tana kuka ya ɗauketa ya leƙa ɗakin Hajiya Sadiya ya ba babu ita ya duba bathroom bata nan ya fito ya shiga kitchen nan ba bata nan. Nan ya tabbatar ta tafi kenan. Mai aikinsu ya ƙira ta haɗawa Muhsin cornflakes kafin ta haɗawa Rukayya madaranta a feeder ta fara sha. Ya gwammace yayi wani auren matar ta kula mishi da yaran shi kafin Sadiya ta haihu ya dawo da ita, ya kyautar da abinda zata haifa. ... Hajiya Sadiya tafiya kawai tana hawaye da ta rasa dame zata ƙirashi. Na bakin ciki ko na barin ƴaƴanta da tayi. Kukan Rukayya na mata yawo a kunnenta har zuciyarta yake ratsawa. Ƙasar su nisa, gidan da in taje ma zata zauna take tunani, wacce take gabanta ta rasu balle bata jin babba da ita za taje ta zauna a wani gidan dangi ga ciki. Yayanta shima kanshi ta lura lallaɓawa yake da zaman gidan shi da matanshi ba za taje ta ƙara mishi nauyi ba. Waɗan can biyun kuma basa neman su balle tasan takamaiman inda suke. Gidan ƙawarta ta nufa Zarah. Zarah tayi mamakin ganinta balle da taji abinda yake tafe da ita ta shiga tashin hankali sanin soyayyar da yake tsakanin mata da mijin. "Ni yanzu ba wannan ba Zarah, gida nake so mai ko ɗaki ɗaya ko biyu in zauna zuwa nan da wani lokaci." Hajiya Sadiya tace da Zarah. "Ki zauna anan mana Sadiya, kin san dai Baban su Ƙasim ba zai hana ba." "A'a ina son zama ni ɗaya, ina son yin nesa da Abban su, bana son ya san inda nake." Shuru Zarah tayi can tace. "Hakane, amma mai zai hana ki bashi lokaci ya gane kuskurenshi, gani nake kamar ba a hankalinshi yayi hakan ba. Rana tsaka kace a zubar da ciki daga cewa a'a ka yanke hukuncin saki." Idanuwan Hajiya Sadiya ya cika da kwalla ta hanasu zuba. "Nima haka nake ji Zarah. Ni yanzu ki tashi mu fita nema ko kinsan wata da take bada gidan haya ko wani." "Na sani, Aisha ƙanwata mijinta yana bayarwa, gidanta yana layin bayan nan kin sani ai, muje in sanar da ita in mun ci sa'a mu sameshi a gida ma yanzu sai in haɗa ku dashi." To! Hajiya Sadiya tace Zarah ta ɗauki mayafinta bayan ta sanar da mijinta suka fita, a gidanta Hajiya Sadiya ta bar kayanta. Sun ci sa'a sun same shi yana shirin fita, bayan sun gaisa ta sanar dashi abinda suke so. "Kin ci sa'a akwai gida ciki da falo da ɗaki biyu a ciki, akwai mai ɗaki biyu daban daban, anjima da yamma sai muje ki gani ko yanzu." "Muje dai yanzu, in son samu ne, ina son mai ciki da falon." "To to shikenan muje." Daga nan suka fita gidan ba nisa sosai unguwar ba mutane sosai an fara gine gine sabon unguwa ne, gidan sabon gini ne an gina shi sabo anyi paint anyi wearing na wuta da komai. Ɗakuna biyu da falo sai kitchen da bathroom a waje da filin gida wadatacce. Ta gani ta yaba ya mata kyau, anan ta roƙeshi zuwa gobe zata kawo kuɗin ko yau da yamma. Yace ba komai duk yadda tayi shikenan. Gidan Zarah suka nufa, Ƙadaranta na ɗan kunne da sarƙa na gwal ta ɗauka da Alhaji Mamman ya bata a haihuwar Rukayya. Tace zata siyar ta biya gidan haya, Zarah bata hanata ba ta goyi bayanta. Kasuwa ta nufa ta sayar bisa kuɗi mai yawa dubu ɗari da sittin aka bata kuɗin ta dawo bata biya gidan Zarah ba ta wuce gidan ƙanwarta A'isha ta bata dubu tamanin kuɗin shekara ta bawa mijinta in ya dawo zuwa gobe zata zo ta karɓi mukullin gidan ya ajiye mata. Sai karfe huɗu na yamma ta samu nutsuwa tana zaune cikin ɗakin da Zarah ta saka mata kayanta ta kawo mata abinci da sai lokacin ta samu cin abincin rana. Tana cikin ci tunanin ƴaƴanta ya faɗo mata, tasan Rukayya zuwa yanzu zata nemi abincinta, ta mata yayen lokaci ɗaya. Ga Muhsin ma da duk inda zata shiga a gidan yana binta har sai ta mishi wayo in zata fita, Su Rahma da Hasiya sun dawo a makaranta zuwa yanzu. Wa zai cire musu kaya ya basu abinci? "Allah raya min ku." Tace tana share hawayen daya gangaro a fuskarta. Ta san mijinta bashi ɗaya bane da zai aikata abubuwan nan cikin ƙanƙanin lokaci. ... Alhaji Mamman Bashir da yaran shi, bai san raino da wuya ba sai da Rukayya ta fara kukan yunwa tana son abincinta, ga Muhsin, ya shiga ya fita ya rasa ya zai yi da taimakon mai aiki ta samu ta sake bata kunu ta goyata tayi bacci. Haka Muhsin dawowar su Rahma ya shiga cikin su ya sashi mantawa da komai. Su Rahma da suka tambayi Mami aka ce musu ta tafi unguwa. Daren fa kasa bacci su kayi dukkansu dakyar suka samu yaran su kayi bacci. Mai aiki ta kwana da Rukayya da cikin dare ta dinga mata kuka dakyar ta sake bata kunu ta sha ta koma bacci kafin ita ma ta samu bacci. Alhaji Mamman Bashir da duk yana jin kukanta ya kasa fita ya tashi ya fara zagaye ɗakin shi yana safa da marwa. "Aure zan yi." Shine amsar da zuciyarshi ya bashi kafin ya zauna bakin gado yana dafe kan shi. .... Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE 4. Pharty Bb Wattpad phartybb. .... Kwana biyu da haka Hajiya Sadiya ta koma gidanta ta fara rayuwarta. Ta sayi kayan abinci da sauran kuɗin hannunta da duk abinda take buƙata. Sai daga baya take jin haushin barin Rukayya da tayi, ji take kamar taje ta ɗauko ta amma tana gudun wulaƙanci gurin Alhaji Mamman. A lokacin ta fara tunanin sana'ar da za tayi dan taimaka kanta. Ƙadarorinta na filiya biyu ta sai da ta fara saro atamfa da taimakon Zarah ta fara tallata makota. ... Bangaren Alhaji Mamman bai sanar da kowa abinda ke faruwa ba sai Alhaji Tukur, har yake ce masa ya nema mishi matar aure da zata kula masa da ya'ya. Budar bakin shi yace. "Ga ƙanwata Jidda, shekarun mijinta goma da rasuwa taƙi aure har yanzu tana da yaro ɗaya Muhammad Al-ameen." "Jidda dai ɗaya." Faɗin Alhaji Mamman sanin ya ganeta. "Eh ita dai, ka gwada sa'ar ka ko zaka samu shiga. Nima kuma zan mata magana." "To shikenan Allah yasa ta yarda, ka fara gabatar da kai na a gurinta sai in je mu dai-daita dan bana son a ɗauki lokaci." A haka suka rabu Alhaji Tukur yana komawa gida ya sanar da mahaifiyar shi yadda su kayi, ya ɓoye mata cewa ga dalilin daya rabu da matar shi, ce mata yayi kawai yana neman auren Jidda. Mahaifiyarsa bata kawo komai a ranta ba tace yaje ya samu Jidda ya sanar da ita duk yadda su kayi shine dai-dai. Bayan fitar shi ne daga gurin mahaifiyar shi ya sameta har ɗakin ta ya sanar da ita yana da magana da ita. Bata kawo komai a ranta ba ta amince suka fita falon da ba kowa suka zauna. "Kin san abokina Alhaji Mamman Bashir ɗan Gombe ko?" Da mamaki Jidda tace. "Eh na sanshi Yaya, wani abun ya same shi." "A'a ko ɗaya, auren ki yake nema, babu dole in har bakya so, amma dai kiyi tunani bisa maganar nan, ɗazu mu kayi magana dashi yace shi dagaske yake yi idan har kin amince baya son a ɗauki lokaci." "Ni kuma Yaya? Haba dai, dan Allah yayi hakuri, ina zan kai shi ga mata ga yara, kamar kwanaki naji kana cewa matar shi ta haihu. Balle ma ni bazan yi aure ba in bar Muhammad Al-ameen." Jidda tace tana haɗa rai. "To ai sun rabu da ita Hajiya Sadiyan, kuma kin san dai babban mutum ba zai iya zama ba mace ba, to shine yace in nema mishi mata ni kuma naga gaki nan mai zai sani neman wata." Jin furucin shi ya bawa Jidda mamaki tace. "Rabuwa dai? To ina yaransu?" "Suna gidan, mai aiki ne take kula dasu." Sam har cikin ranta bata ji daɗin abin ba na rabuwar Alhaji Mamman da matar shi Hajiya Sadiya ba, kamar yadda take samun labari suna zaman lafiya ta san da kyar in ba wani abun bane ya faru babba da zai raba su. Lallai akwai wani abun a ƙasa tsakanin miji da matar da har cikin ranta taji tana son sani da kuma jihadin mayar da ita ɗakinta kan ƴaƴanta. "Tunanin mai ki ke Jidda, ko dai bakya ra'ayi." "Na amince." Ta bashi amsa. "Dagaske? Yazo kenan?" Kai ta ɗaga mishi, yayi mamaki yaji farin cikin jin ta amince da wuri. ... Cikin wata ɗaya daya wuce iyaye suka san maganar auren Jidda da Alhaji Mamman Bashir. Lokacin da yayun Alhaji Mamman suka samu labarin fitar Sadiya sun mishi faɗa sosai duk da ba wanda yasan dalilin rabuwarsu. Anan babban yayansu yace maza ya maida matarshi a fili yace to amma a zuciyar shi bai shirya yanzu sai lokacin daya ɗauka ya cika. Biki saura sati biyu Alhaji Mamman Bashir ya gyara gidanshi, ya maida shi babba bangaren amarya daban, nashi daban sai na Hajiya Sadiya da shima ya gyara mai aikinsu babbar mace ita take zaune taci gaba da lura da yaran da suke ganinta tamkar kakarsu. Sun shaƙu da ita musamman Rukayya. Ita take shirya su suje makaranta ta musu wanka ta musu girki da komai na buƙata dan ta san suna buƙatar kulawa, kuma ko ba Hajiya Sadiya zata iya riƙe mata yara dan kyautatawa da take mata itama lokacin da take gidan. Sati biyu wata ranar Jumma'ah aka ɗaura auren Alhaji Mamman Bashir da Amaryar sa Jidda Lawal sati ɗaya da biki ta tare a gidan mijinta. Ƙin ɗauko ɗanta Al-ameen tayi ta barshi a gaban mamarta. ... Zarah da take zuwa ganin yaran Sadiya a ɓoye ko ita Sadiyar bata sani ba daga ita sai Innana mai kula da yaran Sadiya. Anan ta samu labarin auren data kasa barin abin a ranta ta je gidan Hajiya Sadiya ta sanar da ita. Har hawaye Hajiya Sadiya tayi tana zaune ga katon ciki haihuwa yau ko gobe. "Yara na Zarah, kar su haɗu da kishiyar uwa mai mugun hali ta cutar min dasu. Gashi ban san wani hali suke ciki ba musamman Rukayya." Ita kanta Sadiya taji ba daɗi amma ba yadda za tayi da ta goge wannan shafin Ƙaddarar tsakanin su, bata da wani taimakon da zata basu sai na addu'a. Zuwanta gidan jiya ta haɗu da Jidda a yadda ta ganta ta sake mata fuska suka gaisa fatan ta har cikin zuciyarta haka take. Dogon numfashi ta sauke "Addu'a za kiyi ta musu inshaAllah babu abinda zai same su, mahaifinsu kuma shima addu'ar yake buƙata Allah dawo dashi hankalin shi ya dube ki." Kai kawai Hajiya Sadiya ta girgiza tana share hawayenta. Tunanin halin da yaranta suke take. "*" Amarya Jidda da angonta rayuwarsu suka kafa cikin amince dan Jidda akwai nutsuwa da hankali. Binshi take sau da kafa tana son bashi lokaci kafin ta fara abin da ya kawota. Alhaji Mamman Bashir kuwa da ikon Allah sai ya zama babu abinda ya ƙara faruwa daga ɓangaren aikin shi zuwa kasuwanci. Ƙoƙarin shi yanzu ya samu kuɗaɗen shi ya dawo da yayi asarar su. ... Tun cikin dare take jin ciwon mara duk tasan alamun naƙuda ne, haka ta daure tayi ayyukan ta da basu da yawa. Wajen karfe goma ta lallaɓa tayi wanka ta zurma dogon riga dakyar dan ciwon yana cinta dauriya kawai take. Tana gamawa kayan haihuwa ta ɗauka ta nufi gidan Zarah ta samu bata nan ta bar sallahu kafin ta wuce asibiti. Kafin ta isa ciwo sai gaba yake tana isa dakyar ta ƙarasa cikin asibitin kai tsaye labour room ta nufa suna ganinta suka karɓeta suka taimaka mata ta shiga ciki. Sosai ta wahala a nakudar har dare bata haihu ba. Zarah data samu labari ta iso amma an hanata shiga haka ta zauna ta jira a waje. Sai gabanin asuba naƙuda ya taso mata gadan gadan da taimakon Allah ta samu ta haifi ƴarta mace ƙatuwa. Hamdala tayi ta jerowa da godiya ma Allah kafin a gyarata da yarinya, ganin lafiyarsu dukka ƙalau da safe ƙarfe tara aka basu sallama. Duk yadda Zarah tayi suje gi idanta ƙi tayi suka wuce gidanta. Wuta Zarah ta hura ta ɗaura ruwan wanka ya tafasa ta wanke yarinya kafin Hajiya Sadiya tayi, Zarah ta kawo mata abincin da tasa mai aikinta ta dafa ta aiko. Bayan taci ta sha shayi data haɗa mata ta samu shayar da babynta da sam bata da kuka sai bacci take, bayan ta gama ta kwanta gefenta itama bacci ya ɗauketa. Ganin sunyi bacci Zarah ta koma gida ta samu mijinta ya dawo ta sanar dashi, kuɗi ya bata yace ta musu siyayyar ɗan abun buƙata ta karɓa ta mishi godiya kafin ta shiga kasuwa. Abubuwan da tasan mai jego take buƙata ta siyo da su kayan baby. Data koma ta nuna Sadiya tayi murna tace ta saka mijinta da ita wahala. "Ba komai wallahi Sadiya, duk garin nan kin manta ke kika fara zama kawata." Murmushi kawai tayi tace. "Hakane, nima akwai wasu kuɗaɗe hannuna sai a saya abin yanka." "Shikenan zan samu wani ko Audu mai gadi in bashi ya sayo." Anan suka yanke maganar Hajiya Sadiya ta bata kuɗin ta bashi ya sayo. Washegarin kuwa ya cika alƙawari ya kawo. Kafin satin makota duk sun leƙo mata barka haka har ranar suna gidan da ɗan mutane. NURATU shine sunan data sakawa jaririyar ta. Da Zarah taji haka ta tambayeta. "Mai yasa kika zaɓi sunan nan Sadiya?" "Haske ce a gare ni in har mahaifinta ta zame masa duhu." Hajiya Sadiya ta bawa Zarah amsa tana kallon ƴarta dake bacci abinta. Jinjina kai Zarah tayi tace. "Allah raya Nuratu. Amma mahaifinta ya kamata ya san da haihuwarta." "Ameen, bana buƙata, kamar yadda baya buƙatarta nima bana buƙatar ƴata ta san shi." Kai kawai Zarah ta girgiza tana mamakin ta ya uba lokaci ɗaya yace baya son cikin jikin matarshi bayan duk son da yake ma matarshi da sauran ya'yan sa. Haka aka watse Hajiya Sadiya taci gaba da kula da yarinyarta ... "Ya ku kayi da Sadiya ta amince?" Girgiza kai Zarah tayi tana miƙa ma mijinta ruwa a cup. "Wallahi taƙi yarda, amma ni kam a nawa ganin ka je ka samu Alhaji Mamman Bashir kuyi magana dashi, mai yiwa mu samu takamanmen amsa ko dalilin da yasa yayi sakin." "Hakan za'a yi kawai. In ba haka ba bana jin daɗin ganin Sadiya zaune ita ɗaya a gida daban anya ma can gidansu an sani." "A'a bata sanar dasu ba har yanzu." "Kinji irinta ko, wata huɗu fa yanzu gashi yanzu har ta haihu ta gama idda, ya kamata ƴan uwanta su sani. Amma bari muji ta bakin Alhaji Mamman ɗin in zai mai da aurensu." "Shikenan sai yanda ta yiwu." Cewar Zarah tana ajiye abincin data zuba mishi. ... Washegarin mijin Zarah yana fita bai shiga shagon shi ba ya biya shagon Alhaji Mamman bai zo ba sai da azahar anan ya bar sako ya tafi. Azahar yanayi ya dawo ya samu yana nan. Bayan sun gaisa ya kawo masa maganar da ya zo da ita. "Dama jira nake ta haihu mu maida auren mu." Cewar Alhaji Mamman cike da murna abin ya bawa Alhaji Audu. "To Allah yasa hakan shine alheri, sai mun jika." "InshaAllah za kaji ni cikin satin nan, zan zo har gida na same ka." Alhaji Audu yayi makin maganganun Alhaji Mamman, da ya koma gida ya sanar da matar shi Zarah ita ma tayi mamaki kuma tayi murna jin yadda Alhaji Mamman ya amince da wuri zai mai da Hajiya Sadiya, fatan ta itama Sadiya ta amince ta koma kan yaranta. ... Fitina Rukayya ta saka mata sai ta goyeta, haka ta saɓata a baya ta goya tana yawo da ita a falon. Yaran gaba ɗaya sun fi wuni a gurinta dan yadda take zuwa har ɓangaren su ta ƙirasu suzo nata, jansu take a jiki sosai tun basa sakewa har suka saba da ita ya zamana watarana har bacci suke a bangarenta. Rahma tana koyawa Hasiya rubutu a takardunta na makaranta, gefe kuma ɗanta Al-ameen ne da Muhsin suke kallon American film. Al-ameen kasa zama yayi a gidansu Jidda ya dawo gurin mahaifiyar shi. Alhaji Mamman ya amince zai riƙeshi har ya cigaba da biya mishi kuɗin makaranta da yake aji biyu na sakandare. Sallamar Alhaji Mamman cikin falon ya sa yaran barin abinda suke yi suka tareshi da gudun su, ya ɗaga wannan ya sauƙe yana tambayar su ina Rukayya suka ce tana kitchen da Amma. Sunan da suka sakawa Jidda kenan kamar yadda su kaji yaronta yana ƙiranta dashi. Samunta yayi tana aikinta ga Rukayya a bayanta ya tsaya baƙin kofar kitchen din. "Sannu da aiki." Yace mata ta juya haka Rukayya ma jin muryar Abbanta ta juya, sai ta fara kukan za taje gurin shi tana haɗa sunanshi da hausar da ta fara yi. "Bazan sauƙe ki ba, tun ɗazu ki ka kafa min fitanar sai na goye ki, yanzu kuma kina kallon Abba kice in sauƙe ki." "Ki bari in kin haifi naki mana kiyi ta goyon yadda ki ke so, sauƙe ta dan Allah." Sarai ta gane nufinshi dan ta lura ya sa mata ido cikin kwanakin nan, basar maganar tayi ta juyar kanta tana sauƙe Rukayya da gudu tayi gurin Abban ta ya ɗauketa suka fita a kitchen ɗin. Da dare suna shirin kwanciya Alhaji Mamman ya sako zancen da yake son mata amma yana son ta fahimce shi. "Rukayya ta samu ƙanwa." Kallonshi Jidda tayi ya ƙara da cewa. "Kin san dai da ciki na rabu da Mamin su Rahma, to ta sauƙa lafiya, shine nake son maida auren mu, banyi hakan dan ɓata miki rai ba ki fahimci ne Jidda." .... Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE 5. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... "Na amince." Amma Jidda tace da sauri da hakan ya bawa Alhaji Mamman mamaki. Murmushi tayi. "Ka na mamaki ko? Wallahi ina son sanar da kai amma na rasa hanya, kamar yadda ba zan iya barin ƴaƴana ba haka bana son kowacce mace ta fita ta bar ƴaƴanta. In sanar da kai gaskiya, na aureka ne dan in sasanta tsakanin ka da matar ka, kuma yanzu allahamdulillahi tun da kanka ka kawo maganar, na amince ka dawo da matar ka." "Allah miki albarka, ya sauƙe ki lafiya." Ya furta cike da farin ciki. Shi kam ya godewa Allah da yake azurta shi da mataye nagari. Ameen! Amma Jidda ta amsa dashi ganin ya gano dai ciki ne da ita na wata ɗaya. Da safiyar ranar asabar ba aiki bayan ya gama abinda zai yi a gida ya fita kasuwa, shagon Alhaji Audu ya nufa kai tsaye ya sanar dashi zuwa yamma in anyi sallar la'asar zai kai shi gidan da Sadiya take. Hakan kuwa a kayi ana gabatar da sallar la'asar suka wuce gidan kai tsaye bayan sun biya gida Zarah sun ɗauki Zarah ta musu rakiya. Nuratu ta ɗan mata rigimar ciwon ciki da take ji, ta goyeta tana jijjigata ta samu tayi bacci tana ƙoƙarin kwantarta a falon saman katifar ta taji sallamar Zarah. Da murmushi ta amsa ƙasa ƙasa dan kar Nuratu ta farka. "Sannu da zuwa Zarah." "Sannu Mamin Nuratu, bacci take ne." "Eh wallahi ciwon ciki ke damunta." Hajiya Sadiya tace tana dan bubbuga bayan Nuratu. "Allah kawo sauƙi tare da baƙi muke suna waje." "Baƙi kuma? Su waye?" Hajiya Sadiya tace da mamaki. "Eh kimin izinin shigowa dasu, sai ki gansu." "To shigo dasu." Hajiya Sadiya ta ce tana ɗaukar mayafi ta rufe jikinta dashi. Fita Zarah tayi ta musu iso zuwa cikin falon, tare da sallama suka shiga. Jin sallamar Alhaji Mamman ya saka Hajiya Sadiya duban shi cike da mamaki ta bishi da kallo. "Kinyi mamakin ganina Sadiya ko?" Faɗin Alhaji Mamman yana duban Sadiya da ta haɗa rai. "Sadiya!" Alhaji Audu ya ƙirata dashi ta kai kallonta gurin shi tana gaishe sa dan tana ganin girman shi. "Sadiya ga Alhaji Mamman ya dawo gare ki a karo na biyu yana neman auren ki in har kin amince, bamu san dalilinsa na ƙin cikin ki ba da har ya janyo saki tsakanin ku, amma yanzu tunda kin haifa ya dawo zai aure ki sai ku koma gidanku, fatan za kiyi hakuri ki yafe masa ki karbi buƙatar shi." Kan Hajiya Sadiya ƙasa. "Ba zan koma gidan shi ba sai ya faɗa mini dalilin da yasa ya ƙi abin cikina lokaci ɗaya, kuma sai ya amince itama yana sonta zai bata kulawa kamar sauran yaran." Sai lokacin Alhaji Mamman yayi magana. "Sadiya ki fahimce ni, yarinyar nan ba alheri a tattare da ita, in har zan rayu da ita gida ɗaya to arzikina da komai nawa sai na rasa, farar ƙafa ne da ita." Kallon da Hajiya Sadiya take watsa mishi ya sashi kasa ƙarasa maganar ya dakata. "Ba zaka rayu da ita gida ɗaya ba. Kuma ka ke son in koma gidan ka? Ta ya kenan hakan zai faru?" Hajiya Sadiya tace da zuciyarta ya fara tafasa tsabar baƙin ciki jin maganganun shi. "Dama cewa nayi zan kaita gidan marayu, sai muna zuwa muna dubata, ko in kaita can Nijar gurin yaya Muhammad." Dariyar baƙin ciki Hajiya Sadiya tayi tana girgiza kanta. "Ba inda ƴata za taje ina raye, ka je kawai duk ranar da ka shirya karɓar mu ni da ita mu zauna a gidan ka sai ka zo." "Sadiya ki fahimce ni, duk ..." "Bana buƙata Alhaji Mamman." Tace tana ɗaga mishi hannu alamar yayi shuru ta ɗauki Nuratu data farka tana ƙananan kuka ta wuce ciki da ita tana jijjigata. Zarah da mijinta duk sun kasa cewa komai dan Alhaji Mamman ya basu mamaki jin furucin shi. Uba ya haifi ƴa ya tsana tun kafin tazo duniya. To wanene ya faɗa masa wannan maganar da har ya amince dashi ya yarda ya tsaka tsanar yarshi cikin zuciyarsa. Wannan alamar jahilci ne da yake buƙatar ƙarin haske na ilimi. Hajiya Sadiya lallashin Nuratu tayi ta koma bacci ta kwantar ta ta fito suka ci gaba daga inda suka tsaya. Duk yadda Alhaji Audu yayi Alhaji Mamman ya fahimci wannan abun jahilci ne kasawa yayi, sam ya toshe kunnuwanshi ya kasa gane gaskiya. Abun ya ƙonawa Hajiya Sadiya rai daga ƙarshe tace. "Alhaji Mamman bana ganin akwai sauran zaman aure a rayuwar mu. Rabon ya'ya ne ya haɗa mu kuma na haifesu, Allah raya su, dan haka kawai Allah haɗa kowa da rabonsu." "Kar kice haka Sadiya." Zarah tace da sauri ganin ƙawartan zata yanke hukunci bisa dokin zuciya. Bata kulata ba ta wuce ɗaki ta rabu dasu. Ta tsani Alhaji Mamman da duk abinda ya shafe sa, zata goge babin shi a rayuwarta ta kama mutuncinta kanta ta kula da ƴarta ta bata tarbiyya. Sauran yaran Allah raya mata su, in da rabon tana ganinsu in sun girma su neme ta. Haka Alhaji Audu da matarshi suka fita cikin juyayin wannan lamarin. ... Da daren Amma Jidda ta tambayi Alhaji Mamman ya su kayi da Mamin su Rahma dan ko ɗazu Muhsin ya tambaye ta yaushe Mami zata dawo. "Mun rabu da Sadiya gaba ɗaya, tace ba zata dawo ba." Da sauri Amma Jidda ta kalle shi. "Mai yasa? Dan Allah fa, bata tunanin yaranta." "Ko ɗaya, ki bar maganar kawai." Alhaji Mamman yace yana canza hiran dan shima ya tsani hiranta yanzu. Jikin Amma Jidda sanyi sosai ta shiga damuwa jin abinda mijinta yace. Alƙawari ɗaya ta ɗaukarwa kanta sai ta haɗa uwa da ƴaƴanta. ... Sati biyu da faruwar haka Aunti Zarah tayi tafiya da bata samu damar zuwa duba su Rahma ba. Amma Jidda tayi ta zuba idanu tun lokacin tana jiran zuwan Aunti Zarah shiru, ta damu sosai gashi bata san gidanta ba balle ta je. Mami Sadiya kuwa hankalinta ta maida kan sana'ar ta na sai da atamfofi da Allah ya albarkacin sana'ar ana saya ba laifi duk da rabi ma bashi ne. Ana biyan albashi aka tattara mata kuɗinta tayi sari da rabin kuɗin rabi kuma ta fara shirin tafiya Nijar dan sanar dasu halin da ake ciki. Kwana biyu ta gama shiryawa abinta da ƴarta suka ɗauki hanya. Yamma lis ta isa kai tsaye gidan Yaya Muhammad ta sauƙa kowa yayi mamakin ganinta da jaririya suna cewa bata sanar dasu ba, sai dai tayi murmushi. Bata samu sun keɓe da Yayanta ba sai da safe taje gaishe sa ya karɓi Nuratu yana gani ya tambaye ta sauran yaran da mai gidanta. Kan Mami Sadiya ƙasa tace. "Mun rabu Yaya, yau wata takwas kenan." "Rabuwa kuma Halima? Garin yaya? Mai ya faru yayi zafi? Kuma shine bani da labari? A ina kike zaune yanzu?" A nutse Mami Sadiya ta sanar dashi komai tana yi yana girgiza kansa har ta gama. "Shikenan Halima Allah yasa haka shi yafi alheri. Ita kuma Allah rayata kici gaba da addu'a Allah zai kawo mafita. Su Rahma kuma Allah rayasu." Ameen ta amsa dashi yana ta mata nasiha a ƙarshe ta sanar dashi tana son saida kayan gadonta ta ƙara jari dan kula da kanta da ƴarta. Bai hanata ba yace zai saka Shanun a kasuwa zuwa yamma in aka saya zai kawo mata kuɗin. Godiya ta mishi kafin ta mishi sallama. Kwanan Mami Sadiya biyu ta dawo bayan ta karɓi kuɗin gadonta hannun yayanta da take jin shi tamkar Mahaifinta, sauran biyun kam tama fara mance kamarsu dan tun kafin aurenta suka bar ƙasar. Dawowarta da sati ɗaya ta saro kaya masu yawa daga atamfofi, kayan yara, da takalma. Yau aka kawo mata kayan cikin falonta ta baza tana kallo tana ware masu tsadar da mai ƙaramin kuɗi. Gefenta Nuratu tana wasa da kafafunta, yarinyar ƴar wata huɗu tayi wayo abinta, duhu take yi yarinyar irin na mahaifinta dan bata biyo hasken yayunta da suka ɗauka na ta ba, amma kallo ɗaya zaka mata kasan tafi su kyau duk da jaririya ce, irin baƙaƙe masu kyau ne da ake ƙira chocolate beauty. Sallama taji daga waje cikin baƙuwar murya fita tayi tana leƙawa taga mace da zata haura shekaru talatin gefenta yaranta ne Muhsin da Rahma da Hasiya tana ɗauke da Rukayya data maƙale mata. Ihu Rahma da Hasiya suka saka ganin Mamin su suna yin kanta da gudu ta rumgumesu cikin farin ciki tana miƙa Muhsin hannu alamar yazo ya tsaya yana son tuna inda ya santa, sai da tace. "Muhsy na babana." Kafin yaron ya kwace hannunshi cikin na Amma Jidda ya faɗa kan Mamin shi. Murmushi kawai Amma Jidda take ganin burinta ya fara cika, ganin uwa da ƴaƴan sun haɗu ta dalilinta. "Sannu da zuwa." Mami tace tana miƙewa tsaye ganin ta barta tsaye. Murmushi kawai tayi ta girgiza mata kanta tana miƙa mata Rukayya, yarinyar taƙi zuwa. "Ki barta kawai ta jima ne, a hankali zata tuna ni. Mu shiga ciki." Bayan sun zauna yaran suka nufi gurin Nuratu Rahma ta ɗauketa Hasiya na ƙoƙarin karɓar ta. "Zaku jefar ta ai. Kawo ta nan mu ganta." Yaran basu so ba suka miƙa Amma Jidda ita ta karɓeta tana gani, Rukayya dake gefenta itama ta zauna alamar a bata yarinyar. "Mami waye ce?" Cewar Rahma tana leƙa fuskar Nuratu. "Ƙanwar ku ce, sunanta Nuratu." "Allah rayata, bamu samu zuwa ba sai yanzu." Amma Jidda tace. "Ameen, sai dai har yanzu ban shaida ki ba." Shuru Amma Jidda tayi ta rasa ta ina zata sanar da ita hakan ya bawa Mami Sadiya gaskata abinda yazo ranta. "Auntyn su Rahma." Kai Amma Jidda ta ɗaga tace. "Tun da naji labarin rabuwar ku hankalina ya kasa kwanciya, wallahi kinji na rantse ban aure Abban su ba dan ina son shi sai dan in haɗa kan zuri'ar ku. A rayuwata ina tausayin ya'ya da mahaifiya take barinsu ta fita. Tun bayan da ki kayi nesa dasu Rahma, bayan kwana biyu sai Aunti Zarah tazo ganinsu ko kin sani ko a'a, kwana biyu bata zo ba sai jiya, shine na tambayeta gidanki dan ina kawo miki yaran kuna samun lokaci kuna gaisawa da juna, kar gaba sun girma su manta dake musamman yanzu Rukayya da take ƙarama zata iya mantawa da komai daya shafe ki, hakan kuma ba zai min daɗi ba. Munyi magana da Abban su yace min yazo kunyi magana amma abun bai yi ba, sam banji daɗi ba, dan Allah Mamin Rahma kiyi hakuri ki koma kan ya'yan ki, ki duba yadda su kayi kewan ki, suna buƙatar ki kusa dasu." Tabbas in har yadda Amma Jidda ta nuna mata tana son ƴaƴanta har cikin ranta ne to ta yarda ko bayan ranta zata kula mata dasu. Gashi nan taga alama yadda suka sake da ita, da bata basu fuska ko kusa ba za su zo inda take ba balle har tayi tunanin kawo mata su. "Dan Allah Mamin su kiyi tunani akai." Sai lokaci Mami Sadiya ta buɗe baki. "Kiyi hakuri amma zama ya ƙare tsakani na da Alhaji Mamman. Ga yarana na baki amana kici gaba da kula dasu, duk lokacin da kike so zaki iya kawo su in gansu bazan takura miki ba." "Dan Allah kar kice haka ki duba yaranki." Amma Jidda tace alaman roƙo. Mami Sadiya ta duba yaranta da sun zagaye Nuratu da take cinyar Amma Jidda hatta ɗanta Al-ameen da ido kawai ya zuba mata yana kallonta. Tana son kasancewa tare dasu har girmansu da aurensu amma abinda mahaifinsu yake so ba za tayi ba. Gwara su su rayu da mahaifinsu da ta kai Nuratu gidan marayu ta girma. "Ba zai yiwa, kici gaba da kula dasu ɗa na kowa ne." Shuru Amma Jidda tayi ta rasa mafita, Mami Sadiya ta miƙe ta kawo musu ruwa da abinci data girka dan kanta. Sun ci sosai yaran anan Rukayya ta sake jikinta ta shiga cikin su, tun tana bin Mamin ta da ido har ta ganeta ta fara binta duk inda za taje haka Muhsin ma dama shikam ta saba. Abin yayiwa Amma Jidda daɗi ganin yaran sun sake da mahaifiyar su shiga su fita tare. Awansu huɗu suka fara shirin tafiya. Anan Mami Sadiya ta ɗauka yarantan takalma iri ɗaya gaba ɗaya da kayan yara kala ɗaɗɗaya. Rahma, Hasiya, Rukayya nasu iri ɗaya sai na Al-ameen da Muhsin iri daya. Duk yadda Amma Jidda ta hanata ƙi tayi tace su riƙe. Godiya su kayi tayi yaran suna murna. Sai da aka zo wajen tafiya suka ce sam sai sun tafi da Nuratu, Rukayya har da kukanta akan a bar ta, dakyar dai aka shawo kansu su ka tafi gida bayan alƙawarin ƙarya da aka musu zasu zo gobe. Mami taji daɗin ganin yaranta, ta yaba Amma Jidda da ƙoƙarinta ganin tana kula da yaranta, ta san zata basu kulawa har girmansu, sai lokacin taji hankalinta ya kwanta. ... Gidan Alhaji Mamman Bashir. .. Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE 6. Pharty Bb. Wattpad phartybb. Littafin MADUBIN GOBE littafin kyauta ne❤️. ... Gidan Alhaji Mamman Bashir. Da dare da Alhaji Mamman ya samu labarin zuwan yaran gurin Mami Sadiya faɗa yayi tama Amma Jidda da abin ya bata mamaki har tana cewa. "To wai naga mahaifiyarsu ce, taya zaka rabasu, duk yadda kayi fa ɗa baya gudun mahaifiyar shi." "To ki kiyaye ni, na faɗa miki kar ki ƙara kai su tunda ita taƙi bin shawarar da na yanke ta rabu dasu." Shuru kawai ta mishi tana juyar kanta, haushin maganganun shi take ji. Sannan ƙasan ranta tana son sanin menene Alhaji Mamman ya nemi Mami Sadiya taƙi yi har ta ke ganin gwara ta bar yaranta. Fushin kwana biyu yayi ya sauƙo dan tace ba zata sake kai su ba amma tasan ƙarya ta mishi kawai dan ya daina fushi da ita. .... Tun daga ranar Amma Jidda a ɓoye take kai yaran gurin Mamin su shima sai a hutun ƙarshen mako. Sannan ta gargadesu karsu ƙara sanar da Abban su. Mami Sadiya tana jin daɗin haka dan yana ƙara mata shaƙuwa da yaranta haka kuma da yar uwar su Nuratu da in ta gansu ta dinga miƙa hannu su ɗauketa dan ta gane su. Mami Sadiya tana ƙoƙarin kyautata Amma Jidda dan yadda ta riƙe mata ƴaƴa, kullum sai ta mata godiya sai dai Mami Sadiya tayi murmushi tace ta daina gode mata. "To wai so kike duniya ta zage ni ace na raba uwa da ƴaƴanta, a'a ni kam bana so gwara ki zama shaidana ko da an zage ni." Murmushi kawai Mami tayi tace. "Bama mai zagin ki sai yabon ki." Aunti Zarah da ta samu labari itama tayi farin ciki tana yabawa Amma Jidda dan da wuya a samu matar uba mai irin halinta. A cikin haka Amma Jidda ta haifi ƴarta nace mai sunan mahaifiyarta tana ƙiranta Walida **** Bayan shekaru goma. Abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwar su da suka saka shi cikin kundin Ƙaddarar su. Yara sun girma su Rahma sun girma shekara goma sha huɗu ba wasa ba, Hasiya mai bi mata da ita suna aji uku na sakandare, Muhsin yana ajin ƙarshe na Firamare sai Nuratu da Walida ajinsu ɗaya suna aji huɗu sai Rukayya data fi su da aji tana aji biyar, Muhammad Al-ameen ya wuce makarantar gaba da sakandare wato digiri a garin Zaria wajen dangin mahaifin shi da yake zama a can gaba ɗaya ya koma. Tun lokacin da Nuratu ta isa shiga makaranta Amma Jidda ta haɗa da Nuratu ta sakata tare da ƴarta Walida. Mami tayi mamaki dan tana da burin sakata makarantar sauran yaran sai gashi ta shammace ta. Godiya ta mata tace sai ta bari za taci gaba da biya mata kuɗin Amma Jidda tace babu komai. Yaran sun shaƙu da juna musammam matan, Rahma, Hasiya, Nuratu da Walida, duk ƙanƙantar su baka bambanta ya'yan waye. Tun lokacin da Rahma da Hasiya suka fara girma suka fahimce Mami da Abban su basa tare. Kasuwanci da Mami Sadiya take yi Allah ya sanya masa albarka sai bunƙasa yake, gidan da take ciki ta sayeshi dukka a hannun mijin ƙanwar Zarah ya zama halal ɗinta, ta ƙara gyarashi. Tsakanin ta da Zarah har yanzu suna mutumci. Alhaji Mamman kuɗi ya zauna masa sosai, kasuwanci ya buɗe, Company sai samun cigaba yake, hankalinshi kwance yake rayuwarshi ya riga ya mance da wata Sadiya balle ƴarta da har yau bai san sunanta ba ko kamanninta. Shekaru na ta tafiya abubuwa na ta faruwa, wani da daɗi wani babu, wani mai kyau wani marar kyau, shekaru sun ja kwanaki sun wuce sun zama satikai, sati ya shuɗe ya zama watanni. .... Leaders Private School. Makaranta da yayi tashe ake ji dashi a cikin garin Damaturu jihar Yobe. Yaye ɗalibai ake na ajin ƙarshe da suka kammala karatunsu suka fita da sakamako mai kyau. Ciki har da Rahma da Hasiya da suka gama tare. Sunyi kyau abinsu sai murna suke zasu kammala sakandare, Rukayya Nuratu da Walida da suma sun zama ƴan mata sai murna suke ganin yayunsu musamman Nuratu data kasa rufe bakinta murmushi kawai take zubawa da yake saka kumatunta lotsawa yake ƙara fito da kyan fuskarta. Taro a kayi sosai da hotuna Alhaji Mamman yazo shi da Amma Jidda, ana zuwa yin hoton iyali dukka suka haɗu waje ɗaya har Nuratu. Bayan an ɗauki hoton Alhaji Mamman yana lura da Nuratu da duk inda yaran su kayi tana binsu tare suke. "Wacece wannan? Kawar ku ce?" Ya tambayi yaran. Kafin Amma Jidda tayi magana Rukayya tace. "Ƙanwar mu ce fa Abba, ta gidan Mami." Kallonta yayi sosai baƙace bata da hasken fatar sauran amma tafi su kyan fuska sosai. Sai lokacin ya kalli kamannin Mami Sadiya a fuskarta dan sauran da shi suke kama ban da Rahma da itama da Mami ta ke kama hatta farin fatarta na Mami Sadiya ne. "Ke zo nan!" Yace a tsawace yana haɗa rai. Nuratu da ta san da ita yake ta tashi ta taho gurin shi ta tsugunna kanta ƙasa. Rankwashi ya kai mata da taji zafin shi har tsakar kanta tana sosa gurin idonta cike da hawaye. "Menene haɗin ki da yarana, baki da alaƙa dasu ko kaɗan dan haka ki daina binsu kar ki shafa musu farar ƙafa. In ma uwarki ta turo ki kije ki sanar da ita haka. Idan na ƙara ganin ki dasu sai na ɓata miki rai. Tashi ki bar min guri." Sum Nuratu ta miƙe ta bar gurin tana share hawayenta. Bata san mai ta mishi ba tun tasowarta ta nemi sanin wanene shi Mami ta kasa sanar mata sai ita da kanta ta san matsayin shi gareta. Yau kaɗai ta fara ganinshi duk yadda suke faɗan sunan Abban su amma ya faɗa mata wannan maganar. Lokacin data fara tasowa ta ɗauka mahaifinta daban sai da tayi wayo ta gane suna duk iri ɗaya suke amfani dashi na uba. Data tambayi dalili Maminta ta sanar da ita shine mahaifinta tace mata eh ta kasa sanar da ita dalilin da yasa baya basa tare ko bata tare da ƴan uwanta. Duk yadda take son zuwa gidan su Rukayya hanata Mami take sai dai su suzo wataran har kwana suke in Abban su yayi tafiya. To ita kuwa mai tama Abban su ya tsaneta. Mai yasa ba'a barinta taje gidan itama kamar sauran yayunta tunda shine Abban ta. Cikin class ta shige tana cigaba da kukanta ba wanda ya biyo bayanta domin a gaba Abban su ya sasu ya musu faɗa sosai akan su daina mu'amala da ita ƙarshe ma ya ɗauke su suka wuce gida kowa yana tunanin halin da ya bar Nuratu. Amma Jidda tafi kowa shiga damuwa dan gani take bata kyauta mata ba, tare ake ɗaukarsu a sauƙeta a gida kafin sauran yaran. Bata san ta ya zata tafi gida ba yau. Nuratu kam kukanta tasha har aka fara watsewa ta leƙo ganin wasu har sun fara tafiya ya sata fara duba su Rahma, duban duniya tayi bata gansu ba ta hakura ta zauna zaman jiran azo a ɗauke su. Har aka gama watsewa babu alamar su Rahma. Nuratu duk tsoro ya kamata sai lokacin tunanin kar fa Abban su ya ɗaukesu yazo kanta haka ta miƙe ta fara tafiya. Tafiya nisa tsakanin makaranta da unguwar su. Haka taci tafiya sai wajen huɗu saura ta isa. "Lafiya kika daɗe haka?" Mami ta tambayi Nuratu da isowarta ta kwanta mata shame shame a ƙasa. "Da kafa na dawo Mami." "Da kafa dai? Ina Amma ɗin? Ko bata je ba." "Amma taje tare da Abba, Mami yau naga Abban mu dasu Aunti Hasiya yake kama. Mami wai mai nama Abba ne? Ban taɓa kallon shi ko mishi magana ba, sai yau muka haɗu amma bai tare ni ko kallona a matsayin ƴarshi ba sai hantara da faɗa. Anya Mami shine mahaifina? In kuma shine mai na mishi haka ya tsane ni?" Mami da take sauraron Nuratu ta gama maganarta kafin tace. "Shi ya haife ki kamar sauran, wani camfi nashi can ya haddasa mishi tsanar ki, amma ba komai kar ki damu komai zai wuce ki zame masa MADUBIN GOBE. Dalilin da yasa ma bana son kije gidan su Rahma na san hakan zai faru, kinga kuwa yanzu sai ki kiyaye." Kai kawai Nuratu ta ɗaga tana son fahimtar maganganun Maminta ganin haka Mami ta miƙe tana cewa. "Kar kisa damuwa a ranki ko tunani, ki tashi kiyi sallolin daya same ki a hanya." Tashi tayi tayi sallah taci abinci kasa aikin komai tayi dan ciwon kafa daya fara damunta. Da dare sai da Mami ta mata gashi da ruwan ɗumi dan ciwo ta shafa mata man zafi. Tun daga ranar Nuratu ta kauracewa duk abinda zai haɗata da Abban ta dama ba su taɓa haɗuwa, har lokacin ƙasan ranta tana son sanin dalilin da yasa ya tsaneta. Tsakanin ta da ƴan uwanta sai dai su zo dan an bada hutun makaranta kuma islamiyya ba ɗaya suke ba. Alhaji Mamman duk shekarun da aka ɗauka ya tsammaci Amma Jidda taji maganar shi sai yau da ya saka yaran gaba yana musu faɗa tace ita take kai su ba laifinsu bane. Faɗar da ya mata har yana mata barazana da igiyar aurenta ta tsorata sosai ta bashi hakuri. **** Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta da ake shi ya farkar da ita daga tunanin abin da ya shuɗe ta sake labulen window ɗakin ta juya tana bada izinin shiga. Nuratu ne ta shigo ɗakin cikin sauri fuskarta alamun damuwa. "Menene kuma?" Mami ta tambaye ta. "Mami Aunti Hasiya ba lafiya tana asibiti. Yanzu Aunti Rahma ta sanar dani." "To ko dai labour ne." "Ni ma shi nake tsammani. Dan Allah muje mu dubata." Nuratu tace kamar za tayi kuka. "To ɗauko mayafinki muje." Ai bata jira Mami ta gama magana ba ta fita da sauri, a falo ta tarar Mami suka fita. A motar Mami suka tafi, ita take jan motar Nuratu a gefe ta buga uban tagumi. Wayarta yana ta ƙara ta kasa ɗauka. "Ba ki ji ana ƙiran ki ba ki ɗauka mana. Haihuwa na biyu fa, ni ba dan ke ba maa ba zan zo ba, in ta haihu na je." Kallon fuskar wayar tayi taga Dr Awwab ne yana ɗaya daga cikin mutanen da suke da muhimmanci a rayuwarta. Kasa ɗauka tayi ta tura mishi saƙon zata ƙira shi anjima ta kashe wayar. Bai ƙiranta ba bayan ya karanta saƙon. Bayan sun isa asibitin sai kuma ta kasa shiga. "Muje ko." Taji Mami tace ta girgiza kai tana kama jikinta waje ɗaya, fahimtar haka ya saka Mami cewa. "Ki kwantar da hankalin ki babu komai, muje." "Ba zan iya shiga ba Mami." Nuratu tace da taji kanta yana neman juyawa, anan asibitin wasu abubuwan suka faru da ba zata iya fahimtarsu ba a lokacin balle yanzu. "Ke fa kika dame ni muzo." "Mu koma gida kawai." Tace tana kwantar kanta ta rufe idanunta zuciyarta yana bugawa da sauri sauri, tsoro ya fara shigarta kamar kullum in ta tuna ko tayi tozali da abun da ya shafe rayuwarta na baya. Shurun mintuna biyu Mami tayi tana dubanta hakan yasa ta kasa shiga ta kasa komawa gida. Wayarta ta ciro ta ƙira Aunti Rahma take tambayarta tazo, Aunti Rahma ta sanar da ita Hasiya ma ta haihu tun ɗazu an sallamesu yanzu zasu wuce gidanta ba sai tazo ba. Bayan sun kashe wayar Mami taja motar suka bar harabar asibitin. Sai da ta hau titi tace. "Nuratu buɗe idonki mun bar asibitin." Sai lokacin ta ji hankalinta ya fara kwanciya ta buɗe ido tana kallon titi. Mami ido kawai ta zuba mata lokaci zuwa lokaci ganin yanayinta ya canza. Har yanzu ta kasa cire abinda ya faru a ranta, tasan dama da wuya hakan ya kasance, tayi ƙoƙari ma na ganin ta dawo da walwalarta kamar baya duk da wani lokacin tasha kamata cikin tunani ko damuwa. Girgiza kai tayi cikin ranta tana mata fatan ƙarin lafiya. .... Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE 7. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... "Nuratu?" Da kyar ta buɗe idanunta da suka fara canza launi ta dubi Mami dake zaune gefenta bayan sun shigo gidan ta zube saman kujerun falon tayi kwanciyarta. Hannu Mami ta saka ta kamo hannuwan Nuratu da ta bita da ido. "Bana hana ki saka damuwa a ranki ba, bana son ciwon ki ya tashi dan Allah ki daure ki kawar da komai a ranki, ki duba halin da muka shiga dalilin haka, Nuratu in bana ganin dauriya tattare dake bana jin kwanciyar hankali a rayuwa ta, sai in ga har yanzu baki gama warkewa ba. Duk da nasan kina ƙoƙari, ki daure ki ƙara. " Mami ta ƙarasa maganar cikin ƙarayar murya. Murmushi Nuratu tayi ta damƙe hannun Maminta. "Mami kai na yake ciwo, amma babu komai." "Shikenan to tashi muje ganin babyn Hasiya, waya sani ma ko sabon miji na samu." Mami tace tana dariya dan kawarwa Nuratu damuwarta. Itama dariyar Nuratu tayi tana ƙoƙarin danne damuwarta, ta tambayi Mami. "Sun koma gidane?" "Eh muje can, in zaki zauna mata zuwa bayan suna sai ki ɗauki kaya." To Nuratu tace ta miƙe ta shiga ɗakinta ta ɗauki kayanta cikin kits ƙarami ta fito suka fita. ... Gidan har ya fara cika da mutane suka karɓi baby suna gani, babynta mace kyakkyawa fara tasha kayan sanyi farare. Bayan Mami ta miƙawa Nuratu babyn ta hana kowa karɓa. Mami bata jima ba ta koma gida ganin su kansu sun isa kula da mai jego, ga Aunti Rahma ga Walida da Ameera mai bin ta ga Nuratu da Aunti Rukayya. "Ki kula da ita Rahma dan Allah. Ki tabbatar tasha maganinta a kan lokaci." Mami take faɗawa Aunti Rahma kafin ta wuce. "Mami menene? Wani abun ya faru." Aunti Rahma tace cikin damuwa. "Kusan hakan ne, lafiyarta ƙalau ta dawo daga gidanki amma zuwanmu asibiti ya kusan dawo mana da aiki baya, ki kula da ita kar ku barta cikin damuwa." "InshaAllah Mami komai zai wuce." Aunti Rahma tace cikin tausayin ƙanwarta da wannan ƙaddara ta gifta a rayuwarta da nasu gaba ɗaya. Tun da Mami ta tafi Rahma ta saka ido akan Nuratu har dare da ta lura ta kasa walwala gaba ɗaya ta zauna ta zuba jaririyar ido, Walida da Aunti Hasiya sai hira suke Ameera da Rukayya sun koma gida. Da ido Aunti Hasiya ta nunawa Aunti Rahma Nuratu ta ɗaga mata kai alamar ta ganta. "Ƙanwata!" Aunti Rahma tace tana zama gefen Nuratu da ta juya a ɗan firgice ganin Aunti Rahma ne ya sata sauƙe ajiyar zuciya. "Wa kike tunani? Yaya Al-ameen ko sauran samarin ki?" Ɓata rai Nuratu tayi tana yamutse fuska. "Babu kowa ciki. Ni fa ba samarina bane, dukkan su mutunci muke, kuma kun sani." "Hakane kuma fa." Aunti Rahma tace tana murmushi tare da ɗaga kai. Turo baki Nuratu tayi ganin Aunti Rahma ta maida abin wasa. "Tashi kiyi wanka ki kwanta, ga kuma can maganin ki yana jiranki." Miƙewa Nuratu tayi ta shiga wanka, data fito ta saka kayan baccinta tasha maganinta kafin ta kwanta gefen baby. Wayarta ta ɗauka ta ƙira Dr Awwab tunawa da ya ƙirata ɗazu. "Har na cire rai da ganin ƙiran ki Noor." Dr Awwab ya amsa mata dashi bayan ya amsa sallamarta. Murmushi Nuratu tayi. "Ina Hanan? Ya aiki?" "Lafiyar ta lau, tayi rigama ta gaji tayi bacci duk ta ishe ni in kawota gurin ki." Har lokacin murmushi bai gushe saman fuskarta ba dan tana girmama Dr Awwab. "Allah sarki My Baby, yaushe zaka kawo ta?" "Duk lokacin da kike da free har Daddyn Hanan na son ganin ki ba ita ɗaya ba." Shuru Nuratu tayi kamar ba zata amsa ba kafin ta sauƙe numfashi. "Ni dai Hanan zan gani." "Ni fa?" Yace mata da sauri har ya bata dariya ta ɗan dara. "In na samu time zan sanar da kai." "Godiya muke ranki daɗe, ya jiki fatan babu wani matsalar?" "Babu komai sai godiyar Allah." "To allahamdulillahi haka ake so, Allah ƙara lafiya." Ameen ta amsa dashi su kayi sallama ta kashe wayar tana kwanciya. Tun tana jin hiransu Aunti Rahma da Hasiya har bacci ya ɗauketa. "Tausayi take bani Aunti Rahma." Aunti Hasiya tace tana kallon Nuratu dake bacci. "Addu'a za muyi ta mata, Allah zai yaye mata komai." "Hakane Allah kawo mata sauƙi." Ameen Aunti Rahma ta amsa mata dashi tana shirin kwanciya ita ma dan ba zata koma gida ba ta bar yaranta da mai aikinta ta kula dasu, babansu yayi tafiya. Gidan bai rabu da mutane ba har ranar suna Baby taci sunan kakarta ta wajen uba, dangin mijin Aunti Hasiya sun yi murna sun haɗa mata kayan goyo duk da haihuwa na biyu ne. An yi taro lafiya an watse, ƙannenta sun zage sun mata aiki, Mami ma ta haɗa nata kayan ba laifi, Amma Jidda ma haka da ita ta tsaya kan komai. Haka Abban su ma ya aiko mata kuɗi masu yawa. Washegarin Aunti Rahma da Rukayya da Walida da Ameera suka tattare komai suka gyara mata gida kafin su watse dan an nema mata dattijuwa da zata zauna mata. *** Sati ɗaya da haka Nuratu suka fara final exam, ta maida hankali tana karatu sosai bangare ɗaya kuma tana ƙoƙarin ganin ta kawar da duk damuwar da yake damunta, ga maganinta da bata bari ya wuce ta tana sha akan lokaci. Hakan yanama Mami daɗi ganin tana ƙoƙarin kauda komai a ranta ta maida hankali kan karatunta. Sati biyu da kwanaki suka gama sai fatan samun sakamako mai kyau. Agajiye lis ta dawo gidan cike da murnar yau ta kare exam ɗinta. Cikin falon ta shiga ganin wanda yake zaune ya sa murmushin fuskarta ya ɗan gushe ta ɗan haɗa fuska. Shi ko ido kawai ya saka mata komai zai faru da Nuratu ba zai taɓa daina sonta ba, ba zata taɓa tashi daga Nuratun daya sani ba ta koma wata Nuratun da ƙaddara ta faɗa rayuwarta ba. "Ƴan makaranta." Yace mata ganin bata da niyar mishi magana. "Ina wuni Yaya Al-ameen." Ta faɗa ganin irin kallon da Mami ta watsa mata. Bata jira amsar shi ba ta wuce ɗakinta. Duk fa ta gane take taken su musamman shi da yasha furta mata yana sonta kuma ta amince tun kafin ƙaddara ta faɗa rayuwarta. Babu wani ɗa namiji a rayuwarta yanzu ko zuciyarta da zata iya so har ta aura. Matsalar rayuwarta da damuwar da take ciki ma kaɗai ya isheta balle wani namiji da sanadin shi duk wani farin cikin rayuwarta ya tarwatse. Ta tsani duk maza in ka cire mutane ukun da take ganin mutuncinsu suka taimaka rayuwarta sai shi da take ganin girmansa matsayin Yayanta. Babu aure a tsarin rayuwarta burinta tayi ta karatu ta gama ta samu aikin yi ta kula da maihaifiyar ta data sha wahala a kanta tun haihuwarta har girmanta, a dalilinta duk wani kadara nata ta siyar dan ta sama mata rayuwa mai kyau mai inganci, a dalilinta taƙi zaman aurenta, a dalilinta ta rabu da ƴaƴanta a dai-dai lokacin da suke buƙatar ta. Kwanciya tayi ta ƙi fita tana jiran ya tafi. .... "Bari in ƙirata ku gaisa." "A'a Mami ki barta in ta gama ta fito babu matsala zan jira ta." Yaya Al-ameen yace duk da yana son ganinta da sauri dan yana da gurin zuwa. Mami bata jira mai yake faɗa ba ta shiga ɗakin Nuratu. "Kin zo kin kwanta, kin san dai dan ke yake zuwa gidan nan." Rai Nuratu ta ƙara haɗawa. "Ni Mami kin san dai.." "Na san me? Tashi dalla kije. Al-ameen ɗin ne zaki fara nuna hali. In bakya son sauran maza ai shi baya cikin su saboda ya nuna miki so da kauna duk da abinda ya faru bai gujeki ba." "Kiyi hakuri Mami bari in je." Nuratu tace ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta fita. A falon ta sameshi zaune ta zauna tana sake gaishesa. "Na takura miki ko na hanaki hutawa." Kai Nuratu ta girgiza cike da kunya dan tana jin nauyin shi ita kanta bata san lokutan da take mishi haka ba. So take ya gane yanzu da baya ba ɗaya bane. Wannan wata Nuratu ce da duniyarta ta canza mata. Ba zata iya cigaba da soyayya dashi ba, ƙaddara ta hana hakan baya gani ne. Koma waye yanzu bata da lokacin ɓata mishi lokaci domin aure baya tsarin rayuwarta. "Ƙanwata!" Yaya Al-ameen ya ƙira ta ganin ta faɗa tunanin da baya so. Murmushi yaƙe tayi tace. "Na'am Yaya Al-ameen. Ya gida dasu Amma Jidda?" "Lafiyarsu ƙalau, kina bani wahala ƙanwata har yanzu kin ƙi bani lokaci muyi magana. Karatu kullum shine uzirin ki, yanzu kuma gashi kuna exam in ma baku gama ba." Kan Nuratu ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa bashi amsa dan yasha neman lokaci suyi maganar da bata da amsar shi. "Ke nake saurara ƙanwata. Zan wuce wani guri nace bari in shigo miki in miki zuwa bazata." "Za muyi magana ta waya ko WhatsApp." Amsar da ta iya bashi dan neman mafita ma kanta. Murmushi yayi yana miƙewa. "Shikenan Allah yasa in ga canji, zan wuce sai munyi magana." Itama miƙewa tayi tana bin bayan shi lokacin da ya nufi kofa. "Nagode ka gaishe da Amma dasu Walida." "Za suji." Yace ya fita kafin ta koma falon ta samu Mami ta fito zata wuce ɗakinta Mami ta bata umarnin ta zauna za suyi magana. Zama tayi ta san dai kullum maganar ɗaya ne ta bashi dama da ita kam bata jin zata iya haka. "Mai yasa kike bawa yaron nan wahala ne Nuratu, kina ganin dai shekarunsa sun kai aure har sun wuce shekara talatin da biyu, dalilin ki har yanzu ya kasa hakura yana binki kina mishi wulaƙanci." Idanun Nuratu cike da hawaye take duban Mami data haɗa rai. "To ni kam Mami na nuna mishi bana so ya yake so in mishi." "Auren ne ba za kiyi ba?" Kai Nuratu ta ɗaga hawayema zuba saman kuncinta. "Babu aure cikin tsarin rayuwata Mami, ba zan yi ba." "Saboda abin da ya faru?" Mami ta tambayeta itama da dauriya take ganin hawaye saman fuskar ƴartan da tasan dole in ta tuna abinda ya faru da ita sai ta zubar da hawaye balle kuma maganar aure. Ajiyar zuciya ta sauƙe. "Ba zan miki dole ba Nuratu, amma duk da abinda ya faru aure shine mutuncin ki, ki cire komai a ranki ki cigaba da rumgumar Ƙaddarar ki. Shi Al-ameen ɗin ya san abin da ya faru kuma ya yarda a haka zai aure ki to ki godewa Allah, kiyi ta addu'o'i in da alheri tsakanin ku Allah tabbatar muku in kuma babu Allah muku canji mai alheri. Share hawayen ki Noori." Murmushi Nuratu tayi jin maganar Mami na ƙarshe dan ta kwantar mata da hankali. Nasiha ta mata kamar kullum dan yadda da ƙaddara duk da itama Mami dauriya take. Sai lokacin Nuratu taji nutsuwa ta samu cin abinci taci ta wuce ɗakinta ta kwanta dan jiran ƙiran sallar magriba. Yaya Muhammad Al-ameen shi ya fara nuna mata menene so, ɗa namiji da ta fara saka sonshi cikin zuciyarta da rayuwar ta. Har yanzu tana son shi tana kaunar shi amma Ƙaddarar da ba zata iya goge shi ba ya rabata dashi. Ba auren shi ne ba za tayi ba abinda zata tarar gaba take tunani, balle bata tsammanin danginshi zasu barshi ya auri mace irinta, duk da Amma Jidda ta nuna itama tana son auren su. Tunani ta faɗa na abinda ya wuce. *** Shekaru biyu kenan da gama makarantar su Rahma da Hasiya suka shiga makarantar gaba da sakandare dan ci gaba. Suna aji biyu a lokacin samari suka dame su dan son aura ganin haka Alhaji Mamman ya ce su fitar da mazajen aure. A ciki suka zaɓa ko wanne ya turo aka saka ranar auren su. Daga lokacin Alhaji Mamman ya fara shirin aurar da yaranshi, kaya ya musu na gani na faɗa dan arziki shi sai bunƙasa yake. Mami sai a bakin Amma Jidda taji da yaranta, dan su Rahma har gidanta suka kawo samarin da zasu aura suka gaisheta. Ta yaba da tarbiyyarsu dukkansu biyu ta musu addu'a da samun zaman lafiya. Lokacin Rukayya tana ajin ƙarshe na sakandare, Walida da Nuratu suna aji biyu. Muhsin yana aji ɗaya a digiri nashi. Amma Jidda ta sake haihuwar ƴa mace Ameera. Biki saura sati yan uwa daga Gombe sun zo dangin Alhaji Mamman haka Amma Jidda tayi nata gayyar dan wasu ma sun ɗauka itace mahaifiyarsu. Anan Amma Jidda ta samu Mami ta roƙeta ta bar Nuratu ta zo gidan dan ayi biki da ita dan ta ɗinka mata har anko na aure da dinner party. Mami bata so ba amma ganin itama Nuratu tana so ta barta akan ranar wuni maza ta dawo dan tana guje mata haɗuwa da Abban ta gudun wulaƙanci ko zagi. Amma Jidda itama ta san nufin Mami dan haka ta mata alƙawarin ba abinda zai faru. Nuratu a gidan Alhaji Mamman. Like. Comments. Share. MADUBIN GOBE 8. Pharty Bb. Wattpad phartybb. ... Tun da Nuratu ta koma gidan Abba da tun girmanta da wayonta bata taɓa takawa ba, basa zama yau lalle gobe wanke kai har aka shiga Washegarin ranar ɗaurin aure. Ƴan uwan Alhaji Mamman da basu santa ba wannan ya ƙira ta su gaisa wannan ma ya ƙirata haka yan mata suka dinga janta a jiki. An ɗaura aure da dare aka kai amare Washegari a kayi buɗan kai da safe da dare aka shirya dinner party da suka gabatar da hall. Hall yayi kyau an ƙawatashi da ado amare da angwaye sunsha kyau, ƙannen amare sunsha anko iri ɗaya cikin lace nasu peach color ba suyi wani tarkacen kwalliya ba sun sha kyau. Taro yayi taro aka ƙira amare da ƙannensu su zo su taka rawa, Rukayya da Nuratu da Ameera kaɗan kaɗan suke tasu rawar banda Walida da take tikar rawa kamar ba gobe. Idonshi saman kanta tun da ya shigo hall ɗin yana zaune a baya, kallonta yake ya ganeta sarai, yayi mamakin yadda tayi tsayi ta zama budurwa, har yanzu tana nan yadda take chocolate color sai ma ƙara glowing da take. Murmushi kawai yake zubawa ya miƙe ya nufi wajensu, ƙannen shi suna ganinshi suka hau murna, anan ya ciro bunch na ƴan ɗari ɗari ya fara zuba musu da hakan ya basu karfin gwuiwar yin rawa har su amare suka fara takawa kaɗan kaɗan. Nuratu da kallo ɗaya ta mishi ta ɗauke kanta ganin idonshi cikin nata dan ta ganeshi itama, ta fara ƙoƙarin barin gurin ganin hankalinshi yana kan ƙannen shi. Wani haushi ne ya kamata za ta bar gurin ya juyo kanta ya fara juye mata kudi da bai san nawa bane. Cak ta tsaya sai taji kamar ta nutse ganin idon kowa yana kansu ban da yayunta dasu Walida. "Ci-gaba da rawarki ƙanwata." Yace yana rankwafowa kusa da ita taja baya kaɗan tana kallonshi yayi mata murmushi da taji numfashinta yana neman ɗaukewa dan ya daki zuciyarta ba kaɗan ba. "Zan je in zauna." Tace tana barin gurin da sauri har tuntuɓe ta kusa yi dan yadda ta kasa saita kanta. Zama tayi tana dafe kirjinta da hannu hankalinta ya kai gurinsu ta ga ya nufo gurinta ta miƙe da sauri ta fita. Wajen ajiye motoci ta isa tana zama. Mai yake damuna? Ina ruwana da shi da zai dame ni? Ta tambayi kanta tana waige waige jin ƙamshin turare kusa da ita. Bata ga kowa ba amma jikinta ya bata akwai wani kusa da ita. Haka aka gama taron aka fara fitowa dan wucewa, sai lokacin taji daɗi sai kuma ta tuna yau ne ƙarshen kwananta gidan Amma Jidda dole ta koma gida komai dare. Motar dasu Rukayya suka shiga ta shiga ya maida su gida. Tana jin suna ta zuba surutu har Walida tana sakota cikin zance ta kasa tanka mata burinta su isa gida ta haɗa kayanta komai dare ta tafi gida. .... Kayanta ta gama haɗawa tsaf ta ɗauki mayafinta da jakanta. Rukayya dake canza kaya zuwa na bacci riga da wando tana kallon ƙanwartan. "Wai dan Allah Nuratu tafiya za kiyi ba zaki jira gobe ba? Karfe tara fa ta wuce. In dan Mami ne zata miki uzuri ai." "A'a ni kam Sister na mata alƙawari yau zan koma, kinga gwara na tafi dan wataran ta barni zuwa gaba." "Hakane amma ai auren ƴan uwanki ne, Allah zan haɗa ki da Amma in ba zaki zauna ba." "Dan Allah ki barni. In ban samu Ilyas ba zan dawo, muje ma ki rakani neman shi." Nuratu tace ta miƙe tare da akwatin ta, Rukayya ta ɗauki mayafinta suka fita. Filin gidan suka fara duba shi baya nan suka fito waje da dai dai lokacin motar Abban su ya faka. Take cikin Nuratu da Rukayya ya duri ruwa. "Shiga motar nan in a buɗe take." Rukayya tace a ruɗe tana nunawa Nuratu motar dake gefenta. Ai bata gama magana ba Nuratu ta faɗa motar da sauri dan ta mugun tsorata da ganin Abban su da har ta mance rabon data ganshi. Ta tsane shi haushinsa take ji, ta rasa mai ta mishi ya tsaneta da har ta jawo dalilin rushewar auren shi da Maminta. Rukayya dake waje tayi mutuwar tsaye haka aka wangale masa get ya shiga kafin taji hankalinta ya kwanta ta matsa kusa da motar tana buɗewa taga abin mamaki. Nuratu da Yaya Al-ameen da suka tsaya kallon kallo cike da mamaki, tayi mamakin ganin shi. "Shikenan Yaya Al-ameen sai ya mai dake gida, kin huta ma." Rukayya tace tana ƙoƙarin rufe kofar Nuratu ta riƙe. "Ki bari kawai zan nemi taxi." "Dalla koma ki zauna." Rukayya tace tana hararanta da hasken kwan lantarki ya bawa Nuratu daman ganin Rukayya. Al-ameen da sai lokacin yayi magana ganin zata fita yace. "Ƙanwata kimin alfarma na kai ki gida Please." Nuratu bata so haka haka ta hakura ta zauna Rukayya ta rufe motar tana cewa ta gaishe da Mami. Tafe suke shuru ba wanda yake ma wani magana sai ƙira'ar Alqur'ani da yake tashi kaɗan kaɗan har suka shiga kwanan da zai sada su da layinsu kamar daga sama taji yace. "Mai yasa kike gudu na?" Kallonshi tayi da sauri hankalinshi yana ga titi itama ta juyar da kanta gefe ta daure tace. "Babu komai. Ni ba gudun ka nake ba." Kai ya ɗaga bai ce mata komai ba har suka isa ƙofar gidan Nuratu zata buɗe ta fita taji a kulle ta juya ta kalleshi shima ita yake kallo. "Kimin izini in shiga in gaishe da Mami?" "Ai ba sai ka nemi izini ba tun da ka saba zuwa dama." Tace tana ɗauke kanta. "A da ba, ban da yanzu." Yace yana buɗe mata kofar ta fita da sauri tare da kayanta. Kulle motar yayi shima ya bi bayanta cikin gidan. Mami na tambayar ta waya kawota cikin daren nan yayi musu sallama. Amsawa Mami tayi Nuratu ta wuce ɗakinta. "Al-ameen yaushe a gari? Ya makarantar ko har yanzu bai ƙare ba." "Bai ƙare ba Mami da saura inshaAllah." "To Allah taimaka, ya taron biki." "Allahamdulillahi. Zan wuce dama na ga dare yayi shine nace bari in kawota bai dace ta hau taxi ba." Yace ya miƙe tsaye. "To na gode ka gaishe da gida." To ya amsa mata dashi ya fita kafin ta miƙe ta nufi ɗakin Nuratu dake ware kayanta masu datti. "Fatan anyi taro lafiya?" Nuratu barin abinda take yi tayi ta juya tana kallon Mami dake tsaye bakin kofa. "Lafiya lau Mami, kin ga gidajensu masu kyau abinsu, sunyi ƙoƙari sosai." "To Allah basu zaman lafiya." Mami tace tana fita cike da farin ciki jin ƴaƴan ta sun samu kwanciyar hankali. Bayan Nuratu ta gama kimtsa kayanta ta ware mai datti ta gabatar da sallar isha'i ta kwanta. Abubuwan daya faru tsakanin ta da Yaya Al-ameen shi ya faɗo mata rai, daga kallon da yake mata zuwa maganganun da yake furta mata duk ya canza salo, sun jima basu haɗu ba. .... Auren su Rahma da sati biyu tayi ƙoƙarin mancewa dashi ta bar abin a matsayin yanayine ya shigar dasu haka dan har lokacin kallon da yake mata ya kasa barin zuciyarta sukuni sai kallonshi take a idon zuci. Tun jiya asabar take shirye shiryen komawa makaranta dan Litinin zasu koma inda zasu shiga ajin ƙarshe na sakandare. Gugan kayanta take a falon Mami bata nan ta tafi gidan Aunti Zarah. Sallamar Yaya Al-ameen taji da sauri ta amsa tana mamakin zuwan shi dan har ta cire tsammanin zai dawo duk da yanzu ma bata tabbatar dan ita yazo ba. Amsawa tayi ya shigo daga ciki ya zauna saman kujera, ta gaishe sa ya amsa yana cewa. "Ina Mami?" "Ta tafi gidan Aunti Zarah." Nuratu tace tana kashe iron ɗin ta miƙe ta kawo mishi ruwa ta ajiye. "Zauna magana za muyi dama dan ke nazo." Tana shirin barin gurin taji yace. Zuciyarta ne ya amsa mata ta zauna ɗayan kujera babu mutsu tana sauraran shi. Nutsuwa yayi dan yana son ta fahimce zancensa ta masa fassara mai kyau. "Nuratu!" "Na'am." Ta amsa jin yadda ya faɗa sunan sai taji yafi kowa iya faɗar shi. "Ina so muyi magana na fahimtar juna amma ban san ya zaki ɗauka ba, Please ki fahimce ni bada wasa nazo ba ko na faɗa miki haka ba. Idan har baki da wani a zuciyar ki, ni Muhammad Al-ameen ina sonki zan aure ki in har kin amince. Ba abin gaggawa bane ko takura, na san kina makaranta kuma sai kin gama za kiyi aure may be ma sai kin shiga wani, ina so ne kawai ki san da zamana in da hali a karɓi tayin soyayyata Please Nuratu." Ita kuwa in dai haka ake cewa shine so to tabbas tana jin Yaya Al-ameen a cikin ranta da zuciyarta tun bayan rabuwarsu, amma kunyar amsar da zata bashi take ji, lokaci ɗaya tace ta amince taji ba zata iya ba. "Ke nake saurara ƙanwata, kar kice min dai akwai wanda ya rigani dan ba zan hakura ba sai in da karfina ya ƙare." Ya ƙarashe maganar yana murmushi. Cike da kunya Nuratu ta murmusa tana girgiza kai tare da saka hannu ta rufe fuskarta. "Ka bani lokaci zan yi tunani." "Wani tunani kuma da lokaci. Nagode miki kawai da kika karɓa tayi na, inshaAllah zaki sameni cikakken masoyi na har abada. Ba zan miki alƙawura ba amma zan yi ƙoƙarin baki farin ciki da kyautatawa a rayuwarmu mu biyu inshaAllah." Ita dai Nuratu kunyane ya kamata kanta ƙasa tana tana wasa da yatsum hannunta, murmushi mai tsada kwance saman fuskarta, maganganun da Yaya Al-ameen yake faɗa mata suna shiga cikin zuciyarta suna samun guri ɗaya bayan ɗaya. Yaya Al-ameen ganin bata da niyar masa magana ya sashi tashi dan barinta tayi aikinta. "Zan tafi gida, nima cikin satin nan zan koma makaranta." "Allah kiyaye." Ta iya faɗa mishi ya fita cikin farin ciki. Nuratu kasa cigaba da aikinta tayi tana juya maganarshi cikin ranta, lokaci zuwa lokaci sai tayi murmushi. Ashe haka so yake. Take tambayar kanta. Har Mami ta dawo ta lura ƴartan tana cikin farin ciki da nishaɗi, bata tambaye ta ba ta bar abin a ranta. Ranar Litinin su Nuratu da Walida suka koma makaranta sun zama manyan yan mata. ... Bayan sati biyu. Wata ranar Alhamis Mami ta samu baƙoncin Amma Jidda. Kamar yadda take taran ta haka ta tareta cikin farin ciki suka gaisa ta kawo mata ruwa da abinci data girka. "Har yau kin ƙi zuwa ganin ɗakin yaran nan." Murmushi Mami tayi. "Zanje ai ke nake jira kimin jagoranci." "Haba dai ai baki sanar dani ba, ni ma sai shekaran jiya naje duk na ɗauka kinje sai da naje suke sanar dani." "Zan je dai amma ba yanzu ba." "To Allah kaimu. Wata magana nake so mu yi Mamin Rahma." Amma Jidda tace tana canza hiran. "Ina jinki, fatan dai lafiya?" Cewar Mami. "Lafiya lau, Muhammad Al-ameen ne ya zomin da wata magana, ban yarda da gaske yake ba sai da naga ya tabbatar min da hakan. Auren Nuratu yake nema in har zaki bashi. Na nuna mishi karatu take yace zai iya jiranta, dan har sunyi magana da ita Nuratun tace za tayi tunani, to har yanzu shuru bai samu amsa daga gareta ba, kuma yana so iyaye su san da maganar." Shuru Mami tayi har Amma Jidda ta gama magana kafin tace. ..... Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE 9. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... "Ba zan hana Nuratu son Al-ameen ba haka ba zan hana Al-ameen auren Nuratu ba, domin na yarda da tarbiyyarshi da nutsuwar shi. Sai dai hanzari ba gudu ba dukkkan su karatu suke mai zai hana a bari su ƙarasa in yaso sai ayi maganar, sai yaje can Nijar ya samu Yaya Muhammad suyi magana." Amma Jidda ta gamsu da maganarta kuma gaskiyar ta. "Hakan ma yayi, dama shima cewa yayi a san da zaman shi ne amma zan ƙara tunatar dashi hakan." "Ba komai sai ya cigaba da neman amincewar Nuratu balle ma ina ga ta amince." Da murmushi kan fuskar Amma Jidda tace. "Yaran zamani sai dai muji labari a wajensu bamu san lokacin da suka haɗa kansu ba." "Wallahi fa." Cewar Mami tana mamakin wannan lamarin, ko ba komai tayi farin ciki da Muhammad Al-ameen ya nemi auren Nuratu shi da yasan komai na rayuwarta tsakaninta da mahaifinta akan wani bare da watarana dole ya mata gori ba fata take ba. Suna cikin hira Nuratu ta dawo daga makaranta ta gaishe da Amma Jidda da taji wani kunyarta ya kamata daga gaisuwar ta wuce ɗakinta suka bita da kallo. Jin ana ƙiran sallar la'asar ya saka Amma Jidda yiwa Mami sallama ta tafi. Da dare Mami da Nuratu suna zaune gaba ɗaya hankalinta a kan kallon da take Mami na mitar ta hanata kallon wa'azi da za'a gabatar, ganin an fita talla ya saka Nuratu kallon Mami. "Mami ki saya min waya dan Allah, har Ameera tana da waya. Ni kaɗai ce bani dashi." "Ki samu damar yin hira da saurayinki ko?" Wani tashi zaune Nuratu tayi ta zauna tana duban Mami ta kasa magana. "Kin saka min ido kamar zaki cinye ni, ba gaskiya bane. Wato har kun gama magana da Al-ameen baki sanar dani komai ba." Kunya ne ya kama Nuratu ta kasa magana, wato dai Yaya Al-ameen dagaske yake har ya sanar da Amma dan ta san ita kaɗai ce zata sanar da Mami. Ji tayi Mami tana cewa. "Ba zan hanaki soyayya dashi ba ko aure, amma ina da burin kiyi karatu Nuratu ki samu ilimi mai amfani ki tsaya da kafafun ki." "Kiyi hakuri Mami amma har yanzu ban faɗa mishi hukuncin dana yanke ba, zan sanar dashi yayi hakuri kawai in har hakan zai faranta miki rai, in yi karatu nima ina son hakan." "A'a, bance ba. Jidda tamin abinda bani da abinda zan saka mata dashi sai aura miki ɗan ta. Ki sanar dashi kin amince in har kina son shi. Maganar waya ina sane dake cikin satin nan nake son saya miki dama." Kan Nuratu ƙasa tace. "Nagode Mami Allah ƙaro buɗi." Daga haka ta maida hankali kan tv a zahiri kallo take cikin zuciyarta kuma tunani take. ... Haka kuwa a kayi cikin satin Mami ta harhaɗa kuɗaɗen bashin da take bin mutane ta bawa Nuratu tare da jagorancin Rukayya ta rakata ta siyo waya haɗe da gidan layi. Nuratu tayi murna sosai. "Sai ki saka numbern Yaya Al-ameen ya daina damuna da ƙira dan jin lafiyarki." Rukayya dake kwance ta faɗawa Nuratu haka yayin da take duba wayar Nuratu. "Kai sister kin saka min ido, babu komai tsakanin mu fa." "Hakane kuma fa, shi yasa ya ke damuna da ƙira dan jin lafiyarki. Waye bai san sonki yake ba, Ni kam dai bana son ƙauyen ci, ki saki jiki kuyi soyayya naga dai ba aure za kuyi yanzu ba sai kun gama karatu, in baki nuna mishi kulawa ba can wata zata ɗauke mishi hankali." "Allah dagaske sister." Nuratu tace tana neman ƙarin bayani. "Zauna nan kiga ikon Allah." Rukayya tace taci gaba da bata shawarwari har da saka mata numbern shi ta mata saving da My Dear kafin ta miƙa mata. "Zan tura mishi contact naki ya ƙira ki." Karɓa Nuratu tayi ta saka wayar a charge, Sai yamma lis Rukayya ta tafi gida dan ƙaryar tana da lecture tama Abban ta ya barta tazo, amma dai Amma Jidda ta san inda za tazo. Da daren ta samu ƙiran Yaya Al-ameen ta ga My Dear raɗau ya fito a screen ɗin, cike da kunya ta ɗauka. "Ƙanwata." Ya ce bayan ta ɗauka ta amsa tana gaishesa. "Ina wuni ya karatu?" "Lafiya ƙalau sai kewarki, amma yanzu komai yazo da sauƙi tun da munyi waya kullum za ina jin muryarki." Murmushi kawai tayi yaci gaba da zuba mata zance daga Um sai a'a take bashi amsa har wajen karfe tara kafin suyi sallama ta kwanta. Tun daga lokacin wanda ya kamata su san san cewa Yaya Al'ameen da Nuratu suna soyyaya sun sani in ka cire iyayen shi da Alhaji Mamman da kuma can Nijar. Aunti Rahma, Hasiya, Walida sun fi kowa farin ciki in ka cire Ameera da haka kawai bata so dan ko hiran ake barin gurin take dan wani haushin Nuratu take ji, ganin kowa yinta yake, ko gidansu bata cika zuwa ba. *** Rayuwa sai tafiya yake abubuwa sai faruwa suke a cikin shekara ɗaya daya wuce kusan sau biyar Yaya Al-ameen ya zo Damaturu dan ganin Nuratu, soyayya suke cikin nutsuwa babu wani zurfafawa. Su Nuratu sun gama makaranta har sun samu cigaba a digiri. Yaya Al-ameen ya gama karatu ya samu aiki a kamfanin MTN a can Zaria. An saka ranar auren Rukayya, Aunti Rahma ta haifi ɗa namiji, Aunti Hasiya ne shuru har yanzu ba labarin ciki. Sun shirya event biyu kafin aure da bayan ɗaurin aure za suyi kamu da dinner. Wannan lokacin Mami ta sanar da ƴan Nijar wanda suka samu labari sun zo dan mata kara da murna, hatta Yaya Muhammadu ya zo. Ana washegarin ɗaurin aure suka shirya kamu a Gat hotel, atamfa su kayi mai shudiyar color da ratsin yellow duk ƴan matan, manya nasu daban, sai na yara. Amarya da ango sunsha kyau abin su cikin nasu kayan. Taro a kayi cikin nutsuwa ga kawayen amarya da ango da wasu daga wani gari ma sun zo dan abokantakar su da shi. Nuratu da sune gaba kan komai su shiga su fita cikin hall din ta samu saƙon Yaya Al-ameen. *"Ki nutsu ki zauna ƙanwata, tun ɗazu sai shiga da fita kike."* Murmushi tayi ta tura mishi da amsa inshaAllah za tayi hakan. Waje ta fita dan taro ƙawayenta biyu data gayyata ƴan makarantar su, sun iso sun kasa shiga, suma sunyi ƙoƙarin yin anko dan har mamaki suka bata. "Kinyi kyau ƙanwar amarya." Rufaida tace dan ba laifi Nuratu tayi kyau sosai kayan ya karɓi baƙin fatarta. "Nagode." Tace tana murmushi da ya saka gefe gefen kumatunta lotsawa ya ƙara fito da kyan fuskarta. "Ki tsaya muyi hoto gaskiya." Cewar ɗayar tana ciro wayarta a jaka. Hakan ya saka Nuratu da Rufaida tsayawa ta ɗaukesu, itama ta tsaya da Nuratu kafin a ɗaukesu ta ɗaga tana musu selfie. "Ya isa Fa'iza." Cewar Nuratu suka shiga cikin hall ɗin ta nema musu gurin zama. .... Zafin ƙunar wuta da yaji yana ratsa yatsun hannunshi ya ankarar dashi daga inda yake kallo ya yarfar da sauri yana yamutsa fuska, ya bi sigarin da ko rabi bi sha ba iska ya kwashe yace. "Oh God." Cikin motar shi ya koma ya zauna sosai, siffanta da kyakkyawar fuskarta yana mishi yawo. "She's damn pretty." Ya furta yana rufe idanuwanshi ya buɗe. Kamar an mintsile shi ya tashi ya fita da sauri ya nufi cikin hall ɗin da zuwansu da abokansu sunyi sunyi ya shiga yaƙi yace zai zauna a waje, wanda ya bashi damar zugar sigarin shi da bai samu sha ba tun safiya. Ya fara kenan ya hango fitowar Nuratu da yaji ta kusa tafiya da numfashinsa da ruhin sa. Bayan shigarsa cikin hall ɗin ya isa wajen abokai ya zauna yana baza idanu dan hangota ya ganta zaune da ƙawayenta biyu da suka shiga ciki tare, ciki har da ƙanwar shi Rufaida da yayi mamakin ina ta santa. Bata kama da amarya sannan bata kama da ango, shigar jikinta ya bashi tabbacin tana da alaƙa da amarya. Murmushi take yi ya zuba mata ido. "Mufid!" Abokin shi na kusa dashi ya ƙira shi jin hankalinshi ya koma wani guri daban. Juyowa yayi ya kalleshi da lumshashshun idanuwansa bai amsa ba. "Ana ƙiran abokan ango su fito." Filin gurin ya kalla yaga babu mata wanda hakan bai mishi ba ya girgiza kai alamar ba zai je ba. Daga haka yaci gaba da kallon in da take, yaga bata gurin ta tashi ta nufi wajen amarya da ango tare da Rufaida da ɗayar da bai su. Bayan ta mata magana suka fita haka shima ya bashi damar miƙewa ya bi bayansu ya samu ta musu rakiya ta juyo dan komawa ciki. Nuratu tana ƙoƙarin shiga ciki ta samu ƙiran Yaya Al-ameen ta ɗauka tana komawa baya. Tsaye ta same shi ya harde hannunshi saman kirjinshi. "Kin yi kyau ƙanwata, ban so kina yawo haka ba wasu su ganki." Kunyane ya kamata tace. "Sorry Yaya." "Ya zanyi tunda bikin Rukayya ake ƴar uwa rabin jiki." Dariya tayi da ya ƙara mata kyau, shi kanshi Yaya Al-ameen da yake kallonta kullum baya gajiya da ganinta. Hira suka taɓa kaɗan ta ce zata koma ciki yace yana jiranta a tashi ya mai data gida tace to. Ganinta da wani tsaye ya haddasa Mufid jin wani abu a kirjinshi da yaji ya tokare masa zuciya ya kasa ƙarasawa wajenta ya tsaye kallon su har suka gama magana ta zo ta wuce ta gefenshi bata lura ba. Kwakkwaran motsi ya kasa yi ƙarshe ya koma motarshi ya shiga. Mai yake damunsa akan yarinyar da bata san da zamanshi ba. Yan mata sai dai ya zaɓi na zaɓa ya yaudara amma baya jin komai a kansu akan yadda yake ji yanzu akan Nuratu. Yarinya kowacce irice daga ya mata magana take amincewa ta so shi ya yaudara ya bar su baya jin komai a kan su sai ita bata san ma yanayi ba. Yana zaune har aka tashi yaga sai fitowa ake ana tafiya ya hangota ta fito ta shige mota suna barin gurin. Sigarin hannunshi da ya zuƙa na uku kenan ya zuge gilashi motar ya jefar ragowar yana jan motar yabi bayansu. Tafiya suke yana bin bayansu har ƙofar gidan su amarya ya faka motarshi gefe da wanda take ciki kaɗan. Yana gani ta fito ta shige cikin gidan kafin ya ja motar shi yana barin gurin. Gida ya nufa kai tsaye bayan ya kashe motar ya shiga cikin falon da ƙannensa mata kusan biyar ya samu a falon ciki har da Rufaida data jima da dawowa har ta canza kaya. Ɗakin shi ya wuce yana banka kofar ya saka lock, tunanin mafita kawai yake yadda zai yi ya sameta. Son ta yake a cewar nashi zuciyar da take neman yaudaran shi. Kanshi ya hau caji sosai ganin ciwon kai na neman kamashi ya sashi tashi cikin inda yake ajiye cigarinshi ya ɗauki kwali ɗaya ya fara zuga duk ya cika ɗakin da hayaki. Bugun kofar ɗakin ake cikin magagi yace. "Waye zai balla min kofa." "Uwarka ce, ka buɗe min ƙofar nan." Bai kashe sigarin ba ya buɗe ƙofar Hajiya Hindatu ta shiga tana maida kofar ta rufe kafin ta juya kanshi. "Yanzu Mufid duk faɗan da ubanka ya maka baka ji ba sai da ka sake sha mishi sigari a gida." "To Ummu ya zanyi, tunani ya min yawa shine zan sha dan in samu sauƙi." Yace yana hura hayakin bakinshi ta toshe hanci. Cikin kulewa ta kai hannu zata kwace ya hanata. Tana cewa. "Ubanka kai da tunanin, mai nace maka kayi duk abinda za kayi a layi kar ka kuma yi a gida, yanzu in babanku yazo wuce fa yaji, ka san dai baya son wannan bushe bushe da ka ke yi a gida ko dan ƙannen ka su gani. Bani nan." "Saura kaɗan bari in shanye daga shi na gama." Yace ya zuge sauran tas ya murje ƙarshen, tana gani ta ɗauki turare ta feshe ɗakin dashi ta haɗa da room fresh kafin wari da hayakin sigarin ya ragu ta fita. MAFARIN HARGITSIN. Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE 10. Pharty Bb. Wattpad phartybb. Mufid Kashim Mufid shine mafarin hargitsewar rayuwar Nuratu. Daga haske zuwa duhun da ya mamaye. Ƙaddarar rayuwarta ya canza. Ɗa na biyar a wajen Alhaji Kashim Mufid mai kuɗi da ake ji dashi, matan sa biyu Hajiya Hindatu da Batula, Bafulatanin Yola da zama da harkar kasuwanci ya kawo shi Damaturu. Ƴaƴan Hajiya Hindatu bakwai mata huɗu sai Mufid da mata biyu da suke binshi. Ganin duk mata take haifa Alhaji Kashim ya auri Hajiya Batula da Allah ya azurta itama mata ta haifi mata gudu huɗu. Ya aurar da yayun Mufid da ƙanwar shi ɗaya saura Rufaida, Suwaiba, Zakiyya, Sadiqa, Khadijah. MKM laƙabin shi kenan, sangartaccen yaro da iyaye suka jawo masa tsabar gata da kuɗi da suka nuna mishi, shi ɗaya ne namiji a gidan da Allah ya azurta Alhaji Kashim Mufid dashi hakan yasa komai yake so yake masa tun yana ƙarami haka ɓangaren Hajiya Hindatu itama sai abin da yaso. Bayan gama karatunshi ya turashi ƙasar waje dan cigaba, ba kamar sauran ƴan uwansa mata ba da a Nijeriya su kayi suna gamawa ya aurar dasu. Zuwan Mufid ƙasar waje ba idon iyaye shine silar fara lalacewarsa ya haɗu da abokan banza, sune zuwa party, gidan rawa har ya zama sun koya mishi Shaye-Shaye banda neman mata da suke yi suna ƙoƙarin koya masa ya nuna sam baya so dan ƙyama yake. Dalilin ƙara lalacewarsa kuɗi da Alhaji Kashim yake tura mishi da zaran ya nema, hakan yasa ya watsar da karatun ya faɗa harkar duniya, duniyarsu suke ci da tsinke. Shekaru shida yaci a ƙasar ganin bashi da niyar kammala karatun ya saka Alhaji Kashim bin diddigi ya samu labari ba karatu yaje ba sai tsiya da yake tsulawa. Alhaji Kashim Mufid yaji baƙin ciki haka ya tura mishi kuɗin jirgi sau biyu ya dawo yana cinyewa yana kashewa, ana uku ya dawo dakyar dan alƙawarin yayi ba zai ƙara tura mishi ba sai dai talauci ya kashe shi. Ranar daya dawo Hajiya Hindatu taga tashin hankali ganin tilon ɗanta ya zama abinda ya zama, banda jerin ɗan kunne harda sarƙa da zobuna kamar ɗan hip hop, hatta ga ƙannen sa tsoronsa suke ji dakyar suka fara sakewa dashi. Bayan dawowar shi Alhaji Kashim bai hakura ha ya nema mishi wani makarantar ko zai yi karatun amma a banza dan wataran in ya fita sai sha biyun dare zai dawo a buge dan har lokacin bai rabu da Faisal da AA ba abokansa da suka yi karatu a waje. A makaranta suka haɗu da Sufyan mijin Rukayya da wasu ɗalibai da ba mutunci yake dasu ba sai ya kama, shi da Sufyan ma mamakin abokantakar su ake dan hali ya bambanta. Abokantakar Mufid da Sufyan ya saka Sufyan ma Mufid wa'azi da a hankali ya rage saka ɗan kunne da sarƙa da shan sigari gaban mutane sai ya ware kanshi. Sufyan ya gama karatu ya bar Mufid da kwata kwata bashi da niyar yi hakan ya ƙara mai da Mufid ruwa tsamo tsamo ya zamto tantiri a makaranta da ya gagari kowa, ƙarshe suka koreshi. Abin yayiwa Alhaji Kashim ciwo, amma son Mufid ya rufe mishi ido yace karatu dan a samu kuɗi ake yi kuma yana dashi dan haka yayi zaman shi gida ko nawa yake buƙata zai bashi, haka ya cigaba da zama a gida yana bashi kuɗi ko nawane, ya yi abinda yake so daga mahaifinshi da mahaifiyarshi. Ranar da suka samu Mufid yana shan sigari sun mishi faɗa sosai daga baya suka watsar abun cewa wataran zai bari. Amma abin sai gaba yake. Ƴan mata kuwa yaudaran su kawai yake babu na aure, baya soyyaya da mace sai soyayyar shan minti ya samu ya rage zafi zai watsar dake. ... Da safiyar Rufaida ta fito cikin shirin makaranta ƙarfe tara sai sauri take dan ta kusa latti. "Ummu na tafi." Tace tana ɗaukar bottle na ruwa tayi hanyar waje. "Tsaya na sauƙe ki." Mufid da yake zaune ya miƙe tsaye. Rufaida da Hajiya Hindatu su ka kalleshi yayi tamkar bai gani ba ya fita, Rufaida bata so ba haka ta shiga motar shi ya ɗauke ta. Kunya take ji a ganshi a matsayin yayanta, wani shegen three quarter ne a jikinshi da riga body hug daya kama shi, kanshi wani arniyar aski. Mufid farine kyakkyawan saurayi bafulatani ne da kyan ɗan macijine dashi domin babu kyan hali balle na zuciya. Shuru su kayi dukkan su biyu har suka isa cikin makarantar da sauri Rufaida na ƙoƙarin fita taji yayi magana da ya sakata duban shi da sauri. "Wacece ita? Menene sunanta?" "Waye kenan?" Tace da sauri cikin rawar murya. "Wacce ki ka je dinner party na auren Sufyan dan ita." Zuciyarta ne ya buga, ba dai Nuratu yake magana a kai ba. "Ban gane ta ba." Rufaida tace tana shirin fita ya daka mata tsawa. "Zaki faɗa min ko sai na saka ki kinyi missing lecture." Tana tsoron shi balle ance ɗan Shaye-Shaye da hauka yanzu zai iya kai mata bugu banda abinda ya faɗa ta san zai aikata. "Sunanta Nuratu Mamman Bashir, class ɗaya muke." Murmushi yayi da yake ɗauke hankalin mata dashi yace. "Ko ke fa ƙanwata. Je ki fito ina jiranki zan mai dake gida." Ya cire lock da sauri ta fita tana jan tsaki ciki ciki. Allah kiyaye a ganta dashi ta zama abin ƙyama. Nuratu fa? Taji zuciyarta ya tambaye ta. Ba zata taɓa barin shi ya raɓeta ba, dan ta san bada alheri yake nemanta ba. Haka ta ƙarasa aji ta samu Nuratu tazo Fa'iza bata shigo ba, gaisawa kawai su kayi lecture ya shigo aka nutsu ya fara koyar musu. Bayan fitar shi suka fita dan shi kaɗai ne yau dasu. A in da ta bar motar shi ta ganshi yana ciki yana jiranta. "Friend sai gobe kin ga ana jirana." Rufaida ta faɗawa Nuratu, murmushi Nuratu tayi murmushi tace. "To shikenan ki gaishe da mutanen gida." "Za suji, bayan har yau kin ƙi zuwa gaishe Ummu." Rufaida tace tana hararanta. "Zan zo inshaAllah kiyi hakuri." Cewar Nuratu tana yin gaba ganin Rufaida ta nufi motar da yake jiranta. Tayi nisa a tafiya taji horn a bayanta ta juya da sauri taga motar da Rufaida ta shiga cikine. Ido biyu suka haɗa dashi, lumshashshun idanuwansa ya zuba mata. "Shigo mu rage miki hanya." Yace mata cikin husky voice ɗinshi. Nuratu ta kawar kanta gefe. "Nagode." Taci gaba da tafiya ya juya ya kalli Rufaida yana mata wani kallo ta fita da sauri a motar ta bi bayan Nuratu. "Dan Allah sister ki zo muje." "Kuje kawai friend zan nemi abin hawa." Nuratu tace tana girgiza kai. "Dan Allah dan annabi na haɗa ki dashi, haba friend ina rokon ki kamar ni kin ƙi ji." Ganin ran Rufaida ya ɓaci, roƙo take da take buƙatar yardarta ya saka Nuratu amincewa. Baya ta buɗe ta shiga Rufaida ta shiga gidan gaba yaja motar yana barin makarantar. Tafe suke shuru a hanya sai kiɗan wani mahaukacin mawaki ke tashi har suka shigo cikin gari. "Bari mu fara sauƙe ki ko?" Mufid yace yana gyaran mudubin mirror dan ganin fuskar Nuratu da kyau suka haɗa ido da Nuratu dai-dai lokacin ta ɗago kanta. Da sauri ta juyar da kanta. "Ku sauƙe ni kawai a bakin cross zan nemi abin hawa." "Why? Saboda baki yarda dani ba ko baki yarda da Rufaida ba. Take me as your elder brother." "Mufid mu sauƙe ta kawai a bakin cross." Rufaida tace da sauri da tsakaninta da Allah bata son abin da yayanta yake hararowa akan Nuratu. "Shut up I'm not talking with you." Yace wa Rufaida a tsawace ta kama bakinta tayi shuru ya maida hankali kan Nuratu. "Faɗa min unguwar ku." A hankali ta sanar dashi ya canza hanya suka nufi unguwar, tana nuna mishi har bakin layinsu tace ya sauƙeta yaƙi dole ta nuna mishi har ƙofar gidansu ta sauƙa. "Nagode." Ta faɗa tana fita ya bita da kallo yana ɗaga mata kai dan ya kasa bata amsa. Sai da yaga shigewarta cikin gidan yaja motar shi. Suna isa gida ya faka motar yaga Rufaida bata da niyar fita ya dubeta. "Fita min a mota, kin gama min amfani." "Dan Allah Mufid kar ka shiga rayuwar Nuratu in ba da alheri zaka je mata ba, dan Allah na haɗa ka dashi, ita ɗin ba irin sauran bane." Rai ya haɗa ya tamke fuska. "Sai akace miki mai zan mata, aurenta zanyi in ajiyeta ina kallo, she's so hot and beautiful baki gani ba." Girgiza kai tayi cikin jin haushin maganar shi tasan duk abinda yake kai shi gurin mace. "Ni dai na haɗa ka da Allah, kuma in ka cutarta Allah ba zai barka ba, sannan nima ba zan yafewa kai na ba da nayi sanadin ka santa." Sauƙar mari taji saman fuskarta ta kasa ƙarasa maganar ta dafe gurin. "Sauƙa min a mota kar min miki mugun duka." Cikin hawaye Rufaida ta buɗe motar ta fita tace. "Allah ya isa na mugu kawai." Kanta yayi yana niyar fita a motar tayi cikin falonsu da gudu. Ummu da ta ga haka tana tambayarta lafiya ta wuce ɗaki da gudu ta saka lock. Mufid da ya shigo yaga haka zai bita Ummu ta tare shi. "Kai lafiya wai?" "Ummu zan karya yarinyar nan in ballata wallahi in tana min rashin kunya." "Allah baka hakuri mai yayi zafi." Kwafa yayi ya wuce ɗakin shi cikin jin haushi. Nuratu take kowa sonta yake kuma aurenta zai yi ba irin son da ya saba faɗawa sauran ƴan matanshi ba yake mata. Murmushi ya suɓuce masa tunawa da yayi sunyi magana har ya gano gidansu yasan komai zai zo da sauƙi, sai yanzu ya tabbatar ba ƙanwar matar Sufyan bace sai dai yar uwarta ganin gidansu daban.. .... Nuratu da ta koma gida bata sanar da Mami komai ba taci gaba da lamuranta dan dai ta san dalilin Rufaida abu ya haɗata da yayanta. Da daren yaya Al-ameen ya ƙirata suka sha soyayya yake ce mata ta kusa shiga aji biyu suyi aure dan yaga sauran yayunta duk hakane. "Tab ai ni sai na kammala tas." Nuratu tace cike da zolaya. "Allah ko zamu gani. Burina kullum in buɗe ido in ga kin shiga aji biyu in taso da maganar auren mu shine yanzu zaki kawo kin wani iyayi ko, shekaru biyu fa ƙanwata ki tausaya min mana." Dariya Nuratu tayi tace. "Wasa nake maka Yaya amma dai zaka bar ni inci gaba da karatuna kamar sauran yayuna." "InshaAllah ƙanwata sai kin gaji da kan ki." Taji daɗin haka su kaci gaba da hira har dare ya tsala kafin su kashe wayar cike da son kasancewa da juna. *** Hawayen da ya zubo saman fuskarta ta share murmushin zafi da ciwon soyayyarshi yana yawo a zuciyarta. Taso Yaya Al-ameen kuma har yanzu tana jin abu a ranta game dashi amma ƙaddararta ya rabasu. Tun daga ranar da ta dawo hankalinta taji maza da duk abinda ya shafe su ta tsana, mutum uku da Yaya Al-ameen na hudu take iya kebewa dasu har ta iya musu magana. Suma ta lura da duk take takensu amma bata jin abinda suke buƙata shine zata saka musu dashi dan karamci da taimako da suka mata a rayuwa. Kowa da rawar da ya taka a rayuwarta bayan rushewar farin cikin ta. Miƙewa tayi tai sallar magriba ta fita wajen Mami, duk yanayinta ya canza Mami tana binta da kallo amma bata tambayeta ba. Abinci ma ba taci ba na daren ta musu sallama zata kwanta sai da safe, da to suka bita dashi. Bayan shigarta ta canza kaya tayi sallar isha'i ta kwanta. Agogo fuskar wayarta ta kalla taga goma ta gota na dare tayi mamakin wucewar lokaci amma ba tayi mamaki ba dan ta daɗe cikin tunanin abin da ya wuce. Idanuwanta ta runtse ko zata samu bacci amma kuma tunanin da ta fara ya kasa barinta runtsawa. Ta runtse idanunta da karfi dan jin abinda ya wuce tamkar yanzu yake faruwa. .... Vote. Comments. Share. MADUBIN GOBE (Haske) 11. Pharty Bb. Wattpad phartybb. ... "Na samu new Baby, she's black but hot and beauty." Mufid yake sanar abokansa Faisal da AA yayin da yake ɗaukar ƙaramin cup na glass cike da abin maye ya jefashi cikin cup ɗin dake ɗauke da ƙanƙara kafin ya ɗauka ya fara sha hankali kwance. Club ne da ya tara gagararrun ƴan iska maza da mata kowa na nashi iskancin da rashin tsoron Allah, waɗansu busar hayaki suke wasu ruwan maye suke sha, wasu na rawa da ƴan mata kiɗa na tashi kamar zai fasa club ɗin da hakan daɗin shi suke ji. Faisal da AA da suke shan nasu ruwan mayen har sun kusa shanyewa Faisal yace. "A ina take? Kun dai-daita?" "No, hasalima bata san abinda nake nema wajenta ba but soon zan sanar da ita, but i think da kyar ta amince, she's so innocent." AA da sai lokacin yayi magana yace. "And so what! in taƙi amincewa. Ba sai mu bi wancan hanyar ba. Force her." Ɗan yamutsa fuska Mufid yayi yana kurɓar wine na hannunshi. "Not now because yadda nake jinta ba kamar sauran bane." "No MKM don't tell us that you love her seriously." Faisal yace cikin mamaki yana dafa cinyar Mufid dan neman tabbas. "I really don't know guys." Mufid yace har cikin ranshi ya yarda da hakan. Daga haka ya miƙe. "See you tomorrow." Hannu kawai suka ɗaga mishi yasa kai ya fita suka cigaba da tsula tsiyarsu. Kafin Mufid ya isa gida abinda yasha ya jika da kyar ya iya kai kanshi gida ya danna wani horn da ƙarfi mai gadi ya wangale get ɗin ya shiga yayi wani wawan parking ya fita ya bar motar a kunne. Bai iya gane su waye a falon ba ya wuce ɗakinshi Ummu da Rufaida dake zaune suka bishi da kallo, kai kawai Ummu ta girgiza, Rufaida kuwa baƙin ciki ne ya rufeta a ga wannan a ƙirashi da yayanta. ... Washegarin Mufid ya karɓi kuɗaɗe gurin Daddyn shi bai ƙirga ko nawa ba ya cire ya bashi ya karɓa yana godiya. Shopping mall ya nufa ya saya kaya sabi da takalma da duk abubuwan buƙatar shi ya dawo gidan. Sabon wanka yayi ya saka riga jeans da t-shirt ya fesa turare tare da gyaran gashin kanshi da yake ɗauke da shegen wani aski, gashi mai kyau na fulanin Yola kwantacce amma bai samu gyara ba. Bayan ya shirya ya fito ya ɗauki mukullin motarshi da jiya bayan shigarshi ɗaki driver da ya gyara parking ya kawo. Gidan su Nuratu ya nufa kai tsaye. Bai mance hanyar gidan ba har kofar gidan yayi parking unguwar ta fara cika da mutane ba kamar shekarun baya ba, yana zaune cikin motar shi yana bin gidansu da kallo neman ɗan aike yake babu yara sosai hakan yasa ya fito. Bakin kofar gidan ya isa yayi sallama sau biyu ya dakata kusan mintuna goma mai aikinsu budurwa ta fito tana amsawa. "Noor tana nan? Ita nake nema?" Ya tambaya kai tsaye. "Nuratu ko Noor?" Ta tambaya shi cike da mamaki tana ƙare mishi kallo ganin kyau da zubin halitta da Allah ya zuba a gurin. Kafaɗu ya ɗaga. "Whatever? Noor she's inside." Bata fahimce mai yace ba kawai tace. "Ta tafi makaranta in dai Nuratu ce." Bai jira ta ƙarasa maganarta ba ya bar gurin ya koma motar shi cikin jin haushi. Ganin haka itama ta koma gidan ta rasa wa zata sanar dan Mami bata nan taje karɓo wasu kaya da tayi order. Har karfe uku saura yana zaune yana jiranta ba batun sallah balle zikiri sai ma chatting da yake bayan sigari daya banka a cikin shi cewarshi zai rage yunwa. Yana nan zaune yaga tsayuwar mashin adaidaita ya ga ta fito daga ciki da sauri ya fito a motar. "Noor!" Yace da ɗan karfi cikin husky voice, ganin zata shiga gida ta juya jin kamar ita ake ma magana tayi ido biyu dashi ta ɗan koma baya kaɗan. "Ina wuni." Tace dashi tana mamakin ganin shi kofar gidansu. Lumshashshun idanuwansa saman kanta yana ƙare mata kallo sosai, murmushi ɗauke saman fuskarshi. "Lafiya ƙalau. Baby kin hanani bacci tun daren dana fara ganinki dan ba jiyanne farkon ganina gareki ba." "Ni kuma?" Tace da mamaki tana gyara tsayuwarta tare da zaman jakarta. Lumshashshun idanuwansa ya zuba mata. "Yes and i means it, i love you." Murmushi Nuratu tayi dimple ɗinta yana lotsawa duka biyu. "Thank you for the love, amma ina da wanda nake so kuma zan aura." Bata jira mai zai ƙara cikin zancensa ba ta shiga gida ta barshi tsaye cikin mamaki. Mace bata taɓa cewa bata sonshi kai tsaye ba tunda yake sai yau akan Nuratu da ba zai iya hakura da ita ba. Motarshi ya koma yaja yana barin gurin. "Kin yi bako, wani yazo zubin larabawa yana neman ki." Munirat take faɗawa Nuratu bayan shigewarta cikin gida. "Mun haɗu dashi, nima ban san shi ba, rabu dashi kawai bar zancen." Tace tana tambayarta Mami ta sanar da ita ta fita. .... Washe gari haka wajen karfe sha biyu da ta fito zata tafi makarantar ta samu yana jiranta, binta yake da motarshi kafin ta samu abun hawa, da ta shiga ya kaita ƙi tayi har ta samu abin hawa ta yi tafiyar ta. Kwana biyun haka duk ya takura mata da kwata kwata wani kyau nashi da kuɗi da take gani ya kasa ɗauke hankalinta zuwa gurinshi dan wani haushinsa take ji ba dan Rufaida da ba, da ta mishi rashin mutumci. Tsakanin ta da Yays Al-ameen har yanzu suna nan yadda suke burin su suyi aure kawai, da zaran ta rubuta exam ta gama suka tafi level two hundred zai zo ayi maganar aurensu. ... Yau bata dawo da wuri ba sai wajen karfe biyar na yamma lis, ya lura duk ranar bata dawowa da wuri. Tana sauƙa a adaidaita ya isa gurinta tana ganin haka ta nufi cikin gida ya saka hannu ya fizgota. "Mace taso ni ma ina mata wulaƙanci balle ta wulaƙanta ni, imagine Baby." Mufid yace yana matse kafaɗunta cikin jin haushi. Tana ƙoƙarin kwacewa cikin tsoro dama ta lura da shigan ƴan isa da yake yi. "Let me go." Tace cikin ɓacin rai ganin yaƙi sakinta. "No Baby, listen to me." Yace yana kai hannunshi saman fuskarta ya shafa, a mugun tsorace taja baya tana kwace jikinta da ya hau rawa, ganin zai ƙara kamata ta kwasa da gudu tayi cikin gida. "Ke lafiyarki zaki shigo min da gudu." Mami dake shirin alwalar sallar magriba ta tambayi Nuratu. "Babu komai sauri nake." Nuratu tace tana wucewa cikin falon da saurinta. Da kallo kawai Mami ta bita. Nuratu tunani ta shiga dan nemawa kanta mafita da kaucewa wannan bawa da bata san sunanshi ba balle wani abu akan shi. Rufaida kawai zata samu suyi magana ta sanar da shi akwai wanda take so ya rabu da ita. Da wannan shawara data yanke ta iya sakin ranta ta samu runtsawa. Da safiyar ranar asabar da misalin ƙarfe tara ta ƙira Rufaida sai da ta ƙira sau biyu ana uku ta ɗauka idonta cike da bacci. "Na tashe ki ko Ruffy." "Babu komai, ina kwana ya su Mami." "Lafiya ƙalau, dama Ruffy magana nake so muyi, Wallahi maganar tana da muhimmanci Please." Nuratu ta ƙarasa maganar cikin nuna lallai tana bukatar yin maganar dagaske. "Ki zo gidanmu mana." Da sauri Nuratu tace. "A'a dan Allah akwai matsala ne, ki taimaka min mu haɗu a makaranta." 'Dagaske take tana buƙatar suyi magana wanda ba kokonto ko ɗaya akan Mufid ne' Zuciyar Rufaida ya bata amsa. "Shikenan zuwa 11 sai mu haɗu." Ajiyar zuciya ta sauƙe tana cewa. "Nagode sai mun haɗu." Daga haka su kayi sallama Nuratu ta miƙe, ɗan ayyukan ta tayi data saba duk weekend tayi wanka, wanki ma da take yi kasa yi tayi burinta suyi magana da Rufaida ko hankalinta zai kwanta. Karfe sha ɗaya saura minti biyar ya sameta a makaranta bayan ta yiwa Mami ƙarya ta samu fita. Har sha ɗaya da mintuna ashirin kafin Rufaida ta zo dan har ta fara cire rai za tazo ga ta ƙira bata ɗauka ba. "I'm sorry Nuratu ban samu fita da wuri ba." Cewar Rufaida tana zama kusa da Nuratu. Murmushi tayi tace. "Babu komai " "Ina sauraronki." Faɗin Rufaida tana zubawa Nuratu idanu. Tun daga farkon zuwa gidansu da yayi har zuwa zirga-zirga da take ganin yanayi da duk zama da yake a kofar gidansu da cikin unguwa har jiya da yayi ƙoƙarin taɓata ta sanarwa Rufaida bata ɓoye mata ba, ƙarshe ta ƙara da cewa. "Rufaida Yayanki ne ina ganin girmanshi albarkacin ki, dan haka ki sanar dashi ya fita daga rayuwata ina da wanda nake so balle ma ko bani da kowa banga abin so a tattare dashi ba." Numfashi Rufaida ta sauƙe. "Kinyi gaskiya Mufid bashi da hali na gani aso, Mufid yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, ban zan faɗi abu dan in kareshi ba amma sam bashi da hali mai kyau, dan haka abin da zan iya faɗa miki shine kiyi gaggawar yin aure kiyi nisa dashi, in ba haka ba babu mai iya hanashi abinda yaga dama ko Daddy ne, dan in har ya kyalle ido yaga mace to sai fa ya ɓata mata rayuwa zai barta sannan ba mai iya ɗaukar mataki. Ni na jawo miki komai amma wallahi ba a son raina bane Nuratu dole ya min kiyi hakuri ki yafe mini." Hawayen data gani idanuwan Rufaida shi ya bata tabbacin dagaske take, tsoro ne ya ziyarci zuciyarta. Rayuwarta yana cikin hatsari, hatsari mafi muni. "Nagode da shawarar da kika bani inshaAllah zanyi ƙoƙarin ganin na kaucewa duk hanyar da nasan zai haɗamu, Allah zai kareni dashi na dogara." Kai Rufaida ta girgiza halin Mufid ya isheta ta tsanesa ta tsani halinsa, kowa ma cikin gidan banda Daddy da Ummu babu mai sonshi kuma duk sune silar lalacewarsa. Anan suka rabu kowa ya nufi gida Rufaida bata sanar da kowa ba amma ta ɗauki aniyar tunkarar Mufid da maganar ko da kuwa zai daketa ne sai ta sanar dashi ya rabu da Nuratu. .... Nuratu tunda suka rabu ta kasa cire maganganun Rufaida a ranta hatta Mami ta lura da ita ta tambaye ta lafiyarta sai lokacin taji tana son sanar da ita komai. Ran Mami ya ɓaci da jin abinda yake faruwa bata sanar da ita ba har sai da ta buɗe baki ta tambayeta. Kallon da Mami take mata ya sata shan jinin jikinta. "Dan Allah Mami kiyi hakuri ban abin zai kai ga haka ba." Nuratu tace kanta ƙasa. "Dole ki ban hakuri ai tun da kinyi laifi. Rayuwar ki tana hatsari kin kasa sanar mini ina matsayin mahaifiyarki. To bari kiji tun da abin ya kai haka zan sanar da Amma Jidda ta yiwa Al-ameen magana, ke ma ki sanar dashi ya tura iyayenshi can wajen Yaya Muhammadu ayi maganar auren ku. Allah yasa haka shi yafi alheri, sannan ki dage da addu'a Allah ya kareki daga sharrin sa bayan haka ki gujema duk hanyar da zai haɗa ku. Ban da yawan fita in ba makaranta ba shima sai kin tabbatar baya nan." "InshaAllah Mami zanyi yadda ki kace." Cewar Nuratu cikin sanyin jiki. Nasiha Mami tayi ta mata daya ƙara kashewa Nuratu jiki. "Wallahi Nuratu kinga dai bamu da wani gata sai Allah in wani abu ya faru a rayuwar ki Nuratu sai dai mu shige ɗaki muyi kukan mu babu mai taimaka mana, mahaifinki har yau bai taɓa sanin ko sunanki ba balle rayuwarki da matsalar da kike ciki ba, kamannin ki ma ya iya mantawa zuwa yanzu, to kina jin in wani abu ya sameki zai iya tsaya miki ya taimaka miki, ko kina ganin shi yaron da kika cewa ba'a shari'a dashi za'a hukunta shi. A'a sai dai mu, mu gujewa duk hanyar da zai jawo faruwar wani abu marar kyau tsakanin mu, fatan mu Allah tsaremu da dukkan sharrin sa." Nuratu dake hawaye kamar wani abin ya faru ta amsa da ameen. Har yanzu tana son sanin mai ta yiwa mahaifinta da ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata. Ga kuma Mufid da yake neman shiga mata rayuwa kai tsaye. ..... Vote. Comments. Share MADUBIN GOBE (Haske) 12. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... Da daren Nuratu bata iya bacci ba sai da ta ƙira Yaya al'ameen bayan sun gaisa sai kuma taji kunyar sanar dashi yadda su kayi da Mami. "Akwai magana ƙanwata a bakin ki, faɗa min menene?" Al'ameen yace dan sai inda inda take mishi kuma bata cika ƙiranshi ba in ba abu zata faɗa mishi ba. "Zan tura maka saƙo." Cewar Nuratu a hankali. "Yau kuma kunyata kike ji? To shikenan ina jira." Yace ya katse ƙiran. Saƙon ya karanta yana murmushi kafin ya fita a gidan saƙonnin ya ƙirata. Ɗauka tayi tai shuru. "Allahamdulillahi." Yace kafin yaci gaba da faɗin. "Allahamdulillahi! nagode ƙanwata da wannan dama da ki ka bani wanda na jima ina jiransa a gurinki, Allah yasa da rai zamu gani." Ameen Nuratu ta amsa ƙasa ƙasa ta kasa sakewa suyi hira kamar yadda ta saba, shi kuma sai janta da hira yake ƙarshe wajen sha biyu su kayi sallama. Kasa bacci tayi ta tashi ta ɗaura alwala tayi ta nafiloli a saman darduma kafin bacci ya kwasheta. Washegarin ranar Lahadi bata da makaranta bacci tayi har ƙarfe tara ta farka, breakfast tayi tayi wankin kayanta kafin ta ɗaura musu abincin rana, data gama kafin ta huta. .... Tun daren jiya take zaman jiranshi bai dawo ba har sha biyu hakan yasa ta hakura ta kwanta. Washegarin da wuri ta farka har ƙarfe goma bai fito ba balle yayi breakfast hakan yasa kawai tayi shahada ta nufi ɗakinshi. Ƙwanƙwasa tayi ya bata umarnin shiga bai tambayi waye ba yadda yake kwance da alama ko sallar asuba bai yi ba. Ganin wacce ta shigo ya sashi ɓata rai. "Mai ya shigo min dake ɗaki?" Dakewa Rufaida tayi ta samu guri ta zauna. "Magana na zo muyi Mufid." "Ke kam dai anyi fitsararriya kowa a gidan nan yana ƙirana Yaya ban da ke. Ina jinki dan bani da lokacin ki." Mufid yace yana ɓata rai. "Nima bani da lokacin ka dole ta sani. Akan Nuratu ne." Da sauri ya tashi zaune. "Meye samu Babyna? Wani abin ya samu Baby." Harara Rufaida ta watsa mishi ƙasa ƙasa. "So nake ka fita daga rayuwarta dan Allah na haɗa ka dashi. Wai mai yake damunka ne? Abinda kake so a gurinta ba zaka taɓa samu ba." "Tashi ki fita ko in ɓata miki rai, fitsararriya idan naje ta hanani gurinki zan dawo, ai ke sai ki bani, kuma ki jira ki gani." A mugun tsorace ta kalleshi. "Yes and i means it, ki cigaba da ƙoƙarin rabamu zan baki mamaki." Bai ƙarasa maganar ba Rufaida ta tashi da sauri ta fita. Lallai Mufid ba shakka abinda yake sha ya fara taɓa ƙwaƙwalwarsa da har zai mata wannan maganar. Duk iskancin dan iska baya haurowa gida. Ɗakinta ta shiga ta ma rasa wani irin tunani za tayi dan ta rabashi da Nuratu, gashi kuma ita da take ganin zata iya ga abinda ya faɗa mata ko kunya balle tsoron Allah. Addu'a kawai za ta mata dan gudun ɓata nata rayuwa dan da wannan mummunan ƙaddarar ta afka mata gwara ta kashe kanta take ji. .... Yaya Al-ameen sun yi maganar da Nuratu da kwana biyu ya samu yayan mahaifinshi da maganar,bai ɓoye masa komai ba dangane da Nuratu iya wanda ya sani. Yayi mamakin jin cewa yar gidan Alhaji Mamman Bashir ne. Haka kawai yaji wannan haɗin bai mishi ba amma ya bar abin a ranshi. Anan yace zai faɗa sauran ƴan uwa za suyi ɗan tattauna akai har da mahaifiyar shi. Godiya ya masa yana fita ya ƙira Nuratu bata ɗauka ba ya hakura zuwa anjima. *** Tun karfe uku yana kofar gidansu yana jiranta dan ganin ta fito har ƙarfe huɗu kafin ya hango ta sauƙa a adaidaita. Sarai ta gane shine cikin motar dan haka cikin sauri ta sauƙa ta miƙa mai adaidaita ɗari biyar ya ɗauki kuɗin shi ya bata canji garin sauri har ta zubar takardunta a jaka dan burinta ya bata ta shige cikin gida dan kaucewa Mufid a tarkonsa da bata san da mai yazo mata ba. "Babu canji nima duk shine a gurina, baki sanar dani ba da ba zan ɗauko ki ba. Canjin duk nasha mai dashi." Cikin jin haushi Nuratu tace. "Nima baka faɗamin ba da bazan shiga ba, bari in dubo maka a cikin gida." Tace da sauri zata shiga taji an fizgota ta juyo da sauri taga Mufid ne da ya ƙaraso kusa da ita. "Ka sake ni." Tace tana dukanshi a tsorace. Mugun tsoronsa take ji. "Ki rufe min baki." Mufid yace yana watsa mata mari a fusace dan ta bashi haushi. Kamar shi yana binta tana gudunshi. Bai jira ta ƙara magana ba ya miƙa mai adaidaita dubu ɗaya. "Jeka dashi an bar maka." Nuratu dake ƙoƙarin kwace jikinta ga hawaye ya wanke mata fuskarta, mai adaidaita ya kalla ya kalli kuɗin. "Ba zan karɓa ba. Ka saketa ta shiga gida." "Ina ruwanka dani ko ita, yanzu sai in kifa ma mari, bar gurin nan." "Ka taimaka min!" Nuratu tace tana kallon mai adaidaita da duk tsoro ya cika shi da a daku da shekaru Mufid sai girmeshi zai dake shi. "I said leave here!" Mufid yace yana dakawa mai adaidaita tsawa da sauri ya kunna mashin ɗinshi ya bar gurin. Ganin haka Nuratu ta fasa ihu iya ƙarfinta tana kai mishi bugu. Baya ji haka ya jata ya buɗe motar shi ya jefata ya zagaya yana shiga ganin mutane sun fara maida hankali gurinsu ya ja motar yana barin gurin. Ihu Nuratu take yi tana bugan gilashin motar tare da ƙoƙarin cire lock ta gwamnace ta buɗe ta faɗi da ta keɓance da Mufid. Ta samu nasara ta cire lock tana ƙoƙarin buɗe ƙofar Mufid ya ankara da haka ya wani fizgota tare da yin wani wawan parking ya juyo yana kifa mata mari. "Kashe kan ki za kiyi?" "Gwara na kashe kai na da ka kai ni in da zaka kai ni. Dan girman Allah kayi hakuri ka rabu dani ka bar ni. Bana sonka bana kaunar ka. Ina da wanda nake so zan aura. Duk matan duniyar nan basu isheka ba sai ni . Ka rufamin asiri ka rabu dani. Bani da wani gata sai Allah in ka cutar dani ba zan taɓa yafe maka ba." Idanu kawai Mufid ya zuba mata har ta gama tana ƙara sautin kukanta. "You're so cute Baby Noor." Wani kallo ta watsa masa da jajayen idanuwanta murmushi kwance saman fuskarshi ta gani. "Ni ke kaɗai nake so kin isheni rayuwa. Duk macen dana kyalla ido na gani burina in samu abinda nake so wajenta in rabu da ita, kuma bana shan wahala wajen haka so mai yasa zaki bani wahala Baby. Na biki amma kin nuna min bakya so to naji na hakura. Zaki aure ni?" Wani harara ta kuma watsa masa cikin muryar kuka tace. "Allah kiyaye in auri mutum irin ka. Gwara na mutu babu aure, ko baka ji mai nace ba akwai wanda nake so zan aura ka rabu dani." "Haka ki ka ce?" Mufid ya faɗa yanayin fuskar shi yana canzawa. Ko ɗar ba taji ba ta ɗaga kai. Yayi wani dariyar shaƙiyanci yana kunna motar ta dube shi da sauri. "Ina zaka kai ni?" Bai kulata ba yaci gaba da tuƙi, Nuratu ta juya ta kalli garin magriba ta kusa saura mintuna ga wani lumshi da garin yayi alamar haɗari yana haɗuwa har iska ya fara kaɗawa. "Ka sauƙe ni." Tace cikin faɗa, tsoro yana ziyartan dukkan ilihirin jikinta da zuciyarta, ta fara ƙoƙarin buɗe lock ɗin motar Mufid yasa hannu ya damƙo hannayenta taji zafi ta kwace tana jan baya. "Dan girman Allah ka sauƙe ni inje gida. Ina zaka kai ni?" "In da ki ke buƙata mana, can za muje in kwashi rabona kafin wani ya kwashe." Nuratu ji tayi duniyarta ya tsaya jinin jikinta ya daina aiki ta tsaya dubanshi tana son fassara maganganun shi bata san lokacin da tayi wani kukan kura ba ta cafko hannayen shi dake saman sitiyari. "Wallahi baka isa ba, gwara na kashe mu daka cuci rayuwata." Zuciyarta gaba ɗaya ya bushe burinta ya tsayar da motar ta fita, ta gwammace ta mutu ko ta kashe kanta da taga wannan ranar, hawayenta ya kafe da duk wani kalma da zai fito daga bakinta. Mufid da kyar ya samu ya saita sitiyari yana riƙo hannun Nuratu da hannunshi ɗaya, ya samun gefen titi da babu mutane yayi parking, ganin haka Nuratu ta buɗe da sauri ta fita ganin yana ciro waya a aljihunsa yana ganin haka ya fita ya bi bayanta. Gudu ta fara dai-dai lokacin da ruwan sama ya sauƙa da ƙarfi lokacin duk ana cikin masallaci ana sallah mutanen dake waje suka fara shiga cikin gida. Ihu take tana gudu a taimaka mata kwata kwata ba wanda yake ji dan ƙarar ruwan saman da yazo da iska kowa burinshi ya shige gida, ta jiƙe sharkaf har ɗisa take a hakan bata fasa gudun ba. Gaf taji an bugeta da ƙarfi dai-dai lokacin da ta hau kan kwalta ta zo tsallakawa, ihu ta sake tayi sama ta faɗo saman hannun damanta da taji zafi ya ratsata ta saki wani azababben ƙara taji hannun ya saƙe. A hakan bata hakura ba ta fara ƙoƙarin miƙewa ganin wanda ya bugeta ya fito cikin sauri ya nufo ta. Dai-dai lokacin Mufid ya iso da nashi motar ya hangosu, cikin sauri ya fito ya isa wajensu. "Sorry Baby motar ne sai yanzu ya tashi. Muje ko." Mufid yace ya riƙo Nuratu ganin tana shirin barin gurin. Ganin haka ta kalli mutumin da ya fito yana binsu da kallon tuhuma ta girgiza kanta ta kasa magana. Zargine ya ɗarsu a zuciyarsa yaji ya kasa gaskata abinda ya gani ya nufi gurinsu dai-dai mota ta shiga tsakaninsu ya dakata yana kallo saurayi ɗaya ya fito daga cikin motar, kafin yayi ƙoƙarin zagayawa dan musu magana d'ayan ya jefa Nuratu cikin mota Mufid ya zagaya ya shiga motarshi suna barin gurin. Cikin sauri shima ya koma motarshi ya bi bayansu a guje, gudu kawai suke yana bin bayansu shima, wayar shi yana ta ƙara ya kasa ɗauka burinshi ya taimakawa budurwan da ya kalli tsantsan buƙatar taimako a cikin idanuwanta. Can cikin motar Mufid kuwa Nuratu ke fitar da hawaye tana roƙarsu da bakinta ke rufe da su rabu da ita, AA yana riƙe da ita ya samu nasarar cire mata hijab da ɗankwalin kanta ya ɗaure bakinta dan ta damesu da ihu. "Kayi sauri ka rigamu isa ka buɗe mana get, kaga wannan mutumin bin mu yake zai ɓata mata shiri." Mufid ke wannan wayar zuwa ga Faisal da yake d'ayan motar. Jin haka ya saka Faisal ƙara gudunshi har cikin unguwar da yake can bayan gari red brick, gidane madaidaici da suke kawo ƴan matansu suyi abinda suke so dasu su barsu. A waje yayi parking motarshi ya sauƙa ya buɗe get ɗin dai-dai lokacin Mufid ya shiga ya rufe get ɗin suka kulle gidan. AHMAD da yana shawo kwana yaga shigarsu da sauri ya ƙarasa da motar shi ya sauƙa. Bugun get ɗin gidan ya fara yaji basu da alamar buɗewa ya koma motar shi ya bar gurin cikin sauri. ... "Munirat shuru dai har yanzu Nuratu bata dawo ba, ga magriba ta wuce ruwan ma har ya fara tsayawa. Zuciyata bugawa yake, ji nake wani abu ya faru da ita ko zai faru da ita." Munirat dake zaune kusa da Mami da ko abincin dare sun kasa ci ta ce. "To Mami ko zaki ƙira Aunti Rahma ko Hasiya ko Rukayya ko taje gidansu." "Hakane kuma ɗauko min wayar, tunanin haka bai zo mini ba." Da sauri Munirat ta ɗauko wayar Mami ta ƙira Rahma da Hasiya sannan Rukayya duk amsa ɗaya suke faɗa mata bata zo ba, har Amma Jidda ta ƙira ko ta wuce nan amma duk amsar ɗaya ne. Mugun tashin hankali Mami ta shiga. "Munirat banga ta zama ba. Nuratu! Nuratu ban san ina ta shiga ba." Dauriya itama Munirat take amma idanuwanta cike suke da hawaye. "Mami ko ruwa ya tsayar da ita a hanya, mu bari zuwa anjima." Mami bata saurareta ba ta ɗauki mayafinta ta fita waje duk da har yanzu ana ɗisɗisa, bakin layi ta tsaya ko za taga zuwanta, hanyar shal kowa ya shige gida babu mutane sai ɗaiɗaiku dan har duhu ya fara shiga balle in anyi ruwa gari yana duhu. *** Kamar ƙaramar yarinya haka Mufid ya ɗauko Nuratu ya jefa saman gado ta faɗa saman hannunta, duk da bakinta rufe hakan bai hanata fasa ihu ba, ta saka d'ayan hannunta tana warware ɗankwalin bakinta domin d'ayan hannun jinshi take tamkar ba'a jikinta ba. "Please!" Tace cikin muryarta da baya fita tana jan baya ganin Mufid ya dumfaro ta. Tsoro, tashin hankali, ruɗani, gaba ɗaya Nuratu ta shiga. Bak'ar rana take gani a wannan ranar da lokaci ɗaya farin cikinta da mutuncinta zata rasa zai tarwatse. Faisal da AA ne suka shigo ɗakin, Faisal ya kalli Nuratu yadda ruwa duk ya jiƙa mata jikinta ya cije leɓɓensa da shaye-shaye ya mayar dasu baki. "She's so hot MK." "Ni zan fara da farko." Cewar Mufid ya nufan Nuratu, tana jin haka ta bi gefe zata sauƙa, AA ya saka mata ƙafa ta faɗi tim a ƙasa, ƙoƙarin tashi tayi tana ja baya. "Dan Allah na haɗa ku da Allah ku rabu dani. Kar ku cutar da rayuwata, wallahi na amince zan aure ka. Ka barni in tafi gida." "No Baby, sai mun fanshe wahalar da kika bamu." AA yace ya saka hannu ya ɗagata sama ya jefa saman gado yabi bayanta. Mufid da sauri ya hana shi ya tare tsakanin su yana cewa. "She's mine, dan haka ni zan fara." Kan Nuratu Mufid yayi ya fizgota ta fasa ihu tana ja baya. Mufid ya damƙota tare da saka hannun iya ƙarfinshi ya yaga rigar dake jikinta daga sama har ƙasa. Kuka ta fashe dashi tana saka hannunta ɗaya marar ciwo dan kare jikinta tare da duk addu'ar daya zo bakinta. Ji take duniyarta ya tashi, komai nata ya tsaya cak. BAƘAR RANA.. #vote #Comments. #Share MADUBIN GOBE (Haske) 13. Pharty Bb. Wattpad phartybb. ..... Runtse idanunta tayi wani hawaye mai zafi ya zubo bisa kumatunta, da sauri ta buɗe idanunta jin ƙiran sallar assalatu ta duba agogan wayarta. Baƙin dare baƙin rana shine sunan da ta ɗaurawa wannan daren da sanadin shi farin cikinta da komai nata ya tarwatse, duniyarta ya zamto babu komai sai duhu da ya kewaye, cike da damuwa da tashin hankali. Motsi taji bakin ƙofar ɗakinta da sauri ta miƙe tana haska gurin da hasken wayarta. "Waye?" Tace cikin dashashshiyar muryarta da tasha kuka cikin tsoro. "Ni ce Mamin ki, ki tashi kiyi sahur." Sai lokacin ta tuna da yau za tayi sahur dan azumin da take yi Litinin da Alhamis. "To ina fitowa." Tace ta koma ta zauna kusan mintuna biyar ta mike ta shiga bathroom ɗinta tayi brush ta wanke idanunta ta fita, bata san lokaci ya ja haka ba. Tea kawai tasha tace ta ƙoshi Mami ta bita da kallo. "Kin yi bacci kuwa?" Girgiza kai tayi tana barin gurin ta ɗauki maganinta tasha dan safiyar ba zata samu sha ba ta wuce ɗakinta. Alwala tayi ta fara nafila har aka fara sallar asuba kafin ta gabatar ta hau saman katifarta ta kwanta, sai lokacin wani bacci ya kwasheta da bata samu yinsa ba. Babu abinda za tayi da safiya hakan ya sata yin bacci har karfe goman safe kafin ta farka shima ƙarar wayarta ya tasheta ta ɗauka. "Aunti!" Taji da ƙarfi cikin wayar, muryar Hanan ne, yarinyar Dr Awwab, tun ranar da yarinyar ta ganta ta maƙale mata da hakan yake ƙara sakata kusanci da Dr Awwab. "Baby Hanan, ya makaranta? Yau mai ya hana ki zuwa?" "Aunti yau hutun mid term, Aunti zan zo wajen ki dan Allah kice Daddy ya kawo ni." Murmushi Nuratu ta yi jin shagwaɓar yarinyar. "Shikenan zan faɗa mishi, bawa Daddy wayar." Cikin ɗoki Hanan ta miƙa babanta wayan da yana aiki cikin computer a office ɗinshi, kasancewar ba makaranta ya shirya Hanan ta biyo shi. Bayan ya karɓa sun gaisa da Nuratu take faɗa mishi saƙon Hanan. "Kin amince in kawota kenan? Za ki gan mu a weekend Insha Allah." "To sai na ganku, ka gaishe da mutanen gida." Dr Awwab ya amsa da za suji kafin suyi sallama ya sanar Hanan ran Saturday za suje gurinta, cikin murna ta rumgume shi. .... Nuratu wanka kawai tayi ta fita falon ta kwanta saman kujera, dama in tana azumi bata iya ɗaukan ko tsinke amma a hakan dole take yi. Wayarta ta ɗauka ta buɗe data. WhatsApp ta shiga tayi dube dubanta da ganin status ɗin wanda zata gani, tana shirin rufe data ta ga shigowar saƙo. Kamar ba zata buɗe ba ta je kan sabuwar lambar da ya turo mata ta buɗe. *"Baby Noor."