[23/06/05, 12:30pm] Yusrah Musa Abubakar📝 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💰'DAN MILLIONAIRE💰 ('Dan miloniya) WHATAPP NO: 📱+2349055273614 YUSRAH MUSA ABUBAKAR Mrs Al'ameen Ahmad ce. (*)(SHORT STORY)(*) 📚 LITTATTAFAI NA 👑Yarima Abdul-maleek 🌹Rayuwa biyu 🍇Safreeyyah 🎉Haskena sauban 🎀 Mina-Umer 🌷Karuwar boye 💰'Dan millionaira. Ga me bukatarsu ya tuntube ni ta wannan number👉 09055273614 littattafai na free book ne ga duk wani masoyi na a duk inda yake afadin duniya I love u with all my body and heart💞. 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 🏡 home of hospitality and 🕊harmony. In the of Allah the most benefits and the most merciful we love our nabeey s a w we like him and peace be upon him ameen🙏👏. Some say hello some say hay but in islamically said assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatihu. Tofa reader's na kumin afuwa wannan karon son kai zan nuna sosai first page na yan group dina ne Annuri ina alfahari dasu may Allah help them any where they are amin. Page 01 to 02 Wani irin 'kayataccen ginannen gida ne wanda hatta fetin gidan gwal aka nike akai fetin dashi da safe ne amma ko'ina 'kyal'kyali ne ke fita a jikin bangon gidan da dare kuwa har dauke ido yake . Tsararran palor ne dankarere daya sha kayan alatu na more rayuwa iri daban daban wanda wani abin ma na'ura ce ke sarrafa aikin sa ba mutum ba. Zaune suke su uku samari ne guda biyu fitattatu na ajin farko yan gayu tsaf dasu kyawawa farare tar dasu kamar larabawa sai mace a tsakiyar su wacce kallo daya zakai mata kasan itace mahaifiyar wadannan zukakan samarin. Amma kana ganin fiskokin su kasan akawai matsala domin a samarin wanda yafi hasken ransa a mugun bace yake kallo daya zakai masa ka fahimci haka . Saidai bacin ran bai hana kyansa bayyana ba da kuma annurin fuska. Cikin fad'a matar ta kalleshi tana cewa "kasan Allah Al'ameen ka fita idona na rufe idan banda shashanci me zakai da wannan banzar yarinyar wacce ba yaren kaba ba jinsin kaba 'kabila tubabbiya yar wata kasar ba zaka je ka yayo min masifa ba duk yan matar kasar ka da jihar ka saika haura wata uwa London to bari kaji bada yawu na ba ban amince ba kuma ko bayan raina ka aure ta ban yafe maka ba sai ka zaba koni ko ita". Cikin tsananin firgici da tashin hankali wanda ta kira da Al'ameen ya dago kyawawan idonsa yana kallon mahaifiyar tasa jin furucin da take akan wacce bazai iya hada sonta da kowacce mace ba bayajin zai samu madadinta. Iya kallon da yake mata ya tabbatar mata da cewa Abni ce numfashin sa bazai iya rayuwa ba tare da ita ba wanda hakan yai matukar firgita ta. Cikin 'kunar rai ta mike bata sake cewa komai ba jin yawun bakin ta ya kame yasa da sauri tabar gurin zuciyarta na turiri da zafin al'amarin yaron nata wanda ta damu dashi . Dafa shi dayan yayi cikin tausaya masa da halin daya tsinci kanshi na jarabtar soyayya yace "Al'ameen dan Allah kayi hakuri da halin mami tunda bata son wannan baturiyar ka daina furta koda sunanta ne a gaban ta domin mami idan ta fadi magana bata sauyawa kaifi daya ce nasan baza ta taba bari ka aure ta ba". A damuwance Al'ameen ya dago yana kallon dan uwan nashi yace" ni da kaina na fada mata cewa babu kyau karya alkawari a addinin musulunci saboda ni tabar nata addinin ta musulunta bata yarda tayi imani ba saida na mata alkawarin zan aure ta sakamakon nima ina sonta yanzu me kake tunanin zata dauke ni idan nace tayi hakuri na fasa auren ta wanne irin hali zata shiga dan Allah ka taimaka min". Kai Sadiq ya jinjina shikenan 'kani na zan taimake ka insha Allahu tamkar ka auri Abni ne domin bana son rasa ka kuma na fahimci itace bugun zuciyar ka". Wata karamar yarinya ce tazo da gudu tana kuka ta fada jikin Al'ameen cikin rashin walwala yace" momy na me akai miki"?. Da yatsa yarinyar ke nuna wajen dinning tana cewa he spoiled my shirt". Kallon farar rigar ta ta yai ganin duk miya ya bata ta yasa ya kalli wajen dinning din wani yaro ne tsaye rike da spoon a hannunshi karasowa gurin yai yana cewa small dad ban sani ba na shafa mata miya a jikin rigar ta sorry sister". Kafada ta make wallahi bazan hakura ba saika biya ni riga ta kona rama". Zare mata ido yaron yai yana cewa baki isa ba tunda na baki hakura kuma bazan wanke rigar ba ". Kuka ta kara fashewa dashi cikin lallashi dason raba rigimar hayaniyar da suke Al'ameen yace" muje na sai miki wata momy na rabu dashi". Goge hawayen fuskarta tai tana dariya suka fita daga palon yayin da Sadiq shima ya mike yana cewa Ameer meye abin bata ran kaga kada kayi kuka muje kaima na saya maka". Tsalle Ameer yai yana rungume Sadiq yace thnk dady " rike hannunsa yai suka fita wanda mami najin kara tashin motoci yasa taja tsaki cikin takaici tana bude window ta daga labule tana kallon su har suka fice daga gidan". Sauke numfashi tai tana cewa amma wallahi Al'ameen sam bashi da hankali ina yabar ajin nasa wata shegiya take neman mayar min dashi shashasha duk yabi ya susuce akanta ko yar uban waye ita a London nata isa ta rabe muba duk kudin su saita raba su kota halin 'ka'ka. Fita tai daga nata part din tana shiga wata kofa ta bude bedroom tare da lekawa tace" wato Afeeyah baki da hankali ko sai ulcer ta kama ki zaki gane gata ake miki tsabar iskanci kisa waya agaba ki manta da komai bari dadyn naku ya dawo zansa ya karbe wayar ne". Cikin shagwaba wata budurwa dake kwance a wani makeken gado ta dago tare da cewa kai mami bafa wani abu nake ba kuma indai breakfast ne nayi tun karfe bakwai". "Hum haka ne da gaske kinyi"?. Eh mami nida wafer na karya ba abinci naci ba". "To yayi miki kyau ki fito haka zama ni daya a palon ya ishe ni". Shikenan to muje mami yadda kika ce haka za'ai mikewa tai suka fito tare yayin da mami ta danna wani karaurawa dake palon". Da sauri wasu masu kaya iri daya su biyar suka shigo palon cikin ladabi jikin su na rawa suka durkusa tare da gaishe da ita bata amsa ba sai wani kallo datai musu tana cewa. "A cikin ku wadanne banzayen ne masu lura da dinning mikewa hajar tai tana cewa mune nida ma'u ". A tsawace mami tace sannu yayan talakawa wato daula tasa zaku fara shagala da abinda ya kawo ku uban waye ya zubar da miya akan farin carpet din can"?. Zaro ido hajar tai wallahi hajiya ban sani ba tunda mukai servingg dinku ban sake fitowa ba". "Saboda gaki isashshiya ko ke nana baki karanta musu ka'idojin gidan nan bane domin ba irin kowanne gida da suka sani bane sai wane da wane". Nana dake shirin magana mami ta katse ta rufa min baki nan gaba aka sake samun kuskure daga wadannan 'kazaman new comer bazan daga miki kafa ba". Hakuri nana ta taba domin marar abu baya zuciya sannan ta mike da kanta ta gyara dinning din da komai tana komawa bangaren ma'aikata ranta duk ba dadi ta gaji da wulakancin da mami ke mata". Koda dare lokacin da daddy ya dawo haka mami ta cika ta kumbura tai fam taki sakin ranta akan lamarin dazu". Kallonta alhaji Mustapha yai cikin mamaki domin da ba haka take ba yace" uwar gida ran gida ya akai ne naga kina fushi meya faru". Kamar jira mami take ta ture plate din abincin gabanta tana cewa nida Al'ameen ne mana yana neman dora min hawan jini ya kashe ni lokaci na baiyi ba". "Tofa meya miki haka auta na akwai hakuri kodai kece da tsokana"?. "Kaji irin abin ko babu dama a fadi laifinsa a gaban ka saika wanke shi tas ". "Ba wannan ba fada min meyai miki". "Ranta a hade tace wai dan Allah kaji shi da wani hauka yaje wata kasar ya hadu da yar arna ta kaishi church sun burkita masa kwakwalwa ya dawo ya susuce". "Subahanallahi da yaushe wani abu kika ga yana yi wanda ya saba hankali"?. "Yo meye ma baiyi ba alhaji dazun nan na gama cin kaniyarsa akanta ala dole ita yake son aura duk Nigeria baiga wacce tai masa ba saiya debo mana masifa da bala'i sun zuge mana jini". "Gaskiya ka sameshi ka masa fada tunda ni na gaza yaki fahimta ta". "Ok yayi shikenan karki damu uwar gidan Mustapha Aminu zan same shi as you wish kamar yadda kike so". Murmushi mami tai cikin farin ciki yauwa alhaji yanzu naji magana nina manta sunan shegiyar yarinyar ma sunan kalar amai"😣. Ki daina rage mata alhakin data deba a cocin tunda kince kirista ce". Allah wallahi abin ne da haushi duk gayun sa da tsananin kudin ka maimakon ya nemi yar shugaban kasa nasan duk inda yaje neman aure da gudu za'a bashi". Kai alhaji Mustapha ya jinjina yana mamakin mami daga anyi magana saidai ta ambaci kudi💰😂. BY MRS AL'AMEEN AHMAD CE. 💰'DAN MILLIONAIRE💰 #Comment #✅ote #Fallow. 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 Home of hospitality and harmony. Yusrahms Abubakar Mrs Al'ameen Ahmad ce. Page 03 to 04. Sati biyu da faruwar haka Al'ameen na zaune shi kadai a palor yaji wayarsa na kara wakar da Abni ta dora masa ce tun a London . Yana kallon screen din wayar saida gabansa yai mummunar faduwa ganin sunan Abni din baro-baro. Bai daga ba saida ta katse ya kira ta amma abin mamaki data daga saiya kasa ce mata komai kawai yai shiru yana sauraronta". Jin yayi shiru yasa tace dear lafiya kwana da yawa wayar ka a rufe kasan irin tashin hankalin dana shiga kuwa please kada ka sake". Sauke ajiyar zuciya yai muryarsa kamar yana mura yace fatan kina lafiya ina mom da saira ko kina ma'aikata ne kamar naji hayaniya". Dariya tai domin tana da yawan fara'a tace a'a kawai dai zan baka mamaki ne". "Kamar ya wanne iri"?. "Idan nace maka ina kasarka Nigeria zaka yarda ". Zuciyarsa na harbawa sosai kamar zata fito waje yace zan yarda amma da gaske kike kina Nigeria"?. Allah dear ina nan Abujan ku ba nan kace state naku ba na rako daddy na ne wani aiki baifi sati zamuyi ba". "Ok you are welcome". "Thank dear amma yanzu ina ne zan same ka domin na sanar da dad dina zamu zo gidan ku"?. A firgice da karfin gaske har saida ya tsora ta yace "what you mean........ "Yes ta katseshi batare daya karasa ba tace ka sanar dani addresss din gidan ku". Babu yadda ya iya dole ya tura mata kamar yadda ta bukata tare da dafe kansa cikin damuwar mezai iya faruwa". Fitowar mami kenan ganin a yadda yake yasa ta fasa wucewa ta tsaya tana cewa "lafiya meye ya faru na ganka a haka kodai wannan banzar yarinyar kad'anin kake tunani da wahalar da kanka a kant.......... Bata karasa ba taji anyi sallama da wata irin murya da ba hausa ba kanaji kasan yare ce". Juyawa mami tai ganin mace tsaye bakin palor fara tar jawur baturiya yasa cikin kaduwa tace" wace ke ya akai me kike nema anan din"?. Dan murmushi tai idonta nakan Al'ameen da shima ita yake kallo tace "barka da gida mah suna na Abni Jonah daga London nazo gurin dear ne" ta fada tana nuna Al'ameen. Wata irin zabura mami tai tana jefar da glass cup din hannunta ya fadi ya tarwatse idonta kamar zasu fito waje dan razana tace". "Me Abni Jonah wato kece wannnan matsiciyar yarinyar da kika lashe kurwar dana ko baya ganin ko wacce mace saike shine yanzu kika biyo shi har kasar sa ki cinye shi ko mayya "?. "Kallon Al'ameen Abni tai tana tambayarsa akan me mahaifiyarsa take cewa". Kafin yai wani yunkuri mami tace ubanki nace tsinanniya la'ananniya harda me nace da yake ya zama sako tumaki saiya fada miki jaka kawai". Cikin takaici Al'ameen yace wai mami me kikeyi haka haba dan Allah ki daina zagin ta ". Bazan daina ba kazo ka dake ni saboda na zagi wannan shedaniyar arniyar". Mami ki daina kafurta ta musulmace fa"?. "Au a haka shine ta sako wannan dan mitsitsin hijab din kila ma wanda take zuwa coci ne". Fahimtar da Abni tai kamar bata samu karbuwa agurin mami ba ganin yadda take magana da fada duk da batasan me take cewa ba yasa ta kalli Al'ameen ba tare da nuna wata damuwa ba tace" suje waje ko gardan suyi magana". A tsawace mami tace idan ka fita ka bita ban yafe maka ba saina tsine maka wallahi,". Iya rudewa yayi cikin yanayin ladabi Abni ta roki mami cewa ta kyale suyi magana amma mami tace ya fita ya gani". Dafe kansa Al'ameen yai jin lokacin guda yayi mugun sara masa da hanzari Abni ta karasa tana tambayarsa lafiya"?. Wata hankada mami ta mata wanda saida ta buge da kujera cikin tsawa tace fice daga nan idan ba gidan ubanki bane bakadaddiya karuwa wato a gaban nawa ma fayde zaki masa"😨😱. Abni zatai magana mami ta sakar mata wani zazzafan marin dayasa ba shiri ta fita a palon da gudu tana kuka". Al'ameen dake numfashi dakyar muryarsa na rawa yace mami me kika aikata kin aibata kin zage ta kin mare ta me tai miki dan Allah mami meyasa kika tsani Abni ni kuma baki tsane niba domin nine ita itace ni kowa ya kita ya kini". "Ai kai yanzu na fahimci mahaukaci ne bakasan ciwon kanka ba idan ba mayya bace kalli mana kafin tazo kana irin wannan numfashin ne shashasha ana maka gata da yake idonka ya rufe baka gani". Barin gurin tai yayin da Al'ameen yake yunkurin tashi yabi bayan Abni ya kasa. Abni na zuwa hotel inda suka sauka ita da dad dinta tasha wani marin a gurinsa yana huci yace dole soyayya dashi kina neman kashe kanki ga samarin ki can ki zabi daya mana Abni ina kika kai tunanin ki,"?. Kuka Abni ta fashe dashi tana rungume mahaifin nata tace kayi hakuri dad Al'ameen na sona kada ka raba mu nima ina sonsa ba laifinsa bane". Cikin tausayawa daddyn ta ya rungume ta shima yana cewa shikenan naji yi shiru haka na gama komai a cikin kwana biyu saboda ke gobe zamu tafi". Zaro ido tai tana mikewa tsaye zatai magana ya girgiza mata kai yana cewa". "Bazan barki ki sake komawa wannan gidan ba kada ki batawa kanki lokaci Abni auren ki da yaron nan bamai yuwuwa bane". A rude tace dad zai yuwu dan Allah ka kara min lokaci zanji da komai"'. "Na sake baki lokaci amma wannan shine na karshe idan aka sake samun matsala bazan daga miki kafa ba". Murmushi tai eh dad thank you na yarda". 🌹 Mrs Al'ameen Ahmad ce. Yma Dutse new world🌎 new life🌲 and new style💈 sabuwar duniya🏙. NAJA'AT MUSA ABUBAKAR ZARAH MUSA 'DAN ADAN THIS PAGE IS FOR U I LV💝 U EVERYTHING ABOUT YOU IS SO GOOD BUT ONE THING IS WRONG THAT YOU ARE NOT MIND. Page 05 to 06 Wani karamin kauye wanda yake cike da mutane iri daban daban wani gida ne daya sha fenti harta waje kamar yana cikin gari gidan yayi kyau sosai kana gani kasan me gidan nada abin hannu a kauyen. Wata mace ce ta fito daga daki tana rawa tayi daurin kwalin soke irin ture kaga tsiyarnan tace. "Ahayye nanaye yan gidan nan ku fito kuyi kallo Zainabu abu na me 'kashin arziki ce ba irin su o'o da ba'a da farcen susa ba". Jin shiru yasa tace Salamatu kina ina ne kodai bakin ciki ya kashe ki a daki lallai kina da aiki ". Fitowa wata farar mata tayi daga wani guri da hayaki ke fita wanda kana gani kasan dakin girki ne ta kalli waccan dake rike da atamfa tana cewa". "Akan me zanyi bakin ciki saboda Zainab ta samu atamfa kowa ai da nasa rabon Allah ne ya bata". Dariya Saude tai tana tafi tace tofa masu tawakkali kamar gaske kina magana a salihance nan kuwa zuciyar bakin kirin take"". Murmushi Salamatu tai an fada miki kowa irin ki ne ni abin wani bai dame niba Fatima bata rasa kaya ba". "Humm karyar banza kayan gida ba badan ubansu meyin suturar bane idan ta samari za a biye wata rana saidai ta fita yawo tsirara". Salamatu dake shirin komawa kitchen tace Allah ya kiyaye kedai tunda kinbi son zuciya ki taka a sannu ina gargadin ki". Kugu saude ta rike jimin munafikar mata koke kika samu duniya yarki tai farin jini haka sai kinci kudin samari". Sallama wata budurwa tai tana sauke fantekar dake kanta tace gaskiya nifa na gaji da wannan tallar ehe "'. Baki saude ta bude ke baki da hankali yi kasa da muryar ki kada salamatu taji tai min dariya dama yanzu ita da shegiyar yarta suka gama kukan bakin cikin atamfar da ilya ya kawo miki ". Dariya Abu tai lallai ahe bakin ciki zai kahe su dan wallahi yace saniyarsa ta haihu idan ina dan zai bani". Da sauri kamar wani zai rigata Saude tace kice kina so dan ubansa tunda bashi da hankali ki wanki gara😂. "Ai dama taliyar murjin da kika dafa min yau shi kadai ya saye ta". Zaro ido saude tai sadaka yayi a dandalin". Baki Abu ta tabe a'a kawai yaji da manjan ya juye a cikin fantekar ya cinye shi kadai sai yar kadan daya bawa wani almajiri🙊😹. Saude tace kaji jakin mutum wannan kada ayi auren ya kasa rike ki mahaukaci ne shi zai cinye taliyar rabin kwano da kofin wake". Hade rai Abu tai nifa ina sonsa ki daina zagin sa yace min gobe zai turo iyayensa". Cikin murna Saude ta rafka guda tana cewa abin yazo yar albarka ta kusa tafiya daki bari muntarin ya shigo muyi magana". Mikewa Abu tai tana cewa nifa yunwa nake ji saude dake kirga makudan kudin da ilya ya baiwa Abun tace ki buda daki yana nan a langa". Kai Salamatu ta girgiza tana daga kitchen tana tuka tuwo tace Allah ya shirye ku kada wata rana kuci kudin matsafi". Kwanan Al'ameen goma baida lafiya gashi yana so ya koma gurin aikin sa amma babu dama dole ya hakura zuwa wani lokaci idan yaji ya dawo daidai". Daddy na zaune kusa da Al'ameen bayan Sadiq ya duba shi ya daura masa ledar ruwa cikin lallami yace. "Aminullahi meke damun ka Sadiq yace min har yanzu bugun zuciyar ka bai dawo daidai yadda yake ba ka fada min matsalarka". Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai domin maganar dazai fada ba lallai daddyn nasu ya amince ba yace. "Dan girman Allah daddy ka dube ni da idanun rahma ka tausayawa zuciya ta ka fahimcr cewa danka ya fada cikin jarabtar soyayya kamin maganin damuwa ta". "Me kenan zanyi maka Al'ameen ka fada min kada kaji shakka niba mami bane babu abinda zai gagara". "Daddy na roke ka ka duba Allah ka amince min na auri Abni yarinyar nan ta sadaukar da rayuwar ta saboda na samu farin ciki ta kula dani lokacin da bansan kowa ba a London. Ta musulunta saboda ni ta yarda zata aure ni ta zauna dani sannan mahaifanta basu nuna min kiyayya kamar yadda mami ta tsane taba. Da tazo gidan nan ta rako mahaifin ta mami ta zage ta ta aibata ta ta kafurta ta sannan ta mare ta amma batai zuciya dani ba saboda tana sona". Cikin mamaki daddy yace ita Aishan ce ta mare ta ". "Eh daddy wai tazo har gida zata cinye ni". Murmushi daddy yai kuma an fada mata mayun 'kiri da 'kiri suke kama mutum su cinye shi yanzu dai me za'ai". "Daddy abin da za'ai shine zan aure ta ina sonta da ita zan zauna dan Allah daddy ka fahimce ni itace komai nawa banajin zan samu madadin ta". "Ok yanzu kana so aje nemar maka auren tane "?. Eh daddy wannan shine damuwa ta ka taimaka min". Hannunsa daddy ya rike karka damu zan yi kokari akan hakan zamuje london cikin satin nan domin kudi ba sune kwanciyar hankali ba". Tashi zaune Al'ameen yai ba shiri yana cewa a satin nan na gode daddy Allah ya kara daukaka". "Amin daddy yace yana kallon yadda lokaci guda fuskar Al'ameen din ta washe da farin ciki". Lokacin da mami taji wannan maganar kuka ta fashe dashi na bakin ciki tana cewa yanzu alhaji tsakani da Allah aura masa arniya zakai karya fa take bata sallah". "Shine damuwar ki"?. Shiru mami tai tana goge idanunta da sukai jawur saboda kiyayyar Abni. Ganin taki magana daddy yaci gaba inda rashin sallah shine matsalar me sauki ne zata musulunta tunda tana sonshi kuma ba haramun bane danya aure ta". "Dan haka ranar monday jibi kenan ki shiri za muje london nema masa auren ta kiyi fatan itace alkairi a rayuwarsa". Hannu mami ta dora akai tana sake zunduma wani ihun cikin burgima tace wallahi bada yawu naba kuma ko kofar gate bazanje ba balle naje wata london gurin shegun arna naje su bawa gunki jini, na". "Bazai auro min wata baturiya ba saidai ya mutu baiyi aure ba". "Aishaa" daddy ya fada a tsawace tare da nuna ta da yatsa yace. "Idan ke bakya sonsa ni ina sonsa kuma na amince ya auri wannan baturiyar tunda itace zabun ransa kece zaki zauna masa da yan mata da kike kawo masa"?. "Shashancin banza kin girma amma kina shiga daji bakisan kaddara ba na biye miki kina neman kashe min yaro kamar ba kece kika haife shi". "Saiya aureta idan har matarsa ce saiki dau mataki kuma umarni nake baki ki shirya tafiya ranar monday nan da kwana hudu na gama yanke magana". Yana fita ta mike da gudu tana shiga part din Al'ameen yana zaune ruwan ya kusa karewa tana zuwa cikin karaji da ihu da yage yage kamar me ciwon hauka ta fisge ledar ruwan tana wurgi da ita sannan ta fadi kasan carpet tana shure shure. "Tace Al'ameen ka cuce ni nayi asarar haihuwa Sadiq bai taba sani nayi bakin ciki ba balle kuka haka kanwarka Afeeyah daka girmeta da shekaru sosai bata bani wahala ba. "Amma ka sani kuka na zubar da hawaye saboda kai idan har kana so na yafe maka kaje ka samu daddyn ku kace ka fasa auren wannan banzar yarinyar". Al'ameen dake mata kallon mamaki ganin yadda take kuka kamar yarinya ya mike tare da dago ta yace mami lafiya wani abu ne ya sake faruwa". Fisgewa tai tana cewa ban sani ba wallahi Al'ameen nayi asarar haihuwa amma ba lallai kai dana bane ne tunda haihuwar asibiti nai kila an canza min kai dan da na haifa bazai rika wahalar dani haka ba ". Zaiyi magana ta daga masa hannu babu abinda zakace min baka da wani abu da zaka fada min kaje ka karata" tana fadin haka ta fice a bedroom din. Typing📲 💰'DAN MILLIONAIRE💰 YUSRAH MUSA ABUBAKAR Page 07 to 08 Iya tsananin damuwa Al'ameen ya shiga domin bai taba tunanin kiyayyar mami zata sa tace kila anyi mata canjinsa a asibiti lallai dole ya samu daddy koda son Abni zai kashe shi ya hakura". Fita yai daga part din nasa yana shiga bangaren daddy cikin sallama zaune ya same shi a palor yana duba takardu masu yawa zama yai a kasan carpet yana kallon daddy cikin dauriya dason ganin ya jure yace. "Daddy na fasa auren Abni na hakura basai kunje ba Allah zai musanya min da mafi alkhairin ta dama ba komai mutum keso ya samu ba". Batare da alhaji Mustapha ya dago daga kan aikin da yake ba yace " me kake cewa banji sosai ba hankali na ya kasu gida biyu". Sauke numfashi Al'ameen yai yana cewa daddy na hakura da auren Abni na fasa". Murmushi daddy yai yana dan kallonsa yace saboda Aisha ko "?. Shiru yai domin gaskiya badan mami ba babu abinda zai hana shi auren zabin ransa". Dawowa daga tunani yai jin daddyn na cewa" nace saboda mamin ku. Ka hakura ko"?' "Eh daddy domin mahaifiya ta tafi min komai mahimmanci tace duk cikin yaran ta nine batai sa'ar haihuwa ba ina wahalar da ita ni kuma banason saba mata na fasa auren amma bazan auri kowacce yarinya ba". "Ni kuma ban fasa ba Aminu ina nan akan bakana saina baka abinda kake so aure meye baya samarwa dan tana yar wata kasar saiya haramta ka aure ta ka kwantar da hankalinka idan yarinyar nan matar kace saika aure ta ba gida daya zaka zauna da mamin kaba balle kace kana can gurin ka daban". "Daddy na sani cewa tai idan na aure ta bata yafe min ba". "Zata yafe maka idan taga abinda auren ya kawo mata kaga bar bata wa kanka lokaci wajen tunani da damuwa ranar monday zamuje London babu fashi". Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai cikin tunanin ya zai kare da mami baya son hayaniya ko kadan. Washe gari suna zaune a palor mami ta fito daga part dinta tana waya ganin su a zaune yasa bayan ta gama tace. "Al'ameen kadau mota yanzu kaje airport ka taho da Zainab munyi waya da hajiya Binta tace min driven ta ba lafiya". Tun kafin Al'ameen yai magana Sadiq yace amma mami ga direbobi da yawa anan mezai hana daya yaje ya dauko ta yarme iyayi ta fito ta tari motar haya man a kaita gida". Cikin harararsa mami tace to uban yan shishshigi banyi dakai ba kaiba asibiti zakaje ba meye ya biyo dakai tanan gidan". "Mami nida gidan mahaifina kice meya kawo ni dan kawai aure yasa nabar gidan". Bata bashi amsa ba ta kalli Al'ameen tana cewa kaji dai na fada maka ko tana can tana jiranka"?. "Jiwai tana jiran ka kamar wani driven ta wato wannan yar iskar yarinyar hajiya Bintan ce ta dawo". Cikin yanayin tambaya Al'ameen yace wace ne yarinyar wai yar gidan umma kanwar mami dai ina take da yar dahar take fita waje". Daidai sun mike Sadiq yace kai amma Zainab wata yarinya me shegen tsiwa kodan ba a hannun hajiya Bintan ta girma ba tana dangin babanta amma kai da yar uwar ka". Shiru Al'ameen yai suna tafiya yana tunani amma gaskiya ya manta yarinyar saidai yanzu idan ya ganta. Tana tsaye tadau wankan riga da wando wanda sunyi bala'in matseta gashi tasa wani dan mayafi wanda dashi gara babu tana sanye da glass . Sadiq da yake shike driving yace kalli to gata can wani irin kallo Al'ameen ya bita dashi ganin shigar datai arniya sak ba wanda zaiyi tunanin yar musulmai ce. Tsaki yaja yana fita a motar daidai ta karaso ta zare glass din idonta tana kallon su sai kuma tadan murmusa cikin yanga tace Sadeeq ashe zan iya gane ka tsawon lokaci bamu hadu ba". "Eh shigo muje" abinda yace kenan domin shima shigar datai ta bashi haushi". Juyawa tai saitin da Al'ameen yake tsaye tace driver samin kaya a bayan mota kayi sauri nan, da minti biyar na ganni a gida". Zaro ido Sadiq yai ke driver fa kika ce ya miki kama da driver"?. Yatsina fuska Zainab tai mezai hana direbobin aiba kamace dasu ba". Kai Sadiq ya jinjina bai sake magana yace Al'ameen shigo mu wuce". Katseshi Zainab tai wai dan Allah Sadiq nice zansa kayan cikin mota shi meye amfanin sa". Banza Sadiq ya mata jin motar ta tashi tsoron karsu tafi su barta yasa dole tasa kayan da kanta sannan ta shiga motar". Sun danyi tafiya kadan tace gaskiya ne haka nake son driver babu sanya amma Sadiq ina wannan 'kanin naka mejin kannan naji umma na tace yanzu ya zama soja ko"?. Lallai yarinyar nan ba karamar yar iska bace Sadiq ya. Fada a ransa yana kallonta tta mudubin mota yace. "Ga miciji ai ba a neman ja ki tambaye shi da kanki". "Oh shine wannan sorry nace maka driver ya kake". Babu wanda ya kula ta zuwa wani lokaci tace yauwa na tuna shakka babu sunan ka Aminu na manda'ko😂. "Dariya ce ta kama sadiq lalli Zainab taci kai amma bari ya kyale ta Al'ameen na daidai da ita". Cigaba tai ko shekarun baya na tuna ya tsani zuwa kauyen mahaifin ku wata rana zakuje ya fadi a kasa yana burgima shi bazai jeba daddyn ku ya ciro bulala a garden ya zane sh...........' Wani irin taka burki Al'ameen yai wanda saida ta gwaru da kujera a fusace yace "fita a motar nan". Zaro ido tai baka karaso ba ga gidan can dan kawai na fadi gaskiiya na tuna maka da baya"?. Cikin tsawa yace "get lost". Kallon Sadiq tai ko zai magana taga yayi banza ya dauke kansa daga saitin su dole ta fita daga cikin motar tana daukar kayan ta"". Wata irinn 'kura ya buleta da ita yaba bawa motar key tari ta kamayi sosai har saida idonta yai ja". Dakyar ta samu ta daaina barin kayan tai a gurin da sauri ta shiga gidan su tana zuwa ganin ummanta a palor yasa ta fada kanta tana kuka". Cikin tashin hankali hajiya Binta tace lafiya dota daga dawowa ina murnar ganin ki sai naga kina kuka meya faru ina su Al'ameen din kosun tafi". Cikin shagwaba tace ba shinee ya ajiye ni a wajen gidan alhaji Faruq ba kuma ya tule ni da ''kura a gaban mutane dan kawai nace masa ya karaso dani gida kayan nawa ma suna can". Cikin bacin rai hajiya Binta tace kan uba amma wallahi yaron nan baida mutunnci wato ya tule miin ke da 'kura bari zan kira auty Aishan na fada mata". Kayan hajiya. Binta tasa ma'aikatan gidan suka dauko mata sai bala'i take. Ita kadai. 💃 🎶 By mrs Al'ameen Ahmad ce. Page 09 to 10 Kamar yadda alhaji Mustapha ya fada haka ce ta faru ranar Monday sukai shiri suka wuce london Afeeya kuma tace gidan Sadiq zata zauna gurin matarshi kafin su dawo sai kuma ta fasa ta tafi gidan kanwar mami hajiya Binta idanuwan mami a kumbure sakamakon kwanan datai tana kuka kamar ranta zai fita. Da yake Al'ameen yasan gidan kuma saboda kada a samu matsala yasa bai sanar dasu ba Saira kanwar Abni na zaune a tafkeken palon su sai ganin mutane tai cikin mamaki ta mike tana cewa bros kaine sannu da zuwa". Dan murmushi Al'ameen yai tuna rayuwar da sukai lokacin yana nan cikin yan mintuna tasa aka hada musu kayayyakin ci dana sha na alfarma". Fafur mami taki shan koda ruwa ne zama ma dan ba yadda zatai ne amma yadda take jin tsanar mutanen nan da wuta zata kone gidan sai tafi kowa farin ciki". Tambayar Saira yai ina mom domin yasan Abni da daddyn suna gurin aiki. Sauyawa fuskar Saira tai daga yar walwalar da take zuwa damuwa tace" mom na asibiti bata zama a gida". Waye baida lafiya "? Ya tambaye ta cikin faduwar gaba. Kuka ne ya kwace mata tana girgiza kai tace" Abni ce ". Wata ba'kar hajijiya ce yaji ta kwashe shi lokaci guda idonsa ya rufe luuuu ya tafi zai fadi da sauri Saira zata tare shi mami ta ture ta tana cewa. "Karki taba shi arniyar banz...... "AISHA" daddy ya fada da karfi cikin fushi yace wato kinzo gidan su ma saikin nuna rashin arziki ko kinga ki kiyaye ni ". Jijjiga mami keyi tana huci yayin da Saira taja baya daga gareta Sosai cikin jin tsoro". Da murya a nutse daddy yace" kinga Saira karki damu muje ki kaimu asibitin". Kai ta jinjina tana shiga ta shiryo tare da dauko key din motarta ta fito suka wuce". Dukda su mom suna cikin damuwar rashin lafiyar Abni din hakan bai hana su nuna matukar farin cikin su da ganin familyn Al'ameen din ba kuma sun karbe su hannu biyu". Tambayar inda take Al'ameen yai cikin damuwa mom tace " son Abni tana ICU". "Mom muje na ganta". Kai mom ta girgiza babu dama muma basa bari mu shiga balle mu ganta saidai ta na'ura". Tabe baki mami tai tana dauke kai daga kallon su domin ko ganin su bata son yi". Haka suka zauna har dare a asibtin ganin lokaci zai kure yasa mom tace Saira kuje gida ki basu masauki gobe sa dawo". "Ok mom" Saira tace sannan ta dauko su a mota suka dawo gida a ranar Al'ameen bai runtsa ba ko kadan kwana yai akan Sallaya har asuba yana rokon Allah". Kwanansu uku da zuwa iya gajiya da bacin rai mami tayi bata da buri kamar taga ta dawo gida gashi basa zance tahowa". Samun alhaji Mustapha tai ranta a hade tace waini sai yaushe zamu koma gida ne kawai munzo garin mutane mun zauna". Ko karasa kallonta alhaji Mustapha baiyi ba yace sai ranar data warke idan bazaki iya jira ba ga hanya nan". "Gaskiya bazan jira saita warke ba kamar wasu dangina tafiya zanyi saikun taho". "Ki gaida gida Allah ya kiyaye amma ki sani bada kudina zaki koma ba ki biya da naki". Zaro ido mami tai dan akwaita dason kudi kamar me tace" haba alhaji da kudi na kuma dama nice na kawo kaina". "Oh da wa ya kawo ki gurin nemawa d'anki aure kika zo". "Nidai wallahi ba ason raina nazo ba gaskiya ka biya min kudin jirgi na tafi gida". "Aisha idann kinga na biya miki kudin jurgi munyi abinda ya kawo mu muddin baza ki jira muba saidai ki biya kudin jirgi da kanki". Bakin ciki ne sosai ya mamaye mami ga koshi ga kwanan yunwa dole ta hakura dan bazata zare wadannan mmakudan kudin ta bbiya jirgi ba". Satin su guda babu wani labari don haka mom da daddyn Abni suka roki alfarma a bari su shiga su ganta ko minti biyu ne". Tare da Al'ameen suka shiga Abni na kwance akan gado ganin Al'ameen yasa tadan juyo saitin sa muryar ta can kasa tace" Al'ameen kaga halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashin ka ko na sani ba tashi zanyi ba inai maka fatan alkairi ka kasance cikin farin ciki Allah ya baka madadi na". Kai Al'ameen ya girgiza" a'a ki daina cewa haka kece nake so Abni zaki warke muyi rayuwa tare bana fatan na raasa ki tare da mahaifa na nazo domin su karba min auren ki please Abni ki tashi muyi rayuwa me kyau". Dan lumshe ido tai tare da budewa tana kallonshi ta riko hannunshi muryarta kamar bata me jinya ba tace. "kada ka damu zaka kasance cikin farin ciki koda babu ni bazan taba rabuwa dakai ba muna tare bazan taba barin ka ba". Tari ne ya kama ta harda jini ke fita a bakin ta da sauri su mom suka yo kanta kallon su tai bata ce komai ba". Al'ameen wanda tashin hankali da rashin nutsuwa sun mamaye shi ya sake rike hannunta wani zobe ne a yatsan ta tacire shi tana baiwa Al'ameen . Ganin tai shiru yasa da karfi Al'ameen ya kira sunan ta bude ido tai tana murmushi a hankali ta furta" I LOVE YOU AL'AMEEN". Daga haka bata sake cewa komai ba sai kallon da yaga ta koma yi masa wanda bai gamsu dashi ba jin ta sake hannunsa yasa yace Abni Abni Abniiiiiiii da mugun karfi yaja sunan. Ji yai daga bayansa mom ta fashe da kuka domin shakka babu Abni ta rasu". Ganin dayai daddyn ta ya matso ya lullube ta yasa hannu zai bude rike masa hannu daddyn yai yana girgiza kai". Wanda hakan ya tabbatar masa da mutuwa tai a take ya fadi a gurin ya suma😢😭 . [23/09/05 12:44pm] Typing📲 ANNURI W ASSOCIATION Home of hospitality and harmony YUSRAHMS CE😜😍. Page 11 to 12 Fitowar Afeeya kenan zata tafi makaranta Zainab tasha gabanta tana cewa ke dan rainin hankali wato ke isashshiya ko maza ki koma saikin gyara bedroom din idan ba haka ba ki hakura da zuwa makarantar". Wani kallo Afeeyah ta mata. cikin rainin hankali tace Allah ko mami da gaske kike"? To bazan gyara ba makaranta zanje ba irin kice me zaman kashe wando a gida ba zan fita idan kin isa ki dakatar dani ko kidau mataki". Da kallo Zainab ta bita lallai yarinyar nan zaki ci ubanki bin bayan ta tai da sauri daidai Afeeyah ta tashi mota tasha gaban motar. Afeeyah bata fasa ba tayo kanta zata bigeta da gudu Zainab tai tsalle tana fadawa cikin fulawoyi😂🌻🌷🍁 ". Dariya Afeeyah tai tana lekowa ta glass din motar tace au dama zaki gudu dakin tsaya saina maida ke gurguwa nakasashshiya nasa ki zama mabaraciya a cikin gari amma a juri zuwa rafi mu zuba nida ke dan halas ka fasa". Tana gama fadin haka tai kofar gate tsaki Zainab tai tana mikewa ganin yadda ta taba farar rigarta domin ba a dade da yiwa flowers din bayi ba". Tana komawa ciki hajiya binta na fitowa ganin kayanta a bace yasa tace daga ina meye ya bata miki riga"?. Cikin takaici Zainab tace waye zaimin haka idan ba wannan shegiyar yarinyar Afeeyah ba". Toke meye damuwar ki da ita kuna yan uwa amma jinin ku bai hadu ba". "Yo umma dan ubanta waye jakin ta da zata kwanta da safe bazata gyara gado ba". "Ok akan haka ne amma dai aiba wani ne ya hana kiba kece kikai ra'ayi" . "Allah ni umma bana son yar aiki tana shiga daki na tana kallon asiri na". "Yayi masu asiri karki sake cewa ta gyara miki gado bansan shashanci". Cikin jin haushi Zainab ta mike tana 'ku'kuni tabar palon hajiya Binta data bita da kallo tace humm Zainab kenan indai Afeeyah ce tana daidai dake". Kwana Al'ameen yai a sume baisan inda kansa yake ba sosai daddy ya shiga damuwa mami kam suman Al'ameen bai d'ara taba saima wani irin farin cikin data tsinci kanta aciki na muutuwar Abni din ji take kamar ta taka rawa🙊🙄. Wanda dole sai a asibitin suka baro shi domin bai dawo hayyacin saba Abni kuwa tun jiyan akai mata sutura😢. Abuh da 'kawayen ta suna zaune a dandali suna musu akan samarin 'kauyen suka hango Fatima tsaye a 'karkashin wata bishiya tana dariya". Rabi tace lah Abu ga hegiyar gidan ku can tana dariya ita kadai kamar me aljannu". Abu data kalli gurin tace barni da yar iska tunda bata da samari dan ta fini kyau a banza". "Ahayye ji tsinannun munafikai wato kun zauna kuna gulmar 'kawata ko inji uban waye ya fada muku bata da saurayi ita data fi kowa sa'a ma tunda Sa'adu ne yake sonta dan gidan me gari". Juyawa sukai inda ake maganar suka ga Asabe tsaye da itace a kanta alamar gida zataje daga gonar baban su take". 'Duuuu sukai kanta zasu rufe ta da duka ta sauke icen tana zaro guda daya tace naga hegiyar da zata taba ni saina fasa mata kai". Duk tsayawa sukai cikin huci Abu tace idan kin isa ki aje itacen mana wallahi saina fasa miki baki". Aje itacen Asabe tai tare da shakar wuyan Abu wacce batai zato ba tana cewa" na aje da kina nufin dan kina tare dasu yasira bazan iya dukan kiba zanji tsoronki". Idon Abu sun fitfito sakamakon Asabe jibgegiya ce dakyar ta samu su Balki suka babbare hannun Asabe daga wuyanta". Tari ta kama yi babu kakkautawa kamar zata shide Asabe data dau kayanta tace nan gaba ki sake kawo min raini saina kusa kahe ki shashasha". Saida Asabe ta tafi sannan rahma ta samu bakin magana kiyi hakuri Abu bamusan zata shake kiba amma nan gaba zamu shigar miki😹😀". Tsaki Abu taja ke dalla matsa gefe matsoraciyar banza duk yawan ku mutum daya ta gagare ku". Ihu suka sa mata suna wakarsu ta dandali suka ce dama waye ya tsokane ta tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka. Mikewa Abu tai a fusace tana kallonsu tace kada hegiyar data sake kula ni a cikin ku tsinannu kawai". Dariya suka kwashe da ita suna tafawa to sai me dan mu daina kula ki wata uwar kike bamu. Daukar fantekar abincin ta Abu tai tana barin gurin dama a wuya take domin tayi kwashe ilya baizo ya sayi abincin ba". Mrs Al'ameen Ahmad ce Page 13 to 14. Satin Al'ameen guda aka bashi sallama ya dawo gidan su Abni nan sabon ciwon sonta ya bude babi ganin da daddy yai ba warkewa Al'ameen zaiyi su dawo Nigeria ba yasa yace wa su mom kawai zasu koma gida". Anan daddyn Abni yace mr Mustapha mezai hana ka amince a bashi 'kanwarta Saira". Al'ameen dake gefe tun kafin daddy yai magana yace a'a daddy na hakura bazan yi aure ba a rayuwa ta". "Me yasa my son? da Abni da Saira daya ne"?. Kai Al'ameen ya girgiza yana cewa" daddy bazan iya auren Saira ba badan bana son hada jini daku ba dan Allah ka fahimce ni aure ya fita a raina". "Shikenan son ba komai na fahimce ka" alhaji Mustapha ya kalla cikin fara'a yace babu komai ai muna tare mun zama dangin juna Allah ya tsare hanya yasa kuje gida lafiya". . Anan mami ta gane cewa da gaske Al'ameen yake ashe gidan su Abni musulmai ne amma itafa duk da haka gara da Abni din nan ta mutu hankalin ta ya kwanta yanzu d'anta zai dawo daidai. Sosai alhaji Mustapha ya tausaya musu kuma ya sake yi musu ta'aziyyah da godiya akan abinda sukai musu "gaskiya kuna da karamci mun gode sosai Jonah mu zamu tafi". Har airport sukai musu rakiya sannan suka sake yin ban kwana da juna. Wanda Al'ameen baisan lokacin daya rungume Jonah ba hawaye na zuba a idonsa". Mami taji haushin rungumar dayai masa Allah-Allah take su tafi kamar tana kan 'kaya dakyar Al'ameen ya saki Jonah suka shiga jirgi domin dawowa Nigeria. Mutuwar Abni hatta Sadiq da yazo gidan washe garin da suka dawo mutuwar ta taba shi wani irin mugun tausayin dan uwan nasa ne ya kama shi". Yace" Al'ameen kayi hakuri dan Allah kada kasa damuwa aranka ka zama musulmi me daukar kaddara da cinye jarrabawarka Allah ya canza maka da mafi alkhairin Abni a rayuwar ka". "Amin" kawai shine abinda Al'ameen yace dan bai cika magana sosai ba Afeeyah tayi kuka sosai domin ya taba bata wayarsa sunyi vidio call da Abni kuma sun saba da ita sosai". Tana kwance akan kujera tai ruf da ciki idonta a rufe kamar me bacci saidai zurfi kawai tai cikin tunani mami dake tsaye a kanta tana kiran sunan ta . Ganin bata amsa ba yasa afusace ta sakar mata duka wanda a razane ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya me karfi tace " mami lafiya". Tsaki mami tai tana cewa wato kema ashe sakarya ce ban sani ba ko dan ubanki wannan yarinyar dangin kice zaki dorawa kanki masifa kullum kina cikin tunani wanda kila koni na mutu bazaki damu haka ba". Hade rai Afeeyah tai tana kau da kanta gefe cikin takaici tace mami ko makiyin kane ya mutu jikinka yana sanyi balle Abni me ta tare miki wanda tabar duniyar baki daina ambaton taba". "Kwarai Afeeyah zage ni zamani ne yaya su zagi iyayen su kwalliyace duniya tazo karshe dan jakin ubanki har tambaya ta kike me tai min ta kusa kashe min yaro ta mutu ma ban huta ba kema da baki je ba gashi nan ta hada da kurwarsa da taki ta tafi dasu lahira meye na bata lokacin ki wajen tunanin ta kome zakuyi ba dawo wa zatai ba". Kai Afeeyah ta girgiza batare data sake magana ba Zainab ce tai sallama da dumemen akwatin ta bayan ta driven gidan sune daya kawo ta dauke da wani akwatin. Cikin mamaki Afeeyah ke kallonta yayin da mami ta washe baki cikin murna tace tun shekaran jiya da Binta ta kira ni tace zaki zo kimin kwana biyu nake zuba ido saiyau sannu da zuwa". "Yauwa mami ina kwana Zainab tace tana zama kujeran dake facing din Afeeyah a fakaice ta nuna Afeeyah da yatsa tana maganar kurame". Tsaki Afeeyah taja cikin tsanarta ta mike zata bar gurin mami tace ke Afeeyah ja akwatunan nan ki kai mata su part din ki acan zata zauna cikin daya daga bedroom din part din". Matukar takaici ne ya kama afeeyah har bata san sanda hawaye ya zubo afuskarta ba amma ta goge tana rike hannun akwatin ta wuce kamar yadda mami ta umarce ta". Zaunar da Zainab mami tai tana cewa kinsan me yasa nace ki dawo gidan nan da zama "?. Kai Zainab ta girgiza mami taci gaba babu komai zan fada miki ba yanzu ba wani aiki zaki min". Daidai Afeeyah ta dawo tadau dayan akwatin Zainab tace hay madam kidan hada min ruwan wanka no hot no cool". Cikin bacin rai Afeeyah ta juyo muryarta da fushi tace ko kinfi uwarki kokari baza ki samu abinda kike so ba ni ba sa'arki bace nafi karfin yi dake jaka kawai". Zanci uban ki fa Afeeyah jimin shashashar yarinya". Mami ta fada tare da kallon Zainab tace rabu da ita dama fushi take bari zansa a hada miki yanzu". Afeeyah na shiga bedroom dinta ta fada kan gado tana fashewa da kuka tace" ya Allah kaine ka fimu son Abni ka karbi kayar ka kayi mana canji da mafi alkhairin ta ka tausayawa dan uwana ka bashi mace ta gari me share hawayen mijinta". Hayaniya ce sosai ke tashi da shewar mata a gidan su Abu domin anzo nemawa ilya aurenta. Lami makwafciyar su dake duba kayan da komai kala bibiyu ne ta rafka gud'a kamar zata cire hancinta tace. "Kai masha Allahu Allah yasa Jamila ta tayi 'kashin arziki kamar Abun ki Saude ni ina Salamatu ne". Saude dake rausaya kai irin uwar 'yar nan tace wai ta tafi gidan su tun safe munafika". Aliya ta amshe da cewa ba wani bakin ciki take saboda 'yarta zatai kwantai tunda dame Abun ta fita yan watanni ne". Gadoji tace humm aiko bakin ciki zai kashe ta don tunda nake ban taba ji ance ga wani yana san fatin taba inaga bakin jinin daga sune". Mukam biki zamusha mu gwangwaje matsalle me kalangu zamu gayyato yazo ya buga mana gangar cahiya😂🙉. Laraba tace ni kuma hankalina be kwanta da fitar Salamatun nan kar muje munna nan mun bude baki da hanci tana can tana gunbudowa Abuwa asiri". Zaro ido Saude tai tana dafe kirji tace Allah ko 'kawata har kinsa naji nima nawa hankalin ya tashi". Tsomo baki tabawa tai to meye muma sai mu tashi tsaye ko taki ko taso aure sai Abu nada 'ya'ya Fatima bata samu mashinshini ba ehe🙄. "Kunga mubar wannan maganar bari na duba mana jalaf din shinkafar kota nuna muci" cewar Saude tana mikewa. Lami na ganin Saude ta wuce kitchen ta rike baki cikin munafirci tace" jama'a yau nake ganin wani ikon Allah mutuwar zuciya ta 'kare a dangin su ilyasu kalli wai komai biyu". Tabawa na kallon kofar kitchen tace hum abinda yake cin raina kenan yar uwa kika riga ni furtawa mutum da hankalinsa bazai kai yarsa wannan gidan ba". Gadoji tace nima sheda ce ina marsida yar gidan Bala sai daga gida ake kai mata abinci mijin ya kasa riketa kuma ai kinsan mijin nata Sado (Sa'idu) dakin su daya da ilyan". Laraba tace mukam ai taushe zamu zo mu kwasa ina ruwan mu dama irin su abuh ai sai ana basu tantirai kuma nasan zataci ubanta a gurin Halima domin ita bata zama lafiya da surukai". Aliyah tace yo matar da ko naman miya ne sai a gaban ta ake rabawaa dan kar a cuceta duk cefanen da yayanta zasuyowa matan su saita burkice kowacce leda idan kaje kasuwa baka biyo ta dakin taba kuna zaune zata fado muku daki ba sallama🙊". Lami dake dariya tace kice Saude abar hankata baki Abuh karamar bazawara za ai sakin uwar miji ba sakin wawa ba". Duk gurin dariya suka kaure daidai Saude ta fito da katon tire fal da abinci ta ajiye tana cewa dariyar me kuke"?.. Lami tace dariyar farin ciki kawata sai aurar da yaran mu muke asirin mu a rufe tuna hakan ne ya samu dariya". "Wallahi kuwa lami ai abin da dadi zuma da madara muci kartai sanyi dan nasa mana kitse a ciki . Hummm ayya Saude kin 'baro🙄😖😠😕. 