* Kawai ta ga an saka bata gama karanta sauran saƙon ba, ya haddasa mata tsoro ta miƙe zaune jin zuciyarta kamar zai faso kirjinta, wayar ta ajiye gefe tana matsawa. Mutum ɗaya ne zai ƙirata da sunan da ta tsana ji ta tsani mai furta shi. Cikin rawar jiki ta danna saman numbern ta saka shi cikin black list. "Ke lafiyarki ƙalau?" Mami da ta fito a ɗakinta ta hango Nuratu zaune cikin wannan halin. Hawaye take ma bata san ya fito ba sai da taji maganar Mami ta san da hakan. A tsorace take duban Mami tana nuna mata wayarta da hannu ɗaya ta kasa magana, maganar ya maƙale a bakinta. "Menene ya faru? Meye a cikin wayar?" Faɗin Mami cikin sauri tana ƙarasawa wajenta ta ɗauki wayar ta buɗe, ta dudduba babu komai sai datar ta a buɗe, ta kashe ta ajiye tana kallonta. "Menene Nuratu? Faɗa min." Tace ta riƙo hannunta tana danƙewa da ya saka Nuratu kallonta tare da faɗawa jikinta ta rirriƙeta, ta fashe da kuka. Mami duk ta shiga damuwa bata son ganinta cikin wannan halin, lallashinta ta hau yi har ta samu ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take sauƙewa. "Menene Nuratu na?" Mami tace tana dafa kanta, Nuratu ta riƙo hannunta. "Mami shine wallahi. Mufid ne, ya ƙi barin rayuwata na huta." "A ina? Ƙiran ki ya yi ko menene, kimin bayani." Shuru tayi kafin ta sanar da ita saƙonsa data samu ta WhatsApp yanzu. Mami kanta ta tsorata amma dan kwantar mata da hankali tace. "Ki bari ki ƙara bincike a kai ki tabbatar shine. Mufid baya nan yayi nisa da rayuwarki. Wani daban ne can bashi ba. Kuma tunda kin rufe layin bashi da damar sake miki magana. Ki kwantar da hankalin ki." Kai Nuratu ta ɗaga mata, haka Mami tayi ta kwantar mata da hankali har ta nutsu taji damuwar da take ciki ya ragu. Anan ta sanar mata Dr Awwab zai zo ran asabar shi da Hanan. Allah kawosu lafiya Mami tace cikin ranta tana wani tunani daban akansu dukkan su. Ganin ta samu nutsuwa ya saka Mami tashi ta koma ɗaki taci gaba da aikinta ta bar Nuratu. Ranar Munirat ta samu ƙira daga wajen kakarta ta musu sallama ta tafi, haushi Nuratu kamar tayi ihu haka ta daure ta dama musu kunu ta haɗa ƙosai da abincin da za suci in ansha ruwa. Ta gaji ta galabaita sosai sai daf da magriba ta gama ta watsa ruwa tare da ɗauro alwala, ta fito kenan ana ƙiran sallar magriba. Ruwa suka sha kafin su gabatar da sallah suka dawo dan cin sauran abinci. Washegarin a gida ta wuni dan makaranta ya ƙare sai jiran sakamakon mai kyau da shirin fita service. Haka kwanakin da ya biyo baya cikin hutu tayi su, bata ƙara samun saƙo daga wani daban ba, hakan yasa hankalinta ya kwanta. *** Ranar asabar. Tun safe aikinta tayi dan taran baƙonta da Hanan, da farko ta haɗa zobo mai kyau ta saka a fridge kafin ta haɗa fried rice da kaza yasha kayan lambu, tana gamawa ta shiga wanka. Bayan ta fito ta saka riga da skirt da ya zauna jikinta ba tayi wani kwalliya mai yawa ba sai hoda da kwalli da jambaki kalar kayanta maroon ta saka a bakinta. In ka kalli fuskarta za kace babu wani damuwa ko kunci a tattare da ita. Sai karfe biyu kafin Dr Awwab ya ƙirata cewa ya shigo yanzu zai ƙaraso. Tashi tayi ta ƙara kimtsa falon ta feshe jikinta da turare, har Mami na mamakinta a ranta tana cewa ko dai shine gwarzon. A waje yayi parking motarshi suka fito da Hanan yana riƙe da hannunta suka shiga cikin gidan da sallama, Nuratu da taji ta fito ta amsa tana musu sannu da zuwa murmushi kwance saman fuskarta da yake ƙara fito da dimple ɗinta gaba ɗaya yake lotsawa. Hanan tana ganinta da gudu ta sake hannun mahaifinta ta ƙarasa wajenta tana rumgumeta. Ɗagata sama Nuratu tayi ta rumgume yarinyar, ta mata kyau kamar kullum cikin riga t-shirt da wando kanta rufe da hula, ba wai dan babu gashin ba sai dan mutunta shi. Dr Awwab da ya zuba musu ido yana kallo, murmushi yake zubawa hannunshi cikin aljihun ƙananan kayan jikin shi. In yace basu burgeshi ba ya yaudari zuciyarshi. "Ni fa?" Ya samu kansa da furta hakan da ya saka Nuratu duban shi tamkar bashi yayi maganar ba. "Mu shiga daga ciki." Tace cikin basar da maganar bayan ta watsa mishi harara ta wuce cikin falon tana ɗauke da Hanan, ganin haka shima Dr Awwab ya bi bayansu cikin sallama yana zuba murmushi, idanuwan burgeshi suke duk lokacin da ta masa wannan kallon. Babu kowa cikin falon hakan yasa ya zauna saman kujera, sai lokacin Nuratu ta gaishe sa ya amsa yana tambayarta Mami ta miƙe ta ƙirata ta fito suka gaisa kafin ta koma ciki ta basu guri. Sama sama suke hiran dan yawanci hiran tsakanin Nuratu da Hanan ne kafin Nuratu ta gabatar musu da abinci da zoɓo da tayi. Kaɗan yaci sai dai yasha zoɓon sosai dan ya mishi daɗi. Hanan kam taci abincin sosai musamman kazar dan yaro da kwaɗayi ba kara. Sai bayan ya dawo daga sallar la'asar kafin yace za su koma. Hanan bata so ba, kamar tayi kuka suka fito waje bayan Nuratu ta cika ta da kayan zaƙi da ta saya ta ajiye musamman dan ita. Cikin mota Dr Awwab ya buɗe mata ta shiga tana ma Nuratu bye bye itama ta ɗaga mata hannu. Ya juya yana kallon Nuratu kafin yace wani abun ta rigashi. "Nagode Dr, Allah ya bar zumunci. Haƙiƙa naji daɗin zuwan Hanan yau." Nuratu ta faɗawa Dr Awwab haka da bai shiga cikin motar ba dan akwai sauran maganganun da baya son Hanan taji. Jin Nuratu na mishi godiya ya mai da hankali sosai kanta. "Ni ne da godiya Noor. Sai dai hanzari ba gudu ba. Ina da buƙata a wajenki, ni a gurina babba ne amma ban san ke ya zaki ɗauka ba. Ba maganar wasa bane Noor, ina so kiyi tunani a kai bazan takura miki ba. In har kin amince ina son auren ki Noor please ki bani wannan damar." Tun daga farkon soma maganar shi ta san in da ya dosa, bata ji haushinsa ko kaɗan ba ballantana Dr Awwab yana cikin jerin mutanen da suka taimaki rayuwarta, tana ganin mutuncinshi ko dan taimakon da ya mata a rayuwa. Murmushin saman fuskarta bai gushe ba tace. "Na ji Dr Allah ya saka, sai dai babu aure a cikin kundin rayuwar Nuratu, muci gaba da mutumcin mu ci gaba da mutunci kamar yadda mu ka saba." "Kar ki ce haka Noor, kar ki yanke hukunci cikin lokaci ɗaya na baki lokaci zan iya jiranki ko nan da yaushe ne." Shi kanshi mamakin kanshi yake yadda yake buɗe baki yake mata maganar aure. Ta san dama dakyar ya amince ko ya yarda tamkar sauran dan haka tana shirin shiga gida tace. "Shikenan zanyi tunani, Nagode sosai Dr." Daga haka ta shige gida ya juya ya shiga motarshi su ka bar gurin ko ba komai yaji kalamai daga gurin Nuratu mai daɗi. Tausayin halin da ta shiga tun ranar da ya fara ganinta shi ya rinjayi zuciyarshi akanta, wanda ya ɗauki abin ya ɗaura a mizanin tausayi daga baya ya ga sam ba haka bane. Duk da yayi ƙoƙarin kawar da hakan a ranshi amma zuciyarshi ta kasa nutsuwa. Tun bayan da mahaifiyar Hanan ta yi nesa dashi ya tarkata soyayya da komai ya jingina a gefe yaci gaba da kula ƴarshi kwaya ɗaya da Allah ya mallaka masa. *** Dr Awwab yana cikin jerin mutanen da take girmama su, suka mutunta ta suka taimaka mata lokacin da take tsananin buƙatar taimako. Bata san ta ya ya zata kaucewa buƙatarshi ba shi da sauran. Bata da komai bata da abinda zata saka musu dasu. Nuratu ke wannan tunanin yayin da take kwance cikin kujeran falon bayan ta dawo daga raka Dr Awwab, maganganun shi suke mata yawo a kai da ya sakata faɗawa tunanin rayuwarta kamar kullum yadda ta saba. Runtse idanunta tayi tamkar yanzu abubuwan suke faruwa. **** Tana ji tana kallo Mufid ya hawo jikinta tare da shafarta ta ko ina, mutsu mutsun kwace kanta take har lokacin bakinta bai daina ambaton Allah ba da roƙarsu akan su kyaleta. Hannunta ɗaya da yake iya motsi tasa take dukan Mufid dashi tare da ture shi iya ƙarfinta. "Ku riƙe min ita." Cewar Mufid cikin jin haushin yadda ta hana shi sakewa a jikinta. Jin haka AA da Faisal suka matsa tare da rirriƙe masa ita kafin ya afka mata cikin ƙarfi. Ba ya ji ba gani kawai ya fara ƙoƙarin shigarta domin ta riƙita shi sosai. Nuratu ji tayi wani azababben zafi ya ratsata ta fasa ihu da ƙarfi, cikin sauri AA ya rufe mata bakinta da hannunshi. Ihu Nuratu take ba ya fita, idanunta tamkar garwashi tsabar fitar hawaye da azaban zafi da take ji yana shigarta yana ratsa dukkan ilahirin jikinta. Tun tana ihu su saketa har tazo ta gagara yin komai jikinta ya sake idanunta suke rufe ta daina jin komai da kowa numfashinta ya ɗauke. Mufid bai ma sani ba domin yi yake yana sakewa dan ya samu abinda yake so, yana shirin sakewa Faisal ya dakatar dashi. "Ai ya ishe ka Mufid, sai ka bari mu yi ai." Faisal yace ko duba da halin da Nuratu take ciki baya yi. "Ai baku ku ka kawota ba." Mufid yace yana sake komawa kan Nuratu. Kamar daga sama suka ji ƙarar bindiga sau biyu a ƙofar gidan da ya saka su tashi tsaye gaba ɗayan su cikin tsoro, kafin suji an fara sanarwa cikin loud speaker cike da umartan su. .... #vote #comments #share MADUBIN GOBE 14. Pharty Bb Wattpad phartybb. *** Cikin umarnin da tsoratarwa aka fara sanar dasu cewa. "Ku fito da kan ku, ko in muka shigo mu harbeku! Wanda yayi yunƙurin guduwa in har mu ka kamashi bayan azaba da zamu gana mishi akwai hukuncin kisa ta hanyar wulaƙanci." AA da Faisal sun tsorata sosai musamman Faisal dan ya fisu tsoro da ma, Mufid kayan jikinshi yake maidawa ko a jikinshi, in dai irin wannan kamu ne ansha musu kuma ana yin belin su mai na jin tsoro. "MK ya za muyi, wallahi tsoro nake ji. Mu gudu mu haura gini yadda ba su isa su kama mu ba." Faɗin Faisal a gigice. "Calm down Fai you have me. So mai ka ke jin tsoro? Mintuna kaɗan za muyi a cell mu fita kuma kasan haka, so mai abun tsoro to? Mu je kawai." Faɗin Mufid yana nufan kofar waje ko a jikinshi, an sha kama su da kayan maye, harkar fyaɗe duk suna tsira to menene kuma sabo. Suma sun san hakan domin in dai an kamasu to mahaifin Mufid duk in da zai shiga zai shiga ya fita sai ya fitar da ɗanshi da su, amma yau haka kawai suka ji tsoro. Hannunsu a sama sun sadauƙar suka fito, Mufid ne a gaba sai AA da Faisal a bayanshi suna ƙare kansu, hasken motocin police da na Ahmad ya haskasu sosai. "Go down." Ɗan sanda ya basu umarni yana nunasu da bindigar hannunshi, ba musu suka durƙusa saman gwuiwowinsu a ƙasa duk da anyi ruwan sama caɓi ya ɓata ƙasar, hannayen su a sama Mufid ya ɗaga ido suka haɗa ido da Ahmad da ranshi haɗe tamkar bai taɓa dariya. Ahmad ji yake zai iya kashe Mufid da da bindiga a hannunshi. Ganin dukkansu sun fito cikin sauri Ahmad ya nufi cikin tare da ƴan sanda biyu suka fara bincike. Tun a falon suka fara cin karo da hijabin Nuratu da yake yashe. Ɗakuna biyu a jere wanda yake buɗe idanuwan Ahmad suka kai gurin da sauri ya nufa nan. Abinda ya gani ya mugun tayar mishi da hankali, tashin hankalinshi ya ƙaru, idanuwansa ya runtse dan ba zai iya juran ganin halin da take ciki ba, dakatawa yayi ya juya sauran ƴan sandan suka ƙaraso wajen. "Ka sameta Sir?" Ɗaya daga cikin ƴan sanda investigator Lawan ya faɗa yana ƙoƙarin shiga da sauri Ahmad ya tare shi yana tare hanyar, ransa a mutuƙar ɓace. "Ƙira motar emergency daga asibiti, sun riga sunyi raping ɗinta, Ina ga babu numfashi a tare da ita." Su kansu ƴan sandan sun ji abin wani iri, duk da ba yau suka sa ba samun case na fyaɗe ba domin abin ya zamto musu kamar karatu ba'a kwana biyu ba'a kawo musu case na fyaɗe ba, abin ya zama tamkar cin tuwo a rayuwar yanzu, yiwa yara, ƴan mata, matan aure fyaɗe ƙarfi da ya ji. Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya fita ya sanar da Ogansu, investigator Lawan ya fara ɗaukar rahoto dan samun shaida. Cikin sauri Oga Salisu ya bada umarni aka ƙira emergency tare da sakawa su Mufid ankwa aka jefasu a cikin mota. Mintuna goma sai ga motar emergency ta iso suka shiga cikin gidan, abinda suka gani ya basu mamaki, zuciyoyinsu suka cika da tausayi da rauni tare da ruɗani, Nurse biyu aka haɗasu da shi suka zo mace da namiji.  Macen tsorata tayi jikinta ya hau rawa, Namijin ne yayi ƙoƙarin rufe jikin Nuratu sai ya kasa ɗaukarta ya ɗaurata saman ƙaramin gadon da suka shigo dashi, ganin haka Ahmad da yake baƙin kofa ya juyo ya ga ya rasa ta ina zai ɗagata. Cikin sauri ya iso ya saka hannun sa ya ɗauketa tare da bismillah suka fita. Cikin motar ya kwantarta saman gadon Nurse ya fara ƙoƙarin saka mata Oxygen ganin bata numfashi. Tafiya kawai suke motar ƴan sandan ta wuce da su Mufid Police station bayan sun bar saura biyun sun bi motar asibiti,  Ahmad daya koma motarshi shima yana bin bayansu. Ƙiranshi ake a waya ya duba ya ga mahaifiyarshi ce tun tasowar shi take ƙiran. Ɗauka yayi bai iya jira ta faɗa abinda zata faɗa ba ya tari maganarta. "Umma dan Allah kiyi hakuri, na shigo Damaturu ruwa ya tare ni a hanya, ki bani mintuna talatin yanzu zan shigo garin." "Ka koma inda ka fito bama buƙatar ka." Bata jira mai zai ƙara faɗa ba ta kashe wayarta. ... Suna isa asibitin aka karɓi Nuratu aka wuce da ita ɗakin aikin gaggawa, Dr Sadiq da yake duty ya shiga ya fito ya samu ƴan sanda da Ahmad da suke tsaye. "Is a rape case." "Yes we know it, kayi aikin ka ka ceto ran yarinyar nan, and i need proof. Dan billahil azim ba zan bar yaran nan ba sai an musu hukunci dai-dai da abin da suka aikata." Ahmad yace har lokacin ransa a haɗe, bai taɓa jin ɓacin rai irin na wannan ranar ba. Jin haka ya saka Dr Sadiq komawa ɗakin ya fara taimakawa Nuratu da duk abinda ya san zai iya, shi kanshi ya wahala domin Mufid ya mata rauni sosai ban da gurɗewar da hannunta yayi. Numfashinta ya samu ya dawo dai-dai ya kimtsa ta ya saka mata drip da alluran bacci ciki, tare da taimakon Nurse ɗin suka rufeta suka fito. Awansu biyu kafin su fito har lokacin Ahmad tsaye yake kyam ya kasa ko motsawa, ganin fitowar Dr ya nufeshi. Ofishin Dr Sadiq suka nufa da Ahmad da investigator Lawan bayan sun zauna, yana dubansu. "Numfashinta ya dawo dai-dai, tana bacci zata iya farkawa ko yaushe, ta ji ciwo sosai saboda ƙarfi suka nuna mata, amma Insha Allahu na shawo kan matsalar, zata warke amma zai ɗan jima sai an haɗa mata da magunguna da wasu abubuwa " "Kana ɗaukar jawabin sa?" Cewar Ahmad ga investigator Lawan bayan ya gama sauraron bayanin Dr Sadiq. "Yes Sir." Cewar investigator Lawan da yake ɗauke da takarda da biro yana rubuta duk abinda Dr Sadiq ya faɗa. Miƙewa Ahmad yayi tsaye. "Mungode Dr fatan in an ƙira ka gaban kotu zaka maimaita abinda ka faɗa yanzu." "InshaAllah zan faɗi komai cikin abinda na faɗa har da wanda zan sani nan gaba domin akwai bincike da za muci gaba da yi dan samun cikakken shaida." Faɗin Dr Sadiq bai ji ko dar a jikinshi ba domin shi kanshi ya tausaya yarinyar, kuma ya ji zai iya bada shaida ko dan a hukunta waɗanda suka aikata mata haka. "Mungode Dr, ka kula da ita abar mata Nurse ɗaya a wajenta, za mu koma Division." To Dr Sadiq ya faɗawa Ahmad da investigator Lawan kafin suka wuce. Suna zuwa Division suka samu an saka su Mufid a cell. "Zan wuce Maiduguri da ma wucewa na ke Allah ya ƙaddara zan shiga cikin lamarin kamar yadda na sanar da ku. Ga card nawa dan in wani abin zai taso ina buƙatar sani, may be gobe da safe zan shigo. And lastly wallahi kar wanda ya bada belin su, idan iyayensu sun zo ku sanar dasu mu haɗu a court domin babu bailing. Batun iyayen yarinya kuma idan ta farka za ta sanar da Dr a ƙirasu su zo, kar ku damu da wannan." Ahmad ke wannan bayani har ya gama ba wanda yayi magana. "Ok Sir za'a yi yadda ka faɗa." Cewar DPO Salisu ya karɓi card ɗin Ahmad ya jefa cikin wardrobe ɗinshi kafin suyi musabaha Ahmad ya wuce. Cikin daren ya kama hanyar Maiduguri, ƙarfe goma saura ya isa cikin unguwar su GRA kai tsaye gidansu ya nufa bayan yayi parking ya wuce babban falon babu kowa hakan yasa ya hau stairs ya duba ɗakin Umma bata nan ya wuce ɗakin mahaifin shi, gaba ɗayan su har ƙannenshi mata suna nan. Jin motsi da sallamar shi ya saka su juyawa suka dube shi babu wanda ya tanka. "Ka fita ka koma in da ka fito." Cewar Umma tana sharan hawaye.  Da sauri Ahmad ya ƙarasa ciki. "Umma dan Allah kiyi hakuri, wallahi wani case na tarar ya sani dakatawa dan ɓullowa lamarin amma yanzu allahamdulillahi gani na zo lafiya." Girgiza kai ta yi. "Yanzu Ahmad in mahaifinka ya mutu kace me? Shekaru nawa mu ke binka ka zo? Yanzu mun samu ka taho shine ka tsaya a wani hargitsi da bai shafeka ba." "Ki yi hakuri Umma." Ahmad yace dan shima ya san bai kyauta ba. Jikin mahaifinsu ya duba ya ga yana bacci hakan yasa ya fita, ɗakin da babu komai ya shiga yayi wanka ya canza kayan jikinshi kafin ya gabatar da salloli ya fito. A falo ya samesu zaune harda ƙannen shi masu aure wasu da ƴaƴan su. Yarinyar da ya gani ƴar shekara biyu zaune tana wasa ya ɗauka. "Babyn waye?' Yace yana ma yarinyar wasa. "Ƴar Suwaiba ce." Cewar Umma dan sauran duk sunƙi masa magana kuma yasan fushi suke da shi. Ya kasance shine babba kuma shekara huɗu tinda ya tafi bai waiwaye su sai waya. "Shi yasa na ganta mummuna." Yace yana jan kumatun yarinyar. "Wallahi ta fika kyau." Cewar Suwaiba jin an zaga mata ƴa hakan ya sa sauran suka kwashe da dariya. *** Mami ta mugun shiga tashin hankali marar misaltuwa, ta ka sa zama ta ka sa nutsuwa, hawaye kawai take fitarwa tana addu'a Allah ya sa Nuratu tana hali mai kyau. Haka Munirat ma da dauriya kawai take. Sun je gidan Aunti Zarah babu Nuratu, ta ƙira Amma Jidda babu Nuratu, ta ƙira Rukayya Aunti Rahma da Hasiya duk Nuratu ba ta je musu ba. Kawayenta biyu ta sani kuma ba ta tunanin za ta je musu ba tare da izininta ta ba, har ta kai karfe goman dare bata dawo ba. A ranta kawai ji take an sace mata Nuratu. *** Sai washegarin da kusan azahar iyayen Mufid suka san baya gidan, shima sai da ya ƙirasu da wayar ɗan sanda ya mishi ƙaryar abinci zai kira a kawo mishi. Anan ya ƙira Daddyn shi ya sanar dashi yana police station an kama shi. Sababi da faɗa Alhaji Kashim Mufid ya hau yi kafin ya sanar da shi yana zuwa yanzu. Ummu kawai ya sanarwa ya kaɗa babban rigarshi ya fita. Rufaida da take zaune kusa da Ummi jin an kama Mufid yana Division ta shiga ruɗani. "Kar dai fyaɗe ya yi wa Nuratu?" Cikin sauri tambayar yazo kanta, da sauri ta miƙe ta shige ɗakinta, kukan da take dannewa ta fashe dashi. Shikenan dalilinta rayuwar Nuratu ya lalace, addu'a take da fatan Allah yasa ba haka bane wani abun daban ya aikata. ... Nuratu bata farka ba bata san in da kanta yake ba har ƙarfe goman safe, Nurse da take kula da ita ta gama duty nata ta sanar da Dr Sadiq ya canza wata bayan ya duba jikin Nuratu, drip ɗin ya ƙare ya canza mata wani, yana mamakin har yanzu bata farka ba balle ta sanar da su iyayenta a sanar da su dan ya san zuwa yanzu hankalinsu a tashe yake. *** "Uban waye ya ce ba za'a ba da bailing ɗana ba? Fyaɗe to kanshi aka fara ko kanta aka fara? Shi waye da zai hana ba da bailing ɗin a sanar da ni wanene shi. In Kuɗi yake buƙata ko nawa ne ya sanar da ni in bashi ya a sakar min ɗa na?" "Ni ne nan na hana." Gaba ɗaya suka juya gurin Ahmad da isowar shi kenan ya juyo maganganun Alhaji Kashim Mufid. "Kai waye? Kuɗi ka ke buƙata ko menene? Ka sanar da ni zan baka ko nawa ne ka saka a fitar min da yaro." Faɗin Alhaji Kashim Mufid. Guri Ahmad ya samu ya zauna cikin kujeran ofishin yana nuna kanshi da yatsar shi manuniya. "Ni Col. Ahmad Tafida bana buƙatar kuɗinka domin za su maka amfani, ka shirya sammaci kawai domin yau ba gobe ba court za'a taru mu." Cikin faɗa Alhaji Kashim ya miƙe. "Ka isa? Wallahi baka isa ba! amma ba komai muje mu gani waye zai faɗi, ina jiranka." Daga haka ya sa kai ya fita ko ta kan Mufid bai bi ba ya bazama neman lauya da zai kare ɗanshi kamar kull dan ya lura wannan yaron yana neman shiga masa hanci. Bayan fitar Alhaji Kashim, Ahmad ya kalli DPO Salisu. "Thank you da ku ka bi magana na, ina son a tura mu court zuwa gobe, zan je duba jikin yarinyar sannan in sanar da iyayenta in sun zo su shirya." "Babu komai Sir Allah taimaka." Cewar Salisu sali yana mamakin ƙarfin hali irin na Ahmad da ya jajirce sai an kwatarwa Nuratu haƙƙinta. Ko ba komai ya burgeshi dan da wuya shari'a na fyaɗe yake faruwa a ɗauki mataki a yanzu. .... Asibiti kai tsaya Col. Ahmad ya wuce dan duba jikin Nuratu, ɗakin da take ciki ya leƙa ya samu Nurse zaune kusa da ita. "Ya jikinta bata farka ba?" Ahmad ya tambayi Nurse ɗin yana ƙarasa bakin gadon. "Eh tun jiya har yanzu." Ta bashi amsa. "Iyayenta fa? Har yanzu? Sun samu labari?" Yace yana kai kallonshi kan Nuratu da bata san wani duniya take ciki ba. "A'a ba wanda ya zo a matsayin nata har yanzu?" Shuru Ahmad yayi kafin ya fita a ɗakin ya wuce office din Dr Sadiq Shima dai maganar ɗaya ne har yanzu babu wani nata da yazo. Ya tambayi jikinta yace sai ta farka za su ga yanayin. Har karfe uku kafin Ahmad ya kama hanyar Maiduguri dan gudun fushin Umma. *** "Officer yarinyana tun jiya da ta fita dan zuwa makaranta bata dawo gida ba, na duba duk in da zan duba mun bincika amma babu labarin ta." Mami ke wannan bayani tana sharan hawaye da idanuwanta da suka kumbura tsabar kwana da tayi tana kuka. Safiyar yau ya sameta a police station dan ba da report ko zasu taimaka mata. #vote #comments #share MADUBIN GOBE  15. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Me ye sunanta da shekarunta da kuma unguwa?" Faɗin ɗan sanda da yake ɗaukar rohoto. "Sunanta Nuratu Mamman Bashir, shekarunta ashirin tana unguwar nan." Faɗin Mami hawaye wani yana bin wani. Report suka ɗauka da komai na dangane da Nuratu da lokacin fitarta kafin su sallame Mami cewa Insha Allahu zasu yi ƙoƙari akan maganar. Mami gidan Aunti Zarah ta nufa tana kuka ta sanar da ita har yanzu Nuratu ba ta dawo gida ba kuma ta ƙira kowa bata tare dashi. Tashin hankali Aunti Zarah ta shiga, shuru kawai tayi ta rasa abinda za tace kafin ta hau lallashin Mami. ... "Ina son ganin Mufid Kashim Mufid domin mishi tambayoyi." Faɗin lauya da Alhaji Kashim ya ɗauko har zuwa Division dan a fitar masa da ɗansa. Ba musu DPO Salisu ya ba da umarni aka ciro Mufid ya zo. Tambayoyi lauya ya mishi akan abinda ya sani. Buɗar bakin shi yace ya aikata abinda lauya baya son ji kenan. Haka ya saka AA da Faisal gaba da tambaya dukka cewa suke ba su yi ba su. Sallamar su yayi aka mai da su cell. "Yara dai sun ce basu aikata ba. Dan haka wannan abun ya zama tuhuma a bamu belin su kafin a shigar da ƙaran koto a saka ranan zaman shari'a, na maka alƙawarin su Mufid za su halarci wannan zaman domin ni ne lauyan da zan kare su." Faɗin lauya bayan an shigar dasu Mufid cell. DPO cike da mamakin ƙaryar su Mufid yake duban lawyer da yabi bayansu. Sun amsan laifinsu har sun saka hannu a jiya yanzu kuma suce basu aikata ba. Murmushin taƙaici ya yi. "Haka suka ce, amma da idona na gani. Ba wannan ba ma, ba zan bada bailing ɗinsu ba sai wanda ya kawo ƙarar ya amince." "Waye shi?" Cewar Barrister Auwal cikin jin haushi. "Zuwa gobe ku dawo za ku haɗu dashi yanzu baya nan." Ya basu amsa. "Wani asibiti take yarinyar?" Barrister Auwal ya nemi sani dan samun ƙarin wani bayanin. "Mai za ku mata? Gargadinta akan kar tayi ƙara da ku? Ko kuɗi zaku bawa Dr ya ɓoye gaskiyar lamari?" DPO Salisu yake zuba musu wannan tambayoyin kai tsaye. Murmushi Barrister Auwal yake kamar maganganun DPO Salisu bai shige sa. "Ko ɗaya DPO. Tambayoyi kawai zan mata, ina son tabbatar da su Mufid sun aikata laifinsu in nemi hanyar ɓullowa lamarin kafin a shiga koto." Kamar mai nazari sai kuma DPO Salisu ya sanar da su sunan asibitin da Nuratu take, Alhaji Kashim da lauyan shi Auwal suka nufa can. *** Ita kaɗai ce cikin duniyar da babu komai sai duhun da ya mamaye, babu kowa sai ita, gabas da yamma ta duba babu wani haske balle hanyar fita, kamar daga sama ta dinga jin kuwar dariyarsu da tashin muryoyinsu cikin kunnuwanta suna ƙoƙarin kusanto ta. Bata ganin mai zuwa dan duhun da yake mamaye da ita, hakan yasa tasa hannuwanta take kai naushi a cikin duhun da bata ganin komai. A zahirin gaske kuma Nuratu ce da tun farkawar ta take kokuwa da Nurse da Dr Sadiq. Nurse dake zaune tana lura da ita ta ga ta fara motsi da sauri ta ƙarasa wajenta tana dubata. Buge buge kawai ta fara tana jijjiga gadon da jikinta. Nurse ɗin ta tsorata da ganin haka ta fita da sauri ta ƙira Dr sadiq  Tare suka dawo ta sanar dashi abinda ya faru. Jin muryoyinsu shi ya ƙara rikita ƙwaƙwalwar Nuratu ta fara kuka tana bugunsu tamkar mahaukaciya dan ganinsu take kamar su Mufid, abin da suke faɗi kuwa jinsu take kamar kalaman su Mufid suke maimaitawa yayin da suke saman kanta. Sai da taimakon Nurse biyu mata suka danneta Dr Sadiq ya samu ya mata alluran bacci ta sulale ta kwanta a gadon. "Hauka take ko me?" Su ka tsinci muryar Lauya Auwal a baƙin kofar ɗakin da sauri suka juya dan babu wanda ya ankara da shigowarshi. "Ba hauka take ba. Who are you?" Faɗin Dr Sadiq ya kalli Nurse. "Kar ki bari kowa ya shigo ɗakin har sai iyayenta sun bayyana." Daga haka ya fita yana rufe ƙofar Auwal ya bishi da sauri. "Gurin ka na zo Dr." "Biyo ni office ɗina." Yace yana yin gaba. Bayan ya shiga ya zauna Auwal da Alhaji Kashim suka shigo tare, hannu suka miƙa masa ba musu ya amsa su ka yi musabaha. "Ina jinka?" Cewar Dr Sadiq. "Iyayenta fa? Ba su da labari?" Barrister Auwal ya faɗa. "Yes." Dr Sadiq ya bashi amsa. Gyaran muryar Barrister Auwal ya yi. "Akan rape case ɗin Mufid Kashim Mufid ne na shekaran jiya an kama su sun yi, yarinyar tana asibitin nan. Ko dai ita ce wannan mai haukan? Shin dagaske ka ga alamar fyaɗe a tattare da yarinyar ko kuma da son ranta a ka mata haka? You know what i mean you're a doctor." Wani kallo Dr Sadiq ya ke masa yana juyi saman kujeransa har Barrister Auwal ya gama magana kafin ya gyara zaman kujeransa yana fuskantar shi. "This is rape case, rape ne da na jima ban haɗu da irinshi ba, ba zan baka any proof ba dan nema maka hanyar kare masu laifi, mu haɗu a koto kawai. Sannan yarinya yes tana hauka, tana hauka ne bisa abinda ɗanku ya mata, but inshaAllah zuwa nan da wani lokaci muna sa ran samun sauƙinta a shiga koto. And you can go out please." "Haka ka ce?" Cewar Alhaji Kashim da sai lokacin yayi magana. "Yes akwai wani abun?" Dr Sadiq ya ce yana watsa masa wani kallo. Alhaji Kashim zai faɗi wani abun da sauri Barrister Auwal ya tare shi. "Mu je Alhaji za mu san yadda zamu ɓullowa lamarin." Bayan fitarsu Dr Sadiq ya cire eyeglasses ɗinsa, halin da Nuratu take ciki ya faɗa tunani. Ya kamata ƴan uwanta su san halin da take ciki musamman mahaifiyarta. Abinda ya faru da ita yayi ƙoƙarin taɓa mata lafiyar ƙwaƙwalwarta da tana bukatar taimakon gaggawa. .... Alhaji Kashim Mufid da Barrister Auwal Division su ka koma. Bayan sun zauna da DPO Salisu, Barrister Auwal yace. "Muna son magana da wannan yaron da ya kawo karan." "Sai dai gobe ku dawo idan ya shigo zan sanar dashi ya jira ku." DPO Salisu ya basu amsa yana mamakin ƙarfin halinsu da su ka jajirce sai an bada belin su Mufid ko duba da laifin da suka aikata basa yi. "Shikenan ka tabbatar ka sanar dashi dan Allah." Barrister Auwal ya faɗa daga haka suka fita Barrister Auwal yayi ta kwantarwa Alhaji Kashim hankali akan zuwa gobe zai san yadda ya ɓullowa lamarin tun da dai yarinyar bata hankalinta za su samu bailing su Mufid, maganar shiga koto dole za'a jingina a gefe har sai ta warke. *** Hijabinta kawai ta zurma saman kayan jikinta ta fita waje ko duba lokaci ba ta yi. Adaidaita ta shiga ta sanar dashi in da zai kaita, tafe suke tana sharan hawaye tausayin halin da Nuratu take ciki take. Tana jin sadda Daddyn su yake sanar da Ummu yadda aka yi. Ba abinda yafi ɗaga mata hankali sai jin Nuratu bata hankalinta ga har yanzu iyayenta basu da labarin, ta gwammace ta sanar dasu ko da rabin abinda ta sani ne. Ba tasan sun shiga unguwar ba sai da mai adaidaita ya sanar da ita wani layi za su shiga ta ankara ta sanar dashi, har ƙofar gidan su Nuratu ta nuna mishi ya sauƙeta ta bashi kuɗin kafin ta shiga cikin gidan da sallama. Munirat ita kaɗai ne a gidan ta amsa tana shimfiɗa mata abin zama dan ta ganeta. "Mami bata nan." "Bata nan tana gidan Aunti Zarah." Cewar Munirat. "Ko gidan da nisa ina son sanar da ita wani abu ne." "Kin san inda Nuratu take?" Ta tambayeta da sauri. Idanuwan Rufaida cike da hawaye tace. "Ban sani ba amma ina tsammani na kusa sani." "Dagaske, tashi mu je." Munirat tace da sauri ta miƙe suka fita, sun samu Mami na ƙoƙarin barin gidan suka isa Rufaida ta sanar da ita cewa ta san dai Division da suka san in da take, su za su san asibitin da take, kwata kwata ta kasa sanar dasu abinda ya faru balle su ji haushinta. Mami, Aunti Zarah da Munirat suka nufi station ɗin Rufaida ta koma gida ganin anyi magriba. Tafiya suke zuciyar Mami bugawa yake burinta ɗaya abinda take hasashen ya faru da Nuratu addu'a Allah yasa ba haka bane. Bayan sun gabatar da kansu shi kan shi DPO Salisu ya yarda ita ce mahaifiyar yarinya duba da yadda take fitar da ruwan hawaye ga kamanni, anan ya haɗasu da investigator Lawan ya ɗauki information na su kafin ya musu rakiya zuwa asibiti akan in sunje Dr ya sanar da su abinda ya faru dan su ma sun gagara sanar da su. Abin ne da ciwo. Suna isa asibitin kai tsaye ɗakin da take ciki suka shiga basu jira fitowar Dr Sadiq da aka ce yana ciki ba. Yarta ta hango ana ɗirka mata allura sai rirrike ta ake tamkar mahaukaciya dan buge buge take. Salati Mami ta saka tana fashewa da kuka da sauri ta ƙarasa wajen Nuratu tana ƙiran sunanta, hakan shi ya ƙara hargitsa kan Nuratu ta dinga wani kuka kamar ba ita ba, wani ihu ta fasa tana neman kwace kanta dan tun jiya in sun mata alluran ji take kamar ranta zai fita, ga hannu da ya kumbura da ciwo ko zafin shi ba ta ji. "Mama ku fita dan Allah." Dr Sadiq yace bayan ya samu ya yiwa Nuratu allura ya riƙeta yana son bacci ya ɗauketa. Kasa motsi Mami ta yi jiri yana neman ɗaukarta da sauri Aunti Zarah ta riƙeta suna ganin ikon Allah. Domin ana yiwa Nuratu allura bata jima ba bacci ya kwasheta. "Mu je waje." Dr Sadiq yace bayan ya kwantar da Nuratu yayi gaba su ka bishi a baya har office ɗinshi. "Menene haɗin ki da ita?" Dr Sadiq ya tambaye Mami da take jin kamar ta zauce dan tashin hankali. "Yarta ce, tun shekarsn jiya take nemanta daga fita makaranta bata dawo ba." Aunti Zarah take wannan bayani dan Mami ta kasa magana sai kuka da take yi. "To allahamdulillahi tun da kun samu labari, dan yau kwana biyu muna jiran ta dawo hankalinta ta sanar damu inda iyayenta suke amma abin ya gagara, dan a birkice take farkawa domin abinda ya faru da ita yana neman shafan ƙwaƙwalwarta." "Me ye faru da ita Dr. Bani da labarin komai." Cikin sauri Mami ta tambaya sai lokacin ta iya magana. "Baku da labari?" Dr Sadiq ya tambayesu cike da mamaki. Kai kawai suka ɗaga masa. Nauyi bakinsa ya mishi da kyar ya furta. "Fyaɗe aka mata wasu samari uku, yanzu haka suna kame domin wanda ya taimaka mata ya saka an kamasu sai an bi mata haƙƙinta." Numfashin Mami ne ya tsaya cak cikin tashin hankali, da kyar ta samu tayi kokuwa dashi ta fara shaƙa, hawayenta ya kafe zuciyarta ya bushe tana duban Dr da gani take tamkar a mafarki yake faɗa mata haka. A hankali take furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihin rajiun. Aunti Zarah da take kuka ita ma ta kasa magana domin ba su san mai za suce ba. Ganin halin da suke ciki Dr Sadiq yayi ta kwantar musu da hankali duk da ya san da wuya hankalinsu ya kwanta. Ƙarshe yace. "Za ku iya shiga ku zauna da ita mu ga zuwa tashin ta." Miƙewa su ka yi suka fita basu iya mishi godiya ba Mami ta wuce ɗakin Aunti Zarah ta tsaya magana da investigator Lawan. Mami idanu kawai ta zubawa Nuratu mata duk ta hargitse gashin kanta duk ya warware. Kallo ta bita dashi gaba ɗaya ta canza cikin kwana biyun. Kifa kanta tayi jikin gadon ta fashe da kuma mai cin rai. Shikenan rayuwar ƴarta ya lalace akan wani yaro. Basu da wani gata da ko kuɗi da zai kwata musu haƙƙin su sai Allah. Kuka take har maganganun zuciyarta yana fitowa waje taji an dafata. "Kiyi hakuri Hajiya Sadiya ƙaddarar ta kenan, ke in ta farka ta ganki wannan halin a hakan za ta ji kwanciyar hankali a duniyar ta." "Ki bar ni nayi kuka Zarah, rayuwar yata ya lalace, duniyarta ya tarwatse, farin cikinta ya gushe, maza uku fa? Nuratu nawa take? ko namiji ɗaya ya mace take ji balle maza uku! Tsakani na dasu sai Allah ya isa domin ba zan taɓa yafe musu ba. Bamu da wani gata ko kuɗi da mulki da zai kwatawa ƴata haƙƙinta, sun riga sun cuce ta sun cuce ni." "InshaAllah Allah ya nan zai taimaka mana." Shuru kawai Mami take tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai. "Ƙira min Munirat taje gida ta kwaso mana kayanmu da duk abin buƙata." "Bari mu je mu dawo." Aunti Zarah tace ta fita suka wuce gida da Munirat tare bayan sun kwaso komai Aunti Zarah ta wuce gida dan har lokacin Nuratu bata farka ba. *** Washegarin ranar Ahmad bai samu zuwa ba sai wajen sha ɗaya, bai isa asibitin ba ya fara wucewa station dan tun safiya ya samu labarin ana neman shi. Anan ya tarar Barrister Auwal ya iso tare da Alhaji Kashim. Kallo ɗaya ya musu ya zauna yana gaisawa da DPO. "Belin Mufid suke buƙata Col. Ahmad." "Akan wani dalili?" Yace yana ƙara haɗa rai. "Akan dalilanmu. Na farko dai alƙawari na maka in an tashi case ɗin nan za'a shiga kotu da kai na zan kawo su Mufid domin za muyi yarjejeniya kowa ya saka hannu ka ga babu batun yaudara. Na biyu kuma yarinyar da ake case a kanta har yanzu iyayenta basu bayyana ba, sannan bata cikin hankalinta balle ta bada shaidar eh an mata fyaɗe a'a ba'a mata ba. To ka ga ana buƙatar lokaci dan samun lafiyarta. Shine nake neman alfarma a bamu belinsu dan Allah Sir a taimaka." Barrister Auwal ya ƙarasa maganar cikin kwantar da kai da roƙo. Col. Ahmad kallon DPO Salisu yayi kafin yace. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  16. Pharty Bb. Wattpad phartybb. **** "Sir! Za'a iya bada bailing su sai har yarinyar ta warke a shigar da ƙara kotu, muna da every record na case ɗin nan kuma na maka alƙawarin babu abinda zai canza a ciki Insha Allahu. Kuma za muci gaba da zuwa dubata har ta samu lafiya muna ɗaukan wasu bayanai da za'a rasa ba." Col. Ahmad ya yarda da zancen DPO Salisu da kafin yayi magana ya sanar dashi haka. Anan ya amince DPO ya rubuta takardan yarjejeniya su kayi signing. A take DPO Salisu ya saka aka fito da su Mufid da Faisal a gaban Col. Ahmad. Kallon kallo Mufid da Col. Ahmad su kayi kafin Mufid yayi wani yunƙurin Col. Ahmad ya ciro bindiga Piston cikin coat ɗinshi ya saita Mufid dashi. Mutuwar tsaye mutanen gurin su kayi hatta Mufid ɗin duk iskancin shi yana tsoron harbi da mutuwa. "Dan Allah kar ka kashe sa." Cewar Alhaji Kashim cikin rikicewa. "Calm down Sir, kar ka aikata abinda za kayi dana sani." DPO Salisu ya faɗawa Col. Ahmad. Bai kulasu ba ya saita Mufid dashi tare da sakin harsashi, dukkansu suka fasa ihu zatonsu duk ya harbeshi su ka ga ya harbi ginin gefenshi. "Sai haɗuwa ta biyu." Daga haka Col. Ahmad yasa kai ya fita yana mayar da bindigarshi riga ya wuce asibiti. Daga nan Alhaji Kashim ya ɗauki Mufid suka koma gida bayan ya cika Barrister Auwal da kuɗi in da ya mishi alƙawarin case yasha ruwan kanwa tunda dai har Mufid ya fito, zai san yadda za suyi ta kaucewa case ɗin har a hakura dashi. .... Col. Ahmad yana kan hanyar shi ta isa asibiti ya samu ƙiran Umma tana tambayarshi yana ina. 'Ina zuwa.' kawai ya sanar da ita ya kashe wayar. Asibitin ya isa ya sanar da Dr Sadiq cikin kwana biyu ba zai samu zuwa ba, sannan an ɗaga case har sai Nuratu ta samu lafiya, kafin ya bashi card ɗinshi ko wani abu zai taso. Ɗakin da Nuratu take ya shiga ya samu Mami zaune sai su Rahma, Rukayya da Walida a ɗakin tare da Amma Jidda ba'a sanar Muhsin ba dan yana makaranta. Aunti Zarah da Munirat suna gida dan haɗa musu abincin rana. Ɗakin tamkar wanda aka yi mutuwa shuru, har lokacin Rahma ta kasa saida hawayenta, tayi kukan tayi ta kasa daina yi. Rukayya da Walida in ka gansu suma fuskar nan a kumbure alamar sunyi kukan sun gaji, Mami Kam ta zama tamkar mutum mutumi. Hasiya na emergency dan tana samun labarin jini ya ɓalle mata da ya jawo sanadin zubar cikin jikinta na wata uku. Nuratu na kwance tun safe da ta musu haukarta aka ɗirka mata alluran bacci ta koma, Mami ne ta goggoge mata jikinta da ruwan zafi ta gasa mata hannunta, anan ta dubata in da ta ƙara shiga tashin hankali dan har ɗinki aka mata kuma tana buƙatar shiga ruwan zafi. Tana kuka tana yi Rahma da Rukayya suka shigo daga baya Amma Jidda da Walida suka shigo. Anan Mami ta sanar da ita tana buƙatan shiga ruwan zafi suka samu Dr Sadiq yace a yanda take haukan nan in za'a samu masu riƙeta sai a shigarta ciki a riƙeta. A haka suka bari akan in ta farka zasu haɗa karfi da ƙarfi su sakata ko dan samun lafiyarta. Mami da kowa na ɗakin bin Col. Ahmad da kallo su ka yi, ya tsaya kusa da gadon yana gaishe Mami da sauran suka amsa yana tambayar mai jiki suka ce da sauƙi bai iya sanar dasu shi waye ba ya fita. Bayan fitar shi Amma Jidda tace. "Kun san shi?" "A'a ko ɗaya." Kowa yace hakan sai kowa yayi shuru su kaci gaba da zaman su haka kusan mintuna goma Amma Jidda ta miƙe. "Bari in dubo Hasiya, tashi muje Rukayya." Ba musu ta miƙe suka fita tare suka dubo Hasiya ta farka sai kuka take mijinta yana lallashi. Suma lallashinta su ka yi tace sam zata bisu ta duba Nuratu, Dr ya hanata aka mata alluran baccin ita ma. Da ƙarfe taran dare bayan sunci abinci wanda suka iya ci, Mami tace su koma gidajensu in yaso gobe su dawo. Basu so ba suka tafi aka bar Mami da Munirat, Hasiya aka bar mata Walida a wajenta. *** Wanka yayi bayan yaci abincin da Ummu ta girka masa ya shige ɗakinsa ya banka sigari kusan biyar dan ya jima basu haɗu ba. Babu sallah balle azkhar ya mingire da bacci a kan gadonshi da ya jima bai samu ba cikin kwana biyun. Sai biyar ya farka ya fito falon gidan ya samu ƙannen shi sun shigo wajen Rufaida. Da kallo ya bi Rufaida ta watsa mishi harara tana jan tsaki suka bar gurin suka wuce sashin Hajiya Batula. Yana zaune har karfe taran dare kafin Rufaida ta dawo ta ɗauka duk ya fita, tana ganin shi ta nufi hanyar ɗakinta ya tashi ya biyo bayanta da sauri. Tana ganin haka ta saka key a ƙofar ɗakin. "Iskanci ka bai ƙare ba har sai ka dawo kai na? Anya Mufid kana tsoron haɗuwar ka da Allah?" "Ina tsoro mana. Kin san dai duk iskancin na bazan iya haura miki ba tsorata ki nake. So nake mu gaisa kwana biyu kowa yayi kewata banda ke uwar rashin kunya." Tsaki ta buga har yana ji. "Allah dai wadaran naka ya lalace. A rayuwar ka burinka ka cuci yaran mutane, to wallahi ka sani akwai ranar kin dillacin da za kazo ka zubar da hawaye kana neman gafarar su suƙi yafe maka, banda na Ubangijinka da bani da tantama sai ya hukunta ka. Sanadina ka cuci rayuwar Nuratu Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya saka mata tun a duniya na faɗa na sake faɗa, mugu azzalumi." Daga haka Rufaida ta fashe da kuka zuciyarta ya raunana tuna halin da Nuratu take ciki, ta kasa zuwa dubata gani take tamkar da ita aka shafawa rayuwarta baƙin fenti. Mufid da ya gama sauraronta ya wuce ɗakin shi, duk zagin data mishi bai ji komai ba domin shi yaga Nuratu yaji yana sonta tun a wajen dinner abokinsa mijin Rukayya. Ya nuna mata yana sonta taƙi ji tana da wanda zata aura dole yasa ya mata haka. Kuma har yanzu yana sonta in har za'a hukuntashi a kanta zata aure shi ya yarda zai amince a mishi hukunci ya aureta. .... "Ɗan gidan uban waye ya aikata mata haka?" Amma Jidda dake zaune bayan Alhaji Mamman ya sata gaba da tambayar ina taje tun safe da yara ya dawo basa nan ya ƙira bata ɗauka ba ta sanar dashi halin da Nuratu take ciki bai gane wacece ba sai da ta sanar dashi ƴarshi ta wajen Hajiya Sadiya da ya mance da ita a rayuwar shi. Tayi mamakin jin abin da ya faɗa sai kuma ya hau kame kame. "Waye shi? Waye uban shi?" "Ɗan gidan Alhaji Kashim Mufid." "Allah rufa asiri." Kawai yace ya mike ya shige ɗakinsa Amma Jidda ta bishi da kallon mamaki. *** Ƙarfe takwas na safiya kamar kullum Nuratu ta farka cikin ihu da buge buge da take yi, wannan lokacin har ƙiran sunan Mami take ta zo ta taimaketa zasu kasheta. Rukayya da Rahma da su kayi safiyar zuwa tare da taimakon Nurse suka taimakawa Mami da rirriƙe Nuratu suka shiga bathroom. Ruwan zafi da ta haɗa suka sakata ciki ta fasa ihu tana kai musu bugu suka rirrike ta sosai, Mami tana riƙe da kafafunta dan so take ruwan ya shigeta sosai. Kuka take tana zare musu ido babu wanda ya kulata har ruwan ya huce suka fito da ita suka zaunar da ita ta kwasa a guje suka riƙota. Nurse da sauri ta fita ta ƙira Dr Sadiq ya zo ya mata allura kafin ta samu bacci. "Ku same ni anjima za muyi magana." Dr Sadiq yace yana juye ruwan allura a drip ɗin hannunta bayan ya ɗaura mata, ya saka mata robar da ake dura mata kunu ta hanci ya dura mata. Mami ta saba ganin hakan banda Rahma da Rukayya da a take hawaye ya cika idon Rahma dan ita kam ba dai saurin kuka ba. Bayan fitar Dr Sadiq, Munirat da Aunti Zarah suka shigo ɗauke da abincin safe bayan sun gaisa sun tambayi mai jiki, Mami da Rahma da Rukayya suka fita dan amsa ƙiran likita. Sai da suka biya suka duba jikin Hasiya da sauƙi har ta farka tana ƙoƙarin shiga wajen su. Daga nan ofishin likita suka wuce kai tsaye bayan sun shiga da sallama suka zauna. Kanshi a ƙasa ya cire eyeglasses ɗinsa ya ajiye yana haɗa hannayensa waje ɗaya kafin ya fara musu jawabi. "Mama ko ince Mami kamar yadda na ji suna faɗa. Akan maganar patient ɗin nan ne, maganar gaskiya wannan rashin lafiyarta gwara a dangana da psychiatric hospital domin abinda ya faru yana neman taɓa mata ƙwaƙwalwarta. Nan in muka barta anan maganar gaskiya kuɗinku kawai za'a ci, amma batun sauƙi babu shi amma can za su dubata su duba mai ya dace da ita, kuma Insha Allahu muna fatan samun sauƙi daga can duk da Allah ne yake warkarwa. In kun amince sai in muku hanya zuwa gobe sai kuje ku, ko zuwa nan da Maiduguri ne sai mu gwada sa'ar mu." Bayan gama jawabin Dr Sadiq shuru ɗakin ya ɗauka Rahma ta kalli Mami ta kalli Dr. "Za mu yi hakan Dr inshaAllah mun gode da taimako. Maganar tafiya bamu shirya zuwa gobe ba, za mu yi shawara zuwa anjima zamu sanar da kai in ya so jibi sai mu tafi." "Shikenan duk yadda ku kayi." Daga haka suka fita suka koma ɗakin da Nuratu take suka samu Amma Jidda da Ameera da Walida sun zo har da Hasiya da ta saka na cin sai ta zo ganin Nuratu. Kuka kawai take ganin halin da ƙanwarta take ciki. *** Kallonshi take yadda yake cin abincin kamar ya kwana biyu bai ci irin shi ba. To ba dole ba shekaru huɗu ya tafi can garin iyamurai yana cin nasu dubi duk ya zama wani kato. Tas Col. Ahmad ya cinye abincin gargajiya da Umma ta dafa masa ya sha ruwa tare da hamdala. "Yayi daɗi Umma na daɗe ban ci irin shi ba." "Ba dole ba. Ni kam dai wannan aikin sojan ya gama dani ace mutum bashi da zama." Murmushi Col. Ahmad yayi. "To Umma nan Allah ya tsaga abincina yake, sai kuyi ta mana addu'ar samun nasara." "InshaAllah muna yi. Amma mai yake kai ka Damaturu kwana biyu, ina sane fa da shiganka da fitarka. Kar ka saka kan ka abinda ba'a gayyace ka ba ka jawo mana wani fitinar Ahmad." "Babu komai Umma, taimako nake yi kuma Insha Allahu ina fatan samun nasara." "Wani irin taimako." Tace tana haɗa rai. Anan Col. Ahmad ya sanar da mahaifiyar shi komai dangane da abinda ya sani. Ta ji wani iri amma haka kawai taji bata son ɗanta cikin case ɗin. "Ka min alƙawari bayan taimako babu wani abin da zai biyo baya?" Cewar Umma tana kafeshi da idanuwanta. "InshaAllah babu komai Umma daga zaran an yanke hukunci, zan tattara in koma wajen aikina dama hutun ƙarshen shekara na ɗauka." "To Allah yasa, amma in ka zo min da wani maganar zan baka mamaki." Murmushi kawai Ahmad yayi bai kawo komai a ranshi ba yace babu komai, daga nan suka gangara hiran fitar da mahaifin shi zuwa ƙasar Egypt domin duba lafiyar shi. **** A hargitse ya shigo office ɗin tare da banka ƙofar, mutanen da suke ciki suna meeting suka bisa da kallo yana huci kamar zaki yana dubansu ɗaya bayan ɗaya ya kasa banbance waye Alhaji Kashim Mufid. Hakan yasa ya ƙarasa ciki. "Waye ko wanene Kashim Mufid?" "Gani!" Cewar Alhaji Kashim Mufid yana tashi tsaye ya isa wajen shi yana miƙa masa hannu suyi musabaha ya ƙi bashi hannu. Ganin haka ya sallami baƙin shi suka fita sum sum kafin ya juya yana kallon bakonsa. "Bismillahi have a sit." "Ba zama ya kawo ni ba, gargadi na zo maka." "Ina jinka." Faɗin Alhaji Kashim yana juyi saman kujeransa ya haɗa hannayensa yana duban baƙonshi fuskarsa cike da alamar yana sauraron shi. ..... #vote #comments #share MADUBIN GOBE  17. Pharty Bb. Wattpad phartybb. "Idan har kuɗi yana danne gaskiya ya hana a kwatarwa mai haƙƙi gaskiyar shi to kuɗi zai saka a hukunta mai laifi. Dan haka mu zuba ni da kai." Dariya Alhaji Kashim ya kwashe dashi ko a jikin shi yace. "Who are you." Teburin gaban Alhaji Kashim ya dafa yana dubanshi. "I'm Alhaji Mamman Bashir father of Nuratu Mamman Bashir. Wanda ɗanka ya ɓatawa rayuwa. Dan haka ka shirya shari'a." "Oh shikenan ina jiran ka." Alhaji Kashim yace ko a jikinshi. Daga haka Alhaji Mamman ya fita a fusace. Tun da Amma Jidda ta sanar dashi maganar kasa zaune yayi, tun yana son kawar da maganar ya ji ya kasa hakan. Duk da haushin Nuratu da na Hajiya Sadiya da yake ji amma abin da ya faru da ita yaji ya kasa hakura ko ba komai kwansa ce itama kamar sauran, rayuwa ne da ita har lokacin yake jin ba zai iya gida ɗaya ƙarƙashin inuwa ɗaya da ita ba, baya son duniya ta zageshi ya sashi saka kanshi cikin shari'ar. Dole ya bincika wajen aikin Alhaji Kashim dan shaida mishi shirye yake ya kwatarwa ƴarshi haƙƙinta. *** Asibiti. Da azahar Mami da Rahma suka hau shirin tafiya Maiduguri bayan sun sanar da Dr Sadiq ya basu copy na komai dangane da rashin lafiyar Nuratu da abin da ya jawo hakan har zuwa yanzu da babu wani canji. Rahma ce kawai za ta raka Mami, ta sanar da mijinta ya amince ta shirya ita da Babynta. Sauran duk sai sun isa za su bi bayansu daga baya. Hasiya taso zuwa mijinta ya hanata cewa sai ta warke zuwa nan da kwana biyu. Ƙarfe uku su ka ɗauki hanya cikin motar asibiti da Dr Sadiq ya basu. Nuratu alluran bacci aka mata dan karta farka musu a hanya. Isan su kai tsaya asibitin Asylums suka isa kasancewar an san da zuwansu aka tare su, Dr Awwab da aka sanar da zuwansu ya dubata aka bata ɗaki. Bincike sosai yayi a foldern ta da ita kanta kafin ya samu zama da su Mami. "InshaAllah zata samu sauƙi, firgicin da ta shiga ya haifar mata da haka. Amma sannu a hankali komai zai wuce. Daga gobe zamu fara ɗaurata saman magani in ta farka, babu batun alluran bacci sai dai zuwa dare dan ta samu bacci. Muna so mu ga yanayin yadda sauƙin zai samu." "Nagode Dr. Allah biya ka." Mami tace tana sharan hawaye. Murmushin sa mai kyau yayi duk da abinda ya samu Nuratu yana jin shi a zuciyar shi dan ya taɓa masa zuciya ba kaɗan ba, tausayinta ya cika masa zuciya. "Babu komai. Mu ci-gaba da addu'a." Daga haka suka koma ɗakin da Nuratu take babu kowa, tsakanin su da ita akwai gilashi suna ganin komai na ciki. Tana kwance kamar kullum cikin bacci ba ta motsi sai in har alluran ya saketa. Kuɗaɗen Mami na hannunta duk ya ƙare dan kafin ta zo ma sai da ta saida ɗan kunnenta mai tsada ta samu suka taho. Burinta kawai Allah tashi kafaɗar Nuratu ta samu lafiya, maganar hukunci da shari'a duk bai dameta ba, burinta lafiyar ƴarta. Ta manta rabonta da taci abinci kwakkwara sai kunu shima sai an matsa mata. Hira sama sama Rahma take mata tana sanar da ita kyan asibitin da kuma halin Dr Awwab da ta kula ya san kan aikin shi, hiran ne ya ja lokacin har aka ƙira magriba suka gabatar da sallah. Sai da Mami tayi kafin ta riƙewa Rahma ƴarta mai shegen ƙiwa kafin itama tayi. Cikin daren ƙarfe goma Nuratu ta farka, Mami da Rahma suka rirriƙeta suka kai ta bathroom, Mami ta sakata cikin ruwan zafi sai bugesu take tana ture su. Haka suka fito da ita suka canza mata kaya kafin Nurse ta mata allura wani bacci ya ɗauketa suka samu suma suka kwanta. Washegarin har karfe sha ɗaya kafin ta farka lokacin Dr ya iso, hana kowa zuwa kusa da ita ya yi suna kallonta ta cikin gilashin ta farka tana zare idanuwa kafin ta miƙe ta isa ƙofa tana bugawa a buɗe mata sai ƙiran Mami take, da ta gaji ta koma ta samu lungu ta shige tare da fashewa da kuka ta kama jikinta, sai kuma ta saka hannu tana rufe bakinta alamar kar kukan ya fito. Ji take kamar tana tare da su, gani take za su zo mata, mafaka ta samu ta ɓoye kanta daga gare su da har bata son su juyo sautin kukanta. "Tana cikin damuwar abin da ya faru da ita ne, tsoro ne a tare da ita. Gani take za su zo mata" Faɗin Dr Awwab yana kallonta yana karantar yanayinta. Kallonsu gaba ɗaya suke idanuwan Rahma cike da kwalla, Mami kam ta fara sabawa domin ta ɗauki dangana ta sakawa zuciyarta. Buɗe ƙofar gilashin Dr Awwab yayi ya shiga, Nuratu tana kallon shi ta fara jan baya tana roƙarshi ya rabu da ita kar ya ƙaraso. Ganinshi take tamkar Mufid da kamannin shi ya juye mata zuwa fuskar shi. A bakin kofar ya tsaya yana dubanta can kuma ya miƙa mata hannu. "Shit babu mai zuwa." Dube dube ta fara ta zaro ido tana kallon shi ya ɗaga mata kai yana nufanta, tana ganin haka ta fasa ihu ta fara ƙoƙarin gudu ya riƙota, ta sake fasa wani ihun tana son kwace jikinta. Kokuwa su kayi sosai da ita duk yana son ta nutsu ta ƙi, dole a ƙarshe ya mata alluran da ya kashe mata jiki ta kasa motsi amma ba bacci take ba ya kwantar ta ya fita. Ita ɗaya cikin ɗakin tana binshi da kallo ta kasa magana balle ɗaga yatsun hannunta, jikinta yayi nauyi. Mami da Rahma suna kallon komai har ya fito ya tsaya kusa da su. "Tsoro ne ya shigeta sosai, gani take har yanzu za su iya zuwa mata, wani lokacin kuma gani take duk mutanen da take tare dasu cutarta za suyi, wani lokacin kuma yanayin da ta kasance shi yake dawo mata ta dinga kallon mutane a matsayin su. Mu fara barinta tana samun zama ita ɗaya na wasu mintuna." "InshaAllah Dr za muyi hakan." Cewar Mami cikin gamsuwa da bayanin shi. "Dr. Ba ta cin abinci fa kwata kwata." Rahma ta ce cike da damuwar hakan. "Kar ki damu za ta fara, ba tana shan kunu ba. Abincin ma zamu fara gwada mata ko zuwa gobe." Shikenan suka amsa dashi kafin ya fita, sun gamsu da bayaninsa ko ba komai sun samu wani kwanciyar hankali jin sauƙi ya zai fara samuwa. Bayan fitarshi suka saka idanuwa suna kallonta sai juya idanunta take tana lumshe su har bacci ya ɗauketa da yau cikin hankalinta tayi shi. *** Abincin dare da ta haɗa masa take zuba mishi har ta gama ta ajiye masa kafin ya wanke hannunshi ya fara ci yana kallon labarai. "Wani asibiti su ke ne?" cikin mamaki furucin shi Amma Jidda tace. "Su waye?" Sai kuma da sauri tace. "Nuratu?" Shi sau yau ma ya san sunanta dan haka ya ɗaga kanshi. Murmushinta ta faɗaɗa ganin tsawon shekaru ashirin ya waiwayi baya. "Suna General hospital amma an tura su psychiatric hospital dake Maiduguri yau." Kwarewa yayi jin abinda ta faɗa da sauri Amma Jidda ta miƙa masa ruwan cikin kofin ya karɓa ya shanye kafin ya dai-daita kanshi. "Jikintan yayi tsanani ne?" Ya tambaya. "Eh har yanzu bata san inda kanta yake ba." Anan ta sanar dashi iya abubuwan da ta sani har tana neman izinin tafiya gobe zuwa dubata. Bai ce komai ba harta ya gama ta miƙe ta fara tattare gurin. "Ku shirya gobe mu je dukkan mu." Dakatawa Amma Jidda tayi da ɗaukar babban tray da yake ɗauke da komai tana juya furucin shi. Ganin za ta fassara maganganun shi ya miƙe ya wuce ɗakin shi. Sai da ta gama ta bi bayanshi. *** Nuratu ba ita ta farka ba sai ƙarfe bakwai na safe, ba wanda yayi gigin shiga gurinta, suna kallonta sai dube dube take ta duƙunƙune cikin blanket din saman gadon tana bin ɗakin da kallo. Yau babu wani buge buge da kuka, hakan ya musu daɗi sosai. Ƙarfe tara Dr Awwab ya shigo dubata suka gaisa da su Mami. "Bari mu gwada bata abinci sai a mata wanka." To suka amsa dashi abincin da ya shigo dashi ya ajiye musu manya manyan Warmers biyu ya ɗauki plate ya zuba dankali ya buɗe gilashin ya shiga gurin Nuratu. Tana ganinshi ta miƙe ta fara ƙoƙarin gudu ya ajiye mata abincin ya fita. Ganin haka Nuratu ta dakata ta koma baya, sai kuma da sauri ta miƙe tana leƙa abin cikin plate din, har juyar da kanta take yi dan son tuna menene. Hannu ta saka ta taɓa ta ɗauki kwaya daya ta kai bakinta ta tauna. Cikin sauri ta fara kwasa tana turawa bakinta har da kwaruwan ta. Duk ta hargitsa wajen kafin ta bari ta koma gefe. "A wanke mata jiki za mu shigo in bata magani. Ga breakfast ba sai kun saya ba." Dr Awwab yace yana shirin fita bayan ganin yanayi na Nuratu da yayi. "Harda wahala Dr." Cewar Rahma, Mami na mamakin kirkinshi da sanyin halinshi. Ban da wasu likitoci da suke ji da kansu. "Babu komai." Yace ya fita kafin Rahma ta buɗe ta zuba musu, dankali da fefesun kayan ciki da ya sanar daga can gida aka girka ya biya ya ɗauka da zai taho asibitin. Bayan sunyi breakfast su ka shiga ɗakin Nuratu ta kallesu tana miƙewa, zuwansu su biyun ya tsorata ta, ta fara jan baya ganin sun nufota. "Nuratu!" Mami ta ƙirata tana matsawa kusa da ita, Nuratu ta fasa ihu tana ja baya ta runtse idanunta. "Kar ki taɓa ni!" Dakatawa Mami tayi ta hana Rahma isa wajenta. "Je ki waje Rahma." Ba musu Rahma ta koma waje tana kallonsu. Mami ta ƙara matsawa kaɗan gurinta. "Nuratu! Mami fa, Mamin ki. Buɗe ido ki gan ni gani kusa dake na zo taimaka miki, babu wanda ya isa ya cutar dake." Idanuwanta kaɗan Nuratu ta buɗe tana duban Mami. "Mamin ki. Babu wanda zai cutar ki gani kusa dake." Mami tace tana matsawa kusa da Nuratu sosai. "Mami!" Nuratu ta furta tana zarewa Mami ido. Ta ɗaga mata kai. "Nuratu na." Shuru Nuratu tayi ta zubawa Mami ido tana kallonta ta komo hannayenta. "In miki wanka kin ga kin ɓata jikin ki." "Wanka." Tace cikin ƙarin bayani kamar mai koyan magana. Mami ta ɗaga kai tana ɗagata suka miƙe suka nufi bathroom. Mami hawayenta take dannewa duk lokacin da za ta saka Nuratu ruwan zafi. Tana lallashinta kamar tana ji ta samu ta gasata ta ɗauraye mata jikinta ta fito da ita ta samu Rahma ta gyara ɗakin ta fita. Kayan asibiti ta maida mata sabo ta zaunarta tana shirin fita Nuratu ta riƙota alamar kar ta fita ko ina. Hakan ya sa Mami zama kusa da ita, Nuratu ta kwantar kanta da yake ciwo saman cinyar Mami. Abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata ta hau juyi domin kanta da ta ji yana neman tsagewa. Rahma dake waje tana shayar da Ikhram da sauri ta fita ta ƙira Dr Awwab suka shigo tare da magunguna a hannun shi. A waje Rahma ta tsaya ya shiga. Nuratu tana ganinshi ta riƙe Mami. "Mami. Mufid ne ya fita." Tace da ƙarfi tana riƙe Mami. Mami na riƙe da ita tace. "Bashi bane, Dr ne zai baki magani. Ciwon kan ki zai daina" Gurinta Dr Awwab ya ƙarasa ta riƙo Mami tana kallon shi. Maganin ya ɓalla ya bawa Mami ta bata yana duban Nuratu. "Babu abinda zan miki, magani zan baki ki sha sai ciwon kai ya tafi. Babu kowa anan da zai cutar dake." Jin maganganun shi Nuratu ta kalli Mami, Mami ta ɗaga kai alamar eh, hakan yasa ta buɗe bakinta Mami ta bata magani da ruwa ta sha har lokacin tana riƙe da ita dan ta kasa yarda da Dr Awwab. Ganin tasha ya saka Dr Awwab fita. Sai da tayi bacci kafin Mami ta samu ta fita wajen Rahma. "Allahamdulillahi sauƙi ya fara samuwa." Cewar Mami cikin farin ciki. "Sosai Mami tun da ta fara yarda da mutane. InshaAllah gaba kaɗan za ta dawo normal." "InshaAllah, nagode Allah na godewa Dr Awwab." Sallamar Amma Jidda da Walida, Ameera da Hasiya ya katse musu hiransu su ka shigo. Bayan an gaggaisa suka tambayi mai jiki ta sanar dasu da sauƙi har ta fara gane mutane. "Akwai baƙo a waje Mamin yara." Cewar Amma Jidda. Da mamaki Mami tace. "Baƙo kuma?" "Eh muje ku gaisa." Ba musu Mami bata kawo komai ba ta fita bayan ta gyara zaman mayafinta. Alhaji Mamman ta tarar yana jiranta, ganin fitowar ta ya sashi tashi tsaye. Shekaru ashirin bai sata a ido ba, ta zama babbar mace. Duk ita ta jawo musu da ta bi shawaran shi da yanzu babu abinda zai dame su. Albarkacin ƴaƴa Mami ta gaishesa ya amsa yana tambayar mai jiki. Maimakon ta amsa tace. "Sai yau ka san da zamanta?" Tsayuwar shi ya gyara. "Sadiya kenan, yanzu ma na zo ne ko in ce na shiga cikin lamarin ne dan kar duniya ta zageni domin ko ba komai ita ma ni na haifeta." "Oho kar duniya ta zage ka, ba dan Allah ka zo ba. To bama buƙatar ka cikin rayuwar mu, tun ranar da ka ciremu cikin rayuwarka muka cire naka babin a rayuwar mu." Daga haka Mami ta juya ta koma cikin jin haushinsa da har yanzu yana nan da wannan banzan ƙudirunsa. .... #vote #share #comments MADUBIN GOBE (Haske) 18. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Alhaji Mamman yaji zafin maganganun Mami amma burin shi dama kar azo shari'a a nemi uban yarinya a rasa a tuhume shi da rashin kula da ita, da yana jin ko duniya zata taru a kanshi ba zai rayu da Nuratu gida ɗaya ba. Yarinyar da dalilin ta duk wata arzikin shi ya nemi karaya. Fita yayi cikin asibitin ya nufi cikin gari bayan ya sanar da Amma Jidda ta ƙirashi bayan sun gama. Mami fushi tayi sosai har ya shafi Amma Jidda sai taji abin ba daɗi amma ita burinta ta haɗa kan tsofin mata da mijin in da rabon aure su sake zama. Sai bakin magriba Nuratu ta farka tana neman Mami da sauri Mami ta shiga gurinta ta sanar da ita fitsari take ji, Mami ne ta kai ta bathroom tayi ta sata tsarki da ruwan zafi kafin ta sata alwala, da kyar ta iya tunawa tayi suka fito ta nuna mata gabar ta bata hijab tace tayi sallar magriba. "Sallah? Raka'a nawa?" Ta tambaya. "Uku." Mami tace cikin tausayin ƴarta. Sai lokacin ta tuna ta hau yi, sama sama tayi tai sallama Mami na zaune kusa da ita, taji daɗin ganin ƴarta ta fara samun sauƙi da har tana iya fara wasu abubuwa. Bayan Nuratu ta idar Mami ta dubeta. "Za kici abinci?" Kai Nuratu ta ɗaga Mami ta miƙe zata fita da sauri Nuratu ta riƙota tana girgiza mata kai alamar kar ta fita. "Abinci zan ɗauko miki kici da magani." "Za ki dawo?" Kai Mami ta ɗaga kafin Nuratu ta saketa ta fita da sauri ta zuba mata abincin da su Amma Jidda suka kawo ta tura Rahma gurin Dr Awwab ya bata magunguna kafin ta koma. Duk abubuwan da suke suna kallonsu kowa yaji farin cikin ganin ta dawo cikin hankalinta sai tsoro da har yanzu yake damunta. A baki Mami tayi ta bata abincin tana ci. "Mami zan kashe su." Faɗin Nuratu da ya saka Mami kallonta da sauri itama kallonta take. Kasa cewa komai Mami tayi dan ta san ko ta mata magana ba ganewa za tayi ba ko ta hakura. Shigar Dr Awwab yasa su kai dubansu gurin da sauri Nuratu ta matsa gurin Mami ta ɓuya. Gurinsu ya ƙarasa yana duban Nuratu da itama shi take kallo, ya ɗauke idonshi cikin nata. Duk namiji tsoro da tsanarshi take ji. "My patient." Kallonshi kawai take ta kasa amsa mishi. Dr Awwab ya juya ya kalli Mami. "Ga magungunan ta, za taci gaba da sha har zuwa nan da wani lokaci, in ta gama shan wannan zamu ɗaurata kan wani da za ta jima tana amfani dashi zuwa nan da shekaru huɗu zuwa biyar, har sai ta daina shiga damuwa ko in ta fara tunani kanta ya hau ciwo. InshaAllah komai zai dai-daita, taci gaba da shan magani tana samun kulawa zuwa nan da wata ɗaya za ta dawo normal mu sallameta." "Mun gode Dr." Faɗin Mami cikin murna da jin daɗin bayanin Dr Awwab. Ya kalli Nuratu da take kallonshi har lokacin, ƙwayar idanuwanta suka sarƙe nashi yayi saurin ɗauke idonshi. "Allah ƙara sauki." Ameen! Mami ta amsa da shi yasa kai ya fita Nuratu ta bishi da kallo. "Mami waye?" "Dr Awwab ne, shi ya ci gaba da kula dake bayan Dr Sadiq." Kai kawai ta girgiza tana son sanin mai ya faru da ita dan iya saninta tun lokacin da Mufid ya sata jin azaba ta suma bata ƙara sanin komai ba sai jiya zuwa yau da ta fara tuna abubuwan da ya faru da ita. Hawaye ta fara mai cin rai tunawa da shikenan Mufid da abokan shi sun cuceta sun cutar da rayuwarta. Ba ta da wani ƙima ko daraja a tattare da ita a matsayin ta na ƴa mace. 'Fyaɗe aka mata! Ita ce wacce aka ma fyaɗe!' Shikenan abinda za ana ƙiranta da shi har ƙarshen rayuwarta. Ji tayi ta tsani ko wani namiji a duniya. "Ki daina kuka kin ji Nuratu, Allah ya riga ya rubuta ya ƙaddara hakan sai ya faru babu yanda muka iya, Allah zai saka miki. InshaAllah haƙƙin ki ba zai taɓa barinshi ya runtsa ba da yardar Allah." Kuka kawai Nuratu take yi wanda sauran ƴan uwanta dake waje duk ya saka su zubar da hawaye. Sun san dole tayi kuka na wannan rashin imani da aka nuna mata. Ciwon kai ya zuba mata bayan kukan da take da kyar Mami ta lallasheta ta yi shuru ta bata magani kafin ta kwanta bata jima ba bacci ya ɗauketa. **** Ƙarfe goma ya dawo daga airport bayan tashin jirgin mahaifinsu zuwa ƙasar Egypt tare da ƙanin babansu da zai kula dashi, ya dawo gidan bayan ya sauƙe Umma bai shiga ba ta dakata. "Fita za kayi?" "Eh Umma ina son zuwa Damaturu in duba jikin yarinyar." Kallon shi tayi ita dai wannan sa kai da yake cikin rayuwar mutanen da bai san su ba bata so. "Kar ka dai dare." Kai kawai ya ɗaga ya ja motar ta wuce cikin gida. Karfe sha biyu saura ya isa cikin Damaturu kai tsaye asibitin General ya nufa. Dr Sadiq yana duba marasa lafiya, bayan ya sallami marasa lafiya ya shiga suka gaisa. "Ina patients ɗi ta." Faɗin Col. Ahmad yana zama saman kujeran cikin ofishin. "Lafiyarta lau, baka da labarin na turasu Maiduguri psychiatric hospital." "Yaushe?" "Kwana biyu yau. Jikin yaƙi sauƙi anan, but Allahamdulillahi munyi waya da Dr Awwab yace sauƙi ya fara samuwa dan har ta fara gane mutane da yarda dasu." Col. Ahmad kai ya girgiza yana dafewa. "Allah ƙara mata lafiya. Zanje dubata ka bani address ɗin." Anan Dr Sadiq ya bawa Col. Ahmad address din asibitin da take. Col. Ahmad yace. "Na sani nima ɗan can ne aiki ne ya kai ni Ibadan." Sunyi sallama cikin aminci Dr Sadiq yaci gaba da aikin shi *** Kwana biyun duk a ƙofar gidan su yake wuni ko zai ga shigarta da fitarta amma baya ganin hakan domin gidan tamkar babu mutane. So yake ya ganta suyi maganan yarjejeniya idan har ta amince zata aure shi, shi kuma ya yarda a hukunta shi kamar yadda ubanshi ya so rufe shari'ar. Sonta yake so irin wanda bai taɓa ma wasu matan ba, ba wai dan ya aikata mata wani laifin ba. Asali ma tun farkon ganinta yake sonta, son da yake mata ne ya jawo ya aikata mata haka. Da ya gaji da zaman jiran har yamma lis ya bar unguwar, sai da ya biya gurin shaiɗancin su ya sha wine ya zuƙi sigari kafin ya nufi gida. A falon gidan ya samu Ummu da Rufaida, tana cin abinci dawowarta daga makaranta kenan. Saman kujera ya zauna kusa da ita ta miƙe tana toshe hanci dan warin sigari da ya bugeta. Harara ya watsa mata da idanuwanshi da suka fara canza launi. "Uban wa ki ke toshewa hanci?" "Sai in zauna wari ya halakar ni ko zunubi ya shafe ni." Kanta yayi zai kai mata mari Ummu ta tare shi da sauri dan tasan yanzu zai iya marinta dan ya saba. "Kar ka yarda ka daka min yarinya. Ƙarya tayi ne ba warin sigarin ka ke ba. Na ga dai ranar shiryuwar ka Mufid." Tsaki ya buga ya miƙe ya wuce ɗakin shi. Ganin haka Rufaida ta koma ta zauna. "Ki dai bishi a hankali kin san yanzu sai ya bubbbugeki babu ruwana." Faɗin Ummu. Rufaida ba tayi magana ba taci gaba da cin abincin ta, ita yanzu da za'a tambayeta wata tsana a duniya zata ce shine, ta tsane shi a rayuwarta, tana jin kunya da haushi a ƙirata da ƙanwar shi. *** Col. Ahmad ƙarfe uku ya isa garin Maiduguri, gida ya koma yayi sallah yaci abinci kafin ya nufi asibitin dasu Nuratu suke. Kai tsaye Asylums center ya nufa, bayan ya nemi ganin Dr Awwab ya sanar dashi shine wanda Dr Sadiq ya sanar dashi zai zo kasancewar bayan tafiyar Col. Ahmad, Dr Sadiq ya sanar da Dr Awwab ko shi wanene. Bayan sun gaisa Dr Awwab ya masa iso zuwa wajensu Mami. Mami dai ta ganeshi dan yazo sau ɗaya haka Munirat ma da yau tazo dan taya Mami, Rahma dasu Amma Jidda sun koma. Kallon Nuratu yake ta cikin gilashin tana zaune shuru tunani take ta zubawa waje ɗaya ido, babu wanda ya ankara da hawayen da take zubarwa sai Dr Awwab. "Bari in shiga in sanar da ita in ta yarda sai ka shigo." Cewar Dr Awwab ya nufi wajen shigan duk suka bisa da ido. *"Noor!"* Ya ƙirata bayan ya shiga da sauri ta goge hawayenta tana kallon shi. Cikin kwana biyun ta kula shine Dr da yake zuwa dubata, in bashi ba babu kowa da yake shigowa sai ƴan gidansu da duk sun shigo kafin su tafi kuma allahamdulillahi ta ganesu, da suka fara damunta da hayaniya za su tada abinda ya wuce aka fitarsu. Bata amsa ba sai idanu da ta zuba mishi dan ta fara yarda da shi. "Kina da baƙo. Ya shigo?" "Waye?" Ta tambaye shi tana ɗauke idonta cikin nashi. "Bari ya shigo ki ganshi." Yace ya fita ya ƙira Col. Ahmad ya shiga da sallama. Idanu ta zuba mishi shima ita yake kallo har ya samu guri ya zauna. "Sannu ya jikin?" Kamar ba zata amsa ba tana kallonshi. Ta gane shi, shine wanda ya bugeta lokacin da take gudun ceton ranta, ta nemi ya taimaka mata yana gani Mufid da abokansa suka sakata a motarsu. Kallon Dr Awwab tayi da shima ita yake kallo. "Ka ce ya fita." "Why Noor?" Dr Awwab yace yana matsawa kusa da ita, ta ja baya da sauri tana mishi wani kallo tare da watsa masa harara. "Ka ce ya fita." Nuratu tace tana haɗa rai, dole yasa Dr Awwab kallon Col. Ahmad da ya zubawa Nuratu ido yana kallo, sai yaji ransa bai so kallon ba. "Mu je waje, may be bata gane ka ba." Babu musu Col. Ahmad ya miƙe suka fita da Dr Awwab yayi wa su Mami sallama. "Bata gane ni ba, ko ni ne bata son gani?" Col. Ahmad yake tambayar Dr Awwab bayan fitarsu. "Tana ganewa tunda har ta gane ƴan gidansu. Yarda da mutane ne zai yi wuya tayi cikin sauri." "Hakane kuma? Zuwa yaushe za'a sallameta." "Za ta kai one month? Wani abun ne?" Dr Awwab ya faɗa dan son ƙarin bayani. "Yeah akan case ɗin tane ina son a shigar da ƙara kafin in koma wajen aiki." "InshaAllah kar ka damu zamu sallameta da zaran lokaci yayi, ko bata gama shan maganininta ba na wata ɗaya da zaran ya kusa ƙarewa zamu sallameta." "To shikenan Allah ƙara mata lafiya. Zan koma gida gobe zan shigo." Faɗin Col. Ahmad yana wuce. Dr Awwab ya amsa da ameen ya koma office ɗinsa ya samu an kawo ƴarshi Hanan daga gida da ta matsa sai tazo wajenshi. *** Shigar dare su kayi ana ƙiran sallar magriba, bayan an sauƙe Rahma da Hasiya da Rukayya a gidansu suka isa gida. Wangale get ɗin a kayi Alhaji Mamman ya shiga da motar yana bin motar da ke fake da kallo kamar ya gane mai motar. Amma Jidda da ta riga ta gane tayi mamakin yaushe ya shigo bai nemeta ba. Ciki suka ƙarasa kowa ya wuce ɗakin shi yayi sallah kafin su fito. Ana idar da sallar magriba ya dawo ya samu sun dawo. Cikin falon ya shiga da sallama, Ameera dake kusa ta amsa tana tashi ta tare shi. "Sannun ku da dawowa ya hanya?" Yaya Al-ameen yace yana zama kusa da Amma Jidda. "Lafiya ƙalau yaushe a gari?" "Ban jima da shigowa ba. Na ƙira ku duk babu wanda ya ɗauka. Ina ku ka je ne? Naje gidan Mami a kulle, ƙanwata ma numbern ta a rufe." "Maiduguri mu ka je." Sai kuma Amma Jidda tayi shuru tuna bashi da labarin mai ya faru da Nuratu. Tambayar da ya watsa mata ya sata miƙewa tace. "Mu je ciki." Ba musu ya miƙe ya bita cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da ya kasa fassara abinda yake ji. Stool ya samu ya zauna ta zauna bakin gado tana dubanshi. "Al'ameen!" "Na'am!" Ya amsa ƙasa ƙasa yana sauraron mai zata furta. "Ka san ƙaddara?" "Na sani Amma." Yace zuciyar shi yana bada wani sauti. "Ka san rubuce yake baya wuce lokacin shi, kuma ana so bawa ya karɓa." "Hakane Amma." Yace har lokacin zuciyarshi yana bugawa. Tsoronsa ɗaya kar Amma tace Nuratu ta daina son shi ko Abba ya hanashi aurenta. ..... #vote #comments #share MADUBIN GOBE 19 Pharty Bb. Wattpad phartybb. A hankali cikin nutsuwa da yadda zai fahimci zancen ta sanar dashi halin da Nuratu take ciki har zuwa yau da suka je dubata. Kallonta kawai yake yana sauraron ta idanuwanshi sun kaɗa sunyi jajir, ɓacin rai da baƙin ciki ne cike, ya shiga tashin hankali jin abinda ya samu Nuratu da bashi da labari. "Ko gobe sai ka je dubata duk da jikin da sauƙi." Kai kawai ya girgiza ya fice a ɗakin ta bishi da kallo. Ta san duk wanda yaji abin da ya samu Nuratu dole hankalinshi ya tashi. Ta hango tsantsan tashin hankali cikin idanuwanshi. Yaya Al-ameen kasa bacci daren ranar yayi, hawaye ya zubar sosai daren ranar na tausayin Nuratu. A ranshi ya kudurta ko mai zai faru ba zai taɓa fasa niyar abinda yayi niya ba, dole ya nuna mata itama abin so ne ya share mata hawaye. Washegari weekend da kyar Amma Jidda ta saka shi yayi breakfast kafin ya ɗauki hanyar Maiduguri, tafiya kawai yake shima baya jin daɗin jikinshi dan rashin baccin da bai samu ba. Karfe sha ɗaya ya shiga cikin asibitin da Amma Jidda ta bashi address ɗin. Garin anyi ruwa, ɗauke da iska mai sanyi yake kaɗawa ga garin ba rana a lumshe. Allahamdulillahi sauƙi sai samuwa yake, jiki ya fara warwarewa sai dai har yanzu bata son cikin hayaniya, sai kuma in ta zauna ita ɗaya sai tunani da yake haddasa mata damuwa daga nan kuma sai kuka da ciwon kai. Dr Awwab duk safiya da rana da yamma yana zuwa dubata kamar kullum. Sun saba tana sakar mishi fuska, shine namiji na farko ta ji ya burgeta bayan abubuwan da suka faru, tana ganin mutuncinshi dan taimakon da ya mata ta dawo hankalin kanta. Yau weekend da safe bayan ta yi wanka dan tana iya yin wanka da kanta yanzu, kullum sai tayi kuka in ta zo gasa kanta dan baƙin ciki da yake ziyartan zuciyarta in ta tuna shikenan Mufid da abokansa sun ɓata mata rayuwa. Ji take zata kashe Mufid da za ta ganshi, ta tsane shi ta tsani komai nashi. Wanka ta yi ta fito ta saka kayan asibitin riga da wando, Mami tana zaune tana jiranta har ta gama tana shirin kwanciya, Dr Awwab ya shigo yau tun safe bai shigo ba har take tambayar Mami yau bai zo ba. Harara ta watsa mishi lokacin da ya iso wajenta ta kawar kanta tana ɓata rai. Duk ya lura da hakan ya tsugunna ya gaishe da Mami ta amsa kafin ya ƙarasa kusa da ita sosai yadda za taji shi. "Sorry Noor amin afuwa." Kafaɗa ta maƙe alamar a'a, murmushi yayi da yake karɓar kyakkyawar fuskarshi. "I said I'm sorry. Hanan ce ta samun rigima sai ta biyo ni." Sai lokacin ta juya ta kalleshi taƙi magana ya ɗaga mata gira ɗaya, ta ɗauke idanuwanta cikin nashi. "Muje ki ganta." Yace da dan yana son ta fara fita kuma tana yin doguwar tafiya ya faɗa haka. Ƙi tayi hakan yasa ya kalli Mami. "Mami ki mata magana ko za taji." Murmushi tayi tana mamakin diramarsu. "Tashi Nuratu ku je kin ji. Yanzu fa ki ke tambayana bai zo ba, kuma yazo ki ƙi kulashi." "Ni dai Mami." Nuratu tace haka kawai ta je matarshi ta gansu ta zata wani abu ne tsakanin su da har ta saka rigimar biyo shi. "Please Noor." Dr Awwab yace dole ta miƙe ta ɗauki Baby hijab ta saka suka fita tare. A hankali take tafiya suna wuce ɗakuna ɗakuna duk tsoro ya kamata dan rabon da ta ganta a waje har ta manta, da za'a tambayeta ina take ma za tace bata sani ba. Waje taga sun nufa ta kalle shi hankalinshi yana kan hanya. "Ina za muje?" "Office ɗina, ai tana can." "Ba zan iya ba." Tace tana tsayawa ya kalleta. "Please ki daure mu ƙarasa." Ganin zata koma ya sashi shan gabanta yana saka idanuwansa cikin nata data marairaice su. "Please Noor nan kusa ne fa, kuma ba jimawa za muyi ba." Ji tayi ta kasa masa mutsu ta juya suka ci-gaba da tafiya. Har suka fita tana bin filin asibitin da kallo mai kyau cike da shuke shuke anyi ruwa garin yayi kyau yayi luf dashi. Ɓangaren ofishin likitoci suka nufa. Shigowar shi kenan da motar shi ya hango wata kamar Nuratu da Dr suna shiga floor da yake ɗauke da ɗakunan likitoci. Da sauri yayi parking ɗin motarshi ya bi bayansu. Abin mamaki da Nuratu ta tarar cikin ofishin yarinya ƙarama ƴar shekaru biyu, kyakkyawa mai hasken fatar mahaifinta, kama suke sosai da Dr Awwab, sanye take da gown ja kanta da ribbon kala kala an mata kitson kalaba. Kallon yarinyar Nuratu tayi ta kalli Dr Awwab ta sake kallonta yarinyar da take hannun Nurse da Dr Awwab ya bata ta kula da ita kafin ya wuce wajen Nuratu. "She's My Baby. Hanan." Sai Nuratu ta ji wani iri ta miƙa hannu ta karɓi yarinyar. "Za ki iya?" Faɗin Nurse ganin Nuratu itama kamar bata da lafiya, Nuratu ta ɗaga kanta ta karɓi Hanan tana zama. Shima Dr Awwab zama yayi saman kujera yana sallamar Nurse ta fita. "Ina mamanta ta yarda ta biyo ka?" Faɗin Nuratu tana ma Hanan wasa yarinyar ta shiga ranta. Kafin Dr Awwab ya bata amsa su ka ji knocking ya kai dubanshi kofa ya ba da izinin shiga, da kallo ya bi wanda ya shigon. "Ƙanwata!" Faɗin Al-ameen da yayi ƙoƙarin ƙarasawa wajen Nuratu. "Yaya Al-ameen." Tace cike da mamakin ganinshi a wannan lokacin, kwata kwata ta mance dashi da wani abu da ya shafesa. Dr Awwab ido kawai ya zuba musu wani abu yana taso masa ganin kallon da Al'ameen yake bin Nuratu da shi, ganin ba zai jura ba ya sashi miƙewa yana shirin fita Al-ameen ya miƙa masa hannu su kayi musabaha, da kyar ya iya sakin fuska suka gaisa. "Mu je ko?" Dr Awwab yace yana karɓar Hanan, haka yasa Nuratu miƙewa ta dubi Yaya Al-ameen da ya kasa faɗin komai. "Yaya Al-ameen mu je wajen Mami." A kofar ɗakin da Nuratu take suka rabu da Dr Awwab ya wuce ɗauke da ƴarshi data saka kuka sai ta bi Nuratu. Bayan sun shiga ɗakin Nuratu ta ƙarasa wajen Mami, Al'ameen ya shigo. Mami tayi murnan ganin shi suka gaisa yace ya mai jiki tace da sauƙi. Har yamma yana nan duk yadda ya so ya samu guri shi da Nuratu su gaisa abin ya gagara, har biyar kafin yace zai koma. *** Dr Awwab bai wuce gidanshi ba ya wuce family house nasu, da ƙannen shi ƴan biyu mata ya fara cin karo suka karɓi Hanan da ta hakura ta yi shuru. Babban falon mahaifiyarshi ya isa ya samu tana gishinkiɗe ya rissuna yana gaidata. Cikin sakin fuska da walwala ta amsa. Mace ce da kallo ɗaya zaka mata ta kalli dattako da kamala a tattare da ita. Yanayin damuwa ta gani kwance saman fuskar ɗan nata da kwata kwata bata son haka. Shekaru biyu kenan suna ƙoƙarin bashi dukkan farin ciki da mance damuwar da ya shiga ta dalilin rashin matar shi abin son shi da yayi a haihuwar Hanan. Cikin yaren fillacin ta canza harshe take tambayarshi lafiya. Girgiza kai yayi shi kan shi in da za'a kwana ana tambayarshi ba zai ce ga damuwarshi ba, kawai dai ya ji ba daɗi irin kallon da tsakanin Nuratu da wanda ta ƙira yayanta, haka kawai ya ji ba yaya uwa ɗaya uba ɗaya suke ba. In da hakan ta kasance da ya ga kama ko jini a jikin junansu. Ganin kamar zai saka Ummi damuwa ya miƙe ya mata sallama zai wuce. "Ummi zan wuce. Hanan zata zauna kwana biyu tare da ku." Ta san da damuwa tare dashi amma yaƙi sanar mata, bai cika barin Hanan ta zauna a gida ba kullum tana maƙale dashi dan ko da ta fara wayo ya ɗauke abarshi suka koma gidanshi, sai dai ya kawota su ganta in an ce ya kawota hutun kwana biyu ji yake kamar za'a rabasu. Kai kawai ta ɗaga mishi har ya fice. Bai biya inda su ƴan biyu su ka yi da Hanan ba ya bar gidan. *** Washegarin da safe Col. Ahmad ya zo gaishe su Mami tare da breakfast da ya saka aka haɗa musu. Nuratu dai ta sanshi kuma har lokacin taƙi sake mishi fuska. Mami bata san komai ba ido kawai take binshi da shi, kuma yaƙi basu fuskar tambaya dan da zaran yazo ya tambayi mai jiki yake tafiya. Haka yau ma suna gaisa da Mami ya tambayi jikin Nuratu tace da sauƙi ya ajiye musu abincin da ya kawo ya musu sallama. Nuratu ko kallon inda yake ba tayi ba, shi kam ma dariya take bashi sai da ya murmusa. A yau da karfe goma suka samu ziyarar Aunti Zarah da Rahma sun zo duba Nuratu. Allahamdulillahi yadda su kaga ta samu sauƙi abin ya musu daɗi. Suka wuni har yamma kafin su fara shirin tafiya. *** Sati biyu kenan Mufid ya rasa mafita ina zai ga Nuratu, ya je makaranta babu ita babu labarin ta, har ana shirin fara exam. Ya je gidansu har yanzu da kwaɗo rufe. Rufaida kuma duk hanyar da zai haɗasu ta toshe balle ya tambaye ta inda kawarta take.   Ita kanta Rufaida ta je asibiti ta je gidansu Nuratu duk bata samun su, abinda ya zo ranta shine ko sun bar garin, gashi ta gagara ƙiran wayarta dan tafi son suyi magana gaba da gaba. Da daren Rufaida ta fito wajen su Hajiya Batul, zata shiga ɓangaren su wajen ƙarfe goma sha ɗaya sun gama hira, abinda ya jimarta ma wani film suke kallo da aka saka a Mbc Bollywood mai suna Hichki, shi ya sata zama har aka gama kafin ta fito. Mota ta gani yayi parking ta juya ta kalli mai fitowa ta ga Mufid ne, kai ta ɗauke ta wuce ciki da sauri, bata kai ga ƙarasawa ɗakinta ba ta ji an fizgota ta juya a fusace. "Ni fa ba ƴar iska bace da zaka din ga taɓa ni. Dan ina matsayin ƙanwarka hakan bai baka damar shiga cikin rayuwata ba." A buge yake yasha yayi tatil, burinshi tunanin Nuratu ya fita a ranshi ko zai samu yana runtsawa domin har cikin baccin shi zuwa take. "Bari in nuna miki halinmu mu ƴan iska." Mufid yace cikin maye ya fara jan Rufaida zuwa ɗakinshi. Ihu ta fara ya rufe mata baki ta fara kai mishi duka. Ummu tana bangaren Daddy abinda Rufaida ta manta da shi kenan domin duk ranar girki acan mai girki rake kwana. Tsakiyar ɗakin ya wurgata ta tashi da sauri za ta gudu ya sakawa ƙofar mukulli ya zare mukullin ya jefa a aljihunsa. Bugun kofar take tana kuka jikinta duk rawa yake. "Dan Allah Mufid ka buɗe min ƙofa. Ummu ki zo ki cece ni." Bathroom ɗinshi ya shige ya barta anan, wanka yayi duk cikin magagin maye ya fito ɗaure da towel Rufaida na ganin haka ta ƙara sautin kukanta tana bugun ƙofar tare da ƙiran duk sunan wanda ya zo bakinta dan neman taimako. Mufid bai kulata ba ya juyo ya ɗauki kayan bacci ya saka ya koma kan gadon ya kwanta. "In kin gama ihunki ki zo muyi magana, amma ki tabbatar zaki bani amsa gamsashshiya, sai in buɗe miki ƙofar." "Ni dai dan Allah ka buɗe min ƙofar in fita." Rufaida tace cikin kuka. "Baki yarda ba kenan. Bani da lokaci bacci nake ji." Yace ya mayar da kanshi ya kwanta. Kamar mai tsoronshi dama tsoron take ji ta matsa kaɗan. "Gani nan." "Matso dai mana." Mufid yace yana ɗago kansa daga kwancen wanda yake masa nauyi ya kalli Rufaida. .... #vote #comments #share MADUBIN GOBE  20. Pharty Bb. Wattpad phartybb. "Baki da niyar tafiya kenan kin fi so ki kwana anan." Mufid yace yana maida kanshi ya kwanta. Ganin haka da sauri Rufaida ta matsa bakin gadon. "Gani na zo." Jin muryarta kusa dashi ya sashi buɗe lumshashshun idanuwansa da suke cike da maye suka canza kala. "Ki sanar dani ina Baby take, na san kin san komai a kanta." "Wace Babyn kuma?" Ta tambaye shi duk da tasan akan wa yake maganar. "Kin fini sanin ta. Babyna Nuratu." "Ni ma ban san inda take ba." "Au haka ne, haka ki ka ce." Yace yana miƙewa zaune. "Eh wallahi Mufid ban san ina take ba, ko makaranta bata zuwa, na je asibiti ma bata nan, na je gidansu a kulle ina tsammanin an turasu babban asibiti ko sun bar garin." Shuru Mufid yayi kamar ba zai yi magana ba har Rufaida ta dinga rantse mishi. "Shikenan ta shi ki je na baki aikin nemo min in da take in ba haka ba in baki mamaki. Mukullin yana cikin kayan dana cire yana bathroom." Da sauri Rufaida ta wuce ciki ta ciro mukullin ta buɗe ta fita. Ɗakin Ummu ta wuce bata nan anan tayi kwanciyarta bayan ta sakawa kofar key. Da kyar ta iya bacci dan firgita tayi tai gani take tamkar zai mata. *** MAIDUGURI. Washegari Dr Awwab ƙarfe takwas a gidansu ya same shi. Ummi da ido kawai ta bishi, kanshi sunkuye a ƙasa. "Ummi na kasa bacci ne wallahi." Yace yana zama. "Naga alama. Ga ta nan bacci take bata farka ba." "Zan leƙa asibiti in dawo." Dr Awwab yace ya miƙe ya isa kan gadon Ummi ya sumbaci kumatun Hanan dake bacci ya fita, sai da yayi breakfast kafin ya fita a gidan. Kai tsaye asibitin ya wuce ya hau aikin shi bai leƙa wajen Nuratu ba. *** "Ina kuma za ka kai wannan abincin haka Ahmad?" Umma ta tambayi Col. Ahmad da yasa aka haɗa masa breakfast mai rai da lafiya aka jera mishi a gabanshi. "Asibiti zan kai Umma." Yace yana murmushi. "Wato har yanzu baka cire kan ka cikin abinda babu ruwanka ba ko?" "Umma dai taimako nake." "Wani irin taimako? Mahaifinka nan yau kwana nawa da tafiyarshi ka kasa binshi ka duba jikin shi ka tsaya wajen wanda basu san ma kana yi ba. To wallahi kaji na rantse ka shirya ka bi bayansu ban amince ka dawo ba sai in har ya samu lafiya ko hutunka ya ƙare. Kai kana zaune ba aure sa'anninka duk sunyi aure wasu da ya'ya biyu, du bi fa Suwaiba itace ƙarama amma da aurenta har da ƴa. To wallahi na gaji da rashin zamanka ba aure, ido kawai na zuba maka in ga gudun ruwanka." "Kiyi hakuri Umma zan yi, lokaci ne bai yi ba." Col. Ahmad ya tari maganganunta da sauri ta dakata tana kara haɗa rai. "Na dai faɗa maka, ka bishi in ka dawo muyi maganar auren." "Shikenan Umma zan yi ƙoƙarin yin hakan." Daga haka Col. Ahmad ya miƙe ya fita tare da warmers ɗin da aka haɗa masa abinci. Daga gida asibiti ya nufa ya samu Mami bata nan daga Munirat sai Nuratu dake wanka bata fito ba. Bayan sun gaisa da Munirat yake tambayarta mai jiki tace da sauƙi, yace Mami fa tace ta fita. Sai da ta gama shiri cikin bathroom ta fito cikin doguwar abaya da tace zata saka ta gaji da sa kayan asibiti. Waje ta fito dan yunwar cikinta ta samu Col. Ahmad. Bata kalli in da yake ba ta nemi guri ta zauna tana haɗa rai. Lokacin da ta nemi taimako bai mata ba sai yanzu zai zo yana bibiyarta to mai zai mata ko za ta mishi. Murmushi kawai Col. Ahmad yayi da bai cika yi ba sai ya kama ya miƙe ya nufi gurinta, ganin haka Munirat ta miƙe ta fita dan basu guri tsammaninta duk wata alaƙa ce tsakanin su. Nuratu da ta ga sun rage su biyun zuciyarta ya fara bugawa ta fara waige waige neman hanyar gudu. Ganin da gaske yake zai iso gurinta ta ce. "Kar ka ƙaraso dan Allah." Dakatawa yayi daga in da yake yana hango tsantsan tsoro a tattare da ita hakan yasa ya tsaya yana dubanta. "Wata kila daga yau ba za ki ƙara ganina ba sai wani lokaci." Bata mishi magana ba sai ido da ta zuba mishi yaci gaba da faɗin. "Please ki daina fushi dani akan na kasa kubutar da rayuwarki daga waɗancan azzaluman, Allah ya riga ya rubuta hakan zai faru, ƙaddara ce, amma Insha Allahu na miki alƙawarin ɗauka miki fansa bisa abinda suka aikata miki. Zan yi tafiya na ɗan wasu kwanaki, fatan kafin na dawo kin ƙara samun sauƙi." Kasa ce mishi komai tayi ya nufi hanyar waje ganin bata da niyar mishi magana. "Allah kiyaye hanya." Ya tsinci muryar ta da saurinshi ya juyo ta kawar kanta gefe. Murmushi yayi ya amsa da amin kafin ya fita. Munirat tana ganin ya fita ta koma ɗakin, suna zaune Mami ta dawo ɗauke da breakfast da ta sayo musu. Ganin Warmers ya sata tambayar Munirat waya kawo duk tsammaninta Dr Awwab ne, tace a'a wani ne ita ma bata sanshi ba. Mami ta kalli Nuratu ganin kamar tana cikin damuwa ya sata fasa tambayarta wanene ko ta sanshi. Abincin suka buɗe ferfesun kan rago ne sai fankasu da ya soyu mai kyau, Munirat da Nuratu su kaci, Mami kasa ci tayi. "Mami! Dr ya zo ina bacci ne?" Nuratu ta tambaya tana zuba magungunanta a baki. "A'a ban sani ko kina wanka ba." "Bai zo ba." Cewar Munirat tana tattare gurin da suka yi breakfast. Ba wanda ya ƙara magana Nuratu tayi baya ta jingina da gini tana tunanin mai ya hana Dr Awwab zuwa yau har gurin ƙarfe goma. Ranar haka ya wuni har yamma bai leƙa wajen Nuratu ba, so yake ya yakice kanshi daga inda zuciyarsa yake son kanshi. Haka ya gama aikinshi ya wuce gida. Hanan da take saman cinyar Hussaina tana bata kunu ta dinga miƙa masa hannu ya ɗauketa, hannu ya sa ya ɗauketa sama yana kai mata kiss kumatunta. "My love nayi missing ɗinki." Yace yana zama saman kujeran falon ya ajiyeta saman cinyarshi sai baki take buɗe masa da hakwaranta biyu a baki da jagwalgwalon maganarta. "Ina Ummi?" Dr Awwab ya tambayi Hussaina da take ƙoƙarin barin gurin. "Tana falonta." Miƙewa yayi ya nufi cikin falon bayan sun gaisa yayi alwala ya fita, sallah yayi ya dawo ya ɗauki Hanan suka tafi gidansu. *** Washegarin zuwan su Aunti Zarah, Hasiya da Rukayya tare da Yaya Al-ameen shi ya mantar da Nuratu komai. Ba laifi ta shiga cikinsu sun yi hira, kasancewar sun san matsalarta suka rage surutun sai sama sama da suke yi. "Muje waje ƙanwata." Yaya Al-ameen yace da Nuratu da ya sata kallon shi ya ɗaga mata kai alamar roƙo ta dubi sauran kowa yana harkar gabanshi. "Mu je." Ta miƙe ganin ya miƙe ya fita ta bi bayanshi, da kallo suka bisu sauran. Marasa lafiya da suka fara samun lafiya suna filin asibitin tare da masu kula dasu. Ƙarƙashin wani bishiya ya sama musu suka zaune saman kujeran wajen. Idonshi yana gefe ya zubawa bishiyar dake gefensu ido. "Ƙanwata ya kuma mu ka ji da abinda ya faru? Bana son tada abinda ya wuce amma ya zamemin dole ne, fatan Allah bi miki haƙƙin ki ya saka miki." "Ameen ya Allah." Nuratu tace idanuwanta na cika da hawaye da kullum sai ta zubarsu cikin dare. Kallonta yayi jin muryarta ya canza suka haɗa ido ya hango kwantaccen hawaye cikin kwayar idonta. "Bana son kukan nan Please kar ki yi. Ko kina tunanin dan wannan abin ya faru Muhammad Al-ameen zai ja baya ko fasa auren ki. Hasalima ƙara son ki yake, ki saka wannan a ranki. Jira nake a sallameki ku koma gida in tada maganar auren mu, kin tuna ke kika min alƙawarin haka." Tabbas ita ta mishi maganar aure a lokacin da take ƙoƙarin raba kanta da Mufid. Yanzu kuma fa da komai ya lalace, bata da wani daraja da ƙima da za tayi tinkaho a matsayin ta na ƴa mace. Ita da shi ɗin basu dace ba yanzu, ko ta aureshi cutan shi za tayi. A zahirin girgiza kai tayi tana share hawayenta. "Yaya Al-ameen ka bar wannan maganar ba yanzu ba dan Allah." "Saboda mai yasa. Wani tunanin ki daban?" Yace kamar ya karanci maganar zuci da take. "Ni dai ba yanzu dan Allah." Bai so ba amma ganin kamar zata shiga damuwa har yanayin fuskarta ya fara canza ya miƙe. "Shikenan na bari ƙanwata. Tashi mu je ciki." Da sauri ta miƙe ta fara tafiya ya bi bayanta suka koma. Ƙarfe huɗu suka musu sallama suka tafi. *** Cikin kwana biyun Dr Awwab ya kauracewa idanuwansa da zuciyarsa ganin Nuratu. Bai yarda tana da muhimmanci a rayuwar sa ba sai da ya rasa ganinta, haka ya ɗauka a cikin zuciyarsa shaƙuwa da su kayi ne sam ba sonta yake ba. Aikin shi yake zuwa yayi ya koma, wataran yazo da Hanan wataran ya barta wajen su Hussaina. .... Col. Ahmad ranar da ya zo da kwana biyu ya bi mahaifinshi ƙasar Egyp, allahamdulillahi ya samu jikin da sauƙi dan har ya fara gane mutanen kanshi yana magana ƙasa ƙasa. Burin Umma ya cika ta rabashi da wannan jarababbun mutanen da suka liƙe masa. *** DAMATURU. Mufid ban da Shaye-Shaye da kashe kuɗi bashi da aiki tunanin Nuratu ya sashi a gaba, ko bacci yake sunanta yake ƙira. Tin Ummu bata sani ba har ya zamto ta lura da halin da yake ciki. Ummu tsorata tayi cewa take ko aljana ya yiwa fyaɗe ta shiga jikinshi dan ɗaukar fansa tana neman haukatar dashi. Rufaida tun ranar da su kayi, ta haɗa kayanta da duk abinda zata buƙata ta tafi gidan babban yayarsu Aunti Humaira sai ƙura ya lafa, daga can take wucewa makaranta hankalinta a kwance. *** Bayan sati uku. Jikin Nuratu yayi sauƙi sosai, babu wani matsala ko damuwa sai in har ta fara tunanin za taji ciwon kai ko shiga cikin hayaniya tuni zata birkice. Maza kuwa duk ta haɗa su ta tarkata ta watsa a kwandon shara. Mutum biyu take ganin kutumcin a rayuwarta Dr Awwab da Yaya Al-ameen da take ganinshi matsayin yayanta. Yau ta cika wata biyu cib, wajen ƙarfe biyu na rana bayan taci abinci tasha maganinta ta koma ta kwanta. Tunani kawai take mai ya hana Dr Awwab zuwa yau tsawon sati biyu babu shi babu labarin shi. Maimakon ya zo duba ta kullum sai ma wani Dr da yake zuwa a madadin shi. Zumbur ta miƙe daga kwancen da take ta saka hijabin Mami tare da zura silifas ɗinta. "Ina zuwa?" Cewar Munirat kasancewar Mami tana sallah. "Waje zan leƙa ba zan jima ba." Daga faɗar haka ta fita Munirat ta bita da ido. Kai tsaye in da ta taɓa bi suka je ofishin sa ta bi, wasu suna kallonta wasu suna harkar gabansu har ta isa bangaren da ofishinsa yake. Bakin kofar ta tsaya ta riƙe handle ɗin shiga, sai kuma ta ji ta kasa, ta sake handle din har za ta juya taji muryar Hanan ta dawo ta buɗe tana shiga da sallama. Jin muryar mai sallama ya saka Dr Awwab kallon gurin suka haɗa ido, rai ta haɗa. Wato ma yana zuwa gurinta ne kawai baya zuwa. Hanan da ta ganta ta rarrafa ta taho, hannu Nuratu ta saka ta ɗauketa kafin ta zauna tana fuskantar Dr Awwab da ido kawai ya saka musu, sun mutuƙar masa kyau. "Mai yake hanaka zuwa duba ni yau tsawon sati uku." Nuratu tace tana kallon cikin idanuwanshi da sosai tayi ƙoƙarin saka nata cikinsu domin yadda suke lumshashshu ya zuba mata su wani abu sai fitowa yake yana shiga cikin nata da ya haddasa zuciyarta dukan uku uku. .... #vote #comments #share MADUBIN GOBE  21. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Dr Awwab idanuwanshi ya ɗauke cikin na Nuratu da ta sarƙesa da nashi ya kawar gefe ya ɗaura saman Hanan da ta kwanta luf a jikin Nuratu tamkar ta santa. "Babu abinda ya faru Noor, aiki ya min yawa. Idan har hakan ya ɓata miki ki gafarce ni." Ajiyar zuciya Nuratu ta sauƙe tana miƙewa. "Babu abin ɓacin rai, Allah ya baka hakuri bisa katse maka aikin ka da nayi." Daga haka ta ajiye Hanan, yarinya tace bata san zancen ba ta fara kuka sai ta ɗauketa. Dr Awwab ya saka hannu ya ɗauketa ya fara lallashinta. Nuratu har ta kai bakin kofa ta juyo ta kalleshi. "Nagode Dr da taimakon daka min a rayuwa, ka sani kai ne mutum na farko dana fara yarda da shi bayan abinda ya faru a rayuwata. Nagode." Maganganunta sun shige shi yana kallonta har ta juya ta fice ya kasa cewa komai. Tafiya Nuratu take yi haushin kanta take ji da tayi saurin amincewa da shi ta shigar da kanta rayuwarshi da ƴarshi da matarshi. Tana komawa ɗaki Mami ta dinga tambayarta ina ta je. "Nan ne ba nisa. Mami na gaji a sallame ni mu koma gida ni na warke." Kallonta Mami tayi fuskarta sam ba alwala. "Sai Dr Abbas yazo zan mishi magana mu ji mai zai ce." Bata ce komai ba ta kwanta. *** Col. Ahmad yana ƙasar Egyptian amma hankalinshi yana Nijeriya a gurin Nuratu, tsoronsa ɗaya kar a sallami su Nuratu su koma gida bai san address ɗinsu ba. Jikin mahaifinshi da sauƙi dan har ya fara takawa, paralise ne ya kama shi kuma yanzu da sauƙi. Kullum sai sunyi waya da ƴan gida, musamman ƙannenshi mata da suke yawan ƙira da jin jikin babansu. Watansu ɗaya yau cib a can ya samu ƙira daga gurin aikin shi, dole ya sashi shiryawa ya musu sallama ya taho Nijeriya in da yake saka ran suma sati mai zuwa zasu taho . Gida ya nufa duk ƙannenshi sun zo masa sannu da zuwa da tambayar jikin mahaifinsu yace da sauƙi suma nan da sati ɗaya za su taho. Abinci kawai yaci ya kwashi mukullin motarsa ya fita burinshi da addu'ar shi Allah yasa Nuratu ba'a sallamesu ba. Yayi kewarta sosai da fushin da take mishi. Murmushi kawai yayi dan tunawa da kwata kwata bata mishi magana sai ta ga dama. A harabar asibitin ya samu wanɗansu wanda zai iya cewa yayunta ne dan ya sha ganinsu tare da ita. Gaishesu yayi ya ga babu Nuratu cikinsu ya nufi ciki, a hanya suka haɗu da ita Mami suna fitowa. Har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da Mami ta amsa kafin duk su fito waje. Yaya Al-ameen shima ya zo da Rahma ɗaukarsu a yau aka sallamesu zuwa gida bayan magunguna da aka ɗaura Nuratu a kai da wanda za tana zuwa karɓa. "Dr in da zai yi wu za muna aikowa a karɓa mana saboda zuwan watarana ba za'a samu ba." Mami ta tambayi Dr Awwab da zuwanshi yau bayan tsawon wata ɗaya da ya kaurace musu. Shima dan Nuratu ta matsa a sallameta ne kuma ya ga dacewar hakan, kewarta zai yi ya sa baya son sallamarta. "Zan aika mata, ki bani Address." Cewar Dr Awwab yana kai dubanshi kan Nuratu ta watsa mishi harara ta ɗauke idanuwanta. Murmushi kawai yayi, hararan yana taɓa mishi zuciya da tsaya mishi a rai, ya karɓi address ɗin su gurin Aunti Rahma. "My patients an sallame ku ne." Col. Ahmad yace ganin suna shiga motar Yaya Al-ameen. Kai ta ɗaga mishi, Mami ta zagayo gurinsu. "Yaro gashi har zamu rabu ban san ko sunanka ba balle in maka godiya. Nagode da irin dawainiya da kayi damu Allah saka da alheri." "Mama! Nuratu ta san ni, sai dai tana min ganin mai laifi. Amma komai zai bayyana. Ku bani address ɗinku saboda za'a nemeku kwanan nan." "Nema kuma." Mami ta tambaya da mamaki. "Kar ki damu, ba wani abu bane, za ki ji komai." Ko ba komai ya nuna ƴarta kulawa hakan yasa ta bashi address ɗinsu kafin su shiga mota Yaya Al-ameen ya ja suna barin harabar wajen. Sai da yaga fitar motarsu kafin ya koma gida. *** "Ummu wai ina Rufaida? Bana ganinta kwana biyu shegiyar yarinya." Dubanta Ummu ta kai kan Mufid dake kwance rashe rashe saman kujeran falon ta yau sunyi faɗa da Faisal akan ya damesu da zancen Nuratu ya dawo gida. "Tana gidan Humaira." "Au can ta gudu?" "Ban sani ba nima. Na rasa mai aka mata ta kauracewa gidan nan." Dariya Mufid ya kwashe da shi yana tafa hannunshi, wato dan shi ta gudu, ai kuwa zai bita can sai ta nemo mishi Babyn shi Noor. Ƙarfe biyar na yamma a ƙofar gidan Yayarshi Humaira ya sameshi ya yi parking a waje ya tura get ɗin gidan ya shiga har falon babu sallama. Humaira dake falon jin an buɗe kofa ta ta juya ta kalli ƙanintan. "Sannu babbar yaya." Yace yana zama ta watsa mishi kallon banza. "Wallahi ka ji kunya Mufid, ace za ka shigo gidan mutane babu sallama." "Allah baki hakuri mantawa nayi. Assalamu alaikum." Tsaki ta buga. "Mai ya kawo ka?" "Wajen ƙanwata na zo. Ina Ruffy?" "Ban sani ba, ka bani ajiyarta. Ka ga in tsiyace ta kawoka gidana ka tattare kan ka da iskancin da ka ke ji dashi ka fitar min a gida kar ka tsorata min ƴaƴa." Baki sake yake duban Aunti Humaira, ita ce ƴar farinsu kuma kowa yana bata girma. "Allah baki hakuri Aunti Humaira, laifine dan na zo wajen ƙanwata, amma ba komai ni na zo gidanki, ki faɗa min komai son ranki. Sai anjima" Mufid yace yana tashi, sai kuma taji ba daɗi ɗan uwa dai ɗan uwane balle ciki ɗaya. "Kai ne ai Mufid ban san yaushe nutsuwa zata shigeka ba. Dawo ka zauna muyi hira, na aiki Rufaida yanzu zata dawo." Dama ba son tafiyar yake ba jin haka ya sashi dawowa ya zauna. "In baki labari. Na san ma kina da labarin." "A'a faɗa min. Mai kuma ya faru?" "You know Baby Noor?" Girgiza kai tayi alamar a'a. "Oh baki da labari kenan, wacce dalilinta na shiga cell da nayi raping ɗinta, three month ago." Murmushin taƙaici Aunti Humaira tayi ko kunyar faɗar hakan baya ji, tana da labarin komai da yake faruwa. "Na gane ta. Mai ya sameta?" "Aurenta nake son yi, sonta nake yi wallahi kin ji. Idan na rasata mutuwa zan yi, in kuma ta auri wani to wallahi kashesa zanyi." Dariya Aunti Humaira ta kwashe dashi, wani ubane zai ɗauki ƴarshi ya bawa Mufid. "Allah baka Sa'a." Kawai tace dan gudun bambamin shi ta miƙe ta kawo masa ruwa da abin motsa baki. Rufaida da ce ta shigo falon ganin Mufid kamar ta koma, ta haɗa rai ta ƙaraso ta bawa Aunti Humaira saƙonta zata wuce ɗaki ta dakatar ta. "Gurinki Mufid ya zo." Rai ta haɗa ta dawo ta zauna. "Wato nan ɗin ma sai da ka biyo ni." Rufaida tace tana duban shi ta wani haɗa rai. "Eh mana rasa kunya. Ina aikin dana saka ki." "Ban yi ba! Ni ma neman in da take nake." Miƙewa yayi ya nufi gurinta ta fasa ihu. "Wallahi kar ka taɓa ni gaskiya na faɗa maka. Allah ban san inda take ba har yanzu, naje gidansu har yanzu a kulle, amma zan ƙara zuwa gobe." "Ko ke fa. Aunti na tafi dama abinda ya kawo ni." Mufid yace ya fita ko kallon ruwan da ta kawo mishi bai yi ba yasa kai ya fice. "Menene ya faru." Aunti Humaira ta tambayi Rufaida. Anan ta zayyana mata komai tun daga farko har ƙarshe da zuwa yanzu. "Allah dai ya shirya Mufid, Daddy da Ummu sun gurɓata masa rayuwa a matsayin so da ƙauna. Dan Allah ya baka namiji haka ya kamata ka mai dashi, yanzu da su da yawa ne fa haka duka zasu tashi a lalace. Allah shiryasa ita kuma Allah bi mata haƙƙinta ya saka mata dan in ba hukunta irinsu aka fara ba, ba za'a samu ragowar fyaɗe a Nijeriya ba." Ameen Rufaida ta amsa da shi ta miƙe ta wuce ɗaki dan sallar magriba. **** Da karfe uku suka shigo gari, tayi ta bin garin da kallo abubuwa da yawa suna dawo mata ƙwaƙwalwar kanta, idonta ta runtse har suka shigo layinsu da komai anan ya fara. Har kofar gida Yaya Al-ameen yayi parkinga suka sassauƙa. Nuratu taƙi sauƙa. "Fito mana Nuratu." Faɗin Mami tana buɗe gefen da take. A'a tace tana ƙamƙame jikinta tamkar gani take tana fita Mufid zai kamata. "Fito babu komai gida zamu shiga." Nan ma kan ta girgiza, sai da su kayi da gaske kafin ta fito ta rirriƙe su suka shiga cikin gida. A falon suka sauƙa, Munirat ta hau tattare da share kura kura kafin su ƙarasa cikin ɗakunan suka ajiye kayansu. "In babu komai Mami zan wuce gida, Yaya Al-ameen zai sauƙe ni." Aunti Rahma tace tana gyara zaman ƴarta a kafaɗarta. "Babu komai Rahma. Ki je gida sannu da ƙoƙari Allah ya miki albarka." "Ameen Mami, babu komai." Daga haka ta fita Yaya Al-ameen ya sauƙeta a gida kafin ya wuce gida ya sanar da Amma Jidda sun dawo. Da daren abinci marar nauyi Munirat ta girka musu, bayan sunci Nuratu tayi wanka tasha magungunanta ta kwanta, a tare suka kwana da Mami a ɗakinta dan sam ƙi tayi ta kwana a nata ɗakin. Da taimakon maganin da tasha ta samu bacci ya ɗauketa. Washegarin gidansu cike da yayunta da mazajensu da suka zo dubata, Aunti Zarah da ƙanwarta itama ta zo har da mijin Aunti Zarah ya duba Nuratu yayi tama Mami nasiha akan abinda ya faru, ta mishi godiya domin cuta an riga an cuci ƴarta da ita. Har dare suna gidan har da Amma Jidda da su Walida, zuwansu ya saka Nuratu fargaban da take ciki ya ragu. Abin mamaki da daren ta samu baƙoncin Alhaji Mamman, duk yadda su kaso Mami ta fita ta saurareshi ta ji da mai ya zo kasawa tayi dan bata buƙatarsa a rayuwarta har abada. Nuratu dai ƴarshi ce zai iya iko da ita amma ban da ita, Nuratun ma bashi da hurumi tun da bai san haihuwarta da girmanta da wahalar ta ba sai ita. Dan yanzu abu ya samu rayuwarta zai ce zai shiga ciki shi a wa? Ya mata mai? Kar duniya ta zageshi. **** MAIDUGURI. "Awwab tun jiya na lura baka da walwala duk da dai dama fuskar a haka take." Ummi ta ƙarasa tambayar Dr Awwab cike da zolaya ko zai sanar da ita abinda yake faruwa dashi, fuskar shi babu hayaniya in anyi abin dariya zai yi murmushi amma baya haɗa rai. Murmushi yayi da shi kaɗai yake yi shima sai Ummi da wanda suke da muhimmanci yake musu. "Babu komai Ummi. Ki taya ni da addu'a kawai." "To Allah yaye maka damuwarka, amma matsayina na mahaifiyar ka ya kamata in sani tun da dai ka nuna akwai damuwar." "In lokaci yayi zan sanar dake Ummi na." Daga haka ya miƙe ya fita yana ɗaukar Hanan da tayi bacci dan su wuce gidansu. ... #vote #comments #share MADUBIN GOBE  22. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Shirin kayansa yayi tsaf ya fito da akwatin shi, Umma ta bishi da kallo. "Ina kuma zuwa da kaya haka? Ko hutun ya kare ne?" Col. Ahmad da ya zaune saman kujera yace. "Umma ya ƙare zan tafi an neme ni. Amma ba zan jima ba zan dawo bai fi in yi sati biyu ba. Ki mini addu'a akwai yaƙin da nake son cimma nasara a kai." "Allah baka sa'a ya dawo da kai lafiya." Ameen ya amsa dashi ya tashi ya fita direba ya kai shi har airport ya bi jirgi zuwa Ibadan. *** "Amma ni fa har yanzu ina kan bakana." "Na me kuma?" Amma Jidda ta tambayi Al'ameen duk da ta fahimci akan mai yake magana. Kai tsaye yace. "Na auren Nuratu." "Ni dai ba zan hanaka auren Nuratu ba, amma da ka bari zuwa wani lokaci kaɗan, yaushe ma ta samu lafiya?" Ya san hakan amma dai so yake a san har yanzu yana nan akan bakarshi na son aurenta babu abinda ya canza wai dan ƙaddara ya faɗa rayuwarta. "Shikenan Amma zan ba ta lokaci, amma ba mai tsayi ba." .... Tun ranar da su Nuratu suka dawo ba ta fita ko nan da ƙofar gida, daga falo sai ɗaki, tsoron fita take, duk bayan kwana biyu sai yayunta sun zo dubata tana jin daɗin haka. Magungunanta baya wuce lokaci take sha akai akai da hakan yana mutuƙar taimaka mata, maganar makaranta ta jinginar shi a gefe ba yanzu ba. Yau suka samu baƙoncin Rukayya da Walida, gidan ya mata daɗi. Mami ta fita sarin kaya da ɗan kuɗaɗen hannunta da suka rage dan duk ta cinye jarin a jinyar Nuratu dan ma tana samun taimako daga ƴaƴanta da mutane. Har dare kafin suka tafi, da daren Mami na duba kayan data saro Nuratu na gefe tana gani har ta nuna wani atamfa da ya mata kyau, Mami tace ta ɗauka ta ba ta. Godiya tayi ta ajiye a gefe tana kallon Mami. "Mami ina son miki wani magana, sai dai ban san ya za ki ɗauka ba." "Ina sauraronki." Mami tace taci gaba da duba kayanta. "Ina son shigar da ƙara, ina son kwatar haƙƙina. Ina son ɗaukar fansa bisa abinda aka min." Kallonta Mami tayi ta hango tsantsan buƙatar hakan a fuskarta. Numfashi ta sauƙe. "Kina ganin hakan mai yiwa ne? Ko kin shirya yaƙi da masu hannu da shuni? Ko kina da wani wanda zai tsaya miki ya taimaka miki ya kwatar miki haƙƙin ki. Ko kina da kuɗaɗen da za ki shigar dan samun nasara. Zamani ya canza Nuratu, masu kuɗi ba'a hukunta su, duk abinda suka aikata komin munin shi rufewa ake. Kai talaka in an cuce ka sai dai ka ɗauki hakuri ka kai kukan ka wajen Allah. Cuta an riga an cuce mu an cuci rayuwar ki, bamu da ikon ɗaukar hukunci. Allah kaɗai zai saka miki." "Mami zan kashe Mufid." Nuratu tace tana fashewa da kuka mai cin rai bayan gama bayanin Mami, rayuwarta ya lalace ya tarwatse dalilin shi. "Kul na ƙara jin maganar kisa a bakin ki, ki barshi da Allah kaɗai ya isa da shi. Sannan ki godewa Allah da basu shafa miki wani cutar ba ko sun bar ki da ciki ba." Nasiha da faɗa Mami tayi ta mata tun tana kuka har tayi shuru, wani mugun ciwon kai ne ya zuba mata a daren da kyar ta samu ta sha magani ta zube a gurin ta hau bacci. *** Ibadan. Satin Col. Ahmad ɗaya ya ƙara ɗaukar hutu ya taho Maiduguri, gida ya fara biyawa dan a ranar Baban shi ya dawo, jiki yayi sauƙi sosai. Yayi murnan ganin ya warke tamkar ba shi ba, bayan sun gaisa da kowa ya ɗauki hanyar Damaturu. Kai tsaye Police station ya nufa, yaci sa'a ya samu DPO Salisu akan aiki. Yayi mamakin ganin shi tsammanin shi duk ya bar case ɗin har abun ya fara damun DPO Salisu yake cewa zai ƙira shi ya ji sai kuma ya fasa. Bayan sun gaisa da Col. Ahmad yace. "Sai kaji shuru kuma. Uzuri ne ya taso min, sannan ita yarinyar sai kwanan nan ta samu lafiya. Fatan har yanzu maganarmu tana nan." "Yana nan mai zai hana, shin ka shirya da shigar da ƙara?" DPO Salisu ya tambayi Col. Ahmad. "Shirye nake tsaf da gwagwarmaya da kowa." Col. Ahmad ya bashi amsa dan a shirye yake tsaf. DPO Salisu tashi yayi daga saman kujeransa ya ƙira ɗan sanda biyu, ɗaya mai rubuta jawabi ɗaya shi za'a bawa sakon. "Rubuta takardar tuhuma zuwa koto ana ƙarar Mufid Kashim Mufid da abokansa, sun yiwa yarinya ɗaya fyaɗe a ranar ashirin ga watan Satumba." Bayan ya rubuta ya linƙe ya miƙawa ɗaya ɗan sanda da zai kai koto DPO Salisu yace ya kai shari'a court, babu musu ɗan sandan ya fita da saurin shi. DPO Salisu ya juya ya dubi Col. Ahmad. "InshaAllah ina sa ran zuwa jibi za su neme mu, zan sanar da kai da zaran an neme mu, za su tura takardar tuhuma zuwa gidan su Mufid, sannan iyayen yarinyar ya kamata su sani dan su nemi lauya da zai tsaya musu." "Nagode DPO, sai dai maganar lauya, na fi son da zan samu ta waje na, domin komai in zai faru kar iyayen yarinya su sani, sai ranar shiga koto kaɗai zan sanar dasu." Shuru DPO Salisu yayi ya rasa Col. Ahmad wani irin mutum ne, sune dai irin mutane masu yin abu dan Allah ba dan idon mutane ba. "Akwai lauya dana sani sunanshi Affan lauyan gwamnati ne, yana aiki a high court ya san kan aikin shi, zan baka number nashi ka ƙira shi nima zan ƙira in sanar dashi ni na turo ka." "Nagode da taimakon da ka ke mini, Allah biya ka da alherin shi." Col. Ahmad yace yana miƙa masa wayar shi. "Kai za'a ma godiya ganin ka jajirce an kwatarwa yarinyar nan haƙƙinta, abinda yayi ƙaranci kenan a zamanin yanzu." Anan su ka yi sallama bayan ya bashi numbern Lauya Affan. Bai ƙira ba sai da ya isa gida ya huta yaci abinci ya fito filin gidan nasu zuwa wajen da suke shan iska. "Assalamu alaikum Malam Affan ne?" Col. Ahmad yace bayan Barrister Affan ya ɗauka. "Walaikum Salam, tabbas ni ne, an wuni ƙalau." Barrister Affan ya amsa daga ɓangaren shi. "Ko kunyi magana da DPO Salisu da ke garin Damaturu, shi ya bani numbern ka." "Mun yi magana dashi yanzu bai jima ba. Ya sanar dani ƙiranka da wasu abubuwa kaɗan." "Hakane, ina son haɗuwa da kai dan Allah in zai yiwu, saboda bamu da lokaci, abin da ya faru ya jima yanzu kuma ya zo a ƙurarren lokaci." "Zuwa yaushe kenan?" "Gobe dan Allah." Da sauri Col. Ahmad yace. "Allah kai mu, zan turo maka address ɗin in da zamu haɗu." "Ameen Nagode sosai." Bayan sunyi sallama Barrister Affan ya turowa Col. Ahmad address ɗin gurin da zasu haɗu. .... Washegarin ranar Alhamis ƙarfe goma ta samu Col. Ahmad a cikin garin Damaturu, kai tsaye in da su kayi zasu haɗu da Barrister Affan ya nufa. Gurine na zama, kewaye yake sai rumfa rumfa da kujeru a zagaye gurin ba hayaniya sosai. Bayan sun gaisa suka gabatarwa da juna kai kafin Col. Ahmad ya yiwa Barrister Affan bayani abinda ke tafe dashi. "It's rape case?" Barrister Affan yace bayan gama sauraron bayanin Col. Ahmad. "Yes and ina son kwatar mata haƙƙinta ko dan masu hali irin na shi, sannan in nuna uban yaron nan kuɗi ba komai yake magani ba." Barrister Affan na sosa saman kanshi yace. "Hakan ma yayi, ina son ganin yarinyar da duk wanda tayi mu'amala dasu kafin da bayan abin ya faru." "Bana son su sani Barrister." "Saboda? Haƙƙinta ne fa, ta ya za kace baka so, in ma tsoro ka ke ji suce ba zasu iya shari'a da masu kuɗi ba kar ka damu na san yadda zan ɓullo mata." "Shikenan mu je gidansu." Babu musu Barrister Affan ya miƙe suka fita a gurin. Basu da lokaci dan haka basu ga ta zama ba. *** Mai gadin sai Knocking kofar falon ya ke babu wanda ya buɗe har ya juya riƙe da farin takardar da ɗan sanda ya kawo a bawa Alhaji Kashim. Yana zama aka danna horn ya tashi ya buɗe. Alhaji ne da kanshi. Bayan ya rufe get ɗin har zai zauna ya ɗauki farin takardan ya bi bayan Alhaji dashi. "Alhaji! Alhaji!" Yace da karfi Alhaji Kashim ya tsaya yana duban shi har ya ƙaraso ya miƙa masa farin takardan. "Saƙo ne aka bani in baka." Hannu yasa ya karɓa yana wucewa ciki. A falon shi ya tsaya ya samu Hajiya Hindatu tana jiran isowar shi. Ciki ya shiga ya watsa ruwa ya fito cikin jallabiya ta kawo masa abinci, yana cikin ci ya tuna saƙon da aka bashi. "Miƙo min wancan papern Hindatu." Hannu tasa ta ɗauka ta miƙa mishi bayan ta warware ya karɓa ya hau dubawa. Takardar tuhuma ce na Mufid da abokansa bisa fyaɗe da suka yiwa wata yarinya watanni uku da suka wuce, ana neman su ranar Litinin a koto dan amsa laifin su in basu yarda kuma ba ayi shari'a da su. Dariya ya kwashe da shi bayan ya gama karantawa. "Wato wannan yaron har yanzu bai hakura ba ko?" "Wani yaro kuma?" Cewar Ummu dan bata gane inda zancen ya dosa ba. "Case ɗin nan ya ɗago na Mufid, ana nemansu a koto ranar Litinin dan yin shari'a, ni zai yi wa haka, to mu zuba ni da shi zan bashi mamaki." Ummu da ta gane inda bakin zaren yake tayi ta surfa ruwan bala'i. "Kar ki damu Hindatu, zan samu Barrister Auwal muyi magana. Ina shi Mufid ɗin?" "Ya fita." "In ya dawo ina neman shi." To ta amsa dashi tana sauƙe huci ranta ɓace an sawa tilon ɗanta namiji ido. *** "Nuratu ki buɗe baki ki sanar da shi abinda kika sani." Col. Ahmad yace yana roƙar Nuratu da take kuka sosai. Bayan zuwansu gidan da kyar suka shawo kan Mami ta yarda da batun shiga koto. Nuratu da ta ji hakan kuka ta fara da ta rasa na farin cikin za'a kwata mata ƴancinta ne ko na tuna abinda ya shuɗe. A hankali Nuratu ta sanar da Barrister Affan farkon haɗuwarsu da Mufid da irin kalaman da yake mata har zuwa ƙofar gidansu da yake yi da kuma ranar ƙarshe da ya ɗauketa. Anan ta dakata ta kasa ci-gaba da maganar ta fashe da kukan da yake taɓa zuciyarta da su masu sauraron ta. "Daga nan sai suka afka miki ta ƙarfi ko da son ranki." Barrister Affan ya tambaye ta ganin ta tsagaita kukanta. Kallon Barrister ta yi da jajayen idanuwanta. "Ƙarfi suka nuna min, Mufid kaɗai na san ya fara amfani dani daga nan ban ƙara sanin komai ba sai tsintar kai na nayi tamkar mahaukaciya marar amfani." "Fatan duk abinda kika faɗa zaki iya maimaita shi a gaban alkali domin a kwatar miki haƙƙin ki a hukuntasu dai-dai da laifin da suka aikata." Tambayar farko ta ji ya bata haushi amma faɗar haka ya bata kwarin gwiwa ta ɗaga kanta. "Zan yi, zan faɗa komai." Tace tana share hawayenta. "To mun gode Malama Nuratu." Barrister Affan yace yana rubuce rubuce, duk tambayar da ya mata dan ya tunzura zuciyarta ne ta ji haushi ta cire tsoro ta faɗi gaskiya kuma hakan yayi aiki. "Ki zauna cikin shiri Nuratu za'a neme ki cikin satin nan. In akwai wani abin da ku ke buƙata ki sanar da ni." Kai ta ɗagawa Col. Ahmad, kunyarshi ya kamata da ta kasa fahimtar shi a baya take mishi ganin mai laifi. *** Bayan Barrister Auwal ya gama karanta abinda ke rubuce a papern ya kalli Alhaji Kashim. "Wato Alhaji lokaci ya ƙure mana. Amma shawara ɗaya zan baka ka yi gaggawar fitar da Mufid a ƙasar nan ko kuma ka gargadesu kar su amsa laifinsu. Domin da zaran ya amsa komai zai kwaɓe mana. In kuma bai amsa ba zan san yadda zan ɓullowa lamarin." "Barrister ka na ganin hakan mai yiwa ne?" "Sosai ma, ka yarda dani kawai." Cewar Barrister Auwal yana nuna kanshi. "Shikenan Barrister na yarda da kai. Zan gargadi Mufid, domin maganar fitar shi a gari lokaci ya ƙure." "Hakan za'a yi." Faɗin Barrister ya tashi ya mishi sallama ya fita. **** Barrister Affan da Col. Ahmad ba su zauna ba sai da suka karɓi dukkan information a gurin Dr Sadiq na abinda ya shafi Nuratu. Suka sanar da shi ya kamata ya halarci zaman koto dan bada shaida kuma ya amince domin yayi alƙawarin hakan a baya. "Ya za'ayi mu samu sauran bayanai bayan barinta asibitin nan." Barrister Affan ya tambaya. Dr Sadiq yace. "Sauran kuma suna Maiduguri asibitin da muka tura su." Col. Ahmad yace yana duban Barrister Affan. "Kar ka samu damuwa Barrister, zuwa gobe zan sanar da Dr Awwab." "Shima ya kamata ya halarci zaman koto." Faɗin Barrister Affan. "Za muyi magana da shi." Col. Ahmad yace suka ma Dr Sadiq godiya suka fita. A hanya suka rabu Barrister Affan ya wuce gidanshi, Col. Ahmad ya kama hanyar Maiduguri lokacin ƙarfe biyar na yamma. Washegarin juma'a ya samu Dr Awwab da maganar. "Insha Allah za ku ganni." Dr Awwab yace bayan ya bashi duk abin da ya shafi Nuratu. Godiya Col. Ahmad yayi kafin ya mishi sallama ya fita. Baya yayi ya jingina da kujeran da yake kai ya lumshe idanuwanshi. Yayii kewarta sosai, tunaninta ya hanashi hutu cikin sati biyun, hotonta yake gani cikin zuciyarsa, Allah Allah yake ƙarshen wata yayi ya kai mata magungunanta ya samu abinda zai fake da shi yaje kallonta ko zuciyarshi za ta samu ta barshi yayi sukuni. Shaƙuwa su ka yi ba sonta yake ba cewar shi. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  23. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Wallahi ka ji na rantse kar ka yarda ka amsa laifinka bisa ƙarar ka da ake yi. Idan ka amsa ka san dai babu abinda zai hana a hukunta ku, sannan ka sanar da su Faisal suma haka. Ka ji mai na faɗa maka." "Na ji Daddy. Baby Noor ta dawo ne?" Kallon Mufid Alhaji Kashim yayi yana mishi wani faɗa daban shi kuma yana tambayarshi wani abun daban. "Ban sani ba. Tashi ka bani guri." Yace rai a ɓace. 'Anya zai aikata abinda suka nema a gurin shi.' Zuciyar Daddy ya tambayi shi bayan tashin Mufid a gurin. Mufid fitarshi bai tsaya ko ina ba sai wajen shashancin su da su AA da Faisal. "Guys Baby Noor ta dawo." Faɗin Mufid yana ɗaukar kwalbar wine ya a zuba cup bayan ya zauna. AA da Faisal suka zaro ido kamar zai faɗo jin maganar shi. "Kana nufin waccan yarinyar da dalilinta muka kwana a cell." AA ya tambaya cike da tsoro. "Yes ita mana." Mufid yace yana kafa cup ɗin a baki ya shanye tas kafin ya kallesu yana faɗa musu abinda Daddyn shi yace, duk sun yarda da hakan. Mufid ya miƙe yana cewa. "Mu je ku rakani gidansu." "Waye ni? Ba inda zan je." AA yace da sauri. Faisal ma ya girgiza kai alamar a'a haka yasa ya fita. Kai tsaye gidansu Nuratu ya nufa rabon shi da zuwa tun watannin baya da ya yi ta zuwa a kulle. Kofar gidan a buɗe kai tsaye ya nufi cikin gidan yana ƙare masa kallo. Munirat da ta fito daga kitchen ta bishi da kallo, ta so gane fuskarshi tace. "Bawan Allah lafiya?" "Baby Noor tana nan? Ƙiramin ita Please." Sai yanzu ta gane fuskarshi ta haɗa rai. "Bata nan." Wani kallo ya watsa mata ya nufi falon gidan ta bishi da sauri, kafin ta ƙarasa ya jawo ƙofar ya kulle da ƙarfi, ta tsora ta tsaya tana bugun ƙofar ya buɗe. "Baby Noor! Baby Noor." Mufid yake faɗa yana buɗe buɗen ƙofofin da suke cikin falon, ɗakuna biyu ne, ya buɗe na farko ba ta ciki ya buɗe d'ayan ya hangota kwance tana bacci hankali kwance. Kamar wani mahaukaci ya ƙarasa da sauri bakin katifar da take kwance ya durƙusa ya zuba mata idanu. A cewar shi sonta yake domin yadda zuciyarshi yake fisgar gangar jikinshi zuwa gareta. "Baby Noor i missed you." Yace hannunshi saman fuskarta yana zagayawa, ƙaramin bakinta ya zubawa ido. Cikin bacci Nuratu ta ji ana taɓa mata fuska, turare da wani irin hayaki mai wari na shiga hancinta. Idanuwanta cike da bacci ta buɗe, dishi dishi take ganin mutum zaune kusa da ita har ta buɗe tas saman fuskar da ko mafarki take ba zata mance ba. "Babyna kin farka?" Ta ji muryar Mufid. Wani razanannen ihu Nuratu ta sakar mishi tana ja baya, hannu ya kai zai taɓa ta ta sake fasa wani ihun iya ƙarfinta. "Kar ka taɓa ni. Mami ki zo ki taimaka mini zan kasheni." "Oh Baby, tsorona kike je. Ki bari ko gaisawa muyi mana sannan muyi maganar da ya kawo ni." "Ka fita dan Allah Mufid, ka fita. Ko ka dawo ne ka ƙarasa ni ka ƙarasa sauran rayuwata." Nuratu tace tana fashewa da kuka tana kama jikinta da duk rawa yake. Bai damu da kukan da take ba ya ƙara matsawa kusa da ita ta ja baya, ya dakata yace. "Ko ɗaya Baby Noor, kin san nasha faɗa miki ina son ki ko? To har yanzu ina son ki. Dan Allah ki bani dama in aureki please." "Da na aure ka gwara na mutu ba aure. Ka fice mana a gida." Tace cikin kuka jikinta mugun rawa yake take ta ji kanta ya fara juyawa. "Please na ce miki dan Allah. Kin san mai yake tafe da ni, zan amsa laifina a kotu a mini hukunci in har hakan zai saka ki aure ni." Girgiza kai tayi ta miƙe cikin sauri za ta fita ya saka hannu ya fizgota jikinshi. Nuratu abubuwan da suka wuce suka dawo mata, kamar lokacin ne ya jawota jikinshi a wancan daren. Ihu ta fasa mishi tare da kai masa cizo a dantsen hannunshi ya saketa da sauri. Waje tayi ta taɓa kofar a kulle ta fara ƙoƙarin buɗewa ta ga ya fito. Wani ihun tayi da ya ƙara rikita Munirat dake waje tana ihu a kawo mata agaji. Tana ganin ya nufota ta juya tana bugan ƙofar a buɗe mata. Mufid gurin ya iso ta bayanta ya saka hannu ya cire lock tana ganin haka ta fita da gudu suka haɗu da Munirat, ta faɗa jikinta. Bai ko kula da Munirat da take surfa masa tsinuwa ba ya sa kai ya fice. Babyn shi Noor ya zo gani kuma ya ganta ya sanar da ita zai amsa laifinshi in har za ta aure shi. Bayan fitar shi Munirat ta ɗago Nuratu dake jikinta babu numfashinta ya ɗan dakata. A mugun tsorace ta jata zuwa falo ta kwantarta tare da ɗauko ruwa ta dinga shafa mata tare da ɗiga mata a baki sai kuka take. A cikin wannan halin Mami ta dawo daga gidan Aunti Zarah da ta je dubata bata da lafiya. Ta tsorata ganin halin ƴartan tana tambayar Munirat mai ya faru ta sanar da ita abin da ta sani. Shine! Faɗin Mami ranta a ɓace tana mamakin tsaurin ido irin na Mufid, ji tayi da tana nan ya zo babu abinda zai hanata ɗaukar hukunci a hannunta. Da ihu Nuratu ta farka tana ƙiran Mami ta zo Mufid zai kashe ta, riƙo ta Mami tayi da kyar suka samu hankalinta ya dawo suka ɗura mata magani ta kwanta bacci ya kwashe ta. Mami hawaye ta dinga sharewa ta zuba mata ido, shikenan Mufid bayan cuta da ya ma ƴarta ya haukata mata yarinya. Daren Nuratu ta din ga firgita haka ta hana su bacci. *** Allah ya yi dare gari ya waye yau Allah ya kaimu wayewar garin ranar Litinin. Misalin ƙarfe goma na safiya (10:00am). Kotu ta cika makil ana jiran zuwan alkali, idan ka duba hagu ahlin gidan Alhaji Kashim Mufid ne da matarsa Hajiya Hindatu da shi kansa Mufid da Rufaida da Aunti Humaira da suka samu labari suka zo, gefensu AA ne da Faisal gaba ɗaya ido ya raina fata. Gefe ɗaya kuma Mami da ƴaƴanta gaba daya har da Muhsin da ya samu labari ya zo. Amma Jidda, Aunti Zarah duk sun zo, abin mamaki har da Alhaji Mamman Bashir da Alhaji Tukur. Nuratu na kusa da Mami kanta a ƙasa tun haɗa ido da su kayi da Dr Awwab ta watsa mishi harara bata ƙara ɗago idanuwanta ba. Yaya Al-ameen, Dr. Sadiq, Col. Ahmad da Dr Awwab na zaune a kusa da juna kowa da abinda yake saƙawa a rai. Dr Awwab suna haɗa ido da Nuratu da ta watsa mishi harara ya jefeta da murmushin da bai san yaushe ya iya shi ba yana mamakin rigimar ta. Shigowar Alkali ya saka kowa nutsuwa aka ce Court! aka miƙe, Alkali ya shigo ya zauna kafin aka zauna. Alƙali ya gyara zamanshi yace. "Rejista yau me muke da shi?" Rejista yayi gyaran murya yace. "Ya mai girma mai shari'a yau muna da case number YB/CV/UPC/20/2018 tsakanin Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru da Nuratu Mamman Bashir." "Wanda ya kawo ƙara yana kotu?" Rejista yace. "Eh ya mai girma mai shari'a." "Wanda ake ƙara yana nan?" Alƙali ya tambaya. "Eh ya mai girma mai shari'a." Faɗin rejista. "Ko zai iya fitowa gaban kotu." Miƙewa rejista yayi. "Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru ko za ku iya fitowa." Babu musu suka miƙe jikin AA rawa ya fara aka nuna musu cikin Doc suka shiga suka tsaya. Alƙali ya dubesu yana gyara zaman gilashin idonshi. "Wakilci." Faɗin alƙali. Barrister Affan ya miƙe. "Sunana Barrister Affan Zubair ni ne lauyan mai ƙara." "Ni sunana Barrister Auwal Sanusi ni ne lauyan mai ƙare wanda ake ƙara." Faɗin Barrister Auwal bayan Barrister Affan ya gabatar da kan shi ya zauna. Investigator Lawan ya mike ɗauke da content a hannunshi ya fara karantawa. "Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru a rana na ashirin ga watan Satumba sun aikata laifin fyaɗe a wani gida dake red bricks, misalin karfe takwas na dare,  sun danne yarinya mai suna Nuratu Mamman Bashir sun sadu da ita. Kun aikata wannan laifin?" Kafin Mufid ya yi magana AA da Faisal suka ce. A'a! Barrister Affan da sauri ya miƙe. "Ya mai girma mai shari'a, mun kama waɗannan yara uku sun yi wa yarinyar nan fyaɗe kamar yadda investigator ya faɗa. Mun na da shaidu da shaidar tuhumar su hakan, a bamu dama." Ganin dama ta samu abinda suke nema su Mufid kar su amsa laifi ya saka Barrister Auwal tashi da sauri. "Ya mai girma mai Shari'a ina neman alfarma a bamu dama mu kawo namu shaidun zuwa wani zama tun da masu laifi sun ce basu aikata ba. Sannan ina rokon koto da ta ba da belin masu laifi." Rubuce rubuce alƙali yayi ya ɗago yana dubansu. "Mai ƙara yana da shaidu, wanda ake ƙara ta ɓangaren su basu amsa laifinsu ba kuma basu da shaidu. Kotu ta ɗaga wannan Shari'a zuwa nan da kwana goma ana fata zuwa zama na gaba za su zo da shaidunsu. Sannan kotu ta bada belin masu laifi." Surutu ne ya kaure cikin kotun, Nuratu tana jikin Maminta tana zubar da ruwan hawaye. Ta yarda da maganar Mami cewa shari'a da mai kuɗi sai an dage. Mami da yaranta duk sun sare ganin tun farko an fara wasa da hankalinsu. Alhaji Mamman dan neman burge idon jama'a ya fara faɗa ga masu laifi an kasa ɗaukar hukunci wannan ai ƙaryace. Haushin maganganun shi ya saka Mami tashi ta fita tana riƙe da Nuratu bayan alƙali ya bada izinin fita. Haka sauran ma da suka zo dalilinsu duk suka fita. "Ya haka Barrister Affan?" Cewar Dr Sadiq dan Dr Awwab da Col. Ahmad kasa cewa komai su kayi tun a gurin har zuwa fitansu suna tsaye bakin floor na gurin. Yaya Al-ameen da shi kuma ya bi bayan su Mami bai tsaya gurinsu ba. "Kar ku damu, wasa suke so suyi da hankalinmu, zama na gaba in har suka kasa bayyana shaidunsu zamu bayyana namu, dama da wuya yau a gabatar da komai a yanke hukunci, muyi fatan su rasa shaida ko ɗaya kuma su amsa laifinsu dan hakan shi zai bamu damar gabatar da komai." "Ka tabbatar da haka." Col. Ahmad yace, Barrister Affan ya ɗaga masa kai. Dr Awwab kasa magana yayi fuskar Nuratu yake gani lokacin da take fitar da hawaye, bai ƙi ace ya sameta ya lalleshata ba ya nuna mata cewa komai zai wuce. ... "Mami na hakura, na barsu da Allah, shi zai saka mini." Nuratu tace tana kuka da tun dawowarsu ta kasa yin shuru kowa yana faɗan albarkacin bakinsa tayi shuru tana jin su. "Ai basu isa ba wallahi, akan me za ki ce kin hakura, mu bari mu ga zuwa zaman gaba, inshaAllah zamu samu nasara." Muhsin yace cike da faɗa. Kowa na jimamin abinda ya faru a koton. *** "Cheers Oga Sir." Faisal yace yana miƙa Barrister Auwal cup cike da juice ya karɓa yana kurɓa cike da farin ciki. Kuɗi sosai Alhaji Kashim ya bashi bayan dawowarsu daga kotun ganin tun yanzu an fara samun nasara. Mufid da suka hanashi cewa komai ya koma gefe ya saka musu ido, ƙarshe ya miƙe ya fita a falon Daddyn shi ya shige ɗakin shi, hayaki ya busa kafin ya zube saman gadonshi. Basu san yadda yake son jin Nuratu a zuciyarshi ba da ba zasu hana shi karɓar laifinshi ba. ..... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 24. Pharty Bb. Wattpad phartybb. ... Tun da ya dawo ya zube saman kujeran falon ya kasa samun sukuni a zuciyarshi, fuskarta kawai yake yawo a kanshi da ƙwaƙwalwarsa, zuban hawayenta jin su yake tamkar ruwan zafi. Ji yake ina ma yana da dama da ya nuna mata itama mace ce tamkar kowa, tana da gata da komai. "Awwab lafiyar ka ƙalau?" Ya tsinci muryar Ummi da ta jima a saman kanshi bai san da zuwanta ba, idanuwansa ya buɗe ya kalleta da su. "Babu komai Ummi, gajiya ce kawai." Zama tayi dan bata yarda dashi ba. "Yanzu Awwab har ya kai ka fara ɓoye min damuwa rka?" "Ummi ki yarda da ni, gajiya ce." Daga haka ya miƙe tare da ɗaukan Hanan data shige jikinshi bayan kwanciyar shi saman kujera yana jinta ya kasa mata magana a haka bacci ya ɗauketa. "Sai da safe Ummi." "Allah kai mu." Tace ta bishi da kallon mamaki. Gidansa ya nufa yana isa ya kwantarta saman gadonshi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya kwanta kusa da ƴarshi bacci ya ɗauke shi. *** "Ahmadi ya maganar mu ne?" Faɗin Abban Col. Ahmad bayan dawowarsa daga Damaturu ya zo gaishe da mahaifinsa. 'Kullum magana ɗaya dai.' Yace a ranshi a zahiri yace. "Abba ina nan ina dubawa ne, a taya mu addu'a." "Kullum muna yi Ahmadi, kai ɗin ne kullum kamar yaƙice ka ake daga mata. Ko dai sun maka wani abun ne?" "A'a Abba, ina dubawa dai." Col. Ahmad yace yana murmushi jin maganar Abban shi. .... Kafin zuwan kwana goma Mufid da su Faisal rayuwarsu suke cikin jin daɗi tamkar babu komai, yau sune club gobe zuwa party, ƴan mata kuwa sai sai abinda ya ƙaru, ban da Mufid da tun farko hakan bai dame shi ba sai dai ya rage zafi. Barrister Auwal duk inda zai shiga ya samu ya lalata shari'ar abin ya gagara. Nuratu tun ranar bata ƙara ƙoƙarin fita ba dama ba fitar take yi ba tun da suka dawo daga Maiduguri. Kullum tana ɗaki ko filin gidan bata fita, kullum cikin tunanin zaman yadda shari'ar su zata kasance. Mami na bakin ƙoƙarinta ganin ta rage shiga damuwa. *** Zuwan kwana goma ya kama ranar talata. Misalin ƙarfe biyu aka cika kotun dan jin yau kuma mai za'a gudanar. 'Court!!!' Aka ce zuwan alƙali aka miƙe ya zauna kafin kowa ya zauna. Alƙali yace. "Rejista yau me muke da shi?" Rejista yayi gyaran murya yace. "Ya mai girma mai shari'a yau muna da case number YB/CV/UPC/20/2018 tsakanin Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi Faisal Tahiru da Nuratu Mamman Bashir, Shari'a ne na fyaɗe." Dafe kai alkali yayi ya miƙe tsaye cikin ɓacin rai. "Case na fyaɗe, case na fyaɗe. Kullum case da ake gudanarwa a yanzu kenan, a kalla a rana sai munyi shari'ar case na fyaɗe sama da biyar. Wai mai yake faruwa a duniyar yanzu da aka mai da fyaɗe ruwan dare, ba'a bar ga ƙananan yara ba ba'a bar ƴan mata ba wasu har matan aure ba su bari ba. Mai yake faruwa ne? Maza mai ku ke buƙata da yake saka ku ke aikata haka? Bakwa tunanin yaran nan da halin da za su shiga, bakwa tunanin dilmeye musu farin cikinsu da rayuwarsu, kun mai da hasken su zuwa duhu, dalilin haka rayuwar yara mata dayawa ya lalace. Waye sanadi? Ku ne, kun rusa musu rayuwa kun ɓata musu tarbiyya, Future na su da komai na su, suyi aure basu da nutsuwa da kwanciyar hankali, yau gori, gobe zagi, faɗa daga nan saki ya biyo baya sai lalacewar aure. Dan Allah na roƙeku da sassauta wannan abinda kuke yi. Wace irin rayuwa ku ka ɗaukarwa kan ku? Ko kuna tunanin in kun lalata ya'yan wasu naku yayan barinsu za'a yi. Annabi yace duk abinda kayi wa ɗan wani kai ma ɗanka za'a mishi." Daga haka alƙali ya koma ya zauna yana goge hawayen idanuwanshi da kowa gurin jikinsa yayi sanyi banda wanda bai shiga kansu ba. "Rejista cigaba." Yace bayan ya saita kanshi. Investigator Lawan ya miƙe ya fara bayani. "Ya mai girma mai shari'a a zaman da ya gaba mun sanar muna da shaidu bisa laifin da Mufid Kashim Mufid da abokansa suka aikata bisa fyaɗe da su kayi wa Nuratu Mamman Bashir. We have four witnesses PW1 PW2 PW3 PW4." "Wanda ake ƙara yana nan?" Alƙali ya tambaya. "Eh, Mufid Kashim Mufid Abdullahi Abdullahi da Faisal Tahiru." Faɗin rajista. Babu musu suka miƙe suka shiga cikin Doc suka tsaya. "Investigator officer cigaba da bayanin ka." "Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru a rana na ashirin ga watan Satumba sun aikata laifin fyaɗe a wani gida dake red bricks, misalin karfe takwas na dare,  sun danne yarinya mai suna Nuratu Mamman Bashir sun sadu da ita. An kamasu anyi arresting ɗinsu an kawo su police station mun tuhume su sun aika suka ce eh. Mufid ne kuma ya amince ya yarda ya aikata ya saka hannu." Alkali ya dube su Mufid. "Mufid Kashim Mufid kai ka aikata wannan abin?" "Eh ni na aikata." Faɗin Mufid kai tsaye. Investigator yana nuna Mufid papern da Mufid ya saka hannu ya ce. "Can you recognize that?" "Yes by my handwriting." Cewar Mufid dan ya gane papern. Investigator ya miƙawa rejista takardar da Mufid ya saka hannu ya koma ya zauna. Rajista ya miƙawa alƙali ya karɓa ya karanta ya gani. "Lauyan wanda ake ƙara kana da abin cewa?" Alƙali ya tambaya. "Eh ya mai girma mai Shari'a." Barrister Auwal yace ya miƙe ya isa gurin su Mufid. "Malam Mufid Kashim Mufid. Ko zaka sanar damu daren ranar da abin nan ya faru da misalin ƙarfe biyar kana ina?" "Ina ƙofar gidansu Baby Noor." "Babu in da ka je kafin zuwanka gidansu." "Babu, hasalima na saba zuwa kofar gidan dan jiran dawowarta ko fitar ta." "Hakane ka tabbatar?" Kai Mufid ya daga ko a jikinshi domin ya riga ya rantse gaskiya zai faɗa ko dan ya wanke kanshi gurin Nuratu ta aureshi. Barrister Auwal ganin Mufid bashi da niyar bashi haɗin kai ya koma ya zauna kar yayi wani abun da zai saka ya rasa aikinshi. Bayan zaman Barrister Auwal alƙali ya ɗago yace. "Lauyan mai ƙara kana da abin faɗa?" Babu musu Barrister Affan ya miƙe ya gabatar da kanshi yana ƙarawa da. "Ya mai girma mai shari'a zamu fara gabatar da PW1 namu wato shaida na farko, shine investigator Lawan." Alƙali ya bada damar investigator Lawan ya miƙe ya shiga cikin Doc. Barrister Affan ya isa gurinshi dan masa tambayoyi. "Investigator ko zaka sanar damu abinda ka sani." Hulanshi ya cire ya gabatar da kanshi yana cewa. "Ni sunana Lawan, Misalin karfe takwas na dare muna cikin station har wasu sun fara ƙoƙarin tafiya gida saboda ruwa da ake yi ranar daga baƙin magriba zuwa karfe takwas, muka samu baƙoncin wannan bawan Allah a rikice yake cike da tashin hankali ya sanar damu an sace yarinya, duk tsammanin mu kidnapping ne har muna cewa ai war haka sun tafi da ita inda za su tafi sai ya sanar damu ya ga inda su ka kaita wato gidan da suka shiga. Anan muka ɗauki mota mu ka bi bayansu har da Ogan mu DPO Salisu, bayan isar mu, muka samu gidan a kulle. Da loud speaker mu kayi amfani muka tsoratar su suka fito aka kama su. Ni da Col. da Ɗan sanda John ne muka shiga gidan dan duba yarinyar anan muka samu sun riga sunyi raping ɗinta har ta suma. Rasa taimakon da zamu mata Col. Ahmad yasa aka ƙira motar emergency ta zo ɗaukarta. Daga nan aka wuce da ita asibiti yaran kuma aka wuce dasu station." Bayan gama bayanin investigator Lawan aka nemi Barrister Auwal yana da tambaya yace a'a. "Shaida na biyu?" Alƙali ya buƙaci a gabatar ganin Barrister Auwal bashi da tambaya. Barrister Affan ya miƙe yana cewa. "Ya mai girma mai shari'a shaidar mu na biyu shine Col. Ahmad." "Col. Ahmad ko zaka gabatar da kan ka." Cewar alƙali ya buƙaci haka. "Mai ya faru ko ince mai ka sani game da hakan?" Barrister Affan ya tambayi Col. Ahmad. Col. Ahmad da ya shiga cikin Doc idonshi akan Mufid yace. "A rana na Ashirin ga watan Satumba misalin ƙarfe shida na yamma, na shigo garin Damaturu daga Kano, ranar anyi ruwa daga misalin ƙarfe biyar zuwa takwas na dare. Na zo wuce ta titin Maiduguri dan ba Damaturu na zo ba Maiduguri zan wuce. Anan ban ankara da zuwan Nuratu ba na bugeta da mota na, na fito dan duba halin da take ciki na samu ba taji wani ciwo ba, ina cikin tambayarta lafiya na ga zuwa wannan yaron yana cewa wai motar ne bata tashi ba sai yanzu. Ban yarda da abinda ya faɗa ba ina ƙoƙarin isa wajenta waɗannan biyun suka iso gurin a mota suka ɗauketa da ƙarfi suka jefata cikin motar su. Na bisu a motana har gidan da suka kaita kafin in isa sun kulle get ɗin gidan, nayi nayi in buɗe ko su buɗe sunƙi hakan yasa na isa police station mafi kusa na sanar dasu muka dawo tare dasu, kafin mu zo sun riga sun yi abinda za suyi da ita." Shuru cikin kotun ya ɗauka kowa yana sauraran Col. Ahmad har ya gama. Barrister Affan yace. "To mungode Col. Ahmad." Daga haka Barrister Affan ya zauna. Mami da kowa daya danganci Nuratu hatta ita Nuratun jikinta yayi sanyi jin Col. Ahmad da taimakon da yayi ƙoƙarin bata. "Lauyan mai kare mai laifi kana da abin faɗa?" Cewar alƙali. Barrister Auwal ya miƙe ya isa gurin Col. Ahmad. Ba dan kar Alhaji Kashim ya ga gazawar shi ko ƙin sallamar shi ba da babu abinda zai saka shi tambaya bayan kuma Mufid ya amsa laifinshi ga kuma shaidu an kawo. "Ahmad ko ince Col. Lokacin da ka fito dan dubawa ko ka bugeta shi Mufid ɗin ya iso gurin? Ko sai da ka fito ya iso? Kuma kana gani suka ɗauketa ba kayi yunƙurin taimaka mata ba a matsayin ka na Col. Ko baka yawo da bindigar ka?" "Bana yawo da shi, ko in ce yana cikin mota ban fito da shi ba, kamar yadda na faɗa uzuri ya kawoni Maiduguri a Ibadan nake aiki. Lokacin dana fito dai dai lokacin Mufid ya iso, kafin in musu magana sauran suka iso." Col. Ahmad yace ganin kamar tambayar rainin hankali Barrister yake mishi. "Shikenan mungode." Barrister Auwal yace ya koma ya zauna, aka sallami Col. Ahmad yaje ya zauna. "Shaida na gaba." Alƙali yace yana rubuce-rubuce. "Let go to PW3 Dr Sadiq." Bayan Barrister Affan ya miƙe ya ƙira Dr Sadiq. Dr Sadiq ya miƙe ya shiga cikin Doc, Barrister Affan ya miƙawa rajista shaidan asibiti da Dr Sadiq ya basu original kafin ya koma gurin Dr Sadiq. "Dr Sadiq ka sanar damu iya gaskiyar abinda ka sani bisa yarinyar da aka kawo maka ranar ashirin ga watan Satumba misalin ƙarfe tara na dare." "Ni sunana Dr Sadiq ma'aikacin likita a asibitin General, rana na ashirin ga watan Satumba da misalin karfe tara an kawo min yarinya mai ɗauke da case na fyaɗe, a yanda na dubata nayi examining nata, akwai penetration(shigar da gaban shi cikin gabanta), akwai using of forced (ƙarfi), akwai sexual intercourse (Jima'i) wato saduwa, akwai ejaculating (inzali) wato fitar da abu daga jikin shi zuwa jikinta." Bayan sauraran bayanin Dr Sadiq Barrister Affan yayi godiya ya koma ya zauna. Barrister Auwal ya miƙe ya isa wajen Dr Sadiq. "Haka kawai aka kawo maka yarinta aka ce an mata fyaɗe sai ka hau dubata. Baka sanar mana da su waye suka kawota ba?" "Ƴan sanda ne biyu, sai Col. Ahmad wanda sai daga baya na san tare yake da su, kuma dama kowa ya sani in dai an kawo case na fyaɗe mu likitoci bama karɓa sai ƴan sanda sun shiga ciki." Ƙarya ta ƙare! Cewar Barrister Auwal a zuciyarshi ya ma Dr Sadiq godiya ya koma ya zauna aka sallami Dr Sadiq ya koma ya zauna. "Shaidarmu na gaba shine Dr Awwab PW4 ya mai girma mai Shari'a." Barrister Affan yace yana miƙewa yana murmushin cin nasara. "Ina Dr Awwab?" Faɗin alƙali. Dr Awwab ya miƙe ya shiga cikin Doc ya gabatar da kanshi. Barrister Affan ya isa kusa dashi. "Kai ne Dr da ka ci gaba da kula da Nuratu a ɓangaren masu fama da cutar ƙwaƙwalwa." "Hakane! Dr Sadiq shi ya turosu gurina da duk wani bincike na dangane da abinda ya jawo mata hakan. Ba komai bane illa firgici da ta shiga bisa abinda ya sameta ya haddasa mata fita hayyacinta. Amma kuma da taimakon magani da taimakon Allah muka samu ta dawo cikin hankalinta, sannan kuma har yanzu tana kan magani kuma zata daɗe tana amfani da shi zuwa shekaru biyar zuwa shida." "To mungode Dr Awwab." Faɗin Barrister Affan. "Lauyan wanda ake kara yana da tambaya?" Alƙali ya nemi sani. "A'a babu ya mai girma mai Shari'a." Barrister Auwal yace yana share gumi. "To mungode Dr Awwab zaka iya komawa ka zauna." Aka bashi dama ya koma ya zauna bayan ya kai kallon shi kan Nuratu da ta kwantar kanta a kafaɗar Mami rabin hijabinta ya rufe fuskarta, hawaye ne yake zuba a kumatunta take sharewa. Shuru cikin kotun ya ɗauka kowa da abinda yake sakawa a rai in ka cire Hajiya Hindatu da Alhaji Kashim da suna ji suna gani za'a hukunta ɗansu akan wata yar talakawa abinda ba'a taɓa yi ba. Nuratu kuka take ƙasa ƙasa haka sauran yayunta da zuciyarsu ya karaya tamkar yanzu abin yake faruwa. Alhaji Mamman sai baza hanci yake za'a hukunta Mufid ko ba komai duniya ba zata zageshi ba akan bai zo ba. "Za'a je hutu ayi sallah a dawo karfe biyar." Alƙali ya bada umarni dan samun lokaci na duba duk takardun shaida. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  25. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... Bala'i da masifa Alhaji Kashim yake zubawa Hajiya Hindatu tana taya shi, duk laifin ɗan su ba'a taɓa hukuntashi, amma yau gashi har ana maganar zartar da hukuncin da ya dace da shi. Cewa suke basu yarda ba za su ɗaukaka ƙara, Barrister Auwal dake zaune shima ya samu nashi rabon zagin bai kulasu ba dan shi kam yayi iya ƙoƙarin shi ya kasa. Can Nuratu sallah take tayi tare da addu'ar Allah yasa a hukunta Mufid da abokansa dai-dai da abinda suka mata, haka Mami ma da sauran da suke tare dasu. ... Ƙarfe huɗu da mintuna aka dawo kotun, bayan shigowar alƙali kowa yayi shuru ya na sauraron bayanin alƙali. "Kamar yadda shaidu suka bada shaida gamsashshiya bisa kan masu laifi, kotu mai adalci tayi amfani da ayar da Allah ya faɗa a cikin Suratu (Nur) aya ta biyu inda yake cewa 'Mazinaci da mazinaciya hukuncinsu shine bulala ɗari in har sun kasance basu da aure.' Aya na uku yace 'A kowa shaidu huɗu wanda in har basu bada shaida dai-dai ba a musu bulala tamanin.' To allahamdulillahi mun samu huɗu dai-dai kuma kowa ya bada shaida gamsashshiya da kotu tayi amfani da su wajen hukunta mai laifi. Kotu tayi amfani da wannan ayar ta biyu zata hukunta Mufid Kashim Mufid, Faisal Tahiru da Abdullahi Abdullahi bisa laifin fyaɗe da suka aikatawa Nuratu Mamman Bashir, fatan wannan hukuncin ya zama izini ga masu yin wannan laifin. Sannan ina jan hankalin mutane musamman ƴan sanda da ake sanar daku case na fyaɗe ya faru, da ku ke ɓata lokaci gurin zuwa inda abin ya faru wala a gida ko unguwa ko asibiti. Hakan yana jawo duk shaidar da ake samu ya goge, likitoci kuma kuna naku ƙoƙarin amma ku dage. Sai ku iyayen yara ko wanda abin yake faruwa a kansu. Ke budurwa ko yarinya ƙarama ko babba, an miki fyaɗe ba za ki iya sanarwa a gida ba har sai abin yayi tsamari saboda kina tsoro a gida aji kar a ɗaura miki laifi. Iyaye mata da zaran kin ga an yiwa ƴarki fyaɗe sai ki bi ki ɓoye, wani lokaci har uba baya sani sai ciki ya bayyana sannan zaku taho kotu cewa anyi wa ƴarki fyaɗe har ciki ya bayyana. Ta ya? Yaushe? Ina zamu sani bayan tun lokacin da abun ya faru baku sanar ba balle a samu shaidar eh lallai anyi fyaɗen. Dan Allah a kiyaye, bama fatan hakan yayi ta faruwa amma mu saka ido kan yaranmu musamman ƙananan yara, yanzu duniya ta lalace. Wannan shari'ar wata uku da shigar shi amma saboda tun farko an tsaya an ɗauki dukkan shaidu, mun samu cikin sauƙi mun warware shari'ar. Godiya ga dukkan wanda suka bada shaida domin abune mai wahala a yanzu a samu masu irin haka. Fatan Allah kiyaye mu ya ƙaremu da yaranmu." Ameen! Aka amsa da shi gaba ɗaya cikin kotun banda Alhaji Kashim da cewa yake ta ya za'a yiwa ɗanshi bulala har ɗari. Haka Ummu ma da har hawaye ta fara shikenan an sawa ɗan ta namiji kwaya ɗaya a gaba. Cikin wani ɗaki aka kai Mufid da su AA, alƙali da sargent ɗaya. Gefe Nuratu da take jikin Maminta hawayen idonta har sun bushe idon ya kumbura dan kuka. Alhaji Kashim da Hajiya Hindatu hanasu shiga a kayi dan yadda suke bala'i. Daga waje suna jin ƙaran bulalan da ake zubawa Mufid da abokansa da ana gamawa suka sume a gurin. AA har fitsari ya sake dan azaba ana gamawa aka cicciɓo Mufid aka jefa motar Alhaji Kashim da su Faisal. Kai tsaye asibiti ya wuce dasu dan yadda fatar jikinsu ya tashi, ga Mufid da babu numfashin kirki a jikinshi. *** Gaba ɗaya ahlin suka dunguma zuwa gidan su Nuratu hatta Dr Awwab da bai taɓa zuwa ba. Nuratu rasa kalmar da za ta musu godiya tayi a bakinta sai murmushi take zubawa da kumburarren idanunta. Idanun Dr Awwab saman fuskarta dimple ɗinta shi ya fi komai masa kyau yadda yake lotsawa dukka biyu. Yayi kewarta yayi kewar idanuwanta da yadda take watsa masa harara da su. Rigimar ta burgeshi yake. Mami ta musu godiya haka sauran yayunta suka shiga kitchen suka haɗa abincin dare har da su. Bayan sun gama suka bar musu falon. Col. Ahmad, Dr Awwab da Yaya Al-ameen da Muhsin da ya shige cikin su dan shegen tsawon kafa ne da shi, su kaɗai suka rage a falon, sunci abinci ba laifi ban da Dr Awwab da kaɗan ya ci ya bari. Matan suka shige ɗaki Mami da Amma Jidda da Aunti Zarah da Rahma. Can ɗakin Nuratu ce da Hasiya da Rukayya da Walida sai Ameera da sai hura hanci take. Bayan mazan sun gama suka miƙe dan Col. Ahmad da Dr Awwab suna son wucewa Maiduguri komai dare. Mami da sauran suka fito kowa bakinshi in ya buɗe godiya yake musu musamman Col. Ahmad da ya jajirce akan case ɗin har aka hukunta masu laifi. "Nagode Col. na gode sosai da taimako. Allah ne kaɗai zai biya ka." "Kar ki damu Nuratu, tamkar ƙanwata haka na ɗauke ki. Sai bayan kwana biyu, ga numbern wayana za muna waya, in na samu lokaci za ina zuwa duba ki." Kan Nuratu ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta karɓi card ɗin da ya bata kafin ya shiga motar shi ya tafi, ta koma cikin gida. Dr Awwab da tun farkon tsayuwarsu ya ji ya kasa juran ganin su haka ya bar gurin da motarshi ko sallama bai samu ya mata ba. Nuratu tana shiga ta samu Muhsin da Yaya Al-ameen suna zaune, Rahma da su Hasiya da Walida suna tare dasu, bata zauna cikinsu ba ta wuce ɗakinta in da Ameera take. Bata mata magana ba dan ta lura yarinyar bata da daɗi, alwala tayi ta fito jin ana kiran sallar magriba ta gabatar da sallah. Sai wajen ƙarfe taran dare kafin kowa ya wuce gidanshi aka bar Nuratu daga ita sai Mami da Munirat. *** Kwanan Mufid ɗaya kafin ya farka, jikinshi duk shatin duka da ya warke sai tabon da bai gama gushewa ba, yana samun kulawa sosai, a rana na uku aka sallameshi ya koma gida. Hajiya Batul da yaranta sun shigo sun mishi ya jiki suka koma dan babu jituwa tsakanin matan sai yaransu. Burin Mufid ya cika sai burin auren Nuratu, yana taso da maganar Alhaji Mamman da ya ji ya nema masa visa zuwa ƙasar Las Vegas wajen abokinsa da yake can, yace ya zauna ya kula da kanshi maganar auren Nuratu ba yanzu ba sai zuwa wani lokaci kafin nan kowa ya mance abinda ya faru. Da wannan ƙaryar ya samu Mufid ya amince ya tafi ba dan ya so ba, haka Hajiya Hindatu ma ta amince. Rufaida ta fi kowa murna amma dai ta san silar ƙara lalacewarsa ne zuwa ƙasar waje ba wai dan neman sulhu ba. *** Tun da wannan rana da lokaci Nuratu take ganin mutuncin mutanen huɗu nan, Col. Ahmad, Dr Sadiq da Dr Awwab sai Yaya Muhammad Al-ameen da shima ganin mutunce take masa tamkar sauran. Su kaɗai take ganin mutuncinsu take sakar musu fuska. Maganar aure da soyayya ta cireshi a ranta ba yanzu ba ta ajiye a gefe. Duk da har lokacin in ta tuna abinda ya samu rayuwarta sai ta zubar da hawaye. Har lokacin tana kan shan magani da yake hanata yawan ciwon kai. Sai shiga cunkuso da ta daina yi sosai. Dr Awwab yana zuwa duk ƙarshen wata shi ya ɗauke mata wahalar siyan magani, tare da Hanan yake zuwa da tun lokacin ta maƙalewa Nuratu har zuwa yanzu da tayi wayo. Dr Awwab ya riga ya amince ya yarda son Nuratu yake ɗari bisa ɗari. Col. Ahmad yana ƙiranta suna gaisawa da sabuwar wayar da Mami ta saya mata, shi kam har yanzu ya ɓoye mata cewa sonta yake ya rasa ta inda zai sanar da ita domin shi ya fara jefa zuciyarta ta bashi matsayin Yaya ba masoyi ba, gashi yanzu abin yana damunshi. Bayan wasu watanni yana samun zuwa dubata, lokacin da iyayenshi suka sake mishi maganar aure yace ya samu mata, anan ya sanar da su ga wacce yake so. Nan Umma ta daka tsalle tace ba zai yiwu ba ya aure sauran wasu ba. Numbern Nuratu ta bi ta nema ta ƙirata ta mata tas. Ranar Nuratu kukan da tayi har wani numfashinta sama sama yake da kyar Mami ta lallasheta tayi shuru bacci ya ɗauketa daga baya ta sanar da ita ga abinda ya faru. Nan Mami tace tayi hakuri dama dole ta fuskanci irin haka amma kar ta faɗawa Col. Ahmad haka suka bar abin a ransu. Haka Yaya Al-ameen ma da ya taso da maganar aure Nuratu ta dakatar da shi bai ji zafi ba ya bata lokaci. Aunti Rahma ta sake haihuwar ƴa mace sai Khair da yanzu take goyo. Aunti Hasiya ta haihu namiji sai wanda ta haifa yanzu. Haka Rukayya ma ta haifi ƴan biyu mace dana miji yanzu shekarunsu uku bata ƙara haihuwa ba cewarta hutu take. Yanzu maganar auren Walida ake. Alhaji Mamman tun lokacin ya ƙara watsar da lamuran Nuratu da Hajiya Sadiya. Rufaida har gida ta zo ta bawa Nuratu hakuri tace babu komai domin hakan Allah ya rubuta yana shafin ƙaddarar ta, su kaci gaba da mutuncinsu sama sama dan Rufaida baya baya take ja da ita. Bayan an cinye shekara ɗaya Nuratu ta koma makaranta bisa matsawar yayunta da Mami, hakan yasa ta koma taci gaba da karatunta har Allah ya sa yanzu tana shekarar ƙarshe. Kasuwanci Mami ya dawo arziki Allahamdulillahi ya zauna mata ta ƙara gyara gidan, ta sayi mota, Muhsin ya koya mata ita da Nuratu da karambani ya ke sata ɗauka bata kware ba. **** Ci-gaba. "Nuratu!" Mami da ta tsaya a kanta tsawon lokaci bata sani ba sai da ƙira sunanta kafin ta buɗe idanunta da hawayen yana zuba bayan fuskarta da ta ɓata da ruwan hawaye. Zama Mami tayi kusa da Nuratu, Nuratu ta gyara kwanciyar ta ta ɗaura kanta saman cinyarta. "Mami na kasa cire abin nan a raina. Ban san ya zanyi ba. Bana kwana na tashi bai faɗo mini ba." "Addu'a za kiyi duk lokacin da hakan ya bijiro miki. Ki daina tuna baya domin bayanki ba alheri bane. Mu fuskanci gabanmu." Shuru kawai Nuratu tayi Mami tana ta mata nasiha kamar kullum har ta daina hawaye. Ta san da wuya ta cire abinda ya faru a ranta. Munirat ce ta musu girkin dare dan Nuratu ciwon kai ne ya zuba mata. Bayan taci ta shige ɗaki anan ta tarar ƙiran Dr Awwab. "Noor ina ki ka shiga ne ina ta ƙira, har ina tunanin dawowa gobe." Murmushi tayi tana mamakin Dr Awwab da duba ɗaya zaka mishi kace bashi da magana, ko da yake hakan ne dan in har suna tare baya wuce magana biyu zuwa uku yake yi mai tsayi shikenan kuma yayi shuru. Akwai jan aji da miskilanci a tattare dashi, sai ka zauna da shi yake iya kauda su gefe ya maka magana. "Dr wayar yana ɗaki ina waje ne. Kun isa lafiya? Ina Hanan?" "Lafiya ƙalau. Hanan tana wajen su Hussaina. Na manta ban baki sakon Ummi ba ɗazu tana gaishe ki." "Ina amsawa. Allah dai ya dawo dani Maiduguri in zo gaisheta." "Za ki zo zuwa na musamman Noor. Ko ba haka ba?" "Bance ba?" Tace tana murmushi ganin yana neman kawo mata wani hirar ta canza salon hiran. "Zanyi sallah ban yi isha'i ba." "Shikenan a samu a addu'a sosai Noor ina buƙatar hakan." "InshaAllah kullum kuna cikin addu'ata." Bayan sunyi sallama ta gabatar da sallar isha'i ta kwanta, bacci ya gagari idanuwanta, mutanen nan uku suna shirin sakata cikin damuwa. .... Kiɗa ne yake tashi a motar ya shigo gidan, kan shi yasha aski ƙasa an aske, sama an bar gashin da yake kwance irin na asalin fulani. Kyau har kyau babu tarbiyya da kyan hali. Wani shegen wandone jikinshi duk a yayyage, rigar kuwa farace tas sai tarin sarƙoki a wuyanshi har da ɗan kunne ɗaya. Busar iskar sigarin shi yake yana waya da Faisal akan maganar zuwa birthday party na shi da za'a gudanar anjima yake sanar dashi yana tafe zuwa dare. Mufid Kashim da shekara ɗaya kenan da dawowarshi daga ƙasar Les Vegas zuwa Nigeria. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  26. Pharty Bb. Wattpad phartybb. ... Shekara ɗaya kenan da dawowar Mufid Nijeriya ya kasa zaman ƙasar waje, duk da kuɗi da Daddynshi yake tura mishi kuma yana jin daɗin zaman gidan abokin babanshi da babu mai shiga harkar wani kowa rayuwarsa yake a gidan. Kasa zama yayi a ƙasar dan har lokacin son Nuratu ya kasa barin zuciyarshi, wani mahaukacin so yake ji a ranshi na Nuratu, siffanta da zumarta ya kasa barin ƙwaƙwalwarsa. Mafarkin shi take zuwa da hakan yake ƙara kusanta zuciyarsa da sonta, sai ya farka yake ganin mafarki yake. Haka yasa ya tattaro ya dawo gida. Alhaji Kashim yayi ta faɗa amma Hajiya Hindatu ta nuna tana son zaman ɗanta kusa da ita ya sa Alhaji Kashim hakura ya barshi. Tsakanin shi da AA da Faisal sai dai waya dan basu ƙara haɗuwa ba tsawon shekarun sai dawowar shi suka ci-gaba daga inda suka tsaya. AA mahaifinshi ya kore shi a gidan dan ya gaji da iskancin shi, ya koma gidansu Faisal da zama da shima mahaifinshi ya cire hannunshi a komai na rayuwarshi ya zuba masa idanu. Yau ake birthdayn Faisal tun jiya suke shirye-shirye, babban hall suka kama inda za su gudanar, sun gayyaci abokansu manya manya har daga wata ƙasa banda ƴan matansu da suma suka zo. Karfe takwas aka fara gudanarwa gurin cike yake da yara masu ji da kuɗi da iskanci da duniyanci, kiɗa ke tashi wasu na busar sigari, wasu shisha wasu suna kora ruwan wine wasu kuma rawa suke yi kamar ba gobe. Mufid da busar sigari ya zame masa jinin jikin, yana zaune yana ta busar abin shi yana buɗe idanuwansa lumshashshu yana rufe su yana jin daɗin kiɗan dake tashi. Ƴan matan gurin rabi da kwata duk hankulan su na gurinshi da ya tafi da imaninsu domin yayi kyau sosai, dan Mufid akwai kyau ga haske, sai ya zama tamkar gayun Amurka da suke jin daɗin duniyarsu. Idonshi ne ya kai kan wata black yarinya da take sanye da bakaken kaya riga da wando ta juya baya, rabin fuskarta yake kallo tana magana da yar gefenta tana murmushi, dimple ɗin ta dake na gefe ɗaya ya lotsa. Zuciyarshi ta kasa hanashi da yarda cewa ba ita bace domin idanuwansa sun nuna masa tabbas ita ce. Bai yarda ba ita bace sai da ya kai kanshi gurinsu ta juyo ya ga ƙarya idanuwansa suke masa. Tsaki yaja ya bar gurin, cikin hall ɗin gaba ɗaya ya bari ya fita waje, motarshi ya shiga ya cigaba da shan sigarin shi. Sai da ya shanye tas kafin yana ƙoƙarin barin gurin AA ya fito. "Ina zuwa?" Fadin AA. "Gida." Mufid ya faɗa yana ƙoƙarin kunna motarshi. "Na ga dai ba'a tashi ba." "To nace maka gida zan je." Mufid yace ya kunna motarshi ya ja da ƙarfi yana barin gurin. Kai tsaye gida ya nufa ya samu kowa ya kwanta hakan yasa ya wuce ɗakinshi bai iya ko wanka ba ya zube saman gadonshi. *** MAIDUGURI. "Ahmadi wai ba za ka yiwa kanka faɗa ba, shekarunka talatin da bakwai amma har yanzu ka kasa ajiye mata. Abin nan fa yana damuwa, kawai magana ne bana yi." "Kai ma dai ka mishi magana, nayi faɗan nayi har na gaji. Kamar wanda aka asirce shi." "Babu batun asiri, ra'ayi ne ina ga har yanzu bashi dashi ko Ahmadi? Ko dai budurwarka ta yaudare ka?" Baban Ahmad da Umma suke mishi faɗa akan rashin aurenshi, shi kam banda murmushi babu abinda yake yi sai ma dariya da yayi jin abin da babanshi yace ya girgiza kai. "Abba har yanzu ita ɗince a raina." "Wacece kenan?" Faɗin Baban Ahmad. "Nuratu, yarinyar nan dai." "Ka isa? Ya mu kayi da kai." Faɗin Ummu tana watsa mishi harara fahimtar inda maganarshi ta dosa. Kanshi ya ƙara sunkuyarwa ƙasa zai yi magana Abba ya tare shi. "Gobe da safe za mu yi maganar tashi ka je." Babu musu Col. Ahmad ya miƙe ya fita. Abba ya juya yana kallon Umma. "Ke kuma ai ba haka ake yi ba a hankali zaki bishi." "Wani irin a hankali Alhaji. Kana dai ji abinda yake shirin jajiɓo mana." "To ya za mu yi a hankali za mu bi mu hanashi auren. Dan gaskiya nima har cikin raina bana son abin nan." Faɗin baban Ahmad, dan tun shekarun baya Umma ta sanar da shi komai lokacin da suka buƙaci yayi aure ya nuna musu ga wacce yake so. Umma kuwa mamaki take da har yanzu wannan shegiyar yarinya ta kasa rabuwa da ɗanta. Washegarin Col. Ahmad ya samu zama da Abban shi akan maganar Nuratu. "Wanene mahaifinta?" Shine tambaya na farko da Abba ya watsa mishi da ya rasa amsa dan basu bata zancen da Nuratu ba, ya dai san yayunta banda haka bai san komai a kanta ba. "Kai nake sauraro Ahmadi. Wanene mahaifinta?" Dakyar ya iya buɗe baki yace. "Ban sani ba Abba wallahi. Bamu taɓa hiran ba, amma ina tsammani ya rasu ko basa tare da mahaifiyarta." "To ka binciko hakan da kan ka, in ka samu ka sanar da ni. Amma a yadda na fahimce ka yarinyar nan gaban mahaifiyarta take. Ƴar mace ce." "Hakane Abba su biyu suke rayuwa asalin su ƴan Nijar ne amma?" Cike da mamaki Abba yake dubanshi kafin yace. "Ka binciko sai musan abin yi." To Ahmad ya amsa dashi yana yiwa Abban shi godiya ya fita. Hutun sati ya samu daga Ibadan yau kwanan shi biyu da zuwa. Abba da kallo ya bishi. Wannan aure da yake so ba zai taɓa yarda da shi ba. Yarinya ƴar mace tarbiyyar mace ina ta ga nutsuwa da kamun kai, dole rayuwarta ya samu tangarɗa mana balle kuma dangi suna wata ƙasar su suna zaune a wata ƙasar. Ko haka aka sanar da mutum sai ya kafa ayar tambaya. **** DAMATURU. "Daddy aure nake so." Mufid yace kai tsaye yayinda yake zaune saman table suna breakfast su ukun da Ummu da Alhaji Kashim. Da mamakin jin furucin shi suka kalle shi ya sake maimaitawa cewa aure yake so. "Zan maka babana. Kana da wacce kake so?" Alhaji Kashim yace yana duban Mufid. "Ina da ita mana kai ma ka sani Baby Noor ce." "Wato har yanzu baka rabu da sonta ba Mufid. Anya yarinyar nan bata tsafeka ba." Hajiya Hindatu tace cikin ɓacin rai. Murmushi Mufid yayi da yake fito da kyakkyawar fuskarshi. "Tsafi kuma Ummu. Ni dai Daddy ka nema min aurenta. In kuma ba haka ba?" Da sauri Alhaji Kashim yace. "Dan Allah kar ka kuma jawo wani abun Mufid, zan nema maka aurenta." "You're the best Daddy thank you." Mufid yace yana miƙewa ya bar musu gurin. "Yanzu kai Daddym Humaira da gaske ka ke. Kar ka saka mishi abu a rai ya zo bai yu ba." Murmushin ƙyeta yayi. "Hajiya Hindatu ko ince Ummun Humaira, in baki sani ba mun samu hanyar rama abinda suka saka aka yiwa ɗan mu. Alhaji Mamman sai ya gane ƙarfin kuɗi da mulki yanzu dashi ake takama. Auren yarinyar nan tamkar anyi an gama Mufid ya sameta." "In kuma ta shigo sai ta gane shayi ruwane, sai ta zubar da hawayenta, sai na tarwatsa sauran farin cikinta da ya rage." Hajiya Hindatu tace suka kwashe da dariyar mugunta dukkansu. *** MAIDUGURI. Kwance yake saman gadonshi babu inda yake zuwa a garin, datar wayarshi kunne yana duba sakwanni ya ga notification cewa Nuratu tana online. Kan sunanta ya shiga ya tura mata saƙo. *"Mai ki ke yi da safe haka a online. Kin bar Mami tana aiki."* Nuratu da ta kulle kanta tun safe a ɗaki dan sanyi da ake babu makaranta ya ƙare ta shige cikin bargo, bacci tayi har ƙarfe goma kafin ta farka bata iya fita ba ta jawo wayarta ta kunna tare da duba sakwannin safiya da ya wuceta bata online ta samu saƙon Col. Ahmad. Murmushi tayi ta tura mishi. *"Sanyi ake sosai, ni kuma ina tsoron sanyi."* "" Amsar da ta bashi ya sashi yin murmushi ya mai da mata da amsa. *"Kina tsoron sanyi? In kin yi aure fa? Wa zai miki?"* Karanta saƙon tayi taƙi bashi amsa ƙarshe ma ta sauƙa a online ta ajiye wayar, kafin ta matsa ya ɗauki ƙara ta ga dai shine. Ɗauka tayi ba dan taso ba ta mishi sallama ya amsa yana haɗa mata da tambaya. "Muna cikin hiranmu kika sauƙa kuma?" Rasa amsar da zata bashi tayi tai shuru yaci gaba da cewa. "Ki shirya karɓa na gobe ina hanya. Fatan ba zan takura miki ba?" Kamar ta kurma ihu ta girgiza kai ƙasa ƙasa tace. "A'a sai ka zo Allah kawo ka lafiya." "Ameen Nuratu ki gaishe da Mami." "Za ta ji." Tace ta kashe wayar ta ajiye ta shiga bathroom dan fitsari da ya matseta, brush tayi tai fitsarinta ta fito cewarta sanyi ake sai azahar za tayi wanka. A falon ta samu Mami ta farka, Munirat har ta ɗaura abincin rana dan sha ɗaya ta gota. Bayan ta gaishe da Mami ta ci abincinta da har yayi sanyi. Anan ta sanar da Mami cewa Ahmad yana zuwa gobe. "Wannan yaran dai basa gajiya da zirga zirga. Ke kuma kin zuba musu ido ba za kiyi abu ɗaya ba kowa ya huta." "Ni kuma Mami mai zan musu. Duk wanda ya gaji ya hakura kawai." Nuratu tace tana tauna abincin bakinta. "Au haka kika ce. Shikenan ni zan zaɓa miki wanda ya dace dake." "Waye? Yaya Al-ameen?" Nuratu ta tambaya. Mami ta girgiza kai, Nuratu tace. "Dr Awwab?" Nan ma ta girgiza kai. "Limamin unguwar nan zan haɗa ki dashi." Mami tace tana dariya ganin yanayin fuskar Nuratu ya canza amma jin maganar Mami ta faɗa ya sata fashewa da dariya har tana neman faɗuwa. "Ki dai yiwa kan ki faɗa. Kiyi ta addu'a Allah cire miki mafi alheri a cikin su." Mami ta faɗa haka bayan ta tsagaita dariyarta ta miƙe ta bar mata gurin. Kullum dai magana ɗaya, aure, aure, ba za'a barta ta ji da abinda yake damunta ba, ko gaba basa dubawa abin da zai biyo baya bayan auren. Bayan ta gama cin abincin ta kwanta sai azahar tayi wanka ta fito. Ranar haka ta wuni a gida babu inda ta je. Da dare ita ta musu abincin dare dan hutar da Munirat da ake shirin aurenta a ƙauyen Buni Gari dan har an bada ita ga ɗan uwansu da yake aiki a birni, har gidan Mami yake zuwa hira wajenta. Kuma ba laifi Mami ta yaba da hankalin shi. *** MAIDUGURI. "Yaya Awwab!" Hussaina tace da ɗan saurinta dan ganin zai shige mota. Jin ƙanwarshi na ƙiranshi ya sashi dakatawa yana dubanta. "Yaya Awwab da ma nace kuɗin da kace zaka bani ne na siyayyar Hanan." "Oh na mance. Zan miki transfer." To tace ya wuce ta koma cikin gida, wajen sha biyu ta samu saƙon kuɗin daya turo mata na siyayyar Hanan da yana ji yana gani ta fara ƙin zama gurinshi sai gidansu ba kamar da ba. Tare da Hanan su ka je da Hassana su ka mata siyayya. Da dare da ya dawo suke nuna mishi yace babu komai. Ummi dake gefenshi tana kallonsu ta saka baki. "Tun da dai taƙi zama sai kayi ƙoƙari ka ajiye mata in kana son ta koma." Murmushi Dr Awwab yayi. "Ummi har yanzu taƙi bani damar gabatar da kai na a gida." "Mata kenan, hakuri za kayi ka bita da sannu za ta amince." Ummi tace kasancewar ya riga ya sanar da ita ga wacce yake so duk da ya ɓoye mata sirrin Nuratu da yake ganin bai dace kowa ya sani ba. Ummi tayi na'am da buƙatar shi fatanta Nuratu ta amince ta auri ɗanta ta maye gurbin Nusaiba da ya rasa. Murmushi kawai Dr Awwab yayi ya mata sallama ya suce gidanshi, da babu kowa sai mai mishi gadi, ya sallami duk masu kula da Hanan dan taƙi zama. *** DAMATURU. Cikin takama ya shigo Companyn da yayi bincike ya samu nan ne wajen aikinshi da ya san ta wannan hanyar kaɗai zai amince da buƙatarshi. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  27. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Tunda ya samo bayanin sa yana sauraran shi har ya gama kafin ya gyara zaman gilashin idonshi. "Kar ka damu Alhaji Kashim wannan abun tamkar anyi an gama domin in dai akan kuɗi ne Alhaji Mamman zai iya komai ballantana abin da ya shafi aikin shi." "Kana gana babu wani matsala da zai biyo baya." Alhaji Kashim ya tambayi Oga Dauda jin yayi saurin amincewa da buƙatarshi. "Kana kokonto ne? Ni na san waye Alhaji Mamman. Tashi muje idanuwanka su baka shaidar haka." Daga haka suka fita dukkansu zuwa ofishin Alhaji Mamman Bashir, yana tsaka da aiki ya samu baƙoncin su. Kallon kallo su ka yi tsakanin Alhaji Kashim da Alhaji Mamman. "Mai kuma ya kawo ka ofishi na?" "Laifi ne dan mutum ya zo wa da ɗan uwanshi alheri?" Alhaji Kashim yace yana zama cikin ɗaya daga kujerun dake ofishin bayan zaman Oga Dauda. Alhaji Mamman kallon Oga Dauda yayi yana neman ƙarin bayani dangane da maganar Alhaji Kashim, fahimtar haka ya saka Oga Dauda gyara babban riganshi. "Alheri Alhaji Kashim ke tafe dashi Alhaji Mamman. Buƙatarshi ɗaya ne zaka biya masa ka samu alheri mai yawa ban da ƙarin girma da zai biyo baya ta ɓangare na." Ya faɗa yana nuna kanshi. "Mai ka ke buƙata?" Tambayar Alhaji Mamman ga Alhaji Kashim yana binshi da kallo. Kuɗi da mulki ya zauna a jikin Alhaji Kashim sosai, duk tinkahon arzikin shi ashe akwai wanda ya fishi. Shaddar jikinshi ma kaɗai abin kallo ne. "Auren ƴar ka nake nemawa ɗa na Mufid." "Wace ƴar? Ba zai yiwu ba." Alhaji Mamman ya tambaya da sauri tsammanin sa duk Ameera ce ko Walida. "Mai ka ke sauri haka? Wannan yarinyar auren ɗa na shine rufin asirinta ko baka ganin hakan?" Alhaji Kashim ya ce ga Alhaji Mamman da yake binshi da wani kallo. "Kana nufin ƴar wajen Sadiya?" Ya tambaye shi dan neman ƙarin bayani. "Wacce dai aka yi shari'a da ita shekaru huɗu da suka wuce. Nuratu take kowa?" Shuru Alhaji Mamman yayi a ranshi yana jin zafin Nuratu da duk ƙoƙarin shi na ganin ya rabata da rayuwarshi abin ya gagara. Ance masa itace silar ƙarayar arzikin shi gashi yanzu kuma dalilinta arziki na tunkaro shi da in yayi wasa, zai rasa baya ya rasa gaba. "Tunanin mai ka ke Alhaji Mamman? Babu batun takura, kayi tunani a kai." Faɗin Alhaji Kashim yana miƙewa tsaye tare da saka hannu cikin aljihunsa ya ciro tailan kuɗi da tun a gida ya saka hannu na miliyan biyar. Ajiye masa saman teburin shi yayi. "Ga wannan na bani lokacin ka da kayi mu kayi magana, ina jiran amsar ka, duk shawaran da ka yanke ka sanar da Ogan Dauda sai na jika." Daga haka suka fita Alhaji Mamman ya bisu da kallo kafin ya juyo da hankalin shi kan tailan dake ajiye ya ɗauka ya gani. 'Milayan biyar.' Ya faɗa da sauri yana ajiyewa sai kuma ya miƙe tsaye kafin ya ƙara komawa ya zauna. Ya ma rasa wani irin tunani zai yi bisa wannan lamari da yake tunkaro sa na wannan yarinyar da bai taɓa jin sonta a matsayinta na ƴarshi ba. *** Ƙarfe biyu ya shigo cikin Damaturu bayan ya gabatar da sallar azahar ya ƙarasa gidan, ya gaishe da Mami har cikin falon kafin ya fito waje in da Nuratu ta ajiye musu fararen kujeru a ƙarƙashin bishiyar dake filin gidan. Bayan gaisuwa tsakanin su shuru ya biyo baya dan nauyin Col. Ahmad take ji sosai. Matsayin babban Yaya ta bashi da take ganinshi tamkar uba dan abinda ya mata a rayuwa ko jinin jikinta albarka. Maganarshi shi ya dawo da ita hankalinshi lokacin da ta ji ya ƙira sunanta. "Nuratu!" Idanuwanta ta ɗago ta kalleshi da su ta juyar kanta tana amsawa bugun zuciyarta na ƙaruwa. "Sai ki ka ji ina son ganin ki." "Eh." Ta bashi amsa kanta ƙasa. "Ya kamata Nuratu in san wasu abubuwa a kan ki, kar kimin fassarar wani abu, hakan na gani ya kamata ko dan gaba, duba da yadda alaƙar mu ya daɗe kuma ina neman ya ƙara ƙarfin da yafi na baya. What i means ina son gabatar da kai na wajen dangin Baba ko Mami a san da zamana?" Maganganun shi na ƙarshe ya sata ɗago idanuwanta ta kalleshi dashi nashi idanun a kanta. "Bangane ba?" Ta tambaye shi dan neman ƙarin bayani da sauri. Murmushi yayi yace. "Kin fahimce ni kawai dai kina son basar da maganar ne kuma na lura da hakan tun ba yau ba. So nake ki sanar da ni wanene babanmu ina son zuwa gaisuwa wajen shi ko dangin shi." Fara'ar fuskarta ne ya ɗauke tana kawar da idonta. Tun da take bata taɓa ji ko ganin labari irin nata dana mahaifinta ba, ba tasan mai ta mishi ba, ba tasan mai ta tsare mishi ba a rayuwa ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata. Da mahaifinta a raye amma ta zamto tamkar wata marainiya marar gata, wani marayan ma tasan ya fita jin daɗi dan tasan ko ya ya dai yaji daɗin mahaifi kafin ya rasashi. Ita fa? Sai dai kallo daga nesa. Col. Ahmad da ya hango tsantsan damuwa a fuskar Nuratu sai yaji jikinshi yayi sanyi. A ranshi yaji cewa akwai wani abu tsakanin uba da ƴar. Gyaran murya yayi da ya sata juyowa ta dubeshi. "Maganganu na sun ɓata miki rai ko?" Girgiza kai tayi tana ƙirƙiro murmushi ta ɗaura saman fuskarta. "Ko ɗaya Col. Mahaifina Alhaji Mamman Bashir sunan shi, nima ban gama sanin shi ba saboda sun jima da rabuwa da Mami na." Iya abinda ta sani ta sanar dashi domin Col. Ahmad ya cancanci ya san komai game da ita har da wanda ita kanta bata sani ba. Mamaki da al'ajabi su suka cika zuciyar Col. Ahmad kawai ya zubawa Nuratu ido bayan gama sauraron bayaninta tana share hawayen da suka zubo mata. Rayuwarta na baya ne ya dinga dawo mata da ya ƙara saka zuciyarta karaya. Ba dan Col. Ahmad ba da shikenan Mufid yaci bulus a rayuwar ta babu mai kwatar mata haƙƙinta. Numfashi ya sauƙe har lokacin yana dubanta. "Shikenan dai na kukan. Muna tare da ke Allah yana tare dake Nuratu, shine gatan ki." "Haka ne." Tace tana share hawayenta da yatsun hannunta. Daga nan hiran ya tsaya kowa da abinda yake saƙawa a zuciyar shi kafin Col. Ahmad ya miƙe. "Zan wuce kar yamma yayi kin san hanyar garin mu." "Haka ne Allah kiyaye hanya Nagode sosai ka gaishe da mutanen gida." Nuratu tace bayan ta miƙe ta ƙira Mami su kayi sallama ya wuce. Tafiya kawai yake labarin Nuratu na mishi yawo a zuciyarshi tamkar yanzu take bashi. Ta yi ƙanƙanta da fuskantar waɗannan jarabawar rayuwa, sai dai Allah ne ya ɗaura mata babu yadda za tayi sai karɓa hannu bibbiyu dan cinye jarabawar. *** "Aikin ka yana kyau Daddyn Humaira." "Kina wasa dani ne? Sai Alhaji Mamman da yarshi sun fuskanci hukunci daidai da yadda suka aikata wa Mufid har ma wanda yafi nashi." Faɗin Alhaji Kashim bayan ya sanar da Mufid da Hajiya Hindatu yayi magana da Alhaji Mamman amincewar shi kawai yake jira kuma ya san nan ba da jimawa ba zai amince. Bayan sauraronsu Mufid ya miƙe ya wuce ɗakin shi cike da farin cikin ya kusa mallakar Baby Noor. Wayarshi ya jawo ya lalibo lambar wayarta da yasha wahala wajen samu tun dawowar shi ƙasar. Kullum sai ya tura mata saƙo ta WhatsApp da baya ganin ta gani balle amsa da baya samu. Bai taɓa ƙiranta ba dan gudun kar ta ƙi ɗauka sai yanzu da ya ƙira har ya gama ringing bata ɗauka ba ya hakura ya san zuwa nan da wani lokaci kaɗan zai mallaketa. *** Tun da Alhaji Mamman ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, Amma Jidda na tambayar shi ko baya jin daɗi ne ya tabbatar mata da lafiyarshi ƙalau. Mai neman shawara yake nema zuciyar shi ta raya mishi abokinsa Alhaji Tukur. Girgiza kai yayi domin Alhaji Tukur yayi nisa baya ƙasar da iyalansa kusan shekaru uku, kuma baya jin zai goyi bayan sa akan hukuncin da ya yanke. Hukuncin da zuciyarsa ya yanke mishi dashi ya kwana ya tashi washegari ya wuce aiki. .... Tun jiya Mami take lura da yanayinta gaba ɗaya babu walwala a tattare da ita tun tafiyar Col. Ahmad jiya, dan daren ko abincin dare ba taci ba ta kwanta. Yanzu kuma tun safe ko wanka ba ta yi bayan ta taɓa abinci kaɗan ta kwanta saman doguwar kujera. Shirin da ake maimaitawa da safiya take gani wanda ya wuceta jiya da yamma dan bata cikin yanayin kalla ba ta samu gani ba. Kallon take amma hankalinta yana wani waje daban, idonta saman talabijin. "Aunti Nuratu wayar ki yana ƙara." Ta ji muryar Munirat saman kanta kafin ta kai dubanta saman fuskar wayarta dake saman center table yana ruri ta ɗauka. 'Sis Walida' Ta gani ta ɗauka da sauri tana miƙewa zaune. "Fatan kin shirya ba ki manta ba?" Walida ta watsa mata tambaya bayan amsa sallamar Nuratu. "Ina kenan? Au sorry Sis ki zo, bari in shirya." Nuratu ta faɗa duk lokaci ɗaya tunawa da sunyi magana da Walida yau za su je raba ankon aurenta. "Ai na fito ina hanya. Ki yi sauri." Kit Walida ta kashe wayar Nuratu ta miƙe da sauri ta wuce ɗakin Mami ta sanar da ita ta amince kafin ta wuce ɗakinta ta yi wanka. Tana cikin shiri Walida ta iso bayan ta gaishe da Mami ta wuce ɗakin Nuratu ta samu ta shirya cikin doguwar riga abaya ta yane kanta da maroom gyale. Yayi mutuƙar amsar baƙin fatar ta. "Kinyi kyau Sis. Da ma Yaya Al-ameen yana nan ya bada kyautar wannan kwalliyar." Rai Nuratu ta ɓata tana ɗaukar jakanta ta fita tana cewa. "Ki fito mu tafi in har za ki." Girgiza kai Walida tayi ta fita suka ma Mami sallama suka fita. A cikin motar da ango ya turo suke tafe Nuratu ta jawo wayarta anan ta ga missed call din Dr Awwab guda ɗaya. Sanyin halin Dr Awwab yana burgeta abinda yake ƙara kusantasu dan bashi da takura, in har ya ƙirata sau ɗaya bata ɗauka ba, ba zai ƙara ƙiranta ba gani yake tamkar takura mata yake. Col. Ahmad akwai zafi a lamuransa a yadda ta fahimta amma Dr Awwab sanyin gareshi ga miskilanci da yake taɓawa. Ƙiran shi tayi bai ɗauka ba har sai da ya yanke, shigowar ƙiran shi ya shigo ta ɗauka tare da sallama. "Ina wuni, ya weekend?" Nuratu tace bayan ya amsa mata sallama. "Lafiya lau Noor, ya gida da su Mami?" Ya amsa mata ta ɓangaren shi yayin da yake kwance bisa doguwar kujeran falon Ummiz gefenshi ƴan biyu ne sun saka Hanan gaba suna mata tsifa. "Kowa lafiya ƙalau. Ina Hanan?" Kallonshi ya mai da kan Hanan da ta zuba masa ido jin ya ambaci Noor ta san Aunti Noor ce. Kanshi ya ɗauke ƙasa ƙasa ya ce. "Lafiyarta lau. Mun yi kewar ki fa?" Murmushi kwance saman fuskar Nuratu jin amsar Dr Awwab, wani maganar in ya faɗa mata mamakinsa take tamkar bashi yayi maganar ba. Ɗayan sashi na zuciyarta kuma sam bata son abinda suke nema wajenta dan ba za su taɓa samu ba, duk yanda zata kauce musu sun kasa fahimta kowa burinshi ya samu gurbi cikin zuciyar ta. Ajiyar zuciya ta sauƙe tana cewa. "Dr ina hanya in na koma gida za muyi waya." "Wayo kawai zaki mini Noor." "Dagaske nake." Tace alamar ya yarda da ita. Baya son takura mata hakan yasa yace. "Shikenan ki dawo lafiya, ki kular mana da kan ki." Kit ta kashe wayar tana jefawa jaka daidai sun iso gidan kawar Walida da za su fara kaiwa kuma ta kasance kawar Nuratu a baya dan tare su kayi sakandare. Har karfe shida kafin suka gama suka koma gida, sai da suka sauƙe Nuratu kafin Walida ta wuce. *** ZARIA. Ƙarfe taran dare ya sameshi a babban falon gidan Alhaji Isma'il Yaya ga mahaifin shi, yana zaune a falon tare da matarshi yana kallon labarai. Yaran duk sun wuce ciki. Guri ya samu ya zauna bayan ya sake gaishesa sai kuma yayi shuru ya rasa ta ina zai soma maganar abinda ya kawo shi. "Al-ameen menene? Kana da magana?" "Eh Baba." Yace kamar yadda suke ƙiran shi da sauran yaranshi gaba ɗaya. "Faɗa mini meke tafe da kai?" Alhaji Isma'il yace yana maida kallonshi kan Al'ameen da kanshi yake ƙasa. Bai san ko zasu karɓi buƙatar shi ba? Bai san ko sun san har yanzu yana kan bakarshi ba na son ganin ya auri Nuratu ya share mata hawaye. "Baba ina son ku nema mini auren Nuratu dan Allah in har hakan mai yiwa ne?" Al-ameen ya samu kanshi da faɗar haka zuciyarshi yana bugawa ko wani daƙika dan jiran amsar da zai fito daga bakin mutumin da yake ganinshi tamkar mahaifin shi. *** MAIDUGURI. "Abba mun yi magana da ita ta sanar dani wanene mahaifinta." Col. Ahmad yake sanar da Abban shi bayan tashin Umma a gurinsu. Jin maganar Col. Ahmad ya saka Abba fuskantar shi cikin zuciyarsa yana mamakin ƙarfin hali na yaronshi na ganin ya dage da son auren wannan yarinya. "Shikenan zan maka magana zuwa nan da kwana biyu sai ka mana jagora. Amma baka sanar dani komai ba dangane da ita?" "Abba gaban mahaifiyarta take sun rabu da mahaifinta amma duk a cikin Damaturu suke zaune, dangin mahaifinta yan Gombe ne mahaifiyarta ƴar Nijar." Jingina kai Abba yayi zarginshi ya tabbata jin girman ƴar mace, tarbiyyar mace, dole rayuwarta ya samu tangarɗa, a zahiri kuma yace. "Shikenan za muje da yardar Allah. Amma maganar gaskiya Ahmad ba dan ka saka kan ka dole ba, da babu abinda zai sani nema maka auren ƴar mace, nawa mace take da har zata bada tarbiyya ita ɗaya, kasan girman ƴar mace? Sam ban yarda da tarbiyyar ta ba." Shi dai shuru Col. Ahmad yayi yana sauraron Abban shi, babu abinda ya canza a ranshi dangane da neman auren Nuratu domin bata farin ciki da nuna mata itama mace ce tamkar kowa. *** ZARIA. #vote #comments #share MADUBIN GOBE (Haske) 28. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** ZARIA. "Na amince zan nema maka aurenta. Amma ka sani Al'ameen duk abin da ya biyo baya babu ruwana cikin auren ku." Kan Al'ameen ƙasa jin maganganun Baba har ya gama yace. "Na amince Baba, inshaAllah babu abinda zai biyo baya." "Allah ya sa." Baba yace kafin Al'ameen ya miƙe ya mishi sallama. Bayan dawowar Hajiya A'isha cikin falon Baba ya sanar da ita yadda su kayi da Al'ameen. "Ni dai bana son auren nan." Hajiya tace har cikin ranta take jin hakan. Shima Baba haka nashi bangaren zuciyar. "Nima dai Hajiya, ace yaron nan shekaru talatin da ɗauri babu aure amma ya tsaya kan wata da babu komai tattare da ita, shi ko tsoron bata da wani ciwon ma baya yi." "Nima abin da nake gudun masa kenan." Hajiya tace cike da jimami da taƙaici. *** DAMATURU. Ƙarfe goman safe ya shigo office ɗin da har yau bai mance kamaninsa ba tsawon shekaru huɗu da ya wuce, an gyara sosai anyi canje canje zamani tamkar ba cikin garin Damaturu yake ba dan tsaruwarshi da kuɗi da aka zuba aka kashe. Da tambaya ya samu iso cikin ofishin da numfashinsa kaɗan ya ɗauke dan haɗuwar shi, yana iƙirarin da takama shi mai kuɗi ne amma yaji bashi da komai ganin wannan haɗaɗɗen ofishin da mutumin cikin shi, ya san in har ya yarda da hukuncin da ya yanke zai samu sabon matsayi ban da arziki da yake jiyo ƙamshin sa yana tunkaro sa. Mamallakin ofishin yana zaune saman kujera yana juyi, fuskarshi ɗauke da murmushin ƙyeta ganin wanda ya shigo ya nuna masa gurin zama. "Bismillahi Alhaji Mamman." Zama yayi saman kujeran da Alhaji Kashim Mufid ya nuna mishi tare da miƙa masa hannu su yi musabaha, babu musu Alhaji Kashim ya miƙa hannu su kayi musabaha dan shi yake neman abu a wajenshi in ba haka ba bai kai ba. "Fatan zan ji alheri Alhaji Mamman?" Faɗin Alhaji Kashim bayan ya bada umarni a kawo wa Alhaji Mamman coffee da wayar landline dake ofishinsa. Bsbu musu babu tsoron Allah Alhaji Mamman yace. "Na amince zan bawa ɗanka auren ƴata, sai ku zo da ƴan uwa ayi magana in son samu ne zan haɗa auren da na ƴar uwarta da za'a yi nan da wata biyu." Faɗaɗa murmushin sa Alhaji Kashim yayi cike da farin ciki. "Allahamdulillahi, ai mu ko yau ka tashi a shirye muke kasan bamu da matsalar komai. Za ka ganmu cikin weekend da yardar Allah. Nagode sosai." Tabbas hakane basu da matsalar kuɗi a rayuwar su kamar yadda ya faɗa, miƙewa tsaye yayi. "Zan wuce Alhaji Kashim sai na ji ka." "Ko ruwa baka sha ba?" Alhaji Kashim yace yana miƙewa tsaye shima. Girgiza kai Alhaji Mamman yayi yace. "Na ƙoshi. Sai wani lokaci." "Nagode sosai." Yace ya masa rakiya ya dawo ofishin sa. Wayarshi ya ɗauka yayi ƙira ringing daya aka ɗauka. "Ka ƙara masa matsayi ya amince da buƙatar mu. Maganar kuɗi za kaji alert." "An gama ranka daɗe." Oga Dauda yace cikin farin ciki jin ta dalilin Alhaji Mamman zai samu wani alheri. Yana ajiye wayar ya rubutu shaidar ƙarin girma ya aika ofishin Alhaji Mamman aka ajiye masa. **** Yau tun safe wanki take yi duk ta gaji sai mita take kamar tayi kuka, mai wankin su yayi waya ba zai samu zuwa ba ya saka Mami tace tayi. Kuka ne kawai ba tayi ba dan a rayuwar ta ta tsani wanki, tana yi tana turo baki ran nan a haɗe dan ma Munirat tana taimaka mata. Saura kiris ya ƙare ta ji Mami na kwala mata ƙira ta ɗauraye hannunta ta shiga falon. "Wayar ki yana ta ƙara tun ɗazu." Mami tace hankalinta a kan talabijin. Gurin socket ɗin da wayar ta yake caji Nuratu tayi ta ɗauka, ƙira ne daga Yaya Al-ameen kusan uku da sakwanni biyu. Ɗaukar wayar tayi ta buɗe ta karanta saƙon. *"Na kira ki baki ɗauka ba na so muyi magana mai muhimmanci, zan shigo gari gobe ƙanwata. Zan zo ganin ki, nayi wani karambani cikin rayuwar ki amma ina fatan zaki amince da hakan domin alheri ne."* Ta karanta sakon yafi sau biyar ta kasa fahimtar takamemmen mai yske nufi, abinda ta gane daga ciki shine yace zai zo, sai kuwa ya zon za tafi fahimtar maganganun shi. "Waye ne haka?" Ta tsinci muryar Mami ta juya tana mai da wayar ta ajiye. "Yaya Al-ameen ne. Gobe yana zuwa." "Su dai basa gajiya." "Ni fa sun ishe ni Mami, na faɗa musu ba zasu taɓa samun abinda suke nema gurina ba sun kasa fahimta. Babu aure a rayuwar Nuratu." Cikin fushi Nuratu ta ƙarasa maganar tamkar a gabansu take, duk yadda tayi dan ta sanar da su sun kasa janye kudirin su a kanta. Shuru kawai Mami tayi ganin ran Nuratu ya ɓaci yanzu in ta biye mata wani abin zai biyo baya ya sata yin shuru ta rabu da ita da ta gama faɗar ta fita dan kanta. Bayan ta gama wankin tayi wanka kafin ta gabatar sallar la'asar ta kwanta hutu, Munirat ce ta ɗaura abincin dare dan Nuratu cewa tayi ta gaji haka Mami ta rabu da ita. Tana danna wayarta tana jin daɗin hiran da suke gudanarwa a group ɗinsu na mata su ƴan uwan juna, Aunti Rahma, Aunti Hasiya, Walida, Ameera sai ita da ta shigo daga baya, tsokanar Walida suke akan yadda take juya wanda zata aura tana sassauta mishi duk ya zauce a kanta. Wani magana da Walida ta faɗa ya saka Nuratu shiga tunani, zuciyarta ya faɗa wani tunanin da bata taɓa kawo hakan a matsayin duk so ba ne, inda Walida tace. 'Kun san Allah duk abin da nake masa bana iya kallon kwayar idonshi.' Ƴan uwan su kayi caa akan ta cewa hakan shine soyayya zazzafa. Wayar ta kifa tana dafe kanta tare da girgiza kan lokaci ɗaya dan ƙaryata zuciyarta. Shi ɗaya ne take jin nauyin shi da nauyin kallon cikin idonshi duk yadda ta so hakan, duk lokacin da tayi ƙoƙarin haɗa kwayar idanuwan su to harara take watsa masa da ita kanta ta rasa dalili domin idanuwansa lumshe suke tattare da wani sihirtaccen kallo da yake watsa mata ya hana idanuwanta sukuni. Idanuwanta ta buɗe jin har lokacin sakwanni suna shigowa cikin wayar ta ɗauka ta rufe data, ta kasa ci-gaba da hiran dan ji take hiran zai jefata cikin wani yanayi da bata shirya hakan a rayuwar ta ba sam, musamman akan wanda ba ta taɓa tsammani ba. *** Da daren Amma Jidda ta samu ƙiran Al'ameen akan yana hanya ga kuma abin da yake tafe dashi. "Kun yi magana da Nuratu?" Tambayar da ta aika masa bayan ta gama sauraron jawabinsa. "Na ƙira ta bata ɗauka ba amma gobe inshaAllah in na zo zan sanar da ita komai." Ajiyar zuciya ta sauƙe. "Ba zan ɓoye maka ba amma kayi gaggawa Al'ameen." Ya san da hakan amma in ba ta nan ya ɓullo mata ba, ba zata taɓa amincewa ba yadda ya lura da ita kuma ta faɗa masa hakan. Ajiyar zuciya ya sauƙe yana fatan ta amince yace. "InshaAllah Amma zata amince ki mini fata mai kyau." "InshaAllah ina maka." Tace suka yi sallama. "Ke dawa haka?" Taji Alhaji Mamman na tambayarta ta juya da sauri tana murmushi. "Al-ameen ne yake sanar dani gobe yana tafe." "Allah kawo shi lafiya." Yace ya wuce side ɗinshi ta miƙe ta bi bayan shi. ... Da safen Nuratu bayan ta gama abin da za tayi wajen ƙarfe hudu na yamma ta zauna jiran Al-ameen da ya ƙira ya sanar mata ya shigo zuwa dare zai shigo. Har bayan magriba ta cire rai da zuwan shi har tana cewa ta huta ta samu sallamar shi. Har cikin falon ya shigo suka gaisa da Mami tana tambayar shi ya hanya. Da lafiya ya masa mata ta shige cikin bedroom ta bar su daga shi sai Nuratu. Shuru falon ya ɗauka sai ƙarar Tv da yake yi. Al-ameen ne yayi ƙarfin halin furta abinda yake tafe dashi domin so yake ta fahimce shi. "Kin ji na nemi ganin ki ko ƙanwata?" "Eh. Fatan ba wani laifi nayi ba?" Ta faɗa tana kai dubanta gurin shi. Murmushi yayi yace. "Babu laifi ko ɗaya sai dai ma ni ne na aikata laifin. Fatan zaki karɓi buƙatana a karo na biyu ƙanwata, ga Muhammad Al-ameen ya dawo miki da bukatar aurenki Please kar ki ce wani abu, domin har na sanar da su Baba za su samu Abba suyi maganar." Kallonshi take cike da mamaki shigar sauri da ya mata ba tare da neman shawara ko tuntuɓarta ba, a zahiri kuma murmushin yaƙe take tace. "Amma Yaya Al-ameen abin har ya kai haka? Da ka bani lokaci ai." "Gani nake ba zaki amince ba ƙanwata." Rasa mai za tace mishi tayi kawai sai tayi shuru ta dafe kanta, amsa ɗaya za ta bawa duk wanda ya tunkareta da maganar da Al'ameen ya zo mata da shi, dan shi kam a yanzu haka ba zata iya bashi amsa kai tsaye ba domin tana jin nauyin shi ko dan Amma Jidda. Fes zuciyar Yaya Al-ameen ganin yake tamkar Nuratu ta amince da buƙatar shi, da ma ya san hakan in har ta samu labari iyaye sun shiga maganar ba zata ƙi ba. Da farin ciki ya koma gida ya sanar da Amma Jidda yanda su kayi. Itama tayi farin ciki sosai da jin Nuratu ta amince. Ko ba komai auren shine rufin asirinta. ... Tun bayan rabuwarsu ta mishi rakiya ta dawo gidan faɗa take zubawa tamkar akwai wanda zai kulata. Mami da Munirat suna jinta babu wanda ya mata magana. Da Mami ta gaji ne ma tace. "Ai wallahi ya mini dai-dai, maganin ki sai shi, yaran nan suna binki duk kin mai da su mashirmata." "To Mami na faɗa masa ina son shi har yanzu ne? Ko ina da ra'ayin auren shi, ni fa bana son shi haushinsa ma nake ji. Wallahi ki sanar da su ni ba zan aureshi ba, kunyar Amma nake ji ya saka ni ƙin sanar mishi." "Ke ki ka sani. Aure ne da Al'ameen sai kin yi." Kuka Nuratu ta fashe dashi tun Mami tana kallon abin da wasa har ta koma lallashi domin kuka take kamar babu gobe. Bayan ta tsaida hawayenta Mami tace. "Auren ne ba za kiyi ba ko Al'ameen ɗin ne bakya so?" Girgiza kai tayi tana share hawayenta. "Ko ɗaya Mami, ban dace da Yaya Al-ameen ba Mami, ba da mace irina ya dace ba, dan Allah ki sanar dashi hakan." Cikin kwantar hankali Mami tace. "Shi ya gani a hakan ya ji yana sonki ya amince zai aure ki sai ki godewa Allah." Mami da take tsammanin zata fahimceta ta kasa dan ita ma tana son ganin tayi aure, amma ita ta san zafi da kunci da take ji a zuciyarta duk lokacin da aka mata maganar aure. Ba ta da komai da zata bawa mijinta a matsayin babbar kyauta daga wajenta matsayinta na budurwa. Kwanciya tayi tana share hawayenta ta ji shigowar saƙo wayarta. Ƙin ɗauka ta yi ta san duk Al'ameen ne ƙarshe ma ta kashe wayar ta san zai ƙira daga baya. Ranar bata iya runtsawa ba, kwana tayi tana juyi da neman mafita ma kanta dan kaucewa wannan aure na Yaya Al-ameen. Idanuwanta a kumbure ta farka bayan bacci da ta samu ya kwasheta bayan sallar asuba da ta gabatar. Ƙarfe tara tayi breakfast ta kimtsa ɗakinta ta fito falon ta kwanta. Munirat ce ta gyara falon ta share wajen sha biyu ta fara ƙoƙarin ɗaura abincin rana. Cikin falon Mami ce zaune tana duba kayan da tayi order ta samu isowar shi yanzu lokaci zuwa lokaci tana kai kallonta kan Nuratu da idonta ke rufe kamar mai bacci. Cikin sallama da ya iya yi bai manta ba ya shigo falon cikin manyan kaya da ya amshi farin fatar jikinshi har da hula a saman kanshi, yayi mutuƙar yin kyau sai ƙamshi yake zubawa. ... To fa ga Alhaji Mamman ya bada auren Nuratu ga Mufid. Ga Al'ameen yayi shigo shigo. Col. Ahmad fa? Dr Awwab da yayi shuru fa🙄 Ko waye mai nasara? ... Wattpadian bana ganin Comments ɗinku 🥺😌 #vote #comments #share MADUBIN GOBE (Haske) 29. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "My Baby Noor." Mufid yace yana zama saman kujeran da Nuratu take zaune, ta fasa wani ihu tana miƙewa tsaye jikinta duk rawa yake ta nufi gurin Mami, Mufid ya saka hannu ya fizgota ta dawo baya ya zaunarta saman kujeran. Ji tayi numfashinta baya fita dai-dai da kyar tayi ƙoƙarin saita kanta kafin tayi yunƙurin saka jarumta a ranta ta fizge hannunta tana ja baya. "Ina wuni Mamin mu?" Faɗin Mufid yana dan durƙusawa dan gaishe Mami da ta zama kamar dutsi tana binshi da kallo da mamakin rashin kunyar Mufid da har zai iya shigo mata gida har cikin falo. Yaron da ya tarwatsa ƴarta farin ciki, ya hargitsa mata rayuwa ya mai da duniyarta baƙi babu komai ciki sai damuwa da tashin hankali. Tana mamakin yaushe ma ya dawo ƙasar. Bata iya amsawa ba sai kallonta da ta kai kan Nuratu dake duƙunƙune waje ɗaya ta cure, jikinta duk rawa yake ta kasa kwakkwaran motsi, hawaye ya wanke fuskarta. Kallonshi Mufid ya mai da kan Nuratu yana ƙara matsawa kusa da ita. "Oh My Baby Noor, wannan kuka haka in mu kayi aure kuma fa? Haka zaki dinga min kukan nan, share hawayenki My Baby Noor, kar ki ɓata min kyakkwayar fuskar ki. Na zo muyi maganar bikin mu kuma kin tsaya min kuka. Bana so." Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin kai hannunshi saman fuskarta dan goge ruwan hawayenta ta ja baya cikin kuka tace. "Kar ka taɓa ni, ka fitar mana a gida. Allah ya kiyaye in aure ka. Mugu, macuci, azzalumi sai Allah ya saka min cutar da ka yiwa rayuwana, Allah ba zai taɓa barinka ba. Ba zan taɓa yafe maka ba. Ka fita nace." Tace cikin kuka tana nuna masa hanyar waje da hannunta dake rawa. "Tashi ka fita ko ka sani aikata abin da banyi niya ba." Suka tsinci muryar Mami saman kansu riƙe da wuta sai sheƙi yake ta nuna Mufid da shi, ranta a mutuƙar ɓace ji take in Mufid yayi wani abun zata buga mishi. Ta nuna masa hanyar fita. "Fita min a gida. In ma ubanka ya aiko ka kaje ka sanar da shi Nuratu tafi ƙarfin ka, duk cutar da ka mata bai isheka ba sai ka sake shigowa rayuwarta? Mai kake buƙata?" "Auren ta Mami." Mufid yace yana miƙewa tsaye cike da tsoron wuƙar hannun Mami. "Ka fita nace ko in buga maka! Ɗan iska macuci." Mami tace cikin tsawa tana kai mishi wuƙar ya wani buga tsalle ya koma gefe kafin cikin sauri ya bar falon dan ya tsorata da Mami. Yana fita Mami ta ajiye wuƙar ta zauna kusa da Nuratu, Nuratu tana ganin haka ta faɗa jikin Mami ta ƙara sautin kukanta. "Dalla kimin shuru, ni da nake son ganin kin zama jaruma kin kwatarwa kan ki ƴanci za ki tsaya masa kuka. Ki cire tsoro ki tsoratar shi ki nuna masa bakya tsoron shi, balle daga yanzu ba zai ƙara gigin shigowa ba. Shegen ashe matsoraci ne." "Mami fa cewa yayi zai aure ni?" Nuratu tace tana share hawayenta maganganun Mufid na yawo saman kanta da taji ta yarda da hakan domin Mufid zai iya aikata komai yace musamman ubanshi da ya goya masa baya. "Ƙarya yake, ki cire komai a ranki." Mami tace cikin kwantar mata da hankali amma ita ma ƙasan ranta tana juya kalaman shi. Wayar Nuratu ne yayi ƙara Mami ta miƙa mata ganin Dr Awwab ne, kasa ɗauka tayi ta kashe. "Ki ɗauka mana." Mami tace Nuratu ta girgiza kai. "Zan ƙira shi anjima, kai na ya fara ciwo." "Kin sha maganin ki?" Kai ta ɗaga mata ta kwanta saman doguwar kujeran bayan Mami ta miƙe tana ɗauke wuƙar ta fita. *** Wayar ya ajiye saman kirjinshi bayan taƙi ɗauka ya lumshe idanuwanshi yayin da yake kwance saman doguwar kujeran falon Ummi. Bai cika ƙiranta ba dan kar ta ga kamar ya takura mata amma sosai yake kewarta da son jin muryarta, sau biyu ya ƙirata tun bayan dawowarsa daga gurinta amma bata ɗauka balle ta bashi amsar shi da yasan har lokacin da kyar ta karɓi buƙatar shi. "Awwab lafiya kuwa?" Ummi tace cikin harshen fillanci ganin yanayin ɗanta kamar da damuwa tun kwanciyar shi. Idanuwansa lumshashshu ya buɗe da suke ciki da damuwa ya miƙe zaune. "Mami bata ɗaukar waya na sau biyu ina ƙiranta." "Noor?" Tace dan sunan da yake ƙiranta da shi kowa tsammanin sa shine asalin sunanta. Ɗaga kai yayi yana ɗan yamutsa fuskarshi. "Ni dai Ummi zan ƙara komawa, sai ina jin kamar ba lafiya ba." Zama Ummi tayi ɗayan kujera tana fuskantar shi. "InshaAllah lafiya, amma kyanta ka samu zuwa a weekend ka dubata kar ka mata wani maganar. Kawai ka duba lafiyar ta." "Hakan za'a yi Ummi. Kar Hanan ta sani." Murmushi ta faɗaɗa ita ma kanta tana mamakin soyayyar Hanan da Noor, duk da ba ta taɓa ganinta ba amma haka kawai tana jin ƙaunar Noor, haka kawai take jinta a ranta. Sun yi waya sau biyu zuwa uku, biyu Hanan ce ta haɗa su ɗaya Dr Awwab bayan ya sanar da Ummi ita yake son aura ya haɗa su suka gaisa. Nuratu tana jin kunyar ummi sosai da ta rasa dalili. "Sai ka mata wayo kasan dai weekend tare ku ke wuni." Ummi tace ta miƙe. Hanan ce da Hassana suka shigo falon da gudu Hanan ta ƙarasa jikinshi. "Daddy Aunti Hassana ta siya min takalmi." "Allah My love kin mata godewa." Dr Awwab ya ce yana shafa kan yarinyar shi da yake mutuƙar ƙaunarta. Ta ɗaga mishi kai tana cewa. "Zan nunawa Aunti Noor." "Sosai ma zamu nuna mata." Ya ce ya miƙe yana ɗaukarta. "Za muje gidanmu ko za ki zauna wajen Aunties da Ummi." Zamewa tayi daga jikinshi bata son gidan babu kowa sai su biyu, ba ta da aiki sai kallo da wasa da teddy sai kuma makaranta. "Bana so, zan zauna gidan Ummi." Hanan tace da gudu tayi gurin Hassana. "Ki kula da ita Hassana." Yace yana sa kai ya fita, Hassana tayi murmushi, kullum sai ya faɗi hakan kamar wadda ba'a kula da ita. *** Bayan kwana biyu. Ranar jumma ƙanin Alhaji Tafida da amininsa ɗaya da ya kamata su san da batun zuwa Damaturu dan nemawa Col. Ahmad auren Nuratu duk sun shirya a yau dan tafiya har da shi Col. Ahmad din da shi zai yi jagorancin tafiyar, Alhaji Tafida bai sanar da Umma ba har yanzu yafi son sai yaje yaji abin da ya biyo baya. Alhaji Tafida cikin kwana biyun yayi iya abin da zai yi na bincikar waye Nuratu bai samu ba balle sanin halinta sai dai wani abu kaɗan da ya samu game da Alhaji Mamman Bashir. Bayan samun haka ya nemi zama da Alhaji Mamman akan zai zo har gida saboda muhimmanci abin da zai zo mishi dashi. Alhaji Mamman da farko yaƙi sai kuma yayi tunanin kar yazo masa da wani alherin ya sashi amincewa. Har ƙarfe sha biyu basu iso ba Alhaji Mamman sai mita yake, yana zaune a babban falonshi na baƙi cike da kayan abinci da abin sha an tara musu, an gyara falon an share sai ƙamshi yake. Sai ƙarfe biyu suka iso bayan sun gabatar da sallah a masallaci. Gaisuwa suka gudanar cikin mutunci kamar sun san juna, Alhaji Mamman yana kallon Col. Ahmad yace. "Kamar na so gane fuskar ka." Kan Col. Ahmad ƙasa ba dan yana jin nauyin Alhaji Mamman ba yace. "Eh Baba Col. Ahmad Tafida ne, a court muka haɗu shekaru huɗu" "Akan case ɗin yarinyar can ko?" Alhaji Mamman yace da sauri dan har cikin zuciyarsa mance sunan Nuratu yake. Kai Col. Ahmad ya ɗaga cike da mamakin Alhaji Mamman, gaskiyar Nuratu da ta sanar da shi wanene mahaifinta, bai ga laifinta da tace ta tsane shi ba. Gyaran murya Alhaji Mamman yayi. "Sai dai har yanzu baku sanar da ni mai ke tafe daku ba?" "Ka faɗa mishi Alhaji Inusa." Alhaji Tafida ya nemi hakan wajen abokinsa. Hakan ya saka Alhaji Inusa gyara zama yana fuskantar Alhaji Mamman. "Da alheri muke tafe Alhaji wanda mu ke saka ran inshaAllah zai zame mana alheri gaba ɗaya." "To to ina jinka." Alhaji Mamman yace yana ƙara baza kunnuwa. "Auren ƴarka ta wajen mahaifiyarta muke nemawa ɗan mu Ahmad in har baka mata miji ba balle ma inshaAllah muna da labarin babu wani." "Ita Nuratun ce ta turo ku, ko ita ta sanar da ku ban mata miji ba?" Cewar Alhaji Mamman fara'ar fuskarsa yana ɗaukewa. "Ko ɗaya bata sanar damu an mata miji ba, maganar zuwa kuma ita ta bamu adireshi da komai a matsayin ka na mahaifinta." "To na mata miji. Na yiwa yarinya ta miji, aurenta saura wata biyu da kwanaki." Ya ce yana miƙewa tsaye, da yasan abun da ke tafe da su ba zai ɓata lokacin shi ba. "Hakane?" Alhaji Tafida yace cikin ɓacin ran game da halin da Alhaji Mamman ya fara nuna musu. "Eh ko da akwai wani abun? Na ga dai ƴa tawa ce, to na mata miji." Col. Ahmad da yake kallon Alhaji Mamman cike da baƙin cikin wulakanci da cin fuska da yake neman yi wa iyayenshi sai lokacin yayi ƙoƙarin saka baki yace. "Amma Baba ba muyi haka da ita ba." Wani kallon banza ya watsa masa. "To yanzu ka sani." Col. Ahmad zai kuma magana Alhaji Tafida ya miƙe. "Kar ka sake magan Ahmad tashi mu tafi." Babu musu suka miƙe ko damar mishi sallama ba suyi ba dan ya zubar da ƙimar shi a idonsu suka fice. Shima ya kaɗa babban rigarshi ya fita. Suna tafe kowa yayi shuru suna jajanta abin da Alhaji Mamman ya aikata musu babu wanda ya sako Ahmad da yayi shuru yana jinsu sai tuƙi yake zuciyarshi yana cike da baƙin ciki da tunanin da kyar in Nuratu tana da labarin abin da mahaifinta ke shirin aikata mata, in ba haka ba da ta sanar da shi. "Ahmad ka ji abin da ya faru ko, sai ka janye niyar ka, ka hakura, dan ba zan sake taka kafana in je gurin wannan marar mutuncin in nema maka auren ƴarshi ba. Haba no wonder ƴar ta zama marar yanci mana, ban da girman mace abin da gado wajen uba." "Abba bata da labari." Col. Ahmad yace cikin sanyin murya. Abba ya buga tsaki. "Sai kuma kayi ta yi." Shuru yayi yaja bakinsa kawai yaci gaba da tuƙi burinsa ya samu zama ya ƙira Nuratu suyi magana. *** Washegarin ranar asabar haka kawai Nuratu tun daren take jin bugun zuciyarta ya ƙaru, har Mami ta sanarwa tace tayi ta addu'a inshaAllah alheri ke tunkaro ta kar ta saka damuwa. A cikin zuciyar Mami kuma duk ta saka abin ne a matsayin zuwan Mufid ne. Kamar ƙarfe uku tana kwance cikin falon taƙi fita tun safe tun bayan ta gama ayyukan ta, Munirat ta wuce islamiyya daga ita sai Mami. Cikin muryar da basu taɓa tsammani ba ko manta mamallakin murya ba ya shigo cikin gidan kai tsaye zuwa falon bai nemi umarnin shiga ba yana kwalawa Mami ƙira. "Sadiya! Ke Sadiya." Mami da ke kokarin shiga ɗaki jin muryar shi ya bata mamaki ta dawo baya ta ganshi tsaye kyan a tsakar falon yana bi da kallo har idanuwansa suka sauƙa saman kan Nuratu da ta tashi zaune tana bin wanda ake ƙira da mahaifinta da ido ba wai dan bata taɓa kallonshi ba sai dan halinshi da ya kasa canzawa. "Lafiya?" Mami ta ce ta dawo cikin falon tana haɗa rai dan jin yau kuma da mai ya zo mata. Nuratu da ke zaune ta saka musu ido tana kallo. Yatsa ya nuna mata kar zai saka cikin indanuwanta in da tana kusa dashi. "Wato ke kin girma kin san aure ko? Har ni zaki turawa mutane su je nema miki auren ɗan su, to ki buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau. Ni Alhaji Mamman Bashir a matsayina na mahaifin ki na zaɓa miki mijin aure dai-dai da ke. Ba kowa bane sai wanda ya fara lalata ki wato Mufid. Ke kuma Sadiya dan munafurci har da ke za'a haɗa baki ko? To ki fara shiri dan da Walida zan haɗa ayi auren rana ɗaya." Murmushin taƙaici Mami ta yi kafin ta haɗa rai. "Kar ka kai ni bango Alhaji Mamman. Ina ganin darajar ka har yanzu albarkacin ƴaƴa." "Kar ki gani Sadiya ki fito ki sanar da ni meke ranki." Tsayuwarta ta gyara tana fuskantar shi. "Mamman ka taɓa kallon Nuratu a matsayin ƴarka ƴar da ka haifa kamar sauran, ko ka taɓa ɗaukar nauyinta ko sauƙe haƙƙinta a matsayin ka na mahaifinta, baka taɓa nunawa ka santa ba tun kafin haihuwar ta har zuwa yanzu, dan haka ka fita harkar ƴata bata buƙatar ka a rayuwarta da har za ka zama wani abu balle ubanta. Maganar aure kuma in ka fasa to wallahi shari'a ce zata rabamu." Dariya ya kwashe da shi yana mamakin ƙarfin halin Mami. "Haka kika ce? To mu zuba. In shari'a ce ke zaki wahala domin aure tamkar an yi an gama." Daga haka ya juya ya fice a fusace. Da sauri Mami ta koma ɗakinta tana ɓoye hawayenta kar Nuratu ta gani. Nuratu da ke zaune dafe da kanta ruwan hawaye ya kasa daina zuba a idanuwanta. Duniyarta da rayuwarta babu komai sai baƙin ciki da damuwa, daga wannan sai wannan. Jin taɓa ƙofar ɗakin Mami ya sata ɗago kanta ta kai kallonta ƙofar. Tura ƙofar ɗakin tayi tana shiga. "Ki koma ina buƙatar hutu." Mami tace da ta juya mata baya tana sharan hawaye. Ƙi Nuratu tayi ta lallaɓa ta rumgumeta ta baya ta ɗaura kanta saman gadon bayanta taci gaba da kukanta. Shuru dukkansu su kayi kowa yana zubar da hawaye, bayan Nuratu tayi mai isarta ta sako tambayar da kullum yana damun ranta da Mami ta kasa sanar da ita gaskiya. "Mami mai nayi wa Abba? Ya tsane ni, baya so na, ya hana ni zuwa gidanshi, baya mini komai a matsayina na ƴarshi baya sauke haƙƙina dake kanshi, yanzu kuma yazo yace zai haɗa ni aure da Mufid. Mami ki taimaka ki sanar da ni menene ko zuciyata za ta samu nutsuwa duk da banga ranar nutsuwa a tare da ita ba." .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  30. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Mahaifinki ya tsane ki ne Nuratu bisa wani canfi nasa can da ya yarda da shi. Ni da Alhaji Mamman auren soyayya mu kayi har Allah ya bamu Rahma, Hasiya, Muhsin da Rukayya. Ina da cikin ki wata biyar mahaifinki ya fara samu ƙaddara cikin dukiyar shi da ya kasa yarda da hakan cewa komai daga Allah ne ya nemi aka masa duba aka sanar da shi cewa cikin jikina ne in bai rabu da shi ba to ƙarayar arziki yanzu ya fara. Duk yanda na so ganar da shi yaƙi yarda, ya so a zubar da cikin ki na ƙi daga ƙarshe ya jawo rabuwar auren mu. Bayan haihuwar ki ya dawo akan mu mai da aurenmu akan mu kai ki gidan marayu ko Nijar wajen Yaya Muhammadu na ƙi amincewa. Daga nan na ci gaba da kula da ke har zuwa yanzu. Kin ji dalilin da yasa mahaifinki baya son ki raɓe shi, gani yake farar ƙafa ne da ke." Kuka kawai Nuratu take jin bayanin Mami, rayuwarta daga wannan sai wannan. 'Ya ake so tayi?' Ba ta san maganar zuciyarta ya fito fili ba sai da taji Mami tace. "Ki ɗauki ƙaddarar ki inshaAllah za ki ga sakamako mai kyau." Sai a sannan Nuratu ta ɗago ido fuska shaɓe shaɓe da hawaye tayi murmushi mai ciwo. "Mami na jima da rumgumar ƙaddarar rayuwata, tun ban kai haka ba nake fuskantar yanayin rayuwa har zuwa yanzu. Shin sai yaushe zan ji daɗin rayuwa tamkar sauran mutane?" "Za ki ji Insha Allah Nuratu, Allah yana tare da ke." Kai ta ɗaga ta yarda ta amince jarabawa ce daga Allah duk abin da ya sameta. "Mami kina ganin zai aikata abin da ya faɗa. Mami zai iya aura min Mufid, Mami ki taimaka mini in gujewa auren Mufid, Mami na tsaneshi, tsoron shi nake ji." Hannunta Mami ta kamo murmushi mai ciwo take yi. "Alhaji Mamman zai iya aikata duk abin da ya faɗa, sai dai kar ki damu domin wannan lokacin shari'a ce zai raba mu, sai in da ƙarfina ya ƙare." Girgiza kai Nuratu tayi wani hawayen na zuba bisa kumatunta. "Mami shari'a? Shari'a ba zai yi magani ba, shari'a bata aiki a zamanin yanzu musamman in sun haɗu da marasa tsoron Allah. Mami zan yi nisa da garin nan da ƙasar nan, zan yi nisa da kowa in kafa sabuwar rayuwa ko zan samu kwanciyar hankali. Ki nema min mafita." Shuru ɗakin ya ɗauka Mami tana juya maganganun Nuratu, tabbas in har Alhaji Mamman ya faɗi abu to zai aikatawa musamman akan kuɗi dan bata da shakka wani abun Alhaji Kashim ya masa. "Za ki iya rayuwar ƙauye?" Mami ta tambayi Nuratu da itama tunani ta take. Kallon Mami tayi tana neman ƙarin bayani. "Za ki iya rayuwar ƙauye, in har za ki iya ki shirya gobe in tura ki can Nijar wajen Yaya Muhammadu ki zauna mu gani zuwa wani lokaci, zan ƙira shi in sanar da shi komai na san shi kanshi ba zai yarda da abin da Alhaji Mamman ya faɗa ba." "Zan iya Mami, zan tafi wallahi." Nuratu tace da sauri ko ba komai za ta gujewa auren Mufid da kowa da yake shiga rayuwarta ko zata samu kwanciyar hankali. "Shikenan ki shirya kayan ki gobe sai ki tafi." Kai Nuratu ta ɗaga tana tashi ta fita, ji tayi damuwarta rabi ya kau ta san dai duk tsiya in bata nan ba za su ɗaura mata aure da mutumin da tafi tsana a duniya ba, wanda ya ɓata mata rayuwa ya cuceta. *** Col. Ahmad bayan isar su yayi ta ƙiran Nuratu bata ɗauka ba har ƙarfe biyar na yamma bai sanar da kowa ba ya fita a gidan ya kama hanyar Damaturu, so yake komai cikin dare ya isa ya sameta su yi magana, shi ba ma ta kanshi yake ganin iyaye sun ƙi yarda da aurenshi da ita ya sashi jin neman aure ya fita a ranshi, dan share mata hawayenta ya sashi neman aurenta, tausayi take bashi, matsayin ƙanwa ya ɗauka ya bata tun ranar da ya fara sanin ta. Taimakon rayuwarta kawai yake jin yake son yi ta samu ƴan ci da farin ciki tamkar kowa. Ya riga ya hakuri ya cire son auren a rayuwar shi ko duba da yadda iyayenshi basa so ya san ko anyi ba daɗi zata ji ba. In har akwai wanda take so ta sanar da shi suyi magana ayi aurensu cikin wata ɗaya kafin kudirin mahaifinta ya cika a kanta. Karfe bakwai ya isa hotel ya kama ya gabatar da sallar magriba kafin ya watsa ruwa yaci abinci da rabon shi dashi tun safe. Sai da ya gama ya fito ya nufi gidan su Nuratu. A waje yayi parking kafin ya shiga da sallama, babu kowa cikin gidan ya sashi nufan falon tare da sallama. "Kamar muryar Ahmad." Mami tace cike da mamaki, Nuratu da ke cin abincin ta zubawa ƙofar ido. Shi ɗin ne ya shigo cikin sallama bayan sun amsa, Nuratu ta miƙe ta bashi gurin ya zauna a ƙasa ya gaishe da Mami, tana shirin tashi ta shiga ciki dan basu guri yace. "Mami gurin ki na zo muyi magana." Komawa tayi ta zauna. "Ni kuma Ahmad? Fatan dai lafiya." Ƙanshi ƙasa ya fara mata bayani. "Mami nayi karambani cikin rayuwar Nuratu, bayan na nemi ta sanar dani waye mahaifinta na samu iyayena da maganar son nema min aurenta, ɗazu da safe mun zo mun samu Alhaji Mamman da maganar ya sanar damu ya riga ya mata miji. Mami iya sani na da yanda Nuratu ta sanar da ni bata da wani karfaffan shaƙuwa ko alaƙa dashi tun haihuwarta. Ina tsoron Mami ya cutar da ita, kar ya aura mata wanda ba za taji daɗin rayuwa da shi ba. In har tana da wanda take so ta sanar dashi ya fito ayi maganar aurensu, in son samu ne ma a ɗaura auren kafin lokacin da ya ɗauka." "Mufid zai aura mata ya sanar damu ɗazu." Mami tace bayan gama sauraron bayanin Col. Ahmad. Cike da mamaki yace. "Mufid dai wannan yaron?" Kai Mami ta ɗaga. "Shi dai, gata nan yaran nan Al'ameen da Dr Awwab suna binta tana kaucewa bayan koran Dr Sadiq da tayi, ga ka kai ma.  Ta sanar da kai in har akwai wanda ya kwanta mata cikin su kuyi magana da shi. In kuma babu mun riga mun yanke hukunci ni zan turata can Nijar wajen Yayana Muhammadu ta zauna zuwa wani lokaci." Kallon Nuratu Col. Ahmad yayi dan son jin ta bakinta ta ƙara sunkuyar kanta ƙasa tace. "Ni babu wanda nake so. Nijar kawai zan tafi." "Hakan shine dai-dai Nuratu?" Col. Ahmad ya tambayeta ta ɗaga mishi kai. "Shikenan Mami Allah yasa haka shi yafi alheri, amma ki yi wa kan ki faɗa Nuratu, zama ba naki bane ya kamata kiyi aure a matsayin shekarun ki." Bata ɗago ba bata amsa ba tana jinshi har ya gama ya miƙe ya musu sallama bayan Mami ta sanar da shi gobe ƙarfe goma Nuratu za ta tafi ya mata alƙawarin zai zo dan a gari zai kwana. Bayan fitar shi Mami ta koma kanta. "Kowa in ya tashi maganar aurenki kiyi tunani Nuratu, ba fa rayuwa za tayi ta tafiya a haka ba, dole kina buƙatar aure dan ganin kin kama mutuncin kan ki, ko dan in ga ƴaƴan ki auta na." Rai Nuratu ta ɓata tana turo baki. "Ni dai Mami bana so ba yanzu ba." "Ke ki ka sani." Mami tace ta tashi cikin jin haushi. Tunani Nuratu ta faɗa, shigo shigo ba zurfi Col. Ahmad ya mata da sai an gama komai zai sanar da ita sai dai ta ji labarin an sanya ranar aurensu. Bata taɓa jin sonshi ba hasalima kunyarshi take ji, tana bashi girma da daraja a rayuwarta na ganin shine mutum na farko da ya fara taimaka mata a rayuwa ya kwata mata ƴancin ta, ganin babban Yaya da uba take mishi. Da bata san ta ya ya za suyi zaman aure ba balle ma bata jin zata amince da auren shi. Bayan ta gama cin abincin ta ɗauke plate din ta kai kitchen ta wuce ɗakinta, kasancewar tana hutun sallah wanka ta yi ta saka rigar baccinta marar nauyi ta duba kayanta wanda ta haɗa ko akwai abin da ta manta ta ga babu komai ta yi addu'a ta kwanta tare da jawo wayarta. Buɗe data tayi sakwanni suna ta shigowa wanda za ta iya buɗewa ta buɗe ta leƙa groups ɗin su ta ga hiran duk Rukayya da Walida ne sai Ameera sama sama take jefa musu baki, tana mamakin baƙin halin yarinyar. Tana gama dubawa tana shirin sauƙa aka nuna mata alamar Dr Awwab yana online, searching ta yi ta shiga gurin sunan shi ta gani yana online sai lokacin ta tuna da ɗazu ya ƙirata bata ɗauka ba. .... Dr Awwab kwance yake saman gadonshi wayarshi a hannu yana duba sakwannin da yayi sati bai buɗe datar ba ya ga an nuna mishi Noor tana online, saman sunanta ya hau kamar zai tura mata saƙo ya zubawa fuskar wayar ido tamkar zai hangota. Wani mugun sonta da ƙaunarta yana fizgar zuciyarshi, yayi kewar kwayar idanuwanta da suke ɗauke da wani sihirtaccen kallo da yake son gani duk lokacin da ta watsa masa harara. Neman nutsuwar sa da numfashin sa yake, sai yayi ƙoƙarin dai-daita kan shi. Ya san ya so Nusaiba amma Nuratu daban yake jinta, shi ya ganta yaji ta shiga ranshi da bai taɓa jin son wata sama da ita ba, yana buƙatar kasancewa kusa da ita, ya ganta ya ƙirata a matsayin matar shi amma taƙi bashi dama. Ya ƙirata bata ɗauka ba kuma bata ƙira shi ba, gata nan a online ta kasa mishi magana, yana son mata magana baya son ta ga kamar ya takura mata. Hakan ya sa ya hakura ya sauƙa yana ajiye wayar a gefe ya rufe idanuwanshi yana tuna every movement na su da ita. .... Nuratu tana kallo ya sauƙa ya nuna mata last seen ɗinshi hakan ya sa itama ta sauƙa ta ajiye wayar, sai taji kwata kwata bata kyauta mishi ba zuciyarta yayi wani iri da ta kasa fahimtar menene. Addu'a tayi tun tana tunane tunane har bacci ya ɗauke ta. Washegarin kasancewar ba sallah take ba ya sata sai karfe takwas ta farka, wanka tayi ta shirya cikin abaya da ya amshi baƙin fatar jikinta ta yane kanta da gyale, ba tayi wani kwalliya ba sai hoda da man baki da ta saka, ta jawo akwatinta babba ɗaya ta fito falon. Breakfast tayi ta zauna jiran Col. Ahmad da ya ƙirata yana hanya. Mintuna ashirin ya iso bayan sun gaisa da Mami yace Nuratu ta fito ya kaita tasha. Kuɗi dubu talatin Mami ta bawa Nuratu da lambar wayar Yaya Muhammadu in ta sauƙa ta ƙira shi azo ɗaukarta, Nuratu sai taji bata son tafiya ta bar Mamin ta, tun da tayi wayo basu taɓa rabuwa ba ko tayi nesa da ita ba. Shan kwanar motarsu kawai ya gani dai-dai isowar shi garin ya nufo gidan dan kawai ya sata a idanuwanshi ko zai ji sauƙin abin da yake ji dan daren jiya bai iya baccin kirki ba tsabar tunanin da ya kwana dashi. Sauƙa yayi a motar ya shiga cikin gidan tare da sallama Mami ta amsa cike da mamaki. "Dr Awwab." "Ina kwana Mami, sai ki ka ga bakon safiya." "Laa ba komai mu shiga ciki." Tace tana shiga falon ya bi bayanta cike da kunya, a ƙasa ya durƙusa ya gaisheta tana tambayarshi mutanen gida ya amsa da lafiya. "Sai kuma a kayi rashin sa'a yanzu Nuratu ta bar gari." "Gari kuma lafiya Mami?" "Lafiya ƙalau, ina jin ma warhaka ba ta tafi ba ka ƙirata ko ka sameta a tashar mota kuyi sallama." Bai iya jira Mami ta ƙarasa maganar ba ya miƙe. "Bari in sameta." Daga haka ya fita daga gidan gaba ɗaya, motarshi ya shiga ya ja tare da ƙiranta a waya yana ta ringing bata ɗauka ba ya ajiye wayar cikin jin haushi. Tuƙi kawai yake cikin sauri har ya isa cikin tashar ya fito cikin motarshi tare da wayar a hannunshi yana cigaba da ƙiranta. Bata ɗauka ba ya fara juye juye tare da tambayar motar da zai tashi yanzu suka sanar da shi a akwai na state akwai na local government. "Ga can mota za ta tashi saura mutum biyu." Faɗin kwandasta yana nuna mishi wani mota yaga an rubutu Geidam local government. Da sauri Dr Awwab ya ƙarasa wajen yana raba ido ko zai ganta. Har ya hakura zai juya ya hango Nuratu ta kifa kanta da kujeran dake gabanta, bai yarda ita bace sai da ya ƙarasa sosai ya ƙira sunanta. *"Noor."* Da sauri Nuratu ta ɗago kanta jin wanda take tunanin shi a zuciyarta ya ƙira sunanta, tsammanin ta duk cikin tunanin ne sai da taji ya maimaita lokacin da ya iso gurinta ta dai-dai window da take. Kallo ɗaya ta iya mishi ta kawar da idanuwanta kamar kullum ta kasa saka idanuwanta cikin nashi, shi nashi bangaren kuma ba haka ya so ba, yayi kewarta yayi kewar ganin cikin idanuwanta kar ta mishi rowar gani. "Mai yasa bakya ɗaukar ƙira na. Kin san ƙira nawa na miki daga gida zuwa kafin in iso." "Kayi hakuri, wallahi wayar yana cikin jaka ban ji ba." Ta iya bashi amsa bayan kallo ɗaya da ta masa yana sanye da ƙananan kaya kamar kullum yayi mutuƙar yin kyau. "Ba wannan ba ina za kije babu sanarwa? Ko dai ina takura miki ne Noor in hakura?" Sai lokacin tayi ƙoƙarin kallonshi karo na biyu suka haɗa ido tayi saurin ɗaukewa zuciyarta yana bugawa jin maganar shi na ƙarshe da ya sakata shiga ruɗani da ta rasa dalili. Girgiza kai tayi. "Kayi hakuri Docter." Tace muryarta yana rawa, ya ƙara matsawa kusa da window sosai jin muryarta ya canza. "Kar ki min kuka, bana son muyi rabuwar da ba daɗi." "Ni fa tafiya zan yi ba wani gurin zan je ba." Tace tana turo baki tare da ƙoƙarin mai da hawayenta. Idanuwansa ya ɗauke saman fuskarta yanda ta yi da bakinta ji yayi har tsakar kanshi. Da kyar ya furta. "Ina za ki je?" "Nijar gurin Yayan Mami." "Sauƙa ki fito." Yace da ita ta juyo da sauri ta kalleshi shima lokacin ita yake kallo ta ɗauke kanta. "Na ce ki sauƙo. Magana za muyi kafin a cika." Daga haka ya bar baƙin window ya koma gurin boat ya saka aka ciro mata akwatin ta. "Lafiya Oga? Ko ta fasa tafiyar ne?" Faɗin mai motar. "Ku je kawai kuyi hakuri." Dr Awwab yace ya ja akwatin Nuratu yayi gaba da shi, Nuratu da ta fito jin maganganun su ta bi bayanshi da sauri cike da mamakin ina kuma zai kai mata kaya ita da take son isa kafin dare. Cikin boat din motarshi ya saka akwatin ya zagaya ya buɗe wajen zaman banza dai-dai lokacin Nuratu ta iso ta ja ta tsaya. "Shiga mu je." Yace da ita ta kalli cikin motar tana girgiza kai. "Dan Allah kar ka mai dani gida. Rayuwana yana cikin hatsari ka bar ni in tafi." "Ni ma ba gida zan maida ke ba, tafiya a motar kasuwa akwai wahala Noor." Girgiza kai tayi tana rau rau da idanuwanta za tayi magana ya rigata. "Zan saka ki da kai na in baki shiga ba." Kallonshi tayi ya ɗaga mata gira. "Yes ko in gwada ne?" Da sauri ta shiga ya rufe ya zagaya ya shiga ya kunna motar yana fita a cikin tashar, babu wanda yayi magana har su kayi nisa ya samu babban mall ya tsaya. "Bari in mana guzuri." Ba ta kulashi ba ya fita ya shiga ciki ya fito da kaya niki niki a hannunshi daga snack da drinks ya saka a kujeran baya ya koma ya shiga yana kunna motar suka bar gurin, tafiya suke har suka fita a garin Damaturu suka ɗauki hanyar Geidam ya ɗauki wayarshi ya ƙira Ummi. "Ummi ki min addu'a zan yi tafiyar gaggawa." Ya faɗa bayan Ummi ta ɗauka. "Ka isa Damaturu ne?" Ta tambayeshi ta ɓangaren ta. "Eh zan yi nisa kaɗan zuwa gobe zan dawo inshaAllah, a kula min da My Love." "To Allah ya kiyaye a dawo lafiya." Ameen ya amsa ya kashe wayar yana ajiyewa a gefe ya kai dubanshi gurin Nuratu da ta kwantar da kanta saman kujera tayi baya. "Bacci zaki min a mota?" Sai lokacin ta juyo hankalinshi yana kan hanya ta ɗauke kanta ba tace komai ba. "Bari in kara gudun AC sai kiji daɗin baccin ki, mai da kujeran baya kaɗan." Babu musu ta maida kujeran yayi baya ta kwanta ta ja gyalenta ta rufe fuskarta da shi, ya ƙara mata gudun AC. Tafiya yake yana tuƙi ba ji ba gani, Nuratu bacci ne ya ɗauketa bata san lokacin ba. ... #vote #comments #shar#share MADUBIN GOBE (Haske) 31. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Sun yi tafiya mai nisa tsawon awa huɗu kafin su shiga cikin garin Geidam, lokacin karfe biyu na yamma. Hotel mai kyau ya nema dakyar ya samu ya kama dan su gabatar da sallah kafin su wuce. *"Noor."* Yace yana buga seat din Nuratu ta buɗe idanunta fes cikin nashi fuskarshi ɗauke da murmushi, da sauri Nuratu ta runtse idanuwanta bayan ta watsa mishi harara dan kallon da yake mata. "Ni ka dai na kallo na." Murmushi Dr Awwab yayi. "Why Noor?" Bakinta ta tura tana juyar da kanta gefe ta fara ƙoƙarin fita taji yace. "Bamu iso ba, sallah za muyi muci abinci sai mu ƙarasa." Kai ta ɗaga mishi ta fita shima ya fito ta ga ya nufi cikin hotel ɗin ta ja ta tsaya. Juyowa yayi yana kallonta yaga ta tsaya. "You don't believe me Noor? Girgiza kai tayi yayi gaba yana cewa. "To mu je." Babu musu ta bi bayanshi har cikin hotel ɗin ba laifi yana da kyau da komai har cikin ɗakin sai taji gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, zuciyarta ya fara bugawa, tsoro ya fara ziyarar ilahirin jikinta, jikinta ya fara rawa. Kallo ɗaya Dr Awwab ya mata bayan ya gabatar da alwala a bathroom ya fito ya karanci yanayinta. "Kiyi sallah kafin na dawo sai mu wuce." Daga haka ya fita sai lokacin ta ɗan ji sauƙin ta samu nutsuwa ta miƙe ta shiga bathroom, jikinta ta gyara ta fito dan ba sallah take ba ta zauna jiranshi. Bai jima ba ya dawo ɗakin ta miƙe tsaye ganinshi, da kallo ya bita. "Kinyi sallar ma kuwa?" Tambayar da ya mata kenan kai ta ɗaga mishi ya juya suka fita yana riƙe murmushin sa dan fahimtar yanayinta. Cikin motar suka koma ya ja suna barin harabar wajen, suna cikin tafiyar ya faka ya miƙa hannunshi baya ya ɗauki snack da drinks da ya saya a cikin Damaturu ya juyo ya ɗaura saman cinyar Nuratu. "You can eat, duk abincin su bai min ba." Kai ta ɗaga masa yaci gaba da tuƙi. Har suka fita cikin garin ya ga bata da niyar ci ya sashi faka motar ya juya yana kallonta kafin ya kai hannu ya ɗauki snacks din dake saman cinyarta ta kasa ci, ba wai dan bata jin yunwa ba sai dan kunyarshi da take jin ba zata iya cin abu a gabanshi ba. Tana kallo ya ɗauka ya buɗe ya miƙa mata. "Karɓi kici ko in ɗura miki dan na san kina jin yunwa gulma ce ta hana ki." Rai ta ɓata ta karɓa ya ɗauki drinks din ya buɗe mata. "Karɓi ki haɗa." Shima karɓa tayi ta riƙe yana kallo bata da niyar ci ya haɗa rai. "Sai na miki ɗurai ko?" "To ni ka daina kallo na." Nuratu tace tana ɓata rai ita ma. Murmushi yayi ya juya yana kallon titi ya kunna motar yana ja, ganin haka ta fara ci kaɗan kaɗan har taci sosai tasha drinks din, tana ƙoƙarin ajiyewa a gefe taji yace. "Ban sauran." Kallonshi tayi ya juyo ya saka ɗayan hannunshi ya karɓi snacks din hannunta ya kai baki yana ci, sai da ya cinye ya ɗauki sauran drinks din ya shanye ya buɗe gilashin motar ya jefar da robar yaci gaba da tuƙi. Nuratu idanu ta zuba mishi ganin baya kallonta kafin ta ɗauke ta mai da kan titi, shuru babu wanda yayi magana har sun kusa shiga border ya sako zancen da yake son mata. "Me za kiyi a Nijar?" Shuru tayi bata bashi amsa ba ya sake maimaita tambayar ta buɗe baki da kyar ta sanar dashi. Sai da ta gama tayi shuru yace. "To a bani dama mana na fito Noor, a shirye nake ko yau kika bani dama." Shuru ta mishi taƙi bashi amsa ya canza salon maganar. "Allah yasa hakan ya zamto rushewar auren, amma fa ba zan hakura ba har yanzu ina kan bakana, kinga in munje ma sai in gabatar da kai na wajen Kawu." "Ni dai bana so dan Allah." Tace tana haɗa rai yayi murmushi yana shafa kanshi cike da gashinsa na fulanin asali kwantacce. "Allah ni ina so Noor, bani da wani burin ya wuce in aure ki." Bata kulashi ba ta juyar da kanta tana haɗa rai, ganin da gaske tayi fushin ya sashi yin shuru dai-dai sun isa border suka tsaya. Fita yayi a motar ya nufi masu kula da shiga da fita, yayi duk abinda zai yi dakyar suka bashi damar shiga ƙasar bayan katin shaidar ƙasa dana aiki dana tuƙi da ya nuna musu kafin su barshi. Bayan ya koma motar ya ja aka barsu suka wuce cikin Maine anan ya tambayi hanyar garin Doso aka nuna masa. Ƙarfe biyar ɗin yamma suka shiga cikin garin, Nuratu sai bin garin take da kallo, bata taɓa zuwa ba sai dai shi Yaya Muhammadu ya zo wani lokacin. Guri ya samu yayi fakin motarshi yana fuskantar Nuratu. "Sai kuma ina Noor, ina ne hanyar gidan." "Dama in na sauƙa ne zan ƙira in sanar dasu da wayar direba, kuma yanzu kam sai dai in sayi sabon sim." "Bari mu nema to." Yace yana jan motar ya fara neman masu sai da kati ya sayi sim da kati ya karɓi wayarta ya buɗe, sim ɗinta ɗaya na Mtn hakan yasa bai cire ba ya saka sabon da ya saya ya kunna yana miƙa mata. "Saka numbern ki ƙira su." Karɓa tayi ta saka numbern sai da ta ƙira sau biyu aka ɗauka, Yaya Muhammadu ne. "Ina wuni Kawu." "Lafiya ƙalau sai dai ban gane waye ba?" Yace daga ɓangaren shi. "Nuratu ne ƴar Hajiya Sadiya, na shigo garine dama shine na ƙira a zo a ɗauke ni." "Oh Nuru, to to kina ina ne in turo Musalle." "Nima ban sani ba." Ta fada, ƙasa ƙasa Dr Awwab yace mata. "Ya same mu a tasha ko ma shigar gari." "Kawu ina tasha yazo." Nuratu ta faɗa jin me Dr Awwab yace. "To yana zuwa kar ki je ko ina." To ta amsa dashi ta kashe wayar Dr Awwab ya ja motar bayan sun tsaya an musu kwatancen tasha suka isa gurin. "Bari in yi sallah in dawo." Dr Awwab yace Nuratu ta ɗaga masa kai ya fita, bayan yayi sallah ya dawo Musalle ya ƙirata ta ɗauka. "Kai ne ka sauƙa a mashin yanzu?" "Eh kina ina?" "Gani nan a cikin farin mota ka ƙaraso." Daga haka ta kashe wayar Musalle ya juya ya kalli motar gefenshi kafin ya ƙarasa wajen ta buɗe ta fita suka gaisa ta koma ya shiga baya. Suna tafiya yana nuna musu har cikin unguwar su, unguwa babu laifi amma akwai rashi tattare da unguwar dan babu sosai, ginin bulo da bulo ma babu sosai balle kwalta da wani abun more rayuwa. Baƙin ƙofar gidan ya faka motarshi suka sassauƙa, Dr Awwab ya fito da akwatin Nuratu suka shiga cikin gidan da sallama. An shimfiɗa musu taburma a filin gidan, Nuratu ta zauna Dr Awwab ya zauna a gefenta shi kanshi yana mamakin ƙarfin halinshi. Yaya Muhammadu zaune gefensu saman nashi taburman matar shi da ƴarshi budurwa suna gefe a saman kujeran tsungunno. Bayan gaisuwa da aka gudanar tsakanin su, Yaya Muhammadu na tambayar ƴan gida ya juya kan Dr Awwab suka gaisa. "Amma dai dole za ka kwana, ka ga dai dare yayi." "Eh Kawu nima hakan nace, zan nemi gurin kwana." "Wani irin kuma za ka nemi gurin kwana bayan ka zo gida, ka ga nifa ɗaya na ɗauke ka da ƴaƴan Sadiya. Ga ɗakin Musalle in har zaka iya kwana sai ya bar maka." Idanu Dr Awwab ya ɗago ya kalli Nuratu ta juyar kanta gefe. "Shikenan Kawu nagode babu komai." "Ko kai fa, Musalle ɗauki abinci da kindirmo ka kai masa, in akwai abinda yake buƙata ka sanar mishi." Yaya Muhammadu yace Musalle ya miƙe ya ɗauki abinci da ruwa ya kai masa ɗakinsa ya dawo ya ɗauki kindirmo suka koma tare da Dr Awwab. Ɗakin bashi da laifi, lailaye ya ke da leda sai babbar katifa da bedsheet a kai da ɗan hasken shi sai akwatinan kayan shi a gefe, yaron da gani akwai tsafta. Dr Awwab mamakin kanshi yake in aka sanar da shi zai kwana a irin wannan ɗakin ba zai yarda ba amma gashi yau har daɗi yake ji zai kwana gida ɗaya da Noor ya wayi gari ya buɗe ido ya sata a idonshi. Bayan wucewar Dr Awwab ciki Kawu yace wa Nuratu. "Yaron akwai hankali kamar mahaifiyar shi, sau ɗaya na haɗu da ita ko biyu ne, auren Rukayya da zuwana na ƙarshe." "Kawu ba fa ɗan Amma Jidda bane, ba Yaya Al-ameen ba ne." Nuratu tace ganin Yaya Muhammadu duk zaton sa Yaya Al-ameen ne. Da mamaki Yaya Muhammadu yace. "To wanene shi kuma? Duk na ɗauka ɗan wajen babar su Rahma ne." "Bashi bane, Dr Awwab ne, shi ya ci gaba da kula da ni a Maiduguri a asibitin su." "Allah sarki, oho sai yanzu na shaida fuskar na ganshi a kotu tabbas, Allah sarki akwai hankali daga ganin shi. Ko dai shine surukin mu." Da sauri Nuratu tace. "A'a wallahi Kawu mutumci muke, ya zo ni kuma zan taho shine ya kawo ni." "Oho hakane. Ki ci abinci ki hutu anjima zan zo muyi magana. Hafiza shigar mata da akotin ta(akwati ta) ɗaka." To tace yarinyar ta miƙe ta ja akwatin Nuratu ta shigar da shi ɗakinsu, Nuratu taci abincin sosai dan rabonta da abinci tun safe. Bayan magriba ta watsa ruwa ta saka dogon riga da hijabinta har ƙasa ta kasa fitowa filin gidan. Tare Kawu da Dr Awwab da Musalle suka dawo daga masallacin sallar isha'i, a soro suka rabu Dr Awwab ya shige ɗaki, Kawu da Musalle suka shige cikin gida. Abincin dare aka jera musu Kawu Muhammad ya dubi matar shi. "Ki bawa Nuru ta kaiwa bakonta ɗaki yana ciki, kin san dai da kunya ya zauna cikin mu." To ta amsa dashi ta zuba a food flask mai haɗe da tuwo da miya tuwan biski miyar ɗanyar kuɓewa da ya sha kifi ta tura Hafiza ta ƙira Nuratu a ɗaki. "Ga abinci ki kaiwa bakon ki." "Mama Yawuro ki bawa Musalle ko Hafiza dan Allah." Nuratu tace dan gaskiya bata so. "Wuce ki kai mishi Kawun ki ne ya faɗa, baƙon ki ne fa ki girmama shi, Annabi yana girmama baƙi kuma yana son mai girmama shi." Shuru Nuratu tayi ta ɗauki flask din da ruwan sha a jug haɗe da plate na silba a babban tray ta nufi ɗakin dake soro in da Dr Awwab yake. Da sallama ta shiga yana zaune a ƙasa ya kwantar rabin shi akan katifar yaji sallamar Nuratu ya miƙe zaune yana amsa mata ta shigo ta ajiye a gaban shi. "Ga abinci nan, fatan zaka iya cin abincin su." "Saboda me yasa, duk abin da Noor taci nima zan iya ci ko rai na baya so. Balle ma na san abincin ƙauye da daɗi." Murmushin Nuratu tayi da bata san dalili ba har dimples ɗinta suka lotsa dukka biyu. Yana son abin ba zai iya ɓoyewa a ranshi ba. Dr Awwab yace a ranshi a fili ƙasa ƙasa yace. "I like your dimples Noor." Fuskarta ta rufe da tafin hannunta, zuciyar Dr Awwab cike da nishaɗi ganin Nuratu ta fara amsar saƙonshi da jin abin da yake ji a kanta. Fuskarsa cike da murmushi yace. "Bana son wannan kunyar da babu ita tsakanin mu. Zai cuce ni." "Ni dai ka bari dan Allah." Nuratu tace tana cire hannunta saman fuskarta ta ƙara da cewa. "Ya gajiyar hanya, nagode sosai na baka wahala." "Ni ne da godiya Noor kin kawo ni har gida ban sha wahala ba, kin ga gaba ba zan ji wahalar gabatar da kai na ba in na dawo." Miƙewa tsaye tayi jin maganar da ya sako. "Sai da safe." "Allah kai mu, thank you Babyna." Dr Awwab yace da sauri Nuratu ta fita dan bata iya hanashi wanɗannan maganganun da yake mata ba, kunya yake sakata ya jefa zuciyarta cikin wani shauƙi. Abincin Dr Awwab yaci kaɗan dan bai jima da ci ba, Musalle ya shigo ya kwashe komai ya fita kafin ya kwanta dan huta gajiya. Ɓangaren Nuratu ba ta ci abinci ba dan ta ƙoshi bayan Kawu Muhammad ya gama cin abincin ta ƙira Mami suka gaisa tana tambayarta ya hanya, bata ɓoye mata ba ta sabar da ita Dr Awwab ne ya kawo ta. Mami tace. "Ya zo na sanar dashi kuna fita ya iso. Mai yasa kika bashi wahala." Nuratu tace. "Shi yasa kansa." Bayan sun gama magana ta miƙawa Kawu Muhammad dan jin bayanin Mami. ... #vote. #comments #share MADUBIN GOBE  32. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Kawu Muhammad sauraran bayanin Mami yake har ta gama ya sauƙe numfashi yana cewa. "Sadiya anya Alhaji Mamman kan shi ɗaya." "Ni ma ban sani ba Yaya Muhammadu, ni dai ga Nuratu dan Allah ta zauna zuwa nan da wani lokaci." Mami tace ta ɓangaren ta. "Shikenan amma kar ki damu, kinyi dabara da ki ka turo ta, sannan kar ki damu wannan lokaci ba zamu barshi ba." Sun jima suna waya kafin ya kashe ya miƙawa Nuratu wayar ta karɓa ta shige ɗaki bayan dogon nasiha da Kawu Muhammadu ya mata akan kar ta damu komai zai wuce. Da safe ƙarfe tara Dr Awwab ya shirya zai wuce, bayan ya yiwa su Kawu Muhammadu sallama tare da godiya suka ce sune da godiyar dawainiya da yayi da Nuratu. Har ƙofar gida suka suka rakoshi kowa ya koma ciki aka barshi da Nuratu. Yana zaune cikin motar, ƙofar a buɗe Nuratu ta riƙe murfin motar, duk yanda ya so su haɗa ido ta ƙi yarda. "Babyna." Yace yana riƙe da wayarshi ya saita dai-dai fuskarta yana ɗaukar hotanta da bata ma san mai yake ba. Jin abin da ya faɗa yasa Nuratu haɗa rai ta watsa mishi harara. "Ni ba Baby bace, bana so." "To Babyn waye? Mami? Kin ma Mami girma. Babyna ce ke soon za ki yarda da hakan Noor." "Ni dai ka gaishe da Hanan da Ummi sai anjima, Allah ya kiyaye hanya." Tace ta rufe motar. "Ameen Babyna za su ji." Yace ya kunna motar yana barin gurin ta juya cikin gidan cike da kewa. Haka kawai ta ji kewar rashinsa kusa, yana sakata nishaɗi. Tana komawa gida wanka tayi ta kimtsa jikinta ta canza kaya ta ɗauki wayarta ta ƙira Col. Ahmad, yana shirin tafiya duk ya harhaɗa kayansa zai koma Ibadan ya samu ƙiranta suna tare da Umma tana mishi faɗan da har jiya ta kasa dai masa akan ya rabu da Nuratu ko ta ɓata masa rai, kuma aure ne ta bashi nan da sati biyu in ba haka ba zata aura masa ƴar uwarsa ƴar ƙanwar babanshi. Col. Ahmad bayan ya gama sauraran faɗan Umma yace. "Mami maganar gaskiya ba zan miki ƙarya ba bazan iya rabuwa da ita ba amma maganar aure na janye tsakanin mu da ita. Kallon ƙanwata nake mata Umma, abin a tausaya mata ne wallahi, tana buƙatar taimako da kulawan uba ko yaya, dan Allah kar ki rabani da ita. Maganar aure kuma na amince in har hakan zai saka ki yarda da ni." "Ka amince har ranka, kuma ka min alƙawari ba zaka taɓa kawo min maganar auren wannan yarinya ba ko gaba, in har kayi hakan ka tabbatar zan nuna maka ni na haifa ka." "Na amince Umma in har za ki barni in taimaki rayuwar Nuratu." Col. Ahmad yace har cikin ranshi. Shi ba wai auren bane baya so yawan canje-canje wajen aiki da yake samu ba zai iya yawo da iyalai ba. Rashin aurenshi da Nuratu ya riga ya amince cewa babu aure tsakaninsu sai dai wani ikon Allah. Ko kuma Alhaji Mamman ya janye kudirin shi na auren Mufid da Nuratu. Ganin ƙiran lambar Nijar ya san daga Nuratu ne, ya sashi miƙewa tsaye. "Umma zan wuce ku gama magana da su Baba." "To yaushe za ka dawo? Kar fa ka tafi ka ƙi dawowa kamar kullum." "Zan dawo Umma inshaAllah zuwa nan da wata ɗaya da kwanaki." Yace ya ja akwatin shi ya fita a falon. Driver ne ya kai shi airport, jirgi zai bi ya tafi, bayan ya sauƙe shi ya ƙira Nuratu da tana waje tana ta ya Nazifa aiki da duk yanda taso ta hanata taƙi. Jin ƙarar wayar ya sata miƙewa daga wanke wanke da take yi ta shiga ɗaki tana ɗauka. "Col. Ina kwana? Na ƙira baka kusa, na isa lafiya ƙalau tun jiya da yamma." "Ya hanya ƙanwata, to allahamdulillahi, kin same su lafiya?" Ya faɗa ta ɓangaren shi yana taka matakalar hawa jirgi. "Eh ya mutanen gida?" "Lafiya ƙalau, nima ina hanyar komawa Ibadan." "Allah ya kiyaye hanya, sai anjima aiki nake." "To shikenan ki gaishe da mutanen gida in na dawo zan zo." To ta amsa dashi ta kashe wayar ta fita taci gaba da aikinta. *** Waya suke da Yayan marigayin mijin matarshi yana shaida masa akan zai shigo zuwa nan da kwana biyu dan tattauna wani magana. Alhaji Mamman sauraron shi kawai yake har ya gama kamar yana son fahimtar mai yake shirin zuwa yi yace. "Amma Alhaji da ka sanar da ni dalilin zuwan dan zan yi tafiya zuwa Gombe." Alhaji Mamman yace dan son sanin dalilin shi kawai na zuwa. "Laa ba wani abu bane, ƴar wajen tsohuwar matar ka Al'ameen yake neman aure, shine za mu zo muyi maganar." Dama yaji hakan a ranshi in ba haka ba menene zai neme shi abinda bai taɓa faruwa tsakanin su ba. Murmushi taƙaici yayi yace. "Ita Nuratu ce ta turo shi bata sanar daku na mata miji ba. To aurenta saura sati bakwai ba sai kun zo ba Alhaji." Da mamaki Baba yace. "Ikon Allah wallahi bamu da labari ina tsammani ko shi Al-ameen ɗin bai sani ba." "Ai yanzu kun sani." Alhaji Mamman yace ya kashe wayarshi yana buga tsaki. Wannan yarinya na gaza mishi maganganu. ... Ɓangaren Baba yaji wani iri sosai jin wacce Al'ameen yake nema an mata miji, da ma bai fita aiki ba ya leƙa ɗakin matar shi ya sanar da ita yadda su kayi da Alhaji Mamman ya ce ta sanar Al'ameen shima za suyi maganar da shi. "Wallahi kamar ya san bama son auren nan." Tace cikin farin ciki. "Zan wuce aiki sai anjima." Yace ya fita sai yaji gaba ɗaya bai ji daɗin haka ba ko dan yanda Al'ameen ya so aurenta duk da abin da ya faru da ita. ... Bugun ƙofar gidan yayi ya ji shuru babu kowa ya shiga kai tsaye cikin falon gidan kamar yanda ya saba. "Wai ke Sadiya wace irin ƴa kika haifa? Anya yarinyar nan jinina ce? Ko dai aljana ce ba mutum ba ce?" Mami da ke zaune tana bin Alhaji Mamman da kallo yana wannan maganganun, huci yake kamar zaki da zai ci babu. "Me kuma ta yi?" Ta tambayeshi cikin jin zafin munanan kalamai da yake jifan Nuratu da shi. "Wato yarinyar nan sai tayi ajalina ta haɗa ni da hawan jini na mutu ko? Wannan da gida ɗaya muke raye ashe da ta daɗe da kashe ni. Duk iskancinta bai tsaya anan ba sai ta turomin samarinta da suke hure mata kunne suna neman aurenta ko? To ki buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau, na matso da auren nan da kwana goma. Ko taƙi ko ta so sai ta auri Mufid domin shine dai-dai da ita." Taƙaici da baƙin ciki ne suka cika zuciyar Mami ta girgiza kai, tabbas zai aikata abin da ya faɗa amma za tayi maganin shi, dan haka ta miƙe tana nufan ɗakinta. "To mun ji Allah ya kaimu." "Wato ina miki magana kin mai dani mahaukaci ko?" Yace ganin Mami ta shiga ɗakinta. Bata kulashi ba hakan yasa ya sa kai ya fita yana surfa ruwan bala'i. Jin ya fita ya saka Mami fitowa, mukullin motarta ta ɗauka da mayafinta ta fita, gidan Aunti Zarah ta nufa ta tare ta da fara'a, bayan sun zauna sun gaisa Mami ta sanar da ita komai dan ita ɗaya ta yarda da ita zata bata shawara mai kyau ta ƙara da cewa. "Zarah. Gombe zan tafi in sanar da yayansa komai, in har ni yafi ƙarfina ai shi ba zai fi ƙarfin sa ba, ya ishe ni, ya cire mu a rayuwar shi tsawon shekaru, bai san cinta ba, bai san shan ta ba, tun da take bai taɓa sayo ko minti da sunan na Nuratu ba. Sai yanzu rana tsaka yace zai aura mata yaron da ya ɓata rayuwarta ya lalata ya kawar mata da dukkan farin cikinta." Mami dake wannan bayanin ta share hawayenta da ta samu damar zubarsu yau dan zuciyarta ya karaya. Ajiyar zuciya Aunti Zarah ta sauƙe tace. "An ya ba wani abun Alhaji Kashim yayi wa Alhaji Mamman ba? Kina hasashen abin da nake yi." "Duk nayi tunanin wannan Zarah, Alhaji Mamman zai aikata komai akan kuɗi tun da har ya guji jinin shi." Jinjina kai Aunti Zarah tayi tace. "Hakan nake tunani nima. Mafita ɗaya ki sanar da yayansa kafin lokaci ya ƙure in har ya kasa ɗaukar mataki sai mu jingina abin da kotu daga nan komai ya tonu. Ko kuma ita Nuratun ta fitar da miji a ɗaura aure balle lokaci ya ƙure mana." Shuru Mami tayi tana sauƙe ajiyar zuciya. "Shikenan Zarah hakan zan yi. Gobe zan tafi." Sun jima suna maimaita zance har wajen la'asar kafin Mami ta mata sallama ta tafi. A daren ta shirya kayanta kala ɗaya na tafiya ta sanar da Munirat gobe za tayi tafiya. Da safe karfe takwas ta kama hanya a motar kasuwa bayan ta tura Munirat gidan Aunti Zarah dan bata son su Aunti Rahma su sani sai abu yayi tsanani. *** MAIDUGURI. Dr Awwab bayan ya sauƙe gajiyar hanya ya huta, bacci yayi daren ranar sosai dan gajiyar tuƙi da yayi, bai taɓa tuƙi mai tsawo ba. Da safe ya leƙa asibiti ko gida bai shiga ba, bayan ya gama abin da zai yi wajen la'asar ya bar asibitin ya nufi gida dan ganin sanyin idaniyar shi. Ai kuwa yana shiga falon ya sameta zaune ta baje takardunta na makaranta a dole ance suyi karatu za'a fara exam next week. Tana kallon mahaifinta tayi watsi da takardun ta nufeshi ta. "Daddy!" Tace da ƙarfi bayan ya ɗagata sama ya cafke suna dariya ya nufi kujera da ita ya zauna tana zaune jikinshi. "My Love Ina Ummi?" "Tana sallah." Tace tana ƙara shigewa jikinshi. "Ke kin yi sallar?" Ya tambayeta yana ɗagota ta ɗaga masa kai. "Na yi da Aunti Husna tare." Shuru ne ya biyo baya Hanan tace. "Daddy za ka kai ni wajen Aunti Noor in munyi hutu in kwana mata." "Kina son Aunti Noor? Nima ina sonta." "Dagaske Daddy? To ta dawo gidanmu da zama dan Allah ka ga sai muna ganinta kullum." Murmushi yayi ya shafa kanta. "Ni ma zan so hakan My Love, in kunyi waya ki sanar da ita ko zata yarda." "To ka ƙira min ita." Tace cike da murna. Wayarshi ya ɗauka ya lalibo lambar Nuratu da yayi saving da Noor da hoton heart a gaba, murmushi yayi sai kuma yayi tsaki tunawa da ya manta layin nan ba zai shiga ba kuma ya manta bai karɓi na Nijar ba. "Menene Daddy?" Hanan tace kamar zata fashe da kuka ganin ya ajiye wayar. "My Love wannan number is not available, sorry zan ƙira miki ita wani lokaci." Kuka ta saka mishi ya hau lallashi, fuskar nan duk hawaye Ummi ta sauko ta ƙarasa wajen. "Meye faru?" Ta tambaya cikin harshen fillanci. "Rigima ce Ummi, wai na ƙira mata Noor kuma numbern ta is switch off." "Zo nan Hanan, da kai na zan kai ki wajen Aunti Noor in kin gama exam." Ummi tace ta ɗauketa, haka suka lallasheta ta mance ta koma kan takardunta. "Ummi ina yaran nan?" Yace yana maida kallonshi kan Ummi. "Sun fita makaranta." "Yunwa nake ji." Yace ya miƙe yana isa table ya samu abin da zai iya ci yaci ya musu sallama ya tafi. Hanan na mishi bye bye ƙarfi da yaji taƙi binshi gida. *** GOMBE. Bayan Mami ta isa bata sha wani wahala ba dan bata mance unguwar da gidan ba dan sai canje-canje da aka samu sosai a garin. Bayan ta sauƙa ta shiga ciki da sallama aka amsa mata, matar gidan ta tare da da mutumci da karamci suka shiga cikin falon, bayan gaisuwa tace. "Sai dai kamar na gane fuskar, Hajiya Sadiya ko?" "Hakane ni ce baki mance ba, shekaru dayawa." "Wallahi dai tun abubuwan da suka faru." "Eh wallahi ya kuma abin da ya faru? Allah ya rufa asiri ya kiyaye gaba. Lokacin bamu samu zuwa ba sai daga baya muka samu labari" Da murmushi saman fuskar Mami tace. "Babu komai, Allahamdulillahi. Wajen Alhaji na zo yana nan ma kuwa." "Yanzu ya fita wallahi sai zuwa yamma zai dawo, sai dai in zaki jira shi." Shuru Mami tayi kafin tace. "Wallahi ina son komawa a yau in da zan samu." "Kar ki damu in dai akan matsalar wajen kwana ne Hajiya Sadiya na gane nufin ki. An zama ɗaya fa, jini ya haɗa ko dan albarkacin yara ai an zama ƴan uwa. Ba dan Abban su Rahma ba ai da zumuncin yafi haka." Hajiya Maimuna tace tana murmushi ta nunawa Mami har yanzu matsayinta na Hajiya Sadiya take a gurinta ko dan albarkacin yara ai an zama ɗaya. Mami ta ji daɗin karamci da Hajiya Maimuna ta nuna mata, duk da ta girme mata amma matar ta nuna mata kamar ƙawarta ta ɗauketa, ta kaita har bedroom ɗinta tayi alwala ta rama sallolinta ta kawo mata abinci da ruwa. Da rana yaranta sun dawo a makaranta suna ta binta da kallo dan yanayin kammani da suka gani na yan uwansu a fuskarta. "Mamin su Aunti Rahma ne ƴaƴan Alhaji Mamman ƙanin Babanku." Hajiya Maimuna tace musu ganin kallon kallo da suke yi bayan sun gaisheta. "Haba naga kama wallahi, sak Aunti Rahma sai yanayin Nuratu da take dashi, shuru kawai nayi." Ƙaramar ƴarta ta faɗa duk su kayi murmushi kuma hakanne banda Aunti Rahma babu mai kama da ita dan har tafi kama da ƴan uwanta na Nijar, sai Nuratu da ta ɗaukota kaɗan sai dai ita baƙace da sai ka kula za kaga kamar. Sauran duk mahaifinsu suke kama dashi sai farin fatar Mami da suka ɗauka. Muhsin tun da ya tafi makaranta kusan shekaru huɗu bai ƙara dawowa ba sai waya da yake ƙiran Mami kullum, dan ma ya kusa gamawa burinshi ya zo yaga ƴan uwanshi su ganshi. Daga nan hira ya barke tsakanin su suna tambayarta sauran har suna sanar da ita suna son zuwa Babansu baya barinsu. Sai yamma lis Alhaji Inuwa ya dawo bayan ya ci abinci ya huta har bayan magriba kafin Hajiya Maimuna ta sanar da shi yana da baƙuwa. Da mamaki yace. "Sadiya da kanta kuma yau. Sanar da ita ta shigo." Babu musu Hajiya Maimuna ta miƙe ta fita ta sanar da Mami suka dawo tare cikin hijabinta har ƙasa. Bayan sun gaisa yake tambayarta ya yara da yar wajenta. "Duk lafiyar su ƙalau." Ta amsa da shi a nutse ta sanar da shi abin da ke tafe da ita. "Dan Allah Alhaji ka mishi magana ya janye maganar auren nan da yaron nan da Nuratu, yaron da ya lalata mata rayuwa ya cuceta yanzu kuma shine zai haɗa su aure in ba wani abun nashi daban ba. Albarkacin yara nake barinshi wallahi, bana so yayi rashin hankali in yi rashin hankali abin ba zai mana daɗi ba, in ba haka ba shari'a ce zata rabamu." "Gaskiya bai kyauta ba, amma kiyi hakuri zan ƙira shi zuwa gobe a gabanki mu yi maganar in ya kama ma zan je can Damaturu in same shi. Kinyi tunani da kika zo baki biye mishi ba Sadiya." Alhaji yace yana mamakin halin ƙaninshi da gaba ɗaya ya canza akan dukkan lamuransa tun ba yau ba, ba shekarun yanzu ba tun shekarun baya. Godiya Mami ta mishi kafin ta koma ta barshi da Hajiya Maimuna. .... MADUBIN GOBE  33. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Da safiyar ranar Alhamis bayan Alhaji Inuwa ya gama abin da zai yi kamar ƙarfe goma ya aika Hajiya Maimuna ƙiran Mami da ta shirya tana zaune da zaran sun gama magana ta koma. Bayan sun isa ta gaishesa ya ɗauki waya ya ƙira ƙanin shi Alhaji Mamman da sai su yi wata ba su yi waya ba sai idan shi ya ƙira, gani yake ko dan ya fishi arziki. Ya jima yana ƙara bai ɗauka har ya kusa tsinkewa kafin ya ɗauka da sallama. Bayan sun gaisa yake cewa. "Mamman ina buƙatar mu yi wani magana in har kana da lokaci, maganar mai muhimmanci ne, da son samu ne ma zan shigo Damaturu amma abin gaggawa ne." "Ina da shi Yaya Inuwa, ka sanar dani menene. Wani abun ya faru?" Alhaji Mamman yace ta ɓangaren shi jin maganar yayan shi. "Labari na ji ko in ce dagaske ne ka bayar da auren Nuratu ga wannan yaron Mufid?" "Eh hakane babu maganar ƙarya." Alhaji Mamman yace ranshi ya fara ɓaci jin maganar da ya zo masa dashi yana mamakin ina ya samu labari. "Amma Mamman kana tsoron Allah? Kana tsoron ranar da Allah zai tuhume ka da haƙƙin yarinyar nan. Yanzu abin naka har ya kai ka ɗauki aurenta ka bada ba tare da izinin mahaifiyarta ba wacce tasha wahalarta tun haihuwarta har girmanta. Ina laifin a mutumin kirki ne tun da dole sai an zo wajen ka neman aurenta amma sai wancan banzan yaron." Sai da ya gama sauraron shi har ya gama kafin yace. "Kayi hakuri Yaya amma yarinya ƴata ce ko?" "Eh ƴarka ce?" "To kayi hakuri ka fita cikin maganar nan dan Allah ina ganin girman ka. Ita Sadiyar ta ƙira ta faɗa maka, to ka sanar da ita babu fashi domin aure tamkar an yi an gama. Sai anjima ka gaishe da yaran." Daga haka ya kashe wayar shi cike da jin haushin Nuratu da Mami. Jin ya kashe Alhaji Inuwa ya ajiye wayar cike da taƙaici. "Kin ji mai ya faɗa Sadiya ko. Mamman ya canza, dama haka yake amma yanzu kwata kwata ya sake canzawa. Mutanen nan ba a banza suka barshi ba Sadiya. Kuyi magana da Nuratu ta turo yaron da take so zan samu Mamman za ayi abu ɗaya." Mami da kanta ke ƙasa hawaye ya taru a idonta jin har lokacin Alhaji Mamman ya kasa janye kudurin shi ta ɗago kanta. "Alhaji har yanzu babu aure a cikin ranta tun abin da ya faru, tana da wanda suke sonta, amma yanzu na san dole ta zaɓi ɗaya cikinsu." "To ki sanar da ita ta turo ɗaya cikinsu wanda ya kwanta mata a rai, ni zan gama komai. Zan nunawa Mamman ina da iko a kanshi, ko shari'a ce shi zai wahala domin tauyewa yarinyar nan haƙƙinta." "Ba ta nan tana Nijar wajen Yayana tsoron auren ya sa na tura ta can." "Au to shikenan ki sanar da Yayanki ku yi magana ɗaya cikin gaggawa. Ku sanar da ni duk abin da kuka yanke." "To nagode Alhaji." Mami tace ta miƙe tana mishi godiya. Bayan fitarta ya tura Hajiya Maimuna da dubu goma ta bata tayi kuɗin mota, da kyar ta karɓa, ta saka yaron su babba ya kaita tasha ta hau mota. *** DAMATURU. Bayan gama wayarsu Alhaji Mamman faɗa ya hau yi sosai cikin gidan Amma Jidda na bashi hakuri da bata san kan zancen ba har sai da ya sauƙo ta tambayeshi da ta gwanmace bata tambaya ba dan amsar da ya bata. Dakyar ta samu bakin furta. "Amma Alhaji baka kyauta ba, yanzu wannan yaron zaka bawa auren Nuratu ko duba da halin da ya jefata baka yi. Wannan yaron da babu tarbiyya a tattare da shi." Amma Jidda tace cikin ɓacin rai da tsananin mamaki. Ƙara haɗa rai Alhaji Mamman yayi. "To sai me? Na ga dai shine dai-dai ita dama shi ya lalata abin shi, ko kina tunanin akwai wani wanda zai fito yace zai aureta a yanda taken nan." "Akwai su da yawa, ko Al'ameen neman aurenta yake." "Na riga na gama magana Jidda. Ina ganin mutumcin ki dan haka ki rufe bakin ki babu ruwanki cikin wannan maganar." Miƙewa tsaye tayi cike da takaici bata mishi magana ba ta wuce ɗakinta, yaja tsaki ganin kowa yaƙi bashi goyon bayan auren Mufid da Nuratu. A yanda yake jin daɗin ƙarin girma da ya samu banda kuɗaɗe miliyan goma da Alhaji Kashim ya bashi bayan amincewar shi baya jin zai iya fasa auren nan, auren za'a yi sai dai duk abin da zai faru ya faru. Amma Jidda da ta shige ɗaki tausayin halin da Nuratu zata shiga take ciki, wani haushin Alhaji Mamman ya mamaye ta. 'Al-ameen fa?' Zuciyarta ya tambaye ta da ya ɗauki aniyar ganin ya aureta in ya ji wannan labari bata san ya zai ji ba, yana son Nuratu tun ba yau ba har ƙaddara ta gifta a rayuwarta zuwa yanzu babu abin da ta canja. *** Da karfe uku Mami ta shigo garin Damaturu gidan Aunti Zarah kai tsaye ta nufa, bayan ta huta taci abinci tayi sallah ta sanar da ita yanda su kayi da Alhaji Inuwa. Bayan ta gama sauraronta cikin haushi tace. "Ki sanar da Yaya Muhammadu kawai ya aurar da ita ga duk wanda ya masa, na san dai ko ba komai za tafi jin daɗi da shi akan Mufid. Domin Alhaji Mamman ba zai taɓa fasa abinda ya yi niya ba ko da shari'a zata hana, balle ma babu lokacin kai ƙara. Ina ma zamu iya shari'a da su Sadiya, kuɗi za su zuba yayi aiki, mu zamu sha wahala." Mami idonta cike da kwalla tace. "Ni ko Al'ameen da ya shirya zan tura shi wajen Alhaji Inuwa ayi auren, amma abubuwan gaba ɗaya sun kwaɓe har na rasa tunanin mai zan yi. Bana son Nuratu ta auri yaron nan, wahala kawai za tasha." "Kin sanar da Amma Jidda ne?" Aunti Zarah tace. Girgiza kai Mami tayi. "A'a ba mu yi maganar ba, ko su Rahma babu wanda ya sani." Shuru ɗakin ya ɗauka kowa ya rasa tunanin da zai yi dan ɓullowa lamarin kusan mintuna goma Mami ta miƙe. "Bari in je gida zuwa nan da kwana biyu inshaAllah zamu samu mafita, zan yi waya da ita Nuratun da Kawun ta mu yi magana." "To shikenan ki kwantar da hankalin ki Allah yana tare da ku." Aunti Zarah tace ta miƙe ta mata rakiya har waje tare da Munirat suka koma gida. *** Bayan kwana biyu ya ji shuru Baba bai masa magana ba akan maganar da suka yi, yana son masa magana baya son ya ga tamkar ya matsa masa ne amma haka kawai zuciyar shi yake jin akwai abin da yake faruwa, musamman in ya ƙira Nuratu wayarta ba ya shiga. Aniyar tunkarar shi da maganar yayi yau daren juma'a, da daren ya same shi har falonshi. Ƙanshi sunkuye ƙasa ya rasa ta ina zai soma zancen, Baba yana lura da shi kuma ya san mai yake tafe da shi sannan dole ya sanar da shi abin da yake faruwa. Ƙiran sunan shi yayi kansa a ƙasa ya amsa kafin ya ɗago da kyar. "Na san magana ne yake tafe da kai akan maganar da mu kayi ba?" "Eh wallahi Baba na ji shuru ne, na ce ko lafiya." Al'ameen yace yana sosa kanshi. Murmushi Baba ya faɗaɗa. "Lafiya lau, mun yi waya da Alhaji Mamman ya sanar da ni ya riga ya yi wa ƴarshi miji." "Miji dai Baba, Nuratu fa?" Yaya Al-ameen yace cike da tashin hankali da ruɗani. "Ita dai na sanar da shi ta wajen tsohuwar matar shi." Girgiza kai Yaya Al-ameen yayi yana dariya. "Kai Baba ba dai Nuratu ba sai dai Walida." "To shikenan tun da baka yarda ba." Baba yace yana komawa ya jingina kansa da kujera. Tashin hankali da ruɗani Al'ameen ya shiga jin maganganun Baba, gani yake tamkar tatsuniya yake sanar da shi ya miƙe da sauri ya fita ya nufi bangaren su na samari. Saman kujera ya zauna ya ɗauki wayar shi yaci gaba da ƙiran numbern Nuratu a kashe har lokacin, sai yaji zuciyarshi ya ƙara shiga ruɗu ya kasa nutsuwa. Daren ranar bai iya runtsawa ba washegarin da safe karfe bakwai ya nufi hanyar Damaturu dan tabbatar da gaskiyar maganar da yake jin ba zai iya hakura Nuratu ta auri wani bashi ba, yarinyar da yake sonta yake kaunarta yake burin aure tun shekaru biyar baya. *** Dr Awwab yana zaune yana jiran Hanan ta fito su wuce. Shigowar shi gidan cikin shirin ƙananan kaya zai yi tafiya ta saka masa kuka sai ta bishi jin in da zai je ya barta tun da weekend ne babu makaranta, islamiyya kuma an ba da hutu. Bai so ba dan kar ta takura masa dole Ummi ta saka baki yace Hassana ta shiryata su tafi tare da kayan sawanta kala biyu. Mintuna arba'in suka sauƙo tare da Hassana ta mata wanka ta saka mata riga gown brown color da takalminta cover shoe, kanta da hula an rufe dogon gashinta na fulani da sai an buɗe ake ganin yawan shi. Har bakin mota suka masa rakiya, Hanan ta shiga gidan gaba kusa dashi aka saka mata ƙaramin jakarta gidan baya kafin ya kunna motar suka bar harabar gidan. Tafiya suke cikin nutsuwa Hanan na ta zuba mishi surutu yana amsa mata sai lokacin ya ji daɗin tahowa da ita dan tana ɗeba mishi kewa. Tun yana amsa mata har ya ji tayi shuru ya juya ya ga bacci ya ɗauketa ya gyara mata kujeran da kwanciyarta kafin yaci gaba da tuƙi. Sai da suka shiga cikin Damaturu ya tsaya ya saya musu abinci da abin da ya san za taci in ta farka kafin ya ɗauki hanyar Nijar dan ganin hasken zuciyar shi da yau ya ɗauki aniyar zuwa ganinta. Yayi kewarta yayi kewar jin muryarta da ganinta. *** Yamma lis Al'ameen ya shigo Damaturu bai iya biyawa gidan mahaifiyarshi ba dan tabbatar da gaskiyar maganar ya wuce kai tsaye gidan Mami. A ƙofar gida ya faka motarshi ya sauƙa ya shiga gidan da sallama kai tsaye cikin falon ya nufa. Mami tana cikin yin waya da Kawu Muhammadu ta sanar da shi duk yadda tayi da Alhaji Inuwa da hukuncin da suka yanke ta ji sallamar Al'ameen ta mishi sallama akan za ta ƙira su ƙarasa maganar. Fita tayi ta amsa tana mamakin ganin shi cikin wannan lokacin. 'Yana da labari kenan.' Zuciyarta ya bata amsa ta zauna tana karɓar gaisuwar shi. Fuskar shi cike da damuwa take duban shi. "Mami dagaske ne abin da naji labari?" Yace cikin murya cike da karaya. Kai ta ɗaga mishi. "Gaskiya ne Al'ameen, bamu da mafita? Har na rasa ya zan yi, ya dage sai an yi auren nan." Kai ya girgiza yana share gumin fuskarshi. "Ina ƙanwata?" "Tana Nijar wajen Yayana, ka san shi ai Yaya Muhammadu." Kai ya ɗaga alamar ya gane shi ya miƙe. "Shikenan gobe zan zo ki ban address zan je gurinta za mu yi magana da ita." "To shikenan Allah ya kai mu gashi ko ruwa baka sha ba Munirat bata nan." "Kar ki damu Mami ni ma ɗan gida ne kamar kowa." Yace ya fita ta bishi da kallo tare da godewa Allah da ya kawo shi cikin lokacin da dai-dai suke buƙata. Fatan ta gobe in ya samu Nuratu da zancen da take fata ta amince balle ma bata tunanin ba zata ƙi ba dan neman mafita da gujewa auren Mufid. Kai tsaye Al'ameen gidan Amma Jidda ya nufa, anan tayi ta bashi hakuri da bashi goyon baya ya tafi Nijar wajen Yaya Muhammadu suyi maganar auren Nuratu kafin lokaci ya ƙure. *** NIGER. Ƙarfe biyar na yamma Dr Awwab ya isa cikin garin bayan tsaye tsaye da yayi a hanya dan sun tsaya a Geidam da Garin Gada Hanan ta farka tayi fitsari taci abinci kafin yaci gaba da tuƙi. Bacci ta koma kafin su isan. Parking yayi kofar gidan ya sauƙa ya fito da Hanan a kafaɗarshi kafin ya shiga cikin gidan da sallama. Nuratu da take tankaɗen garin tuwo da Nazifa za ta tuƙa ta ji sallamar shi ta ɗago kanta dai-dai lokacin ya shigo ciki Nazifa ta amsa suka haɗa ido. Da sauri ta mayar kanta ƙasa tana mamakin ganin shi cikin wannan lokacin ko nisan hanya baya dubawa. Tun komawar shi bai ƙirata ba ita kuma ba tayi tunanin ƙiran shi ba. "Sannu da zuwa." Ta tsinci muryar Nazifa na masa ta shimfiɗa masa abin zama, ya fara ƙoƙarin zama da Hanan ya kasa ya kalli Nuratu da ta gama ta miƙe tana karkaɗe jikinta. "Noor zo ki karɓeta ki kwantar." Babu musu ta isa wajen ta saka hannu ta karɓeta, garin haka fatar hannunsu ta haɗu ta ji wani yarr, kaɗan ta sake Hanan a ƙasa ta ji yace. "I miss you Babyna shi yasa na zo ganin ki musamman. Na kasa hakurin rashin ki kusa da ni." Ba ta mishi magana ba amma kaɗan ya hana ta sakar masa ƴa jin abin da yace, dakyar ta samu ta karɓi Hanan ta wuce ciki ta kwantar ta, ta fito ta samu Nazifa ta kawo masa ruwa a randa mai sanyi cikin kofin silba, duk tsamaninta ba zai sha ba sai ta ga ya kafa baki ya sha sosai. "Ina Kawu da Mama na ji gidan shuru." Ya tambaye Nuratu bayan ta zauna kusa da shi a saman kujera. "Kawu sai yayi sallar magriba yake dawowa, Mama Yawuro ta shiga maƙota barka. Ya hanya?" "Allahamdulillahi hanya sai kewar ki Noor, babu waya babu number ki, ke kuma baki ƙira ni ba, kina ja min aji Noor. Shine tayi taktaki na zo zance gurin ki." Ya ƙarasa maganar yana aika mata murmushi mai tsada da take jin zuciyarta yana amsa. Idanunta ta ɗauke bayan kallo ɗaya da ta masa, na shi idon cikin nata kamar kullum yana son kallonsu. "Kun sha hanya, ina Ummi?" Ta faɗa tana kawar da maganarsa na farko. "Allahamdulillahi lafiyarta ƙalau." Daga haka tayi shiru ganin haka ya miƙe. "Bari in shigo da kayan Hanan." Ya faɗa yana fita ya shigo da kayanta da katan katan na drinks da ya kawo da kwalin indomie da su madaran gwangwani dan ya tsaya yi musu tsaraba a hanya rasa mai zai saya kawai ya saya wannan. Baki Nuratu ta sake tana bin shi da kallo har ya gama shigo da shi ya dubi Nazifa cikin harshen fillancin yace. "Zo ki kai kitchen." Tsaf ta jide ta kai kitchen kafin Nuratu tayi magana ya nufi waje yana cewa. "Na tafi masallaci in an yi sallah zan dawo hira, kimin kwalliya Babyna." Tana kallo ya fita ta kasa kwakkwaran motsi har ya fice da kyar ta ja ƙafarta ta zauna saman abin shimfiɗar da ya ta tashi tayi tagumi. Dr Awwab ya shammace ta sosai, lamuran shi na burgeta a rayuwa musamman kwanan nan da yake saka zuciyar jin wani abu da ta kasa tantance menene hakan yake nufi. .... To fa ga Dr Awwab ya zo ga Yaya Al-ameen yana hanya? Ko waye me rabo? Col. Ahmad fa shin ya hakura? #vote #comments #share MADUBIN GOBE  34. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Sai bayan sallar isha'i, Kawu Muhammadu da Dr Awwab suka dawo gidan da Musalle. A tsakar gidan aka shimfiɗa musu taburma biyu dan kunya ya hana Dr Awwab zama kusa da shi. Nuratu da Hanan a saman baranda tana bata abincin bayan farkawarta ta ganta wani gida daban tare da Nuratu ta rumgumeta, bini bini duk in da tayi tana binta tace yunwa take ji ta zuba tuwo miyar kuka ta fara bata, ta ɗauka ma ba za taci ba sai taga har neman ƙari take. Idanu ta ɗago suka haɗa ido da hasken lantarki da ya haska wajen da farin wata ya basu daman ganin fuskar juna, Dr Awwab ya ɗaga mata gira tare da sakar mata murmushi, da sauri Nuratu ta mayar kanta kan Hanan da take cewa. "Aunti ki bani na cinye." "Ɓingel ma? (Yarinyar ka?)" Kawu Muhammadu ya tambayi Dr Awwab cikin harshen fillanci bayan sabon gaisuwa da su kayi. Dama fulani ba dai afkin gaisuwa ba ayi a sake. "Eh ita ɗaya ce, rigama tasa min sai ta biyo ni." Ya mayar masa da amsa ta nashi fillacin. "Yayi kyau. Ashe dama kana da iyali?" Girgiza kai Dr Awwab yayi. "Yanzu dai babu sai fatan samu. In har za'a bani?" Ya ƙarasa maganar ƙasa ƙasa cike da kunya. Murmushi Kawu Muhammadu yayi fahimtar maganar Dr Awwab. "Insha Allah za'a baka in ka shirya." Da sauri Dr Awwab yace. "A shirye nake ko yau wallahi Kawu. Ta ƙi bani dama ne." Dariya Kawu Muhammadu da Musalle suka saka ganin ya basu amsa da sauri. Halin Dr Awwab ya burge shi, duka duka sau biyu ya zauna dashi amma ya yaba da halin shi da nutsuwar shi. "Za mu yi maganar da safe. Musalle kai shi ɗaki yaci abinci kasan dai ba zai iya ci a nan ba gaban suruki." "Allah ya kaimu. Nagode." Dr Awwab yace ya miƙe cike da kunya ya bi bayan Musalle zuwa ɗakin shi. Bayan wucewar Dr Awwab, Kawu Muhammadu ya kalli Nuratu da ta gama bawa Hanan abinci tana wanke hannunta. "Ke Nuru zo ki kai mishi abinci." Babu musu ta isa gurin ta ɗauki kayan abincin da Mama Yawuro ta jere a tray ta wuce ɗakin Hanan ta biyo bayanta da sauri. Cikin sallama ta shiga ɗakin Hanan tana ganin mahaifinta ta isa gurinshi ta rumgume ya zaunarta jikinshi tana cewa. "Aunti Noor ta bani abinci mai daɗi." "Dagaske?" Yace yana kallon Nuratu da ta ajiye abincin ta kasa tashi kuma. Ya mayar kallonshi kan Hanan. Kai ta ɗaga mishi ya ajiyeta a gefe ya miƙe ya nufi gurin Nuratu. Tana ganin haka ta miƙe da sauri ya tare hanyar ta ja baya tana watsa mishi harara da manyan idanunta da hasken kwan lantarki ya haska fuskarta ya bashi damar ganin haka. "Wannan kallon yana hanani nutsuwa Babyna." Rai ta haɗa tana neman bin gefe ta wuce ya saka hannunshi ya tare ta turo baki. "Dan Allah ka bani guri in wuce, Hanan tana kallon mu fa." Kallonshi ya kai kan Hanan da ta zuba musu ido, yayi murmushi ya juya yana kallon Nuratu da ta kawar da kanta gefe yace. "My Love je ki waje ki jira Aunti, Daddy zai yi zance da Babyn shi." Juyowa Nuratu tayi idonshi a kanta. "Me haka dan Allah kai ko kunya baka ji. Ni ka daina ƙira na da Baby dan Allah." Ganin Hanan ta fita ya sashi matsawa kusa da Nuratu sosai, ta ja baya ta haɗu da gini, tsoro ne ya ziyarci zuciyarta, muryarta har ya fara rawa tace. "Me haka dan Allah in wani ya shigo fa." "Soyyaya ce Babyna. Yau dai rana ɗaya ki bari muyi hiran masoya." Yace yana bin fuskarta da kallo. Rai ta haɗa kamar za tayi kuka tace. "Dan Allah ka bar ni in wuce." "Sai kin ce kina so na." Ya bata amsa har lokacin yaƙi matsawa ta wuce. Jin abin da ya faɗa ya sata kallon shi, idonshi cikin nata ta ɗauke da sauri dan wani kallo da ya aika mata. "Ba zaki faɗa ba? Zamu kwana a haka kenan Babyna." "Dan Allah kayi hakuri. Ni wai ce maka a kayi ina sonka? Ko ce maka a kayi zan aureka? Na faɗa maka babu aure cikin rayuwar Nuratu." Bai ji haushin kalamanta ba ya san duk cikin ruɗu ne kuma ta kasa bawa zuciyarta daman duba abin da take so. But soon zai tabbatar mata da haka. Matsawa yayi gefe ya bata guri ta wuce. "Shikenan sai da safe." Ta tsinci muryar sa cikin sauri ta fita a ɗakin, ta samu filin gidan kowa ya shiga ɗaki dan sanyi da ya sauƙo, ɗakin da take kwana da Nazifa ta shiga ta samu ta kwantar da Hanan ta sauya mata kaya zuwa na bacci, ita ma kwanciyar tayi gefenta, Hanan ta da idonta biyu ta matsa kusa da Nuratu ta shige jikinta, jin haka ya saka Nuratu rumgumeta a jikinta. "Aunti mai Daddy ya miki?" "Babu komai, kiyi bacci." Tace ta rumgume yarinyar tana ji bacci ya ɗauketa. Tunani ta faɗa sai taji kwata kwata bata kyauta mishi ba, shi da yake tasowa daga can wani gari dan ita ta tsaya mishi wulaƙanci. Da safiyar ƙarfe tara ya shigo cikin gidan bayan Kawu Muhammadu ya sameshi da asubanin ranar sun tattauna, sun jima suna magana kafin su rabu. Har ya mishi godiyar kayan abinci da ya kawo yace babu komai. Cikin shirin tafiya ya shigo ya gaisa da Mama Yawuro. Hanan da ke cikin ɗaki taji muryar Daddyn ta ta fita da sauri cikin kwalliyarta da Nuratu ta mata. Sanin da wuri zasu wuce ya sata ɗumama ruwan zafi ta mata wanka ta shiryata cikin kayanta ta haɗa sauran da ta cire ta saka a jakanta. "Zamu wuce Mama kar dare ya mana a hanya." Dr Awwab yace bayan sun gaisa da Mama Yawuro. "To Allah ya kiyaye muna godiya. Kun yi sallama da Kawu Muhammadu?" "Eh mun yi." Yace ya kai idonshi kan Nuratu da ta fito ɗauke da jakan kayan Hanan, bai jira ta ƙaraso wajensu ba ya fita ganin haka ta bi bayansu har waje. Ya saka Hanan a front seat ya zagaya ya shiga. "Ina kwana?" Nuratu tace tana rufe ƙofar baya da ta saka jakan Hanan. "Lafiya ƙalau Babyna. Ya kika tashi?" Ita dai bata son wannan sunan da yake ƙiranta dashi sai kace ƙaramar yarinya. Duk tsammaninta yayi fushi kan abin da ta masa daren jiya sai taga akasin haka. "Sai na dawo." Yace ya kunna motar yana barin gurin cike da kewa Hanan tana ɗaga mata hannu. Haka ta koma cikin gida. Tafiya yake farin ciki yana ratsa zuciyarshi tuna maganar da Kawu ya zo masa dashi da asuba. Cike da farin ciki Dr Awwab ya yi godiya sosai dan bai taɓa tsammanin haka lokaci ɗaya ba, bai taɓa tsammanin zai samu Nuratu a kwana kusa ba. Har musayar lambar waya su kayi har lambar Alhaji Inuwa ya bashi kafin su rabu. *** Al'ameen Pov. Tun asuba ya ɗauki hanyar Nijar akan yana son isa komai cikin dare hakan bai samu ba dan matsalar mota da ya samu a Babban Gida. Sai yamma lis ya shiga Geidam hakan yasa ya kwana da safe ya ɗauki hanya. *** MAIDUGURI. "Ummi na samu Baffa mun yi magana da shi, na sanar da shi akan ranar asabar nake buƙatar mu je, ya sanar da ni babu komai." "Kana ganin babu gaggawa cikin lamarin nan Awwab?" Ummi tace dan Dr Awwab bayan dawowarsa ya sanar da ita maganar da su kayi da Kawu Muhammadu. Bayan sun gama maganar ta turashi wajen baffansa, yanzu yake sanar da Ummi yadda su kayi. Kai ya girgiza. "A'a Ummi kiyi addu'a kawai." "To Allah kaimu ya sanya alheri." Da ameen ya amsa ya tashi ya wuce gidanshi. *** Azahar ya shiga cikin garin dan sammako da yayi, lambar wayar da Mami ta bashi na Kawu Muhammadu ya ƙira ya sanar da shi wanene bayan ya saya sabon Simcard da katin waya. "Bari azo ɗaukar ka zan turo yaro." Kawu Muhammadu yace bayan sauraran bayanin shi. To Al'ameen ya amsa da shi ya kashe wayar ya zauna zaman jira. Mintuna ashirin wayar ya ɗauki ƙara ya ɗauka Musalle ya sanar da shi ya iso ya fita suka haɗu suka koma motar kafin su nufi gida. Sai da ya huta yayi sallah yaci abinci ya gaishe da Mama Yawuro kafin ya zauna jiran Kawu Muhammadu zuwa dare dan baya nan. Nuratu ba ta da labarin zuwan shi sun fita kasuwa ita da Nazifa. *** DAMATURU. Mufid party daban daban yake haɗawa shi da abokansa Faisal da AA, Daddyn shi ya sanar dashi an rage kwanakin auren shi da Nuratu saura kwana biyar, in da hakan ya sashi amsar kuɗi wajen mahaifinsa miliyoyi kusan biyar da ya bashi damar wasa da su. Party yafi kala biyar suka shirya, sun gayyaci abokansu da su kayi karatu a tare. Wanda tun daren jiya suka fara gudanar da shi. Har office ya kaiwa Sufyan invitation card mijin Rukayya yana ta mamakin wannan aure da Rukayya bata da masaniya da ta sanar da shi. Kasa barin abin yayi a ranshi ya samu Rukayya da dare ya sanar da ita. Tana kwance tana kallo jin bayanin mijinta ta miƙe cikin sauri tana kallonshi. "Ba dai Nuratu tamu ba Lovely?" "Ga IV ɗazu ya kawo min office, nima nayi ta mamaki ban tsamman ita bace, amma na kasa barin abin a rai na." Yace yana miƙa mata IV da ya shigo dashi falon ta karɓa cikin gaggawa. Sunan Nuratu ta gani ɓaro ɓaro tare da Mufid za'a ɗaura aure ranar asabar ƙarfe ɗaya da rabi bayan sallar azahar a cikin gidansu. "Ba zai yiwu ba." Tace tana yaga IV ta laliɓo wayarta ya kwace. "Me za kiyi." "Mami zan ƙira na san bata da labari wallahi. Wannan shegen yaro tsinannen ɗan iska Abba zai haɗa aure da ita. Baya tuna ko halin da ya jefata ciki zai ɗauki aurenta ya bashi. Anya Abba yana tsoron haɗuwar shi da Allah na tauye mata haƙƙinta da yake kanshi." Da sauri Sufyan ya toshe mata baki kar ta kwasa zunubi. "Kar kice komai Lovely, mahaifinki ne. Tabbas Mami bata da masaniya amma ba haka lokaci ɗaya ya kamata ta sani ba. Ki ƙira Aunti Rahma da Hasiya kuyi magana in ya so sai gobe kuje ku sameta dan samun mafita. Amma yanzu sai ki hanata bacci ai." Hawayen da ya zubo mata ta share tana gyaɗa kai ta ƙira Aunti Rahma, a nutse ta sanar da ita abin da ta samu labari. Tashin hankali da ta shiga tace za ta je gidan ta samu Mami ta sanar da ita, Rukayya ta hanata ta sanar da ga yadda su kayi da mijinta ta amince. Bayan ita ta sanar da Aunti Hasiya gobe su haɗu a gidan Mami akwai maganar da za suyi ta ɓoye mata gaskiya gudun tashin hankalinta ita ma. *** NIGER. Da daren Kawu Muhammadu da ya dawo kafin suka gaisa da Al'ameen yana tambayarshi hanya da kuma wajen mahaifiyarshi kasancewar ya ganeshi kuma ya bayyana masa kanshi. "Lafiya ƙalau Kawu duk suna gaishe ku." "Sosai muna amsawa. Kun haɗu da ƙanwar ka." "A'a wallahi Kawu." Al'ameen yace da saurin shi. "Ikon Allah ɗazu sunce za su tafi kasuwa da Nazifa, ko dai sun biya wani gurin." "Hakane dama gurinka na zo Kawu, magana ce akan Nuratu." "To ina sauraron ka." Kawu Muhammadu yace yana sauraran bayanin Al'ameen har ya gama. Tun farkon haɗuwarsu da soyayyar da su kayi da Nuratu har zuwa abin da ya faru ya dakata har zuwa yanzu da ya dawo da niyar aurenta. "Ai kuwa mai suna an yi ba'a yi ba an raka bako ya dawo. Domin na tura wancan Likitan gurin mahaifinta duk da ya ce ya mata miji, za su samu yayanshi za'a yi abu ɗaya. Jiya jiyan nan ya tafi, yaron sai zirga zirga yake a kanta kuma ga abin da yake shirin faruwa, kawa na yanke hukuncin ya aureta." Idanuwansa kaɗai zaka gani ka hango tsantsan tashin hankali da ya shiga, girgiza kai yake alamar kar hakan ya kasance gaskiya ya kasa magana. Kawu Muhammadu da jikinshi yayi sanyi jin shima Al'ameen ɗin yana so sai dai Allah ya riga ya saka ba matar shi bace yace. "Hakuri za kiyi mai suna ka karɓi ƙaddara, Allah ya riga ya rubuta hakan sai ya faru shi yasa tsawon shekaru aure bai yu a tsakaninku ba." Nasiha sosai Kawu Muhammadu ya yi ta yi wa Al'ameen na yarda da ƙaddara har ya ji zuciyarshi yayi sauƙi daga raɗaɗin da yake ji. Haƙiƙa ya so Nuratu tun ba yau ba ya so aurenta musamman yanzu da rayuwarta ya shiga wani hali dan ya share mata hawayenta ya nuna mata itama mace ce kamar ko wace mace mai ƴan ci. Sai da yaji zuciyarshi ya samu nutsawa ya ɗago idanuwansa yana kallon Kawu Muhammadu da shi. "Haƙiƙa Kawu na so auren Nuratu, na so ganin na share mata hawaye amma Allah ya riga ya rubuta ba ita bace matata, ba ni bane mijinta. Allah yasa haka shi yafi alheri, Allah ya basu zaman lafiya." "Ameen ya Allah. Ina ƙara baka hakuri mai suna." Kawu Muhammadu yace cikin sanyin jiki hakan bai mishi daɗi ba kwata kwata ko dan mahaifiyarshi da ta riƙe ƴaƴan ƙanwar sa. Suna cikin haka Nuratu da Nazifa suka shigo da sallama, runtse idanuwansa Al'ameen yayi jin muryarta ya san da wuya ya mance Nuratu da soyayyarta a cikin ranshi. Kawu ne ya iya amsawa Al'ameen ya miƙe. "Zan je in dawo Kawu." Kai ya gyaɗa masa ya fita bai ko kalli in da Nuratu take ba da ta bishi da kallon mamaki ganin shi wannan lokaci kuma yaƙi tsayawa su gaisa ya nuna tamkar bai ganta ba. "Kawu yaushe ya zo?" Ta tambaya tana ajiye abin hannunta. "Tun safe ya zo." Ya bata amsa maimakon ya ga damuwa tattare da ita sai yaga akasin haka yana mamaki. Sai ya ji ranshi yayi sanyi ganin kamar ita bata ma damu dashi ba shi yake son, ya ga alamar tafi shiri da Dr duk da shima tana nuna masa hali. ... Da safe Al'ameen ya ma Kawu sallama ya tafi bai jira ya yi wa Nuratu magana ba. Da ta farka ta ji labari sai ta ji abin bai mata ba, ta ƙira lambar shi har ya gama ringing bai ɗauka ba ta hakura. Sai da ya isa gida ya huta ya sanar da Amma Jidda yanda su kayi, ba ta ji daɗi ba sosai abin da su kayi, Al'ameen yayi ta kwantar mata da hankali ya nuna mata shi fa ya hakura. Yanayin sa take kallo har wani yar rama yayi. "Al'ameen zan samu Mami muyi magana ta sanar sa Dr Awwab ya hakura kawai." "Amma na hakura fa babu kyau neman aure cikin aure kin sani." Yace yana girgiza kai zuciyarshi cike da damuwa fuskarshi ɗauke da murmushin dole. "Shikenan Allah sa shine mafi alheri." Ameen ya amsa dashi ya miƙe ya wuce ɗakin Muhsin da yake sauƙa ya mayar nashi. Sai lokacin ya ji son ƙiran Nuratu ya ɗauki wayar shi ya ƙira numbern da ya gani na Nijar ya san nata ne. ... Tana zaune tana figar yakuwa da za su ɗaura abincin dare dashi ƙarar wayar ya ankarar da ita daga tunanin da ta shiga na son ƙiran Dr Awwab ta tambayeshi sun isa lafiya kuma maganinta ya kusa ƙarewa zuwa wani sati tana buƙata. Ɗauka tayi ta ga Yaya Al'ameenn ne ta kara a kunnenta tare da sallama. "Ƙanwata!" Ya faɗa mata kamar kullum ta amsa da. "Ina wuni Yaya Al-ameen ya hanya? Zuwa babu sanarwa kuma ko ka tsaya mu gaisa ka koma." "Wani uzuri ya taso min. Ya kike?" Ya faɗa yana ƙoƙarin danne abinda yake taso masa. "Lafiya ƙalau ina Amma?" "Tana lafiya. Shikenan sai anjima zan ƙira ki wani lokaci." "To sai na gani." Tace ta kashe ta ajiye wayar, muryarshi ya canza mata da yanayin shi gaba ɗaya. *** DAMATURU. Ƴan matan Mami sun sata gaba daga mai faɗa sai mai hawayen abin da mahaifinsu ya aikata, daɗin su ɗaya da Mami ta sanar da su yadda su kayi da Kawu Muhammadu akan Dr Awwab da ya ƙira ya sanar mata komai, ta ji daɗi amma har ranta ta so Al'ameen aka bawa wannan damar dan irin son da ta ga yake yi wa Nuratu. Sannan ta gargadesu kar su sanar da Nuratu dan bata da labari kuma za tace ba za tayi auren ba ya zama anyi gudun gara. Sosai sun ji daɗin hakan musamman Aunti Rahma tace. "Wallahi dama sonta yake. Kin ga yadda yake zirga-zirga bawan Allah ta dinga masa wulaƙanci. Ashe shine mijin." Hasiya da ta cika tayi fam jin abin da ubansu yayi da yanzu sun fara ganin baƙin shi ta ƙara da. "Ai wallahi ya burge ni. Ita ma banza sai kace a kanta aka fara ƙaddara. Ai da Mufid ɗin ne ma ya ɗan cimin kaniyarta." Dariya suka kwashe dashi ban da Mami, Rukayya tace. "Amma wallahi ina tausayin Yaya Al'ameen, shi ma yana sonta tun ba yanzu ba. Allah sarki yayi ta dakon so." "Rabu dashi shima bashi da niyar auren, masu niya sun fito da su za'a yi." Aunti Hasiya tace dan dama bata son soyayyar su tun asali faɗa ne taƙi. Har dare suna gidan kafin su mata sallama su tafi mazajen su su kazo ɗaukar su. .... Bayan kwana biyu ya kama ranar asabar. RANA BATA ƘARYA. .... #vote #comments #share. MADUBIN GOBE  35. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... Da safiyar ranar asabar ƙarfe goma dai-dai Alhaji Inuwa ya samu ƙiran Dr Awwab da mutanen shi sun iso. Tun daren jiya ya iso gidan Alhaji Mamman zaton Alhaji Mamman duk dan auren Nuratu da Mufid da za'a ɗaura ne safiyar gobe. Gidan duk ya cika da mutane abokan Alhaji Mamman da ya gayyato su dan zuwa shaida ɗaurin auren Nuratu da Mufid. Alhaji Inuwa na zsune yana duba agogo burin shi Dr Awwab ya ƙira shi kar lokaci ya ƙure musu kamar yadda suka ɗiba ya samu ƙiran da shigowar su kenan. Cikin sauri ya ɗauka ya musu kwatancen gidan kafin ya koma ya samu ana haɗa haɗar ɗaura aure Alhaji Kashim ya iso da nashi mutanen. Ciki har da Mufid da yasha bakin yadi da ya amsa sunanshi dan kuɗi da aka zuba aka kwashi kayan, yayi kyau sosai kamar ba ɗan shaye-shaye Mufid ba, dan ma daren jiya sai da su kayi tatil dakyar yau ya samu ya farka ya shirya ya taho sai washe baki yake Faisal da AA suna mara mishi baya. Alhaji Inuwa da ya iso yana jiransu Dr Awwab ya dubi ƙaninshin Alhaji Mamman yace. "Mamman ka ɗan ban lokaci akwai bakina da za su iso cikin ƙanƙanin lokaci." Ganin idon jama'a da kuma yayan shi ne ya sashi cewa. "Shikenan Yaya amma suyi sauri, mahaifin yaron nan sun iso tun ɗazu." Sallamar Alhaji Abubakar ne da mutanen shi ya hana Alhaji Inuwa magana ya tashi ya tare su suka ƙaraso cikin babban falon da yake cike da mutanen da za su shaida auren. Dr Awwab da yayan mahaifinshi Alhaji Abubakar da abokinsa ɗaya da abokin marigayi Alhaji AbdulRamat mahaifi ga Dr Awwab su huɗu. Alhaji Mamman da Alhaji Abubakar kallon kallo su kayi a junansu, Alhaji Mamman na tunanin ina ya san malallakiyar fuska mai irin nashi. Zuciyarshi ya kasa bashi macece ko namiji? Babba ne ko yaro?. "Ga baƙina. Bismillah Docter ku zauna." Alhaji Inuwa yace yana nuna musu kusa da Alhaji Mamman suka zauna tare da gaishe da mutanen wajen alhazzai masu ruwan kuɗi abokai ga Alhaji Kashim da su kazo shaida ɗaurin auren tilon ɗan sa. Mufid ido kawai ya sakawa Dr Awwab cikin bakin gilashin da ke manne a idanun shi, ya gane shi shekaru huɗu da suka wuce shine Docter da ya bada shaida a kotu shi ya kula da Nuratu bayan barinsu nan. Dole ya masa godiya in an gama ɗaurin auren shi da Baby Noor. Dr Awwab yayi kyau cikin farin yadin da ɗinkin ya zauna a jikin shi, hula da yake saman kanshi da farin gilashin dake manne a idonshi ya fitar da kyan kyakkyawar fuskarshi. Fuskarshi ba zaka bambance wani yanayi yake ciki ba, babu fara'a kuma ba'a haɗe ba. "Ayi shuru za'a fara gudanar da ɗaurin aure." Faɗin mutane masu roƙo dan samun nutsuwar mutanen gurin. Tuni guri ya ɗau shuru kowa ya zuba kunne. Gefe ɗaya Alhaji Inuwa da Dr Awwab da yake kusa da Alhaji Mamman ta damanshi, gefe ɗaya kuma Alhaji Kashim da yake hannun hagunshi dasu Mufid. "Mamman." Alhaji Inuwa ya ƙira sunan shi da ya saka gurin gaba ɗaya sauraron mai zai faɗa har shi kansa Alhaji Mamman ɗin ya amsa. "Mamman ka ɗauke ni matsayin uba kamar yadda mahaifin mu ya faɗa maka kafin rasuwar shi ka ɗauke ni tamkar shi, ka min biyayya kar ka saɓa umarni na, in har ka saɓa hakan to ka tabbata yana fushi da kai haka Mama ma maganarta na ƙarshe a duniya in za ka tuna." "Yaya mai ya kawo maganar nan ana cikin shirin ɗaura aure." Alhaji Mamman yace ƙasa ƙasa da wanda suke kusa duk sun ji kasancewar falon an yi shuru. "Shine dai Old man ka bari daga baya kuyi komai." Faisal yace Mufid ya watsa masa wani kallo bayan ya cire gilashin idonshi. "Rufewa mutane baki." Girgiza kai Alhaji Inuwa yayi. "Na isa inyi iko da kai in baka umarni. Tambayar ka nake?" "Sosai ma Yaya. Menene kuma?" Alhaji Mamman cije da tashin hankalin da yake taso masa. Ajiyar zuciya Alhaji Inuwa ya sauƙe ya juya ya kalli Dr Awwab da kan shi yake ƙasa yana jin komai. "In har na isa da kai ka bawa Dr Awwab auren Nuratu yanzu kuma a ɗaura aure, in kuma ba haka ba, ka sani babu ni babu kai sannan ka sani har abada ina fushi da kai. Kar ka manta maganar Baba." "Akan me Yaya? Me yasa zaka min haka? Ga can yaron da na zaɓa mata zai aureta mai ya kawo wannan maganar dan Allah?" Alhaji Mamman yake wannan tambayoyin cikin tashin hankalin jin furucin Yayanshi baya ma jin maganganun da ya kaure a falon. Alhaji Kashim na bin Alhaji Mamman da wani kallo, Mufid da abokansa na kudunduma ashar da wasu suka saki baki suke gani suke ji. Alhaji Inuwa ko a jikinshi yana duban Alhaji Mamman. "Umarni na baka in har zaka iya, in kuma a'a shikenan." "Ba zan iya ba." Yace yana girgiza kansa. Shi ya zai yi? Ya zai yi da Alhaji Kashim da Mufid? Kuɗin da suka bashi fa? Ko matsayi da suka ƙara masa? Ba zai iya mai da ko ɗaya ba sannan ba zai iya bin umarnin yayan shi ba amma yana gudun fushin mahaifinshi da ranar haɗuwar shi da Allah. Miƙewa Alhaji Inuwa yayi, dama ya san da kyar Alhaji Mamman ya amince. "Shikenan Mamman amma ka sani babu ni babu kai har abada kar ka ƙara zuwa in da nake ko nuna ka sanni har abada na faɗa maka. Hatta ƴaƴan ka. Sannan ka shirya karɓar tsammaci bisa tauyewa yarinya haƙƙinta da kayi tsawon shekaru ni da kai babu sani babu sabo." Daga haka ya juya ya kalli Dr Awwab da Alhaji Abubakar da mutanen sa da abun ya zama musu wani iri. Can kuma Mufid da Alhaji sun daina zage zagensu jin Alhaji Mamman yaƙi amincewa. "Mu je Docter." Yace yasa kai zai fita suka miƙe, Dr Awwab ya kasa dan ji yayi kafafunsa sun kasa ɗaukar shi. Yana ji yana gani zai yi asaran Nuratu. Ina! Yace har maganar zuci ya fito fili ya matsa kusa da Alhaji Mamman. "Dan Allah Baba kar ka hanani aurenta, Noor bata dace da wannan yaron ba." Kallon shi Alhaji Mamman yayi kyakkyawan saurayi matashi da ba zaka rantse yayi auren fari ba ko shekarun sa sun haura talatin ba, ya gane sarai. A sanya juya ya kalli yayan shi da yake shirin fita maganganun shi ɗaya bayan ɗaya na dawo masa suna masa yawo a kai. Da sauri ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Na amince Yaya zan bashi ka dawo dan Allah kar na haɗu da fushin Baba." "Akan wani dalili." Cewar Mufid yana buga wani tsalle ya shiga tsakanin su, Alhaji Kashim ya miƙe shima yana cewa. "Saboda mai yasa? Ka san dai mai zai biyo baya." "Alhaji za muyi magana daga baya." Alhaji Mamman yace da yaji gwara ya mai da masa da arzikin sa da ya haɗu da fushin Allah da mahaifin sa. 'Wannan yarinya masifa ce.' Yace a ranshi yaji ya ƙara tsanar Nuratu. "Ba zai yiwa ba!" Alhaji Kashim yace cike da masifa jin za'a hana tilon ɗan sa cikar burinshi bayan shiri da suka shirya shi da Ummu. Alhaji Inuwa da ya dawo baya shi da Alhaji Abubakar da mutanen shi ya dubi Alhaji Kashim ya masa wani kallo. "Za ku iya bamu guri Please." Ashar Alhaji Kashim ya danna mishi ko kunyar mutanen gurin bai ji balle ɗan shi da abokan ɗan shi. "Ka amince kanan?" Alhaji Inuwa yace da Alhaji Mamman da ya zama mutum mutumi tsabar baƙin ciki ya cika zuciyarshi da tsanar Nuratu. Kai kawai ya ɗaga, Alhaji Inuwa yayi murmushi yana duban Alhaji Abubakar. "Alhaji ka amince za ka karɓawa yaronka auren Nuratu Mamman Bashir." Alhaji Abubakar da sai yanzu ya saka baki yace. "Abubuwan da ke faruwa akwai ɗaure kai, ina bukatar sanin wasu abubuwan duk da na fahimci in da maganar ya fara dosa." "Baffa dan Allah ka ce ka amince abar ko wani magana daga baya." Dr Awwab yace cikin sauri bayan ya cire kunya ya ajiye a gefe. Kallon shi kawai Alhaji Mamman yake jin muryar Alhaji Abubakar irin na wanda fuskar ke masa gizau ne, hatta muryar iri ɗaya da har lokacin ya kasa tantance ina ya san malallakiyar fuskar. Murmushi Alhaji Abubakar yayi da ya ƙara jefa zuciyar Alhaji Mamman ruɗani da tunani yace. "Shikenan na amince." "Kun fito da kuɗi?" Alhaji Inuwa ya buƙaci sani. "Eh akwai." Alhaji Abubakar yace yana saka hannu cikin aljihunsa ya ciro kuɗaɗen ciki. "To ku biya sadaki a ɗaura aure kawai tun da mahaifin yarinya ya amince ya bada ita ni zan zama waliyanta ga shaidu su shaida ɗaurin aure." "Wallahi baku isa ba sai na kashe ka in ka auri Baby Noor." Mufid ke wannan hargowan aka riƙe shi Faisal da AA cikin sauri ganin yayin kan Dr Awwab. "Mu tafi Faisal ku sashi a mota. Mamman ka shirya haɗuwar mu" Daga Alhaji Kashim yace ya kaɗa babban rigarshi ya sa kai ya fita Faisal da AA su ka bi bayansu suna riƙe da Mufid da ashar kawai yake ɗurawa son ranshi yana cewa sai ya kashe Dr Awwab in har ya auri Nuratu. Mutanen Alhaji Kashim ganin wanda su ka zo dan shi ya fita ya sa suka kwashi takalmansu suka fice cike da jimamin wannan lamari, dama mamaki suke wani ubane na gari zai ɗauki ƴarshi ya bawa Mufid sai dai lalatacciya ƴar uwar shi. Kankara kaf kuɗin jikinshi Dr Awwab ya ciro da shi, Alhaji Abubakar ma haka suka haɗa dubu ɗari uku sadaki suka damƙawa Alhaji Mamman da ya ji kamar ya watsar dan bai ɗauke shi kuɗi ba, ga in da za'a bashi miliyan biyar sadaki ya ƙare da dubu dari uku. A gurin a take jama'a suka shaida ɗaurin auren AWWAB ABDULRAMAT da NURATU MAMMAN BASHIR akan sadaki dubu ɗari uku. Alhaji Inuwa ya zama waliyanta Alhaji Musa (Abokin mahaifin Dr Awwab) ya zama waliyin Dr Awwab. Hamdala Dr Awwab yayi ta jerowa cikin zuciyarsa jin an shafa fatihar auren shi da Noor sai kuma diramar da zasu ɗeba in ta ji labari. Idanuwansa ya lumshe ya buɗe yayi murmushi. "Haƙiƙa ka cika min burina Mamman haka ake so ɗa ya bi umarnin iyayenshi ko basa raye. Allah yaji ƙan Mama da Baba." Ameen mutanen gurin suka amsa dashi ya ƙara da cewa. "Bani sadakin zan kaiwa Sadiya ta ajiye mata, arziƙinta ne." Babu musu ya miƙa masa dan bai ɗaukesu kuɗi ba, ya kasa cewa komai kamar wanda aka rufewa baki ido kawai yake zuba musu har suka gama gaisuwa da murna murnan su suka miƙe dukkan su. "Alhaji mun gode Allah ya saka da alheri." Alhaji Abubakar yace yayin da ya miƙe, da kallo Alhaji Mamman ya bishi da shi har lokacin zuciyarshi ta kasa tantance masa malallakiyar fuskar. Yana kallo suka fice ɗaya bayan daya daga falon suna masa sallama har abokansa suka watse kaf, reception da suka haɗa basu samu damar gudanar dashi ba kenan. Ya jima zaune kafin ya miƙe ya nufi cikin gidan sai lokacin bakin shi ya buɗe. "Ni Sadiya za ta wulaƙanta ta tozarta cikin ɗimbin jama'a, ta ciwa fuska cikin taron jama'a a idon duniya, wallahi dai nayi shari'a da ita." Faɗin Alhaji Mamman yayin da yake shiga cikin falon. Amma Jidda da tayi jigum tana jimamin abin da yake faruwa ta ji ya fadi haka ta dubeshi lokacin da yake zama saman kujeran falon. "Mai kuma tayi? Ita kullum cikin laifi." "Wannan yaron shege ta turo da Yaya Inuwa dan ta ci min fuska ta saka ni na bashi auren yarinyar nan, har an ɗaura fa. To wallahi kotu za ta rabamu in Alhaji Kashim ya nemi kuɗin shi dan ita ma sai ta biya." "Dama sai da yar ka yi?" "Ban sani ba Jidda." Yace cikin ɓacin rai ta buga tsaki ta wuce ɗakinta haushin sa take ji, bata taɓa tsammani haka halinshi yake ba. Gefe ɗaya kuma zuciyarta taji farin ciki jin Nuratu bata auri Mufid ba, duk da ta so Al'ameen ya aureta amma Allah bai yi ba. *** "Sadiya ki riƙe ki damƙa mata hannu da hannu dukiyar tane na aure. An riga an ɗaura aurenta da Dr Awwab Allah yayi shine mijinta. Sai ranar tarewa duk lokacin da suka saka daidai ne kar suyi gaggawa." Cike da murna Mami ta karɓi kuɗin tana kallo. Sadakin ƴar ta, ƴarta Nuratu wacce ta cire rai ga aure da zaman aure. "Nagode Yaya Allah ya biya ka da mafificin alheri." "Babu komai wallahi, Nuratu tamkar sauran na ɗauketa infact ma kamar ƴata take nima ubanta ne. Sai abu na ƙarshe duk abin da Mamman zai zo miki da shi kar ki kulashi ki sanar dani. Sannan ke ma ya kamata ki yiwa kan ki faɗa zama ba naki bane, tun da yarintar ki gashi har girma ya zo." Kanta kasa ta girgiza kai da sauri. "Yaya mun barwa yaran dai. Nagode sosai." "A'a Sadiya kiyi dai tunani, ina da wani tsoho ma zan baki." Jin ya maida maganar wasa ta murmusa su kayi sallama ya tafi ta koma cikin falon ta ƙira Yaya Muhammadu ta sanar da shi yadda aka yi. Yayi murna sosai yace nan da sati zai turo Nuratu tun da komai ya daidaita tace to kafin su kashe wayar ta ƙira sauran ƴaƴanta ta sanar da su an ɗaura auren Nuratu da Dr Awwab. Har lokacin ta gargadesu kar su sanar da Nuratu ba yanzu ya kamata ta sani ba suka ce to. *** Dr Awwab bayan fitar su kayi sallama da Alhaji Abubakar ya wuce gidan Mami suka ɗauki hanyar Maiduguri. Suna tafe Alhaji Abubakar ya sako masa tambayar da ya tsaya masa a rai. "Awwab wai mai yake faruwa a wannan iyalin?" Dr Awwab da yake cikin farin ciki ji yake babu mahalukin da ya kai shi farin ciki ya shafa kan shi idonshi akan titi yana jan motar yace. "Baffa mahaifinta wannan yaron yake son aura mata kuma ɗan iska ne, to kowa baya so kuma shi ya dage sai ya aura mata shi, shi wannan yayan shi ne, shine ya dage sai an yi auren da ni." "Allah sarki amma ya kyauta wallahi. Shi kuwa wannan wani irin uba ne." "Baffa sai addu'a kawai." "Hakane kam. Ai naga alaman yaron akwai iskanci a tattare dashi har uban na shi." "Hakane." Dr Awwab yace yaci gaba da tuƙi bai sanar dasu wanene ainihin Mufid ga rayuwar Nuratu ba, dan wannan sirrinta ne da ya kamata a rufe mata har dashi yanzu da ya zama cikon rayuwarta. Shigar yamma lis su kayi Ummi ta tare su cikin mutumci kamar kullum bayan sun gabatar da sallah suka sanar da ita yadda a kayi. "Allah sanya albarka da alheri." Tace buɗan bakinta suka amsa da ameen kafin su mata sallama. Bayan fitar su ta kalli Dr Awwab da yake shirin tashi. "Sai ka fara shirin gyaran gida da kayan akwati." "InshaAllah Ummi, Ikhram da Zaituna zan tura kuɗi su haɗa su taho da shi zuwa kafin nan da a saka ranar tarewar ta." "Hakan ma ya yi." Tace ya fita ko Hanan bai nema ba, gidan shi ya bayan yayi wanka ya daura alwala ya wuce masallaci ya yi sallar magriba ya daɗe yana addu'a da nuna godiyar shi ga Allah kafin aka gabatar da sallar isha'i yayi ya dawo ya zube cikin falon dan huta gajiya ya kunna kallo tare da ɗaukar wayar shi. Missed call ɗin Nuratu ya tarar guda ɗaya da wanda ba za'a rasa ba, ya ƙirata. .... Tana kwance bacci bai ɗauketa ba tana ta buga game da wayar da shi yake ɗebe mata kewa babu kallo ta samu ƙiran Dr Awwab. Zaune ta tashi dan ɗazu ta ƙira ta sanar da shi magungunan ta sun kusa ƙarewa kuma ba zata samu anan ba ya za tayi bai ɗauka ba ta hakura. Ɗauka tayi ta saka a kunne tare da sallama taji yace. *"Babyna."* ... #votes. #comments. #share. MADUBIN GOBE  36. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** *"Babyna."* Dr Awwab ya furta cike da nishaɗi da farin cikin da yake shigar shi a ko wani daƙika. Ɓangaren Nuratu kamar yana gabanta ta ɓata rai tana turo baki tace. "Ni bana so ka daina ƙirana da wata Baby." Yadda tayi maganar da shagwaɓe murya sai da ya saka Dr Awwab runtse idanuwansa ya buɗe, ƙasa ƙasa yace. "Babyna kar ki sa cikin daren nan in taho ganinki." "Ni dai dan Allah ka tsaya in faɗa maka abin da zan faɗa." Nuratu tace cikin sauri jin muryar shi ya canza mata gaba ɗaya, da ya haddasa mata bugawar zuciya. "Ina jinki Babyna faɗi damuwar ki." Dr Awwab yace yana nemawa kanshi nutsuwa. "Magunguna na za su ƙare nan da kwana biyu, kuma babu anan infact ma dai ka san kai kake kawo mini. To zai ƙare." "Ki ce dai kinyi missing ɗina kina son gani na." Da sauri Nuratu tace. "Ni wallahi ba haka bane, Allah dagaske nake maka." Murmushi yayi cike da nishaɗi yace. "Shikenan zan aiko miki zuwa nan da kafin ya ƙare." Shuru Nuratu tayi sai taji kamar bata kyauta mishi ba tace. "To kai baza ka zo ba?" "A'a ina da aikin yi." "Shikenan sai anjima." Tace ta zare wayar a kunnenta ta kashe tana ajiyewa a gefe. Sai ta ji bata kyauta masa ba. ... 'Yarinya ki yarda kin faɗa tarkon so.' Dr Awwab yace yana murmushi lokacin da ta kashe wayar ya ajiye wayarshi yana mai da hankali kan laptop dake gabansa. Sai da ya gama ayyukan da zai yi ciki kafin ya runtsa. *** DAMATURU. Zagi da ashar Mufid kawai yake zubawa cikin falon Ummu bayan buge buge da fashe fashe da ya mata na asarar kayan falo, da kyar Daddy ya bashi hakuri da alƙawarin ƙarya ya masa zai aura masa Nuratu. "Haba babana nace maka kar ka damu in dai yarinyar nan ne zan aura maka ita." A harzuƙe Mufid ya daka Daddyn shi tsawa. "Akan me? Dalla ka rufemin baki, kana gani dai ya bada aurenta a wancan tsami gayen. Wallahi sai na kashe sa." Mufid yace yana zuƙan karan sigari na biyar kenan yana bankawa a cikin shi ko zai ji dai-dai. Ummu da ido kawai ta zubawa uba da ɗan taƙaici kamar ya kasheta abun Mufid ya fara isarta, shaye shaye har gida gabansu, duk da ba yau suka saba kama shi ba amma yau ɗin a gabamsu suna kallo ba yanda za su hana shi. Daddy da shima abin ya fara ci masa rai amma kwanciyar hankalin Mufid ya fi masa komai ya sashi miƙewa. "Ka bani lokaci Mufid zan neme ka dan Allah ban da wani rigimar, kar ka janyomin wani abun ka rabu dashi. Waya sani ma ba'a ɗaura auren ba." Daga haka ya fice Mufid yana ganin haka ya miƙe zai fita Ummu ta tare shi. "Ina za kaje?" "Dalla ki bani guri, in da kika aike ni." Daga haka ya bi ta gefenta ya wuce ta matsa da sauri kar ya bigeta. A buge ya fita ya faɗa cikin motarshi ya nufi club dan neman abun da gusar masa da hankali da samar masa nutsuwa. *** Washegarin yaran Mami su ka zo mata, Rukayya ce ta fara zuwa da ƴan biyunta da sunyi wayo sai ƙaramin cikin dake jikinta babu wanda ya sani sai ita da mijinta. Da gudu yaran su kayi kan Mami ta ɗaga su suka zauna saman cinyarta. Mami kallo ta bi Rukayya da shi yadda tayi wani haske ga ƙiba. "Mami wannan kallon fa?" "Babu komai, mamakin wayon yaran yanzu nake." Tace tana murmushi. Ganin Mami zata sako wani zancen da sauri Rukayya ta miƙe. "Mami mai za'a ɗaura na rana kar wannan yaran masu ci suzo su dame mu da yunwa yunwa." "Ki ɗaura ko ma menene, ci kuma ke suka biyo." Mami tace tana murmushi ganin ta basar da maganar. "Uwarsu dai Aunti Hasiya." Rukayya tace ta wuce kitchen. Bayan sallar azahar Aunti Rahma da ƴaƴanta suka taho bayan an tashi a makaranta ta ɗauko su, Aunti Hasiya da nata yarinyar ta ɗaukota su ka wuce gidan Mami sai da ta tashi a aiki ta biya gidan. Cikin sauri ta shiga ɗakin Nuratu ta ɗaura alwala ta fito ta samu Aunti Rahma na cirewa babynta pampers. "Ya cika da fitsari ko tun safe fa." Ta tambayeta tana ƙoƙarin saka hijab. Kai ta ɗaga mata tana ɗaukar yarinyar su kayi bathroom. Ita kuma ta tada sallah. Bayan ta fito ta canza mata pampers da kaya cikin baby bag dinta ta ɗauketa suka fita, Aunti Hasiya bayan ta gama ta fita ta samesu a falon gaba ɗayan su ta ƙarasa wajen Mami suka gaisa kafin ta zauna Munirat ta kawo mata abinci. "Mami mai kuke shiryawa ne?" Aunti Rahma tace tana bawa Babyn Hasiya kunu, Allah ya ɗaura mata son yarinyar kuma kowa ya lura da hakan, yarinyar bata da kiriniya. Jin zancen da ta sako ya saka kowa caa a akan Mami. Mami tace. "Ni kuwa mai zan shirya, kuyi komai tsakanin ku, bari ita Nuratun ta dawo ta sani kafin komai." "Hakane amma an saka ranar tarewar ta." Aunti Hasiya ta tambaya. Mami ta girgiza kai. "Ni fa ban san komai ba, sai yadda su kayi da Dr Awwab, in ma ta yarda da auren ba. Bana son fushin autana." "Kar ta yarda ɗin, aure an riga an ɗaura sai kuma tayi, shikenan yanzu sai ta dawo asan mai za ayi." Aunti Hasiya tace tana tauna abincin bakinta. Burinsu kowa ya bawa ƙanwarshin gudunmowa kafin ranar tarewarta, su kimtsa ta ko ba komai tayi ƙima a idon mijinta. Har dare suna gidan kafin su mata sallama suka tafi. **** Cikin magagin maye ya shigo gidan tun fitarsa na rana, duk abin da yasha bai gusar masa da tunanin Nuratu ba sai da ya danganta da yiwa kansa allurar kwaya yaji hankalinshi ya gushe ya nufo gida. Allah kaɗai ya kawo shi gida ya shigo cikin falon a hargitse. Ummu da ke zaune ganin har karfe ɗaya bai dawo ba ya sata zaman jiran shi ta ji hankalinta ya kasa kwanciya. Yadda ya shigo mata ya mugun tsoratata ta miƙewa. "Baby Noor." Shine kalmar da Mufid ya faɗa ya nufi Ummu da shi domin idanuwansa gizau suke masa baya gani mai kyau. Ummu da taji abin wani iri ta ja baya zuciyarta na bugawa da ƙarfi. "Mufid ni ce Ummu fa ba wannan shegiyar yarinyar ba." "Baby Noor." Ya sake maimaitawa ya yi kanta. Da sauri ta ja baya duk ƙoƙarin ta nuna masa ita ce mahaifiyarshi abun ya gagara gadan gadan yayi kanta. Ganin babu sarki sai Allah ya sata faɗawa ɗakinta ta kulle da mukulli kafin ta fashe da kuka tana dafe kirjinta da yake bugawa sosai. "Ya Allah wani irin masiface wannan? Wani iri ɗa na haifa?" Mufid kam bugun ƙofar yake yana kiran Baby Noor har ya hakura ya shige ɗakinsa ya faɗa saman gado yana sumbatu kafin wani mahaukacin bacci ya ɗaukeshi. ... Washegarin da safiyar ranar juma'a Alhaji Mamman Bashir ya shiga cikin Companyn su, kai tsaye ofishinsa ya nufa baya amsa ko gaisuwar da ake masa ya san duk gulmace. Abin mamaki ofishin a kulle an canza gurin mukullin, duk yanda yayi ya buɗe kasawa yayi haka yasa ya nufi ofishin Oga Dauda rai ɓace. Ƙwanƙwasa ƙofar yayi aka bashi izinin shiga ya shiga, ganin wanda ya shigo ya saka Oga Dauda haɗa rai yana dubanshi har ya zauna. "Oga mukullin office ɗina naga kamar an canza." Alhaji Mamman yace cikin ƙarfin hali kar abin da yake gudu ya faru. Oga Dauda bai yi magana ba har ya gama maganarshi ya miƙe ya ɗauki doguwar letter cikin envelope ya ajiye gabanshi ya koma ya zauna. "Mun gode da ƙoƙarin da kake cikin Companyn nan tsawon shekaru, amma yanzu bama buƙatar ka a gaskiya. Mun sallame ka." Cikin ruɗu da tashin hankali Alhaji Mamman yake duban Oga Dauda ya kasa kwakkwaran motsi ya kasa ɗaukar envelope ɗin. "Ka ji mai nace ai. You can go out please." "Sir me yasa aka min haka? Me yasa haka? Me nayi? Kar dai kace min Alhaji Kashim ya saka ka aikata min haka." Sai lokacin Alhaji Mamman ya samu bakin furta haka. "Ko ɗaya, ka je kawai ina da abun yi bani da lokacin tattauna wannan maganar." Oga Dauda yace ya miƙe yana barin gurin. Alhaji Mamman ya daɗe zaune cikin ofishin kafin ya miƙe ya fita, ya san duk aikin Alhaji Kashim ne da ba zai iya ja da shi ba, da babu abin da zai hana shi shari'a da shi da, daɗinta ma in ya tuna ya banzar da maganar kuɗaɗen shi da ya ci. Tafe yake cikin motarshi yana tunane tunane, bai san ya iso traffic light ba jan wuta ya tsayar da su ba, sai da ya bugawa motar da ke gaban shi da ƙarfi, da kyar ya tsayar da motarshi kafin ya fito mutanen gurin har sun cika gurin ganin asaran da ya jawowa mai motar gaban shi. Samari ne biyu yan jagaliya cikin motarsu mai tsada suka fito. "Motar Dad!" Ɗaya yace da karfi yana ɗaura hannu a kai. "Wallahi sai ya biya." D'ayan yace yana nufan Alhaji Mamman da ya fito dan ganin abin da ya aikata. "Kuyi hakuri zan biya. Zan biya ku ko nawa ne wallahi." Alhaji Mamman yace da sauri dan ya lura yaran basu da mutumci za su iya masa komai. Ɗaya ne ya shiga motar Alhaji Mamman d'ayan yaja nasu su ka bar gurin bayan mutane sunyi ta tofa albarkacin bakinsu. Kai tsaye gurin gyara suka isa in da suka san mutumin, gyaran da bai fi dubu ɗari ba sai da ya kai su ga gyaran miliyan biyu. Cike da mamaki Alhaji Mamman yake kallon mai gyaran da ya maze yayi tamkar ba daidai ya faɗa ba. "Haba makanike, ko motar za'a canza ai za'a samu na miliyan ɗaya. Wannan gyaran bai fi na dubu sittin ba fa." "To sai ka gyara mu gani." "Ba zai yiwu ba. Wallahi ko ka bada a gyara yanzu ko mu maka shegen duka kuma ka biyamu kuɗin gyara. Ka san waye uban mu a garin nan." D'ayan da ya fisu iskanci yace yana yin kan Alhaji Mamman da cikinsa ya ɗuri ruwa. "Kayi hakuri zan biya ku abin bai kai haka ba." Alhaji Mamman ya faɗa da sauri yana zaro wayarshi. "Transfer zan muku ban da cash." "Hakan ma yayi." D'ayan yace ya bashi lambar asusun bankinsa ya tura masa miliyan ɗaya da rabi. "Wallahi bani da shi ku bini bashin dubu ɗari biyar." Kallon kallo su kayi tsakanin su ɗayan mafaɗacin yace. "An yafe maka Alhaji wannan ma yayi. Mun gode." Ajiyar zuciya ya sauƙe yana cewa. "Nagode nagode sosai." Daga haka ya shige motarshi da shima yana buƙatar gyara ya bar gurin. Sai da su kaga ɓacewar shi kafin su kwashe da dariya. "Oga mun ja kuɗi wallahi." "Sosai ma. Yanzu bari mu gyarawa mai mota motarshi kafin ya dawo, yau akwai cin kaji." Cewar Ogansu yana juyi sun canki kuɗi. Daga sun gama gyaran motar da aka kawo musu suka ɗauka su gwada ya gyaru suka nufi cikin gari tsautsayi ya haɗasu da Alhaji Mamman suka yaudare shi. A birkice Alhaji Mamman ya shiga gidanshi yana saɓaɓi da in mutum bai lura ba baya fahimtar mai yake faɗa. Amma Jidda da ta ga wucewar shi side ɗinshi ta fito ta nufi can. Waya yake da yayanta Alhaji Tukur ta tarar yana sanar da shi halin da yake. Daga can ɓangaren Alhaji Tukur yake cewa. "Kai ma Mamman ka yi gaggawa, sai da aka sanar da kai yarinyar nan babu alheri a rayuwarta amma ka biyewa son zuciya gashi yanzu ta jawo maka asara garin kallo zata zame maka hanyar arziki. Babu aikin babu kuɗi. To kuma kana tsammanin Alhaji Kashim zai bar maka kuɗaɗen da ya baka ne? To wallahi ka shirya haɗuwar ku dashi." "To ni ya zan yi, dubi fa yanzu abin da ya same ni. Kuɗaɗen gurina sun fara ƙarewa gashi kasuwan cin ma ya ja baya. Ni kam yarinyar nan ta zame min bala'i." "To ya za kayi. Haka zaka hakura ka tattara masa kuɗin shi in ya nema ka bashi, gwara ku rabu lafiya dan abin ya wuce haka kasan ba zaku kwashe da daɗi ba. Ni lokacin da ka bani shawara zan hanaka amma tun da yanzu abu ya lalace ka sanar da ni, na baka shawara ka haɗa masa kuɗaɗen shi kafin ya nema ka bashi." "Shikenan Alhaji Tukur zan yi yadda kace." Alhaji Mamman yace su kayi sallama. Wani tsanar Nuratu na shiga cikin zuciyarsa, duk ita ta jawo masa wannan asaran. Zuwan Amma Jidda ya sashi ɗan mance damuwar shi duk da har lokacin tana fushi da shi abin da yayi amma ta ajiye a gefe ganin shima ba'a dai-dai yake ba. *** NIJAR. "Nuru gobe za ki koma gida, kun yi waya da Maman ki?" Kawu Muhammadu ya ke faɗawa Nuratu lokacin da ta zo gaishe sa da safe. Kai ta ɗaga masa alamar eh tana cewa. "Eh jiya ta sanar da ni in dawo." "To sai ki shirya inshaAllah gobe sai kiyi fitar safe dan ki samu isa da wuri." "To Allah ya kaimu." Tace tana miƙewa ta koma. Bayan taci abincin safe tayi wankin kayanta Nazifa na taimaka mata da ɗauraya. "Ni kam Nazifa har zan koma baki kai ni naga kogi ba." "Idan kina so zuwa da yamma sai mu je ai yafi daɗin zuwa." Nazifa ta bata amsa, duk da Nuratu ta girmeta da shekaru kusan uku amma ta ɗauketa tamkar sa'ar ta haka Nuratu ma hankalin Nazifa na burgeta. "Ai kuwa bari in na gama sai mu je." To Nazifa tace suka gama wankin kafin su ɗaura abincin rana, bayan sun gama wajen karfe uku, sallah su kayi kafin su ci abincin suka yi wanka suka shirya. Abaya Nuratu ta saka da ya amshi baƙin fatar jikinta, ba tayi wani kwalliya ba ta feshe jikinta da turare suka fita, tayi kyau sosai cikin abayan daga hoda sai chappate a bakinta. Bakin kogi suka nufa garin babu rana dan sanyi da ya shigo, yamma yayi sosai, a bakin kogin suka tsaya in da babu mutane sosai, Nuratu gurin ya mata kyau ta zubawa cikin ruwan ido ta lumshe idanuwanta iska yana kaɗawa, wani ƙamshi mai daɗi yana shigarta da ya sauƙar mata nutsuwa. "Is so romantic right Baby?" Ta tsinci muryar Dr Awwab cikin kunnuwanta har tsakar kanta da sauri ta buɗe idanunta ta juya in da taji muryar, ganinshi tayi daf da ita sai lokacin ta ankara da ƙamshin turaren shine ya mamayeta. Baya taja kaɗan tana ɗauke idanuwanta cikin nashi tana tambayarshi. "Yaushe ka zo? Ina Hanan?" Ƙara matsawa yayi kusa da ita kaɗan ganin idanunta suna wani gurin yace. "Yanzu zuwana na samu labarin kin zo nan na biyo kayana. My Love tana lafiya, ta so zuwa na hanata kar ta hanani sakewa da Babyna." "Ni bana son sunan nan na faɗa maka." Nuratu tace tana yin gaba ya biyo bayanta da sauri. "Ni ina son sunan. Na faɗa miki ke Babyna ce kin ƙi yarda ko? But soon za ki yarda da hakan." Dakatawa tayi da tafiyar da take ta watsa mishi wani kallo ta ɗauke kanta ya ƙaraso kusa da ita dai-dai lokacin iska ya kaɗa gyalen dake saman kanta zai fita har gashin saman kanta ya bayyana, da sauri ya saka hannu ya cafke gyalen ya mayar mata ta riƙe tana gyarawa. Cikin sauri tayi gaba ta barshi tsaye cike da mamakin ganin kwantaccen gashin da yake kanta, bai taɓa tsammanin tana da tsantsin gashi ba duk da kwantaccen gashin goshi da take dashi, ya ɗauka iya nan ya tsaya. A ranshi yaji kawai yana son ganin jelar gashinta ya ga iya tsawon sa. Bayanta ya bi cikin sauri yana ƙiranta. "Babyna! Babyna." Nuratu kamar ta shige ƙasa dan kunyar sunan da yake ƙiranta da shi ga Nazifa da tayi gaba ta barta. "Ki tsaya ko in na zo na baki mamaki." Dr Awwab yace dole ya saka Nuratu dakatawa ya iso ta. "Kin bani wahala. Mu je to" Yace yana fara tafiya tabi shi. Bata mishi magana ba dole ya sata jerewa suka kama hanyar gidan tare, da ka gansu sun dace da junan sai bambancin launin fata dan Dr Awwab akwai haske. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  37. Pharty Bb Wattpad phartybb. *** Tafiya suke babu wanda yayi magana sai Dr Awwab da sanyi ya ishe sa yace. "Kai garin nan akwai sanyi, Nijeriya bai kai haka ba." "Sai cikin dare ma." Nuratu ta bashi amsa suna cigaba da tafiyar har suka iso gida ana ƙiran sallar magriba. A soron gidan ya dakata yace. "Babyna." Dakatawa Nuratu tayi ta fasa shiga cikin gidan ta tsaya tana juyawa ta kalleshi, ya sakar mata murmushin da bata iya juran kallo ba ta ɗauke idonta. "Kin yarda ke Babyna ce?" Taji maganar shi sai lokacin ta ankara da abin da ta aikata ta juya da sauri ta shiga cikin gida, kwata kwata bata san tayi hakan ba, bata san ta tsaya ba. Haushin kanta ne ya kamata da ta biye masa, ai sai ya tsammanin ta fara faɗawa tarkon shi. Murmushi Dr Awwab yayi bayan shigan ta ciki, ya koma ya riga ya amince Nuratu tana son shi kawai taƙi bawa kanta da zuciyarta daman hakan ne. Yasan ko ta samu labarin da aurenshi a kanta ba zai sha wahalar shawo kanta ba. Sai da su kayi sallar isha'i suka dawo gidan tare da Kawu Muhammadu da Musalle. Kawu Muhammadu yana cewa. "Kai kam dai baka gajiya wallahi, kullum kana hanya, kafin ta zama mata ma kullum kana hanya balle yanzu ta zama matar kam sai ka dawo da aikin ka nan garin." Murmushi kawai Dr Awwab yayi cike da kunya yana sosa kan shi. "Kawu magungunan ta na kawo mata, sun kusa ƙarewa." "Babu wani ka zo dai ganin matar ka, bana son wani gulma a dangana da magunguna. Ita ma gobe zata tafi sai ku tafi tare, na gama daku sai mun zo biki." Sosai maganganun Kawu suka saka Dr Awwab jin kunya amma in ya tuna Nuratu zata koma tare za su tafi yaji daɗin hakan. Da daren duk yadda a kayi Nuratu ta kaiwa Dr Awwab abinci ɗaki ƙi tayi tace kanta yana ciwo aka bawa Musalle ya kai mishi. Da safe ta samu labarin tare za su koma da Dr Awwab kamar tace ta fasa amma ba yanda ta iya haka ta gama shirya kayanta tsaf ta fito da shi ta shirya cikin riga da skirt da babban mayafinta ta yafa a jikinta. Bayan sun yi sallama da ƴan gida suka ɗauki hanya, suna tafe babu wanda ya yi magana har sunyi nisa da tafiya Dr Awwab ya juya yana kallonta hankalinta a kan titi. A hankali ya saka hannunshi ya riƙo hannunta da yake saman cinyarta. A wani mugun tsorace Nuratu ta juya a firgice tare da kwace hannunta ta ja baya, wani shork ta ji a jinin jikinta da ya haddasawa zuciyarta bugawa. Guri ya samu ya faka motarshi ya juya ya kalleta ta takure guri ɗaya. Idanuwansa kawai ya zuba mata wani mugun sonta da kaunarta yana shiga ranshi, ji yake kamar ya rumgumeta a jikinshi su haɗe su zama abu ɗaya. Ganin ya faka motar kuma yaƙi magana ya saka Nuratu kallonshi ta ga idanuwansa yana yawo a jikinta ta haɗa rai. "Bana son haka Docter." "Ina son ki sosai Babyna." Yace yana murmushi tare da ɗaura hannunshi saman cinyarta yana ƙoƙarin kamo hannunta ta ɗauke tana matsawa. "Ni ka dai na kallona." Tace bayan ta ɗauke idanuwanta cikin nashi. Murmushi ya ƙara yi yace. "Laifi ne dan na kalla abin da zan mallaka." Baki ta tura ta juyar kanta gefe taƙi masa magana, hakan yasa ya ja motar suna barin gurin, sun yi nisa a tafiya ta ji ya fara magana. "Noor kar ki ce dan ƙaddara ta faɗa rayuwarki ki kasa bawa zuciyar ki dama ta dubi abin da take so, kar ki hana kanki ki cuci kanki kan abin da kike so ki ke muradi. Ki rumgumi ƙaddarar ki da hannu bibbiyu ki kawar da komai ki fara rayuwar ki tamkar kowa." Shuru Nuratu ta yi tana jin maganganun shi suna shigarta ya juya ya kalleta ya mai da hankalin shi kan titi ganin ya fara cin nasara a kanta yaci gaba da cewa. "Ina son ki ina ƙaunar ki Noor, tun lokacin da na fara ganin ki, tausayin ki ya rinjayi zuciyana har na faɗa son ki, ban yarda da haka ba sai daga baya. Dan Allah ki bani dama Noor, zan mamaye wannan duhun da haske, zan zame miki gata, zan baki dukkan kulawa, zan baki farin ciki dai dai yadda Allah ya hore min. Ɗan adam ajizine dole wataran ya ɓatawa mutum amma Insha Allah zan yi ƙoƙarin ganin na kiyaye. Ni Awwab sonki nake tsakani na da Allah ba wai dan wani abu naki ba." Maganganun Dr Awwab ɗaya bayan ɗaya suke shiga zuciyar Nuratu suna neman gurin zama, ta kasa magana ta kasa tantance mai take ji game da maganganun shi. Jin shurunta ya saka Dr Awwab juyawa ya kalleta fuskarshi ɗauke da murmushin cin nasara, gani yayi ta mai da kanta kan kujera ta lumshe idanuwanta. "Bacci ko?" Kai ta ɗaga masa ya tsayar da motar yana gyara mata seat ɗin yayi baya ta gyara kwanciyarta yaci gaba da tuƙi. Bacci ne ya kwashi Nuratu tana juya maganganun Dr Awwab a ranta, gaba ɗaya ya sata tunani. Ta san aure shine rufin asirinta amma tunanin abin da yake cikin aure take tunawa. Ba ta san me zata tarar ba, bata san me zai faru ba, bata san yaya mijinta zai ɗauketa ba ko zai karɓeta ba, bata da komai ba, bata da abin da za ta bashi a matsayinta na ƴa mace, tsoro take wata rana ya mata gori. Wa zata zaɓa cikinsu Yaya Al-ameen da ya jima da sonta da kaunarta itama taso shi, ko Col. Ahmad da ya tsaya mata ta kwaci haƙƙinta, ko shi Dr Awwab da ya taimaka mata ta dawo hankalinta da yanzu take jin wani abu a zuciyarta a kan shi da ta rasa taƙamemen menene. Tana wannan tunanin bacci ya kwashe har suka shiga Geidam ya tsaya yayi sallar azahar ya saya musu abin da za suci kafin yaci gaba da tafiya. Yamma lis suka shiga kafin Nuratu ta farka, jin motsinta ya saka Dr Awwab kallonta suka haɗa ido ta watsa mishi wani kallo yayi murmushi ya ɗauke kan shi. "Mun shigo kin farka." "Yamma yayi sosai, nayi bacci ashe." "Za ki biyani ladan wahalar da ni da kike." Dr Awwab yace lokacin da ya ɗauki hanyar gidan su Nuratu. Bata mishi magana ba ta juyar kanta, har ƙofar gida ya sauƙeta ta fita tana miƙa kafin ta shige gidan da saurinta, shi ya ciro akwatinta ya bi bayanta zuwa cikin gidan ya samu ta rukunkume Mami tana murnar ganinta kamar yarinya ƙarama. "Ina wuni Mami?" Dr Awwab yace yana ajiye jakan Nuratu a gefe, jin muryar Dr Awwab ya saka Nuratu sakin Mami ta kalleshi suka haɗa ido ta ɗauke kanta. "Lafiya lau Docter ya gajiyar hanya, kun sha hanya." Cike da kunyar Mami ya amsa ya miƙe daga durƙushen da yake. "Mami zan wuce sai wani lokaci." "Haba Docter ba zaka jira zuwa gobe ba? Akwai gajiya ai." "Babu komai Mami zan wuce kawai." "To shikenan ka gaishe da mutanen gida." "Za su ji inshaAllah." Yace ya nufi waje Nuratu ta bishi da kallo, Mami na ganin hakan yasa tace. "Tashi ki raka shi mana." Kamar jira take ta miƙe ta nufi wajen tana gyara zaman mayafinta. Murmushi Mami tayi ganin ƴartan ta fara karɓar Dr Awwab a rayuwarta ta san ko ta samu labarin da aurensa a kanta ba zata ƙi ba, ta ji daɗin da ya kasance shine mijin ƴartan ko ba komai asirinta a rufe babu wanda yasan mai ya faru cikin dangi sai in har shi ya furta wanda bata tunanin zai faɗa hakan. Bayan fitar Dr Awwab kamar ya san Nuratu zata fito ya kunna motar ya zauna, tana fitowa ta isa wajen motar shi. "Thank you so much Docter, ka gaishe min da Baby Hanan." "Za taji, sai munyi waya. Yaushe zan dawo." Ya tambayeta yana ɗaga mata gira ganin sun haɗa ido. Da sauri ta juyar kanta. Shi kam yana mamakin yadda bata iya juran kallonshi ko na minti ɗaya, ya lura kwata kwata bata iya kallon cikin idonshi kamar mai tsoron shi. Nuratu da ta juyar kanta tace. "Nima ban sani ba." "Kina so in zo kenan, kin bani damar zuwa ko wani lokaci." Ya faɗa jin amsar da ta bashi. Girgiza kai tayi. "Ni dai bance ba." "Shikenan karɓi drugs ɗinki, inshaAllah kin kusa rabuwa da shi gaba ɗaya. Ina yanzu babu ciwon kai?" Kai ta ɗaga masa yaci gaba da cewa. "Insha Allah in har babu wani matsalar za ki dakata da sha mu gani. Yanzu dai ki bani abun da in na gani za ina tunaki duk da hotonki kullum yana cikin zuciyana ban da na waya." Harara ta mishi ta juya ta nufi cikin gidan sai da ta kai bakin kofa ta juyo tana cewa. "Ka gaishe min da Ummi da Hanan." Murmushi ya sakar mata ta shige cikin gidan da sauri ya ja motar shi yana barin gurin cike da nishadi. Da ya rasa Nuratu bai san ya zai yi ba. Wajen taran dare ya isa Maiduguri duk ya gaji, wanka yayi ya gabatar da salloli kafin ya nufi gidan Ummi a babban falon gidan ya same su har Ummi da Hanan. Hanan tana ganin shi ta ƙi masa magana tana fushi da shi tun safe, murmushi yayi ya saka Hassana haɗo masa abinci ta miƙe ta kawo masa tana zubawa. "My Love fushi take dani har yanzu." Dariya Hassana tayi. "Ai yau mun sha rigima, gashi nan har yanzu fushi take maka sai kayi aikin lallashi." "Dole na ai." Yace ya ɗauki spoon ya fara cin abincin shi yana kallon Hanan. Sai ta ɗago ta kalle shi ta ɗauke kanta ko zai mata magana, ganin ya kamata tana kallon shi tana neman lallashi ayi sulhu ya sashi barin abincin ya miƙe tsaye. "Wa zai sha ice cream muje siya?" Yace bayan ya miƙe. Hussaina tace. "Yaya ni." Hassana ma ta miƙe tace. "Ni Yaya." Ya girgiza kai yana nufan gurin Hanan. "My Love nawa kaɗai zan siyawa, in ta yarda sai in saya muku." Yace ya zauna kusa da ita da take kusa da Ummi tana jin shirmen shi da ƴar shi. Hanan jin maganar ice cream ya sata lallaɓawa kusa da Dr Awwab. "Za ki sha?" Yace yana jawota jikinshi ta rumgume shi da ƙarfi ta ɗaga misa kai tace. "Zan sha." "Za ki daina fushi dani?" Kai ta ɗaga masa. "Amma zaka kai ni wajen Aunti Noor Babyn k..." Da sauri ya rufe mata baki ya miƙe yana ɗaukarta jin zata baro masa zance suka nufi waje. "Ummi za mu je mu dawo." Murmushi Ummi tayi ta amsa da to, ta fahimci maganar jikarta da take nema ta saka ubanta kunya. A gajiye yake amma dole ya saka ya kai su wajen shan ice cream ya sayawa Hanan kafin ya ɗauki hanyar gidan shi. "My Love yau gidanmu za mu je." "Daddy babu kowa fa." Tace tana shagwaɓe masa. "Yau kaɗai gobe zan maida ki." Ba dan taso ba ta bishi suka je gidansu da bata son zaman ita ɗaya, har ɗakinshi ya kai ta bayan ta sashi ya goyeta ya ajiye saman gado. Tsalle take masa saman gadon ya rabu da ita ya ɗauki laptop ɗinsa yayi aiki ya haɗata da game tana yi har bacci ya kwashe ta. Sai da ya gama abin da zai yi kafin ya rufe ya ƙarasa bakin gadon ya musu addu'a ya shafa ya rufeta kafin ya kwanta kusa da ƴar shi ɗaya tilo abun son shi. *** A haukace ya farka musu da safiyar cewa sai ya kashe kansa idan ba'a nemo mishi Nuratu ba. Ummu da ta kasa yi da shi ta gudu ɓangaren Hajiya Batula ta ƙira Daddy ya zo da saurin sa ya samu Mufid riƙe da wuka yana cewa. "Wallahi ko a nemo min ita a kawo ko in kashe kai na. Ku kun san yadda nake jin zuciyana? Zafi yake min kamar ya fita. Ku nemo min ita." Daddy da ya shigo ya ga tilon ɗan san cikin yanayi na marasa hankali ya ja baya gudun kar ya ganshi ya ƙara tunzura. "Ina za ka je?" Ummu tace tana ganin yana komawa baya. "Motar asibiti zan ƙira su zo ɗaukar shi, bazan iya masa ba, bakya ganin baya hankalinshi. Wani abun yasha wallahi ya taɓa ƙwaƙwalwarsa na sani." "Kana nufin Mufid ɗin hauka yake?" "Ga alama nan." Daddy yace ya nufi ɓangaren shi ya ɗauki waya ya ƙira emergency cikin gaggawa kafin ya zauna. Yama rasa wani irin tunani zai yi dan nema Mufid Nuratu. Alhaji Mamman ne yaci kuɗin shi da baya jin zai iya bar mishi sai ya biya shi. Kusan mintuna goma motar ta iso tare da security guda uku majiya ƙarfi suka nufi falon Ummu. Mufid duk ya hargitsa kayan falon bayan na jiya da ya farfasa aka gyara. Cikin sanɗa da dabara security biyu suka damƙe shi ɗaya ya kwace wuƙar hannunshi da sigarin kafin su fara kokuwar fita da shi. "Ina za ku kai ni? Wani irin abune wannan. Ummu kina ganin za su tafi dani, ku rabu dani dalla." Mufid yace yana turjewa yana kallon Ummu da take hawaye tana ji tana gani za'a ɗaura tilon ɗanta hauka. Duk kokuwa da Mufid yake haka aka saka shi a motar suka ɗaure shi kafin likitan da ke ciki ya masa allurar bacci, tuni kagin su isa asibitin bacci ya kwashe sa. Bai san sun isa ba har ɗakin da Daddy ya kama masa aka saka shi suka ɗaure hannunshi da kafarshi jikin gadon suka fito, Docter da zai duba shi ya shiga ya fito ya samu Daddy. Gilashin idonshi ya cire yana duban Daddy. "Yanzu dai ba zamu iya cewa komai ba sai ya farka mun ga yanayin jikinshi. Sannan abin ya fara shafar ƙwaƙwalwarsa, zai iya sai an dangana da psychiatric hospital saboda su bincike ƙwaƙwalwarsa." Alhaji Kashim da ya kasa ko tari balle kwakkwaran motsi yana sauraron bayanin Docter har ya gama ya miƙe yana cewa. "Shikenan Docter zamu san yadda za ayi. Bari in je gida in dawo zan sanar da mahaifiyarshi halin da ake ciki." To Docter yace Alhaji Kashim ya fita cike da tashin hankali abin da ya samu tilon ɗan shi namiji akan wata yarinya. Da ya koma gida ya sanar Ummu da har lokacin ta kasa tsaida hawayenta. Kuka ta ƙara fashewa da shi. "Yanzu Mufid ne ke hauka akan mace? Wallahi ƙarya ne." "Sai kuma kiyi ai, kina gani dai da na bar muku shi sai ya miki rauni ko ya yiwa kan shi fa." Girgiza kai tayi tana share hawayenta ta ɗauki wayanta ta sanar da Aunti Humaira da sauran yaran halin da ɗan uwansu yake ciki. Kowa ya ji abin babu daɗi ban da Rufaida da a zuciyarta ta san haƙƙin Nuratu ne da sauran mutane ya fara bibiyar shi. *** Nuratu washegarin ba ta farka da wuri ba har wajen ƙarfe goma tana cikin bargo har sai da Mami ta shigo ta tashe tana faɗa. "Yanzu in kinyi auren haka za ki dinga baccin safe. Wa zai dafa mijin abinci da safe yaci ya tafi aiki? Lallai aiki ya same ki, in ma za ki gyara ki gyara wallahi." Gunguni Nuratu tayi ta wuce bathroom ta wanke bakinta ta fito ta samu Mami ta bar ɗakin ta fita falon. Breakfast ɗinta ta samu Munirat ta zuba mata cikin flask ta ɗeba a plate ta dawo falon ta zauna ta hau ci. "Ki gama ki saka min lambar Ahmad in ƙira shi, tun da ya tafi ba muyi waya ba." "Ni ma wallahi Mami, bari zan ƙira shi ta wayana sai in haɗa ku." "To ki gama." Mami tace ta wuce kitchen dan duba kayan abinci da babu ta aiki Munirat. Bayan ta gama ta lissafa mata abubuwan da za ta siyo ta fita ta dawo falon ta samu Nuratu. "Kiyi ki ɗaura abincin rana na aiki Munirat. Ita ma bikinta ya kusa saura sati biyar zan tura ta gida. Ga na Walida shima ya gabato saura wata ɗaya." Mami ke wannan bayani tana zama lokacin da Nuratu ta gama ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen ta dawo ta wuce ɗakinta ta ɗauko wayarta ta dawo falon. Col. Ahmad ta ƙira ringing ɗaya ya ɗauka yana mata sallama tare da cewa. "Nuratu ya kike? Ya gida? Kin dawo kenan?" Bayan ta amsa ta ce. "Lafiya ƙalau. Ya aiki?" "Allahamdulillahi. Ina Mami?" "Ga ta nan za kuyi magana." Tace ta miƙawa Mami wayar Mami tace. "Je kiyi aikin da na saki." Babu musu ta miƙe tana mamakin menene Mami za ta faɗawa Col. Ahmad da za ta ɓoye mata. Kitchen ta shiga ta fara hada hadar ɗaura abincin rana. Col. Ahmad bayan ya gama sauraron bayanin Mami yace. "Allahamdulillahi Allah ya sanya alheri, Allah yasa shine mijinta har a aljanna. Na ji daɗi wallahi da ta kaucewa wannan mutanen." "Ameen. Ameen ya Allah." Mami ta amsa da shi tana jin Col. Ahmad a ranta tamkar ita ta haife shi. Col. Ahmad cike da farin ciki yace. "Ni ma ƙarshen watan nan ina hanya. Ku bani wannan damar in sanar mata  in na zo, na san za ta ji magana na ta karɓi auren nan ko bata so." "Shikenan an baka sai ka sanar da Dr Awwab kar yayi gaggawar faɗa mata." "InshaAllah zan yi hakan, Nagode Mami sosai." Yace su kayi sallama ya shiga neman lambar wayar Dr Awwab. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 38. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Hauka Mufid ya yi ta musu a asibitin ƙarshe suka dangana da asibitin mahaukata da ke Maiduguri, bayan gwaje gwaje da Docter yayi ya samu harda cutar zuciya da ya kamashi dan hayakin sigarin da yake sha ya fara lalata masa. Yau suke shirin tafiya, da Ummu kaɗai sai Daddy za a tafi, daga asibitin za su wuce sun dawo gida dan shirya kayan su. A ƙofar gidan ya yi parking ɗin motarshi, dan ya je har ofishin sa ance bai fito ba kuma baya fitowa yanzu, sannan sun samu labarin yau zai bar gari. Daga nan ya nufo gidanshi bayan kwatance da aka masa cikin sauri dan ya same shi. Bayan sauƙar shi a motar ya ƙwanƙwasa get ɗin gidan mai gadi ya buɗe masa ya shiga. "Alhaji Kashim yana nan?" Alhaji Mamman ya tambaya yana gyara jakan hannunsa tare da babbar rigarshi. "Eh yanzu ya shiga ciki amma zai fito." Faɗin mai gadi ya bawa Alhaji Mamman gurin zama ya zauna dan jiran shi. Gidan yaje bi da kallo ɓangare ɓangare uku, gidan babba ne, an zuba kuɗi gurin mallakar shi, ga motoci kusan huɗu a fake. Tun jiya ya harhaɗa masa kuɗaɗensa, har sai da ya haɗa da kuɗin cinikin da suka tara na sati kafin ya samu kuɗin ya cika, dan samun kuɗi gurin Alhaji Kashim bai iya ajiyewa ba ya hau kai ya kashe. Babu abin da ya rage masa sai shago da kayan ciki, kuɗaɗensa kaf ya haɗa kafin ya haɗawa Alhaji Kashim kuɗaɗensa. Duk ya rame yayi duhu dan tunanin kuɗaɗen shi da har cikin ranshi yake jin zafin rashin su. Mintuna ashirin Alhaji Kashim ya fito da Ummu cikin sauri ɗauke da kayansu suka shiga mota, ganin haka da sauri Alhaji Mamman ya miƙe ya isa wajensu. "Ina kwana Alhaji." "Lafiya ƙalau. Alhaji Mamman?" Faɗin Alhaji Kashim yana mamakin ganinshi wannan lokaci. Jakan hannunshi ya miƙa masa cikin motar. "Fatan abin da ya haɗa mu ya raba, ga kuɗaɗen ka nan na dawo maka da su." "Nagode, mu je driver." Alhaji Kashim ya faɗawa driver, kafin ya rufe gilashin motar direba ya ja motar suna fita a gidan. Ko ba komai ya ji daɗin dawo masa kuɗinshi da yayi, dan shima yana buƙatar su domin fitar da Mufid ƙasar waje dan binciken lafiyar shi. Alhaji Mamman ji yayi ya sauƙe wani kaya, amma ya ji haushi da baƙin ciki rashin kuɗinshi da yayi. *** Dr Awwab gyaran gidanshi yake sosai, sama da ƙasa, sama ɗakunan baccin su, ɗakuna uku ɗaya na shi, gefen shi na Nuratu, sai can daga ƙarshe na Hanan da ƙannenta masu zuwa a cewar shi. Ƙasan falo ne babba da ɗakin baki da dinning area, sai kitchen da store da ta hanyar dinning da zaka isa ciki. Ya bar fenti da sauran abubuwan sai Nuratu za ta tare. ... Yaya Al-ameen duk yadda zai yi yayi ƙoƙarin cire Nuratu a ran shi tunawa da yanzu ta zama matar aure, da addu'a ya samu ya cire ta a ranshi yaci gaba da kallonta tamkar su Walida. Ya san babu aure tsakanin su shi yasa duk wannan abubuwan suke faruwa, har zuwa yanzu da ta auri wani bashi ba. Ganin wanda ta aura yasa hankalin shi ya kwanta, ko ba komai ya yaba da hankalin shi, ya san zai kula da ita, asirinta a rufe. Baba nasiha ya masa sosai har ya zo ya faɗa sirrin zuciyarshi cewa dama shi baya son auren nan tun ba yanzu ba. A lokacin ya ji gwara da bai aureta ya kawota in da nan gaba za'a mata gori ko jifanta da munanan kalamai da zai sata hawaye. Aikin shi ya mai da hankali yake yi hankalinshi kwance, lokaci zuwa lokaci yana ƙiran Amma Jidda su gaisa yake sanar da ita ƙarshen wata yana hanya kafin bikin Walida. *** MAIDUGURI. A gajiye lis ya dawo gidanshi bayan aiki da su kasha fama da shi har da meeting da su ka gabatar bayan sallar azahar, bai samu zama ba sai karfe biyar ya dawo gidan. Wanka yayi ya fito, farin jallabiya kawai ya saka ya ɗauki wayarshi ya fito, har zai wuce zai sauƙa ƙasa, ya fasa ya nufi ɗakin Nuratu. Tsaye yayi yana imagining ranar da zai buɗe ido ya ganta an kawo masa ita, bai san wani irin farin ciki zai shiga ba, ban da wanda yanxu yake ji idan ya tuna da aurenshi a kanta. Ya jima tsaye a ɗakin kafin ya sauƙa ƙasa. Takeway da ya siyo yaci ya hau sama ya ɗauki mukullin morarshi ya nufi gidan Ummi. Babu kowa falon ya hau sama ya nufi falon ita ɗaya, tana kishingiɗe ya ƙarasa ya zauna ƙasa yana gaishe ta. "Ya aiki Awwab, yau ko da safe baka shigo ba, wannan ƴar kan duk ta dame ni." Murmushi yayi yana ɗaukan jug ɗin gefenta ya ga kunu ne a ciki na gyaɗa mai kyau, tsiyaya yayi a cup ya kurɓa kafin yace. "Ummi aiki ya mini yawa. Tana ina?" "Sun fita da su Hassana gidan Baba Abubakar." "Hakan ya yi." Shuru ne ya biyo baya yaci gaba da shan kunun, Ummi ne ta sako zancen da take son mishi. "Awwab ya labarin tarewar Noor ne? Ba kuyi magana ba har yanzu?" Shafa kwantaccen gashin kan shi yayi yana murmushi yace. "Ba muyi ba Ummi, sai ƙarshen watan nan nake son zuwa muyi maganar. Kin san har yanzu bata da labarin auren." Da mamaki Ummi tace. "Me yasa ba'a sanar mata ba? Ko dai dole ka yiwa ƴar mutane Awwab." Dariya Dr Awwab yayi, bai taɓa sanar da Ummi ko wani sirrin Nuratu ba kuma yana jin ba zai taɓa ba har abada. "Babu komai Ummi, kar ya zama bata shirya yanzu ba ranta ya ɓaci ne. Amma InshaAllah zan sanar da ita sai daga baya muyi maganar tarewar." "To Allah taimaka ya kaimu lokacin." Ameen yace yana miƙewa jin an fara ƙiran sallar magriba dan fita, Hanan da ta shigo da gudunta tun a waje ta ga motar Daddyn ta ya sata shigowa da gudu tayi kan shi ya ɗagata sama yana cafkewa kafin ya riƙota. "Kin fara nauyi My Love, gaba gaba zan dai na ɗaukar ki. Mai Aunties suka ba ki?" "Ni dai bani da nauyi. Auntie babu abin da suka bani." Hanan tace tana turo baki suka fita Ummi ta bisu da kallo tana mamakin soyayyar ƴa da uban. A falon ƙasa ya ajiyeta saman kujera tana tsalle ya ɗauketa, goshinta ya sumbata yana cewa. "Sallah zan yi in dawo, yau sai kin yi bacci zan tafi gida." Jin haka ya saka Hanan barin shi ya wuce masallaci. Sai da yayi sallar isha'i ya dawo gidan, Hanan har ta hakura ta ɗauka ba zai dawo ba ta ganshi, da sauri ta je ta haye jikinshi ta kwanta tana kallon cartoon da aka sanya a MBC MAX na Frozen II. Wayar shi ya ɗauka ganin babu abin da zai yi ya buɗe Data ya hau WhatsApp da rabon shi da shi har ya mance. Saƙonnin ne su kayi ta shigowa cikin wayar har suka gama ya dudduba ya gama tsaf, babu ko ɗaya na Nuratu hakan ya sa ya laliɓo numbern ta, gani yayi tana online ya tura mata saƙo. *"Babyna nayi missing ɗinki, yaushe zan zo ganin ki?"* ... Nuratu tana kwance saman kujera hankalinta rabi a waya rabi a Tv, hira suke a group ɗinsu na auren Walida da suka buɗe akan event da za su shirya, jifa jifa take saka musu baki dan ganin Ameera ta jajirce sai zuba rawan kai take da hakan haushi yake bawa Nuratu ta ga shigowar saƙon Dr Awwab. Fita tayi a group ɗin, da ma sun isheta ta buɗe saƙon shi ta gani. Luf tayi kamar ruwa ya cinyeta, in zata tuna yau kusan sati ɗaya rabonsu da juna. A hankali ta miƙe ta wuce ɗakinta ta kwanta saman katifarta kafin ta fara ƙoƙarin bashi amsa. *"Hanan nake son gani. Ita nayi missing."* ... Dr Awwab ya cire rai da za ta bashi amsa ganin kusan mintuna biyar ya samu shigowar saƙon ta. Murmushi yayi ya tura mata amsa. *"Ni kuma fa? Bakya missing ɗina." Karanta saƙon Nuratu tayi ta rasa amsar da za ta bashi, kawai sai ta kashe data ta ajiye wayar. Tana shirin miƙewa ta shiga bathroom wayar ya ɗauki ƙara ta ɗauka. Dr Awwab ne ya ƙirata ganin ta sauƙa a online. Kamar ba za ta ɗauka ba ta amsa tana kafawa a kunne ta masa shuru. Yana jin ta ɗauka taƙi masa magana sai sauƙan numfashinta da yake ji, ajiyar zuciya ya sauƙe da ya daki dodon kunnen Nuratu ta ji tsikar jikinta ya tashi, da sauri ta zare wayar a kunnenta kafin ta mayar jin ya fara magana. "Babyna ina son zuwa za muyi wani magana da ke. Please kar ki hana ni." Ta san dai duk maganar ɗaya ne, bata san mai za ta faɗa musu su yarda da ita ba, su fahimceta babu aure a rayuwar ta. Kamar ba za ta bashi amsa ba, har ya cire rai ko ya ɗauka bata ji shi ba, ko ƴan shan ƙamshin suna kusa ne yaji tace. "Docter dan Allah in dai akan wannan maganar ne ni kam..." "No Babyna wannan maganar yafi ko wanne muhimmanci. Please My Baby." Mamaki take shi dai baya gajiya da zirga zirgan hanya, bayan haka ma ƙarfi da yaji ya raɗa mata wani wai Baby kamar wata yarinya, ko Hanan baya ƙira haka sai ita babba da ita. A zahiri ta sauƙe numfashi tace. "Shikenan Allah kaimu. Yaushe za ka zo?" "Nan da ƙarshen wata yayi." "To sai ka zo." "Thank you My Baby." Kit ta kashe wayar tana ajiyewa ta yi baya ta kwanta, bathroom ɗin da bata shiga ba kenan, ta shiga tunanin me kuma Dr Awwab zai sanar da ita. *** Ƙarfe taran dare Alhaji Mamman da Amma Jidda suna zaune ta kawo masa abinci yaci rabi yace. "Zo ki kwashe Jidda na ƙoshi." Abincin ta kalla ta ga kaɗan ya ci, ta dube shi gaba ɗaya ba'a nutse yake ba cikin kwana biyun, ga wani rama da ya fara tace. "Haba Abban su Rahma, ka ɗaure ka ci ko kaɗan ne, dubi fa har wani rama kayi, ko dai abincin bai maka daɗi babe in tafasa make wani abu?" "Ko ɗaya Jidda kawai dai bana jin daɗi ne. Ni na rasa me yake damuna a rayuwata, tun da Sadiya ta haifamin yarinyar nan babu alheri a rayuwana, kullum daga wannan sai wannan." Amma Jidda da take jin maganganun shi har ya gama ta gyara zama tace. "Abban su in faɗa maka wani magana? Ban san ya za ka ɗauka ba, amma maganar gaskiya babu wani abun a rayuwar Nuratu da zai shafi rayuwar ka. Ban san mai ka ke tunani ba ko hasashe ba, ka ɗauka laifi ka ɗaurawa yarinyar da bata ji bata gani ba. Ka san ƙaddara? To wannan ƙaddara ne daga Allah dan ya jarabci imaninka. Maganar kuɗi kuma ko ƙarayar arzikin ka duk wannan ƙaddarar Allah ne. Ko bayan rabuwar ku da Mamin su Rahma kayi duba da babu wani abin da ya ƙara samun dukiyar ka sai yanzu. Yanzu kuma fa? Kai ka ɗaurawa kanka, ka karɓi tayin Alhaji Kashim ko duba da halin da ɗan sa ya saka Nuratu ba kayi ba, ka karɓi tayin shi. Baka san ta wani hanya ya samu kuɗin ba? Baka san halal ne ko haram ba? Ka ɗauka ka saka cikin dukiyar ka, gashi nan ya barka da asara. Ni na faɗa maka gaskiya in har magana na ya ɓata maka rai Allah baka hakuri." Daga haka Amma Jidda ta miƙe ta ɗauki kwanukan abincin ta wuce kitchen, Alhaji Mamman ya bita da kallo cikin mutuwar jiki kalamanta suna ratsa ƙwaƙwalwarsa. Baƙin tea ta haɗa ta kawo masa za ta wuce ɗakinta ya dakatar da ita. "Maganar kayan abincin da za'a yi na ranar bikin Walida, baki ce komai ba lokaci yana ta matsowa." "Duk abin da ka bayar yayi." Amma Jidda tace, dama tana son masa magana, amma ganin halin da yake ciki ya sata ƙasa masa magana. "Shikenan zuwa gobe zan ga me ya kamata ayi." "Nagode Allah kaimu." Daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta. Alhaji Mamman ya jima zaune cikin falon ya saƙa wannan ya warware, komai ya kwaɓe masa. Ya ma rasa wani irin tunani zai yi. *** Alhaji Kashim da Ummu suna Maiduguri asibitin Asylums center da aka riƙe Mufid, jikin Mufid kullum gaba yake, rashin shan sigari da wine ɗin ya girgiza shi sosai, ya saba ya bi jinin jikinshi da ba zai iya rayuwa babu shi ba. Rashin shan komai shi yake ƙara birkita ƙwaƙwalwarsa kullum a rikice yake, ban da allurar bacci da magunguna babu abin da ake ɗura masa. Ganin lafiya yaƙi samuwa Alhaji Kashim ya fara shirin fitar da shi ƙasar India dan ci gaba da duba lafiyar shi. Aunti Humaira ta zo da sauran yayun shi har Rufaida da Babynta tayi wayo. Hajiya Batula ma ta zo da ƴaƴanta. *** Kwanaki sai tafiya suke har aka cinye sati biyu in da ya zamto daidai da ƙarshen watan Oktoba, ya kama saura kwana huɗu bikin Walida. Shiri sosai su Nuratu suke yi basa zama, anko kala uku su kayi, ɗaya kamu ɗaya bridal shower ɗaya ɗaurin aure, duk a gidan Aunti Hasiya za'a yi, dan Nuratu tace in har ba anan za'a yi ba, to baza taje gidansu ba, kafin su yarda sanin tsakaninta da Abban su. Yau tun safiyar ranar laraba su kaje wanke kai, har yamma lis kafin su dawo gidan Aunti Hasiya gaba ɗaya su. Ameera da aka fara gama mata ta riga su zuwa gidan, sai Nuratu da Walida a ƙarshe suka taho cikin motar Mami da Nuratu ta ɗauka dan zirga zirganta, da kyar Mami ta bata har da kukanta kafin bata bayan gargaɗi da tasha. A waje tayi parking dan tana son komawa gida dan ɗaukan wasu kayanta da ta mance a gida. Bayan tayi parking suka fito suka nufi cikin gidan, a harabar gidan taga motar da bata tsammaci gani yanzu ba. "Yaya Al-ameen! Ko yaushe ya zo?" Walida tace ita ma cike da mamaki dan ta gane mai motar. Nuratu baya taja ta tsaya dan bata shirya ganin shi yanzu ba, yanzu zai tsayarta da maganganun shi, ta dubi Walida. "Walida zan je gida in dawo, zan ɗauko kayana da na faɗa miki." Hararanta Walida tayi tai murmushi. "Bakya son dai ganin Yayana." "Wallahi ba haka bane, zan je in dawo, kar ma kice tare muke, kice na wuce daga can dan Allah." "To ki gaishe da Mami." To Nuratu tace ta fita da sauri tana barin gidan Walida ta shiga ciki. Nuratu har cikin gida ta shigar da motar dan ba zata koma ba sai gobe. "Ya haka kuma ke da sai wani sati." Mami ta tambayi Nuratu da mamakin ganinta wannan lokaci. Nuratu da ke kwance saman doguwar kujera tace. "Ni nayi kewar ki ne na dawo, sai gobe zan koma da safe muyi lalle, da yamma ne event ɗin." "Ke ki ka sani. Ahmad yana hanya gobe." Sai lokacin Nuratu ta kai kallonta kan Mami tace. "Docter ma yace yana zuwa ƙarshen wata, amma ban san yaushe bane, dan bamu ƙara magana da shi ba." "To Allah kawo su lafiya." Mami tace ta miƙe dan kar Nuratu ta sako mata wani zancen. Duk waya da Walida da Rukayya suka mata ƙin ɗauka tayi, ƙarshe ta tura musu saƙon cewa kanta yana ciwo sai gobe za ta dawo. Washegarin. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 39. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Da safe ƙarfe takwas Nuratu ta wuce gidan lalle acan suka haɗu da Walida da Rukayya da Ameera. Ameera aka fara yiwa sai Walida da ta ja lokaci sosai dan lallen amarya, kafin Nuratu. An gama mata kenan wajen karfe biyu wayarta yayi kara, Rukayya ce ta ɗauka mata ta ga Col Ahmad ne. "Saka min a handfree Sister." Babu musu Rukayya ta saka mata da d'ayan hannunta marar lalle, an fara mata kenan, ta ɗaurawa Nuratu wayar saman cinyarta. Bayan tayi sallama ya amsa ya sako mata tambaya. "Na iso bakya nan in ji Mami kin tafi lalle. Ashe biki sister ku ke babu gayyata." A hankali tace. "Dan Allah kayi hakuri wallahi na ɗauka na sanar da kai, abin ne yazo a ƙurarren lokaci." "Shikenan ina jiranki, za ki biyo gida in kin bar gidan lallen?" Ya tambayeta. "Eh zan zo." Da to ya amsa da shi kafin ya kashe, ko ba komai za ta biya su gaisa, mutum musamman dan ita ya taso daga wani garin ya zo. Mintuna biyu da ajiyar wani ƙiran ya shigo ta kai dubanta ta ga Dr Awwab ne, ta kalli Rukayya. "Yi hakuri sister ki ɗauka min." Babu musu Rukayya ta amsa ta saka a handfree tare da ɗaura mata saman cinyarta. Dr Awwab da tun ɗazu ya ƙira ya ji line busy tana waya ya kasa samun nutsuwa, haka yaci gaba da ƙira, abin da bai taɓa mata ba, dan wani mugun kishi ne ya kama shi, burin shi ɗaya ba da wani take wayan ba. Jin ta ɗauka ya watsa mata tambaya. "Babyna da waye kike waya haka?" Jin sunan da ya ƙirata da shi kamar ta nutse ƙasa, ido ta ɗago gaba ɗaya sun zuba mata shi. Walida na gumtse dariyarta, hakan yasa ta haɗa rai ta juyar kanta tana bashi amsa. "Da Col. Ahmad ne." Ajiyar zuciya ya sauƙe bayan ya ji mai tace, yace. "Ina da kishi sosai Babyna." Shiru Nuratu tayi tana hararan Walida da ke dariya kasa ƙasa bata ce komai ba. Jin haka shima Dr Awwab yace. "Na shigo gari shine na ƙira in sanar miki ina tafe nan da some minutes." "Yau ɗin?" Nuratu ta tambayeshi da sauri. "Yes mana Babyna, na sanar miki ina hanya ai ƙarshen wata. Ko har kin manta?" "To sai ka iso. Amma ina gidan lalle yanzu." Nuratu tace ta ma rasa mai za tace tunawa da Col. Ahmad yana gidan. "Lalle ki ke mini Babyna?" "Biki muke yi na sister na." Tace da sauri jin sai baro zance yake. Murmushi yayi yace. "Bari in biyo in ɗauke ki, ki turomin address." "A'a akwai motar Mami a hannuna." "Shikenan bari in ƙarasa mu gaisa da Mami kafin ki iso. Take care My Baby." To tace da sauri ta kashe wayar da gwuiwar hannunta tana hararan Walida da ta kwashe da dariya. "Su Baby manya. Anya ba da Dr Awwab za muje ba, kun ji yadda take kashe masa murya tana sha masa ƙamshi, duk ta rikita bawan Allah." Harara Nuratu ta watsa mata. "Sharri zaki mini Walida, ni ba wani kashe masa murya da nake balle shan ƙamshi. Duk cikin su babu wanda nake so, kallon mutunci nake musu." Nuratu tace tana tashi tsaye. Rukayya da sai lokacin ta saka baki dan tasan komai tace. "To waye Baby? Muna ji ya ƙira ki da Baby kika amsa. In ba so mai ya kawo haka." Jin maganar Rukayya ya sa Nuratu kallonta kamar za tayi kuka. "Maman twins zamu ɓata, ina ganin girmanki dan su twins, kin san ba wani girmana ki kayi ba, just some months kika bani." "To yi min rashin kunya, ƙarya mu kayi ne?" Nuratu rai ta haɗa ta kalli mai lallen da take musu murmushi tace. "Ƴar uwa zan iya wankewa?" Kai ta ɗaga mata tace eh. Da sauri Nuratu ta fita ta wanke lallen ja da baƙi da ya yiwa fatar jikinta kyau, ta dawo wajensu ta ɗauki jakanta da wayarta ta nufi waje tana cewa. "Sai mun haɗu anjima." "To a gaishe mana da Docter Babyn Docter." Cewar Walida tana dariyar da yake bawa Nuratu haushi, hakan yasa Nuratu fita taƙi kulata. ... "Kana so kana kaiwa kasuwa." Rukayya tace bayan fitar Nuratu. Da murmushi saman fuskar Walida har lokacin tace. "Shine dai nima na gani, ji fa yana ƙiranta ta fice fit, amma yanzu da za kayi magana zata fara musaka." Ameera da take jin su tun faruwar maganar ta kasa cewa komai, musamman da taji Dr Awwab irin maganganun da yake zubawa Nuratu ta ji ta kasa kwakkwaran motsi. Bata taɓa tsammani Nuratu za ta samu masoya haka ba har da Dr Awwab da take ganin yafi ƙarfin Nuratu ya wuce ajinta. Bata tammaci zai so Nuratu ba kai ko wasunsa ma bayan yayanta Al'ameen da ya nuna ita yake so. Bayan ma abubuwan da ya faru a rayuwarta ta ɗauka za'a gujeta a ƙyamace ta. Tun tasowarta haushinta take ji har zuwa yanzu da girmansu. *** Nuratu a waje tayi parking dan tana son komawa bayan la'asar za su gudanar da kamu, motar Dr Awwab da Col Ahmad a waje ta gani sunyi parking. Cikin wani irin yanayi ta ƙarasa cikin gidan har cikin falon da sallama, ta samu Dr Awwab da Col Ahmad suna hira tamkar sun saba. Dr Awwab sai zuba murmushi yake Col Ahmad ne yake magana da yake saka shi murmushi. Jin sallamar Nuratu ya sasu kallo kofar suna amsawa. Dr Awwab ido ya zuba mata idonshi ya kai kan jan lalle da baƙi da ke jikin hannunta, ji yayi tamkar ya riƙo hannayenta ya sanar da ita sun yi mutuƙar mata kyau ya bata tukuici. Col Ahmad kallo ɗaya ya mata ya ɗauke idanuwansa tunawa da yanzu da baya ba ɗaya bane, halaliyar wani ce. Guri ta samu ta zauna tana ce musu. "Ina wunin ku ya hanya?" "Lafiya lau masu biki. Ya zirga zirga?" "Allahamdulillahi." Ta amsa da shi ta ɗago kanta jin Dr Awwab bai amsa mata ba, idanuwansa fes a kanta yana yawo da su a jikinta. Suna haɗa ido ta watsa mishi harara ganin ya ƙura mata ido. Murmushi yayi bai ce komai ganin Col Ahmad yana gurin. "Nuratu ƙira Mami za muyi wani magana da ke da ita." Col. Ahmad yace ya katse shuru da kallon kallo da suke tsakanin su da Dr Awwab. Babu musu ta miƙe ta wuce ɗakin Mami, Dr Awwab ya bita da kallo, ta masa kyau sosai. "Ina dai wajen kuma ni babban yaya ne, ana jin kunya mana." Maganar Col. Ahmad ya dawo da Dr Awwab hankalinshi ya juya yana sosa kanshi, bai san yaushe idanuwansa suka aikata hakan ba. Yasan dai zuciyarshi da gangar jikinshi suna buƙatar ta. Fitowar Mami da Nuratu yasa su tashi suka zauna a ƙasa, ganin haka itama Nuratu ta zauna a ƙasa suka tsinci muryar Yaya Al-ameen yana sallama. Bayan sun amsa ya shigo ya zauna yana gaishe da Mami, kafin ya amsa gaisuwar Nuratu yana cewa. "Gwara da na zo ashe. Ga ni ga angon mu, in bashi amanar ƙanwata, in kuma yayi ba daidai ba in hukunta shi." Col. Ahmad da Dr Awwab suka yi dariya, har da Mami ta murmusa ban da Nuratu da aka sakata a tunani ta haɗa rai. "Haka za'a yi Yayanmu, na baka matsayin, ni na ɗauki matsayin Baba." Col. Ahmad yace yana kai kallon sa kan Nuratu tana binsu da ido. Dariya su kayi Mami tace. "Bari in baku guri ku gama maganar, nayi mata sauran bayani daga baya." Daga haka Mami ta tashi ta shige ɗaki ta bar su, Col. Ahmad yayi gyaran murya yana kai duban shi kan Nuratu da ta kawar kanta daga hiran su ta faɗa tunani daban. "Nuratu!" Col. Ahmad yace dan so yake ta fahimci bayanin da zai mata, juyawa tayi tana kallon shi ta amsa. "Ina son ki bani aron hankalin ki, ina so ki fahimci zance na ko abin da zan faɗa miki, ba mun yi haka ba ne dan cutar ki sai dan kuɓutar da ke daga dukkan sharrin Mufid. Kuma mun san bamu miki banzan zaɓi ba, dan mun kai ki hannu mai kyau nagari wanda zai kula da dake da dukkan lamuran ki, zai share miki hawaye kuma mun ga hakan tun yanzu. Kin san dai dalilin zuwan ki Nijar gurin Kawu Muhammadu ko?" Ya ƙarashe maganar da tambayar Nuratu, ta ɗaga kanta domin ta kasa bashi amsa tana juya maganganun shi cikin ranta ta ji ya cigaba da bayani. "Zuwan ki Nijar gurin Kawu Muhammadu kin san duk dan mu kwacewa Mufid ne kuma allahamdulillahi mun yi hakan, kuma baki tambayi dalili ba?" Sai lokacin Nuratu ta ɗago kanta ta kalleshi, yaci gaba da maganar shi ya sanar da ita komai tun daga barinta gidan da aurenta da aka ɗaura da Dr Awwab wanda sauran bayanan zuwan shi yau Mami ta sanar da shi, ya ƙarasa maganar yana cewa. "Ga Dr Awwab nan shi yayi nasara cikin mu, Allah ya riga ya ƙaddara shine mijin ki, ɗaura auren ku yau tsawon wata ɗaya da sati biyu. Ni a matsayina na babban Yaya kiyi masa biyayya Nuratu, na sanki baki da wani matsala, kiyi ƙoƙarin masa biyayya Allah baku zaman lafiya. Ki cire komai a ranki ki rumgumi mijin ki ku zauna lafiya, shi ya ganki a haka yake son ki  kuma ya ji zai zauna da ke, dan haka ki cire komai ki mance da abin da ya faru." Nuratu da idanuwanta suka cika da ruwan hawaye jin abin da suka aikata mata, zuciyarta yayi zafi ɓata ce komai ba har Col. Ahmad ya gama maganganunta shi ta ji Yaya Al-ameen ya ƙara da cewa. "Ni kam babu abin da zan faɗa Col. Ya gama faɗin komai. Abin da zan ce ƙanwata ki yi biyayya Allah baku zaman lafiya." "Ameen ya Allah." Col. Ahmad da Dr Awwab suka faɗa a tare, Col. Ahmad ya miƙe yace. "Mu basu guri su tattauna." Bayan fitar Col. Ahmad da Yaya Al-ameen Nuratu ta ɗago kanta jin falon yayi shuru kusan mintuna, ta kalli Dr Awwab ta ga ya zuba mata. Kanta ta ɗauke tana share hawayenta wani haushinsa ne ya kamata tace. "Ka dai na kallo na." Murmushin sa ya faɗaɗa yana tashi a in da yake zaune yace. "Laifine dan na kalli halal ɗina." Tsaki ta buga ƙasa ƙasa tana miƙewa ganin zai zauna kusa da ita ta nufi hanyar ɗakinta tace. "Ba zan taɓa karɓar auren nan ba." "Dagaske?" Yace ya sata dakatawa ta juya ta watsa mishi harara ta wuce ɗakinta. Murmushi yayi ya miƙe yana fita bai ji zafin abin da ta masa ba, ya shiga cikin motarshi, dan ya samu Col Ahmad da Yaya Al-ameen sun tafi. ... Nuratu kwanciya tayi bayan shigarta ɗakinta ta fashe da kuka. Haushin kowa take ji musamman mahaifinta dashi ya jawo mata komai, da bai karɓi tayin auren Mufid ba, da babu wanda ya isa ya mata wani aure dan bata shirya yanzu ba. Bata san mai zata tarar? Bata san ya ya mijinta zai karɓe ta ba. Shine abin da take tsoro yake hanata sha'awar yin aure. Abubuwan da suka faru a rayuwarta suka din ga dawo mata. Da Mufid bai ɓata mata rayuwa ba da yanzu itama tayi aurenta hankalinta kwance tana rayuwarta. Sallamar Mami da shigowar ta lokaci ɗaya ya saka Nuratu ɗago kanta ta kalleta da idanuwanta da suka sha kuka. "Auren ne bakya so ko Dr Awwab ne bakya so. Ki sanar dani" Mami tace bayan zamanta kusa da ita. "Dukka Mami." Tace tana share hawayenta. "Amma dai wannan kin san shine hanyar tsiratar da rayuwar ki ba?" Shuru tayi Mami tayi ta mata nasiha sai kuka take har tayi shuru tana sauƙe numfashi. "Mami tsoro nake ji." "Tsoron me?" Mami ta faɗa cike da tausayin ƴarta. "Kar watarana ya min gori." "Na san Dr Awwab ba zai taɓa hakan ba. Kici gaba da addu'a, inshaAllah na ji a jikina za kiji daɗin zaman dashi." Ita dai Nuratu bata ce komai ganin Mami ta goyi bayan auren nan, da kwata Nuratu tana jin ba in da zai je. Kamun da bata samu zuwa da wuri ba sai ƙarfe biyar, shima sai da Walida ta ƙira Mami kafin Mami ta sata dole ta shirya ta tafi. A motar Mami ta tafi, tayi kyau sosai, kayan ya karɓi fatar jikinta, ba tayi wani kwalliya ba sai hoda, fuskar nan a haɗe ta haɗa giran sama da ƙasa. Tun da taje tana zaune ta ƙi tashi balle sa ran za ta musu rawa, ko ƙarin kuɗi ba tayi ba sai dakyar Aunti Hasiya ta sata tayi mata, tana yi ta fita a hall ɗin ta shiga motar Mami ta kulle kanta ta shiga tunani. Wayarta ne yayi ƙara ta duba ta ga Dr Awwab ne, ta buga tsaki ta ajiye. Ganin bata ɗauka ba ya saka Dr Awwab tura mata saƙo. ..... #vote. #comments #share MADUBIN GOBE  40. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Dr Awwab ƙiran Nuratu yaci gaba da yi kusan sau uku bata ɗauka ba, sai yaji babu daɗi gaba ɗaya, hakura yayi ya rabu da ita. Saƙon da ya tura mata ma babu amsa, ƙarshe da ya ƙirata a kashe ma wayar. 'Akwai aiki gaba na.' Yace a zuciyarsa yana mamakin Nuratu, bai taɓa tsammanin za ta ƙi auren nan kai tsaye ba, duk tsammanin shi zata hakura ta karɓa hannu bibbiyu amma abin ya canza. Shigar shi Maiduguri gidan Ummi ya nufa, da Hanan ya fara cin karo a filin gidan tana lilo, tana ganin shi da gudu ta sauƙa ta nufi gurin shi ya ɗagata sama suka nufi entrance na gidan. Ummi bata falon hakan yasa suka wuce sama falonta, zama yayi yana gaisheta tare da ajiye Hanan a gefenshi. "Kun yi magana da ita?" Ummi tace sanin in da ya tafi. Girgiza kai yayi yana miƙawa Hanan wayar shi da ta tambayeshi ya bata game. "Ummi ta ƙi yarda fa, wai bata shirya ba, yanzu ma haka tun fitowa na ita nake ƙira ta ƙi ɗauka." "Ko sai naje?" Ummi tace tana murmushi. Murmushi Dr Awwab yayi shima yace. "May be hakan za ayi. Ina yaran nan?" "Sun fita gidan Baffanku." "Shine suka bar min My Love ita ɗaya." "Ƙin zuwa tayi har sun shirya ta." Miƙewa yayi tsaye yana cewa. "Mu ma mun tafi unguwa sai anjima. Tashi mu tafi My Love." Da sauri Hanan ta miƙe ya ɗauketa suka ma Ummi sallama suka fita. *** DAMATURU. Ranar Nuratu yanda ta ga rana haka ta ga dare, ta kasa kwakkwaran tunani da zai sama mata mafita bisa abin da suka mata. 'Aure dai!' Ta faɗa ta sake maimaitawa a fili da zuci. Auren ma tare da Dr Awwab da ta kasa tantance me take ji a kansa. Gefe ɗaya na zuciyarta haushinsa take ji na shiga rayuwarta da yayi, gefe ɗaya kuma ji take gwara da ya kasance shine mijin ba Col. Ahmad ba domin Yaya Al-ameen ta daɗe da cire shi cikin ranta. Ta kasa tsaida zuciyarta guri ɗaya ta samu shawaran da take nema da zai amfane ta. Da irin tunane tunanen nan daga ƙarshe wani bacci ya ɗauketa bayan ta gabatar da sallar asuba. Ƙarfe takwas Mami ta ga shuru ta shiga ta sameta tana bacci ta tashe ta. A gurguje tayi wanka ta saka doguwar riga marar nauyi ta fita bayan ta ɗauki wayarta da mukullin motar Mami, ta sanar da ita sai dare ko kuma gobe, ko damar yin breakfast ba tayi ba. Gidan Aunti Hasiya tayi, anan ta samu Walida tayi ta faɗa da kyar ta bata hakuri kafin ta shiga ciki suka fara aiki. Har azahar kafin su samu zama su ka sake yin wanka suka saka ankon su. Biki aka yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, aka ci aka sha aka watse lafiya, da dare a ka kai amarya gidan mijinta. Nuratu bata koma gida ba bayan sun dawo daga kai amarya ta wuce gidan Aunti Hasiya suka gyara mata gida har wajen sha biyun dare kafin suka kwanta. Washegarin suka yi wuni, da yamma aka gudanar da dinner da mutane da yawa sun samu halarta, hatta iyaye sun je anan ne Mami tayi ƙoƙarin zuwa dan yiwa Amma Jidda kara kuma ta ji daɗin hakan. Karfe goma aka watse kowa ya wuce gida. Nuratu tare da Mami suka koma ta wuce ɗakinta ta watsa ruwa ta canza kaya ta kwanta. Sai lokacin ta dauki wayarta ta buɗe, ƙirane daga mutane daban daban har da na Dr Awwab da tun jiya ya ƙira bata ɗauka ba. Lambar shi ta kurawa ido kamar za ta hangoshi ciki. Dr Awwab yana cikin mutanen da take ganin mutuncin su, tana jin wani abu akan shi tun ranar da ta ɗaura idanuwanta a kanshi, ji take bata iya jumurin kallon cikin kwayar idanuwanshi, duk yanda taso kasawa take. Zaman aure da shi abu ne mai wahala a tare da ita, bata jin zata iya, sannan bata son rabuwa da shi a rayuwar ta. Jin tunani babu abin da zai haifar mata ya sata rufe wayar ta ajiye ta runtse idanuwanta, shuɗaɗɗen lokacin da ya wuce kwanakin baya yake dawo mata. Ashe shi yasa yayi ta mata wasu abubuwan da ta kasa fahimtar shi, har yayi ƙoƙarin riƙe hannunta ranar da za su dawo daga Nijar. Ta daɗe kafin ta samu bacci ranar ya ɗauketa. *** INDIA (New Delhi). Rayuwa cike yake da dana sani da ƙaddarori ma bambanta da ko wani bawa baya wuce ƙaddarar shi. Duk abin da ka shuka sai ka girba, sannan duk abin da ka yiwa ɗan wani kai ma sai an maka tabbas haka Annabi Muhammad (SAW) yace kuma hakanne. Zuwan Alhaji Kashim da Hajiya Hindatu India tare da Mufid dan jinyar shi babu abin da ya canza sai ma ƙoƙarin masa aiki da ake a zuciyarshi, domin shaye shaye ya lalata zuciyar saura kiris ya ɓaci da in har hakan ya kasance sai dai su hakura da shi. Alhaji Kashim kuɗaɗen shi da ya taho da shi da kuma wanda yake can gida ya saka aka tattara aka turo mishi ya haɗa ya bada kuɗin aikin da za'a gudanarwa Mufid, babu abin da ya rage masa sai gida da motarshi, domin ƙadaran shi kaf ya saka aka siyar aka aiko masa kuɗin. Yau talata za a shiga da shi aiki bayan alluran bacci da aka ɗura masa. Hajiya Hindatu duk ta sare da yanayin ɗan tan da yake kwance ya ƙara haske yana fitar da numfashi kaɗan kaɗan ta cikin Oxygen da yake taimaka masa. Hawaye take share lokaci zuwa lokaci tana addu'ar Allah bashi lafiya in kuma lokacin shi ne yayi Allah karɓi abin shi. Ƙarfe tara aka shigo aka wuce dashi dakin da za'a masa aikin, Ummu ta bishi da addu'a tana kuka sosai, Daddy yana bata baki da shima dauriya yake. "Addu'a zamu masa Hindatu babu yanda muka iya." Hawayenta Ummu ta share duk tayi baki ta rame tace. "Ji nake kamar Mufid ba zai tashi ba. Ina tsoro ya mutu ya barni. Ina tsoron ya mutu bai nemi yafiyar jama'a ba. Ina tsoron ya mutu bai tuba zuwa ga Allah ba bai nemi yafiyar shi ba." "Nima ina jin hakan, amma InshaAllah zai tashi da yardar Allah, mu mishi addu'a." Shuru Ummu tayi tana sharewa hawayenta, a ranta ta riga ta saka duk alhakin mutane yake bibiyar ɗanta, musamman wannan yarinyar da sanadinta komai ya faru. *** DAMATURU. Amma Jidda da ta ƙira sunan Alhaji Mamman sau biyu bai ji ba dan tunanin da ya faɗa sai ƙira na uku tace. "Haba dan Allah Abban su, yanzu ba za ka dai na saka kanka a damuwa ba. Ka daina wannan tunanin mana, shi yake ƙara haddasa maka jinin yake hawa, du bi yanzu Docter mai ya gama sanar da kai." Ajiyar zuciya ya sauƙe yana dubanta, shi kaɗai ya san mai yake ji a ranshi yace. "Jidda bazan iya daina tunani ba, bazan iya daina dana sanin abin da na aikata ba. Jiya na ji wani wa'azi ga duk mutumin da ya yarda da shirka da boka ko wani wanda zai saka ka yarda da shi ba Allah ba, Allah ya masa haramcin da Aljannah bayan azaba. Ya zan yi Jidda? Na yarda na bi na amincewa aboki ya jefa ni halaka, ya raba ni da matata da ƴata, ga shi yanzu ban da wutar tsana babu komai a tsakanin mu. Ta ina zan fara? Ta ina zan soma goge tabon da na saka a rayuwar su, musamman ita Nuratu da bata taɓa samun gatan uba ba tun tasowarta har zuwa yanzu. Na saka mata tsanana a zuciyarta da rayuwarta. Ki taimaka mini in samu yafiyarsu ko da kaɗan ne cikin abin da na aikata musu ko Allah zai yafe mini. Wallahi na tuba" Tabbas duk mai rai baya cire tsammani, ranar da Amma Jidda take jira ya zo. Ranar da Alhaji Mamman zai buɗi baki ya dubi abin da ya aikata har ya nemi gafaran su. Cike da murna da farin ciki tace. "Kar ka damu Abban su Rahma, Mamin su Rahma za ta fahimce ka ta yafe maka har ita Nuratun." "Kina ganin hakan. Sadiya tana da sauƙin kai amma tana da zuciya." "Ka yi kyakkyawar zato." Tace cikin tsananin farin ciki. Ya sauke ajiyar zuciya yana fatan hakan, domin in har ya samu yafiyar Mami da Nuratu ya san sauran kudirinsa zai cika cikin sauƙi. *** Bayan sati biyu. Tun ranar Dr Awwab bai ƙara ƙiran Nuratu ko nemanta ba, ya barta sai ta sauƙo, baya son takura mata ta ga tamkar wani buƙatarshi ke kawosa gurinta. Ummi bata ƙara masa maganar tarewar Nuratu ba ta saka masa ido. ... Bangaren Nuratu ta ajiye maganar aure a gefe ta fara kiciniyar mai da hankalinta a kan service da za'a tura su. Mami dai tace ba zata hanata zuwa ba amma ta sanar da Docter kafin ta kammala komai tun da dai da auren shi a kanta. ... Ranar wata Juma'ah Dr Awwab da wuri ya dawo daga aiki, gidanshi ya wuce yayi wankar Juma'ah cikin blue black din shadda da ya fito da fatar jikin shi ya mutuƙar masa kyau ya saka hula ya nufi gidan Ummi. Da sallama ya shiga falonta tana can cikin bedroom ya jira fitowarta ta fito tare da Hanan ya gaishe ta. "Daddy kayi kyau." Hanan tace tana matsawa kusa da shi, yayi murmushi ya shafa kanta da aka parker mata gashinta mai tsawo da tsantsi yana reto yace. "Thank you My Love. Ummi zan wuce masallaci." "To a dawo lafiya. Akwai in da za muje in ka dawo." "To Allah kaimu." Yace ya fita Hanan ta biyo shi da gudu. "Daddy ka kawo min abu mai daɗi." "To My Love." Yace ya sunkuya ya sumbaci kumatunta kafin ya wuce ta koma ciki. Masallaci ya wuce kai tsaye ya gabatar da sallar juma'a ya dawo, karfe biyu da rabi ya dawo gidan yaci abinci, Ummi ta shiga ɗakinta ta shirya ta sauƙo kasa ƴan biyu suka fito. "Ummi unguwa za kije." Faɗin Hussaina da mamaki. "Eh ba jimawa za muyi ba, ku kula da gidan za mu kai magriba amma." "To Ummi Allah kiyaye." Ameen tace ta kama hannun Hanan da ta saka Hassana ta canza mata kaya suka fita Dr Awwab ya bi bayan su. Sai da suka hau titi Dr Awwab yace. "Ina za muje Ummi." "Damaturu wajen Noor." "Ummi na." Dr Awwab yace yana murmushi har hakoransa suka bayyana wushiryar shi ya fito. Daga haka bai ce komai ba yaci gaba da tuƙi suka ɗauki hanya. Kamar ta san gobe yake da niyar zuwa wajen Babynshi su yi magana ɗaya. Yayi missing ɗinta sosai, yana buƙatar ganinta. Ƙarfe uku da mintuna ya same su ƙofar gidan Mami, bayan yayi parking suka sauƙa yana riƙe da hannun Hanan suka shiga cikin gidan da sallama. Filin gidan babu kowa suka nufi cikin falon. Nuratu ne kaɗai a gidan Mami ta tafi auren Munirat da yau ake ɗaurawa. Tana kwance tana canza tashoshi dan neman abun kallo ya shigo cikin falon, kallon baƙin kofar tayi jin muryar wanda take tunanin me ya hanashi ƙiranta, ko yayi fushi ne? Ido suka haɗa ya bita da wani kallo, da sauri ta miƙe ta faɗa ɗakinta dan ba wani rigar kirki bane a jikinta, ta laliɓo hijab ta saka ta fito falon ta same shi da Ummi da Hanan, ta taho gurinta da gudu ta rumgume ta. Kallo ɗaya Nuratu ta ma Ummi ta hango tsantsan kama da take da Dr Awwab, wani kunya ne ya lullubeta ta zauna a ƙasa tana gaishe da ita kafin ƙasa ƙasa ta gaishe da Dr Awwab ya amsa idon shi saman fuskar wayar shi amma hankalinshi yana kanta. "Maman ki bata nan ne Noor?" Ummi ta tambayi Nuratu da har lokacin ta kasa kwakkwaran motsi a gurin, Hanan na jikinta ta cukwuikuyeta. Girgiza kai tayi cike da kunyar sunan da Ummi ta ƙirata da shi tace. "Eh ta fita, amma tace ba zata jima ba." "Shikenan bari mu jira ta zuwa nan da wani lokaci." To Nuratu ta amsa da shi ta miƙe ta wuce kitchen Ummi ta bita da kallo. "Noor akwai hankali, na lura tana da nutsuwa ga kunya." Murmushi kawai Dr Awwab yayi jin Ummi ta ya ba da zaɓinshi. Nuratu ne ta dawo ɗauke da tray babba da plate a sama ruwa ne sai zoɓon da Mami ta yi da rana da doughnut ta ajiye kusa da Mami ta wuce ɗakinta. Wayarta ta ɗauka ta ƙira Mami ta sanar da ita zuwan su kafin ta fito ta zauna nesa da su kusa da Hanan da take bata labarin makaranta tana amsa mata. Kusan mintuna goma Mami ta shigo da sallama, suka amsa Ummi ta ɗago idanuwanta ta bita da kallo cike da mamaki. Wani bugawa zuciyarta yayi ganin fuskar Mami. 'Suna kama.' Faɗin Ummi a zuciyarta cike da mamakin kamannin da ta hango saman fuskar Mami da wanda ba zata taɓa mance kamannin ba. "Sannun ku da zuwa." Mami tace tana zama. Sai lokacin Ummi ta amsa tana murmushi tare da dawowa hankalinta. "Sannu da dawowa." "Sannu ya hanya, kun sha hanya." "Allahamdulillahi na biyo ƴata ne." Ummi tace tana murmushi. "Ai kuwa gaki ga ita nan." Mami tace Ummi ta kai kallonta kan Nuratu da kanta yana ƙasa, a ƙarshe ta miƙe ɗauke da Hanan, Ummi tana ganin haka ta dakatar ta. "Dawo ki zauna Noor, magana za muyi dan ke na zo." A kunyace Nuratu ta dawo ta zauna kamar ta nutse ƙasa, ban da nauyin Ummi da take ji har shi Dr Awwab ɗin da yaƙi barin gurin idanuwanshi suke yawo a kanta sun takura mata. "Noor sai kuma abu ya zo lokaci ɗaya. Kuma na ji shuru nace bari in yi tattaki in saka baki." Nuratu da ta kasa cewa komai nauyin matar take ji sosai, ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa. Mami ne tace. "Nima dai ido na saka musu, amma kar ki damu, inshaAllah za ayi abu ɗaya za ku ji daga gareta kwana kusa." "To Allah ya kai mu." Ummi tace ta miƙe tsaye tana kallon Dr Awwab da ya kasa cewa komai. "Ta shi mu tafi kar muyi dare." Sallama suka ma Mami ta yiwa Ummi rakiya, Nuratu a bakin kofar falon ta koma tana sauƙe numfashi bayan ta yiwa Hanan bye bye ta koma. Mami a ƙofar gida ta tsaya kafin ta dawo ta samu Nuratu da ta koma ta kwanta. "Sai kiyi hakuri ki rumgumi ƙaddarar ki, kin ga dai matar nan takanas ta tako kafa dan ke. Dan haka ki saurari Doctor kuyi magana ɗaya." Mami tace tana zama kusa da Nuratu da ta saka kunne tana sauraron Mami. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 41. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Mami na amince na yarda zan zauna." Nuratu tace cikin sanyin jiki. "Ko ke fa Allah yasa haka shine alherin gaba ɗayan ku." Faɗin Mami. "Ameen." Nuratu ta amsa da shi ta wuce ɗakinta ta kwanta, wani zazzaɓi zazzaɓi ne ma ya kamata ta rufe jikinta. A hankali wani siraran hawaye suka zubo mata da ta rasa na menene. ... Dr Awwab bayan ya sauƙe Ummi da Hanan ya wuce gidanshi, ruwa ya watsa ya saka jallabiya ya sauƙo falon ƙasa yana neman lambar Nuratu. Yana ta ringing bata ɗauka ba ya tura mata saƙo. *"Babyna ki ɗauka ko gobe ki ganni na zo."* ... Nuratu da tana ganin ƙiran ta kasa ɗauka ta rasa mai za tace masa ta ga shigowar saƙon shi ta karanta, haka ta kasa ɗauka, ƙarshe ta kashe wayar gaba ɗaya. Ƙiranta Dr Awwab yayi yaji wayar a kashe yayi murmushi, yana son rigimar Noor. Tana son abu tana kaiwa kasuwa. Allah nuna masa ranar da za ta buɗe baki tace tana son shi. .... "Suna kama su biyun." Ummi tace riƙe da hoton marigayin mijinta da take hango fuskar Mami a jiki, duk da hoton ya tsufa ya jima amma kamannin bai ɓuya ba. Tun da ta dawo ta kasa nutsuwa, zuciyarta ya kasa tsayawa waje ɗaya. Hoton ta laliɓo cikin ma'ajiyar kaya da suke adanawa. Anan ta ƙara hango tsantsan kama da su biyun suke yi. Tayi mamakin Awwab da bai hango hakan ba tun tsawon shekaru. 'Akwai wani abun.' Ummi tace cikin zuciyarta kafin ta ajiye hoton ta fito falon jin hayaniya. Anan ta samu Binta ƙanwar mamar Hanan ce ta zo. Matashiyar budurwa, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe da Ummi ta amsa tana tambayar mutanen gida. "Duk lafiyar su ƙalau. Kwana biyu shuru shine na zo gaishe ku." "Yayi kyau mungode sosai." Ummi tace ta saka Hussaina kawo mata ruwa. Binta bata jima ba ta miƙe tsaye. "Ummi zan wuce sai anjima." Har waje suka rakota, duk yanda taso Hanan ta zo gurinta yarinyar ƙi tayi ta wuce, zargin su da mahaifiyarsu ya tabbata sun rabasu da jininsu. *** New Delhi. A hankali ya buɗe ido har ya buɗesu gaba ɗaya, tsawon kwana ɗaya kenan da masa aiki bai farka ba sai yau. Ummu da ke zaune da sauri ta danna wani guri da zai sanar da Dr ya farka kamar yadda suka nuna mata. Cikin sauri Dr ya shigo ya duba shi. Mufid sai binsu yake da ido. Ummu ta fita ta ƙira Alhaji Kashim suka dawo ɗakin tare. "Barka ya farka, a bashi abu mai ruwa ya sha sai ya fara shan magani. Zai ci gaba da shan magani na tsawon wata ɗaya kafin mu sallame shi. Sannan ya kiyaye shan duk wani abu da zai taɓa masa zuciya, in kuma ba haka ba aiki zai koma baya. Ko da ya warke ne ya ƙauracewa duk wani kayan maye dan lafiyarshi." Faɗin Dr Kushal cikin harshen turanci da yake gauraye da indiyanci. Alhaji Kashim ma cikin harshen turanci ya mayar masa da amsa. "Mun gode Dr Kushal. Amma har tsawon wata ɗaya bamu da isasshen kuɗin da zamu zauna anan ƙasar, in har zai yu zuwa nan da sati biyu a sallame mu." "Sai mun ga yanayin jikin shi." Dr Kushal yace yana fita. Alh aji Kashim ya matsa kusa da Mufid da ya rufe idanuwanshi. "Sannu Mufid ya jikin?" Sai lokacin ya buɗe ido ya kalleshi ya buɗe baki ƙasa ƙasa yace. "Da sauƙi." "Mufid ya jikin. Mai za kaci in kawo maka." Ummu tace tana matsawa kusa da shi ya kalleta. "Da sauƙi Ummu. Bana jin yunwa." "Ka daure dan Allah." Girgiza kai yayi ya juya. "Ki haɗamin black tea." Da sauri Ummu ta haɗa ta kawo masa da taimakon Daddy ya zauna, bathroom ya kaishi ya wanke bakinshi ya fito ya zauna yana jingina da filo dan jikinshi ba ƙarfi ko kaɗan. A baki Ummu ta dinga bashi ya sha kaɗan ta bashi magunguna kamar yadda Dr ya faɗa ya sha ya koma ya kwanta. Bai san mai ya faru da shi tsawon lokaci ba, shi dai ya farka ya ganshi kwance babu lafiya. *** Nigeria (Maiduguri). "Mama wallahi yarinyar nan ba yanda ban yi ta zo guri na ba taƙi. Ke kin ga har da kukanta kamar taga dodo." Binta tace da Mamarta bayan dawowarta daga gidan su Dr Awwab dan tabbatar da gaske ne kamar yadda su ka ji yayi aure, sai dai bata ga alamar hakan ba ya sata dawowa gida. Mama da ta ji mai tace tayi kwafa tace. "To ya maganar auren?" "Ban ji komai ba Mama." "To dai Allah yasa karyane, dan ba zan taɓa bari jikata ta tashi wajen matar uba ba." "Ah to dai." Faɗin Binta cike da jin haushin jin labarin da suke Dr Awwab yayi aure. Duk tsawon shekaru da aka ɗauka tsammanin su zai nemi auren Binta bayan su da suka nemi hakan ya nuna a'a, sun tsammaci bayan lokaci zai yarda, ta zauna ɗakin yayarta ta kula da ƴarta, sai suka ji labari ya sha bambam. *** Washegarin ranar Asabar babu aiki bacci Dr Awwab yayi har wajen goma kafin ya farka, yayi wanka ya shirya cikin ƙananan ya fita. Gidan Ummi ya biya suka gaisa yayi breakfast kafin ya musu sallama ya fita. Kai tsaye Damaturu ya nufa dan yana son suyi magana ɗaya da Nuratu. Ya ƙirata taƙi ɗauka ya tura mata saƙo babu amsa yana son ya ji mai ta yanke game da shi. In ta yarda ta zauna to in kuma ta ƙi su san abin yi. Ƙarfe ɗaya ya shiga cikin garin, sallar azahar yayi kafin ya ƙarasa gidansu. A waje yayi parking ɗin motarshi ya ɗauki wayarshi yana ƙiranta har lokacin yana ringing taƙi ɗauka ya tura mata saƙo. *"Babyna ki fito ina ƙofar gida."* ... Nuratu da tun safe take aiki dan babu mai yi, a lokacin ta samu ta kwanta bayan tayi wanka ta ɗauki wayarta ta ga missed call ɗin Walida ta ƙirata tana mata tsiya. Bayan sun gama wayar tana ajiyewa ta ga kiran Dr Awwab ta kasa ɗauka ta ajiye, shigowar saƙo taji ta ɗauka ta karanta. Da sauri ta miƙe daga kwancen da take jin abin da yace cike da mamakin rashin hutu da baya bawa kanshi kullum yana hanya. Kamar ba zata tashi ba ta miƙe ta ɗauki hijabinta ta ɗaura saman riga da skirt din jikinta ta fita, dan tunawa da nasihar Mami da ta mata akan tayi hakuri ta bawa zuciyarta dama. Ɗakin Mami ta shiga ta samu ta runtsa ta ja ƙofar ta fita, waje tayi anan ta hango motar shi ta tabbatar da gasken yake ya zo. Ido ya zuba mata yana murmushi, yana son Babynshi sosai. Fuskarta yake kallo har ta ƙarasa wajen shi kanta ƙasa ya buɗe gilashin motar yana ci gaba da kallonta yace. "Shigo ciki Babyna. Magana za muyi." Sai lokacin ta iya kallonshi, ya sakar mata murmushi ta ɗauke kanta zuciyarta yana bugawa ta girgiza kai. "Mu ƙarasa ciki dai da zai fi." "No wannan maganar sirri ne tsakanin mu. Please ki daure ki shigo ciki dan Allah ba danni ba." Dr Awwab ya ƙarasa maganar cike da roƙo. Haka ya saka Nuratu zagayawa cikin sanyin jiki tare da bugun zuciyarta da yake ƙaruwa ta buɗe ɗayan gefen ta shiga. Ƙamshin turaren shi dana morar ya haɗa ya bada wani ƙamshi mai daɗi da sanyaya rai, ga sanyin AC da ya gauraye cikin motar. Bayan ta shiga ta zauna ya juya yana kallonta yana ƙoƙarin juya kan motar yace. "Bari in nema mana wajen da za muyi maganar zai fi." "Ni dai muyi anan, ban sanar da Mami ba fa." Tace cikin sanyin murya cike da tsoro tsoro. "Mami ba abin da za tace in ta samu labarin kina tare da mijinki." Nuratu dai bata so haka ba, tana gani ya juya kan motar suka fita a unguwar bugun zuciyarta ya ƙaru. Tafiya suke babu wanda yayi magana sai kiɗan da yake tashi a motar na wakar larabci na Ali Abed, waƙar soyayya ne da Nuratu tana fahimtar wasu kalmomin, hakan ya sakata yin baya ta jinginar da kanta waƙar da sautin yana ratsa dodon kunnenta da ilihirin jikinta. Sosai Dr Awwab ya fahimci waƙar ya mata daɗi, hakan yasa ya kai hannu ya ƙara Volume su kaci gaba da tafiya. Kusan mintuna biyar dai dai waƙar ya ƙare sun tsaya a wani gurin shakatawa da babu mutane sosai ya shiga da motarshi gurin ajiye motoci da babu mutane a gurin, ya kalli Nuratu da take bin gurin da kallo. "Za mu shiga ciki ko za muyi maganar anan." "Muyi a nan dan Allah." Tace da sauri yayi murmushi yana gyara zamanshi ya rage volume din wakar da ya shiga na biyu ya fuskanceta. Kanta ƙasa tana wasa da zoɓen hannunta tana jiran ta ji mai zai faɗa mata. "Noor!" Ya ƙirata da sunan da ya jima bai ƙirata ba, ta ɗago ido ta ga nashi idanuwan cikin nata ta kawar da kanta gefe tana amsawa ƙasa ƙasa. "Baki za ki buɗe muyi magana Babyna." "Ina jin ka." "Ina so ki sanar da ni abin da yake cikin zuciyarki game da ni da auren mu. Shin kin yarda kin amince za ki zauna da ni a matsayin mijinki ko kuma har yanzu babu zancen aure cikin zuciyarki da rayuwarki. Ki sanar da ni gaskiya kar ki ɓoye min zan fahimci zancen ki." Shuru ne ya kauraye cikin motar bayan gama maganar Dr Awwab yana jiran amsar Nuratu da tayi shuru tana juya maganganushi cikin zuciyarta da ƙwaƙwalwarta. Bata ankara ba taji saukar hannunshi duka biyun saman nata ya riƙo. Wani ɗumi taji a hannuwansa duk da sanyin AC dake kunne a motar. Da sauri ta ɗago kai tana ƙoƙarin kwacewa tace. "Me hakan dan Allah. Ka sake min hannuna." "Sai kin bani amsa." Dr Awwab yace yana ƙara damƙe hannunta. Kamar za tayi kuka tace. "Ni tsoro nake ji." "Tsoron me? Ni ko kuma waye?" Kan Nuratu ƙasa tana kallon hannunta da ke cikin na Dr Awwab da ya damƙe tace. "Tsoron gori nake, bani da abin da zan baka Dr, bani da komai, baka cancanci haka ba, baka cancanci mace kamata ba, ina tsoron watarana ka mini gori, ina tsoron danginka su mini gori ko su dinga jifa na da munanan kalamai, ba zan iya jura ba." Shuru Nuratu tayi wani abu ya tokare mata wuya, hawayen da ya taru a idonta ya zuba saman hannun Dr Awwab da sai lokacin ya ankara, wani tausayin Nuratu na ƙara shiga zuciyarshi. Hannunta ya ƙara damƙewa cikin nashi da hannu ɗaya, ya saka ɗayan hannunshi ya ɗaura saman fuskarta Nuratu ya ɗago kanta yana kallon cikin idanuwanta, ta runtse idanuwanta da sauri. Hannu ya saka ya share mata hawayenta yana cewa. "Nasha faɗa miki cewa Awwab ba abin da yake buƙata wajenki sai soyayyar ki da neman amincewa ki aure shi. Ni fa musulmi ne Babyna na san ƙaddara, ni Awwab na miki alƙawari ba zan taɓa buɗe baki in miki gori ba da sunan wani abu daban ba. Ba zan ce miki babu abin da zai shiga tsakaninmu ba, amma duk yadda ki ke haka na ji na gani zan karɓe ki." Wani nutsuwa ne ya shiga Nuratu, ajiyar zuciya Nuratu ta sauƙe tana kwace fuskarta a hannun Dr Awwab dan wani iri take ji a fuskarta, kanta ta sunkuyar ƙasa. "Faɗi maganar ki Babyna. Na lura kina da abin faɗa." Dr Awwab yace yana ƙara matse hannuwanta ta lumshe idanunta buɗe jin yadda yake matsa hannuwanta, ƙasa ƙasa tace. "Yanzu Ummi ma ta san mai ya faru da ni, da kowa ma cikin family?" Girgiza kai yayi yace. "A'a, babu wanda ya san mai ya faru da rayuwarki daga ni sai ni, ban sanar da kowa ba. Sirrin mu ne fa Babyna, in na faɗa tamkar tonawa kai na asiri ne. Kuma babu ranar faɗar hakan har abada. Zuwan Ummi na jiya kawai ta zo ne gani take tamkar dole na miki bakya so na na aureki, nima ban san da tafiyar ba sai da muka fito." "Nagode." Nuratu tace cike da nutsuwar da ta ji ya sauƙar mata a zuciya da gangar jiki. Murmushi Dr Awwab yace. "To ya muke ciki yanzu? Kin yarda za ki zauna da ni?" Kunyane ya kama Nuratu ta kwace hannunta ta rufe fuskarta da shi tana murmushi. Dr Awwab ya matsa kusa da ita daf da kunnuwanta ta ji ya furta. "Nagode sosai da ki ka yarda da ni ki ka amince dani na zama mijinki. Ina mana fatan alheri. Ina son ki sosai Babyna." Baya Nuratu ta yi tana jan hijabinta ta rufe fuskarta da shi cike da wani mugun kunyarshi da ya lulluɓeta. Dr Awwab motar ya buɗe ya fita ya shiga ciki ya fito kusan mintuna ɗauke da ledoji ya saka a baya ya shiga motar yana barin gurin. A ƙofar gidan su yayi parking, Nuratu tana ƙoƙarin fita ya kwaso ledojin baya gaba ɗaya ya ɗaura mata saman cinyarta. "Na san ba kici komai ba na ɗauko ki." "Yamin yawa ai. Na ci abinci fa." Tace tana marairaice masa. "To raba mana." Babu musu Nuratu ta buɗe tarkacen, ice cream ne da burger da shawarma. Ta raba kashi uku ta haɗa kashi biyu ta ɗauki kashi ɗaya, duk Dr Awwab yana kallonta, ganin abin da za tayi ya sashi saka hannu ya karɓi na hannunta, babu musu ta sakar mishi ya ɗauki mai yawan ya ɗaura mata. "Ki gaishe da Mami sai munyi yawa. Wannan ma ya ishe ni ba ci zan yi ba My Love zan kai wa." Nuratu ba taso ba ta ɗauka ta fita tana mishi godiya, sai da yaga shigewarta cikin gida kafin ya ja motarshi yana barin harabar wajen. Zuciyarshi fes ciki da farin ciki Babynshi ta amince ta yarda zata zauna da shi a matsayin miji, ya san gaba kaɗan zata fahimci soyayyar da take masa. ... Tana shiga cikin gidan a falo ta samu Mami ta farka ta bita da kallo. "Ina ki ka je ne tun ɗazu ina ta neman ki." "Na ɗan fita ne." Nuratu tace ta ajiye kayan hannunta ta wuce ɗakinta, alwala tayi ta gabatar da sallar la'asar kafin ta fito falon ta zauna tana buɗe kayan da Dr Awwab ya saya mata. Burger ta iya ci ta sha ice cream din kaɗan ta tarkata sauran ta saka fridge. Mami dai ido ta saka mata har ta gama ta kwanta. "To mai amfanin kin saya kin kasa ci." "Na ƙoshi sai anjima." Nuratu tace ta canza salon hiran. *** MAIDUGURI. Dr Awwab yana isa Maiduguri gidan Ummi ya nufa, a falo ya samu Hanan tana kallon cartoon ya zauna kusa da ita yana ajiye mata kayan hannunshi kusa da ita. Juyowa tayi tana buɗewa lokacin da yace. "Ga tsaraba My Love." Ihu ta saka ganin abinda ya kawo mata ta rumgumeshi. "Thank you so much My Daddy." Ihunta shi ya fito da ƴan biyu da sauri, duk tsamanin su wani abin ya sameta ne suka ga ita da mahaifinta ne suka koma. Ice cream din ta sha dayawa da shawarman, ta ɗauki sauran ta kai kitchen ta saka fridge ta fito ta samu baya nan taci gaba da kallonta. Dr Awwab gidan shi ya wuce dan huta gajiya, wanka yayi ya gabatar da sallar magriba ya kwanta saman doguwar kujera ya laliɓo numbern Nuratu. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  42. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... "Babyna shine babu ƙira ki tambaye ni na isa lafiya." Dr Awwab yace jin Nuratu ta ɗauka tayi shuru. Kamar ba za tace komai ba ƙasa ƙasa tace. "Ya hanya? Ina Hanan?" "Allahamdulillahi lafiyarta ƙalau. Me ki ka cewa Mami da ta tambayeki ina ki ka je?" "Babu komai." "Sai ki sanar da ita mijinki ya ɗauke ki kun fita." Yace yana murmushin da take jin sautin shi. "Ni dai sai anjima, bacci zan yi." Nuratu tace da sauri ya dakatar da ita. "Wayo za ki mini dai. To ki yi bacci lafiya sai da safe." Kit ta kashe wayar ta ajiye tana sauƙe numfashi, ji take kamar yau suka soma waya da shi, dan jin yanda numfashinta yake riƙewa kamar budurwar da take hira da saurayin da ta mutu a son shi da ko muryarshi ta ji sai jinin jikinta ya tsaya. *** New Delhi. Ɓangaren Mufid yana samun dukkan kulawar da ya kamata a bashi daga Ummu da likitoci, jikin shi yayi sauƙi har ya fara wasu abubuwa da kanshi. Daddy kuɗaɗen hannunshi duk ya ƙare burin shi su cika sati uku a sallamesu. Can gida yayi waya a turo masa kuɗi, an sai da motar Mufid da nashi ɗaya an haɗa an turo shima ya kusa ƙarewa. Cikin ikon Allah Mufid tun farkawar shi bai ƙara musu maganar Nuratu ba, hakan ya yiwa Ummu da Daddy daɗi, na shi bangaren kuwa har lokacin da tunaninta yake kwana yake tashi. Duk da ya san zuwa yanzu ta masa nisa ta zama matar wani ya san abu ne mai wahala ya cireta a ranshi. Wahalar da ya sha ganin ya kusa mutuwa ya sashi jin tsoron Allah da duniya ta shigesa. Ya cire komai na harkar barikanci a ranshi, yaji komai ya fice masa a rai. Burin shi ya koma gida ya nemi yafiyar duk mutanen da ya zalunta ko zai samu rahamar Allah. Bashi da aiki kullum sai zama cikin tunanin rayuwar da ya gudanar da babu komai na khairi sai lalaci da hakan yake saka shi nadama sosai. Shuru shurun da ya zama shi yafi damun Ummu, take cewa ko dai bashi da lafiya, ya nuna mata lafiyar shi lau kawai hayaniya ne baya so. *** DAMATURU. Ranar wata alhamis karfe taran safe Alhaji Mamman ya shirya bayan ya yi breakfast ya miƙe yana kallon Amma Jidda. "Zan leƙa kasuwa in dawo. Ki shirya za ki min rakiya in na dawo." "To a dawo lafiya." Amma Jidda tace ta miƙe ta tattara wajen ta koma ɗaki. Ameera ce ta shigo ta mata sallama za ta wuce makaranta ta ciro ɗari biyar ta bata. "Gashi kiyi kuɗin mashin, har yanzu Abban ku bai samu kuɗi ya gyara wancan motar ba." "Amma, Amma ya haka dan Allah yau fa wajen sati biyu mashin nake hawa." Fuska Amma Jidda ta ɗaure tana duban Ameera. "Eh sai aka yi ya? Ke da fa ba yanzu bane komai ya lalace sai addu'a. Kina ganin dai abubuwan da suke faruwa a gidan nan. Abban ku bashi da aikin yi sai kasuwanci da yanzu shima ba tafiya yake ba." Gunguni Ameera tayi ta fita, ita dai ba zata iya sabuwar rayuwar da aka soma a gidan ba da hatta cimarsu ta fara canzawa. Abin da basu sani ba tun tasowarsu, sunga kuɗi sunga jin daɗi, yanzu lokaci ɗaya ace za su fara wani rayuwar. .... Alhaji Mamman ƙarfe uku ya dawo, sai da ya gabatar da sallar la'asar yaci abinci kafin yace. "Ɗauko mayafinki mu je." Da sauri ta saka mayafinta babba suka fita a gida. Tafe suke tana ganin ikon Allah da bai mance unguwar da gidan ba har kofar gidan Mami ya faka motarshi yana kallon Amma Jidda da take bin shi da kallon mamaki. "Shiga ki sanar da ita zuwa na." Babu musu ta fita ta shiga cikin gidan Mami da fara'a ta tare ta suka shiga falon. Bayan sun gaisa Amma Jidda tace. "Tare muke da baƙo Maminsu Rahma." Da mamaki Mami tace. "Baƙo kuma? Waye haka da ba zai shigo ba." "Abbansu Rahma ne. Dan Allah kar kice ba za ki saurareshi ba. Wallahi ya canza, komai ya canza Mami. Yanzu da baya ba ɗaya bane, nadama ya shigesa ya gane laifinshi." Fuska Mami ta ƙara ɗaurewa. "Jidda ina ganin mutumcinki da ƙimarki albarkacin yara, dan haka in dai abin da ya kawoki ne kiyi hakuri ki dai na min maganar nan. Na riga na cire shafin Alhaji Mamman a rayuwata haka Nuratu ma." "Yafiyar ki ya zo nema. Shin ba zaki yafe masa ba." "Ki bar maganar nan Jidda." Mami tace tana ƙara haɗa rai. Duk yadda Amma Jidda tayi Mami ta saurareta ƙi tayi, haka ta hakura ta mata sallama ta fita. "Ya ya ta amince?" Alhaji Mamman yace bayan zaman Amma Jidda a motar. "A'a wallahi ta ƙi sauraro na." "Shikenan kar ki damu na san mai zan yi." Daga haka ya ja motar suka bar ƙofar gidan. *** Bayan sati uku. Yau an tashi da sanyi sosai dan sanyi da ya shigo. Har ƙarfe goma Nuratu tana cikin bargo bata farka ba, duk faɗan Mami ta fito ta ɗaura abincin safe ko ta mata shara kasawa tayi dan tana tsoron sanyi sosai. Bacci ta koma bayan sallar asuba, sai karfe goman ta farka ta ƙi fita, duk da yunwar da take ji kasawa tayi tana duƙunƙune cikin bargo, wayarta da ƙaranshi ya farkarta da ita ta ga Dr Awwab ne. Kwana biyun ba suyi waya ba, ji tayi kewarshi da sauri ta ɗauka. "Babyna." Yace daga ɓangaren shi da ya saka Nuratu lumshe idanuwanta ta buɗe. Dole ta fara amsa sunan da duk lokacin da ya ƙirata dashi sai taji yafi kowa iya furtawa akan leɓɓanshi. Katse mata tunanin da take yayi ta hanyar cewa. "Babyna yau sanyi ake sosai gashi na kasa fita aiki, na san da kina kusa za kimin maganin sanyin." Nuratu kamar ta zuba ihu jin abin da yace ta ɓata rai kamar yana gabanta tace. "Ni ma sanyin nake ji ai." "Don't tell me kina cikin bargo har yanzu." Yace da mamaki. "Eh ban fita ba tun safe." Dariya Dr Awwab yayi har taji sautin shi yace. "Babyna in kin zo ma haka za kina mini. Tsoron sanyi kike ji." "Sosai ma." Tace tana turo baki. "Kin cika ragwanta Babyna. Allah dai ya kai mu in rage miki wannan ragwantar." Nuratu kamar za tayi kuka jin abin da yace tace. "Wallahi zan kashe wayar in ba zaka daina min irin wannan maganar ba." Dariya ya sake yana ɗaukar tissue ya tare atishawar da zai yi, dan mura ne ya kamashi saboda sanyi, bayan yayi yace. "To na bari. Yaushe zaki tare ne? Na fara gajiya wallahi." "Ni ba yanzu ba dan Allah. Sai nayi service nan da shekara ɗaya." "Service dai Babyna? Ke da service sai dai a gidanki, kafin lokacin mana. Ki tausayawa maraya mana, kin ga yau ma ban da lafiya, mura yamin mugun kamu, na san da kina kusa rashin lafiyan zai zo da sauƙi." Wani tausayin shine ya kama Nuratu jin bashi da lafiya tace. "Allah sarki Allah baka lafiya. Ni dai sai nayi service dan har sunan mu ya kusa fitowa a second batch." "Dan Allah fa maganar gaskiya Babyna? Har lokacin ya kusa." "Dagaske nake Allah." 'Na shiga uku.' Dr Awwab yace a zuci da ya fito har fili ya saka Nuratu yin dariya ƙasa ƙasa, shima dariyar yayi jin ta ji yace. "Allah yasa kar su tura min ke wani garin can mai nisa su duba aure, balle ma inshaAllah ba za suyi haka ba tun da mun sanar da su akwai aure." Ba tayi magana ba dan ita ma bata son yin nisa da gida. Jin shurunta ya saka Dr Awwab cewa. "To Allah kaimu lokacin, mu ga ina aka tura ki sai mu san abin yi." Ameen ta amsa da shi yace. "Zan ƙoƙarta in fita office." "To a dawo lafiya. Ka biya ka gaishe min da Hanan." "An gama ranki daɗe." Yace Nuratu tayi murmushi ta kashe wayar ta miƙe, bathroom ta shiga tayi brush ta fito falon ta samu Mami. "Mami breakfast ɗina?" "Kina kwance zan dafa miki? Ki je ki dafa abin ki." Kitchen Nuratu ta wuce ta tafasa indomie da kwai ta dawo falon ta zauna ta hau ci. ... Satin biyu kafin hakan wata ranar juma'a Dr Awwab ya zo ya taimaka mata ta bada shaidar aure, ta canza sunan mahaifi zuwa sunanshi dan yin hakan shi zai saka su turata guri mafi kusa ko garin mijinta. *** Ƙarfe shida ya kama hanyar dan so yake ya isa da wuri ya dawo komin dare. Wajen ƙarfe sha ɗaya ya shiga cikin ƙasar ya kama hanyar garin da ba zai taɓa mantawa. Abubuwa da yawa suna dawo mishi na shekaru da ya shuɗe. Bai kyauta ba, bai kyautawa rayuwarta ba a matsayinta na marainiya babu uwa babu uba. Nadama da dana sani ne yake shiga zuciyarshi dangane da abinda da ya aikata mata da kwanshi. Ya bi ruɗin shaidan da zuciya da aboki da ƙarya ya wulaƙanta jininshi da matarshi da tun haɗuwar saurayi da budurwa. Har ƙofar gidan yayi parking bai mance ba tsawon shekaru ashirin da huɗu. Sauƙa yayi ya tsaya kofar gidan tare da sallama. Musalle da yake ɗakinshi ya amsa ya fito ya bishi da kallo. "Yaya Muhammadu yana nan?" Alhaji Mamman ya tambaya yana amsa gaisuwar Musalle. "Ya fita kasuwa tun safe." "Ko zan iya jiran shi, Baban Nuratu ne." Alhaji Mamman ya faɗa cikin wani irin yanayin danganta kanshi da yayi da Nuratu. "Baban Nuratu dai? Shigo ciki babu damuwa." Musalle ya faɗa yana bashi hanya ya wuce ciki, har ɗakinshi ya shigarshi ya shimfiɗa masa darduma ya kawo masa ruwa. "In kana saura in ƙira shi ya dawo." Faɗin Musalle. "Da hakan zai fi ina son in koma gida a yau." To kawai Musalle yace ya kira Kawu Muhammadu ya sanar da shi yayi baƙo daga Damaturu, kuma a yau zai koma in zai samu ya zo. "Bari in zo sai ka zauna min in kaji sauƙi." Faɗin Kawu Muhammadu ta ɓangarenshi Daga haka ya amsa da to ya kashe wayar ya sanar da Alhaji Mamman yana zuwa ya fita. *** Maiduguri International Airport. A hankali ya sauƙo cikin jirgin yana takawa a hankali tare da taimakon sandarshi da take tukarawa. Bayan shi Ummu da Daddy ne suka bin sa a hankali suna riƙe da jakakkunan kayansu, har suka gama fitowa suka fita a airport ɗin suka tare taxi dan wucewa gida. Mufid sai bin garin yake da kallo da mutanen ciki yanda kowa yake gudanar da rayuwarshi hankali kwance a nutse. 'Duk su suka gurɓata mini rayuwa.' Yace a ranshi, dan duk abinda ya samu rayuwarshi laifin kwacakom ya ɗaura akan Ummu da Daddy da kwata kwata baya sake musu fuska, baya marmarin sake rayuwanda su. Har ƙofar gidansu mai taxi ya ajiyesu, Alhaji Kashim ya bashi kuɗinshi kafinsu ƙarasa shiga cikin gidan. A falon Ummu suka sauƙa, suka samu Aunti Humaira da sauran yayun Mufid biyu sun zo da mai bin shi da Rufaida da ƴaƴansu. Kowa ya gaishe sa ya mishi ya jiki ya amsa yana wucewa ɗaki, Rufaida ta bishi da kallo tana addu'ar Allah yasa shiriyarshi kenan. Da daddaren ya samu baƙoncin Faisal ban da AA, hanashi shigowa falon yayi ya lallaɓa suka filin gidan duk da sanyi da ake yi ya saka rigar sanyi. "Gaye ka ga mutuwa ashe." Murmushin ƙarfin hali Mufid yayi. "Sosai da taimakon Allah na taso. Ina AA ne? Babu wanda ya neme ni cikin ku, da mutuwa nayi sai dai ku zo ta'aziyya." "Komai ya lalace MKM, bamu da gabas da yamma da tudun dafawa. AA yana asibiti ya kamu da cuta mai karya garkuwar mutum, bayan ciwon jeji da yake shirin kamashi. Ni kuma nan da ka ganni gurin kwana ma ya fara gagarana balle ci da sha." Faisal yace cike da jimamin halin da suka tsinci kansu. Mufid yana duban shi da haske kwan lantarki da na farin wata yace. "To Allah dafa mana, domin ni kam bani da wani burin sake gurɓattacciyar rayuwa." Dafa kafaɗarshi Faisal yayi. "Anya Mufid ba alhakin yarinyar nan yake bibiyar rayuwar mu ba?" *** Bayan dawowar Kawu Muhammadu Musalle ya wuce kasuwa dan zama masa a shagon, ya rage daga Alhaji Mamman sai Kawu Muhammadu da yake cike da mamakin ganin Alhaji Mamman bayan tsawon shekaru ashirin da huɗu. Bayan haka ma rashin mutumci da ya shuka kwanan nan akan auren Nuratu bai tsammaci ganin shi ba a daidai wannan lokaci. "Ina sauraron ka Alhaji." Kawu Muhammadu yace fuskarsa babu alamun fara'a babu alamun ɓacin rai dan jin da me ya zo. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 43. Pharty Bb Wattpad phartybb. *** "Alhakin Nuratu ke bibiyar rayuwar mu Faisal, alhakinta da na mutanen da muka cuta ne yake bin rayuwarmu da har abada ba zai daina hakan ba sai mun samu yafiyarsu musamman Nuratu, bata ji bata gani ba na cuci rayuwarta, na gurɓata mata rayuwa, na tarwatsa farin cikinta da komai nata." Mufid yake faɗan haka da Faisal ya ji jikinshi yayi mugun sanyi. Lalle rayuwar bariki ba rayuwa bace. "Mufid mun zaɓarwa kan mu rayuwa mafi muni, fatan mu Allah ya yafe mana, duk da wuya mu bar wasu abubuwan domin ya riga ya zama jinin jikinmu." Girgiza kai Mufid yayi yana kallon taurarin da suka fito ɗaiɗaiku dan hazo yace. "Na tuba Faisal, na tuba daga yin komai, burina da addu'a na Allah yafe min kura kurai na, sannan Nuratu ta yafe min abin da na aikata mata, in samu aikin yi nima in yi aure in ga nawa kwan a duniya kafin in koma ga mahalicci na, in bar iyaye na da sune duk sanadin ɓacin rayuwana." Faisal da yake kallon Mufid tamkar ba shi yake furta kalmomin ba yace. "Allah baka nasara Mufid, nima zan so neman yafiyar yarinyar nan." "Ameen. Zan koma ciki akwai sanyi. Ka gaishe da AA in na ƙara jin sauƙi zan leƙo in gaishe sa." "Zai ji da yardar Allah." Faisal yace, anan su kayi sallama Mufid ya koma cikin falo, Faisal ya fita. *** Kawu Muhammadu yana sauraran bayanin Alhaji Mamman har ya gama ya kara da cewa. "Wallahi Yaya Muhammadu sharrin shaiɗanne da zuciya da kuma biyewa shawaran aboki. Dan Allah ka taya ni neman gafaran Sadiya, na san na cutarta ita da ƴata, amma wallahi nayi nadamar abin da na aikata musu. Dan Allah ka nema min gafarar su." Ajiyar zuciya Kawu Muhammadu ya sauƙe sai lokacin ya sake fuska yace. "To dai Alhaji Mamman taimako ɗaya zan maka shine in ƙira Sadiya in mata magana, idan amince to. In kuma ta ƙi ba yanda zan mata." "InshaAllah za ta amince in kai ne." Alhaji Mamman yace har lokacin zuciyarshi tana hasko masa tsantsan kamanni da su biyun suke, har da ita Sadiyar da kamanceceniyar da nasu da ita kaɗan ne. "To zamu gwada mu gani." Kawu Muhammadu yace ya miƙe ya fita dan kawo masa abin sha. 'Suna kama sosai.' Alhaji Mamman yace duk da wahala da girma ya kama Kawu Muhammadu amma hakan bai ɓoye kamanceceniyar fuskar su da shi ba, duk da shi wancan kuɗi da jin daɗi ya ɓoye girman fuskarshi da shekarunshi. Shigowar Kawu Muhammadu ya dawo da shi hankalin shi ya karɓi abun hannunsa ya ajiye. Abinci ne da kindirmo mai kyau. Kaɗan ya ci yace ya ƙoshi ya miƙe. "Zan tafi Yaya sai na ji daga gurin ka." "To Allah kiyaye." A gurin su kayi musayar lambar waya kafin Alhaji Mamman ya tafi. Ji yake komai zai zo da sauƙi tun da ya samu Kawu Muhammadu kuma ya yarda da batunshi. *** Kwanakin da suka gabata Nuratu bata samun zama dan zirga zirga da take na tafiya service in da sunansu ya fito suka turata Maiduguri kasancewar tana da aure. Nuratu bata so hakan ba ganin sun turata Maiduguri ta sanar da Mami. "Sai ki tare kawai kinga kin hutar da kowa." Jin abinda Mami tace yasa Nuratu ɓata rai. "Mami sati biyu fa ya rage, haba dan Allah ku bar ni na gama mana abun shekara ɗaya." Rai Mami ta ɓata. "Bana son wannan shashancin, idan har Dr Awwab ya tambayeki mafita, sannan ya buƙaci ki tare ki sanar da shi kin amince." "Amma Mami ba ayi gaggawa ba. Dan Allah kiyi hakuri ki barni." "Ba zan yi ba, aure ne a kan ki, umarnin mijinki za ki bi, ba na kowa ba, duk abin da ya nema ki yarda dashi ki masa biyayya." Daga haka Mami ta shige ɗakinta ta bar Nuratu zaune da turɓunannen fuska. Mami tana shiga ɗaki ta ƙira Rahma ta sanar da ita ta zo gida tana nemanta, ƙiran Aunti Zarah ma tayi tace ta zo za suyi magana. Dukkansu suka ce da yamma suna tafe. Nuratu babu walwala ta wuni, Mami na lura da ita ta ƙi mata magana. Zamanta ya isheta haka ta je itama gidanta ta zauna tayi bautar aure kamar kowa, tasan Dr Awwab ya mata hakuri har tsawon wata ɗaya da wani abun bai mata maganar tarewa ba. Da yamma Aunti Zarah da Rahma har da Aunti Hasiya suka zo, bayan Nuratu ta gaishesu ta ƙi barin gurin ko za su sako maganar su saka baki Mami ta janye kudurinta. Amma abin mamaki Mami tana sanar da su hukunci da ta yanke suka amsa. Aunti Rahma tace. "Kinyi daidai Mami, hakan yafi ai ta je can gidanta ta yi service ɗinta, ta godewa Allah ma da garin mijin aka tura ta." "Aunti Rahma ke ma." Nuratu tace kamar tayi kuka. Harara ta watsa mata tace. "Dalla rufemin baki, ana nema miki gata kin tsaya wasa da shi. Ƙira Dr Awwab ɗin ki haɗani da shi a waya." Gunguni Nuratu ta fara za ta bar gurin Aunti Hasiya ta fizgota rai ɓace. "Zan ɓata miki rai wallahi banza wawiya kawai." Kuka Nuratu ta fashe da shi ganin haka ya saka Aunti Zarah kama hannunta suka fita. Cikin ɗakin Nuratu suka shiga ta zaunarta a bakin katifarta ta zauna. "Share hawayenki haba amaryar Awwab." Hawayenta ta share Aunti Zarah tace. "To me na kuka kuma Nuratu bayan an riga an ɗaura auren, komai dai daren dadewa sai kin tare. Kiyi hakuri ki tare gidanki kiyi karatun ki cikin nutsuwa. Amma yanzu kina zirga zirga da aure kina jin za ki ji daɗin haka, ko shi Dr Awwab ɗin zai so haka, ko danginshi za su so haka? Kina gani dai mahaifiyarshi har gidan nan ta taso musamman dan ke, to ko albarkacinta ai kya hakura Nuraru." "Ni dai Aunti yayi sauri sati biyu ne wallahi." Nuratu tace tana share guntun hawayenta. Girgiza kai Aunti Zarah tayi. "Bai yi ba Nuratu kwana goma sha biyar, ana kai ki da kwana biyu sai ki shiga fara zirga zirganki. Wa yaga amarya a camp." Aunti Zarah ta ƙarashe maganar tana dariya da ya saka Nuratu jin kunya ta rufe fuskarta. Nasiha Aunti Zarah tayi ta mata har taji nutsuwa ta saka hakuri a ranta kafin ta fita ta sanar Mami cewa ta amince nan da kwana goma sha biyar. Mamu tace. "Sai ku fara shiri ku manyan yayu, ni na gama nawa dan na riga na sayi kayan ɗaki da wasu abubuwan, tun sati biyu da ya wuce babu wanda na sanar." Da mamaki Aunti Rahma tace. "Shikenan zamu haɗa da Hasiya muyi sauran." "To Allah kai mu ya bamu iko." Aunti Hasiya tace suka amsa da ameen, anan su kayi ta tattaunawa kan bikin har ƙarfe shida kafin su bar gidan. Da daren Dr Awwab kamar yasan mai yake faruwa ya ƙira Nuratu. Tana kwance dan ciwon kai da yake damunta ta samu ƙiran ta ɗauka. Ƙasa ƙasa ta amsa tana gaishesa. "Me ya samu Babyna? Na ji muryarta wani iri?" Dr Awwab yace jin muryar Nuratu ya canza. "Bana jin daɗi kai yake ciwo." Ta faɗa tana ƙara ƙasa da murya. "Sorry My Baby kinsha magani? Da ina kusa nayi maganin ciwon nan amma kin hanani dama." Shuru ta mishi tana son sanar da shi yadda su kayi da su Aunti Zarah ta kasa. A hankali tace. "Doctor sunan mu ya fito." "Sunan ina? Zuwa camp? Ina suka turomin ke, bana son kiyi nisa ki barni Babyna. I need you beside me." Dr Awwab ya ƙarasa maganar cike da buƙatar hakan, dan hakurinshi ya fara gazawa. Kamar me bata so tace. "Maiduguri suka turo ni." "Allahamdulillahi." Dr Awwab yace da ƙarfi Nuratu tayi murmushi har yaji sautinshi. Cike da farin ciki Dr Awwab yace. "Thanks God, kamar sun san ina buƙatar matata kusa da ni. Please Babyna kafin ki tafi ya kamata ki tare gidanki, in kuma ba haka ba kin ga kin zo garinmu wallahi har camp za ina biyoki in ɗauke ki, balle ma babu zaman camp tun da kina da aure." Baki buɗe dan mamaki tace. "Ni dai ka rufamin asiri." "Gani ki ke ba zan iya ba?" "Yanzu kai sai ka ɗauke ni." Murmushi yayi daga kwancen da yake yana cewa. "Sa wasa ki gani, duk abin da Awwab ya faɗa sai ya aikata shi fa. In kuma so kike ki gama bautar ƙasa da jikan Ummi to shikenan." Da sauri Nuratu tace. "Dan Allah kayi haƙuri. Ka ƙira Aunti Rahma kuyi magana." "Dagaske Babyna." Dr Awwab yace cike da ɗoki tace masa eh ta kashe wayar gaba ɗaya tana juya kalamanshi. Rashin kunyarshi gareta ya fara isarta. Dr Awwab kasa nutsuwa yayi a laliɓo lambar Aunti Rahma ya ƙirata, bayan ta ɗauka sun gaisa sai kuma ya rasa ta ina zai tambayeta hakan yasa Aunti Rahma tace. "Kunyi magana da Nuratu ne?" "Eh Aunti." "To sai ka fara shiri nan da kwana goma sha biyar mun riga mun yanke ranar." "Allah kaimu Aunti nagode." Yace ya kashe wayar cike da farin ciki ya miƙe ya fita a gidan. Gidan Ummi ya isa bayan sun gaisa ya sanar da ita yanda su kayi. "MashAllah Allah kaimu da rai da lafiya, sai mu fara shiri." "Sosai ma Ummi ban ga zama ba." Dr Awwab ya ce yana fita a gidan ko ta kan Hanan bai bi ba. *** "Daddy ina son cigaba da karatuna tun da na samu lafiya, ina son in gama nima in samu aikin yi in tsaya da kafafuna kamar kowa." Alhaji Kashim yana jin mai Mufid ya faɗa har ya gama yana dubanshi ko ya koma shaye-shaye ne yace. "Yanzu kai Mufid duk tsawon lokacin ba kayi karatun ba sai yanzu. Kar ka sani asaran kuɗi ka ga komai ya lalace bani da wasu ashasshen kuɗi yanzu." "Shi yasa nima nace zan koma karatu dan in samu na kai na, in kuma ba zaka iya min komai ba zan fita na nema da kai na." Cikin sauri Alhaji Kashim yace. "Abun bai kai ga haka ba, in an koma zan nema maka gurbin karatun, sai ka gyara papers naka muga abin da Allah zai yi." Jin abin da Daddynshi yace ya miƙe ya bar masa gurin. A gidan baya shiga harkar kowa baya fita sai ya kama, wani shuru shuru ya zama, magana ma baya yi sai dole. *** Cikin satin dukka familyn biyun shirye-shiryen biki suke, Mami da yaranta sai shiri suke sosai kowa yana ƙoƙarin kyautawawa Nuratu. Ɓangaren Nuratu jinta take wani iri, zata shiga sabuwar rayuwa da bata taɓa kawo haka a rayuwarta ba. Mai gyara na musamman Aunti Rahma ta kawo daga Maiduguri dan ta gyarata ciki da waje. Ita dai Nuratu nata ido, domin abin da ka riga ka rasane wanda ba zai taɓa dawowa ba. Dr Awwab nasu bangaren ma shiri suke duk ya gayyato na kusa dana nesa, duk da ya sanar da su ɗaurin auren an riga anyi reception kawai za ayi sai ɗauko amarya. Ummi har danginta na Libya da zama ya kai su can ta sanar da su tare da basu hakurin abin yazo cikin gaggawa ne, sun mata alƙawarin zuwan mutum biyu zuwa uku inshaAllah, haka danginta na Nijar ma. Alhaji Mamman ta bakin Amma Jidda ya samu labarin dan zirga zirga da take babu zama ta sanar da shi Nuratu ne zata tare. Murmushi yayi yace. "Allah ya bata zaman lafiya da mijinta. Yaron yana da nutsuwa na san zai bata gatan da duk ta rasa." "Ameen ya Allah. Hakane kam Dr Awwab akwai nutsuwa." Amma Jidda ta amsa da shi daren ranar da ta dawo daga gidan Mami su kayi wannan maganar. Washegarin Alhamis akan jibi Asabar Nuratu za ta tare, da safe Alhaji Mamman ya wuce kasuwa kuɗaɗenshi ya haɗa na cinikin kwana biyu dubu ɗari biyar ya nufi gidan Mami da su. Gidan mutane sun fara taruwa dan ƴan Nijar yau suka iso ciki har da Nazifa da Mama Yawuro. A ƙofar gidan ya tsaya kafin ya shiga ciki kai tsaye matan ɗaiɗaiku da suke filin gidan suka amsa da shi ya wuce falon, babu mutane sosai domin ƴan matan sun ɗauki amarya Nuratu sun tafi gidan lalle. A falon ya zauna ya tura ƙaramar yarinya ta ƙira masa Mami. Mami da ke cikin ɗakin tana shirya wasu kaya ta samun ƙiran ta fito. Ganin wanda yake zaune ya sata haɗa rai, ba dan Yaya Muhammadu ya ƙirata ya sanar da ita komai ba, da babu abin da zai saka ta saurareshi. "Sannu." Tace tana zama shima ya gyara zama yace. "Sannu Sadiya ina wuni." "Lafiya." Ta amsa a kan labbenta ƙasa ƙasa. Murmushi yayi yana mamakin har yanzu tana da zafin nan yace. "Babu maganar tone tone yafiya na zo nema." Kalaman da Yayanta ya faɗa mata ne suka faɗo mata akan ta yafe mishi dan haƙiƙa yaga buƙatar yafiya a idanun shi tare da nadama, hakan yasa tace. "Allah yafe mana gaba ɗaya." "Ameen nagode sosai. Ina Nuratu?" Da mamaki ta dubeshi tare da alamar tambaya, yayi murmushi da ya sakata ɗauke kanta dan sai ya koma mata Alhaji Mamman Bashir ɗinta na baya yace. "Nuratu dai?" Sai lokacin ta fahimta tace. "Sun fita da su Rahma amma nasan suna hanya." Miƙewa tsaye yayi ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kuɗaɗen ciki ya ajiye saman table ɗin da yake tsakiyar falon. "Sai sun dawo zan wuce. Ga wannan ki ƙara cikin hidimomi biki. Nasan duk abin da zan yi ba zai taɓa burgeku ba saboda na riga na shafawa kai na baƙin fenti a gurinki da gurin Nuratu ba. Haƙiƙa na so haɗuwa da Nuratu in nemi yafiyarta, amma babu komai zan taka har gidanta na je. Sai wani lokacin. Allah bata zaman lafiya." Da kyar Mami ta samu bakin furta. "Ameen! Amma da ka ɗauki kuɗaɗenka bama buƙata." Bai saurari mai take faɗa ba yasa kai ya fice. Cikin sanyi jiki Mami ta tashi ta ɗauki kuɗaɗen ta wuce ɗaki da su. Kirgawa tayi ta tsorata da yawansu bata taɓa tsammani Alhaji Mamman zai yi saurin gane hanyar gaskiya ba cikin kwana kusa, tasan yayi nisa amma tayi mamakin saurin ankara da yayi ya dawo hanya. Su Nuratu sai yamma lis bakin magriba suka dawo, tun a hanya Dr Awwab ya ƙirata bata samu ɗauka ba dan gudun su Rukayya su sata gaba da tsokana, ban da wanda suke mata yanzu. Tana dawowa ta ɗauki wayar ta shige bathroom ta ƙirashi. Yana zaune gaban Ikhram da Zaituna ƙannenshi da suka iso tun tsawon kwana biyu tare da lefen da ya tura musu kuɗi suka haɗa. Suna lissafin abubuwan da za'a ƙara ƙiran Nuratu ya shigo. Rabon da suyi wayar kirki har ya manta, baya samun zama ga aikin asibiti ga zirga zirgan biki bai samu kiranta ba sai ɗazu kuma ba ta ɗauka ba ya barta, yasan itama tana cikin rububin biki. A gabansu ya ɗauka yana kafawa a kunne yace. "Babyna." Ikhram da Zaituna har rige rigen juyawa su kayi kallonshi dan jin sunan da ya faɗa, ya watsa musu harara suka ɗauke kansu suna kunshe dariyar bakinsu. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  44. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Jin abin da ya faɗa ya saka Nuratu yin shuru har sai da yace. "Babyna me kike shirya mana?" "Ni babu abin da na shirya." Nuratu tace ƙasa ƙasa tsoron kar su Walida su jiyota. "Seriously fa maganar gaskiya?" Ta ji Dr Awwab yace ta ƙara maƙe murya. "Dagaske, su Walida da Aunti Rukayya dai sun dage za suyi dinner." "Zan zo nima kenan in gayyato friends ɗina." "Nima ban sani ba." "Shikenan zan ƙira Walida na ji mai suke shiryawa." To tace tana kashe wayar ta fita, bata tsaya ɗakin ba ta fita falo jin Walida ta fara mata tsiya dan duk sun ganota waya tayi a bathroom ɗin. Gidan hayaniya sosai har ranar asabar Mami ta haɗa walima ta ƙira Malama tayi wa'azi da duk ya kashewa mutane jiki. Nuratu lulluɓe cikin abaya haɗe da alkyabba sai sharan hawaye take domin tamkar fami aka mata a nata rayuwar. Har ƙarfe biyar kafin a watse aka tashi. Mami da su Aunti Rahma sun raba kyautattuka. Gidan su Dr Awwab reception ya haɗa tare da abokansa da ƴan uwansa samari daga Libya da Nijar da kuma ƴaƴan Baffa Abubakar. An ci ansha anyi taro lafiya domin Dr Awwab ya kashe kuɗi sosai babu harkar reni. Kayan jikinsa kaɗai ma abin kallone, banda hall da ya kama da kayan ciye ciye da kuɗi kawai ya zuba aka haɗa komai, ga masu ɗaukan hoto sama da mutum biyar. Da ka ganshi murmushi kawai yake zubawa cike da farin ciki. Bayan an kusa tashi ya sanar da su akwai dinner a Damaturu karfe takwas na dare, duk da mai buƙatar zuwa. Anan suka yanke shawarar tafiya su kwana in an gama gobe da safe su ɗauko amarya su juyo. Kowa yayi na'am da shawaran, bayan sun tashi ƙarfe biyar suka ɗauko hanya. Karfe shida suka iso, sallah suka gabatar kafin Dr Awwab ya kama musu hotel, duk da Aunti Rahma ta matsa su je gidan da aka basu su kwana ya nuna babu komai. Karfe bakwai motoci suka taru a kofar gidansu Nuratu dan tafiya wajen dinner da yayunta suka haɗa mata tare da taimakon Col. Ahmad da Yaya al'ameen da kwana biyu da zuwansu kenan suka taimaka musu suka shirya komai. Kowa ya fito ya shiga motar sai amarya da ake jira ta fito tare da Walida, cikin lace material ruwan gold da ya amshi baƙin fatarta da yake glowing. Tayi kwalliya dan mai kwalliya suka ɗauka ta tsara mata kwalliya da ya karɓi fuskarta babu wani tarukuce amma tayi mutuƙar yin kyau. Har cikin motar da Dr Awwab yake ciki da ya bawa abokinsa yake ja ya koma baya ta shigar Nuratu ciki, kanta sunkuye a ƙasa, zuciyarta sai bugawa yake dan ma ba su biyu bane. Babu wanda yayi magana cikin su har aka fara tafiya kafin ta ji maganar Dr Awwab yace. "Allahamdulillahi Masha Allah, just Masha Allah." Murmushin dole Nuratu tayi ta kasa magana har lokacin kanta a ƙasa tana watsa da hannunta da yasha jan lalle da baƙi yayi kyau. Shima bai ƙara magana ba sai idanuwansa da suke yawo a jikinta yana kallon halal ɗinshi da malak. A harabar hall din wasu suka tsaya, tasu kuma motarsu har ƙofar hall ɗin ya tsaya, kusan mintuna biyar an gama jera komai aka buƙaci su fito. Kowa ta ƙofa daban ya fito suka haɗu aka shiga gaban su da bayansu kafin a fara tafiya ciki. Babu kunya Dr Awwab ya saka hannu ya riƙo hannun matarshi da ya sakata jin wani shork ta kasa zare hannuwanta har suka isa wajen zamansu suka zauna sauran suka koma kafin a fara gudunar da bikin. Tsawon mintuna arba'in ana abu ɗaya aka ƙira ango da amarya suka fito yanka cake. Dr Awwab ne ya fara miƙewa ya riƙo hannun Nuratu ya mikar da ita suka isa gurin. Ita dai da ido take bin su domin jinta take tamkar ba ita ba. Mamaki take wai yau ranar dinar bikin aurenta, abin da ta riga ta cire rai da tsammani. Dr Awwab ne ya kama hannunta ya haɗa da wuƙar suka yanke cake ya ajiye ya gutsuri kaɗan ya bata da kyar ta karɓa akace ita ma ta bashi. Kallon Dr Awwab tayi, ya ɗaga mata gira ta girgiza kai yanda zai fahimta alamar ba zata iya ba, ganin haka ya haɗa rai. "Amarya ke ake jira." Fadin Dj dan yadda gurin ya ɗauki shuru dan son ganin yadda za'a kaya. Ko motsi taƙi yi balle ya saka ran zata bashi da mutane gurin. Aunti Hasiya kamar ta hau saman ta mammake Nuratu ta ake ji tsabar ta bata haushi. Ganin da gaske take Dr Awwab ya sashi matsawa kusa da ita ya saka hannunshi ya riƙota tare da kama hannunta ya haɗa da nashi ya guntsiri cake din ya kai bakinshi guntun ya tura mata a baki ƙasa ƙasa yace. "Cinye Babyna." Dolenta ta haɗiye ganin haka aka saka ihu tare da tafa musu Dj yayi gyaran murya yace. "Wannan amaryar ƴar shagwaɓa ce wato sai dai su ci tare." Nan ma ihun aka saka Dr Awwab yaja Nuratu suka koma suka zauna har lokacin yana riƙe da hannunta ta kasa kwacewa. Kwata kwata ya hanata yin rawa duk ƙiransu da ake su fito, haka shima. Ɓangaren Nuratu da ma bata iya ba balle tace za tayi, hanata tashi da yayi ya mata daɗi. Yaya Al-ameen da yake zaune kusa da Nazifa da ta saka musu ido babu ko kiftawa, yayi dariya da ta ji sautin shi bata juya ta kalleshi ba yace. "Sun miki kyau ne ƴar ƙauye." "Sosai baka ganin yadda yake lallaɓa ta kamar ƙaramar yarinya." "Kema in kina so za'a miki har yafi wannan in dai kin amince." "Dagaske Allah?" Ta tambaya tana juyowa da sauri tana kallonshi yana murmushi yace. "Yes in dai kin amince za ki zama matar Al'ameen shi kuma ya amince zai miki har abinda yafi wannan." Kallonshi take ta kasa fahimtar zancenshi, kusan mintuna biyu kafin ta miƙe da sauri ta bar gurin dan fahimtar mai yace har tana kusan cin tuntuɓe, yana dariya ya ga ta shige cikin su Walida ta ɓuya. Tin jiya da suka haɗu zata raka Walida gidanta ɗauko wasu kayanta ya ganeta sarai ƴar Kawun Nuratu ne dan ya ganta a Nijar. Shi ya taimaka musu ya kai su gidan Walida da motar shi bayan isar su a wajen fita Nazifa tayi ƙauyencin buɗe motar ba wai dan bata iya ba sai dan ta rikice, daga nan ya fara ƙiranta ƴar ƙauye babu musu ta amsa dan ta san tayi ƙauyencin. Yaji a ranshi in har za'a bashi aurenta kuma iyayenshi za su yarda zai aureta domin ya yarda da hankalinta da nutsuwarta. Zuwan Col. Ahmad wajenshi ya sashi kawar da tunanin suka gaisa kafin su maida hankali kan abin da ake gabatarwa. Karfe tara aka tashi kowa ya fito ya fara shiga mota, Dr Awwab da Nuratu kamar zuwansu haka suka shiga su biyu a bayan sai mai ja. Suna ciki kafin motoci su fara tafiya Dr Awwab ya juya yana kallonta, ƙamshin turarenta da nashi ya haɗe ya bada wani ƙamshi mai fisgar tunanin mutum. Ƙwanƙwasa gilashin motar a kayi ta daidai inda Nuratu take, abokin Dr Awwab ya buɗe wanda ya ƙwanƙwasa ya leƙo kanshi. A mugun tsorace Nuratu taja baya tare da faɗawa jikin Dr Awwab ta riƙo shi, shima Dr Awwab ɗin ganin haka ya sashi riƙota jikinshi sosai yana bin wanda ya leƙo da kallon mamaki. "Congratulations Nuratu and Dr, Allah baku zaman lafiya. Na so mu zauna ko in zo har gida in nemi yafiyarki, sai dai na samu labari gobe za ku wuce. Ina neman afuwarki da yafiyarki ga duk abinda na miki. Dan Allah kiyi hakuri ki yafe mini. Wallahi ni Mufid na gane gaskiya na tuba zuwa ga Allah. Allah baku zaman lafiya, Dr a riƙe mana ita amana." Daga haka Mufid ya ajiye enbulof ɗin hannunshi ya bar gurin, Dr Awwab da Nuratu da suka bi shi da kallon mamaki sun kasa kwakkwaran motsi dukkansu biyu. Har lokacin tana jikinshi bata san da hakan ba sai da ta ga ya saka hannu ya ɗauki enbulof ɗin ya jefa aljihunsa kafin ta fara ƙoƙarin kwace jikinta ya hanata ya riƙeta. "Ke ki ka kawo kan ki jikin mijinki fa." Yace yana ƙara ƙarfi wajen riƙeta sosai, tana mutsu mutsun kwace jikinta tace. "Dan Allah ka bari Dr, baka ganin akwai mutane." Bai mata magana ba ya sassauta riƙon amma har lokacin hannunshi a jikinta ya riƙo kugunta yana cewa. "Soon zan riƙe ki son rai na." Bata mishi magana ba ta turo baki tana juyar kanta. Daga haka aka fara tafiya har ƙofar gidansu Nuratu, aka fara sauƙa, tana ƙoƙarin fita taji Dr Awwab yace. "Ki shirya gobe da wuri zamu zo." Fit ta fice bata gama sauraranshi ba, ya bita da kallo har ta shige kafin ya fita ya koma gaba suka bar harabar gidan. ... Washegarin da safe aka fara shirin kai amarya, inda amarya Nuratu tana can ɗakin Mami tun safe ta rufe kanta da bargo tana ta kuka sosai kamar wanda aka mata dole. Anyi lallashin anyi taƙi shuru sai ma ƙara kuka da take, Aunti Hasiya faɗa ta dinga mata kamar za takai mata bugu. Mami da taga kukan ƴartan yayi yawa ya sata koran duk wanda suke ɗakin ya rage su biyun ta zauna kusa da ita. "Wai menene Autana? Auren ne bakya so ko kuma Dr ne bakya so. Ko dai har yanzu ba ki cire wannan abun a ranki." Ita dai Nuratu shuru tayi tana share hawayenta, wani mugun tausayin kanta take ji da irin sabuwar rayuwa da za ta tsinci kanta. Hannunta Mami ta kama ta ɗagota zaune. "Ki cire komai a ranki ki rumgumi ƙaddararki kinji, ki riƙe mijinki, tun da shi ya nuna yana sonki a haka to kuma menene za ki damu kan ki? Uwar mijinki tana sonki da kowa nashi to menene abun damuwa. Kiyi hakuri kinji inshaAllah zaki ji daɗi zama da Dr Awwab." Nasiha Mami tayi ta mata har Nuratu tayi shuru ta kwantar kanta saman cinyar Mami. "Ni Mami bana son yin nisa dake." "Hakuri za kiyi aure ya gadi haka, wasu fa wani ƙasa ake ɗaukarsu akai balle ke nan zuwa Maiduguri da ko ihu kinyi zanji. Tashi kiyi wanka ke kaɗai ake jira." Da kyar ta miƙe Mami ta fita ta turo mata mai gyaran jiki ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka da turare da sabulu mai ƙamshi tayi ta fito ta lulluɓeta da bargo ta saka wuta da turaren wuta ciki na tsugunno da na jiki ta ɗumamata sosai, har wutan ya mutu kafin ta bata kaya atamfa da zani ta saka ta lullubeta da luffaya suka fita. Ƙamshi kawai take fitarwa tayi kyau. Motoci dayawa sun zo ɗaukar amarya duk an shiga ciki, motar da amarya za ta shiga har cikin gidan Mami ya shigo aka shigar da Nuratu da kyar dan yadda ta ƙamƙame Mami sai kuka take. Motar daga ita sai Rukayya dake gaba, baya da Walida da Aunti Zarah sun sata tsakiya, suka ɗauki hanya ta kwantar kanta saman cinyar Aunti Zarah taci gaba da kukanta. Ƙarfe sha biyu aka suka shiga cikin Maiduguri, kai tsaye gidanta aka fara wucewa da ita in da mutane suka saki baki ganin kyan gidan da kuɗi da aka kashe masa. Kayan ɗaki da su Aunti Rahma suka zo jerawa a ɗakin ƙasa suka saka domin Dr Awwab ya gama komai na ɗakin sama da falon. Kayan falon ƙasa ma abubuwa kaɗan suka ƙara mata sauran suka saka a wani ɗaki, sai kitchen da shine kaɗai bai saka komai ba amma ya mata komai na zamani. Banda kayan akwati jeri 4 da ya haɗa na lefe. Har cikin ɗakinta da yake sama aka sakata aka zaunarta saman gadon kafin su fita kallon cikin gidan, sosai gidan yayi kyau dan Dr Awwab yayi ƙoƙari ya zuba kuɗi an masa gyara. "Gidan ki yayi kyau Sister, Docter yayi ƙoƙari sosai." Walida tace tana cire kayan da Nuratu za ta saka dan zuwa buɗan kai gidan su Dr Awwab da suke shirye-shirye buɗar kan amarya. Nuratu da ta zama wata shuru shurun ƙarfi da yaji ta karɓi kayan ta wuce bathroom ta watsa ruwa ta canza kayan ta fito, mai kwalliyar da suka zo da ita ta mata suka lullubeta da luffaya sai ƙamshi yake. Bayan kowa ya gama shiryawa abokan Dr Awwab suka zo suka ɗauke su suka wuce gidan Ummi dan buɗan kai. Gidan Ummi cike yake da ƴan uwa da dangi da abokan arziki ana ta shirye shirye dan buɗan kai. A falon gidan har ciki aka ajiye Nuratu saman darduma da aka shimfiɗa, kanta a sunkuye a ƙasa ta kasa ɗagowa, mayafin jikinta taja ta ƙara rufe fuskarta dashi. Hussaina ce ta zo ta buɗe mata fuskarta bayan ta raɗa mata suna. "Haske." Kamar yadda ma'anar sunanta yake haka suka bi. Daga nan ango Dr Awwab ya iso ya zauna kusa da Nuratu aka fara basu kyautan kuɗi, zubasu ake saman cinyar Nuratu, wani Dr Awwab wasu dukkansu biyu suke bawa. Aunti Rahma a gefenta ganin sun fara mata yawa ta fara kwasa tana sawa a jakan gefenta. "Suna kama da marigayiya Sumayya." Ummi taji Ammi ta faɗa mata ga Baffa Abubakar tana duban Aunti Rahma da tun shigowar su ta bisu da kallo gaba ɗaya ƴaƴan Mamin, musammam Aunti Rahma da take kama da marigayiyar ƴarta da ta rasu wajen haihuwa shekara biyu da ya wuce. Ummi ma kallon Aunti Rahma take tana ƙara hasko kamanninta da mutane biyun sai ta ga har tafi kama da shi akan Mami, ga kuma Ammin Sumayya da ta ƙara sakawa zuciyarta ruɗani da kalamanta, dan tabbas tana kuma kama da ƴarta Sumayya fiye da shi. 'Akwai wani abun tsakanin su tabbas.' Tace a zuciyarta a fili kuma tace. "Sosai ma nima na ga hakan." .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 45. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Biki aka gudanar me tsafta kamar yadda al'ada ya koyar, bayan an gama bada kyauta aka buɗe fuskar amarya aka fara ɗaukar hoto. Ita dai Nuratu ta zama mutum mutum dan duk yadda aka juyata bi take. Anyi hotuna sosai aka fara ƙoƙarin cin abinci, aka saka ƴan uwan amarya a falon Ummi bakin Ummi suka sauƙo falon ƙasa. Nuratu kasa cin komai tayi, ko ruwa ta kasa sha, kanta ta mayar cikin luffaya dan masu shiga da fita. "Ga amaryar." Taji ance daga saman kanta, ta cikin luffayan ta ɗago ido ta kalli mai faɗar haka. Matashiyar budurwa da za takai sa'arta tana tsaye kanta tana nunawa wata Nuratu da yatsa. Kanta ta mayar ta sunkuya duk tsammaninta ƴar uwar Dr Awwab ce,  ta ji fitar su. "Gashi Dr Awwab yana ƙiranki." Walida ta miƙa mata wayarta da yake hannunta tun fara hidimar. Karɓa tayi ta ɗauka ta kafa a kunne tana masa sallama ƙasa ƙasa. "Babyna ya taro? Fatan kinci wani abun?" "Ni na ƙoshi." "Au hakane, shikenan babu matsala anjima zan ciyar da ke da kai na. Dama ki sanar da su Aunties ne za a mayarsu zuwa la'asar, dan babu mai kwana." Cikin sauri Nuratu da bata san yaushe ta ciro kanta cikin mayafi ba ta jero masa tambaya. "Kamar ya? Akan me? Wallahi zancen ka ke, kasan dai ba zai yiwu ba, kuma ba za a fara a kai na ba." Murmushi yayi har taji sautinshi. "Haka al'adar garinmu yake, ba a kwana in an kawo amarya." Kuka ta saka mishi ganin haka Aunti Hasiya ta karɓi wayar tana tambayarshi. "Menene ya faru Docter ka saka amaryar ka kuka?" Cike da kunya yana murmushin kukan da Nuratu ta saka mishi yace. "Babu komai Aunti, ce mata nayi kawai zuwa la'asar za'a mai da masu tafiya." "Shikenan shine za ta tsayawa mutane kuka. Ka sanar da masu zuwan su same mu gidan amarya yanzu zamu wuce." To yace yana kashe wayar. 'Akwai drama.' Yace a ranshi yana dariya, dan ya san dai mutane ba za su bar kowa ya kwana ba kamar yadda al'adarsu yake. ... Ƙarfe uku da rabi aka mayar da su gidan amarya bayan godiya da suka ma Ummi da mutanen ta na karamci da suka musu da kyautatawa. Bayan sun isa motocin suka iso aka fara ɗaukar mutane, inda aka ce Aunti Zarah da Rahma za su kwana zuwa gobe, nan abokan ango suka ce sam ba'a haka anan. Ko su tafi ko kuma su ɗauke amarya su kai wa ango. "Amma dai ko ina ana kwana a gidan amarya in an kawota." Aboki da ya kasance makusancin Dr Awwab ya kalli Rukayya da ta faɗi haka yace. "A wani wajen ba, amma mu nan ba a haka. Ku fito kawai mu tafi kar dare ya mana, muna son dawowa a yau." "Ikon Allah." Aunti Rahma tace ta ƙara da cewa. "To ku bamu minti goma dan Allah." "Shikenan kuyi sauri." Suka ce dan alƙawari suka ɗauka yadda ba'a kwana a gidan amarya a al'adarsu, haka za suyi in sun dage su kwana su ɗauke amarya su kaita wajen ango kamar yadda shima ya buƙaci haka. Aunti Rahma da Hasiya, Zarah, Rukayya da Walida, Nazifa da sauran mutane suka haɗu suka gyara gidan cikin sauri suka saka turaren wuta, suka saka Nuratu tayi wani wankan ta saka lace suka feshe jikinta da turare suka zaunarta. Aunti Hasiya ta ajiye mata wayarta kusa da ita tana cewa. "Kuma ki fito waje ni da ke." Baki Nuratu ta tura tana gunguni faɗan Aunti Hasiya yana damunta, shekaru huɗu ta bata amma kamar itace gaba da Aunti Rahma. Waje suka fita dukkansu ɗaya bayan ɗaya dan kar Nuratu ta lura da hakan, kafin su shiga mota aka tafi da su suna ma ƙanwarsu fatan zaman lafiya. Shuru taji gidan ya ɗauka bayan dirin motocin sun ɗauke, zuciyarta ya bada wani irin sauti ta miƙe tsaye ta isa bakin window ta ɗaga labulen ta ga filin gidan babu kowa, da sauri ta sake tana nufan ƙofar waje. Babu kowa a falon sama ta sauƙa ƙasa nan ma shuru gidan sai ƙarar Ac da Tv. 