💰'DAN MILLIONAIRE💰 Page 15 to 16 Zaune suke a palor misalin karfe tara na dare daddy dake rike da wani photo ya mikawa Al'ameen yana cewa. "Aminullahi wannan 'yar gidan abokina ce Mudansur sunan ta Afnan ban sanii ba ko tayi maka saika aure ta". Da sauri mami ta amshi photon daga hannunn Al'ameen tana cewa me laifin wannan yarinyar ta hadu kawai ka nema masa ita". Hade rai Afeeyah tai tana kallon daddy tace nidai a shawara ta abar min dan uwana ya huta ya nutsu daga baya zai samu wacce yake so da kansa". "To uwar iyayi wa ya sako dake" mami ta fada tana harararta. Murmushi daddy yai yayi kyau Afeeyah kin fadi gaskiya amma bari naji ta bakinsa Al'ameen kana son ta"?. " a'a daddy" shine kawai abinda yace . "Ji banza " mami ta fada cikin haushi". Dariya Afeeyah tai tana kallon mami tace gaskiya ne yaya Afnan bata dace dakai ba kalleta fa fiyu da ita kamar an zana d'aya . Duka mami ta kawo mata tana cewa jakin uban ki Afeeyah". "A'a daina zagin ta mana karki debe mata albarka tabi 'ya'yan kaji🐣🐤🐥. Amma tsakani da Allah alhaji meye abin kushe a wannan yarinyar". "Babu amma tunda baa kece zaki zauna masa da ita ba shi kuma yace baya yi shikenan abar maganar". Mikewa mami tai irin tayi zuciyar nan tace saida safe". Har hada baki daddy da Afeeyah suke wajen cewa Allah ya tashe mu lafiya". "Zan kama kine Afeeyah zaki min bayani". Bayan wata daya Abuh ce ta shigo gida da kukan ta Saude dake kan tabarma tace lafiya kukan me kike ko keda ilyasun ne yaron nan ya fara bani haushi ba wata uwar ya bamu ba tun kafin a kaiki gidan sai wulakanta ki yake zaici kwal ubansa😜😂". Kai Abu ta girgiza a'a ba shi bane Sa'adu ne dan gidan me gari". Ba shiri Saude ta mike na shiga uku meya hada ku zaki yayo min masifa😁". "Abu na kuka tace wai Fati yake so😱". "Wacece Fati kuma ina ruwanki koma wa yake so tunda kina da naki". "Kefa Fatin nan gidan yake so". A zabure Saude tace me karya ne akan hakan kike kuka". "Wallahi ba karya bane yanzu na wuce su suna waje akan dakali suna hira". "Kan bala'i wato Salamatu dan me gari kika yiwa asiri ko aiko sai kowa yaji a garin nan kina zuwa gidan boka bari gari ya waye tabdijan wallahi da sake dan kinga bikin shekara ya kusa kada yarki tasha kunya agaban dunbin jama'a na gari da gari". Tari dabai kama Salamatu ba bataiwa Saude ba ta tura mata aniyarta domin batasan ma wani Sa'adu nason Fati ba". Kasa nutswa Saude tai saida ta sayar da akuyarta ta dangana gurin boka akan ya karkatar da hankalin Sa'adu kan Abu ". Yaji ya tsani Fati haka ta juyewa boka dukkan kudin sisi bai bari ta dawo dashi gida ba amma fa ya mata aiki domin tun a ranar labari ya sauya akala". Da dare sai akace Abuh tace inji Sa'adu wata irin faduwa gaban Salamatu yai cikin tashin hankali ta kalli fati dake kallon Abu". Dariya Saude keyi tana juyi da habaice habaice tace dadi na da gobe saurin zuwa maza Abuh shirya kije kada ki bata masa lokaci tsuntsun soyayyar🕊 ya dawo kanki ahayye ayyuriri nanaye nisa tazo kusa". Kallon Fati Salamatu tai cikin tausayawa tace kada ki damu Allah yasa haka ne mafi allhairi kinji babu komai kai Fati ta daga cikin damuwa sosai amma batace komai ba"'. Tashin hankali ne karara ya bayyana da kiyayyar 'kauye🏕 a fuskar mami lokacin da daddy yace mata ta shirya yana son zai gano danginsa". Cikin cika da batsewa tace amma alhaji mezai hana kaje kai kadai". "Saboda me" ya tambaye ta cikin mamaki. Kai tsaye tace" dole sai munyi gayya me zamu ciyo"?. A garin daya tare dukkan zuriya ta kike cewa me zaki ciyo Aisha tun ba yau ba na fahimci bakya kaunar zuwa dangi na saboda a kauye suke amma ki sani sune komai nawa idan kika 'kisu nine kika 'ki fito fili kice mustapha bana sonka basai kinbi ta bayan gida ba". Zaro ido mami tai ni da yaushe nace bana sonka"?. "Yanzun nan kika fada tunda bakya bukatar asalina kinga son karya kike min yaudara ta kikeyi". Kuka mami ta kama yanzu alhaji shedar da zakai min kenan"?. Mikewa daddy yai ransa a hade yace na fada miki ki shirya idan kuma baki canza halayen kiba zan dau mataki a kanki". Yana fita tace na shiga uku ni Aisha wannan tsinannan 'kauyen kuma zanje daga wannan masifar takau sai wannan😢. Humm mami manya 'kauye🏘 tushe da asalin kowa😘 duk wanda bashi da 'kauye to bashi da asali😠 tsintaccen kan hanya ne🙄. Washe gari motoci biyu suka dauka yayin da Zainab tace baza ta bisu kauye ba ta wuce gidan su kafin su dawo". Da matukar murna Muntari ya tari yayan nasa nan aka hau yi musu hidima da bajinta duk wani abu dazai burge su na gargajiya". Afeeya dake shan fura ganin mami tayi gurum yasa tace wai mami bazaki ci komai ba to kisha wannan akwai dadi". Cikin bacin rai mami tace zanci 'kaniyarki fa Afeeyah ni abokiyar wasan kice"?. "Yi hakuri mami " daga haka bata sake magana ba". Sadiq kam dama ya shiga gari idan yazo baya zama guri daya kamar kifi🐟". Al'ameen da yake suna tare da daddy a dakin muntari yace dad nifa yunwa nake ji". "Kuma Aminullahi ga abinci iri daban daban sai wanda kake so". "No daddy ba irin wannan nake so ba". "Uhmm wato sai kwai ko wannan abincin yafi wanda kake ci a birni sa lafiya da gina jiki". "Nidai daddy mubar maganar samo min mafita Allah ina jin yunwa sosai". Daddy dake kallon shi yace to Aminullahi hanya mafi sauki ga yaji da mai nan a kusa dakai dauki ka cinye ni amma ka fara ta 'kafofi na saboda kar na gudu😂😝". Dariya wacce babu shiri Al'ameen yai yana kallon daddy yace haba dad idan na cinye ka babu wanda ya kaini asara". Muntari dake gefe yace to yanzu me kake so a dafa maka". "Am small dad in son samu ne dan wake". "Shikenan karka damu bari yanzu zansa ayi maka" mikewa yai yana fita". Al'ameen dake kallon photon Abni dake screen wayarsa yace daddy bari naje gurin grand-mah". "Ok yayi ka gaishe ta" Al'ameen na fita daidai Fati ta shigo da bokitin ruwa a kanta tana cewa wash Allah umma ki sauke ni". Da sauri Salamatu ta fito daga daki tana cewa meyasa kika ciko". "Umma bana son na koma ne". Zama Salamatu tai tana hada kayan wanke wanke Fati tace barshi zanyi umma ki huta". To Allah ya miki albarka". "Ameen umma motar waye guda biyu a kofar gidan nan masu kyau". "Ayya Fatima yan uwan kine suka zo daga birni da yayan babanki Mustapha yana dakin baban ku kije ki gaishe shi". "To umma " fati tace tare daa mikewa kusa gwaruwa tai da al'ameen da sauri taja baya tana cewa yi hakura dan Allah ban ganka ba sannu da zuwa ". "Thank" yace daga haka bai sake magana ba yai hanyar waje cikin mamaki ya tuna yarinyar nan kamar ba ita yake dauka a hannu ya sayo mata chocolate ba shakka babu amma girmanta ya gani sai yaga ta cika masa ido. Yana zuwa gidan ya tarar da Sadiq acan da ido ya masa magana cikin tsokana Sadiq yace . "Lah hajiya kinsan me Al'ameen yace wai ya yaga kin kara tsufa sosai kin ragargaje kiji fa hajiya kamar wata kwarya". "Rabu dashi Saddiqu lokaci ne shima wata rana zai taka wannan matsayin". "Matsala ta dake hajiya bata suna meye zakice Saddiqu just kice Sadiq". "Bazan ce jas Saddiq dinba karka dameni😂😜". Al'ameen ta kalla tana cewa zauna mana Aminu kana tsaye kamar wata bishiya". Zama Al'ameen yai cikin hade rai yace ba suna na Aminu ba Al'ameen nake". Hajiya dake kallonsa domin yana kama da kakansa wato mijinta tace. "Bazance Alemin din ba da Aminu zan kira ka ya zakai ubanka Aminu ya rada maka a haka suka sha minti da goro da naman suna". "Nidai na fada miki suna na Al'ameen"' "To kinji hajiya ni Sadiq shi Al'ameen sai ki gyara". "Bazan gyara ba duk wanda na kira karya amsa ". Kallon Al'ameen tai tana cewa" Aminu ya batun aure naji har yanzu shiru"'. "Babu ruwan ki in zanyi in bazan yiba wannan ganin dama tane". "Karya kake sai kayi d'an kare da fari kamar........... Sai kuma tai shiru bata karasa ba murmushi Al'ameen yai dan ya gane nufin ta yace. "Karasa man da fari kamar wa zaki ce kuma kin manta ba d'an kare zaki ce ba saidai kice dan kwikwiyo🐩😂. Dariya Sadiq yai yana kallon hajiya yace hajiya kinji fa saidai kice d'an kwikwiyo ba d'an kare ba". Da sanda hajiya ta nuna shi tana cewa kai kuma kayi man shiru bansan shishshigi zuwa dangin miji da ganamasgo ka rufe min baki". Dan zaro ido Sadiq yai ciki tsokana yace na rufe ruf🤐 hajiya me ran karfe ki shirya idan zamu koma dake zamu tafi kiga birni ki huta kiyi 'kiba". "Ni ka rufa min asiri da zuwa birni bazan iya rayuwa acan ba". "A haba dai hajiya me yasa"?. "Abincin kune bazan iya ci ba gara na zauna anan naci wanda na saba dashi". "Wanne kalar abincin ne baza ki iya ciba"?'. Cikin tsufa hajiya tace kaga ta farko wacce na tsana andosi da kwai dinnan". Dagowa Al'ameen yai cikin mamaki yace" me andosi kuma? abinci ne? ni ban ma sanshi ba". Dariya sosai sadiq keyi yace hajiya kina burgeni wato indomie kike nufi itace andosi". Hajiya tace "Eh da wannan abin me kamar tsutsa da kuke ce masa damaroni da sifagatin du bana ci ko an kawo min daga gidan muntari". Sadiq dake rike da ciki yace lallai kam hajiya yi shiru haka ciki na ya fara ciwo makaroni da spagetti ni kuwa abinci na kenan". "Shiyasa gaka nan kamar iska ta bushe kun 'ki al'adun hausa sam". "To hajiya yanzu ba gani nazo ba saina cika ciki na da rama da zogale kafin na tafi"'. "Daka kyauta Saddiqu ina iyalin taka ne Ri'kayye ko tana gida nasan da daita kuka zo da yanzu ta karaso" Cikin mazu Sadiq yace bansan wata Rikayye ba idan mata na kike nufi sunanta Ru'kayyah". "Ita nake nufi mana saboda bakin ciki shine ka 'ki zuwa da ita". Batare da Al'amin ya dago ba yace hajiya meye abin bakin cikin dan kawai baizo da ita ba"?. Hajiya data balli goro tace kai kuma kamin shiru ba dakai nake ba tuzurun banza kalleka kato dakai idan anan ne kana da 'ya'ya wajen biyar". "Ai hajiya daina fada 'ya'ya biyar sai kace na hada dangi da kaji uku ma sun isheni shiyasa bazanyi aure da wuri ba". "Ashsha kayi ta banza bari ai Mustaphan zaizo ya same ni zanji idan shine ma yake karanta maka kada kayi auren da wuri saiya bani amsa". Page 17 to 18. Basu bar gidan hajiya ba sai bayan sallar isha a kofar gida saman dakalin Al'ameen ya zauna sa'banin sadiq daya shiga cikin gida". Yana nan a zaune Sa'adu yazo yasha wanka ya sako gwanjola irin takalmi sau ciki na roba"'. Kallon sa Al'ameen yai tun daga kai har kafafu lokaci guda murmushi ya 'kwace masa ganin sai wani buda kafada yake". Fati ce ta fito tana nufar inda yake tsaye wanda ko minti biyu basuyi ba Abuh ta karaso gurin da 'kawayenta tana haki tace". "Amma Sa'adu me nace maka ba nace kada ka sake zuwa gurin Fati ba nice nake sonka ba ka amince rannan a dandali ba saboda kai mun rabu da ilya". Shiru Sa'adu yai cikin takaici Fati tace wai dan Allah Abu meye hakan me na tare miki da bakya son gani na cikin farin ciki"?. A gadarance Abu tace ban sani ba bani da lokacin ki kai kuma muje ". Kamar rakumi🐪 haka Sa'adu yabi Abu zuwa dandali kamar yadda ta bukata 'kawayen Abu na yiwa Fati dariya da habaici suka bar gurin". Wasu zafafan hawaye ne suke zuba a idanuwan Fati gashi gobe ne gasar nuna samari yanzu ita ya zatai da rayuwar ta cikin takaici ta juya zata shiga gida". Al'ameen dake kallon ta yace " madam ji mana ". A firgice Fati ta kalli inda yake tana goge hawayen fuskarta" Jitai yace mene sunan ki"?. Muryarta na rawa sakamakon kukan da take tace suna na Fatima". "Ok yayi jeki" kawai yace yana mayar da hankalin sa kan waya wucewa tai ta shiga gida. Cikin shishshigi da cusa kai Saude ta shiga dakin da mami suke tana cewa Aisha a karo muku abincin ne". "A'a ya isa haka mun gode". "To shikenan bari na kawo miki wata kyakkyawar fura ko zaki sha". Fita tai tana daukowa ta kawo mata sannan ta musu saida safe ta fice tsaki mami taja tana rakata da harara tace ko ina ruwanta dani mayya bazan sha ba aikin banza kawai". 'Yar dariya Afeeyah tai tana gyara kwanciyar ta yayin da mami take ta maganganu da fada ita kada kadai. "kawai an kawo mutum wannan mugun kauyen an ajiye duk zafi babu wata ni'ima ko jin dadi ba a.c haba wallahi bazai yiwu ba dole gobe na samu alhaji idan shi bazai koma gida nikam na gaji zan tafi". Shiru kawai Afeeyah tai tana sauraron mami da mamakin furucin ta amma batai magana ba saboda gudun abinda mamin zata ce mata saidai bata jin dadin yadda take kushe 'kauyen mahaifin nata domin itama tana son garin ". Washe gari Al'ameen bai tashi bacci da wuri ba har rana tai saida Sadiq ya tashe shi yana mikewa ya rike kansa tare da cewa. "Subahanallahi wannan karar haka kamar zata fasa min kunne kuma daga ina me suke". Sadiq dake shirin fita yace bazan jira kaba domin an fara wai wani biki suke na nuna samari" yana fadin haka ya fice. Shiru Al'ameen yai kamar kuma an tsikare shi ya mike cikin gaggawa yai wanka ya shirya yana fita yaga Salamatu ta fito daga daki. Bayan sun gaisa yace ina Zarah". Cikin mamaki tace wace haka"?. Tunawa yai sai kuma yace oh Fati nake nufi tana nan". "A'a wallahi bata nan ta dade da fita ban sani ba ko tana gurin bikin wasan samarin can nasu da suke". "Ok" yace yana fita daga gidan harya kusa zuwa yaji kid'an na hawa kansa domin makad'a ne da yawa da maroka na gari da gari suke taruwa su zo". Juyawa yai ya fasa zuwa hango wasu gajerun bishiya masu ni'imtacciyar inuwa yasa ya nufi gurin dan yadan huta". Yana karasawa yaji ana shashshekar kuka cikin mamaki ya soma dube dube can ya hango me kukan zaune ta kifa kanta". Har zai rabu da ita sai kuma ya tuna duk wanda ya sharewa wani hawayen sa Allah zai share masa shima". Tunani ya farayi to me zaice mata zuwa wani lokaci da yaga bashi da mafita yai gyaran murya". Da sauri ta dago a razane wanda shi yana mamakin ganinta a gurin ita ma tana mamakin ganin sa". "Kukan me kike"?. Shine tambayar dayai mata kaita girgiza tana cewa" ina kuka ne saboda dazan aje abin fada zanyi abin kunya yau ranar fitar da gwani ne a dandali". "Kamar ya"? Me kuke yi idan kunje"?. Gyara zama tai tana cewa da farko idan kowa yaje me kira zai rika kiran suna mutum da budurwar shi su fita fili ya bata kyautar zobe da agwagi guda uku shikenan sai su fita wasu su shigo. To kowa ya sheda ya gani wace nada saurayi kuma baza a kada mata kalangun tayi kwantai ba idan kuma baka da saurayi kowa saiya sani ayi ta maka dariya". "Toke yanzu bakije ba kina nan idan aka kira sunan kifa kisa saurayin naki ya rude". "Ni bazan je ba". "Saboda me"?' "Idan naje ma babu amfani wazan nuna wanda yake sona yayata Abu tamin 'kwacen sa bani da kowa". "Zaki are ni"?. Cikin rashin fahimta tace aron me". Basarwa yai tare da cewa muje na ga abinda kuke yi a bikin. Badon taso ba jikinta a sanyaye ta mike suka tafi dandalin shake yake sosai da mutane suna zuwa sai zance da yamud'id'i da munafirci ake ana ta kallon Al'ameen'. Me shela ne ke cewa anzo gidan. Muntari na alhaji attajirin yan kauyen nan me taimako muntari gwani me 'kwazo ina babbar 'yarsa Abu ta fito mana fili da nata gwanin". Fita Abu tai tana hura hanci yayin da Sa'adu ya fito ya tsaya a gefen ta yana cire zobe ya bata sannan ya bata agwagi guda biyar. Lallai su Saude za a sha dafgen nama🍖. Suna fita me hela ya sake rafka cikiya ina 'yar uwarta Fatima ta fito fili da nata gwanin itama". Jikin Fati tai yadau rawa cikin nadama da dana sanin inama bata zo gurin ba . Kaurewa akai da surutu kowa da abinda yake fada wasu na mata dariya wasu na tausaya mata". Ina Fatima ne ko mu buga miki gangar bandaro me kwantai" maroki ya fada yana le'ke -le'ken inda zai hangota". "Ehhhh kawai a kad'a mata mu cashe " guri ya kaure ehhh a buga ehhh a buga. Al'ameen da abin ya bashi dariya shiga cikin filin yai yana murmushi yaiwa me hela magana". "Heeee a saurara jama'a ina mewa Fatima dariya😂? To ka rufe bakin ka🤐 ina maison jin jarumin💪 Fatima? To bude kunnen ka👂 dakyau ina mai nuna Fatima da yatsa👉? To ka sauke hannunka ina me son ganin gwanin Fatima ya matso kusa ya bude idonsa 👀yai kallo inji wannan zankadedan saurayin yace shine saurayin Fatima"' Me hela ya fada tsit guri yai kamar sun mutu kowa idonsa nakan Al'ameen wasu suce ba mutum bace aljani ne wasu suce daga ina ta samo wannan. Fitowa filin Fati tai tana mamaki kare tan da Al'ameen yai a haka idan ka kalleshi zakai tunanin zaiyi girman kai. Kudi masu yawa Al'ameen ya baiwa marokan da makadan wanda me hela da lasafika a susuce ganin kudin da baiyi zato ba yace. "A saurara Fatima me 'kashin arziki ce tafi karfin kaji koda na turai ne balle agwagi masu wuni a cikin kwata😂". "Sannan ku kalli zoben💍 daya bata na gwal ne babu wacce ta samu koda na azurfa dan haka dole yau a yabe ta itace ta cinye gasa a wannan shekarar musbahu ku bamu sauti". Kid'a🎶 da algaitu🎺 ne ke tashi kamar gidan sarki suna kuma yabon Fati da mata kirari suna kod'ata sun samu kudi sosai a gurin Al'ameen saida ya tabbatar daya wanke Fati tas daga jin kunya". Abuh na komawa gida taje ta fadawa Saude abinda ya faru tsaki Saude tai to saime inace ba saurayin nata bane idan ya tafi shikenan ta fito rana karki wani ma damu kanki". Da salon munafirci Saude taje ta karancewa mami komai harda abinda ba'ai ba saida tai 'kari. Mami kam bata juri zuga ba tuni ta cika tayi fam waya ta dauka tana danna masa kira yana dagawa tace duk inda kake kome kake kazo yanzu ina son ganin ka". Yana zuwa ta balbale shi da masifa Al'ameen kana hauka ne? Akan me zakaje ka 'barnatar da kudin ka saboda ka kare wata banzar yarinya". Tun kafin yai magana Afeeyah tace kai mami kamar ya banzar yarinya yar uwar sace fa kuma koba haka ba duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi". "Ke kuma rufe min baki bake nake tambaya ba dakai nake". "Gashinan ta fada miki mami duk wanda ya taimaki wanI Allah zai taimake shi"'. "Hummm shiyasa kaje ka zubar da ajinka a gurin yan kauye a gaban mutane sama da kirge wai yaushe ka lalace da shashanci haka ne". "Mami ki fahimta yarinyar nan sister nace fa yar uwa tace jinina ce da ita da Afeeyah duk daya ne". "A wajen ka sakarai ba wacce kuke uwa daya uba daya da wacce kuka hada kakanni saboda mutuwar zuciya kace daya suke". "Maamii gaskiya maganar sa koni Fatiman nan tana burge ni wallahi amma komai mami idan ba kece kika zabe shiba baiyi miki ba " Afeeyah ta fada da yanayin damuwa". "Ke dalla 'kyale ni yar iyawa gwana saina fadi abinda ke raina ". Mikewa Al'ameen yai yana cewa good night mami". Ya fita daga murya tai yadda zai jiyota tace kowa ya kwana lafiya shi yaso" murmushi yai yana rokon Allah daya shirya masa mahaifiyar tasa. We will meet👪 again. See👀 you next time Typing📲 +234 905 527 3614. Yusrah Musa Abubakar Gimba. Page 19 to 20. Tun asuba Saude da Abu suke gyaran agwagin nan kamar wanda suke gyaran saniya gari na wayewa Abu takai markade aka dafe su"'. Wani abin mamaki a fanteka aka zuba guda uku wai gidan me gari za'a kai haka suke yi biyun sune na budurwar . Dariya sosai Afeeyah tai ita bataga abin farin ciki dan an baka wadannan agwagin ba tunda babu riba". Kai da kafa harshi Saude ta dafe duk kayuwan ta debo a wata langar kwano me tsatsa tana kaiwa Salamatu ". Kai Salamatu ta girgiza tana cewa" a'a alhamdulillah na gode". " iheee bakin ciki kike ne Salamatu dan 'yarki bata samo ba kome"?. "Eh shi nake yi". "Aiko zaki mutu da bakin ciki domin Abu sai zaman gidan me gari su o'o kuwa bamusan inda za'a hara ba ko kuturu ko makaho waya sani". Ta fada tana dariyar mugunta tare da daukar langar kayukan ta koma dakin ta". Daddy na zaune tare da Muntari daren da ana gobe zasu koma Abuja muntari ke cewa'. "Nikam yaya inaso yara na suyi ilmi sosai amma sa idon 'kauyen nan ya hanani sakat gashi ita Zainaba har ana zancen aurenta". "Daddy yace toba tana da 'kanwa ba 'yar gidan Salamatu ko har ita za'ai auren"?. "A'a iya zainabun ce ita har yanzu bata samu tsayayye ba tukuna dai". "Ok mezai hana mu tafi da ita tunda kana so tai ilmi sai a sai mata makaranta". Muntari yace da naji dadi yaya wallahi inason dana yai karatu". "Shikenan babu damuwa ka sanar da mahaifiyarta gobe da wuri kafin mu wuce ya kamata ta sani". "Eh zan fada mata duk da nayi shedar Salamatu bata da matsala". Washe gari jin harda Fati zasu tafi yasa saude tace tab kace su Aisha zasu debi masifa yarinyar da kauye ma idonta a tsaye yake balle tana birni . Nasiha sosai Salamatu taiwa Fati duk da a ranta bata son rabuwa da yarta ta kamar yadda itama Fatin bata kaunar binsu. Da kukan ta tashiga mota suka tafi yayin da Afeeyah ke mata dariya tana cewa ayya keda dawowa sainan da shekara uku Allah sarki". Da fati iya hawaye take jin abinda Afeeyah ke cewa yasa ta soma shashsheka". Al'ameen dake driving Sadiq na kusa dashi ya joya yana cewa mene haka zan sa'ba miki ba jiya kika gama cewa she's our sister ba". Murmushi Afeeyah tai tana kallon Fati tace sorry sis ita kam Fati babu bakin magana har sukaje gida". Cikin fushi na sun taho da Fati yasa mami ta fice fuuu daga motar daddy ko kasheta baiyi ta shige cikin gida". Afeeyah kam bedroom dinta takai Fati tana cewa sannu da zuwa gidan mu ki kwantar da hankalin ki nan tamkar gidan ku ne ki dauke ni matsayin 'kawarki". Murmushin dole Fati tai tana cewa nagode". "No baki da matsala Afeeyah ta fada tana shiga toilet tayo wanka da alwala sannan ta fito tana cewa fati kema kije kiyi wanka". Shiga toilet Fati tana mamakin kyausa kamar ka kwanta a kasan tayis din sai 'kyalli yake kamar mirror. Ganin bata ga ruwa ba ta leko tana cewa wai ina ruwan kuma banga baho ba sai wani kwale-kwale😀 ko a ciki ake wanka"?. Dariya ce ta kama Afeeyah saida tagama shiryawa sannan taje ta kunna mata ruwan ta fito. Sanin datai cewa bada son ran mami Fati ta biyu su ba yasa tasa kawai aka kawo musu abinci part dinta". Kwanan Fati biyu daddy ya sai mata school ta fara zuwa itama driven ta daban . Korar yan aikin gidan mami tai mutum uku tabar biyu cewa meye amfanin fatin idan ba bauta ba". Tasa ta a cikin 'yan aikin batare da sanin daddy ba hakan datai ya 'kona ran Afeeyah dan haka itama take shiga kitchen din tana koyawa fati wasu abubuwa. Ina Fatima ban ganta ba jiya da yau lafiya kuwa"?. Kau dakai mami tai tana cewa tana kitchen ita da su nana". Cikin mamaki daddy yace me take yi a kitchen din"?. Rasa abinda zatace mami tai ta kama kame-kame daidai Afeeyah sun fito ita da Fatin jikin su duk a 'bace. Daddy da ransa ya soma baci ganin yadda suka fita hayyacin su ya kalli mami cikin fushi yace". "Aisha yanzu sune kika mayar kitcinonin ki yara nane fa amma zaki wani tura su kitchen sun zama kuku ne". Ganin daa Afeeyah tai daddy ya damu da yawa yasa cikin son kare mamin tace. "Lah daddy ba ita ta tura muba kasan ban iya girki ba kuma gashi kullum lokaci yana ja gidan wasu zanje shine nace bari na koya abin kunya ne ace kamar ni ban iya komai ba". Sauke ajiyar zuciya mami tai a boye jin Afeeyan ta ceceta mikewa daddy yai yana cewa shikenan amma ku rika aikin baya baya sannan ku rika lura da wuka kada ku yanke. "To daddy mun gode zamu kiyaye" cewar Afeeyah. Barin gurin yai mami dake shirin tashi ita ma tace tunda kin biyewa wannan yar kauye wahala yanzu kika fara shanta ". Kai Afeeyah ta girgiza ba tare datai magana ba shigowar Zainab kenan ko zama batai ba ta kalli Fati a 'kyamace tana cewa". "Ke village girl dauko min abin sha a fridge sannan ki wuce kitchen ki zubo min abinci me zafi". Wani kallon baki da hankali Afeeyah ta mata tana cewa itace zatai miki bauta aiba yar aiki bace idan bazaki nemi nana ta kawo miki ba ki barshi". Ke na sako dake ne gada wacce nake yinan". "Kin sako dani tunda kika ambaci yar uwata bazatai ba kinji na fada miki". Tsawa mami ta saki tana hararar Fati tace ke dalla wuce ki mata abinda take so sa'ar kice ita". "Maamii" Afeeyah ta fada ranta a bace. Ke kuma zaki ci ubanki Afeeyah idan baki min shiru ba". Barin falon Afeeyah tai yayin Fati ta wuce kitchen ta zubo mata abincin tare da dauko juice ta kawo mata . Banza jaka yar kauye akuya" zainab ta fada tana dauko spoon. Juyowa Fati tai tace duk sunan kine gaskiya kin more jaka akuya toga dusa nan da ruwan tsami na kawo miki saiki fama". "Keee tsaya dan kan uwarki". A haba dai na tsaya saboda ke baki da wannan matsayin babyn daud'a jeki wanka da brush kafin na saurare ki, domin wari kike"😁🙊. Sai kuma ta fashe da dariya tana kallon Zainab tace ki fama ina zuwa idan dusar bata isa ba akwai wata a kitchen kice meeeyyy🐐🙈 zan zo na karo miki dan wallahi ganin ki ya tuna min da tinkiya ta🐏. Tana fadin haka ta bude kofa ta shige tana cewa sorry idan kinji haushi na kinsan mu villagers bamu iya magana ba". Cizon yatsa Zainab tai cikin takaicin tsayawar datai ta zuba ido Fati ta fada mata son ranta amma bari ta shiga part din saita fasa mata baki. Al'ameen dake tsaye a kofar palor ya jinjina kai yana karasowa zai wuce ganin sa da uniform din army yasa Zainab ta fahimci tafiya zaiyi cikin sauri tace". "Yaya Al'ameen". Cikin mamaki ya juyo jin yadda ta kira sunan a tausashe yasan akwai abinda zata ce". Mikewa tai tana zuwa har gaban shi ta ciro wani zobe daga cikin karamin abu me kyau tana mika masa". Batare daya karba ba yace na mene"?. Murmushi tai cikin karya murya tace kaima ka sani kawai ka fuske ne Allah Al'ameen ina cikin matsala na rasa yadda zanyi da rayuwa dole na fada maka cewa na kamu da ciwon sonka😱. Wani irin kallo ya mata zai wuce bai tanka ba ta sake shan gaban sa idon ta da hawaye cikin magiya tace". "Na roke ka Al'ameen ka soni ko kadan ne kaji tausayi na kada zuciya ta tabuga na mutu". "Da kin huta da matsalolin duniya ke dan kin raina min hankali nine zan soki are you out of your sense😠. A'a ina cikin hankali na koda na zauce to lallai sonka ne ina kaunar ka kuma da aure". "Ashe zaki mutu baki aure ba babu abinda zanyi da mace irin ki kada ki batawa kanki lokaci zuciya ta tamace daya ce kuma bata raye dan haka na kulleta". "Dan Allah Al'ameen ka bude ta gani nazo zan maye maka gurbin wacce ka rasa". "Ta ya kenan". Zoben ta mika masa amsa yai yana jifa dashi yace ko mata sun kare saike bazan aure kiba babu abinda zanyi dake bakya cikin kalar matan da nake son kasancewa dasu". Kuka ta saki lokacin daya wuce ta yana shiga part dinsa hannu ta dora aka tana cewa . Na shiga uku zuciya ta baki min adalci ba meyasa zaki kamu dason mutumin da ko kadan jinin mu bai hadu ba". Bayan wasu watanni Fati harta saba da tsangwamar mami data Zainab domin duk wanda zasu kare ta basa nan Afeeyah taje gidan su mami Al'ameen bayanan daddy ba zama yake ba". Kullum zuba ido Zainab keyi da kwadayin ganin Al'ameen amma shiru wai mushiriki yaci shirwa . Suna Zaune a palor Afeeyah data fito ganin yadda zainab ta barbada kwalliya a fuskarta zata fita gurin bikin 'kawarta yasa cikin tsokana tace. "A'a yau kuma harda su biri🐒 muka samu a gidan namu lallai kice zamuje wasa". Cikin alamun tambaya Fati tace biri dai? Ke kuma a ina kika ganshi"?. Afeeyah dake shirin fita tace gashi zaune akan kujera ya dora kafa daya kan daya yana kallon fuskarsa a mudubi". Kallon Zainab dake duba mudubi Fati tai sai kuma ta kalli Afeeyah suna hada ido suka kwashe da dariya". Cikin bacin rai Zainab tace ke dan uwarki nice birin"?. Dakatawa da dariyar Afeeyah tai tana nuna ta da yatsa tace" kul kada ki kuskura na sake ji kin ambaci uwata saina zubar miki da hakora". Fita Afeeyah tai daga palon yayin da fati ta mike zata bar palon itama taji ance "Zarah". A firgice ta juyo ganin Al'ameen tai tsaye sanye da kananun kayan da sukai matukar yi masa kyau kuma ya kara kyau da 'kiba. Dan murmushi tai tana cewa sannu da dawowa". Bai amsa ba sai zama dayai yana cewa dafa min wani abu naji ko kin iya girki". Yar dariya tai tana nufar hanyar kitchen a rayuwa Al'ameen yana burgeta da sam bashi da girman kai idan wani ne ko karasa kallonta bazai ba". Zainab datai suman zaune muryar ta na rawa saboda bakin ciki abinda yace yanzu tace. "Amma gani ka rasa wa zakasa ta hada maka breakfast sai wannan kucakar 'kazama yar kauye"'. Itace ta cancanta nasa domin tafi ki matsayi kucaka 'kazama kece sunan kine dake hakan ya dace". A fusace ta mike tana nufar kitchen din tarar da fati tai tana kokarin kunna gas ta buge mata hannu tana huci tace. "Ke dalla matsa min jaka ". "Jaka dai" Fati ta maimaita. Cikin karaji tace eh nace jaka dabba jahila kibar kitchen dinnan domin Al'ameen nawa ne nice zan aure shi dan haka ki fita daga gona ta ko kallonsa na sake gani kinyi saina faffasa miki ido". Dariya Fati tai Allah da gaske amma sai naga wanda kike wahalar da kan naki a kansa bakya gabansa son maso wani kike". "Inji uban wa" zainab ta fada tana yowa kan Fati". Cikin dakewa Fati tace inji uban ki ke bari kiji bafa ki isa ki shiga tsakani na da dan uwana ba indai akan ala'kar mune bakin ciki zaisa zuciyarki ta buga dare daya ki mutu Al'ameen baya sonki". Wuka Zainab ta dauko tana kawo wa Fati wani irin wawan yanka gocewa Fatin tai a bisa tsautsayi ta yanke ta a hannu". Rike gurin da jinin ke fita Fati tai tana dagowa zatai magana zainab ta dauke ta da mari. Itama Zainab din babu zato taji zazzafan marin ya sauka a kuncinta wanda a gigice ta fasa kara". Tana kallon Al'ameen basu ankara ba suka sake jin karar mari mami ce ta shigo daidai Al'ameen ya mari zainab shine itama ta mari fati dan tasan a kanta ne". "Mami" Al'ameen yace ransa a bace. A fusace ta juyo gurinsa tana cewa rufa min baki wanda baisan ciwon kansa ba akan wannan tsinanniyar yarinyar shine zaka fidda hannu ka mareta". Cikin tsawa mami ta kalli Fati da hawaye ke fita daga idonta tace ke kuma yau saikin bar gidan man tunda ke shedaniya ce kinzo kin hana mu zaman lafiya ". "Mami ina zataje da zakice yau saita bar gidan ba laifin ta bane nawa ne". "Sakaran banza dama ai nasan laifin kane basai ka fada ba". "Ke kuma kafin naci uban daya haifeki kije ki tattare tsunmokaran ki ya mayar dake. Fita Fati tai tana zubar da 'kwallar bakin cikin zagin da mami tai mata ita daman hanyar garinsu take neman komawa". Cikin mamaki shigowar Afeeyah kenan ganinta janye da akwati yasa tace lafiya ina zuwa haka". "Nice na kore ta domin hatsabibiya ce". "Kika koreta kuma mami ina zataje kenan"?. "Ruga zata koma can gayyar tsiya kauyen su". "Haba mami me kike cewa haka dan Allah kiyi hakuri". "Wallahi tunda na rantse saita bar gidan nan a yau bazan yi kaffara ba". Al'ameen dake tsaye yace Zarah⭐ muje". Mami dake hararar Fati tace ka manta baka ce wata🌙 ba". Daidai zasu fita yayi murmushi yana cewa to ai nine watan mami munyi ruga". "As as as ta kaji idan kaga dama kaima karka dawo ka zauna acan". Kuka Afeeyah ta fashe dashi tana shigewa part dinta mami data bita da kallo tace zaki kuka ki gaji har hawayen ki ya kare kora ce na kore ta kuma babu yadda za'ai dani"'. Bintu Musa Abubakar. Page 21 to 22. Gidan Sadiq Al'ameen yakai Fati cikin mamaki Sadiq yace ina fatiman zataje na ganta harda akwati ga fuskarka da damuwa lafiya"?. Kai Al'ameen ya girgiza yana kallon Sadiq yace" zata cigaba da zama anan". "Me yasa"?. "Saboda wani dalili" Rukayya ya kalla yana cewa" please auty na ga sister na zata taya ki zama". Murmushi Rukayya tai ok babu damuwa 'kani na sannunki da zuwa Zarah ko". "Eh sunan ta kenan "Al'ameen ya fada yana zama a dinning . To ai bakai na tambaya ba ". "Idan kin tambayeta tamkar kinyi da nine". Cikin tsokana Rukayya tace a'a fa Al'ameen kodai-kodai". Aje cup din daya hada tea yai yana cewa kodai kodai me. Da ido Rukayya ta nuna masa kodai son fati yake". Kafada ya daga yana cewa kibar ma wannan tunanin sam ba haka bane nida soyayya munyi ban kwana balle wani aure". "Humm yadda kake dinnan inaga mace daya ma ta maka kadan saidai biyu". Ni biyu ma sun min kadan saidai hudu". "Aiko zamu duba cikin dangi mu zabo maka". "Ba wannan maganar bana ra'ayin aure a cikin dangi idan ma zanyi gara bare". Mukam munfi so ka samu a dangi zanyi ta maka addu'a". Bana bukatar auren dangi Idan abinda kika fada ya faru zan baku kyautar visa kuje honeymoon duk kasar da kuke so". Rukayya tace tab aiko zan dage har fata na yaci kuma wallahi saika yi alkawarin daka dauka". Bai amsa mata ba sai mikewa dayai yana kallon Sadiq sannan ya kalli hannun fati yace please kadan duba ta taji ciwo da wuka a hannunta. Yana fadin haka ya fita dan bayason yawan tambayoyi da kallo Sadiq ya bishi tareda girgiza kai kafin ya fara duba mata hannun. Al'ameen bai koma gida ba sai dare daddy daya dawo ya tarar da Afeeyah idonta sunyi ja kuma sun kumbura ya tsareta da tambayoyi. Kasa fada masa cewa mami ce ta kore ta tai yayin da mami tai wi'ki-wi'ki tana rarraba ido alamar rashin gaskiya da kad'uwa. Mami daddy ya kalla yana cewa ina fatima Zarah take"?. Hautsinawa cikin mami yai ta rasa abin cewa sai kallon daddyn da take da tsoron idan yasan ta koreta kila itama yau tai kwanan gidan. Da fari Al'ameen yayi burus ya dauke kai kamar baya falon sai da yaga ran daddy yai masifar baci sannan ya gyara musu al'amarin da cewa. "Amm daddy Zarah tana gidan Sadiq taje musu wuni ne yanzu zanje na daukota". "Ok babu damuwa ai tunda tana can dama rashin ganinta ne yasa hankali na ya tashi". Mikewa Al'ameen yai yana fita a palon daddy dake kallon mami wacce tun dazu take susa kamar me ciwon 'kazuwa ko sabuwar kamu yace. "Dama tana gidan Sadiq amma kika barni nai ta ihu da baki na"?. Sauke ajiyar zuciya mami tai tana godewa Allah da yasa Al'ameen ba garin su ya mayar da ita ba tace". "To ai alhaji nayi tunanin zakai fada ne kace nabar bakuwa kuma budurwa tana yawo". "Akan me zanyi fada dan taje gidan dan uwanta ai zumunci tai yarinyar nada hankali". Kallon Afeeyah dake goge sauran hawayen fuskarta jin fatin na gidan Sadiq yai yana cewa". "Me akai miki ke kuma kike kuka gashi idanuwanki harsun kumbura. Sauke kai Afeeyah tai tana cewa daddy banda lafiya ciki na ke ciwo". "Kuma baki daa lafiya bazaki fada a kaiki asibiti ba kuka yana magani ne"?. "Daddy nasha magani tun dazu na samu sauki"'. "Shikenan Allah ya rufa asiri". "Amin tace". Daidai fati tayi sallama tana zama ta gaishe da daddy". Amsawa yai yana kallon bandejin hannunta yace ciwo kika ji Zarah da yaushe"?. Kafin fati tai magana Afeeyah tace daddy dazu ne a kitchen Zaina......... Dafe kirji mami tai tana tarin karya harda shidewa saboda kada Afeeyah ta fada". Ruwa Al'ameen ya miko mata karba tai tana sha kamar gaske fati data fahimci mamin bataso daddy yasan gaskiya tace". Daddy dazu a gidan auty Rukayya na yanke da wuka a kitchen shine yaya Sadiq ya samin magani a gurin". Ayya sannu Zarah ku daina daukar abu me had'ari irin su wuka kuna nisa dasu kinji". "To daddy na gode" Shikenan afeeyah tashi kije ku kwanta". "To daddy good night". "Ok daughter sleep well Allah ya tashe mu lafiya". Mami ganin datai sun rage saura su biyu a palon yasa ta kalli daddy tana cewa" alhaji dama wata magana nake so muyi". "Ta me"? Daddy ya tambaya. Gyara zama mami tai tana dan yin kasa da muryarta kadan tace akan Al'ameen ya kamata ace yanzu yayi aure domin zamansa haka nan bazai yuwu ba na samo masa matar aure". "Tofa a ina take yar waye"?. "Tana gidan nan yar 'kanwata Binta nake so ya aura gatanan Zainab". "Kece kika riga masa shiga masallaci ko shine kikaga alamar yana sonta". "A'a kawai ta dace dashi ne dan Allah alhaji ka amince". "Shikenan zan same shi da safe naji daga gare shi". Cikin faduwar gaba domin tasan bazai taba amincewa ba mami tace alhaji ba wani jin ra'ayinsa umarni zamu bashi idan tashi zamu biye bazai taba aure ba kullum saidai yasa hoton wannan baturiyar a gaba yana kallo screen din wayarsa photonta ne hatta cikin laptop dinsa photonta ne akai bana tunanin yana aiki ma yadda ya kamata idan kaje bedroom dinsa photonan ta sunfi goma a bango ta riga ta shanye shi babu yarinyar da yake kallo matsayin mace balle yaji yana sonta". "Haka dai kikace kuma, haka kike gani da zato a naki tunanin zuciya bata da 'kashi muddin ya samu wacce yake so da kansa zai nuna ta". "Alhaji baka yarda ba kenan saboda kai Al'ameen duk abinda zaiyi daidai yayi a gurin ka gaskiya ni ban amince ba ka sashi yai aure". "Zaiyi idan lokacin sa yayi wannan ba wata matsala bace kada ki manta gadona yai domin kafinki nima haka naso wata mai suna Hauwa amma da ban sameta ba nace bazanyi aure ba har abada kwatsam babu zato na hadu dake dan haka shima zaiyi ki rabu dashi kada ki sake dora masa wata damuwar". Son Al'ameen ya rufe maka ido kwata-kwata baka ganin laifinsa ko"?. "A'a ba haka bane kece dai kikewa abin gurguwar fahimta ni duk yarana daya suke a gurina dan haka kibar wannan maganar lokuta da dama ina tunanin kamar kin fara gigi alhalin tsofa bai kama kiba". Ni zan wuce ki kawo min abin sha" yana fadin haka yabar gurin kamar mami zatai kuka ta mike tana bin bayansa. Bikin Abu kam ya karaso 'kememe mami tace baza taje ba daddy ko kadan bai nuna damuwa ba saboda ya kudurin aniyar indai bata jeba suna dawowa zai kara aure. Kamar tasan abinda ke ransa sai ranar tafiya tace zataje baiso haka ba amma ya rabu da ita a tari gaba. Harda Rukayya Zainab ma ta bisu wai zata gano kauyen su Fati wanne kalla ne. Ranar daurin aure sukaje kwana biyu zasuyi Rukayya kam suna sauka ta debi yaranta ita da Sadiq suka tafi gidan hajiya acan zasu zauna domin sun saba sosai. Fati da Afeeyah gari suka shiga Zainab da batasan garin bama haka ta fita yawanta ita kadai har kasuwar garin. Lokacin da suka dawo Fati ta tsaya a gurin babarta Afeeyah kuma ta shiga gurin mami cikin fada mami ta kalleta tana cewa. "Wato Afeeyah kin biyewa wannan shegiyar yarinyar ko wai kune har kasuwa wani ya sai muku nama dan ubanki saiya sa muku magani a ciki. Cikin mamaki Afeeyah tace ni kuma mami da yaushe waye ya fada miki"?. "Nice domin na ganku da idona" Zainab ta fada tana sakin murmushi tare da yimata gwalo. Takaici ne ya kama Afeeyah wato sharri Zainab ta kulla musu jin mami tace wallahi kika kara binta yawo saina ci ubanki". Yasa ranta a bace tace nifa mami ba muje kasuwa ba karya tayi min". Ita kike cewa ta miki karyar saboda baki da kunya wannan yar 'kauyen ta koya miki rashin arziki". Shiru Afeeyah tai karshe ma ta mike zata bar dakin mami tace gidan uban wa zakije ko yawon barbadancin zaki koma". Kamar Afeeyah zatai kuka tace babu inda zanje fa kawai cikin gidan zan shiga". "To cikin gidan da zaki shiga kin aje wani abu ne"?. "Gurin yan uwana zanje". "Dakyau sannu me yan uwa mu kuma daga gidan marayu muke ko? to dawo ki zauna har gobe da zamu tafi babu inda zaki sake fita" dawowa Afeeyah tai tana kwanciya akan katifa cikin tsantsar bacin rai. MRS AL'AMEEN AHMAD CE😜. Page 23 to 24. Washe gari suka koma Abuja Fati da kukanta ta shiga mota dan cewa tai baza ta bisu ba ta dawo gida kenan saboda tsangwamar mami da take sha dakyar dady ya lallameta suka tafi". Wanda suna komawa mami ta hura wutar sai daddy ya daurawa Al'ameen aure da Zainab wani lokacin har kuka take da hawaye a gaban sa. Afeeyah na zaune a palor misalin karfe bakwai da rabi na safe Fati ta fito ganin ta yasa ta tsaya tana cewa . Na dauka kina kitchen muje kada lokaci ya 'kure ". Afeeyah dake duba abu a waya tace a'a ke kadai zaki nan da kwana hudu domin ina period idan yayana yaji sai yafi kwana goma baici abinci a gidan nan ba". "Wanne yayan naki"?. "Al'ameen mana ya Sadiq yana can gidansa da matarsa me zai kawo shi yin breakfast gidan nan. 'Yar dariya Fati tai tana zama kusa da ita daidai Al'ameen ya fito batare daya kalli inda suke ba yace. "Naji abinda kika ce " yana fadin haka ya fita a palon rufe baki Afeeyah tai". Fati dake kallonta tace to kinji abinda yace" mikewa tai suka shiga kitchen din dama saboda shi ne bazata taba kayan aiki ba. Al'ameen gidan Sadiq ya wuce a dinning ya same su Amir da Aisha sai fada suke kamar kaji ga driver yana jira zai kaisu makaranta. Zama yai yana hada tea bai kalli kowa ba cikin tsokana Sadiq yace sannu matashi ziyara ka kawo mana da safen nan kenan". Al'ameen dake shan tea yace no breakfast nazo yi kawai". "Ina na gidan ku" cewar Sadiq. "Yana nan kawai na fito naji yaran nan suna zance period shiyasa bazan iya cin abincin gidan ba". "To ai nima period din nake" Rukayya ta fada cikin boye dariyarta. Aje cup din Al'ameen yai tare da sauya fuska zaiyi magana sai kuma ya fasa yana mikewa ya fice. Da kallo suka bishi Sadiq ya girgiza kai yana cewa Al'ameen na rasa wanne kalar 'kyan'kyami gareshi ace mutum bazai ci abincin me period ba saboda me"?. Dariya Rukayya tai tunda haka kawai idan yayi aure basai ya dauki yar aiki ba saiya samo namiji". "Tab Al'ameen dinne zai dau namiji dan aiki a gidansa lallai har yanzu bakisan waye shiba bari na wuce hospital kada na makara da yawa". Al'ameen na zuwa gida ya soma sheka amai kamar ba gobe karshe ma zazzabi ne ya rufe shi amma duk da haka bai fasa ba domin Lagos zasu wuce yasa kayan army dinsa kawai ya tafi". Kwana uku da faruwar haka suna zaune shida Sadiq a palor ranar weekend cikin tsarguwa Sadiq ya kalli Al'ameen yana cewa". "Wai kai na tambaye ka mana murmushin me kake tun dazu"?. "Babu murmushin jin dadi ne kawai saboda na fahimta na gane wata gaskiya". "Gaskiya ta me kenan". "I am in love". Zaro ido Sadiq yai cikin mamakin furucin Al'ameen din jin zancen nasa kamar mafarki yace. "Da gaske kake ka samu wacce kake so"? Lallai zanso ganin yarinyar me sa'a data sace min zuciyar dan uwa na wacece ita a ina take ka sanar dani"?. "Ok zan fada maka amma ba yau ba saboda tsaro ita din tauraruwa ce me haske zuciya ta saida ita ina sonta so me tsanani ma". Sadiq da dadi ya gama cika shi cikin farin ciki yace mene sunan ta"?. Dan shiru Al'ameen yai kamar me tunani sai kuma yai murmushi yana kallon sadiq yace Zarah "' "Zarah yar waye" Sadiq ya tambaya. Al'ameen yace no zaka santa ba yanzu ba tana da daukar hankal........... Bai karasa ya dakata tare da kafe guri daya da ido muryarsa cikin wani yanayi yace" Zarah no one but you, I love u with all my body and heart bana iya hada ki da kowa". Kallon inda yake kallo Sadiq yai wanda har saida yadan zabura yana dafe Al'ameen cikin mamaki yace" wai dama Fati na nan gidan kake nufi"?'. "Eh ita bansan ya akai ko kuma yaushe bane haka nan rana daya na tashi naji na kamu da ciwon sonta kuma zan aureta ina da ra'ayin zama da ita zuciyata ta Abni ce amma yanzu ta Zarah ce . "Wow gaskiya na taya ka murna ka kuma yi dacen mace idan har ka aureta domin tana da tarbiyya. "Haka ne kyawawan dabi'unta ne suka rinjaye ni amma alfarmar da nake nema a gurin ka shine ya zama sirri tsakanin mu kada kowa ya sani". Murmushi Sadiq yai cikin tsokana yace babu wanda zan fadawa masoyi zasu sani da kansu". Bayan watanni uku Al'ameen na zaune a gaban su mami yana sauraron kiran da sukai masa'. Daddy yace" wato Aminullahi dama batu ne akan aure ka samu wacce kake sone"?. Kai Al'ameen ya girgiza a'a daddy babu". "To maminka ce tace ya kamata a hada ku aure kai da Zainab shin me kake gani hakan yayi maka". Caraf mami tace wanne irin yayi masa bashi zamu biye ba . Daddy da hankalinsa ke kan yanayin da Al'ameen ya shiga yace bake na tambaya ba saiya yarda idan bai amince ba dole abar batun". Kuka mami ta saka tana cewa shikenan nikam na kade na gama yawo alhaji meyasa kake min haka ne. Hade rai daddy yai yana cewa Al'ameen tashi kaje kada ka damu Allah ya baka wacce kake so ta maye maka gurbin waccan. "Amin daddy na gode" Al'ameen ya fada cikin jin dadi yana mikewa ya fita. Mami dake goge hawaye tace yanzu alhaji haka ak......'. Katseta daddy yai saurara Aisha bansan shashanci mubar maganar shiru mami tai tana sauke ajiyar zuciya takaici ya gama cika ta. Yau da gobe tafi karfin wasa daddy ya gaji da nacin mami ta hana shi sakat tabi ta hargitsa kanta ta hargitsa gidan saida ya amincewa abinda take so. Suna zaune Zainab ta fito cikin shiri zata fita tana kallonsu babu gaisuwa sa'kam-sa'kam tazo zata wuce. Cikin tsawa mami tace ke gidan ubanwa zakije da yammar nan. Dan tabe baki Zainab tai tana cewa bikin kawata ake zanje mata gurin event data gayyace. Mikewa tsaye mami tai koma ciki babu inda zakije". Zaro ido Zainab tai tana cewa tabdijan kinsan yadda muke da ita kuwa. Mami tace dan ubanki ni kike cewa tabdijan ina matsayin yayar mahaifiyarki zaki iya fadawa Binta. Zainab dake kad'a key din mota tace sosai ma saidai idan batai min abinda zance matan bane kinga ni kina bata min lokaci na wuce dan banga me hana ni naje ba . Tana fadin haka ta bude kofar palor ta fita tana wa'ka mami data bita da kallo tace jimin shegiyar yarinya zaki dawo ki same ni ne". Wani irin kallo daddy ya mata wato wannan yarinyar take son aurawa dansa yarinya mara tarbiyya amma bari ya kyaleta tayi gaban kanta babu ruwansa. Batare da Al'ameen ya sani ba domin bayanan aka karba masa auren Zainab a gurin mahaifinta ranar mami kamar ta zuba ruwa a 'kas tasha dan farin cikin har ta 'kagu lokacin biki yayi ta ganta tare da Al'ameen muradinta. Afeeyah kam iya damuwa tayi saidai ba yadda zatai har daddy ta samu da kukanta amma yace tayi hakuri matar mutum kabarinsa komai me wucewa ne. Al'ameen yasan da zancen domin Afeeyah ta kira shi a waya ta fada masa amma yai burus kamar abin bai dame shiba saidai bazai taba kallonta matsayin mata ba. Biki ya matso ya kankama sai shiri akeyi mutari ma da tawagarsa sukayo mota guda harda hajiya ranar farin ciki a gurin Fati ganin mahaifiyarta. Suna zaune a bangaren baki sai kalle-kalle suke mami tasa nana ta kai musu abinci da abin sha me kyau wanda basu taba ganin irin saba. Shigowa mami su gaisa da yake a cikin farin ciki take saita saki fuskarta har tana tambayarsu. "Sannun ku da zuwa hajiya fatan kunzo lafiya akace tun asuba kuka taho amma baku zo da wuri ba. Saude data yago cinyar kaza tace" wallahi nake fada miki da wuri muka taho 'yan ro santi ne suka tare mu". "Ro santi kuma"? Mami ta fada cikin rashin fahimta. Saude tace eh wallahi sune suka tare mu sunaiwa driven mu rashin arziki". Dariya Afeeyah tai sosai tana cewa wai yan road safety kike nufi"?. Mami tace" oh sune yan ro santi"? Gaskiya ne bari na dawo" ta fada tana mikewa domin zama dasu ya isheta . A ranar su Afeeyah suka je aka tsara musu lalle ita da Fati sunyi kyau sosai duk da basa tare da walwalar wacce ake neman cusawa Al'ameen din aurenta. Da yamma wajen magriba suna kitchen mami ta shigo dawowar ta kenan daga gidan hajiya Binta 'kanwar ta ganin basa part dinsu yasa tayo kitchen. Juyowa Fati tai jin motsi a bayansu ganin mami yasa tace sannu mami ina yini"?. Dan kallonta mami tai a yankwane kamar baza ta amsa ba cikin basarwa tace lafiya kune za ayi wa sannu". Kallonta ta mayar wajen Afeeyah wacce ke ta aikinta kamar batasan da zuwanta ba tace" Afeeyah idan kun gama kI sameni a part dina zan aike ki gidan uncle dinki Nasiru ki kaiwa Zainab wasu kaya tana can". Cikin kunar rai Afeeyah tace to mami". Juyawa mami tai tana fita a kitchen din sannan ta leko tana cewa" ke kuma ki shirya kayanki domin ranar da 'kyauyawa zasu koma tare zaku tafi aje can aci gaba da bikin agwagi kinji na fada miki" tafiyarta tai babu abinda ya dameta. Afeeyah data gama kulewa da lamarin mami tace wallahi bazan bari haka ta faru ba dole na fadawa daddy bari ya dawo gidan". Kai Fati ta girgiza a'a Afeeyah karki haka bana bukatar ace ta sanadiya ta mami da daddy sun samu matsala ki kyale kawai ni kaina nafi son na koma garin mu". "Meyasa saboda bakya bukatar zama damu ko"?. "A'a ba haka bane ". "Haka ne mana Fati tunda gashi kin fada da bakin ki". "Ba ina nufin haka ba ki yarda dani" Fati ta fada a damuwance. "Shikenan na yarda dake". . Page 25 to 26 Sai bayan sallar isha Afeeyah ta shirya tare da Fati suka tafi kaiwa Zainab sakon magungunan da mami ta basu . A palon aunty Maryam matar uncle Nasir suka samu Zainab tana tsakiyar kawayenta sai shan kamshi take tana nuna isa". 'Dan tsaki Afeeyah tai cikin takaici ta aje mata jakar maganin babu ko magana ta juya zasu tafi Zainab ta dakatar da ita". "Ke mene haka zaki aje min, kaya babu bayani waye ya aiko ki". Ba tare da Afeeyah ta juyo ba tace I think kina da ido saiki duba bom ne a ciki". Fati dake tsaye jikin kofar falo tana jiran Afeeyah tazo su tafi tace kaya ne mami ce tasa a kawo miki"' Cikin tsawa Zainab tace ke bakauyiya na sako dake ne 'bace min da gani"'. Wata kawarta dake kusa da ita tace wannan me kamar 'kanzon fa daga ina me take anan ". Cikin harara Zainab tace na tsane ta matuka yar talakawan kauye ce mabaraciya ce jahila ba kowa ba. Juyowa Afeeyah tai tana kallonsu tace kamar yadda su o'o masu ido ba dan ciki suke yan maula talakawan birni ba ki iya bakin ki ina daidai dake sakaryar mata.".". " oh da gaske? kai amma abin yayi kyau saiki daura niyya ni roba ce ina daidai da kugun kowa". Kiran mami Zainab tai ta fada mata abinda ba'ai ba suna zuwa gida mami ta rufe su da bala'i musamman Fati da batasan tabi Afeeyan ba. Harda aibata ta da mata gori iri iri Fati saida tai kukan bakin ciki yadda mami taci mata mutunci ta zagar mata iyaye akan abinda batasan ta aikata ba. Da zazzabi me zafi sosai Al'ameen ya kwana har akai kiran sallar asuba baiyi bacci ba saida yai sallah akan sallayar baccin ya washe shi . Haka ya wuni bai fito ba a ranar yana part dinshi duk da yana ganin kamar wasa ne ba aure za'a daura masa da tabarya ba. Saida lokaci yai yaga daddy ya shigo cikin shiri tare da muntari baban fati muryarsa da alamar yana cikin matukar damuwa yace. "Daddy wai dan Allah da gaske aure za'a daura min da wannan yarinyar? zainab fa"?. "Eh Al'ameen mamin ku naso kayi fatan hakan ne mafi alkhairi a rayuwar ka". "To amma daddy bana sonta wallahi ko kadan". "Na sani hakuri shi baya 'baci tashi ka shirya muna jiran ka kuma ka cire damuwar dake ranka". Kai kawai ya iya dagawa cikin dagulewar lissafi yayin da su daddy suka fita daga bedroom din nashi. Matar mutum kabarin shi haka Al'ameen yana ji yana gani daddy ya bada sadaki aka daura masa aure da Zainab kamar ya dora hannunsa aka yayi ta kuka😭 haka yaji zuciyarsa sai tafasa take. Abokansa sai gaisawa suke suna taya shi murna basu san dawar garin ba harda masu tsokanar sa saidai yai murmushin dole". Jin an rude guri ya sake dauka yasa zuciyar Al'ameen ta tsinke zuwa wani lokaci yaji ana ambaton an sake daura auren Al'ameen Mustapha Rich da amaryarsa Fatima Zarah Mukhtar😱🙊. Wani irin zaro ido yai yana kallon daddy wanda ya rike masa hannu bayan an kammala komai ya sashi a mota suka tafi gida. Zaunar dashi daddy yai cikin bada hakurin lallasi me tafe da nasiha yace". "Aminullahi kayi hakuri da abinda ya faru bawa baya tsallake kaddarar sa matar mutum kabarinsa tunda har kaga auren nan ya yuwu karkai fushi da maminka daga Allah ne shine ya baka Zainab ba tinsasawar mami bace . sannan ina mai sake baka hakurin akan rashin neman shawarar ka ko amincewar ka na sake daura maka wani auren da yar uwarka Zarah. Kai Al'ameen ya girgiza yana cewa karka damu daddy gata kayi min na gode kuma na karbi zabinka domin ka iya zabi me kyau". "Da gaske kayi farin ciki da aura maka Zarah danai". "Kwarai daddy domin ina sonta tun kafin yanzu kuma ina son samun ka na sanar dakai dama". Murmushi me kyau dady yai cikin nuna farin cikinsa ya rika jerowa Al'ameen addu'a mai kyau. Fati na zaune a bedroom tana kwalliya Afeeyah ta shigo tana guda har saitin kunnen Fati". Toshe kunne Fati tai tana cewa au kin sauko kenan harda gud'a? a lallai abu yayi kyau". Dariya Afeeyah tai tana kallonta tace dole nayi guda na dad'a domin ke nakewa". "Ni kuma meye hadina da guda a garin dame? Zainab zakije ki yaryarawa amma kya zo ki kama gaibu". "Waye ya fada miki wallahi ke nakewa domin kin zama amarya". "kamar ya? Amarya a ina?. "A gidan yaya Al'ameen yanzun nan na shiga part din dasu hajiya inda suka sauka naji daddy yana fada mata kiyi farin ciki Fati kin samu miji me kyan hali". Gaban Fati daya yanke ya fadi zuciyarta ta sauya burgu muryarta na rawa tace dan Allah Afeeyah da gaske kike ko wasa"?. "Haba Fati wallahi babu wasa a cikin abinda na fada miki da gaske an daura muku aure yanzu ke matar Al'ameen c......... Ai bata karasa jin abinda Afeeyan zatace ba da gudu ta mike tana fita a bedroom din. Kamar an jefota haka ta shiga part din su hajiya tana kuka hajiya dake goga goro tuni ta ajiye tana cewa. "Fatima lafiya kike kuka"?. Durkusawa Fati tai a gabanta cikin kuka tace hajiya dan Allah ki taimake ni wallahi bana son auren". Hajiya dake kallonta a kaikaice tace jimin sakarya au dama dalilin kukan kenan daga daura auren ko kwana daya ba'ai ba kike neman saki kul na hane ki kada na sake jin kin furta wata magana anan ranki zai baci". Kuka sosai Fati keyi jin abinda tace zata tashi ta tafi hajiyan ta hana ta". Kamar yadda Fati tai kuka haka mami ta rika tumuwa a kasa tana kururuwa an cuci dan ta sai rirrike ta mutane keyi. 💰DAN MILLIONAIRE💰 😘YUSRAHMS ABUBAKAR Page 27 to 28. Washe gari tun asuba Al'ameen yabar gidan ya nufi lagos mami bata sani ba iya daddy ne ya sani domin yaje shiga part din yaji kukanta da alama batai bacci ba sai kawai ya juya ya fita. Satin su hajiya uku suka tafi kauyensu batare da sun samu koda kallon arziki agun mami ba. Fati kuwa sai boyewa take saboda tsananin tsoron haduwarta da mami take kamar wacce zata dau ranta. Abin yana damun Afeeyah saidai ba yadda zatai a halin yanzu mami ta sake korar yar aiki mutum daya Fati ce ke aikin mutum uku a kitchen kamar jaka gashi Afeeyah bata isa ta taya taba ko a boye ne.. Satin Al'ameen uku ya dawo ranar mami da Zainab suna zaune a palor ya shigo tsallen murna Zainab ta daka tana mikewa da gudu taje zata rungume shi ya daga mata hannu. Mami dake kallon su tace amma da wannan shashashar baturiyar ce ko ba'a daura muku aure ba zata rungume ka ko". Dan hade rai yayi daidai Fati ta fito da cooler a hannunta batare data lura dasu ba . Yace" Zarah". A firgice ta juyo ganin wanda batai tsammani ba tsaye bayanta ya bude mata hannuwa alamar tazo gare shi yasa a rude ta nemi hanyar guduwa. Rikota yai batare da kawaici ko jin kunyar mami ba ya rungume ta tare da cewa I miss u fatan kina lafiya". Zaro ido tai jikinta na rawa dago fuskarta yai yana sakar mata kyakkyawan kiss me dumi a lips din ta sannan ya saketa. Tana jinta free ta ruga da gudu tana shigewa part dinsu mami da haushi ya gama cikata tace kayi asara dai wallahi ka rako maza duniya meye abin so a jikin wannan yarinyar "?. Bai bawa mami amsa ba sai Zainab daya kalla yana cewa kinga yadda tarbiyya take ya kamata ki koya nine na kirata amma neman guduwa take saboda kunya ke kuma saboda sakarci kin wani taho a guje zaki rungume ni kada ki kuskura ki sake ko a mafarki ne". Yana fadin haka ya wuce kuka Zainab tasa tana zama a gurin yayin da mami bakin ciki ya hana tace komai. Ganin ya dawo yasa ta fara shirye shirye a raka Zainab gidansa taro ta sake kira sosai na dangin ta Zainab taci wanka sukai mata rakiya". Fati kam daddy ne da kansa shida Afeeyah suka je gidan ya sake zaunar da ita ya mata nasiha sosai sannan suka taho. Al'ameen na zaune a palor idonsa a rufe yaji an shafa fuskarsa yana bude ido yaga Zainab zaune kusa dashi ta manne masa bai kula taba ya mayar da idonsa ya rufe. Cikin shagwaba tace wai Al'ameen me yasa ka fiya tauri kamar dutse ne ka sani nice matar ka wacce na dace dakai wannan bakauyiyar bata da wani amfani yar aikin muce kawai". Ganin bai kula taba yasa taci gaba Al'ameen yaufa ranar farin ciki ce a gare mu daren mune zamu raya shi please ka tashi" ta karasa maganar tana kwantar da kanta a kafadarsa. Tun tana jiran tashinsa har bacci ya dauke bai motsa ba sai wajen sha biyu ya barta a gurin ya mike yana shiga bedroom dinsa Fati kam tunda su Afeeyah suka tafi ta kwanta tana kuka daga nan bacci ya dauke ta. Washe gari da wuri ta tafi makaranta domin daddy ya bata driver Zainab kam tana palor inda Al'ameen ya barta tana sheka bacci". Lokacin data farka rana tayi sha biyu da rabi kallon palon take yi cikin takaici tare da jan tsaki kamar zatai kuka cikin masifa ta soma magana. "Amma wallahi Al'ameen yayi mugun raina min hankali wato anan ya barni na kwana ji yadda jikina yake min ciwo dan yaga ina sonsa shine zai wulakanta ni kome"?. Mikewa tai tabar palon bata daina maganganu ba tana shiga bedroom ta kira mami da kukan ta tafada mata karya son ranta. Wanda Al'ameen na zuwa maimaakon mami ta karbe shi da fara'a daya gaida ita bata amsa ba sai hade rai datai tana jefa masa tambaya. "Dakyau Al'ameen ka kyauta wato dama baiwa nakai maka ko yanzu kai a ganin ka kayi daidai kenan"?. "Ka kulle kofar bedroom kace Zainab bataje dashi daga gidan uban taba sai a palor ta kwana ". "Da safe ka watsa mata ruwan fridge mai sanyi wai hutu dama taje gidan ka prisoner dinka ne babu maganar yar aiki hatta wankin motar ka itace zatai saboda dama abinda ya dace da ita kenan". "Humm lallai kam ina ita wannan dod'addiyar jahilar yar kauyen meye take a gidan dama aiki ne ya dace da ita". "Wato ka fifita sashin mahaifinka da zabinsa akan na mahaifiyar ka ko"?. Mamaki ne sosai ya kama Al'ameen jin sharrin da Zainab ta 'kuga masa alhali tunda aka kaita magana bata hada su dashi ba". Jin mami tace dakai fa nake tunanin me kake? Wato saboda ka mata gargadin karta fada min shine ka kasa ban, amsa ko"?. Kallon ta yake kamar sa na sauyawa zuwa yanayi na fushi yace wai mami ita Zainab dince tace na fada mata haka"?. "Eh ko kana son kace tai maka karya ne da kukanta ta kira ni dazu". "Ok shikenan zan tafi ki huta lafiya mami". "Ina zakaje baka bani amsa ba "?. "Ina zuwa mami dole sai mun zauna dan bazan dauki rainin yarinyar nan ba". Tun kafin mami tai magana ya fita a palor ransa a bace. Zainab na palor zaune tana danne danne a waya kamar walkiya haka ta ganshi cikin palon sakamakon tasan karyar data shirga masa yasa da sauri ta mike zata gudu". Wata irin damka ya mata wanda cikin azabar radadin da hannunta ke mata ta kwalla kara tana sakin wayarta". Muryarsa kausashe yace" ki tsaya iya matsayin ki idan tsautsayi yasa kika sake kuskuren fada wa mami abinda bansan dashi ba saina kusa kashe ki wawuya". Kuka ta saki domin rikon dayai mata bana wasa bane hannunta yayi jawur ya tara jini yafi awa rike da ita saida ya tabbatar ta wahala ya saketa cikin bacin rai yabar gurin. Kuka tai sosai domin hannunta ya kumbura amma a ranta yanzu ta fara indai bakanta masa ne a cewarta tunda ya nuna baya sonta". Hanyoyi da dama ta soma bi na jan hankali amma