'Shike nan sun tafi sun barni." Tace wani hawaye yana zubo mata ta share, da sauri ta koma ɗakinta ta ɗauki wayarta sanan gado ta shiga ƙiran Aunti Rahma ta san ita kaɗai zata saurareta. Bata ɗauka ba ya saka Nuratu fashewa da kuma ta faɗa saman gado taci gaba da kukanta. Tun bata so har wani bacci ya fisgeta dan ta jima ba tayi baccin kirki ba. Ƙarfe takwas na dare Dr Awwab ya shigo cikin gidan, shuru babu kowa sai Tv da Ac da ya wuce sama kai tsaye ɗakin Nuratu ya nufa ya tura. Saman gado ya hangota tana bacci tayi ɗaɗɗaya bata ma san in da kanta yake ba, luffayan jikinta ta cire ta ajiye gefe daga ita sai riga da skirt na lace din jikinta da ɗankwalin kanta bai fita ba. Zama yayi ya zuba mata ido yana bi da kallo. Bai taɓa tsammani zai samu Nuratu cikin sauƙi cikin kwana kusa ba. Allah kenan da ya saka ya zamto shine mijinta cikinsu. Allah ne ya ɗaura masa sonta tun ranar da ya ganta har zuwa yanzu kuma yake fatan har ƙarshen rayuwarsu da aljanna. Hannunshi ya ɗaura saman nata yana ɗan bubbugawa ganin ta fara motsi yace. "Tashi kiyi sallah Babyna. Na san ba kiyi ba." Jin muryar Dr Awwab ya saka Nuratu tashi da sauri tana gyara zamanta ta ja baya kaɗan ganin sun yi kusanci, tana watsa mishi harara, haushinsa take ji da ya hana kowa kwana, tasan aikinsa ne. "Kiyi sallah ki sauƙo ina jiranki a falonki." Ba ta kula shi ba ta miƙe ta sauka ta ɗayan gefen ta wuce bathroom ya bi bayanta da kallo kafin ya miƙe ya fita a ɗakin. Alwala tayi ta fito ta buɗe wardrobe ɗinta ta ga gurin komai daban-daban in da aka jera mata, hijab ta ɗauka ta gabatar da sallar magriba da isha'i, ta ga agogon bango ta ga an jima da yi, bayan ta idar ta zauna tana addu'o'inta ta kasa fita. Dr Awwab fitar shi ɗakinsa ya wuce shima yayi wanka ya saka jallabiya ya fito ya sauƙa ƙasa ya ɗauko ledan da ya shigo da shi ya wuce falon Nuratu ya zauna zaman jiranta. Kusan mintuna talatin babu ita babu labarin ta ya kalli agoga ya ga ƙarfe tara da mintuna. Miƙewa yayi ya nufi ɗakinta ya buɗe ya shiga, tana zaune har lokacin saman darduma. "Babyna ke nake jira fa kin sani." "Ina zuwa ai." Tace sai lokacin ta miƙe ta linƙe darduman ta ajiye ganin haka ya fita ta bi bayan shi cikin hijabin ta sameshi a falon. Saman kujera ta zauna yana ganin haka ya ɗauki ledar da ya shigo da shi ya juye kazar ciki ya ajiye a ƙasa kusa da Nuratu ya sauƙa ƙasa. "Sauƙo kici na san ba abinda ki kaci na kirki." "Na ƙoshi." Tace tana ɗauke kanta saman plate ɗin kazar da kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta taji kazar ya fita a ranta da yunwar gaba ɗaya. "Kina so in dura miki kenan." Dr Awwab yace yana murmushi dan ya fahimceta tsaf. "Ni na ƙoshi Allah." Dr Awwab bai saurareta ba ya miƙe ya hau saman kujeran da Nuratu take, tana ganin haka ta fara ƙoƙarin tashi ya fizgota jikinshi, a mugun tsorace ta fara ƙoƙarin raba jikinsu. "Ka barni dan Allah me haka?" "Abinci zan baki. I told you ai daman ai." "Wallahi na ƙoshi dan Allah ka barni." Tace gab take da fashe masa da kuka. Bai kulata ba ya saka ɗayan hannunshi ya ɗauko plate ɗin ya ɗaura saman center table, ya ɗauki yanka ɗaya ya riƙo fuskar Nuratu ya tura mata a baki. "Cinye in ƙara miki." "To ka sake ni." Tace bakinta cike da naman da ya saka mata, ganin haka ya sassauta riƙon da ya mata ta fara taunawa a hankali. Yana ganin ta haɗiye ya ƙara ɗauko ɗaya ya tura mata a baki ta fara ci. Yunwar da take ji shi ya sata cin yanka kusan goma Dr Awwab yana bata yana kallon ƙaramin bakinta da yadda take tauna abincin kyau yake masa. Take yaji ranshi ya biya. "Na ƙoshi ya ishe ni." Nuratu tace tana janye kanta ganin Dr Awwab zai ƙara bata wani. "Saura milk." Yace ya ajiye ya ɗauki cup ya tsiyaya mata ya miƙa. "Sha ko shima sai na baki." Karɓa tayi tasha kusan rabi ta miƙa masa sauran kafin ya matsa baya ya fara ciyar kanshi. Ganin haka ya saka Nuratu tashi ta bar gurin. Ɗakinta ta wuce ta watsa ruwa ta buɗe wardrobe ɗinta wajen kayan baccinta ta duba ta ɗauki riga mai kauri ta saka ta kashe wutan ɗakin ta kwanta. Dr Awwab sai da yaci ya ƙoshi kafin ya kwashe komai ya kai kitchen ya kashe wutan falon ƙasa da Tv ya kashe na falon Nuratu kafin ya wuce ɗakinshi ya kwanta. Bai yi gigin zuwan mata ba dan kar ta tsorata ko tunanin wani abin daban. ... "Aunti A'isha kin ganta dai kinga danginta. Babu abin da zata nuna mini sai ma in nuna mata hasken fata da arziki." "Hakane Binta. Ni nayi mamaki ma, Dr Awwab ban san ina yake kallo ba ya kwaso wannan baƙar yarinyar, an daina yayin baƙaƙe fa, ko da baƙinka sai ka ƙara da mai ka yi haske, samarin yanzu shi suke ganin kyan ka." Aunti A'isha tace ga ƙanwarta Binta Yaya ga Nusaiba. Tun dawowar su daga buɗan kai suke mai da zancen akan Nuratu da Dr Awwab dan sun so bayan rasuwar Nusaiba ya auri Binta ko dan Hanan amma sam hakan ya kasa yiwa wa. Har Ummi mahaifiyar Nusaiba ta samu da zancen tace ba za ta mishi dole ba amma in ya yarda shikenan. Ummi da ta samu Dr Awwab da maganar ya nuna sam lokacin bashi da ra'ayin aure, kuma ko zai yi banda Binta. Da suka samu labarin auren Dr Awwab sunyi mamaki kuma har lokacin basu cire rai ga cikar burinsu ba. Dalilin zuwan buɗar kan da Binta da Aunti A'isha su kayi kenan, dan ganin amarya da kuma nunawa Dr Awwab har yanzu suna da alaƙa da shi tun da jinin Hanan ya haɗasu. "Ku bi komai a hankali dai, sannu sannu baya hana zuwa." Mahaifiyarsu tace da sai lokacin ta saka baki. "Za muyi komai cikin nutsuwa babu zargi Mama." Aunti A'isha tace suka ci gaba da hiran da Binta. *** Ƴan biki sun koma gida lafiya kowa maganarshi gidan Nuratu ya masa kyau. Sun kwana Washegarin suka haɗu suka tattarewa Mami gidanta suka gyara tsaf kafin kowa ya kama tafiya. Sai da kowa ya watse Mami ta fara kewar Nuratu gidan ya zama ita ɗaya sai wanda ɗaiɗaiku basu gama tafiya ba. ... Kwance yake cikin ɗakinsa ya zubawa silin idanu, burinshi da addu'arshi Allah yasa Nuratu ta buɗe enbulof ɗin da ya bata, ta karanta me yake ciki tayi hakuri ta bawa zuciyarta hakuri ta yafe masa cuta da ya mata a rayuwa. Baya fita ko ina daga gida sai gida yana ɗakinshi a kwance rai da rai, ko falon Ummu baya zama sai ya zama dole, abinci ma in ya ɗeba ya shiga ɗakinshi yaci ya kai plate din kitchen ya ajiye. Ya je duk gidan Yayunshi da ƙannenshi sun sada zumunci, musamman Rufaida da yafi jimawa a can suna hira kamar ba ita ba, yayi ta roƙanta gafara. Sau ɗaya yaje duba AA da yaga halin da ya shiga shi ya mugun tayar masa da hankali, wani tsoron Allah da duniya ya shigesa, ya san shima da yanzu shine kwance a mummunar halin da yake ciki. Ko da yake shima menene bai yi ba tun da yayi hauka tukuru da kashi da fitsari sai an wanke masa. Bashi da buri yanzu ya wuce ya gyara karatunshi ya samu aikin yi ya tsaya da kafafunsa yayi nisa sa iyayenshi da yake jin duk su suka nuna masa hanyar rayuwarsa ta ɓaci. *** Ƙaran wayarshi shi ya farkar da shi daga nannauniyar baccin da ya ɗaukeshi bayan dawowarsa daga sallar asuba, wayar ya jawo ya ɗauka yana sakawa a kunne. "Yaya Awwab ka buɗe mana kofa." Yaji muryar Hassana, tsaki yayi ciki ciki yace. "Ina zuwa." To tace ta kashe wayar ya miƙe da kyar ya fita yana zubawa ƙofar ɗakin Nuratu ido. Ƙofar falon ya buɗe musu ya samu Hassana ce da kayan breakfast da Ummi ta aikota da shi, a saman dinning ta ajiye ta mishi sallama ta koma. Sama ya nufa ɗakinshi ya shiga ya wuce bathroom dan yin wanka domin baccin duk ya wartsake, wanka yayi ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya ya feshe jikinsa da turare ya nufi ɗakin Nuratu. Har lokacin ba ta farka ba, ya isa bakin gadon ya zauna daf da ita kafin a hankali ya rankwafo saman fuskarta har numfashinsu ya gauraye yana shaƙar numfashinta da ke fita a hankali. ... InshaAllah daga yau sai kuma wani lokaci, zan fara jarabawa kwana kusa ku sani a addu'a. Masu jiran Farha zan ƙoƙarta na turo ko page ɗaya, sai kuma bayan exam. Allah bamu sa'a gaba ɗayan mu da wanda su ka yi da wanda za mu yi. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE (Haske) 46. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Fuskarsa ya haɗa da nata ya sumbaci leɓɓenta, ƙasa ƙasa ya fara ƙiran sunanta. "Babyna! Baby!!" Cikin baccinta mai daɗi taji ƙiran daf da ita, buɗe idanuwanta ta yi cike da bacci, fes cikin nasa idon da ya saka cikin nata. A zabure ta miƙe garin sauri ta haɗa goshinsu ya bugu. "Awwch." Su ka faɗa a tare, kowanne ya dafe goshin sa, Dr Awwab ya yi ta maza ya sa ke goshinsa, yana ƙoƙarin ɗaura hannunsa saman goshin Nuratu ta ja baya ta sauƙa a gadon gaba ɗaya, hakan ya sa ya basar. "Ki yi wanka ki zo mu ci abinci, Ummi ta aiko." Jin abin da ya faɗa ya sa ta shigewa bathroom ya bita da kallo. Kusan minti ashirin ta gama wankan, ta leƙo kanta, tsammaninta duk Dr Awwab ya fita. Jin ƙarar buɗe ƙofar ya sa shi kai kallonsa gurin su ka haɗa ido, da airpods a kunnensa da alamar waya ya ke amsawa. Da sauri Nuratu ta koma ta rufe ƙofar, hakan ya sa shi ya taso zuwa bakin ƙofar ya tsaya, bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron bayanin da ake masa ta wayar. Jin shuru ya sa ta buɗe kofar a hankali tare da leƙo kanta, ganinsa tsaye a gurin daf da ita a mugun tsorace za ta koma ya fizgota ya fito da ita ya haɗata da ginin gurin. "Wai tsorona ki ke ji?" Yace bayan ya cire airpods a kunnensa yana mayarwa. Za tayi magana ya ɗaura yatsarsa saman leɓɓenta alamar tayi shiru. Dolenta ta haɗiye maganarta. Yana sauraran bayanin wayar yana amsawa da eh ko a'a, idanuwansa akan Nuratu yana bi da kallo, kanta ƙasa zuciyarta yana bugawa, domin haƙiƙa ta ji idanuwan Dr Awwab suna yawo a jikinta gaba ɗaya, towel ne jikinta ko gwiwa bai kai ba. Sun kusa mintuna shida a haka kafin ya gama wayar ya kashe ya ƙara kusanta kanshi gareta, tsorone ya ziyarci zuciyar Nuratu jin yadda ya matso daf da ita, numfashinsa yana bugun fuskarta, ta ƙara mannewa da gini, jikinta ya hau rawa, sai lokacin ta samu bakin yin magana murya yana rawa. "Don Allah ka matsa kin in wuce, kaya zan sa ka." Yatsun hannunshi ya sa ka a fuskarta ya ɗago kanta suka hada ido da idanuwanta da suka cika da ruwan hawaye, tayi saurin juyar kanta gefe. Murmushi Dr Awwab yayi yana bin fuskarta da kallo. "Hausawa su ka ce duk wayon amarya sai ansha zumarta, gashi ni tawa amaryar kwananta ɗaya har yanzu ban sha ba." Jin abin da ya faɗa shi ya ƙara tsorata Nuratu ta fara ƙoƙarin kwace fuskarta ta wuce ta gefenshi ya sa ka hannunshi ya riƙeta sosai yana haɗa fuskar su waje ɗaya, numfashinsa yana sauka bisa na ta tana shaƙa. "Daga yau zuwa gobe ki bar angonki ya ɗanɗani zumar ki Babyna please.' Dr Awwab yace cikin wani irin yanayi da ya jima bai ji shi ciki ba. Nuratu ta kasa motsi kwakkwara dan yadda ya mata riƙo ba wasa ba Hawayen idonta ne ya zubo bisa kumatunta lokacin da ta ji ya ɗaura leɓɓensa saman nata. A hankali cikin nutsuwa ya fara tsotsan bakinta da ya jima yana burin tsotsa. Ta kasa hana shi ta kasa kwacewa, tana jin shi har tsawon mintuna kafin ya sa ki bakinta ya sassauta riƙon da ya mata. "Ki shirya ki fito ina jiran ki." Haka kawai yace ya saketa gaba ɗaya ya fita a ɗakin, idan ya ci gaba a wannan safiyar za a yi wani abun. Nuratu ka sa tsayuwa tayi ta zauna bakin gado dan shi tafi kusa da shi ta fara share hawayenta, kusan mintuna biyar ta miƙe ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗauki riga da skirt na atamfa mai ratsin ja da ruwan goro ta saka. Ba ta yi kwalliya sai hoda da ta shafa ta saka kwalli da jan baki ja kaɗan ta saka turare kafin ta fita. Ba ya falonta hakan ya sa ta fita ta fara sauƙa, mamakin girman gidan da kyawunshi da uban kuɗin da Dr Awwab ya kashe ta ke. A saman dinning ta hangosa, har bakin dinning table ɗin ta ƙarasa ta zauna ta ka sa haɗa ido da shi balle ganin in da yake. Kasa taɓa komai tayi bayan zamanta, ganin haka ya sa ka Dr Awwab yin murmushi ya jawo warmers ya zuba a plate ya ajiye mata gabanta ya saka fork, ya ɗauki cup ya haɗa tea ya hau sha yace. "You can start." A hankali ta ɗauki fork din ta fara cin abincin da ya zuba mata ya ajiye, Dr Awwab bai yi gigin saka hannu ba dan kar ya takura mata ya zuba mata ido yana kurɓan tea kaɗan kaɗan, movement din da ya shuɗe yanzu yake masa yawo a kai, bai ƙi ya kara ba yake ji. Sai da taci sosai kafin ta tura alamar ta ƙoshi, ganin haka Dr Awwab ya ja plate ɗin gabanshi ya ajiye mata cup ɗin hannunsa. "Ki sha na ƙoshi ni ma." Sai lokacin ta kalleshi, ya kafeta da lumshashshun idanuwansa, da sauri ta kawar kanta ta ɗauki cup din ta sha kaɗan ta ajiye, tana kallo ya hau cin wanda ta rage. Tana ajiyewa ta miƙe. "Ina za ki je?" Ya tambayeta yana bin ɗinkin jikinta da kallo, kayan sun zauna a jikinta sosai. "Zan gyara ɗaki." Tace tana wucewa sama ya bita da kallo har ta ɓacewa ganinshi. Nuratu ɗakinta ta gyara duk da bai yi wani datti ba ta fito ta sauƙa ta wuce kitchen ta ɗauko tsintsiya da parker da mopper ta koma ɗakinta, Dr Awwab yana gamawa ya wuce ɗakinsa, hakan shi ya bata daman zirga-zirga. Da ta gama ta sauƙo falon ta tattare dinning din ta kai kitchen ta share falon da shima ba datti, ta gyara ta wuce kitchen ta wanke kayan da su ka ɓata, bayan ta gama ta tsaya kallon kitchen ɗin da yayi mata kyau sosai. Mami da yayunta sunyi ƙoƙari, sun mata kayan zamani da gara da laifi. Falonta koma tana mamakin shurun da ta ji. Ko Dr Awwab ya fita bai sanar mata ba? Ta tambayi kanta. Ɗakinta ta shiga ta ɗauki wayarta ta fito falon ta zauna tana ƙiran Maminta. "Mamina ina kwana." Nuratu tace bayan Mami ta amsa sallamarta. Daga ɓangaren Mami tace. "Lafiya lau Nuratu, ya gajiyar biki." "Allahamdulillahi Mami." "Ina su Aunti Rahma? sun tafi?" "Eh ba su gama tafiya ba sai anjima ko gobe." "Ai wallahi Mami fushi na ke musu, za su tafi su barni ni ɗaya." Nuratu tace tana bata rai kamar tana gabanta. Murmushi Mami tayi tace. "To sai hakuri. Ki ci gaba da hakuri da biyayya Allah baku zaman lafiya." Ameen Nuratu ta amsa ƙasa ƙasa, nasiha Mami ta ci gaba da mata kafin suyi sallama. Kwanciya ta yi sama doguwar kujeran da take ta faɗawa tunani. Wai yau ita ce matar aure. Abin da bata taɓa tsammani ba. Ba ta ji shigowarsa ba sai tafiyan tsutsa da ta ji ana ma kafarta, a tsorace ta janye kafar tana miƙewa zaune ta ga Dr Awwab ne. "Tunanin me ki ke haka. Ni? Gani nan." Dr Awwab yace yana zama gefen gadon kusa da Nuratu da ta sunkuyar kanta ƙasa. "Me ki ke tunani Babyna?" Ya faɗa yana kamo yatsun hannunta ya murza. "Babu komai, kawai gida na ke tunawa." Tace tana turo baki, tare da ƙoƙarin janye yatsunta. Bakin yabi da kallo yana murmushi yace. "Tun yau Babyna, yanzu fa aka soma." "Ni dai nayi kewar su. Ka ɗauko min Hanan don Allah." "Hanan dai?" Yace yana sakin dariya ya kwantar kanshi saman gadon bayan ya ba ta dama ta zare yatsunta cikin na sa, duk ya lura da ita amma ya basar. Ganin ya kwanta ta juya tana fuskantar shi. "Eh mana, ka ga za ta ɗauke mini kewa." "Hakane, amma ba yanzu ba, sai mun gama amarci." Shuru ta masa taƙi masa magana, ganin haka ya ɗago kansa yana kallonta. "Hanan za ta dawo amma ba yanzu ba. Na je gida Ummi tana gaishe ki." Ƙasa ƙasa tace. "Ina amsawa." Kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa ya tashi zaune yana riƙo hannunta ya maida ita ta zauna. "Waya ce miki amarya tana aiki. Please ki huta." Kai ta gada tana jan baya kaɗan, ta ɗauki wayarta ta kunna Data, sakwanni su ka yi ta shigowa na ƙawayenta da basu samu zuwa ba, tana ta mamakin ina su ka ji dan ba tayi gayya ba sai wanda suka samu labari su ka zo. Ganin shurun ya yi yawa ya sa shi dubanta, hankalinta akan wayarta, murmushi ta ke dimples na ta yana lotsawa dukka biyu. Zaune ya miƙe ya kai yatsansa cikin ramin gurin ya tura. "I love your dimples Baby." Tin lokacin da ta ji sauƙar yatsarsa saman fuskarta ta fara ƙoƙarin kawarwa gefe ya riƙe sosai yana gyara zamansa. "Ki na mini rowar kan ki wallahi. Ni kuma babu sassaucin da zan miki. Yes Baby, ko in fara gwada miki." Ya ƙara faɗa ganin har lokacin tana ƙoƙarin kwace jikinta. Ba ta yarda da batunsa ba sai da ta ji hannunsa cikin rigarta saman shafeffiyar tumbinta. A mugun tsorace ta riƙe hannunsa. "Ka bari mana don Allah." Bai kulata ba dan ya lura tana son nuna masa ƙauyenci a wannan harkar. Shi kuwa hakan baya tsarinsa, a ci soyayya a nuna juna so tamkar babu gobe. Ƙara shiga cikin jikinta ya yi sosai ya tura fuskarsa tsakanin wuyanta yana shaƙar fititinannen ƙamshin jikinta da ke tashi, yayin da hannunsa ke shafa saman tumbinta, tsantsi da laushin fatar jikinta na jefasa cikin wani yanayi. "Zan ma ka kuka." Nurata tace ganin ya kasa dai na abin da ya ke mata. Jin abin da ta faɗa ya sa ka Dr Awwab ɗago fuskarsa ya zuba mata idanunsa da su ka fara canza launi, su ka ƙanƙance cike da fitina. Runtse idanunta ta yi, hakan ya basa damar haɗa bakinsu ya fara tsotsan bakinta. Shuɗaɗɗiyar lokacin da ya wuce ya dinga dawowa ƙwaƙwalwar Nuratu, tuna hakan ya sa ta kwace bakinta ta fashe masa da kuka. Rumgumeta ya yi yana shafa bayanta, bai zai iya mata abin da ba ta so ba, amma shi kam ba haka ya so ba. Cikin sanyin jiki yace. "Shish is ok My Baby." Ajiyar zuciya ta fara sauƙewa bayan tsagaita kukanta, ɗumin jikinsa yana ratsata da ya haifar mata da kasala ta ƙara kwancewa a kirjinsa ba ta ankara da hakan ba. Kusan mintuna biyu kafin ya ɗagota jin ta yi shuru numfashinta ya dawo dai dai. Yatsunsa ya saka yana goge guntun hawayenta, ya kalli gaban rigarsa. "Aww dubi kin ɓata mini riga da baƙin kwalli." "Sorry don Allah." Tace cikin sanyin murya, sai ta ji duk babu daɗi. Duk abin da ta ke masa bai taɓa nunawa ya yi fushi ba, sai dai ma ya maida abin wasa, ya ci gaba da nuna mata cewa yana sonta ko ya yane. Suna zaune shuru baƙi suka fara zuwa dan ganin gidan amarya hakan yasa Dr Awwab fita ya bar gidan. ... Bayan fitan Dr Awwab a gidan Ummi da safe, Ammi da jikokinta su ka shigo gidan dan yau ake wunin gidan ango. Ba ta da ƴaƴa mata sai marigayiya Sumayya da ta bar mata ƴaƴanta uku riƙonsu ya dawo hannunta. Sai Yayunta maza biyu da kannenta maza uku. Kwana ta yi ta tashi da fuskar da ta gani mai kama da na Sumayyar ta. Hakan shi ya fama mata rashin Sumayya, ta farka cikin rashin walwala har ta taho gidan wunin. "Ammi me ya faru ne? Na lura ba ki da walwala yau kwata kwata." Ummi tace ganin yanayin matar yau sam babu walwala a tattare da ita. Numfashi ta sauƙe. "Ummin Awwab na kasa samun nutsuwa tun jiya, bacci kirki na kasa yi, fuskar yarinyar nan ya kasa barin zuciyata. Ba dan Babansu Aliyu bai taɓa sanar da ni cewa bashi da wasu ƴan uwa ba, da zan ce tabbas yaran nan akwai jini a tattare da su, musamman wannan babbar cikinsu." Ummi da ita ma hakan ɓangarenta tun ba yau ba, jiya ma abin ya ƙara dilmaye lissafinta da tunaninta, da damunta bayan kuma wanda kwanaki ya sakata ta kafa ayar tambaya tace. "Hakane Ammi, tabbas akwai wani abun ɓoyayye tsakaninsu. Amma ba mu san ta ina ba. Ta ya? Ba su taɓa sanar mana ba. Mahaifin Awwab har ya koma ga mahaliccin shi ba mu taɓa maganar wa su danginshi ba, balle ma bana jin su ɗin sun haɗa dangi da su, sai dai ikon Allah babu ta in da baya bayyana abu." Shuru dukkansi biyun du ka yi kafin Ummi ta miƙe dan fita amsa ƙira da aka mata. "Ki kwantar da hankalinki, InshaAllah Allah zai bayyana komai." Ummi tace ta fita ta bar Ammi cikin juya wannan lamarin da ta rasa me warware mata. ... Gidan amarya Nuratu bai rabu da masu ganin gidan ba bar karfe biyar. Aunti Ikhram da Zaituna duk sun zo, har Hassana da Hussaina da Hanan da ta maƙalewa Nuratu ta zauna a jikinta. Bayan an fara watsewa su ka tattare mata gidan su ka gyara su ka saka mata turaren wuta ganin babu ƴan uwanta, kuma tana buƙatan hakan, kafin su fara haramar tafiya. "Tashi mu tafi Hanan." Faɗin Hussaina tana ɗaukar jakarta ta miƙawa Hanan hannu, maƙalewa ta yi jikin Nuratu. "Ku barta mana." Nuratu tace ita ma, dan tana son hakan ko dan ta rage mata kewa. "Rufamin asiri. Zo mu tafi Hanan." "Ni da Aunti Noor zan zauna." Tace tana make kafaɗa. ... Tun shigowar su gidan ba ta hau saman ba balle ganin ɗakin amarya, dan ta shaƙa iya shaƙa ganin dukiyar da aka narkar a gidan. Ta ji haushi sosai kuma har lokacin ta ci alwashin shigowa cikin gidan. Ganin shuru Hussaina ba ta sauƙo da Hanan ba ya saka Aunti Ikhram aikenta ta ƙirata. Ba ta so ba ta hau saman, banka ƙofar ɗakin ta yi, da ya saka Nuratu da Hussaina kallon ƙofar su ka ga Binta tsaye ranta haɗe. "Hussaina ku sauƙo mu tafi in ji Aunti Ikhram." "Hanan ce ta ƙi, ku bar mini ita." Nuratu cikin sanyi ganin kamar Binta ba ta da daɗi. Tsaki Binta ta ja bayan ta watsa Nuratu harara da kallon ba ki isa ba, ta ƙarasa shigowa ɗakin ta finciko Hanan daga jikinta ta dauƙeta, ganin haka Hanan ta saka kuka sai ta zauna, ba ta saurareta ba ko bin abin da Nuratu take cewa m ta fice a ɗakin. Ganin haka Hussaina ta yi wa Nuratu sallama ta fita suka barta ita ɗaya. Tashi ta yi ta buɗe labulen windown ɗakinta, tana kallo Hanan na kuka suka sakata a mota suka wuce. A sanyaye ta sake labulen ta fita. Sun gyara falon sun gyara ko ina sai ƙamshi yake, ɗakinta ta koma tayi wanka ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallar magriba. Tana cikin sallar Dr Awwab ya shigo cikin sallama, ganin tana sallah ya zauna ta idar ta miƙe ta linke darduman ya miƙe tsaye. "Ki same ni a falo, saura kuma ki jima." To tace ya fita ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗauki riga doguwa na material marar nauyi da hayaniya ta saka, turare kawai ta saka ganin dare yayi ta yafa kanta ƙaramin gyale ta fita. A falonta ta sameshi zaune yana kallon labarai ta zauna ɗayan kujera. Hankalinsa ya dawo da shi kan Nuratu da ta ɗaura idonta saman Tv kamar mai fahimtar wani abu. Remote ya ɗauka yayi searching zuwa MBC Bollywood ya kai mata. "Na san mata da son kallon Indian drama." Murmushi tayi bata ce komai ba dan ba ƙarya in bata da abin yi tana kallon shirin su da American. Hira jifa jifa ya ke mata dan kawar da shurun, sama sama ta ke amsawa da eh da a'a har suka gangaro hiran gobe yace. "Yanzu dole goben nan sai kin je." "Eh mana, kaya kawai zan karɓa in dawo ai." Ganin yadda ta yi da fuskarta ya sa shi ya murmusa. "To Allah kai mu lafiya. Na godewa Allah ma da aka yi auren nan, da yanzu babu auren nmfa can wani ƙasar za su tura min ke. Tab da kin ga zirga zirga." "Sai ka je, ai ba'a bari." Nuratu tace da sauri tana kallonshi, yayi murmushi ta mayar da hankalinta kan Tv ta ji yace. "Na shiga wani ƙasa ma balle zuwa wani garin. Kin manta ance garin masoyi baya nisa." Ba tace komai ba dan ta yarda zai aikata, dai-dai lokacin ana ƙiran sallar isha'i ya miƙe. "Bari in yi sallah in dawo, zan kai mintuna talatin zuwa sama a waje kar ki ji shuru." "A dawo lafiya." Tace ya amsa da ameen ya fita, kafin ita ma ta miƙe dan sallar ta shige ɗakinta. Tana idar da sallar ta dawo ta zauna ta ci gaba da kallon dan dawowarsa. ... #vote. #comment #share. MADUBIN GOBE (Haske) 47. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Ƙarfe tara Dr Awwab ya shigo gidan, kitchen ya wuce ya ɗauki plate da cup, falon ƙasan ya kashe wuta da komai ya hau sama, falon Nuratu ya shiga ya sameta kwance saman doguwar kujera tana kallo. Tana jin ya shigo ta miƙe zaune. "Sannu da zaman kaɗaici." Ya faɗa mata da murmushi yana ƙarasa ciki. "Yawwa Barka da dawowa." Nuratu tace tana gyara zamanta sosai. Shima zaman yayi kusa da ita yana ajiye abin hannunshi ya ce. "Je kiyi alwala ki zo muyi sallah ko? Mu godewa masa." "Nayi sallah ai." Tace ƙasa ƙasa cike da tsoron da ya fara sauƙa mata, har wani tsuma jikinta ya fara, tasan yau duk gudunta duk wayonta babu mai iya kwatarta hannun Dr Awwab da ta hango babu alamar sassauci ko ɗaga ƙafa a tare da shi. Dariyar da ya ke tasowa Dr Awwab yayi ƙoƙarin dannewa amma duk da hakan bai hanasa murmusawa ba ya juya yana fuskantarta, ƙamshin da yake tashi a jikinta kaɗai ma ya fara tasiri a jikinsa, ya fara amsarshi tun yanzu. Kallonta ya yi alamun tsoro duk ya bayyana a jikinta musamman fuskarta. "Na sani ai, wannan dabanne. Ki fito mana da abin sallah, bari in yi alwala nima." Dr Awwab yace ta miƙe ya fita, Nuratu kamar tayi kuka ta miƙe ta wuce ɗakinta, alwala ta yi ta saka hijabinta ta ɗauko sallayu biyu ta fito ta samu ya shigo. Karɓa yayi ya taimaka mata ta shimfiɗa ya kashe Tv kafin yaja su suka gabatar da sallah raka'a biyu, ya jima yana musu addu'a tana amsawa da ameen a hankali, haka ya juyo ya dafa kanta ya mata kamar yadda Annabinmu Muhammad (SAW) ya koyar damu. Nuratu duk ta tsorata, zuciyarta sai buguwa yake tamkar ya fito, tsoro ya cika ilahirin jikinta. Abu biyu ya sakata tsoro, farkon kasancewarta da namiji da kuma abin da ya wuce ya ke dawo mata. Yadda jikinta ke rawa har Dr Awwab yana ji da ya dafa kanta, hakan bai sakasa barinta ba ko fasa niyarsa ba ya ci gaba. Bayan ya gama suka shafa ta hau linƙe sallayun. Dr Awwab zamansa ya gyara saman kujera yana ɗaukar takeaway da ya shigo da shi ya buɗe ya kalli Nuratu. "Idan kin gama ki zo mu ci." "Na ƙoshi." Ta ce jin maganarsa ya daki dodon kunnenta. Ji tayi abincin da komai ya fita a ranta. Shi ya barta da halin da take ciki mana ya tsaya mata ta abinci. Murmushi yayi yana ci gaba da kallonta ta gama linƙe sallayun ta ɗauka a hannayenta, ya ce. "So kike in ba ki yau ma a baki kenan. Is ok babu matsala zo na baki, daren yau naki ne ai Babyna." "Ni fa na ƙoshi Allah." Nuratu tace tana wucewa ɗaki ko kallonsa ba ta ƙara ba, tare da ajiye sallayun da ta shiga ta shiga kenan. Kyakkyawan murmushi Dr Awwab ya sake yana cije lips ɗinsa na ƙasa, mamakin tsoronta yake dan abun yanzu dariya ya soma ba shi. Baya yayi ya ɗaura kansa saman kujera yana faɗin. "Ki fito, ko in zo in fitarki da kai na wallahi. Duk wayonki da tsoronki bazan fasa abin da nayi niya ba." Ba ta masa magana ba ta barshi, amma maganarsa na ƙarshe da ta jiyo ya sake tsananta bugun zuciyarta, hawaye ta ji ya cika idanunta, kafin ta ankara har sun zubo. Bayan ta ajiye ta wuce bathroom tayi wanka ta fito ta saka rigar baccinta marar nauyi, duk tana yi tana share hawayen da suke zuba bisa kumatunta lokaci zuwa lokaci. Turare kawai ta saka ta haye gadon ta kwanta bayan ta kashe wutan ɗakin. Har kanta ta rufe da bargo tsoro kawai take Dr Awwab ya zo mata. Tana tsoron wannan ranar domin bata da komai da za ta iya bashi washegarin yayi alfahari da ita. Baƙar ranar da lokacin da Mufid ya kwace mata komai ya tarwatsa mata farin ciki ne ya dinga dawo mata tamkar yanzu yake faruwa. Kuka ta fashe da shi ƙasa ƙasa tana share hawayenta, kusan mintuna talatin ta ji an taɓa ƙofa. A hankali ta ciro kanta cikin bargon Dr Awwab ne ya shigo tare da haska ɗakin da fuskar wayarsa. A mugun tsorace ta mai da kanta cikin bargo zuciyarta yana ci gaba da bugawa, da ƙyar ta ke jawo numfashinta tana shaƙa. Kan gadon ta ga ya nufo, tana ji yayinda hawayenta ya ci gaba da silalowa bisa kumatunta ta kasa sharewa. Zama Dr Awwab yayi yana ajiye wayarsa a saman bedside drower, tare da ya janye jallabiyan jikinsa ya cire yana ajiyewa a gefe daga shi sai boxer. Bargon ya ɗaga ya shiga ciki. Nuratu tana jin haka ta juya tana matsawa baya a tsorace. Dr Awwab yana jinta ya saka hannunshi ya riƙota, fizgota yayi ta faɗa saman jikinsa ya saka hannayensa ya rumgumeta, kafafunta ya harɗe da na sa. Murya cikin raɗa ya mata magana cikin kunnenta, tare da hura mata sanyayyar iska ciki. "Dan jiya na ɗaga miki ƙafa yau babu ita Babyna." Kasa masa magana tayi taci gaba da ƙoƙarin kwace jikinta. Bai kulata ba ya mirginata ta koma kasa ya haye samanta ya rumgume. Jin hakan ya saka Nuratu sake fashewa da kuka, kukanma da karkarwa yake fita dan tsoro. "Menene kuma?" Dr Awwab ya faɗa yana sassauta riƙon da ya mata, kukanta taci gaba da yi kusan sakwanni. Ganin ba zata kulashi ba ya sashi cewa. "Shikenan bari in miki abin da za kiyi kukan dagaske." "Ni bana so Doctor. Tsoro nake ji." "Tsoron me kuma? Na faɗa miki bana son wannan tunanin naki. Kar ki ɓatawa Awwab darensa mai cike da alheri, babu abin da zai canza dan wani abu ya faru, ki bari a daren nan mu haɗe mu zama abu ɗaya Babyna. Kar ki hanani wannan damar." Shuru ta masa tana sauƙe ajiyar zuciya tana jin wani sanyi a ranta da Dr Awwab kullum yana cikin fahimtarta, ko ba komai ta ji nutsuwa amma tsoron nan na dankare a ranta. Za tayi magana taji ya rufe bakinta da nashi ya hanata ya fara kissing ɗinta, a hankali ya fara mata wasu abubuwan da ƙwaƙwalwarta ya kasa ɗauka, tun tana iya jurewa har ta zo ta fara tureshi tana hanashi. Dr Awwab yayi nisa baya jin ƙira, ta rikitashi sosai, daren bai bar Nuratu ba sai da ya cika burinshi na ganin sun haɗe sun zama abu ɗaya. Duk kuka da magiyan Nuratu ya rabu da ita bai ji ba. Sai kuka take mishi domin ba za tace ba tasha wahala ba, abu da ba sabo. Wahala kam ta shashi dan Dr Awwab ya gurjeta son ranshi daren, ya hanata duk kan motsi ko ƙoƙarin kwatar kanta. "Allah ya miki albarka ya ba ki dukkan farin ciki kamar yadda kika bani." Dr Awwab yace yana sauƙe numfashi tare da kissing ɗin forehead na Nuratu cike da farin da ta sakashi. Tureshi tayi cikin rashin kuzari, tana share hawayenta ta juya bayanta tana jan bargo ta rufe jikinta, kukanta ta ci gaba da yi, jikinta duk ciwo yake mata ban da kanta da ke sarawa shima dan ciwo, ga wani zafi da ke ratsata tamkar yau aka fara saninta. 'Shikenan yanzu mijinta ya sameta bata da komai, ba a budurwa ba.' Maganganun da suke dawo kwanyar kanta ta ƙara sautin kukanta. Shuru kusa mintuna biyar ɗakin shuru sai sheshshekar kukan Nuratu. Kasa lallashinta Dr Awwab yayi, haka ya sakasa miƙewa ya kunna ƙananun wutar gefen gadon, ya shiga bathroom ɗinta ya tsarkake jikinsa, ruwan zafi sosai ya haɗa mata ya fito ya hawo gadon. "Tashi in taimaka miki kiyi wanka, ko in ɗauke ki." Ya faɗa tare da juyo da Nuratu ya ga tayi bacci tana sauƙe numfashi tare da ajiyar zuciya a tare wani na bin wani. Ɗagata yayi ya ɗaura saman kujera ya yaye bedsheet din ya saka wani kafin ya maidata ya kwanta ya rufe su da bargo bayan ya musu addu'a. Bacci ya kauracewa idanunsa ya zuba fuskar Nuratu ido da hawaye ya bushe, idanunta duk sun kumbura dan kuka. Hannun ya saka ya shafa kumatunta. 'Ƙadan ya rage hankalinsa ya bar jikinsa kukanta ya dawo da shi, ta zautarsa ta rikitasa yadda bai yi tsammani ba, idan ba dan duk ƙaddarorinta ya sani ba zai iya bugan kirji ya ce shi ya fara saninta, bayan haka ma a budurwa ya samu Nusaiba. Ba dan abubuwan nan biyu ba, da zai iya cewa ba budurwa ba ce.' Maganganu dai iri iri yayi ta saƙawa a ransa a daren nan, wani so da ƙaunarta ne yake huda tsoka da jijiyoyin jikinsa yana shiga jininsa. Mutuncin da ƙimarta yana girma a idanuwansa. A haka bacci ɓarawo ya sacesa. ... Washegarin sai ƙarfe tara Nuratu ta farka bayan farkawar asuba da Dr Awwab ya sa ta. Ya rigata farkawa karfe huɗu na asuba, bayan ya farka ya wuce bathroom ɗinta ya haɗa ruwan zafi ya zo ya tasheta, da kyar ta iya tashi ya taimaka mata shiga bathroom, duk yanda ya so ya taimaka mata ƙi tayi ya fita ya barta, haka ta gyara kanta ta gasa jikinta sosai, duk da tana yi tana hawayen zafi haka ta daure dan shine hanyar warakarta, kafin ta fito ta samu baya ɗakin. Kaya ta saka ta tayi sallah tana hauwa gadon sai bacci dan wani mugun gajiya take ji da zazzaɓi zazzaɓi. Haka Dr Awwab da ya dawo daga sallah ya sameta ya kwanta gefenta. ... Da kyar ta lallaɓa ta miƙe ta wuce bathroom ko kallonsa ba tayi ba, ta sake yin wanka ta fito baya ɗakin. Riga doguwa na atamfa ta saka ta ajiye jakanta da mayafinta da komai da za ta buƙata kafin ta hau tattare ɗakin duk cikin dauriya take yi aikin, har lokacin jikinta babu daɗi. Bayan ta gama da ɗakin ta fita ta ɗauki tsintsiya ta dawo ta share. Tana cikin sharan Dr Awwab ya shigo kusan karfe goma da wani abu. Da sauri ya ƙarasa wajenta yana karɓar tsintsiyar. "Waya faɗa miki amarya tana aiki. Please ki bari, ki zo muyi breakfast in kai ki kar kiyi latti. Zan ƙira twins su zo su miki." "Ka bari zan iya." Nuratu tace a hankali dan wani mugun kunyarshi take ji, ta kasa ko kallon fuskarsa balle cikin idonshi da yake yawo jikinta. Da ma bata juran kallo balle yau da anyi me gaba ɗaya. "Zo muje." Yace ya ajiye tsintsiyar ya kama hannunta su ka fita waje. A hankali ta dinga sauƙa a matattakalar benen. A dinning table ya zaunarta bayan ya ja mata kujera, ya zauna shima. Abincin da Ummi ta aiko musu ya ɗauka ya zuba ya saka cokali mai yatsu dan dankaline da kwai. Shayi mai zafi da madara ya haɗa musu. "Mu ci sai muje, ko in ciyar ki." Yace da ita yana ɗaukan fork ɗin kafin ta ɗauka ya ɗauki dankali ya nufi bakinta da shi. Sai lokacin ta ɗago kanta suka haɗa ido ta kawar kanta gefe. "Zan iya." Ta basa amsa a hankali. "Karɓi wannan tun da na ɗebo." Dr Awwab yace ya kai saitin bakinta, dole ta buɗe ya saka mata ta fara ci a hankali. Fork biyar ya bata bai ci ba, a hankali tace. "Kai ma ka ci mana." Murmushi yayi yayinda ya ƙara ɗauka ya kai bakinta yace. "Sai na gama ciyar da amaryata.". Shuru ta masa tana tauna na bakinta taji yaci gaba da cewa. "Kin sani farin ciki sosai daren jiya. Allah ya miki albarka ya bani ikon baki farin ciki kamar yadda kika bani." Ɗago idanuwanta Nuratu tayi da suka cika da ruwan hawaye ta kalli Dr Awwab jin maganganunshi, shi kuwa ya zuba mata ido yana murmushi. Ganin ruwan hawaye kwance cikin idanuwanta ya haɗa rai yace. "Bana son kukan nan Babyna. In kuma so kike mu ɓata to shikenan kiyi ki ga yadda ake shanye hawaye." "Ni bana so." Nuratu tace tana turo baki tare da murmushin da bata san ta yi ba ta ci gaba da cewa. "Doctor ban taɓa tsammani za kayi alfahari da ni ba, shi yasa kullum nake tsoron kasancewa matar aure, dan bani da abin da zan bawa mijina yayi alfahari da ni har in sa shi farin ciki." "Ya isa Noor." Dr Awwab yace yana ɗaura yatsansa saman leɓɓenta ya hanata ƙarasa sauran maganganunta. Shuru ta masa tana share hawayen idonta da su ka zuɓo, lokacin da ya cire yatsarshi a leɓɓanta taji yace. "Bana son ki ƙara irin maganar nan Please, in kuma ba haka ba zamu ɓata. Kin ma shiga ruwan zafi sosai, naga da ƙyar ki ke jan ƙafar." Kai ta ɗaga mishi ta miƙe cike da kunyar jin maganarsa, ya dubeta yana dakatar da ita. "Ina zuwa ba dai kin ƙoshi ba, shayinma ba ki sha ba." "Eh! zan ɗauko jakana." Daga haka ta wuce sama ya bita da kallon tausayi, so, kauna. Yana mutuƙar tausayawa rayuwarta da halin da ta tsinci kanta, dole ta dinga tunanin cewa bata da komai amma shi kam daren jiya ta sashi farin ciki sosai. Kuma zai yi alfahari da ita, dan ta riƙe mutumcinta ko bayan abin da ya faru da ita saɓanin wasu da suke faɗawa wani halin. Sauƙowar Nuratu ya sa shi dubanta, cikin mayafinta babba ta yane har kanta, da handbag ɗinta da duk tasan za'a buƙata. Har ta iso gurin Dr Awwab bai daina binta da kallo ba domin tayi kyau sosai, ba abin da yafi jan hankalinshi kamar jambakin leɓɓanta. Yadda ta rufe kanta da jikinta yafi burgesa tayi shigar mutunci. "Na shirya." Nuratu tace tana kai dubanta gurin Dr Awwab da ya kafeta da ido, ɗauke kanta tayi domin wani kallon da yake watsa mata ya kasa hanata kallon cikin idonshi da sakewa. Miƙewa yayi daga in da yake zaune ya isa gurinta yace. "Ina zuwa minti biyu." Sama ya wuce ɗakinta, hakan yasa ta isa table din ta tattare gurin ta kai Kitchen ta fito falon. Kusan mintuna uku ya dawo ɗauke da hijab ruwan gyalen jikinta, da kallo ta bishi har ya ƙarasa kusa da ita ya saka hannu ya fara warware gyalen jikinta. Ba ta hanasa ba. "Zai ba ki wahala sosai gyalen, ki saka hijabi za ki fi jin daɗi da shi dan zirga zirga." Ba tace komai ba ya gama warwarewa ya saka mata hijabin ta gyara ta ɗauki handbag ɗinta ta saƙala a kafaɗarta ya riƙo hannayenta. "Saura abu ɗaya." Yace ya rage tsawonshi ya rankwafo tare da ɗago kanta da hannunshi ɗaya, fuskarsu ya haɗe numfashinsu ya gauraye guri ɗaya. Nuratu runtse idanuwanta tayi domin ta fahimci mai yake shirin yi, tana shaƙar numfashinsa da ƙamshin turaren jikinshi. Tana jinshi ya ɗaura bakinsa saman nata, a nutse ya fara kissing ɗin bakinta, sai da ya shanye jambakin tas kafin ya saketa. Kasa tsayuwa tayi dai dai, ta yi tangal tangal za ta faɗi ya riƙota jikinshi tana sauƙe numfashi. Sai da ya ga ta samu nutsuwa ya tsayarta yana riƙo hannunta suka nufi waje. Falon ya kulle ya buɗe motar ta shiga kafin ya zagaya yana shiga ya kunna motar mai gadinsa ya buɗe get suka fita. Babu wanda yayi magana har sai da suka hau titi ta ji yace. "Bana son wani ya gani shi yasa na shanye abu na, ina da kishi sosai Babyna." Shuru ta masa magana sai juyar kanta da tayi tana bin garin Maiduguri da kallo. Murmushi yayi yasan ba za ta tanka ba, ya kai hannunshi ya kunna wakar Ali Abed, Nuratu tana jin waƙar ta juyo, ba ƙarya waƙar sau ɗaya ta ji amma ya mata daɗi, tana saurara har suka isa ya sauƙeta a bakin get in da za su taru su tafi. "Sai yaushe kuma Babyna?" "Nima ban sani ba, in mun gama zan ƙiraka." "To Allah yasa ki samu da wuri." Yace ya saka hannun cikin aljihunsa na jeans ya ciro kuɗi da ba tasan nawa bane ya ɗaura saman cinyarta. "Gashi ko za ki buƙaci wani abun." "Akwai kuɗi a hannuna." Ta faɗa tana ɗauka ta mayar masa. "Wannan ni na baki a matsayina na mijinki. Ki riƙe ki je kar kiyi latti." Nuratu ba taso ba ganin ya haɗa rai ya sata ɗauka ta fita tana masa sallama, sai da ya ga shigarta kafin ya ja motarshi ya bar gurin, kai tsaye gidan Ummi ya wuce dan ganin sanyin idaniyarshi. **** DAMATURU. "Abban su tun jiya nake tambayar ka ina za ka je baka sanar dani ba. Kasa na haɗa maka kaya." Alhaji Mamman da yake gyara hulan kanshi yana sauraran Amma Jidda da tun jiya ya sata haɗa kaya take masa wannan tambayar. Juyowa yayi bayan ya saka yana kallonta tana zaune bakin gadonshi yace. "Gombe zan je wajen Yaya Inuwa." "Lafiya? Gombe dai" Ta tambaya cike da mamaki dan ya jima da ta ji ya ambaci sunanshi cikin lumana sai dai da faɗa. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE (Haske) 48. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Lafiya lau Jidda ki kwantar da hankalin ki, babu komai sai alheri." Ajiyar zuciya Amma Jidda ta sauƙe tana fatan hakan, tare da miƙe daga zaunen da take ta ɗauki jakan kayansa da babu komai sai kaya kala ɗaya da abubuwan buƙatarshi. Har cikin motarshi ta ajiye masa jakan tana ce masa. "A dawo lafiya ka gaishe da su." "Za su ji. Ki kula da gidan." Kai ta gyaɗa masa yaja motar ya bar harabar gidan kafin ta koma ciki. ... Hanyar Gombe ya ɗauka dan tunkaran Yayansa da buƙatarshi, wanda yake fatan bayan yafiya da zai masa ya amshi buƙatarshi, ya tsaya masa bisa cikar burinshi a karo na biyu, ba shi kaɗai ba har sauran yayunsa. *** Dr Awwab minti minti yake ƙiran Nuratu ya ji ta gamane, sai tace masa da saura domin abin da yawa kuma suna da yawa. Duk ta gaji kamar tayi kuka haka take ji, ba ta taɓa tsammani akwai wahala ba sai yau ga tayi lattin zuwa. Dan ma matan aure na su layin daban da masu ciki da masu shayarwa da kuma wanda ƴan kudune aka turosu nan. Sai ƙarfe shidan yamma da mintuna ta samu ta karɓi komai nata tun daga uniform, takalma da komai da ya danganci abin shiga camp. Aka sanar da su sai bayan sati biyu za su dawo dan babu zaman camp ga matan aure. Tayi murnan jin haka kuma dama taji labari. Tana gamawa ta ƙira Dr Awwab. "Na gama Doctor." Da sauri yace. "Gani nan zuwa Babyna, kar ki tafi ko ina." To tace masa ta kashe wayar ta zauna tana bin gurin da kallo, kowa da abinda da yake yi. Mintuna kusan ashirin ya ƙirata ta ɗauka. "Ki fito na iso." Kayanta ta ɗauka ta fita tana fita bakin get ɗin ya nufeta da sauri ya karɓi kayan hannunta yana mata sannu. Bayan boat ya sakaa zagaya ya buɗe mata ƙofa ta shiga ta zauna kafin shima ya zagaya ya shiga motar suna barin gurin. "Sannu duk kin gaji." Dr Awwab yace yana mai da kallonshi kan Nuratu da ta jinginar da kanta kan kujeran motar ta lumshe idanuwanta. Jin maganar Dr Awwab ya sata buɗe idanunta tana faɗin. "Na gaji sosai wallahi." "Naga alama. Kina buƙatar hutu da tausa." Yace yana murmushi ya ɗaura hannunshi saman cinyarta ya matsa kafin ya riƙo hannunta. Kanta ta kawar gefe. Sauƙar hannunshi da ta ji saman nata ya sata juyowa ta kalleshi, fuskarshi ɗauke da murmushi ya ɗaga mata gira ɗaya yace. "Ko ba haka ba?" "Ni bana so." Tace ta zare hannunta cikin nashi, bai ce mata komai ba yayi murmushi yaci gaba da tuƙi. Wahalar da ya bata jiyama kaɗai ya isheta, da nashi da na yau duk sun mata rubdugu. Horn yayi aka buɗe ƙofar gidan ya shigar da motar ciki, bayan ya faka Nuratu ta sauƙa tana ɗaukar jakanta. Shi ya shigo da kayanta ciki falon ya samu bata nan, ya wuce da shi ɗakin ƙasa ya saka, ya fito ya wuce bedroom ɗinshi. Alwala yayi ya wuce masallaci jin ƙiran sallar magriba. Nuratu tana shiga ta cire hijabinta tayi wulli da shi saman gadon da jakan ta faɗa kan gado dan ta gaji sosai. Ƙiran sallah ya sata tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta ɗauro alwala, riga marar nauyi ta saka ta gabatar da sallah. Bayan ta idar har ta kwanta ta miƙe tsaye ta fita da sauri dan ɗaura musu abincin dare. Ba dan dole ba, ba za tayi ba, ta gaji sosai. Cikin kitchen ɗin ta tsaya tana tunanin mai zata girka marar nauyi mai saurin dahuwa, tana tunanin hakan ta ji an buɗe ƙofar falon ta fito dan ganin waye, Dr Awwab ne ya shigo da ledoji hannunshi. Ƙarasa tayi tasa hannu ta karɓa ya miƙa mata. "Abinci ne ba sai kin wahalar da kan ki ba." Hamdala tayi cikin zuciyarta, taji daɗi da yayi hakan, zama tayi saman kujera, ya wuce kitchen ya ɗauko musu plate da spoon da ruwa mai sanyi ya fito ya zauna shima, ya buɗe ya juye naman cikin plate ɗin ya ajiye mata gabanta tare da saka spoon biyu ya kalleta. "Bismillahi sa hannu ko in baki a baki, na lura bakya son cin abinci da hannu sai dai a ba ki. Amma babu komai in dai aikin Babyna ne zan yi dan na samu lada a wajenta." "Zan ci da kai na." Nuratu ta faɗa tana ɗaukan spoon ta buɗe ɗayan takeaway ta fara cin abincin ciki shinkafa da miya ne da kayan lambu. Murmushi Dr Awwab yayi ya saka hannu shima ya fara ci bayan ya ture naman gefe. Sosai taci abincin dan rabonta da abincin mai yawa ta manta, dan na safe ma ba sosai taci ba. Bayan ta ƙoshi ta miƙe ta ɗauko cup saman fridge ta tsiyaya ruwa ta sha ta ajiye masa sauran ta wuce ɗakinta. Sallar isha'i da taji ana yi ta gabatar ta hau saman gado ta kwanta cike da gajiya. Sosai ta gaji fatanta ta samu barci me yawa. Bayan Dr Awwab ya gama ya kwashe komai ya zuba a dustbing sauran ya saka a deep freezer kafin ya wuce masallaci, sallah yayi ya dawo ya shiga bedroom ɗinshi, wanka ya yi ya saka boxer da jallabiya ya feshe ya jikinsa da daddaɗan turarensa yana wucewa ɗakin Nuratu. Wutan ɗakin a kunne hakan yasa ya kashe ya hau saman gadon. Nuratu tana ji amma bacci ya cinye idanuwanta ya hawo gadon, yaye bargon yayi ya shiga ciki. Jallabiyar jikinsa ya cire kafin ya kwanta tare da rumgumota jikinshi. "Please Doctor." Ta furta da ƙyar ƙasa domin ta gaji mutuƙa, in yace zai mata wani abun mai ɗagata a gadon gobe sai ya dage. Ba ta son maimaici dan ba ƙaramin wahala tasha jiya a hannunsa ba. Kissing ɗin tsakanin wuyanta yayi yana goga hancinsa a wajen tare da lumshe idanunsa, ƙamshin jikinta na buganshi, da ƙyar ya danne abin da ke taso masa, murya cike da kasala yace. "Ba abin da zan miki, kiyi baccinki na daga miki ƙafa yau." Sai lokacin ta ji sanyi a ranta ta lumshe idanuwanta tana juya masa baya ta ci gaba da baccinta. A hankali ya saka hannunshi ya zagayo ta kugunta da cikinta ya matsota jikinsa ya rumgume, fuskarsa saman gashinta da yake fitar da wani ni'imantaccen ƙamshi, a hankali kafin shima baccin ya ɗaukeshi. *** GOMBE. Alhaji Inuwa yayi mamakin zuwan ƙaninshin, amma bai nuna masa komai ba ya karɓe shi hannu bibbiyu suka gaisa yana tambayarshi kwana biyu. "Lafiya ƙalau, Yaya ya yaranmu?" Faɗin Alhaji Mamman cike da kunyar Yayansa da ya sauƙar masa. "Lafiyan su ƙalau. Ina na wajenka?" Alhaji Inuwa ya faɗa dan ganin ya sake jikinsa da shi. Ko ba komai cike ɗaya ya wuce wasa. Har lokacin Alhaji Mamman ji yake tamkar abin da ya aikata yana jikinsa. Ƙara ƙasa da kansa yayi yana cewa. "Duk lafiyar su ƙalau wallahi. Sai kuma abubuwan da suka faru. Yaya ina neman afuwa bisa abin da na aikata dan Allah ka yafemin. Idan da son rai wallahi da sharrin shaiɗan, domin ɗan Adam dole a rayuwarshi ya aikata wani laifin a lokacin da duk yadda za'a fahimtar shi ba zai gane ba sai daga baya. Kayi hakuri ka yafemin bisa laifin dana aikata maka." Ranar yake jira, kuma ya hango tsantsan nadama a fuskarsa da neman gafara, dogon numfashi ya sauƙe yana murmushi yace. "Allah ya yafe mana gaba ɗaya Mamman. Amma gaskiya abin da kamin ya ɓata mini rai, amma ni dama ban riƙe ka ba, jira nake duk lokacin da ka zo da ƙafarka neman yafiya in yafe maka. Haƙiƙa ka aikata kuskure sosai a rayuwarka Mamman, Sadiya da yarinyar nan ka tauye musu haƙƙi, musamman yarinyar nan da ka cutar tun tana ciki." "Yaya na nemi yafiyar Sadiya ta yafe mini, saura Nuratu." "Ya kamata kam, duk da tana ƴarka akwai haƙƙin neman yafiyarta a kanka, domin amanar Allah ce gurinka, kuma zai muku hisabi. Ƴaƴan nan amanace a wajenmu, Allah zai tambayemu irin tarbiyyar da muka basu, cinsu, shansu da komai nasu na rayuwa. Mu zama masu kyautata musu da jihadi a cikin tarbiyyarsu, sannan ka da mu cutarsu ba bisa doka ba, kar mu musu tsatstsauran hukunci." Nasiha sosai Alhaji Inuwa ya yiwa Alhaji Mamman cikin kwantar da hankali da nutsuwa, dan so yake ya ci gaba da gane kuskurensa da ya aikata. Misalai na rayuwa da hadisin Annabi shi ya saka Alhaji Mamman ya ji jikinshi ya ƙara sanyi idanuwansa suka cika da hawaye har suka samu zuba ya saka babban rigarshi ya share. "Wallahi Yaya sharrin shaiɗan ne da kuma aboki, son duniya da dukiya ya rufe mini ido, ga shi yanzu kuɗin babu, matar babu, ƴar ta gujeni ta tsaneni na sani." Anan Alhaji Mamman ya sanar da Yayanshi duk abin da suka aikata da Alhaji Tukur shekaru ashirin da huɗu da suka wuce. Tun da ya fara jinjina kai Alhaji Inuwa yake har ya kai aya. Idanu ya tsura masa, wannan wai ƙaninsa duk ya aikata haka. Kai ya girgiza yana cewa. "A'uzubillahz subhanallahi, Mamman da hankalinka ka yarda da wannan shirkar. Inna lillahi wa inna ilaihin rajiun, gaskiya ka tafka babban kuskure a rayuwarka, kayi gaggawar neman yafiyar Allah kafin na kowa. Gaskiya ka bani mamaki amma tun da har ka gano illar haka allahamdulillahi Allah karɓi tubanka." "Ameen ya Allah." Alhaji Mamman yace cike da dana sani marar adadi. Duk yadda Sadiya ta so fahimtar da shi lokacin ya kasa fahimta, irin wannan ranar take gudun masa ashe, ga shi yanzu ba shi da komai, komai ya kare masa. A gidan ya kwana bangaren baƙi, dan duk yanda yaso kwana a hotel Alhaji Inuwa hana shi yayi ya saka aka gyara masa bangaren. *** Nuratu sai ƙarfe goma ta farka da mintuna na safiyar ranar, Dr Awwab baya ɗakin, wanka tayi da ruwa mai ɗumi dan ta warware gajiyarta, kuma ta ji daɗin haka, ta gyara jikinta tayi cikin riga da skirt na leshi kalar madara, simple makeup tayi ta feshe jikinta da turare, kana ganinta kaga amarya sabuwa fil sai ƙyalli take da tashin daddaɗan ƙamshi. Gyara ɗakin tayi ta fito falonta ta gyara ta share shi ta goge kafin ta sauƙa falon ƙasa, ba tayi gigin shiga ɗakin Dr Awwab ba ta wuce kitchen. Dankali ta kwaso ta fara fere daidai wanda zai ishesu, har ta gama babu motsinshi, ta soyawa ta gama ta kwashe a flask mai kyau ta soya ƙwai ta ɗaura a sama ta ɗaura ruwan shayi. Tsaf ta gama aikinta cikin nutsuwa har lokacin ba taji motsin Dr Awwab ba, ta jera a dining ta gyara kitchen ɗin ta fito falon ƙasa ta fita waje, ƙiran mai gadi da Baba. Yana ganin ta fito da sauri ya nufeta. "Hajiya kina buƙatar wani abu ne?" "Abinci ne dama." Nuratu tace ta miƙa masa flask ɗin hannunta ya karɓa yana zuba godiya da karamcin Nuratu. Cikin falon ta koma ta share ta goge ta wuce sama dan duba Dr Awwab ko bai farka bane. A hankali ta tura kofar falon ta shiga ciki, babu komai sai ƙaran Ac, cikin falon komai blue black, ya mata kyau, sai ta ga color ya shiga ranta, a kimtse komai tsaf, ana nan ta tsaya ko za taji motsinshi shuru, hakan ya sa ta wuce cikin bedroom ɗinsa cikin tsoro. A tsorace ta ƙwanƙwasa ƙofar amma shiru babu amsa, hakan ya sata tura ƙofar ta shiga, yadda colorn falon yake haka ɗakinma sai sanyi, komai tsaf sai ƙamshi, anan ta ƙara jinjinawa Dr Awwab ba shi da ƙazanta sam. "Doctor! Daddyn Hanan!!" Nuratu tace idanuwanta suna yawo a ɗakin tana bi da kallo har ya tsaya ƙofar bathroom. Shuru babu amsa ya sa ta juyawa ta fita da sauri a cikin ɗakin, tana mamakin ina ya tafi da safiyar nan bai sanar mata ba. 'Ko office ya wuce?' Zuciyarta ya tambayeta yayin da ta ɗauki wayarta ta sauƙo ƙasa ta fara ƙoƙarin ƙiranshi. Ringing ɗaya bai ɗauka ba domin ya shigo gidan. Sake ƙiranshi tayi daidai ya sako kansa cikin falon ɗauke da takeaway da sauri ta ƙarasa wajenshi. "Ina ka tafi tun safe?" Tace tana karɓar abin hannunshi ta kallesa tana duƙunƙune fuska. Hancinta ya lakace ya rankwafo saman fuskarta ya hura mata iskar bakinsa yace. "Abinci na sayo mana kina bacci. Please ki sa ki ran mana." "Ai na dafa mana. Na haɗa breakfast ɗin." Tace tana ƙara haɗa rai ta kawar fuskarta daga kallonsa. "To ya za mu yi da wannan Babyna?" "Ka kyautar wallahi dan ba zanyi asara ba." Nuratu tace ta wuce saman kujera ta zauna bayan ta ajiye ledan saman dining, bayanta ya bi yana ɗauka . "Shikenan bari in bawa mai gadi." Kai ta ɗaga masa ya fita ya bawa mai gadi ta harshen fillancin yace. "Modibbo gashi ka ƙara ta riga tayi abinci, ko ka sadakar in almajiro yayi bara." "Ya mini yawa Alhaji nima ta ƙirani na karɓa bayan wanda ka bani ma zan ajiye da rana." Dariya Dr Awwab yayi cikin farin cikin tunanin Nuratu yace. "Duk yadda kayi." Godiya ya masa yana ƙara cewa ama amarya godiya kafin DrAwwab ya dawo falon ya ƙarasa kusa da Nuratu ya zauna. "Babyna zuba mana to. Amma ki sa ki fuskar nan." Murmushi ta yi har dimple ɗinta suka lotsa, babu musu ta miƙe ta ɗauki plate ta zuba, ta haɗa musu tea a cup biyu ta ajiye musu kafin ta zauna ta ɗauki fork ta fara ci, a plate ɗaya su kaci kamar yadda ta ga yake musu . Ita ta fara tashi ta koma cikin falon ta zauna, ba dan ta ƙoshi ba sai dan idanun Dr Awwab da yake yawo a jikinta ya hanata sakewa, duk ɗago ido da za tayi sai ta kamasa yana kallonta, sai dai ya mata murmushi ba dai ya janye daga kallonta ba. Ko dan rigar jikinta ya kamata kuma yana bin jikinta ne. Tv ta kunna ta ɗauki remote ta fara canza tasha, Dr Awwab daga can yana kallon duk abin da take amma baya samun damar ganinta fuskarta, dan kujeran da take zaune ya basa baya. Tashi yayi ya nufi wajenta bayan ya ƙoshi, zama yayi saman ɗayan kujeran falon, ganin ya haka Nuratu tashi ta kwashe kayan saman dinning ɗin, sai da ta wanke tas dan kar su zama mata aiki ta fito ta koma falon ta zauna saman dogon kujera ta mai da hankalinta kan wayarta ganin Dr Awwab na wani kallon daban a Tv. Daga inda yake ya tashi ya zauna gefenta. Duk Nuratu bata lura ba, domin hankalinta ya tafi kan wayarta tana duba saƙwannin da ba ta samu dubawa ba jiya zuwa yau, duk da ƙamshin turarenshi ya cika mata hanci ba ta kawo sunyi kusanci haka ba. Ba ta ankara ta ji sauƙar kanshi saman cinyarta ya gyara kwanciyar shi ya kwanta. Idanu ta zaro tana kallonshi, ya kashe mata ido ɗaya tare da sakar mata murmushi da yake karɓar kyakkyawar fuskarsa, murmushin da yake haddasa Nuratu bugun zuciya da kasa jure ganin idanunsa. "Kar ki ce komai." Dr Awwab yace ya ci gaba da kallonshi a haka. Baki ta tura ta ƙira Mami yayin da ta kashe Data ta fita a manhajar WhatsApp. "Mami na!" Nuratu tace da ɗan ƙarfi bayan Mami ta amsa da sallama, ɓangaren Mami ta amsa da. "Nuratu! Ya gida ya kowa da kowa." "Lafiya ƙalau Mami, na yi kewarki sosai." "Za ki saba. Ina Doctor? Fatan komai lafiya?" A shagwaɓe Nuratu ta amsa da. "Lafiya lau, duk nayi kewarku wallahi." Dr Awwab yana jinta yana jin daɗin shagwaɓan da take zubawa Mami, ya lumshe idanuwanshi ya buɗe ya kai hannunshi saman cinyarta ya mintsina. Jin zafi ya rasata ya sakata sakin ƙaramin ƙara tana cire wayar a kunnenta. "Me ye haka dan Allah, akwai zafi fa." "Ki rage min shagwaɓan nima ki mini." Harara ta watsa mishi ta maida wayar kunnenta ta ji Mami ta kashe ta kalleshi tana ajiye wayar. "Ka ga ta kashe ko? "Ta san kina tare da mijinki." Yace ya miƙe zaune ya zauna daf da ita, ganin haka ta ja baya ya ƙara matsawa ya riƙota jikinshi. Idanuwanta ta runtse yayinda zuciyarta ya tsinke da ya haddasa mata rawar jiki. Ba abin da ya zo mata kai sai wahalar da ya bata shekaran jiya. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE (Haske) 49. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Har ya gama bayaninsa yana sauraranshi tsaf, bayan ya gama ya sake dubanshi, kansa a ƙasa, numfashi ya sauƙe yace. "Amma Mamman idonka babu kunya? Duk abin da ka aikata har zaka iya buɗe baki ka faɗi haka ko neman buƙatar haka daga gurinta." "Yaya ka taya ni addu'a, sannan kai ma ina buƙatar taimakon ka." Alhaji Mamman yace yana ƙara yin ƙasa da kansa. Jinjina kai Alhaji Inuwa yayi yana cewa. "Allah yasa ta amince. Amma a jikina nake jin babu nasara a wannan buƙatar ka." Miƙewa tsaye Alhaji Mamman yayi yana cewa. "Zan wuce Yaya a gaishe min da yarana. Zan yi latti." Daga nan su kayi sallama Alhaji Mamman ya kama hanya, zuciyarshi fes yake ji domin ji yake buƙatarshi kamar ya biya. Burinsa na farko ya cika, saura wannan da yake fatan shima ya cika, kafin na gaba dan sai na biyun ya cika kafin na ukun. *** "Mene ne hakan Docter?" Nuratu tace tana ja baya tare da buɗe ido ɗaya tana kallon Dr Awwab. Shigar da ita jikinshi yayi sosai tare da riƙo fuskarta da hannunshi, ta runtse idanuwanta da ƙarfi. Sumbatar saman hancinta yayi yace. "Inyi kissing ɗin bakinki?" Girgiza kai tayi tana buɗe idanunta da sauri, mamakin rashin kunyar Dr Awwab take,kai tsaye yake faɗa mata abu babu maganar jin kunya. Shima girgiza kai yayi yana murmushi yace. "Ko bakya so sai na yi." "Ni dai a'a." Tace har lokacin idanuwanta rufe, hakan yasa ya ɗaura yatsansa saman leɓɓenta ya fara zagayewa, taushi gare su. Bai mata magana ba sai jin sauƙar nashi leɓɓan tayi saman nata ya fara kissing ɗinta. Da kansa ya saketa domin Nuratu ta kasa hanashi. Fuskarta ya riƙo har lokacin idanuwanta rufe yace. "Buɗe idonki." Ƙi tayi ta girgiza kai, jikinta na rawa. Ganin haka Dr Awwab yace. "Shikenan bari in sake bai isheki ba." Da sauri ta buɗe idanunta suka sauƙa cikin nashi da suka ƙara ƙanƙancewa da fitina, ya ɗaga mata gira tare da jifanta da murmushin da yake hanata kallon cikin idanuwanshi. Da sauri ta ɗauke kanta tana juyarwa gefe. Sakinta yayi yana murmushi. Tashi tayi da sauri ta shige kitchen dan nan tafi kusa da shi. Jingina tayi jikin ƙofar kitchen ɗin tana lumshe idanuwanta tare da dafe kirjinta dake bugawa tamkar yanzu yake mata abubuwanshi. Dr Awwab kan saka zuciyarta da kanta cikin wani shauƙi da nutsuwa duk lokacin da suka kasance tare, Yanzu kam jin abin da yake mata take har cikin kahon ranta, wani farin ciki na shiga kofofin jinin jikinta da zuciyarta. Murmushin da bata san daga ina yake ba ta yi, sai dai tasan zuciyarta na farin ciki. Jin maganarshi tayi da ya ankarar da ita, in da yake sanar da ita zai fita sai anyi sallah zai dawo. Kanta ta saita kafin ta fara ƙoƙarin ɗaura abincin rana. Tsaf ta gama haɗawa ta jera a saman dinning table tana wucewa ɗakinta, sallah tayi ta sauko ƙasa ta ɗauki wayarta ta ƙira Aunti Rahma da su Hasiya. Kowa dai in ya buɗe bakinsa cewa yake ta cire komai a ranta ta riƙe mijinta sannan taci gaba da gyara kanta, dan duk kwalliyar mace da kyau sai ta ƙara da wanka. Da to ta bisu ƙarshe ta ƙira Walida suka sha hiransu, Walida tana tsokanar ta kafin ta kashe ba tayi gigin ƙiran Ameera ba. Haƙurin nan dai za tayisa dan ganin ribarsa. Babu shskka zuciyarta ya fara amincewa da Dr zai bata dukkan farin cikin da take tsoron rasawa. Wanka tayi ta zuba kwalliya cikin doguwar riga sai ƙamshi turare ke ta shi a jikinta. *** "Wai ba za ki fito ki wuce ba, rana yayi fa." "Gani nan Mama, turare na fesa." Binta tace ta fito cikin doguwar abaya baƙi da ya amshi farin fatar jikinta, ta yane kanta sai ƙamshin turaren da ke cike da surkulle take. Binta farace kyakkyawa tamkar Nusaiba, banbanci su hali. "Na tafi Mama." Tace tana gyara zaman jakar mta da ke kafaɗarta. "Kinyi kyau sosai, ki gaishe su." Da to ta amsa ta fita, adaidaita ta ɗauki shata ya ɗauketa har ƙofar gidan ya ajiyeta, ta biyashi tana shiga ciki. Cike da farin cikin ganin motarshi yana nan ta gyara tafiyarta kafin ta ƙarasa babban falon gidan da sallama.Babu kowa a falon hakan ya sata wucewa sama falon Ummi tayi sallama aka amsa mata ta shiga. ... Shigowar Dr Awwab kenan ya gaishe Ummi, ya sauƙa ƙasa ɗakinsu Hassana dan duba Hanan, tana ganinshi ta maƙale masa sai ta bishi gidansu wajen Aunti Noor. "Gobe zan zo mu tafi My Love, ke da bakya son gidan." "Ai wajen Aunti Noor zan je?" Tace tana turɓune fuskarta cike da shagwaɓa. "To gobe zan kai ki." Ya faɗa yana jan kumatunta ya miƙe yana sumbatar kumatunta kafin ya fita tana ta turɓune fuska. Baya son zuwa su haɗu a gidan dan sai ya mata wayo yake tafiya. Bai shiga wajen Ummi ba ya fita dan sun riga sun yi sallama. ... "Ummi ina Hanan? Ban ji motsinta ba." Binta ta tambaya bayan sun gaisa da Ummi, kamar kullum da fara'a ta karɓeta, dan Ummi macece da ba'a ganin ɓacin ranta, kullum cikin fara'a sannan akwai dattako. Yanzu ma murmushi tayi tace. "Tana wajen su Hussaina, yanzu Awwab ma ya wuce ganinta." "Allah sarki. Mama tace a miki ya gajiyan biki, bata samu zuwa ba." "Ina amsawa sosai wallahi, kun wakilceta ai." Ummi tace ko bayan rasuwar Nusaiba basu cika mu'amala ba sai yanzu da su da kansu suka dawo garesu. Miƙewa Binta tayi tana ɗaukar jakarta tace. "Ummi zan wuce zan leƙa Hanan daga nan." "Nagode sosai ki gaishe da Mama, tsaya ina zuwa." Miƙewa Ummi tayi ta shiga bedroom ta ɗauko dubu biyu kuɗin mashin ta bawa Binta, da ƙyar Binta ta karɓa. Daga haka ta mata sallama ta sauƙa fatan ta Allah yasa Dr Awwab yana ciki su haɗu. Da sallama ta tura ƙofar ɗakin ta shiga lokacin Hussaina ta fito tare da Hanan a bathroom ta mata wanka. "Aunti Binta." Hussaina tace da mamakin ganinta, dan Hassana bacci take tun bayan fitar Dr Awwab. "My Baby zo gurin Auntin ki." Binta ta ce idonta kan Hanan ko gaisuwar Hussaina bata amsa ba. Ganin haka itama ta watsar ta buɗe wardrobe dan ɗaukarwa Hanan kaya. Jin shuru da kuma Hanan ta matso gurinta ya sata juyawa ta kalli Hanan. "Ki je wajen Aunti kinji My Love." Make kafaɗa Hanan tayi tana kallon Binta da ta miƙa mata hannu. Ta juya ta kalli Hussaina. "Za ta kai ni wajen Aunti Noor." Hanan ta faɗa ta juya tana zurawa Binta manyan idanuwanta kyawawa. Binta da taji baƙin ciki ya rufeta jin sunan da ta ƙira ta ƙirƙiro murmushi ta ɗaura saman fuskarta. "Sosai ma zo muje." Da gudu Hanan ta je jin hakaz ta isa wajen Binta ta ɗauketa sama ta kalli Hussaina. "Haɗa min kayanta mu tafi. Kawo wannan in saka mata" "Aunti Binta amma Daddyn ta fa ya hana kuma bai sani ba." "Nace haɗa min kayanta ke kam. Kina tunanin zan cutarta ne?" Girgiza kai Hussaina tayi tace. "Bari in sanar da Ummi to, ko in ƙirashi a waya." "Haɗa kayan ni bari in sanar da ita daga nan zan masa waya." To Hussaina tace ta ɗauki ƙaramin jaka ta sakawa Hanan kayanta kala biyar dan ta san ko an kaita Dr Awwab zai dawo da ita. Binta kuma ta sakawa Hanan gown ɗin da Hussaina ta bata suka fita. ... "Ummi zan wuce sai wani lokaci." Binta tace ɗauke da Hanan da ta maƙale mata jin za ta kaita wajen Aunti Noor. Ummi dai da mamakin ganin Hanan da Binta dan tasan sam Hanan bata zuwa wajenta tace. "To ki gaishe da gida mun gode sosai Allah ya bar zumunci." "Ameen ya Allah." Binta ta faɗi haka ta fita da Hanan, sauƙa ƙasa tayi ta karɓi kayan Hanan wajen Hussaina ta fita. Daga nan Hussaina ta hau tattare ɗakinsu. *** Bai sameta a falon ƙasa ba ya wuce sama, falonta kai tsaye shiga shigowar sa gidan kenan bayan ya tsaya yayi sallah a masjid. A falonta ya sameta kwance tana ganinsa ta miƙe zaune. "Sannu da dawowa." Ta faɗa tana gyara ɗankwalin kanta. "Yawwa sannu Babyna." Yace yana jin daɗin yadda take masa tarɓa in ya dawo. Zama yayi kujeran da yake facing ɗinta ya ɗaura kafafunsa saman center table. "Abinci fa?" Ta tambayeshi tana kai kallonta kan shi shima ita yake kallo babu kiftawa, kwalliyar ya burgesa, simple doguwar rigane jikinta na wani yadin material mai kyau. Murmushi ya mata yace. "Ba dan zan saki wahala ba da kin kawo mana nan." "Babu komai bari in ɗauko." Daga haka ta miƙe ta nufi waje. "Yawwa Babyna ƴar albarka." Dr Awwab yace yana sauƙa ƙasa ya zauna, ta ɗauko komai ta kawo falonta cikin babban tray ta ajiye a ƙasa ta zauna ta buɗe. Idonshi ya lumshe ya buɗe jin ƙamshin abincin, tun kafin ya ci yaji yawunsa ya tsinke, ta duba musu cikin plate ɗaya, jellof ne na shinkafa da ya ji kayan lambu da kifi. "Bismillahi." Nuratu tace ta ajiye plate din da ta saka abincin ta saka musu spoon domin har ta saba da cin abinci da shi tare. Hannu ya saka ya ɗauki spoon ɗaya ya fara ci. Taunawa yake ya zuba mata ido, Nuratu da take cin abinci ta ga kallon ya mata yawa tace. "Zan kware Doctor, wannan kallon fa?" Murmushi yayi yana shafa kwantaccen gashin kan shi, ya kai hannun ya shafi gefen kumatunta yace. "Kin iya girki sosai Babyna, tun ba yau ba na lura da hakan." "Nagode." Nuratu tace cike da jin daɗi mijinta ya yaba girkinta. Haka suka gama. Bayan sun gama ta kwashe komai ta saukar ƙasa ta wanke kafin ta dawo falon. Zama tayi gefe da shi ganin yana aiki a laptop ɗinsa. *** Tun a hanya take mata kuka ganin sun ɗauki wani hanyar ba hanyar gidansu ba. Lallashin duniyar nan ta mata ta ƙi shuru sai ma ƙara kukanta take har suka isa gidansu. Mama da ta ga abin ya isheta tana kallon Hanan dake rizgar kuka tace. "Yanzu ke Binta kin kwaso yarinya babu sani ubanta, sannan ga shi ta ƙi miki shuru. Wannan abun zai kai labari." Faɗin Mama tana kallon Hanan da har farin fuskarta yayi ja dan kuka. Cikin yarda da kai Binta tace. "Za tayi shuru Mama zuwa gobe ne, ko babu komai yarinyar nan kamar ƴata take, ya kamata ta sanmu ta saba da mu, balle kuma ina saka ran zame mata uwa gaba kaɗan ba wata bare ba." "Ni kam ina tsoron abin da zai je ya dawo. Kina sane fa matar nan mun nuna mata hakan tun farko ta ƙi balle shi Awwab ɗin." "A baya kai tsaye muka je mata. Yanzu kuwa shigo shigo ba zurfi zamu musu. Dan ba zan taɓa barinta ta tashi gurin wata wacce ita ma bata riƙe tarbiyyar kanta ba." Jingina kai Mama tayi itama ba za taso hakan ba, domin Binta ta samo musu labarin Nuratu, tun ganin farko da ta mata taji kamar ta santa, hakan ya sa ta kasa zama sai da ta samu sanin wacece ita. Sun shiga mamaki da ruɗanin jin wacce Dr Awwab ya kwaso, da hakan ya ƙara wutar tsanarta cikin zuciyar Binta da Aunti A'isha har da Mama da ke taya ƴarta farautar zuciyar Awwab. Gurin Hanan ta nufa ta zauna kusa da ita, duban yarinyar tayi da ba abin da ta ɗauko nasu ko na Nusaiba sai na Dr Awwab. Hannunta ta kama cikin nata ta murza. "Idan kinyi shuru muka kwana a gidanmu yau, gobe da kaina zan kai ki gidan Auntinki." "Da gaske?" Hanan tace tana kallon Binta cike da farin ciki. Ta ɗaga mata kai hakan yasa ta daka tsalle ta rumgume Binta, jin haka itama Binta ta rumgume yarinyar cike da kaunarta. Da daren ta aika aka sayo mata indomie ta dafa mata da kwai ta ci, ta mata wanka ta canza mata zuwa kayan bacci ta kwantarta kusa da ita suka kwanta tana rumgume da ita. *** Har ƙarfe goma suna zaune falonta yana aiki yana mata hira sama sama tana amsa masa, abinci da ta sauƙa ƙasa ta dafa nan ta kawo su ka ci ta kwashe komai ta sauƙa ta gyara kitchen da fakon ta dawo. Bacci take ji amma ta ƙi tashi ta bar falon sai ta fara a saman kujeran sai ta farka. Dr Awwab duk yana lura da ita, laptop ɗinsa ya rufe yayi murmushi ya miƙe ya fita. Sai da yayi shirin bacci cikin riga da wando mai laushi fari tas, kafin ya dawo falon yadda ya barta haka ya dawo ya sameta. Gyangyaɗi take, ya kashe Tv da wutar falon ya isa gurinta ya ɗagata cak ya nufi ɗakinta. A mutuƙar tsorace Nuratu ta buɗe idanunta jinta a sama, ta riƙo Dr Awwab a tsorace. "Zan faɗi Doctor, ka sauƙe ni." "Not now Babyna." Yace da ta ita, bai tsaya a ɗakin ba ya wuce bedroom ya ajiyeta. Zip din rigarta ya fara zugewa ƙasa. "Ki yi wanka ki fito ina jiran ki, ko in miki da kaina." "Wallahi zan yi da kai na." Tace tana riƙe hannunsa. Yayi murmushi ya fita, kayan jikinta ta cire tayi wanka ta ɗaura towel ta leƙa kanta ta gani baya ɗakin. Da sauri ta fito ta isa gurin wardrobe ɗinta ta ɗauki rigar bacci, tana ƙoƙarin sawa ya shigo. Kamar ta fasa ihu musamman da taga ya nufota, tayi saurin ja baya daidai ya iso ta jingina da jikin wardrobe ɗinta. Rankwafowa yayi saman fuskarta ya goga hancinsa saman nata. "Na lura rowar kan ki za ki mini yau ma." Dr Awwab yace ya karɓi rigar hannunta ya ajiye gefe, ya saka hannu ya ɗauketa cak zuwa gado ya kwantar da ita. Wutan ɗakin ya kashe ya dawo saman gadon kafin ya jawota jikinshi. "Menene kuma Babyna." Faɗin Dr Awwab yana ƙoƙarin warware towel din jikinta ta riƙe. Nuratu kamar tayi kuka har lokacin ta ƙi sakar masa towel ɗin tace. "Ni wallahi akwai wahala ga gajiya." Dariyar da Dr Awwab bai yi niya ba yayi ya sake towel ɗin ya ɗaura kansa saman kirjinta yace. "Za ki saba Babyna, duk na lokaci ne. Kin cika ragwanta wallahi." "Ni dai dan Allah..." Tace cikin rawar murya da tsoro, wahalar da ta sha kawai take tunawa. Bai bari ta ƙarasa maganarta ba ya rufe mata baki da nashi ya fara kissing ɗinta tare da aika mata sakwanninsa. Shuru ta masa tana jinsa a haka ya samu nasarar rabata da towel ɗin duk tana jinsa ta kasa hanashi, luf tayi tana jinshi yana aika mata manya manyan sakwanninsa da suka fara samun guri suna zama cikin ƙwaƙwalwarta da gangar jikinta. Duk ɗaga ƙafar da Dr Awwab yake yiwa Nuratu da hakurin da ya mata daren ranar sai da ya fanshe abinsa. Nuratu duk ta gaji sosai sai da fara masa magiya da kukan gajiya kafin ya kyaleta ya rumgumeta tare da saka mata albarka. Ya bata wahala sosai tamkar ranar can. Ba zai iya wanka bai tsarkake jikinsa ba, hakan yasa ya ɗaga Nuratu ya ji ta sakar masa jikinta, ya kunna wutar bedside drower ya ga tayi baccin wahala sai numfashi take fitarwa. Kwantarta yayi ya shiga bathroom ɗinta ya tsarkake jikinsa ya fito ya cire bedsheet ya canza ya mayarta kan gadon ya kwanta bayan ya musu addu'ar bacci. Kissing ɗin forehead ɗinta yayi ƙasa ƙasa yace. "Kin cika ragwanta Babyna." ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE (Haske) 50. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Wai yau ba za kaje gaishe da Ummi ba ne?" Murmushi Dr Awwab yayi yana bin Nuratu da kallo yayin da take kwashe kayan da su kayi breakfast, ta masa wannan tambayar. "Yau kallonki zanyi ta yi, babu inda zan je." Murmushi Nuratu tayi tana tura baki ta wuce kitchen ta barsa zaune, fara wanke kwanukan tayi ta ji shigowarsa, juyawa tayi ta kalli bakin ƙofar yana tsaye ya zuba mata ido, kanta ta ɗauke, wannan kallon dai yau ya fara takura mata. 'Mutum ko motsi yayi idonsa a kanka.' Ta faɗa cikin ranta tana tura bski gaba. Ganin ta juya ya saka Dr Awwab ƙarasawa inda take tsaye. Tana jinsa dalilin ƙamshin turarensa da ya ƙara ƙarfi yake shiga kofofin hancinta. Ba zato ta ji ya rumgumeta ta baya tare da saka hannuwansa ya riƙe kugunta, hakan ya hana Nuratu ci gaba da aikinta ta dakata, yaar taji tare da wani sabon abu yana bin jinin jikinta. Idanuwanta ta lumshe ta buɗe cike da shauƙi da bata san ya ɗebeta ba. Baya tayi ta kwantar ksnta sanan kirjinsa. "Zan je wajen Ummi me zan faɗama ta." Ta tsinci muryar Dr Awwab yana mata magana daf da kunnuwanta. Sake lumshe idanuwanta tayi ta buɗe murya can kasan makogoro tace. "Ka gaisheta, ka taho min da Hanan." "Ok My Sweet Baby." Dr Awwab yace bayan ya ba ta kiss a tsakanin wuyanta ya saketa, dukkansu biyun suka sauƙe ajiyar zuciya a tare. Kasa tsayuwa Nuratu tayi ta dafa sink tana jinsa ya fita. Ta rasa me yasa duk lokacin da ya mata haka neman nutsuwar ta take ta rasa. Da kyar ta daidaita nutsuwarta ta ci gaba da aikinta tana maganganun zuci. In ance za tayi sure ta samu farin ciki a rayuwarta baza ta taɓa yarda ba. Ta san dai bata son Dr Awwab a kayi aurensu ko tace ba ta da masaniyar hakan, amma gaba ɗaya ya fara canza mata ra'ayin zuciyarta. Ba ta taɓa tsammanin irin karɓar da Dr Awwab zai mata ba kenan a matsayinta na matarsa, shi yasa take tsoron kasancewa matar aure a rayuwarta. Ita ko da mai za ta saka masa bayan ta basa farin ciki kamar yadda yake sakata, ta basa komai da ta mallaka. ... Gidan Ummi kai tsaye Dr Awwab ya wuce dan gaishe da ita ya kuma ga ƴarshi. Falon shuru ƴan biki sun watse kowa ya tafi. Sallama yayi har sau biyu kafin Hussaina ta amsa ta fito a kitchen. "Babu kowa ne?" Ya tambayeta bayan ya amsa gaisuwarta. "Ummi tana ɗaki." "Ina My Love?" Da mamaki Hussaina tace. "Hanan?" "Eh ko tana tare da Hassana." Tsoro ne ya ziyarci zuciyar Hussaina ganin ya juyo gaba ɗaya da hankalinsa kanta, ya kafeta da idanuwansa masu tsoratasu. Masu hana ƴan mata rashin juran gani. "Ke nake tambaya?" Dr Awwab yace yana haɗa giran sama da ƙasa ganin kamar bata da gaskiya. Hussaina da idanuwanta sun cika da hawaye da ƙyar ta buɗe baki tace. "Ba tana gidanka ba. Aunti Binta ta ɗauketa da kayanta jiya tace za ta kaita gurinka." Mari ya kwasheta da shi yana nunata da yatsa. "Are you mad Hussaina? Za ki bar mini yarinya da wannan matar? Ni na faɗa miki ta kawota ko wani ya saka ki." Hussaina da hawayen idanunta sun samu zuba jikinta na rawa tana dafe da kumatunta, ganin ran yayanta ya ɓaci tana girgiza kai tace. "Tace mini Ummi ne ta barta su tafi tare. Wallahi bani na sakata ba." "Rufe min baki wawiya kawai." Dr Awwab cikin ɓacin rai yana yin kanta zai daketa yaji an ƙira sunanshi. "AWWAB." Juyawa yayi ranshi a ɓace ya ga Ummi tana sauƙowa, dan tsawan da yake dakawa Hussaina ya sauƙo da ita. Bayan ta iso ta zauna ta dube shi tace. "Zauna Awwab. Hussaina je ki ɗaki." Da sauri ta bar gurin tana share hawayenta. Ummi ta juya wajen Dr Awwab da ya zauna ya dafe goshinsa da hannunshi. "Lafiya kuwa?" Ya ji tambayar Ummi ya ɗago kanshi idanuwansa har sun kaɗa. "Ummi ƴata zan je in ɗauko, ba zan iya barinta wani gurin ba, bata saba da kowa ba sai mu, ta ya ya zata iya rayuwa da wasu bayan mu. Wai ma wa ya bada izinin tafiya da ita." "Koma ka zauna." Ummi tace ganin ya miƙe tsaye bayan gama maganarshi. Tasan ɗantan yana da sanyi amma idan ransa ya ɓaci fa yana ɗaukar zafi sosai, kuma duk abin da ya zo ransa aikata maka yake. Dole ya koma ya zauna dan jin mai Ummi zata faɗa masa. Ganin ya zauna ya sata sauƙe numfashi. "Ka nutsu ka saurare ni Awwab. Nusaiba ya zame mata dole ta saba da dangin mahaifiyarta, dole ta sansu ta shiga cikinsu. Dan haka ni ban ga abin damuwa ba dan Binta ta ɗauki Nusaiba ba, suma suna buƙatar zama da ita suna buƙatar kasancewarta kusa da su. Ka barta ta kwana biyu gurinsu, idan ya so sai ka ɗaukota ka. Ka ji mai nace? Ban yarda ka ɗaukota ba sai ta kwana musu biyu." "Na ji Ummi." Dr Awwab kawai yace ya miƙe ya fita a gidan gaba ɗaya. Da kallo Ummi ta bishi tana mamakin halin Dr Awwab da kwata kwata baya son dangin Nusaiba. Ko dan abin da ya faru a baya ne Oho. *** Bayan sun tattauna bisa lamarin da kullum sai sunyi akai. Mami ta sauƙe ajiyar zuciya tana canza wayar zuwa kunnen damarta tana cewa. "Shikenan Yaya ka gaishe da ƴan gida na gode. Hafiza sai ta kwana biyu zata dawo, kuma ka shirya akwai waɗanda ta turo wajenka ɗan Babar su Rahma ne, na sanshi na san halinsa, kar ka damu da wani binciken sanin halinsa ɗan gida ne." Fara'a ɗauke saman fuskar Kawu Muhammadu ta ɓangarenshi ya amsa da. "To Masha Allah, haka Allah yake abunsa, Allah kawosa lafiya." "Ameen ya Allah." Mami ta amsa da shi tana kashe wayar hannunta ta ajiye cike da jimamin wannan lamari, gefe daya kuma na zuciyarta lamarin Al'ameen da Hafiza yayi mata daɗi sosai. Ko ba komai za ta fita a kunyar Amma Jidda. *** Cikin fushi ya shigo gidan baya ko ganin gabansa. Da sauri Nuratu ta miƙe dan taranshi. Bayan ta gama ayyukanta tayi wanka ta yi kwalliyarta da haka kawai ta ji tana son ma Dr Awwab ya gani, cikin riga gown da ya bi jikinta ya fito da dirinta kalar purple, ba tayi wani kwalliya a fuskarta ba sai turare da yake tashi a jikinta. Kafin ta kai ga ƙarasawa wajenshi ya haura sama ko ta kanta bai bi ba. Da kallo ta bishi baki buɗe tana jin sanda ya buga ƙofar ɗakin da ƙarfi har zuciyarta sai da ya tsinke. Cikin sanyin jiki ta koma ta zauna tana mamakinsa, tun da suke ko tunda ta sanshi ba ta taɓa ganin ɓacin ransa haka ba. Sanyin halinsa ba zai taɓa baka cewa yana da fushi ba. Har ƙarfe biyu bai fito ba bai sauƙo ba, dan a cikin ɗaki yayi sallah ya ci gaba da kwanciyarshi yana tunanin halin da ƴarshi take ciki. Ba ta saba da su ba, ba ta saba da rayuwarsu ba, yana tsoron ta ga wani abun da sam bai dace ta gani ba a gurinsu, domin shi yasan su yasan su waye su. Yana tsoron su cutarta kamar yadda suka ma mahaifiyarta. Ganin shuru ba shi da alamar sauƙowa kasa da ƙyar Nuratu ta iya yin jarumta ta nufi ɗakinsa dan ganin lafiya jin shurun yayi yawa. Falonsa a buɗe hakan yasa ta shiga cike da tsoro, baya nan ta nufi bedroom ɗinshi. Ƙofar ta taɓa a hankali ta ji a kulle tayi knocking. Dr Awwab kallonshi ya kai kan ƙofar sai lokacin ya tuna halin da ya bar Nuratu, wani tausayinta ne ya kamasa. Da sauri ya miƙe ya buɗe ƙofar, tana tsaye jin an buɗe ƙofar ta ɗago kanta suka haɗa ido. Tsorone ya ƙara shiga zuciyarta ganin har yanzu ranshi a haɗe. Ganin ba ta da niyar magana ya sashi barin ƙofar ya koma ya zauna bakin gado. Da ƙyar Nuratu ta ja ƙafarta ta shiga ciki, a bakin ƙofar ta tsaye ta kasa ƙarasawa wajenshi. Ta wutsiyar ido ya kalleta duk a tsorace take da shi, zai ce ma tamkar jikinta rawa yake. Rai ya ƙara haɗawa ya kalleta ganin bata da niyar cewa komai yace. "Ke zo nan." Hannunta har rawa yake ta nuna kanta cikin rawar murya tace." "Ni!..." "Ke mana, zo nan." Yace yana ƙara haɗa rai tamkar ba shi ba. Idanuwan Nuratu ne suka cika da kwalla ganin zai huce a kanta da bata san me ya ɓata masa rai ba. Da ƙyar ta ja ƙafarta ta ƙarasa wajenshi kanta ƙasa, durkusawa za tayi ya saka hannu ya ɗagota tsaye. Kallonta yayi dressing ɗin jikinta ya mutuƙar masa kyau. Da ya shigo cikin daɗin rai da ya yabi kwalliyar, amma ko yanzu dole ya biyata. "Zauna mana." Yace da ita, da sauri ta ƙarayin ƙasa za ta durƙushe ya saka hannu ya tarota ya zaunarta kusa da shi. Jikin Nuratu mugun rawa yake ta ji yace. "Kalle ni." Idanuwanta ta dago da suke cike da ruwan hawaye ta kallesa da su suka haɗa ido. Rana na farko da ta kasa janye idanunta cikin nashi. Murmushi ta gani kwance saman fuskarshi ya daura hannunshi saman fuskarta ya shafa. "Kar ki mini kuka, in kuma ba haka ba yanzu in saka ki kuka mai dalili." Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta, bayan ta watsa mishi harara ta ɗauke idanuwanta cikin nashi ta fara ƙoƙarin tashi. Awwab ya saka hannu ya fizgota ta faɗo jikinshi ya riƙeta sosai, hannu ya saka ya tallafo fuskarta da hawayen idanunta suka zubo ya fara share mata yana cewa. "I'm sorry My Sweet Baby, wasa nake miki. Zo in ya bi kwalliyar. Na san dai ni aka ma ko?" Ya ƙarasa maganar yana kallon cikin idanuwanta, ta lumshesu tare da ɗaga masa kai. Ba zato ta ji saukar bakinsa saman nata ya haɗa ya fara kissing ɗinta. Tana jinsa ta kasa hanashi ta ƙara damƙe idanunta. Sosai ya yabi kwalliyar, bai barta ba sai da yaji duk ɓacin ransa ya gushe. Bayan komai ya lafa ya rumgumeta cikin jikinshi, hancinta yaja ganin tana lumlumshi ido. "Kar kimin barci raguwa." Murmushi Nuratu tayi ta rufe idonta cike da kunya jin abinda yace. Wato ya lura barci take daga zaran komai ya lafa. To shiɗin ne bana wasa ba, sai ya gajiyar da ita lis. Tana jinsa ya sumbaci lips ɗinta ya miƙe, ba zato ta ji an ɗagata sama. Da sauri ta buɗe idanunta tana tattaro bedsheet ta rufe jikinta da shi ta riƙosa. Cikin bathroom ya ajiyeta duk yanda ya so ya taimaka mata ƙi tayi, ya rabu da ita ya fita, gyara jikinta tayi kafin ta fito ya shiga. Ɗakinta ta wuce ta canza kaya ta gabatar da sallar la'asar kafin ta sauƙo. Dr Awwab masallaci ya wuce ya dawo, sai lokacin wajen ƙarfe huɗu su ka ci abincin rana. Haka suka wuni a gidan Nuratu tana lura da shi minti minti sai ya yi tsaki. Ganin bai sanar da ita ba ya sata kasa tambayarshi dalili. Haka har dare ya kwasheta suka haura sama, babu abin da ya mata ya sata cikin jikinshi su kayi barci. ... Washegarin babu in da yaje a gida ya wuni har lokacin ransa dai a haɗe, duk ƙoƙarinshi ganin ya kawar da abin a ransa ya kasa. Sai ya ga Nuratu yake ƙoƙarin kawar da komai ganin duk itama ta hana kanta walwala. Ita ma duk yanda ta san zata cire masa damuwarshi ta yi. Bai leƙa gidan Ummi ba ranar har dare ya saka Nuratu ta shirya suka fita. Abaya ta saka da mayafinsa ta samesa a wajen mota ta shiga. "Anya za mu fita kuwa." "Lafiya wani abun ya faru?" Nuratu ta tambaya tana bin jikinta da kallo ganin shima idonshi na yawo a jikinta. "Kinyi kyau ne, ina kishi. Gaskiya sai dai ki zauna a cikin mota." Murmushi tayi tace. "Eh na ji zan zauna." Faɗar haka shi ya sashi jan motar suka bar harabar gidan. Cikin gari su kayi ya saya musu kayan ciye ciye suka dawo gida. A falon suka baje su ka ci, shi ya ci kazar da ya siyo Nuratu ice cream ta sha ta ci gaba da kallo. Sai da ya gama ya kai komai kitchen, ya fito ya sunkuceta suka wuce sama, ganin ya nufi ɗakinsa tace. "Zan shirya dan Allah Doctor." "Na ƙi wayon." Yace suka wuce sama sai ɗakinsa, wutar ɗakin ya kashe. Akan gado ya ajiyeta ya bi yana sumbata tare da buɗe musu sabuwar shafin soyayyarshi da ya rikita Nuratu, domin daren ranar manya manyan sakwanninshi ya koyar mata kuma yace yana son ta koya. Bata fahimci komai ba dan sun rikitata sun fi ƙarfinta. Barci ne ya kwashe kamar kullum bayan komai ya lafa, ganin haka ya miƙe yayi wanka ya dawo ya kwanta. ... Kwana biyun ya yi sune tamkar ya jawo su dawo kusa. Yana buƙatar ƴarsa kusa da shi, yaga halin da take ciki. A bakin gadon ya tsaya tare da rankwafowa saman kanta ya tsura fuskarta ido, ruwan saman gashin kansa ya fara ɗiga saman fuskar Nuratu da take barci hankali kwance, ta duƙunƙune cikin bargo sai fuskarta kaɗai a waje. Fuskarta fiyau sai yaga tayi haske, jajayen leɓɓenta ya zuba ido tamkar ba daren jiya ya moresu ba son ransa. Ya shagala da kallonta ya mance da shirin da zai yi. Motsa idanuwanta ta fara tare da motsa leɓɓenta cikin magagin barci. Bai matsa ba bai kuma ɗauke kansa daga gareta ba har ta buɗe idanunta ras a kansa. Murmushi ya sakar mata tare da shafa kumatunta. "Good morning sleeping beauty." Kallonsa tayi karo na biyu sai lokacin ta lura dagashi sai rigar wanka ya ɗaure. Idanuwanta ta mayar ta rufe. Murmushi ya kuna saki yana matsawa. "Buɗe ki kalli sadakinki Babyna, halal ɗinki ne, shaidu sun shaida." Girgiza kai tayi tare da jan bargon har saman kanta ta rufe, wani muguwar kunyane ya kamata. Shirinsa ya hau yi cikin ƙananan kaya kamar kullum riga fari an rubuta PUBG a gaban rigar sai wando baƙi na jeans. Turare ya fesa da ya kauraye ɗakin da ƙamshi. "Na kamaki. Na miki ƙyaune?" Ya faɗa yana juyawa tare da nufan kan gadon. Tun da ya fara fesa turaren ta ciro kanta sanin sai ya gama shiryawa yake shafawa. Ta cikin madubi ya ganta sai dai bai bari ta gane ya ganta ba sai da ya gama. Zama yayi gefenta ya yaye bargon ya buɗe fuskarta. "A farashin nawa kika kalleni?" "Ni fa ba kai nake kallo ba." Tace tana tura baki. Ganin kallon da yake mata ya sata rufe fuskarta da tafin hannunta. Hannunsa yasa ya cire fuskarsa ɗauke da murmushi. "Wannan bakin... A biyani da shi sai in yafe." Jin ya canza salon maganar ya sata itama cewa. "Bari nayi wanka." "Wayo ko?" Marairaice masa tayi tana girgiza kai, dan tasan ya kamasa ba bari zai yi kusa ba. Miƙewa yayi tsaye yana ɗagata ta tashi zaune. "Zan ɗan fita kafin ki gama, bazan jima ba. Ki kularmin da kanki." Daga haka ya sunkuya ya sumbaci kumatunta da leɓɓenta kafin ya fita ta bisa da kallo. Yayi mutuƙar yin kyau sosai. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 51. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Cike da farin ciki Binta ta miƙe ta shiga ɗaki ta fito cikin ƙamshi ta gyara fuskarta cikin kwalliya. Ta samu Hanan da ta hana fita suka fita tare. Yana ganin fitowarsu ya hango hannunsu sarƙe da juna. Hakan ya mutuƙar ɓata masa rai ya ƙara haɗa rai sosai. Ƙwanƙwasa gilashin motar Binta tayi, ya sauƙe ya ɗaura idonsa saman Hanan. "Daddy." Tace da ƙarfi tana son kwace hannunta Binta ta hanata tana bin Dr Awwab da kallon ƙauna tsagwaran tace. "Daddyn Hanan mu shiga ciki mana ka gaishe da Mama, ta samu labarin zuwanka fa." Sai lokacin ya kalli Binta suka haɗa ido, da sauri ya kawar da kansa, baya son ko ganin fuskarta balle jin muryarta. "Ki sakar mini hannun yarinya ta shiga mota." Ƙara ƙasa da murya tayi cikin salon takunta da ta shirya masa. "Haba Doctor kayi haƙuri mana, cikin mintuna da bai fi biyar za ku gaisa." Binta tace tana rankwafo da kanta. Ji yayi ya kasa mata musu yace. "Matsa a ƙofar." Da sauri Binta ta matsa ya buɗe motar ya fito, ganin haka Hanan ta isa wajensa ya ɗagata sama suka nufi cikin gidan, Binta a gaba tana kwarkwasa. Da hoton Nusaiba dake maƙale a falon ya fara cin karo, tayi kyau fuskarta ɗauke da murmushi, tana sanye da abaya. Ya so kamannin Hanan ya zamto nata, sai dai Allah yasa da shi za tayi kama. Kansa ya ɗauke yana zama saman kujera, Hanan ta haye kan cinyarshi. Da sauri Binta ta wuce ciki ta ƙira Mama suka fito tare. Binta tana ɗauke da jakan kayan Hanan. "Ina wuni Mama." Dr Awwab yace da ƙyar yana miƙewa tsaye. Da hannunsa ɗaya ya ɗauka jakan kayan Hanan. Ya riƙo hannunta da ɗaya. Mama da take binsa da kallo ta girgiza kai tana cewa. "Lafiya lau Awwab, ba za kasha ko ruwa ba?" "Bana buƙata." Yace ya fita. Ganin haka da sauri Binta ta bi bayanshi, har ya shiga mota ta zagaya ta tsaya gefenshi. "Haba Doctor me yasa baka mantuwa? Kayi hakuri mana, abin da ya faru ya riga ya faru ya wuce, ɗan adam ajizine, munyi kuskure mun gane laifinmu." Wani kallo ya watsa mata ya juyar kansa kan titi. Tamkar bazai tanka mata ba kusan mintuna biyu, motar ya kunna kafin ya kalli Binta da ta tsaresa da manyan idanuwanta. "Magana ɗaya zan faɗa miki, babu ku babu Hanan, kamar yanda ku ka ƙi mahaifiyarta haka bana son yarinyata ta sanku." Ba ta daddara ba ta gyara tsayuwarta tana faɗin. "Oh dom Allah ka daina wannan maganar. Wallahi mun gane kuskurenmu kamar yadda na sanar da kai. Ko ba kaga hakan ba?" Bai kulata ba ko ƙara wani maganar balle gama sauraronta ya ja motar yana barin gurin. Ya bar Binta cike da takaicinsa, sam ya kasa manta abin da ya faru balle har ta samu gurbi cikin zuciyarsa. 'Anya kuwa haƙarsu za ta cimma ruwa? ... Tafiya yake sai lokacin yaji hankalinsa ya kwanta ganin gudan jininsa cikin ƙoshin lafiya. Kallonsa ya kai kan Hanan ya ga ta zubawa titi ido. "My Love babu wani abin da suka miki?" "Babu komai Daddy, Aunti ta bani abu masu daɗi, haka Mama ma. Su waye su?" Amsar da Hanan ta basa a jere, ƙarshe ta sako masa tambaya. "Good." Yace kawai yana shafa kanta, tare da kaucewa tambayarta na ƙarshe. Gidan Ummi ya nufa dan cewarshi sai ya gama amarci kafin ya ɗaukota gaba ɗaya. ... "Ga ta kuma na dawo da ita. Wallahi idan yarinyata ta ƙara taka ƙafarta ta fita ba tare da sanina ba sai nayi mummunan ɓata muku rai. Oya ku tashi ku bani guri." Sum ƴan biyu suka wuce ciki tare da kayan Hanan zuwa ɗakinsu. Ummi da Hanan suka sauƙo tare dan tana zuwa wajenta ta wuce ta rukumkumeta. Fuskar Ummi babu fara'a ta ƙarasa ta zauna. "Hanan je ki wajen Aunti Husna." Ta faɗa, babu musu yarinyar ta wuce ɗakin ƴan biyu. Ummi ta juya ta kalli Dr Awwab da shima ransa a haɗe. "Wato sai da ka ɗaukota. Me yasa kake haka Awwab?" Sai lokacin ya ɗan saki ransa ganin mahaifiyarsa ranta a haɗe. Ana jimawa kafin aga ɓacin ranta. Cikin kwantar da murya yace. "Ummi kwana biyu fa kika ce, kuma naga ya cika." Girgiza kai tayi tace. "Haka nace, amma ba yana nufin kwana biyu tal ba Awwab. Zuwa wani lokacin tun da hutun makaranta take." "Ummi bazan iya barinta cikinsu ba, gani nake za su cutar mini da ita kamar yadda suka cutar da mahaifiyarta." Hannunta ta ɗaura saman nasa. Abin da hakan yake jimawa bai faru tsakaninsu ba, dan wani lokaci tana masa fulako shi yasa shima bai cika sakewa da ita ba. "Sun canza Awwab ba ka gani ba? Tsoron Allah da dana sani ya shigesu. Basu da burin da ya wuce su shiga cikinmu. To kai me yasa ba za ka manta abin da ya faru ba. Ka bar yarinya ta san dangin mahaifiyarta." Miƙewa tsaye Dr Awwab yayi bayan ya zare hannunsa yace. "Kiyi hakuri Ummi abune mai wuya a guri na. Ku kula min da ita." Daga haka ya fice, Ummi ta tashi ta koma sama tana mamakin rashin mantuwar Awwab akan abin da ya faru a baya. Ita kam ta yafe musu dana basu mata wani laifin ba. Ta sakar musu fuska kamar kowa, ko ba komai jini ya haɗa ta dalilin Hanan. ... Shuru falon babu komai babu kowa sai ƙaran Tv, har zai haura sama yaji ƙaran ruwa a kitchen, da sauri ya sauƙa ya nufi can. Tana tsaye tana juya miyarta sanye take da dogon wando da riga ya bi jikinta ya mata kyau, dan tsantsine da shi kayan, kanta cikin hula mai kyau ta juya bayanta. Bayan ya bi da kallo, ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi, domin kwalliyar ya tafi da tunaninsa, idanu kawai ya zuba mata. A jikinta Nuratu ta ji ana kallonta, ga ɗan duhu da ta gani a kitchen din alamar an tare ƙofa. Cikin sauri ta juya baya, idanun Dr Awwab ƙyam a kanta. Ba shiri ta juya baya domin ba ta tsammaci ganinshi yanzu ba, masa cigaba da aikin tayi. Ji tayi an dafa kafaɗarta ta runtse idanunta da sauri. Juyo da ita yayi, sosai ta bashi dariya ganin ta rufe idanunta, yayi murmushi ya kai hancinsa kan nata ya goga. "Kinyi kyau sosai My Baby. Zan ba da kyautar wannan kwalliyar, fatan duk kin haddace karatunmu." Kunya sosai Nuratu ta ji ta ƙara runtse idanunta tana yin ƙasa da kanta jin maganarshi na ƙarshe. Sauƙar lips nasa ta ji bisa kumatunta zuwa wuyanta yana sumbata. Kusan mintuna biyar kafin ya saketa, da sauri ta juya masa baya ta ji yace. "Bari in yi sallah." Ba ta iya basa amsa ba ya fita, dafa inda take tayi tana sauƙe numfashi. Bayan nutsuwarta ya dawo ta sauke miyar ta kwashe a flask ta kai dinning, kafin ta wuce ɗakinta, dama shine ƙarshe dan ta riga ta gama haɗa tuwo. Sallah ta gabatar sai kuma ta ji kunyar fita haka ta canza riga zuwa dogo ta sauƙo. Da ya dawo daga masallaci ya sameta haka ya haɗa rai. "Ina kwalliyar nawa?" "Nayi girki da kayan shine na cire." "Wayo dai, ai akwai wasu kayan." Yace yana zama gefenta har jikinsu na gugar juna. "Zan saka wataran. Abinci fa." Tace tana canza maganar, dan ita kam wannan kayan ba yanzu za ta saka su ba, sai ta saba dashi sosai dan har yanzu tana jin kunyarsa. "Kawo mana nan, na gaji da zaman table." Miƙewa tayi ta kwaso komai ta kawo falon kafin ta zauna ya sauƙo ta zuba musu suka hau ci. Ta ji daɗin ganin yau ya saki fuskarshi ba kamar kwana biyun da ya wuce ba. Kuma taji daɗi yadda ya zage ya ci abincin. ... Kwana biyun soyayya mai tsayawa a rai Dr Awwab yake nunawa Nuratu, wani mugun kunyarsa take ji sosai har ta rasa dalili, ba ta taɓa tsammani za taji kunyarsa haka ba sai yanzu da yake matsayin mijinta. Kullum sai yaje gidan Ummi duba Hanan da suke rabuwa da rigima sai ta bisa gurin Nuratu. Amarci yake baya fita aiki dan hutun da ya ɗauka, in abun ya kama yayi a laptop, baya fita ko ina daga gida sai gidan Ummi. Nuratu tana ƙiran ƴan gida suna ƙiranta dan jin lafiyarta. Yau ta cika sati ɗaya za'a mata bakwai kamar yadda al'ada ya tsara. Ummi tun da safe ta turo ƴan biyu suka taimaka Nuratu ta tsife kanta, har da Hanan da ta biyo su ta maƙale mata. Tana son yarinyar. Bayan sun gama Hussaina tace. "Aunti kitso za kiyi ko wankewa, amma kanki babu datti sai ƙamshi, kiyi kitso Allah zai fi kyau." "Duk yanda ku kace shi zan yi." "Mu ko Yaya Awwab? Ai shi za a yi wa kwalliyar." Hassana tace tana dariya Hussaina ma ta saka dariya jin abin da Nuratu tace, sai kawai Nuratu ta fara kallonsu domin sun burgeta, komansu ɗaya dan kama suke sosai. Ji tayi da Allah ya bata tana so musamman da Dr Awwab in suka ɗauko kyansa. Hassana ce ta tsagaita dariyarta tace. "Bari in ƙira mai lallen ta zo. Har da me kitson, sun iya sosai." To Nuratu tace tana kama gashin kanta bayan Hussaina ta taje mata. Cikin mintuna talatin mai lallen ta iso ta fara aikinta, lallen ja ta fara saka mata a yatsu maroon kafin baƙi. Mintuna kaɗan me kitso ta iso ta fara mata. Awa ɗaya da sakawa suka tsinci muryar Aunti Rahma da Aunti Hasiya. Nuratu kamar tayi tsalle ta rumgume su musamman wacce ta gani a bayansu. Mami ce da Aunti Zarah ta zo ganin ɗakin ƴarta, kamar yadda ake yi ran bakwai uwa za tazo ganin ɗakin ƴarta. "Mamina don Allah ki zo kusa da ni, ko in tashi in taka lallen." Nuratu tace kamar tayi kuka. Mamin ma tayi kewar ƴarta da sauri ta matsa kusa da ita, Nuratu kanta ta ɗaura saman cinyar Mami cikin shagwaɓa tace. "Nayi kewarki Mamina. Fatan kina lafiya." "Lafiya lau Autana, ya zaman aure?" Tace tana shafa gashin Nuratu. Kunyane ya kama Nuratu ta kasa magana. Ta gaishe da Aunti Zarah da Rahma da Hasiya kafin ƴan biyu suka gaishesu suna mamakin wannan ahli. "Ƙannansa ne." Nuratu tace da su Aunti Rahma ganin kamar basu ganesu ba, sai da Nuratu ta faɗi haka suka tuna sun gansu ran buɗan kai a gidan Ummi, duk tsammaninsu mutum ɗaya ke wulgawa. Aunti Zarah ne da Rahma suka ma Mami jagora ta ga falon ƴarta da ɗaki, kafin ta sauko tana yaba ƙyan gidan da godewa Allah da ya bawa ƴarta miji nagari da arziki mai albarka. Wajen karfe sha biyu Ummi ta iso da nata jama'ar ganin gidan ɗanta. Lokacin Nuratu ta cire lallen ƙafarta dana hannu, an mata kitso ƙanana, tayi wanka ta saka atamfa mai blue da ratsin ruwan toka tayi kwalliya, tayi kyau ga kyallin amarci da take yi. Kafin zuwan su Ummi Aunti Rahma da Hasiya da Aunti Zarah sun haɗa abinci mai yawa dan baƙi tare da abin sha, haka kuwa bayan gaisuwa suka zuba aka hau ci da sha. Nuratu dai sama ta hau da yayunta suka sata tsakiya da tambayar lafiyarta. Kunya ya hanata faɗin komai sai murmushi da tayi ta ɓoye fuskarta. Dama suka ba hakan suke son ji ba, fatansu tana jin dadin zama, ta tabbatar musu da haka. Daga nan su ka ci gaba da bata shawarwari. ... Ta shiga ruɗani sosai, ganin babbar mace da ake ƙira da uwar amarya tayi kama da yarinyar da take ƙira da mai kama da ƴarta Sumayya. Ganin fuskar Mami ya ƙara rikita zuciyar Ammi, domin gani tayi tafi kama da shi akan ƴarta da kuma yarinyar, domin su biyun kamanninsu har ya ɓaci, duk da ta kasance mace shi kuma fuskar girma ya sameshi. 'Lallai akwai ayar tambaya kan waɗannan bayin Allah. Kuma dole sai na binciko.' Zuciyarta ya faɗa da ta ji tana neman mai amsa mata. 'Ta ya? Ta ina sata soma?' Ta watsa zuciyarta tambayar da ta rasa mai amsa mata, sai ta nutsu tayi tunani. Duk inda Mami da Aunti Rahma suka wulga sai ta bisu da ido tana ƙare musu kallo ko akwai inda ta kuskuro cikin kamanninsu. Sai ta ga kallon da take musu yafi ƙara hasko mata tsantsar kamansu, domin komai Aunti Rahma take gani take tamkar Sumayyar ta. ... 'Ba zan taɓa daina ganin kamanninsu da ita ba.' Faɗin Ummi cikin zuciyarta, da tun ranar da ta saka idonta saman fuskarta ta kasa dai na tunanin hakan. Ta rasa wa za ta tunkara da wannan maganar. 'Awwab da ya jawo komai, kuma ya nuna bai ga hakan ba, sannan ya nuna tamkar bai san meke faruwa ba.  Ko kuma waye?' Wani sashi na zuciyarta ya faɗa mata haka. ... Dr Awwab bai san meke faruwa ba, dan tun fitarshi na safe ya wuce ɗaurin auren abokinsa daga masallacin juma'a. Ƙarfe biyu da mintuna ya shigo gidan, tun a harabar gidan ya ga motar Ummi da sabbi wasu kusan biyar. Sai da ya isa kofar falon ya ji hayaniya ya buɗe ya shiga. Ummi da baƙinta suna Awwab a sama, Mami da nata baƙin a falon ƙasa. Bini bini Nuratu ta cukwuikuye Mami, duk faɗar Aunti Hasiya haka ta ƙi sakinta. Jin sallamar Dr Awwab ya sasu kai duba wajensa. Cike da kunya ya ƙarasa ya gaishe su suka amsa, ya wuce sama cikin sauri. "Tashi ki kai masa abinci Nuratu." Faɗin Aunti Hasiya tana duban Nuratu da ba ta da niyar tashi. "Ni kuma." Tace tana kallon Mami, Mami ta ɗauke kanta. Aunti Hasiya ta daka mata tsawa. "Ba dake nake ba." Gunguni ta fara ta miƙe ta wuce wajen table, ta ɗauki warmers ɗin dake jere a cikin babban tray, plate da cup da ruwa ta ɗaura a sama, ta ɗauka ta wuce falonta ganin nan ya wuce. Da sallama ta ta tura ta shiga.   Jin sallamarta ya saka Dr Awwab miƙewa zaune daga kwancen da yake. Nuratu ta ƙaraso ta ajiye warmers ɗin center table da yake tsakiyar falon. "Ga abinci nan." Wani kallo ya mata dan ta masa kyau sosai. "Da haka kike bani." Girgiza kai tayi tana buɗe warmers din dan zuba masa. "Wai ma taron me ake na ga har da motar Ummi tana ina?" "Yau bakwai ai, shine su ka zo. Suna falonka." "Menene shi?" Ya tambaya domin yama manta da wani abu sunanshi bakwai. .... #vote #comment #share MADUBIN GOBE 52 Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Kinyi kyau." Ya faɗa yana kamo hannunta da ya sha lalle, gefenshi ya zaunarta ya zame ɗankwalin dake saman kanta yabi ƙananan kitson da aka mata da kallo. Nuratu da idanu take binsa. Kitson ya shafa har zuwa jelan gashinta dogo yaja mata kaɗan. "Ban taɓa tsammani kina da dogon gashi ba, na ɗauka kawai tsantsine sai ƙananu da suke kwance na goshi." Murmushi ɗauke saman fuskar Nuratu tace. "Abincinka zai huce." "Ni ki bani a baki." Ya faɗa yana narke mata tare da kamo hannunta. Idanuwanta ta waro farare masu haske tace. "Ka rufamin asiri don Allah. Ummi, Mami sunanan ga Aunties. Ka ga tafiyana ma kar ace na daɗe." Daga haka ta fara ƙoƙarin tashi a gefensa, ya saka hannunsa ya riƙo hannunta tare da jawo jikinshi ya mata kyakkyawar masauƙi bisa cinyarsa, mamaki dai duk ya kama Nuratu, ga tsoro da kunyar kar aga tajima. A cikin kunnenta ya mata raɗar da ya sata cikin sauri ta ƙwace jikinta tana tashi ta fita tana dariya cike da kunyar maganar da ya faɗa mata. Sai da ta saita kanta ta gyara ɗaurin ɗankwalinta kafin ta sauƙa falon ƙasa. Har yamma ƙarfe huɗu kafin kowa ya fara haramar tafiya, duk a tare suka shirya. Yayunta sun gyara mata gidan sai ƙamshin turaren wuta yake. Mami da ƴan matanta su suka fara fitowa za su tafi bayan sunyi sallama da su Ummi da Dr Awwab da ya sauƙo. Nuratu har da guntun hawayenta ta hana Mami tafiya. Muhsin da daga baya ya shigo sai dariya yake mata tana ƙara turɓune fuska. "Ni wallahi Mami bana son ki tafi." Tace tana ƙara riƙe Mami. Itama dai dauriya take dan tana son Nuratu. Kara da kawaici kawai take da ta zauna ta lallashi abunta. "Za ki saketa ko sai ɓata miki rai." Aunti Hasiya tace tana zagayowa ta wajensu. Ganin haka ya saka Nuratu sakin Mami tana ɓata rai tare da turo baki. "Da kar ki saketa kiga, na zagayo sai na ɓata miki rai da dalili." Baki ta ƙara turawa ta ƙi kulata. Tana kallo suka shige mota suka barta. Hawayenta ta share tana rufe fuskarta dan Ummi da bakinta. Sosai za tayi kewar su kuma tasan za su jima basu haɗu ba. Ammi kawai kallonsu take dukkansu, musamman wanda yake jan motar da take ganin tamkar nata ɗan Abdallah. Ji tayi kamar ta ƙirashi ko zai ƙi amsa sunan dan ta tabbatar ba ɗanta Abdallah bane. Dariya yake yiwa Nuratu har da gwalo kafin su fice a gidan Nuratu tana cewa. "Yaya Muhsin zamu haɗu ai." Sunan da Nuratu ta ƙirasa da shi ya bawa Ammi tabbacin ba Abdallah bane, sai da tsantsan kama da yanayi da suke, kamar yadda ƴar uwarshi ke kama da ƴar uwarsa Sumayya. ... "Yaya Awwab ka zo in ji Ummi tana waje." Hussaina tace da Dr Awwab da yana falon yana jin duk abin da ake. Babu musu ya miƙe ya fita wajen. "Ummi ga ni." Yace idonshi kan Nuratu da ta kasa motsi tana sharan hawaye ta cikin mayafinta. "Ja matarka ka je ka lallasheta. Mu zamu tafi sai wani lokaci." Cike da kunya ya ƙarasa wajen Nuratu ya kamo hannunta suka shiga falo. Ganin haka ya saka Ummi da baƙinta tafiya, har da Hanan da kamar tayi kuka dan tana son zaman gidansu. "Ummi zan wuce gida kawai." Faɗin Ammi tana tsaye. "Ammin Sumayya lafiyarki ƙalau? Na lura kwata kwata ba ki da walwala tun zuwanmu." Ummi tace tana duban Ammi da tsabar tunani ya sauƙar mata ciwon kai. Kai ta girgiza tana nufan motarta. "Kai na ya fara ciwo, zan wuce gida na huta." "To mun gode. Sai wani lokaci." Faɗin Ummi, daga haka kowa ya shige motarshi direba ya ja suka bar harabar gidan. ... Me ta haɗa da su? Me ta haɗa da matar da ƴaƴanta da suke kama da yaranta? Me yasa take kama dashi? Me yasa hakan? Me yasa Ummi da Awwab basa ganin hakan sai ita ɗaya. Ko dai gizau suke mata? 'Ko dai ko dai?' Ta tambayi kanta tana lumshe ido dan ciwon kai da yake addabatar. ... Rumgumeta Dr Awwab yayi cikin jikinshi bayan shigarsu falon. Ajiyar zuciya kawai take sauƙewa, ɗumin jikinshi yana ratsata da ya haddasa mata kasala. Sun jima a haka kafin ya ɗagota yana riƙo fuskarta. Cikin idonta yake kallo, kasa janye nata Nuratu tayi. Rana farko da ta kai tsawon mintuna ta jure kallon cikin idanuwanshi. Tana gani ya ɗaura bakinsa saman nata ya bata light kiss. Idanuwanta ta lumshe ta buɗe sai lokacin ta janye daga kallonshi tayi ƙasa da idanunta. Har lokacin yana riƙe da fuskarta taji yace. "Kin cika shagwaɓa Babyna." Baki ta tura ta juyar kanta gefe. Kwantowa yayi jikinta tana jin hannunshi na yawo jikinta ta kasa hanasa. "Muje ki cika alƙawarinki." Ta ji yace murya ciki can da ƙyar ta iya jiyoshi da kyau. "Wani alƙawari kuma?" Ta ambata kamar dole duk da ta fahimci zancensa. Hannu ya saka ya juyo da fuskarta da ƙyau yace. "Wanda na faɗa miki ɗazu mana." "Ai ni banyi magana ba." "To ai shine kin yarda kenan." "Zan maka kuka wallahi." Tace tana kifta idanuwanta. Murmushi yayi ya sumbaci goshinta. "Shikenan, zuwa dare na miki afuwa yanzu." A haka suka zauna har aka ƙira magriba yayi alwala ya wuce masallaci. Wanka tayi ta gabatar da sallah. Riga doguwa marar nauyi ta saka, tabi duk lungu da saƙo na jikinta ta shafa turaren da Aunti Rahma ta bata tace idan ya ƙare ta ƙira ta faɗa mata za ta aiko mata wani, dan yana da amfani sosai. Bayan ta gama ta zauna zaman jiranshi, duk tsoro ya kamata dan gidan ya mata girma sosai. Sai bayan sallar isha'i ya dawo ɗauke da takeaway da ya musu. A falonta ya sameta kwance tana kallo ya zauna kusa da ita. "Zan fara bin ka masallaci wallahi." Tace daga kwancen da take cikin doguwar kujera. Dariya yayi yana jan yatsun kafarta. "Me ya farune My Queen?" "Ba ka dawowa da wuri ba. Ni kuma tsoro nake ji." "Da gaske." Yace yana rankwafowa saman kanta, ganin haka ta runtse idanuwanta tana ɗaga masa kai. Ƙamshin turarenta ne ya bugi hancinsa ya kasa janyewa daga saman kanta. Kansa ya kai jikinta ya fara shinshina duk inda ya ji ƙamshin yana sumbata, domin ya tafi da tunanin ainun. Kasa hakura yayi dan gaba ɗaya ta rikitashi da ƙamshinta. Ya ɗauketa suka wuce ɗakinta, rikice mata yayi sosai, ita kanta Nuratu ta tsorata, dan bai taɓa mata haka ba. Haka tana ji ta kasa hanashi abubuwan da yake mata, duk ya kashe mata jiki, har sai da ya sakata itama ta fara tilawar karatun da yake koya mata, ya sata bin umarnin maganar da ya faɗa mata. Abincin da basu ci ba kenan daren ranar. Da asubanin kusan a makare suka farka wajen Shida saura, a gurguje yayi wanka yayi alwala ya fito ya tasheta kafin ya fara gabatar da sallah. Wanka Nuratu ta gasa jikinta dake ciwo dan ta murzu wajensa. Tayi ɗaura alwala ta fito ta saka kaya tana gabatar da sallah, lokacin ya idar yana azkhar. "Ina kwana?" Tace bayan ta durƙusa kusa dashi. Kai ya ɗaga mata, ta miƙe ta nufi gadon ta janye bedsheet ɗin saman cike da kunya, ta wuce bathroom dashi ta saka a washing machine. Fitowa ta ciro wani cikin wardrobe ɗinsa ta hau canza wani, tana jin ya gama azkhar ɗin duk tsammaninta fita zai yi sai ta ga ya nufota. Mazewa tayi taci gaba da aikinta ba zato taji ya riƙota sun faɗa saman gadon ya rumgumeta. Hijabin jikinta ya zare. "Bari mu biya barcinmu na daren jiya da bamu samu yi ba." Za tayi magana ya ɗaura yatsansa saman leɓɓenta. "Barci Please. Da safe zan bada tukuici mai tsada, ko ki zaɓi abun da kike so daga gareni, in har Allah ya hore mini zan ba ki." Kunyane ya rufe Nuratu ta tura kanta cikin jikinshi. "Please ki faɗamin. You're so sweet My Love. Ina alfahari da ke kasancewarki matata, ina fatan ki zama uwargidana a matan Aljannahtul Firdausi. Allah yayi miki albarka." Ta ji maganarshi cikin kunnuwanta yana hura mata iska. Cikin mutuwar jiki da ya sauƙar mata ta lumshe idanuwanta tana ƙara gyara kwanciyarta cikin jikinsa. Wani yanayi take ji yana bin jinin jikinta game da Dr Awwab. Murya ƙasa ƙasa tace. "Ban baka kaina ba dan ka biyani, asalima farin ciki nake da yadda ka ke shiga farin ciki a kullum idan mu kayi tarayya, wannan kaɗai ya isheni, addu'aarka ya wadatar da ni." Matseta yayi har sai da tayi ƙara ya sassauta riƙon, ji yake kamar ya haɗiyeta ya huta dan kauna. "Ina sonki sosai Matata." Ita dai Nuratu ta kasa magana dan kunya da farin ciki, idanuwanta suna cika da hawaye tana ƙoƙarin shanyewa kar su zubo. Ita shaida ce dan taga so jiya wajensa, dan abubuwan da Dr Awwab ya mata ba za ta iya faɗarsu ba sirrinsu ne. A haka wani baccin ya ɗaukesu. *** Sha biyu da mintuna uku. "Kamar sallama nake ji Hajiya Sadiya?" "Nima hakan na ji kamar." Mami tace ga Aunti Zarah kafin ta yi shuru, dan jin da gasken sallama ake. Ba zato taji muryar da bata tsammaci ji yanzu ba, domin alaƙarsu ya jima da yankewa. Kuma bata burin sake ganinshi a rayuwarta. Aunti Zarah ne ta amsa tana gyara zaman mayafinta, ta kalli Mami da ta kasa daina tunanin me ya zo yi a wannan lokaci kuma. Me ya dawo dashi rayuwarta. "Hajiya Sadiya ki gyara mayafinki zai shigo fa, kina jin na bashi umarni." Wani baƙin ciki ne ya rufe Mami, cike da taƙaicin da ya rufeta ta haɗa rai tana jan mayafinta ta rufawa jikinta. "Suwaiba ki je ɗakin can ki jira ni." Aunti Zarah tace tana nunawa matashiyar budurwa da ta kawo dan taimaka mata ɗakin Munirat na da. Babu musu ta miƙe tare da kullin kayanta ta shiga, dai-dai lokacin ya shigo cikin falon haɗe da wani sallamar a bakinsa. Aunti Zarah kaɗai ta amsa. Jin rashin amsar Mami ya kai dubanshi gareta, ranta a haɗe ta juyar kanta gefe. Tana nan a Sadiyarta mai son ƙamshi da gayu, duk yaran da ta tara har da jikoki amma jikinta bai nuna ba, ko dan ta jima babu aure kuma babu haihuwa, sai jin daɗin rayuwa, babu takurar miji balle wani aikin gida da dawainiyar shi kansa miji. "Bismillahi Alhaji Mamman." Ya tsinci muryar Aunti Zarah, a dadare ya zauna yana cewa. "Ina wuninku?" "Lafiya ƙalau, ina Amman yara?" "Lafiyarta ƙalau." Yace yana sake kallon Mami a karo na biyu dan har lokacin ta ƙi duban inda yake balle yasa ran zata gaishesa ko ta masa magana. 'Maganar da ya zo mata da su fa?' Ya tambayi kansa, ganin haka ma ta ƙi masa magana balle ya sako zancen da yake son mata tsawon lokaci. Yana jin za ta koreshi, kora na ƙare. Bai san me zai yi ba? Bai san ta yaya zai warware wannan abun ba? Bai san ko zata karɓi buƙatarshi ba? Yana son faranta ranta ta wannan hanyar da shi kaɗai zai saka ta gane cewa shi Mamman ya gane gaskiya. Ba Mamman da ta sani a baya bane. Wannan wani ne da yake da buƙata da burin ƙara haɗa rayuwa da ita. Jin shurun yayi yawa tsakanin mutane biyun ya saka Aunti Zarah miƙewa. "Bari in baku guri." Sai lokacin Mami ta juya ta kalleta, kafin tace wani abu Aunti Zarah ta ƙarasa inda take ƙasa ƙasa tace. "Ki ji mai zai faɗa miki Please Hajiya Sadiya." Girgiza kai tayi, kafin tace wani abu Aunti Zarah ta nufi ɗakin Mami. In har hasashen da ta hango zai zama gaskiya, ita kam bata san da me zata ƙira wannan abun ba. ... "Ina wuni?" Suka faɗawa juna a tare, sai Mami ta ji wani iri tayi shuru, hakan yasa Alhaji Mamman cewa. "Shikenan bari ni in amsa lafiya ƙalau. Ya labarin wajen Nuratu?" "Lafiya." Mami tace taba jin wani abin banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Jinjina kai yayi cikin ƙarfin hali ya kai dubanshi gareta. Tattare da ƙarfi da jarumta ya samu bakinsa da furta. "Sadiya aurenki nake son yi a karo na biyu in har kin amince? Kar kice a'a don Allah. Sannan in za kiyi duba da abin da ya faru a baya kice a'a, to ina jin kamar har yanzu ba ki yafe mini ba." *** "Ammi menene? Ammi tun jiya nake lura da rashin walwalarki. Ko dai har yanzu ciwon kai ne muje asibiti." Ammi dake zaune bakin gadonta ta kalli ɗanta matashin saurayi ɗan shekaru ashirin da takwas. Tun jiya yabi ya damu kanshi da rashin fara'arta, tace masa kanta yake ciwo amma yaƙi kwantar da hankalinsa. Zuwa safiyar yau ya tambayeta rashin walwalarta yafi goma. Murmushin dole tayi tana dubanshi. "Abdallah babu komai fa. Kawai dai?" "Kawai me Ammi? Dan Allah ki sanar dani wani abun in yana damunki?" Ya katseta da sauri. Yanda yayi da fuskarshi sai ya ƙara jefa zuciyar Ammi cikin kogin tunanin da ta kwana tana yi, domin fuskar sai ya koma mata na matashin saurayin da ta gani tare da Mami sak. Ta bishi da kallo zuciyarta na bugawa tamkar yau ta fara ganinsa. "Ammi!" Abdallah yaja sunan da hakan ya fargar da ita tunanin da ta faɗa. "Kace menene?" "Ki faɗamin damuwar ki don Allah. Ko dan kinga ni ƙaramine, sai Babban Yaya ko Yaya Sajeed." "A'a ba sai ka ƙirasu ba, na faɗa maka babu komai." "Ammi wani abun ya faru?" Ya tambayeta da sanyin jiki ganin cikin sanyi take masa maganar. Kai ta girgiza tana ƙoƙarin mai da hawayenta da ta rasa na menene tace. "Wani abu ne. Amma bansan ta ina zan fara ba, ban san ta ina ba Abdallah. Ka bani lokaci." Hannun mahaifiyarshi ya kamo ya damƙe. "InshaAllah Ammi za kiyi na nasara. Za muyi nasara. Kar ki damu, ina tare dake." "Ina fatan hakan." Tace tana sauƙe numfashi tare da murmushi. Sai lokacin taji sauƙin abin da take ji. Sallama ya mata ya fita dan zuwa aiki. A harabar gidansu ya shiga motarsa da yake wanke sai sheƙi yake. A hankali ya murɗa sitiyarin ana buɗe masa get ya fita. Yayi nisa cikin tafiyar ya jawo wayarsa yayi ƙira, ya kusa tsinkewa aka ɗauka. Bayan gaisuwa ya sanar da wanda ya ɗauka. "Ka ƙara bani lokaci." Banji na gefen me yace ba su kayi sallama ya ajiye wayar yana cigaba da tuƙi. *** Ba ta taɓa tsammani rainin hankali da rashin tunani na Alhaji Mamman ya kai haka ba, sai yanzu da ya furta mata kalmomin rainin hankali, kallonshi tayi duk da ya kasƙantar da kai ya zama wani abun tausayi hakan ba zai sa yayi nasara akanta ba. Ɗauke kanta ta yi ganin idanuwansu sun haɗu yana aika mata saƙonnin hakuri da yarda da buƙatarshi. "Kar kice a'a Sadiya dan Allah na haɗa ki dashi. Wallahi wannan ba Mamman da kika sani bane. Wani ne wanda yayi sabon tuba yake muraɗi da burin auren Sadiya, in har ta amince. Dan Allah Sadiya wannan shine rufin asirin mu." Girgiza kai tayi duk maganganunsa ba suyi tasiri akanta ba. "Da baka san auren shine rufin asiri na ba sai yanzu? Da da ka rabu da ni kasan bani da uwa da uba, babu inda zanje, baka san auren shine rufin asirina ba. Kai ko kunya baka ji? Ko kuma kana ganin idan ni na yarda da buƙatarka na kyautata Nuratu? Ba zan iya ba, ba zan koma aurenka ba, na riga na gama magana zaka iya tafiya." Bai ji haushin kalamanta ta ba domin shi ɗin ya san mai laifi ne gurinta, da ƙyar ta yarda da buƙatarshi cikin lokaci ɗaya ba. Zama ya gyara yana dubanta, ranta a haɗe cikin fushinta da yake burgeshi. "Sadiya ko dai dan kinga bani da arziƙi yanzu ne? Ko kuma har yanzu ba ki yafe mini bane?" Wani kallo ta jefeshi da shi. "Da da arziƙin na aure ka?" "To yanzu ma bani da shi sai mu koma rayuwarmu na baya. Dama ance wani arziƙin masifa ne, kuma na yarda. Sannan nima bana cire haƙƙin ciki, shi yasa Allah ya jarabceni da hakan. Sannan aboki wanda ba nagari ba shi ya sani wannan hanyar, bai nuna mini hakan ƙaddara bane da rashin cire haƙƙin ciki ba ya sani aikita dana sani. Dan Allah ki yafe mini mu koma rayuwarmu kamar baya." A fusace tace. "Nace maka bazan iya ba ko. To na gama magana. In auren kake son ƙari ka tafi ga can mata a titi." Daga haka ta miƙe za ta wuce ɗaki taji yace. "Ni ke nake so. Kuma inshaAllah sai mun mai da auren mu Halima." Juyawa tayi ta watsa mishi wani kallo tana jan tsaki kafin ta wuce ta barshi zaune. Ya jima kafin ya miƙe ya fice. Dama ya san da wuya ta amince dan abubuwan da ya mata, sai dai hakan ba zai sa ya hakura ba fa sai ya sake mallakarta a karo na biyu domin cikar burinshi. ... Gida ya nufa kai tsaye, a harabar gidan ya ciro wayarshi ya ƙira Aunti Rahma. Bayan amsa sallamarta ya bata umarni. "Rahma ran Juma'a ina son ganinki da ƙannenki, ki sanar da su hakan, ku zo gida." Daga haka ya kashe wayar ya jefa a aljihunsa yana shiga falon. Amma Jidda cikin fara'a ta tareshi kamar kullum duk da yana ɗan ƙoƙarin ganin ya danne abin da yayanta ya sashi aikatawa, domin laifinsa ba zai shafeta ba kuma halinsu ya bambanta. Ruwa ta kaeo masa tana masa sannu da hanya. "Ina Ameera?" Shine tambayar da ya mata jin shurunta yayi yawa ga yamma ya gabato. "Tana ɗaki." "Ƙiramin ita." Yace dan ya tabbatar, ya fara lura da yawan fitarta ko bata da lecture. Babu musu ta miƙe ta leka ɗakin ta dawo. "Wallahi yanzu na barta nace bari in gama ayyukana." "Ƙirata a waya." Babu musu ta ƙirata. Kiɗane yake tashi inda take basa jin maganar da ake, hakan yasa ta kashe ta tura mata saƙon ta dawo gida yanzu. *"Tana cikin maye, ku zo ku ɗauketa a Gat hotel."* Shine amsar da aka turo musu kenan da ya saka Amma Jidda buga ihu iya ƙarfinta. ... Aci gaba da comments, ku sha karatu. #Vote #comment #share MADUBIN GOBE  53. Pharty Bb. Wattpad phartybb. ... Zuciyarta zafi yake, ta kasa magana, ta kasa aiwatar da komai, ta kasa kwakkwaran tunani dangane da abin da ya wuce cikin ƙanƙanin lokaci. Aunti Zarah da ta ji komai ita ma ta kasa magana sai bin Hajiya Sadiya take da kallo, yanayin fuskarta kaɗai zai nuna maka tsantsar ɓacin ranta. A hankali ta bar gurin zamanta ta zauna kusa da ita ganin shurun ya yi yawa. "Hajiya Sadiya." Ta ƙirata a hankali cikin nutsuwa. Sai lokacin ta kalleta ta kasa amsawa. Hakan yasa Aunti Zarah ci gaba da maganarta. "Na ji komai. Naji bayanin Abbansu Rahma." "Kina ji ko. Kinji komai ko? Ko kunya baya ji fisabilillahi. Wani irin mutum ne Mamman, wani irin mutum na haɗa jinin ƴarana da na shi." Mami tace cikin ɓacin rai sai lokacin ta samu bakin magana. Da sauri Aunti Zarah ta rufe mata baki. "Har yanzu uban yaranki ne, basu da wani uban sama dashi hatta ita Nuratun. Abin da ya yi yai tsaurin ido. Idan wani ne ko dan abin da ya aikata bai kamata ya dawo da niyar sake aurenki ba. Amma ba komai ki yi ta addu'a Allah shige miki gaba." "Ba zan iya ba Aunti Zarah. Ba zan iya ba ko dan Nuratu. Kar ya ƙara shigomin gida, babu shi babu ni, yara ne suka haɗamu gasu can da shi dama ban raba su ba." Ita dai Aunti Zarah shiru tayi domin abin ma ta rasa me zata ce akai. Wani gefe na zuciyarta yana son ganin Mami tayi aure tun ba yau ba, wani kuma yana ganin rashin dacewar ta komawa Alhaji Mamman. Miƙewa tayi dan bawa Mami damar yin tunani tace. "Zan tafi Hajiya Sadiya, fatan Suwaiba ta miki." "Nagode ta minin sosai tamkar Munirat." "To yayi kyau. Iyayenta nan PomPomari su ke, in kin shirya sai muje ku gaisa su ganki." "InshaAllah na gode sosai. Ki gaisheta da yaranmu." Daga haka Aunti Zarah ta fita ta bar Mami tsamotsamo cikin kogin tunanin lamarin Alhaji Mamman Bashir. *** Washegarin. Maiduguri. "Ka tashi kar ka makara fa.* Nuratu tace tana kama dogon hancin Dr Awwab dake kwance yana barci wajajen karfe taran safe. Tun kafin ya kwanta ya sanarta gobe zai fara fita aiki, hakan ya saka da ta yi sallah duk yadda yaso ta koma barci ƙi tayi. Da yaga haka ya ja ta jikinshi ya dameta da fitinarsa, dole ta hakura bayan komai ya lafa suka koma bacci. Wajen takwas ta farka, a gaggauce ta yi wanka ta sauƙa ta haɗa masa breakfast ta hayo dubawa ko ya farka. Abun mamaki barci ta samu yana yi shine ta hau tashinsa, yana jinta yaƙi magana. Hancinsa ta ƙara ja ya riƙo hannayenta ya jata ta kwanto saman jikinshi, hakan yasa fuskarsu ta zo daf, tana sauƙe masa numfashinta, yana shaƙa yana fitar da na shi tana shaƙa. Har lokacin idanuwansa rufe yana riƙe da ita. "Ke fa ki ka hanani barci da asuba, kuma yanzuma ki hanani." "Na hana kuma? Ka hanamu dai." Tace tana tura baki gaba. Sai lokacin ya buɗe idanuwansa ya saka cikin nata. Dakyar ta yi ƙoƙarin bata janye nata ba, dan so take ta fara jure kallonsa, tunda dai zama ya haɗa kuma babu abin rabawa sai ikon Allah. Tana son yanayin da take shiga in ƙwayar idanuwansu suka haɗu. Ta rasa menene amma tana ji tun daga ƙwaƙwalwar kanta har yatsun ƙafarta cikin wani shauƙi. Wani kallone me tattare da bata san me za ta faɗa ba, ko sai nan gaba in ta fahimta. Sauƙar iskar bakinsa me ƙamshi ya fargar da ita daga kallonsa, ta lumshe idanuwanta ta buɗe akansa. Ƙara matseta yayi jikinsa ganin kallon da take masa. "Muje ki mini wankar, duk kin gajiyar ni wallahi." Fahimtar inda zancensa ya nufa tace. "Sharri zaka mini Doctor, kai fa ka hanani runtsawa." Hannunsa dake bayanta ya kai kan kugunta ya damƙe, wani ƙaramin ƙara ta sake tana kallonsa. Dan ba ƙarar zafi ta ji ba, sai na yanayin da ya tsarga mata a jinin jikinta. "Ni nace ayi, ke kuma kina so amma kin cika ragwanta. Ina son mayarki jaruma, ko yaushe na zo za ki amsheni, sannan ba za ki nuna min gajiya ko ragwanci ba." Shurunta ya sashi sake murza hips ɗinta, ta buɗe idanunta da suke lumshe da sauri. "Please My Baby." Murya can ciki tace. "Ni dai.... Na ji zanyi ƙoƙari." Bayanta yaci gaba da shafawa yana sama da hannunsa, jin yana neman fara wuce gona da iri ya saka Nuratu miƙewa. "Za ka yi latti. And you're not clean." Daga haka ta fita da sauri a ɗakin. Da kallo ya bita yana mamakin baki da ta fara yi, and yaji daɗin haka yadda ta fara sakewa da shi, hakan shi zai ba shi damar nuna mata so da kulawan da ya ke son nuna mata. Wanka yayi ya shirya cikin coat sai ƙamshi ya ke ya fita ya nufi falonta. Bata ciki sai ƙamshin turaren wuta yake. Falon ƙasa ya sauka  ya samu tana sharewa ya ƙarasa dinning. Tana ganin haka ta ajiye moppern hannunta, ta ƙarasa ta zuba masa plantain da dankali da ta soya masa, sai coffe ganin yafi so akan tea. Duk abin da take Dr Awwab kawai kallonta yake yana murmushi. Tea ta haɗa nata ta zauna ta dubeshi. "Bismillahi." "Thank you My Baby." Yace ya fara ci, ya ci sosai ya sha coffee, har lokacin bata gama ba ya miƙe ganin me ƙiransa a waya, abokin aikinsa. "Na tafi Babyna, sai zuwa uku in Allah ya yarda." "A dawo lafiya." Tace tana ƙoƙarin miƙewa dan masa rakiya. Murmushi yayi ya matsa kusa da ita, sauƙar lips ɗinsa taji a goshinta ya sakar mata kiss. "Nagode da rakiya, koma kiyi breakfast ɗinki." Daga haka ya fice ta koma ta zauna ta ƙarasa abinta, kafin ta miƙe ta hau aikin gidan sai wajen sha ɗaya ta gama gyara ɗakinta, falonta, ɗakinsa, falonsa da falon ƙasa, ruwa ta watsa ta zube cikin kujerun falonta dan ta gaji. Bacci tayi har ƙarfe biyu ta farka ta gabatar da sallah, kafin ta fara ƙoƙarin ɗaura musu abincin rana. *** Ƙarfe biyu ya dawo gidan, da safen ba su samu yin maganar ba ya wuce aiki cikin gaggawa. Da sallamarshi ya shiga cikin falon idanuwansa sai kan abar sonshi, murmushinsa ya faɗaɗa ya shiga cikin falon. Tun da taji sallamarshi ta daburburce zuciyarta ya fara bugawa, bata tsammaci ganinsa yanzu ba, dan duk so take suyi sauri su koma kafin yamma lokacin dawowarsa, sai akayi rashin sa'a. Guri ya samu ya zauna kujeran da yake facing Hassana. "Zo yarinyata." Ya ce da Hanan da take jikin Hussaina, sanin wanene shi ya sata barinta ta nufi gurinshi ya ɗagata saman jikinshi. "Ina Daddynki?" "Yana lafiya?" "To ya school?" "Lafiya lau." "Ina wuni." Ƴan biyun suka haɗa baki wajen gaishesa, ya ɗago yana kallon Hussaina ya amsa kafin ya maida kallonsa kan Hassana, kanta yana ƙasa ta kasa nutsuwa. Murmushi yayi. "Ƴan matana." Yace yana son ta ɗago idanuwanta ya kalli fuskarta ta hanasa hakan. "Bari in baku guri." Hussaina tace tana kama hannun Hanan suka hau sama wajen Ammi. Ganin haka ya saka Abdallah tashi ya zauna kusa da Hassana. "Ni kam dai wannan kunyar yana cutana. Tun da nace ina sonki shikenan kika canza min, wani kunya kunya ya fara shiga tsakaninmu. Please ni bana so don Allah. A haka za muyi auren." Ita dai Hassana ta kasa ko tari domin numfashinta ma da ƙyar take shaƙa, ƙamshin turarensa duk ya cikata. Tsoronta kar wani ya shigo ko Ammi ta sauko, hakan yasa ta miƙe tsaye. "Ina za ki je bamu ko gaisa ba." Abdallah yace yana shan gabanta. Kamar za tayi kuka ta ɗaga kanta suka haɗa ido tace. "Dan Allah kayi hakuri Yaya Abdallah." "Wuce to, amma ku jira zan maidaku gida in gaishe da Ummi." Daga haka ya bata guri ta wuce saman da saurinta ya bi bayanta. Tun shekaru biyu da ya dawo daga karatu a UK ya faɗa sonta. Dama ya sansu amma sunfi sabawa da ita dan tafi Hussaina nutsuwa, surutun Hussaina da tsokana yasa basa shiri. Duk ƙoƙarinshi ya danne hakan a ranshi kasawa yayi, sai da ya sanar da ita watanni biyu da suka wuce. Tun lokacin wani mugun kunyarshi Hassana take ji. Ta kasa bashi amsar tana sonshi, domin ba za tayi ƙarya ta cuci kanta ba tana sonshi, amma mugun kunyarshi take ji bata iya sakewa su gaisa balle hira. Shi kuwa Abdallah bai fasa koya mata sonshi ba, kuma bai faɗa a gida ba har sai sun gama daidaita kansu. Hussaina kaɗai ta san tsakaninsu, Hassana ce ta sanar da ita sannan ta roki ta ɓoyewa Ummi. Samu yayi suna ma Ammi sallama za su tafi. Ammi dake zauna ta dubi Abdallah. "Ko za ka sauƙe su a gidan indan baka gaji ba." "Babu komai muje." Yace yana ɗaukar Hanan suka fita. A cikin motarshi suka sameshi ya saka Hanan a baya, Hussaina tayi saurin shiga itama bayan, Hassana kamar tayi kuka ta shiga gidan gaba. Tafe babu wanda yayi magana sai surutun Hanan da Hussaina. "Ya school ya kusa ƙarewa?" Hassana taji tambayar Abdallah. Kai ta ɗaga kamar me ciwon baki tace. "Eh saura shekara ɗaya." "Allah ya kaimu." Ameen ta amsa da shi, a haka suka isa gida ya gaishe da Ummi tare da Dr Awwab da ya iso gidan bayan barinshi aiki, kafin Abdallah ya musu sallama ya koma. Da gudu Hanan tayi gurin Dr Awwab ta maƙalƙaleshi tana tsalle dan duk yau kwana biyun bai zo ba. "Daddy don Allah ka tafi dani." Faɗin Hanan kamar tayi kuka. Kanta ya shafa kafin yace wani abu Ummi tace. "Ka taimaka mata ko sati ɗaya ta bika tayi." "Ummi driver nake nema mata da zai dinga kaita school da islamiyya daga can, shi yasa ki kaga shuru banyi maganar ɗaukarta ba. Nima ina son ganinta kusa da ni." "To hakan ma yayi Allah taimaka." Ameen yace ya miƙe. "Zan wuce Ummi sai gobe." "To ka gaishe da gida da Noor." "Za taji." Yace ya ajiye Hanan dake hawaye. Ya nufi hanyar fita. "Daddy." Tace tana binshi a baya tana kuka. Hakan ya saka ya dakata ta iso wajenshi ta rumgumeshi. Sai yaji tausayinta ya ɗauketa. "Hussaina haɗamin kayanta ko kala biyu ne, zuwa gobe ku gama haɗa sauran zan zo ɗauka." Tashi Hussaina tayi ta wuce ɗakinsu ta ɗauki kayan Hanan a ƙaramin jaka kusan kala biyar da kayan makarantarta da jaka dana islamiyya da takalma kala biyu ta fito. Karɓa yayi da d'ayan hannunshi ya sauƙe Hanan. "Je kima Ummi sallama." Da gudu ta isa gurin Ummi da taji bata son tafiyarta kuma, dan ta saba da ita sosai. Rumgumeta tayi ta bata sumba a kumatunta. "Ummi zan tafi." "Allah bada sa'ar karatu, kiyi ta ƙoƙari kinji Nusaiba." "To Ummi." Tace ta rumgume Hassana da Hussaina duk basa son tafiyarta, kafin ta isa gurin Dr Awwab ta riƙo hannunsa suka fita. Murna fal ran Hanan sai surutu take zuba masa. A haka suka isa gidan me gadi ya buɗe masa get ya shiga ya faka motar suka sauƙa, suka nufi cikin gidan. Da gudu ta shiga falon tana kwalawa Nuratu ƙira. Shigowar Dr Awwab ya hanata yace. "Ke! Ki nutsu. Tana falon sama." Da sauri ta haye tana nufan falon Nuratu da take ta sharan bacci bayan gama aikinta. Bin bayanta Dr Awwab yayi ya samu ta dakata tana turɓune fuska. "What?" "Tana bacci." "Ok then muje in nuna miki ɗakinki." Ɗaya ƙofar dake cikin falon Nuratu suka shiga ciki. Ya zuba mata komai na yaro ɗan shekaru biyar, duk da ba ta ciki, ba zama take ba. Wardrobe nata ya buɗe ya sa ka mata kayanta da duk abin cikin akwatin, kafin ya juyo ya ganta saman gadon tayi ɗaiɗaya. Kallonsa tayi kamar za tayi kuka. "Ni kaɗai za ina kwana? Ba tare da Aunti Noor ba ko kai." "Za ki iya, zamu na tayaki kwana kinji My Love." Murmushi tayi ta miƙe ta rumgumeshi. "I love You Daddy." "I love you too My Love." Yace ya rumgumeta shima, kafin ya saketa ya kunna mata ƙaramin Tv dake ɗakin ya kai mata cartoon. "Kiyi kallo bari in tashi Aunti Noor." Kai ta ɗaga mishi ya fita. Bacci take sosai, ya tsungunna kan kafafunsa ya zuba mata ido. 'Noor akwai kyau, baƙace amma baƙinta glowing yake, kyakkyawace sosai da ake ƙira da black beauty. Sai ka nutsu zaka hango kyawunta.' Haka ya faɗa a cikin ranshi kafin murmushi ya suɓuce masa, ɗaura hannunsa yayi saman cikinta yana tura hannun cikin rigarta. Cikin bacci taji abu yana yawo a jikinta, ta buɗe idanunta suka sauƙa saman na Dr Awwab. "Sleeping beauty." Murmushi tayi ta lumshe idanuwanta ta buɗe, har lokacin hannunsa na cikin rigarta yana taɓe taɓensa. "Yaushe ka dawo?" "Ban jima ba Babyna. Na zo kina barci, ko dai me barci na samu." Yace yana zare hannunsa ya miƙewa ya mikar da ita, bai bata damar yin wani magana ba, ya riƙeta suka nufi ɗakinsa. Wanka yayi ta ciro masa kaya ya fito ya shirya suka fito. Sun fara sauƙa a stairs yace. "Tare muke da Hanan tana ɗakinta." "Dan Allah. Kuma shine baka sanar mini ba tun ɗazu." Bai mata magana ba ta zare hannunta cikin nashi ta koma. Ɗakin Hanan ta buɗe tana shiga. Hanan da sauri ta diro a gadon ta isa gurin Nuratu ta ɗagata sama suna dariya. Sun jima haka kafin ta riƙeta. "Aunti mun zo kina bacci." "I'm sorry ban sani ba, yanzu na farka. Muje kici abinci My Baby." Daga haka suka fita tana ɗauke da ita ko nauyinta bata ji. Ido Dr Awwab ya saka musu har suka ƙaraso saman dinning ta zaunar da Hanan. Abinci ta zubawa Dr Awwab ta zuba nata da Hanan. Wani kallo ya watsa mata. "Yau kaɗai Doctor please." Nuratu tace tana marairaice masa. Kai ya girgiza ya ɗauki nashi ya juye cikin plate ɗinsu. "Mu ci tare dukka." Ya faɗa ya fara ci, Hanan kam ta saba cin abinci dashi hakan yasa ta saka nata spoon ɗin ta fara. Ganin haka ya saka Nuratu fara ci a hankali. Bayan sun gama ta tattare gurin duk inda ta shiga Hanan tana binta. Hakan ya yiwa Dr Awwab daɗi ganin ta ɗauketa matsayin uwa, saɓanin wasu da suke ɗaukar matar uba maƙiyiya. Ko dan ita bata san nata mahaifiyar ba. Daren hana Nuratu girki yayi ya sasu suka shirya suka fita, wajen shan ice cream ya kai su da kayan ciye ciye, suka ci suka sayo wasu wajen karfe goma. A fridge ɗin falo suka ajiye. Ɗakin Hanan ya kaita ya kwantarta ya lulluɓa mata bargo tare da tofeta da addu'a. Yana shirin fita Nuratu ta shigo da shirin kwanciya. Kallonta yayi ya kamo hannunta suka fita ta ƙofar falonta, bayan ya kashe mata wuta. "Ita ɗaya zamu bari. Ba za taji tsoro ba." "Za ta saba kafin siblings ɗinta su zo." Yace yana kashe mata ido ɗaya ta ɗauke kanta. "Ni dai da ka barni na tayata kwana, ko kuma ta zo mu kwana a ɗakina." "Ni kuma fa kiyi ya dani?" Kallonshi tayi ya ɗaga mata gira ɗaya ta girgiza kai tana wucewa ɗaki, bayanta yabi yana murmushi ya hangota gaban mirror. Bakin gadon ya zauna. "So kike ki zautar ni ko, kina ta zuba turare." Bata kulasa ba taci gaba da shafe shafenta ta gama ta kashe wutan ta isa bakin gadon ta zauna. Addu'a tayi ta shafa. "Ni fa ki shafa mini." Wani tayi ta shafa masa a fuska, tana ƙoƙarin ɗauke hannunta ya cafke dan ƙamshin turaren jiki ya shigesa. Daga kan hannun ya fara sumbata har zuwa wuyanta, dan ƙamshin ya ƙara rikitashi. Daga nan komai ya canza suka mance da kowa da komai. Bai iya barinta ta yi bacci ba sai da suka tsarkake jikinsu. Da asubanin bayan ta idar da sallah ta gaishesa ya amsa yaci gaba da azkhar ɗinsa kafin ya kwanta wajen ƙarfe shida. Nuratu tana jin yayi bacci ta lallaɓa ta fita. Breakfast ta haɗa masa da Hanan ta ajiye saman dinning table, ta sakawa Hanan a lunch box nata, kafin ta wuce ɗakin Hanan ta cikin falonta ta shiga tasheta. Wanka ta mata ta ciro kayan makarantarta da yake goge ta saka mata, ta shafa mata mai da turare suka fito falonta. "Ki zauna bari in taso Daddy." Kai ta ɗaga mata ta wuce ɗaki. Samu tayi ya farka. "Ina kika je?" "Ni kayi wanka ka shirya, za kayi latti." Agogo ya kalla bakwai da wani abu ya koma ya kwanta. "Da sauran lokaci." "To wa zai kai Hanan makaranta." Sai lokacin ya tuna ya miƙe zaune. "Ta farka." "Tun yaushe, kai muke jira muyi breakfast." "Ɗauko min kaya to." Yace ya miƙe tsaye yana wucewa bathroom. Fita Nuratu tayi ta wuce ɗakinsa, kamar yadda taga jiya ya saka coat haka ta ɗauko masa wani launi ta feshe da turare, hatta boxer da singlet sai da ta fesawa turare ta kai masa. Ta samu ya fito daga shi sai tawul, ta ajiye saman gado tana fita da sauri domin har yanzu tana jin kunyarsa. Sai da ya gama shirinsa tsaf ya fito ya samesu a falon ƙasa suna jiransa. "Good morning Daddy." "Good morning My Love." Yace yana sunkuyawa ya sumbaci kumatunta. Dinning su kayi Nuratu ta zuba musu breakfast a babban plate ta haɗa masa coffee ta haɗa musu tea kafin su fara. Cikin 20mins suka gama ta goya Hanan jakanta ta riƙe mata lunch box ɗinta. Har bakin mota ta rakasu ta saka Hanan ta rufe mata, kafin ta zagaya gurin Dr Awwab. "Sai ka dawo Allah ya kiyaye." "Ameen My Baby." Yace kafin ta ankara ya sakar mata kiss a kumatunta. Da sauri tayi baya tana harararsa. Ya gane nufinta, yayi murmushi ya shiga motar suka bar gurin, kafin ta koma ciki. Aikinta tayi kamar ko yaushe tayi wanka ta zauna hutawa wajen sha ɗayan safe. *** DAMATURU. "Ta farka." Faɗin Amma Jidda da take tsaye saman kan Ameera ta fara motsi, bacci take tun daren shekaran jiya har yau da safe. Da sauri Alhaji Mamman ya fita ƙiran likita. ... #vote #comments #share MADUBIN GOBE  54. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Awanni saba'in da huɗu kafin faruwar haka. Da ƙyar Amma Jidda ta sanar da Alhaji Mamman abun da ya ke rubuce a saƙon da aka turomata. Wani jirine ya kwashesa kafin ya daidaita nutsuwarsa sannan ya miƙe. "Bari in je wajen." "Muje tare don Allah." Amma Jidda tace, hawaye take zubarwa mai zafi. Kai kawai ya ɗaga mata ya fita. Da sauri ta ɗauki mayafinta ita ma ta fita, samunsa ta yi har ya kunna motar. Tana shiga a guje ya fita. A harabar Hotel ɗin ya yi parking ya dubi Amma Jidda da ke kuka. "Bari in shiga in fito da ita." Kai kawai ta ɗaga masa ya fita ya wuce ciki. Kiɗane ya ke tashi a gurin, ƴan mata da samari sun cika gurin sai rawa suke yi. Wasu kuma a zaune suna shan drinks da ya ke cike da kayan maye, da alama birthday party ake yi, domin duk an cika gurin da kayan kwalliya da balloons, kuma kowanne ƙananan kayane a jikinsa. Da ƙyar ya iya jan ƙafarsa ya ƙarasa ciki yana raba idon inda zai hango ɗiyarsa. Ganinsa fa hankalin mutane ya fara yin kansa. Wasun ma zaton ko mahaifin uwar gayyarce. "Kai old me ye haka? Me ka ke yi anan?" Faɗin wani saurayi da yake gefen Alhaji Mamman shigowarsa kenan. Kallon saurayin ya yi da ƙyar ya furta. "Ameera nake nema. Zainab Mamman Bashir." "Oh kai ne Daddynta. Ga ta can." Idanuwansa ya kai gurin inda yayi arba da mummunan gani, ƴarsa ce tsakiyar maza tana tikar rawa, tare da wani namiji da ya ke tayata sai shafa jikinta ya ke. Jirine ya kwashesa kafin ya kai ƙasa ya dafe kujerar gurin, kusan mintuna biyu ya samu ya dawo daidai yana nufar gurin, yana isa cikin zafin nama ya fizgota tare da kwasheta da mari tagwaye. Duk da cikin maye take ta ji marin ya shigeta sosai, ta ɗago kanta da idanuwanta da suka canza launi. "Abba!" Ta faɗa da karfi cike da mamaki da tsoro. Bai iya bata amsa ba sai wani marin da ya kai mata kafin ya hau dukanta tamkar an aikosa. Duk ihu da ake ya rabu da ita kasawa yayi har sai da samarin gurin suka rirriƙesa, tuni Ameera ta sume don ta bugu. Ko ta kanta bai bi ba ya fizge jikinsa ya fita. Cikin sauri samarin suka ɗagota suka fita da ita. Gaba ɗaya sun fahimci mahaifintane Amma Jidda da ta ga fitowarsa ta fito da sauri. "Tana ina?" "Tana ciki." Ya faɗa yana shiga motarsa. Za ta yi magana ta ga an fito da ita, da sauri ta ƙarasa gurinsu. "Me ya sameta?" "Ku sakata a baya." Alhaji Mamman yace daga cikin motar, bai bari sun bawa Amma Jidda amsa ba, babu musu suka sakata suna matsawa. Da sauri Amma Jidda ta shiga ya kunna motar sai asibiti. "Dan Allah Abbansu Rahma ka sanar dani me ya sameta." Amma Jidda tace cike da tashin hankali, fatanta ya sanar da ita ba abin da ta ke zargi bane. "Bani da lokacin wannan maganar Jidda." Yace daidai sun isa asibitin. Karɓanta aka yi sai emergency, suka tambaya me ya sameta. "A buge take, tasha wani abu." Alhaji Mamman ya faɗa. Likitane ya dubata ya mata alluran barci da kuma karya garkuwar abin da tasha. Tun lokacin barci take sai yau da ta farka. ... Shigowar likita Amma Jidda ta fita ta basa guri. Duba Ameera yayi yace. "Akwai inda ya ke miki ciwo?" Murya can ƙasa tace. "Kai na da jikina." "How old are you?" "19 years." Ta basa amsa tana dafe kanta da ya ke ciwo sosai. Kan ya riƙe mata ya ji bugawarsa kafin ya sa ke. "Me ya kai ki aikata haka? Ba ƙya tsoron lafiyarki ko iyayenki su shiga wani hali. Da ƙarancin shekarunki." Bata masa magana ba ta lumshe idanuwanta, ya girgiza kai ya fita. Burinta kawai Abba da Amma suyi ƙoƙarin fahimtarta, bata da wani kalma da za ta faɗa ta ƙare kanta. Duk hukuncin da suka yanke mata za ta ɗauka. Buɗe ƙofar ya sa ta kai kallonta ƙofa. Amma ne ta shigo ranta a haɗe, fuskarta a kumbure alamar tayi kuka. "Amma zan rama sallolina." Ta faɗa kamar me tsoro, dama a tsorace take. Bata kulata ba ta fara harhaɗa kayansu. Bayan ta gama ta nufi ƙofar fita. "Fito mu tafi gida." Idanuwanta cike taf da hawaye ta sauƙo daga gadon da ƙyar, hijabinta da ta gani a gefe da bata san yaushe ya zo ba, ta ɗauka ta saka ta fita. Da ƙyar ta ke jan jikinta, dan ciwon da ya ke mata ga ciwon kai. A taxi suka koma gida dan tuni Alhaji Mamman ya bar asibitin tun farkawarta. Suna isa gidan ta shige ɗakinta, ruwa mai zafi ta haɗa tayi wanka ta ɗauro alwala kafin ta fito ta gabatar da sallolinta ta zauna a ɗaki. Yunwa ta ke ji ga ciwon kai amma haka ta zauna ta hau kuka. Buɗe kofar ɗakinta ya sata share hawayenta ta kalli ƙofar. "Ki fito kici abinci ki sha magani." To tace cikin sanyi ta tashi ta fita, babu kowa falon, ta isa dinning ta zuba abinci ta ci, ta ɗauki maganin da ta gani saman table ta sha ta wuce ɗakinta. Har dare babu wanda ya bi ta kanta, sai ta ƙara jin tsanar kanta. Haka ta zauna har daren. Ƙarfe takwas aka buɗe ƙofar ta kai kallonta gurin. Abbansu ta gani tsaye bakin ƙofar. A zabure ta miƙe zaune cikin rawar jiki. Shigowa yayi ya rufe ƙofar ɗakin da key, ta ke ta ji zuciyarta ya buga, idanunta ya cika da hawaye. Takowa yayi ya tsaya saman kanta. "Abba don Allah kayi hakuri." Ta samu bakinta da furta haka cikin rawar murya. "Rufemin baki." Yace yana kaiwa bakinta bugu, da ƙarfi ta fasa ihu dan zafi. Dukan fitar hankali Abba ya yi wa Ameera da bulalar iccen maina, tana ihu tana kuka tare da ƙiran sunan Amma bai ƙyaleta ba. Amma tana ji ta kasa zuwa kwatarta, domin tasan ita ta jawowa kanta. Sai da ya ga ta daina motsi kafin ya haureta da ƙafa. "Ki faɗamin uban me ya kai ki hotel." Da ƙyar muryarta ya ke fita tace. "Abba ƙawatace ta gayyace ni birthday party. Wallahi ban taɓa zuwa hotel ba, ban taɓa shan wani abun ba, ban san sun saka abin maye ba nasha." "To babu ke babu fita, makarantar ma na kashe zuwansa, aure zan miki nan da wata biyu." Ba ta ce komai ba sai kuka da take yi cike da nadama. Fita yayi ya barta warwas. Side ɗinsa ya nufa ya kulle kansa a daki. 'Hotel kaɗai taje ita ta kai kanta amma na shiga tashin hankali. Nuratu fa da aka yiwa fyaɗe ba tare da son ranta ba. Ya Sadiya ta ji? Wani irin tashin hankali ta shiga? Wani irin rayuwa ta yi? Ita Nuratun fa." Maganganun da Alhaji Mamman ya ke faɗa a zuciyarsa cike da nadaman abin da ya aikatawa Sadiya da Nuratu. Wani mugun tausayin ƴarsan ya lulluɓesa. Bai iya runtsawa ba har karfe biyun dare, kafin wani barci ya ɗaukesa. Ƙarfe shidan safe ya bar gidan dan tafiya da zai yi cikin gaggawa. Ko takan Amma Jidda bai yi ba, dan ita ma da laifinta a fitar yarinyar. *** Da gudu Nuratu ta ƙwace bakinta a gurin Awwab ganin Hanan ta nufo wajen. Yana ƙoƙarin magana ta wuce kitchen da sauri ta shiga tana dariya dan nan tafi kusa da shi. Har zai bi ya kamota ta masa bayanin hakan ya ji muryar Hanan. Turus yayi ya tsaya yana mata wani kallo. Tsorone ya kamata ta fara matse hawayen. "Zo nan." Yace da ita yana harararta. Haɗiye kukanta tayi ta isa wajen tana ƙoƙarin durƙusawa ya riƙota. Kuka ta saka masa. "Yimin shuru." Yace da ita yana zaunarta saman kujeran dinning ɗin. Jin kukan Hanan ya saka Nuratu fitowa da sauri. Dariyarta ta kunshe ganin itama ta samu tsarabar harara. Zama ta yi ta ɗaura Hanan saman cinyarta. "Yi shuru My Love." Tace tana sharewa mata hawayenta. "Za ki ci abinci?" Kai ɗaga mata, haka yasata sauƙarta ta miƙe ta zuba mata ta koma ta zauna. A baki ta dinga bata har ta ƙoshi suka koma falon suka bar Awwab zaune ya cika yayi fam. Hira suke yi suna kallo abunsu. Hanan tana yin barci ƙarfe goma ta ɗauketa suka wuce ɗakin Nuratu. Kwantarta tayi ita ma ta yi shirin bacci ta hau gadon. Miƙewa tayi dan ɗauko ruwa dan kar ko Hanan za ta nema cikin dare. Cikin tafiyarta mai ɗaukan hankali ta sauƙo. Har lokacin yana zaune a saman dinning, sai lokacin ya samu damar cin abinci shima tea ya haɗa. Yana sha yana aiki a laptop ɗinsa. Jin motsi ya sa shi kai duba wajen ya ga Nuratu ne. Kai tsaye dinning ta nufa, gorar ruwan da ba'a buɗe ba ta ɗauka bata masa magana ba. Za ta bar gurin taji maganarsa. "Za kiyi bayani yarinya. Ki jira zuwana." Da murmushinta ta juya ta masa wani kallo tana juya idanuwanta. "Za mu yi bayani tare ni da kai." Daga haka ta ci gaba da tafiya tana danne dariyarta dan tuna muguntar da ta shirya masa. Galala Dr Awwab ya bita da kallo cike da mamakinta. Wani yanayi ya ke jin kansa, da ƙyar ya ci gaba da aikinsa. Shuru shuru ba su dawo ba ya saka Dr Awwab kashe Tv da wutan falon ya hau sama. Ɗakinsa ya wuce ya yi shirin barci ya nufi ɗakin Nuratu. Turus yayi ya tsaya ganinsu su biyun kwance suna barci. Ƙaramin tsaki yaja ya isa bakin gadon ya janye Hanan gefe, Nuratu tana jin shi tayi luf kamar me bacci. Hannunshi ta ji a jikinta ya gyara mata kwanciya ya maidata tsakiyar gadon kafin ya hau gefenta ya kwanta. "Na san idonki biyu Babyna. Me yasa ki ka min haka bayan ga ɗakinta can." Murmushi Nuratu tayi tana gyara kwanciyarta jikinshi ta ƙi magana. Hakan yasa yayi ƙasa da murya a kunnenta ya raɗa mata. "Mu je ɗakina please. Ina son muyi bayani ni da ke, kamar yadda ki ka ce." Nan ma shuru tayi ya fara ƙoƙarin tashi ta riƙesa. "Am not clean." Komawa yayi ya kwanta ya ce. "What! When kuma hakan ya faru." "Ɗazu da yamma." "Dama lokacinshi ya yi? Kuma ki ka sakamin rai." Kai ta ɗaga mishi, ajiyar zuciya ya sauƙe yana ƙara ƙarfin rumgumeta kamar ba zai ce komai ba can yace. "Kwana nawa ya ke yi?" "Kwana biyar." Daga nan bai ƙara magana ya karanto addu'a har barci ya ɗaukesu. Da asuban bai tasheta sallah ba ya wuce masallaci. Da ya dawo ya koma ya kwanta. Ƙarfe shida Nuratu ta farka ta haɗa musu breakfast kafin ta tashi Hanan ta mata wanka ta shiryata, ƙarfe takwas saura suka bar gidan ta ci gaba da aikinta. *** Har ya kwana washegarin da safe yana shirin tafiya ya kasa faɗan meke tafe tashi. Ganin zai yi asaran zuwa babu cikar buri ya sa shi yin ta maza ya sanar da Kawu Muhammadu abin da yake da buƙata. Murmushin taƙaici ya yi. Tun zuwansan daman yasan ba abin ƙirƙi ya kawosa ba. Yana dubansa kansa ƙasa tamkar mutumin ƙirƙi ya ce. "Amma Mamman ba ka da ta ido. Kai ko kunya ba ka ji." "Kawu ba haka bane. Ni dai dan Allah ka saka baki ko za ta amince." "Ba zan yi ba, ka je ka sameta, idan ta amince to idan ta ƙi shikenan. Ba zan mata dole ba, Sadiya tana da damar zaɓawa kanta abin da ya dace da ita." Ajiyar zuciya Alhaji Mamman ya sauƙe. "Shikenan Kawu na gode sosai da karamci." Daga haka ya musu sallama ya fita. Da kallo Kawu Muhammadu ya bisa. Har cikin ransa ya ji daɗin batun da Alhaji Mamman ya zo da shi, amma yana son sai ya garu ya gane laifinsa kafin Sadiya ta yarda, balle ma yana jin da wuya ta amince. Ƙarfe biyu da wani abu ya shigo gidan, bai shiga falon Amma Jidda ba ya wuce side ɗinsa. Dirin motarsa ya sa ka Amma Jidda leƙa wajen ta hango motar, fita ta yi ta nufi side ɗinsa. Sallah ta samu yana yi ta zauna ya idar. "Sannu da zuwa." "Yawwa ya gida?" Ya amsa mata. "Lafiya lau, Ya hanya? In kawo maka maka abinci?" Kai kawai ya ɗaga mata, ta fita ta kawo masa ta zuba masa ya hau ci. Sai da ta ga ya ci ya ƙoshi ta fara masa magana. "Don Allah Abbansu kayi hakuri, kar fushin Ameera ya shafeni, ban san duk tana aikata hakan ba, ko ta fita ba." Kai ya girgiza mata. "Ya wuce, ki sa mata ido sosai kawai, maganar makaranta na hana. Aure zan mata." "Hakan ma yayi." Tace ko ba komai hukuncin da ya ɗauka dai-dai ne da ita, kuma taji daɗin ya sauƙo daga fushin da ya mata dalilinta. ... Mami ta kwantar da hankalinta ganin Alhaji Mamman bai ƙara dawo mata da maganar ba. Kasuwancinta ta mayar kai sosai, ƙoƙarin buɗe shago take ta zuba kaya ta saka ma'aikata. Kullum sai tayi waya da ƴaranta, ba ta faɗa musu komai ba. Muhsin yana zuwa mata akai akai dan aikin da ya fara baya samun zama sosai. *** Washegarin juma'a ƙarfe sha biyu ƴaran Mami suka halarci ƙira da mahaifinsu ya musu. Alhaji Mamman bai dawo gidan ba sai bayan sallar juma'a. Tun a farfajiyar gidan ya fara cin karo da jikokinsa, murmushi yayi ya fita ya ɗauki wannan ya sauƙe yana jin daɗi. 'Me yafi haka daɗi. Sadiya ta ga jikokinmu sun cika mana gida." Yace a ranshi yana shigan falon Amma Jidda ya samu duk suna falon, Aunti Rahma, Hasiya, Rukayya da Muhsin, hatta Ameera tana rakuɓe a cikinsu, babu Walida da take laulayi. "Sannu da zuwa Abba." Suka faɗa suna gaishesa ya amsa ya miƙe. "Ku same ni a falonal." Daga haka ya fita kusan mintuna goma su ka bi bayansa. Zama su kayi gaba ɗayansu ba ƙasa. Bayan sabuwar gaisuwa ya dubi yaransan da suke sauraronsa ya ce. "Ina son mayar da Maminku, sai dai duk yanda zan yi ta ƙi yarda. Taimakonku nake nema, ina son mu koma tamkar daa tamkar babu abin da ya faru, mu mayar da aurenmu." "Aure dai Abba!" Aunti Hasiya tace da mamaki, ita kaɗai ta samu damar magana duk cikin falon. Kai ya ɗaga mata. "Eh in Allah ya yarda. Ku ce wani abun kunyi shuru." "Ni kam na amince Allah yasa hakan shine alheri." Faɗin Rukayya harda guntun hawayenta. "Nima haka Abba." Aunti Rahma tace cikin sanyin jiki ita kuma. Dama yasan ita za ta yarda akan Hasiya. "Ke fa Hasiya?" Ya tambayeta. Murmushi ta yi. "Abba ni kuma me zance, idan har Mami ta yarda babu yanda muka iya, amma in ta ƙi fa babu dole." "Nima bazan mata dole ba, so nake ku nemo min yardarta kawai. Ko albarkacinku za ta hakura ta amince." Shuru kowa yayi bayan sun amince. Muhsin sai danne danne yake a wayarsa yana jinsu. Yaji daɗin hakan domin haƙiƙa baya jin daɗin zaman Mami ita ɗaya kuma babu aure. Yasan ko ya ya ana maganarta ko da baya isosu. "Baban Mami ba ka ce komai ba." Yaji maganar Abbansu, murmushi ya yi ya ce. "InshaAllah Abba za ta amince." Cikin farin cikin da ya kwana biyu bai ji ba yana dubansu ya ce. "To na gode muku, Allah ya gode albarka. Duk yadda ku ka yi da ita ku sanar da ni Please." Da ameen suka amsa ya sallamesu suka koma, har ƙarfe biyar suna gidan, kafin kowacce ta fara shirin tafiya gidanta. *** Mufid Kashim Mufid. Rayuwa ya ke tsakanin rai ko mutuwa, damin magani shine cikon rayuwarsa. Sosai tsoron Allah ya shigesa, don ya ga ishara tun a duniya. A yau suka wayi garin da samun labarin rasuwar AA, hakan shi ƙara saka tsoron Allah a zuciyar Mufid. Kansa ya kulle a ɗaki yayi kuka ya yi ta roƙon gafarar Allah. Da ƙyar ya samu zuwa jana'izar AA ya dawo gidansu da babu komai, kowa ta kansa yake. Alhaji Kashim kusan sati biyu da ya wuce aka basa dogon letter na koransa da a ka yi a aiki, bisa kuɗaɗen da ya ɓatar tsawon shekaru cikin rashin sani, aka nemi dalili ya rasa hujjar kare kansa. Ranar ƙaramin hauka ya yi. Babu kuɗi babu aiki babu sana'a, dan ya dogara da aikin gwamnati da yake satan kuɗaɗen ciki, bai taɓa sha'awar kama sana'a ba. Hajiya Hindatu zama kawai take da shi dan babu inda za ta je, Hajiya Batula daga wajen iyayenta take samun taimako tana kula da ƴaranta. Yanzu ma shirin aurar da su biyun ta ke. Ƴaran Alhaji Kashim Mufid masu aure duk sun ji babu daɗin abin da ya samu ubansu, duk sun zo masa jaje tare da taimako daga wajen mazajensu, mijin Rufaida har gida ya zo masa tare da ita da ƴarta ɗaya sai ciki da ta ke fama da shi. Burin Mufid yanzu ya samu aikin yi, ya dogara da kansa dan ci da shansa da kuma magungunansa, dan idan Alhaji Mamman ya basa kuɗin sai yasha gori. Dukka ya sayar kadaransa ya saya mai yawa kusan na rabin shekara da zai masa amfani. Abincin kirki basa ci a gidan, balle maganar karatu, hakan yasa ya bazama neman aiki. Ya zama tamkar ba Mufid ɗan gayu da kwalliya ba, ya zama wani shuru shuru duk ya rame sai haske. Shaye shaye kuwa da bin mata rabonsa da hakan har ya manta. Ko ido ba ya iya ɗagawa ya kalli mace, balle ta basa sha'awa. ... #vote #comments #share MADUBIN GOBE  55. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Yau weekend (hutun ƙarshen mako), ko wani mahluki ma'aikacin gomnati shi ne ranar hutunsa. Garin babu sanyi kasancewar zafi ya fara gabatowa. Ga sabin aure kuwa wannan ranar ya musu daɗi don ya basu damar kasancewa da juna. Haka ga Dr Awwab da Nuratu ma da suke rama barcinsu, duk da Nuratu ta so farkawar wuri dan Hanan amma ya hanata ya nuna mata sai ƙarfe tara za ta tafi islamiyya, ita ma barci ta ke. Haka ta biye masa har ƙarfe takwas da mintuna sannan ta lallaɓa ta zare jikinta ta maye masa gurbin da filo ta fita. Kitchen ta wuce ta dafa mata abu mafi sauƙin dahuwa ta fito, ɗakinta ta nufa ta samu yarinyar ta farka tana zaune saman gadonta. "Sorry My Baby love. Mu je in miki wanka." Babu musu ta miƙe tana gaishe Nuratu, ta amsa tana murmushi tarbiyyar yarinyar yana burgeta, kayanta ta cire mata su ka wuce bathroom. Tsaf ta shiryata cikin uniform ɗin islamiyya, kafin su fito. Saman dinning ta ajiyeta ta wuce Kitchen ta ɗauko mata breakfast ta fara, sannan ta wuce dan tashin Awwab. Ɗaure da rigar wanka ta samesa tsaye gaban mirror yana shafa mai, jin motsi ya sa shi juyawa. Ganin Nuratu ya sake mata murmushi, ita kuwa ganinsa haka ya sa ta juyawa tana faɗin. "Hanan ta shirya kar tayi latti." Girgiza kai kawai yayi yana taɓe baki yana mamakinta. Ko me kuma na wani munafurcin kunya, wani darene jemage bai gani ba. Shirinsa ya yi kamar kullum cikin ƙananan kaya sai ƙamshin turare yake. Bayan ya gama ya sauƙo ya samu Hanan ta gama suka fita yana amsa gaisuwarta. Nuratu na su breakfast ɗin ta haɗa musu, bayan ta gama ta hau gyaran gidan, tsaf ta gama kamar kullum ta shiga wanka, tana wanka Awwab ya dawo. Ganin ba ta falon ya sa shi hawa sama, ɗakinta ya nufa nan ma shuru, motsin ruwa da ya ji ya sa shi zama yana zaro wayarsa a aljihu. Danne danne ya yi ya kafa a kunne. "Kun gama?" Shine abun da ya faɗa. Can na gefen bansan me yace ba naga Dr Awwab ya dafe kansa. Kamar ba zai ce komai can yace. "Shikenan, ka ƙara dagewa don Allah." Daga haka ya kashe wayar jin motsin taɓa ƙofar bathroom. Kallonsa ya kai gurin, daga ita sai towel daidai gwuiwarta, duk ba ta ankara da zamansa ba, tana goge fuskarta da ƙaramin towel. Har tsakiyar ɗakin ta tako ta tsaya a gaban madubi, towel din da ta ajiye shi ya ba ta damar hangosa ta cikin madubi. Ihu ta sakar ba shiri tana neman abin rufe jikinta. Har ga Allah ta tsorata dan bata tsammaci ganinsa ba. Babu komai kusa da ita sai ƙaramin towel, shi ta ɗauka ta kare kirjinta da sauri. Baki ya taɓe yana miƙewa ya nufeta, ai sai ta ƙara tsorata. Tana gani ya iso gareta ta runtse idanuwanta. Rumfa ya mata yana rankwafowa saman kanta ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta. Da sauri ta buɗe idonta su ka shiga cikin nasa. "Wai don Allah kunyata ki ke ji?" Ya faɗa yana ɗaga mata gira ɗaya. Kai ta ɗaga sai kuma ta girgiza dan yanzu sai ya mata abin da zai ƙara sakata wani kunyar. Murmushin gefen ba ki yayi ya matsa baya. "Ki gama shiryawa." Sanin tana buƙatar kimtsa jikinta ya faɗi haka yana fita. Ajiyar zuciya ta sauƙe ta nufi ƙofar ta sawa key, kafin ta gyara jikinta ta shirya tayi shafe shafenta ta fita. A dinning ta samesa yana waya, yana ganinta ya sanar da wanda suke wayar za su yi magana anjima. Ba ta zauna ba ta hau zuba musu abincin, sai da tagama kafin ta zauna. Ɗago ido tayi ta kallesa ganin ya kafeta da idanu. Murmushi tayi ta ɗauke idonta. "Allah ya miki albarka Noor." "Ameen Ya Allah." Tace tana murmusawa don ta ji daɗin addu'ar. Hannu ta kai za ta ɗauki spoon ya ɗauke, dubansa tayi ya ɗaga mata gira. "Bari in ciyarki, nasan kin gaji." "Zan yi da kaina fa." "No, buɗe bakin kawai." Yace ya ɗebo abincin ya kai bakinta, dole ta buɗe ya samata, daga nan ya ci gaba da bata har ta ƙoshi kafin ya hau ci. A nutse suka gama abunsu yana mata hira dangane da service ɗinta. Bayan sun gama ta tattare wajen ta kai kitchen ta hau wankewa. Shi kuma ya zauna falo yana danna wayarsa. Ta gama wanke wanken ganin sha biyu saura ta fara ƙoƙarin ɗaura abincin rana. Ƙwanƙwasa ƙofar kitchen ɗin ya yi yana tsayawa. Barin wanke kayan miyar da take ta yi ta juya. "Kana buƙatar wani abu?" Kai ya girgiza mata. "Kiyi dayawa akwai baƙi masu zuwa." To tace ta bi bayansa ganin ya fita, bai san tana binsa ba har ƙofar falon ya buɗe ta riƙe ganin zai kulle. Da mamaki ya juya sai ta sunkuyar kanta ƙasa. Matsawa yayi ya jata jikinsa yana zagaye hannunsa a bayanta, hakan ya bata damar ɗaura hannunta saman kirjinsa. Sumbatar saman hancinta ya yi, ganin yana shirin yin ƙasa da bakinsa ya sata kifa kanta a kirjinsa. "Yau kuma rowa ki ke mini?" Kai ta girgiza masa ta kasa ɗagowa. Rumgumeta yayi gaba ɗayanta, sonta da ƙaunarta na shigarsa. "Zan je gidan Ummi na dawo, me zan kawo miki." "Babu komai, ka gaisheta." "Za ta ji. Koma kiyi aikinki na hutarki rakiyar." Ya faɗa yana sakinta, sai da ya ga ta shiga kitchen ya fita. Gidan Ummi yaje ya gaisheta daga nan ya fita dan abin da ya fito da shi. Sai azahar ya dawo gidan don zuwan baƙinsu. A harabar gidan ya samesu suna jiransa, musabaha su kayi kafin ya musu jagora zuwa ciki. Shi ya fara shiga dan tabbatarwa ba ta falon kafin ya ba su izinin shiga ciki. Babu kowa falon, bayan ya ba su izinin shiga, ya wuce sama dan ƙiran matar gidan su gaisa. Kwance ya sameta barci ya fara fisgarta, gefenta ya zauna yana shafa bayanta da tayi rubda ciki. Idanuwanta ta buɗe tana gyara kwanciyarta. "Sannu da dawowa." "Yauwa ya gajiya. Tare muke da baƙi, ki canza kaya ki fito ku gaisa." Kai ta ɗaga masa daga haka ya fita, ta shi ta yi ta canza kayanta zuwa doguwar rigar atamfa ta yafa mayafi ganin dagasken mijinta na kishinta. Tana gamawa ta fita, ba ta jin hirarsu sosai har sai da ta shigo falon sosai ta tsinkayi muryar mutane biyun da su ke da mutuƙar mutunci a gareta. "Col! Yaya Al-ameen!!" Ta faɗa da ɗan ƙarfi tana ƙarasawa wajensu, murmushin su ke suka amsa mata. Rasa inda zata sa ranta tayi dan murna ta hau gaishesu, har da guntun hawayenta. "To me na kukan kuma? Duk shagwaɓa ce?" Col. Ahmad yace yana murmushi. Murmushi ta yi tana share hawayenta ta girgiza kai, juyawa gurin Yaya Al-ameen ta yi. "Yaya yaushe ka zo? Ina su Amma? Ya aiki?" "Lafiya lau ƙanwata, ya amarci." Kunya ta ji ta rufe fuskarta ta miƙe. Cikin sauri ta haɗa musu fruit salad da juice din kwakwa da abarba ta jefa kankara, bata da matsalar abinci dan ta haɗa kala biyu da gashashshiyar kaza, bayan ya sanar da ita akwai baƙi. Tsaf ta jera komai saman dinning ta gama ta koma gurinsu. "Abinci fa an kammala." "Ayi haka kuma Nuratu, a matsayina na Baba in zo gidan ƴata inci abinci." Col. Ahmad ya faɗa cikin zolaya. "Kai Yaya Ahmad, don Allah fa. Doctor ka masa magana." Dr Awwab da ya ke jin duk shari'arsu ya yi murmushi ya miƙe. "Ni na isa shiga faɗar Baba da ƴa. Al'ameen zo muje mu cika cikinmu." Yaya Al'ameen da ya miƙe tuni yariga Dr Awwab isa table din dan dama a yunwace yake. Ganin haka Col Ahmad ya miƙe. "Wasa nake miki." Daga haka shima ya isa wajensu, zama tayi a falon ta juya musu baya. Yaya Al'ameen shi ya yi serving ɗinsu, kowa sheƙe da plate, ga kofuna cike da juice ga bowl plate da fruit salad. A nutse su kaci sai da suka taɓa ko wanne suna santi. Bayan sun gama su ka koma falon su ka hau hira, ita kuma ta tattare gurin. Kwata kwata Dr Awwab ya manta da batun ɗauko Hanan har ƙarfe uku. Masallacin su ka je tare suka dawo, idan ka gansu ba za ka taɓa cewa sunyi tarayya wajen son abu guda ba. Sai dai abin mamaki ga su waje guda. Shigowarsu gidan Nuratu ta sanar da shi maganar ɗauko Hanan. A kiɗime ya zaro wayarsa ya ƙira Hussaina ta ɗaukota ta kawota dan yana da baƙi. Bai samu nutsuwa ba har tsawon mintuna goma Hussaina tayi sallama tare da Hanan. Kusan tare suka amsa ta gaishesu su ka amsa, daga nan suka wuce sama da Nuratu tare, Hussaina ce ta yi wa Hanan wanka ta canza mata kaya, ta sauƙo ta ɗauko musu abinci. Duk motsinta akan idonsa, shima kuma duk motsinsa akan idonsa, yana addu'a da fatan hasashensa ya zamto gaskiya akan wannan bawa. ... Sai biyar saura suka bar gidan, Nuratu sai ta ji duk babu daɗi dan tana ƙaunar mutane biyunnan tsakani da Allah so na ƴan uwantaka. Haka suka mata sallama bayan doguwar nasiha da kyauta mai tsoka da su ka mata, tana kuka tana musu godiya su kayi sallama. Tare suka fita da Dr Awwab ya musu rakiya gidansu Col Ahmad suka gaishe da Umma. Sai ƙarfe takwas ya dawo gidan sanin tana tare da Hussaina zata ɗebe mata kewa. Bayan ya dawo yayi wanka ya ƙira Nuratu ta kai masa abinci falonsa, anan ya tsareta ya hanata komawa wajensu. Bayan ya gama ya sanar Ummi dare yayi Hussaina zata kwana, da ƙyar ta barta akan gobe ya barta ta dawo, da to ya amsa ya kashe wayar. Haka Nuratu tana ji tana gani ya hanata komawa, shima anan yayi sallar isha'i, duk kumbure kumburen fuska haka ya hanata har lokacin barci ya kwasheta suka kwanta, duk da yasan babu abin da zata masa. Hussaina da Hanan ganin shiru bata dawo ba suma suka kwanta. ... Washegari har tara Dr Awwab ya hana Nuratu fita a ɗakin, duk da ya tabbatar mata Hussaina za tayi komai. Hakanne kuwa domin tun bakwai ta farka ta fara gyaran gidan, bayan ta gama ta haɗa breakfast, kafin ta yi wa Hanan wanka ta shiryata, tsaf ta gama komai ta shiga wanka. Har ta fito ta shirya babu alamun mutanen gidan, ita dai mamaki ma da kunya yake damunta. Babu yadda ta iya ganin Hanan za tayi letti dole ta nufi falon Dr Awwab. Ƙwanƙwasa ƙofar tayi tare da sallama. Daga can rigima ake tsakanin Dr Awwab da Nuratu, sam ya dage sai sunyi wanka tare, ita kuwa tace hakan ba zai taɓa yi wa ba wannan kayan kunyar, bayan hakama tana buƙatar kimtsa jikinta kafin ta fara wankar. Fahimtar haka yace mata ya yarda ta kimtsa jikinta sai suyi wankar, ai kafin su gama ba zata ɓata jikinta ba. Hakan da ya faɗa ya ƙara bata tabbacin dai ya dage, ita kuwa ba zata iya ba ta fara ƙoƙarin fita ya cafkota yana ɗaukarta sama. Bathroom ya nufa da ita suka ji ƙwanƙwasa ƙofa, dakatawa yayi ya ji an sake ci gaba. Sauƙeta yayi ya kalleta, kanta kasa ga hawaye kwance saman fuskarta. Hancinta ya lakace. "Allah ya taimake ki yarinya, da yau kinga yadda ake wanka." Wani mugun ajiyar zuciya ta sauƙe tana share hawayenta. Murmushi ya yi ya shiga bathroom ya barta tsaye. Ganin haka da sauri ta nufi waje. Ƙofar ta buɗe su kaci karo da Hussaina. "Aunti ina kwana." Tace tana ƙasa da kanta. "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya." Faɗin Nuratu taba yabawa da hankalin yaran. Kai ta ɗaga tana cewa. "Hanan za tayi letti." "Zai fito yanzu." Tace suna barin gurin ta wuce ɗakinta, Hussaina kuma ta sauƙa ƙasa. Nuratun tayi mamakin ganin ko ina fes sai ƙamshi yake. Murmushi tayi tana godema ta a zuciyarta. Ganin haka ta shiga wanka tana yi tana murmushin tuna rigimar Dr Awwab, haka ta gama ta fito ta shirya cikin riga da skirt na les me kalar maroon da sea green. Kayan ya mata kyau, kwalliya kaɗan tayi ta feshe jikinta da turare ta fito, daidai Dr Awwab shima fito. Yana ganinta ya buɗe hannayensa, bata da zaɓi da ya wuce ta isa garesa ta faɗa kirjinsa ya mayar hannayen ya rumgumeta. Shinshinar wuyanta yake yana sumbata kusan mintuna biyu, kafin ta fara zamewa tunawa basu kaɗai bane ga Hanan tana jiransa. Kallonsa tayi, shi ma ita ɗin yake kallo da idanuwansa da suka fara ƙanƙancewa. Fuskarsa takai hannunta ta shafa kwantaccen sajensa tare da kashe masa ido ɗaya. "Bamu ɗaya bane." Daga haka tayi gaba ta barsa tsaye tamkar an dasashi, bayanta ya bi da kallo. Da tana sallah yau da babu abin da zai hanasa nuna mata tasirin abun da ta masa, ba baƙi ba ko Hanan sai dai tayi letti ko ta fasa zuwa islamiyyar. Ya kusa mintuna da ƙyar ya samu nutsuwarsa ya sauƙo falon ƙasa. A dinning gaba ɗaya ya samesu, Hussaina da Hanan sunyi breakfast tana tattara plate ɗinsu. Bayan ya amsa gaisuwar Hussaina da Hanan yace. "Mu je idan na sauƙeta na kai ki gida." To tace masa ta kai kayan kitchen ta fito ta wuce ɗauko hijabinta. Ganin haka ya ƙarasa wajen Nuratu da tayi tamkar ba ita ba. Hucin numfashinsa ta ji saman fuskarsa, a razane ta matsa ya ƙara matsota. Marairaice masa tayi. "Hanan fa tana kallonmu." Wani kallo ya jefa mata ta yi kasa da kanta. "Kin ci bashi yarinya, ki guji ranar shiga hannuna." Daga haka ya matsa yana kallon Hanan da ta kafesu da ita. Harararta yayi yace. "Taso mu je kin wani sakawa mutane ido." Babu musu yarinyar ta miƙe ta bi bayansa tana yi wa Nuratu sai anjima. Haka Hussaina ta sauko tamata sallama ta wuce. Bayan fitarsu ita ma ta ƙira Mami suka gaisa. Sai goma saura ya dawo tare da wanda yayi mutuƙar tsorata Nuratu. Suna yin sallamar ta hangosa bayan Dr Awwab da gudu ta bar wajen tana hayewa saman, ba ta tsaya a falo ba ta wuce ɗaki ta kulle kanta sai kuka. Ganin haka ya saka Awwab taran baƙonsa cikin girmamawa da mutunci, ya nuna masa wajen zama ya zauna. "Bari in ƙirata Baba, nasan tana cikin ruɗune." "Babu komai." Ya faɗa fuskarsa tsantsar damuwa ganin gudan jininsa na gudunsa. ... Can ɗaki kuwa Nuratu kuka take ta yi tana mamakin ganinsa cikin gidanta. Tsawon shekaru huɗu rabon da ta sakasa a idanuwanta a matsayinsa na ubanta. Me ya zo nema wajenta? Me ya ke buƙata? Ruguza farin cikin da ta samu gidan aurenta domin tasan burinsa kenan a rayuwa, ya hanata jin daɗin ciki... Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ya hanata ƙarasa maganar zuci ta miƙe cike da tsoro. "Babyna buɗe ƙofar ni ne." Ta tsinci muryar Dr Awwab, cikin sassarfa ta isa tana buɗe masa, sai da ta leƙa ganin babushi ta buɗe ƙofar gaba ɗaya. Yana shigowa ta faɗa jikinsa tana fashe masa da kuka, rumgumeta yayi su ka isa bakin gado ya zauna ya zaunarta jikinsa, hannu ya saka yana shafa bayanta da bubbugawa alamar lallashi. Sai da tayi me isarta ta fara sauƙe ajiyar zuciya. "Ki daure mu je ku gaisa, ki ji me zai faɗa miki." Girgiza kai tayi tana ɗago kanta wani hawayen na silalowa a idanuwanta. "Ba zan iya ba, zai cutarni, ya tsaneni." "Kiyi hakuri, mu saurari me yazo da shi." Yace yana saka hannu ya share mata hawayenta. Za tayi magana ya ɗaura yatsarsa saman bakinta, dole tayi shuru. Ganin haka ya miƙe ya ɗauka mata mayafi ta rufe jikinta. Yana riƙe da hannunta su ka fito, jikinta rawa yake lokacin da suka shigo falon. Durƙushewa tayi lokacin da suka iso tsakiyar falon, muryarta na rawa tace. "Ina kwana Baba." Wani sanyi yaji cikin ransa jin rana ta farko ta ƙirasa Baba. Kai ya jingina ya amsa da. "Lafiya lau Nuratu. Ya zaman ibada." Ba ta iya amsawa ba sai kai ta girgiza masa. Ganin uba da ƴar suna buƙatar samun guri ya saka Dr Awwab miƙewa. "Bari in amsa ƙira." Daga haka ya fita ya basu guri. Ganinsa ya saka Nuratu ƙarfin halin zama, ganin kuma ya fita ya sata jin tsoro sai dai kalaman da Alhaji Mamman ya fara mata ya sa ta dubansa. "Autar Mami kiyi haƙuri kinji, nasan ke me hakurice ki ƙara hakuri. Ina neman yafiyarki badan na cancanta ba sai dai gudun haɗuwata da Allah, kiyi hakuri ki yafemin." Kuka Nuratu take ta rasa na farin ciki ko akasin haka, mahaifintane yake neman gafarta bisa abubuwan da ya aikata mata, tabbas duk me rai baya wuce rahmar Ubangiji. "Ki daina kuka kin ji, kar kice ba za ki yafewa mahaifinki ba, nasan ni mai laifine a wajenki, amma gani yau ina neman gafararki don Allah." "Baba ka daina roƙona." Nuratu tace tana share hawayenta. Hannu ya miƙa mata, babu musu ta saka nata cikin nasa ta rarrafa wajensa tana ɗaura kanta saman cinyarsa. Wani kukan ta fashe da shi, duk abin da ya aikata mata amma take wani muguwar sonsa da ƙaunarsa suke lulluɓeta, mahaifi dabanne, ƙaunarsa dabanne. Kukanta tasha har ta fara sauƙe ajiyar zuciya, har lokacin kanta saman cinyarsa yana shafa mata kai, shi ma nasa ɓangaren ji yayi zuciyarsa ta raunana, ya yi wa shaiɗan da aboki ala tsine yafi cikin kwando. Ƙaunar ƴarsa da sonta na ratsa jininsa. Tsakanin iyaye da yara fa sai Allah, domin akwai wani sihirtaccen kauna a tsakani da Allah kaɗai yasan iyakarsa. Sun jima a haka kafin Nuratu ta ɗago kanta da idanuwanta da su kayi jajir, murmushi ya mata ta mayar masa tana yin ƙasa da kanta. "Ba ki ce komai ba." "Baba ni fa dama ban riƙe ka ba. Na yafe wallahi duniya da lahira." "Allah ya miki albarka ya baku zaman lafiya." Kunya ya hanata amsawa ta miƙe, kitchen ta shiga ta jido masa duk abin da tasan zai iya ci da sha. A saman table na tsakiyar falon ta ajiye masa. Da murmushi ya kalleta. "Baba kasha wani abun." Tace tana buɗe murfin jug ta tsiyaya masa a cup ta miƙa masa, babu yadda ya iya ya karɓa ya kurɓa yana ajiyewa tare da miƙewa. "Zan wuce Nuratu sai munyi waya." Turɓune fuska tayi kamar za tayi kuka. "Baba daga zuwa, ka ga ko hira ba muyi ba." "Karki damu za muna waya. Saka mini lambarki." Babu musu ta karɓi wayarsa ta saka masa lambar. Har ƙofar falo ta masa rakiya anan suka haɗu da Dr Awwab ya masa rakiya zuwan bakin mota, sun ɗan tattauna kafin ya shiga motarsa ya wuce shi kuma ya nufi cikin falon. Ta tattare komai ta mayar kitchen, murmushi take wani sa'in hawaye ya zubo ta share dan farin ciki, ta rasa wa zata fara nunawa farin cikinta. Ba zato taji an ɗagata sama, ihu za tayi jin ƙamshin turaren Awwab ya sa ta sakin ajiyar zuciya. Sauƙeta yayi ya rumgumeta. "Babyna tana cikin farin ciki naga alama." Juyawa tayi ta ɗaura hannunta ta saƙalo saman wuyarsa, ganin haka shima ya ɗaura hannunsa saman kugunta ya rankwafo yana haɗa goshinsu. Ba zato yaji sauƙar bakinta saman nasa ta fara kissing ɗinsa, a rikice ya fara mayar mata da martani duk ya rikicemata, abin da ya jima yana burin samu daga gareta. Sun jima haka ganin za ta fitarsa hayyacinsa ta kasa magance masa ya sa ta zare bakinta. Tsam ya rumgumeta yana sauƙe numfashi tare da tagwayen ajiyar zuciya. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE Haske 56. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Ina cikin farin ciki marar misaltawa yau, haƙiƙa yau rana ta dabanne a gareni dama na kusa da ni, ko yau na komawa Ubangiji allahamdulillahi burina ya cika." Sakinta yayi daga rumgumar da ya mata ya riƙo fuskarta, sumbatar leɓɓanta ya yi. "Ni ma naga hakan a zahirance da aikatance. Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki Matata." "Ameen na gode, kaima haka Awwab AbdulRamat." Ta ƙare maganar tana ɗaura kanta saman kirjinsa ta lumshe idanuwanta tana shaƙar ƙamshin turarensa. Shock Dr Awwab ya ji jin yau rana na farko da ta ƙira sunansa, wani kasala ya sauƙar masa, da ƙyar ya riƙeta mai kyau suka fito, a saman kujera ya zubarsu yana ƙara kamkameta. "Maimaita sunan saman harshenki please." Yace yana tallafo fuskarta, idanu ta lumshe ta buɗe tana sakar masa murmushi har dimple ɗinta suka lotsa tace. "Awwab AbdulRamat mijin Nuratu Mamman Bashir, Baban Hanan da ƙannenta." "Kina sona?" Ya tambayeta da rawar jiki, gaba ɗaya jikinsa tsuma yake. Kalamanta ne suka haddasa masa hakan. Kanta ta mayar saman kirjinsa. "Sosai ma, idan har abin da nake ji idan mun kasance mu biyun so ne, to na daɗe da sonka a raina tun ba yau ba, tun ranar dana dawo hayyacina daga wancan duniyar. Ban tantance hakan ba sai dana zauna da kai. Ina ƙaunarka fisabilillahi." Shuru kawai ya yi ya zagayeta da hannunsa ya rumgumeta, ajiyar zuciya ya ke sauƙewa akai akai. Allah ya nuna masa ranar da Nuratu ta buɗe baki ta ce tana sonshi. Abu ɗaya zai hanasa nuna mata tsantsar son da yake mata yau. Kusan mintunan su biyar a haka ta dago kanta ta ga idonsa a rufe. "Doctor karmu manta da Hanan yauma." Sai lokacin ya buɗe ido suka sauka cikin nata, sakinta yayi kafin ya miƙe. "Bari inje in ɗaukota." Kai ta ɗaga masa ya fita. Ita ma ta shi ta yi ta ci gaba da aikinta. Yau ranar na musammanne a gareta. Ita kanta ta manta kanta wacece lokacin da take faɗa masa kalamannan. Kusan mintuna ashirin ya dawo da Hanan, da gudu ta nufi Nuratu suka rumgumi juna. Ɗakinta suka wuce ta canza mata kaya suka fito. Abincin da ta haɗa bayan fitarsa ta gabatar musu, suna ci Hanan na bata labarin islamiyya, Nuratu mamakin surutunta take, ita dai taga alamar Dr Awwab ba shi da surutu, sai dai ko mahaifiyarta ta biyo. Sai lokacin taji tana son sanin wacece ita. "To aku sarkin surutu, na nemo miki driver, daga gobe zai fara kai ki ya ɗauko ki." "Driver kuma Daddy." Tace tana kallon mahaifinta ta kalli Nuratu tana turɓune fuska. "Aunti ni dai bana son driver." Rankwashi ta ji saman kanta ta dafe gurin tana matso hawaye. Harararta yayi. "Ni fa bana son taɓara, yanzu zan bubbugeki kin sani. Ni kike so na zama driver naki, to bazan iya ba, nima ina da aikin yi." Shuru tayi ta haɗiye kukanta ta matsa gurin Nuratu. Ɗaukarta tayi ta ɗaura saman cinyarta ta share mata hawayenta. "Daina kuka kin ji, Daddy yana da aikin yi da safe da yamma, kuma idan ya ce zai ɗauki nauyin kai ki makaranta zai takura. Ki bari driver yana kai ki kinji." Kai ta ɗaga tana murmushi. "Na hakura Aunti." "Yawwa My Baby." Daga haka Hanan ta miƙe ta basu guri. Kallon Dr Awwab ta yi tana ɗaga masa gira ɗaya alamar kallon fa. Murmushi ya yi yana shafa sajensa ya kashe mata ido ɗaya. "Ina son tambayarka Doctor?" Ta faɗa masa. "Ina jinki My Baby." "Dangin mahaifiyar Hanan fa? Suna ina." Abin mamaki sai taga ya haɗa rai yana miƙewa tsaye. "Sunanan. Zan je in dawo." Baki sake ta bisa da kallo, mamaki ƙarara shimfiɗe a fuskarta. Ko me abun ɓata rai kuma? Bata da amsa ya sata miƙewa ta fara gyara wajen. Sai dare kusan takwas ya dawo har lokacin babu fara'a a fuskarsa, abincin ma kaɗan ya ci ya wuce ɗakinsa ya barsu. Nuratu ma kasa ci ta yi, ta jira Hanan ta kammala ta gyara gurin, ɗaki ta wuce ta mata shirin wanka ta kwantarta, kafin ta fito ta wuce ɗakinta, wanka ta yi ta shirya cikin kayan barcinta masu kyau, lungu da sako ta bi da turare, kafin ta wuce ɗakin Awwab. Samu ta yi yana aiki a laptop ɗinsa, bakin gadon ta ƙarasa ta zauna gefensa. Duk yana lura da ita ya basar, kusan mintuna uku suna haka, ganin shurun yasa Nuratu tashi ta hau gadon ta kwanta tare da jan bargo tana rufe rabin jikinta. Juyawa yayi ya kalleta ta juya masa baya, aikinsa ya ci gaba da yi kusan mintuna talatin ya gama ya ajiye laptop ɗin saman bedside drower ya miƙe. Bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito bai saka komai ba sai boxer ya feshe turare ya hau gadon. Bedside lamp ya kashe ya gyara kwanciyarsa tare da rumgumo Nuratu cikin jikinsa, ita ma ba tayi barcin ba har lokacin, kwanciyarta ta gyara a jikinsa, a tare suka sauƙe numfashi. Shuru kusan mintuna biyar. "I'm sorry please Doctor." "Is ok My Baby." Yace yana karanto musu addu'ar barci. Haka barci ya kwashesu. ... Washegari bayan sun gama breakfast ta masa rakiya zuwa compound ya ce. "Ƙarfe sha biyu zan dawo mu je gidan Ummi da Ammi." "To Allah dawo da kai lafiya." "Ameen My Baby." Ya ce ya shafa kumatunta kafin ya shiga ya kunna motar yana barin wajen. Ayyukanta ta gama ta haɗa miyar allayahu da kifi sannan cous cous sai kunun gyaɗa mai kysu da ta dauraye da nono, wajen sha ɗaya ta gama. Abbanta ya ƙirata suka yi maganar da yake son faɗa mata, sun jima suna wayar kafin ta kashe. A gaggauce ta shiga wanka, har lokacin bai dawo ba. Cikin doguwar rigar shadda ruwan ƙwanduwa ta shirya kanta, zama tayi ta tsara kwalliya marar hayaniya, ta feshe jikinta da turare, tana cikin ɗaura ɗankwali ya shigo. "Masha Allahu." Ya furta yana ƙarasawa wajenta. Ta cikin mirror suka haɗa ido ya mata murmushi ta mayar masa da amsa ta ci gaba. "Sannu da zuwa." Jikin mirror ya tsaya ya fuskanceta. "Kina da kyau kuma kinyi kyau." "Na gode, sai ka yi sallah zamu je." Kai ya jinjina mata. "Da sauran lokacin sallah, saura mintuna goma sha biyar, kuma zai ishemu mu isa. Mu je kawai." To tace ta gama ɗaurin ta yafa gyalenta Babba ta ɗauki handbag ɗinta. Shi dai bin ta kawai ya ke da ido, tasan dressing wadda ya dace da ita. "Mu je to." Tace yayinda da take saka takalminta memai tudu kaɗan. Hannunta ya kamo suka nufi waje, har tsakar falon ta tsaya tana miƙa masa handbag ɗinta. "Zan ɗauki abubuwa Please." Da mamaki ya kalleta sai dai bai tambaya ba, fahimtar hakan yasa marairaicewa ta ce. "Please mana." Karba ya yi ba musu yayi gaba ya barta. Kitchen ta wuce da sauri ta ɗauki babban basket ɗin da ta zuba komai ta fito. Tun da ta fito da kallo ya bita, hankali da tunanin da tayi amfani da shi dan kyautatawa mahaifiyarsa ya yi mutuƙar burgesa. Wani sonta da mutuncinta ya ƙara girma a idonsa. Kujeran baya ta buɗe ta saka tana komawa gaba ta shiga, motar ya ja su na fita a gidan, mai gadi ya kulle. Sai da su ka hau titi ya ɗan juya ya kalleta, hannunta ya kamo. "Thank you Babyna, haƙiƙa nayi dace a duniyata da Allah ya haɗani da ke har ya mallakamin ke matsayin mata, mace mai nutsuwa, haƙuri, tunani da hangen nesa duk ƙarancin shekarunki. Ina sonki sosai, ina fatan Allah ya sa ki zamto uwargidana a gidan Aljannahtul Firdausi." Da murmushi saman fuskarta tace. "Ameen Ya Allah. Daga Mamin Hanan sai ni dai." Kallonta ya yi ya maida hankalinsa kan titi, kamar ba zai yi magana ba can ya ce. "Kowa da matsayinsa a zuciyata. Ki amsa da ameen kawai." Bata daddara ba a dadare ta leƙa fuskarsa tace. "Na amsa, amma ai ita ma matarka ce, kuma nasan kunyi zaman daɗi da ita. Idan aka ba ka zaɓi fa?" Kusan mintuna biyar ya yi tamkar bai ji ta ba. Mamakine ya kamata da kwata kwata baya son tuna baya ko wani abun da ya shafe su. Ta buɗe baki za ta basa haƙuri ta ji yace. "Hakane kam, munyi zaman lafiya da Nusaiba, kuma har yanzu ina yaba kyautatawarta da soyayyarta gareni. Ina mata fatan samun sakamako mai kyau. Zaɓi kuma idan aka bani dukkanku zan so ku kasance matana a Aljannah. Amma matsayi a zuciyata kowa da nasa, saboda kowa da yanayin yadda na fara sonsa duk da silar son gaba ɗaya tausayine. Bayan aurena da Nusaiba na fara sonta sakamakon cikin Hanan da ya bayyana jikinta, duk da ita tun farko haɗuwarmu na fahimci tana sona sai dai kunya ya hanata nunawa, taimako da kyautatawa rayuwarta da nake ta kamu da sona amma haka ta danne, babu batun sonta a raina mu kayi aure, amma kyautatawa, kulawa da tausayi yasa ni fara sonta ga kuma cikin Hanan. A haihuwa na rasata, rashi na har abada kamar yadda na sanar miki. Amma ke..." Ya ƙarasa maganar yana kallon Nuratu da ta kura masa ido, murmushi ya yi yana mayar da hankali ga tuƙinsa. Ita dai ba haka ta so ba, ya ci gaba da bata labarin rayuwarsa da Nusaiba, ya faɗaɗa mata ba a dunkule zai bata ba. Iska ya furzar ya ci gaba da cewa. "Amma ke shigar ba shiri ki ka mini, ki ka ma zuciyata bake bake ki ka hanani runtsawa. Ranar da na fara ganinki tausayinki ya kamani, na kasa barci kullum cikin tunaninki, halin da ki ke ciki, zafin da ki ke ji a zuci. Idan za ki iya tunawa akwai lokacin da tsawon sati biyu na kauracewa zuwa gurinki a asibiti, to wallahi so nake na rarrashi zuciyata akan ki, amma ina na kasa. Tun ina iya ɓoyewa Ummi har na kasa, duk zurfin cikina haka na sanar mata na samu macen aure duk da ke ban faɗa miki ina sonki ba. Ta yi mamaki ganin duka duka shekara biyu da rasuwar Nusaiba, haka ta yi ta bani baki dai tana ƙarfafa mini gwuiwa. Ɓangarenki kuma yadda kika nuna baƙya son aure yanzu ya ƙara tada hankalina, duk rashin son takuwara mutum a rayuwata haka ki ka sani na fara takura miki. Ƙarshe dai ban hakura ba har na mallake ki, ga ki gabana. Kinga kuwa kowacce da matsayinta a raina." Dogon numfashi Nuratu ta sauƙe tana ɗaura kanta saman damtsen hannunsa. "Allah ya ji kanta ya gafarta mata." "Ameen ya rabbi." Ya furta can ƙasan maƙoshi. A haka suka ƙarasa gidan Ummi, da taimakonsa ta shigar da basket ɗin. Da sallama suka shiga falon, kullum a gyare fes yana ƙamshi. Hassana da take kitchen ta fito ta amsa tana ƙarasawa wajensu ta rumgume Nuratu. "Sannu da zuwa Aunti. Ya hanya?" "Lafiya ƙalau. Ya gida?" Dan ta kasa tantance Hassana ko Hussaina. Da murmushi Hassana ta masa tana sakinta ta matsa ta gaishe Awwab ta karɓi basket ɗin hannunsa. "Mu je sama wajen Ummi. Ina Hussaina." Ya tambayeta. "Tana can ita ma." Ita ta musu jagora har falon Ummi. Jin masu sallamar ta faɗaɗa fara'arta tana musu sannu da zuwa. A kunyace Nuratu ta gaishe da Ummi ta amsa tana tambayarta gida. Hassana da Hussaina duk sun bi sun dabaibayeta suna mata hira, dan ma Hassana ba ta da surutu. Ummi da Awwab hiransu suke. Sallar azahar da aka ƙira ya sa su miƙewa suka sauƙa ƙasa dakin ƴan biyu da Nuratu, Dr Awwab ya wuce masallaci. Bayan ya dawo ya ƙira Hussaina ta zuba musu abincin shi da Ummi wanda Nuratu ta kawo, sauran kuma ta kai musu. Sun ci sunyi santi sun yaba da girkinta, ta ji daɗi Awwab ma yaji daɗin yabon matarsa da aka yi. Har lokacin tashin Hanan suna can, driver ma da ya ɗaukota gidan ya kaita. Tare suka shiga kitchen da ƴan biyu suka yi girki. Bayan la'asar ƙarfe huɗu suka musu sallama za su je gidan Ammi. Acan suka bar Hanan faɗin Dr Awwab ta kwana musu biyu. Ita ma yarinyar ko dan tayi kewarsu ya sa ta bata damu ba. Kyautar turare mai tsada da ƙamshi Ummi ta bawa Nuratu, tana ta godiya haka suka fito. Gidan Ammi suka nufa. A falon suka yada zango har ta fito a kitchen. Har ƙasa Nuratu ta durƙushe ta gaisheta. Da murmushi ta amsa. "Amaryace a gidanmu. Sannu da zuwa." Ita dai Nuratu kunya ya hanata motsi, kusan mintuna biyu ta miƙe ta koma kitchen, fahimtar kamar aiki take ya saka Nuratu ta shi tabi bayanta. Da ido Dr Awwab ya bita yana mamakin kuma me za tayi. Da sallama ta shiga kitchen ɗin Ammi ta juyo. "Kina buƙatar wani abu?" "A'a Ammi. Bari in ƙarasa miki aikin." "Ayi haka kuma amarya daga zuwa. Na kusa kammalawa, ki je ki huta." Ƙarasa shiga ciki tayi ta karɓi muciyar hannunta. "Don Allah Ammi ki kawo." Babu musu ta sakar mata. "Abincin kawai za ki tuka sai ki haɗa miyar kuɓewa na haɗa ruwa da komai. Mai gidan yafi son in girka da hannuna." "To Ammi." Tace ta zare mayafinta ta ajiye ita kuma Ammi ta ɗauki ruwa ta fita. Abincin ta tuƙa ta rufe, ta hau haɗa miyar. Har magriba Dr Awwab da ya samu Abdallah ya shigo da Yaya Sajeed suna hira bata fito ba, masallaci suka wuce suka dawo. A dinning ya hangota da Ammi suna jera abinci, can suka ƙarasa. "Amarya dai ta zo ba muje ganinta ba. Wannna kayan kunyar har ina a matsayinmu na manyan yayu." Faɗin Abdallah. Murmushi Nuratu tayi ta durkusa ta ce musu. "Ina wuninku?" "Lafiya lau amarya. Ya ki ke?" "Lafiya lau." Ta amsa. Ɗago ido tayi ta ma Dr Awwab kallo daya ta ɗauke tana miƙewa ta koma kitchen dan ɗauko sauran abubuwan buƙata. "Ga abincin amarya ku zo ku ci." Ammi ta ce tana ɗaukar abinci Abba. "Da gaske Ammi." Faɗin Abdallah yana zama. Haka sauran suka zauna har Dr Awwab a table, Ammi ta kwashi na mijinta ta wuce sama da shi. Fitowar Nuratu ya sa ta ajiye abin da ta ɗauko ta bar gurin. Duk kaɗan ɗin abincin haka suka ci suna yabawa. Dr Awwab wanda ya zuba ya ɗauka ya nufi inda Nuratu take zaune. Kusa da ita ya zauna ya saka plate din abincin tsakaninsu. Bai mata magana ba ya ɗauki loma ɗaya ya kai bakinta. "Ke kin cikawa mutane ciki da abinci ke za ki zauna da yunwa. Buɗe bakin in ba ki." "Zan ci da kaina." Tace tana girgiza kai ganin idon mutane. Ga kuma abin mamaki da take kallo, kammannin yayanta Muhsin a gurin wanda aka ƙira Abdallah. Abin ya ɗaure mata kai. Hannu ta kai za ta fara ci, hanata yayi ya kai abincin bakinta, dole ta buɗe ya sakamata. Shi ya bata yana ci har suka cinye, dama ba wani yawane da shi ba. Shi ya ɗauke ya kai dinning ita kuma ta tattara gurin ta gyara ganin sun bar gurin. Har ƙarfe taran dare kafin Ammi ta sauƙo ta sanar musu su hau su gaisa da Baffa. Ita ta musu jagoranci har falonsa. Haka kawai dukkansu biyun zuciyarsu ya buga tare bayan haɗa ido da suka yi. Nuratu ne ta janye nata ta durkusa tana gaishesa. Amsawa yayi yana mata godiyar abinci da ta girka masa, can ƙasan zuciyarsa kuma wani tunani yana taso masa amma wani abu me nauyi yana dannewa. Bayan gaisuwar kusan mintuna goma suka masa sallama, nasiha ya musu tare da ma Nuratu kyautar kuɗi, da ƙyar ta karɓa, haka Ammi ma turaren wuta ta ba ta da kayan shafe shafe. Ta rasa me zata bata ya faranta mata ranta. Tana son yarinyar tun ranar da ta fara ganinta. Haka Abdallah da Sajeed ma kyautar kuɗi suka bata har Abdallah na cewa. "Babban Yaya yayi missing, amma za mu kai miki ziyara." "Dan ku cika tunbinku ba." Awwab yace yana harararsa. "Afuwan Baban Hanan. Za mu je ganin ɗakin ƙanwarmu ne." "To sai kun zo na gode sosai." Ta faɗa tana murmushin rigimarsu. "Mune da godiya amarya." Abdallah ya faɗa, Sajeed ma ya musu sallama kafin Awwab yaja motar suna barin harabar gidan. Sunyi nisa a tafiya Dr Awwab ya riƙo hannunta. "Don Allah ki sanar da ni me zan miki in nuna miki farin cikin da na ji." Hannunta ɗaya ta ɗaura saman nasa da ya riƙe nata. "Farin ciki ka ke? Ka godewa Allah." "Na gode masa. Allah na gode maka da ka mallaka mini Noor a matsayin mata." "Ameen Ya Allah." Ta faɗa tana godewa Allah a ranta ita ma. "Ina da wani buri Noor, ki tayani addu'ar cikarsa kwana kusa." "Allah ya cika maka dukkan burinka My Doctor." Ta basa amsa cikin zuciyarta tana masa addu'ar cikar burinsa. Hira suke sama sama, barci take ji sosai. Suna isa gidan wanka kawai suka yi suka bi lafiyar gado. ... Washegarin bayan farkawarsu ta ga ba shi da niyyar tafiya aiki sai ma shiga da fita da yake. Ta gama gyaran ɗakinsa da shine ƙarshen aikinta, tana riƙe da burner ya sake shigowa ta bisa da kallo. "Wai lafiya Doctor?" Ta tambayesa tana ajiye burner ta isa wajensa. Hotunan hannunsa take ƙoƙarin karɓa ya hanata ya tura cikin file ɗin gabansa. "Ki shirya zamu fita." "Amma lafiya? Aikin fa." Fuskarta ya shafa yana cewa. "Lafiya ƙalau. Baƙon bai tafi bane?" "Wani bako kuma?" Murmushin gefen baki ya yi yana ɗaga mata gira ɗaya. "Baƙon da ya mini shamaki da ke. Ya hanani jin daɗin matata." Babu shiri ta bar masa gurin sai da ta kai bakin kofa ta juya tana masa murmushi. "Dubawa za ka yi ka gani." Daga haka ta fice da gudu tana dariya. Shi ma dariyar ya yi yana girgiza kansa. Zai bata mamaki kuwa, tunda ita ta faɗa hakan da bakinta. Tsaf ta shirya cikin riga da skirt na atamfa me ratsin ja da yellow, sai gold kaɗan, hakan yasa tayi amfani da kalar gold a jakanta da takalmi da mayafi. A gurin wanka ta ga bakonta ya tafi, dama tun asuba ta gani. Haka tayi wankar tsarki da wanka ta fito ta hau shiri. Kwalliya tayi ba wani sosai ba ta fito, kusan mintuna biyar ya fito shi ma cikin manyan kaya. Sosai ya mata kyau cikin shaddar kalar gold da ya amshi fatarsa, harda hula ya ɗaura, sai ƙamshi yake. Abin na su sai ya zama tamkar haɗin baki tamkar anko suka so yi. Falon ya kulle bayan sun fita, shi ya buɗe mata ta shiga motar kafin ya zagaya ya shiga shi ma yana kunnawa suka bar harabar gidan. Tafiya ta ga suke sun nufi hanyar fita a gari duk da bata gama sanin garin ba. "Damaturu za mu je fa." Ya faɗamata. "Da gaske." Tace cikin murna. "Ga alama nan." "Na gode, zan ga Mamina." "Uhmmm." Kawai ya ce ya ci gaba da tuƙi. Tun Nuratu na sauraransa har barci ya kwasheta. Ba dan bata sallah ba da ya ce yayi ajiye a gurinta dan wannan barcin. Ƙarfe sha ɗaya suka isa cikin Damaturu. Sai da ya shigar da motarsa har harabar gidan kafin ya tasheta ta hanyar shafa fuska. Baki ta tura tana yamutsa fuska. Sumbatar leɓɓanta ya yi ya ce. "Wakeup Baby, mun iso." Idanuwanta ta buɗe a hankali, sai lokacin ta tuna da inda take. Harabar gidan ta bi da kallo, gani take ta san gurin amma ta manta. Kallonta ta maida kansa. A shagwaɓe tace. "Gidan Mami fa?" "Mu fara shiga nan, daga baya sai mu je wajen Mami." Ba dan taso ba ta sauka shi ma ya sauƙo suka nufi falon ɓangaren da suka isa. Da sallama suka shiga falon aka amsa musu. "Amma!" Ta ce da mamaki tana nufarta ta faɗa jikinta. Tun bikinta basu haɗu ba. Ita dai Amma kunyane ya kamata ga Dr Awwab ya shigo. Hakan yasa ta zare Nuratu a jikinta suka zauna. Gaisawa suka yi da har ƙasa ya durkusa ya gaisheta. Da fara'a ta amsa masa kafin ta ƙira Ameera ta fito ta kawo musu ruwa. Babu musu ta fito, kallon kallo suka yi da Nuratu kowanne ya ɗauke kansa. Ko Dr Awwab bata iya gaishewa ba ta wuce Kitchen. Duk ta koɗe ta rame sai duhu, babu makaranta sai zaman gida da aiki, aurenma ba'a ƙara mata maganarsa ba. Haka ta dawo da ruwa gora ɗaya da cup ta dangwarar ta wuce ɗakinta. Girgiza kai Amma tayi ta miƙe. "Ina zuwa minti ɗaya." Daga haka ta nufi ɗakin Ameera. Ruwan Nuratu ta zuba a cup ta miƙawa Dr Awwab, kai ya girgiza yace. "Ki sha." "Ka fara." Karɓa yayi ya kurɓa ya miƙa mata ta amsa dai-dai Amma da Ameera sun fito. Ranta a haɗe ta zauna, ita ma Ameera ta zauna tana cewa. "Ina wuninku." Daga haka bata ƙara komai ba su ka ci gaba da zama sai Nuratu da Amma suke hira. Dr Awwab wayarsa yake dannawa, yayinda Ameera ke musu kallon ƙasan ido tana taɓe baki. Kusan mintuna Dr Awwab ya musu sallama zai je ya dawo zuwa azahar. Bayan fitarsa Amma da Nuratu suka wuce Kitchen ta taimaka mata suka haɗa abincin rana. Suna gamawa Rukayya da Walida suka yi sallama. Wani ihu Nuratu ta saka ta fito da gudu ta ɗale kan Rukayya ganin Walida cikinta ya fito. "Allah sarki ni Walili." Faɗin Walida ganin ta ƙi rumgumeta. Sakin Rukayya tayi ta ɗan rumgumo Walida. "Ke ɗince kin fara zama kaya." Dariya suka kwashe da shi, Walida tayi wani dariyar mugunta. "Yarinya kina layi. Waya sanima ko Dr yayi ajiya a wannan shafaffan cikinki." Harara Nuratu ta watsa mata tana yin gaba, Rukayya ta kwashe da dariya tana cewa. "Da gaske Walida maganarki ya zama gaskiya. Ji daga magana." "Kwa sani magulmata." Ta faɗa tana ɗaukar yara ƴan biyu na Rukayya mace. Wasa ta fara mata tana tambayarta, yaran dai sun ganeta dan suna da ɗan wayo, namijinne ma ya nuna rashin sabo sai kuma ya sake ganin ƴar uwarsa ta sake da ita. Hirane ya barke tsakanin ƴan uwa, ƙawaye, makusantan juna da suka yi kewar juna. Rabin hirar duk tsokanar Nuratu suke, sai dai ta girgiza kai tana dariya, na haushi kuma ta hararesu. Har azahar suna falon, su dai sunyi mamakin ganinta cikin gidansu, amma sun bar abun a ransu, bayan hakama sun bari akan kafin dawowar Abbansu za ta tafi. Amma dai cikin ɗaki ta tafi ta barsu dan basu waje. Har azahar suka wuce ɗakin Amma suka yi sallah, kafin su fito. Zuwan Aunti Hasiya da Rahma ne tare da yaransu ya saka Nuratu hawaye duk suna mata dariya. Ta ɗauki wannan yaron ta sauƙe, ta sumbaci wannan duk son yaran yayunta take. "Kena dai kin kusa samun naki." Walida tace tana kai abinci bakinta. Shuru Nuratu tayi tamkar ba da ita ake ba ta ci gaba da bawa ƙaramar ƴar Aunti Hasiya abinci. "Ke kam dai Allah ya shirya ki Walida. Gaba daya kin ƙara fitsarancewa ga sa ido." Faɗin Aunti Rahma. Aunti Hasiya da sai lokacin ta saka baki tace. "Ta ji me ake ji a auren ba dole ba, tasan sirrin. Ta sawa autan Mami ido. Ita ma gata kamar me yaron ciki." Dariya suka sanya gaba ɗaya ban da Nuratu kamar tayi kuka tace. "Aunti wallahi sharri suke mini. Ni yauma na fara sallah." "Sallah ki Godewa Allah da ya baki kyauta ba." Faɗin Rukayya tana yin wani dariyar. Aunti Rahma Nuratu ta kalla, tasan ita kaɗai zata fahimceta ta kwaceta wajensu. Hakan kuwa yayi tasiri, Aunti Rahma ta haɗa rai tana cewa. "Kai ya isheku kun takurawa autan Mami. Ko laifine in tayi cikin, ai ba'a kanta aka fara ba, ko kuma dama mun kaiwa Doctor ne ya sata a gaba yana kallo. Kun san dai dole nan da wasu watanni Mami ta samu jika a wajen autarta." Ta ƙarasa maganar tana murmushi. Nuratu dai taga ta kanta tace. Haka suka yi ta mata daga ƙarshe Aunti Hasiya ta kwaceta a gurinsu ta tsare su. Duk da kowa ƙasan zuciyarsa cike ya ke da tambayoyi akan zuwan Nuratu gidan kuma sunsan tsakaninta da Abbansu. Ƙarfe biyu Alhaji Mamman ya dawo gidan daga kasuwa wanda ba laifi kasuwa ya fara dawowa. Amma Jidda ne ta sanar musu. Gaba ɗaya suka dungama da yaransu zuwa gaisuwa, anan suka tarar Muhsin da ya dawo daga aiki. Da fara'a ya amshi yaransa abin alfaharinsa. Ɗaya bayan ɗaya suka gaishesa, abin mamaki wajensa kai tsaye Nuratu ta nufa ta zauna kusa da kafafunsa. Kanta ya shafa yana mai da hankalinsa gaba ɗaya kanta. "Autar Mami kun iso lafiya?" Kai ta ɗaga masa tana cewa. "Lafiya lau. Na sameka ƙalau." Shi ma ɗaga mata kai yayi, daga haka ta ƙarasa wajen Muhsin suka gaisa. Yana tambayarta gida. Gurinta ta koma kusa da Abbansu. Kallon yaran yayi ya hango tsagwaran mamaki da al'ajabi saman fuskokinsu, kuma yasan suna buƙatar ƙarin haske. Ban da ma dalilin wannan taruwarsu anan gaba ɗaya. .. #vote #comment #share MADUBIN GOBE  57. Pharty Bb. Wattpad Pharty BB. *** "Kun ga duk abun da ba ku tsammaci gani ba ko? To haka Allah yake abun sa. Sannan komai da ya faru ƙaddara ce da son zuciya. Babu maganar tone tone akan abin da ya wuce. Magana ta gaba shine maganar da mu ka yi kwanaki da ku akan Mamin ku, na ji shuru." Dukkansu farin ciki ne ya mamaye zuƙatansu ganin uba da ƴar sun sasanta kansu, abin da suka jima suna burin gani. "Abba za mu mata magana Insha Allah, za a samu mafita da yardar Allah." Aunti Rahma fada. Nuratu da ta gano kan zancen ta ƙara da cewa. "Idan ma danni take ji zan sameta." Anan kowa ya dinga bada ta shi shawarar har Muhsin da baya yawan magana shi ma ya saka baki. Haka dai har kusan la'asar kafin suka koma ɓangaren Amma Jidda da ba tasan me ake tattaunawa ba. Muhsin da Abbansu su ka wuce masallaci. Bayan sallar la'asar da su ka gabatar Nuratu ta ɗauki wayarta ta lallaɓa ta fice a ɓangaren. Mijinta ta ƙira cike da kewarsa tana tambayarsa ya ci abinci. "No Babyna." Ya faɗa yana daga kwancen da ya ke cikin katafaren hotel ɗin da ya kama. Narkar da murya ta yi ta ce. "Haba dan Allah Hayat, ka daura ka sa wani abu a cikinka." "Haka aka damu da ni Noor?" "Sosai ma Hayati." Ta basa amsa cikin kulawa. "Noor." "Hayat." Su ka faɗa ta basa amsa tsammaninsa ko suɓutar baki tayi, shuru dukkansu suka yi suna jin hucin numfashin juna cike da saƙwannin da yake kai kawo a zuƙatansu. Dr Awwab ne kaɗai ya fahimci abin da su ka faɗa. Cikin murya ƙasa ya ce. "Kece haskena ni ne rayuwarki *NoorHayat*." Nuratu da ba tasan hakan ba sai yanzu, murmushi ta yi da ya ji sautinsa. "Tabbas hakane." "Akwai babban tukwuici da zan ba ki." Dariya ta kuma sawa tace. "Godiya nake ranka daɗe." Kusan mintuna goma suna wayar ya tambayeta ta ci abinci kafin shi ya ci ta basa amsa da eh, anan suka yi sallama bayan ya tabbatar mata zai ci. Daga nan ta tafi inda za ta je bayan ta tabbatar babu mai kallonta, kuma tasan tana da ishashshen lokaci. Sai bayan magriba Dr Awwab ya dawo gidan. Har ɓangaren Abba aka masa rakiya suka gaisa kafin a kai sa ɓangaren baƙi, abincin da Amma Jidda ta haɗa ta saka Nuratu ta kwasa ta kai masa. Da kunya dai haka ta ɗauka dan ma su Rukayya sun koma gidajensu bayan sunsha hira ta musu alƙawarin za ta je kafin su koma. Abincin ta ajiye saman center table ta fara ƙoƙarin zuba masa ya riƙo hannunta. Fizgota ya yi ta fado jikinsa ya rumgumeta. Ba ta yi yunƙurin hanasa ba dan tasan babu mai shigowa sai ma ƙara lafewa da ta yi a jikinsa, suna shaƙar turaren juna. "Za mu je gidan Mami fa." Yace yana ɗago fuskarta. Fara'a ne ya bayyana a fuskartan. "To ka ci abinci sai muje." "Za ki bani a baki?" "Idan wani ya shigo fa." Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa dan zuba masa. "Mijinki ki ke ciyarwa." Murmushi ta yi ta ɗauki plate ta zuba masa ta saka spoon ta koma saman kujeran gefensa ta zauna, plate ɗin ta ɗaura saman cinyarta ta saka hannu ta ɗauki spoon. Ganin haka ya sa ka Dr Awwab riƙo spoon ɗin yana mata nuni da hannu da ido. Fahimtar haka ya sa ta tashi ta wanko hannunta ta dawo ta zauna. Hannunta ta saka kamar yadda ya so ta ɗeba ta kai bakinsa, buɗe bakin yayi ta zuba masa ya fara ci. Bai tsammaci za ta iya basa bai sai ga shi ta basa mamaki. Tana bana basa yana ci suna hira sama sama tana basa labarin yayunta. Kaɗan ya ci yace ya ƙoshi ta dakata. "Saura ke." Ya faɗa ya karɓi plate ɗin zai zuba ta riƙe. "Wallahi a ƙoshe nake." "Sai ki ƙara. Ni ma ina son ladar." Ganin ya dage ta sakesa ya zuba kaɗan ya hau bata ita ma. Kaɗan ta ci dan a ƙoshe ta ke, kafin ta musu jagora zuwa bangidan da ke falon suka wanke hannu suka dawo. Tattare komai tayi ta kai cikin gidan ta yi wa Amma sai anjima za su je gaishe da Mami, ta shiga gurin Abba ma ta masa sallama. Samunsa tayi har ya shiga motar ta shiga suka bar gidan. Tafe suke shuru ya ɗan ratsa cikin motar kafin Dr Awwab ya riƙo hannunta. "Gobe za mu koma fa." "Gobe kuma? Na ɗauka ganin gida na zo ai." Murmushi yayi me sauti ya dubeta yana maida kallonsa kan titi. "Ke da ganin gida sai kin zo wankan jego, in har lokacin na ji zan iya barinki." Marairaicewa tayi ta kamo damtsen hannunsa. "Ina son zuwa gidan su Aunti Rahma da Hasiya, har da Rukayya da Walida. Akwai wata friend nawa ma idan har ka bani izini ina son kai mata ziyara Please." Shuru yayi ya ƙi mata magana hakan yasa ta fara masa kukan shagwaɓa. "Ni wallahi ka yarda." Dariyace ta kwace masa jin tana mintsilinsa a hannu. Hannunta ya riƙo da ɗayan hannunsa, ɗaya nakan sitiyari. "Is ok My Baby. Wannan muguntar zan rama. Zan yarda amma za ki rakani hotel mu kwana tare. Da nayi niyar barinki gidan Mami ki kwana." Ƙara turɓune fuska tayi ga samu ga rashi. "Dan Allah fa Hayat." "Zan duba." Ya faɗa daidai sun iso babban mall din da ya faka. Ba ta ma lura ba sai yanzu tsabar taɓara da take zuba masa. Kallonsa tayi yana shirin fita yace. "Fito mu ma Mami tsaraba da yaranmu." Da sauri ta fito ya rufe suka shiga ciki yana kamo hannunta. Turaruka masu ƙamshi ta ɗaukawa Mami da katan na maltina da peack milk. Ƴaran Aunties kuma tace ya bari gobe idan za ta je ta siya musu abu. Yayi na'am da hakan yasan duk wayo take son masa. Gurin biyan kuɗi suka nufa ya biya. Mai kula da gurin ya ƙira yaron shagonsu ya zo ya kai musu. Cikin sauri ya iso gurin yana rissinawa. Kayan aikin shagonne jikinsa, blue riga an rubata WALID PROVISION STORE, da baƙin jeans na wando. Kansa ƙasa ya ce. "Oga Khamis bayanan ya barmini aikinsa." Ya faɗa cikin girmamawa. "Oh hakafa. To MUFID ɗauki ka kai musu mota." Tun sanda ya iso komenta ya tsaya cak, dariyar da take yi Dr Awwab na tsokanarta shaf ya ɗauke, jikinta mugun rawa yake musamman da aka ƙira sunansa ta tabbatar shi ne. Dr Awwab da ya ji shuru yayi yawa ya ɗago kai ya kalleta, ganinta yayi tamkar an kafata. Hannunsa ya ɗaura saman kafaɗunta ya taɓata. "Noor! Noor!!" Ya faɗa da hakan ya dawo da ita hankalinta, ba zato ta kankamesa. "Ka fitar ni anan." Ta faɗa cikin rawar murya tare ƙara riƙesa. Maganarta ya saka Dr Awwab ganin cikin mall ɗin ko ta ga wani abune, ganin mai dosowa garesu ya fahimci me ta gani. Hannunta ya jawo su ka fita waje, shi dai mai karɓar kuɗi ya bisu da kallon mamaki. Sai da ya shigar da ita ya ga ta zauna ya fara ƙoƙarin fita ya ga amma sai waige waige ta ke. "Bari in sallamesa." Girgiza kai tayi tana shirin fashe masa da kuka. "Haƙƙinsa ne fa." Shuru ta masa tana kawar kanta gefe hawaye na kwaranya bisa kumatunta. Dr Awwab bai so ba ya fita. Ya samu Mufid ya gama saka musu kaya yana tsaye. Ba don a sallame sa ba sai dan yana son tunkararsu ya rasa ta ina zai fara. Fitowar Dr Awwab ya sa shi yin ƙasa da kansa cike da kunya, yasan dawowa ya yi ya masa rashin mutunci kawai ko tozartasa har wanda basu sanshi wanene ba su sani yau. Amma abin mamaki hannu Dr Awwab ya miƙa masa tare da ƙiran sunansa. Idanuwansa masu kyau ya ɗago ya dubesa ya girgiza kai. Ba zai iya haɗa hannu da mutun mai daraja irin wannan ba. Ganin ya ƙi amsa Dr Awwab ta kamo hannunsa ya saka cikin nasa suka yi musabaha. "Baka son samun lada kenan." Girgiza kai Mufid yayi yana ƙasa da kansa. A hankali ya buɗe baki ya ce. "Ku yafemin, ka nemamin yafiyarta don Allah ko zan ga daidai a rayuwata." Kafaɗunsa Dr Awwab ya dafa. "Haƙiƙa da a irin rayuwar da na sanka na sake ganinka zan ji baƙin ciki da takaici rashin shiryuwarka, amma babu tantana na ga dana sani sosai a tare da kai. Ina jin baƙin ciki da haushinka na wanda ya ƙetawa matata mutunci bazan ɓoye maka ba, amma babu yadda na iya haka Allah ya ɗaura babu yadda muka iya. Maganar yafiya kuma zan tayaka roƙarta. Idan ta yafe maka walillahil hamd." "Na gode sosai. Allah ya ku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba." Faɗin Mufid na share hawayensa. Sai yau ya ji wani sanyi a zuciyarsa tun abun da ya ma Nuratu, duk da bata ce ta yafe masa ba amma yana sa ran albarkacin mijinta za ta yafe masa. Sauƙar abu ya ji sama hannunsa ya sa shi dubawa. Kuɗi ne me yawa Dr Awwab ya damƙa masa. "Ka kula da kanka, sai wani lokaci." Daga haka ya juya ya koma mota. Cike da mamaki da karamcin wannan bawa ya bisa da kallo. Lallai wasu basa saka sharri da sharri sai alheri da sharri da zai saka mutum da na sani. Da ana haka da an daina yawan bibiyar mutum da sharri. Ciki ya koma jiki a sanyaye bayan ya ƙirga kuɗin dubu hamsin ya saka a aljihunsa yana murna, rabon da ya samu kuɗi me yawa har ya manta, dan kuɗin sallamarshi aiki dubu gome ne a wata. 'Lallai yau Daddy da Ummu za su ci daɗi.' Ya faɗa yana shiga cikin shagon. Wai yau shi Mufid ke murnar samun dubu hamsin, abin da shekarun baya bai kuɗin askin sa ba ko yankan farce. Tun da yaga ba shi da mafita a rayuwa ya bazama neman aiki, inda Allah ya taimake sa ya samu kula da shagon ana sallamar sa, duk da aikin ba wani aiki bane sai kula da customers da kai musu kaya mota. Allahamdulillahi hakan ma yana jin daɗinsa domin gidansu ya zama kowa shi ya ɗauki nauyin kansa hatta abinci. Mazajen yaran Alhaji Kashim Mufid suna bawa gidansa taimako daidai gwargwado da abin da Allah ya basu dan taimakawa surikin su da ahlinsu. Alhaji Kashim da Hajiya Hindatu rayuwa ta musu juyin waina, babu kuɗi babu mulki duk sun yi sanyi. Hakan ya dasa tausayin su a zuciyar Mufid har ya zamto komai ya samu sai ya basu rabon su. Hajiya Batul ta aurar yaranta biyu saura Suwaiba. Iyayenta da yayunta masu akwai su suke taimaka mata da wasu kuɗin buƙata. Rayuwa kanan, Allah ka mana kyakkyawar ƙarshe. Ameen! ... Tun da su ka ɗauka hanyar gidan Mami babu wanda ya yi ko tari, sai lokaci zuwa lokaci Nuratu ke sharar hawaye. Ita kanta ta rasa na menene, ba na ganin Mufid ba bana tausayin sa. Bayan Dr Awwab yayi fakin tana shirin fita ya riƙota, ta ɗago za ta masa magana ya ɗaura bakinsa saman nata, idanu ta rufe tana jinsa yana yadda yaga dama, ba ta hanasa ba kusan mintuna har ta samu nutsuwa ta fara mayar masa da martani kafin ya saketa ya rumgumeta suna sauƙe ajiyar zuciya. Sai da ya ga ta daidaita kafin ya saketa ya shafar fuskarta. "Muje ko." Kai ta ɗaga masa suka fita, shi ya ɗauki kayan ita kuma ta ɗauki ledar suka shiga da sallama. Mami tana ɗaki Suwaiba tana kallo ta ji sallamar. Amsawa ta yi ta bisu da kallon rashin sani. "Su waye ku?" Ta tambaya tana yatsine fuska. Nuratu da mamaki ta dubeta ita ma cikin rashin sani. Sannan ta duba Dr Awwab tace. "Mu shiga Doctor." Tare hanyar Suwaiba tayi tana hararar Nuratu. "Ku shiga ina. Hajiya tana hutawa tace kar a tasheta..." Ba ta rufe baki ba Nuratu ta hankaɗata gefe dama a cike take, ta yi tangal tangal da ƙyar ta dafa kujera ta bi bayanta ganinta nufi hanyar ɗakin Mami. Dr Awwab dai murmushi yayi yana mamakin ashe ta iya faɗa. Da gudu Nuratu ta ƙarasa gadon ta faɗa jikin Mami da take zaune bakin gado tana duba wasu kaya a iPad ɗinta da za'a mata sari a ƙasar Turkiyya. Ba za to taji hakan ta ɗago a tsorace, sai dai ganin Nuratu ya bata mamaki. A ruɗe take tambayarta me ya faru. "Gurinki na zo ai, tare muke da Doctor." "Haba dai..." Suwaiba da ta shigo ta rissina. "Hajiya na hanata ta shigo." Murmushi tayi ta ce. "Babu komai Suwaiba Auta ce." Da mamaki Suwaiba ta kalli Nuratu ai kuwa saƙon harara ta sanu tana yatsine fuska. Rissinawa tayi ƙasa. "Ina wuni Autar Mami." "Lafiya." Tace ta kawar kanta, ganin haka ta fita simi simi, tasan ita ce me laifi. Mami kallon ƴarta tayi. "Me ya faru na ga kin ɓata ran ganinta." Ta san dai Nuratu ba kasafai take nuna abu ba. "Bata da kunya Mami, amma bar zancenta. Mu je ku gaisa da Doctor." Murmushi Mami tayi ta ɗauki hijabi ta saka tana mamakinta, babu kunya ta dameta ta je su gaisa da mijinta. A falon suka samesa Suwaiba ta cika masa table da kaya, bai ko kalli komai ba ya ci gaba da kallonsa. Sallamar Nuratu da Mami ya sauƙa ƙasa suka gaisa, Mami tana tambayarsa hanya. Cike da kunya ya amsa mata. Kusan rabin awa yana gidan ganin Nuratu ta samu nutsuwa ya musu sai da safe zai zo ya kaita gidan yayunta da ƙawarta in ta shirya ta ƙirasa. Har mota ta rakosa ta koma. Bayan tafiyarsa Mami da Nuratu suka shige ɗaki sai hira, sallar isha'i ta gabatar ta canza kaya zuwa doguwar rigar marar nauyi da ta ɗauka cikin sabbin kayan Mami na sayarwa, ta ɗale gado tana tayata zaban kayan da za'a mata sari. Sun jima suna hira Nuratu na bata labarin abubuwan da suka faru har ta gangar zuwan Abbanta gidanta, sai dai ta ɓoye dalilin zuwanta yau akan maganar komawarta ne gidan Abbansu. Ita dai Mami shuru tayi tana jinta sai dai ƙasan ranta hakan ya mata daɗi bayan shekaru ashirin da huɗu ya shirya da ƴarsa. Da safe har ƙarfe goman safe Nuratu tana barci, Mami bata tasheta ba dan kanta ta tashi ta shiga wanka. Suwaiba tun safe ta haɗa breakfast mai rai da lafiya dan wanke kanta gurin Autar uwargidanta. Ko ta kansa Nuratu bata bi ba ta shiga kitchen ta dafa indomie ta fito ta ci. Suwaiba kamar tayi kuka ta durƙusa ta gaisheta. Lafiya kawai ta amsa da shi ta jawo wayarta ta ƙira mijinta. Yana cikin shirin fita ya samu ƙiran, da sauri ya ciro ya ɗauka. "My sweetest baby girl." Rai ta ɓata tana tura baki. "Bayan sai da na neme ka?" "Sorry Sweet amini afuwa. Gani tafe." "To sai ka zo." Kit ta kashe wayar bata bari ya ƙara magana ba. Ƙiranta yayi ta ƙi ɗauka ya hakura ya fita. Gidan ya nufa, bayan ya shiga suka gaisa da Mami ta koma tana masa godiyar kaya. Da ƙyar ya ci abincin da Nuratu ta kawo masa kafin ta shiga tama Mami sallama za taje gidan yayunta sai ta dawo. Murmushi kawai Dr Awwab ya yi ya fita. Gidan Aunti Rahma suka fara zuwa, bayan sun gaisa ta ja Nuratu ɗaki, kayan gyara nasha da ke cikin fridge ɗinta su dangin kayan itace ta kwaso wanda ba'a rasa abubuwan da aka saka ciki ba ta bawa Nuratu. Sai da ta shanye tas ita ma ta ji zagi kafin ta barta. Ta haɗata da turaren kwanaki. Mintunansu ashirin ya ce su tafi, babu yanda ta iya bayan Doctor ya ajiyewa yaranta kyautar kuɗi dan dukkansu sun manta batun tsaraba. Godiya ta masa sosai Aunti Rahma. Daga nan gidan Aunti Hasiya suka nufa, nan ma dai sai da ta haɗa Nuratu da shan natan abun kafin ta barta. Nan na ya yiwa ƴaranta kyauta. Sai gidan Rukayya suna kule ɗaki. "Wai da gaske yarinyar nan kike ba ki da ciki." Faɗin Rukayya dan dai ta ɗauka duk ƙarya take. Dariya Nuratu tayi. "To wai yaushe aka yi auren. Ko wannan watan nayi period." "To Allah yasa kar ki wuce next." A zuciyarta ta amsa a fili bata amsa ba ta miƙe tana ɗaukar handbag ɗinta. "Idan babu abin da za ki bani zan tafi." Fahimtarta ya saka Rukayya yin dariya. "Yarinya ta shigo gari." Dariya Nuratu tayi bata ce kala ba, wasu kayan fruit da ta ma haɗi dan kanta ta saka a fridge ya yi sanyi ta ɗauko ta bawa Nuratu. "Kinga wannan haɗin fruit ne zalla. Yarinya sai na ji ƙira." Sosai Rukayya ta koro mata bayani tana sha, tas ta shanye dan taji daɗinsa. Bayan ta gama ta miƙe. "To na gode. Sai wani lokaci." "A dai tausayawa Doctor. Sannan ayi jarumta, dan nasan su Aunties sun cika ki da nasu." Faɗin Rukayya dariya. Dan tasan me raba Dr da Nuratu yau sai Allah, yadda kowanne ya bata gudunmowarsa. Burin su tayi daraja da mutunci idon mijinta, tausayinta suke ji. Ita ma ya mata kyauta. Gidan Walida ne ƙarshe ita ma sunsha hira tana ta tsokanar Nuratu, dariya kawai take tana cewa ke ce abin tsokanar dubi ciki duk ya mayar da ke ƙatuwa. Sun ɗan yi hira ta mata sallama, ita ma Doctor ya bata nata kyautar.  Bayan sun fito ya ce sai ina. "Gidan ƙawata Rufaida." "Wacece ita?" Dan shi ya ɗauka bata da ƙawaye sam sai ƴan uwanta. "Za ka santa." Daga haka ta dinga masa kwatance har kofar gidan yayi fakin. "Bazan jima ba yanzu zan fito. In kuma zamu shiga." Kai ya ɗaga mata ta fita ta shiga, da sallama ta shiga cikin gidan. Rufaida da ke fama da cikinta ta fito jin yadda zuciyarta ya buga da taji muryarta tamkar a mafarki. Ido biyu suka haɗa. Murmushi suka sakarwa juna dan tsakani da Allah suna kaunar junansu. Da sauri Rufaida ta isa wajen Nuratu ta rumgume tana fashewa da kuka. "Nuratu ke ce, dama za ki neme ni." Ita ma cike da kewar ƙawarta ta kamo hannunta. "Ni ce Rufaida, ya gida ya bayan rabuwa." "Lafiya lau, mu shiga ciki." Bayan sun zauna suka sake sabon gaisuwa, Rufaida ta rasa me za ta yi wa Nuratu ta faranta mata. Ta cika gabanta da kayan ciye ciye. Ganin ta kasa nutsuwa ta kamo hannunta ta zaunar. "Ya isa Maman Baby kar ki wahalar mana da shi." Murmushi Rufaida ta yi tace. "Ya wajenki? Fatan lafiya?" "Lafiya lau. Ba ki neme ni ba kema?" "Ina son zuwa wajen Mami amma kunya da tsoronta nake ji." "Haba dai, ko da Mami bata riƙe ki ba balle ni. Komai fa ya wuce Rufaida. Ina ɗayan Babyn mu." "Sun fita da babanta." Shigowar mijin Rufaida da Babyn da kuma Dr Awwab suka basu guri. "Ke kuma za ki bar miji a shanye." Ya faɗawa Nuratu cikin zolaya, dan kallo ɗaya ya mata ya gano ita ce wacce kullum Rufaida take maganarta. "Zamu wucene." Ta faɗa tana gaishesa ya amsa. Ba su jima ba suka musu sallama bayan Nuratu ta ɗauki Babyn Rufaida ta mata kyauta. Rufaida na ta godiya har da hawayenta ta musu rakiya. Nurata tana jaddada mata ta faɗa mata idan ta haihu, suka yi musayar lambar wayar. Sun ɗauki hanya Dr Awwab ya dubeta. "Wacece ita Baby, sai dai kamar nasa fuskarta." "Ƙawatace kut da kut, sai dai ƙaddara ta rabamu wanda take ganin samuwar ƙaddarar rayuwata da saka hannunta." "Ki mini bayani. Ban fahimta ba." Ya ce dan sam bai fahimci zancenta ba. Rana ta farko da Nuratu ta so bawa Dr Awwab labarin wacece ita tun farko har zuwa inda ya sani. Ta sanar da shi menene tsakaninta da mahaifinta, ta ba shi labarin yadda Mufid da abokansa suka lalata mata rayuwa. Da irin gudummawar da Col. Ahmad da Yaya Al-ameen da shi kansa suka bawa rayuwarta. Ƙarshe ta sanar da shi Rufaida ƙanwar Mufid ne. Tana yi tana hawaye har ƙarshe, bayan ta gama ta yi dariyar taƙaici. "Amma komai ya wuce dalilin samunka a rayuwata, ka maida duhuna haske, ka maye soyayya da gurbin tsana da yake cikin zuciyata, ka kyautatawa rayuwata, ka nuna mini so da kauna, ka nuna mini nima macece tamkar kowa me daraja da ƙima. Ta ya bazan kauna ce ka ba?" Shuru kawai Dr Awwab yayi bai yi magana ba illa hannunsa ɗaya yasa ya jawota jikinsa ya rumgume. A haka suka isa harabar hotel ɗin. Kashe motar yayi ya juya ya rumgumeta tsam a jikinsa. "Komai ya wuce tunda komai ya daidaita, ki daina tuna baya. Ina kaunarki sosai." Sun jima haka kowanne na sauƙe numfashi. Dr Awwab mamaki kawai yake cike da al'ajabin rayuwar da Nuratu ta gudanar, bai taɓa tsammani haka nata rayuwar yake ba. Lallai ta ga rayuwa tun tsowarta bayan fyaɗe da aka mata. Kusan sakanni ya saketa suka fito ya riƙo hannunta suka nufi cikin hotel ɗin. Bata ma lura hotel bane sai da suka shiga ciki. 'Ko me ya kawosu kuma nan.' Ta tambayi kanta da mamaki. ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  58. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Har ɗakin da ya sauƙa ya musu jagora su ka shiga ciki, bayan sun yi wanka ya musu odan abinci. Daga nan sai barci dan huta gajiya. Washegarin ƙarfe goma suka je har gidan Mami da Amma Jidda suka musu sallama, sannan sai shagon Abbanta. Ta yi murna sosai ganin kasuwanci ya ƙanƙama. Ƙarfe sha biyu suka bar cikin Damaturu cike da kewanr ƴan uwanta, sai ta waya ta musu sallama. Kai tsaye gidansu su ka sauƙa duk roƙonsa da take yi masa su fara biyawa gidan Ummi yace a'a yana da uzuri. Yana shiga yayi fakin ta fice ta barsa, da sauri ya buɗe motar ya fita ya bi bayanta. A falon ya sameta ya ɗauketa cak suka nufi sama. "Muje in duba." Yace ya nufi ɗakinsa da ita. "Me kuma?" Ta faɗa da mamaki. Ido ɗaya ya kashe mata yana buɗe ɗakinsa suka shiga. Bai tsaya ko ina ba sai saman gado ya kwantarta yana ƙoƙarin ɗaga doguwar rigar jikinta. Da mugun mamaki ta riƙo hannunshi. "Me haka Doctor?" Kansa ya ɗago yana faɗin. "Dubawa zan yi inga ko ya tafi. Ke fa ki ka ce in duba." Sam ta manta da ta faɗa hakan. Karyar da wuya tayi a maraice ta ce. "Ni wasa nake maka. Kuma kai ba likitan mata ba ina kai ina dubawa." "Dan ina likitan ƙwaƙwalwa ai ni likitan matata ce. Bayan hakama duk namiji shi likitar matarsa ce, balle ma ko da likitan ƙwaƙwalwa na ke ina da damar taɓaki." "To na ji, yanzu ka yi hakuri." Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa ya hanata. "Ai sai na dubata." Bai bata damar motsi ba ya yaye doguwar rigar ya duba. Ganin da gaske babu shi babu alamar sa ya sa shi tun daga nan ya fara aika mata sakonsa. Luf tayi tana jinsa har ya ɗago ya haɗa bakinsu. Daga nan suka buɗe shafin so da ƙauna. Ranar ta banu hannun Dr Awwab, sai da ta fara masa kuka abun da bata masa kenan. Ashe gaskiyar Rukayya da tace ta yi jarumta, bayan hakama ita ta jawowa kanta yadda duk wanda ya bata abu sai ta ɗura a cikinta har da neman ƙari wajen Rukayya. Aikuwa da ƙyar ya barta, ta gurzu mutuƙa a gurinsa. Barcin wahala ne ya kwasheta sai wajen ƙarfe huɗu ta farka da kukan shagwaɓa, shi ya dinga lallaɓata ta samu tayi wanka ta fito ta zurma riga marar nauyi ta gabatar da sallah. Abinci kam sai takeaway ya musu suka ci. Washegari Dr Awwab ya wuce aiki bayan ya dameta da fitinarshi ta samu ta korasa. Tun lokacin kusan kwana huɗu bai samu zama sosai ba dan aiki da yake tukuru, haka ya cinye satin kafin ya samu nutsuwar ruhi. A gida suka cinye hutun ƙarshen mako babu inda ya je ko ya bar Nuratu ta fita, sabuwar amarci yake yi. Ranar Litinin yasa ta shirya suka fita, passport ya kaita aka mata kafin ya dawo da ita gida. Tun a hanya take masa magiyar ya kamata Hanan ta dawo. Murmushi yayi yace. "Za ta dawo ba yanzu ba amma." "To wai me yasa?" "Akwai suprise da zan miki." "Suprise?" Ta tambaya, kai ya ɗaga mata. Haka suka isa gida ya sauƙeta ya koma aiki. Bayan kwana biyu da maganar har ta manta wani ranar laraba da karfe biyu ya dawo gidan. Tayi mamakin dawowarsa da wuri, bayan ta taimaka masa yayi wanka ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya. Abinci ta gabatar masa ya ci kafin ya ce ta haɗa kayanta da nasa akwai inda za su je. Babu musu ta haɗa musu cikin babban akwati. Bayan ya gama ɗaukar wayarsa da mukullin mota ya kashe komai na wuta ya sameta a ɗaki ta gama. "Muje ko." Ya faɗa yana jan akwatin, ta ɗauki mayafinta babba ta rufe jikinta suka fita. Ita dai ta kasa tambayarsa ina za su je. Haka suka shiga motar bayan ya gargaɗi me gadi ya kula da gidan kafin su bar gidan. Hanyar gidan Ummi suka yi, sun gaisheta anan ta samu labarin za su yi tafiya, sai dai bata san ina ba. Sallama suka musu suka fito akan sai sun haɗu acan. Anan ya bar motarsa drivern Ummi ya kai su airport. Nuratu baki buɗe take bin gurin da kallo. 