kullum labarin daya ne ta gaji da zama haka amma tasa a ranta zata fito ta masa zanga-zanga. Wata daya dayin bikin nasu amma babu abinda ya sauya kullum itace a 'kar. Tana tsaye da bayan sallar magriba a gaban dinning bayan yar aiki ta gama dinner ya shigo a gajiye sosai yanayinsa zai fada maka haka. Tararsa tai tana kashe murya tace" sannu my hero gaskiya yau ka gaji da yawa Al'ameen muje na maka tausa da wanka ga dinner na jiranka". Ta gefen ta ya wuce yana cewa bana bukata". Tsaki taja mai karfi wanda ya dakatar da tafiyar da yake yi ganin ya tsaya a dake tace". "Ahaf dan ina tausaya maka ma shine zaka nemi tozarta ni karka manta ba wani abin arziki kake bani ba ". "Karka manta akwai gwarazan maza a gabanka soja suna kawai kaci domin baka da wani amfani gurin mace saidai ka kalle ta da ido". "Tunda kai famkon namiji ne babu wani katabus da kake dashi kai muna maza sunan ka mata maza domin babu wani abu da zakai tunkaho dashi famko kawai". Wata irin juyowa yai da dukkan karfinsa wanda tasa ta kwasa da gudu ta shige part dinta . "Famkon namiji"? Ya fada cikin mamaki wato kallon da take min kenan lallai zan nuna miki iyakar rashin kunyar ki" juyawa yai yana shiga part dinsa. Misalin karfe tara na dare Zainab na kwance akan gado taji an bamko mata kofa da karfi cikin tsoro ta zabura tana mikewa ta diro daga kan gadon. Ganin wanda batai zato ba yasa ta sake rudewa ga wani yanayi da tsantar fushi da take hangowa a cikin idanun shi. Jikin tane ya soma rawa ta kankame guri daya cikin tashin hankalin meya kawo shi. Har inda take yaje yana sa hannu a gaban rigar baccinta da dukkan karfinsa ya yaga ta. Yana mata wani kallo me ma'anoni da nuna ta shirya famko ya kawo mata ziyara". Tana kokarin guduwa ya cafko ta yana dora ta akan bed din ya bita ya danne domin yayi alkawari yau saita gane bata da wayo. Fati na kwance a daki bacci ya fara daukarta sama-sama take jin ihu da kuka tayi zaton mafarki take sai gashi kamar ana matso mata da kukan kunnen ta. Tashi zaune tai cikin magagin bacci jin muryar zainab tana a taimake ta zata mutu yasa ta mike da sauri tana fita. Har part din zainab din ta shiga cakk ta tsaya tare da zaro ido tana dafe kirji zuciyarta na bugawa jin zainab na cewa". "Wayyo Allah na shiga uku na lalace Al'ameen zaka kashe ni na tuba kayi hakuri wayyo wayyo umma mami kuzo ku taimaka min zai illata ni ". Muryarta harta dashe kamar me mura bata fita sosai jikin Fati na shaking ta juyo har tana tuntube ta fita daga part din. Koda ta koma bedroom dinta kasa kwanciya tai balle ta runtsa saboda fargaba gani take kamar idan ya rabu da Zainab gurinta zaiyo". Zazzabi ne ya rufe ta da gari ya waye tana zaune bakin gado tana tunani Al'ameen ya shigo ganinsa yasa ta mike zumbur tana jada baya. Muryarta na karkarwa tace kayi hakuri dan Allah bani da lafiya". Bai daina binta ba harta kure bango sannan ta tsaya tana yarfa hannu kamar wacce ta yanke". Da dan mamaki a fuskarsa ya karasa inda take yana daukota ya dawo da ita bakin gadon cikin alamar tambaya yace. "Lafiya hakurin me kike bani"?. Kuka Fati ta fashe dashi tana cewa" dan Allah kar kamin abinda kaiwa Zainab". Sai sannan ya gane manufar ta murmushi yai yana rike hannuwan ta yace . "Zarahh amfanin zunubi romo babu 'kira mezai ci gawayi ita ma laifi tamin babu abinda zanyi miki ki kwantar da hankalin ki ke ta musamman ce kinfi karfin yi anan". Dan sauke ajiyar zuciya tai jin ya dora hannunsa akan fuskarta yana goge mata hawaye. Kallon cikin idonta dake cike da tsoro yai yana cewa" shikenan karki damu komai ya wuce, kinsha magani"?. Kaita daga masa". Kwantar da ita yai yana rufa mata bargo bai sake magana ba ya sakar mata kiss a saman lips dinta sannan ya fita da kallo ta bishi tana sauke ajiyar zuciya. Al'ameen ba rabuwa yai da Zainab ba saida yai mugun horata na sati tayi kuka tayi ihu ta kira agaji amma babu mai taimako tsabar azabar data sha ko tafiya ta gagare ta. Fati da ta daina ganin wulgin Zainab din yasa ta yi tunanin ko bata gidan amma data tambayi yar aiki sai tace batajin dadi tana part dinta. Breakfast ta hada a madaidaicin kyakkyawan tire ta shiga part dinta daidai ta fito daga toilet alamar wanka tayo sai bin bango take dakyar tana cije baki cikin dabara take daga kafarta. Ganin Fati tsaye yasa ta doka mata wata muguwar harara tana cewa". "Uban me ya kawo ki fita min a daki". Aje tiren Fati tai kamar baza tai magana ba sai kuma tace yaya jikin naki"?. A fusace Zainab tace jikin uwar wa munafika dama ce miki akai bani da lafiya"?. Dan murmushi Fati tai tana kallonta tace" ke kuwa kike rashin lafiya ga breakfast nan na kawo miki". "Uban breakfast malama get lost wallahi ki shiga hankalinki zan miki mugun rashin mutunci". Dariya Fati tai tana kallonta tace" ah haba dan gurgu da wacce kafar"?. Iya cika Zainab ta gama 'kulewa ji take inama zata iya kama Fati dasai ta dirzata son ranta yau din nan". Juyawa Fati tai zata fita tace to Allah ya sauwake nina wuce". "Kima tsaya da na nuna miki iyakar ki"'. "Rufe mata kofa Fati tai tana cewa idan ma na tsaya babu abinda zaki iya yi min". Page 29 to 30. Kwana biyu Zainab data samu lafiya ta warke haka ta hada kayan ta cikin akwati ta koma gidan mami da kukanta. Mami ranta ya 'baci dan haka tace Zainab tayi zamanta baza ta koma ba sai Al'ameen yazo ya bata hakuri. Shiru tun suna zuba ido har mami ta gaji ta kira shi a waya cewa yazo tana nemansa. Yana zuwa ta rufe shi da fada dakyau Al'ameen nagode da kake nuna ban isa dakai ba ina matsayin mahaifiyarka wato kana son zabin uban ka amma ka'ki nawa ko". Kamar baisan akan me take magana ba yace" mami meya faru ne". "Oh bakasan meka aikata ba kenan yanzu Al'ameen Zainab ba matar ka bace amma kai mata fayde saboda rashin hankali". "Amm mami nine tace nai mata fayde da yaushe wato dama shine dalilin tahowa gurin ki don tamin sharri"?. "Kana nufin karya ta maka"?. "Umh ban san komai ba". "Shikenan duk da haka bazata koma ba sai kazo biko". Murmushi yai yana mikewa yace to mami nizan tafi sai wata ran maybe nan da wata biyar". Da kallo ta bishi tana cewa idan ma shekara biyar zakai duk inda kaje duk shawagin da zakai a duniya karshe dai gida zaka dawo". Dakatawa yai batare daya juyo ba yace" albarkar ki da addu'ar ki nake nema dan zan dawo miki da kyakkyawar tsaraba🙈". Jin haka yasa mami washe baki ciki farin ciki tace Allah sarki Aminu na Allah ya tsare min kai a duk inda kake sannan tsarabar kayo min me yawa saboda yan uwa😱😀". , Fuskarsa har lokacin da murmushi annuri ya bayyana yace. "Karki damu mami wanda ba familin mu bama saiya ga wannan tsaraba kuma fatana tsarabar ta amfanar da al-umma"😁. Sosai mami ta zage ta masa addu'a har dariya ta bashi yasan dazai fada mata manufarsa baza tace 'kala ba kila fitina cema zata tashi". Kwana biyu a tsakani Al'ameen suka bar kasar shida Fati zuwa bangkok domin zaiyi wani uziri acan tare da abokinsa Aliyu suka tafi shima da matar sa Ummul-khairi (maman Affan). Fati taji dadi tafiyar da sukai musamman da suka hadu da maman Affan mace mai kirki babu ruwanta da girman kai duk da kuwa ta girmewa Fatin". A wasu kyawawan estate masu kyau da tsaruwa suka sauka da yake sun debo gajiya sunayin wanka da sallah a daddafe fati taci abinci saboda bacci hakan ma saida Al'ameen ya matsa mata. Washe gari sakamakon ba kowa sun tafi gurin aiki yasa maman Affan ta shigo gurin Fati dan duba lafiyarta. A makeken falon ta sameta zaune tana kallon Tv ganin su yasa cikin murna ta mike tana karbar Affan dan shekara daya da rabi. Cikin fara'a ta kalli maman Affan tana cewa" sannun ku da zuwa maman Affan ga guri zauna gaskiya naji dadi". Maman Affan dake murmushi tace karki damu ai mun zama yan uwa tamkar 'kanwa haka na dauke ki". "Na gode maman Affan kuma nima na dauke kI matsayin aunty na na yarda dake zan iya fada miki dukkan matsala". Kai maman Affan ta jinjina tana cewa gaskiya Zarah kinyi dacen miji Al'ameen mutumin kirki ne na sanshi tun kafin na auri Daddyn Affan". "Amma fa saidai sojoji suna wuyar sha'ani sai kina hakuri kila auren ku baifi shekara ba ko"?. Kai Fati ta girgiza" a'a banfi wata uku bama". Zaro ido maman Affan tai tace tab kice kune a ruwa yanzu kuke cin amarcin ku honey moon kuka zo ba aiki ba". Wanne amarci ana zaune lafiya". "Amarci wanda kika sani saidai ina miki fatan Allah yasa Al'ameen ba irin daddyn Affan bane dan har yanzu ina shan wahala a hannunshi gashi dai na haihu amma wani lokacin sai nayi kuka nake samu ya rabu dani". Cikin fargaba Fati ke kallon ta domin ta fahimci me maman Affan din ke nufi lokaci guda ta rude taji dama bata biyo shiba ashe Zainab bada gangan take kuka da kiran ta shiga uku ba. Jaka maman Affan ta bude tana dauko wata kwalba ta mika mata tana cewa" amma kiyi amfani da wannan yana da muhimmanci sosai". Kai Fati ta girgiza. Cikin mamaki maman Affan tace meyasa"?. Shiru tai ta kasa bata amsa cikin karantar yanayin ta tace" to ko baki tare ba sai yanzu da zaku taho akai miki rakiya domin a yadda naga kin rude haka ya tabbatar min dake sabuwa ce". "A'a na juma a gidansa saidai kowa yana part dinsa kuma bai cika zaman gidan ba". "To kinga ma yanzu ne zaku shakata". Kamar Fati zatai kuka tace ki barshi kawai Allah ni tsoro nake ji". "Tsoro dai? Ba matsala amshi kowa da haka ya fara bafa wani abu ne na tashin hankali ba". Karba Fati tai jiki a sanyaye murmushi maman Affan tai tana kallonta tace babu komai fa idan kika saba ki kwantar da hankalin ki". Anan maman Affan ta wuni tana baiwa Fati shawarwari wadanda suka kamata sai bayan sallar magriba tayi mata sallama ta tafi". Haka Fati ta zauna shiru jikin ta duk yayi sanyi har Al'ameen ya dawo kamar mara laka a jikin ta haka take komai". Shima yaga sauyin yanayi a tare da ita kamar akwai abinda ke damunta dan haka ya riko hannunta yana zaunar da ita kusa dashi". Muryarsa a nutse ya dago fuskar ta yana kallon cikin idonta yace" Zarah baki da lafiya ne". Kaita girgiza zatai magana saiga hawaye cikin mamaki ya d'age gira" what"?. Karka min abinda kaiwa Zainab ka mayar dani gida" shine abinda ta fada muryarta na makalewa. Goge mata hawayen yai yana murmushi yace" wato kina matukar tsoron abin nan idan na fahimce ki babu matsala amma ki sani ke matar soja ce domin saki ki zama jaruma dole saina cire miki tsoron nan". Kallonshi tai cikin alamar tambaya tace "taya kenan "?. "Ta yadda akeyi jarumtacciya nake so na maida ke ki zama kin daina jin tsoro". Dan hadiye yawu tai har yana sarketa tace" kullum kana gurin aiki yaushe zaka mayar dani jarumar"?. "Karki damu wannan shi yafi komai sauki zan fada miki sai anjima". Cikin yar shagwaba tace" nidai a'a ka fada min yaushe zaka mayar dani jaruma na fara shiri". Mikewa yai yana daukar ta batare daya bata amsa ba saida ya kaita har bedroom ya kwantar da ita akan bed fuskarsa daf data ta muryarsa can 'kasa yace. "Tunda so kike ki sani yanzu ma kuwa saiki dau shiri". Bata gama fahimtar saba taji ya dora bakinshi akan nan ya kuma zuge zip din doguwar rigarta yana sa hannunsa a gadon bayanta yana shafawa da tafiya dashi cikin salo. Zaro ido tai jikin ta yadau rawa kaf kaf kaf kamar me farfadiya kuka ta fara tun kafin ayi komai. A hankali yake binta dan dauke mata hankali harya yi nasara ta fara karbar sakon da yake bata. Batasan sanda rigarta ta koma gefe ba idonta na rufe kawai numfashi take saukewa. Shiga jikinsa take sosai wanda da alama batasan tana yi ba ganin ya samu abinda yake so gashi ta kawo yasa yai addu'a ya fara shigarta a hankali. Farko yabi a sannu dayai rabi shima yaji kawai fa a tafi danna joystick dinsa yai cikin hq dinta". Lokacin guda ta saki kara a gigice tana kankameshi cikin azaba ta fashe da kuka tana mishi magiya". Tab su Al'ameen kam anyi nisa ba'a jin kira baisan tanayi ba balle ya sassauta mata. Sha'awarsa nada karfi amma saida yaji yayi full sannan ya rabu da ita wanda dakyar take iya jawo numfashin ta". Rungumeta yai a jikinsa yana kallon fuskarta dake jike shakaf da hawaye yace" Zarah". Kasa amsawa tai sai bude ido datai tadan kalleshi ganin shima ita yake kallo yasa da sauri ta rufe idonta. "Zarah bude idonki". Kaita girgiza yace meyasa"? Baki son gani na ko na miki laifi"?. Nan kai ta sake girgizawa yasan bazatai magana ba dan haka ya gyara mata kwanciya a jikinshi yana dan shafa mata gashin kanta cikin salon lallashi har bacci ya dauke ta. Yaso tashinta tai wanka amma ya 'kyaleta saida asuba shima da kuka dakyar yaa samu ta shiga ruwan zafin sai raki take masa. Bayan sunyi sallah bacci suka koma sai sha biyu da yake ranar Al'ameen baida aiki sai bai fita ko'ina ba ya wuni yana kula da shagwababbiyarsa". Da dare fur kin yarda tai ta kwanta saida lallami da magana me dadi yaja hankalinta tace jikinta ciwo yake". Kwantar da ita yai yana mata tausa sannu-sannu yana binta ga'ba-ga'ba yadda zata ware daga nan ya sauya ra'ayi. Hankalin Fati ya mugun tashi ganin zai sake maimaita abin jiya da iya karfinta take so kwacewa amma ta kasa katabus. Haka ya more dadin shi wanda yau daya samu hanya sosai yafi jiya zaucewa Fati kam dama ta sallama wuya tasa tayi gajeran suma sannan dole azaba ta farfado da ita. Lallai ta jinjinawa Zainab ashe bada banza ba itama daya bita a sannu tasha ba'kar wuya balle Zainab dayai nufin horata". Mami tayi tunanin da wasa Al'ameen yake tafiyarsa amma taji shiru wai mushiriki yaci shirwa taso basarwa amma ta kasa hakuri ta tambayi daddy. "Ni kuwa alhaji kuna waya da Al'ameen"?. "Eh munayi ke bakwayi"?. "Kenan da gaske dama yake kasar zai bari". "Baiyi miki sallama bane kome". A'a yace min zaiyi tafiya na dauka fada kawai yake". "Ba fada kawai yake ba sunyi tafiya". Cikin alamar tambaya mami tace sunyi tafiya kuma kamarya shida waye"?. Kai tsaye daddy yace dawa zaiyi tafiya kuwa bayan matarsa". A zabure mami ta mike tana cewa" wai da Fatima suka tafi"?. "To Aisha waye matarsa bayan ita". Mami har tana sarkewa tace" shakka babu Al'ameen yana nuna min kamar ba nice na haife shiba wato ita kuma Zainab meye matsayinta ya sata a kwandan shara kenan"?. "A'a ba shine ya sata a kwandon shara ba kece tunda bakya son ganin laifin ta". Hade rai mami tai kenan alhaji yanzu bakaga laifin saba akan abinda yai sai nawa ya debi wata sakaryar yarinya ya fita da ita har wata kasar". Mikewa daddy yai yana cewa" Aisha kina da abin mamaki sakarci aka kai ki kalli har jikanu kike dasu amma bakida tunani kin kasa gane meya dace baza ki iya bambance abun da yake fari da wanda ya kasance ba'ki ba kibi a sannu kafin nadau mataki". Cikin takaici mami ke kallon daddy dajin zafin maganganun daya fada mata jitai wata irin 'kiyayyar fati ta sake shiga zuciyarta domin dalilinta daddy ke mata haka. Bangkok Da yamma lis suna zaune a wani gurin shakatawa yayin dasu Al'ameen ke gefe suna duba wasu muhimman takardu. Maman Affan ta kalli Fati datai shiru tana dan ta'bo ta dagowa Fati tai tana sauke ajiyar zuciya". "Meke damun kine naga tunda muka zo bakya walwala ga abin sha nan an aje miki har sanyinsa ya huce". Dakewa Fati tai tace babu komai". "Babu komai kika zubawa guri daya ido waima na tambaye kI kinyi amfani da wannan abin kwalbar dana baki"?. Kai Fati ta girgiza tace a'a maman Affan ina jin tsoro a haka ma yaya nake karewa wallahi kina da gaskiya maman Affan ba kuka ba yar karamar mutuwa ma sai kayi". Dariya maman Affan tai tana kallonta tace" yayi kyau kina jina babu wani cutarwa game da wannan magani ki jarraba nina fada miki saikin tambaye ni inda ake saidawa". "To shikenan maman Affan zan gwada na gode". "Karki samu damuwa ke yar uwa tace". Dan kasa tai da murya tana mata rad'a su Haidar da suka karaso ya kalli maman Affan yana cewa" wacce gulman ake gutsira mata". Dagowa maman Affan tai da murmushi a fuskarta tace sirri ne tsakanin mu". "Yayi sarkin za'ki lokaci yayi". ganin sun gama aikin ga magriba ta rufa yasa suma suka mike suna fita daga waje mota daya suka hau suka nufi gida . Kamar yadda maman Affan ta bata shawara tare da karfafa mata gwiwa haka tayi bayan tai wanka ta shafe dukkan jikinta dashi. Aikam dai ranar taji sauyi sosai kuma taji dadi round biyu yai da dare da asuba ma haka amma bataji ta kosa ba. Shi kanshi yaji canji kuma yayi mamakin ta ko lokacin da suka kasance a palor tare tana kwance a jikinsa yace. "Zarah kinban mamaki kodai har na mayar dake jarumar ne fada min mene sirrin jiya naji kin dage sosai kin karbi gayyata ta"?. Rufe ido Fati tai cikin kunya tana rike hannunsa tace babu komai". "Babu komai amma kika sani na zauce"?. "Nidai babu komai ka yarda". "Na yarda amma fa naga wani abu cikin kwalba kuma kamshin iri daya ne da kamshin jikin ki"?. "To ai maman Affan ce ta bani". "Oh na canka daidai kenan? Please yau ma kisa ina so". Adan tsorace ta kalleshi gira ya dauke yana cewa" yes yauma zamu kasance tare har asuba babu maganan bacci". "Kai nidai bazan iya ba". "Bazaki iyaba kin taba ganin wanda kake so kayi nisa dashi"?. Kallon mamaki ta mishi har tana tsayar da idonta cikin nashi tace" so"?. "Eh so" ya bata amsa. "To amma son wa". Rike fuskarta yai yana dora lips dinsa saman nata ya bata burkitaccen kiss me dumi wanda yasa ta dauke numfashi yace. "son wa kuwa Zarah ki gode wa Allah domin kin maye min gurbin Abni a zuciya ta ina sonki". Rungume shi Fati tai tana kuka tace" Allah ya mata rahma amma kafi karfin yin soyayya dani". "Waye ya fada miki kece kika dace dani duk duniya bani da tamkar ki kina da babban matsayi a zuciya ta tun kafin na fahimci cewa sonki nake". "But do u luv me". Kara kankame shi tai cikin farin ciki har yana jin sautin murmushinta akan idonsa beauty point din ya lotsa tace. "Nima ina sonka son gaske bana hada ka da kowa kaike da mukullin zuciya ta fatana mu kasance tare har abada". "Zamu kasance tare Zarah kece numfashi". Dagowa tai tana kallonsa ranta fari tas zuciyarta cike dajin dadi fuskarta da annuri. Zatai magana ya katseta da cewa" muje ina son mu gana🙈". Fuska ta shagwabe tana komawa kalar tausayi tace" Allah nina gaji kafa na ciwo take". "Wanda kake so baka gajiya dashi Zarah dan haka muje na cewa mami zan koma mata da tsaraba kinga dole na dage". Yana fadin haka ya dauketa yana barin palon cikin rad'a ya mata magana a kunne wacce tasa da sauri ta kifa fuskarta a kirjinshi tana dariya kasa kasa. 👉 Mrs Al'ameen Ahmad ce. 