'Tabbas airport ne.' Ta faɗa a ranta suna shiga ciki. Bayan an gama musu komai suka shiga cikin jirgin suka zauna. Nuratu kallon Dr Awwab kawai take. Ganin tana buƙatar amsa ya sa shi saƙale yatsun hannunsa cikin nata. "Suprise My Baby." Murmushi tayi har dimple ɗinta ya lotsa, ta matse yatsun hannunsa. "Thank you Hayat. Amma ina za muje?" Hannunta ya kai bakinsa ya sumbata. "Dubai zuwa honeymoon." "Dubai dai ni Nuratu." Tace da tsantsan mamaki. Kai ya ɗaga mata yana murmushi. "Ban tambayeki ra'ayinka ba sorry." Naushi ta kai masa a damtsen hannunsa hawaye na silalowa bisa kumatunta. "Ka shammace ni sosai but zan rama. Na gode sosai Noor Hayat." Hawayenta ya share mata yana cewa. "No need My Noor Hayat." Daga nan jirginsu ya lula ƙasar United Arab Emirates ƙarƙashin birnin Dubai. Hotel mai kyau mai tsada ya kama musu, bayan sun huta sai barci. Tun ranar suka buɗe sabuwar rayuwa, soyayya suke gwadawa junansu tamkar su haɗiye juna, da dare ko yamma su zaga gari. Duk wani kunya Nuratu ta ajiye a gefe ta fara kula da mijinta. ... Can Nigeria kuwa yau safiyar juma'a Mami ta samu baƙoncin Yayanta, ta karramasa sosai suka yi ta hira har suka gangara hiran Al'ameen da Hafiza da aka saka biki bayan sallar azumi da sati biyu. Dalilinsa ya zo faɗamata har take cewa da ya mata waya ai, ya ce babu matsala. Daga nan masallaci ya nufa tare da uzurin da ya kawosa. Tafiyarsa da mintuna goma yaran Mami suka iso gidan. Fitar Kawu Muhammadu bayan an idar da sallar juma'a ya yi uzurin da ya kawosa ya koma gidan Mami. Tare da yaran gaba ɗaya a falon an haɗa Suwaiba da reno a tsohon ɗakin Nuratu. Bayan gaisuwa ya zaro kuɗin aljihunsa dubu hamsin ya ajiye gefen Mami. "Sadakin kine Sadiya, bayan fitana ko ince dalilin zuwana kenan, na miki wakilci an ɗaura aurenki da miji ko mutumin da nake ga shine daidai da ke. Wannan zaman ba naki bane haka Sadiya, yaranki ba sa jin daɗin zamanki haka, haka ni ma. Kuma ko ba komai mutane za su yi ta magana har da masu ƙazafi, don haka na zaɓa miki rayuwar aure akan wannan rayuwar na kaɗaice. Allah ya ba ki sa'ar ma mijinki biyayya, ki zama mace ta gari tamkar yadda na sanki. Allah ya ba ku zaman lafiya." "Ameen." Yaran suka amsa banda Mami duk bata saurara sauran maganganunsa ba, burinta ya sanar da ita waye ya aura mata. Ita dai da aure, da girmanta da yara har da jikoki. Kawu Muhammadu ne yaci gaba da cewa. "Sati biyu masu zuwa za ki tare, mun riga mun gama magana da shi. Zarah da makota za su miki rakiya. Mama wuro za ta zo ta taimaka miki da wasu shirye shiryen sai kuma su Rahmatu suma gasu nan." A hanzarce Mami ta dubesa. "Sati biyu dai Yaya? To waye mijin?" Sai lokacin ta samu bakin yin magana. "In kin je za ki gansa. Kinga tafiyana ina son isa gida duk dare. Sai munyi waya." Daga haka ya miƙe ya musu sallama Muhsin ya kaisa tashar mota, ya biya masa kuɗi ya basa kuɗin shan ruwa. Bai so karɓa ba dole ya sa shi amsa. Mami ta kasa zaune ta kasa tsaye duk wanda ta tambaya ko yasan da labarin sai yace a'a, balle su san wanene mijin. Duk ta zama shuru shuru har dare ya yi suka mata sallama bayan Rahma da Hasiya sunyi ta kwantar mata da hankali. ... Cikin sati biyun Mami ta yi su cikin fargaba, har wani rama tayi. Aunti Zarah ta zo sunyi maganar sai dai duk hasashe sun kasa gano wanene. Har Aunti Zarah tana ce wa. "Ko dai Abbansu Rahma ne." Girgiza kai tayi ta ce. "A'a, duk wulaƙanci dana masa bana zaton haka. Amma dai." "Menene?" Aunti Zarah tace. Nan Mami ta sanar da ita yadda suka yi da Nuratu kamar yadda ta sanar da ita. Shuru Aunti Zarah ta yi can tace. "Amma ai bata miki maganar kome ba tunda bai mata ba. Kinga kuwa ba shi bane. May be shi ma ko ba shi da labari." "Hakane kuma fa. Ni koma waye fa sai dai ya gaji ya rabu da ni." Tace cikin fushi. ... Washegari Asabar Mama Yawuro ta iso gidan da Hafiza. Da yamma yaran Mami suka iso dan kwana za su yi. Tun daren suka fara shirye shiryen haɗamata kayanta da duk abun buƙata, mota babba da mijin ya aiko ya ɗeba ya kai gidanta. Da ƙyar Aunti Zarah da Rahma suka saka Mami yin jan lalle, Hafiza ta mata ƙananan kitso a gashinta me tsantsi da tsayi. Ban da haka babu abun da ta yi, amma ta yi masifar ƙyau, ta saka lecca da ya amsa sunan sa lecca, ya zauna a farin fatarta ya haskakata, kana ganinta kasan amaryace tamkar kowacce amarya ranar bikinta sai tayi sheƙi, haka Mami ma. Yaranta sai hotuna suke mata suna yi tare. Sai dare ƙarfe takwas motoci kusan biyar suka zo ɗaukar amarya. Kaf sai da suka kaita har gidanta cikin ɗakinta. Wasu suka zauna anan wasu suka koma gida dan gyarawa. Yaran tun da suka ga gidan da Maminsu ta shiga murnarsu ya ƙaru. Ango bai shigo ba sai ƙarfe goma bayan ya gama lallashinta uwargidansa da duk ƙoƙarinta ta danne kishinta kasawa tayi sai da ta zubar da hawaye. Bayyanarsa falon me cike da tarihin da baya son tunawa ya saka mutanen ciki dubansa. An gyara falon da komai na zamani an ƙawatasa ya zamto tamkar falon amarya ƴar sha takwas. "Sannunku ina wuni." Ya faɗa yana ƙarasawa ciki. A hanzarce ta ɗago ta dubesa jin muryarsa, idonsa tar a kanta. Nata idon ta janye cike da baƙin cikin da ya taso mata. "Abba bismillahi, ko in maka jagora." Faɗin Rukayya tana tasowa ta riƙo hannun Abbansu ta shigo da shi falon. Saman kujera ta zaunarsa kusa da Maminsu ta koma gefe. Cikin dabara ta dinga musu hoto tana dariya. Bayan tsawon lokaci iyayensu sun kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya. Doguwar nasiha Aunti Zarah ta musu mai kashe jiki, kafin su musu sallama zuwa ɓangaren baƙi aka bar amarya da angonta. Bayan watsewarsu falon ya ɗauki shuru tsawon mintuna. "Sai kuma ki ka ga bazata ko Sadiya?" Matsawa Mami tayi tana masa wani mugun kallo. "Kar ka ga ka mini fin ƙarfi ya tabbatar maka ko na yarda. Har abada ba zan ƙara amincewa da kai ba." "Na sani amma ki ƙara bani dama don Allah." Ya faɗa yana kamo hannunta. Da sauri kuma ya sake jin sabon abu ya ziyarce sa. Mami ta shi tayi, ɗaki ta shige ta bar zauna dan wani iri ta ji lokacin da ta ji saukar hannunsa a nata. Ya jima zaune kafin ya koma sashinsa yayi shirin barci ya kwanta, baya son takura mata sam. Ganin bai dawo ba ita ma ya sata shirin barci ta kwanta. Washegari kowa ya gama shiri suka haɗa Amma Jidda da Mami suka musu nasiha da sallama suka tafi. Mamin kunyar Amma Jidda take ji sosai, gani take bata kyauta mata ba duk irin ɗawainiya da yaranta da tayi. Fahimtar haka ya saka Amma Jidda ajiye kishinta a gefe ta ƙara shiga jikinta, tasan dai ba dan ƙaddara ba, da tsawon lokaci tana matsayin matarsa, bayan haka ga yaransu. Kwana biyun Alhaji Mamman ya kasa gane kan Mami duk hanyar da zai bi ya yi ta ƙi yarda masa. Zai sameta suna hira da Amma Jidda amma da zaran ta gan sa take barin gurin. Amma Jidda dai ido ta saka musu, tasan komai daren dadewa za su shirya kansu. ... A haka aka soma azumi bayan sati biyu daa tarewarta. Har lokacin babu wani shiri tsakanin ma'auratan, Mami fa ta kasa ta tsare, tsakaninta da Alhaji Mamman ta girka ta basa. Shikam har wani rama yayi dan ya kasa gane kanta fa. *** Ɓangaren Dr Awwab da Nuratu har azumi suna can suna amarci. Sunyi kyau dan tsabar hutu, danma Dr Awwab yawanci yana aiki ta hanyar kwamputa. Duk abun da ya faru Nuratu tana da labari duk da kowa ya ƙi sanar mata. Sallar azumi saura kwana goma suka tafi Umrah daga nan za su koma gida Nigeria. Hakan kuwa aka yi, acan suka samu Ummi da Hanan hatta ƴan biyu sun zo Umrah. Murna gurin Nuratu ba'a cewa komai, nan ta tattara ta koma ɗakin ƴan biyu duk kashedin Dr Awwab. Dole ya hakura ya barta dan suyi ibada mai kyau. Tun lokacin suka dage da yin ibada hatta Hanan. Anyi sallah da kwana ɗaya suka dawo Nigeria, a gidan Ummi suka yada zango. Bayan an gyara musu gidansu washegari suka tafi. Tun da suka dawo Nuratu take roƙon Dr Awwab ya barta ta je Niger auren Hafiza saura kwana uku Mami da yara za su tafi. Shikam dai ganin yadda tayi wani haske da kyau kallon mai ciki ya ke mata, dalilin da ya sa baya son yawan zirga zirganta. Amma yadda yau ta sa shi gaba da kuka ya sa shi cewa ta shirya zai kaita da kansa. Murna har da tsalle tsallenta. Da sauri ya riƙota. "Ki yi a hankali kar ki mini asara, na yi wahala kafin na samu." Da mamaki tace. "Asara me kuma? To na bari." Hancinta ya lakace ganin bata fahimcesa ba ya rabu da ita. Da taimakonsa ta haɗa musu kayansu dan yace ƙafarta ƙafarsa. Washegari sai Damaturu ta samu duk an shirya za'a wuce har Abbansu da za su je ɗaurin aure da dangin mahaifin Yaya Al-ameen daga Zaria. Keɓewa Nuratu da Abbansu ta yi bayan gaisuwa suka tattauna kafin su wuce. Kowa yayi mamakin ganin bata damu ba da maganar auren iyayenta ba, hasalima babu wanda ta ma magana hatta Mami da ta ke wasi wasi kar ƴarta ta ga bata kyauta mata ba. Tafiyar ta kasance Mami da Alhaji Mamman motarsu daban. Ɗayar motar da Abbansu ya basu Aunti Zarah, Aunti Hasiya, Rukayya, sai yaransu. An bar Ameera a gida da Abba ya haɗawa zafi akan ana gama auren ta ciro mijin aure. Amma Jidda kuma da Aunti Rahma an barsu a gida dan kula da baki, Walida ciki ya girma ya sata a gaba dole ta zauna, don ma ana ɗaura auren za su juyo su taya Amma Jidda hidima sauran. Mami ma badan dole ba, don ƴar yayanta ne ba zata ba. Motar Dr Awwab kuwa daga shi sai matarsa suna tafiya suna shan soyayya. Shigar yamma suka yi gidan cike da baki, Kawu Muhammadu ya rasa ina zai saka ƙanwarsa da ahlinta. Abinci kala kala aka kawo musu, masauƙi daban daban aka bawa Alhaji Mamman da Dr Awwab. Washegari ango da yan uwansa suka iso da abokansa ciki har da babban abokin ango Col. Ahmad Tafida, anan suka haɗe da Dr Awwab. Ga mazan Yayun Nuratu anan suka fara haɗuwa suka gaisa. Ƙarfe sha daya aka shaida ɗaurin auren Muhammad Al'ameen da Hafiza Muhammad. Bayan ɗaurin auren aka buƙaci tafiya da amarya. Dole aka basu bayan doguwar nasiha da tasha, suka kama hanyar komawa. Bayan isarsu gidan Amma Jidda aka kaita dan za su yi event kafin ya ɗauki amaryarsa su wuce Zaria wajen aikinsa. Hakan ko a kayi da yamma suka yi dinner. Amarya tayi kyau haka ango ma, sai yan uwa masu anko, Nuratu ma ta samu sun ɗinka mata ta saka. Dr Awwab ne ya kaita bata bi motar kai kawaye ba ko bin yayunta ba. Bini bini ya hanata motsi hatta kari tare suka yi yana tareta kar wani ya ganta, haka suka koma wajen zamansu. Bayan an tashi kowa ya watse suka koma gida. Bayan Nuratu tayi wanka taci abinci ta dale gadon Maminta. Rukayya ana can ana sallama da miji da ya ɗauke daga wajen dinner ya dawo da ita gida, shigowar da ba tayi ba har yanzu, Aunti kuma suna falon Mami kowa yana faɗar hiransa akan yadda bikin ya gudana. .. "Mami za muyi magana idan kin gama." Faɗin Nuratu tana kai dubanta gurin Maminta. "Magana kuma Auta? Lafiya dai ko?" Ta tambaya dan gudun faɗawa tambayar me yasa ta aikata haka bayan abin da ya faru. Girgiza kai Nuratu tayi ta sauƙo a gadon ta zauna kusa da Mami. "Mami me ya sa kike wa Abba haka? Ko har yanzu ba ki yafe masa ba? Don Allah ni kam idan dan ni ce na hakura ki bar komai. Ko kin san ni nasa Abba ya aureki kai tsaye tun bayan da ya nemi yardarki ki ka ƙi. To ranar da za muje Nijar munyi magana da shi ya sanar da ni duk irin zaman da ku ke. Ni kam idan ta ni ne kiyi hakuri don Allah ki sassauta masa." "Kece Nuratu?" Mami ta tambaya da mamakinta. Kai ta daga mata. "Tun bayan ya nemi yafiyana na yafe masa nuna waya har ya sanar da ni buƙatarsa, anan na basa shawara kawai ya samu Kawu da maganar, ya sanar da ni sunyi magana da Kawu kuma Kawu yace sai da yardarki. Ni kuma yadda fahimta ke ba za ki taɓa yarda ba. Shi ne kawai na ƙira Kawu na sanar masa komai. Daga nan shi ne Kawu ya zo aka ɗaura auren, kuma ya ɓoye miki wanene akan sai an kai ki. To sai ga shi Mami kin ki kwantar da hankalinki kamar yadda mu kayi fatan idan kinga inane gidan auren za ki hakura." Bayan ta gama bayanin, Mami ta kai hannunta fuskar Nuratu ta dan bugi kumatunta. Babu alamun ɓacin rai a fuskarta. "Autar Mami ta girma ta yi hankali." Murmushi Nuratu ta yi ta ce. "Kin yarda za ki kyautatawa Abbanmu." Kai ta ɗaga hakan ya sa Nuratu ta faɗa jikinta ta rumgumeta tana murna. Mami kam mamaki yake yadda uba da ƴar suka fara faɗawa juna sirrinsu bayan tsawon shekaru. Ringing ɗin wayarta ya sata sakin Mami ta ɗauka ta ga mijinta ne. A gaban Mami ta fara zuba masa shagwaɓa, haka yasa Mami ta lallaɓa ta bar mata ɗakin. Sun jima suna waya kafin ta kashe ta kwanta. Murmushi take yi yadda duniyarta ya canza lokaci ɗaya. Ta yi aure ta samu miji nagartacce, mai ilimi addini da boko, mai dukiya mai albarka, kyakkyawa mai kyakkyawar zuciya. Iyayenta sun koma rayuwarsu tamkar babu abin da ya faru. Komai ya wuce tamkar babu abin da ya faru sai an sanar maka. ... Washegarin ango ya ɗauki amaryarsa suka wuce, Aunti Rahma da Hasiya sun bita ganin ɗakinta dan bata da yayu mata. Duk yadda Nuratu taso zuwa Dr Awwab ya hanata. Ƴan biki kuwa ƙarfe sha biyu suka watse ciki har da Nuratu da Dr Awwab ya ɗauka sai fushi ta ke. Bayan biki da sati ɗaya Alhaji Mamman ya ga canji wajen Mami. Tun lokacin suka buɗe sabuwar rayuwa, a lokacin ta basa damar yin amarci, aikuwa yana amarcinsa yadda duk yabi ya nane mata. Sun mance da komai duk da lokaci zuwa lokaci abin yana faɗowa Mami a rai, haka shi ma amma suna dannewa. Burinsa ya faranta mata ya kyautatawa rayuwarta. Kwata kwata baya son ɓacin ranta dan yasan ya wahala kafin ya sameta kuma. Tsakaninta da Amma Jidda suna zaman lafiya. Ameera kam tuni ta koma bangaren Mami ganin iyayenta har lokacin sun kasa sake mata fuska. Abba ya sake mata maganar aure, Mami tace ba yanzu ba karatu za tayi, tun da tayi nadama kuma ciki har da sharrin ƙawaye. Dole ya hakura ya barta taci gaba da sharaɗin tana gamawa sai aure, ta ce ta yarda. Ameera murna harda kuka, tayi ta godewa Mami da yabawa karamcinta. Sai lokacin take jin haushin kanta na rashin fahimtarta da bata yi ba ita da Nuratu. Rayuwar gidan ya dawo sabo. ... Bikin Hafiza da wata ɗaya aka tsaida wata biyu akan ranar auren Hassana da Abdallah, Hussaina da wanda ya tako har gida ya sanar da Dr Awwab yana sonta. Yarda da shi da kuma sanin wanene ya sa shi basa aurenta kai tsaye. Hassana da Abdallah dama suna son juna. Hussaina kuwa tashin hankali ta shiga da jin yayanta ya bada aurenta ga wani wanda bata sani ba. Kuka take yi kullum ta kasa kwantar da hankalinta duk ta rame dama ba wani abincin kirki take ci ba. Hassana ma kanta sai ta ji wani iri. Ummi kaɗai Dr Awwab ya sanar da ita wanene, kuma ya hanata fadawa musu duk da yasan da wuya su san sa. ... Komai yayi farko. #vote #comment. #share MADUBIN GOBE  59. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** Tun da kwanakin bikin ya rage saura kwanaki hankalin Hussaina ya ƙara tashi, ta yi kukan t ayi har ta gaji, ta roƙi Ummi ta saka Dr Awwab ya janye ƙudirinsa ya ƙi, ta je da kanta ta samesa ta sa shi a gaba tana kuka ya ƙi sauraronta, sai ma faɗa da ya rufeta da shi yana cewa ai ba zai mata zaɓin da zai cutarta ba. Haka ya ƙara tada hankalinta ganin babu me sauraranta sai Hassana. Mai gyaran da Ummi ta ɗauko take musu da ƙyar take lallaɓata ta yi mata, duk ta rame sai haske. Kayan baƙin cikinma angon bai ƙirata ba balle suyi maganar biki ko event. Kuma jiran ƙiran sa take ta zuga masa rashin mutunci. ... Yau talata ƙarfe uku suna zaune Dr Awwab Nuratu yasa ka a gaba ya koma kalar tausayi, tun da ta sanar da shi bata sallah. Ita ma ɓangarenta tasan dai babu cikin, amma yadda ya nuna damuwarsa sai ta ji babu daɗi, tana buƙatar hakan ko dan faranta masa. Aure kusan wata huɗu. Kallonsa ta yi ta matsa kusa da shi ta kwantar kanta saman cinyarsa tare da laliɓo hannunsa ta rumgume a kirjinta. "Hayat ka daina damuwa, Allah zai kawo a lokacin da ba muyi tsammani ba." "Na sani Babyna, kawai dai na jima ina miki kallon mai ciki a ko wani wata, musamman wannan watan." Murmushi ta yi tana kallon cikin idonsa da yanzu take iya kallo, don yanzu ta fahimci wannan rashin jumurin kallon duk cikin so ne. "Ni ma haka fa." Sunkuyawa yayi ya sumbaci leɓɓanta ya ɗago yana kashemata ido ɗaya. "To ki bada himma next month mu samu." Kanta ta ɗago ita ma ta sumbaci nasa leɓan tace. "Insha Allah Hayat." Lips ɗin ya hanata ɗaukewa ya ci gaba da kissing ɗinta. Door bell da ake dannawa ya dawo da su hankulansu. Wani mugun tsaki ya ja yana sakin bakinta ya koma ya kwanta. Miƙewa Nuratu tayi tana gyara rigarta ta nufi ƙofar fita. Buɗewa tayi ta tsaya tana kallon mai danna door bell din daga sama har ƙasa ta tsayar kallonta kan fuskarta kafin ta ba ta hanya ta shiga falon. Cikin takunta mai jan hankali ta ƙarasa falon tana bi da kallo. 'Lallai munyi asara, amma kissa yafi magani.' Ta faɗa a ranta, har lokacin sun kasa nasara akansa sai asaran kuɗi da suke yi. Nuratu na ƙoƙarin rufe ƙofar drivern Hanan ya shigo gidan. Tana tsaye har ta fito cikin shirin makaranta ta ƙarasa wajenta ta ɗagata sama suka shiga falon. Zuciyarta ne ya buga ganin Binta ta saka mijinta a gaba tana masa hira sai wani fari da ido take yi. Kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta. Ta rasa wacece ita tun ranar bikinta. Kanta ta ɗauke tana wucewa ciki da Hanan. Wanka ta mata ta canza mata kaya suka sauƙo. Samu ta yi Dr Awwab har lokacin yana wajen. Kitchen suka wuce ta zuba mata abinci ta zauna ta bata. Suna cikin haka Dr Awwab ya shigo. "Babyna kinyi baƙuwa ba za ki bata ko ruwa ba." Wani kallo ta watsa masa. "Na santa ne? Baƙuwar ka dai. Wai wacece ma?" Ta faɗa tana tambayarsa ranta a haɗe. "Za mu yi maganar anjima, yanzu ki kai mata ruwa." Ɗauke kanta ta yi daga kallonsa ta miƙe tana ɗaukar Hanan tabi ta gefensa ta wuce. Murmushi yayi ya ƙarasa ciki ya ɗauki ruwa a plate ya koma falon wajen Binta kafin ya bi bayan Nuratu. Ɗakin Hanan ya fara shiga ya samu tana kallo, fita yayi ya wuce ɗakin Nuratu, a saman kujera ya sameta kwance a falo. Sheshsheƙar kukanta ya ji da sauri ya ƙarasa yana ɗagota. A rikici ya fara tambayarta. "Menene kuna Babyna, don Allah ki sanar da ni." Zama ya yi yana rumgumeta. Fizge jikinta tayi cikin kuka. "Ka rabu da ni." "Ba zan iya ba, ki sanar da ni me ya faru?" "I said ka rabu da ni." Ta faɗa da ƙarfi tana ƙwace jikinta. Rumgumeta ya yi sosai a jikinsa ta fashe masa da kuka, mugun kishi ke cin ranta. Sai da ta yi kukanta ta fara sauƙe ajiyar zuciya yana shafa bayanta sannan ya mata raɗa a kunne. "Ƴar uwar mahaifiyar Hanan ne, ban taɓa sake mata fuska balle ta samu gurbi a gurina, ɗazuma kar ki fahimci wani abun ya sani tsayawa sauraronta. But I'm sorry My Baby." Ɗago idanuwanta ta yi da suka yi jajur don kuka. "Really?" "Yeah." Ya faɗa yana sumbatar lips ɗinta. Ba ta bari ya cire nasa ba ta ci gaba da kissing ɗinsa, bai musu ba ya karɓeta. Sun fara sakin layi ta tuna bata da tsarki ta zare jikinta ta kwanta. Ganin haka ya miƙe tsaye. "Bari in sallameta." Kanta ta juyar ganin haka ya fita. ... Da sauri ta bar gurin tana mayar da hawayenta. Tun hawarsa sama ta bisa ta ga me zai yi. Kasa kunne ta yi tana leƙar su ta ga faɗa suke sai dai kasa jurewa tayi lokacin da ta ga Nuratu na kissing ɗin Dr Awwab ya biye mata, bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba. Ganin zai fito ya sata sauka ƙasa, bata tsaya a falon ba ta fita a gidan gaba ɗaya. Bai sameta a falon ba ya koma ɗaki ya samu Nuratu ta rage kayan jikinta za tayi wanka. "In zo in taya ki?" Girgiza kai tayi ta wuce bathroom ta barsa zaune. Har ta fito yana nan yadda ta barsa, kaya ta canza ta fita ta barsa. Ajiyar zuciya ya yi ya fita. Har dare ta kasa sakar masa fuska duk da ta ga zuwan Binta, dalilin kissing ɗinsa da tayi. Da daren bayan ta gama Hanan hidimarta ta kwantarta ta wuce ɗakinta. Wanka tayi ta saka night gown nata ta kwanta. Haka Dr Awwab ya shigo ya sameta. Kansa ya dafe, wannan fushin dai ya ishesa. Wanka yayi ya hau gadon yana jawota jikinsa ya rumgume. Kansa ya tura tsakanin wuyarta ya fara mata magana a hankali, hannunsa a saman cikinta yana shafawa a hankali. "Wai ba ki huce ba, ni kam fushin nan ya ishe ni. Please i said I'm sorry. Wallahi babu komai tsakani na da Binta." Kwanciyarta ta gyara a jikinsa, tana jin daɗin yadda yake mata, iskar da ya hura mata a kunne yafi komai kashemata jiki. Sai lokacin ta buɗe baki. "Idan kana so na huce za ka bani amsar tambayata?" "Ina ya jinki." "Me ya ka ke raba Hanan da dangin mahaifiyarta. Sam na lura ba ka son abun da ya shafe su. Abar maganar Binta a gefe don ni bansan ita ɗin ƙanwar mahaifiyarta bane sai yau. So ka faɗamin Please." Ƙara rumgumeta yayi cikin jikinsa sosai, har ta cire ran zai yi magana ta ji ya fara a nutse tamkar baya so. "Na haɗu da Nusaiba a hanyar unguwar su bayan na kai abokina unguwar, a hanyar dawowana na haɗu da ita cike da buƙatar taimako. Kinsan taimakon me take buƙata?Abinci. Abinci take buƙata da za taci. Ganinta da nayi budurwa da ita tana neman taimako nayi tunanin kar ta faɗa halaka yasa na taimaka mata. Bayan ta ci ta ƙoshi tayi ta mini godiya. Daga nan na kaita har gidansu bayan ta nunamin. A raina ina mamakin to me ya fito da ita neman abinci bayan suna da gida tana da iyaye. Kinsan dana koma gida na kasa cire abin da ya faru a raina, haka washegari na dawo unguwar ko zan ganta. A ƙofar gidansu na tsaya, kusan mintuna ta dawo da bokatin ruwa a kanta, ina ganinta na taimaka mata ta kai gida ina mata faɗar ya mata nauyi. Bayan ta kai ciki ta fito ta gaisheni tare da mini godiya jiya na taimaketa, ban ce mata komai ba na ɗauki siyayyar dana mata na bata. Ƙin karɓa tayi kuma alama ya nuna tana buƙata. Dana matsa mata tana kuka ta ce ƙwacewa za ayi. Da ƙyar dai na bata ta koma ciki. Kullum idan bani da aikin yi sai na je wajenta, abun mamaki tun lokacin na fahimci ta ɗauka sonta nake, ni kuma burina in taimaka mata kar ta lalata rayuwarta tun da na fuskanci kamar tana matsin rayuwa a gidan. Mun shaƙu da Nusaiba sosai har na zo nasan a gaban matar babanta take, mahaifinta bai jima da rasuwa ba, mahaifiyarta kuma tun tana ƙarama ta rasu. In taƙaita miki dai dalilin haka tausayinta da son taimaka mata ya sani auren Nusaiba duk da ita ta ɗauka sonta nake. Da ƙyar aka bani aurenta, dan matar baban ta dage sai dai ƴarta kamar yadda ta faɗawa dangin mahaifinsu ai ita zan aura. Sai ranar ɗaurin aure na gane ƙullin da ta mini ta canza sunan Nusaiba zuwa Binta. Bayan auren bata haɗata da komai ba, ni kuma ba haka nake buƙata ba dama. Haka muka yi rayuwar mu kamar yadda na sanar miki har Allah ya kawo Hanan. Kinji dalilin da yasa duk ƴan gidan bana sake musu. Bayan haihuwar Hanan basu san da komai nata ba har sai da ta shekara uku kafin su ce za su shigo rayuwarta. No bazan yarda ba, nasan wani abunsu daban ne." "Ko dai sonka take ka aureta?" Dr Awwab ya tsinci muryar Nuratu. Ɗago kansa ya yi ya kalleta ta rufe idonta. "Na yi tunanin hakan. Idan kuwa hakane har abada babu shi, domin basa cikin jerin mutane da suke da muhimmanci a rayuwata balle samun gurbi a rayuwata ko wani so." Ba ta masa magana ba daga nan, kowa yana juya abin da ya faru a zuciyarsa har barci yayi awon gaba da su. Washegari kamar babu abin da ya faru suka farka, bayan ta shirya Hanan ta tafi makaranta shi ma ya wuce aiki. ... Biki sai matsowa yake yau saura sati biyu, ƴan biyu banda Hassana babu mai shiryawa bikin, Hussaina ta barwa Hassana komai tace idan tayi daidaine. Cikin satin sunyi kyau na fitar hankali hatta Hussaina da bata son gyaran. Zaituna da Ikhram su saka haɗawa ƙannensu komai na kayan ɗaki da Kitchen da taimakon Ummi da Awwab. Ɓangaren Ammi ma shiri suke na aurar da autan gidan. Ciki sati aka fara taruwa, dangin Ummi sun fara zuwa haka wanda su ka yi zaman mutunci a Libya ma sun taho. Ranar farko su kayi kamu inda iya mata zalla ne, da ƙyar aka lallaɓa Hussaina ta je dan harda kukanta. Ga biki yana matsowa amma har yau babu ango babu labarinsa. Washegari suka yi walima a filin gidansu. Nuratu tun biki saura kwana biyu ta tare gidan, ita take ƙarfafawa Hussaina gwuiwa akan ta yi hakuri ta yi wa iyayenta biyayya za ta ci ribarsa, balle ta tabbatar mijinta yana sonta. Hussaina da ke kuka har zazzaɓi ya rufeta bayan dawowar su daga walima, ta ɗago ta kalli Nuratu. "Aunti Noor a hakanne yana sone, bayan bai taɓa nuna kansa gareni ba. Wallahi bana son aurennan, don Allah ki faɗawa Yaya Awwab a fasa bikinnan." "Kiyi hakuri." Kawai Nuratu tace ta kwanta. Zirga zirgar da tayi ya saka duk jikinta take jin yana mata ciwo. Babu jimawa barci ya ɗauketa. Ko da Dr Awwab ya ƙira Hassana ce ta sanar da shi tayi barci. ... Washegari ƙarfe goma aka shaida ɗaurin auren Abdallah Abubakar da Hassana AbdulRamat sai Col. Ahmad Tafida da Hussaina AbdulRamat akan sadaki mai albarka. Bikin da ya tara taron manyan mutane daga gurare daban daban, sojoji runduna runduna tun daga ibadan har nan Maiduguri da duk garin da ya zauna sun zo. Gefe ɗaya kuma ga dangin Ummi da suka zo daga Nijar wasu Libya, dangin Ammi ma haka. Bayan ɗaurin auren maza suka tafi reception. Can gida kuma ana ta hidima, amare sunyi ankonsu an musu kwalliya marar hayaniya, Hussaina dai daurewa take. Balle da ta ji sunan ango da ba ta taɓa ji ba ko tayi zargin ko cikin samarinta ne. Wai soja ma kayan haushin. Nuratu kam tafi kowa murnar jin wanda ya auri Hussaina, tuni ta laliɓo wayarta ta ƙirasa, yana ta ringing bai ɗauka ba ta kashe ta ƙira Awwab. Ringing ɗaya ya ɗauka duk da yana cikin hayaniya, ya matsa gefe. "Hayat dagaske ne?" Ta watsa masa tambaya. "Yes My Baby. Col ya zama angon Hussaina. Ina fatan wannan haɗin ya zamto alheri." Cikin murna tace. "Insha Allah Hayat, amma ina da tambayoyi." "Zan amsa miki amma ba yanzu ba." Dariya tayi tace to kafin ta kashe wayar. Cikin sauri ta miƙe, jirin da ya kwasheta ya sata zama ba shiri tana dafe kanta, kusan mintuna kafin ta miƙe a hankali ta fita. Bayan sallar azahar dangin Col Ahmad suka kawo akwati seti biyu, sun zuba kaya na gani a faɗa ciki harda kyautar mukullin mota daga baban ango, haka uwar amarya ma ta saka danƙareren setin gold a bawa amarya. Kallon kallo aka shiga yi mutanen gurin, duk da suma dai akwai arzikin basu tsammaci ganin waɗannan kyautattukan ba. Kaya kam MashAllah. Ƙarfe uku aka kawo na Hassana abin mamaki ita ma da mukullin mota irin na Hussaina sak da kuma setin gold babu abin da ya banbanta tamkar haɗin baki. Nan fa aka ɗauki kabbara masu guɗa nayi. Ƙarfe takwas na dare aka fara shirin kai amare, inda aka tsaida za'a fara kai Hassana sai a wuce a kai Hussaina gidan su Col. Ahmad ta zauna a bangarensa bayan sati biyu zai ɗauketa su wuce Ibadan. Haka kuwa a kayi bayan sun kai Hassana har gidanta mai kyau da tsari aka wuce da Hussaina. Nan fa hankalinta ya ƙara tashi ta ci gaba da kukanta da take tun daren jiya. ... Rana ta farko da ta fara taka gidan mutumin da yake da muhimmanci a rayuwarta. Bayan anyi fakin suka fito aka nuna musu ɓangaren da amarya za ta zauna suka wuce da ita. Ana gama ganin gidan amarya aka fara watsewa, nan Hussaina ta riƙo Nuratu ta hanata tafiya sai kuka take. Ganin haka ya sata zama dole suka kwana gidan amarya. Washegari wuni anyi budan kai da yamma aka shirya dinner. Amare dukkansu cikin ankonsu an musu kwalliya. Ƙarfe biyar aka fara tafiya. Motar da zata kai amarya ta iso wanda ango yake ciki. Har cikin motar Nuratu ta sakata tana gaishe da Col. Ahmad tana faɗin. "Na ƙiraka ba ka ɗauka ba." "Sorry ƙanwata ina cikin jama'a ne. But mu haɗu a gurin dinner za muyi magana, ko gobe." Kai ta jinjina ta rufe motar tana wucewa wajen mijinta da ya ke jiranta. Bayan tafiyarta Col. Ahmad ya juya yana kallon amaryarsa da ta sunkuyar kanta ƙasa. Idonsa ya lumshe ya buɗe ya riƙo hannunta. Cikin nutsatstsiyar murya yace. "Love!" Hannunta ta zare ta ɗago ta dubesa tana kawar da kanta gefe. Tabbas tasan fuskarsa amma ta rasa a ina ne. Sauƙar kansa da ta ji a kafaɗarta ya sata tsorata ta ja baya ya riƙota gaba ɗaya jikinsa. Kuka ta fashe masa da shi. Sassauta riƙon yayi yace. "Is ok Love, ni ne ko? Na ɓatawa twins rai, kullum kuka kina kokonto waye Yayanki zai aura miki ba? I'm sorry kar ki ciremin kunama." Ba ta san lokacin da ta murmusa ba jin maganarsa na ƙarshe. Ba ta masa magana ba a haka suka isa wajen dinner. Bayan an gama komai suka fito, gefe da gefensu sojojine a jere sun riƙe bindiga. Hassana da Abdallah a gaba sai su biyun a bayansu, a haka suka isa wajen zamansu. Taro aka yi cikin nutsuwa da raha. Nuratu dai gefe da Dr Awwab ya kasa ya tsare ya hanata ko motsi, duk idon yayunsa da yaran Ammi bai ji kunya ba balle kuma wasu dangi. Ita ma dai bata damu ba dan duk jikinta ciwo yake, burinta ta kwanta, ga jiri jiri da take ji. Yaya Al-ameen da yake gefensu bayan ya gama waya da matarsa ya kalli Dr Awwab yace. "Doctor ko za ku je gidane? Kamar ba ta jin daɗin zaman." Kallon Nuratu Dr Awwab yayi hankalinta yana kan ma'auratan yace. "Na mata magana ta ƙi, wai sai taga komai." Kai Yaya Al-ameen ya jinjina yana murmushi. "Kasan mata da son ganin kwakwaf." "Hakane, bari in lallaɓa mu yi wa Col sallama mu tafi, in je in kula da kayata." "Daɗinta kowa yana da na shi kayar." "Daga can nesa ba." Faɗin Dr Awwab ya matsa gurin Nuratu. "Babyna muje ki yi wa Col da twins sallama muje gida." Kallonsa ta yi tana marairaice masa, za ta yi magana ya miƙe ya riƙo hannunta suka tashi. Haka suka ƙarasa wajen suka musu sallama Dr Awwab ya basu excuse tana buƙatar hutu. Murmushi Col Ahmad ya yi ya ce. "To a huta lafiya." Ita dai bata fahimci komai ba suka bar gurin bayan ta yi wa twins sallama. Kai tsaye gida ya nufa bayan sun fita a hall din ta dubesa. Murmushi ya yi hankalinsa a titi ya ce. "Tausa zan miki ki yi barci, gobe zan mayarki ki haɗo kayanki." Daga haka ya rufe bakinta suka isa gida, ruwan zafi ya haɗamata ya taimaka mata tayi wanka ta gabatar sallah ta kwanta gadon. Matsa mata jikinta ya yi a haka barci ya kwasheta ya lulluɓa mata bargo. Ya jima yana ƙaremata kallo kafin ya bar gurin, shi ma ya yi shirin barci ya kwanta. ... Washegari ta ji sauƙin ciwon sai jiri da take ji, haka ta daure tayi ayyukanta ta shirya suka je gidan Ummi wajen karfe biyu. Zaituna da Ikhram suna ta lallaɓata suna mata korafi ba ta zo musu ba. Ita kam murmushi ta musu sai Dr Awwab ne ya ce. "Za mu zo sisters. Kuma ai tun biki ba ku zo gidanta ba." Harararsa Zaituna ta yi ta ce. "Mun gani, ai ba da kai muke ba. Ke kuma wallahi idan ki ka biya masa ba za kiyi zumunci ba. Kinga Babban Yaya ɗan Ammi, da Yaya Sajeed gari ɗaya suke amma sai suyi shekara basu haɗu ba, gwara Abdallah." "Kai dai Sister." Awwab yace yana ma ƙaramin ɗanta wasa ɗan wata shida. "Ai gaskiya ta faɗa." Ikhram ta ƙara da haka. Nuratu dai dariya take musu, shi ma dariyar yake yana ta kare kansa. Ƙarfe uku ya ɗauketa suka je gidan Hassana da kallo ɗaya ta mata ta gano Abdallah bai sarara mata ba. Sun ɗan taɓa hira suka bar gidan ganin yanayi ya canza. Gidansu Col. Ahmad suka je daga can, bangaren Hussaina suka fara sauƙa, gata nan dai alama ta fara kwantar da hankalinta. Bayan sun gaisa Col.Ahmad da Dr Awwab suka dawo daga masallaci suka ƙira Nuratu ta fito suka shiga cikin gidan. A falon suka zauna har lokacin da ɗan baƙi, Umma ta sauko ta musu jagora zuwa falon baki ganin nan akwai mutane. Bayan sun gaisa da Dr Awwab tana ce masa tun ranar shuru, Nuratu ta gaisheta. Da fara'arta ta amsa. Col. Ahmad yana kallon Umma ya ce. "Umma ita ce Nuratu fa." "Nuratu dai? Wacece? Banganeta ba? Ba matar likita ba ne. Na gansu tare wajen dinner jiya." Murmushi Col Ahmad yayi ya ce. "Eh matarsa ce. Ita ce yarinyar nan, wacce na taimaka. Na so aurenta ki ka hana ni." Nadama tare da kunyane ya lulluɓe Umma, ta matsa kusa da Nuratu da kanta yake ƙasa, kamo hannunta ta yi cikin sanyin murya tace. "Kiyi hakuri don Allah, na kullace ki ba tare da kin mini komai ba. Sai ga shi Allah ya ba ki jin daɗin rayuwa da miji nagari." Nuratu da har lokacin kanta yana ƙasa tana tuna baya. Matar da ta ƙirata ta ci mata mutunci yau ga shi tana bata hakuri. Murmushi ta yi ta ce. "Babu komai Umma, dama Allah yariga ya rubuta haka." "Ya gida ya mutane gidanku." "Duk lafiyarsu ƙalau." Ta amsa. Sun dan jima suna hira tun Nuratu bata sakewa har ta sake, Umma ta cika musu guri da kayan ciye ciye, Nuratu ba komai ta ci dan ji ta yi komai ya fita a kanta. Wajen karfe biyar suka mata sallama suka raka Col Ahmad sashen amaryarsa suka sake musu sallama suka tafi. Gida suka koma, ruwan zafi ta haɗa ta gasa jikinta ko zai daina ciwo. Bayan ta yi sallah ta kwanta ta rufe jikinta har saman kai, jiri da mugun zazzaɓine ya rufeta, ga yunwa amma komai ta tuna tashin zuciya take ji. Haka Dr Awwab ya dawo ya sameta, saman gadon ya hau ya yaye bargon ya ga barcin wahala take. Jikinta ya taɓa ya ji da zafi rau, bargon ya mayar mata zuwa kafaɗunta ya sauka ya shiga ɗakinsa ya ɗauko magani da ruwa ya fita. Kitchen ya shiga ya haɗamata tea ya koma ɗakinta. Bakin gadon ya zauna ya fara tashinta, da ƙyar ta farka ya lallaɓata ta sha kaɗan ya bata magani ta sha ta koma ta kwanta ya rufeta. Barcin kirki bai yi ba ranar duk motsinta yana tambayarta lafiya, cikin dare zazzaɓin ya sauƙa ta samu barci. Washegari da sauƙi amma haka ya sata ta shirya suka nufi asibiti, duk yadda taso haka ya ɗauketa suka shiga ciki. A office nasa ya zaunarta ya ƙira abokinsa ya zo asibitinsu. Bayan ya dubata ya ɗebe jininta zai mata test gobe zai kai masa gida, daga nan ya musu sallama ya tafi. Dr Awwab bai yi aiki ba ya koma ya ci gaba da kula da Nuratu, duk da jikinta da sauƙi sai jiri wanda kuma rashin cin abinci ne. Da daren Nuratu ta samu ƙiran Mami. Lokacin tana kwance jikin Dr Awwab yana lallaɓata ta sha maltina da peack na ruwa da ya haɗamata, don Doctor ya ce jininta ya hau shi yasa ta ke jin jiri kuma da rashin ci. Wayar ya jawo ya saka mata a kunne yana cewa Mami ce. Bayan ta mata sallamarta ta gaisheta ta amsa, sannan ta sako mata zancen da ya sa ta ƙirata. A zabure ta miƙe har ra kusa bige cup ɗin hannun Dr Awwab tana cewa. "Da gaske Mami?" ... #vote #comment #share MADUBIN GOBE  60. Pharty Bb. Wattpad phartybb. *** "Yi a hankali mana." Faɗin Dr Awwab yana ajiye cup ɗin hannunsa sannan ya riƙota. Jikinsa ta faɗa ta sa masa kuka, duk ya rikice yana tambayarta menene, sai da tayi mai isarta ta ɗago kanta tana kallonsa kafin ta ce. "Na gode sosai Hayat, bani da abin da zan saka maka da shi." Hannunsa ya sa ya tallafo kumatunta. "Me ya faru don Allah duk kin tayarmin da hankali." Fuska duk hawaye ga dariya ta ce. "Ka biyawa Kawu Muhammadu zuwa Umrah har jibi zai tafi, yanzu Mami ta faɗamin. Amma shi ne ba ka taɓa faɗamin ba." Ta faɗa tana haɗa rai. Leɓɓenta ya sumbata yana jan hancinta ya ce. "Ai badan ke nayi ba balle ki sani. Oya zo kisha kar ya huce." Ya ce ya ɗauki cup ɗin ya kai bakinta. Murnar da take ciki ya sata sha sosai, sai da tace masa ta fara jin amai ya rabu da ita. Ranar wuni ta yi cikin farin ciki, yayunta duk sun ƙira suna cewa ta miƙa godiya ga Dr Awwab, haka Kawu Muhammadu ma da maganar ta zo masa ba za ta ya ƙirata. Haka su ka cinye wunin, da daren wani mugun zazzaɓi irin na daren jiya ya ƙara lullubeta, duk taimakon da zai bata ya bata kafin wayewar gari ta ɗan ji dama dama. Tuni ya harbo jirginta, amma bai sanar mata ba yafi son sakamako ya nuna. Da safe ta farka da ji sauƙi sai jiri da ta ke ji. Maganar girki kam babu sai fita yayi ya siyo musu dan ya hanata yin aikin komai. Shi ya taimaka mata ta yi wanka ta saka doguwar riga ta kwanta a falon. Tea ya haɗamata da ƙyar tasha kaɗan ta koma ta kwanta, duk ta zama so weak, gaɓoɓin jikinta duk ciwo. Ƙarfe sha ɗaya yana zaune saman kujera ta yi matashi da cinyarsa idanuwanta lumshe tamkar mai barci, jinta take tamkar ta yi ta kuka. Yadda yake shafa mata gashinta tana ɗan jin sauƙin abin da take ji. Kallon tv yake amma hankalinsa yana kanta, gaba ɗaya tausayinta yake ji, ya lura irin masu shegen laulayi ne, danma ba ta amai kuma tana ƙoƙarin cin abu me ruwa, abinci kam rabonta da shi tun shekaran jiya. Ƙarar wayarsa ya sa shi duban wayar da yake saman Center, Nuratu ta buɗe idanunta ta dubesa. Ɗauka yayi ya ga mai ƙiran, ya kalleta kafin ya ɗaga wayar ya amsa. "Ina zuwa." Kawai ya faɗa ya kashe wayar, ɗaga Nuratu ya yi yana kallonta ya ce. "Dr Sageer ne, za ki iya fita." Kai ta ɗaga masa ya taimaka mata ta miƙe tsaye, mayafi ya saka mata yana riƙe da ita suka sauƙa ƙasa. Saman kujera ya zaunarta ya fita ya shigo da Dr Sageer. Bayan sun gaisa, Nuratu ta gaishesa ya amsa yana ciro result ya miƙawa Dr Awwab. "Congratulations Doctor, you're lucky." Da murmushi Dr Awwab ya amsa musabahar da ya masa yace. "Thank you Doctor Sageer." Ita dai Nuratu ta zama ƴar kallo ta kasa fahimtar su. Dr Sageer ne ya kalleta ya ce. "Congratulations Madam you're pregnant." Zut ta ji maganar ya shigeta, sai kuma ta ji kunya ta sunkuyar kanta ƙasa ta kasa yin magana. Dr Awwab ne ya tashi ya isa wajenta ya rumgume. "Thank you My Baby." "Umuhm." Dr Sageer yayi gyaran murya, hakan ya ankarar da Dr Awwab ya sake Nuratu. Miƙa masa wani paper ya yi. "Prescription na drug ɗinta, maganin da zai taimaka mata jininta ya sauƙa da kuma wanda zai sa ta cin abinci. Sai kuma zazzaɓin dole sai cikin ya yi ƙwari za ta samu sassaucinsa. Allah ya raba lafiya Madam." Murmushi kawai ta yi Dr Awwab ya masa godiya tare da masa rakiya har waje ya dawo. Ɗaukar Nuratu ya yi cak suka koma sama. A gaba ya sa ta yana kallo tare da yin murmushi ya kasa faɗin komai. "Kallon fa? Ko Babyn za ka hango." Ta faɗa da murmushin kunya. Fuskarta ya shafa yana murmushi shi ma. "Da zan hangosa zan fi kowa jin daɗi. Wani abu kawai yake bani mamaki." "Na me fa?" Kwantarta ya yi a cinyarsa ya riƙo hannunta. "Haka ki ke da dagiya, sai da ki ka dage ki ka samo sakamako mai kyau tun wata ɗaya bai rufe ba, sati uku fa. Shi kuma ya nuna mahaifinsa yana tafe ya bayyana kansa da wuri." Dukan wasa ta kai masa a kirji, cikin shagwaɓa ta ce. "Bana so Allah." Yana murmushi ya rumgumeta yace. "Babyna mamar Babyn." "Sai ka dai na ƙirana da Baby." "Har abada ke Babyna ce." Ya ce ya sunkuya ya sumbaci leɓɓenta. Da daren har gida ya taka ya sanar da Ummi cewa suna buƙatar mai taimakawa Nuratu bata jin daɗi. Fadar haka Ummi ta gano nufinsa abin ka da manya. "Zan yi wa Hajjo magana ta baku aron ƴarta Batula kafin ta sauƙa lafiya." Murmushi Dr Awwab ya yi ganin Ummi ta fahimci zancensa. Sallama ya musu akan su taho da Hanan tare tunda biki ya ƙare. Daga nan gida ya koma ya ci gaba da kula da matarsa. Washegari Batula da Hanan suka taho tare, ɗakin ƙasa ta zauna. Ita ke shara da goge goge sai girki, ba laifi ta iya komai. Hassana da Hussaina sun zo dubata tare da mazajensu, anan Hussaina ta sanar mata jibi za su wuce Ibadan. Daga kallonta tasan ta kwantar da hankalinta ta fara son mijinta. Wuni guda suka mata har dare kafin su tafi. ... Bayan sati biyu allahamdulillahi Nuratu ta fara jin sauƙin jiri sai zazzaɓi da kuma ciwon jiki. Har lokacin ba ta son cin abun kirki duk ta rame sai haske da ta yi. Dr Awwab yana bakin ƙoƙarinsa na ganin ta samu dukkan kulawa, baya fita aiki da wuri, idan ya fita kuma da wuri zai dawo. A gida babu wanda yasan tana da ciki, Dr Awwab ya kasa sanar musu ita ma kuma haka. ... Yau Kawu Muhammadu ya kammala aikin Umrah bayan tsawon sati uku da ya ɗauka. Ya so wucewa gida Dr Awwab ya riƙesa tun da jirgin Nigeria ya bi ya zo kamar yadda ya tafi, haka idan zai dawo ma a jirgin Maiduguri zai dawo, to ya sauƙa a gidansu, idan ya huta zuwa kwana biyu zai bada mota a kaisa har gida. Da ƙyar ya yarda ganin nauyin zai masa yawa. Da yamma jirginsu ya sauƙa a Maiduguri. Dr Awwab da kansa ya je ya ɗaukosa ya kaisa gidan su. Har ɗakin da ya tanadar masa ya kaisa dan huta gajiya. Bayan ya huta Nuratu da Hanan su ka zo gaishesa, sun jima suna hira kafin su barsa ya huta, Batula ta kawo masa abinci da abun sha. .... Dubanta yake sai ɓata fuska take yi, tun jiya ya lura da ita kamar akwai abun da yake damunta. Balle kuma yanzu da ya kawa mata maganar tafiya. Ita kuwa taƙaici goma da ashirin ne ya haɗe mata. "Ni fa bana jin daɗi balle ayi tafiyarnan. Balle ma me abun sai mun masa sannu da zuwa har gidanta. Bayan haka da yarannan." Ƙara sassauta murya ya yi yace. "Dan Allah fa, ba zai ji daɗi ba, balle an sanar masa za ku je. Wuni kaɗai za muyi mu juyo." "To ni dai babu yadda na iya idan ba haka ba babu inda zanje." "Ki ɗaure dai." Dole ta miƙe ta shirya ta fito ta samesa, yaran duk sun iso har da yaransu. Gaba ɗaya suka dunguma a mota babba da ya nema musu suka ɗauki hanya. .... Kallonsa su ka yi dukkansu ganin ya tarasu ya ƙi cewa komai. Abba ne ya yi tsaki. "Kai wai me haka? Zan saɓa maka fa, ka girma ba kasan ka girma ba." Marairaice fuska yayi ya kallin Babban Yayansa. "Yaya to ka sanar da su ba anan zan nuna musu abun ba. Su taso mu je can." Abba miƙewa yayi cikin jin haushi. Da sauri Babban Yaya ya tsayarsa. "Abba kayi hakuri mu je mu gani, idan shirme ya yi ni da kaina zan masa hukunci." Tsaki yayi yana cewa. "Mu je to." Dukkansu suka nufi waje, cike da murna ya ciro wayarsa ya yi ƙira. "Done, gamu tafe nan da mintuna goma." Daga haka ya kashe wayar ya bi bayansu da sauri. ... Ƙarfe sha biyu suka iso gidan, da murna Nuratu ta tari Maminta da yayunta. Kallo Mami ta bita da shi ganin yadda ta rame, Aunti Hasiya marar haƙuri ta ce. "Jinya ki ka yi Nuratu?" "Eh. Mami ki shigo." Ta faɗa ta basar da zancen ta musu jagora zuwa falonta, ta kawo musu abinci da Batula ta girka dan har lokacin ba ta iya yin aikin kirki don ciwon jiki. Da ƙyar Dr Awwab yake samun kanta ta yarda da shi wani lokacin har da kukanta. Alhaji Mamman da Muhsin wajen Kawu Muhammadu su ka zarce su na hiransu, Dr Awwab kuma yana waje don jiran isowar Ummi. ... Aunti Hasiya da ta kasa haƙura tana duban Nuratu tace. "Wai wani irin ciwo ki ka yi haka, kin ga yadda kika rame." "Zazzaɓi ne fa." Ta faɗa kamar tayi kuka, wannan sa idon na Aunti Hasiya ya isheta. "Zazzabi kaɗai." Rukayya tace tana dariya ƙasa ƙasa don ta harbota. "Kai ku daina takurawa autana." Faɗin Mami ta jawo Nuratu jikinta. "A faɗa mana gaskiya, idan kuwa ya fito dole mu ji mu gani." Rukayya ta ce tana fita da sauri gani saƙon harara daga wajen Mami. Zuwansu babu jimawa Hafiza ta iso don ma mahaifinta sannu da zuwa kamar yadda Yaya Al-ameen ya faɗa. .... Kusan tare motar Ummi da Ammi da Abba suka shigo gidan. Ammi kallon Abdallah ta yi da shi yake jan motar tace. "Nan ai gidan Awwab ne." "Na sani Ammi." Abba girgiza kai kawai ya yi, shirmen ɗansan ya fara basa mamaki ba haushi ba. Fita su kayi gaba ɗayansu suka gaisa da Ummi da ita ma kallon mamakin ganinsu ta ke. Hatta Babban Yaya da Sajeed da bai cika magana ba, ko miskilanci ne ko jan aji ne oho. Awwab da ya samu labarin shigowarsu ya fito ya musu jagora zuwa babban falon. Bayan gaisuwa kowa ya zuba ido da kunne ganin me ya tarasu a gurin. Dr Awwab ne ya fara magana. "Ummi, Ammi, Baffa, Yayan mahaifiyar Noor ne za ku gaisa da shi sai mahaifinta. Na san hakan bai taɓa faruwa ba tsakaninku, shi ne nayi tunanin bayan dawowarsa daga Umrah kafin ya wuce ya kamata asan juna har da mahaifinta. To mahaifiyarta ma ta zo duk zan ƙirasu yanzu saboda suna son wucewa a yau suma." "Kayi tunani mai kyau." Baffa ya ce cikin wani muguwar buguwar zuciya da ya kamasa ya rasa dalili. Kowa ya yaba da tunaninsa hakan yasa ya miƙe ya nufi stairs, da sauri Abdallah ya bi bayansa. A stairs suka tsaya. "Kana ganin za su gane juna Yaya?" "InshaAllah, matan su fara fitowa sai mazan, suna falon ƙasa na baƙi." Yarda da shi ya sa shi nufan falon Nuratu, da sallama ya shiga ya durƙusa. "Mami, Ummi, Ammi sun zo, za ku gaisa, sun zo ma Kawu sannu da zuwa. "Har da wahalar su?" Mami ta tambaya tana miƙewa. Fita ya yi ya basu guri suka ta shi dukkansu su ka bi bayansa, har da Nuratu da take jin ciwon jiki. Ɗakin da Alhaji Mamman da Muhsin da Kawu Muhammadu ya ke ya shiga ya sanar da su, su kam tare su ka fito su huɗu harda Muhsin. Fitowar su ya yi dai-dai da sauƙowar Mami da yaranta, wanda ya yi dai-dai da kallon Abba zuwa ga Muhsin. Da mamaki ya kalli Muhsin ya kalli Abdallah. Bai gama fita a mamaki ba ya kalli Alhaji Mamman, tabbas shi ne mahaifin matar Awwab da ya musu rashin mutunci a aurensu. Kallon sa na biyu zuciyarsa kaɗan ya koma ciki lokacin da ya haɗa ido biyu da na gefensa. Salatin da ya ji a gefensa ya sa shi duban inda ya ga an nufa da sauri. Babbar macece take neman kaiwa ƙasa yaran gefenta suka riƙota da sauri cikin tashin hankali. Bayan an samu ta zauna ya samu damar ganin fuskarta da ƙyau. Kansa ya riƙe da sauri jin yana juya masa, jiri ya fara gani kafin yayi wani ƙara numfashinsa ya ɗauke. Gaba ɗaya yaransa su ka yi kansa suna jijjigasa. Falon ya hargitse da hayaniya har an rasa na wanne za'a saurara. Gefe Mami tana kuka da suka rasa dalili, gefe Kawu Muhammadu zaune ya kasa motsi sai ido yake bin su da shi, gefe ɗaya Baffa ya suma yaransa a kansa Dr Awwab yana ba shi taimakon gaggawa. Kusan mintuna biyar ya samu numfashinsa ya dawo, sannan ya buɗe ido da ƙyar. Babban Yaya ya basa ruwa ya sha. Bayan samun nutsuwa ya dubi Babban Yaya murya ƙasa ƙasa yace. "Aliyu! Muhammadu da Sadiya na gani. Dama suna raye? Ko kuma ni ne na mutu na dawo?" Kowa shuru ya yi ya zuba masa ido jin zantukan bakinsa, shi kuwa sai kallon Mami da Kawu Muhammadu ya ke ya kasa musu magana, haka su ma ɓangrensu. Sun rasa ta ina za su fara. "Kowa ya zauna." Abdallah ya ce daga tsayen da ya ke. Hakan yasa yaran Mami suka zauna kusa da ita sun zagayeta suna bin Baffa da kallon mamaki ganin kammanin Mamin su a fuskarsa, hatta Hafiza da take hango kamannin mahaifinta a gurinsa ta yi jugum. Gefe Ummi da Hassana da ta zo da Ummi. Gefe ɗaya kuma Kawu Muhammadu da Muhsin da Alhaji Mamman sai Yaya Al-ameen da bai jima da shigowa ba. Gefen Baffa kuma Ammi da yaranta ne. Abdallah ne ya fara magana ganin an samu nutsuwa. ... #vote. #comment #share MADUBIN GOBE  61. Pharty Bb. Wattpad phartybb. GANGARA. *** Abdallah ne ya soma magana bayan kowa ya baza kunnuwa don jin wannan sarƙaƙiyar. Gyaran murya ya yi kafin ya soma da cewa. "Tsawon shekaru huɗu kenan. Watarana da yamma ina zaune Yaya Awwab ya zo ya same ni har makaranta, nayi mamakin ganinsa a lokacin saboda bamu cika haɗuwa ba sai irin a biki ko a sallah idan ya zo gidanmu, ko idan mun je na su. Bayan mun gaisa na basa gurin zama, anan ya dubeni ya ce. "Abdallah naga abin da ya bani mamaki yau, naga abin da ya birkita tunanina da ƙwaƙwalwata, na kasa tunani na kasa gano komai balle samun haske, na rasa wa zan tunkura in sanar balle ya taimaka mini sai kai." Dubansa nayi yadda yake cikin damuwa, ni ma cike da damuwar dan maganganun sa sun rikitani na ce. "Yaya Awwab me ya faru? Na kasa gane maganganun ka, na kasa fahimtar su ko sanin ina su ka dosa." Kallona ya yi a karo na biyu ya ce. "Shin Baffa ya taɓa sanar da kai suna da wasu ƴan uwa bayan Babban Yayan su Alhaji Yousufa?" Tambayar da ya min shi ya ƙara dilmaye ƙwaƙwalwata, sai girgiza masa kai da nayi alamar a'a. Numfashi ya sauƙe ya miƙe tare da fara zagaye cikin ofishin da muke zaune. Ni dai kawai idanu na saka masa dan na rasa bakin magana. Haka ya ci gaba da yi tsawon lokaci kafin ya dafa teburin da nake zaune. Tamkar ba zai ce komai ba ya ɗago ya dube ni da idanuwansa da su ka canza launi. "Abdallah naga mai kama da iyayenmu, ba kuma namiji ba mace, babbar mace, in taƙaita maka hatta ƴarta babba tana kama da ƴar uwarka Sumayya." "Kama kuma? Kamar ma da iyayenmu kuma mace?" Na tambayesa da mamaki. Kai ya ɗaga mini yana cewa. "Tabbas hakane Abdallah. Marar lafiya aka kawomin kwana biyu da ya wuce, ƙwaƙwalwarta ya samu matsala. Wallahi farin ganin babbar ƴar matar na ɗauka Sumayya ce, amma da na ji sunan da aka ƙirata da shi sai na tabbatar ba ita bace. Sannan matar ita da su Abba bambancin su kawai ita macece sai ƙarancin shekaru. Hatta ita marar lafiyar tana kama da su." ... Shuru Abdallah ya yi yana neman guri ya zauna don ya gaji da tsayuwar. Falon tamkar anyi ruwan sama an ɗauke, babu mai iya kwakkwaran motsi sai idanu da suke bin juna da shi cike da mamaki da son fassara kalaman Abdallah. Bayan zamansa ya ci gaba da cewa... "Ban san me yasa ya zaɓi ya faɗamin ba. Ban san me yasa ni ƙarami a cikinsu ba kuma ya zaɓe ni. Ban yarda da zantukan sa ba a lokacin haka muka rabu. Sai dai abun mamaki bayan lokacin Yaya Awwab ya ci gaba da kawomin bayanai akan waɗannan mutane har Allah ya sa watarana na kai masa ziyara asibiti na gansu da idanuna. Tabbas na shiga rudu, sai dai Yaya Awwab ya nunamin kar mu tono maganar ko mu tunkari wani da shi a cikin iyayenmu sai wani burinsa ya cika. To allahamdulillahi bayan aurensa da Noor mu ka dinga samun ƙarin haske. Misalin ganin Ammi da ta yi ma Aunti Rahma da ita kanta Mamin da kuma Muhsin. Ammi tafi nuna damuwarta a kan Ummi. Na yi ta bibiyarta ta sanar dani damuwarta duk da na fahimci akan menene amma ta ƙi. Anan kuma burin mu idan ta sanar da ni sai in sanar da ita ga yadda abun yake, sai mu tunkari Abba da maganar kamar yadda muka tsara da Yaya Awwab, amma ƙarshema dai ta ƙi maganar gaba ɗaya ta watsar. Hakan ya sa Yaya Awwab neman sabuwar hanya." Daga haka ya yi shuru yana sauƙe numfashi, ruwa ya tsiyaya yasha ya kalli Dr Awwab ya marairaice masa. "Yaya ka ƙarasar musu ni na gaji." "Ka ƙarasar kawai." Dr Awwab ya ce yana ƙoƙarin miƙewa. Cire kunya Mami ta yi ta ajiye gefe ta ce. "Awwab ka warware mana wannan abun. Har yanzu mun kasa fahimtar maganganun Abdallah?" Kunyar Mami ya sa shi komawa ya zauna kansa a ƙasa ya fara magana. "Tun ranar da na ɗora idona akan ku na dasa ayar tambaya a lamarin ku. Sai dai na rasa ta ina zan soma binciken abin da bani da tabbas. Abban mu har ya rasu bai taɓa sanar damu yana da wasu ƴan uwa ba bayan Alhaji Yousufa da ahlinsa da suke Nijar. Balle ma lokacin da ya rasu ban wuce shekaru goma ba. Rasa wanda zan tunkara da wannan batun ya sani sanar da Abdallah, duk da bai yarda da ni ba, haka na dinga kawo masa wasu bayanan har ya zo ya fara yarda kamar yadda ya sanar da ku. Gefe ɗaya kuma ga Noor da na gani ina son aure, duk da tasha sanar da ni babu aure a ranta yanzu saboda ƙaddarar da ta tsinci kanta. Wani lokacin ji nake tamkar in hakura, amma idan na tuna burina fa da nake mafarkin ya kusa cika. Dan na sha yin mafarki da Abba yana sanar da ni yarinyar da nake neman aurenta alheri ce a tare da ni, ita ce silar bayyana ɓoyayyen sirrin da yake rufe, kar na yarda na karaya, Insha Allahu zan yi nasara. Wannan kalaman mafarkin su suka ƙarfafa mini gwuiwa na dage da cusa kaina gurinta. Ranar da Ummi ta je gidansu Noor na ɗauka tun a hanya za ta fara tambayata akan abin da ta gani, sai dai abin mamaki har yau Ummi ba ta taɓa kawomin maganar ba, kuma ban san dalili ba. Haka na dage sai da naga aurena da Noor, bayan auren ni da Abdallah mu ka ci gaba da bin duk hanyar da zamu ɓullowa lamarin. Ammi ta ƙi bamu gamshashshiyar bayani, Ummi sam ta ƙi maganar. Ƙarshe dai bayan zuwan mu Damaturu na samu Abba da maganar. Anan na sanar masa komai, shi ma ya ce mini tabbas yaga kamar Mami a fuskar Baffa lokacin ɗaurin aurenmu, sai dai lokacin ya rasa a ina yasan mamallakin fuskar, sai daga baya ya gano, dalili babba da ya saka shi dagewa ya mayar da Mami. Anan ya bani shawara. Shawarar da ya bani shi na samu Abdallah da shi akan in biyawa Kawu Muhammad Umrah, sannan in dage ƴan uwa zu so masa sannu da zuwa. Hakan mu ka yi da taimakon Abdallah nayi komai har zuwa yau. Iya abin da na sani, ku za ku sanar damu sauran domin mu ma ƙarin haske muke nema a gurin ku. Kawu, Baffa, Mami shin ku ƴan uwa ne?" Yin shurunsa ko in ce dasa ayarsa shi aka fara surutu a falon. Kowa da abin da yake faɗa, burin kowa mutane ukun nan su amsa tambayoyin da yake zuƙatansu. Nuratu da kanta yake saman cinyar Mami ta ɗago tana kallonta tana share hawayenta. Girgiza kai ta yi ta riƙo hannunta cikin ƙarfin hali don zazzaɓine ya rufeta ta ce. "Mami kiyi haƙuri don Allah kiyi shuru ki mana bayani tun da Kawu da Baffa sun ƙi magana. Yin maganar ki ina ga zai saka sauran yi." Kai ta ɗaga mata ta kamo hannunta da take share mata hawaye. Gyaran murya ta yi kafin ta soma maganar da ya sa ka yan falon shuru da dubanta. "Mu ƴan asalin Niger ne kamar yadda ku ka sani, iyayenmu mu huɗu suka haifa. Yaya Abubakar, Yaya AbdulRamat sai Yaya Muhammadu sai ni autar su. Iyayenmu bani da wayo sosai suka rasu, dalilin haka riƙon mu ya dawo hannun kakarmu. Da ɗan wayona Yaya Abubakar da Yaya Abdul suka fara kasuwanci da kuɗin gadonmu tun bayan gama karatun su. Yaya Muhammadu ya bada rabin nasa dukiyar haka ni ma, suka bar bar mana abin da zamu riƙe, a haka Allah ya albarkaci abun har su ka fara fita garuruwa har Allah ya yi zamansu a garin Agadez inda aka fi kasuwanci sosai. Anan suka kafa kasuwancin su tare da taimakon wani Alhaji Yousufa. Ba mu taɓa kallonsa ba, kuma basu taɓa kawosa ba, har Allah yayi su biyu suka yi aure acan Alhaji Yousufa shi ya tsaya musu matsayin dangin su. Auren duk labari suka bamu ta hanyar waya da ya fara zuwa lokacin. Ba su gayyaci kowa ba, da muka nuna ɓacin ranmu musamman Yaya Muhammadu, haka ya sa suka zo suka bamu haƙuri sai dai basu kawo mana matansu ba. Sun mana alheri sosai kafin su tafi, musamman ni da ake shirin aurena lokacin da Abban su Rahma. Wannan tafiyar shi ne na ƙarshe sai waya da suke mana, har aka yi aurena aka kawo ni Damaturu ban ƙara saka su a ido ba, Kawu Muhammadu ya yi aure, har kakarmu ta rasu. Ƙarshema wayar suka daina kiran mu, idan mun ƙira ba ya shiga. Wannan lokaci ni da Yaya Muhammadu mun shiga tashin hankali ba don dukiyarmu da yake gurin su ba, burinmu ƴan uwanmu da su kaɗai suka rage mana su dawo garemu. Tun muna saka ran dawowar su har muka fara haƙuri, mu ka fara addu'ar idan da sauran saduwarmu a duniya Allah ya haɗa mu. Sai bayan tsawon shekaru talatin yau gani ga Yaya Abubakar amma babu Yaya Abdul." Nan falon ya ƙara hargitsewa da kuka, musamman wanda suka tuna mahaifinsu da baya raye. Ummi da Ammi banda hawaye babu abin da suke. Kawu Muhammadu shi ma hawayen yake sharewa lokaci zuwa lokaci domin yariga ya fahimci ɗan uwansa baya raye. Ɓangaren Baffa abubuwan da suka wuce ne suka dinga dawo masa a hankali cikin ƙwaƙwalwarsa tamkar bidiyo. Kallon Mami yayi ya maida kallonsa kan Kawu Muhammadu. Tsam ya miƙe ya nufi gurinsa, mutanen falon gaba ɗaya suka zuba masa ido. Durƙushewa ya yi gabansa ya rumgumosa jikinsa, manyan mazan hawaye kawai suke fitarwa cike da jarumta. Kawu Muhammadu ne ya fara janyewa ya riƙo hannun Baffa. "Yaya Abubakar." Damƙe hannunsa Baffa ya yi ya ɗago kai suka haɗa ido. "Muhammad.." Kawai ya iya faɗa ya yi shuru don wani ɗaci da ya sarƙe masa a maƙoshi, ya rasa me zai fara furtawa, ta ina zai soma. Fahimtar haka ya saka Kawu Muhammadu ƙara damƙe hannunsa. "Ka fadi wani abun don Allah. Ina ku ka shiga?" Girgiza kai ya yi bakinsa yana rawa ya ce. "Bansan me zance ba amma tabbas tun da mu ka barku kullum ku na cikin ranmu, ni da Yaya Abdul ba mu taɓa zancen ku ba amma shi ma nasan yana tunaku a ransa. Sai dai me? A lokacin mun kasa sanar da junanmu balle tunanin komawa gida, da zaran hakan ya bijiro mana sai ɓacin rai ya ziyarce mu. Farko mun haɗu da Alhaji Yousufa a Agadez amma ɗan asalin Libya ne. Da dukiyarmu da nasa muka haɗa hannun jari muna juyawa, sai dai namu yafi nasa yawa kaso saba'in namu kaso talatin nasa. Bayan aurenmu Alhaji Yousufa ya samu dole muka tattara muka koma Libya da zama mu da matanmu. Duk matanmu tsammanin su shi Yayanmu ne, danginsa kuma namu ne. Bayan tafiyarmu Libya Ammi ta haifi Babban Yaya Aliyu, Sajeed, sai lokacin Ummi ta haifi Zaituna daga baya suka haihu kusan tare, Ummi ta haifi Ikhram ita kuma Ammi ta haifi Sumayya, sai bayan shekaru uku Ummi ta haifi Awwab, Ammi kuma sai bayan shekaru huɗu ta haifi Abdallah. Shekarun Awwab biyar mu ka baro Libya muka dawo Maiduguri da zama, lokacin Alhaji Yousufa ya yi bake bake akan dukiyarmu shi da yaransa, ya hana mu amfani da shi sai yadda ya yi, kuma ya hanamu magana don mugun tsoron sa muke ji da bamu san dalili ba. Rabuwar mu bai yi daɗi ba don ya hanamu ko da rabin abin da muka saka a ciki. Dalilin haka Yaya AbdulRamat ya haɗu da hawan jini har ya kwanta jinya wanda ƙarshe ya yi ajalinsa. Bayan mun samu mun saida wasu kadarorinmu mun samu gidan zama, mun saka yaranmu makaranta, mun samu sana'ar yi, a Lokacin muka sanar da Khadijah da Zainab zamu zauna ne a garin kafin zuwa wani lokaci, har zuciyoyin su basu yarda ba amma haka suka ci gaba da zama da mu, kuma sun kasa tambayar mu dalili. Idan na sanar da ku lokacin mun mance da babinku a rayuwarmu ka yarda, don shaf mun mance da ku a zuciyoyin mu. Allahamdulillahi Allah ba azzalumin bawansa bane, kusan shekara uku Allah ya azurtamu da abin da zamu riƙe kanmu da yaranmu, a lokacin Yaya yana jin jiki don yau lafiya gobe jinya, kullum yana sanar da ni ciwon sa bana rashin dukiyarmu bane, akwai wani abu da yake damunsa amma ya rasa menene in masa addu'a. Idan ya min irin maganganun nan irin haka ranar wuni zan yi ni ma zuciyata da kunci. Abun tashin hankali maimakon ya samu sauƙi ganin arziƙi ya ƙanƙama sai ma jinyar da har yake hanasa fita. Haka wata rana ya ta shi da aman jini, a rikice Zainab ta ƙira ni na zo gidansa. Ina zuwa duk yadda nayi mu tafi asibiti ya ƙi, a hannuna a gabana Yayana ya bar duniya, maganarsa na ƙarshe kafin shahada shi ne Muhammad da Sadiya. Dukkanmu mun ji mutuwarsa musamman Zainab da ya kusa jawo mata ɓarin ƙaramin cikin jikinta da shi ma kansa Yaya bai sani ba har ita, da ƙyar aka shawo kan abin. Haka muka kai Yaya Abdul muka dawo. Na yi kuka na yi don shi kaɗai ya ragemin a duniya, sai dai sunan mutane biyun da ya ƙira sun tsayamin a rai. Bayan sadakar arba'in dangin Ummi su ka so ɗauketa na nuna zan kula da ita da yaranta da abin da za ta haifa, ita ma kuma ta yarda don bata son yin nisa da yaranta. Haka ta ci gaba da zama a gidan aka bar mata mace ɗaya tana kula da ita. Duk abin da na samu sai na fara bawa gidan Yaya kafin gidana. Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya har Ummi ta haifi ƴan biyunta mata. Hassana da Hussaina aka raɗa musu babu wani sunan don tace ta bani zaɓi. Har lokacin na kasa tuna mutane biyun su waye su da Yaya ya faɗamin. Rayuwa ya ci gaba da tafiya abubuwa suna faruwa har zuwa girman yaranmu duk nauyin yana kaina, na yi na yi Ummi ta yi aure ta ƙi, haka danginta ma, ƙarshe muka rabu da ita ko don yaranta. Bayan shekaru goma na samu labarin rasuwar Alhaji Yousufa bayan karayar arziƙi. Rayuwa na tafiya yaranmu su ka gama makaranta masu aure sun yi Babban Yaya, Sumayya, Sajeed, Awwab, Zaituna da Ikhram, har yau ga shi yan biyu sun yi aure. Sai dai Sumayya ta rasu a haihuwa shekaru biyu kenan. Sai dai har yau Ummi da Ammi babu wanda ya ƙara tambayar mu zancen Alhaji Yousufa ko wani danginsa da muke ƙira na mu." Daga haka ya dakata yana share hawayensa ya kalli Kawu Muhammadu da yake jin zafin rashin ɗan uwansa. Amma a jikinsa ya ji ba lafiya ƙalau ba ko haka kawai ba mutum zai manta da ƴan uwansa. Cikin raunin murya Baffa ya ce. "Muhammadu, Sadiya don Allah ku yafe mana, wallahi ba haka kawai ba muka mance da ku, ko muka cinye dukiyarmu ba." Mami ne ta yi magana daga zaunen da take cikin sauri, cikin muryarta da ya dashe don kuka tace. "Yaya ka daina bamu hakuri, Allah ya riga ya ƙaddara hakan. Wallahi ni kam na yafe." "Ni ma hakan. Haɗuwarmu da ku yafi komai daɗi da zamu godewa Allah. Sai dai Yaya ka kula haka kawai mutum zai manta da ƴan uwansa." Faɗin Kawu Muhammadu har lokacin suna riƙe da hannun juna shi da Baffa. Alhaji Mamman sai lokacin ya yi magana. "Kamar akwai asiri a tattare da lamuran. Idan hasashena gaskiya ne, Alhaji Yousufa ya yi amfani da wannan hanyar ya mantar da ku ƴan uwan ku don ya mallake dukiyar ku, ƙarshe kuma ya hanaku shi kuma bai basa amfani ba. Ku ya rabaku da danginku kuma ya hanaku tunanin su." Wannan lokacin Babban Yaya ne ya sa ka baki. "Tabbas hakane ni ma nawa tunanin ya ba ni. Amma yanzu allahamdulillahi da komai ya bayyana, shi ma baya raye balle ace za'a ɗauki hukunci." "Yanzu kam na yafe masa, Allah ya ji kansa shi da Yaya. Na so yaga wannan ranar, ga yaranmu da jikokin mu. Ku matso in ganku." Baffa ya ce yana share hawaye. Babu musu su Aunti Rahma suka nufi gurinsa da yaransu har Nuratu da Hafiza. Dukkansu sai da suka yi musabaha yana tambayarsu sunansu. Nuratu ce ƙarshe ya damƙe hannunta ya ce. "Tun ranar dana haɗa ido da ke zuciyata ta buga, da tunaninki na kwana a raina. Ji na ke kamar akwai inda nasan fuskarki. Ashema ƴata ce." Murmushi ta yi kanta ƙasa. "Ni ma Baffa haka." Juyawa ya yi ya kalli Aunti Rahma. "Wannan Sumayya ta ce ta dawo. Ke kuma sak Kaka." Ya faɗa yana nuna Hafiza. Gaba ɗaya dariya suka sanya har manyan su ka dara. Ya kalli Muhsin ya ce. "Wannan kuma Abdallah, amma yafi kama da Yaya Abdul sosai." Murmushi nan ma aka yi, Nuratu ta ɓata rai jin bai ce tana kama da kowa ba. "Baffa ni fa?" Hannunta ya riƙe yana murmushin farin ciki. "Ke ma kina kama da mu amma ba sosai ba, lotsawar kumatun namu ne don Yaya yana da shi." Murmushi ta yi ta ɗan saci kallon Dr Awwab, idanu suka haɗa ta ɗaga masa gira ɗaya. Murmushi ya yi yana lumshe idanunsa tare da lasar lips ɗinsa na ƙasa. Kawar kanta ta yi jin Baffa yana magana. Kallon Hasiya ya yi ganin ta yi shuru ya ce. "Wannan kuma baƙin halin irin na Sajeed, shegen ƙin ma mutane magana. Sai faɗa, na rasa wa ku ka biyo, iyayenmu bamu taɓa jin kansu ba, ni bani da shi Yaya ma haka da Kawun ku, gwara Sadiya wani lokacin tana taɓawa idan an taɓota." Dariya gaba ɗaya aka sanya har Sajeed da Aunti Hasiya da ya ce halin su na kama, sai kuma lokacin kowa ya kula da rashin son maganarsa, za ma su rantse tun da aka zauna ko tari bai yi ba. Haka ya yi ta tsokanar su kamar jikokin sa sun mayar da shi kakan su. Ya karɓi yaransu yana tambayar su sunayensu. Mami ma ƙarasawa wajen su ta yi ta zauna, hannu Baffa ya miƙa mata suka yi musabaha tana murmushi da kuka. "Ya isa kuma kukan haka. Ni fa Sadiyar dana sani tana da jarumta." Murmushi ta yi ta kalli Alhaji Mamman ta kalli Baffa ta ce. "Yaya ga babansu Rahma." "Mun san juna na ɗan lokaci a auren Awwab. Amma yanzu za mu yi sabuwar gaisuwa. Matsonan ƙanina." Da murmushi jin maganarsa Alhaji Mamman ya matsa su ka yi musabaha da sabuwar gaisuwar mutunci. Alhaji Mamman har kunya ya ji tuna rashin mutuncin da ya tsula masa. Mami gurin ta bari bayan ta kora Aunti Rahma da Hasiya da Rukayya kitchen su ɗaura abinci, domin basu ga na tafiya yau ba. Gurin su Ammi ta ƙarasa sai lokacin suka gaisa ana ƙara jajantawa. Wai wannan ƙanwar mazajen su ce, yaranta kamar yaran su. Wani abu sai ikon Allah. Gefe ɗaya su Awwab ne da Sajeed da babban Yaya da Abdallah da Yaya Al-ameen da Muhsin suna hira, hankalin Dr Awwab duk yana kan Nuratu da yake ganin sai ɓata rai ta ke. Ganin hankalin su yana kan hiran da Abdallah yake zuba musu ya miƙe, kai tsaye ya isa inda take ya ɗan rankwafo saman kanta. "Are you ok My Baby?" Girgiza kai ta yi duk da ta ji kunyar yadda ya sata gaba, don ma kowa hankalin sa baya gurin su. "Zazzaɓi nake ji tun ɗazu." Hannunsa ya ɗaura a saman wuyanta. "Za ki iya cin abin da su Aunti Rahma suke girkawa." Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, don ta tsani abu mai suna abinci gaba ɗaya. "To me za ki ci in siyo miki." "Zansha Maltina." "Shi fa ki ka sha da safe kuma yanzuma haka. Wallahi zan fara miki ɗurai." Dariya ta yi ta miƙe tsaye da ƙyar. "Bismillah don Allah." Ƙasa yayi da murya. "Zan kamaki yarinya, za ki yi bayani." Wani murmushi ta masa ta bi gefensa ta wuce. Shi ma gurin zamansa ya koma yana gani ta haye sama da ƙyar. Tausayinta yake ji ya kula ƙarfin hali kawai take. Bayan sun gabatar da sallar azahar a gidan a falon baƙi suka dawo falo, anan suka tarar an jera musu abincin su suka zauna. Can sama kuma iyaye mata ne a falon Nuratu suna cin nasu suna hira, maganar kunya ko surukai tuni sun jinginar gefe don jini ya haɗa su. Hussaina da Zaituna da Ikhram da suka ji labari kamar suyi tsuntsuwa. Nuratu tana ɗakin Dr Awwab a duƙunƙune cikin bargo a gadonsa, mugun zazzaɓi ne ya rufeta. Kiran wayarta Dr Awwab ya yi tayi don ya tabbatar ta ci wani abun bata ɗauka ba. Haka ya ƙira Rukayya ta sanar masa bata tare da su. Babu shiri ya miƙe ya nufi ɗakinsa don nan zuciyarshi ta kaisa. Aikuwa halin da ya ganta ya rikitasa, ruwan sanyi ya haɗamata ya mata wanka ya fito ya nema mata kaya cikin kayakin da take bari a ɗakinsa. Kan gadon ya kwantarta ya lulluɓeta. "Kin ci abinci? Ko in ƙira Dr Sageer ya duba ki. Yau dai babyna ya mana fallasa, kowa fa sai yasan shi yake wahalar ki." Kamar ta yi kuka tace. "To ka fita mana." "Kar wani yayi zargin wani abun muke." Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya. Ƙara turɓune fuska ta yi ta ƙi magana. "Bari in nemo miki abinci da magani kafin su tafi in ƙira Dr Sageer ya zo ya duba ki." Kai ta daga masa ya fita. Fruit salad ya sa ka Hassana ta haɗa masa ya ɗauki ruwa ya koma ɗakin. Da ƙyar ya lallaɓata ta saka abu a cikinta kafin ya bata maganin me haɗe da na barci. Tuni barci ya kwasheta ya lulluɓeta ya fito. Ƙarfe huɗu aka gama yanke shawarar Mami za ta kwana gidan Ammi ita da Kawu Muhammadu, yaran gidan Ummi gobe sai su koma. Kowa ya yi farin cikin haka, don ansan ƴan uwan suna buƙatar hira na musamman tsakanin su. Bayan sallar la'asar suka musu sallama suka watse. Ƴan matan sai da suka gyarawa Nuratu gidanta kafin su tafi bayan Dr Awwab ya sanar musu tana barci bata jin daɗi. Murmushi suka yi kowa yayi shuru da bakinsa don sun gano ta. Suna tafiya Dr Awwab ya kira Dr Sageer ya zo ya dubata, nan ya sanar masa irin haka zai dinga faruwar har sai cikin ya girma. Daga haka suka yi sallama. Zuwa dai dare jikin yayi sauƙi sai ɗan hajijiya. Daren duk motsinta zai tambayeta me take buƙata. ... Can gidan Baffa ɗakinsa ya sauƙar da Kawu Muhammadu don cewa yayi sunfi ƙarfin a ajiye su ɗakin baƙi. Kwana suka yi suna hira su biyun suna bawa juna labarin irin rayuwar da ya fuskanta. Ammi ma a ɗakinta ta sauƙe Mami. Ranar sun ga gata a gidan Baffa. Da asubahi Mami ta samesu suka ɗaura daga inda suka tsaya. Can ma ɓangaren gidan Ummi haka, ɗakinta ta sauƙe yaran Mamin, da taimakon mai aikinta ta musu komai su da yaransu. Ta ɗauko musu album na aurensu da babansu Awwab suna kallo. Duk su huɗun kamarsu ɗaya, dole yaransu suma kamarsu ya yi ƙarfi. Hassana ma dai ranar dole Abdallah ya barta ta kwana gidan, haka Hafiza ma. Washegari a gidan Ammi aka taru wajen ƙarfe goma sha ɗaya, hatta matan Baban Yaya da Sajeed sun zo da yaransu. Mami tun da ta ga ƴar Sumayya ta riƙeta duk inda ta yi yarinyar tana bibiyarta. Hatta Nuratu ta lallaɓa ta zo duk da rashin kwarin jiki da take ji. Kowo da ya mata ya jiki ya yi shuru, don sun gano musabbabin ciwon. Bayan gaisuwa aka zauna sake kafa hira. Har wajen karfe ɗaya suka ci abinci suka gabatar da sallah kafin su ɗauki hanya cike da kewar juna. Daren Baffa ya samu nasarar rokar Kawu Muhammadu ya dawo kusa da su Nijeriya. Ya ƙi amincewa don ya saba da zaman can, haka ya hakura ya barsa akan lokaci zuwa lokaci za suna kai masa ziyara, shi ma ya musu alƙawarin za iya zuwa tun da babu nisa. Haka kowa ya watse ƴan Damaturu suka koma, kowa ya koma gidansa. Amma Jidda dai tasha labari wajen Mami, ta mata murna sosai. Amira dai rumgume Mami ta yi tana murnar dawowarta babu kunya. "Mamina nayi kewarki, gidan duk babu daɗi. Ga fine Baby kin kawomin." Murmushi kawai Mami ta yi ta kalli Islam (Ƴar Sumayya) da ta saka kukan sai ta biyota, dole aka haɗamata kayanta suka zo tare. "Ki mata wanka ki bata abinci zan huta. Jikina duk ciwo yake." Daga haka ta koma ɓangarenta, Amma Jidda ta bita da kallon tuhuma tana murmushi. Amira ma jakar Islam ta ɗauka suka nufi bangaren Mami. Wanka ta mata ta bata abinci kamar yadda Mami tace ta hau mata wasa don yarinya ƙaramace ƴar shekara biyu sai dai bata da ƙiwa ko hayaniya. ... Bayan kwana biyun Mami ta kasa gane kanta, ciwon jiki ya sata a gaba sosai. Amma Jidda da Alhaji Mamman ido suka saka mata, don gani suke tasan abunta ɓoyewa take. Ita kuma har ga Allah ta ɗauka ta wuce level ɗinnan, bata kawo hakan a ranta ba. Ƙarshe dai dole Alhaji Mamman ya sa ta ziyaran asibiti ta dawo masa da damuwar da ta shiga na sakamakon ciki na wata ɗaya. Ranar da damuwa ta wuni Amma Jidda na lallashi. Da ta gaji ta ce. "Haba Amma. Nuratu ma fa laulayi na barta take yi, ita ce autana Bayan tsawon shekaru ashirin da huɗu na sake haihuwa. Haba don Allah in jera haihuwa da autana." "To ni ki haifa ki bani. Kinga dai ni biyu ne nawa, kuma ina son haihuwa Allah bai yi ba, ke kuma sun ishe ki naga alama." "Ba maganar wasa ba Amma. Abbansu ka yi magana asan ya za'a yi da cikin nan." Mami ta ƙarasa maganar tana kallonsa. Murmushi ya yi ya miƙe. "Shaidar kin koma gidan uban yaranki, tsohon zumanki, ki haifa muna so mu ko Jidda?" Kai ta ɗaga tana dariya. "Sosai ma, Allah yasa ma ki yi kunika(kwalba da indagi)...." "Ban ji bakinki ba Jidda." Mami tace tana miƙewa ta wuce ɓangarenta. Idan ta ƙara wani cikin bayan wannan ai ta kaɗe, balle yadda tasan Alhaji Mamman baya son tsarin haihuwa da za ta yi kunika zai so, ko girmansu ba zai duba ba. "Allah ka rufamin asiri ka sa daga wannan haihuwar ya tsaya. Wanda na haifa Allah ka albarkace su ka rayamin su. Ameen." Ta ƙarasa addu'ar tana shafawa ta shafa cikinta. Kunya sosai take ji, tana tunanin idan yaranta suka ji ya ya za su ji. .... Laulayin Nuratu ya fara sauƙi sai rashin ci duk ta rame. Dr Awwab ya rasa ya zai yi da ita, ban da maltina da peack milk bata iya shan komai sai wani lokaci fruit salad, sai kuma idan Ummi ta aiko mata abinci a gidanta na gargajiya, to shi ne za taci da ɗan dama. Haka suka ci gaba da kula da cikin har ya shiga wata biyar ta fara ƙoƙarin cin abinci kaɗan kaɗan, a hankali kuma kwaɗayi ya biyo baya kamar ta ci babu. Kullum Dr Awwab ya fita idan zai dawo sai ya siya mata duk abin da ya gani a hanya. Ummi duk bayan wani lokaci sai ta zo dubata haka Ammi ma da matan Babban Yaya da Sajeed duk sun kawo mata ziyara. Can gida ma kullum sai sun yi waya da su suna tambayarta lafiyarta, babu wanda ya sanar da ita labarin cikin Mami. .... Lokacin da yaran su ka ga ciki jikin Mami babu wanda ya yi magana, Muhsin kam kayansa ya tattara ya bar gidan ya koma gidan da Alhaji Mamman ya mallaka masa. Wannan kayan kunyar har ina. Tsakani da Allah kunya ya ji da ya ga cikin. Matan a hankali cikin dabara suka tambayi Mami watannin cikin ta sanar musu, suna ƙoƙarin taimaka mata haka Amira da tafi kowa murna. Islam kam ta dawo gurinta da zama ta ƙi komawa. Ammi, Ummi da Baffa duk sun kawo mata ziyara, haka Zaituna da Ikhram ma har da yaran su. Mami ta sha tsiya wajen Aunti Zarah da ta kawo mata ziyara ta ga cikin. Nauyin cikinta da laulayi bai sa ta bar sana'arta ba, domin an gama komai saura zuba kayan da tayi order za'a kawo mata. Haka Alhaji Mamman ma kasuwanci ya bunƙasa, shago sai cika yake, wani arziki da Allah ya bunkasa masa baya kwatantuwa. 'Tabbas Sadiya alheri ce' Abin da ya ke faɗa kullum don yasan irinta ne masu ƙashin arziƙi da ake faɗa. ... Bayan wata huɗu. #vote #comment #share MADUBIN GOBE 62. Pharty Bb. Wattpad phartybb. MURFI. *** Da ƙyar ya barta ta sauƙo ƙasan jin ana danna door bell kusan sau uku. A hankali take taka matattakalar benin don cikin jikinta ya girma sosai. Bayan ta gama sauƙar ta isa bakin ƙofar falon ta buɗe. Da kallo ta bi bakuwarta su. Yarinyar na neman shiga mata hanci ta kudundune. Rai ta haɗa tana riƙo kugu. "Lafiya? Ko kina buƙatar wani abu ne?" Murmushin gefen baki Binta ta yi tana jefa mata wani shegen kallo, kai ta girgiza kafin ta ce. "Gurin ƴata na zo. Bani guri in wuce Please." Ta ƙarasa maganarta tana ƙoƙarin bin gefe ta wuce. A zafafe Nuratu ta cafkota ta dawo baya. Cikin ɓacin rai ta hankaɗata baya ta nunata da yatsa. "Last warning da za ki ƙara kwaso shegun ƙafafunki ki shigomin cikin gidana. Banza marar kamun kai, jahila kawai." "Ni ce jahila kuma banza?" Binta ta ce da mamaki da baƙin cikin zagin da Nuratu ta mata ya shigeta. Kafin ta bata amsa ta yi kanta ta cakumo wuyan rigarta ko duban cikinta bata yi. "Ni ce jahila kuma banza. Don ubanki yau za ki mini bayani, sai in illataki yadda mijinki ba zai iya gane ki ba." Nuratu jin bayanta ta yi ya riƙe, da ƙyar ta samu ƙarfin kwace wuyar rigarta ta watsa Binta mari. "Ke kam mahaukaciya ce hala." A haukace Binta ta ɗaga hannu za ta rama marin da Nuratu ta mata ta ji tsawar da ya hargitsa falon da ƴaƴan hanjinta ta dakata. "Kuskure mafi muni da ƙazamin hannunki zai taɓa fuskar matata." Ta mutuƙar tsorata da ganinsa cikin wannan ɓacin rai. Baya ta ja tana ƙoƙarin fita ya buga mata tsawa. "Zan karya ƙafafunki ki ka kuskura ki ka bar falon nan." Cak ta tsaya tana rawar jiki, ba ta taɓa tsammani za ta ji tsoronsa haka ba. Gurin Nuratu ya ƙarasa, lokacin ta samu ta dafa kujera jin ciwon bayan ya kasa falawa, ga shi ya fara sauƙa maranta. Dafa kafaɗunta ya yi. "Babyna lafiya? Ta ji miki wani ciwon ne." Tamkar jira take ya yi magana, wani juyi da maranta yayi ya sata durƙushe ta dafe cikin. "Bayana. Marana, marana Hayat." Ta ce tana yarfe hannu. Ɗagota ya yi ƙoƙarin yi ta ƙasa miƙewa, kuka ta saka masa tana cafko wuyar rigarsa iya ƙarfinta. "Ka taimaka mini mana ka sakamin ido kana kallo." Rikice mata ya yi ya kasa komai, karshe ya ɗauketa gaba ɗaya suka nufi waje sai kuka take masa, bayan ya sa ta ya koma falon da sauri ya wuce ɗaki ya ɗauka mata mayafi ya sauko. A rabe ya samu Binta ya watsa mata wani mugun kallo. "Ki shirya shiga gidan yari idan wani abu ya samu matata ko abun cikinta." Daga haka ya wuceta ya fita. Ba tasan fitsari ya ɗisa a jikinta ba sai da ta fara tafiya ta ji danshi. Ko takai ba ta bi ba a gaggauce ta bar gidan, kai tsaye gidan yayarta Aunti A'isha ta nufa, sai lokacin ta samun damar yin kuka, ta sa ka Aunti A'isha a gaba. "Aunti wallahi na hakura da shi, ni ban zauna ba, kuɗina bai zauna ba, ku ba ku zauna ba, kun hanani kula masu so na, ga shi yanzu wa gari ya waya. Wallahi ko shi ne autan maza na hakura da shi. Yanzu idan wani abu ya samu matarsa ko cikinta fa ni Binta na shiga uku gidan yari zai kai ni. Wallahi zai aikata ko?" Ta rushe da kuka har da ɗaura hannu a saman kai, can ta miƙe zumbur ta shige ɗaki ta kulle kanta. Kamar tayi hauka take ji, burinta Nuratu da abin cikinta suna lafiya don ta hango tsantsan rashin tausayi a idanuwansa. .... Can asibiti suna isa aka karɓi Nuratu aka wuce da ita ɗakin masu haihuwa. Likita tana dubata ta fita ta sanar Dr Awwab haihuwace ya kawo kayan haihuwa, bai gama sauraren su ba ya fita a ɗakin. Gida ya je ya dauko kits din da suka gama haɗawa jiya don EDD ɗinta saura sati biyu. Yana ɗauka ya koma asibitin. A hanyar dawowa ya sanar Ummi, tuni ta nufi can bayan ta sanar da Ammi. Dr Awwab dai ya kasa ya tsare ya ƙi fita don likitar tayi tayi ya fita a ɗakin ya ƙi, ƙarshe ya sanar mata shi ma Dr ne amma na ƙwaƙwalwa kuma abokin Dr Sageer ne shi. Dole ta barshi, duk ya cikata da korafin matarsa tana shan wahala tasan ya za tayi. Nuratu kam haushinsa take ji yadda ya sata a gaba ya zauna, duk motsinta da juyi yana taimaka mata kamar shi ya ke karɓar haihuwar. Ba tayi wani dogon naƙuda ba awarta ɗaya ta haiho yaronta namiji. Murna gurin Dr Awwab ba a magana, a gaban likitar ya sunkuya ya sumbaci leɓɓenta. "Thank you My Baby." Murmushi kawai ta masa, aka miƙa masa Babyn ya karɓa ya rumgume abunsa yana sumbata. Bayan an gyara Nuratu aka mata alluran barci aka kaita ɗakin hutu. Waje ya kaiwa su Ummi yaron suka gani kafin ya koma ɗakin ya kwantarsa kusa da mamarsa. Kafin Nuratu ta farka ɗakin ya cika da ƴan uwan su. Sai yamma lis ta farka da taimakon Ammi ta yi wanka da ruwa mai zafi har da kukanta. Bayan ta fito aka bata abincin da Hassana ta kawo, ta ci sosai da ta gama ta jingina jikin gadon. Kowa ficewa yayi ya bar musu ɗakin daga ita sai Dr Awwab sai babyn su. Ɗaukar Babyn yayi ya ɗaura mata saman cinyarta. "Ba ki tambayi me ki ka haifa ba, sannan kin cika cikinki saura na Babyna." A kunyace ta girgiza kai. "To ai zan gani ka yi sauri ne." "Na yarda da wannan, kunyar fulani za ki nunamin akan ɗan fari, daɗinta jini ɗaya mu ke dake. Yanzu abawa Babyna abinci, ya yi hakuri fa don ma na basa zamzam da dabino." Yana faɗar hakan ya ɗaura hannunsa saman zip ɗinta ya zuge. Riƙesa tayi tana turɓune fuska. "To ka juya ko ka fita." Kumatunta ya sumbata yana murmushi. Kunyar Nuratu yana burgesa wani lokaci. Juyar kansa ya yi gefe yana cewa. "Me kuma ya rage, abun da ragowana za'a basa." Yi ta yi tamkar bata ji sa ba. Mayafi ta jawo ta rufa musu, a nutse ta ciro abincinsa tamkar dama ta iya, saitama Babyn ta yi a baki sai dai ya kasa isowa don kansa ya yi ƙasa, haka ta ɗan sunkuya sai dai za ta gaji da wuri. A hakan ta soma basa, tuni ya karɓa tamkar jira yake. Kanta ta ɗago dan jin shuru, gani ta yi Dr Awwab ya zuba musu ido yana kallo. Harara ta watsa masa ta sunkuya ba ta ce komai ba. Miƙewa ya yi ya fita, tun da ta fara kokuwar bawa Babyn abinci ya ke kallon su, ya taimaka mata yana tsoron ta ƙi. Yana fita Hassana ya ƙira ya aiketa gurin Ammi. "Ki cewa Ammi ƴarta na buƙatar taimako." Daga haka ya fita a asibitin ya nufi gida. Aiken ta kai gurin Ammi, da sauri Ammi ta shiga ɗakin, ita ta taimakawa Nuratu ta nuna mata yadda za ta shayar da Babyn, ta ɗago mata shi sama, sai lokacin ta ji daɗi. Bayan ya ƙoshi ta cire masa ta kwantarsa. Yaron dai ba za tace ga wanda yake kama da shi ba, don jaririn awannine, sai dai hasken fatar mahaifinsa ya ɗauko. Ammi ne ta kwana da ita, Ummi da Hassana gida suka koma, don ita ma cikinta har ya fito kusan watanni huɗu. Washegari da safe aka sallamesu, gidanta aka wuce da ita. Hauwa matar Babban Yaya, da Amina matar Sajeed, da Hassana da Batula su ka haɗu su ka taimakawa Nuratu da gyaran gidan da girki, su suka mata komai. Ammi ta tare ɗakin Nuratu ita take mata wankar ruwan zafi mai rai da lafiya, Ummi dai da akwai ɗan kunya tsakinin su, ko ita Nuratun ba ta sakewa da ita duk da ta kasance matar ƴaƴan mahaifiyarta. Abdallah, Baban Yaya, Sajeed duk sun zo mata barka har Baffa, sun mata alheri ita da Babyn. Ƙarfe biyu na rana Aunti Hasiya da Aunti Zarah suka iso, har da Walida da babynta da ta girma, sai Amma Jidda da ba ta taɓa zuwa ba. Aunti Rahma laulayi take, Rukayya kuma cikinta ya fara girma sai washegari suna za su zo. Amira tana son zuwa halin da Mami take ciki ya sa ta haƙura sai Islam da ta bi Amma Jidda. Cikin Mami ya fito sosai kamar yau za ta haihu. Nuratu ta yi murnan ganin ƴan gidansu, nan gidan ya ƙara hargitsewa da hayaniya. Musamman Nuratu ta ƙira Rufaida ta faɗamata. Ai kuwa washegari sai ga ta da mijinta da yaranta. Ƴan uwan Nuratu sunyi mamakin ganin Rufaida sanin ƙanwar Mufid ce. Wuni ta mata guda da yamma ta koma akan washegari suna tana tafe. Gidan bai rabu da mutane ba har washegari suna. Ana washegari suna Col. Ahmad ya zo shi da Hussaina da cikinta ita ma wata huɗu daidai watannin cikin Hassana. Mama yawuro da Kawu Muhammadu sun zo. A ranar Aunti Rahma da Rukayya su ka zo. Ranar suna Yaya Al'ameen ya zo wuni a tsaitsaye don Hafiza haihuwa yau ko gobe ita ma. Alhaji Mamman da Mami sun haɗawa yar sun kayan goyo na ban mamaki, tamkar amarya za a haɗawa lefe haka Alhaji Mamman ya haɗawa Nuratu setin akwati guda shida da Babynta gudu shida, har kayan ƴan shekaru biyar ya zuba. Har lokacin ji yake bai kyautata mata ba, kamar ya yi kaɗan abun da ya bata. Har sai da Mami ta nuna ɓacin ranta akan ya isa kayan kafin ya hakura, amma sai da ya saka mata kyautar mukullin mota. Nuratu ta yi kuka da idanuwanta na farin ciki, ta rumgume Abbanta tana godiya. Haka ƴan Maiduguri ma sun haɗa mata. Dr Awwab ma ya yi nasa na fitar suna. Oga kwatakwata Col. Ahmad Tafida da ya samu takwara ya haɗo nasa kayan. Umma da ƙannenshi ne mata suka kawo kayan. Ya ce kuma kar a ɓoye masa suna a ƙirasa Ahmad ɗinsa. Ƴan gidan su Col. Ahmad sun ga karamcin wannan bayin Allah, Umma har kunya ta ji. Nuratu dai ranar ta rasa wani irin murna za tayi. Musamman da ta ji sunan da ya saka jariri. Sunan mutumin da ya fara taimaka mata a rayuwa tun kan yasan ita wacece, ya tsaya mata ta ƙwaci haƙƙinta. Haka taro ya watse lafiya aka ci aka sha kowa ya koma gida. Da ƙyar Dr Awwab ya bar yayun Nuratu suka tafi da ita gida wanka kamar yadda ake yi a al'adance, har sai da Ummi ta sa baki ya haƙura akan wata ɗaya tak yaba su ba zai jira arba'in ba. Bayan isar su gida ɓangaren Amma ta zauna don Mami ma na ji da kanta. Amira na kula da Mami sosai, Amma na kula da Nuratu da Babynta, gefe ɗaya kuma tana mata gyara na musamman ciki da waje. Lokacin da Nuratu ta ga cikin Mami kasa shuru tayi ta hau murna. Har da cewa. "Yanzu Mami ƙanwa za ki haifa mini. Shikenan ni ba auta bace. Ki haifamin mai kama da ni." Ta faɗa kuma tana ɓata rai. "Sai ki haɗa da naki ki raina." Mami ta ce tana harararta daga haka tabar mata gurin. Dariya Nuratu ta yi ta riƙe baki. 'Wannan rabo haka, Mami da ciki.' Tace tana kuma sakin murmushi ita ɗaya. ... Satin Nuratu biyu Hafiza ta haihu, duk gargaɗin Dr Awwab kar ta yi tafiyarnan haka ta yi kunnen ƙashi ta bi masu zuwa suna. Anyi suna lafiya yaro ya ci sunan Abban sa suna ƙiransa Aarif. Washegarin su Nuratu su ka dawo, da mugun mura Ahmad ya dawo don sanyi ya shigesa. Duk yadda taso ɓoyewa Dr Awwab sai da ya sani. Ranar ya ƙirata Ahmad yana mata kuka ya ji muryarsa a shaƙe. Ranar taga ɓacin ransa da faɗa. Ƙarshe ta kashe faɗar in da ta saka masa kuka. "Wallahi na kula yanzu ka fi son Ahmad a kai na. Dama an faɗa ai, da zaran mace ta haihu son ya ke komawa kan yaransu." Dafe kansa yayi ya ajiye fushin a gefe ya hau lallashi. "Idan ba so ki ke ki ganni yanzu cikin dare ba ki daina kukan nan Please. Ahmad kuma ƙarami ne bana son kina yawo da shi, gobe zan shigo amma kafin nan ki kaishi asibiti don Allah Babyna. And you know i missed you." "Babu wani missing ɗina da ka yi." Ta ce tana tura masa baki kamar yana kallonta. "Seriously a aikomin kiss." Kafin ya rufe baki ta sakar masa wani kiss mai ƙara, har sakar kansa ya ji kafin ta yanke wayar tana dariya. Yau da tana gabansa tasan sai ta faɗi yaren garin su. Bangarensa kasa ƙiranta ya yi don yasan idan ya ƙira komai zai iya faruwa. Washegari ta kai Ahmad asibiti aka basa magunguna suka dawo gida, ƙiransa tayi ta sanar masa, anan ya bata hakuri rashin zuwansa aiki ya tsayar da shi sai wani sati. A ranar Rufaida ta kawo mata wuni guda, sun sha hira sosai har daren kafin mijinta ya zo ɗaukarta. A tsorace Rufaida ta sanar da ita Mufid ya kusa aure. Da mamaki buɗar bakin Nuratu ta ce. "Allah ya basu zaman lafiya. Ina labarin waɗannan abokansa biyu?" "AA ya rasu kusan shekaru biyu yanzu, Faisal kuma ya koma gurin dangin mahaifiyar sa. Ina ƙara ba ki hakuri Nuratu..." Da sauri Nuratu ta hanata ƙarasa maganar ganin za ta dawo da hannun agogo baya. "Don Allah ya isa haka Rufaida, komai fa ya wuce. Allah ya ji ƙansa, shi kuma Allah ya sa sanadin shiryuwarsa kenan." ... Kwana biyar da sunan Hafiza, ranar wata juma'a Mami ta tashi da naƙuda. Cikin gaggawa Abba ya dawo suka wuce da ita asibiti, wuninsu guda kafin ta haifi ƴaranta biyu maza. Murna cikin dangin ba'a magana. Muhsin ajiye kunya ya yi ya zo kallon ƙannenshi maza da su kaɗai ya ke da su a duniya. Kafin suna mutane da yawa sun zo daga Maiduguri, Gombe, Nijar. Alhaji Inuwa da matarsa da yaransa duk sun zo, Kawu Muhammadu, Ummi da Hassana, Ammi da yaranta da matansu. Haka Zaituna da Ikhram sun zo takanas daga Abuja ganin ƙanwar mahaifin su. Hussaina da Col. Ahmad duk sun zo. Hatta Munirat ta zo, Suwaiba ma da ta koma gida bayan auren Mami ta zo. Hafiza kam dama tana gida yin wanka ita ma. Ranar suna yara suka ci sunan Aliyu Haydar da Umar Faruq. Alhaji Mamman ya taka rawar gani tamkar yanzu aka soma masa haihuwa. Haka Amma Jidda ma tamkar ita ta haihu. Haka yaran Mami ma su suka tsaya mata kan komai da Aunti Zarah. Ba su yi wani taro ba, tsakaninsu suka yi komai. Ranar suna bayan an watse wajen ƙarfe takwas, Mami ta shige ɗaki tare da yaranta, sunyi wanka sun kwanta don huta gajiya. Amma ta koma ɓangarenta, Ameera ta yi wa Islam wanka suma sun shige ɗakinta suna kallo. Hakan shi ya bawa Nuratu damar yin shirinta a nutse. Wanka ta yi ta saka kayan barci mai kauri, ta yi wa Ahmad wanka ta saka masa kayan barci shi ma sai ƙamshin turare da hoda ya ke. A kafaɗa ta ɗaukesa suka fita zuwa bangaren baƙi. Yana zauna ɗaya daga cikin kujerun falon ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya. Sallamarta ya sa shi ɗago ido ya amsa yana buɗe hannayensa alamar su ƙarasa jikinsa. Gurinsa ta ƙarasa ta ajiye masa Ahmad a cinya tana murmushi ta ce. "Ina zuwa." Daga haka ta fita, Ahmad ya ɗauka ya hau sumbata yana ƙiransa tamkar zai amsa. Yaron ya yi bulbul yanzu kam kamanninsa da shi sai fitowa ya ke. Dawowar Nuratu ya sa shi dubanta, faranti ne ɗauke a hannunta ta ƙarasa ta ajiye saman table ɗin falon. Ahmad ya kwantar gefe ya saka hannu ya fizgota jikinsa. Zama ya gyara mata cikin jikinta kafin ya fara sumbatarta daga fuska zuwa wuya, ƙarshe ya tsaya a bakinta bai mata magana ba, martani ta fara mayar masa tuni suka kusa mantawa da gidan surukai suke. Shi ne ya yi ƙoƙarin dakatar da su ya rumgumeta yana kissing ɗin tsakanin wuyarta. Idanuwanta lumshe tana shaƙar ƙamshin turarensa, duk ya kashemata jiki. Ƙasa ƙasa ya yi da murya ganin yanayinta ya canza ya ce. "Ki na son abu amma shi ne ki ka kasa komawa inda za a ba ki." Numfashi ta sauƙe ta ɗago jikinta, maganar ta basar tana ce wa. "Abinci fa? Ko ruwa ban ba ka ba." Hancinta ya ja yana murmushi ya ce. "Yawunki ya wadatar da ni komai." "Ni wallahi sai ka ci. Don kai fa na shiga kitchen na girka da kai na." Ta ce tana bubbuga ƙafa a ƙasa. "Yarinyar nan kin girma har da yaro amma kina ƙara shagwaɓewa. To zubamin kaɗan." Gwalo ta masa ta miƙe ta fara aikin zuba masa. "Ai rainon ka ce." Murmushi ya yi ya ɗan kishingida yana mata kallon ƙasa ƙasa ya ce. "Seriously yaushe za ki koma?" Sai da ta gama saka masa couscous da yasha kayan lambu ta zauna kusa da shi ta ɗaura plate ɗin saman cinyarta, don ita za ta basa tasan zai faɗa. Hannunta ta wanka ta ɗiba ta kai bakinsa ya buɗe ta saka masa yana murmushi. "Saura sati biyu kuma sai nayi yawon arba'in. Zan bi gidajen ƴan uwa da abokan arziki na gaishe su. Sai dai kusan nan da sati uku." Ƙwarewa ya kusa yi, da sauri ta basa ruwa yasha tana masa sannu. Sai da ya nutsu ya riƙo hannunta na hagu da yake empty. "Bana son wannan al'adar Hausawar don Allah. Idan kuma ya zama dole to kiyi cikin sati biyun da ya rage miki. Next upper week zan zo ɗaukar ku, na gama magana." Dariya ta yi ta ɗaga masa kai. "Yes Sir an gama." Kusan goman dare kafin ya musu sallama da ƙyar ya tafi hotel ɗin da ya kama. Ita ma kayan ta tattare ta wuce ɗaki ta kwanta cike da buƙatar mijinta. Washegari Dr Awwab ya zo ya musu sallama ya koma Maiduguri. ... Cikin sati biyun kamar yadda ya faɗa ta gama ziyaran ƴan uwa da abokan arziki, da taimakon Ameera ta haɗa kayanta gaba ɗaya. Ameera da Islam basa son tafiyar don sun saba da ita musamman Ameera da wani mugun son Ahmad take, don ma ga ƴan biyun Mami. Ranar da Dr Awwab ya zo ya kama weekend, bayan ta yi sallama da ƴan gida ya ɗauki matarsa da ɗansa suka koma. Gidan Ummi suka fara sauƙa don ɗaukar Hanan da Batula. Daga nan sai gidansu. Batula girki ta ɗaura na dare, don gidan babu datti jiya ta zo ta gyara. Nuratu ɗakinta ta wuce ta watsa ruwa ta ma Ahmad shi ma suka yi shirin barci, sallar isha'i ta gabatar. Kasa suka sauƙa lokacin Dr Awwab ya dawo daga sallah. Bayan sun ci abinci kusan ƙarfe goma Dr Awwab ya kora Hanan da Batula ɗaki ya kashe telebijin ɗin. Dariya Nuratu ta yi ta ɗauke Ahmad suka wuce sama. Wani wankar tayi ta bi lungu da sako na jikinta da turare. Bayan ta gama ta saka wani kayan barcin mai shegen ƙyau, ta ɗauki Ahmad suka nufi ƙofar fita. Dr Awwab yana shirin shigowa suka haɗu a ƙofar. Ahmad ya karɓa ya kwantar cikin gadonsa ya lulluɓesa ya masa addu'a, kafin ya juya gurin Nuratu. Janta kawai ta yi ta faɗo jikinsa suka zube saman gadon, da mukunnin gefen gadonta ya kashe wutar ɗakin. Daga nan ya buɗe musu shafin soyyaya, sai da abu ya ƙanƙama ganin Dr Awwab yana shirin bin hanyarsa ta taresa da sauri. "Menene kuma?" Ya faɗa da ƙyar jin wani sabon salon da za ta masa. Ƙasa ƙasa ta ce. "Hayat babu wani irin tsarin haihuwa da za mu yi?" "Wani irin kuma tsarin haihuwa? You means family planning?" Kai ta ɗaga masa ƙasa ƙasa tace eh. Tsaka ya yi ya saketa yana komawa gefe yana sauƙe numfashi. Ganin ransa ya ɓaci ya saka Nuratu rumgumesa. "Ka yi haƙuri don Allah, ban san hakan zai ɓata maka rai ba." "Bana son tsarin haihuwa Noor kwata kwata. Ko har kinyi?" Da saurinta ta girgiza kai alamar a'a. Rumgumeta ya yi ya ce. "To bana so. Ki haifamin ko ɗari ne ina so in dai daga gareki ne ina so." Kirjinsa ta buga cikin shagwaɓa. "Ɗari dai Hayat." "Yes My Baby love." Ya ce ya rufe mata baki da nasa ya fara kissing ɗinta. Duk kwanakin da ya ke binta bashi sai da ya fanshe a daren. Tamkar yau ya fara saninta haka ya rikice mata ya hanata sakat. ... Tun ranar da lokacin ahlin suka buɗe rayuwarsu cikin so da kauna, yarda da kyautatawa junansu. Kowanne na ƙoƙarin farantawa ɗan uwansa rai. ... Bayan wata biyar. Lokacin watan Ahmad takwas, Hassana ta haihu ɗa namiji, bayan sun sha suna da sati Hussaina ta haihu ɗanta namiji ita ma. Haka suka tattara suka tafi suna Ibadan, hatta Mami wannan karon ta je da yaranta don ganin gidan ƴar ƙaninta. Ana suna suka ɗauko Hussaina don yin wanka a gida kamar yarda al'ada yake. Anan Ummi ta dinga kula da yaranta da jokokinta. Bayan ƴan biyu Rukayya ta haihu, wannan lokacin ma mace da namiji ƴan biyu, dole dai ta zama maman yan biyu sau biyu. Ikon Allah kenan. Ƴan biyun Mami Haydar da Faruq sai girma suke sunyi wayo. Alhaji Mamman tamkar ya mayarsu ciki, haka Amma Jidda a gurinta suke wuni. An saka ranar Muhsin da autar gidan Alhaji Inuwa mai suna Laila. Tun zuwan su sunan Mami ya ganta, bai barta ba sai da ya samu shiga cikin zuciyarta. Iyayen sunyi murnar jin hakan. Bayan yin komai aka tsaida ranar biki wata biyar. A lokacin Ameera ma ta gabatar da saurayinta aka haɗa ranar bikin duka lokaci ɗaya nan da watanni biyar. Ƴan biyun Ummi suna gama wanka kowacce mijinta ya zo ya ɗauketa suka koma. A wannan lokacin Nuratu da Dr Awwab da Hanan suka kaiwa Zaituna da Ikhram ziyarar kwana ɗaya ɗaya suka dawo gida. ... BAYAN SHEKARU BIYU. Tun lokacin Nuratu ba ta ƙara haihuwa ba, babu ciki babu alamar sa sai fatan samu. Dr Awwab duk ya damu don ya lura haihuwarta akwai tazara sosai, har shekara biyu. Hakan yasa ya matsa mata ta yaye Ahmad ko za ta samu ciki. Ganin yaron ya yi wayo ga ƙiba, yana cin komai yana tafiya ga haƙora ya sa ta yayesa. Ai kuwa yayen da wata biyu sai ga ciki, murna gurin Dr Awwab ba a magana, tamkar lokacin ta fara samu, sai dai wannan karon ba jiri ko zazzaɓi sai amai da kasala. Haka su ka ci gaba da rainon cikinsu. Hafiza ta ƙara haihuwar mace mai sunan Amma Jidda suna kiranta Nana. Walida ta ƙara haifar namiji mai suna Ayaan. Aunti Hasiya ta ƙara haifar namiji mai sunan Alhaji Mamman suna ƙiransa Khalifa. Lailai matar Muhsin ta haifi mai sunan Mami suna ƙiranta Miemaa. Sai Ameera da yau ko gobe don kusan shekara da aurensu kafin ta samu ciki. Mami tun lokacin babu haihuwa ita ma ɓangarenta. Addu'a ta yi kuma Allah ya karɓa. Ƴan biyunta sun yi wayo sosai, sai kyau da bawa mutum sha'awa. ... Cikinta ɗan wata shida tasa a gaba ta zauna, duk da yanzu babu amai da kasala sai kwaɗayi, idan babu kayan kwaɗayi kuma yawu. Rai take ta haɗawa bayan barin Dr Awwab gurin. Tun safe take roƙarsa akan maganar fara aikinta yana basarwa. Gefenta ta kalla da ta ji hayaniyar faɗa, Hanan da Ahmad ne suke wasa sai hargitsa kayan gurin ya ke tana gyarawa tana faɗa. Tsawa ta daka musu don sun isheta. "Ku bar gurin nan ko in ɓata muku rai." "Mimi wasa fa muke Ahmad yana ɓatawa ina gyarawa." Hanan ta faɗamata kamar yadda Dr Awwab ya faɗamata ta daina ƙiranta Aunti sai Mimi. Tsaki ta yi tana ƙoƙarin magana aka danna bell. Batula ce ta fito ta buɗe daga kitchen tana bawa mai sallamar guri ta shigo. Kallo ɗaya Nuratu ta mata ta ɗauke kai. Ita ko idonta kan Hanan da Ahmad kafin ta dawo da kallonta kan Nuratu da cikinta. Sallama ta musu, ciki ciki Nuratu ta amsa, ba ta ce mata ga gurin zama ba don kanta ta zauna ɗaya daga cikin kujerun falon tana gaishe da Nuratu. "Lafiya." Ta amsa ƙasa ƙasa. Hannu ta saka a jakarta ta ciro kati ta ajiye saman table ɗin falon. "Gayyatar ku nake zuwa ɗaurin aurana nan da wata ɗaya, fatan za ku zo ko don albarkacin Hanan." "Insha Allah, Allah ya kaimu. Allah ya sanya alheri." "Ameen." Ta amsa da shi ta miƙe tsaye ta ƙara kallon Hanan. Kwata kwata yarinyar ba ta da niyar zuwa gaisheta. Ƙarfi da ya ji Dr Awwab ya raba su. Ganin irin kallon da take mata yasaka Nuratu ƙiran Hanan. "Hanan zo nan." Babu musu ta barwa Ahmad kayan wasan ta taho gurinta tana amsawa. "Ki gaishe da Aunti Binta. Auntinki ce ita ma, ai kinsanta tana zuwa gidan Ummi." Kai ta ɗaga ta masa kusa da Binta tana ce mata. "Ina wuni Aunti." Rumgumeta Binta tayi ta saka kuka. Tamkar ƴar uwarta Nusaiba sai bambancin kama. Murya kam sak nata duk da muryar yarinya ce. Ita kanta Nuratu ta bata tausayi, ɗan uwan jini ya wuce wasa. Da ƙyar Binta ta tsaida hawayenta ta miƙe. "Zan wuce Noor sai wani lokaci. Kar Doctor ya dawo." "Na gode sosai inshaAllah za ki ganmu." Kai ta jinjina ta fita tana waiwayen Hanan. Bayan fitarta Nuratu ta ɗauki katin ta wuce sama. Da daren suna kwance akan gado, hannunsa saman cikin Nuratu yana shafawa, har lokacin ta ƙi sakar masa fuska. Tunawa da zuwan Binta ya sa ta ƙiran sunansa ta haɗa da cewa. "Hayat ɗazu Binta ta zo, ta kawo katin aurenta tana gayyatar mu." "Allah ya kai mu." Kawai ya ce bai ƙara komai ba. Jin haka ta ɗaura hannunta saman nasa da ya ke saman cikinta. "Wai me ya tsorata Binta. Ni duk tausayi ta ba ni." Murmushi ya yi ya sumbaci kumatunta ya ce. "Babu komai kawai tsorata ta nayi wancan zuwanta." Ita ma murmushin ta yi ta ce. "Aikuwa ta tsorata sosai kusan shekara uku fa. Kuma a tsorace ta ke har yanzu." Bai ce komai ba shuru ya ɗan biyo baya can ta ce. "Hayat maganar aikina." Basarwa ya yi kamar ba zai yi maganar ba sai da ta ƙara maimaitawa ya ce. "Ki hakura da aikin nan Babyna. Zan biyaki biyun abin da za ki samu, ki zauna a gida ki kula da ni da yarana." Shuru tayi kusan mintuna biyar tana tunani a zuciyarta. Dama sha'awar aiki take, kuma don ta kula da kanta da Maminta da ta sha wahala akanta. Kuma yanzu ga shi komai ya wuce, sun samu jin daɗin rayuwa tamkar babu abin da ya faru. "My Baby " Dr Awwab ya faɗa yana juyar da ita suka fuskanci juna. Kanta ta tura kirjinsa ta rumgumesa. "Na hakura Hayat, ba sai ka biyani da komai ba, Allah zai ba ni lada." "InshaAllah ƴar aljanna, Uwar gidan Awwab har a Aljannahtul Firdausi." Ya faɗa yana ƙara ƙarfin rumgumeta kafin ya ɗago fuskarta ya haɗa bakinsu. Da ƙyar ya bata damar furta. "Insha Allah." .... Bayan wasu watanni cikin daren juma'a Nuratu ta tashi da naƙuda. Cikin sauri Dr Awwab ya kwasheta da kayan haihuwa sai asibiti. Suna zuwa aka karɓeta, sai gabanin asuba ta haiho ƴan biyunta mata. Murna gurin alhalin ba'a magana musamman oga kwata kwata. Kafin wayewar gari dangi na cikin Maiduguri sun cika ɗakin. Sai da suka wuni aka sallamesu. Wannan karon ma Ammi ne ta mata wankan jego. Washegari cikin ƴan Damaturu su ka zo ciki har da Ameera da bata taɓa zuwa ba da babynta yar wata uku. ... Da daren Dr Awwab da ya shigo ganin babies Nuratu ta rokesa alfarma. "Doctor idan har ba ka musu huɗuba ba ina neman alfarma." "My Baby kinfi ƙarfin alfarma wajena, faɗi ina jin ki." Ajiyar zuciya ta sauƙe a dadare ta ce. "Ina son ka sakawa Amna Jidda da Aunti Zarah takwara wato Hauwa da Fatima. Mutane biyun nan sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar Mamina. Ina son kyautata musu in faranta musu, sai dai ban san da menene ba. Ammana tunda Allah ya kawo hakan ina fatan zai faranta musu." Fuskarta ya shafa da ɗayan hannunsa yana murmushi. "Me yasa ki ke son sakawa wanda ya miki alheri da alheri kullum." "Saboda ya ji farin cikin da ya sani lokacin da nake neman farin ciki na rasa." Sunkuyawa yayi ya sumbaci ƴan biyun ɗaya bayan ɗaya. "Allah ya raya mana Hauwa da Fatima." Rumgumesa ta yi cikin farin ciki da ɗan guntun hawayenta ta ce. "Ameen Hayat na gode." "Ki riƙe godiyarki sai bayan sati uku." Kashemasa ido ɗaya ta yi ta ce. "Allah ya kaimu." Hancinta ya lakace ya miƙe. "Ameen yarinya za ki yi bayani, sai kin zo kina kuka kina cewa in barki." Murmushi ta yi shi ma ya yi yana fita. Ranar suna yara suka ci sunan Hauwa da Fatima. Bayyana farin cikin mutane biyunan ba a magaba, sun ji abun ba zata a gurin da ba su taɓa tsammani ba. Haka Mami ma ta yi farin ciki sosai har tafi su yi. Duk wadda yasan Aunti Zarah da Amma Jidda ya taya su farin ciki wannan karamci. Aunti Zarah hatta mijinta da yaranta da ƙannenta sun zo. Haka Amma Jidda mahaifiyarta da yayanta Alhaji Tukur ya zo. A ranar ya nema keɓewa da Alhaji Mamman. Bayan gaisuwa sama sama don Alhaji Mamman ya ƙi sake masa fuska ya dubesa. "Mamman sai na ji wani zance kuma. Wai ka mayar da Sadiya, bayan haka ma wannan yarinyar ba ita bace silar komai." Wani kallo Alhaji Mamman ya masa ya gyara tsayuwarsa. "Tukur kenan, ka ɗauka har yanzu Mamman ɗin da ka sani a bayane jahili. To wannan wani ne. Kar ka manta Tukur, kai ka jawomin komai kuma ƙarshe ka zare hannunka ka ɗauki iyalenka ka bar ƙasar. Yanzu ka dawo ka ƙarasa sauran rushe rayuwar ma'auratan ne ko yaya. Wallahi alfarmar Jidda ka ci na ke kulaka kar ta fuskanci wani abun, don ban taɓa sanar da ita kai ɗin wanene a baɗini ba. Don haka ka fita a harkata da iyalina, ka sama rayuwata gaba ɗaya." Daga haka Alhaji Mamman ya kaɗa babbar rigarsa ya barsa a tsaye a gurin. Kafaɗa ya ɗaga yana taɓe baki alamar shi ya sani. ... Bayan suna Nuratu ta ci gaba da rainon yaranta da taimakon Batula take wasu hidimomin gida, yarinyar akwai ƙoƙari. Nuratu ne take girki, ita ta ke sauran ayyuka. Rayuwar Nuratu ya zamto haske daga duhun da ya mamaye. Ya yalwarta da so da ƙauna da farin ciki daga rashin komen cikinta. Rayuwarta tafe yake yanzu cikin haske da daidaitacciyar hanya. Nuratu ta zamto MADUBIN GOBE abin dubawa mai Haske ga wanda suka tsinci kansu cikin hali irin nata ... Allahamdulillahi ƙarshen labarin MADUBIN GOBE kenan. Sadaukarwa ga duk ƴa mace babba, tsohuwa, magidanciya, budurwa, ƙaramar yarinya da ta tsinci kanta a hali na fyaɗe. Allah ya ba ku danga da cinye wannan ƙaddara da jarabawar, ba wai Allah baya son ku ba ne ya ɗaura muku. Sai don ya jarabci imanin ku. Fatan kuma masu wannan hali su dai na. Mai hali irin na Mufid ya tuba ya bari, wanda ya ɗauki duniya ba abun komai ba sai gidan jin daɗi. Ƙarshe tun a duniya Allah ya nuna masa sakamako da danne haƙƙin wani. Kuskuren da na yi ciki Allah ya yafe mini. Saƙon ciki Allah yasa ya isa inda na ke fata. Ƙofar ƙorafi ko gyara da tambaya a buɗe yake. Godiya ga masu comments musamman yan wattpad, gaskiya kun nunamin ƙauna. Na gode muku sosai. Ƴan WhatsApp ma haka musamman yan group ɗina PHARTY BB NOVELS, na gode Allah ya bar kauna da zumunci. Sa sauran manhajar facebook da Telegram. Masu buƙatar tsofin littafaina akwai a Okada book kyauta ne. Sai mun haɗu a sabon littafina mai suna DUHUN ZUCIYA bayan Ramadan inshaAllah ya kaimu da rai da lafiya. Ma su jiran FARHA mu haɗu bayan Ramadan za mu ci gaba. Kar ka bari a ba ka labarin DUHUN ZUCIYA, labari ne da ya ƙunshi abubuwa da dama kama daga hassada da son zuciya, ƙyashi da tsana. Sai mun haɗu kawai domin shi ɗin dabanne da sauran. Bissalam. #onelove #phartybb #vote #comment #share My new Book GOBE DA NISA WhatsApp me 07037487278