🌼🌹🌼🌹🌼🌹🌼🌹🌼🌹🌼🌹 Page 32 to 32. Kamar yadda Al'ameen yace wa mami saida suka shafe tsawon wata takwas harda sati biyu a bangkok saidai sunje london ziyara gurin iyayen Abni". Wanda suka samu kyakkyawar tarba kamar su maida su ciki haka suke nuna musu kauna da basu kulawa har ranar da zasu dawo Nigeria. A ranar da suka dawo mami ta sako Zainab gaba da akwatinta ta rakota tayi sa'a ta samu Al'ameen a gida haka ta balbale shi da masifa kamar zata rufeshi da duka. Sannan ta juya kan Fati dake gefe tai mata zagi na tsamar nama harda kakannu saida suka samu rabonsu. Fati tayi kuka tayi bakin ciki batasan me taiwa mami ba da bata kaunarta sam". Kwanan su goma da dawowa Fati tana part dinta a kwance bata da lafiya Zainab dake palor zaune tana jiran yar aiki ta gama gyara dinning tabar gurin. Da sauri ta mike tana waige-waige ta nufi dinnig din tare da bude cooler ta fara zuba wani abu. Al'ameen na tsaye a bakin kofar palon yana kallonta saida ta juya zata tafi ta ganshi cikin razana da rashin gaskiya tace. "Harka dawo sannu muje kai wanka ga abinci na jiranka da kaina na shiga kitchen na shirya maka shi". Karasowa yai har inda take yana rike hannunta ya mayar da ita gurin dinning din yace. "Me kika zuba a ciki". muryarta na rawa tace mezan zuba kawai gyara murfin coolan nai saboda karta huce. Bude wa yai tare dasa mata spoon a cikin abincin ransa a hade sosai yace. "Eat". Zaro ido tai jikin na kakkarwa ta soma jada baya ganin tana shirin guduwa yasa ya cafko ta yana matseta sosai a jikinsa ya debo abincin ya danna mata da karfe dole saida ta hadiye. Ihu ta kurma domin tasan guba ta zuba a ciki bai damu ba ya sake deba ya cusa mata saida ya bata spoon biyar sannan ya ture ta daga jikinsa yana mikewa ya barta a gurin. Da sauri ta mike tana shiga part dinta ta wuce toilet ta fara amai cikin galabaita ta fito dakyar ta iya lalibo number mami ta kirata tana kuka". Mami na dagawa Zainab tace mami please karna mutu kizo ki kaini asibiti yanz........... Bata karasa tari ya rufe ta sakin wayar tai tana durkusawa a gurin. Mami dake cewa hello zainab kina jina meke damunki ina Al'ameen din"?. Jin shiru ba amsa yasa mami kallon wayar ganin ta katse a firgice ta sa'bi mayafi tana fita taiwa driver magana cikin gaggawa ta shiga mota suka tafi. Lokacin da mami ta samu Zainab cikin mugun hali kwance farin abu na fita a bakinta. Salati mami keyi ta dagota da sauri amma tai luuu ta koma ihu mami tai tana kuka ta ciccibe ta suka fita". Saka ta a mota tai suka wuce asibitin Sadiq domin ya dubata Sadiq yayi mamaki abinda ya gani tattare da Zainab din. Wanda bayan ya fito daga dakin da aka kwantar da ita ya koma office dinshi inda mami ke zaune tana jiransa. Ganin ya shigo da sauri ta mike tana tambayarsa "Abbakar yaya jikin nata meke damubta"?. Zama yai cikin nazari yasan Fati bazata zuba mata guba ba balle Al'ameen shine abinda yake bashi mamaki toshi yanzu mezai cewa Mami na damun Zainab?. Katse masa tunanin da yake mami tai da fadin "Sadiq ka bani amsa mana, ko wani abune ya sameta"?. Kai Sadiq ya girgiza yana cewa "a'a ki kwantar da hankalinki na mata aiki zata samu lafiya da yardar Allah saidai ban gama binciken abinda ke damunta ba". "To amma Sadiq wannan farin abun dake fita a bakinta fa". "Eh mami harda shi zan bincika idan na tattara bayanan zan fada miki". "Shikenan to Allah ya bata lafiya". Afeeyah kam najin batun tasan akwai wata a kasa gashi Al'ameen yace ta dawo gidansa gurin Fati domin har lokacin bata gama warwarewa ba. Sadiq suna zaune tare da Al'ameen yake tambayarsa "kai Al'ameen ya akai Zainab taci guba a cikin abinci ko taje wani gurin ne"?. Kallon Sadiq Al'ameen yai "no ko daya a gidan taci". Zaro ido Sadiq yai to waye yasa mata kenan"?. "Babu kowa ita ta zubawa kanta". "Kamar ya bayan tasan abin cutar da ita zaiyi zata ci please Al'ameen dan Allah ka fada min gaskiya kodai kaine ka zuba mata"?. "Haba Sadiq akan me zan bata guba taci dan kawai bana sonta kka yarda itace tasa abarta da kanta". Sadiq yace taya kenan wanne tabbaci kake dashi ko ka ganta lokacin data zuba din"?. "Kwarai ina tsaye a kofar falo ta zuba data juyo ta ganni kasan me tace min"?. Kai Sadiq ya girgiza. Al'ameen yaci gaba "wai sai tace ga abinci ta gama shirya min dama danni ta shiga kitchen da kanta ta dafa shI saboda ni". "dana tambayeta me ta saka a cikin abincin sai tace babu da tana da gaskiya da nace taci sai taci amma jikinta yana rawa taso guduwa". "Ni kuma na riketa na dura mata spoon biyar kaga nine take shirin kashewa dan haka bazan mata uziri ba"'. Kai Sadiq ya jinjina lallai tayi kuskure amma kasan mami baza ta yarda ba "?. "Na sani". Sadiq yace to kaje ka dubata kafin ka wuce". Mikewa Al'ameen yai yanaa kallon Sadiq yace "Bana bukatar ganinta Sadiq ni dama gurinka nazo muyi sallama dan haka na tafi". Mikewa shima Sadiq din yai yana cewa to Fatin kuma fa bakace batajin dadi ba"?. "Eh Afeeyah tana gurinta". "Ok muje na maka rakiya Allah ya kiyaye saika dawo". "Amin Sadiq dan Allah lokaci zuwa lokaci ka rika zuwa kana duba Zarah". "Ok ba damuwa daddyn baby za'ai yadda kace" fita sukai ya masa rakiya sannan ya dawo". Mami data koma gida haka takai karar Al'ameen gurin daddy domin ita batasan ma baya gari ba. "Yanzu alhaji tsakani da allah abinda Al'ameen yake ya kyauta kenan ka duba yarinyar Zainab ba ta da lafiya kullum ina asibitin amma bai taba lekowa ya duba jikin taba". Wani kallo Alhaji Mustapha ya mata domin yasan komai tun ranar da abun ya faru Al'ameen ya kirashi ya sanar dashi. Ganin irin kallon da yake mata kuma bai tanka zancenta ba taji gaba. "Gaskiya alhaji kanada abin mamaki nace maka ga abinda ya aikata amma saikai burus dani, kana min wannan kallon kamar zaka dake ni saboda na tabo dan lelenka kodan bakason a fadi laifinsa tunda lu'u lu'un zuciyar kane"?.. "Aisha to me kikeso nace meye nawa a ciki kece silar gurbacewar komai kuma laifin kine tunda ke kika 'kulla komai ni babu ruwana a cikin wannan al'amarin". "Abinda zaka ce kenan alhaji a tunani na zakai masa fada ka nuna fushinka ai Zainab dince ta dace dashi shiyasa na dage ya aureta domin auren 'kwarya tabi 'kwarya na musu". Kai daddy ya jinjina yace" to dakyau ai kinyi musu ga sakamako nan na biyo baya kiyi addu'a abin ya tsaya iya haka". Mikewa yai zaibar gurin da gudu mami tasha gabansa tana huci tace" wallahi alhaji nagaji bazan yarda ba domin yanzu kam na gane kaine ke shiga tsakaninsu ka hana su zaman lafiya duk wata kitimurmura da fitina kaine kake shiryata". Cikin tsananun mamaki daddy ke kallon tsaurin idon mami dake fada masa duk abinda yazo bakinta". Ganin tana shirin sake magana ya daka mata tsawa wanda a firgice ta matsa daga gabansa domin iya tsahon rayuwarta dashi bai taba mata tsawa ba saiyau". Cikin bacin rai ya nunata da yatsa yana cewa" babu shakka Aisha yau kin sake tabbatar min da baki da tunani kuma kinsamu gushewar hankali kamar ki ace har yar bakida hankali kinyi asara bari kiji bazan dau wannan shashancin naki ba ina mai baki shawara ki gyara bar ganin mun dau shekaru tare ga zuri'a hakan bazai hana idan kinyi ba daidai ba nadau mataki a kanki". Mami datai tsalle ta koma gefe guda tun sanda ya mata tsawa jin abinda yake cewa yasa ta dafe kirji tana kallon wani irin bacin rai a fuskarsa wanda bata taba gani ba tace. A "Wayyo Allah ni Aisha wannan wacce irin kaddara ce ta sameni alhaji da muna zaune lafiya tun daga lokacin da Al'ameen yazo da bidi'ar sa ya nuna yana son auren baturiyar nan alhaji ka fara juya min baya". "Amma banyi dace ba haihuwar Al'ameen batai min rana ba nayi asarar haihuw...'..... Katse ta daddy yai jin tana neman dorawa Al'ameen alkaba'i yace "Aisha idan kika karasa yau saina baki mamaki dan zanyi abinda bakya zato". Kuka mami keyi na bakin ciki da kuma rudewar abinda daddyn yace tana zama tace" na shiga uku na lalace". Jinjina mata kai dady yai alamar batai karya ba ta fadi gaskiya yace" zadai ki shiga ukun ki lalace din kamar yadda kika fada idan har baki gyara halin kiba" bar mata palon yai ya shiga part dinsa. Page 33 to 34. Sati uku da faruwar haka aka sallamo Zainab daga asibiti mami taci gaba da kula da ita a gida har ta karasa warwarewa". Suna zaune a falo mami ta tasa gaba da tambaya" wai Zainab meke damunki ne kwanan baya Sadiq yaki fada min komai yace tunda kin warke shikenan"?. Kuka Zainab keyi tana kallon mami tace" mami Allah neyai ba gawata zakije ki tarar ba da sauran kwana na a gaba". "Eh meya faru"?. Cigaba Zainab tai "mami wannan shegiyar yarinyar yar kauyen nan wai ta shigo birni ta waye itace ta zuba min guba a abinci naci bansani ba". Zaro ido mami tai "guba ta baki wato kashe ki take sonyi ta zauna ita kadai a gidan ko aiko bata isa ba koda uwar ta take yawo tashi muje yau saita gane kuren ta". Mikewa Zainab tai tana dauko mayafi suka fita ko driver daya zo mami tace bata bukata da kanta tai tukin zuwa gidan. Suna shiga ganin bata palor yasa mami shiga part dinta dama tana wuya da ita akan dawowa gidan da Afeeyah tai gashi alhaji yace bazata koma ba sai Al'ameen ya dawo. Afeeyah bata nan ta tafi makaranta ita kadaice tana gado a kwance sakamakon kanta dake mata ciwo. Mami ta banka kofar da karfi ta shiga ganinta kwance tana bacci yasa ta yaye bargon tana sakar mata wani zazzafan duka tace. "Tashi matsiyaciya kin samu guri wato kura ta mutu ko"? To baki isa ba gata ta dawo". A firgice Fati ta farka cikin magagin bacci ganin wacce ke tsaye a kanta yasa ta wartsake a zabure tace. "Mami kece"? Sannu da zuwa". Cikin tsawa mami tace sannu da zuwan ubanki munafika annamimiya mai hana zaman lafiya yau sai naci uwarki a gidan nan". Mamaki ne ya kama Fati muryarta na rawa tace" mami meya faru wani abu na miki"?. 'Dauketa da mari mami tai a fusace ta fincikota ta soma janta tana cewa "uban maye baki ba ni kike tambaya me kika min zaki gane kurenki yau saikin gwammace mutuwa da rayuwa". Tana zuwa palor da ita ta kifa ta tana kallon Zainab tace "me kike jira fara abinda ya kawo mu ki lakada mata dukan mutuwa". Kanta Zainab tai tana tirmishe ta da dukkan karfinta ta rufe ta da duka ta ko'ina mami na tsaye tana kallo. Dakyar Fati ta samu ta fisge da gudu ta fita daga palon yayin da suka rufa mata baya " Daidai me gadi ya budewa Al'ameen kofa ya shigo Zainab ta shake wuyan Fati'. Ko kashe motar baiyi ba ya fito Afeeyah ma dawowarta kenan taga abinda ke faruwa cikin sauri ta kira daddy da kukanta ta sanar dashi". Hankali tashe Al'ameen ya nufi inda suke yana zuwa wani gigitaccen mari ya sakarwa Zainab wanda azaba tasa da sauri ta saki wuyan Fati tana dafe kunci ta zunduma ihu. Cikin bacin rai yake kallon mami wacce ke aika masa da sakon harara yace". "Mami me kenan kika aikata haka kina kallo a gabanki wannan jakar yarinyar zatai kisa". Wani razanannan kallon 'kiyayya mami kebin Fati dashi tace" ga babbar jaka nan a gabanka mara tarbiyya ita da yake goyon bayanta kake datai nufin kasheta ta zuba mata guba cikin abinci ai baka kula ba". "Itance ta zubawa Zainab guba cikin abinci"?. "Eh ita din karya akai mata"?. Kallon Zainab yai cikin bacin rai yace" ke kuma kinyi sanadin aurenki na sake ki" sannan ya juya gurin mami datai mutuwar tsaye yace. "Kenan mami shine dalilin da yasa kika sakota a gaba tazo tadau fansa bayan bakisan komai game da hakan ba bata da lafiya yanzu da kikasa take dukanta idan ta kashe mata d'a a ciki fa"?.= " 'Da kuma kana nufin ciki ne da ita kome"? mami ta fada tana dafe kirji idonta kamar zasu fito waje Bai tanka ba sai hannu daya rikewa Fati zaibar gurin da ita kukan kura mami tai tana fisgo ta tace. "Wallahi karya ne baki isa ki haifa min jika ba yau saina 'barar da cikin nan". Duka ta sakar mata a ciki harda naushi wanda Fati ta saki 'kara tana faduwa kasa. Daidai shigowar daddy a rude Al'ameen ya durkusa yana dagota kuka Fati keyi sosai ta rike cikin ta. Al'ameen na ganin daddy ya mike da sauri ya rungume shi cikin kunar rai da radadin abinda mamin ta aikata yace. "Daddy mami ta kashe min d'ana ina son baby na amma ta raba ni dashi". Cikin nutsuwa daddy yace" Al'ameen ka saurar..... Shiru yai jin Al'ameen ya tafi luuuu zai fadi yasa yai saurin tare shi yana dago fuskarsa ganin suma yai ya cewa Afeeyah maza ta dauko masa ruwa. Da gudu Afeeyah ta shiga cikin gidan Kasa magana daddy yai tsabar tsananin fushi sai kallo me ma'anoni da yakewa mami wacce ke tsaye gefe duk ta rikice. Ruwan Afeeyah ta kawo masa ya shashshafa masa sannan ya kira Sadiq cewa ya turo motar asibiti guda daya. Harda Sadiq din aka zo ganin haka harda mami a gidan ga Zainab tana kuka yasan ba kalau ba. Sa Al'ameen sukai a mota Afeeyah kuma da Fati suka shiga motar daddy suna fita daga gidan aka bar iya mami da Zainab tsaye'. Dora hannu Zainab tai aka tana rusa kuka tace "na shiga uku shikenan mami Al'ameen ya sakeni wallahi ina sonsa". Tabe baki mami tai ke kada ki wani damu tunda kindau fansa ga kuma na kashe shege ko shegiyar yarinyar dake cikinta ai komai yayi duk wani mataki da zasu dauka aikin banza ne burina ya cika bazan ma koma gida ba yau saboda alhaji yadau fushi bansan mezai faru ba muje gurin Binta" mota suka shiga suma suka bar gidan. Sosai Sadiq ya duba Fati duk abinda ya dace ya mata kuma Alhamdulillahi babu abinda ya samu babyn. Sosai daddy da Afeeyah sukai murnar jin haka kuma suka godewa Allah. Kwanan mami uku a gidansu Zainab bata koma ba saboda tsoron haduwarta da daddy saiyau ta shirya taje asibiti gano Al'ameen. Tana shiga dakin ta ganshi a zaune fati na gefenshi wata uwar harara ta wurga mata tana cewa. "To sarkin kinibibi mahaifiyarsa tazo saiki fita ki bamu guri zanyi magana dashi kinzo kin gurbata mana zama kin zama ba'kar ashana fita nace me idanun mayu kosai kin lashe min tawa kuruwar nima kamar yadda kika lashe tasa mayya kawai". ? Mikewa Fati tai cikin takaicin maganganun da mami ke fada mata ta fita waje tana share hawaye haduwa sukai da Sadiq ganin tana kuka yace. "Zarah lafiya ina zakije ko wani abune ya samu Al'ameen din"?. Kaita girgiza" babu komai gida zan tafi". "Amma Zarah meyasa? ki bari sai dare mana". "Mami tazo itace zata wuni a wajensa". Kallon tsaf Sadiq ya mata haba shiyasa take kuka yasan da dalili. "Ok muje na kaiki to"fita sukai domin ya mayar da ita yana kuma sake bata hakuri. Page 35 to 36. Fati na palor a zaune bayan Sadiq ya ajiyeta ita kadai tai shiru ta nutsa cikin tunani da mamakin wacce irin 'kiyayya mami ke mata abin ya wuce ma hankalinta. Jin karar bude kofa yasa ta dago mami ta gani ta shigo jikinta ne ya soma rawa kamar taga hallaka. Zama mami tai tana kallonta fuska babu wasa tace" ba wata tsiyar ta kawo niba na baki minti biyu ki shiga ki tattaro kayan daud'ar ki kibar gidann nan yadda kikai silar fitar Zainab to kema ya zama haramiyarki saidai ya auro wata yasa". Hawaye suka gangarowa Fati da sauri ta goge tana juyawa ta shiga part dinta bata dade ba ta fito mami na zaune tana kad'a kafa ganin ta fito yasa ta mike tana sakata gaba da, tsinuwa suka fita harabar gidan. Karbe key din gidan tai a hannun Fati sannan taiwa driver umarni cewa. "Ga wannan bagidajiyar ta nuna maka hanyar kauyensu ka mayar da ita yau sai kwanan tabarma cikin 'kunci da zafi ba a.c sai ai ta fama da mafici daula kinyi bankwana da, ita". Tana gama fadin haka ta shige motarta ta fice daga gidan Fati na kuka ta shiga mota bangare guda tana farin cikin barin masifar mami datai. A ranar Al'ameen yabar asibitin Sadiq ne ya kaishi har gida sannan daya huta ya tafi nasa gidan. Karfe goma daidai Al'ameen yace zai tafi gidansa tari mami batai masa ba balle ta nuna masa cewa ta koreta. Tana kallonsa ya fice daga palon dariya tai tana cewa "hummm yaro man kaza ai kaida wannan shegiyar yarinyar har abada je ka dawo ina daidai dakai saika saketa". Kamar an jefo Al'ameen haka mami ta ganshi murmushi tai tana dauke kanta daga saitinsa tace "a'a me kuma ya dawo dakai"?. "Mami ina Zarah"?. "Tambaye nidai baba tunda ajiyarta ka bani". "Mami I know what u have done to my wife na roke ki daki fada min inda take me kikai mata". "Ban sani ba zo ka rufe ni da duka saina fada maka inda na kaita". "Dan Allah mami mubar wannan maganar ina key din gida na"?. cikin gadara mami dake zaune tasa glass da laptop gabanta tana aiki tace". "Wanne gida kake dashi daya wuce nan ai daga yau ka dawo gidan ku da zama zansa a gyara maka part dinka gobe". "Meyasa mami bayan ga gida nacan da matata taya zan barta ita kadai na dawo nan". "Allah ko sannu me mata karka batawa kanka lokaci na kora ta garinsu". Wata irin juyowa Al'ameen yai yana kallon mami cikin tsananin mamaki yace mami kin kora ta garinsu saboda me"?. "To babana matse ni saina fada maka dalili kuma ban yafe maka idan kaje wannan matsiyacin kauyen balle kace zaka dawo da ita yadda ka ci mutuncin Zainab ka wulakanta ta ka saketa haka itama nake so ka rubuta mata takardar saki uku ba maganar kome saidai ka auro wata". Wata iriyar hajijiya ce ta debi Al'ameen da sauri ya zauna tare da dafe kanshi maida hankalinta mami tai akan aikin da take tana cewa". "Kome zakai saika saketa bazan taba daukarta matsayin suruka taba". Jin tafiya yasa ta dago ganin daddy ne tadan zaro ido tana fatan Allah yasa baiji zancen da suke da Al'ameen ba. Shi kuwa ya riga ya gama jin komai muryarta nadan rawar rashin gaskiya domin tun ranar da ta daki Fati basu sake haduwa dashi ba saiyau tace. "Sannu alhaji". Banza yai da ita ya dauke mata wuta kamar baiji ba ya karasa inda Al'ameen ke zaune yana dago kansa. Ganin hawaye a fuskarsa abinda ya manta yaushe rabon daya gani tun yana yaro saiyau cikin tsananin bacin rai da fushi ya juyo inda mami take yana kallonta yace. "Yau tafaru ta kare Aisha kullum ina miki gargadi dajan kunne bakya dauka to yau zakiga sakamakon abubuwan da kike aikata min". Part dinsa ya shiga mintuna biyu ya fito da takarda a hannunshi yana cilla mata cikin kakkausar murya yace". "Ita kin bata minti biyu ni kuma minti daya na baki kada ki kuskura na fito na sameki kibar min gida na". Mikar da Al'ameen yai yana shigar dashi part dinsa sannan ya fito ganinta zaune tana kuka yasa yace ki fita a gidan ko a hanya sai kiyi domin na gaji da ganinki". Cikin kuka mami tace alhaji kayi hakuri bazan sakeba na tuba". Kai ya girgiza ai Aisha bazan iya sake zama dake ba kina lalata min zumunci da hana zaman lafiya ya zaga ahli na". "Wallahi alhaji kaban dama na karshe zan gyara hali na tun muna kuruciya banje gidan mu da sunan yaji ba saiyau naje da takardar saki wannan abun kunya har ina alhaji ka dubeni". "Ai Aisha abinda ya dace dake na baki hukuncin ki kenan". "Kayi hakuri kamin sutura alhaji zan gyara kuskure na namaka alkawari". "Aisha bazan miki uziri ba a yanzu rayuwa ta bata bukatar ki na datse duk wata alaka dake tsakanin mu"'. Cikin kalar tausayi mami ta durkusa gabansa tana masa magiya amma sam ya dauke kai daga saitin ta. Mikewa tai ganin babu alamar zai karbi bada hakurinta tana kallonsa tace" na baka hakuri amma alhaji ka 'ki.............. Katse ta yai "ki barmin gidana bana son jin komai daga gare ki" bar mata falon yai . Dole mami tahau tattara kayanta kamar yadda taiwa wata itama ta nufi gidansu cikin bakin ciki da kunyar yadda zata fuskanci mahaifanta. Ranar kwana cur mami tai a zaune bata ko runtsa ba tana kuka har zazzabi da ciwon kai suka rufeta. Washe gari ma haka ta wuni rim a kwance babu cin abinci babu shan ruwa ga fadan da tasha gurin dattijon mahaifinta. Nadama iri iri babu wacce mami batai ba da dana sani domin a rayuwarta tana matukar son daddy kamar ranta. Fati na zaune a kofar dakinsu tana gyarawa umman ta waken da za'ai abincin rana Saude ta fito daga dakin ganin Fati zaune yasa tace. "Humm yan birni har dubun naku ta cika asirin da kukai musu ya karye ko kuma kinyi halin 'bera sun fatattako ki ko"?. "Meye gaskiyar al'amarin fada min gashi zaki abin kunya ki haihu a gida tir da wannan abu ina tausaya miki domin zilamar uwarki dason zuciyarta ne ya jawo miki". "Koma dai ba cikinsa bane shiyasa suka koro ki iye fada min naji domin yadda idonki yake a tsayen nan zaki iya aikata komai maganin son banzar ku kenan kunga kudi shine kuka rude saida kuka shiga jikinsu ai dama duk wanda yahau motar kwad'ayi yasan baida gurin sauka sai tashar wulakanci". "Kiyi addu'a kada ki haihu su 'ki karbar d'an yan kauyen nan su samu abin gori kI shafawa danginku ba'kin fenti". "Koda yake nasan me za'ayi zan taimake ki na karbo miki magani kawai kisha d'an ya mutu ko idan kin haifeshi ki sha'ke masa wuya bada sanin kowa ba kinji zan rufa miki asiri babu wanda zai sani amma kudin da kika sato musu daga can zamu raba idan kin yarda"?. Ko dagowa Fati batai ta kalli Saude ba balle tayi tunanin zata bata, amsa kawai aikinta take". Tsaki Saude tai ke dalla gafara don ma za'ai miki sutura shine kike min wani gani gani wato ke uwar dabaa lamba d'aya ko"?. "Aiko kin shiga uku a gurina dan saina zaga kauyen nan na sanar dasu kinyo cikin shege a birni". " ta fada tana saka hijab tare da rufo dakinta tai hanyar waje tana cewa" bari na fara daga makotan mu su tabawa da Aliyah" da kallo Fati ta bita tana share hawayen daya zubo mata". Shigowar Salamatu ganinta haka yasa ta tambayeta" Fatima lafiya kike kuka? kiyi hakuri kaddararki kenan ki dage da addu'a babu abunda ya gagari ubangiji shine mai bayarwa,". Kukan Fati ne ya fito fili cikin damuwa tace "umma ba laifin Al'ameen bane baisan ma na taho ba yana asibiti mami ce ta min komai". "Duk da haka kinga ki kwantar da hankali komai yai farko wata rana zaiyi karshe idan Al'ameen mijin zaman kine zaki koma". Kai Fati ta girgiza tace "nifa umma wannan ba shine matsala taba damuwa baba Saude yanzu tasa hijab ta fita wai seta zagaye garin nan tace ba wani aure danai cikin shege ne". Kirji Salamatu ta dafe tana kallo Fati tace" ita Sauden ce tace haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah gamu gareka kaine gatan mu". Fati data sauke ajiyar zuciya tace" amma umma ya kamata a dakatar da ita kinsan halin kauyen nan da kama abu ina tsoron sharrin su". "Ya zamuyi Fatima waye zai iya dakatar da ita baban kune kuma baya nan sharrinta bazai tasiri ba domin muna da gaskiya ita kuma 'karyarta koda tayi fure bazatai 'ya'ya ba dan 'karya 'karya ce koda an lullubeta da sutura". "Shikenan umma zan dage da addu'a Allah ya saukaka min abinda ke damu na yasa karshen wahala ta kenan". "Yauwa Fatima haka nake son ji Allah ya miki albarka ya had'a ki da abinda zai zamo alkairi a rayuwarki". "Ameen umma nagode da addu'arki da kyakkyawan fatan ki gareni" Fati ta fada cikin jin dadi. Page 37 to 38 Bayan wata d'aya Mami na zaune a daki ta zuba uban tagumi naban tausayi ta rame tayi duhu saboda damuwa da rashin kwanciyar hankali. Sallama wata mace tai tana cire nikaf din fuskarta ta zauna kusa da mami tana kallon ta tace . "Haba Aisha kina rage yawan wannan tunanin da kike saikin dorawa kanki hawan jini garin wanke biyar a 'bata goma". Numfashi me zafi mami ta fitar tana kallon 'kawar ta tace "humm Halima hawan jini kuma na nawa zai hauni saidai nasha magani taya damuwa ta zata kare alhaji ya'ki karbar bada hakuri na". "Aisha kina ji ki kwantar da hankalinki Mustapha mutun ne me hakuri may be bango kika kaishi yadau zafi dake haka amma idan ya huce komai zai dawo daidai". Jiki a, sanyaye mami tace "yanzu ba wannan ba da kikaje ya kukai dashi kinga alamar ya fara saukowa daga fushin da yake dani"?. Kai Halima ta girgiza tace ""gaskiya ko fuskar da zamuyi maganar arziki ban samu ba karshe ma securities ne yasa suka fitar dani daga office din a wulakance kamar wacce naje maula". "Amma nashiga uku Halima indai alhaji bai hakuri ya mayar dani ba banajin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare dashi ba domin ina sonsa". Gyara zama Halima tai "a'a karki ce haka ki sa a ranki zai hakura ya mayar dake amma dan Allah ki rage yawan damuwar nan zan sake komawa gurinsa nan da kwana biyu". "Shikenan Halima na gode Allah ya saka miki da alkairi gaskiya ke 'kawa ta gari ce". Daddy kam iya bango mami ta kaishi yama rufe babinta a rayuwarshi ya manta da wanzuwarta balle yai tunanin dawo da ita gidansa aiyukan sa kawai yasa gaba. Wannan hakan dayai na nuna halin ko'in kula ba karamin tsorata mami yai ba ya firgita mata kwakwalwa ya ruda mata tunani ya juyar mata da hankalinta". Har ciwo ya kama ta an kaita asibiti Sadiq na kula da ita sosai haka Al'ameen da Afeeyah kullum suna gurinta domin duk lalacewar uwa uwace. Sunyi matukar damuwa da ciwonta daddy ya sani amma yayi banza ya nuna ko a jikinsa ita yanzu ba matarsa bace bata da wani nauyi akansa. Haka ta 'karaci jinyarta ta shafe satika harta warke baiko le'ka asibitin da sunan ya dubata ba tayi kukan nadama da dana sani harta gaji. Ganin halin da take ciki da yake mahaifinta mutum ne me hikima dattijon kirki me aiki da hankali da tunani ya kira daddy har gida. Dole daddy yazo saboda yana matukar girmama tsohon yana ganin darajarsa cikin dabara da basira baba Ibrahim ya tarbi daddy da magana me dad'i. Cikin fara'a dason gyara musu al'amarinsu ya soma tambayar daddy da kuma lafazi me kyau yake bashi hakuri da nuna bacin ransa akan halayyar mami. Sannan ya kira ta yai mugun sa'ba mata ya kuma ce lallai ta aikata babban zunubi ta bawa daddy hakuri. "Dama abinda take nema kenan wata silar daidaituwar su tazo dan haka da taga ta samu dama haka ta dage da kukanta sosai ta rika bashi hakuri da rantsuwar baza ta 'kara ba. Saboda kunyar baba Ibrahim daddy ya karbi daba hakuri domin badan darajar saba shida Aisha saidai idan zance ya tashi tace da ta aure shi. A ranar saboda zumudi mami taso binsa ta koma yace a'a sai satin sama zai turo driver yazo ya dauketa bataso hakan ba amma zuciyarta mamaye take da farin ciki. Satin nan jinsa take kamar shekara ko baccin kirki batayi saidai tunanin daddy da mafarki komawa gidansa. Lalle da kitso mekyau taje aka tsara mata tai fes da ita tasha sabon dandakeken dinki tayi kwalliya fada sosai baba Ibrahim ya sake mata sannan ta fito 'kawayenta biyu zasu rakata. Halima da hajiya Maryama sai tsiya suke mata a mota har suka je gidan zama sukai saida daddy ya shigo sannan suka tafi. Suna fita mami ta diro daga kan gado tana durkusawa a gaban daddy dake tsaye tare da rike kafafunsa hawaye na zuba a idonta ta soma magana. "Alhaji dan girman Allah ka yafe min abinda nai maka nasan kayi hakuri da halina ina rokon ka kada ka gajiya nayi kuskure amma yanzu zan gyara ka yafe ni". Daddy baiyi magana ba sai kallonta da yake ganin irin kallon da yake mata kuma bai tanka ba taci gaba domin tana son goge laifinta". "Alhaji ka bani dama a karo na karshe ni kuma nayi maka alkawari zan gyara abubuwan dana 'bata maka fushinka a kaina barazana ce ga rayuwata ka yarda dani wallahi ina sonka kuma ina son ahlin ka na tuba kayi hakuri dan Allah". Ta karasa maganar tana fashewa da kuka ganin har lokacin kallonta yake kila bai gamsu da abinda tace masa ba'. Allah sarki zuciyar musulunci d'agota daddy yai daga durkushen da take saboda kada kafafunta suyi ciwo yana mikar da ita tsaye ya goge mata hawayen😉😜. Muryarsa a daidai yace "shikenan Aisha ya wuce Allah ya yafe mana baki daya". 👉 39 to 40 Washe gari da safe suna zaune a palor Afeeyah ta fito da saurinta suna gaisawa tai hanyar fita. Mami data bita da kallon yaushe rabo tace "Wai Afeeyah baki ganni bane ina zuwa haka? maimakon ki zauna mu wuni". "Dan juyowa Afeeyah tai tana cewa "am mami kiyi hakuri saina dawo sauri nake domin mun fara jarrabawa". "Ok shikenan to saikin dawo Allah ya bada sa'a". "Amin Afeeyah tace tana fita. Al'ameen dake kusa da Sadiq cikin tsokana yace" ni kuwa daddy ya batun auntyn nawa naji shiru har yanzu"?. Cikin mamaki daddy yace "wacce irin aunty kuma kake nufi"?. Kamar gaske Al'ameen ya gyara zama yana cewa "daddy aunty na mana dama gurinta zakaje ran nan amma bakace nazo nai maka rakiya ba"'. Da sabon mamaki daddy ke kallonshi amma ganin yana kallon mami yasa ya fahimci tsokanar mamin yake. Dan murmushi daddy yai yana mazewa kamar gaske yace" ayya sorry sorry Aminullahi auntyn ka tana lafiya ko jiya da mukai waya da ita tace na gaishe mata da autan ta". Baki Sadiq ya bude yana kallonsu Al'ameen yaci gaba "daddy yaushe ne auren fatan an kusa domin nine zan mana anko mami wanne kallar atamfa ko less kike so"'. Mami dake kallon Al'ameen jin shine me maganar a kara mata kishiya dukda tasan laifin tane itace tai sake jitai hawaye zasu zubo mata da sauri ta mayar dasu tana mikewa tabar palaon. Daddy dahar lokacin yake murmushi yace "wato Al'ameen ashe kaima 'kafar baya ne😁? gashi kasa maminka kishinta ya motsa zatai kuka". "To ai daddy dama nasan haka zata faru kishin nata nake son gani dama manya ma suna kishi akan tsohon mijins............. Rufe baki yai yana kallon daddy yace "sorry daddy ina nufin soyayya tsohuwar zuma tafi". Kai daddy ya girgiza yana mikewa zai fita yace "Allah ya shirya min kai auta na nabiye maka kasa mata ta kuka". Daddy na fita Sadiq kamar ana tsikarin shi yace" kai daddy dama aure zaiyi ban sani ba a ina ya samu lady"?. Dariya ce ta kama Al'ameen yace "wato kaima kayi zaton da gaske ne ba wata lady dazai aura kawai shiri nane mami nake tsokana"'. Sadiq yace "koda naji nidai nayi mamaki yanzu dai muje kamin rakiya yau tunda kana hutu" mikewa yai suka fita'. Da dare lokacin da daddy ya dawo ganin Afeeyah a palor ya tambayeta. "Daughter ina maminki"?. Dagowa Afeeyah tai tana cewa "sannu da zuwa daddy mami tana part dinta batajin dadi zazzabi ke damunta". "Ok bari muga" wucewa yai zuwa part dinta kwance ya sameta lullube da bargo yaye mata rufin yai yana kunna hasken dakin yace " Aisha". Bude ido mami tai ganin dady tsaye yasa ta tashi zaune tana jingina bayanta da fuskar gadon. Cikin alamar tambaya daddy yace "baki da lafiya"?. Muryar mami na rawa cike da damuwa da tsananin kishi tace "alhaji da gaske ne abinda kunnuwa na sukaji dazu da safe aure zaka kara"?. Kallonta daddy keyi haba yasan zafin kishin mami a kansa tun kafin ya aureta". Mami da zuciyarta tai mata nauyi tace "alhaji kaban lokaci na gyara kuskure na idan kayo aure a wannan halin da muke ciki komai cakude min zaiyi dan Allah karka min kishiya". "Aisha wai waye ya fada miki aure zan karo Al'ameen tsokanarki kawai yake amma ni banida ra'ayin zama da mata biyu karki damu komai ya wuce". Sauke ajiyar zuciya mami tai tana cewa "amma sai naci 'kaniyar Al'ameen wato kakarsa ya mayar dani🙄". "A'a karki taba min auta na babu ruwanki dashi idan ba haka ba muhau sama mu fad'o". Dariya mami tai tana cewa "shikenan tunda abin son kaine". Dan shiru tai kamar mai tunani zuwa can tace "alhaji gobe zanje garin ku". Da mamaki sosai a fuskarsa yace" wai kina nufin kauye na"?. "Eh ina son na gyara mu'amala ta da kowa sannan yarinyar nan Fatima nadau hakkinta zan bata hakuri kuma na taho da ita ta dawo dakin mijinta ta haihu". "Dakyau Aisha kin kyauta kuma naji dadi na gode idan kinje da kwana biyu zamu biyo bayanki". Kai mami ta jinjina tace "ina son atamfofi da kayan abinci na tafi dasu". "Ok yayi zansa a kawo miki komai da kike bukata". Page 41 to 42. Washe gari haka mami tai sammako kamar kasar zata bari dan zumudi ba daddy ba hatta su Afeeyah mamaki ne ya kamasu. Lokaci da mami taje Fati ta fara nema amma bata gidan taje wuni gidan kakannin ta na uwa. Data dawo Salamatu ta sanar da ita mami na nemanta mamaki ne ya kamata amma tai burus bataje ba domin babu abinda zatai mata ko tace mata. Kwanan mami biyu tana bin Fati tazo zasui magana amma harsu daddy suka zo garin Fati bata yarda sun hadu ba". Gidan hajiya ma ta koma da zama gabadaya saboda bata son ganin mami. Da kuka mami ta fadawa daddy Fati ta'ki sauraronta kwantar mata da hankali yai ta hanyar cewa zata hakura saita huce. Su Sadiq na gidan hajiya sai jikin magriba Al'ameen da Fati suka fito saidai shima taki warewa ta masa magana wai tunda tazo gida bai biyo bayanta ba. Ta danyi tafiya mai nisa ta waiga ta gano shi acan baya saitin dabar samarin anguwarsu yayi kneel down, komawa tai tana cewa "ka taso mana mutane fa suna kallon mu". Komawa kalar tausayi yai yana miko mata hannu yace "bazan tashi ba saikin daga ni da kanki". Zaro ido tai tana kallon yadda mutane suka zuro musu ido tace ",nidai ka tashi kona tafi". "Allah Zarah bazan tashi ba saidai ki daga ni". Ganin an kira sallah idan ta biyeshi zasu 'bata lokaci yasa dole ta mika masa hannu rikewa yai yana murmushi ya mike tsaya yana manna mata kiss yace. "I love u my wife". Kunya ce ta kamata tana kokarin zamewa daga jikinsa yaki sakinta ya rike mata hannu ya fara tafiya da ita dole ta bishi har cikin gidansu bai saketa ba saida yaji muryar ummanta. Bayan sallar isha daddy yai kiran Fati dasu salamatu ya musu bayanin komai ya kuma basu hakuri. Mami harda kukanta ta rike hannun Fati tana bata hakuri da mata magiya abinda bata taba yiba". Saboda daddy da kuma Al'ameen yasa tilas Fati tai hakuri ta yafe mata jin daddy yace idan zasu tafi tare da Fati zasu wuce ta koma dakin mijinta. Mikewa Fati tai tana kuka ta fita haduwa sukai da Al'ameen ganin tana kuka yasa ya riketa yana yin bangaren muntari baban su da ita. Har daki yana goge mata hawayen yace "meke damunki"?. Kaita girgiza tana cewa babu komai". "Amma kike kuka? fada min damuwarki". Ganin ya zauna yasa tace "ka zauna akan gadon baban mu"?. Gira ya dage "eh madam to mene a ciki"?. "Amma dai gadon surukin kane". "To Zarah surukin nawa ba ubana bane"?. "Duk da haka". "Ok yayi to zo mu kwanta bacci nake ji". Zaro ido tai "anan din? gaskiya a'a bazan kwana anan ba". Juyawa tai zata fita ya dauketa yana dorata akan gadon yace "wannan daga baya kenan kwana kam sai kinyi". Zatai magana ya rufe mata baki da nasa yana bata kiss mai d'umi wanda yasata sauke ajiyar zuciya. Zuge zip din doguwar rigarta yana zura hannunsa ciki da sauri Fati ta kankameshi tana kwantar da kanta akan kirjinsa". Da yake cikinta ya riga ya tsufa saita dabara yadan karkata ta ta gefe ya shigeta yana binta a hankali sakamakon yanayinta. Page 43 to 44. Washe gari tun kafin asuba tayi ya tasheta suka shirya anayin sallah suka wuce Abuja. Da safe kowa yana zuba idon yaga ta inda zasu bullo amma shiru Sadiq daya shigo jin ana cewa ko suna gidan hajiya. Yace ai yanzu kam Al'ameen yana Abuja domin gida suka tafi shida Zarah motarsa bata nan" mamaki ne ya kama kowa ganin basuyi sallama ba. Kwana biyu da tafiyarsu daddy ma suka bi bayansu a ranar da suka koma suka tarar Fati na asibiti. Dukka asibitin sukaje a lokacin Fati harta haihu ansamu baby boy farin ciki kamar basu taba jika ba sai akansa mami har mamaki ta bawa kowa ganin yadda take rawar jiki. Da aka sallameta gida mami ta wuce da ita domin ta bata kulawa Afeeyah kam tana tare da babyn. Kulawa sosai mami take bata kuma kusan kullum saita nemi yafiyarta bisa abinda tai mata tayi kas dakai ta bata hakuri, Fati kuma tana nuna mata cewa babu komai ya wuce ita mahaifiya ce a gareta. Ranar suna baby yaci suna LABEEB sunan abokin Al'ameen wanda sukai makaranta tare. Zainab na shigowa gidan da yake tunda ya saketa bata gari tana zuwa ta rungume mami tana kuka. Cikin mamaki mami tace "ke lafiya kukaan me kike". Zainab bata iya dakatar da kukan da take ba ta rike hannun mami tana cewa "mami da gaske ne abinda nake ji wannan yar kauyen ce ta haihu tare da Al'ameen ko mafarki nake kunne na baiji daidai ba"?. Mami tace "wanne irin mafarki kuma Zainab? Bayan gashi kinga zahiri Allah ya azurta Al'ameen da samun d'a namiji ya sanya masa sunan abokin sa Labeeb". A rude Zainab tace "dan Allah mami kisa baki ya mayar dani dakina wallahi zamuyi zaman lafiya nayi nadama ina son Al'ameen". Kai mami ta girgiza "a'a Zainab da dayanzu ba daya bane kada kije ki sake gurbata musu zaman su Fatima Zarah ce ta dace da Al'ameen". "Nima na dace dashi mami kalli ki gani ya zauna da yar kauye ma balle ni tashin birni nasan komai". "Ai Zainab da kikasan komai sanin naki baiyi amfani ba tunda kika samu damar zama dashi bakija hankalinsa ba yanzu kam saidai nace kiyi hakuri duk abinda zai takura rayuwar Al'ameen bana kaunarsa". "Mami me kike nufi kenan na hakura dashi"?. "Eh abinda nake nufi kenan ki barshi yai rayuwa da matarsa itace za'binsa domin wancan karon ma nice na tursasa masa baya so amma yamin biyayya dole ya aure ki nayi tunanin kece kika dace dashi ashe abin ba haka bane kawai kiyi hakuri ki kaddara iya bakin rabon zaman ku kenan ki samu miji kema kiyi aure". "Mami na hakura dashi fa kika ce? Tabdijan wallahi bazan iya ba shi nake so dole kisa ya maida ni". "Dan ubanki koke maiya ce bazaki koma gidan Al'ameen ba kinji na fada miki" Hannu Zainab ta dora aka tana kuka ta fita daga bedroom din mami. Tsaki mami taja "jimin shashashar yarinya da dinma kuskure ne da tsautsayin nima za'a sakeni yasa na nace ya aure ki yanzu kuma tayi kai keda Al'ameen saidai zumunci". Wata hudu da haihuwar Fati akai bikin Afeeyah ,wanda Zainab tayi bi da nacin Al'ameen ya mayar da ita tayi kamun kafa tayi kuka da magiya yace bazai iya ba dole ta hakura ta auri d'an gidan abokin babanta". 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Bayan shekara shida😉🌹 wani yaro ne tsaye a harabar wani tabkeken gida sai bubbuda fulawoyi yake daya bayan daya me gadi dake zaune dan dattijo yana murmushi yace" Labeeb". Juyowa yai yana kallonsa da hannu ya nuna masa wata babbar flower mai blue da farin fure. Da gudu yaje ya buda saiga Al'ameen ya fito dariya Labeeb yai yana rungume shi wanda Al'ameen ya cira shi sama yana murmushi. Al'ameen na dire shi ya kuma sake d'afe shi yana yada teddyn hannunsa 'kin daukarsa Al'ameen yai nan suka fara zaga harabar gidan Labeeb na cewa saiya kamashi". Fati dake palor da cikinta da tudunsa ya fara fitowa jin hayaniyarsu ta dameta yasa ta mike tana fita harabar gidan ganin abinda suke yasa tace. "daddyn Labeeb I don't want stop you from your playing with your boy but you are disturbing me ku dan rage hayaniya ina son hutawa ne". Kallonta Al'ameen yai ganin yadda ta tsara kwalliyar datai mata kyau yana murmushi ya kalli Labeeb yana cewa "kaji fa boy abinda mum dinka ke cewa je ka cijeta😁". Da gudu Fati ta juya ciki jin abinda yace shima Labeeb bayanta yabi murmushi Al'ameen yai jin ihunta yasa ya shiga palon'. dariya ce ta kamashi ganin yadda suke kokawa da boy gashi ya bude baki alamar cizo . Zuwa yai ya dauke shi yana cewa "boy mum dinka raguwa ce kalli yadda kasa take gumi bari muzo mubar, mata gidan mu tafi yawo gurin grand-mah dinka". Labeeb yace "daddy zanga Minal (yar gidan Sadiq ce shekararta uku Afeeyah ma nada 'ya Ni'imah)"?. "Eh my boy zaka ganta". Cikin murna yace "to daddy ka ara min kudi nasai mata chocolate irin wacce kake saya min nakai mata". Zaro ido Fati tai jimin yaro da zarar magana idan ka ari kudin a ina zaka samu ka biya"?. Murmushi Al'ameen yai yana kissing forehead din Labeeb yace" that my boy wannan gaskiya ne haka nake so kyan d'a ya gaji ubansa boy dina dan soyayya ne shiryashi muje yaga sahibarsa". Mikewa Fati tai tana rike hannunsa suka shiga bedroom ta mai wanka da shiri ya fito dan gaye. Harda ita suka wuce gidansu mami ranar Afeeyah tazo su Rukayyah sunzo Family ya taru'. Suna zaune ana hira cikin annashuwa Labeeb dake kusa da mami yace "grand-mah nifa zance nazo". Daukarsa mami tana dorashi akan cinya tace" au saurayi na ashe zance kazo gurina ban sani ba"?. Yadda Labeeb yai da fuskarsa kamar faten dankali😕 saida kowa yai dariya a gurin sauka yai daga kan cinyarta yana cewa . "Nifa ba keba Minal". "Oh ita kake so kenan ni ka sani a kwandan shara dan kaga ni tsohuwa"?. Turo baki Labeeb yai "to grand-mah kema baga grand-fa nan ba"?. "A'a ni kai nake so daddy aiya tsufa". Kuka Labeeb ya fara yana cewa "wallahi ni Minal nake so ba keba". Dariya suka rika yi masa domin duk lokacin da yazo haka suke shan drama da mami har dare suna gidan sai wajen karfe goma kowa yai sallama ya nufi gidansa. Labeeb yai bacci amma dole saida Al'ameen ya tashe shi ya masa wanka sannan yasa masa sleeping dress ya kwantar dashi. Fati na tsaye gaban mirror tana tattare gashinta taji anyi sama da ita murmushi tai tana sa'kalo hannunta ta wuyansa tace. "Soulmate yaufa bacci nake ji sosai". Sauketa yai akan gado yana hade kirjinsu cikin dauke gira yace "nima baccin nake ji madam". Ya 'karasa maganar yana zame ribom din data fara daure gashinta dashi yana kissing wuyanta jin hannunsa cikin rigar baccinta yasa zatai, magana. Ya dora bakinsa akan nata cikin salo yake binta ga'ba-ga'ba sauke nannauyan numfashi tai tana rungumeshi idanuwanta a lumshe muryarta can kasa tace. "I love you soulmate". Al'ameen dake shafa breast dinta shima cikin yanayin jin dadin kasantuwarsu tare yace. "I love u too my heartbeat no one but u". Yana gama fadin haka yai addu'a yana danna joystick dinsa cikin jikinta wanda lokaci guda suka 'kan'kame juna cikin yanayin farin ciki da nuna zallar kauna da soyayya🤗". #ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH#. #ALHAMDULILLAH# 👏 Ya rabbi salli ala sahibul-mu'kami annabin da mai so nasa bai zama a hammi sa alihi da sahabbansa zul-kirami a'alal ula duk ma'kiyin sa ya makanta. 😘 MRS AL'AMEEN AHMAD CE. Godiya sosai gareku masoya. 👉 Zarah Musa dan adam 👉Safiyyah Aliyu wakili 👉Naja'at Musa Abubakar 👉Hajara Abdul-khareem 👉Hajara Aminu b/kd 👉Fatima Musa Abubakar 👉Sarah Yakubu 👉Batool Adam Naseer. 👉Zainab b/kd 👉Hafsat maman Aliyu 👉Basirah Muhammad 👉Badariyyah Hassan 👉Ameerah Hassan 👉Aseeyah maman Jabeer 👉Zainab sunusi 👉Saudat Yusuf 👉Salmah Hayat maman Afnan 👉Fatima Idris maman Ousman 👉Khadijat Alhaji Yusuf 👉Khadija Adams 👉Nafisat Mu'awiyyah umar 👉Hauwa Mu'awiyyah umar. YUSRAH MUSA ABUBAKAR. 📚WRITER👇 👑 Yarima Abdul-maleek 🌹 Rayuwa biyu 🍇 Safreeyyah 🎉Haskena Sauban 🎀Minah-Umer 💰 Dan millionaire. ✌️ Husnah ko Badiyat 💕Dama kece 💘 Zuciyar Aliyu 🌃 Royalty. 💖Kowacce 'kwarya 🌹'Dawisu cikin agwagi. 🙏ALLAHUMMA SALLI WA SALLIM ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA JAMI'IL AMBIYA'I WAL MURSALINA WA ALA MALA'IKATUL MUKARRABINA WA ALA IBADALLAHIS SALIHINA MIN AHLIL SAMAWATI WA AHLIL ARDINA WA ALAINA MA'AHUMU AJ MA'INA BI RAHMATIKA YA A ARAHMAN RAHIMINA WA SALLALLAHU ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA ALIHI WA SAHABIHI WA SALLAMAN AJ MA'INA. 🌹 Yusrah Musa Abubakar Mrs Al'ameen Ahmad ce😜 Zanyi kewarku masoya😿 sai rai da nisan kwana ya sake hadamu😭 alhamdulillah kuskuren danai a cikin wannan littafin d'an miloniya ina rokon ubangiji Allah s w t da yamin afuwa fadakarwar dake ciki Allah ya bada ikon yin amfani da aiki da itaa, ameeen. 😉See u next time, 🙏Tnk 4 ur supports 😘Be with me at always 🤗And we will meet again 🎀Domin gyara ko shawara🎀 👉 📱+234 905 527 3614. 🏵❤🔥🏵❤🔥🏵. *Mrs Al'ameen Ahmad ce*.